Compiled by Umar Dalha
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
1
*Dukan yabo da godiya ya tabata ga ubangijin talikai , Wanda bai haifa ba kuma ba'a haifeshi ba , na godewa Allah da ya nuna min karshen novel DINA Duk karyar kada , ina rokonsa da ya bani ikon fara wanan cikin sa'a ya kauceni fadawa halaka dalilinsa, duk wani abin karuwa ya dorani saman sa abin ki ya kauce ni daga shi , wanan novel na kirkiri abina ne ina rokon Allah ya tayani isar da sakon dake cikinsa, masu karatu ina kara Mika sokon gaisuwata da kuma godiyata Allah ya barmu tare, Daukacin jama'ar gidan mu Exclusive Allah ya kara daukaka, marubuta baki daya ina jinjina na gode*
Labari
Kakarin amai take tana jan nunfashinta , ita kuwa ta daneta ta matse mata baki ala Dole sai ta dura mata danyen misan da ta tsinto a cikin bola , MAhaukaciya ce na hango ta dane wata yar budurwa tana kokarin dura mata mushe a bakinta ita kuwa ta gumtse bakin taki budewa , tana tsaka da kokowa da ita sai naga ta dakata , ta ja da baya kuma sai naga ta saka ihu ta shiga shure shure tana dafa cikinta da alama nakuda ce ta taso mata , yarinyar nan naga ta taso da gudu tana ta bibiyar wanan mahaukaciyar tana fadin , sanu haihuwar ce ?
Ita dai Mahaukaciya ba bakin magana banda juya kai ba abinda take hakan yasa yarinyarnan fita da gudu daga cikin tsumakoran da suka saka suka dadaure sukayi dan dakinsu inda zapi , sanyi , damana ke riskarsu , tana FIta tayi ta gudu tana haki da kyar ta samu ta fito cikin layin domin a can cikin bola ne suke can karshen anguwa , tana fitowa ta tsaya tana waige waige ta rasa ina zata dosa domin neman taimako , wani gida ta hango tamkar kango ta nufa domin wani lokacin sunkan sakata kai shara gidansu wato bola , su bata dan kanzo da ruwan daurayarsu na kayan wankin su wani lokacin har barinta suke ta debi na rijiya taje su sha dadinsu ita da Mahaukaciya ,
Tana shiga ta rafka salama ta ja gefe ta rakube , wasu yara naga sun fito su kansu daudar jikinsu ta ishe su suna ta wasa suna ganin wanan yar budurwar saï naji sun fara wake suna fadin *Ke mai suna Yar Mahaukaciya yaya haukan ki Yar Mahaukaciya , shin ina babarki Mahaukaciya tana ta zuba haukan? Yar mahaukaciya* ita kuwa sai murmushi take aika musu bata ce komai ba , har suka gama daukar maganar su suka tafi abinsu , ta kusan rabin awa a tsaye sai ga uwar gidan ta fito ta sha damara da niyar yin surfe tana ganin Yar mahaukaciya tayi hamdallah ta yafitota
Yar mahaukaciya ta matsa da Sauri ta zuguna a gabanta ,
Larai ta ce " idan abinci kike so zan baki da ruwan rijiya ke harma da zanin daurawata aman sai kin surfe min wanan dawar gaba dayanta
Yar mahaukaciya ta juya inda aka nuna mata dawa ta hadiyi wani yawu mai daci ta ce " To uwar gida ran gida zan surfa yanzu kuwa
Larai ta washe hakora ta kama mata buhun dawar suka tsayar da tirmin da tabaryar ta gyara yagegen zanin dake daure a jikinta ta shiga daka ba kakautawa , tun da rana ba ita ta gama ba sai yama lilis , Larai ta aiketa tayo mata cefane taje har cikin kasuwa a kafarta ita dai fama take ta gama ta koma wajen Mahaukaciya tasan yanzu ta dena iface ifacen domin takanyi hakan ,
Ba ita ta gama bautar gidan yawa ba sai da wajen shigar magariba ,
Larai ta harhado mata abinci harda na shekaran jiya ya gama yin tsami ta turo mata harda kanzo ta sauye mata shi a cikin wani bokici da ya gama yin tsatsa sanan ta ce ta jawo guga biyu ta isa gudun kar ruwan rijiyar ya kare ta je ta jawo guga biyun ta sauye a tsohuwar jarkarta ta dauka gaba daya tana tafe tana Sauri yara kuwa sai binta suke suna fadin yar Mahaukaciya ita kuwa bata kulasu famarta ta isa bola
Tana zuwa ta hango dan karton da ta kara ta rufe an janye shi ta kara Sauri ta shige cikin kewayen nasu , jini jini ta fara gani a dashe a ko'ina ta yaye rufar da tayi da ledodi tana yayewa gabanta na faduwa don abinda idanuwanta suka gani bata san sanda ta saki bokicin abincin da ta wuni tana aiki dalilinsa ya zube a nan ba ta dauki hanunta ta dora saman kanta saman bakar ledar da tayi dan kwali da ita ta kurma ihu domin jariri ta gani konce cikin jini yashe a nan gashi ba Mahaukaciya ba alamarta da gudu ta karasa ta shiga dage dage da alama neman Mahaukaciyar take
Shin ina mahaukaciya? Yaron nan wa ya haife shi? Su waye Mahaukaciya da Yar Mahaukaciya? Taku har kulun Sajida
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
2
Dadaga tarin tarikicen su take tana ihun kuka tana Kiran Mahaukaciyata ina kike ? Da kyar ta dena dage dagen ta matso kusa da jaririn nan ta tsura masa ido yaron sai kuka yake tun karfinsa wani tausayinsa ya kama ta ta Mika hanu a nitse ta dauko shi ta jawo ruwan nan ta wanke masa fuskarsa ta dorashi a bayanta ta dauki zanin nan da Larai ta bata ta goya shi ta fito ta fantsama neman Mahaukaciya ,
Wai shin wacece Yar mahaukaciya?
Yar mahaukaciya ita kanta bata san sunanta ba bata san na mahaifiyarta ba , ita dai ta fara wayo ta ganta a gidansu bola kuma taji yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya* ana kiran mahaifiyarta da *Mahaukaciya* duk da irin tarin daudar da suke ciki da cin abinci marar kyau da kwana a waje marar kyau idan ka kalesu zaka gane cewar fararen mutane ne rayuwa ce kawai ta mayar da su masu duhu , Yar Mahaukaciya ba arabi bale boko , bata da kowa sai Mahaukaciya , tarbiyarta tarbiyar Allah ce domin tanada nutsuwa tana masifar son Mahaifiyarta Mahaukaciya , bata son komai ya rabeta kulun cikin shan dukanta take domin idan ta kawo mata abu mushe taki ci sai kawai ta daneta wataran ta dura mata wataran kuwa ta samu ta gudu ,
Abincinsu gida gida take bi tayi aikace aikacen ragwayen mata ta samu abinda ta samu ta kai musu su ci abinsu kuma ruwa na kwata ne kadai basa sha domin tana yin iya kokarinta don ganin mahaukaciya ta kwana da ruwa a dakin , tun tana karama suke cikin bolar nan wataran ta wayi gari taga Mahaukaciya na dauke da ciki bata san KO na waye ba hasalima sai da taji yara na fada ta gane inda suka dosa tayi mamakin inda mahaukaciya ta samu cikin nan harma tayi tunanin KO hakan kawai ake wayar gari da shi , ita dai bata da mai bata amsa hakan yasa ta yi shiru abinta take lalaba mahaifiyarta cikin tsananin so da kauna iya labarin tarihin mahaukaciya Kenan
Tafe take da dan yaro a bayanta tana girgizashi tana fadin kayi shiru dan Mahaukaciya muje mû nemo Mahaukaciyarmu mu kawota gidan mu ta goya sabon dan mu , kayi shiru Dan mahaukaciyana tana ta yawo gaba daya ta jigata sai jiri take na tsananin yunwa ga Dan mahaukaciya sai dai ta bashi ruwa yara kuwa banda tsokanarta ba abinda suke duk inda ta zaga sai an biyota ana fadin lah Yar mahaukaciya ta sato beby har ta ISO wajen wani police zata huce taji yace " ke yar mahaukaciya dan wa kika sato haka?
Tayi narai narai gabanta na mugun faduwa ta ce " Mahaukaciya ta haife shi kuma ta gudu
Ya zabga mata mari har sai da ta dan fara sakin fitsari ya damketa sai police station , suna zuwa ya Nuna cewar ta sato yaro ne suka shiga tambayarta amsar dai data ce Dan Mahaukaciya ne hakan yasa suka kunce yaron suka shiga nadarta Dole sai ta fadi inda ta sato yaro banda kuka ba abinda take suna tsaka da dukanta sai ga tsohon daraja shima police din ne aman ya fisu mukami , yana zuwa ya tambayi mai tayi
Ilyasu yayi masa bayanin ai ga abinda aka kamata da shi
Tsohon daraja ya ce " tabas kwanakin baya naga Mahaukaciya da ciki a jikinta kuma yau na ganta wajen kasuwa ba cikin sanan saninta duk jini ne tabas wanan yaro *Dan Mahaukaciya ne* dan haka ku saki baiwar Allahn nan tayi tafiyarta
Haka suka saketa ba dan ransu ya so ba domin sun so ta kwana a nan suyi anfani da ita ,sai dai kash tsoho ya kawo cikas
Da kyar take takawa domin ta daku ta dauko dan Mahaukaciyar tayi wajen kasuwar don neman Mahaukaciya tana tafe tana kuka yaron na kuka tayi kasuwa neman duniyarnan ba Wanda bata yi ba ta juyo ta nufi wani layi tana tafe 'tana kugin sunan Mahaukaciya har ta isa wata makaranta ta zauna tayi tagumi almajirai sai shigi da fici suke suna ta sha'aninsu har akayi sallar isha'i bayan an gama sallah Malan ya fito daga masalaci ya hangi yatinyar nan zaune tana ta jijiga yaro a hanunta kawai sai wani tausayinta ya kama shi ya matso yayi mata salama
Ta dago jajayan idanuwanta masy shige da na misa ta sauke su saman fuskar wanan Malan mai cike da Haiba ta amsa salamarsa
Ya ce " Baiwar Allah lafiya kike zaune a nan? Ga yaronki da alama yunwa yake ji to ki bashi ya sha mana
Yar Mahaulaciya ta kale shi tace " Malan ai ruwan ya kare babu kuma abincinsa
Malan sai yaji tausayinta ya ce tashi mû shiga gidana a tatsa miki nonon akuya tayi sabuwar haihuwa sai ki bashi ya sha , ta mike har tana harde kafafuwanta ta bi bayansa suka shiga gidansa
Matansa biyu dayar mai kirkin gaske DAyar kuwa tadi dafi zafi hakan yasa ya nufi dakin saratu ya fada mata ta fito ta taimaki yarinyar nan da danta ,
Saratu ta fito suka gaisa da yar Mahaukaciya tace miko yaron a bashi nonon akuya kema kije ga ruwan dumi kiyi wanka domin da alama sabuwar haihuwace
Yar Mahaukaciya ta ce " nayi wanka? Da gaske?
Saratu ta ce " eh man ga bokici ki dauka ki zuba ruwan sai ki dan sirka da na rijiyar ki je kiyi wanka shima bara nayi masa sai a bashi nonon
Sai washe hakora take domin itadai da wayonta har ta manta rabonta da tayi wanka ta jawo isashen ruwa ta kai bayi ta aje saratu ta bata soda ta dauko mata jacen kayanta ta mika mata har tana fadin ki wanka ruwan zafin da kyau fa saboda jego ita dai har lumshe ido take tana zuba ruwa a jikinta kafin ta fito Saratu ta wanke dan mahaukaciya ta bashi nonon akuya ya sha sosai har ya samu wani ni'imtacen baci mai dadi
Wanka take tun karfinta wani bakin ruwa na zuba daga jikinta yana bin magudadar ruwan nan da nan sai gâta ta fara haske tamtar mai , ta cire ledar dake rufe a kanta ta dauki sodar nan ta ringa kwabata a cikin gashin kanta nan da nan naga wata irin dauda mai yauki tana zuba daga kanta ta kama kwarara ruwa gaba dayanta ta darwaye jikinta dagowar da zata yi na zaro ido domin gashin kanta ba baki bane kalar 🙍🏼 masara ne yelow gaba dayansa aman yalow mai haske ga shegen tsayi da gareshi na tambayi kaina wai Yar Mahaukaciya yar hausawa ce kuwa? Ta dauko ledarta ta daure kanta ta saka kayan da Saratu ta bata sai ajiyar zuciya take domin ta rabu da kashi 80 na daudar dake jikinta tana fitowa gaban Saratu ya fadi , duk irin kirkin saratu matsalarta daya ce kishi Allah yayi mata kishin mijinta tamkar mai , hakan yasa da Sauri ta daukowa Yar Mahaukaciya yan tsumakoron da ta dadauko mata ta bata ta hada mata da tuwon lamshi mai yawa ta ce " to yar uwa rufe gidan zamu yi kinsan Malan ba a nan yake kwana ba hakan yasa Mike rufe gida da wuri
Yar Mahaukaciya ta kama godiya harda tsugunawa saratu ta ce ba komai ta dora mata dan Mahaukaciya ta goya ta dauki sauran kayan tayi gaba tana yiwa Allah godiya taci GABA da Neman Mahaukaciya
😌
.[8/11, 06:27] +234 816 681 0364: *'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
3
Tafiya take har karfe biyu na dare yayi mata ta gaji tamkar ta kife idanuwanta sai zugi suke yi mata na baci dan mahaukaciya kuwa sai bacinsa yake shekawa hankalinsa konce domin ya sha nonon akuyar nan ya koshi , wata bishiya ta hango a hankali ta isa ta samu ta rakube ta shinfide dan Mahaukaciya tayi konce a gefensa ta shiga tunanin duniya tana tunani tana share hawayenta ta mike da ruwan na yar jarkar ta zauna ta daura wata kalar alwalah gaba daya ba daidai bace ta juya Gabas tayi sallah Wace bata karanta komai sai dai tayi ta musmus da baki shima wajen Larai ta jiyo idan tana sallah tamkar koton kurciya nan da nan ta gama tana salamcewa ta konta kusa da dan kaninta tana adu'ar Allah ya jikanta ya ya fito mata da Mahaukaciya ,
Haka rayuwa tayi ta tafiyarwa yar mahaukaciya tun bata iya raino ba har ta kware ta iya goya yaron da zuwa wanki , shara a bata nera ashirin nera goma ta je ta siyowa Dan Mahaukaciya koko ta zo ta bashi ya sha , idan ya koshi itama ta samu ta sha , a tanzu yara sun koma tsokanar Yar Mahaukaciya da Dan shege ita dai ta kanta take tana nema musu dan abunda zasu saka a bakarsu har yanzu tana zuba ido ne taga ta inda Mahaukaciya zata bilo duk fitar da zata yi kuwa sai ta nemi Mahaukaciya har yanzu bata fida rai da ita ba ,
Konce take ta samu da kyar barci ya dauke Dan Mahaukaciya ita kuwa sai hama take ga wani uban sauro na damunta inuwa inuwar mutun ta fara gani ta mike zumbur ta fara kalon kofar wani katon mutun ne bakikirin mai murdaden jiki ya shigo kafin ta ankara tayi wani abu har ya watsa mata wata hoda a fuskarta ya kwasheta ya sakata cikin wata bakar mota ya dauko jaririn shima ya saka shi cikin motar wa'inda suke cikin motar suka figi motar ,
Tafiya suke tun karfinsu sai da sukayi tafiyar awa hudu sai gasu a garin jos suka karkata suka nufi wani tankamemen gida mai shegen kyau suna isa aka wangale musu porte din suka dana kai ciki , wata hanya naga sun dauka a cikin gidan sun nufi wani gate din aka kuma bude musu , suna isa ya diro ya bude ya dauko Yar Mahaukaciya a kafadarsa ya nufi wani daki da ita ya dauko yaron shima ya Mika shi wajen wata tsohuwa naga ta nufi ciki da shi ,
Dishi dishi ta fara gani sanan a gankali ta buda idanuwanta , wajen da ta ganta konce saman wani makeken gado Wanda tunda uwarta ta haifeta bata taba sanin akoyshi a nan cikin duniya ba ta Mike tsaye da Sauri ta fara dubedube can ta koma ta zauna ta tare fuskarta da hanayenta ta shiga tinani , watarana taji kishiyoyin Larai suna fadin idan aka mutu akoy wuta akoy aljana , ance a aljanar akoy manyan gadaje da manyan TV da komai da komai a wutar kuwa wutace kawai sunce ai idan Larai ta mutu tace ita aljanar zata zaba su kuwa a kaisu wuta dan sun aure mata miji ( to kaji Larai shawara Kenan za'ayi miki?) , ta kuma daga kanta ta hango babar TV din ta kali gadon da take zaune saman kansa a fili ta furta " Au Kenan mutuwa nayi aka kawoni aljana? To ina dan Mahaukaciya da Mahaukaciya ? Ku zo ku ga aljana ku zo muyi zaman mû a nan aljanar tafi duniyar dadi , tana tsaka da maganarta aka bude dakin wata mata ce ta shigo rusheshiyarta ta ja ta tsaya da Sauri yar Mahaukaciya ta mike tana soshe soshe tana kalonta
Matar nan ta ce " ke yarinya ki tashi nayi miki wanka na shirya ki na kaiki wajen hajiya
Yar Mahaukaciya ta ce" baiwar Allah nan ina ne? Duniya ce KO lahira?
Matar nan ta ce " ke karki kawo min maganar banza ta kama Yar Mahaukaciya kiiii sai cikin bayi tana ji tana gani matar nan ta tube ta tamkar wata beby ta zirata cikin bahon wanka ta kama dirzarta da wani soso mai shegen zafi , tun tana nonokewa har ta hakura matar nan dan rashin imani ta dauko wani tirare da detol ta zuba a ruwan har kanta ta kuma darje jikin Yar Mahaukaciya jikin har wani sulbi yake na wahala ruwan ya kuwa shigar mata ido ta rufe ruf tayi ta murzawa aman matar nan bata damu ba , tana gamawa ta jawo tawul ta nade jikin yar Mahaukaciya ta jawota tsakar dakin nan Yar mahaukaciya ji take tamkar sabuwa har wata iska ke daukan ta tayi fayau da ita farinta yayi mugun fitowa ,
Matar nan mai suna Mesi wato ba musulma bace ta dauko kayan bushe gashi da wani mahaukacin kaya doguwar riga mai daukan hankali ta jawo hanun Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita ta shiga bushe mata gashin kanta ta dauko man shafawa ta shafa mata nan da nan kan nan mai kalar blonde ya fara sheki ta saka ribom ta daure aman har gadon bayanta ya zubo , ta mika mata sabon pant da breziya ta saka gaba daya aikin nan da take yi mata bata yi mata magana itama tayi shiru tana kikifta manyan idanuwanta ta rasa wanan wani irin Abu ne? Wanan wata irin masifa ce? Meye za'ayi mata ne? Ina za'a kaita? Ina Dan Mahaukaciya? Nan din ina ne?
Ni ma ban sani ba yar mahaukaciya sai dai mu bisu mu gani
[8/11, 06:28] +234 816 681 0364: *'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
4
Tana tsaka da sakar zuci taji Mesi cikin wata uwar muryarta tamkar namiji tace " ke tashi mu tapi
Cikin Sauri Yar Mahaukaciya ta mike ta bi bayan Mesi suka ratsa wani falo baba , suna ratsa na biyu ta hango wata tsohuwa tana ta jijiga yaro a hanunta ,
Tsohuwar ta matso ta mika mata yaron ta ce " bashi ya sha
Yar Mahaukaciya tayi shiru ta amshi Dan Mahaukaciya ta rungume shi yana ta bacinsa kawai sai taki cewa komai
Mesi ta ce " yaronta ne kuma mahaulaciyar ce dan Haka kawai mû kaisu wajen Hajiya
Tsohuwa ta washe hakoranta jajaye ta ce " kai aman hauka shi kadai yake wanan yarinyar mai kyau haka ya kamata? ( tsohuwa shin haukan ba kadarar Allah bane? Akoy Wanda ya isa ya kaucewa kadara ne? )
Messi ta ce " baki ma ga gashin kanta ba wani mai shegen kyau sai tambayar masifa ke malama mu je KO na ci ubanki a nan
Yar Mahaukaciya tayi gaba da gudugudu suna biye a bayanta sunyi tafiya mai nisa sai gasu sun bilo dakin wata mata tana zaune bakin gadonta ta hakimce Matar zatayi shekara arba'in da biyar a duniya ,
Suna shigowa su duka suka tsuguna suna gaishe da ita banda yar Mahaukaciya
Hajiya Falmata ta ce " ya zaku kwaso min yarinya karama haka nayi yaya da ita?
Mesi ta ce " ai hajiya wanan ta dade cikin hauka yanzu haka da kokowa da komai muka samu muka fito da ita kinga sai da na sharara mata mari hudu sanan ta dena buge buge kuma kinga yaron nan danta ne ita ta haife shi bashida uba shege ne kuma ita din ma shegiyar
Hajiya Falmata tayi shiru ta ce to ku zaunar da ita
Suka zaunar da Yar Mahaukaciya ita dai binsu take da kalo bata ce komai ba , sai da suka zaunar da ita suka fice
Hajiya falmata ta taso ta zauna nesa da yar Mahaukaciya ta kura mata ido ta ce " ba laifi kina da kyanki , kuma kinfi wancen Wanda nayi da ita kuma na kasheta da alama ke zaki fita iyawa kuma aikina zai fi ci sosai
Gaban yar Mahaukaciya banda faduwa ba abinda yake tayi shiru tana ta kifta ido , ita dai har yanzu bata gane inda Hajiya Falmata ta dosa ba , wani aiki ? Mai zata yi da ita? Tana tsaka da tinani taga hajiya ta Mike tana famar tube kayan jikinta Yar Mahaukaciya ta sada kanta kasa taki dagowa , duk da mahaukaciya ta reneta bata ganin tsiraicin Babar mace haka , gabanta sai faduwa yake
Hajiya falmata ta mika hanu ta dauke dan Mahaukaciya ta ja hanun Yar mahaukaciya ta kontar da ita saman bed din dakin ta yar mahaukaciya tayi zumbur ta Mike tana kalon kasa
Hajiya falmata ta ce ' ke dan ubanki konta min ke badan boka yace na konta da mahaulaciya mai da ai da baki isa na konta dake ba sai manyan hajiyoyi to dan dai kawai ina gudun kar asirin da nayi shekara goma sha hudu da suka fice ne ya karye dan uwarki konta min KO na saka a daure min ke
Yar Mahaukaciya ta zaro ido ta ce " Ni fa ba dana bane dan Mahaukaciya ne
Hajiya Falmata ta zabura ta ce " kutumar ubancan to wacece mahaukaciyar ke kuwa wacece ?
Yar Mahaukaciya ta ce " Ni Yar Mahaukaciya ce Kuma wanan ma dan Mahaukaciya ne Mahaukaciya ta tafi yawo bata dawo ba
Hajiya falmata ta zaburo ta ce " ai kuwa yau sai na kasheki tsinaniya shine kika sakani a gaba har na tube miki ? Yau sai na galabaitaki sanan nayi anfani da ke kuma na kashe ki tayo kan Yar Mahaukaciya ta shaketa
Wayo yar Mahaukaciya
🇳🇪 BElles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
5
Wayo Kano ba wuta sai ingi 🙆🙆🙆🙆🙆🙆
Famar sumewa take domin Hajiya Falmata ta mugun shake mata wuya ta gaza tabuka komai domin karfin ba daya ba , tana kokarin ganin bayan Yar Mahaukaciya wayarta dake aje a gefen bed din ta shiga ringin kuma karar wayar wakar da ta sakawa mijinta ne hakan yasa cikin Sauri ta cikata ta dauki wayar
Daga dayan bangaren Elhaj biloniya ya ce " Hajiya na fasa tafiyar gani na dawo bangarenki bakya nan shin kina ina ne?
Hajiya Falmata ta ce " what? Kana gida?
Elhaj biloniya ya ce" eh lafiya nake jin muryar taki a tsaitsaye?
Hajiya Falmata ta ce " no ba komai dear gani nan zuwa yanzu yanzu
Ta datse Kiran ta danawa Mesi kira tana kokarin mayar da kayanta , Mesi ta shigo da gudu tana amsawa
Hajiya Falmata ta ce " ke sakaran banza da wofi zo ki san yanda zaki fitar min da wanan dabar domin honorable ya dawo gidan nan idan kika yarda aka kama ki da ita ke zaki kwana a ciki , bata samu damar fada mata cewar yarinyar ba mahaukaciya bace hakan yasa Mesi bata tsaya tambayar a kasheta KO kar a kasheta ba kawai ta jata ta bi ta hanyar baya da ita ta tura ta ta wata karamar kofa ta ingiza keyarta sai waje ita kuma ta juyo ta koma cikin gidan tana ta tsinewa halayar Falmata ta samu babar yarinya haka aman tana aikin mita ,
Yar Mahaukaciya da take rungume da Dan Mahaukaciya tana zabga Sauri bata ma san ina zata dosa ba gashi kafarta KO takalmi babu tana godewa Allah da ya kubutar da su daga hanun wa'inan bayahudan
Tafiya take zabgawa tana haki ta rasa ina zata nufa hankalinta duk a tashe ta rasa mai zata yi , ina zasu kwana ga garin bata san shi ba tafe take tana tunani idanuwanta sai zubar da hawaye suke , karar taka birki taji kiiiiiiiii aman ina duk da haka sai da ya buge kafafuwanta ta fadi dabas a kasa aman Dan Mahaukaciya na rike a hanunta , mutumin da ya kadeta ya fito daga cikin motarsa dan matsakaici ne , bashida kiba aman yanada dogon hanci yana cikin jalabiya fara da alama ba nesa zai je ba
Ya ce " Malama lafiya kike tafiya bakya kalon gabanki?
Yar Mahaukaciya ta dago kanta ta sauke idanuwanta a saman fuskarsa bata ce komai ba ta mike taci gaba da tafiya , yayi sororo yana kalonta kawai sai yaji a ransa wanan yarinyar da danta duk inda zata tafi tana cikin damuwa ne gashi kuma ya bigeta da mota kuma bata ce masa komai ba , cikin Sauri ya tayar da motar ya bi bayanta
A hankali yake binta da motarsa yana fadin baiwar Allah lafiya? Mai yake damun ki? Ina zaki tafi? Ina takalman ki? Aman shiru bata bashi amsa ba hakan yasa ya ce to ki shigo na kaiki inda zaki tafi mana?
Tana jin haka ta waigo tana kalonsa ta ce " zaka kaini?
Wanan bawon Allah mai suna Idrissa ya ce " eh ki shigo na kaiki inda zaki je
Ya Buda mata motar ta shiga tana jijiga Dan Mahaukaciya , shi kuwa ya koma ya shiga tuki ,
Tafiya suke ba mai yiwa dan uwansa magana shi jira yake ta fada masa ga kwanar da zai sha KO ga unguwar da zai kaita aman tayi masa shiru hakan yasa ya ce" baiwar Allah ina zamu nufa ne?
Cikin sarkakiyar murya Yar Magaukaciya ta ce " Bawon Allah ina ne nan?
Idrisse ya ce " Jos ne baki san sunan garin ba? Mai yake damunki ne?
Yar Mahaukaciya maimakun ta bashi amsa sai ta jefe shi da wata tambayar ta ce " menene jos? Sunan anguwa ne?
Idrisse yayi tsai yanzu fa ya dan fara tsorata KO dai ya kwaso ruwan dafa kansa ne? Ya nisa ya ce " Dan Allah ya sunan ki?
Yar Mahaukaciya tayi tsam ta ce " ana kirana da sunan *YAR MAHAUKACIYA*
Idrisse ya taka birki ya juyo yana kalonta rigar jikinta duk ta dame mata jiki tamkar karuwa ( yar bariki ) gashi batada dan kwali gashin kanta tamkar ba na bahaushiya ba kai fatar jikinta kanta tamkar na mai Jan kune nasara sai dai kwayar idanuwanta bakake ne sidik shine banbancinta da nasaru ,
Ya ce " ban gane ana kiranki da Yar Mahaukaciya ba , meye ainahin sunan ki na kirki? Wanda aka rada miki? Wanda dadynki ND momynki ke kiranki da shi?
A ranta tana mamakin yaransa meye dadynki ND momynki? Meye sunan da za'a kirayeta da shi wanda ya dara Yar Mahaukaciya? Ta juyo suka hada ido hudu da shi ta ce " haka ne suna na , haka suke kirana da shi kuma wanan sunan sa Dan mahaukaciya
Idriss ya girgiza kai a ransa ya ce bazan iya barin wanan haka ba da alama ta gaji shi yasa take sakin zance ba tsari hakan yasa ya ce " zan kaiki gidan abokina yana da ma'aikata mata ki kwana a can gobe da safe idan Allah ya tashe mu lafiya zan zo muyi maganar abinda ke damun ki da kuma sunan ki aman ki sani bazan yarda cewar sunan ki Yar Mahaukaciya ba because ke din da alamar nutsuwa a tatare da ke so ki yarda da ni bazan cutar da ke tomorrow sai na kaiki gidan ku tunda yanzu kin gaji
Ita dai kalon bakinsa take yanda yake magana ba tun karfi ba daman akoy maza masu magana a hankali? Sai kuma da taji yace tanada wani suna bayan yar Mahaulaciya tana son sanin sunan , sai kuma da yace zai mayar da ita gidansu wato bola hakan yasa hankalinta ya konta harma ta gyara konciyarta tana kalon titi ya tayar da motar ya harbata kan titi ,
Sun dan yi tafiya mai dan nisa suka isa wani gate shima tankamemen sa lokacin Yar Mahaukaciya tayi baci shi dai haka kawai yaji matar nan yana tausaya mata ya dana horm aka wangale masa gate din yana shiga daidai Umar abokinsa ya fito da computer sa zai je jardin ya huta yayi tsai yana kalon Idrisse , Idrisse yayi parking da motar har lokacin bata farka ba , ya fito ya nufi Umar yana isa suka tafa
Umar ya ce " kai mutumina wanan bebyn fa?
Idrisse ya ce " kai karka yi min zakarancin naka wanan wata baiwar Allah ce na hadu da ita na kawota nan tunda kana da masu aiki mata ta kwana a wajen su tomorrow sai na kaita gidan su yeah?
Umar ya ce " wayo baiwar Allahn harda danku kai na tayaku murna abokina Allah ya raya bara na matsa na ga bebyn tamu
Idrisse ya girgiza kai suka matsa tare shi da Umar , Umar ya Mika hanunsa a hankali yana konkwasa gilashin motar
Yar Mahaukaciya dake barcinta ta Buda idanuwanta a hankali ta dago kanta suka yi ido hudu da Umar gabansa ya yanke ya fadi yayi Saurin ja da baya nan da nan jikinsa yayi wata muguwar mutuwa ya saki computer hanun NASA , ,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,
To jama'a mai ya baiwa Umar tsoro? I don't know 🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀
I'm sorry ba wuta ba nepa 😭😭😭😭😭😭
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
6
Na sadaukar da wanan shapin gareki masoyiyar asali AMINA AMINU ina godiya da adu'o'in ki
Umar ya saki computer hanunsa ji yayi duka gabobin jikinsa sunyi wata irin mutuwa
Idrisse da Sauri ya matso ya dafa kafadar Umar ya ce " yayadai abokina lafiya mai ya faru? KO ka Santa ne?
Umar ya ce " abokina yarinyar nan na taba ganinta a turkey naje wani aiki na ganta ana tuka ta ita da kanta aman wanan tafi wacen fari kuma gashin wacen baki ne yarinyar nan aljana ce domin da nayi mata magana gurds dinta sai da suka kusan kashe ni , gaskiya bazan sauketa a gidana ba 😡
Idriss ya zuba masa ido yana sauraron sa ya ce " to aman mai zai kawo mutumin dake turkey saman titin jos ba KO takalmi? Kuma tafiyar nan taka duka duka yaushe ne ai bai kai har ta haihu ba KO? KO da tsohon ciki ka BArTA ne?
Umar ya daga kafada irin bai shafe shi ba ya ce " ni dai banga ciki a jikinta ba may be ta ajiye shi a gida ne kafin ta fito na fada maka wly aljana ce ka rabu da ita tun wuri ,
Idris ya juya yana kalon Yar MaHaukaciya Wace itama su take kalo tana son fahimtar yaren su , abinda suke fada , Idris ya nufo motar jikinsa ba kwari ya Bude mazaunin direba ya tayar da motar ya kama hanyar fita yana tafe yana sakar zuci shi dai Allah baiyi masa tsoro ba kuma ya sani idan har Aljana ce wanan tofa zata bace ne koda tsakar dare ne hakan yasa yayi imani da Allah ya dauki hanyar gidansa da ita , a hanya ya tsaya wani butique ya siyo mata hijabai uku da dogayen riguna ya fito ya sayi kaji ya shigo motar ta koma barcinta hankalinta konce ya tada motar , sai da yayi tafiyar minti ashirin ya isa gidansa mai gadi ya bude masa ya zagaya ya shiga ta baya da ita gudun kar a kai tsegumin ya zo da mace harda yaro gidansa momynsa kuwa mai zafi ce
Bayan ya gama daidaita tsayuwar motar ya rasa taya zai tayar da ita yayi tsai yana kalon fuskarta verry inoscente wanan yasan bazata fice wata shekara 15 a duniya ba , gashin idanuwanta ya tsurawa ido sai yaji sha'awar tabawa yaji KO nata ne domin bakinsu yayi over ga kuma tsayi ga sheki ya Mika hanu a hankali zai taba wani abu yace masa kai Idris matar aurece fa hakan yasa da Sauri ya janye hanunsa ya dan bubuga kujerar da take konce
Firgigit ta farka ta tsura masa idanuwan nan nata masu matukar firgitar da mutun , ya kawar da kansa ya ce " ki fito mu tafi
Ya bude motar ya fita ita dai da kalo take binsa ta rasa ina ne wajen bude motar ganin taki fitowa yasa ya bude mata ya kwashi kayan ta fito ta tura motar irin yanda taga yayi ta bi bayansa cikin gidan suna shiga ya Mika mata leda baka
Ya ce " ga abincin ki da kuma hijabi ga daki can ki kwana ciki da safe idan Allah ya kaimu zamuyi magana kinji?
Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tayi hanyar dakin da ya nuna mata , tana turawa taga dakin masha Allah ya sha kwaliya tayi tsai tana tunanin to wai daman haka suke gidajensu ko'ina ka shiga da shegen kyau haka? Ta samu nan kasa saman kafet din ta shinfide Dan Mahaukaciya ta rungume shi sai baci , KO abincin bata ci ba , baci yayi awon gaba da ita ( baiwar Allah )
Da sasafe taji ana dukan kofar tata ta farka ba shiri taje ta bude kofar tana budewa yayi saurin sunkuyar da kansa domin rigar ta jikinta ta dan yaye daga sama ya juya ya ce " Baba gatanan zan tafi kwana uku zanyi kinsan halin oga idan yana gari dan Allah ki kular min da lamarinta idan na dawo zan mayar da ita gidan su
Baba ta ce " to yaron kirki Allah yasa a dace Allah ya bada sa'a ,
Yar Mahaukaciya dai kalonsu take bata ce komai ba , ya dan kalota ya ce " na tafi ogana ne ya dawo wajen aiki kuma yanada bukatana wajen aiki duk da cikin gari ne ya saba ya rike mu har sati , so kiyi zaman ki idan bukatar wani abin ya tashi ayi kirana Insha Allah zan samu yanda zanyi na fito
Yar Mahaukaciya ta ce " zaka kaini bolar?
Yayi tsai yana kalonta can yace" sunan unguwarku bola?
Yar Mahaukaciya ta ce " aa gidan mu ne can bolar
Idris yayi shiru a ransa ya ce " KO dai ta haukace ne yarinyar nan ?
Yar Mahaukaciya ta ce " kuma kaga ina neman Mahaukaciyata ban ganta ba
Har zaiyi magana wayarsa ta hau ringin da Sauri ya daga yana furta ai na shigoma sir , ya kashe da Sauri ya juya yana fadin eh ki zauna idan na dawo zan kaiki bolar kinji?
Ta gyada kanta baba ta ce " Allah ya kiyaye hanya dan nan
Yana amsawa ya tafi ya Buda motar sa ya tafi
Baba ta juyo wajen Yar Mahaukaciya ta ce " Yarinya muje ki canja kayan nan KO? Ya sunan ki ne?
Yar Mahaukaciya ta ce " *Yar Mahaukaciya* sunana
Baba ta zaro ido ta ce,,,,,,,,,,
Sorry masoyan yar mahaukaciya ina kara baku hakurin kadan in da nake yi hakan ya faru ne da 🏌🏼♀ nepa🏌🏼♀
🇳🇪 Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
7
Na sadaukar da wanan gareki yar uwa masoyiya Maman manal matar oga lolz Allah ya barmin ke
Baba ta zaro ido tace" yar nan bana son neman magana wani irin yar mahaukaciya kuma? Ina babarki take ne?
Yar mahaukaciya tayi tsai ta tuna lokacin idan tana daka a gidan su Larai yayansu suna cewa babata babata nan ta gane Babar mutun tamkar uwa Wace ta haifi mutun hakan yasa ta watsa hanayanta irin bata sani ba
Baba ta ce " mu je kiyi wanka ki ci abinci sai ki bani labari ,
Baba ta shige gaba yar Mahaukaciya na biye a bayanta ta buda bayin ta tara mata ruwa sai da ta nununa mata komai domin a yanda tayi mata tsaye da alama bata iya ba , ta juya ta dauki yaron harda pampos dinsa tun na jiya da suka saka masa ba'a cire ba , hasalima ita bata san menene ba tana tsaka da yiwa yaron wanka yana tsala kukansa Yar Mahaukaciya ta fito ta dauki rigar da Baba ta Nuna mata ta saka tayi tsaye tana kalon yanda Baba ke juya Dan Mahaukaciya tana yi masa wanka , a hankali ta zauna tana kalon fatar hanunta ta zama wata kala wai daman haka take? Tana tsaka da tunanin irin rayuwar nan mai dadi ta ji baba tsohuwa na cewa to bude ki bashi ya sha
Yar Mahaukaciya a ranta ta ce " wai meye ake cewa ta bude ta bashi ya sha ne? Ita fa bata san mai ake nufi da hakan,
Baba ta ce " ke yarinya ki dena yawon tunani kar ciwon nan mai suna totion ya kama ki , ai ina fada miki haka mukayi da sale ya shirishiri ya dankara min saki uku bayan ya dala min mari a gaban sabuwar amaryar sa kuma ya tunkudo ni waje aka yi mana taro jama'a na tambayar mai ya hadamu wai kinsan mai yace?
Yar Mahaukaciya ta girgiza kai tana sauraron baba
Baba ta ci gaba da cewa wai wani cewa yayi fa na saci kudinsa murtala fa
Yar Mahaukaciya ta ce " kai har Murtala ? To wa ya dauka ?
Baba ta karkace ta gyara zama tace" yar nan nera sha biyar ne na dauka aradu ni ba duka na dauka ba kuma wata hudu yayi bai bani kudin cefane ba shine fa na dauka kuma ai ba sata bace KO?
Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tana mamakin wai dauka ne tayi ba sata bane tayi murmushi
Baba ta ce " ke yarnan ai dukan da yayi min da kuma sakin ya saka na kumbure uwa hulawa ni kadai nake kara girma babar uban gidana ta kaini ganin likita a can ne yace min wai totion ( tension ) ce ta kamani kuma har kisa take kinga ki dena tunani dan miji ya sakeki kiyi hakuri Allah zai baki wani cikin ruwan sanyi balatana ke din nan mai kyan aljanu
Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce " toh , domin ta lura Babar nan ba dai surutu ba
Baba ta kama rigar Yar Mahaukaciya ta zuge zup din , ita dai kalonta take tana son ganin abinda zata aikata tana zugewa Yar Mahaukaciya ta saka hanayenta biyu ta rufe mamarta
Baba ta ce " ke kuji mini yarinya da iyayi kunyar shayar da yaron ne kike a gaban idona na FITA?
Yar mahaukaciya ta ce " kunu yake sha
Baba tayi tsai ta ce " dadina da yan gayu Kenan wai baza'a shayar da yaro ba kar nono ya fadi ,hum to Allah shi kyauta ta dauki yaron tayi kicin da shi sai wake take rera masa ta dora kunu ta kada domin shima mai gidan ma'abotin shan kunu ne hakan yasa ta hada ta baiwa yaron ya sha ya koshi sai baci ( bawon Allah )
Wasa wasa yau har sun cika kwana uku a gidan Idriss bata aikin fari bale na baki aman duk da hakan tana fitowa tana kalon yanda baba ke kula da harkokin gidan da irin kulawar da take basu ita da Dan Mahaukaciya , har mamaki take wani abin ,
Zaune take tana kalon TV baba ta zo ta zauna kusa da ita ta ce " yarinya baki fada min inda babarki take da kuma abanki ba fa abun da mamaki har yanzu basu neme ki ba lafiya kuwa?
Yar Mahaukaciya ta juyo tana kalon baba a hankali ta furta nima nemanta nake , Mahaukaciya ta bata ban san inda ta nufa ba , na rasa inda ta tafi ta barmu da Dan Mahaukaciya
Baba ta gyara zama ta ce " ban gane ba
Yar mahaukaciya ta gyara zamanta ta baiwa baba labarin rayuwarta har Wanda bata san sunanta ba bata san kowa ba hasalima bata san sunan garin nan ba wai jos ita kuwa a tinaninta a kano take domin tana ji a bakin mutane
Mai baba zatayi in ba kuka ba harda face majina tana karkata kai ta ce " kai duniya kai duniya ina zaki da mu ? Oh ni habiba ya ga murja jikar saude wayo duniya kana tunanin a kunci kake sai ka tsinci Wanda ya fika oh Allahna , ta juyo ta kali Yar Mahaukaciya ta ce " yarinya Ashe shi yasa da na tambayeki sunan ki kika ce min Yar Mahaukaciya?
Yar Mahaukaciya ta gyada kanta
Baba ta ce " to ni zan ringa kiranki da Rahamu sunan yayi miki?
Yar Mahaukaciya tayi dariya ta ce " eh yayi min baba
Suna tsaka da zance sai ji suka yi an banko kofar dakin an shigo , Baba ta mike tana dafe kirji ta ce " salalahu alaihi wasalam Tawa ta sameni ,
Kafin Yar Mahaukaciya ta fahimci inda baba ta dosa sai jin saukan duka tayi ta ko'ina dukanta ake ba kakautawa , mai dukan ta warto Dan Mahaukaciya ta jefa shi kasa ya rufe da kukan jarirai da gudu Yar Mahaukaciya ta nufi wajen da yake yashe ta rungume shi suna rusa kuka a tatare ,
Mai dukan ta nuna su da yatsa ta ce " """"' """""""" """""
Love u
🇳🇪 Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
8
Mai dukan ta nuna su da yatsa tana kunfar baki tace" ke karamar yar bariki shegiya mai shige da zabaya ( albinos ) a gidan ubanwa ma ya hadu da ke har ya dirka miki cikin nan kika haifo yaro mai kama da ke? Kaga yayan shegu sai dai suyi kama da uwar su to bara kiji na fada miki Idriss nawa ne ni kadai babu ubanda ya isa ya hada shi da wata matar sai dai bayan raina dan haka ki dauki shegen danki da ke ku bace min a gidan mijin da zan aura tun kafin na kontar da ku nayi muku yankan rago
Yar Mahaukaciya dake goge jinin dake zuba a kan Dan Mahaukaciya ta dago idanuwanta ta sauke su a fuskar wanan matar wada da gani ta girmi idriss nesa ba kusa ba kuma tana ambatan mijin da zata aura cikin rashin kuzari ta dauki dan Mahaukaciya ta juya tana share hawayenta daidai zata bude kofa Idriss ya turo ya shigo ta dan ja da baya da sauri ya matso yana tambayar lafiya?
Hajiya Mariya ta taso tana fadin : my man ai na koreta ne kana ganin irin yanda ake zaginka a cikin family dina ana fadin ka ajiye karuwa yar bariki harda danku a cikin gidan ka ?
Idriss yayi gagawar daga mata hanu cikin daga murya yace ubanwa ya baki izinin korar a gidana? KO gidanki ne? An fada miki itama irinki ce? An fada miki itama ta samu yayane a waje irinki?
Hajiya Mariya tace" kai dakata Malan yayan ba da kai na samesu ba? KO an fada maka KO wani jaki nake mu'amala da shi ne? To wly KO ka kori yarinyar nan KO na kirayi mahaifiyarka na fada mata sanan na yada ka har a wajen uban gidan naka na samu na ganshi na fada masa irin abinda kake aikatawa ya koreka banza kawai , ta ficeshi ta ja rigar yar Mahaukaciya tayi waje da ita ta baiwa mudi mai tebur kudin mashin tace ya kaita inda yaga dama ,
Baba tsohuwa ta zauna tana ta hawaye ta fadawa idriss gaba daya abinda Yarinyar nan ta fada mata , harda sunan da tayi mata wato Rahamu ,
Idriss ya nisa ya ce" ban taba tinanin cewar watarana zan hadu da mace lokaci guda naji ta shige min a rai irin wanan yarinyar ya lumshe idanuwansa ya ce na kamu da sonta baba kuma insha Allah KO ina take zan nemota na aureta koda kuwa zan rabu da aikina ne , aman gaskiya ni bazan raka mata sunan Rahamu ba , bakya ganin yanayinta yanayin yayan larabawa ne ina wa laifin sunan Manal?
Baba tsohuwa ta washe hakora tace ai kuwa kaga sunan yayi min dadi sosai wato Manil
Yace aa Manal take baba ya Mike yayi dakinsa yana neman layin yaronsa ya kwatanta masa kamaninta da nufin maza ya zo anguwar su zai ganta da beby a hanunta ya dauketa kafin ya fito ( baka sans cewar a mashin aka dauketa ba ?)
Tafe suke yana papara gudu tun karfinsa ya ce " ke wace unguwa zan kaiki?
Yar Mahaukaciya tayi shiru can tace " Dan Allah ka kaini wajen magani kaga dan Mahaukaciya duk yayi wani iri
Mudi ya juyo kadan yaga yaron duk ya wani banbankare a ransa ya ce " kan uba kar aje ya mace min a rufe ni hakan yasa ya ja ya tsaya daidai wata katuwar asibitin kudi ta Yaron nan mai tashe wato Ibrahim Y Nazir ya ce " ke sauka ki shiga nan zasu warkar da ke kinji?
Yar Mahaukaciya ta sauka da sauri mayafinta har yana dan zamewa ta shige asibitin , tana zuwa ta nufi wajen da taga kamar nan ne wajen maganin , ta shiga layi , tun abin karfe goma sha daya har karfe 12 da yan mintuna sanan layinta ya ISO tana zuwa sai taga wata taga taji ance katin yan me kike so?
Ta dago dan Mahaukaciya ta nuna ta ce " dan Allah kiyi masa magani kina ganin jikinsa?
Matar ta dan bude windows din ta leko ta ce " ke dauke min jini mana karki bata min wajen aiki ki bayar da kudi a yanka miki katin ganin likitan yara
Yar mahaukaciya ta ce " nawa ne kudin?
Matar ta ce " dubu hudu
Yar Mahaukaciya ta ce " dan Allah ki yanka min a bashi zan kawo miki
Matar nan na jin haka ta dana Kiran securitie yana zuwa ta ce masa yayi waje da wanan tana neman tsayar musu da aiki
Sécuriti din ya ce " madame mu je
Haka tana ji tana gani yayi kokarin tura keyarta tana ta magiyar su saurareta , har ya kusan turota waje wata mata da wani a gefenta da alama sun zo dubiya ne ta tsayar da direban dake Jan su ta fito tana tambayar lafiya?
Securitie din ya fada mata abinda yake faruwa ,
Ta girgiza kai ta bude motar ta zaro kudi ta mikawa Yar Mahaukaciya tana fadin take kiyi maza ki kewaya urgence domin wanan ai urgence ne daga baya kwayi katin Allah ya bashi lafiya
Yar Mahaukaciya tayi Saurin tsugunawa da dan Mahaukaciya a hanunta tana hawaye ta shiga godewa wanan mata har ta shige mota direba ya jasu sai cikin asibitin ita kuwa da gudu ta mike tayi inda aka nuna mata , tana isa aka tarota aka dorashi saman wani gado na yara suka tura shi
Suna shiga akace wanan ai tamkar accident dan haka a kirawo Wanda ya kawoshi idan ba haka ba baza'a taba shi ba ( kuji fa )
Wata nurse da gudu ta fito ta yafito Yar Mahaukaciya ta biyo bayanta cikin Sauri
Suna zuwa
Docter mai sunan Abdallah ya ce " mai ya samu yaron ?
Yar Mahaukaciya ta ce " ban sani ba
Ya dan dago idanuwansa ya sauke a samanta domin muryarta mai dadin gaske , a ransa ya ce yarinya ce hakan yasa yace" ina Mahaifiyar sa?
Yar Mahaukaciya ta nuna kanta ta ce " nice Mahaifiyar sa faduwa yayi dan Allah Malan kayi masa magani kar ya mutu
Docter Abdallah ya ce " Malan ? Sai kuma ya basar ya mike domin gaba daya ji yayi ya kasa musa mata , ya nufi dakin da aka shinfidar da yaron ya ce a shiga dakin tiyata da shi ,
Nan da nan aka shirya shi akayi dakin tiyata da shi cikin gagawa domin yaron har wani shidewa yake , suna shiga docter Abdallah da sauran ma'aikatan suka dukufa don ceto rayuwar Dan Mahaukaciya Bawan Allah
Gani nayi Docter Abdallah da Sauri ya cewa nurse ta bashi irin abin nan da idan mutun yayi doguwar suma ake dana masa a kirjinsa , da gudu ta dauko ta daidaita ya kara yage rigar Dan Mahaukaciya ya murza abin ya dora masa saman kirjin sa , aman shiru kake gani ya kara murzawa ya dora masa cikin karaji ya ce " no ,no boy ka tashi mana kar ka yi min haka please ba'a taba mutuwa a hanuna ba ya kara murzawa ya dora masa yana kokarin kara murzawar da Sauri wata nurse ta rike hanunsa suka kama suka duba lokacin mutuwarsa 12h da minti 47
Docter Abdallah ya yi shiru gaba daya jikinsa ya mutu maganar matar nan wato yar mahaukaciya ta fado masa a rai inda take cewa dan Allah ka yi masa magani kar ya mutu , a hankali ya furta i'm sorry ,
Ya fito yana layi yana fitowa Yar Mahaukaciya tayi kuri tana kalon kofar dakin tiyatar sai da gabansa ya fadi ta iso da Sauri tana fadin " Likita ya jikin Dan Mahaukaciya ?
Da kyar ya tataro nutsuwar sa ya ce " Madame i'm sorry Allah ya amshi abinsa
Yar Mahaukaciya ta ce " ban gane ba mai kake nufi?
Docter ya hadiyi wani yawu ya ce " ya rasu ,
Yar Magaukaciya gaba daya taji tana kokowa da nunfashinta da kyar ta iya furta ya mutu? Sai luuuuuuuu ta tafiiiiiiiii
😭😭😭😭😭😭😭😭😭
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
9
Luuuuuuuu ta tafi kafin ta fadi Docter Abdallah ya tarota ya dagata cimak yayi wani daki da ita ya shiga bata taimakon gagawa cikin kankanin lokaci ta dawo hayacinta tana farkawa ta shiga rusa kuka har muryarta na dishewa , shi kuwa yana zaune yana kalonta yana share zufa domin ji yayi kwatakwata baya iya wata magana ,
Tana tsakar kukanta ta daga kanta sama tana kalon pankar dake juyawa a dakin asibitin tana tunanin ya zatayi da rayuwarta ? Tana kalon Dan Mahaukaciya tamkar Tana tare da mahaukaciyarta , Yanzu ta sanadiyarta aka kashe mata dan Mahaukaciyarta? Ta nisa bata san cewar a fili taci gaba da fadin " shin ya zanyi? Wa gareni? Ina zan kai Dan Mahaukaciyana ayi masa sitira? Wayo Allah gani gareka
Docter Abdallah ya dago kansa yana kalonta ga dukan alamu zancen zuci ne ya fito fili ya lura tana boye wani abu a ranta da alama ta fiya zurfin ciki, to aman mai take nufi da ina zata kai Dan Mahaukaciya? Mai yiwuwa yaron nata ne mai suna hakanan domin da ya tambayeta sunan yaron hakan ta fada, to aman ina babansa?
Cikin karfin hali ya ce " ina babansa yake ne?
Ta juyo idanuwanta wa'inda suka koma kalar ja tana kikifta ido ta ce " babansa ya mutu , bamu da kowa a garin nan kuma ban san hanyar bola ba
Ya budi baki zaiyi magana sai yaji karar bude kofa yana juyawa yaga kakarsa ta shigo cikin shigarta ta alfarma ta sha glas na karin gani tana shigowa ta juya ta cewa direban da ya kawota " yaro Kagan shi a nan ai ka juya kawai idan na gama yi masa fadan ya maidani gida KO ya dorani mashin 😌
Shi dai dan ladi direba ya juya yana dariya domin lamarin hajiya Hawaou sai ita , ta shigo cikin nutsuwa ta tsaya ta ce" kai Abdallah ka kiyayeni yanzu dan nayi maka maganar aure shine zaka fice yau baka gaisheni ba? Ai Allah ya taimakeni nasan wajen aikin naka , to ka sani aure ba fashi au ka kawo KO na zabo maka yaro 😏
Docter Abdallah ya taso da sauri a ransa yana fadin wani dan duniyan ya gaya mata yau ga asibitin da yake ? A ransa ya ja dan karamin tsaki haka kawai iyayensa basu takura shi kan yayi aure ba ita tana faman shiga rayuwarsa , ya kamo hanunta ya zaunar saman kujerar da ya tashi sai a sanan taga Yar Mahaukaciya na kuka ta zaro ido ta ce " Ikon Allah yarinya mai akayi miki? KO alurar ce bakya so? Ko dai yaci zalin dinki yayi miki biyu irin yanda yayi min?
Docter Abdallah ya ce " iya dan Allah ki saurara kadan kinga nan fa asibiti ne yama akayi suka barki kika shigo?
Hajiya Hawaou ta ce " gidanku akayi suka barni na shigo, kuma na fada maka ka dena kirana da iya sai kace uwar kaji
Ya girgiza kai ya ce " kinga wanan yarinyar marainiya ce batada kowa kuma yanzu ta kawo yaronta nan ya rasu shine take kuka domin bata san kowa a garin nan ba ,
Ai hajiya Hawaou na jin haka ta shiga salalami tana kuka ta Mike ta rungume Yar Mahaukaciya tana fadin" kiyi hakuri yarinya dukan mai rai mamacine , ai nima dan makociyata tana haihuwar shi ya rasu kai nayi kukan mutuwar yaron nan domin suna mugun neman haihuwa Allah ya basu kuma ya amshe abinsa kiyi hakuri Allah ya jikansa muje gidana ayi masa sitira idan kin huce sai asan yanda za'ayi aman bazan barki haka ba , kawai ta shiga tatara mayafin yar Mahaukaciya ta dagota KO takalmi babu a kafar Yar Mahaukaciya ta kamo hanunta tana kuka itama tana kukan suka shiga cikin mota Shi kuwa ya koma ciki dan ya dauko gawar dan Mahaukaciya
Cikin mutunci aka yiwa dan Mahaukaciya sitira harda taro domin Hajiya Hawau mutuniyar mutane ce sosai aka yiwa dan Mahaukaciya adu'a inda mata ke shiga suna ta'aziya domin Hajiya Hawau tayi ruwa tayi tsaki tace jikanta ne daga kauye suka zo Allah yayi masa rasuwa ,
Ita dai Yar Mahaukaciya tana Zaune da zunbulelen hijabin Iya da tazbaha a hanunta tana ja astagfari kawai take ja itama Iya ta fada mata tace ki ringa hailala kina maimaita astagfrullah Allah ya jikansa ke kuwa ya sanyaya miki zuciyarki ya baki dangana, hakan yasa ta koma gefe daya irin yanda ta saba zamanta tayi shiru tana ta jan carbinta tana astgfari hawaye wani na korar wani ,
Konci tashi har an yi cikon satin Dan Mahaukaciya , aman har yanzu sakewa ta gagari Yar Mahaukaciya domin jira take a koreta ta kara gaba dan tasan hakan rayuwarta take KO an Nuna mata so to fa za'a kyamaceta ,
Dawowarsa Kenan daga asibiti ya nufi can cikin gidan su domin mahaifiyarsa tayi kiransa cewar tana son ganinsa , yana shiga ya tarar da ita zaune ta harde kafafuwanta ya karasa ya zauna yana kokarin gaisheta kamar yanda ya saba , cikin sauri ta katse shi ta ce " abdul wai wacece yarinyar nan? Ni dai a sanina dangin ku duk yawancinsu yan camaru ne ya akayi ita wanan na ganta a nan ? Wa ya kawota ne? Meye halakar kakarnan taka masifafiya da ita?
Abdallah ya rasa amsar da zai baiwa umansa domin ita a rayuwarta ta tsani taga an rabe su idan dai mutun ba mai arziki bane tofah ranta baya so , ya ce " am haba mom kinga nima tare na gansu bansan KO wacece bâ fa ,
Hajiya Marhaba tayi shiru can ta ce " naji can ita da jarabarta aman na haneka da shiga sabgar yarinyar nan idan kuwa ba haka ba wly sai na saba maka , kuma karka manta nayi maka mata dan haka ka mayar da hankalinka kanta kaji KO?
Abdallah ya dan Sosa keya ya ce " an gama mom please ki dena rayar da hankalinki ai itafa bazawara ce kingani ai sai bazawari KO?
Hajiya Marhaba ta daga kafadarta irin su ya shafa din nan ta Mike tana tafiya ciki gadara ,
Bayan ta tafi docter Abdallah ya kontar da kansa jikin baban kujerar dake tsakar dakin su ya lumshe idanuwansa ya ce" ina son sanin labarinki beauty ( wato Yar Mahaukaciya ina ruwanka da labarinta inji ni sajida 😏 )
Zaune take ta saka kwanon furar da Hajiya Hawau ta dama mata a gaba tana ta tunani , Hajiya Hawau ta dauko karamar kujera tayani tsegumi ta zauna ta ce " to yarinya bani labarinki kuma ki fada mini sunan ki
Hankalin yar Mahaukaciya ya tashi a ranta ta ce " Nasan idan kema na fada miki sunana Yar Mahaukaciya zau gujeni ne, ni kuwa wani suna zan fadawa iya?
To jama'a ku taya Yar Mahaukaciya zabar sunanta don gujewa tsanar sabuwar family dinta 🤝🤝🤝🤝🤝
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
10
Yar Mahaukaciya ta gama yanke hukuncin ba Wanda zai kuma sanin labarinta domin idan ta fada kyamarta ake gwara ta boye sirinta ta nemi Mahaukaciyarta a boye daga baya idan ta ganta sai ta gudu da ita ,
Ta dago kanta ta kali hajiya Hawau ta ce " Ni dai Marainiya ce bani da kowa sai Allah ,
Hajiya Hawau ta ce " to shi mijinkin rabuwa kuka yi KO mutuwa yayi?
Yar Mahaukaciya ta ce " mutuwa yayi hajiya , domin tasan idan ta ce rabuwa suka yi za'a nemi sanin KO shi waye dan a nemi yan uwanta ,
Hajiya hawau ta ce " eyah Allah ya jikansa kar ki damu yata kinga daman ni dana daya a duniya Allah ya bani ya aure mata marar mutunci kinga tana can ciki ba ruwanta da ni , yaron ma da yake kulani bakin ciki take kinga kuwa ohon mata Allah ya bani nima yar KO?
Yar Mahaukaciya tayi murmushi a ranta ta ce ki gafarceni hajiya ki gafarceni ,
Hajiya hawau ta Mika mata furar da ta dama ta sha nono mai kauri da cukui sai abin mai take ga siga ta ce " kinga damun Dan Aljana ne wanan kwana biyu bai shigo ba mahaifiyarsa ce bata da lafiya ai har Idrissu ya kamata a gadon asibiti yaki sakinta sai da akayi da gaske
Yar mahaukaciya tayi murmushi ta ce " kai gaskiya bai kyauta ba sam
Hajiya ta kara karkata daurin dan kwalinta tace " kyaji mai yi dan Allah kinga ai ke kinsan abinda kike yi aman sauran gaba dayan su sun goyi da bayan a BArta ta samu lafiya ji suke asibitin ci ce , ai sai sun ga uwar bari kafin su yarda da magana ta ,
Yar Mahaukaciya tayi dariya domin du yanda kaso kaucewa lamarin hajiya to fa sai ta saka ka dariyar ,
Hajiya ta ce " KO ke fa to baki fada min sunan naki ba ,
Yar Mahaukaciya ta ce " sunana RAHAMU domin bata manta sunan da Baba tayi mata ba
Hajiya hawau ta ce " Rahama suna mai dadi To ni dai zan ringa kiranki da Ramatu domin Rahama haka sunan sirikata yake a gaban baban idrisu bazan iya fada ba
Yar Mahaukaciya ta ce " to hajiya ba damuwa na gode , haka suka wuni suna dan tataunawa Yar Mahaukaciya ta dan fara sakewa da hajiya Hawau domin tana kara janta a jiki
Washe gari da safe Hajiya Hawau ta shirya tacewa Yar Mahaukaciya ta tashi su je gidan su Dan Aljana su ga jikin babarsa an sakota daga asibitin,
Haka kawai Yar Mahaukaciya taji bata ra'ayin fitan ta kali Hajiya ta ce " Hajiya ki je ni na karasa aikin mu KO?
Hajiya ta ce " kai Ramatu bakya son yawo kema ga son aiki to ni dai kinga tafiyata sai na dawo
Yar Mahaukaciya ta ce " a dawo lafiya Allah ya tsare
Hajiya ta ce " Amin tayi gaba abinta ,
Bayan tafiyarta Yar Mahaukaciya ta zage damtse ta shiga sharar gidan ta share tsaf ta dawo ta zuba cleam ta wanke da ruwa da tsintsiya ta koma ta harhada kayan wanke wanke ta dawo ta zauna ta cire hijabinta ta kara gyara daurin zaninta ta zauna saman tayani tsegumi ta shiga wanke wankenta
Ya jima tsaye yana kalonta tana ta wanke wanke yana mamakin kalar fatarta har wani yelow yelow yake sakawa faratunan kafarta dogaye ba kananuwan yatsutsai bane da ita a hankali yayi salama ya shiga
Ta razana da jin salamarsa ta dago da Sauri tana konce hijab dinta daga kanta ta saka tana amsa salamar sa ,
Idriss ya karaso ya jawo kujera ya zauna kusa da tata , yana fadin sanu da aiki madame wanan aiki haka?
Yar Mahaukaciya tayi murmushi tana kara gyara zaman hijabinta
Ya ce " ina masu aikin gidan ne?
Ta ce " ai an aiki biyun kasuwa dayar kuwa tana baya tana wanki
Ya ce " ai kuwa sai an karo muku masu aiki KO?
Yar Mahaukaciya ta dago da Sauri suka yi ido hudu kuwa ta kawar da kanta ta ce " ina ma aikin gidan yake ai ni kadai ma na isa nayi shi
Docter ya girgiza kansa ya ce " tap ikon Allah ai bazai taba yiwuwa ba hutawa kawai zakiyi
Yar Mahaukaciya ta ce " hum , a ranta ta ce hutu fa lale KO a mafarki
Ya lura bata cika magana ba aman tana da girmama mutane yana son yi mata tambayoyi sosai aman sosai yake jin nauyin hakan bai san dalili ba haka yayi ta zama har ta gama wanke wanken ya dauke kondon kwanonin yayi kicin da su ita kuwa tayi murmushi ta dauko tabarma katuwa ta shinfida masa ta dauko kwarya da ludayi ta zauna ta a saman yar kujerar nan ta shiga dama furar , shima waje ya nema ya zauna yana kalon yanda take aiki bata da alamun gajiya tana gama damawar sai ga Hajiya hawau ta shigo gidan da salamarta
Yar Mahaukaciya taje da Sauri ta amshi ledar dake hanunta tayi daki da ita fruits ne ta sauye ta wanke ta jera rabin a frij ta debo wasu saman tire da wuta ta fito tana fitowa taga Hajiyar na zaune saman kujerar tana kara dama wata furar a hanunta , gefenta Idriss ne zaune yana shan wada ta dama masa idanuwanta suka ga wata kafa fara kar cikin wani bakin takalmi mai shegen kyau takalmin uwa na sarakai domin kalar adon sa ji tayi bazata iya kalon mai takalmin nan ba hakan yasa a hankali ta ajiye fruits din a kusan Hajiya Hawau ta Mika hanu tana fadin Hajiya kawo na dama miki mana
Hajiya hawau ta ce " aa yar gidana wanan damun sai ni da kaina kowa ya dama baya sha sai ni din nan da kike gani ai ta Dan aljana ce da nake baki labari , ta kuma kalon dan Aljana ta ce " Dan Aljana kaga yartawa da nake fada maka
Bai dago ba bai kuma ce kanzil ba itama haka kawai ta kasa koda dago kanta bare ta kale shi , jin takun tafiyar hils da wani kalar tiraren yasa ta bada hankalinta kan kofar shigowa
Wata budurwa ce ta shigo ta sha mahaukacin hils mai shegen kyau kai ita kanta abin kalon ce domin haduwa iya haduwa ta hadu ga kamshi tana zubawa batayi salama ba kawai shigowa tayi sai da taga idriss na zaune sai naga ta saki murmushi ta ce " Brother daman kana nan har momys take neman ka?
Idriss ya dago kansa daga kwaryar furarsa ya dan kaleta yace " sauran kice mata ina nan
Tayi murmushi bata gaida hajiya Hawau ba bare ta gaisar da Yar Mahaukaciya Wace take kalon takalmin kafarta tana mamakin yanda akayi ta hau saman sa , ta nufi wajen wanan mutumin mai cike da korjini tana zuwa ta saki murmushi ta ce " Honorable barka da warhaka
Sai yanzu Wanda aka kira da honorable ya dago kansa ya zabga mata harara , da Sauri na furta ya Salam na fadi ba shiri ba ni kadai ba Yar Mahaukaciya kanta gani nayi ta zaro idanuwanta tana kalon wanan bawon Allahn
Shin wanene Dan Aljanar da Hajiya Hawau ke fada tana karawa? Wacece wanan budurwar da ta shigo meye halakarta da Irdriss? Mai yasa bata gaishe da Iya ba? Muje zuwa daga Yar mutan niger
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
0 comments:
Post a Comment