_Written by Sofiyyah Galadanchi_
_in dedication to sha'awa Ebrahim_
01
A hankali yake saukowa daga matattakar benen tamkar bayason tafiyan kokuma yayi aikin daya gajiyar dashi, karo yaci da mahaifiyarshi tana shirin hawa saman benen,gaida ita yayi cikin girmamawa ta amsa masa da fara'arta sannan tace " shalele ina zakajene kake tafiya haka kaman bakason yi ko bakada lafiyane?" Murmushi yayi wanda ya kara k'ayatar da kyan fuskarshi sannan yace " lapiya na kalau momy kawai dai bacci nakeji gashi zanje na dauko jawaheer makaranta time yayi" kallon agogon hannunta tayi sannan tace " tunda kanajin bacci shi Adnan yaje ya daukota mana kaisaika kwanta" karasa saukowa yayi sannan yace "mom jeki ki huta zan daukota da kaina baccin ma yafita a idona" juyawa tayi batare da ta tankaba sannan haryakai kofa takira sunan shi "shalele" juyowa yayi yace "Na'am momy"
"Kasiyomun fruits idan zaka dawo kuma plss ka kulamun da kanka" murmushi kurun yayi yafita yana nazarin kalaman momy aranshi yace nakasa gane wace irin kulawa momy ke bani kwanakinnan abin da mamaki!.
Zaune ya tadda ita ta had'a girar sama data kasa domin kuwa dauka cin student duk an daukesu sun tafi gida daga ita sai tsirarun mutane dabasu fi su shida ba,sarai ta ganshi amma ta share shi saida yayi horn sannan ayangace ta tashi taje bude gidan gaba ta zauna da k'yar ta gaidashi shima kuma ya amsa da kyar,batareda yakuma bi ta kanta ba yayi hanyar gawon nama, inda zai sayi fruit din momy bayan ya siyane ya wuce,Agg mall yasiyo popcorn da kuma ice cream sannan ya dauki hanyar Abj road gida kenan,bude robar popcorn dinshi yayi ya fara ci yana bin wakar doro bucci best wakarshi har andaina yayinta amma be daina siyantaba,kallonshi tayi cikin mamaki ganin be mata tayiba gashi tasan halin yaa ghailan da mugun tsare gida Allah ya gani kuma ranta yabiya,shagwabewa tayi tace dashi " yaa ghailan zanci popcorn din plss" ko kallonta beyiba har suka isa gida wannan abun ya mugun Kular da ita aranta tace wlhy siyisa na tsani yaa ghailan nafison yaa Adnan yafishi mutunci shi kullum baya dariya kuma idan kamai magana baya kula ka sai wani jiji dakai shi ala dole babba,tsoki taja adaidai lokacin datake shirin bude kofar motar ta fita janyo hannunta yayi tajuyo jiki na Bari domin tasan hali shibaya duka amma fa yanzunnan saiya sakaka tsallen kwado kokuma jumping narai narai tayi da ido ganin ya had'a fuska kuma yaqi ya sake mata hannu,murya na rawa ta furta "yaa ghailan I'm sorry wlhy badakai nakeyiba malaminmu na tuna daya dakeni d'azu" kuramata ido yayi baice kanzil ba kawaidae ya saka hannunshi daya abayan motar ne ya ciro leda daukeda popcorn da kuma ice cream yace da ita "ungo naki jeki,kuma idan kinje kiyi sallar azahar lokaci ya shige" godiya tamai a kinyace tabar cikin motar aranta tace yaa ghailan akwai jan aji da masifaffen miskilancin tsiya...
Wando ne fari sanye ajikinta iya gwiwa da kuma riga pink karamar top wacce ta d'meta tsam sai gintun gashinta datayi parking a tsakiyar kanta yake yawo tamkar jelar bunsuru saboda rashin tsawo ga ba yawa samsam sai tsantsi da kuma baki wulik,bazamuce jawaheer batada kyau ba haka kuma bazamuce tanada muniba kowanne bangare tana tabawa saidai akwai yalwar kugu domin kuwa kai bakaga jawaheer ka yadda yar shekara sha shida keda wannan mazaunan ba samsam,kare mata kallo yayi harga Allah yaji wani iri gameda ita dukkuwa da yake yasan jawaheer kanwarshi kauda kanshi yayi dayake ita batamasan yana wurinba a fusace ya furta
" jawa kinsan Allah ko,kinsan bana duka amma wannan karon tsinannen duka zan miki akan wannan shigar dakikeyi yarinya saikace wacce ta tashi a turai ke bakisan kin girma bane maza kitashi Kije ki dauko kayan kwari ki saka kuma daganan ki dauko litattafanki zamuyi kara2 kinkusa fara waek kina bata lokacin ki akan kallo" zumbura baki tayi ta tashi tana kunkuni hadda doka kafanta akasa wai ita adole auta haushi sosai tabashi rashin kunyar jawa yayi yawa shiya rasa wayake koya mata wannan dabi'un banzar,dawowa tayi sanye da wata dress ta material me roba dukkanin ilahirin surar jikinta abayyane yake sai yanzu yayi danasanin cewar dayayi ta sauya kaya domin wayannann sunfi na farko muni dauke kanshi yayi daga kallonta yace da ita " zauna kijirani ina zuwa kuma idan kika kuskura kika kunna kallon nan kan in dawo Nida ke ne " tsaki tayi kasa kasa tace " mugu kawai Allah ya isa shiyasa bama kama wata kilama dan tsintuwa ne kalleshi da jar fata saikace haihuwar jan kunne" juyowa yayi yace " mekikace jawa?" Wayan cewa tayi tana dariya tace " cewa nayi yaa ghailan kafiya takura wlhy series dinnan danake kallo anwuceni kenan fa yanzu dan annabi ka barni na karasa kan ka dawo" kallonta yayi ya murmusa gabantane yafadi domin kuwa tasan duk sanda yaa ghailan yayi murmushi toko muguntace zata biyo baya....
_Edited by Billy Galadanchi_
By fiyyah
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞💞Almajirina!💞💞
💞 💞
_Written by Sofiyyah Galadanchi_
In dedication to sha'awa Ebrahim
02
Kallon mamaki ya tsaya yana mata ganin ta kunna Waka a wayar ta ta daddage sai cashewa takeyi tamkar ba agida takeba batamasan da zuwanshi ba ,gyaran murya yayi amma bata jishiba dauko caja yayi ya zo tabayanta ya tsula mata daya rikicewa tayi domin jawa akwai tsoron bulala da gudunta tafada jikinshi ta rungume shi wai hakuri take bashi " yaa ghailan dan Allah karufamun asiri wlhy na daina bazan kumaba" galala yayi yana kallon yanda ta kankameshi haushi duk ya gama cikashi daka mata tsawa yayi ta sake shi da gudu ta haye saman benen tana kuka tamkar wacce aka yanka karo tayi da yaa Adnan
"Ke lapiya meye haka me aka miki kike kuka?"
"Bayan yaa ghailan ne saboda kawai ina rawa ya dakeni kuma ina bashi hakuri ya dakan tsawa kad'an yarage nayi fitsari a wando" dariya sosai yayi yace
"Allah ya shirye ki jawa,kina girma kina cin kasa" kara fashewa tayi da kuka "Allah yaa Adnan kaima yanzu bakasona kaman yaa ghailan, duk kunbi kun takura ni nikadaice bakwaso, friends dina kowa yayyinsu naji dasu" mangareta yayi yace " kyadaiji dashi mara kunya" ihun kuka ta saka tamkar wacce aka yanka tawuce dakin momy tana kuka.
*****
Kwance yake dagashi sai boxer iya gwiwa da yar karamar singlet ajikinshi, aka turo kofar dakin aka shigo da sallama mikewa yayi hade da ansa sallamar a lokaci daya banin momyce
"Sannu momy lapiya dai kika shigo da kanki baki mun waya nazoba" wani kallo tamishi tana murmushin dake kara bayyanarda kyawun fuskarta sannan cikin tafi yar dabai Santa da itaba ta karaso dakin ta nemi kujera ta zauna galala ya saki baki yana kallon wannan sabon sauyin juyowa yayi shima yanemi wuri ya zauna
"Shalele yau duk sai kaji daban ko gidan ba kowa sai mu biyu kadai" murmushi yayi yace
"Allah kuwan momy ba dadi kamar kin gane banji dadin tafiya service dinna da Adnan yayi ya barni ni kadai ba sai naji gidan shiru" dariya tayi har wushiryar ta ta bayyana lokaci daya kuma gefen kuma tunta ya lotsa domin kuwa haj Saratu badai kyauba danma duka yayan ta ghailan ne kadai ke kamata da ita duk kansu margayi mahaifinsu suka biyo, sannan ta furta
"Nikuwa shalele kaga nafijin dadin hakan saboda inason kasancewa dagani sai kai ka iya hira sosai tun kana karaminka" shimadin dariya yayi daganan yaji kiran sallah kan tace wani Abu ya juya ya zura jallabiya a gurguje yace da ita " momy zanje na dauko jawaheer school lokacin tashi yayi zan tsaya masallacin kofar gida nayi sallah,batare da yajira ta cewartaba ya juya aranshi yana tunanin sauye sayen abubuwa da yawa daga wurin momy ya kasa gane inda ta dosa....murmushi tayi ta mike tace shalele baka gajiya da hidimar jawaheer kamar Kaine ka haifeta koda yake kakusa zama ubanta🙄😳😳
Abakin gate ya haduda mutuniyar hijabinta duk a yage tayi duku duku duk gayun jawa,kallon ta yayi sannan ya bude mota ya fito ya zo kusa da ita " ke meye haka? Meya sameki da kika dawo tamkar wacce aka karbo daga bakin kura?" Kuka tasamai sai kawartace tace dashi " wani malaminmu ta zaga agaban y'ay'anshi shine suka mata dukan tsiya yanzunannan suka wuce" dariya taso kwace mai domin yasan halin jawa da neman tsokana saiya kanne yace "meya faru har ta zagi baban nasu" kawar tata uwar kaifice tace " waifa sune suka zageka sukace dakai kafita daban agidanku kacika jiji dakai kake kuma fama da....saikuma takasa karasawa " enhmm fama dame?" Jawa ce ta karbe zancen
"Wai cewa sukayi kana fama da kunnaye tamkar makarantar zomaye da farin fata sai kace zabiya,Arwa
Har cewa tayi wai kadan ne bakazo azabiyan ba kana shawa mutane kanshi nikuwa nace kafi karfinsune kuma fa kawai cewa nayi kafi ubansu me dattin hula da faso akafa " dakyar ya iya gintse dariyar,yamusu fada akan zagin mutane yace koda anzagesu su daina ramawa mutum kansa ya zaga ahanya momy tamishi waya wai yayi sauri tafara kewarshi😳🙄.
_Edited by Billy Galadanchi_
Fiyyah Galadanchi
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞💞Almajirina!💞💞
_written by sofiyyah galadanchi_
_I dedicate this page to all d single ladys (gauraye)of ummyjay&maman nu'aym novel group_...😂😛
03
Shiru yayi a motar tunane fal aransa momy ta sauya Allah kasa abinda nake tunani ba haka bane ya Allah ...jawa ce takatse masa tunani domin kuwa baisanma tazoba saiji yayi tace
"Yaa ghailan " kallonta yayi tawashe hakora bata jira masrshiba tace "kasan me mukayi yau a school nida kawayena?" yace "taya zansani Saikin gayamun"
"antynmu me daukarmu physics tasa mini skirt baka gantaba katuwa skirt dinma ya yage ta baya,ingayamaka tayi tuntub'e tasha kasa skirt ya rabe biyu ta baya baga ganiba d'uwawu duk a titi,malamnmu sauran duk sun ganta su Arwa sai gulmanta sukeyi wai kalan pant dinta pink kuma ma ya mata kadan tsabar katon d'uwawu niko nace baruwana karkaji kamun duka😳
Shiru yayi ya kyaleta yace shigo muje kinji anyi sallar azahar kina girma kina cin kasa. "yaya yau uncle dinmu me maths yasa riga armless naga hammatanshi duk gashi kuma baka gani gashin duk yayi datti ya dawo brown, yaya kaima kanada shi?? Allah dai yasa kana wanke naka karka zama kazami irin uncle honesty me dattin armpit,dariya yasoyi amma saiya danneta sbd yagano jawa mahaukaciyar kuruciya gareta tsab Zatayima terere yakamata yariqe takunsa karyarinyarnan taga wurin kwanansa duk garinnan se anji
Fuska bafara'a yakalleta jawa idan baki kamamin bakinkiba wlhy zantsaya anan inzaneki yarinya ss2 amma ba wayau,siyisa nace momy tabarki kiyi ss3 tace wai yanzu zaki zana waec kinada girman jiki kebakisan kin fara girma bane kike shashanci??
"wlhy yayannan kacika masifa shiyasa yarannan suka zageka"..."mekikace" ya tamabaya yana harararta "cewa nayi na daina karkamun bulala plss" karma kidaina kiga inban fasa bakinki ba" shiru tayi sai can takuma cewa "yaa ghailan birthday na on 17 dis month kuma kaga yaa Adnan keji dani gashi bayanan plss kamun princess cake dana Dora" kallonta yayi shi yanzu dariya ma tabashi wai Dora er 16 years ke maganar Dora " ke yanzu dalleliyar k'atuuwa dake ke maganar dora dawani princess cake harkar yarane fa" kallonshi tayi tace "gaskiya yaa ghailan kai bakauyene yanzu saboda Allah ni zaka kalla kace nawuce dora waini katuwace wlhy a class k'awata muneeba ta gayamun yanzune nake girma saboda yanzu zanyi 16 itakuwa tana 18 wai sunyi breakup da boyfriend d'inta yace tafara zama katuwa shi swt 16 yakeso" baikuma bi takantaba damashi bai fiyason magana ba aranshi yace gwara ma kizana waec din naga alama k'awaye nason rikitamiki kwakwalwa.
Sun isa gida tunkan yakarasa parking tabude mota taruga kadan yaragema ta fadi tsabar hauka shi sedama ya tsorata girgiza kai yayi akwai aiki, wannan yarinyar inaga bazata rasa mutanen boye ba
Tundaga kofar palo ta jefar da jaka takalmi, sucks ma akan stairs ta jefar yana shigowa yai tun tube da jakar tsaki yayi ya fara kwashe kayan da dai dai yabi bayanta dasu dakinta ya nufa koda yashiga ta tube daga ita se shime da wandon uniform tanata famar mita tana zagin yayan uncle dinsu dasuka sauya mata kamanni bece komaiba ya ajiyemata kayan daga gefe ya wuce...
****"har kundawo shalele"momy tace datagansa yana saukowa daga sama yashigo palo "eh momy jawa nakaiwa kayanta daki daga shigowa tahau zubardasu apalo, "ai lamarin jawa se addua ko ganinta ma banyiba ....zo kaci abinci gashichan dinning" kallonta yayi ya sosa keya "senayi wanka yafada yaname cigaba da tafiya " to ai ba ruwan zafi kaci abincin idan mungama saina daura maka ruwan zafi😳😳🤔,kallonta yayi da alamar tuhuma lokaci d'aya ya had'a fuska yace " momy ruwan zafin kuma saikin doramun,kin manta mu toilet heater din dakinmu na aiki bari kawai naje nayi wankan kici abincin kawai" taga alamar sauyawar da fuskarshi tayi aranta tace wannan yaron inaga nayi saurin nuna kaina awurinshi wannnnn ne yasanya tace " kaje kayi wanka bari naci kawai"
**** ......nida nake tsaye inaso tafadi abinda keranta domin na zayyanowa gaurayen gidan Ummeejay amma sedai naga tana kada kai nace hmmmm ajuri zuwa rafi...
*****yadade a toilet yana tunani tabbas da alama momy naso tabijiro da sabon al'amari yaga taketakenta tanaso tarabashi ta farin ciki kwata kwata arayuwa wata kila wannan ne yasanya ta....wai🤐 arufe kashi aci tuwo🤗
*****
Dayamma misalin karfe 5:57 yafito zashi wurin abokinshi sadeeq yahango jawa tana dambe da wata kuma ga dukkan alamu tajigata dafe kansa yayi yakarasa wurin seji yayi jawa tana fadin "wayyo sulaimi muyi hakuri mubar dambennan kinga mungaji kuma anqi arabamu😂😂😂😂😂"
Nace wannan fadanfa kamar fadan maman nu'aym da machioma 😄😄😄😄
****dakyar da sudin goshi yakwaci jawa hannun sulaimi sbd sulaimi akwai💪💪💪
Ya kwashi kayanta yajata suka shiga mota sadeeq najiranshi sbd haka seyawuce da jawa betsaya maida ita gida ba kuma yasan indai yabarta takarasa gd dakanta to kobasu sake fada da sulaimi base tayi da wani fadannan dai dabata tabacin ribaba,
amota yakalleta baki ya kumbure mata suntum sbd sulaimi bakaramin bugu tai masa ba ya kwashe da dariya har suka isa gdnsu sadeeq daga ya kalleta sedariya taso kwace masa amma saiya danne donkar tarainasa ....
sun shiga gdn suka gaisheda maman sadeeq ta amsa tana kallon jawa kana tajuyo ta tambayi ghailan, "meya same ta haka dukta hargitse" yace "mama dambe tayi shine naganta ahanya na taho da ita sadeeq dake fitowa daga dakinsa yakalli jawa aise daria take ta fashe dakuka dakyar aka lallasheta tayi shiru tace "mama plss kicce yaa sadeeq yadaina mun dariya kuma yaya ghailan yabiyani farata daya jefar"
..."yaushe na jefar miki banason karya wlhy" kana kallo tafadi dagacikin jakata kaki sakeni nadauko kuma seka biyani "..seda mama tasa baki kafin tayi shiru tadaina mita akan fararta ....shidai sadeeq yajashi sukabar ta inda mama tunda kanwarsa islamiyarsu se bayani isha I suke tashi.
_edited by billy galadanchi_
😍😍sofiyya galadanchi💋
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞💞Almajirina!💞💞
_Written by Sofiyyah Galadanchi_
_in dedication to sha'awa Ebrahim_
04
Kwace momy take kan mamakeken gadonta tunani dukya addabeta ita kanta tasan cewar abinda take shirin yi bamai kyauba bena amma sam bazata iya hakura da kudirinta amma yanzu da matsala dolenta ta d'age kafa zuwa wani lokacin sallamar ghailan ne ya datse mata tunaninta ta kalleshi da fuska tamau ta ansa sallamarshi yashigo ya gaidata yanemi wuri ya zauna tashi tayi zaune tace dashi " menene kuma bangaya muku kudaina shigo mun daki idan 9 na dare yayiba banason rashin jifa ghailan,Kaine babba kai zanmutu nabar tarbiyar kanenka a hannunka amma saiya kasace bakajin maga nata Allah zan bata maka rai" amaimakon yaji haushin fad'an sai wani sanyi yaji aranshi kasancewar momy ta dawo itadin ta asali sai yanzu hankalinshi ya kwanta domin kuwa harya fara tunanin mafita langabe kai yayi yace
"I'm sorry momy wlhy bansan lokaci yaje hakaba bacci ya daukeni ina idar da sallar magrib ko isha ma yanzu nayi nazaci karfe 8 " kwafa tayi tace "kaje kaci gaba da wasa da salla wlhy nida kaine zakuma ka gane kurenka akan wannan ace bazayi jam'i ba kana name ji " sadda kanshi yayi kasa yabata hakuri sannan yace " momy dama nazone akan inaso inje silame gobe " kallonshi tayi sannan tace "lallaikam ka isarwa kanka wato shalele nunamun ka isa dama banice dakaina nake tsara muku tafiya silame ba sai yanzu dan gulma dududu kwanan Adnan sha shida da tafiya kuma ana gobe ze tafi kukaje dan Allah idan bakada abin fada tashi kabani wuri" rokarta yashigayi dakyar ta amince amma tace saibayan birthday din auta da kwana biyu.
Zaune yake a parlor din sama yana kallon wani series me suna Conqueror wani Korean series ne ya hadu jawaheer tazo ta zauna kusa dashi tace " yaa ghailan kafiya wayau kai kana kallo nikuma saikana hanani Allah yasa a dauke wuta,kuma solar yaqi kawowa gen ma yaqi tashi inga ta tsiyar " kallonta yayi shi rashin kunya irin ta jawa mamaki sosai take bashi da kuruciya komai zata fada ba ruwanta ,baice da ita komaiba ya maida dubanshi zuwaga TV yaci gaba da kallon da yake,tsaki taja tace
"Yaa ghailan ka tayani adua Allah ya bani saurayi nima k'awayena kowa tanada saurayi banda ni,kullum suna labarin saurayinsu wasu biyu ma daga ciki aurensu damun zana waec akace Allah abin namun zafi" kallon mamaki ya mata yace " ke inake ina saurayi yanzu banda hakama kisani wlhy idan naganki da saurayi saikinci duka" kallon raini ta wurga mai tace " toni idan banyi saurayiba Kaine zaka aure ni? Nifa aurena zanyi ba abinda yake burgeni irin nawa mijina girki inga kayan gida ace duk nawane,baka ganin agidanna kullum da mug d'aya nakeshan tea,amma idan nayi auenafa mug talatin duk na wane " kallonta yayi tabashi dariya ya gimtse yace "naji tashi Kije" matso wa tayi kusa dashi tace
"Yaa ghailan kaga idona ya kumbura koka tambayeni meya faru dani " juyowa yayi ya kalli idon nata yace "aikam dai sun kumbura saidai gaskiya bazanma tambayaba nasan dambe kika yi" hawayene yafara zarya akan idonta tace dashi " Bayan wata Atika ce a class d'inmu wai tana sonka kai zata aura nikuwa naji haushi nayita kuka a class kaga ko yanzu bacci nakasa sai haushi nakeji datace tana son ka shine nazo inyi kallo kazan rage jin zafi anan d'ina" ta nuna zuciyarta kura mata ido yayi yace
"Kedanma kinsamu ance anason yayanki meye abin kuka aciki nikam nasamu matana Atika tunkan inganta naji inasonta plss kikaini gobe na ganta" kura mai ido tayi na wasu seconds sannan ta juya da gudu tana kuka tawuce dakinta ta kwanta.
Washe gari har 8 yaga bata fito ya kaita skull ba gashi yanaso ya ajiyeta yazo yayi bacci saikawai yaje dakinta. A kwance ya tadda ita batama yi wankaba da alama kallon mamaki yamata lokaci daya tabashi haushi yace da ita " ke wannan wane irin eskancine bazaki tashi ki shirya muje nakaiki skull ba,banza tamai sanda ya ciro caja din dake manne ajikin sucket kallonshi tayi da sauri ta mike tsaye
"Allah yau ko zaka kasheni bazani skull dinba bayan kaikace zakaje gaka Atika nikuwa baran kuma zuwa makarantarba saidai kaje kaika dai ka ganta" jefar da bulala yayi yazo yajanyo hannunta yace " kiyi hakuri nifa wasa nake miki mezanyi da wata Atika nida nakeda matana already " da sauri ta kalleshi " kanada mata da gaske yaa ghailan ?" Takuma fashewa da kuka mamakinshi yakasa boyuwa me wannan yarinyar keyi haka saiyace " wasa nake mikifa zoki saka uniform nakaiki skull" gajiyar zuciya tayi tace
"Nagode jeka yanzu zan sakko muje"
Fitowa yayi jiki ba kwari yace ina matukar kaunarki jawa,Allah ya shirye ki yasanya kiyi hankali.
_Edited by Billy Galadanchi_
By Sofiyyah Galadanchi
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞💞Almajirina💞💞
_by sofiyyah galadanchi_
I dedicate this page to those who belong to kitchen,living room and other room🤗 .
05
A palo yazauna yanajiranta amma idonsa nakan TV da ake newa a aljazeera zahiri idonsa na chan amma zuciyarsa ba'acan takeba bayama fahimtar mesuke fada bayan kamar 15 mnts segata tafito hijab ahannu "yaa ghailan mutafi yau nayi saurin shiryawa ko??"taji shuru seda tadan tabashi yadawo daga duniyar tunani bece komaiba ya mike yafara tafiya tabi bayansa suka fice...
mota ma ita kadai take surutunta yakyaleta yana ajiyeta yakoma gd tashiga class dinsu tazauna kujerarsu suka fara hira itada kawarta rufaida.. Malamin dayake daukarsu biology ne yashigo(Wanda yayansa suka mata duka)yafara abinda yakawoshi bayan dalibai sungaishi...
*****note yake amma sam su jawa basayi sema kallon pics dasuke awayar rufaida kwatakwaticaly sunmanta da inda suke seji sukayi ana buga desk dinsu afirgice suka dago yamiqa hannu agigice rufaida dake riqedawayar tamiqa masa sedayaduba yaga pics sukekallo bece komaiba yasa wayar a Aljihu yakoma kan aikinsa
bayan yagama aikinsa yace subiyoshi staff room,hada girar sama data kasa yayi yace cikin tsawa
"Who's d owner of ds phone among u?" Rufaidace tace cikin murya kasa kasa
"Its mine sir"
"Then why did bring it to school ???"
Shiru tayi don babu dalili..kuramata ido yayi na en seconds
Kafinyace "since u have nothing to say lemme give d 2 of u dis "yafada tareda zaro dorina yabasu bulala biyar biyar ...harsun juya zasu fice jawa ta jiyo
"sir wat about d phone ??"
" get out "yafada atsawace suka tafi da gudunsu dansunsan halinsa yanzunnan ze karamusu wani bulalan...
*****suna shiga class jawa tayi wurin ersa arwa ..."ke arwa yau babanku ya taro match don wlhy yau in akatashi daga skul sekun bambamce tsakanin aya da tsakuwa dagake har kannanki masu kamada zombies" murmushin mugunta arwa tayi tace
"Jawaheer kenan dagani saike yau zanga wanda zebambance aya da tsakuwar muhadu abayan classes din en ss 1 abuga ta" ..nikuma jikar Fatima ina gefe nace wayyo yauma inaga yaya ghailan baze ganefuskarkiba🤕🤕🤕🤕
*****bayan antashi daga skull suka wuce filin daga😬rufaida dai daga cikin classes din tashiga tana kallonsu ta window don itakam bazata iya dambeba
Abinda jawa batasani ba duka yayan malamin sun hadu tana zuwa suka zaro bulalar dasuka tsinko daga icen long boy kafin tace komai suka hau tsula mata arwa itace riqe da ita basu bartaba seda sukaga jini ajikin hijab dinta kafin arwa tasaketa tahadamata da punch a ido ...rufaida dake chan tanakallo agigice tadiro daga kan window ta janyo jawa da har hancinta jini yake .....eyyah it's a pity jawa😔
*****ashe bakin bemutuba nafada lkcn danaji jawa takira sunan arwa ..."kunmin taron dangi amma bakisan balai ba idan me warin bakinnan bekawo wayarnan ba ko hmm basena karasaba"
ghailan dahar yagaji dajiranta yabiyo sawunta yaje class dinsu arufe yajuyo yanan tunanin ina yarinyarnan tashiga kafin yakarasa tunanin yahangosu rufaida riqe da ita tayi jinajina...wata sabuwa yaukuma dawa tayi fada..itakuma jikinta dukba karfi har wani zazzabi takejin yana taso mata ..
****yakarasa kusadasu hadeda riqo hannun jawa yanda tambayar meyasaki harda jini a hijab dinki rufaida ce ta labartamasa abinda yafaru from A to Z yajinjinakai yadauketa kamar jaririya yasata mota ...
****ransa ya matukar sosuwa Dan ganin jikin jawa yayi ja sbd tanada er farar fatarta yafara fada yanacewa seyaga waya tsayawa wayannan yaran suke dukanta haka kamar jaka momy kam yabata mamaki ganin yadda yaketa masifa fuskarsa hartayi ja tsabar masifa tahango wani Abu acikin idonsa Wanda batasan dawace kalma zata kira abinba..
*****dakinta takoma bayan tasamu jawa taci abinci kadan tasha magani tunani tashigayi yarn nan sunason junansu ji yanda shalele ke huci an taba auta kuma koshi yasan batada gaskiya Allah yasanya kuci gaba da kaunar junanku har abada.
Ah...jawa will never give up.
Fatana jawaheer tacigaba da tsokana tanashan duka😛😛😛😛b
_Edited by billy galadanchi_
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞Almajirina💞
_written by sofiyya galadanchi_
_this page is for u mom cyama,thanks for ur love😍😍😍_
06
Shirye2 birthday din jawa ake babu kakkautawa komai antsara shiyadda yakamata domin gobe ne Saturday za ayi celebrating din birthday a gida zasuyi shi sbd babban gidane momy ta gayyato yayan en uwa da yan uwan da suke kusa sbd birthday din gudar autar ta ga uwar gayyar ta kwaso abokanai ba adadi
_washe gari (ranar birthday din kenan)_
OMG!!!!
I just can't believe this is just a small birthday party🤗 sbd gurin yasha decoration thee green and white color,cake kala biyu nagani akan wani table dashima yasha decoration ya Salam! Aikin yaya ghailan yasa akayima princeess cake da na Dora datace tanaso
Goge idona nayi dan natabbatar da jawa ce nake hangowa ya ilahi!wata gown ce ajikinta seagreen da head white bawani heavy makeup tayiba amma tsayawa fadar kalan kyan datayi bata lkcne yaya ghailan ma ya hadu iya haduwa ash suit yasaka ga kayan sunyi fitting dinsa hakan ya kara bayyanar da kyansa Wanda bazan iya cemuku ga yadda yakeba,sai murmushi yakeyi wanda ke nuna tsantsar farin cikin dayake ciki.
Kowa dai yaci ado nagani afada cah nahango ummeejay ,ummeekhaleel,da Sha'awa suna Harar cake sarai Nagano sosuke sudan laqato butter cream din jikin cake din sulasa sbd basuda dangana😜😜
Abin mamaki arwa nagani da atika suma ashe jawa ta gayyatosu,in takaicemuku batu birthday paty din yatsaru sbd kowa ya gwangwaje awurin
Ummeejay dai seda ta tsaya aka yanka cake aka sammata sbd su jidda(daughter)har sungaji dajiranta sun fara tafiya juyawar da zanyi nahango hamagee ta kutsakai seda tayago kilishin hankalinta ya kwanta😂😂
Yaya ghailan yana tsaye yagama waya da sadeeq kan yazo yadaukeshi sufita bayan ishai sbd yagaji baze iya driving ba
"Yaya inawuni" "lpy " yafada kafin yadago yaga wacce tagaidashi,kallon rashin sani ya bitadashi baikoma cewa komai ba rausayar dakai tayi tace cikin yanga "yaya dama naga zamu wucene nace Bari nagaida babban yaya kafin na wuce" murmushin karfin hali ya qaqalo "nagode" yafada yanacigaba da danna wayarsa yayi minti biyu ahaka yaji kamar ana kallonsa yadago yaganta tsaye a wulaknce yace da ita "kinada Matsala ne?" hakan yayi daidai dakarasowar jawa wurin seji yayi anjashi dakarfi bata tsaya ko inaba se bayan gdn kawai seta samishi kuka "yaa ghailan bakai kace bazaka kula waccen atikar datace tanasonkaba shine yanzu kuka koma gefe kuna tadi ko" tana maganar ne duk acikin kuka
"haba jawa ni wlhy harkin tsoratani nifa batadi mukeba infact nibanma San wacece itaba kawai zuwa tayi tanayimin salo da iyay" tsaki tayi tace
"To basaika zabgeta da mariba?" Dariya sosai yayi yayi ta rarrashinta
Dahaka har yasamo kanta suka koma gurin mutane akaci gaba da sallama domin magriba ta gabato dan haka kowa ya watse sedai fatan Allah ya albarkaci shekarun jawa Ameen.
Washe gari dasafe tafito tanufi dakin momy dan tanunamata gift din rufaida agogone me kyau da tsada dakuma chocale kalabiyu masu dadi😋,saikuwa na sha'awa data kawo hankici sai masifa takeyi wai tarainata,zata kwankwasa ne taji momy na waya dakawarta hajiya Hindu "
"wlhy gamunandai dagani se jawa da ghailan danma ghailan yananan yanaragemin kadaici tunda nayi retire banazuwa ko ina sebayan kwana biyu nake zuwa company naga ya ake ciki,dama jira nake Adnan ya kammala service dinnan ya dawo inyaso namika musu ragamar company din,tadan yi shiru saican takuma cewa
"gsky kam yaron Nada hankali yanayimin biyyaya kamar dan danahaifa dacikina,nima kuma duk abinda yakeso inayimasa wlhy kuma bamai gane cewar shid'in *Almajirinane* ko yanzu yanaso yaje yagaida iyayensa nace yabari sai bayan bikin jawa na birthday inaga gobe zai tafi,shiru takumayi alamar tana sauraren d'ayan bangaren daganan takuma cewa
"Shida Adnan sunsan cewa shid'in *Almajirinane*amma jawaheer bata saniba hakan yafi saita mallaki hankalin kanta tukun" jikin jawa yafara rawa takoma dabaya dabaya tana girgixa kai take tafara hawaye tayi dakinta da gudu...
_eyyah ghailan abin tausayi harnafara kuka_😭😭😭😜
_edited by billy galadanchi_
💞feeyah💞
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞💞Almajirina💞💞
_written by sofiyyah galadanchi_
_this page is for you guys jidda(daughter),Hamagee,Amenatou._
Jawa tahado masa duka abincin a tray kamar mijinta lol😀 "yaya gashi nan adaki zankaima ko anan zakaci?"
mamaki yakamashi sekawai yabata rai donkar ta rainashi,yace da dakakkiyar murya "ajiye anan kallo zanyi"
Kunnenshi yaji yana rawa alamar girkin yakarbu kenan yaushe yarinyarnan ta iya girki haka duk rashin nutsuwar nan ta jawa lallai momy uwace ta gari hakika yana godia ga Allah dayasa takasance mariqiyarsa sbd sun samu ishashshiya tarbiya dazasu iya zama dakoma waye kuma bata nuna banbanchi tsakaninsa da yayanta (kira garemu mu iyaye mata kusani tarbiyar ayayayenku tana hannunku koda bakekika haife shiba to ki riqeshi amana bakisan me gobe zata haifarba watarana kema yayanki ahannun wasu zasu zauna
Koda da wata niyyar kika riqe yaro to yasamu tarbiya kyakkyawa daga gurinki wata kila yazamo meceto agareki. Allah yabamu ikon tarbiyatar da yayanmu da wayanda muka riqa bisa addinin musulunci dakuma sunnar manzo Allah s.a.w.Ameen)
"Yaya kafa cinye tundazu me kake tunani?" jawaheer tafada tana masa wani kallo dayake hango wani wani abu aciki daure fuska yayi bece komai ba
Kamar daga sama suka jiyo muryar momy
"Shalele yaushe kadawo kaida kace zaka wuni shine kaje kayi har sati daya" magana takeyi da fada "kuma tsabar kanunamin ban isaba seka kashe wayoyinka ko?"
Langwabe kai yashiga sosa keya
"Momy kiyi hkr kinsan ba network din MTN achan sekafita bayan gari kuma ba wuta agarin tunda naje ba wuta har na dawo kuma nasamu baba bashida lpy shiyasa nayi kwana biyu har yadan samu sauki" "bazakje bayan garin kayi kiranaba kafadamin ??na lura da sabon salon daka tsiro dashi bakason zama gida yayi maka kyau nida Kaine a gidannan" "momy don Allah kiyi hakuri" batareda ta amsaba tamiqe zata ficee"haba momy kiyi hakuri mana tunda yafadami.......jawaheer wlhy banason ina magana yara suna samin baki a magana sa'arki ceni kinji narantse hakan zesa namiki dan Karen duka" baki asake jawa da yaa ghailan ke kallonta har tabacewa ganinsu shikam kara hade fuska yayi hadi damiqewa yaidakinsa yana mamakin yau momy ce ke fada haka lallai ya aikata babban laifi
Haka suka wuni momy na fushi dasu jawaheer dabazata iya kama bakinta ba seda tabi momy daki tana bata hakuri batasan dalilin dayasa taji ranta ya bala'in sosuwa ba dan momy na fushi da yaya ghailan akarshedai bataci ribaba dan momy seda ta daka mata duka abaya tafice tana kuka
Dakin yaya ghailan tanufa ta sameshi yakwanta a rigingine yana kallon silin da Alama tunani yake "yaya kaga momy ta dakeni kawai dan naje inabata hakuri " kallonta yayi cikin kulawa yace
"yi hakuri mana jawa tunda dai ba fada zan mata ko na rama mikiba" yaa ghailan yafada daga kwancen dayake
"yaya dubafa kilama shatin yatsunta ya kwanta min abaya"tayi magana duk acikin kuka tana kokarin zuge zip din rigarta
"waike wace irin shashace"yafada atsawace ganin zatayi tsirara agabansa "bakisan kin girmaba kike Abu kamar wata ballagaza dalla ni ficemin daga daki"
Fuuuuuuu tafice tana kara sautin kukanta
Kukan yanataba zuciyarsa amma bazai bari ta rainashiba bayanzu ba seta kara hankali
Tayi 20 mnts tana kuka dan azahirin gsky bazata iya tuna when last momy ta daketaba
Fushi tadauka dashi sbd yamata wulakanci
Da darema tafito cin abinci taganshi zaune a dinnin ko kallonsa batayiba ta debi abincinta takoma daki da mamaki yake kallonta amma yaso yayi daria ganin yadda tadauke kanta tana tafiya dasuri dasauri
Azuci yace tafara rainani tun abin bekai ko inaba
Washe gari daze kaita school ma daga gaisuwa ba abinda yasake hadasu haryakaita xata fita daga motar yakira sunanta yamika mata Dari biyar
"kihau adedeta kikoma gd in antashi zamu fita da sadeeq ne bansan yaushe zamu dawoba karkiyita jira banzo ba Tou kawai tace tafita daga mortar
Rufaida bansan menake jiba gameda yaa ghailan, idan baya kusadani senaji ba dadi idan naganshi wani sanyi nakeji araina muryarsa kuwa har wani yanayi me wuyar fassara take sani narasa gane menene yake damuna shikuma yanzu yarage sakemin fuska yakuma dan wulakanci kan zefita tare dayaya sadeek kudi yaban nahau adedeta amma da komai yake ajiyeshi yake yakawoni kuma yadawo daukana.Nisawa rufy tayi sannan tace
A gsky jawaheer u ar in *LOVE*
Afirgice ta kalli rufaida,ta furta "Bangane I'm in love ba? With who?" Dariya sosai Rufaida tamata sannan tace
"Allah jawa son yaa ghailan kikeyi kuma ya kamata ki rike takun ki matsayin ki na mace kisan yanda zakiyi Karya ganoki kawai dai kici gaba da yin abubuwa na nutsuwa yanda zakija hankalinshi zuwa gareki, domin agaskiya kincika wauta,namiji kuwa bazaiso mace hakaba, na dade da gano son yayan naki kikeyi nayi shiru ne saboda nazaci shirmena nakeyi azatona mamanku daya" mutuwar zaune jawa tayi takasa furta komai.
_edited by billy galadanchi_
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞Almajirina💞
_by sofiyyah galadanchi_
_in dedication to Anty billy my luvly sister ever(maman nu'aym)thankyou for taken good care of my son *Nu'aiym*_❤
07
Kan gado tafada tareda sakin wani kalar kuka wanda dagajinsa kasan tundaga cikin zuciyarta yake fita tayi kuka harta koshi take wani tausayinsa ya dirar mata hadi dawani abu datakejinshi daga gefen xuciyarta dabatasan meyeshiba
Dakyar ta tashi tai wanka duk yunwar datakeji kasancin komai tayi sbd wani bakon abu daya ziyarceta.
Mommy kam nadakinta batasan meke faruwa tana gama waya da hjy Hindu takwanta tayi bacci se azahar tatashi tredayin sallah azuciyarta tace
"yaufa banga autaba nasan tanachan tana baccin gajiya dama gata raguwa " mikewa tayi tareda nufar dakin jawa akan sallaya ta sameta tagama sallah hakan yasa tashiga tazauna bakin gado tanajiran jawa tagama addua, bayan ta kammala tace"mommy ina wuni"
"lpy l....bata karasaba sakamakon ganin fuskar jawa takumbura alamar tayi kuka kenan "auta meyasameki ??waya tabaminke? Bakida lpy ne? Ina kemiki ciwo?duk tambayoyinnan ajere tayisu Wanda ko data jawa bata amsaba illama sabon kuka data soma cikin wata dasasshiyar murya wacce seka kashe kunneanka zakaji metake cewa ta furta "momy dama bake kika haifi yaa ghailan ba"??"harda yaya adnan kin sanar masa amma ni bansaniba nikadai ce kika boyewa" ??momy kam mutuwar zaune tayi tana tunanin a ina auta tajiyo wannan lbrn tab..akwai matsala bekamata tasan wannan yanzu ba amma zatayimata dabara irinta manya,jin datayi momy tayi shiru taci gaba
"momy *Almajirinkine*wayyo Allah yaa ghailan dina ashe kaidin bajinina bane"
"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un momy ketafada azuci jin jawa tasan ghailan *Almajirintane*
"Jawaheer yi hkr kinji auta"
"bawani hkri dazanyi momy nikifadamin yadda akayi" atake dabara ta fado mata "auta zakisan komai amma ba yanxuba kibari se yayanki yadawo daga service kinji kuma karki fadamai sbd hankalinsa zetashi" da haka tashawo kanta dakyar kafin itama taji hankalinta yadan kwanta
Yaya ghailan kuwa yanacan shida sadeeq suna zaga gari seyamma koda yadawo mutuniyar tana islamiya hakan yasa yashige dakinsa yadan kwanta kafin lkcn sallah yayi yana kwance yaji anturo kofa yadagokansa yaga momy CE
"momy ina wuni"
"bansan indayake ba, "yauduk ina kashiga abinda Baka saba bane zaka tsira yanzu tunsafe kana ina kwatakwata bakawuni agd ba kasan kuma baxan lamuntaba" shiru yayi yana Sosa k'eya saida tace "kana jiina nace inaka shiga tafada cikin tsawa
"momy kiyi hkr munatare da sadeeq ne"
komadai wanene aringa leqo gd kuma kafito yanzu kaci abinci tafice ajiyar zuciya yayi yafita dancin abincin sbd bashida zabi amma dayaso se dadare yaci gabadaya dan yasan dolekuma seta sakashi cin abincin Daren sbd ita batason taga mutun dayunwa shiyasa ko hadiman gdn suke samun abinci akan lkc kuma ma'ishi.
Yauce ranarda yaa ghailan zeyi tafiya gashi ya shirya yafito amma fir jawa taki tabarshi yatafi, wai ita adole saitabishi, shida momy suka tsaya suna bata hakuri akan tunda tafiyar wunice tabari idan za'ayi ta kwana yaje da ita, sai cewa tayi da momy
"Allah ni kafata kafarsa bayan shi yaa Adnan yasan iyayen yaa ghailan amma ni bantaba zuwaba" kallon kallo aka tsaya yi tsakaninshi da momy, yana mamakin ina jawa taji cewar shid'in *Almajirin* gidansu ne!
_Kuyi hkr dawannan wayar ba chaji tadalilin rashin wutar nepa data addabemu_ 😍😍luv u oll😍😍😍😍
_edited by billy galadanchi_
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: 💞💞Almajirina💞💞
*EXQUISITE ONLINE WRITER'S*
_written by sofiyyah galadanchi_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
10
Bayan da suka tashi daga school su rufaida ne suka maidata gida,sallama tamusu tashiga gidan agajiye bayan ta sauya kaya tayi salla taje tagaida momy
"Auta yaushe kika shigo gidan ne ko motsinki Banji ba" murmushi kawai tayi momy takuma cewa
"auta kije kici abinci kafin lkcn islamiyya yayi" mikewa tayi tana murmushi tace "to momy"
A hanya ta hadu da yaya ghailan ta bishi da ido sosai yamata kyau kananen kayan na masifar masa kyau gashi kuma color dinda yasaka na matukar karbarshi domin ko red & black yayi dakyar ta iya saisaita kanta ta furta cikin wata zazzakar murya
"yaya ina wuni?" Shimadin kallonta yake ta matukar yimasa kyau atamface ajikinta ruwan zuma sak,sannan taji dauri agaskiya ta tafi da imaninsa langwabe mata kai yayi yana wannan kayatacen murmushin nashi "lafiya qlw jawa,sai ina kika caba ado haka?" Kallon kanta tayi ta dago ta kalleshi tace "Nayi kyaune yaa ghailan?" Dariya yayi yace cikin wasa "danla can kyaume kikayi ni wasa nake miki fa" zumbura baki tayi ta karasa sauka kasa tana kunkuni cikin shagwaba, janyo hannunta yayi yace
"Auta wasafa nake miki kinyi kyau sosai wlhy" murna tashigayi taruga da gudu hanyar kitchen,kiranta yayi ta juyo yace
"mekuka dafa yunwa nakeji?" Murmushi tayi tace
"Zomuje dining nima shina sauko naci idan abinda aka dafa bemanaba sena girka wani"
Wow! "Yaya its ur favorite " tafada tashiga zubamasa kafin tagama jiyaai kamar ya kwato plate din sbd cike da yanga takeyi "yaya gashi"bisimillah yayi yafaraci itama zamatayi tana cin abincinal amma tarasa dalilin daya sanya takejin kunyarshi takasa sakewa taci abincin,kuramata ido yayi lura da tayi yana kallonta yasanya ta sadda kanta kasa shikanshi ya kula kunyarshi takeji murmushi yayi domin kuwa wannan hankalin da jawa tayi yana bashi mamaki,dakyar ta tsakuri abincin tana gamawa ta mike zata bar wurin harta fara tafiya yace "Auta yadai naga bakici komaiba?" Kallonshi tayi ya masifar mata kwarjini da sauri ta sauke kwayar idonta kasa tafurta can kasan makoshinta "Naci dayawa ai na koshi"barin wurin tayi da sauri karya mata wata tambayar
Murmushi yabita dashi yana jin wani iri gameda ita,tunaninta yana addabarshi kwanakinnan,shida kanshi yasan lokaci beyiba dazai nunawa jawa tsananin son dayake mata she's just 16 tayi kankanta, dole na danne zuciyata zuwa wani lokaci.
"Kishirya zamu fita bayan sallar isha"yaya ghailan yafada yana kalonta kyawun dayayi ne yasanya ta kasa ansashi sanda ya maimaita mata sannan tace "to yaya" a atakaice,
Exactly 8:03 pm
Tafito tanata sauri shikuma gogan yana gefen mota yana jiranta tun fitowarta yashagala da kallonta har ta iso be ankaraba seda tace" yaya lpy?" Mekake tunani" "bakomai" suka shiga mota wani hadadden mall suka shiga mesuna Agg mall, wurin ya tsaru yajuyo yana kallonta yace
"ki dauki abinda kike so daidai misali kuma kiyi sauri 9 inaso tamana gida"batace komaiba tashiga dauko duk abinda tagani kuma tanaso batayi wata haukaba shima ta daukomasa turare me dadi me suna dark wood na kamfanin oriflame Sweden.
Yasiyo mata ice Cream da chocolates kafin suka koma gida agajiye kowannensu yai dakinsa jawaheer kam sauya kaya kawai tayi ta kwanta,tunanin yayanta ya hanata bacci sam,yanzukam tafara tunanin cewar zancen Rufaidah gaskiya ne tana kaunar yayanta, tana tausayin kanta domin kuwa tasan yaa ghailan bazai taba sontaba amatsayin kanwa ya dauketa...
Washe gari yakaita skul tashiga class rufaida tace "ta yaya ghailan bada kanki asare inkinje gida kice yadafi" murmushi tayi cikin jin dadi ta furta
"kibari rufaida yanxuma jinai kamar kar mu rabu idan ina kallonsa sonsa yana kara shiga zuciyata"
"Allah yabaki yaya ghailan seyadda kikayi dashi "murmushi kawai jawa tayi.
_kuyi hakuri da wannan nayi typing dayawa na nemeshi narasa_luv u oll😘
_edited by billy galadanchi_
0 comments:
Post a Comment