Tsoro na Allah tsoro na muhadu dashi ahanya saboda ko ba komai dai ni nasan bana iya kallon cikin kwayar idanunshi,wani mugun kwarjini yakeman ta bangare guda kuma tsareni da idanunshi masu rikitar dani dayakeyi aduk lokacinda zamu hada hanya.
dukda an bashi shedar tinda ake dashi ba'a taba ganin miskili ta bangare guda kuma kamilin saurayi aduk fadin unguwar ba irin shi.
Unguwar da take cikeda 'ya'yan masu kudi 'yan gata, 'ya'yan masu fad'a aji a fad'in Nigeria, da yawa yawansu ma ba a qasar sukeyin karatu ba ta wani bangare kuma sha'aninsu sukeyi da 'yan matansu 'ya'yan k'usoshin gwamnati irinsu amman duk da haka acikinsu Ya Ameen daban yake.
mata dayawa suna sonshi amman shi Sam basa gabanshi Aikinshi da kasuwancinshi kadai yasanya gaba, acewarshi har yanzu ba'ayi yarinyar dazai tsaya b'ata ma kanshi lokaci akanta ba, kai shi soyayyar ma gabaki dayanta bai yarda da itaba.
Menene abunso a jikin mace? Kullum tambayar da ya keyi ma kanshi kenan.
(Nidai nace bakaje hannu baneba lol🤣)
""""""***************"""""
Ahankali nake takawa cikin natsuwata da tafiya ta mai ban sha'awa da burgewa, ni ahakan ma gani nakeyi sauri nakeyi saboda aiken da ummata tayiman kasuwa banaso na rasa adaidaita din da zai kaini duba da yanayin unguwar tamu, akwai drebobi har guda uku acikin tanqamemen gidan namu ko nace nasu amman dukda haka ummana ta haneni da shiga motocin domin kaini inda zani, a cewarta in tsaya matsayina na diyar mai aikin gidan mara galihu saboda gudun wulaqanci dukda cewa su drebobin ba zasu wulaqantani ba kasancewar mu dasu duk matsalar mu daya na wulaqanci da muke fuskanta daga matar gidan,
A wajen mai gidan da babban yaron gidan ne kawai muke samun sassauci amman ba daga su ba mudin da dabbobin dake gidan gonar bangare daya daga cikin gidan duk daya muke awajen iyalan gidan in kacire mutum uku rak cikin mutum bakwai daga cikin gidan watau Ya ameen Babban Dandan Gidan a maza, afnan watau autar gidan dashi kanshi kuma uban gayyar watau mai gidan Alhj Mustapha Dambulan
Ban aune ba naji nayi karo da mutum kasancewar saurin da nakeyi kuma da son kaucewa idanun drebobin saboda banaso su yiman tayin kaini din, lokaci guda kuma nayi baya zan fadi bankai ga kaiwa qasa ba naji an janyoni dakarfi har na fada faffadan kirjinshi da yake cike da haiba, lokaci guda dad'edd'en kamshin turarenshi da ke kara taimakawa wajen rikitar dani ya yiman sallama a hancina.
"Subhanalla" nace ina mai ja baya dasauri amman dukda haka damtsen hannuna na cikin nashi ba tareda ya sakeni ba,
"yi hakuri don Allah yaya..."
"Shiiii🤫" ya katseman hanzarin bashi hakuri da nakeyi, cikin isa da rashin son magana dinnan nashi ya bude baki dakyar yaceman "is ok ya wuce amman nan gaba ki dinga kula, bakyau ana tafiya ana tinani"
ya fada ahankali yanda nikadai zan iyaji dukda dai cewa dama haka yanayin maganar tashi take don in ba saninshi kayiba saima ka dauka maganar zuci yakeyi labb'anshi ke motsawa
Sakina yayi tareda zagayeni ya wuce kaman ma ba shine ya gama magana ba yanzu
Girgiza kaina nayi yayinda har yanzu ban koma normal ba bugun zuciyata ya qara gudu lokaci daya kuma ina kokarin daidaita numfashina domin ji nayi kaman ya wuce tare da numfashin nawa,
juyawa nayi nabishi da kallo har ya shige dan madaidaicin apartment din nashi da yake cike da kyau da qayatuwa a bangare guda na gidan.
Ci gaba nayi da takawa mamakin shi fal araina, na godema mahalicci na da ba aunty sauda ko nihal ce wannan tsautsayin ya faru akansu ba da na kade har buzuna,bani kadai ba ma har ummata da take cen tana masu iyakar iyawarta cewa zasuyi na bangajesu na daidaita kafada ta da tasu ubanwa ya haifeni,
oh "Allah ya soni" na fada afili ina mai sauke ajiyar zuciya daidai lokacin da na daidaita kaina ta gefen titi ina mai tafiya tareda waige waigen Inda zan hango abun hawa saboda inaso nayi sauri na amsoma ummana aikenta kada mukara yin laifi akan wanda mukayi dasafe wajen Hajiya matar gidan da muke aikatau.
_Muje zuwa Wannan shine mafari_
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)
*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)
*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.
Page ~2~
•∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆•
*Ya kamata musan wannan gidan dakuma rayuwa dake gudana agidan*
_Wacece wannan yarinyar da takema kanta ikirarin marar galihu?_
_Wanene Ya Ameen?_
_Wanene Alhaji Mustapha Dambulan?_
"""""""""""""""**********"""""""""""""""
Alhaji Mustapha Dambulan asalinshi dan jihar Katsina ne A wani Local Government da ake kira kankiya, su shidda ne awajen mahaifinshi da mahaifiyarshi da suke zaune cikin rufin asiri daidai gwargwadon abunda Allah ya hore masu, mahaifinsu Alhaji Isuhu da mahaifiyarsu Hajiya zuwaira suma duk yan asalin karamar hukumar kankiyar ne.
Alhaji isuhu manomi ne rikakke, kuma irin attajiran qauyen nan ne saboda yana noma ga kiwo yanayi, kuma ta bangare guda yana ba mutane jari sudinga sana'a suna raba ribar, akalla mutanen da yake wannan kasuwancin dasu sunkai mutum goma koma fi,
sannan yana kasuwanci na auduga da kamfanin saqa kaya dake Lagos inda dakanshi yake siyen auduga da wadda yake nomawa ya hada yakai kamfanin a bashi kudinshi yazo ya sake juyasu kafin kakar audugar ta dawo.
Yaranshi maza biyu ayayinda mata suke su hudu dukda cewa ya aurar da guda biyu manyan yanzu saura biyu ke gareshi a gabanshi.
Dukda yake mutumin karkara Allah ya bashi matukar tinani hankali da basira, saboda alokacin karatun boko baiyi yawa ba azamaninsu amman ahaka yace insha Allah 'ya'yanshi duka mata da mazan sai sunyi tinda shi Allah bai bashi ikon yi ba,
matan na gama makarantar primary yake aurar dasu ga wadanda sukeso saboda shi babu tsarin auren dole ko hadi a rayuwarshi tinda yace shima ba'ayi mashi dole ba wannan shi yasa yake zaune da matarshi kwaya daya rak kuma uwar 'ya'yanshi duka guda shiddan,ayayinda mazan kuma suke wucewa gaba da primary Allah ya taimakesu kuma suna gamawa suka samu aiki tinda alokacin ko baka gama secondary ba ma in kaso zaka iyayin aiki kuma abiyaka albashi mai tsoka saboda alokacin kudin sunfi daraja ba kaman yanzu ba.
Aisha itace zuwaira tafara haihuwa daganan sai Fatima mai bimata sai kuma Auwalu daganan sai aka haifi Mustapha.
Haihuwar ta tsaya mata kusan wasu shekaru masu dan dama inda har sun gama makarantar primary dinsu sannan Allah yabata haihuwar 'yanbiyu mata aka barmasu sunansu watau Hassana da hussaina.
Kyawawa ne gabadaya gidan jajir suke ga hanci masha Allah wannan shiyasa ma yayinsu mata sukeda manema har Allah yasa aka aurar dasu sai kannensu mata da ake gab da aurar dasu suma kwana kusa.
Aikin da auwalu da Mustapha suka samune yayi sanadiyyar barowarsu mahaifarsu suka dawo cikin garin katsina ayayinda shi auwalu ya dogara da aikin da yakeyi kawai shikuma Mustapha dayake shi ya gado mahaifinsa sak Allah yayi mashi zafin nema sai yake hadawa da kasuwanci ya saro kaya ya dinga sararwa ga masu shaguna inda nan danan Allah ya yi mashi ludufi abun ya bunkasa
kawai sai ya fara gininshi a unguwa mai kyau saboda shi bayada ra'ayin zama gidan gwamnati ayayinda shi yayanshi auwalu bai damuba ganin cewa a albashinsu ake cire kudin
Ganin ya gama gidanshi dan madaidaici yasanya yaso iyayenshi su baro karkarar sudawo maraya, sukau suka kafe kai da fata alambaram bazasu bar mahaifarsu da danginsu sukoma wani wuriba subar noma da kiwonsu, saidai fa in aure zaiyi ya sanya matar acikin gidan, yayinda shikuma yace lallai ba aurene gabanshi ba yanzu ma shirin qaro karatunshi yakeyi a qasar waje amman tinda yayanshi yasamu wadda yakeso ya aura yasanya ta acikin gidan alabasshi sai su warware ahankali.
Lokaci daya akayi bikin auwalu da yan biyu inda su aka ajiesu anan cikin garin kankiya shikuma Mustapha alokacin ya ma dade da tafiya k'aro karatunshi, amman a gidan da Mustapha ya gina nan auwalu yasanya matar tashi maisuna Zainab alokaci guda kuma yana cigaba da aikinshi na gwamnati.
"""""""""""""""**********"""""""""""""""
Mustapha ya kammala karatunshi cike da nasarori ayayinda arzikinshi na Nigeria ya cika ya tumbatsa saboda koda yaje karatunshi baibar kasuwanci ba sai ya koma saro kaya irin na kasar wajen masu masifar kyau yana turowa kuma asaukake inda yakeba babban amininshi da sukeyin kasuwanci tare yana saida mashi yana tura mashi kudin yasake saro wasu.
Gininshi ya farayi tanqameme acikin unguwar GRA yayinda shikuma Auwalu yake layout amman gini ne na fada aji domin fintinkau yafi wanda auwalu ke ciki ya gina apartment guda uku manya aciki yayinda shifa ya kafe akan sai ya maido iyayenshi birni suma suzo su huta tinda suma sun kawo karfi komai zasu iya yima iyayensu harma su taimaka ma 'yan uwansu mata da suke gidan mazajensu da suka fara tara zuri'a
Ganin ya kammala gininshi ga kasuwanci ya habbaka ya gina manyan store store na kayan masarufi da kuma kayan electronics sai kuma motoci daya fara shigo dasu daga qasar waje manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa na siye ta bangare guda kuma bai daina kasuwancinshi na qasar waje ba inda har ya zuba hannun jari a wani babban kamfani a China dayake saqa atamfofi da k'era wayoyin hannu.
K'arin girma sosai ya samu saboda karatunshi da ya qaro inda ya hada digree dinshi na farko da na biyu afannin qere qere da kasuwanci wannan shi yasanya gwamnati tarayya tafara bashi kwangila ta gina gidaje da masana'antu abundai sai Sam barka ba'a cewa komai addu'ar iyayenshi tana binshi tinda Mustapha mutum ne nagari maison kyautata ma duk wanda Allah ya hada shi zama dasu kuma baya kyamatar talaka ko mara shi duk daya ne awajen shi saboda yasan Allah ne mai azurtawa kuma yana azurta wanda yaso alokacinda yaso. Wannan kenan
*KUBRA* d'iya ce ga hamshaqin d'an kasuwa Alhj Nura,
Alhj Nura tare suke kasuwanci da Alhj Mustapha dukda ba tsaranshi bane ko kusa amman dai shi harka ta kasuwanci babu ruwanshi da wannan ta bangare guda kuma yana damawa a siyasar qasar babban dan kwangila ne da Allah ya azurtashi da makudan kudaden da shi kanshi baisan iyakarsu ba saboda yafi Alhj Mustapha kudi nesa ba kusa ba, kubra kyakkyawa ce dukda bazata gwadama Mustapha komai ba, ahaka Allah ya hada jininsu suna soyayyarsu dukda ita taganshi tace tana sonshi wanda hakan tasa Alhj Nura yima Mustapha magana, baiyi qasa aguiwa ba ya amince duba da yanzu iyayenshi babu abunda sukeso dagani irin iyalanshi kada girma ya cimmashi ahaka batare da ya tara zuri'a ba.
Kubra na da wani hali na kyamatar talaka da marar galihu inda Mustapha bayason wannan halin har yana mata magana akai irin yadda yaga in yaje fira gidansu tanama ma'aikatansu bayajin dadi sai yake dan tsawatar mata lokaci lokaci,
to tana dai kokarin kiyayewa saboda irin son da take mashi saboda Mustapha kyakkyawane ajin qarshe ga naira ga Hutu dukda bazai nunama mahaifinta komai ba.
Acikin haka ne Allah yasanya akayi auren Mustapha da amaryarshi kubra suna zaune kalau, wannan tasa ya jama yan aikinsu kunne ya gaggaya masu halinta saboda su kula kuma suna kokarin kiyayewa.
Dangin Mustapha kaf sunason kubra (kundai San yanda akeson mai kudi) iyayenshi girma ya kamasu yayinda mahaifinshi ya koma ya zauna ya barma qaninshi duka hidimominshi tinda 'ya'yan sun kawo karfi, saidai fa Mustapha ya gyara masu gida ya maidashi na zamani tinda sun k'i baro mahaifarsu ya sanya masu masu aiki da masu gadi da dreba guda daya mai suna iro suna kula dasu tinda yanzu babu sauran kowa a gabansu in ka dauke jikokinsu yaran Aisha da Fatima harma da yan biyu dake zuwar masu Hutu kuma tinda akwai ma'aikata suke kula dasu don dai hajiya zuwaira girma ya kamata don ma dai jikin nasu ba irin namu bane ba 'ya'yan yanzu.
Mustapha yaba 'yan uwanshi kaf jari kuma dukansu ya tattara su bayan aurenshi sukaje qasa mai tsarki suka sauke farali harma da wasu daga cikin ma'aikatanshi dayake ya bude babban kamfanin markada qarafuna a jihar legas yayinda ya dauki ma'aikata daga jiharshi ta haihuwa dakuma saura daga saura jihohin nigeriya
Ahaka Allah ya azurta kubra da samun diya mace kyakkyawa aka sanya mata suna Nafisa suna cemata feena daga ita sai Al'ameen suna ce mashi Ameen sai saudatu ana cemata saudat sai mai sunan Hajiya zuwaira suna cemata Nihal saikuma namiji data haifa Yusuf ana ce mashi Abi sai autarsu mai sunan maman Hajiya kubra watau bilkisu ana cemata Afnan.
Yara ne sun taso cikin gata da kulawa,kuma ga karatun arabi dana boko gabaki daya Allah ya basu saboda mahaifinsu mutum ne mai tsantseni yaran wasuma ya tsaya ya kula dasu bare nashi, Sam bayason abunda zai bata mashi tarbiyya da karatun 'ya'yan nashi, wannan ce ta sanya ya tattara kan 'ya'yan nashi ya tafi qasar waje dasu bawai don ya raina tashi qasar ta haihuwa bane a'a saidai kawai irin yanda yanzu karatun kasar namu ya tabarbare
acen yasanyasu makaranta mai kyau da ta Haddar alkur'ani dasauran litattafai, ahaka nafisa tasamu miji a cen qasar ta Dubai inda akadawo nigeriya akayi bikin kasancewar shima dan nigeriya ne iyayenshi yan asalin garin zariya ne,amman acen yake kasuwancinshi dama karatu ya kai shi kuma ya gama harma ya fara aiki da wani kamfanin kera takalma da abaya irin na mata.
Gabadayansu sun gama karatunsu inda mohd Al'ameen ya karanta fannin kasuwanci da fasaha (watau dai ya gaji mahaifinshi) ya hada masters dinshi ya jona yanaso yayi doctrine dinshi ita kuma sauda tayi degree na biyu yayinda Nihal da abi suka kammala degree na daya itakuma afnan tana aji na biyu secondary wannan ne ya sanya Alhaji Mustapha ya tattara kan iyalanshi ya dawo qasarshi ta haihuwa domin qasar ta amfana da ilimin da 'ya'yan nashi suka samu
Amman sun baro afnan gidan aunty feena domin karasa nata karatun, suma su Nihal da abi zasu koma idan sunso su cigaba amman alhaji yace sai sunyi aure tukunna domin ya gaji da ganinsu haka zaga zaga dasu ba aure.
Inda moh'd Al'ameen ya wuce qasar america domin karasa karatunshi daya dauko ta fannin fasahar zamani domin kasuwanci ya iya harma ya fara da taimakon mahaifin nashi
Hajiya kubra tana nan da halinta dakuka Santa dashi tin farko saima abunda yaci gaba domin mahaifinta Alhj Nura Allah yayi mashi rasuwa bayan haihuwar Nihal aka raba masu gadonsu, kasancewar ta na diya daya tilo ta mallaki dukiya da qadarorin da suka kara mata girman kai da dagawa domin yanzu bata jiran Alhaji wajen komai saboda itama ta mallaki dukiyarta ta agani afada wannan shi ya qara sangarta 'ya'yanta dukansu in ka dauke yaAmeen da afnan da bama ta qasar gabaki daya saidai tazo Hutu
Gida na nunama sa'a alhaji mustapha ya qera masu a garin abuja suka tarkato daga gidanshi na katsina, ya ba yayanshi alhaji auwalu da ya tara zuriya shima da matarshi Zainab abun dai sai sam barka yayinda ya sake siyan fili ya k'ek'ara ma iyayenshi gida a cikin kankiyan tunda tsufa ya kamasu kuma sunki barin mahaifar tasu ya kuma Gina masu gidan gona Inda aka cigaba da kiwon dabbobi kama daga su kaji,talo talo dawisu,shanu,awakai da duk wasu nau'in dabbobi da kuka sani ya kuma bada ana masu noma tinda itace tushen arzikinsu shiyasa basu yada ta ba.
'Yan uwanshi mata duka ya gina masu gidaje ya qara masu jari kuma duk shekara sai wasu sunje hajji su da iyalansu
ya dauki nauyin karatun 'ya'yan gaba dayansu kuma sunayin karatunsu cikin kwanciyar hankali wasu ma ya fiddasu qasar waje suna karatun tinda Allah ya hore mashi yanzu duk fadin Nigeria babu dan kwangila sama dashi,ya gina ma'aikatu yana daukar ma'aikata ga sana'ar motoci da qarafuna duk ya nayi,kudi dai ko ta wacce hanya juyasu yakeyi wannan shine silar arzikin Alhaji Mustapha Dambulan din kudi kenan inda ya tara tarin masoya da mahassada arayuwarshi.
YaAmeen ya dawo daga karatunshi hankali kwance da tarin Alkhairai,qasar ta amurka taso rikeshi saboda kaifin hankali da hazakarshi, amman ya qiya saboda irin tarbiyyar mahaifinshi dakuma kishin qasar tashi nigeriya.
*Wannan Kenan Yanzu Aka Fara*
🌹🌺~Oum-Deedat ce~🌺🌹
[8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)
*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)
*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, qanwa daya tamkar dubu,Allah ya barmu tare.
Page ~3~
•∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆•
Muje zuwa.......
Ahankali zanmaku wacece "Suhan" ya labarinta yake kuma me ya kawosu irin wannan gida dayake cike da tarin gadara, shagwaba, mutumci, halarci,dakuma miskilanci
"""""""""""""""""***********"""""""""""""""
Cikin hanzari na siya abunda duk nasan anada bukata na baro kasuwar da tarin idanu yayiman yawa,
adaidaita na hau tare da fada mashi sunan unguwar da zai kaini.
yayinda muka isa nace mashi ya ajiyeni nesa kadan da gidan, sanin danayi cewa YaAmeen yana gida, kuma zai iya tambayata dalilin dayasanya driver bai kaini ba, tinda shikuma ya hanani hawan okada, acewarshi drebobin basuda amfani in har wani acikin ahalin gidan zai dinga hawa hayis,
(oh ko su wanene ahalin gidan oho😵)
Ilai kuwa yana qofar gidan zaune bisa darduma, yana shan daddad'ar iskar dake busowa ta sanyin marece dakuma flowers dake busowa, a lokaci daya kuma yana latsa iPad din dake hannunshi, dagani wani abu muhimmi yakeyi,cikin sanyinshi da halinshi ko wayar ma sai an yi mata Jan aji da yanga?🙄
Suf suf na wuce, wuf na shige ta tamqamemen gate din dake kofar gidan mai double,
saboda har ga Allah yanzu nidai kunyarshi nakeji tun abunda yafaru dazu dani akanshi,wai nice yau kwance a k'irjin yaAmeen...k'irjin da kowa ke mararin ganin mamallakiyarshi shi, k'irjin da mata da yawa keson kasan cewa bisa shi,
ni nayi imani in ka kadauke kannenshi nice ta farko da na fara kwanciya bisa shi, nima fa a tsautsayi ne ba yin kaina bane ba tinda ko magana zamuyi bana yarda in kusanci inda yake kawai ina tsayawa ne ta inda zan iya jin maganar shi
Shima kuma yana k'ok'ari wajen ganin ya ma baya ga duk wata d'iya mace da ba muharramarshi ba.
( yo wa ma zai iya rungumewa wannan sarkin 'yan miskilan🤔)
Da wannan guntun tinanin nashige sashenmu damin isarma da ummarmu aikenta, nima inyi maza in hada ma aunty Nihal fruit salad d'in da ta ceman tana so,wanda saboda tsabar isa da taqama saidai tayiman text din in hada mata d'in.
Shi kau ta bangarenta yana lura da ita tin sa'adda napep ya ajiyeta da sand'on da takeyi kada ya ganta, bata san ta riga ta makaro ba,
murmushi yayi mai kama da an sanyashi dole, domin shidai lamarin yayinyar na bashi dariya, shidai har ga Allah ba shiga lamarinta yakeyi ba, amman ya kula mahaifiyarta na iyakar kokarinta wajen bata tarbiyya, ko motocin gidan ya kula mahaifiyarta ta hanata hawa.
bai gasgata ba saida ya tambayi malam mudi shugaban drebobin gidan yabashi tabbacin hakan, shikuma ya gargadesu da matsa mata kada su sanya ta bijirema umarnin mahaifiyarta, matar da yake girmamawa fiyeda tinanin kowa, yana sonta har cikin ranshi yake tausaya mata saboda ya kula akwai wani sarqaqqen Al'amari mai girma tattare da ita,
matar da kuma duk duniya mahaifiyarshi batada wadda take wulaqantawa irinta, amman ko menene ya sanya ta nace ma zaman gidan? Oho!
Dukda lokuta da dama yasha taddata bangaren masu aikin, ya sanya su kebe ya yi mata tayin barin aikin shi zai kula da ita da duk bukatunta batare da kowa ya saniba
Amman ta kan ce mashi " karka damu muhammadu komai lokaci ne". Iyakar abunda take fada kenan tayi mashi sallama tabar wurin
"Huh" 😯
ya fada tare da guntsar iska ya fesar alokaci guda yana mai kad'a kafad'a "Haka ne umma kamar yadda kika fada Allah yasa lokacin yazo mana da Alkhairi" ya fada a fili yana mai mik'ewa tare da tattara shimfid'ar tashi.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Wanene Moh'd Al'ameen?
'Da na biyu wajen Alhaji Mustapha Dambulan, kuma d'a mafi soyuwa a zuciyar Alhajin,ko dan ya gado shi ne ta fannin harkokinshi? Ko dan shine yaro mafi sauki tareda jinkai da taimakon na qasa dashi? Ko don shine kadai baya daukar irin zuga da halin mahaifiyarshi? Sau dadama ma yana mata nasiha wasu lokuttan dukda yasan ba ta dadin rai suke rabuwa ba, dukda yasan ba dauka takeyi ba, amman yana fata wani lokaci tagane gaskiya kuma tadawo kan hanya.
Kyakkyawan namiji ne ingarman namiji ka fasalta duk wani kyakkyawa da kasani tau YaAmeen ya wuce shi d'an boko ne na bugawa a mujalla kuma dan gayu ne, mutum ne maison tsafta yana da ladabi sosai, bayason bacin ran iyayenshi, matashin mai naira ne domin wasu daga cikin abokanshi kan mashi laqabi da yaro da kudi...,
miskili ne na gidan gaba sau dadama yana kallo anayin abu amman yakasa tankawa saboda k'yashin magana da Allah yayi mashi, kokuma yayi kaman ma baisan anayi ba, bashida business da mata
mace komin kyaunki komin haduwarki Baki kai ya kalleki ba, yana da shekara talatin da biyu a duniya, idan an mashi maganar aure kaka zuwaira wadda suke kira da Hajiya kan ce akyaleshi komai lokaci ne, yayinda Alhj isuhu kan matsanta da maganar, ita ko Hajiya kubra tana ganin an matsanta ma d'and'anta ita har yanzu ma bataga matar da ta kwanta mata ba da zata iya barin d'and'anta mafi soyuwa a wajenta ya aureta ba ta zame mata suruka a ganinta har yanzu cikin masu cewa su a son YaAmeen din da wad'anda iyayensu ke son had'a su dashi har yanzu arzik'insu bai kai mata wanda zata iya had'a zuriya dasu ba,balle tana ganin Al'ameen dinta saurayi ne na nuna ma tsara, yaro ne da kowacce budurwa kan so ya zame mallakinta.
Tanason suruka 'yar babban gida, 'yar masu naira, masu fad'a aji a fadin duniya.
bama Nigeria kadai ba, in haka ta faru ita fiye da burinta ya cika saidai abunda ba'a rasa ba, tinda kishiyace mata ke gudu ita kuwa tasan ta wuce wannan level din koma kawo wannan tinanin a ranta batayi.
Dukda halin YaAmeen na miskilanci hakan bai hanashi tausayi da jin qai na talaka ba, sau da dama ma zaiga su saudat na wulaqanta masu aikin gidan ya tsaya ya tsawata masu, saboda akwai ma lokacin da ya taba marin nihal saboda ta watsama wata mai gyara mata daki ruwa, (tin ma suna farkon dawowa k'asar, kafin zuwan su suhan gidan) saboda tayi mata mopping din daki, bata kunna air conditioner ba ta sanya mata room freshner shine ta taddata harabar gida ta watsa mata ruwa, akayi sa'a akan idanun YaAmeen din ne,aikau batayi aune ba ta ji saukar mari a kuncinta,
wannan ne ya sanya sukejin tsoronshi, saboda ko sun fada ma hajiya kubra bata mashi fad'a sosai saboda irin son da take mashi.
Da wannan ne ma'aikatan gidan suke samun salama indai yana qasar idan kuma yayi tafiya suke kaffa kaffa saboda sanin halin 'yan gidan.
=======================
Da sallama na shiga tanqamemen falon da ya lashe kujeru saiti hudu acikinshi,dukda nasan babu mai jina kuma da wuya ma ka tadda wani a falon, shima a hakan wai an ginashi ne saboda sauke baqi, dukda hajiya kubra ta mai dashi na sauke baqin da sukazo daga kauyen su alhajin, amman batare da saninshi ba.dukda babu kowa dake zaman falon, dukda haka sai na shareshi kullum nayi mopping, wannan shiyasa kullum nake kwana da uban ciwon jiki, wani corridor mai zurfin gaske nabi, banyi wata tafiyaba na tadda kofar falon Nihal da saudat din, kwankwasawa nayi dukda nasan bazan samu amsa ba amman haka dokar take garemu dukkanmu ma'aikatan gidan, kuma ko ma a musulumci haka dokar take shiyasa ma abun baya b'ata man rai.
sallama nayi tura qofar ahankali na shiga cikin salon tafiya ta (kamar ta masu akwai😜) falo ne madaidaici jere da kujeru kyawawa kalar sararin samaniya dukda cewa komai na falon haka yake, kama daga su labulaye Chinese carpet dakuma tiles din da ke malale a dandamalin falon.
K'ofofi biyu ne rak cikin falon, karkatawa nayi nabi ta gefen haguna inda zai sadani da asalin dakin Nihal din, hannuna dauke ba bowl na ceramic cike da fruit salad daya sha madara da zuma, nayi sallama a dakin bayan na murd'a handle din dakin.
Kwance na hangota nutse cikin gadonta da zan iya cewa yafi auduga taushi (🤔 oh ko ina suke samun irin wadannan katifun?) Ni kuma nace kaji suhan da k'auyanci😉.
Hannunta rike da waya k'irar Samsung a hannunta tana waya ga wata ahannunta daya k'irar iPhone tana latsawa,dagani dai da wannan dan gayen saurayin nata takeyin waya.
"Aunty Nee gashi" nafada ahankali saboda kada tace nayi mata ihu a kunne, ko kallona batayi ba balle tayiman magana,dama nasan hakan zata kasance, in kuma ban mata maganar ba ba zata sha ba, kuma nayi laifi, sai an hukuntani, wannan ce ta sanya nake cemata gashi tinda ni ke qasa da ita kuma nema nakeyi.
Takawa nayi na ajiye mata a kan wani qaramin stool dake gefen gadon mai kyau kaman da gold aka qerashi tsabar kyau, na juya da nufin ficewa a d'akin.
"Hey" abunda naji tace kenan cikin maganarta mai cike da shagwaba-shagwaba gadara gadara, isa isa, tinani na ya katse lokacin da naji tace "ki wanke mun toilet dina" abunda tace kenan ta cigaba da wayarta saboda nidai banajin me take cewa a wayar saboda munada dan tazara.
Gaba na ne ya fadi tino danayi naga text din aunty saudat a waya ta,itama tanason meatpie dashi zatayi dinner gashi kuma yanzu lokaci yakusa qure wa inda Allah ya taimakeni ma akwai means meat a fridge..... "Ko bakiji bane?" Ta fad' a sound so harsh
"To aunty" nace tareda shigewa toilet din wanda nidai a iya dubana na tsanaki babu abunda toilet din yayi, saboda dasafe na wankeshi kuma ita kadai take using abunta kawai tsabar mugunta da son sanya aikin.
Agurguje na gama mata na fito tareda shigewa kitchen din da yake main falour din na gasa ma aunt saudat meatpie din tareda hada mata meant juice,saboda nasan k'a'ida duk dare saita sha shi,wai saboda batason tayi k'iba. Fitowa nayi tareda zuwa na sake wanka, nayi alwala na kabbara sallah tinda anriga anyi magriba ban tashiba saida akayi issha'i,
na fito da niyyar zuwa inyi serving dinsu wajen cin abincin da ummata ce ke girka masu wai basu iyacin abincin kowa dagani sai na ummana shiyasa ma mu dakinmu daban ko acen boys quarters din masu girkama 'yan cikin gida abinci da gyara masu sashensu, wannan ka'ida hajiya kubra ce ta sanya ta dole dukansu suke haduwa, wajen yin breakfast da dinner ko da kuwa Alhaji Mustapha na nan hardashi ake haduwa wajen cin abincin
Ummana ce ta katseman hanzarin barin sashen namu da nakeyi "mamana ga abincinki nan kizauna kici naga yau kaman a gajiye kike ni zanje na zuba masu abincin" ta fad'a tana mai kallona cike da tausayawa saboda tasan irin yanda yaran gidan ke gallaza man ta wajen sanyani girkinsu da aikace aikacensu na babu gaira babu dalili,
"No umma banason ayi maki abunda zai bata maki rai, ko kinje zasu maki wulaqanci ne kiyi zamanki yanzu zan dawo ai YaAmeen yana nan basa min wulaqanci sosai in yana wajen jiya ya dawo k'asar kinsan" nafada ina kamo hannuwanta, gyada man kai tayi tareda cewa "Allah yayi maki albarka d'iyata yanda kikeyi man Allah ya baki maiyi maki kema ya baki miji nagari, kicigaba da hakuri watarana sai labari" "to umma nafada" tareda wucewa ina cemata "kije kici abinci kisha magani ki kwanta yanzu zan dawo insha Allah" "to" tace tareda komawa dakin namu, nikuma na wuce dasauri domin nasan suna cen suna jirana.
Ilai kuwa a zaune na tadda su a dinning area din dayake yakusa girman wani qaramin gidan, kaitsaye kitchen din da yake cikin dining area din na shiga tareda kinkimo manyan warmers da plates plates nazo ina jerawa, har na gama na fara serving dinsu ko kallon fuskokinsu banyiba, saboda nasan ko kalla nayi saqon harara ne zan samu, masalan daga 'yan matan gida buyu kyawawa da suke jin Kansu babu ya su a fadin Nigeria, shagwaba kawai suke zubawa, yayinda Hajiya kubra ke biye masu tanata murmusawa irin na manyan hajiyoyi da suka yarda kuma sukejin sunkai ko ina, labarinsu ya baza ko ina a fadin qasar tamu, abie ne ke latsa waya abunshi ta bangare daya yanada kyalkyala dariya, shi ko YaAmeen baima wajen, ahaka na gama serving nasu nayi masu sallama zanbar wajen,
Ya shigo fuskar nan tashi murtuk kaman kullum yake takowa cike da izza da kamala kai kace dandan sarkin kano ne sanusi lamido🤪
"Suhan zo kiyi serving YaAmeen" dayake itama hajiyar haka take kiranshi dashi......"No am ok green tea kawai zansha" ya fada kaman bayason magana yayinda sauran qannen nashi duk suka natsu suna cin abincin su bayan sunce "bigboo u are welcome"
"OK ki jira mu gama ki tattara wurin" ta fad'a tana mai faracin abinci, "to Hajiya na fad'a ina mai dan rissinawa irin na biyayya sannan na juya na wuce babbanb falo domin jiran su gama din tinani fal araina, " Saudat had'a man Lipton din" naji ya fad'a daidai lokacin da nake idasa ficewa daga dining area din.
Sun shafe awa biyu kafin duk suka tashi tareda yima juna sallama hajiya ta haye sama inda abi ya shige sashenshi suma su nihal suka shige nasu sashen sai kuma Allah ya kaimu.
Tattara plates din nayi nakai kitchen na juya zan koma dauko sauran, naga ya shigo da wasu bance komai ba saima dukar da kai danayi na jaye na bashi hanya ya wuce cikin kitchen din nima na fice dan dauko wasu, ahaka ya tayani kwashe kayan dukda hankalina bai kwantaba saidai nasan cewa hajiya na iya saukowa taganshi aiko da na kade har buzu na, bansan me yasanya shi aikata hakan ba yau lokutta dadama naga ko kallo ban isheshi in ka cire 'yan kwanakin nan da yake yawan bina da ido, shima na dauka hakan na da nasaba da tausaya wa duk wani mai aiki ne na gidan daidai da masu sharar lambu, nikau ta bangarenta baisan wata irin kacha bace yake sanya wa yana daure illahirin jiki da jijiyoyon jikina ba,ba bazai hantareni ba amman ko kallo ban isheshi ba, babu fuskan tambayan yasanya naja bakina na tsuke, na isa wajen sinc din ina dauraye abun da suka b'ata naji maganar shi a bayana don har ga Allah na dauka ya fita.
Wannan tasanyani zabura na juyo mamaki fal a raina wanda har saida ta bayyana fuskana
Wace irin mai sa'a ce yau ni?🤩 ni suhan ce yau YaAmeen ke cewa zaiyi magana dani? Tau wacece irin magana? Kodai wani laifin nayi mashi? Kodai bai hakura ba dazu dana tureshi? Ko dai........"Ko baakijii ba ne? Nace inaso muyi magana"
ya fada hankali kwance da maganar nan tashi ta rowa da muryarshi mai kama da goge a cikin kunnen 'yanmata
"Too yaya"
na fada a ahankali cikin dardar tareda juyowa na fuskanceshi zuciyata kaman za tayo tsalle ta fito waje, saboda tsabar kad'uwa
Guntun murmushi yayi iya lebo shi aganinshi nan ya k'okarta hakan sai tasanya kyaun shi ya k'ara fitowa afili kasancewar ba halinshi bane ko da murmushin amman ko baiyi ba kyaun shi na d'aya daga cikin abunda ke fizgar yanmata. Kallona yayi na tsawon second biyu, gamida gyara jinginar da yayi da cabinet ya motsa bakinshi ahankali kaman mai maganar saidawa ya fara da cewa.........
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)
*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)
*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.
*Page* ~4~
°^^^^^^^^^^^^°
"Ajinki nawa a makaranta?" Ya jefa man tambayar bazata.
A d'an firgice na dago ina kallon shi, gami da ɗan zaro idanu na, da sau da dama na sha jin ana cewa kaman na mai jin barci amman suna da girma sosai,tambayar ce ta zo man a bazata, ko da alama ban taɓa kawo tinanin magana makamanciyar irin wannan zata iya shiga tsakaninmu ba;
"na'am, ni?" Na Maida mashi da tambaya a ɗan firgice kuma cikin sigar mamaki,
Shiru yayi na wani lokaci, kaman ma baya da alamar sake tanka mani, nikuma alokaci guda tambayoyi suka ziyarci kwanyata, har banma san mun shafe kusan minti biyu a haka ba, Yayinda shikuma ya kafeni da idanunshi masu kama da na wanda soyayya taci ta cinye😜
"Banjin akwai wani da nake magana dashi a kitchen dinnan da ya wuce ke; Ai ina tinanin mu biyune kadai a nan ko?"
Ya faɗa a gajiye kaman, wanda akeyi ma dole, "Na gama makaranta. "
Na fada a gajiye ciki-ciki ina mai gyara tsayuwata, Tare da janyo hijabi na, na rufe gefen fuska ta, saboda kallon da yake yi man yana distracting din attention dina;
Jina nakeyi kaman a gaban miliyoyin mutane, kai gara ma ace a kotu nake, da sainafi sake wa, Da ace a gaban mutum nake kaman YaAmeen muna magana dashi one on one.
'Yar guntuwar dariya yayi, "Wow kina fadin har kinyi degree da masters, A hakan nan yanda kike yar mitsitsiya?"
Ya fada yana mai nuna ni da duk kan hannun shi yana sama da ƙasa da su saitin Inda nake tsaye, Da wani yanayi, wanda nidai nakasa ganeshi; don bazance zaulaya ba don nasan ba halinshi bane yin hakan.
Sai a lokacin nagane kuskuren danayi,dan zaro idanu nayi alamar wayyo Allah, Gami da Jan sauran hijab dina, na ruge fuska ta ruf, ina dan mai sakin ɗan k'aramin murmushi;
A hankali nace, "am sorry secondary nake nufi yaya"
"OK good " ya fada a gajarce, Yana mai ƙara nazarinta, ko buƙatar da yake da ita zata samu karb'uwa awajenta?
"Ina so kici gaba da makaranta, domin zaman ki a haka kina wahala ba abune mai dad'i ba; ko babu komai ilimi yanada dadi, zaki taimaki kanki ki taimaki ummanki" Ya tsagaita yana mai zura mata idanu da ke taimakawa wajen ƙara ruɗa ta; Domin yaga yanda zatayi, Nikau bansan lokacin da nabude fuskata ba gabaki daya, ina mai sakin murmushi har siririyar wushiryar dake saman hakora na ta bayyana.
"amman kije ki shawarci ummanki, kuma ina so maganar ta tsaya iyakar ni, da ke, da ita; Don bana so wani ya sani kaf gidan nan, idan ta yarda sai ki kawoman takaddunki, da kuma zabin makarantar dakikeso kiyi da abunda kikeson karantawa, kibar sauran maganar a hannuna. Kome zamu ji, ko zaku gani, Ku kauda idanunku gabaki daya, Babu ruwanku a ciki, Ni nace zan yi, kuma insha Allah zanyi;"
Yana gama fadar haka ya juya, Yana mai barin tanqamemen kitchen din, da kai ka rantse da Allah ba'a Nigeria yake ba.
Dakallo na bishi, a yayin da kwalwa ta ta cunkushe,
"tabbas tabbas mafarkina zai tabbata, tabbas lokaci yayi; Alhmdllh naketa faɗa, a cikin raina, saboda na ma rasa tinanin da zanyi, bayan wannan; Juyawa nayi, gami da ci gaba da aiki na.
A gaggauce na gama na rufe kitchen din, gami da barin part din baki daya zuwa namu, Amman zuciya ta cike da tarabbabi, domin nasan halin umma ta, Sannan ni na san kafin in dosheta da maganar, Sai nayi nazarin abunda zance mata tukunna, Don na san ta da gudun duniya da abunda ke cikinta balle wulaqanci irin na hajiya kubra.
Ko da na isa part din namu, Na tadda umma ta, tasha magani amman takasa yin barci, saboda taga na dade har wajen karfe goma da wani abu, Alla Alla take yi, ya kasance lafiya, Gashi ko abinci na ma ban ciba, ina shiga kuwa na taddata zaune bisa sallaya.
Allah sarki umma ta, Mace kamila mai gudun duniya, Mace mai ibada, da rashin hayaniya, Amman dukda wannan halin nata, hakan baisa Hajiya kubra ta ɗaga mata ba, Ni gani ma nakeyi kaman babu wad'anda ta tsana irin mu acikin masu aikin dake gidan, Wanda munfi mu goma sha wani abu, ummata ce ta katseman saqa da warwarar da nake tayi cikin zuciya;
"lafiya dai ko mama na?" ta faɗa tana mai miƙewa a hanzarce, sannan ta ci gaba da magana cikin dan firgici kaɗan; "Naga dare yayi sosai, ya kamata ace yanzu kin kwanta ki huta hakanan"
Ta faɗa cikin sanyinta, mai sanya ni natsuwa, duk da a ɗan firgice take; Kome nake yi, ko ban fad'a ba, son da ummata keman yafi wanda nakeyi mata, Duk da kau a duniya babu wadda tafi soyuwa a raina kamanta, Tinda ita kadai na sani, ita kadai na tashi na gani , ita ce uwata, itace ubana, ita ce yayata, abokiyar shawara ta kuma, ta fanni daya kuma abokiyar wasa ta;
"Ina hankalinki yake ne ummina? Ina ta magana kinyi shiru" ta faɗa tana kamo hannuna, bansani ba ashe har ta nade abun sallar ta iso inda nake tsaye daga bakin ƙofa a tokare.
"Umma saida najira suka gama sannan na wanke kayayyakin kinga gobe in Allah ya kaimu mun rage aikin;" na faɗa, ina mai kama mata hannu nima, muka zauna gefen katifar tamu dake yade a tsakiyar dakin.
"ga abincin ki tau, maza kici ki kwanta, kinga karmu makara gobe dasafe in Allah ya kaimu banaso kullum muke b'atawa hajiya rai;" ta faɗa tana jawoman kwanon abincin.
Kwanon silver ne amman tsaf yake, kaman sabo sai sheqi da walwali yake yi, kaman yau aka budeshi a leda, Allah sarki ummana akwai tsafta, dakin namu ma sai k'amshi yake yi, an goge tiles dinnan sai daukar ido yake yi, abunka ga fari, dakinmu tsaf yake babu tarkace da karikitai, in ka cire katifarmu, sai labulaye da wani teburi a gefe, inda muke ajiye daddumar sallah tamu, da sauran litattafan addini himili guda, kasancewar ummata tayi karatun addini mai zurfi, sai take k'araman duk bayan sallar subhi, akwai wardrop ta bango a dakin, wannan shi ya tak'aita mana tarkace, tinda ba yaro ke garemu ba, kwata kwata ma babu yaro a gidan, kowa da locar ta inda ni biyuma ke gare ni, kasancewar guda uku ce a dakin, amman ajere suke, sai ummata ta dauki daya, tabar man biyu saboda ni budurwa ce zan fita karikitai.
Abincin naci, naje na daurayo bakina na cenza kaya zuwa kayan bacci, muka kwanta umma tayi mana addua muka shafa kowa ya juya cikeda tinani kala kala.
Nikam ta bangare na banyi bacci ba, amman ummana tayi baccinta saboda maganin da tasha, kuma ko ba hakaba, ita bata kwanciya da damuwa ko haushin wani a ranta, takance ba'asan gawar fari ba hakanan kaje lahira da haushin wani duk abun da gaƙuri bai bayar ba ai rashin shi baya badawa.
Gari na waye wa muka gama komai, kama daga salla, karatu, da wanka; zuwa karfe bakwai, kowa yayi shirin fara aiki kaman yanda yake a al'adar gidan namu. Amman mu bamu kai ga fita ba, sabo da ƴan cikin gidan ma basu kai ga tashi ba, kuma ina so in yima umma ta maganar karatu na; sai dai ina zullumin tunkararta da maganar, sabo da na san halin umma ta sarai, wani d'an qaramin yak'i ne gabana, Amman duk da haka hakanan zan daure in tunkareta da maganar domin ga dama ta samu, kuma ko ba komai hakan ci gaba mu ne ni da ita baki daya, fata na dai da addu'a ta Allah ya ɗora ni akan ta, ta yadda ta amince mani, sabo da wannan karon ina tsoron YaAmeen ya ji haushi ya janye burin taimakon mu a ranshi, saboda ba wannan ne karo na farko ba da umma ta ke daƙile shi akan duk wani burin taimaka mana da yake yi, Wanda shi a ranshi har ga Allah taimakon ummana din ne kan ingiza shi ga hakan saboda rashin hayaniyarta da biyayyar ta ga iyayen nashi.
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)
*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)
*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.
*Page* ~5~
°^^^^^^^^^^^^°
Bayan mun gama karyawa ne, muna zaune a ɗaki ni da umma ta,Tana yanke farcen ta na hannu, Yayin da ni kuma nake zaune gefen katifar tamu da littafin hisnul musleem a hannu ina karantawa.
Rufe littafin nayi tare da maida shi ma'ajiyar shi, na dawo na zauna daf da ita, tsawon second biyar na dauka ban iya cewa ƙala ba, tabbas abinda nazo mata dashi ni kaina na san mai girma ne, to sai dai ba yadda na iya, shahada nayi na bude baki na a hankali nace;
"Umma don Allah ina so muyi magana dake" cike da mamaki ta ɗago idanun ta tare da tsare ni da su, take guntun tunani yazo a ranta, wacce irin magana ce wannan da maman tata bazata iya tunkararta kai tsaye da ita ba? Koma dai menene tana fatan ɗiyar tata ba zata zo mata da wani abu akasin tunani nata ba;
"ina jin ki mama na" ta bani amsa tana mai dakatawa daga yanke farcen gami da sauke hannun kan cinyoyinta.
"Umma don Allah ki saurare ni kuna ki fahimce ni, wannan karon izinin ki nake nema; ki duba halin da mu ke ciki na rashin sanin madafa, dama ce ta zo mana da zamu fita daga cikin wannan ƙangin bautar da mu ke ciki, dama ce da zata sanya mu dogara da kanmu har ƙarshen rayuwarmu."
Tinda na fara magana ta tsira man idanu ba tare da tace kanzil ba, sai dai ni bazan iya karantar abunda ke cikin zjciyar tata ba;
Ganin yanda ta kafe ni da idanu ya sanya ni sauke kwayar idanu na ƙasa ina mai murza yatsu na suna bada sauti ƙas, ƙas.
" Uhm, ina jinki mama na, wannan wacce irin dama ce? Ina fatan dai zaki zo mani da buƙatar da kika san zan iya amincewa da ita, ba wadda kika san za ta iya sanyawa ranki ya ɓaci ba"
Tinda ta fara magana bugun zuciya ta ya ƙaru, fargaba da zullumin yadda zata ɗauki maganar suka baibaye ni, dakyal na bude baki na cigaba da cewa;
"Umma jiya ne Ya Ameen yace ya kamata in koma makaranta domin yana so mu zama masu tallafar rayuwarmu da kanmu, kuma yace in nemi izinin ki na bashi takaddu, da kuma zaɓin makarantar da nake so, tin jiya nake zullumin tunkarar ki da maganar, domin ban san yanda zaki kalli abun ba, wallahi umma ba nice nayi mashi magana ba, shine da kan shi ya same ni kitchen ina wanke wanke ya man maganar;
Idan dai ba idanu na bane suke man ƙarya ba, wannan. Karon kallon da ummar tawa take man ya cenza salo, ya rikiɗa ya koma kallo ne mai cike da gargaɗi da kuma tuhuma; kafin ta bude baki ta cigaba da Cewa
"Masu gadi ma da drebobi ban hanaki magana dasu ba? Balle Al'Ameen ɗanɗan masu gida? Miyasa kike son cenza hali ne Hauwa'u"
A firgice na ɗago ina mai kallon ta cikin tsananin firgici damuwa fal a raina, yau ni ce umma ta ta ke kiran sunana kai tsaye; me ya sanya ni? Me ya kai ni? Me ya ja mani? "tsabar son zuciya da hangen gaba" zuciya ta ta bani amsa, tini kwalla suka soma shatata daga idanu na, wanda tini kalar su ta juye daga farare tas zuwa jajaye;
Hannun ta na kamo gami da runtse su sosai sannan naci gaba da magana ba tare da damuwa da goge kwallar ba, gara na barta ta zuba ko zanji saukin raɗaɗin da zuciya ta keyi mani,
"Don Allah umma kiyi haƙuri, wallahi tallahi bani na mashi magana ba, iskeni yayi har kitchen, kuma daga ni sai shi muka yi maganar, umma kiyi haƙuri in na bata maki rai insha Allah bazan sake ba" Na Faɗa wani tuƙuƙi na taso man daga cen ƙasan rai na,
"Ni baki ɓata man rai ba Mama na, gani nayi kawai kaman baki gudun wulaƙanci daga wurin hajiya Babba ne,
sanin kanki ne da ta ita ne ma da yanzu mun bar gidan, sabo da Alhaji ne kawai muke zaune har yanzu, tau minene yasa ba zamu kiyaye ba? Tabbas kinsan idan hajiya taji zaman mu a gidan nan ya ƙare kenan, zata ce ne mun mallake mata yaro gashi har yana wahala akan mu, kinsan kuwa ni bani son abunda zai haɗa ni da su dukkan su balle rayuwa ta ta ɓaci hakanan"
Kuka na naci gaba da yi duk da na ji ta kai aya, Amman zuciya ta na kwadaito man samu ne gashi umma ta na lasa man ɗanɗanon rashi a baki, ban gama maganar zucin da nake ba naji ta cigaba da cewa "idan ya sake maki maganar kice mashi na hana ki, kuma nace mun gode da halacci da irin ƙoƙarin da yake yi a kanmu Allah ya ƙaro buɗi da arziƙi"
Tana gama faɗar haka ta zare hannun ta ta fice a ɗakin, ita kanta cen ƙasan zuciyar tata bata yi mata ɗaɗi, kukan da suhan ɗin ke yi mata yana taɓa mata rai, sai dai babu yanda ta iya wulaƙanci abu ne da kowa ya kamata ace ya guda ba ma ita kaɗai ba, suhan ɗin yarinya ce dududu bata wuce shekara ishirin ba, bata fata wani abu ya shiga tsakanin ta da Al'Ameen, a matsayin ta na babba ta san abu ne mai sauƙi, domin daga tausayi komai ke chanza wa, dukda ta san Al'Ameen ɗin ya fi ƙarfin ɗiyar tata, sai dai ita ba zata so hakan yayi sanadiyyar ɗan zaman da suke yi a gidan ya zo ya gagare su ba.
Ni kau tinda umma ta fice ta bar ni a gurin zaune, fashe wa na kuma yi da kuka tare da faɗawa na kwanta kan katifar tare da kifa kai na, na saki wani irin kuka mai tsuma rai, maraici bai yi ba, mahaifi daban ne a rayuwa, yanzu da yana da rai ko kusa bazan fuskanci irin wannan rayuwar ba, tabbas ummata akan gaskiyar ta take, Hajiya babba muguwar mace ce, yanzu zata sanya a ɓatar da kai a doron ƙasa indai ka nemi shiga gonar ta.
Dukda yace shi kadai zai yi hidima ba tare da ta sani ba, wannan tunani shi ne, Hajiya mace ce mai cikakke iko, komai akeyi a gidan a tafin hannun ta yake, akwai 'yan gulma masu kai mata rahoton duk abin da yake faruwa a gidan;
Ko ba haka ba ma ni mai ya shiga kaina? Mu da muke a ɗosane, sauran ma'aikatan gidan ma duk sun fimu galihu, me yasa nake hangen gaba ne? ALLAH ne kaɗai yasan yanda zai yi da mu, mu bar mashi komai, karatu na ba dole bane, ni cikakkiyar marainiya ce da ban ma san ya kalar mahaifi na take ba, ban taso na ganshi ba, ban taso naji umma ta na maganar shi ba, kuma bata so ina mata maganar shi, shin mai zai sa in ci gaba da damun kaina?
A hankali na rage sautin kukan nawa, gami da goge hawayen, lokacin da idanu na suka kai kan agogo dake maƙale a bangon ɗakin namu, 09:30am, a hanzarce na tashi na shiga bayin dakin namu na wanke fuska ta, ban damu da in shafa ma fuskan komai ba, wa zan ma kwalliya? Rai na a cunkushe yake;
Ƙofar ɗakin namu na fito na tadda umma ta tana tattara sharar tsakar gidan da su sauran ma'aikatan dama basa yi sai ita ko ni, sun ma bar mana mu kadai, a cewarsu ai dama aikinmu ne mu share tsakar gidan tinda ni ke sharar cikin gida, hakan ma baya damunmu in da sabo mun saba.
Wata daga cikin amintattun Hajiyar ce ta zo wucewa zata shiga ɗakin nasu da ke kallon namu, watsa mana wani irin kallo tayi gami da cewa,
"maman Suhana sannu da aiki, Hajiya babba tana neman ku, ya kamata ku tafi domin sun tashi tun ɗazu"
"To uwani, mun gode,an tashi lafiya ko?" umma ta ta maida mata cikin sakin fuska, domin duk kwakwarka ba zaka iya karanto ɓacin rai a fuskan umma ta ba, ko da kayi don ka ɓata mata rai tana tura maka aniyarka ne a wuce wurin; taɓe baki tayi gami da cewa "lafiya" ta shige ɗaki abun ta, muna iya jiyo tashin sauti tsokin ta a hankali.
Juyowa Ummata tayi ta kalle ni cikin sanyi ta tace "Mama na wuce kije gani nan zuwa, sai dai kada ki manta da maganar mu kinji ko?" "To umma" nace gami da juyawa na shiga ɗakin ɗauko hijab ɗina.
*******************************
Yau dai haka na wuni yin aiki sukuku,duk wata hanya da zata haɗa ni da Ya Ameen na toshe ta, ina gama aiki na na koma sashen mu na kwanta yayin da umma ke can tana aikin abincin ranan su, bata bari in taya ta, sabo da Hajiya magana take yi, cewa take kowa yayi aiki shi, ƙarar ƴar mitsitsiyar waya ta rakani toilet ce ta katse man tunanin da nake ina ta juye juye bisa katifar tamu;
Massage ne ya shigo man aunty saudat naso in raka ta shopping, wannan ne ya sanya na miƙe gami da shiryawa domin dama na saba dukan su biyun nice ke raka su, duk lokacin da muka dawo suna kwashe tsofaffin kayan nasu su bani kasancewar su basu da jiki ni kuma ina da ƴar murjewar jiki, dukda sun girmeni sai size din namu yazo daya, haka kuwa aka yi muna dawowa ta tattara tsofaffin abubuwa da bata so ta bani wanda ni a waje na kaman sababbi suke.
*******************************
A haka sai da na shafe kwana uku ina wasan ɓuya da Ya Ameen, sabo da bana so magana ta ƙara shiga tsakani na dashi balle ya tado da maganar karatun nawa, ni a ganina in yaji shiru yasan umma bata barni bane kawai, Daman abunda na sani shine halin yaya Al'Ameen, ba zai man magana ba indai ba nice nayi mashi ba, wannan tasa na saki jiki na ci gaba da ayyuka na yanda ya kamata, na cire ma raina komai da tsammanin zanyi wani karatu a rayuwa ta, na sani dama sau daya take zuwa a rayuwa, ni tawa damar ta zo kuma nayi sake da ita shikenan kawai duk yanda Allah ya so yayi dai-dai ne.
Tafe yake cikin salon tafiyar shi ta ingarman namiji, dan ƙwalisa, ga natsuwa, kamala cike da kwarjini; tabbas Al'Ameen ya kai namijin da za'a kalla a sake kallon shi, fuskar shi cike take da annuri dukda kasancewar shi ba ma'abocin murmushi ba, hakan bai hana tsantsar kyawonshi fitowa ba. Fari ne tas yana da tsawo daidai misali jikin shi ya dace da murzazzar fatar shi da take cike da gargasa kwance luf kai ka rantse bata taba shan zafin rana ba, yana da dogon hanci sosai domin ya dauko kyaun mahaifin shi da mahaifiyarshi duk a cikin su shiddan ya kere su a kyau da haske dukda suma suna da nasu kyaun, bakin nan nashi kuwa kaman gidan tsutsa gashi kalar maroon mai haske, kai kace jambaki ya shafa sannan ya goge, sam baya da girma sai dai sajen da ke gewaye da fuskar ya ƙara ƙawata fuskar, sam baya da sanƙo wannan ne yasa gyaran fuskar ya fitar da ainahin kyawon fuskar dimpul din shi na dashe das a gefen fuskar shi na hagu wanda tasa ko bai motsa fuskan ba kana iya hango kwarin shi kwance a kan fuskar shi, Ya Ameen ba dai miskilanci ba.
Sanye yake da farar riga T-shirt ta polo da farin wando na lallausan jins ɗan kamfani gucci watau kayan botique, ƙafar shi Sanye da farin takalmi samfurin adidas, ni kaina mai Rubutun takalmin ya tafi da imani na, hannun shi riƙe da wayar shi samfurin Apple Phone, tare da sun glass ɗinshi sai makkulin motar shi ƙirar Benz, yana ɗan kaɗa shi a hankali.
Waya yake amsawa cike da natsuwa yake taka wa a hankali, kai da ganin shi kai kasan ba RAGGON NAMIJI bane. (littafin Maman mamy)
Falon ya shiga da sallama ɗauke a bakin shi Amman in ba kai da kake kusa dashi ba ba zaka san yayi magana ba, kai tsaye wajen da hajiya kubra take hakimce ya dosa, a hankali yake taka wa sai dai cikin zafin nama, irin na cikakke namiji, katse wayar yayi daidai lokacin da ya isa daf da inda take zaune saman sofa.
"MOM" Ya faɗa daidai lokacin da yake zama kusa da ita, "Good morning Son" ta faɗa cikin murmushi mai nuna isa a duk lokacin da tayi shi, sam ba zata iya ɓoye son da take yi ma yaron nata ba,
"Morning Mom, How Was Your Night" ya faɗa yana mai ɗan zamewa ya kishingiɗa a saman sofar, "Great dear, Hop there is nothing wrong?" ta maida mashi da tambaya.
"Nothing Mom But i want to enrout to china today" ya faɗa da ƴar damuwa a fuskar shi,
"Wat? Hop dai lafiya son"
"Lafiya Ƙalau Mom, kayan da nayi order ne an samu matsala ne wajen shipping nasu so i need to go there, domin in san matsalar da aka fuskanta sabo da kaya ne na manyan kudi, gashi costomers sai magana suke yi sun ƙagara a basu kaya"
"Well Allah ya kiyaye hanya, fatan dae kayi report wajen aiki?" ta faɗa tana dafa kan shi kaman ƙaramin yaro; "Yes Mom ba wani matsala bari naje sai munyi waya, yanzu muka gama magana da Dad ma shima yana hanya Amman ba zamu hadu ba sai dai na dawo, ban san tsawon lokacin da zan dauka ba acen" ya faɗa a gaggauce yana mai miƙewa gami da gyara zaman rigar shi a jikin shi, bai jira cewarta ba ya fice daga falon, yayin da ita kuma take bin shi da kallon ƙauna irin na uwa ga ɗanɗa mafi soyuwa a rayuwar ta, tana mashi addu'a da fatan nasara domin dai ita idan akwai abunda ta tsana a rayuwar ta tau bai fi ganin ɓacin ran Al'Ameen din ba.
*****
A bakin dry centre na gidan muka haɗu ina shanya cottons na goge goge, aikina nake don ni har ga Allah ma ban kula da tahowar shi ba, tinani na ya tafi ga tinanin da ya zame man abun ci, abun sha, a kullum watau tinanin mahaifi na.
Ƙamshin turarenshi ne ya man sallama, yayin da idanunu na suka gaza juyawa su kalleshi, gaba daya naji an zare man lakkar dake jikina, jinin jikina ya katse ya ci gaba da gudu cikin jiniyoyin jikina, domin dai in ban manta ba kwana uku kenan rabon da in sanya shi a idanu na, ni na ma dauka ko baya ƙasar ne kwata kwata ma;
Tinani na ne ya katse daidai lokacin da ya matso daf da inda nake tsaye
"Hey what are u doing here?"
Haka naji kunnena ya faɗa man, ɗan rusunawa nayi a hankali nace "Ya Ameen ina kwana?" "Lafiya" ya bani amsa a taƙaice cikin salon maganar shi da ke ƙara mashi kwarjini a idona,
"ya maganar mu ne ta rannan banji kince komai ba" ya faɗa yana mai tsare ni da idanun shi masu ƙara ruɗa ni,
ɗan kauda fuska ta nayi, sabo da bana so mu haɗa ido dashi.
"umma ta ta hana ni tace kuma nayi maka godiya ga irin ƙoƙarin da kake yi a kanmu Allah ya saka da alkhairi"
na faɗa ina mai sadda kai ƙasa domin nima na san abun ba zai yi mashi daɗi ba;
"its ok"
Ya faɗa yana mai wucewa ba tare da ya tsaya ƙara jin wani abu da zai fito daga bakina ba,
Ni din ma banyi niyyar ƙara tankawa ba, sabo da na san bani da kuma abun cewa.
Kwalla ce ta taru a idanuna, nayi saurin goge ta ina mai fiƙi fiƙi da idanu,amman wata ke ƙara zubowa, shikenan na rasa dama ta, na rasa buri na, umma tafi so muyi ta zama cikin wannan ƙangin na bauta,
Mu fa ba bayi bane da aka siyo a kasuwa, muma mutane ne kaman kowa, Ya Ameen yayi iya ƙoƙarinshi akan mu, sai dai duk yanda naso in karanci halin da zuciyar shi ke ciki akan fuskar shi, bai bani damar hakan ba, kallo na na maida ta saitin da yabi ya wuce, ko burbushin shi ban hango ba, sai dai Ƙamshin turarenshi irin na maza da suka amsa sunansu ya bar mani,
"Nagode ya Ameen ko a haka ka bar mu mun san kaso taimaka mana na faɗa a fili ina mai durƙushewa, gami da sakin wani maraya kuka.
Ba mu ba kawai, duk wani mai aiki dake cikin gidan yana ƙoƙarin taimaka mana, sam baya so duk wani dake ƙarƙashin shi yayi kukan baya kyautata mashi,
Tabbas da duka masu arziki na duniya irin halin shi garesu da abubuwa sunyi ma mabuƙata sauƙi a rayuwa, duk da cewa halin mahaifin shi ya dauko, sai nake ganin ya ma fi mahaifin nashi kula da al'amurran mu a cikin gidan
*Dukka buri na ya wargaje*
*Mafarki na ya tafi*
*Allah kai ne gata na*
*Ka duba lamurra na*
******************************
~Oum-deedat ce~
[8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)
*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)
*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.
*Fage ~6~*
°^^^^^^^^^^^^^°
Tsawon kwana uku na shafe ban sake jin ɗuriyar Ya Ameen ba, hidimomi na nake yi hankali kwance.
Yau gidan mun tashi da hidimomin aikin abinci, Alhaji Mustapha ne zai yi baƙi, abokan kasuwancin shi daga waje ne zasu zo.
Abinci kala goma Hajiya Babba ta bamu umarnin muyi, mu duka ma'aikatan an rarraba ma kowa nashi aikin, masu gyara gida na yi, masu gogewa nayi, mu da mu ke aikin abincin mun hallara mu duka a babban kitchen ɗin gidan.
Wannan karon harda su Aunty Saudat da Aunty Nihal ne a kitchen ɗin, sai dai banga amfanin su ba, yo eh mana basu da amfani domin kowaccen su kujera ta ja ta zauna suna latse latsen su,sai dai su bada command ɗin yanda zamuyi, wanda a zahiri ma mun fisu iyawa, salon iya yi ne kawai.
Haka muka kammala abincinciccikan duk mun jigata; wannan ce tasa bayan mun gama jejjera abincicikan bisa tangamemen dining table ɗin da yake gefe guda a cikin falon sashen baƙin, na wuce sashen mu domin yin wanka da gyara jikina.
Zuwan su yayi daidai da gama shiryawa ta, kiran Hajiya Kubra ne ya shigo waya ta, tare da bani umarnin zuwa sashen na baƙin domin taya su zuba abincin.
A falon muka haɗu da Alhaji Mustapha ɗin da na kwashe watanni ban sanya shi a idanuna ba domin baya yawan zama; Durƙusawa nayi har ƙasa na gaida shi, yayin da ya amsa man cikin fara'a da sakin fuska, tare da tambayar umma na ko muna cikin ƙoshin lafiya.
A ɗarare nake zuba masu abincin domin harda Hajiya Kubra zaune a wajen saboda baƙi ne abokan hulɗarsu na kasuwanci kuma ita ma tanada share a ciki, wannan ce tasa nake yi a hankali domin kada inyi laifi wajen Hajiyan.
Gama zuba masu abincin yayi daidai da wanzuwar daɗaɗɗen ƙamshi, lokaci guda mamallakin ƙamshin ya bayyana fuskar shi ɗauke da maɗaukakin murmushin da ban taɓa ganin yayi irin shi ba; Sanye yake da lallausan farin tissue yard har kana iya hangen fara ƙal ɗin singlet dake jikin shi, kanshi babu hula hakan ya bayyana kwantaccen sumarshi luf da ita bisa kanshi har sheƙi take yi, hakan ya ba gyaran fuskar shi damar ƙawata fuskar shi da take ɗauke da madaidaici saje, ƙafar shi na Sanye cikin wani cover ɗin takalmi ɗan ƙasar italy sai sheƙi da walwali yake yi.
Cikin hanzari yake takowa cike da kwarjinin shi, lokaci guda yana fadin "am so sorry wallahi na samu tsaikon jirgi ne" ya faɗa daidai lokacin da ya isa gare su yana mai jan daya daga cikin kujerun ya zauna.
Da hannu Hajiya tayi man nuni da in serving ɗinshi, aiko ba ɓata lokaci na duƙa daidai saitin inda zai iya jin me make faɗa, saboda bana so in damesu saboda har wasu sun fara cin abincin;
"Me za'a zuba maka Yaya?"
Na faɗa ba tare da na bari mun haɗa idanu ba, "fried chicken with mixed fruit" ya faɗa shima yana kauda kai gefe cikin salon shi na miskilanci wanda ni na kula ma kwata-kwata shi haka halinshi yake;
Ban ƙasa a guiwa ba kuwa nayi maza na zuba mashi, nuni yayi mani da ido da na bar wajen daidai lokacin da nake miƙa plate ɗin gaba shi, na daga ƙafa cikin sauri na bar falon domin wasu daga cikin baƙin sun fara tsare ni da idanu, ina tunanin shima abunda ya kula dashi kenan.
*******************************
Bansan ya suka ƙare da baƙi ba, domin ni na fita batun su tinda dai na gama masu abin da zan masu, hutu aka bamu cikin gidan na kwana biyu domin family ɗin zasu yi wata tafiya da mu kanmu yan cikin gidan bamu san ina zasu ba, saƙon Alhaji Mustapha ne ya iso mana, dama duk in zasu yi tafiya koda ta yini ɗaya ce ya kan mamu alkhairi irin nashi da ya saba. Kudi ne masu yawa ya bayar a rarraba mana koda zamu buƙaci wani abu baya nan.
"Allah sarki, Allah ya saka ma Alhaji da alkhairi ya ƙara buɗi na Alkhairi" umma ta ta faɗa lokacin da saƙon namu ya iso gare mu, su kau sauran ma'aikatan ƙananan maganganu suka hau yi, wai sun fi so Ya Ameen ya basu kyauta saboda shi bai Iya kyauta ba da yawa yake bayarwa. Kaji butulci irin na ɗan adam, mu dai bamu damu ba ai ance ma raina kaɗan ɓarawo ne, kuma ko ba haka ba umma ta tana da wadatar zuci abu kaɗan ke isar ta a rayuwa hakan ce tasa nima na tashi da irin wannan tarbiyyar.
*******************************
Sun shafe kwana biyar babu su a cikin gidan hakan ce tasa muka samu sauƙin tsangwama da walwala acikin gidan, dama ba mu ke aikin abincin ma'aikata ba iyaka ayi mukai kwano in mun gama ci mu dauraye, iyakarmu gyaran dakinmu sai ko umma ta da take share tsakar gida, domin ita bata son ƙazanta Sam bata iya zama cikin ta, yayin da su kau sauran basu damu ba kitchen ɗin girki kawai suke share wa.
Wani lokaci nakan shiga lambun gidan insha iska ko in katso gwaba ko Apple in ci idan nayi marmarin hakan, umma ta bata hanani domin ta san ko babu komai ba kullum muke samun irin wannan damar ba, hanani sake wa da sauran ma'aikatan kawai ta hanani shima mafi yawancin mazan ne, nima ban damu ba saboda da irin wannan tarbiyyar na taso ta rashin sake wa da maza.
Shugabar ma'aikata mata ce ta leqo ɗakin namu, lokacin ina toilet wankan ƙa'ida na idan na tashi baccin rana ƙarfe uku wanda sake wa yanzu ya zame man kaman nafila cikin ƴan kwanakin nan da sukayi basa nan.
" Maman Suhana Hajiya ce tayo waya, tace a faɗa maku ku gyara masu sashen su duka, Suhana ta gyara na Alhaji ƙarami da na Abie domin dukkan su gobe suna hanya idan Allah ya kai mu"
Dam!! Naji gaba na ya ruguje ya faɗi, daidai lokacin da na fito ina goge kai da towel ɗina na wanka, shi kenan zasu dawo, shi kenan walwala zata ragu, Abunda zuciya ta ke ƙissima man.
"To Talatu, insha Allah yanzu zamuje mu gyara, Amman gyaran zai kai goben tun da kinga yanzu marece ya riga ya kawo jiki" Ummata ta faɗa tana mai kallon Talatun, Talatun ta amsa mata da cewa "To shi kenan Maman Suhana ai ba damuwa gaskiya aikin da yawa, ku fara ɗin zuwa da safen kwa idasa" ta faɗa tana mai ficewa a ɗakin, da kallo na bita, matar kam kaman ta Allah to sai dai fa fuska biyu gareta, domin ita ce ta gaban goshin Hajiya babba a gidan Amman bata bari a sani,; nima na san hakan ne ta dalilin a cikin gidan nake nawa aikin kuma harda ɗakin Hajiyar nice ke gyarawa.
Haka kau aka yi tuƙuru muka hau gyaran cikin gidan, ko ina yayi ƙal, ya rage gyaran ɗakin Abie ne da ya Al'Ameen ya rage, shima idan aka yi Magriba zanje na gyara na Abie, na Ya Ameen ne sai goben Saboda na san halin wannan sarkin ƴan tsaftan, tsaf zan gyara Amman yana zuwa zai ce baiyi ba.
::::::::::
Washe gari tin da duƙu-duƙu na tashi gami da shiryawa na leƙa ɗakin Shugabar ma'aikata na amso makulli, an ma ci sa'a domin bai barin makullin ɗakin shi a hannun kowa wannan sarkin ƴan tsarin.
Yanda yake na daban, haka ma part din nashi yake, komai dake shashen daban yake da sauran abunda ke cikin gidan, ba wasu tarkace amman an narka dukiya wajen;saitin kujeru ne a falon farare ƙal masu kwalliyar golden haka jefi jefi a jikin su, golden tiles ne malale a falon da ya ƙawatu da wani makeken chinese carpet da ya lashe fin rabin falon bayan su babu komai sai center table na zallan glass fari tar dashi mai haɗe da tumtum irin na gidan sarauta guda biyu tsakiyar falon, akwai stools suma kwara biyu tsakanin kujerun, sai saitin kayan kallo ƴan kamfani Samsung haɗe da Italian Tv stand, up White ne fentin falon yayin da ya dace da cottons masu matuƙar kauri suma kalar golden, sai na'urar sanyaya ɗaki da water dispenser dake maƙale a saƙo guda na falon. Kai kanka in ka kalla sai ka sake kallo, iya tafiya da imani falon ya tafi da nawa.
Corridor ne gefe guda daga bangon hagu da ke falon, idan ka bishi shi zai sadaka da ɗaki ɗaya tal acikin shashen da yake mamallakin shashen, sai ƙofar ɗan ƙaramin kitchen da yake ta cen ƙuryar Corridor ɗin da yake ɗauke da madaidaicin dining area a ciki, kitchen din ya tsaru kaman na wata macen komai na aikin gida akwai shi ciki, sabo da Ya Ameen ya iya girki, in ƴan miskilancin nashi suka taso shi ke girkawa da kanshi yaci abun shi ko kuma in yayi baƙin shi yakan dafa masu abinci simple kuma ya wanke dishes ɗin da kanshi.
Yanda falon ya tsaru sai naga ma kaman bedroom ɗin yafi ƙayatuwa, shima komai upwhite ne da kwalliyar golden, saɓanin toilet ɗin da yake kalar sararin samaniya da fitilu farare, sai ya zamana abun burgewa da ban sha'awa.
Zagewa nayi na gyara ko ina na ƙalƙale, shi tas na kunna boner ta ruwan ƙamshi, take part ɗin ya ɗauki ƙamshi mai sanyaya rai, sannan na kunna na'urar sanya ɗaki domin ƙamshin ya kama ko'ina,bayan na gama na kashe komai na janyo part din na kulle gami da mayar ma da Mama Talatu makullin.
*******************************
Ƙarfe biyar sakaliyya suka iso gidan, yayin da dukka mu ma'aikata muka fita taro su da yi masu barka da zuwa, harda umma ta baiwar Allah da take sanye cikin zurmemen hijab ɗinta, wanda bata ma lafiya kwance take zazzaɓi ne rau a jikin ta, Amman hakan bai hana ta fitowa ba, tinda haka aka saba kafin su shiga part ɗin nasu sai an gaggaisa da kowa tare da jin lafiyar kowa, wannan doka ce daga Alhaji mustaphan wanda a haka dole suke tsayawa suna zuzzunɓura baki suna aika mana da harara su sun dawo a gajiye amman baza'a bar su su shiga ciki su huta ba. Hakan baya damun Alhajin domin ya saba da halinsu tsaf halin mahaifiyarsu ne hakan ta saba masu dashi, halinta ne tin kafin ya aure ta kyamar talaka, masu aiki, sai dai yana tausaya masu har faɗa yana masu a lokutta da dama yakan ce "ku shiga taitayinku kuma ku natsu kusan inda yake maku ciwo, faɗi baya dauwama, haka ma wuya, kuma aure zakuyi ba kuma kusan gidan wanda zakuje ba" Hajiyar kan amshe da cewa "a'a alhaji ka rinƙa faɗar alkhairi a bakinka fa, yaran nan fa kai ka haife su"
Wannan karon da Afan mutuniyata aka dawo, sai aunty Feena da yaran ta guda biyu ɗan shekara shidda mai suna Ayan sai ƴar karama da ba zata fi shekara biyu ba Nasreem.
Aiko tana hangoni tayo kaina da ɗan gudun ta, maimakon in ce mata oyoyo sai itace ta rigani cewa "oyoyo aunty suhan sai kuma gaki" ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya gami da daka tsalle ta rungume ni sai kace wata 'yar yarinya, Afnan ba zata kai tsara ta ba, ko ba komai zan iya bata shekara uku haka, riƙe take da hannun Ayan, hakan ce tasa nima murmusawa gami da tsugunna wa bayan na bamɓare ta a jikina; tsugunna wa nayi na cicciɓi Ayan din ina cewa a hankali "aini fushi nake yi da ke, ko waya Afnan kinma manta dani kwata-kwata, sweet Ayan ne kaɗai nawa ni, shi da nasreem.
Ƙyalƙyalewa tayi da dariya," Allah Aunty suhan ba haka bane, karatu ne yayi zafi Amman Allah Allah nake lokacin zuwan mu hutu yayi inzo inga ya kika koma, na san kina nan kin ƙara kyau abunki". Murmushi nayi ina cewa nima nayi missing ɗinki Autan Hajiya, ya kamata kuje ki huta hakanan".
Ashe bamu sani ba duk hankalin su ya dawo kaina Alhaji da Aunty Feena sai murmusawa suke yi, ita aunty Feena ɗaukar da nayi ma Ayan ce ta burge ta kunsan mai ɗa wawa, yayin da su kuma su Aunty Nihal haushi ya cika masu rai, Afnan ɗin na basu haushi, tana zubda masu daraja, wai ace House maid ce take yi ma haka?, dubeta ita kuma dalla har da wani daukar Ayan salon ne ta shafa mashi datti. Tsoki suka yi cikin rai, su kuma sauran ma'aikatan haushi ne ya cika masu rai na fifita ni da Afnan ɗin keyi akan su,basu yi la'akari da cewar su sun girma ba sun manyanta.
Gogan naku na gefe jingine da motar shi, ya harɗe ƙafafu yana ta kallon su, bai ko murmusa ba Amman dai sun burge shi cikin ranshi, shi yasa yake masifar son Afnan ɗin ita ce ƴar gaban goshinshi, saboda ko kusa ba halinta daya da sauran yayyen nata ba.
Mu kuwa hankalin mu ma bai kai kanshi ba da yake gefe yana ta zuba mulki da miskilancin har aka gama gaggaisawa muka juya zuwa shashen mu su kuma suka nufi cikin babban apartment ɗin nasu, har sun kai babbar ƙofar da zata sada su da cikin gidan, Afnan ɗin ta juyo gami da kwalla man kira, "Aunty suhan.!, in na gama hutawa ina nan shigowa ki ajiye man abun daɗin nan" ta faɗa cikin ɗaga murya gami da yin ɗan tsalle ta kashe man ido daya, bata jira cewa ta ba ta shige cikin gidan riƙe da hannun Ayan yaro ɗan gayu ɗan hutu gashi mulmul dashi, hakan ce ta sanya kallo ɗaya yaron ya shigar man a rai tin Wancen zuwan da sukayi, tin kafin ma ayi mashi ƙanwa ne; murmushi nima nayi gami da ƙada kaina "hooo Afnan ba dai rigima ba" na faɗa a fili ina shige wa shashen namu, ko ba komai zan ɗan samu sassauci zuwan Afnan ɗin domin tana ɗebe man kewa, tin umma na hanani har ta haƙura ta barni domin ta kula cewa halin Afnan ɗin ya banbanta da sauran ƴan uwan nata.
**********
"huh...." ajiyar zuciya yayi tare da guntsar iska ya fesar, a hankali ya fara taka wa gami da nufar nashi apartment ɗin domin ya gaji over, makullin dake hannun shi yayi using ya buɗe sashe nashi; Turus ya ja ya tsaya, wani sas-sanyan ƙamshi ne ya bugi dogon hancin shi, lokaci guda ya maida kallon shi bisa kowanne lungu da saƙo na falon, kaman dai an cenza komai?, Amman inaaaa..... Su ɗin dai ne, hmmmm? 🤔 Wanene yayi wannan aikin? Ta bayar kanshi yake Amman ya kasa lalubo amsa.
Jiki a sanyaye ya nufi Corridor ɗin da zai sada shi da bedroom ɗin nashi, still dai nan ma haka, aah! Mamaki bai gama cika shi ba sai da ya murɗa handle ɗin ɗakin ya shiga.; gadon shi an lailaye shi da zanin gado mai kyau da yayi order daga dubai bai iso ba sai da baya nan, hakan ce ta sanya Talatu buɗe ɗakin ta ajiye a cikin wardroop, ni kuma da nazo gyara na gani na yaye na sama duk da baiyi dauɗa ba na shimfiɗa na saka Wancen cikin laundry basket. A hankali ya taka kaman mai tsoron ɗakin, gami da isa bakin gadon ya zauna a hankali.
Taushi da sulbin zanin gadon gami da ƙamshin da suke tashi daga saman gadon ne suka sanya shi sulale wa ya kwanta bisa gadon sosai yana mai kallon POP din dake saman ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke a jere har sau uku gani da furta "Suhan" a hankali domin kuwa ya san wannan aikin ba na kowa bane sai ita.......
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:22 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI ƘARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven, No pain, so Magical Our creative golden pen, Be hold our words, A production of our pen, savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Gaisuwa ga ƴan golden pen, expecially ~Yaya Umar Dalhat Funtua~ muna godiya da ƙoƙarin editing, na baka kyautar wannan Page ɗin, kayi yadda kake so dashi. Allah ya ƙara haɗa kawunamu ameen*
*Page ~7~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Haka kau aka yi, ina gama sallar magariba sai ga afnan saɓe da Nasreem a kafaɗa, riƙe da hannun Ayan tana jan shi a hankali, sallama tayi fuskar ta cike da annuri da fara'a ta shigo, yayin da ta ajiye Nasreem bisa katifar tamu, ta janyo Ayan shima ta zaunar dashi, wutsil yaro ya haye kan cinya ta da nake zaune bisa dadduma.
"ku ji mu da yaro dan Allah, sai san jiki kaman mage" Afnan ɗin ta faɗa tana mai kama baki alamar mamaki, murmushi baiyane a saman kyakkyawar fuskar ta, lokaci ɗaya ta maida duban ta wajen umma ta da take zaune itama bisa tata daddumar domin bata tashi idan ta gama sallar magriba har sai ta kammala isha'i;
"umma ina yini ya kwana biyu ya jiki-jiki, dan ko ba'a faɗa ba naga kaman baki lafiya" ta faɗa cike da girmamawa, Afnan yarinya ce mai cike da natsuwa, biyayya da girmama na gaba da ita ko da kuwa ta fishi da komai, shi yasa rayuwar ta da ta Ya Ameen ta kusan zuwa daya bambancin kawai shi akwai ɗan miskilanci a al'amuran shi in ya so, saɓanin ita mai walwala ce da zaulaya in taso, ta ɓangare daya kuma ga sangarta idan taso gami da shagwaba sabo da ita ce auta, tana da wani hali guda ɗaya da yake burge Alhaji mustapha, hakan ce tasa idan tazo mashi da buƙata ba dai ya Musa mata ba, yakanyi duba na tsanaki ga buƙatar tata, halin kuwa shine *manyance* watau tana da tinani irin na manya, lokutta da dama Alhajin kan zauna yayi magana da ita ta tsanaki idan ya je cen ko kuma idan ita tazo nan.
"lafiya ƙalau Afnan, kun iso lafiya ko,? Ya gajiyar tafiya? Kunsha hanya, maimakon ki zauna ki huta Alabasshi idan mai duka ya kai mu kin shigo ku sake gaisa wa, shine kika kwaso yara kuka taho, kika rabo su da umminsu kika zo nan dasu kina kwasar masu sanyin nan" umman ta wa ta ƙarashe tana mai duban afnan ɗin tare da miƙa ma Nasreem ɗin hannu alamar ta taho, ai kuwa ba musu yarinyar ta muƙe cikin salon tafiyar ta irin ta ƴaƴan turawa ta isa wurin umman tawa tare da ɓangala mata dariya, cikin gwarancinta take ta mata jagwalgwalon surutun su irin na yara; Afnan ce ta amsa mata da cewa "Ai umma ba zama in har banzo mun gana da aunty suhan ba, in wanke laifi na sannan in sake kafa wani gwamnatin domin naga Ayan yana neman kwace man fada, don ma na san ba zaki barta ba da cen ɗakina muka tafi muka sanya labule Alabasshi sai ta kwana cen da safe ta dawo" murmushi kawai umman tawa tayi alamar ba zata bari ba, sannan ta maida hankalinta kan Nasreem ɗin lokaci daya tana cewa "to kiyi maza ki gama kinsan ba daɗewa za'a neme ki sabo da yaran da kika taho dasu" "toh umma insha Allah" Afnan ɗin ta faɗa tana maido hankalinta kaina da nake ta wasa da hannun ayan, son yaron ya shiga raina sosai na rasa dalili, kuma ni ba mugun daɗi ma nake da mahaifiyarshi ba duk da dai cewa tafi su Saudat kirki ko don ta girmesu ne, ta fisu hankali shi yasa? Oho
"Aunty Suhan kinga yanda kikayi shar abunki? Hutu ya ratsa ki wallahi kin ƙara kyau fatar ki sai sheƙi take yi minene sirri?" ta faɗa muryarta cike da zaulaya, ni sai ma ta bani kunya wallahi, sunne kaina nayi cike da kunyar umma ta da take zaune wajen, kuma tana jiyo duk abun da muke faɗa, ita kau Afnan na lura da ko ajikinta ma........" ba wani nan afnan kece zan cema haka Allah" na faɗa cikin murmushi, har cikin raina ina ƙaunar afnan ɗin, sabo da ko ba komai zuciya tana son mai kyautata mata, Afnan ɗin na son mu har cikin ranta, bata gudun mu ko kyamatar mu kaman yanda sauran suke yi, hakan ce tasa daga ni har umma ta muka sakankance mata muka saki jikin mu da ita.
"Humm,,, haka dai kika ce Aunty na, ya Maganar karatu kin ƙarashe kuwa?" ta jefo man tambaya cikin halin ta na manyance; Lokaci guda gaba na ya ruguje ya faɗi, saurin saisaita kaina nayi domin kada ta fahimci wani abu, sannan nace mata "har na gama fa Afnan" "wow, har kin kammala aunty suhan?, wane course kika karanta ne?, na fa dade rabo na da nigeria wlh" ta maido man tambaya cikin tsammanin samun amsa daga gare ni, hakan shi ya ƙara ruɗani har firgici na ya fito fili cikin inda inda na mayar mata da cewa
" Secon. dry school fa na.. ke nufi Afnan" zaro idanu tayi jin abunda na faɗa "meh😳" ta tambaya cikin son jin ba'asi "eh" na mayar mata ina mai gyaɗa mata kai kaman ƙadangaruwa, "look aunty suhan kibar wasa, ni na san umma ba zata hana ki ba, kuma nasan tinda Ya Ameen yana ƙasar ba zai sa maki ido kina zaune baki aikin komai ba kuma ke ba karatu kike yi ba" (kuji Afnan ɗin nan ma, wai bata aikin komai🙄) ta mayar mani cikin ɗan ɓacin rai, sabo da na kula hakan baiyi mata daɗi ba.
Tsam umma ta tayi tana mai son jin amsar da zan bata, yayin da ni kuma nayi ƙasa da kaina ina mai cije laɓɓa na kamar zan huda su, alama nake yi mata da tayi shiru, Amman kaman ma bata san ina yi ba, cigaba tayi da cewa "kinga kin girmeni, Amman kina nan kina kallo zanzo in gama makaranta ta, na fiki ƙananan shekaru amman na fiki sanin abunda zai amfane ni nan gaba, gaskiya in wani ya baki shawara tsaida karatun ki daga iya Secondry bai kyauta ba, sabo da dashi ne zaki tallafi rayuwar ki nan gaba har ma da ta umma" tana kai aya naji kaman in zunduma da gudu, kaman in ɗora hannu a kai🙆🏻 in ta zunduma ihu😵
"afnan ya kamata mu bar maganar karatun nan hakanan shi komai da kika gani muƙaddari ne, idan da rabon inyi nan gaba sai kiga Allah ya kawo wani sanadin" na faɗa ina mai son ta fahimci umma ce ta hanani, ta kuwa fahimta domin naga ta dan zaro idanu waje sai kuma ta gyaɗa kai gami da cewa "tau ai shikenan Allah ya kawo aunty Suhan, dama zuwa nayi in tambayi umma don Allah ko zata barki ki raka ni siyayya zuwa gobe insha Allah ba daɗewa zamuyi ba" ta maida maganar tata kan umma ta da take ta jijjigar Nasreem har ta samu tayi bacci, "Allah ya kai mu" umma ta bata amsa cikin yanayi da na kasa karanta, Sam ba zata iya nuna ma Afnan ɗin ɓacin ranta ba domin ko babu komai maso uwa tau lallai yaso ɗanta, Afnan ɗin na daga cikin mutanen da take ganin girman su duk da ƙarancin shekarun nata kuwa,.
Miƙewa Afnan ɗin tayi gami da gyara gyalen dake saman kafaɗar ta, tana mai cewa "To umman mu, aikau godiya nake yi bari muje sai da safe kinga ma kuwa ta maganar ki har sunyi barci, bari in kai Nasreem ɗin in dawo in ɗauki Ayan ɗin, tinda ban iya ɗaukarsu su duka" "a'a bari Mama na ta ɗaukar maki Ayan ɗin ai ba kin ta jigila ba tinda ga wadda zata iya taimaka maki, kuje ta kai maki shi, sai da safe ki gaida hajiyan da yayar taku" umma na ta mayar mata cikin ɗan murmushi, "to umma aikau na gode, aunty na taso muje aiki ya ganki na ɗaukar wannan gabjejen saurayin haka gashi yayi bacci ya ƙara nauyi, ko in goya Nasreem ɗin muyi kama kamar Ayan ɗin" ta faɗa cike da zaulaya da son sanya ni dariya da ta kula kaman walwala ta duk ta tafi, tinda aka yi maganar karatu, aikau ta ci nasara murmusawa nayi ina mai Miƙewa tare da faɗin "ance maki kowa ma raggo ne irin ki, da sai munyi ma yaro na kama kama?" na mayar mata cikin nima tawa zaulayar daidai lokacin da muke ficewa daga cikin ɗakin a tare.
Ko da muka isa muka kwantar dasu sai da tace zata rako ni, nice na hana ta, ganin dare yayi, nima ina komawa nayi sallah na kwanta tinani fal cikin raina na Afnan ɗin da ƙarfin hali, ko ma dai miye ina fatan ta bar maganar karatun nan haka nan, bana son Abunda zai jawo man matsala da umma ta muna zaman zaman mu lafiya ƙalau, tinda na kula har cikin ranta ba son maganar take ba.
~~~~~~~~~~
Bai san lokacin da bacci ya kwashe shi ba a haka, sabo da sanyi da tsaftar ɗakin gami da taushin zanen gadon, sai dai farka wa yayi yana mai jiyo kiraye kiraye sallar magrib na tashi a laud speaker ɗin masallacin da ke gefen gidan nasu, a kasalance ya tashi gami da cire kayan, ya faɗa toilet domin yin wanka da alwala, mamakin yarinyar yake yi sosai, a ina ta iya irin wannan tsaftar haka? Gashi komai a nutse, ta ajiye komai inda ya kamata, hatta da towels ɗin wanka ta cenza mashi wasu, ta dauraye waɗanda suka yi dauɗa ta shanya a ɓangaren shanya na toilet ɗin, ta kwashe tarkace robobin shower jel da hand wash liquid soap ɗin duk ta zuba su a shara taje ta zubar, toilet ɗin ƙar, kaman an cenza komai na ciki ya koma sabo, shi kanshi cikin jin daɗi yayi wankan, ya fito yana mai jin daɗin jikin shi da ƙamshi da jikin nashi yake yi, shi ya siyo product ɗin Amman ta zaɓi waɗanda suka dace ta ajiye mashi.
(yo Al'ameen wannan ai aikin Suhan ɗin ne a cikin gidan ko baka sani ba?)
Bai sha mamaki ba sai da ya buɗe wardroop ɗaukar kaya,, ya tarad da komai ta ware mashi wajen shi ta kimlace su, ta kwashe duk wasu tarkace masu datti ta zuba a laundry basket; cikin natsuwa ya shirya gami da taje sumar kanshi tayi luf abun ta, ya fesa turare, gami da zura Jalla biya, ya fito yana taka wa cikin salon tafiyar shi ta ƙaƙƙarfan namiji, domin zuwa sauke farali sallar magariba.
*******************************
Washe gari ma da nake nawa aikin, haka Afnan ɗin tazo tana taya ni, rabi surutu rabi tsaukana, yo eh tsaukana mana zance, tinda da ta fara shara ko goge goge sai ta duƙe ko ta faɗa kan sofa tace "wash wlh aunty suhan na gaji da yawa, gaskiya kina ƙoƙari" na kan yi dariya ince "Afnan kenan, miye na gajiya a nan?, aikina ne fa"
A haka muka gama tana mai ƙara tuna man da cewa ƙarfe biyar fa na yamma zamuje shopping ɗin nan don Allah inyi shiga ta kece raini, (Lol🤣 Afnan kenan)
Ƙarfe biyar tayi daidai da shiryawa ta, doguwar riga na sanya irin dubai abaya ɗin nan, da Alhaji mustapha ya taɓa yo man tsarabar ta, abayar na matuƙar karɓa ta, baƙa ce sosai har ƙasa sai dogon wando daga ciki, haɗe take da gyalenta, saboda haka sai Kaga dama sannan ka sanya hijab, kwalliyar golden ne jikin ta da adon wasu duwatsu farare daga sama har ƙasa, wannan shi ya ƙara ƙawata rigar, banyi wata kwalliya ba sosai domin ni ba ma'abociyar shafe shafen nan bace rambatsai.
Hoda kawai na murza, sai kwalli da na zizara ma idanu na, haɗi da shafa lipstick mai ƙamshin Apple shima fari ne da ɗan sirkin Light pink haka, parking ɗin gashina nayi, tini ni dama ba ma'abociyar kitso bace sabo da gashina irin na asalin Fulani ne, mai taushi da sulbi, ga yawa da tsawo, wanda saidai in wanke shi kawai in shafa mashi mai in haɗa shi in ƙulle hakan ya wadatar dashi, turare irin namu na mata mai taushin ƙamshi na fesa haɗi da shafa humra ƴar Sudan da aunty saudat ta bani kwanaki cikin kwalimar ta, sai ƙamshin ya haɗe ya bada wani ni'imtaccen ƙamshi.
(ka ganni kaman ba yar aiki ba😅)
Afnan ce ta shigo cikin saurin ta tana cewa "Aunty Suhan maza ki fito, ga yaya cen yana jiran mu na lallaɓo shi, zai kai mu kinsan halin nashi baya son jira, ɗan oya oya ne." Turus ta ja ta tsaya lokaci guda mamaki fal bisa fuskar ta, lokaci guda ta shiga taɓa hannuwa, 👋🏻 sannan ta shiga faɗin "Aunty Suhan wannan kyau haka? Dubeki dan Allah kaman wadda zata je gasar kyau, kina da irin wannan kyaun haka kike boye wa?" jan hannuna ta shiga yi tana faɗin masha Allah wannan ai ni sai ma inji kunyar jerawa dake wlh abu kaman ƙyanƙyasar inji? " ta ƙarashe da zaulaya
Ja nayi na tsaya ina cewa "Afnan Allah in kwalliyar tayi yawa bari in rage, yo ni wa zan ma kwalliya har haka?" murmushi ta sake yi, da ya riga ya zama ɗabi'arta, "ke wasa fa nake maki, Ya Ameen ɗin ne zai tsaya wani jiranki? Har ma fa ya shiga mota mu kaɗai yake jira, kuma yace in na ɗaɗe zan ga wayam, saidai idi dreba ya kai mu" ta shiga faɗi tana mai sake jan hannu na, ni kuma na shiga binta kaman raƙumi da akala.
A tsakar gida muka haɗu da umman tawa, tana shigowa dan shirya zuwa girkin dare cikin gida, da addu'a da fatan dawowa lafiya ta bimu, sannan ta mana gargaɗi da mu kula da kanmu ƴaƴa mata muke, to muka amsa mata gami da jerawa da Afnan ɗin kai ka rantse ƙawaye ne, domin Afnan ɗin ta taddoni a jiki, saidai ɗan tsawo ne kawai zan nuna mata, ba kowa ne ma za'a gaya ma na girme ta ba ya yarda.
Bayan motar ta buɗe mani na shiga, wani sanyi ne mai ratsa zuciya ya mani sallama, ban san lokacin da na ja mun fashi ba, gami da runtse idanu na ba sannan na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya, mota ce mai suna mota, na tabbata ban taɓa shiga mota makaman ciyar wannan ba, duk kuwa da tarin motoci na alfarma da suke gidan.
Tada motar da yayi, shi yayi sanadiyyar dawowa ta cikin hayyaci na, daidaita kaina nayi cikin sanyin magana nace mashi "ina yini Yaya" duk da bana iya hangen shi sosai bayan shi kawai nake iya gani don ta saitinshi nake zaune sai ayan da ya kwanta bisa cinya ta, ina iya hango motsawar shi da motsawar bakin shi ta cikin mirror dake maƙale na driver, "lafiya" ya bani amsa a taƙaice, ban kuma cewa komai ba, sai wasa da na shiga yi da ayan, yana bani labarin school ɗin su a hankali, ina jiyo Afnan ta cika shi da surutu da take zaune gidan gaba wani abun ya amsa mata, wani kuma yayi murmushi kawai ya share ta.
A haka muka isa tanƙamemen super market ɗin da ya haɗa komai, komai na kayan more rayuwa ana saida shi a ciki; ɓalle murfin motar nayi naja hannun ayan muka fita, yayi daidai da fitowar Afnan ɗin tana cewa "Yaya kai ba zaka shiga ba?" girgiza mata kai kawai yayi yana miƙa mata ATM ɗin nashi gami da cewa "30mnt na baku kuma, kuyi maza ku fito ina jiran ku, ina da nawa uzirin rigimar ki ce kawai bana so Lil" (da yake ya kan ce mata Lil wani lokacin)
"OK Bigboo, insha Allah, ta faɗa tana mai ƙamewa cikin zaulaya, zagayowa tayi gami da kama hannun Ayan tayi gaba ni kuma na bita a baya kaman wadda kwai ya fashe mawa, tinda sanyin ac da ƙamshin motar Yaya suka bugeni naji komai nawa ya kwance, kaman an zare man lakka, lallai Ya Ameen daban ne, komai nashi ma daban yake; Ban san mun isa ba saida naji Afnan ta girgiza ni tana cewa "Aunty suhan lafiya dai kuwa? Ko baki lafiya ne?" ɗan murmushi nayi na shiga girgiza mata kai, ina mai cewa "a'a Afnan babu komai kawai dai wajen ne ya burge ni, mu shiga kada mu cinye lokacin mu anan"
Nacewa Afnan ɗin tayi saidai in taya ta zaɓe, haka kau aka yi, duk Abunda na zaɓa sai ta ɗauki biyu, kama daga kayan shafa, kayan maƙulashe, kayan sawa da su eaner wears, Ayan ma da Nasreem ta ɗaukar masu kayan ciye ciye sabo da su basa buƙatar komai.
Haka muka fito masha Allah gaskiya wurin yayi kyau ya ƙayatar dani, haka nake faɗa ma afnan ɗin a hanyar mu ta komawa motar Yayan.
"Ta bangaren shi baya so tinanin yarinyar kan nushe shi a lokutta da dama, sai dai yakan danganta hakan da tausaya masu da yake yi, dubeta don Allah gwanin burgewa yanzu, kaman tayi ta dauwama a haka, ya kula tin shigar ta motar tashi, kashin turarenta ya bayyana kanshi, ƙamshi mai cike da kwantar da hankali, yana so tayi karatu, yana so ta tallafi rayuwar umman tata, yana so su samu ƴanci, sai dai me yasa?, me yasa umman tata take da wani irin tinani, me yasa ta nace ga rashin son tallafa masu da yake yi? Ya haƙura, ya haƙura tin ma kafin ta fara zargin ko yana da wata manufa tashi ta daban akan su, Suhan yarinya ce mai cike da natsuwa, mai cike da kamewa, tana da gudun abun duniya, wannan kaɗai ya isa ya yaba ma mahaifiyar tata, ta nan fannin kuma ta ciri tuta, ta kai a yaba mata gaskiya, kuma yana ganin ƙoƙarin ta, tayi aikin ta na uwa ta haɗa harda na uban ma; "Huh" ya guntsi iska ya fesar, yana saisaita kanshi ga barin kallon ta tin ma kafin ta ankara don baya son raini ya shiga tsakanin shi da ita. 😂
*********
A haka muka isa gidan Afnan ta kama man kayan muka shiga dasu ɓangaren mu, don ta nace cen zamu ajiye kayan ta fitar ma da kowa nashi, a cewarta rabon mu yau ya rantse don duk siyayyar nan da aka yi, cikin kudin Yaya ne, shi yasa ta zage ta ɗibar mana son ranta tinda ba nata aljihun bane yayi kuka, ina jiyo ta tana cewa "Yaya ina so muyi magana, fa wallahi" amsa mata yayi yana cewa "To my Lil, mu bari zuwa dare in na dawo sai mu tattauna, yanzu dai ina da muhimmin uziri kinji auta" ya faɗa yana mai murmusa mata, "OK yaya, as u said bye-Bye, sai ka dawo, a dawo lafiya" ta faɗa tana mai manna mashi ɗan ƙarami peck a kumatu sannan ta sake ɓalle murfin ta fito, na kula ɗabi'ar turawa ta kama su, har basa jin komai su rungumi juna, ko sumbatar juna a goshi, ko kumatu a gaban bainar jama'a, Ni kau tini nayi nisa da ragowar kayan da Ayan saɓe a kafaɗa ta.
Haka ta wawware ma kowa kayanshi, harta umma ta, ta ɗauko mata atamfofi masu shegen kyau ƙwara uku, da less guda biyu, sai hijabai masu ruwan kayan guda uku, da takalma ƙwara biyu, masu kyau zubin na manya, Godiya umma ta ta shiga yi da faɗan na biye mata ta kaso kuɗi da yawa, wannan ai ɓarna ce, "ba komai umma wallahi Albarkarku kawai muke nema" Abunda tace kenan sannan tayi ma umman Alƙawarin za mu kwashi kayan namu da nata masu buƙatar ɗinki, mu kai ma telan dake ma gidan ɗinki, umman taso ta hana ta a cewarta hakan ma ya isa zamu bada nan cikin unguwa ayi mana, ba sai ta ƙara yin wata hidima ba, Amman Afnan ɗin ta nace ai babu komai wallahi duk yi wa kai ne.
Nima ta ware man nawa kayan, wanda sai da tsoro da firgici suka kama ni, rabi da kwantan siyayyar ma ni tayo ma wa, kai ni afnan wacce irin ƙauna take yi mani har haka?, "Godiya na shiga yi mata tare da faɗin sunyi yawa ta rage" ɓata fuska tayi tana cewa"ga duk kan alamu watan ɓatawarmu yayi, ai in tazo Nija bata da ƙawar da ta fini, don me zan maida hannun kyauta baya, banga yanda nake yin kyau ba idan nayi kwalliya? dama maƙasudin siyayyar nice, sabo da bata yo man tsaraba ba da zata taho" godiya muka shiga yi mata ni da umma ta, lokacin da take kwasar nata kayan da basa da wani yawa sai kayan ciye ciye kawai.
Sallama muka yi da ita, tare da mani Alƙawarin gobe zata shigo musha fira in na gama ayyuka na na cikin gida, har bakin sashen namu na raka ta, ina mai walwala da annuri a fuska ta, domin duk wanda yace yana son ka ai ya gama maka komai a rayuwa, ina ganin sauran ma'aikata ana ta zunɗe na, to suma dai da zata wuce sai da ta gaida su, ta masu ɗan Alkahiri a cikin kuɗin da ke pos ɗinta, Amman duk da haka baiyi masu ba, masu mugun abun ganin wannan tarayya tamu ta watse suka ƙudura, masu gulma suka naɗa, domin a gaban su muka shiga da leda niƙi niƙi, Amman sunga ta fito da guda ɗaya tal a hannu, ita ma ba'a cike ba, ashe yau Hajiya Babba da labari kenan, wai don ma basu san Yaya Al'ameen ne ya kai mu ba, wai ni Allah ai da kashin mu ya bushe daga ni, har mahaifiya ta, a haka dai na tura masu aniyarsu, na juyo salin alin na shige namu ɗakin tare da turo ƙofa, domin ɓoye kayan namu, sabo da wasu daga cikin su ƴan ganin kwam ne, zasu iya leƙo wa ko don ganin wainar da ake toyawa a cikin ɗakin.
***************************
Ƙarfe tara da rabi daidai, Afnan tayi sallama sashen Yayan nata, izini ya bata ta shiga daga ciki, kai tsaye kujerar da yake zaune kai yana latsa laptop ɗin shi ta nufa, sanye yake da 3quater ruwan kunun kanwa, watau army green, da fara ƙal ɗin singleti, sanyin falon madaidaici ne, har yanzu gyaran da Suhan ɗin ta yi ma ɓangaren nashi yana nan, tinda ba yara ke akwai ba a sashen, ba yawan abokai ya cika ba, (yo wannan miskilancin nashi zai bar shi yayi abokai ne?) fuskar shi tar cikin haske da yake fitowa ta laptop ɗin, lallai Yaya Al'ameen ƙaƙƙarfan namiji ne, hakan ko ya samo asali ne da jim ɗin da yake zuwa akai akai, a sashen motsa jiki na gidan, kyakkyawa ne na gaske, cikin kalar fatar shi fara tas tas da ita.
Murmushi yake bin ƙanwar tashi da shi, har zuwa lokacin da ta iso wajen nashi, hannu ya miƙa mata tare da zaunar da ita dab da shi yana mai faɗin "Lil wannan magana dai wace iri ce, da har aka bata muhimmanci haka?"
Kallo ta bishi dashi, tana mai ƙara jin ƙaunar yayan nata cikin ranta, shi kaɗai ne zai zauna da ita ya fahimci damuwarta, har yayi mata maganin ta, in ka ɗauke aunty feena da dama ita wannan kaman uwa ta ɗauke ta, tinda a hannun ta ta taso.
" yaya so nake muyi wata magana mai muhimmanci, dafatan zaka saurare ni, kuma ka fahimce ni, kayi ma maganar tawa kyakkyawa duba na tsanaki, don Allah"
Na ɗaya daga cikin dalilan da yake sanyawa yana ƙara jin ƙaunar ƙanwar tashi fiye da kowa a cikin ƴan uwan nashi kenan, manyance da natsuwa tsara zance ga kuma girmama na gaba da ita, "Yaya wata Alfarma nazo da ita, dafatan zaka taimaka ka biya man wannan buƙatar, na sani duk gidan nan babu wanda zan tun kara ya saurare ni, kaman kai, kuma na san zaka iya shi yasa na zo wurin ka Yaya" ta katse mashi tinanin shi, cikin marairaicewa.
Murmushi yayi yana mai tattara dukkannin natsuwarshi zuwa gareta, "ina jin ki Lil wannan wace ALFARMA ce kike buƙata gare ni haka da kike ta kwana - kwana haka?" ya faɗa cike da murmushin da ke ƙara ƙawata mashi fuskar shi, tare da fiddo zallar kyawon fuskar tashi, dimfull ɗin shi yana mai ƙara nutsewa cikin kuma tun nashi.
" Yaya Maganar SUHAN ce" ta faɗa cikin tarabbabin yanda zai amshi maganar tata....... "Ehem!, ina jin ki Afnan me Suhan ɗin tayi ne?" ya amsa mata fara'ar fuskar shi na raguwa, abun da ya ƙara tsorata Afnan ɗin kenan cikin in ina tace
"maaaganaaar... Kara.. Tun,,, ta Yaaaya"....
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:22 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƘARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
_*Jinjinar ban girma ga mai gida na, Abbu-Deedat. Nagode da irin goyon bayan da kake bani da irin yadda kake ƙarfafa mani guiwa, a duk al'amurran da na sanya gaba. Godiya marar adadi Allahu ya bar ƙauna ya raya mana Ahmad Deedat🥰*_
_*Page ~8~*_
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
"Look afnan✋🏻" ya katse ta daga inda indar da take yi, sannan ya ɗora da faɗin "Na riga nayi duk iyakar ƙoƙarin da zan iya yi akan issue ɗin karatun yarinyar nan, tin ma kafin ke kizo, saboda haka bana jin zan iya maida kaina acikin al'amurran su, tinda har mahaifiyar ta bata son al'amarin karatun nata, zai fi kyau muma mu dakata hakanan, mu barta tayi ma mahaifiyar ta biyayya Allah ya sani mun riga mun yi iyakar iyawarmu" ya ƙarashe maganar cikin wani yanayi na ƙunar rai lokaci guda yana ɗan ƙutawa gami da janyo laptop ɗin tashi ya buɗe, ga duk kan alamu yana nufin ya gama magana kenan.
Shiru falon yayi, in baya ga ƙarar Ac da take bada sanyi ƙaɗan-kaɗan baka jin komai, ita kanta Afnan ɗin shiru tayi kaman ruwa ya cinye ta, ta rasa minene tinanin umman suhan ɗin akan ɗiyar tata, amman dai koma minene ita bazata bar lamarin haka nan ba, za tayi iya yi ta tinda ta kula babban burin suhan ɗin kenan, don dai Allah yayi ta da kawaici da biyayya ga na gaba da ita.
Muskutawa ta sake yi ba don ta gaji ba, sannan ta marairaice dama abunka da auta an saba shagwaba "Na sani wlh yaya na, sai dai ba zamu bi ta kan umman ba, ita ba sanin daɗin abun tayi ba, Yaya Pls, don Allah ba don ni ba, ka taimaka mani, bana so ma ta gane da sa hannuna" shiru yayi mata na wasu daƙiƙai, sannan ya nisa tare da faɗin "Toh Naji, yanzu ya kike so ayi?" tini fara'ar fuskar ta ta dawo, afnan kenan baiwar Allah, yarinya da kyakkyawa zuciya.
"Yauwa Big boo" ta fada cike da jin daɗi sannan ta kamo hannuwa shi ta riƙe su gam, sana ta ɗora da faɗin " Dady, Dady zaka yi ma magana, shine kaɗai zai iya sawa umman suhan ta yarda, ba tare da samun wata matsala ba, Pls my Lovely yaya" shiru yayi sai daga bisani ya nisa gami da faɗin "Is OK dear, Consider it done, kar ki damu ina so ki bar maganar nan a hannuna zamu san yanda zamuyi, ni kaina ina tausayin Rayuwar su, mutane ne da suka cancanci a tausaya masu don ga duk kan alamu sun fi sauran ma'aikatan shiga halin damuwa, masalan ita umman suhan ɗin" ya faɗa cike da basarwa kai kace ma bashi ne yayi maganar ba, saboda bazaka taɓa kawo ma ranka cewa miskilancinshi ma zai bar shi fahimtar wani abu ba.
Miƙewa tayi tsaye, gami da yin wani ɗan tsale cike da annashuwa, "Nagode Yaya, na gode Allah ya saka da Alkhairi ya bar ƙauna, I love u sooo much, Good night Swt Yaya" ta faɗa tana mai nufar ƙofa domin fita, saboda dare yayi, da murmushi ya bita, wannan zuciya ta Afnan da kyau take, tabbas shi ya san ko ba daɗe ko ba jima sai sun yi alfahari da yarinyar
"Ameen" ya furta a hankali cikin salon san kauda tinanin abun a ranshi, domin aikin da yake yi Afnan ɗin ta shigo, mai muhimmanci ne.
×××××××××××××××××××××××
Washegari bayan mun kammala aikin mu, mun dawo sashen mu munyi wanka wajen ƙarfe biyu na rana, aiken Hajiya Kubra ya iske mu, ni da umma ta wai tana neman mu, har ga Allah gaba na sai da ya faɗi, domin har jin daɗi nake inje in kammala aiki na tana sashen Alhajin ta yanda ma babu abin da zai haɗa ni da ita, sai dai wajen zuba abinci. Ummana ce ta amsa da cewa gamunan zuwa, lokacin da ƴar saƙon ta fita ne ta juyo da kallon ta gare ni da nayi fiƙi fiƙi da idanu, ina ta tinanin laifin me kuma muka aikata yau, saboda duk idan aka yi mana irin wannan kiran to fa ba lafiya ba.
"ki kwantar da hankalin ki mama na, insha Allah lafiya lau, babu abin da zai faru sai alkhairi" da to na bita domin in kwantar mata da hankali saboda yanzu umman tawa sai a hankali ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, don ko jiya dakyar muka yi bacci, ciwon zuciyar ta ne ya kusan tashi. Hijabi na na ɗauko na sanya gami da wucewa gaba umman tawa na biye a baya na, babu mai cewa ƙala har muka isa babban sashen gidan, ta bangare guda kuma zuciya ta na luguden duka, domin na san rashin mutucin Hajiya Kubra sosai, fata na dai kada al'amarin ya shafi umma ta, ko minene dai ya tsaya iya kaina.
Sallama muka yi daga bakin ƙofa, Mama Talatu ce ta amsa mana daga ciki tare da faɗin "ku shigo mana, kuka tokare daga bakin ƙofa kaman wasu baƙi" shiga muka yi, ina gaba Ummana na baya; zaune muka iske ta bisa ɗaya daga cikin sofar da suka yi ma falon ƙawanya, gefe na samu da niyyar zama ƙasa ta dakatar dani, "a'a Suhana, ku shiga dai daga cikin falon Hajiyan, tana daga ciki tana jiran ku" "Toh Talatu" Ummana ta amsa mata.
Kai tsaye falon muka shiga tare da sallama, waeh Aljannar duniya kenan, tsayawa fasalta kyaun falon da dukiyar da aka narkar ma ɓata lokaci ne, kawai ka fasalta shi da duk falo mafi kyawo da ka taɓa gani a Rayuwar ka. Zaune take, hakimce cikin isa, izza da taƙama (Hajiya Kubra ba dai ji da kai ba) ko amsa mana sallamar da muka yi bata yi ba, sai ma cen gefe ɗan nesa da tayi mana nuni saman carpet din da ya lashe fin rabin falon tayi, bamuyi ƙasa a guiwa ba muka zauna, muna mai gaisheta cikin ƙan-ƙan da kai, shima bata amsa ba, sai ma shiru da ya biyo bayan hakan na tsawon wucin gadi, sannan ta nisa cike da gadara ta fara faɗin "ina so ku nisanci ɗiyata Afnan, domin duk abubuwan da suke faruwa cikin gidan nan tin zuwanta a kunne na suke, na hana ta taƙi bari, ina so ku sa ta tayi nesa daku, domin ko alama bana son zuwa sashen masu aikin nan da take yi, kuma na san ɗiyarki ke janta" ta faɗa tana maida duban ta kan umma ta da kanta ke sunkuye, sannan ta cigaba "kunsan ko alama ba da son raina kuke zaune a gidan nan ba, saboda har yanzu kin ƙi ki faɗa mana asalin daga inda kuke, daga ke har ɗiyar taki bamu san asalin ku ba, sannan ki shirya bayyana mana komai da ya shafe ku idan ba haka ba, ba jin zaman ku a gidan nan zai cigaba da ɗorewa, bazan lamunci a mallake man ƴaƴa ba idan kunne yaji...... " ta ƙarashe tana mai ajiye maganar cike da gadara, ko ɗar bata ji ba, duk cin mutumcin da tayi mana bata gani ba, wannan ai tozarci ne, ko ba'a faɗa ba, na san mama Talatu da uwani ne suka kawo wannan gulmar, watau ita dai duniya haka take kana barci ana maka mun shari, idan da sabo ma mun saba jin ire-iren wannan tozarci daga gurin Hajiya kubran, muryar Hajiyan ce ta katse man tinanin da na Lula "Kuna iya tafiya Maryama, Amman kada ki manta da buƙata ta a gare ki"
Cikin mutuwar jiki muka taso muka fito, tabbas idan raina yayi dubu ya ɓaci, a bakin ƙofa muka haɗu da afnan ɗin, tana yi man magana amman ni Sam hankali na ma baya kanta, murmushi kawai nayi mata na raɓa ta na wuce, juyowa tayi da niyyar binmu, na sanya hannu na dakatar da ita gami da girgiza mata kai, sannan na sanya ƙafa cikin sauri na bi umma ta da har ta kusa ficewa a babban falon.
Wucewa Afnan ɗin tayi zuwa cikin falon Hajiyan, tare da zama cikin tashin hankali don ta san halin mom ɗin tata sarai "Mom me kika yi masu? For God sake me kika faɗa masu?" ta faɗa kaman zata yi kuka, "ke dallah saka rai shashasha, me kika gani jikin waɗancen faƙiran da har kika liƙe masu, har kina ɗaukarta kuje siyayya tare? Su fa ƴan aikin mu ne, ko kusa ba tsararki bace, bata da wani amfani wajenn mu in ba tayi mana aiki ba mu biya ta, ko kaya sai mun sanya mun cire sana muke basu su sanya, Amman wai kece yau kike haɗa kanki dasu, har kike zuwa ɗakinsu ki zauna, to ahir ɗinki wlh in ba haka ba zan saɓa maki fiye da tinaninki wallahi" ta ƙarashe tana mai nuna zallan ɓacin ranta ga autar tata "mom, ni fa banfisu da komai ba, in fact ma, babu Wanda yafi wani wurin Allah sai wanda yafi tsoron shi, so ni gaskiya momy baki kyauta mani ba, ai su ɗin ma ƴan adam ne, wanda ya halicce mu ya bamu, suma shi ya halicce su, kuma bai manta dasu ba" ta ƙarashe cikin matsanancin ɓacin rai, domin ga alama mom ɗin tata magana marar daɗi ta faɗa masu, kuma akan ta ne, mom ɗin ce ta amshe da cewa "au haka kika ce? Ashe ba zaki dena ba kenan? Maza ki shirya kayan ki, in kin fita ki kirawo man Nafeesa kuzo ku koma inda kuka fito domin bazan lamunci wannan iskancin naki ba wallahi, kada in saɓa maki"
Fashewa tayi da kuka gami da barin part ɗin ma gaba ɗaya, cikin gudu ta sashen yayan nata, ta tarad dashi dawowar shi kenan daga office, don ko takalma ma bai cire ba, faɗa mashi tayi cikin kuka mai fidda zallan ɓacin rai, cikin tashin hankali ya janyo ta gami da rungume ta ya shiga shafa mata baya, cikin sanyin shi mai haɗe da miskilanci yake faɗin " Is OK Lil, is OK, tell me what is happening ne, me ya same ki? Ina ke maki ciwo?" cikin wani sabon kukan ta zayyana mashi komai dake faruwa da Abunda mom ɗin tasu tayi, zaunar da ita yayi yana mai faɗin "is OK Afnan, kinsan halin mom sarai, no, bai ma kamata ki ɓata ma kanki rai ba hakanan, ko ni da kika ga ina gaya mata gaskiya ba saurarena take yi ba a times, sai muyi mata addu'a insha Allah zata gyara halin ta, kiyi shiru babu inda zaku koma sai hutun ku ya ƙare, Amman ina so kema ki ɗan ja baya da su, saboda kada ki dinga ja masu ɓacin rai wajen mom ɗin, kin gane ko? Gyaɗa mashi kai tayi tana mai faɗin "na gane Yaya, amman wlh maman Suhana ba lafiya gareta ba, ina gudun ɓacin rai ya sanya wani abu ya same ta, gashi na baro Phone ɗita ɗaki balle in kira su na basu haƙuri" ta ƙarashe faɗi tana goge kwalla da ke saman fuskanta kwance shaɓe shaɓe.
Is OK, kwanta nan ki huta,bari in shiga in watsa ruwa, sai in fito mu san abun yi,; ya faɗa mata haka ne don ya san rikicin Afnan, tana iya cewa zata kuma zuwa sashen nasu, kuma shi ba zai so hakan ba, gara ace ta ɗan ja bayan dasu, ta bar mashi komai a hannun shi insha Allah shi zai daidaita komai.
Ni kau muna fita na kama umma ta muka nufi sashen namu, ina kallon mama Talatu murna fal cikin ranta, ga duk kan alamu ma laɓe tayi mana, domin taji Abunda Hajiyan zata faɗa, dama ita ta kai mata gulmar, kuma tayi ta zuzuta Hajiyar tana ƙara ma labarin gishiri, har cewa tayi Afnan ɗin sai ta kai ƙarfe sha biyu a ɗakinmu, kuma wai kuɗi take kashe mana sosai muke yi mata wayau, kuma yanzu na fara jin kaina daidai da su Nihal, saboda irin sutura da afnan ɗin wai ta siyo mun daga cen ƙasar wajen.
Lafiya muka isa ɗaki, duk da umman tawa na ƙoƙarin dannewa, tinda ta lura da kwallar da nake share wa akai, akai, Amman hakan bai hana ta kwantawa ba, ba tare da ta furta ko uffan ba, nima bazan tada maganar ba, saboda maganganu ne marasa daɗin ji, to kenan ma tana nufin ƙilan bama da asalin kenan?, me umma ta ke nufi da ɓoye mana salainmu da take yi? Me hakan ke nufi,?
Ganin ta samu barci ne, ya sanya nima komawa gefen ta na kwanta ƙasa, nayi matashi da katifar tamu, ina fata in ta farka komai ya wuce guri ta, ina fata kada ta tashi da :a in rai, domin kafin ta kwanta saida na ɓalli maganin ta na bata, na ƙudurce a raina zan nisanci Afnan ɗin, ba tare da na bari ta zargi wani abu ba, sai dai don mu tsira da mutumcin mu.
Afnan ɗin ce ta roƙi Yaya Al'ameen ɗin da ya ara mata wayarshi ta kirani, sai kuma ta manta bata riƙe number ɗin wayata ba, dole ta sanya ta haƙura da niyyar in mun haɗu cikin gida zata sake bamu haƙuri dangane da Abunda mom ɗin tata tayi mana.
Ta ɓangaren Hajiya kuwa, ko da ta tuntuɓi Aunty feena da maganar komawa, cewa tayi gaskiya ita ba yanzu ba, duka ma yaushe tazo? Kuma wannan dalilin ma bai kai Abunda za'a ce an koma saboda shi ba, ai tinda an ja kunnen Afnan ɗin shikenan bazata kuma maimaitawa ba,; su kuwa su Aunty saudat da sauran ma'aikatan gidan daɗi suka ji, wai ko ba komai an nesa ta ni da afnan, dama ƙaryar tawa ta Afnan ɗin ce (oh🤔 wai ko ma yaushe Afnan ɗin ta dawo, duka duka?)
Haka Ya Ameen ya ta lallaɓa Lovely sister ɗin tashi har ya samu sukayi kwana uku da faruwa Al'amari, dama Alhaji mustapha yayi tafiya, duk wainar da ake toyawa bai sani ba acikin gidan, wannan ce ta sanya bayan ya dawo Al'ameen ɗin ya kuduri niyyar tunkararshi da maganar karatun suhan ɗin, a ganin shi wannan ce kawai damar da zai yi amfani da ita wajen ceto suhan ɗin da mahaifiyarka a halin taskun da suke ciki.
**********************
Ƙarfe takwas daidai 08:00pm yayi sallama falon abban nashi, tafiya yake cikin salo shi na cikakke ɗa namiji, duk da yana da sanyi, wannan ce ta ƙara ƙawata tafiyar tashi, murmushi Alhaji mustaphan ke bi shi dashi, har ya ƙara so ya zauna kujerar dake kallon ta Alhaji mustaphan.
Ɗan sunkuyar da kai yayi alamar girmamawa tare da faɗin "ABBA barka da dare" miƙa mashi hannu Alhajin yayi suka yi musabaha, "barka ka dai Son, ya aiki ya jama'a?" Abban ya faɗa fuskar shi cike da annashuwa, "Lafiya ƙalau Abba , an dawo lafiya.?? " ya faɗa cikin girmamawa, "Lafiya ƙalau Son, ina fata dai lafiya? Al'ameen ɗin ne ya amsa da" Lafiya lau Abba, wata magana ce nazo muyi idan ka da lokaci". "To to to, bismilla ina jinka Al'ameen ince dai ko lafiya ko?" Alhajin ya faɗa cikin dattako, lokaci daya yana mai ajiye kofin coffe da yake sha a hankali, ya tattara duk kan natsuwarshi ya ɗora ta kan mafi soyuwa daga cikin ƴaƴan shi.
Natsuwa Ya Ameen ɗin yayi tare da warware mashi komai da ake ciki, dangane da karatun suhan ɗin, sai dai bai faɗi Abunda mahaifiyarshi tayi ba, sannan ya ɗora da faɗin "Abba kuma ina so asamu wasu masu aikin da zasu mayi gurbin su, Kaga dai ita maman yarinyar ba cikakkar lafiya gareta ba, kowa kuma ya sani, sannan idan Allah yayi ita kuma Suhana makaranta zata tafi, Kaga akwai nbuƙatar wasu madadin su, sannan bana so mom ta san da hannuna ko na Afnan a ciki, ka shige mana gaba wajen ganin ka daidaita komai wajen hajiya"
Murmushi Alhaji mustaphan yayi irin nasu na manya, sannan ya ɗora da faɗa ya aka yi ba'a faɗa mashi hakan ba tun farko? Ai da yanzu ma yarinyar tayi nisa a karatu, ko ma ya tura ta cen wajen Aunty feena tayi karatun ita da Afnan ɗin, Amman ko yanzu babu matsala, babu Abunda zai gagara da izinin Allah, wasu ma an temakesu balle waɗan da suke ƙarƙashin su?, shi ɗa ai na kowa ne, kuma baka san mai amfanar ka ba nan gaba.
"Babu komai Al'ameen, ka bar maganar a hannuna insha Allah da kaina zan samu ita mahaifiyarka tata, zan kuma roƙe ta wannan alfarmar in har na isa tayi man" Alhajin ya faɗa cikin son ƙarfafa ma Al'ameen ɗin guiwa ga temakon da yake son yayi, ko bayan ba ranshi, shi ya san ya bar wanda Al'umma zasu amfana dashi, ya san ya bar ma dadi, ko ma yace mafi yi, domin Al'ameen ɗin yaro ne irin wanda kowanne uba yake da burin ace ya mallake shi, a matsayin magaji.
Cikin jin daɗi da godiya yayi ma Abban nashi sallama gami da cewa "bari in barka haka nan Abba, ka huta na san ka gaji, a tashi lafiya, sai da safe" ya faɗa yana Miƙewa da niyyar barin ɗakin, da kallo Alhaji mustaphan ya bishi yana ƙissima wani al'amari da zai faru nan gaba ƙaɗan akan ɗanɗan nashi mai girma, tabbas yana da buri da fatan hasashen nashi ya zamo gaskiya. Murmushi yayi yana mai janyo kofin coffe ɗinshi ya cigaba da kurɓa cikin dattako gami da faɗin
"Allah shi kaimu Son"
_Toh fa Fans, magana ta girmama, lamarin ya kai kotun ƙoli, ko ta yaya Alhajin zai yi domin shawo kan maman Suhana?, Kudai kuci gaba da bin Alƙalamin Oum Deedat domin ta warware maku zare har abawa_
_~Oum-Deedat ce~_
[8/5, 8:23 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƙARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u nopain✍🏽~*
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Fans ina jin daɗin comment ɗinku, hakan na ƙara man ƙwarin guiwa, nagode akafta*
_*Page ~10~*_
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Takowa ya cigaba da yi a hankali cikin salon tafiyar shi ta ingarman namiji, daf dani ya sunkuyo ta yadda zan iya jiyo shi, sannan ya shiga faɗin "pray for your mom, yanzu ba kukan ki take buƙata ba, sannan ki tashi daga wajen ki koma bisa chair kin tare hanya, wani zai iya bugeki" Abunda ya faɗa kenan a gaggauce ya koma inda yake zaune ya sake zama.
A hankali na tashi ina mai haɗa hanya cikin jin juwa da ke neman yin haji-jiya dani, kujerar dake kallon tashi na zauna tare da juyar da kaina daga saitin shi, ta yadda ba ma zamu iya haɗa idanu ba.
Akai Akai yake ɗaga idanu yana kallon kyakkyawa agogon dake hannun shi samfurin Apple, sai kuma kiran da akeyi mashi Akai Akai yana latse wa. Ƙarar buɗe ƙofa ce ta dawo da hankalin mu duka wajen, zabura muka yi mu duka biyun wanda a tare muka isa ga likitan da ya fito daga cikin ward ɗin "likita umma ta ta farfaɗo? Kaddai kace man ta mutu dan Allah" na faɗa ina mai matso wani sabon kwallar, "ummanki lafiya lau ta farfaɗo amman mun yi mata allurar barci saboda ta sake samun hutu, zaki iya shiga ki ganta nan da anjima idan ta farka" ya faɗa man yana mai maida hankalin shi kan yaya ameen ɗin da yake tsaye ta gefen mu, "a'ah yallaɓai ashe baka shiga office ɗin ba? Sai ka zauna waje?" dan guntun murmushi yayi sannan yace ma Ya Ameen ɗin "to muje sai in maka ƙarfin bayani ko" ya wuce gaba Ya Ameen ɗin ya bishi a baya, da idanu na raka su har suka shige office ɗin sannan na sauke ajiyar zuciya lokaci guda ina mai hamdala gami da sanya hijab ɗina na share dukkan ƙwallar dake kan fuskata, muskutawa nayi sannan na maida duba na kan mama Talatu dake tsaye tana binmu da kallo da kuma naɗe dukkanin motsin mu cikin fai-fain ta na gulma, ɗan taɓe baki nayi kaɗan ina mai rayawa a cikin raina "dukkan ku zaku gama ne, zaku gaji ku bari, ai Hajiya Kubra ba'a mata gwaninta.
***************
Likita ne ya zauna a kujerar sa gami da nuna ma Al'ameen ɗin kujerar zaman patient," Bismillah yallaɓai ga wuri zauna" bayan ya Ameen ɗin ya zauna ne sannan ya muƙa mashi hannu suka sake yin musabaha gami da ƴan gaishe gaishe, dama sun san juna don shine family doctor ɗinsu, kuma a asibitin ne suke da file, Dr. Ashafa kenan kwararren likita ta kowanne fanni.
"Yallaɓai garin yaya haka kuka bar matar nan cikin irin wannan hali? Abun yayi tsanani, zuciyar ta ta kusa ta buga, ta daɗe da ciwon zuciya duk da bincike ya nuna tana kan drugs, sai dai ba wasu masu ƙarfi bane, ba zasu yi tasirin hana zuciyar kumbura ba, gaskiya ba dan kunyi gaggawar kawo ta nan ba da abun ya munana, a dinga kulawa pls" ya sauke maganar tare da ɗora dukkanin idanun shi da natsuwarshi akan Al'ameen ɗin don jin amsar da zai bashi.
"Dr wallahi ban san abun yayi worse haka ba, ban ma san wane asibiti suke zuwa ba, na dai san bata da lafiya Amman ban san me ke faruwa da ita ba, yanzu ya jikin nata? Ba zamu iya ganin ta yanzu ba, ina da uzuri ne tin ɗazu ma ake kira na" ya sauke maganar da gani dai cikin hanzari yake don ya ƙagara ya tafi "No babu wani damuwa yanzu mun shawo kan matsalar, sai dai gaskiya a kula, a dena yawan ɓata mata rai, in da hali ma adena bari tana aiki mai yawa da zai iya gajiyar da ita, yanzu ma zaku iya shiga ku ganta, sai dai zaku barta anan ne, ka san tsari asibitin ba'a zaman jinya" ya faɗa yana mai sake miƙa ma Al'ameen ɗin hannu dan musabaha, shima Al'ameen miƙa mashi yayi yana faɗin "Nagode Dr. Ashafa, sai dai alfarma zakuyi mana wannan karon, ita wannan yarinyar ɗiyarta ce, so ko mun koma da ita zata tashi hankalin ta ne, zata damemu da kuka, ku barta ta zauna wajen ta har muga yanda jikin zai yi, ni zan je, idan na taso daga office zan dawo inga yana yin jikin ko da Abunda ake buƙata" "OK shikenan yallaɓai" likitan ya faɗa, sannan suka juyo a tare suka fito domin shiga ɗakin da umman tawa take; ya ameen ɗin ne ya tsaya yana faɗa mana mu shiga muga jikin ta har da mama talatun domin ita zata koma ne gida.
A tare muka shiga ɗakin da shi da mama talatun, likitan ne yake shaida mana banda hayaniya, kada kuma a tada ta har sai dai ita ce ta tashi dan kanta, kuma kada a bata komai taci, akwai sinadari abinci da ake bata ta iskar oxygen ɗin da yake maƙale a hancin ta.
Duk iya rashin imanin mutum sai ya tausaya wa umma ta, kwance take tayi fayau da ita, numfashi take sauke wa a hankali, babu Abunda ke motsi jikin ta, jawo kujera nayi ta roba mai kyau na zauna yayin da na ƙure ta da idanu hawaye na ɗiga ɗis-ɗis saman hijab ɗina.
Juyawa suka yi suka fita har mama Talatu da Ya ameen ya yafito da hannu, kuɗin taci ya bata tare da mata godiya sosai yace ta koma gida sai ya dawo, dawowa yayi ɗakin tare da kira na domin shi wucewa zai yi, a baya na bishi zarai-zarai har muka fita harabar asibitin da har mama Talatu ta samu abun hawa, ina kallon ta tana leƙowa taga shin ina zamu, sai dai ta makaro dan mai motar ma har yaja sunyi gaba, naso nayi mata godiya Amman ba komai ai bana ma fatan mu daɗe asibitin, zan yi mata idan mun koma gida.
"Is OK Suuhaaan" ya faɗa a hankali bayan ya daidaita tsayuwarshi bakin motar sannan ya juya ya jingina da ita sosai, "Comon goge wannan hawayen naki, kukan ya isa hakanan, ki yi mata addu'a sannan ki guji ɓacin ran ta, a mamadin mahaifiya ta ina mai ƙara baku haƙuri, na san ita ce sanadi, Amman insha Allah komai ba zai ƙara faruwa ba" ya faɗa yana mai ƙoƙarin haɗa idanu dani, ni kau sauke kaina nayi ƙasa ina mai bin umarnin nashi na share fuskar tawa gami da jan majina a hankali na shiga faɗin "Mungode Yaya babu komai wallahi, dama umma ta tana da wannan ciwon, nima dashi na taso na ganta, ba Hajiya bace sila, Mungode da karamci Allah ya saka da Alkhairi" na faɗa ina mai ƙosawa da tsayuwar, ba zan iya jure tsayuwa wuri ɗaya dashi ba, kwarjini yake man, gani nake duk ya cika wajen, Al'ameen ɗin daban ne, akwai kamala da haiba tattare dashi, komai nashi da yake yi cikin hankali da natsuwa yake yin shi, daidai da magana kaman baya son yi, muryar shi, ƙamshin turaren shi na ƙara rikitar dani, bana son irin yanayin da nake shiga a duk lokacin da muka kasance mu biyu a wuri ɗaya, kula yayi da irin yanda duk nabi na takura, motsa bakin shi yayi a hankali ya shiga faɗin "ki koma wurin umman, zan je aiki in dawo tin ɗazu ake jira na babu Abunda zaku buƙata, akwai komai a ɗakin kuma akwai drinks a fridge zan sa a kawo maki break fast ki tabbata kunci don na san baki ci komai ba, sai na dawo" Ya faɗa, bai jira cewa ta ba ya faɗa mota gami da yi mata key, janyewa nayi na bashi hanya, ya zo yawuce bai ko kalli inda nake tsaye ba (hoooo Al'ameen miskilanci)
*******************************
Mama Talatu kuwa na isa gidan sashen Hajiya kubran tayi, ta iske bata tashi ba Amman don tsabar san gulma sai da ta jira ta, bayan ta fito ne take tambayar ta ya bata ganni ba? Ban shigo aiki ba,me yake faruwa, "yo Hajiya ina ko zaki ganta? Ai bama su gidan gaba daya" cikin isa take kallon talatun, "ke Talatu bana son munafunci, faɗa man gaskiya me yake faruwa ne a gidan? Ta faɗa cikin gadara lokaci guda tana mai zama kan ɗaya daga cikin sofa na alfarma da sukayi ma falon ƙawanya, sanye take cikin wani ɗanyen lace mai azabar kyau, dama hajiya Kubra ba dai kyau ba, naira ta kwanta mata ta ko ina sai sheƙi take yi da walwali, nan mama Talatu ta kwashe ƙarya da gaskiya har faɗa mata take yi cen ta baro Al'ameen ɗin ai muna tare.
Ranta ko in yayi dubu ya ɓaci, au ta hana taraiya da afnan shine muka koma ma Al'ameen? Al'ameen ɗin nata da take ji dashi tamkar tsoka ɗaya a miya, me hakan ke nufi? Dakatar da mama talatun tayi gami da miƙewa cikin takon isassu ta fita daga sashen zuwa sashen Alhaji da take barowa da sanyi safiya, Afnan ce ta fito tana kallon mama Talatu, ashe ta zo fitowa taji suna magana shine ta koma da baya take jin duk abubuwan da mama talatun ta faɗi ma mom ɗin tasu "mama kiji tsoron Allah fa, ashe ke ke hadda sa fitina tsakanin hajiya da masu aikin gidan nan? Kina shugaba baki so a zauna lafiya, to wallahi kema ba zaki ci gaba da zaman gidan nan ba muddin kika yi sanadiyyar barin su suhan ɗin gidan nan". Tana kaiwa aya bata jira cewar mama talatun ba ta koma ɗakin nata da gudu tana mai rarumar wayar tata gami da kiran Ya Ameen ɗin, tsaf ta kwashe komai ta faɗa ma gayan nata yanda taji mama Talatu na faɗa ma Hajiya, tare da faɗa mashi yanzu zata bar gidan zuwa asibitin ta taya ni zama, koma minene ya faru ai su ne sila; Dakatar da ita yayi gami da cewa ta bari sai ya dawo baya son wata matsala kuma, shi zai jawo hankalin hajiyar ta bar zancen bari ma ya faɗa ma Alhaji komai kafin Hajiyar ta isa.
Da yake da tazara sosai tsakanin sashen nata da na Alhaji, lokacin da ta isa har Al'ameen ɗin ya kira Alhajin ta iske yana waya da Al'ameen ɗin ta nemi waje kusa dashi ta zauna, tana ta cika da batsewa, bayan ya gama wayar ne ya maida hankali shi kan Hajiya Kubran, da murmushi ɗauke kan fuskar shi ya shiga faɗin "uwargida ran gida, lafiya dai ko naga kin dawo, wannan kwalliya ai sai dai ace in biya" ya faɗa cikin zaulaya da murmushi a kan fuskar shi. Fuska a tamke take cewa "Alhaji ba wannan ba, yaron nan Al'ameen...." Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu gami da cewa "Abunda Al'ameen ɗin yayi shine daidai, ai suma mutane ne, ko kuma zai ƙyale ta ta mutu ne cikin gida yana kallo? Mutane su samu abun faɗa a gari? Kada in kuma jin kince komai akan zancen nan kuma anjima ku shirya ku duka muje a dubo ta, Allah ya bata lafiya shine fatan mu. Sannan ina so ki sanya a nemo maki wasu ƴan aikin da zasu zauna mamadin su, abarsu su huta hakanan ita yarinyar ta kula da mahaifiyarta." Yana zuwa nan a zancen ya miƙe gami da gyara zaman babbar rigar shi yana mai kallon ta sannan ya cigaba da cewa" Ni zan fita sai na dawo, kada ku manta ku shirya fa, sannan idan Allah ya kai mu gobe Asabar mu dukkan mu zamu je kankiya mu gaishe da su Alhaji tinda kowa yana ƙasar ki faɗa ma yaran ma su duka su shirya" da kallo ta bishi har ya fice, ita kanta ba tin yanzu ba ta san Alhajin kaifi ɗaya ne, dukkan isar ta da zartar da hukuncin ta, tana yi ne akan ƴaƴan ta kawai da masu aikin gidan sai kuma abokan kasuwancin ta. Amman Alhajin gagarabadau ne a wajen ta, duk abin da take taƙama dashi ya fita shi tsayayye namiji ne a cikin gidan sa, dukkanin hukuncin da ya yanke ya yanku kenan, ba shan ruwa ba ƙetare hanya.
******
Ƙarfe biyu Al'ameen ɗin ya koma gida bayan salla juma'a gami da yin wanka ya shirya, Afnan ya kira a waya ya sheda mata ta fito su tafi, aikau ta saɓo Nasreem ta kamo hannun Ayan, Afnan kenan sarkin ƴaƴa, ko MOM ɗin tasu bata faɗa mawa ba don ta san hana ta zata yi, biyawa suka fara yi, suka yi take away da sauran tarkace, sannan suka wuce asibitin kai tsaye.
A ɗakin suka taddani zaune bisa kujera, na kifa kaina jikin gadon umman tawa da har yanzu bata farfaɗo ba, ban ma ko ji ƙarar buɗe ƙofar tasu ba, na yi zurfi cikin tunani, ƙamshin turaren shi ya sanya ni sauri ɗagowa, ilai kuwa su ne shi da afnan, sanye yake cikin dakakkiyar shadda fara ƙal, yau juma'a tu babbar rana, fuskar nan tashi fayau, idanun shi tarwai cikin farin glass ɗinshi mai kama da medical glass, idanun shi ƙyam a kaina, kallo yake man mai cike da ma'anoni da tuhume tuhume, tabbas na san laifi na, take away ɗin da ya sanya aka kawo man, tin bayan fitar shi da safe, yana ajiye bisa stool ɗin ɗakin ko taɓa shi ma banyi ba har gashi yanzu Ƙarfe uku saura; ba'a magana da ƙarfi ya sanya bai ce an komai ba, sai ma ɗan ƙutawa da yayi ya ajiye sauran ledojin da suke hannun shi ya fice gaba ɗaya a ɗakin.
Gaisawa muka yi da afnan sosai kaman babu abin da ya faru, na shiga tambayarta sauran mutanen gidan, "suna gaida ki da mai jiki" ta furta ba dan taji daɗin ƙaryar da ta furta ba. Hannun Ayan na kamo ina cewa "zo mana Ayan in ba faɗa mi ya kawo gaba?" cikin ƙarfin hali har da ɗan murmushi na na yaƙe. Text ne ya shigo wayar afnan, Ya Ameen ne yake cewa lallai ta sanya ni inci abinci, shi ya wuce sai anjima zai dawo kuma lallai kar suyi hayaniya a ɗakin nan su tada umman tawa.
_Kuyi manage da wannan please bana ɗan jin daɗi ne ku taya ni da addu'a fans_
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:23 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƙARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u nopain✍🏽~*
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
🤸🏻♀💃🏻💃🏻 Kuzo ku taya ɗan ku Deedat murnar cika shekara uku cif a duniya, ina fatan Allah ya Albarkaci Rayuwar shi, ya shirya shi shirin addinin islam, ya bashi rayuwa mai Albarka, ya bashi ilimi mai yawa mai amfani, ya cika mashi burin shi na zama Soja😄😆 ya bamu ikon tarbiyyantar dashi. AMEEN ya Rab, Deedat yana gaida dukkan fans na *BAN FI ƘARFIN TA BA*
_*Page ~9~*_
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Mu kau cikin ni da umma ta, babu wanda yayi runtsawar kirki, kowa da abunda yake saƙawa cikin rai, har gara ma umman tawa, tana ƙoƙarin ganin ta kau da komai, sabo da shawarwarin likita da ya bata na tayi ƙoƙarin ganin bata riƙe abun ɓacin rai a zuciyar ta ba.
Ni kuwa Allah Allah nake gari ya waye, domin na yanke shawarar ƙundunbalan tambayan umman tawa ainihin labarin mu, da asalin mu, lokaci yayi da zata dena ɓoye mani komai, na mallaki hankalin kaina, yaci ace ta fito ta fayyace mana komai kowa ya sani, ko zata fita a zargin da mafi yawancin ƴan gidan ke mana, a kan kunnen mu mun sha jin ma wasu ƴan ƙanana maganganu akan umman tawa da ni kaina ma, kai wasu ma cewa suke yi ni shegiya ce bana da uba, tinda haka suka ganta tazo gidan a wahale ga ɗiya duƙu-duƙu kuma taƙi faɗin wacece ita da kuma ainahin daga ina take.
Alhaji Mustapha kuma ya kafa dokar kada wanda ya tambaye ta, har sai ta gaji dan kanta ta faɗa, a cewarshi babu kyau shiga rayuwar wani, kuma hakan zai tada mata tsohon mikin dake ranta, gida dai nashi ne, tau tinda haka ne ya bata izinin zama har iya lokacin da take so, kuma tinda aiki tazo nema a zaɓa mata marar wahala a bata har sai ta murmure.
Ciwon umman tawa ya so ya tashi cikin dare, amman cikin ikon Allah abun ya taƙaita, ban so ace zan tada mata maganar da safe ba, gudun sake faruwar tashin ciwon nata, tau sai dai babu yanda na iya, wannan karon haƙuri na da kawaici na yazo ƙarshe, ba zan iya jurar ganin irin wannan rashin mutuncin ba daga wajen Hajiya kubran; da haka na samu bacci ya ɗan figeni har zuwa asubar farko da kiran sallah ya tashe ni.
*******************************
Ya Ameen yana shiga ɗaki waya yasa ya kira Afnan ɗin domin sheda mata yanda sukayi da Dad ɗin nasu, "Hello yaya" ta furta daga cen ɓangaren cikin muryar bacci "My Lil bacci kike yi ne?" ya tambaye ta cikin muryarshi mai daɗin sauraro a hankali, "eh Yaya na kwanta, lafiya dai ko? Ko wani abu kake buƙata? Ta tambaye shi tana mai tashi zaune da ƙara gyara ma Ayan dake gefen ta kwance bisa gadon nata lulluɓinshi," No Lil, ina dai son faɗa maki ne munyi magana da dad ne akan maganar waccen yarinyar, Amman tinda kin fara barci mu bari zuwa safe ki same ni part ɗina kinji, Good night dear" ya faɗa yana mai datse kiran ƙit, domin ya san halin zumuɗinta yanzu tana iya cewa ta taso ta taho, shi kuma baya jin ma zai iya doguwar magana yanzu ya gaji so yake ya kwanta, yana da muhimman ayyukan da zai aiwatar gobe, murmushi ya saki na gefen baki, wanda yayi sanadiyyar ƙara ƙawata fuskar tashi cikin hasken ƙwai mai launin dark blue na dare dake falon.
Miƙewa yayi cikin salon tafiyar shi mai cike da aji, ya shiga bedroom ɗin nashi domin yin shirin bacci, kayanshi kawai ya cire ya faɗa toilet ɗin da baya gajiya da shaƙar daddaɗan ƙamshin da suhan ɗin ta sanya mashi har kawo yanzu.
-------------------
Bayan mun kammala komai na Al'adar mu, kama daga sallah, wanka, sai muka zauna karatu ni da umman tawa, muna gamawa ne naga umman na ƙoƙarin tashi na dakatar da ita ina faɗin
"Umma ina so zamuyi wata magana dake don Allah" na faɗa ina mai rufe littafin umdatul-Ahkam ɗin gami da maida shi ma'ajiyar shi, na sake muskutawa domin girman maganar, ba zan ɓoye ba zuciya ta kaman tayo tsalle ta fito nake ji ta ƙirjina, masalan ma da naga irin kallon da umman tawa ke bina dashi, mai cike da ma'anoni daban daban,
komawa tayi ta zauna domin saurarar ɗiyar tata, da kanta yake duƙe kaman tayi ma sarki ƙarya, "Ehn ina jinki mamana, sauri nake yi domin kinga lokaci ya fara ja.
Sake sunkuyar da kai nayi ina mai komawa kalar tausayi maganar tayi ma baki na nauyi, shahada nayi lokaci guda na shiga faɗin
"Umma ki duba girman Allah ki faɗa mani asalin mu, wanene mahaifina? ina ne asalin garin mu, umma ke kanki su wanene mahaifan ki? Umma kin fi so mu zauna a gidan da ba'a san darajar mu ba? Kin fi so mu zauna ana wulaƙanta mu, ana zargin ki, ni kuma ana sheganta ni? Kada zuciya ta tafara yadda da maganar su fa!, na bani da asali, bani da mahaifi umma! Umma su nan ɗin ba dangin mu bane, basu san zafin mu ba, ƴaƴan su ma basa so su raɓe mu, suna kyamatar mu, suna ganin sun fimu umma, bazan iya jurar aci maki fuska a gabana ba, saboda kina ɓoye mana wani abu, kinƙi ki fito ki faɗa ma kowa mu ɗin su wanene ciki kuwa harda ni...... "
marin da ta sauke man a kan fuska ta har guda biyu, su sukayi sanadiyyar datsewar maganar tawa, ɗif nayi dafe da kunci, kaman ruwa ya ci ni, yau ni ce umma ta ta buga, yau ni ce durƙushe gaban mahaifiyar tawa ina faɗa mata malaman da suke barazana ga lafiyar ta, ba zan iya tuna lokacin da umma ta ta ɗauki hannu ta bigeni ba, saboda ita mace ce mai san yin hali, Sam bata da zafi;
kuka na fashe dashi lokaci guda ina mai ƙanƙame jikina, yanda naga ta hassala kaman zata rufe ni da suka.
"Ashe ke shashasha ce hauwau ban sani ba?, ina tarbiyyar da na baki? Ina kika kaita, nan ɗin da kike ganin ana wulaƙanta mu, ya fiye mana cen, in kika koma kashe ki zasu yi, nace kashe ki zasu yi! Ni ma ba zasu barni ba, saboda ke nake zaune nan, dan ki tsira da mutuncin ki, ki tsira da rayuwarki yasa nake zaune nan, nima abun yana man zafi, Amman ko me zasu yi mana ba zasu iya kashe mu ba, zaki mutu ne muddin kika yarda kika koma cen" kwalla ce ke shata ta a idanun umman tawa, abun da ya ƙara matuƙar firgita ni kenan, rarrafawa na shiga yi ina mai zuwa inda take na rungume ta, ture ni ta shiga yi, jeki, je ki nemi mahaifin ki, ƙila zakiyi sa'ar ganin kabarin nashi, ƙila zai iya tashi ya faɗa maki komai, Hauwa'u ban tsammanin akwai ranar da har ke zaki iya zuwa ki sanya ni a gaba ba, ki titsiye ni sai na faɗa maki wacece ke ba, na ɗauka na gama maki komai, na ɗauka na ishe ki komai, ban tsammanin zaki gaji da zama a inda na zaɓa mana rayuwa ba, nace kashe ki zasu yi, muddin kika yarda suka san kina nan da ranki, jeki jeki ki nemo dangin mahaifin ki, ki nemo dangi na, Amman ni kar ki ƙara tambaya ta game da su, kar kuma ki sake ki dawo inda nake, kuma duk Abunda ya same ku ke ce kika siya da kuɗin ki, kar ki ƙara tambaya ta abunda ya shafe su; Ta shiga ƙara ture ni daga jikin ta tana mai share kwallar da take ta ambaliya a fuskar ta.
Ƙara ƙwaƙume ta nayi, ina mai sakin gunjin kuka lokaci guda ina mai faɗin "Umma kiyi haƙuri ki yafe man, ki gafarce ni umma, nayi maki laifi, na aikata maki ba daidai ba umma, na cutar da zuciyoyinmu umma, bansan haka ba, bansan komai ba umma ki yafe man" shiru naji lokaci daƴa kaman ma bata numfashi, A firgice na ɗago, domin in ga me ke faruwa, abunda idanunwa na suka gani ne ya sani sakin razananiyar ƙara da sai da ta cika ilahirin sashen namu. Jikin ta gaba ɗaya ya saki, kaman wadda ta mutu bata numfashi Sam, "umma ki tashi" na shiga faɗi lokaci ɗaya ina mai jijjiga ta "umma ki tashi don Allah na bari, umma ki yafe man, umma kar ki mutu ki barni don Allah, umma ban da kowa sai ke, ke ce uwa ta ke ce uba na umma, ke ce komai nawa umma, kar ki mutu ki barni a cikin gidan nan umma, zan mutu nima in biki wallahi muddin kika barni, umma basa son mu basa ƙaunarmu, kar ki barni ni ɗaya a cikin gidannan" kuka ne gami da majina suka bi suka haɗe a yalwataciyar fuskar tawa, bama ta su nake yi ba, balle in mai da kai wajen share wa, gunjin kuka na nake yi mai cike da ruɗani kala kala, yayin da umman tawa take sharaf a jikina babu alamar numfashi tattare da ita, kwantar da ita na shiga yi lokaci guda ina mai girgiza kaina "umma ta bazata mutu ta barni nan ni kaɗai ba, bansan kowa ba umma sai ke" haka nake faɗa yayin da na tashi na fice da matsanancin gudu zuwa nemo wanda zai duba man ita, a tsakar gida muka haɗu da sauran ƴan aikin gidan da duk sun jiyo kuka na sun fito hankali tashe, hannun uwani na shiga ja ko sauraren ta banyi ba ina faɗin "mama uwani Kuzo ku duba man umma ta kar kuce man ta mutu, kar kuce man bata da rai, kar ku kashe man ita" mama Talatu Kuzo" na saki hannun mama uwani da nufi mama Talatu da gudu itama na shiga jan ta, ina mai sake sakin kuka mai tsuma rai, "me ya samu maman Suhana ɗin ne wai? " mama uwani take tambaya ta, ban iya bata amsa ba, domin naga sun yi tsaye sun ma ƙi shiga ɗakin, hanyar waje na nufa da gudu cikin kuka ina kwala ma baba idi kira, yazo ya duba ban umman tawa.
Tin daga nesa ya hango ta, Ya Ameen ne da ya fito daga part ɗin nashi cikin shirin zuwa wajen aiki, suit ce sanye jikin shi kalar royal blue, ya matuƙar yin kyau cikin sanyin shi yake takawa da niyya zuwa ɗaukar motar tashi, ya hango ta tayi hanyar fita waje cikin matsanancin gudu, kuka ma take yi, duk ta cukuikuye hijabin tata kaman mahaukaciya, lelleƙawa nayi banga kowa ba, ga dukkan alamu ma basu baro sashen nasu na maza ba da yake cen gefe guda da namu Amman da tazara sosai, juyowa nayi da gudu zan koma sashen namu wajen umman tawa, kuka nake bil haƙƙi da gaskiya ni a tunani na umman tawa ta mutu ne, karo naci da mutum ba tare da sanin ko wanene ba na shiga jan hannun shi, idona ya kulle, bana ganin kowa bana ganin komai, umma ta kawai nake kira, lokaci guda Naji an kama man hannuwa duka an riƙe aka shiga girgiza ni, "ke ki natsu, natsu nace, ki faɗa man me ya sami umman taki? Tana ina ne?" amon murya shi ta bugi dodon kunne na lokaci guda na wara idanuna akan shi, shi dai ne, Ya Ameen ne riƙe dani ni suhan, yana girgiza ni, hannuwa na duka cikin nashi, duk da firici da halin kuka da damuwa da nake ciki, bai hanani jiyo ƙamshin turaren shi ba da kuma taushin hannuwan nashi da suke cike da wani sanyi mai ratsa zuciya, "umma ta, ba zata mutu ba, Ya Ameen kaje ka duba man ita don Allah, bata numfashi, bansan haka ba da ban mata maganar ba, kada ta mutu ta bar ni ni ɗaya cikin gidan nan bansan kowa ba sai ita duk duniyar nan"
Na faɗa cikin kuka ina mai durƙushe wa kan ƙafafu na, gami da sake sakin wani marayan kuka mai ban tausayi ga mai sauraro, durƙusa wa yayi shima gami da kamo dukkanin damatsan hannuwa na ya miƙar dani "is ok, ya isa hakanan, ba zata mutu ba insha Allah muje in ganta" ikon Allah, maimakon ni da ke jan hannuwan waɗanda nake son su taimaka man, wannan karin wanda yake son taimaka man ɗin ne ya shiga jan hannuwa na, kaman makaho da ɗan jagora haka yake janye da hannuwa na, duk da nasan babu kyau hakan, ina jin babu daɗi a jikina duk kuwa da halin da nake ciki, Amman banyi yunƙurin janye hannun nawa ba, saboda da taimakon shi ne nake tafiya, jikina babu kwari Sam, kukan da nayi ya sanya har wata juwa-juwa nake gani, ƙala bance ba, na shiga bin shi kaman wadda bata san hanyar ba, har muka iso bakin ƙofar ɗakin da yake danƙam da ƴan kallon umma ta, dukkan su ma'aikata ne, Amman babu wadda tayi yunƙurin zuwa kusa da umman tawa ma da take yashe a tsakar ɗakin, duk sun tokare wasu daga ciki, wasu kuma daga bakin ƙofar dakin, wannan ƙiyayya har ina?
To fa! Turƙashi, Alhaji ƙarami ne riƙe da hannuwan Suhana yana janye da ita? Me hakan ke nufi? Ita har ta kai ma tsayin wadda Al'Ameen ɗin zai ruƙo ya shigo da ita har cikin ɗakin ta? Take redio masu amfani da jini suka fara naɗar ƙarya da gaskiya, darewa suka shiga yi suna bashi hanya tare da ƙoƙarin gaidashi, ko kallon inda suke baiyi ba, domin shima sun bashi matuƙar mamaki, sai dai Al'Ameen ɗin ba irin mutanen da ke shiga sabgar da babu ruwan shi bace, hannuwan nawa ya saki yayin da yake kamo na umman tawa yana mai ƙoƙarin jin pulse ɗinta.
Miƙewa yayi tare da maida kallon shi kan mama talatin dake tsaye tana recording ɗin duk wani motsi namu a ɗakin ko babu komai yau Hajiya Babba da labari kenan.
"Mama ku kamo ta a sanya ta a mota muje asibiti, bari in fiddo motar" ya faɗa cikin sanyi halin shi mai cike da miskilanci, maganar ma kaman baya son yi, sannan ya juya inda nake tsaye yana faɗin "Muje" a taƙaice, lokaci guda ya shiga takawa da niyya barin ɗakin.
Har yanzu kuma kuka nake, sai dai sauti kukan ya ragu sai dai kwalla da taƙi ta tsaya, bin shi na shiga yi a baya har zuwa parking lot da yake cike da motoci na alfarma; motar shi da tafi kowacce haɗuwa a wurin ya shiga tare da juyo ta daidai saitin da nake tsaye, sannan ya sanya hannu ta ciki ya buɗe man ƙofar gaba ta mai zaman banza, ganin da yayi ina ƙoƙarin shiga baya, banyi musu ba na shiga na zauna ina mai share kwalla ta akai akai, daidai lokacin da mama Talatu da mama uwani suka kamo umma tawa kaman matatta suka buɗe baya suka sanya ta, ya fita ya gyara masu sannan ya umarci mama Talatu da take shugaba ta shiga mu tafi tare da ita, yayin da mama uwani ta juya zuwa sashen namu tana mai taɓe bakin an mata buƙulun shiga haɗaɗɗiyar motar da take ɗauke hankalin duk wani dake zama sashen masu aikin.
Horn yayi mai gadi da fitowarshi kenan daga makewayi, ya rugo da gudu ya shiga wangale tangaman gate ɗin, lokaci guda yana mai ɗaga ma uban ɗakin nashi hannu, ( da yake Al'Ameen ɗin mutumin shi ne sosai da sosai) shima mamaki fal cikin ranshi, ganin suhan ɗin a gaban motar Alhaji ƙarami da mama Talatu a baya sai wata mata da take kwance da bai iya tantance wacece ba bayan motar kaman matatta, Allah dai yasa lafiya ya faɗa yana mai furzar da dattin asuwaki daga bakin shi sannan ya shiga rufe ƙyauren gate ɗin da take turawa da ƙarfi saboda nauyin shi.
Motar ya harba bisa titi, yayin da ya ƙara speed ɗin motar, mu da muke cikin motar gani muke tamkar baya gudu, Amman a zahiri gaskiya gudu yake wanda ya wuce ƙa'ida ma, hakan ce tasa nake ganin nawar tashi kaman in ƙwace tuƙin nake ji.
Lokaci lokaci yakan juyo ya ɗan kalle ni da nake ta sharar kwalla gami da jan majina a hankali, tin kafin mu isa asibiti yayi masu waya gashi da patien emergency, aikuwa muna isa aka turo ɗan gadon ɗaukar marasa lafiya tare da gungura ta zuwa emergency ward, ɗaga ƙafa nayi da niyyar bin bayan su suka dakatar dani ta hanyar ɗaga man hannu, wannan ne ya sanya hankali na ya ƙara tashi fiye na da baya, ganin umman tawa kaman gawa sai yanda aka yi da ita, sake durƙushe wa nayi wurin ina mai sakin wani tsumammen kuka da ya karaɗe ilahirin reception ɗin, Ya ilahi, na shiga furta wa a fili ina faɗin "Ya Rab sa'idnee ya Allah" mama Talatu bata yi yunƙurin zuwa inda nake ba, kaman yanda shi ma gogan naku bai yi yunƙurin hana ni ba, sai ma waje da ya samu ya zauna ya tsura man idanu yana mai ƙara nazari na, lokaci guda ya miƙe tare da nufi inda nake durƙushen cikin sakon tafiyar shi mai kama da ta saraki.....
*Fans Kuzo kuci cake ɗin deedat, fa u are All invited*
~_Oum-Deedat ce_~
[8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~11~*
**********'*********************
Kusan yini afnan tayi mana ita dasu Ayan, tafiya tayi wajen ƙarfe shidda saura, bayan ta sake bani haƙuri, na nuna mata haba ya wuce ai babu komai.
Ya Ameen bai dawo ba har misalin ƙarfe shidda da wani abu kuma umma ta bata farfaɗo ba, hankali na ne ya tashi, office ɗin likitan na koma ya ƙara kwantar man da hankali, cewa yayi lafiya lau idan ta farka zata samu ƙarfi sosai, da wannan ne na samu naji ɗan sauƙi, babu abin da ke tadani kusa da umman tawa sai salla, ko abincin da afnan ta sanya ni inci, kaɗan na ɗan tsakura, ita ma da taga ba zan iya ci bane sai ta haƙura ta ƙyale ni.
Ƙarfe bakwai daidai ya shigo bakin shi ɗauke da siririyar sallama da ni ƙaɗai na jiyo shi, kaina da yake duƙe bisa gadon umman tawa na ɗago a hankali na ɗora idanu na akan shi, idanun mu ne suka sarƙe cikin na juna nayi sauri janye nawa, kujerar da nake zaune kai na miƙe gami da tura mashi domin ya zauna.
Dakatar dani yayi ta hanyar ɗaga man hannu da na lura sana'ar shi ce, watau maganar ma wahala take bashi, da ido nake bin shi har ya zauna kan sofar dake ɗakin ƙwara ɗaya tal doguwa 3seater, "ya jikin umman? Har yanzu bata farka ba?" na tsinkayi muryarshi yana jefo man tambaya cikin muryarshi mai daɗin saurare, ɗaga mashi kai kawai nayi, domin har ga Allah kwarjinn shi na hana ni sukuni, ƙamshin turaren shi duk yabi ya cika man hanci." OK" ya faɗa cen iya leaɓɓa, zaro wayar shi yayi ya cigaba da latsawa kaman ma baya cikin ɗakin.
Sallama aka yi, gami da shigowa baki ɗaya, Alhaji Mustapha ne da iyalanshi baki ɗaya suka iso ta ƙarƙashin jagorancin Afnan da tace ta san ɗakin, miƙewa nayi cikin hanzari tare da masu barka da zuwa na ba Alhaji Mustapha kujerar da nake zaune, Gaishe su na shiga yi su da Hajiya kubra da take tsaye gefen Alhaji cikin isa da taƙama, "lafiya" Hajiyar ta amsa mani tana mai nufar kujerar da Ya Ameen yake kai ta zauna, tana mai sakar mashi murmushi yaƙeda wani irin kallo mai cike da ma'ano ni daban daban;
Shi kau Alhajin amsawa yayi cikin sarkin fuska, yana mai tambaya ta jikin umman tawa, amsa mashi nayi ina mai ɗan murmushi iya fuska ta.
Aunty feena ce ta ja kujerar da na bama Alhaji domin ya zauna sai bai zauna ɗin ba, gaishe ta nayi itama ina mai sa hannu na ɗauki Nasreem da take saɓe a kafaɗarta, ta ko wangale man baki tana wasa da hijabin jikina, Amsawa tayi cikin sakin fuska da har saida ta bani mamaki, (Lallai mai ɗa wawa inji Hausawa) jikin umman tawa ta tambaya na amsa mata kaina duƙe ina ɗan yaƙe, Allah ya bata lafiya, da Allah ya kyauta ta shiga yi man, Ameen mun gode na shiga jerawa
Afnan da Ayan ne suka nufi wajen Yayan nasu tin shigowar su, dama ita ta hannun daman shi ce, Nihal ce ta dire wata ƙatuwar ledar da suka shigo da ita a hannu suna ta cin magani ko tanka man ba suyi ba, balle kuma in samu arziƙi tambayar jikin umman tawa,
Angode na shiga faɗi lokacin da Alhajin ya ke faɗa man su zasu wuce Allah ya bata sauƙi. Da ameen na bishi ina mai masu rakiya har bakin ƙofar motar da suka zo da ita, wata danƙareriyar mota ce duk yawan su ta kwashe su tsaf, gaskiya motar ta haɗu iya haɗuwa, Nidai ba zance ga sunan motar ba, Amman Alhajin ne da kanshi ke tuƙawa.
Hajiya Kubra ce ta kalli ɗan nata cikin wani yanayi na ɓacin rai Amman tana ƙoƙarin dannewa ne saboda kada Alhaji ya gane "Son ko zaka zo muje ne? Zamu yi ma su Hajiya siyayya ne gobe insha Allah zamu tafi cen mu duka muyi masu week end" ta faɗa tana mai gyara zama ta cikin motar,
"No mom ina da uziri yanzu gaskiya, akwai inda zanje mai muhimmanci, zamu haɗu gida wajen dinner kawai" ya faɗa a dake cikin miskalancin shi, lokaci guda yana latsa wayar shi kaman ma ba da mom ɗin tashi yake magana ba; saboda ya kula da hajiyar ko jikin umman tawa bata tambaya ba, hakan bai mashi daɗi ba kuma ya kula ko Alhajin nasu ma hankalin shi bai kai wajen ba.
"OK Al'ameen kayi ƙoƙari dai ka dawo kafin diner ɗin saboda zamu tattauna yanda tafiyar zata kaya" aAbban nashi ya faɗa cikin murmushi yana mai tada motar tashi, Saboda ya ji daɗin yanda ya iske Al'ameen ɗin a asibitn, ko babu komai ya san zasu samu kulawa da ta dace, kuma ya san tausaya war ɗanɗan nashi ga na ƙasa dashi.
Juyawa muka yi ni da Ya Ameen ɗin muka shige asibiti n akan idon Hajiya Kubran,
Cikin ɓacin rai da hajiyar ta kasa dannewa ta shiga faɗa tana faɗin "Amman Ahaji hakan ya dace ace kaman Al'ameen yana zaune suna jinyar ƴar aiki tare wannan yarinyar? Haba Alhaji, ya kake maida mu baya ne? Gaskiya Sam banji daɗi ba, iske shi fa nayi zaune hankalin shi kwance, shi ko iskar da take tasowa daga jikin su ma bai ji gurɓatacciya ce" Alhajin ne ya Dakatar da ita cikin ɗan ɓacin rai da yake ɗan taso mashi na halin Hajiyar "Ya isa Hajiya, kibar wannan maganar, wannan shine abun da ya dace kowanne shugaba yayi, na tsayawa tsayin daka ya tabbatar da lafiyar duk wani da yake aiki ƙarƙashin shi, ina Alfahri da Ameenun yana abunda yake dacewa" ƙutawa tayi cikin ɓacin rai da ƙudurce ɗaukar mataki akan al'amarin.
Afnan da take cen baya sai zumɓura baki take yi tana ƙunƙuni, Saudat ɗin ce ta hamɓare ta gami da cewa "village gal, ai dama ke kullum kina bayansu kullum" Aunty Feena ce ta dalla mata harara gami da cewa a hankali "kedai kin cika baƙin hali Saudat"
Shigarmu ɗakin yayi daidai da farfaɗowar umman tawa ta shiga motsa hannun ta gami da ƙoƙarin buɗe idanun ta.
Cikin hanzari muka isa bakin gadon a tare, gami da furta sannu umma, lafiyar ki ƙlau? "Jiddah! Jiddah, kina ina? Matso nan Suhan, hannuna na saka cikin nata ina mai murmushin farin ciki da ke taho wa da ƴar kwalla ta," Gani umma, gani kusa da ke" na shiga faɗi ina mai durƙusa wa na ranƙwafa daidai kan ta ina mai rungumo ta cikin jikina
"Hauwa'u ki yafe man kinji, na hana ki cikar burin ki, ki kira Alhaji ƙarami ki ce mashi na yarda da karatun ki, kiyi haƙuri da sannu kuma zaki san su wanene dangina, ahalina kuma, kiyi ma su Hajiya biyayya su ɗin iyayen ki ne, amanar ki na hannun su ko da bani da rai" ta ke faɗa cikin zafin ciwo idanu ta na a kulle har yanzu
Kuka na fashe dashi ina mai furta "umma ni zaki yafe mawa, nice sanadin tashin ciwon nan naki umma, kiyi haƙuri umma, na dena tambayar ki komai wallahi insha Allah"
Runtse hannuwa na tayi cikin nata tayi shiru a hankali tana mai sauke numfashi a hankali a hankali da gani bacci ne ta samu.
Kasaƙe yayi yana ta kallon uwa da ɗiyar tata cikin tausaya wa ta ɓangare guda kuma yana mai sakin Sirrin murmushi har dimple ɗinshi ya loɓa, Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaga umman ta samu bacci, ko ba komai zai samu sauƙi da zuciyar shi take yi mashi na kukan da afnan ɗin take yi, ya tsani kuka, ya tsani kuka masalan na mace mai rauni, yanzu zai ruɗe ya rasa inda zai sanya kanshi.
Tasowa yayi a hankali,, ya tako har zuwa gaban gadon da ya koma ya zauna bayan da yaga ɗiya da uwa suna magana cikin shauƙin so, ledar da Nihal ta ajiye ce ƙasa gaban gadon umman tawa ya shiga buɗewa, kayan ciki ya shiga fiddowa a hankali a hankali, yana jera su bisa kyakkyawa locar da take ajiye gefen gadon, kayan tea ne, sai ruwan gora, da plax sai mug na shan tea, sai kayan marmari da su cake da sauran kayan ciye ciye da marar lafiyar zai iya buƙata.
Da gani dai wannan siyayyar ta abban shi ce, dan ko kusa ya san halin mom ɗin tashi ba zata iya tsayawa yima ƴan aiki soyayya ba.
Sai da ya tabbatar da ba zasu buƙaci komai ba sannan yayi mata sallama a gajarce ya fice yana mai ja masu ƙofar, da idanu na bishi har ya wuce, tabɗi Ya Ameen Matarka zata sha miskilanci na raya a rai na ina mai miƙewa domin komawa inda ya tashi dan in samu in miƙe ƙafa ta, da kallo na shiga bin wajen da ya tashin, kaman yana wajen zaune, ƙamshin turaren shi yana nan liƙe kaman nan ya fesa shi, ajiyar zuciya na shiga sauke wa a hankali a hankali ina mai furta Alhamdulillahi!
******************************
Bai shiga babban part ɗin ba saida ya koma nashi yayi wanka ya kintsa sannan ya nufi part ɗin hajiyar cikin takon shi kaman na saraki; Sallama yayi ya shiga, duk sun hallara a dining table suna cin abincin da sai dai aka yi ma mama Talatu umarni da ta girka shi ita da mama uwani, kujera ya ja guda ɗaya ya zauna saitin abban nashi, Mug ya ɗauka gami da haɗa cofee, domin bai jin zai iya cin komai a wajen, tsaftar umman Suhan ɗin ce kawai ya yarda da ita.
A hankali ya ke shan cofee ɗin yayin da Alhaji yayi gyaran murya duk suka maida hankali su akan shi, " Gobe idan Allah ya kai mu zamu tafi kankiya, kaman yanda muka saba in mun yi haɗuwa irin wannan, Hajiya ki rubuta list ɗin abubuwan da za'a buƙata da wanda za'a kai ma su Baba ɗin, sannan ku Saudat da Nihal sanin kanku ne cewa idan muka je sai anyi maku maganar fidda mazaje, idan kuna da tsayayyu ku tura su cen kankiya su gaida kakannin naku kafin mu taho, zan yi ma yaya Auwalu magana sai yazo su gaishe su tare, sannan kai kuma Al'ameen idan an amshi list ɗin ka tabbatar ka haɗa komai cikin daren nan dan ina kyautata zaton da safe zamu wuce don na riga nasa anyi booking flight. Ina fatan babu mai magana ko?" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran da take zaune tana ta cika tana batsewa,"
Alhaji shi Al'ameen ɗin baka ce ya fidda mata ba, don na gaji da ganin shi zaune haka nan, tsararrakin shi har sun yi aure, wasu ma harda ƴaƴa, don haka shima yayi gaggawa fidda wadda yake so, in mun duba munga cancantar ta, sai a haɗa bikin da na su Saudat kawai"
Ɗan murmushi Alhajin yayi yana mai maida kallon shi kan Al'ameen ɗin da ya kafe mom ɗin tashi da idanu yana ɗan murmusawa, shi da ya gano ta, watau tana gudun ya so yarinyar cen dake asibiti tare da maman ta, humm Hajiya kenan, yana fatan Allah ya shirya da mom ɗin tashi ta gane annabi ya faku, koma dai minene shi dai ai ba za'ayi mashi auren dole ba, ba kuma za'a ƙayyade mashi lokacin auren shi ba, duk tsiya dai sai ya samu wadda tayi mashi, kuma har yanzu baya tinanin ya dace, duk cikin ƴan matan da suke cewa suna so shi, shi fa ba suyi mashi ba, bai yarda da natsuwa da inganci shi ba, don duk irin ƴaƴan hamshaƙan masu kuɗi ne, masu ɗabi'a irin ta mom ɗin tashi watau wulaƙanta na ƙasa dasu, Sam basu san babu ba basu kuma san daraja ɗan adam ba, abin da umman tashi bata sani ba shine, duk wacce ya auro cikin su ya kawo mata ba zasu taɓa daidaitawa ba, saboda halin su ɗaya ne, isa, taƙama, izza da son mulki, wa zai bi wani? Murmushi ya ƙara saki daidai lokacin da yaji Dad ɗin nashi na faɗin
"Tau kaji fa Son, Mom ɗin ka na nuƙatar suruka" "Amman sai inga ai shi namiji ne ya kwantar da hankalin shi ya zaɓo wadda tayi daidai da ra'ayin shi, kada ya je yayo zaɓen tumu dare, kinsan matan yanzu ɗin yanda suke" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran.
"Haka ne Alhaji, sai ya duba cikin lokaci, in bai yi yanzu ba, sai yaushe? Ko so yake ayi mashi tare da Afnan ne? "
Ta faɗa tana mai goge baki da soft tissue dake ajiye gefe da gefen dining table ɗin, miƙewa tayi tare da faɗin Al'ameen ɗin ya biyo ta domin su rubuta Abunda za'a buƙata tare, gami da ficewa ta haye sama nata.
Al'ameen ɗin ne ya bita a baya, tare suka isa falon yayin da ta wuce bedroom ta ɗauki wata jotter mai kyau ta zauna ta shiga zana abubuwan da za'a buƙata cikin isa da taƙama, yayin da suka baro Alhaji Mustapha ɗin da sauran ƴaƴan nashi yana jin damuwoyin su, domin shi mutum ne mai yawan jiɓintar Al'aamarin iyalan nashi, dama kuma haka ake so, haka ya kamata ace ko wanne mai gida yana ma iyalanshi, komin girman shi kuma komin matsayin shi.
Bayan Hajiyar ta gama rubuta komai ne ta miƙa mashi, gami da cewa ya duba in da wani abu sai a ƙara, dubawa ya shiga yi cikin halin ko in kula da isar da mahaifiya tashi take ta zubawa, babu komai ya faɗa mata gami da miƙewa don barin ɗakin.
Dakatar dashi tayi, tare da ce mashi ya zauna zasu yi wata magana ne, zaunawa yayi bisa sofar dake kusa da tata ya bata dukkain natsuwar shi, domin shi mutum ne mai biyayya da son gamawa da iyayen nashi lafiya, shiru ne ya biyo baya na ƴan dakiƙu, domin ta san abun da zata zo ma ɗan ɗan nata ba lallai ya ɗauka ba domin ita ta haife shi, ta san halin shi sarai.
"Al'ameen watau na lura ka fiye shiga Al'ameen Suhan da maman ta, bana so fa raini ya shiga tsakanin ku, kuma da me suka fi sauran ma'aikatan gidan nan ne da kafi basu cikakkiyar kulawa, ko dan Kaga mahaifi ka ya ɗaure maka wutsiya ne? Tau fa ka sani ni bazan lamunta ba, tinda Alhaji ya ce a ƙyale su da aikin gidan, da ta samu lafiya ka faɗa masu su tattara su koma cen inda suka fito tinda ba zata faɗi ainahin daga ina take ba ita daƴar tata, kuma ina so ka samo mana kuku cikin ma'aikatan company ɗinka guda biyu, wanda ka san sun ƙware sosai, saboda Sam girkin talatun nan baya man daɗi" ta faɗa cikin muryar ta, da ta koma ta mulki gaba ɗayanta.
"Mahaifiyar tashi ya tsura ma idanu har saida ta kai aya, ba tare da ya katse ta ba, sannan ya muskuta ya gyara zama," Mom ina so ki sani, ni duk cikin ma'aikatan nan babu wanda na fifita, duka matsayi su ɗaya ne a wuri na, mom rashin lafiya tafi gaban komai, kuma ko da sun bar aiki, bana da hurumin korar su, kin manta ne dad yace gidan shi ne? Kuma ya basu izinin zama har zuwa lokacin da suke so, ko kuma suka gaji dan kansu, babu wanda zai hana su tafiya, so mom ina ganin wannan maganar yafi da cewa ku tattauna ta da dad, duk hukuncin da ya yanke a kansu is better" ya faɗa kan shi tsaye, domin Al'ameen ɗin mutum ne da yake kai tsaye, watau babu munafunci ko ɓoye-ɓoye a al'amurran shi.
Sannan ya cigaba da faɗin "maganar kuku kuma zan magana cikin ma'aikatan sai a turo su ko zuwa da safe ne" ya furta cikin salon miskilanci shi, tare da miƙewa ya bar ɗakin ranshi a cunkushe, bai san sai yaushe ne mom ɗin tashi zata bar halin ta ba, bai koma gidan ba ma ga baki ɗaya sai da ya tabbatar ya haɗa komai da aka bashi list, sannan ya kai ma Aunty Feena, domin yin packaging ɗinsu ko wajen mom ɗin tashi bai koma ba ya wuce part ɗinshi kai tsaye.
Yana kai kafaɗar shi bisa gadon nashi, tinanin su yayi mashi sallama, kenan umman tata ta bata dama domin tayi karatun? To ko Dad ɗin yayi mata magana ne? Allah sarki umma baiwar Allah, har yanda take ma ba cikin hayyacin ta ba, maganar ta Suhan ɗin tabi iyayen shi, abun da shi kuma Mahaifiyar tashi ta gaza fahimta, me suka tsare mata? Menene ɓata fi su dashi ba? Koda yake ya lura akwai ƴan zuga cikin Al'amarin, dole ya taka masu burki, dole ya gargaɗe su indai suna son zama cikin gidan, ba zai lamunci munafunci da haɗa husuma ba, hakanan su sanya ma bayin Allah karan zuƙa ba tare da sunyi masu wani abu ba daidai ba.
Yayi Alƙawarin taimaka ma Suhan ɗin domin jin ta yake kaman Afnan ɗinshi, da ƙaunar da Afnan ɗin ke mata da sanyi halin ta da kuma tarbiyyar da ta samu daga wajen umman tata, sai kuma halin da suke ciki da musguna masu da Mahaifiyar tashi ke yi, su suka ƙara mashi ƙaimi wajen ganin son ya taimaka masu bil haƙƙi da gaskiya, baya jin wani abu dangane da Suhan ɗin illa wani narkon tausayinta da ke malala cikin zuciyar shi, yarinya da ita, ba tafi shekara ishirin ba Amman tana fuskantar wannan waƙi'ar, wannan halin da suke ciki kan ƙara jefa zuciyoyin su a damuwa da shi kuma baya jin zai iya lamunta.
A haka ya samu bacci ɓarawo ya sace shi, zuciyar shi fal da tinanin halin da umman ta Suhan ɗin take ciki.
0 comments:
Post a Comment