Zaune yake cikin jirgin, saidai ya ma rasa tinanin da zai yi, gaskiya wani sashe na zuciyar shi na raya mashi yayi wauta, idan har sonta ne baiyi bai kamata ya baro ƙasar ba, sai yayi tinanin hanyar da zai warware ƙullin da shine ya ƙulla shi da kankin kanshi.
Har jirgin su ya dira ƙasar ya kasa natsuwa a zuciyar shi, sai yayi kaman ya juya ya yanki ticket ɗin komawa sai wata zuciyar kuma ta hana, da haka dai har driver ɗin da zai ɗauke shi ya ƙara so bai lalubo mafita ba.
Haka ko da ya isa zuwa gidan, komai a sanyaye yake yin shi, gani yake yi kaman yayi sallama da ita kenan.
Shi me ma ya hau kanshi da har tinanin barin ƙasar yazo kanshi? Bayan ya san mahaifiyar ta Suhan tana da gagarumar lalura ta ciwon zuciya, me zai faru in tashi mahaifiyar ta cigaba da ƙuntata masu da gallaza masu? Meyasa ya baro ƙasar ba tare da ya gano munafikin cikin gidan ba mai ƙulla dukkanin makircin?
"Ooops*
Ya faɗa yana mai dafe kai, lokaci guda ya faɗa bisa tafkeken gadon da yake mallakin shi, tsuru yayi yana mai lumshe ido, kewar gidan har ta fara damun shi, saidai ya gaza gane kewar ta mecece, tin da mai yasa idan ya baro gidan baya jin irin wannan kewar?
Waya ya lalubo gami da danna ma Bilal ɗin kira, ringing biyu kuwa ya ɗauka, shaida mashi yayi ya sauka lafiya, sannan ya ke tambayar shi sauran abubuwa. So yake ya tambaye shi suhan ɗin da ya san dai iyanzu bacci take yi domin idan ya kintata daidai yanzu zai kama kusan ƙarfe sha biyn dare a ƙasar tashi nigeria.
Saidai ya kasa tambayar, ganin Bilal ɗin bacci yake ji sosai, ga dukkan alamu ma ya fara baccin ya tashe shi ya sanya shi datse kiran yana mai ce mashi zasuyi waya dasafe idan Allah ya kai mu.
Shima Bilal ɗin da yake ya fara bacci bai wani ja ba, ya kashe wayar tashi yana mai tura ta ƙarƙashin fillow ɗin, shi kau ta ɓangaren Ya Ameen jifa yayi da wayar tinani fal a ranshi, ya rasa dalilin shi na tinanin ta har haka, to me ma ya hana shi tambayar abokin nashi ita?
Saidai kuma fa yana tsoron kada Bilal ɗin yace bai fita sabgar yarinyar ba, gashi kuma har ya sanya shi zama ƙasar tashi domin ya taimaka masu.
Jawo wayar yayi yana mai ɗan sakin ɗan ƙaramin tsoki, ji yake yi kaman yayi unblocking ɗinta ko status ɗinta ne ya dinga dubawa, saidai fa so yake yi ya manta da Al'amarin ta, so yake yi lokacin da zai koma ta riga da tayi aurenta ta yanda ma ba zai sanya ta a gaban shi ba balle yayi cousing wata matsalar tsakanin shi da tashi mahaifiyar.
Saki wurga wayar yayi bisa gado yana mai miƙewa ya shiga tuɓe kayanshi, so yake yi yayi wanka ko yaji sauƙin Abunda yake ji a jikin shi da kuma zuciyar tashi, domin tinda ya baro ƙasar tashi tsikar jikin shi take a tashe ya rasa kuma dalili.
Da haka ya wuce zuwa toilet ɗin zuciyar shi na raya mashi zuwa dasafe zai kira iyayen nashi domin su san ya isa lafiya.
Ban san wa zan tambaya ba game da tafiyar Ya ameen ɗin ba, beside ma ni meye nawa a ciki? Ai yana yin aikin shi ne, ko yaje zai dawo ne, saidai na rasa dalilin da yasa nake jin zuciya ta ba daɗi sam, duk da yace Ya Bilal ɗin zai mani komai na dangane da karatu na, shima na kula yana da kirki don ma zance yafi Ya Ameen ɗin sakin fuska nesa ba kusa ba.
Washegari da tafiya ta Yayan namu koda Afnan tazo mani da maganar cewa suma Yau zasu wuce ban ko wani damu ba sosai, bansan kuma dalili ba, saidai ta yiman Alkhairi kaman yanda ta saba, a bakin ta ma ne nake jin wai Ya ameen ɗin America ya tafi yin wani aiki, Amman wai ba zai daɗe ba zai dawo.
To sun wuce dai, haka ma Hajiya Zainab da Alhaji Auwalun sun koma Katsinan da motar da dangin mijin Hafsat ɗin suka bata.
Su Goggo Aisha ma da Goggo Fatima da iyalan su duk sun koma, tare suka tafi da ƙanen nasu watau Yaya Auwalun, sai ƴan biyu ne aka bari da Kaka zuwairan su sai ƙarshen sati za'a maida su.
Kafin tafiyar Hajiya Zuwairan tayi ma Ummanmu sha tara ta arziƙi, ganin yanda umman tawa ta tsaya mata ka'in da na'in wajen hidimar bikin nasu, duk da ta san ba don abun duniya tayi ba, Amman saida ta bata maƙudan kuɗi da kaya sosai harda ni ma, fafur taƙi amsa har saida tace zata je ta gaya ma kaka zuwairan ne yasa ta amsa suma ba duka ba, a cewarta ai an zama ɗaya.
Gidan ya koma shiru tsit kaman babu mutane, inda ma zaka ji hayaniya shine sashn kaka zuwairan da akwai ƴan yara ƴaƴan su Aunty Hassana da Hussaina ɗin, shima ba wani fita suke sosai ba, in Kaga sun fito to wajen wasa zasu su hau lilo.
Hnakalin ummata ya kwanta ganin babu wanda ya kuma tada maganar da taji ɗin harma mutane sun watse kowa ya koma muhallin shi, bamu da matsalar komai ga kuɗin da ya Ameen ya bamu kwanaki basu ƙare ba, ga kuma sha tara ta arziƙi da Hajiya Zainab tayi mana, ya sanya hankalin mu kwance bamu da matsalar komai.
Kullum sai umman tawa ta sanya ni naje sashn kaka zuwairan na gyara masu, to suma basu taɓa tada man wani zance ba, illa iyaka dai sanya mani Albarka da kullum suke yi tinda Alhaji Mustaphan ya gaya masu yanzu yana kan bincike ne su ajiye maganar gefe.
Ta fannin Hafsat kuwa kullum muna waya sosai, har take sheda mani suma ƙarshen wata zasu wuce don Allah in zo kafin ta tafi, nan nake ce mata saidai yanda hali ya bada, domin yanzu kaman an zareman wata tsoka daga jikina nake ji na kuma rasa dalili.
Duk da umman tawa ta kula da rashin walwalrr tawa, sai ta dangana hakan dankaɗaici, da ke damuna a kwana biyun ga kuma kwazzabar maree da nake fuskanta, ba damar in fita sai an yada man habaici ko an jefeni da kalma mai muni.
Da su kaka zuwairan suka tashi tafiya, bansan inda ummata ta samo daddawa da kuka dasu kuɓewa masu kyau ba taba kaka zuwairan, aikau tasha Albarka kuma taji daɗin kyautar domin su tsofaffi ne basa yi saida tuwo. Har mot amuka rakasu da duka sauran ƴan gidan muma ɗaga masu hannu har suka fice.
Alkhairi daɗi ne dashi wai wannan ɗan abun da ummata tayi ma mahaifiyar Alhajn saida ta faɗa mashi, aikau yana dawowa sai ga wata sha tara ta arziƙin ya aiko mana dasu jin daɗin kyautata ma mahaifiyar tashi da mukayi da kula da ita a ɗan zaman nata a cikin gidan wanda ko ita matar tashi ma bata yi saboda tsabar girman kai da jin ita ɗin wata ce.
Mun samu sauƙi kam ta fannin hajiya Kubran sosai, kwana uku tsakani da tafiyar su Kaka zuwairan sai ga Mama Talatu da saƙo wai daga wajen hajiyar an maida mu bakin aikinmu.
Ummanmu baiwar Allah sai jin daɗi take yi, tana kimtse kimtsen komawa bakin aiki, domin ita kanta Hajiyar ta sheda cewa Mahaifiyar tawa ta iya girki ba kaɗan ba, Sam basa jin daɗin girkin kukun nan masalan ma Alhaji.
Lokacin da ta sheda mashi maganar son a maida mu aikin bai musa mata ba, sai a cewa yayi hakan yayi daidai.
Nikau a cikin zuciya ta Sam banji daɗi ba gani nake yi kaman za'a daƙile mani maganar karatu na ne, saidai kuma a ranar ne sai ga kiran Bilal ɗin wai in miƙo mashi takaddun na, saboda ayyuka sun rincaɓe mashi ne ya sanya bai amsa ba saida ya gama daidaita komai a office sannan.
Tambaya ta ya shiga yi bamu da matsalar komai dai ko? Babu kam na bashi amsa gami da juyawa na nufi cikin sashen namu, ko ba komai hankali na ya ɗan kwanta, naga alama kaman Bilal ɗinma zai tsaya mani kaman Ya ameen ɗin, to nima dai dama Abunda ya dameni kenan, bana son dukkan wani abu da zai yi mani katanga da cikar nawa burin.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Baya buƙatar tambayar abokin nashi komai akan lamarin karatun Suhan ɗin domin ko ba komai ya san amini nashi zai riƙe amana yayi mata dukkanin Abunda ya dace. Hakan ce ta sanya bai kuma tambayar shi ba akan lamarin nata, ko waya sukayi tau fa zancen da ya shafi kasuwanci ne da ma'aikata sai kuma Abunda ya shafi gida, tinda Yanzu Bilal ɗinne mai yin komai, shi ma Alhajin hidimarshi tasha kanshi da yawa sosai, gashi mai girma shugaban ƙasa ya bashi Ambasador a ƙasar ta Ƙatar, saboda yanda ƙasar take da arziƙin man fetur ya sanya yake ayyuka biyu ga aikin da yake yi ga kuma hidimar mai da ya shiga ka'inbda na'in nan fa likafa ta cigaba arziƙi ya linka nada, tini ya cema Hajiya Kubran ban wuri, duk da itama ba zaune takeba Business ɗinta kawai take yi hankalinta kwance.
Hankalin Al'ameen ya ɗan kwanta tinda yau Bilal yayi mashi maganar an samu admission ɗin Suhan ɗin, tinda ya baro Nigeria ɗin yau tsawon wata biyu cikin na uku kenan Bilal ɗin bai taɓa mashi maganar ta ba sai yau, har ya fara tinanin anya kuwa yana yin alƙawalin da ya ɗauka? Saidai ya san dole ne yayi mashi uziri tinda ya san irin tarin ayyukan da suke gaban shi, wannan ce ma tasa Bilal ɗin ya roƙu su iyayen yarinyar da zai aura ɗin akan A ƙara mashi wata biyu ya gama settling duk wasu muhimman abubuwa dake gaban shi, lallai shi kanshi ya jinjina ma Al'ameen ɗin ga irin ayyukan da yake fama dasu kusan yana running kamfanoni kusan aƙalla bakwai a faɗin nigeria kuma yana da ma'aikata ba iyaka wanda kullum fama yake da tarin jama'a matasa da kuma ƙorafe ƙorafe su.
Yaji daɗin jin wannan kalamn saidai shi inda yaso ta samu ABU zariya, sai gashi ba cen Allah ya cida ita ba, ansha daga da Umman akan nisan da suhan ɗin zata yi da ita kuma ba mai kula da ita ce sai Allah, Bilal ɗinne ya tausheta yace ta bara Allah ɗin, atafau tace ita in karatu ya wuce nan Abujan ba zata yarda ba, dole tasa ya kira Alhaji Mustapha saida fa yace mata zai sa masu kula da ita ne yasa ta yarda saboda ganin girman Alhajin, Amman shi Al'ameen Sam baisa baki ba ganin Alhajin nashi ya sanya, kai shi fa tinda ya tafi bai ƙara ji daga garesu ba, dama Suhan ɗin ba number ɗin shi ta cen ƙasar take da ita ba, balle ta kira ta samu, ko a WhatsApp ɗinma ta dena ganin ɗuriyar shi sai ta bar ma kanta cewa ayyuka ne sukayi mashi yawa in ba haka ba ai Al'ameen ɗin na wajensu ne, ta san haka kurum ba zaiƙi sanya baki akan a shawo kan umman tata ba.
Hafsat tini sun wuce, dakyal na samu naje mata sau ɗaya tin bayan bikin.
Nima yanzu abubuwa sunyi mani yawa shirye shiryen tafiya makaranta ta nake yi, bani da matsalar komai, saidai kula da nayi har yanzu umma ta jikin ta baya bata tafiyar tawa, idan na lura da hakan nima jikina kanyi sanyi, albarka nake so ta sanya mani ba wasu wasu ba, hakan ce ta sanya na zauna na nutsar da ita a hankali, tau ta dai ɗan saurareni kuma ta ɗan fahimce ni harma addu'a tayi man da fatan samun nasara akan Abunda zanje nema ɗin, kunsan a koda yaushe addu'ar iyaye itace abun so ga ƴaƴan nasu ba addu'ar banza ba ko Kaga uwa tana ta ƙunduma ma yaron ta ashar tana la'antar shi cikin zagi kuma tana so ace ya girma yayi albarka kuma ya jiƙanta ya sota, ai da wuya Kaga uwar da take la'antar yaron ta kuma ya girma yayi albarka, saboda addu'ar uwa ƙarɓaɓɓiya ce ba shamaki.
A kulliyaum sai Nihal tazo gidan nan, itace bata tafiya sai dare, kai in taƙaice maku tin bayan bikin nata da kwana biyu ta fara sintiri a cikin gidan, kuma Hajiya Kubran na kallon ta, ta kasa kwaɓa mata, a cewarta ai ba kurkuku ta kai yaran nata ba balle ace ba zasu fita ba, Saudat ɗin cema mai yin kwana biyu bata zo ba, Amman in ta kama suka zo ɗin har kwana suke yy. Ba wadda bata da jarin kanta take juyawa, hasali ma yanzu duk kansu suna aiki ne a wasu kamfanoni da aka buɗe suna jagorantar shi, saboda ɗimbin ilimn dake kansu, da yake Allah yayi ma yaran na Alhaji Mustapha ƙwaƙwalwar, Abie Kuwa tini ya koma ƙaro karatu cen ƙasar ta america tare suke da Al'ameen lokuttan da baya da lecture ya kan bi Ya Ameen ɗin Office yana taya shi ayyuka.
Bikin Bilal ɗin ya matso, duk a gidan su Ya ameen ɗin ake komai, saboda shi iyayen shi ba anan ƙasar suke zaune ba suma, babu Abunda ba'a aiwatar ba na Al'ada, nayi mamaki da ya Ameen ɗin bai zo ba, bashi har ina daf da tafiya makarantar.
A cikin estate ɗin da 'ameen ya gina wadda ya sanya Bilal ɗin yin lunching ɗinta kwanaki ba daɗewa ya ajiye matar tashi, Ummi ɗin yarinya ce mai hankali sosai da sosai, ga fara' a da son mutane kaman mijin nata, lokutta ya kan roƙi umman tawa akan ta barni inje gidan nashi wajen matar tashi, da yake yanzu sun saba da ummata sosai harma dani ɗin, na ɗauke shi kaman ya yana ne komai idan ina da buƙata na kan tunkareshi kai tsaye ne, ba don kar ace nayi butulci ba sai ince yafi Ya ameen ɗin daɗin mu'amala, domin shi akwai sakin fuska da faram faram, ba kaman Ya ameen ɗin ba da lokutta da dama magana ko murmushi ma sukan yi mashi wahala, duk da ba wai yafi Al'ameen ɗin kirki bane da hangen nesa.
Mun saba da Ummin Matar Bilal ɗin domin idan tazo kusan ma ince sashen mu take yini, saboda Hajiya Kubran yanzu bata cika zama ba, sai mu yini muna fira, har kitso na kan yi mata wani lokaci da yake na iya, sai kusan marece mijin nata kanzo ya ɗauke ta.
Wani abu ɗana kula dashi shine, yawan zuba man idanu da Ya Bilal ɗin kanyi lokutta da dama, masalan ma idan ya tadda ni ba hijab, gashi ni kuma ganin sabon d a mukayi dashi ne ya sanya ni bana ganin hakan a matsayin wani abu, ashe ban sani ba kuskure nake yi, ɗana kula da hakan ne sai na fara janye jikina ko in sanya hijab idan ya shigo ɗakin namu, ko gidan shi na rage zuwa, shima bansan dalili ba sai naga ya rage kawo Ummin tashi gidan namu.
Ban damu da hakan ba, illa iyaka dai bana yarda wani abu ya haɗa mu, ko maganar shirye shiryen makaranta ta ni nake yin abuna bana tsayawa jira, Tinda yanzu ina ɗan samun kuɗin aiki na, kuma an koma bamu abinci a gidan.
Ko ya kula ne shima? Sai naga duk ya sha jinin jikinshi, sai dai fa a zuciyar shi wani abu kan bijiro mashi a duk lokacin da yake tare da suhan ɗin, ba don yana so ba, tinda sai a yanzu ne ya ƙara yarda d a maganar Abokin nashi, Suhan ɗin nada wasu abubuwa da suke kaman maganaɗisu ga maza, duk namijin da zai ɗora idanu akan fuskar ta to fa abun nan zai ja shi har zuwa gareta. Sau da dama abokan shi kan mashi maganar Suhan ɗin saidai bai san dalilin shi na rashin ba maganar tasu muhimmanci ba.
***************************
Ƙarfe takwas a rabi na safiyar ranar Litinin ɗin da ta kama itace ta ƙarshen wata, wayar Bilal ɗin da take ajiye bisa side drower ce tayi ƙara, Ummi ce ta ɗaga ganin sunan da yake jiki *Friend* taga an rubuta, cikin sallama ta kara wayar a kunnen ta.
Daga cen ɓangaren aka amsa mata cikin sakin fuska da gani fara'a mutumen dake wayar da ita yakeyi
"Friend ya kike? Ina angon naki ne? Ko har yanzu bai tashi ba?
Cikin dariya itama ta mayar mashi, yau kam abun nashi ya bata mamaki wai Al'ameen ɗinne yau da zaulayarta haka?
" Ya tashi Ya Ameen yana toilet ne yana wanka, ya aiki?"
" Lafiya lau Pls idan ya fito ki faɗa mashi ya kira ni" daga cen ɓangaren ya amsa mata, to tace mashi tana mai bashi saƙon gaisuwa ga ameen ɗin.
Baisan dalili ba, yau kam hakanan ya tashi da kewar gida, duk da suna waya da sauran ƴan gidan har ya kan tambayi mudi driver Lafiyr umman suhan ɗin, Amman ita ko da alama bai taɓa tambayar ta ba.
Saidai yau ba zai iya jurewa ba, tin cikin daren ne tinanin ta ya matuƙar damun shi, sai mafarkai marasa daɗi da yake yawan yi kwanakin nan, shi kanshi ya rasa dalilin son tafiyar tashi ƙasar tashi. Amman gaskiya bai jin zai iya tsallake yau bai bar ƙasar ta amurkan ba.
A hannun Abie yanzu da ya riga ya ƙware da komai ya bar office ɗin, har ya haɗa jikka sai kuma ya koma ya zauna ya kira aminin nashi, fuskar shi babu walwala Sam, saidai wani fari daya ƙara, fatar nan ta murje kaman bature don in ba hausa kaji yayi ba babu Abunda zai hana kace mashi ba'indiye, ga gashin nan baƙi siɗik daya kwanta mashi har ƙyeya, ba aski kanshi saidai gyaran fuska.
Sanye yake cikin lallausan yadi ɗan ƙasar Turkiyya mai walwali anyi mashi ɗinkin gudluck, Al'ameen ɗin mutum ne mai kwarjini da haiba, duk wanda ya kalle shi sai ya sake waiwaya wa ya kalle shi.
Wayar shi ne da take cikin aljihun gabar rigar tashi ta ɗauki tsuwwa, ƙirar iphone 11 pro max ce da ko ƙasar tamu ta nigeria bata kai ga shigowa ba, sai faman tallar ta da ake tayi.
Ɗagawa yayi gami da cewa "Friend how far?" Bilal ɗinne ya shiga cewa "Shegen kaya, kayi wuyar ji fa mutumena, na san ayyuka ne sukayi maka yawa"
"Wallahi kuwa, Amman gani na shirya yanzu zuwa Nigeria nan da ƙarfe uku kazo ka ɗaukeni, domin yanzu haka kai tsaye airport na nufa"
"Wat?". Bilal ɗin ya amsa mashi ta ɗaya ɓangaren bai tsaya jin me zai ce mashi ba ya cigaba da faɗin
"Gaskiya bakayi shawara dani ba da ban barka kazo ba, yanzu haka kana dawowa komai zai kwaɓe bros, ina mai baka shawara, gobe ne Suhan ɗin zata tafi makaranta, ka bari har sai ta tafi sannan kazo, kasan yanzu abubuwa sunyi masu sauƙi sosai, sanin da Mom tayi yanzu baka nan, yarinyar na shirin ta a tsanake, domin yanzu babu damuwar komai a ranta, Amman fa ni a ganina"
Shiru yayi ta cen ɓangaren, sai kuma lokaci ɗaya ya koma ya zauna, yana mai sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi har saida Bilal ɗin ya jiyo shi, dafe kanshi yayi, lallai fa shi wannan abun ya fara damunshi, yana buƙatar yaga kowa nashi, kusan yanzu wata bakwai kenan fa, lallai ashe ya yaudari kanshi da har yake tinanin sai Suhan ɗin ta gama makaranta tayi aure sannan zai dawo, sai gashi ko tafiya ma batayi ba ya fara kewar su.
Jin da Bilal ɗin yayi Al'ameen ɗin yayi shiru, ya san ya yarda da maganar shi tankawa ne kawai ba zai yi ba, ya sanya shi shiga lallashi shi, saidai fa shi a ganinshi Al'ameen ɗin na zuwa zai dagula komai, gashi yanzu baya son duk wani abu da zai taɓa mashi suhan ɗin tashi duk da ya kula da janye jiki da take yi dashi.
Kuma tabbas ya san yanzu Al'ameen ɗin nayin arba da ita mikin dake cikin ranshi zai tashi ne, domin yanda hankalinta ya ƙara kwanciya, ta sake yin ɓul-ɓul da ita, ga kyaun ta daya ƙara fitowa a fili, yana so ne ya kafa gwamnatin shi gareta duk da ya san abu ne mai wahala a yanzu kam har sai ta fara karatun nan tukunna, domin yanzu ita karatun ne gabanta.
Bai ƙyale shi ba har saida ya tabbatar ya kwantar mashi da hankali sannan ya kashe wayar, shi kau Al'ameen ta ɓangaren shi zama wa yayi ya kwanta rigingine kan bayan shi, ya rasa dalilin shi na amincewa abokin nashi, ya rasa kuma me ya hana shi gaya mashi hankalin shi ne ya kasa kwanciya, gani yake yi kaman wani abu zai same su, duk da Bilal ɗin ya shaida mashi cewa yanzu komai lafiya lau?
Baijin zai sake fita ko ina, kallon shi ya kai kan jikkarshi da take ajiye gefe wadda ya haɗa ƴan abubuwan buƙatar shi, ji yake yi kaman ya tashi ya tafi, Amman wata zuciyar na bashi cewa yabi shawarar abokin nashi, da haka har wani ɗan bacci ya sure shi a wurin yana saukar da ajiyar zuciya a hankali.
Bilal ɗin na kashewa ya cigaba da shirin shi, ummin dake zaune bakin gado ce ta kalle shi cikin rashin jin daɗin barin abokin nashi yazo yaga iyayen shi.
"Nikau dear sai inga kaman ka basshi yazo ɗin, alabasshi ko kwana biyu sai yayi ya koma hankalin shi dai zai kwanta atlist"
Baibar Abunda yake yi ba ya shiga bata amsa
"ba zaki gane ba ne cwthrt, a halin da ake ciki yanzu yarinyar bata buƙatar zuwan shi, shi kuma ya fake ne da iyayen nashi Amman a zahirin gaskiya zuwan nata ne, ni kuma ba zan lamunta ba ya dagula lissafin bayin Allah, yayi haƙurin har ta tafi" nan ne yake faɗa mata duk halin da suka shiga cen baya da dalilin tafiyar Al'ameen ɗin american.
Ajiyar zuciya ta sauke tana mai cewa Allah ya zaɓa mata Abunda yafi zama Alkhairi a Rayuwar ta, da ameen ya amsa mata har yanzu yana mai ɗaura links a hannun shi, saida ya gama ne sannan ya ɗauki briefcase ɗinshi ya fice. Har bakin ƙofa ta raka shi, saida taga fitar shi ne sannan ta juya zuwa cikin gidan tana mai tausaya ma Suhan ɗin.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Shiri na nake yi hankali kwance, na gama haɗa komai, saidai fa akwai Abunda yake muntsili na a zuciya, tinanin Ya Ameen ya dameni cikin kwanakin nan, ba waya ba aike ba saƙon gaisuwa? Saidai wani lokaci idan na tambayi mudi yaceman suna waya, ko da na amshi numb shi In kira shi in gaya mashi batun karatun nawa da inda na samu admission da Abunda zan karanta duk da shi ya zaɓa man tin wajen cike jamb, ban same shi ba, na kira sau ba adadi shiru, hakan ce ta sanya na haƙura duk sanda Allah ya kawo shi zan faɗa mashi baki da baki, tinda ba wai don Bilal ɗin ya gaza bane ta kowanne fanni.
Kwanaki ne ummata taje ma da Hajiya Kubran maganar tafiyata makarantar, bata hana ba Abunda ya bamu mamaki kenan, saidai tace Albashi zai dakata da shiga har sai lokacin da na koma bakin aiki, ummata bata da zaɓi illa iyaka ta amince, ta taimaka mani wajen shirya komai ta yi tana mani wa'azi da faɗan in kama kaina inyi Abunda naje nema, banda shashanci banda kula ƙawaye barkatai banda kula samari. Karatu shi ya kai ni shi kuma zanyi.
Yau Bilal ɗin bai zo gidan namu ba, saidai ya kirani akan cewa in shirya gobe zai zo ya kai ni da kanshi, umman tawa zata rakamu, Naji daɗi har na gaya mata, to itama ɗin ta amince da hakan saboda tana so taga inda zanje koda Allah zai sa ta buƙaci zuwa wata rana ta subani.
Har dare yayi ina ƴan tattare tattare na, ita kuma ummata tana kwance tana kallona har take bani wasu ƴan labari, kewar ɗiyar tata na tsira mata a cikin rai, tana jin kaman tace ta fasa, saidai ba zata iya yin wasa da Rayuwar ɗiyar tata ba.
Kaman an zabureta naga ta tashi, ba tare data ceman komai ba, naga ta zari hijabin ta ta fice, ban kawo komai a raina ba, har na gama na koma na kwanta, bansan lokacin da ta shigo ɗakin ba domin bacci tini yayi awon gaba dani.
Da asubar farko kiran sallah ya tashe ni. Da mamaki nake bin ko'ina na ɗakin da kallo. Komai namu an tattara shi guri guda hatta da kayanmu duk an ƙuƙƙule, bokitan mu duk an rafke su guri guda, katifar da nake kai ce kawai ta rage, itama ina tashi ta jingine ta.
To me hakan ke nufi ne? Lafiya kuwa? Tambayar kaina na shiga yi, ganin tana ta ƴan haɗe haɗen kaya ne nayi shahadar murtsike idanuna na shiga tambayar ta.
"umma lafiya kuwa?" ina zamu ne naga kin haɗa kaya duka?
Bata tanka mani ba ko alama, ko kallona ma batayi ba, tambayar ta na cigaba da yi, kaman ina magana da kurma. Sallama najiyo daga bakin ƙofar ɗakinmu, ban tantance muryar wanene ba, sai Naji ana cewa" Maman Suhana wai dreban ya iso, ku fito" to tace gami da cewa "muna zuwa" bata bi ta kaina da nake tsaye ba mamaki ya kashe ni na kasa tankawa, ta shiga kinkimar kaya zuwa wajen, ta dawo ta ƙara kwasa, to dama kayan ba wasu yawan kirki ne garesu ba, hakan yasa tini ta fice dasu tas, illa katifa da take ba mallakin mu ba, kai hatta da kayan ɗana haɗa na tafiya makaranta yau ta fice dasu zuwa motar.
Ban abune ba, naji ta kama hannuna, zan ƙwace hannuna ne in ƙara jefa mata tambaya, naga ta juyo tayi mani wani irin kallo, sannan tace
"Nan gidan ubanki ne?"
Ƙwalalo idanu na shiga yi, tinda nake ban taɓa jin irin wannan kalmar a bakin ummata ba, ai bansan lokacin da na girgiza mata kai ba, na shiga binta kaman wadda aka zare ma lakka, har zuwa lokacin da muka fita gare ɗin, mai gadi na kallonmu yana ta yi a umman tawa magana ko sauraren shi batayi ba, ta danna ni cikin mota data kasance ƙirar bus mai cin mutum goma.
Itama shiga tayi gami da zama, ba tare da ɓata lokaci ba tace ma dreban "Muje Malam"
Baiyi wata wata ba ya tada mota gami da danna ta da gudu muka bar cikin unguwar motar sai wata irin ƙara take saki.
Daidai lokacin ne ni kuma na haɗe kaina da guiwa ta gami da sakin wani irin kuka mai matuƙar cin rai....
*Ya Rab wannan wace irin Jarabawa ce take bibiyar rayuwa ta ni Suhan? Shikenan kuma nayi bankwana da cikar buri na, nayi bankwana da Ya Ameen, nayi bankwana da Afnan, nayi bankwana da Ya Bilal ɗin*
Ai bansan lokacin da na ƙara rushewa da kuka ba kaman raina zai fita a jikina....
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~31~*
Motar na ta faman sharara gudu da burari irin na babbar mota, yayin da ni kuma kukana yake daɗa lunkuwa, tin inayi da dukkanin ƙarfi na har muryar ta dusashe na koma share kwalla kawai, idanu na kuwa sunyi luhu luhu sai faman raɗaɗi suke yi mani.
Ummata bata ko kula ni ba, sai ma faman sakin tsoki take yi a hankali a hankali, kaman yanda shima dreban ya dage sai bama mota wuta yake yi.
A hankali gari ya soma wayewa, rana ta soma hudowa ta gabas, har wajajen ƙarfe takwas Nidai ina nan dunƙule a kujerar tsakiya tinda ta cen baya an cika ta da kayanmu.
Ban aune ba naji an jefo mani leda gami da robar nutri milk, tini dama muna dasu a ɗaki, tinda aka fara hidimar biki Hajiya Zainab taba ummata su da yawa, to da yake ba wani sha mukeyi ba, har ma gara ni domin ummata ko sau ɗaya bata kashi a bakin ta ba.
Na san shine yau ta fiddo mani, bredi ne a cikin ledar, tin da na buɗa na gani, na ajiye shi gefe ban kuma bi ta kanshi ba, dreban lokaci zuwa lokaci ya kan yi parking ya duba motar, yayin da har kusan ƙarfe uku muna tafiya, salla kawai muka tsaya yi.
Har yanzu ban ɗauki bredin naci ba, shi kau dreba saida ya siya shinkafa da wake ya afa lokacin da muka tsaya salla a wani ƙauye da bana ce ga sunan garin ba.
Itama ummata har yanzu ban ga ta sanya komai a bakin salatin ta ba, saidai lazumi da take ta faman yi ko kallon a ta ƙiyi.
Da naga ba sarki sai Allah ne bansan lokacin da na jawo ledar da gorar madarr ba na shiga kwankwaɗa, bata ko kula ni ba illa ma taɓe baki da tayi ta juya abun ta.
Ƙarfe takwas a cikin gidan tayi mashi, saida ya leƙa ya gaida hajiya sannan ya wuce sashen Alhajin domin gaida shi ya faɗa mashi yanzu zasu wuce makarantar ta su Suhan ɗin da yake kyautata zaton ma jirgi zasu bi domin su isa Kaduna daganan su wuce zariyn kai tsaye.
Addu'a yayi mashi da fatan dawowa lafiya, sannan yace suzo shi da yarinyar yana son ganinta.
Hakan tasa ya wuce kai tsaye sashen na su Suhan ɗin. A tsai tsaye ya tadda dukkanin ma'aikatan ana ta maida yanda aka yi, maree na gefe taja ta tsaya sai faman taɓe baki take yi tana ta faman jijji ga jiki murna fal a ranta har fuskar ta saida ta nuna.
Da ɗan sauri ya ƙara sa garesu yana tambayar su lafiya kuwa?
Gaida shi suka shiga faman yi, bai ko amsa ba domin hankalin shi ya matuƙar tashi, ga dai dukkanin ma'aikatan gidan mata Amman babu su Suhan ɗin.
Maida duban shi yayi ta ɓangaren da ɗakin namu yake, aiko ya hango shi haihan, babu ko tsinke ciki in ka ɗauke katifa da take jingine.
Da ƴar sassarfa ya isa wurin kaman zai tashi sama, lelleƙawa yayi ko ina sannan ya dawo inda suke tsaye, mamaki da tashin hankali kwance kan fuskar shi yake sake tambayar su ina suka je?
Mama talatin ce cikin halin ko in kula ta shiga cewa "wallahi yallaɓai muma bamu san ina suka je ba, haka muka tashi muka ga ɗakin, hasali ma ko fitar su bamu gani ba"
Cikin ɗaga murya ya dakatar da ita...
"Ne kike nufi da hakan mama? Ba kece shugabar su ba? Zasu fita ne ba da saninki ba? Anya ko kina yin aikin ki yadda ya dace?"
Bai ko jira amsar da zata bashi ba ya juya a sukwane ya bar sashen, kaman zai kife ya nufi bakin gate, domin dai babu yadda za'ayi ace sun fita mai gadi bai sani ba.
Ya kuwa ci sa'a duk mazan sun firfito sun fara aikinsu, tin daga nesa yake kwala ma maigadin kira, kaman zai tsuntsuwa ya isa inda yake zaune riƙe da radio a hannun shi ya karata a kunne yana ta faman saurare yana gƴaɗa kai.
Daga nesa ya jiyo muryar abokin mai gidan nasu yana ta faman kwala mashi kira gashi kuma yana nufi inda yake.
A hanzarce ya tashi gami da nufar inda ya hango Bilal ɗin na tahowa.
"Gani Yallaɓai, Allah dai yasa lafiya" ya faɗa yana mai isa ta inda Bilal ɗin yaja tunga ya tsaya.
"Ina su Suhan?"
Tambayar da ya jefa mashi kenan cikin hargagi da ɗaga murya.
"Yallaɓai wallahi tin asuba suka fita, ba yanda banyi dasu ba su tsaya, don ita Yarinyar ma kuka take yi lokacin da uwar tajata suka bar gidan domin....."
" *MMe?"
"Me kake faɗa ne haka da hankalin ka, me yasa kabarsu suka fita ba tare da sanin kowa ba, kasan aikin ka kuwa? Meyasa baka tada kowa ba ko kaje ka faɗa cikin gidan?"
Ganin yanda Bilal ɗin ya hayayyaƙo mashi kaman zai bigeshi ne ya sanya shi fara rantse rantse gami da zuƙunnawa ƙasa, daidai lokacin ne sauran ma'aikatan da matan duka suka firfito suka tsaya suna kallon ikon Allah
Bilhaƙƙi da gaskiya Bilal ɗin ke shrfa bala'i wa maigadin da mama talatun da yace duk basusan aikinsu ba, su ajiye aikin nasu domin bayada amfani.
Sai kaiwa da komowa yake yi daga wajen mai gadin zuwa inda mama talatun take tsaye kanta duƙe hankalin ta kuwa a matuƙar tashe taji ance ta ajiye aikinta.
Ƙarasowar Alhaji mustaphan ne ya dakatar da Bilal ɗin daga masifar da yake balbale su da ita.
Alhajin yayi matuƙar kyau cikin shadda fara dakakkiya anyi mata ɗinkin babbar riga da hula dara a kanshi, da alama dai fita yakeson yi, dama shi baya jiran dreba ya tuƙa shi, cewa yake yi ayyukan shi da hulɗoɗinshi na buƙatar sirri, ba ko ina bane idan zai je yake buƙatar a sani saboda insecurity na ƙasar tamu.
Tambayar Bilal ɗin yake yi me yake faruwa ya gansu cirko cirko haka tsaye, bayan shi yana cen yana fama jiran zuwan Bilal da Suhan ɗin da yace yana son gani.
Nan kuwa Bilal ɗin ya shiga zayyane mashi Abunda ke faruwa, idanun shi kuwa sun kaɗa sunyi jajur, ga dukkan alama ko ina su Suhan ɗin suka tafi basu da niyya ko alamar dawowa, shi ya ma zai ce ma Abokin nashi da ya bar mashi amanar su? Me yasa ya hana Al'ameen ɗin tahowa a jiya? Me ma ya sanya su barin gidan, bayan har yana murna ganin yanzu sun fara samun sauƙi a zaman gidan?
Shima Alhaji Hankalin shi ya matuƙar tashi, a karon farko a Rayuwar shi da yace a nuna mashi ɗakin nasu ya gani, Bilal ɗinne ya wuce gaba Alhajn na biye dashi a baya, cikin sauran ƴan aikin kuwa babu wanda yayi alamar motsawa ma balle ace su bisu, jikin su duk yayi sanyi, yau sunga tashin hankalin da basu taɓa gani ba, wai sauƙin ta ma ace Al'ameen ɗin bai nan da duk sunyi imani yau ƙarshen aikinsu yazo a gidan.
Hatta da maree ɗinma hankalin ta a matuƙar tashe yake, an sallami maman tata a nan take kuma? Saura ita in har asiri ya tonu na irin abubuwan da suke yi ma su Suhan ɗin.
Ta kuwa san maman tata sarai wajen shegen son kuɗin tsiya, yanzu idan taji sallamar ta tabbata zata tona masu asiri ne, hakan kuwa zai iya shafar nata aikin da take matuƙar so. Yanzu in tabar nan gidan ina zata dosa? Gashi dai tini ta san bata da mahaifi balle ace ta nufeshi hakan ta ta taso a rariya, sai daga baya ne data gano inda maman tata take shine fa tazo aka yi kutun kutun da aka sama mata aiki a gidan ba tare da kowa ya san alaƙar ta da mama talatun ba.
Mamakin Alhaji Mustaphan ya daɗa lunkuw ganin ɗakin ƙwalam babu komai ciki, gashi dai tsaftsaf kaman ba'a taɓa rayuwa ciki ba, cikin al'ajabi ya juya ga Bilal ɗin da yake ta faman leƙe-leƙe gani yake yi kaman fa zai hango su a wani saƙo na ɗakin laɓe.
"Ka kuwa kira layin su?"
Alhajin ya faɗa yana mai kallon Bilal ɗin da yafi kowa rikicewa, tsoron shi ɗaya kada abokin nashi yace saboda haka ne ma ya hana shi tahowa jiya daya buƙaci zuwan, tsoron shi ɗaya kada Al'ameen ya zarge shi akan shine dalilin shi na rabuwa da Abunda ya san yana so, kuma yake da burin taimaka masu, to ina alƙawalin da ya ɗaukar ma aminin nashi? Zai ce ya yaudare shi ne gashi ta dalilin shi sunbar gidan.
Tinanin haka da yayi ne ya sanya shi zaro wayar shi daga aljihu, hannun shi na karkarwa ya danna kira zuwa ga Layin Suhan ɗin, saidai fa not reachable ake daɗa faɗa, yana share zuba da take daɗa tsattsafo mashi yana sake kira, kaman ya kurma ihu haka yake ji, Rayuwar shi kaf ta gama ɓaci ayau, lallai mutanen nan biyu zasu bar gidan nan ayau muddin ba'a gano inda suka tafi ba, a ganin shi ai basu san aikinsu ba.
Alhajin ne daya kula da yanda hankalin Bilal ɗin ya tashi, kamo hannuwan shi yayi duka biyun yana kwantar mashi da hankali gami da gargaɗar shi kada a gaya ma kowa wannan maganar dake waje, ciki kuwa harda Al'ameen ɗin da tin safe ya kira shi a waya cewa lallai fa ayau ɗinnan zai taho domin jikin nashi yana bashi ba daɗi, Allah sarki bawan Allah, dama Alhajin koda shi Al'ameen ɗin ya faɗa mashi ba soyayya tsakanin su bai yarda ba, sai gashi kuma ta tabbata, so da kusancn da zuciyar shi take da tata ya sanya jikin shi yake gaya mashi lallai fa wani gagarumin abu zai faru ayau ɗin Shiyasa ya matsa da tahowar.
Hannun Bilal ɗin yaja yana faɗin yazo suje wajen hajiyar yaji ko tan ada masani yar barin gidan nasu Mama Maryam ɗin, domin shi fa jikin shi na bashi harda sa hannun Hajiya Kubran wajen tafiyar tasu. Domin yasan ko wacece matar tashi, in ta tsani abu, tau fa sai taga ta rabu dashi hankalin ta zai kwanta.
****************************
Wayar ta ce ta shiga burari alamar kira ya shigo, cikin barci ta sanya hannu da niyyar latse wa, saidai ganin mai kiran ne ya sanya ta tashi zaune sannan ta ɗaga.
Daga ɗaya ɓangaren aka yi ta magana, yayin da ita tayi shiru tana ta faman ɗaga kai, alamar gamsuwa da maganar da ake faɗa mata.
An kusa minti biyar ana maganar daga cen ɓangaren, lokaci guda Hajiya Kubran ta saki wata shu'umar dariya tana ɓaɓɓakewa da muguwar dariya cikin isa, har ta zuro ƙafafun ta daga bisa gadon gami da miƙewa ta nufi window ta zage labulayen da suke masu matuƙar kyau.
"Allah ya raka taki gona, kin biya ni Hajiya Sa'a, don haka ki saurari tukuicin ki zuwa anjima"
Abunda ta faɗa kenan ta datse kiran, hango Alhajin nata da tayi riƙe da hannun Bilal sun nuof sashen nata cikin sauri, wata shu'umar gajeriyar dariya ta saki tana mai sakin labulen ta koma gami da ɗaukar hular ta ta aza a kanta jikin ta sanye cikin lallausar farar doguwar riga ta barci, saidai bata kama jikin ta ba sosai.
Tana saukowa daga bisa benan suna isowa cikin falon, cikin salon Munafurci ta shiga tambayar Alhaji ko Lafiya?
"Kubra Inaso ne inji ina Su Maryama suka tafi ne? Don na san dai duk inda suka tafi da sanya hannunki ciki"
Alhajin ya faɗa yana jifan ta da wani irin kallon tuhuma idanun shi na a kanta ko ɗauke wa ba yayi.
Cikin ɗan firgici da son nuna bata san me ke faruwa ba ta shiga dafe ƙirji
"Alhaji ni kuma? To ina suka tafi? Wallahi bani da masaniya a cikin Al'amarin nan, ni fa tashina kenan yanzu"
"Yau ne aka tashi ba'a gansu ba, kuma banyi mamaki ba domin kinsha yin iƙirarin sai sun bar maki gidan ki, bayan kina manta wa cewa lokacin da zan gina gidan nan babu ko sisin ki a ciki"
"To fa Alhaji yau harda gori abun? To inaso ka sani ni bani da masaniya akan komai, tafiya kuwa sun daɗe basu tafi ba, ƙila gajiya sukayi ne Shiyasa suka cenza sheƙa, dama ai a haka muka gansu kwatsam sun zo mana, yanzun ma a haka kwatsam muka gansu sun tafi, menene na tada hankali a ciki? "
Da kallon mamaki ya shiga binta, shi kau Bilal da yake ta faman safa da marwa a cikin falon, bai san lokacin da ya matsa kusa da hajiyar ba yana faɗin
" Haba Mom? Kinsan kuwa irin alƙawalin da na ɗaukar ma Al'ameen? Nace zan kula dasu zan basu dukkanin Abunda suke buƙata, ba zan iya faɗa mashi cewa sun tafi ba yanzu, ki taimaka in kinsan inda suke ki kira su kice masu su dawo"
"Au dama ashe ƙarya yake yi mani bai rabu da yarinyar ba, ashe dama yaudara ta kukayi, me kuke shiryawa ne? Bilal ka fita a cikin idanun a fa in kulle tin wuri, dama kai ke zuga shi kana ɗaure mashi gindin Abunda yake yi, gashi kai kayi auren ka hankalin ka kwance da yarinyar da kake so ƴar gidan manya sai shine zaka so haɗa shi da wannan ƴar matsiyatan"
Cikin sauri Alhajin ya dakatar da ita, yayin da shi kuma Bilal ganin ba zai iya jure kalaman Hajiyar a kansu ba ya sanya shi juyawa da niyyar fita, dakatar dashi Alhajin yayi yana faɗin "ka jira mugama magana Bilal, zata kira su ne yanzu su dawo"
"Ni babu wanda zan kira, domin bansan a wace ma duniyar suke ciki ba, na ji daɗin faruwa hakan don haka suje cen su mallake ƴaƴan wasu Amman dai ba na Kubra bB, kuma inaso ku sani babu wanda zan kirawo ai kuna da waya a hannuwan ku duka"
Tana gama faɗar haka ta juya cikin isa zuwa ga upstairs ɗin domin komawa ɗakin nata, su kuwa da kallo suka bita galala, shi Alhajin ma mamaki yake yi yaushe Kubran tashi ta koma haka? Yasan halin ta duka, Amman bai san na ta tsaya tana fuskantar shi take faɗa mashi magana ba haka a gaban yaro.
Girgiza kai kawai Bilal keyi, yana binta da kallo, daf da zata shiga ɗakin nata ne wayar ta dake hannun ta riƙe ta hau ƙara, ganin Abie ne ya sanya ta ɗauka tana mai ƙara ta a kunnen ta.
***********************
Ba yanda Abie ɗin baiyi dashi ba na akan ya tsaya ya kai shi airport ɗin, tinda ya matsa lallai lallai yau sai yaje ƙasar tashi, ganin Abie ɗin zai ɓata mashi lokaci ne ya sanya shi cewa yabarshi kawai zai tau taxi, idan ya shirya kawai ya wuce office kai tsaye, shima ba wani daɗewa zai yi ba zai juyo.
Ba yanda ya iya, shi ɗin mai biyayya ga yayan nashi ne, saboda yawan jiɓintar Al'amarin shi da yake yi a kulli yaum, hakan ce ta sanya shi haƙura ya shiga shiryawar shi a tsanake bayan ya raka yayan nashi ya hau taxi ɗin.
Saidai ko minti ashirin baiyi ba da tafiya, wayar Bilal ɗin ta soma ruri, bai ɗaga ba har ta tsinke aka kuma kira domin lokacin yana sanya kaya ne, tankawa yayi a hankali da niyyar duba wanda ke kiran shi, Telephone ɗin landline ɗin ta ɗauki burari itama.
Fasa ɗaga wayar tashi yayi kuma ya juya ya nufi falon domin ɗaga kiran, saboda duk a zaton shi daga hotel ɗin da ake kawo masu abinci ne, niyyar shi ma yace su bar shi kawai domin ya riga ya shirya zai yi break fast ɗin a office.
Kafin ya isa ta katse kuma, ɗan tsoki yayi yana mai juyawa, daidai lokacin door bel ɗin gidan ta ɗauki ruri itama.
Cikin Al'ajabi ya juya ya nufi ƙofar yana faɗin what co-insidence is that?
Daidai lokacin da ya buɗe ƙofar, ɗan sanda ya gani tsaye sanye cikin kakin shi kalar na ƙasar american, gaisawa sukayi cikin turancn da ya riga ya zauna a halshen su, id card ɗinshi ya nuna mashi yana mai cewa ya biyo shi suje domin ɗan uwanshi ya samu accudent a hanyar shi ta zuwa airport ɗin, yanzu haka ma bai san wanene ke a kanshi ba.
Cikin tsanann firgita ya dafe kanshi, yana mai rugawa ɗaki ya ɗauko wayar tashi, ko kulle gidan ma bai tsaya yi ba, ya fito gami da bin bayan ɗan sandan yana ta salati.
Motar ƴan sandan suka shiga kai tsaye zuwa wajen, daidai isar su tayi daidai da isowar Ambulance ɗin, da gudu suka ɗauke shi gami da aza shi bisa ɗan gadon ɗaukar marasa lafiyar gami da tura shi zuwa cikin motar, Abie ɗin baiyi wata wata ba ya shige shima inda aka ajiye gadon yana riƙe da Hannuwan Al'ameen ɗin da yake kwance samɓal ko numfashi ba yayi, ya sake yin haske fayau idanun shi a kulle.
Jini ne yake ta zuba daga hancin shi da kunnuwan shi, hakan ce ta sake gigita Abie ɗin ya shiga rusa kuka rurus, bai ma san Abunda zai iya yi ba kuma, faɗi yakeyi
"Yaya ka tashi don Allah, kada ka tafi ka barni ni ɗaya Yaya, su wanene sukayi maka haka? Me kayi masu? Ina shi dreban yake yaya? Me ka aikata masu haka da suke neman Rayuwar ka?"
Baisan ma har sun isa ba asibitn, saida yaga an buɗe ana kiciniyar ɗaukar gadon, hakan ce ta sanya shi dirowa, shima ya shiga binsu da gudu yana riƙk hannuwan ɗan uwan nashi.
Tin a waje suka maƙala mashi robar shaƙar iska, ko ta kan Abie basu yi ba suma suna ta dalla gudu da keken har zuwa ɗaki da aka rubuta Emergency a jiki.
Daga bakin ƙofar ne suka dakatar da Abie ɗin suka shige suna mai rufo ƙofar, saidai da yake ƙofar ta glass ce yana hango yanda suke ƙoƙarin samo numfashin shi, jikin Abie ɗin kuwa ya ɓaki da jini sosai, saboda yada ya rinƙa rungumo Al'ameen ɗin a jikin shi lokacin da suna mota.
Zubewa yayi a wurin yana sakin gunjin kuka, da yake ƙasar ta turawa ce, babu ma mai kula dashi sai ɗaiɗaiku, ganin kukan ba zai fisshe shi bane ya sanya shi kiran Alhajin nasu, sai akaci sa'a shi kuma ya manto wayar tashi ɗaki da zai fito, sai kuma ya fito ya tadda Wancen tashin hankalin, hakan ce ta sanya Abie ɗin cenza akalar kiran zuwa ga Mom ɗin tasu.
********************
"Wat Abie, me kace? Yanzu ina Son ɗin yake? Kadai kace man ya mutu?" ta faɗa cikin matuƙar tashin hankali, a sukwane ta juyo zuwa ƙasan inda tabar su Alhaji Mustaphan da ɗinbin mamakin ta yanda ta rinƙa zuba masu ruwan rashin mutumci.
"Alhaji kaji Al'ameen yayi haɗari, yanzu ma yana asibiti Baisan inda kanshi yake ba" ta faɗa cikin tashin hankali, ruwan hawaye har sun fara ɗigowa a daman fuskar tata.
Zaburowa Bilal ɗin yayi yana faɗin
" WHAT? Me ke faruwa damu ne yau? Ina Friend ɗin yake yanzu?"
Girgiza mashi kai ta shiga yi bata ma san tana yi ba, hankalin ta a matuƙar tashe, miƙa ma Bilal ɗin wayar tayi, ya amsa yana mai tambayar Abie ɗin Abunda ke faruwa, shima ta cen ɓangaren cikin kuka ya zayyane ma Bilal ɗin Abunda ya faru, jin hakan da kuma kukan da Abie ɗin keyi yasan abun yayi worst cikin salati ya miƙa ma Alhaji wayar da yake tsaye baka ma gane Abunda ke kai kawo a ƙwaƙwalwar tashi.
Hannu ya sanya gami da amsar wayar, yayin da Bilal ɗin ya juya a sukwane ya bar sashen. A inda ya bar su nan ya tadda su, cewa yayi kowa ya koma bakin aikin shi har zuwa anjima idan komai ya lafa, jiki a matuƙar sanyaye suka juya zuwa bakin aikin nasu, bama kaman mama talatun da zata iya kintatar dalilin da yasa su Suhan ɗin barin gidan.
Kai tsaye ticket yaje ya yankar masu, ya kuwa ci sa'a ƙarfe 11 jirgi zai tashi, don haka uku ya yanka harda Alhajin da Hajiya Kubran sannan ya juyo zuwa gidan shi, domin faɗa ma ummin Abunda yake wakana.
"Hajiya kiyi mani shiru hakanan da kukan nan naki fisabilillahi, da wanne kike so inji ne? Da ciwon yaron ko da ɓatar wannan matar. Iye"
Alhaji mustaphan dake zaune dage da kai ya ɗago yana mai kallon matar tashi da take ta safa da marwa tana fama rusa kuka.
"Ya za'ayi kace inyi shiru? In yarona ya mutu fa? Ko don kai baka son shi ne yasa baka san zafin shi ba?"
"Eh bana son shi ɗin, ke ai son da kike mashi ne ya sanya gashi nan nagani kina son sa bauta mashi rayuwa, duk Abunda yake so ke bakya son shi, su waɗancen da kikayi sanadin barin su gidan su ba mutane baneba ko. Wallahi Kubra kiji tsoron Allah, gabaki ɗaya yanzu kina neman canza hali, kina neman ki nuna baki jin magana ta ko? Na san irin matakin da zan ɗauka akanki wallahi, kuma abun ba zai yi maki da daɗi ba"
Suna cikin haka ne Bilal ɗin ya kira wayar ta hajiyar yake shaida mata su shirya an samu jirgin sha ɗaya, zasu tafi su dubo jikin na Al'ameen, tana jin haka kuwa ta juya gami da hayewa sama tana faɗin
"Duk fa Abunda zaka yi Alhaji wallahi ko a jikina, yaro na kawai nake so a bar mani kayana, muddin ina raye bashi ba waccen kilakin mai mallaka ma maza jikin ta"
Da fatan shiriya ya biya yana mai miƙewa ya fice daga sashen nata, zuciyar shi a cunkushe shi ya ma kasa gane daga inda zai fara neman waɗannan bayin Allah.
************************
Bansan sunan garin da muka dosa ba, kawai dai naga har ƙarfe shida na yamma muna ta faman tafiya a mota, tin ina ƙorafin kuka na har na gaji na dena.
Gashi umman tawa ta ƙi koda kula ni ne ma, saidai ta siya mana abinci munci a wani gari da muka tsaya da bazan iya cewa ga sunan garin ba, duk da dai cewa babban gari ne.
Duhu yayi lokacin da naga mun doshi wani ɗan ƙauye marar girma haka, na kula ma kaman bukkoki ne a cikin shi.
Jikin wani ruɓaɓɓen guda naga munja mun tsaya, hamdala Naji umman tawa nayi, hakan ce ta sanya na gane mun iso kenan, fitowa mukayi mu duk kanmu, dreban na sakin wata uwar miƙa gami da hamma.
Sauke mana kayanmu ya shiga yi, da yake ba wani yawa ne dasu ba, duk ƙulluka ma sunfi yawa a kayan.
Ummata ce Naji tana cewa ya kamata dai ya tsaya ya kwana dare ya fara rufawa, ce mata yayi a'a ta sallameshi kawai ya wuce.
Kuɗi da bazan iya faɗar yawan su ba ta ƙirga gami da bashi yanƙilga yaga sun cika cif cif yanda sukayi da ita, juyawa yayi gami da shiga motar bayan yayi mata godiya yaja motar shi yayi gaba.
Nimau saboda tsabar gajiya takalmi na na cire gami da zama bisan su, yayin da umman tawa take tsaye riƙe da ƙugunta da na fahimci ga dukkan alamu ya ƙage mata ne.
Juyawa tayi gami da shiga cikin gidan a hankali ba tare daya ce mani komai ba, ganin hakan ne ya sanya ban ko yi yunƙurin binta ba, na dai san duk wuya ba zata barmu mu kwana anan ba.
Gashi waya ta ta ɗauke tin muna mota, da na kuka ma babu service a hanyar bare inyi yunƙurin kira wani.
Sallama ta shiga kwaɗawa, gada cen cikin ɗaki na bukka aka amsa mata, wata dattijuwa ce ta fito riƙe da Aci balbal tana ta fama karewa da hannu kada iskan sanyin da akeyi ya kashe wutar.
"Wacece?" ta faɗa daga bakin ƙofar ɗakin d ataja ta toge.
Ba tare da umman tawa tace mata komai ba, ta shiga matsawa kusa da inda take tsaye sannan ta buɗe baki a hankali ta shiga faɗin
"Nice Hajjo"
Jin matar ta kira suna ta, gashi kuma bata ɗauki murya ba ya sanya ta matso wa, ko ba komai dai tinda taji an ambaci sunan ta, to ta san ba mai cutar da ita bace.
Salati ta saka lokacin da tayi arba da fuskar umman tawa, ai tini ta yarda acibalbal ɗin gami da artawa a na kare zuwa cikin ɗakin tana ƙwala kiran
"Malam fito Kaga fatalwar Maryam"
Cikin hanzari ya miƙe yana faɗin "Ke Hajjo bana son shirme da shiririta, ina kika baro fitilar ne kin barmu a duhu?" ya faɗa yana laluben inda yaji hajjon na zunduma ihu gami da faɗa wa cikin shirgi.
"Wallahi malam itace, ita ce malam kuma je ka gani, wayyo Allah na Maryama me nayi maki haka ne?"
Malam ɗin baibi ta kanta ba ya nufi inda suke ajiye ashana cikin laluba ya ɗauka gami da dosar ƙofar fita yana faɗin
"Yau Naji sakar ci, wace Maryamar kuma banda wadda muka binne da hannuwan mu, shekaru da dama?"
A bakin ƙofar ɗakin ta inda yake jiyo warin kalanzir ɗin ya zuƙunna gami da lalubo ƴar fitilar sannan ya koma cikin ɗakin nasu ya sake kunna wa, yana miyar ta sakar masu fitila wajen sakar ci duk ƙasa ta ɓata lagwanin da ya murza ba jimawa.
Duk abun nan fa da akeyi, umman tana tsaye tana kallon shi, hawaye tuni ya jiƙe mata fuska, nima dai da nake tsaye ta jikin ƙofar gidan ina iya hango Abunda akeyi cikin gidan, kaina ne ya sake ƙullewa, hango umman tawa nayi ta sake matsawa jikin ɗakin nasu tana mai sake yin sallama lokaci guda tana faɗin
"Nice Malam, da gaske Hajjo keyi, nice Maryamar Muhammadu"
Jin kalaman dake fitowa daga waje ne, ya sanya shima jinin shi ya tsinke ya fara gudu, lokaci guda ƴan cikin shi suka fara yamutsawa, kaman zawo ma yake ji, saidai yayi ta maza yana cewa
"Kiyi ma Allah Maryama ki tafi abunki, i ma fansa kika zo ɗauka wallahi ba nan ya kamata kizo ba, bamu da hannu ko alhakin ki a kanmu ko ɗaya"
Ya faɗi hakan ne, sanin da yayi cewa da hannuwan shi suka birne Maryamar da ɗiyar ta, yanzu kuma ta yaya za'a kuma zuwa ace mashi Maryama ce?
Ganin ba zasu yarda da ita bane, ya sanya ta ɗaga labulen kai tsaye ta shige cikin ɗakin, a sukwane nima na biye bayan ta, domin ganin yanda zata kaya a cikin ɗakin
To me kalaman su ke nufi ne? Me suke nufi da kiran umman tawa fatawa?
Basu yi aune ba saidai suka ganta tsulum cikin ɗakin,
"Malam ka kalle ni da kyau, nice Maryama, bamu mutu ba ni da yarinya ta Hauwau gata cen waje ma"
Cikin salati ya buɗe idanun shi yana mai sake ƙullewa, addu'a yake yi ace mafarki yake yi, domin shi fa bazai taɓa lamunta da wannan al'amari ba.
Ita ɗin daice tsaye a gaban shi, gashi dama shi cen baiyi imani da akwai fatawa ba a zahiri, matsowa ya shiga yi kusa da ita, duk da jikin shi har yanzu karkarwa yake yi, hannuwan shi riƙe da fitila yana mai haske ma umman tawa fuska.
Lokaci guda ya saki wani ƙaton salati yana faɗin
" *ikon Allah sai kallo, shin Maryama kece da gaske?, ina ita Hauwa'un?*"
_A yiman uziri, wallahi wasu ayyuka ne suka taso man masu yawa, ina barar addu'ar ku_
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~32~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Cikin sa'a kuwa lokacin da suka isa har dare ya rufa, duk da haka har yanzu Hajiya Kubra bata bar kuka ba, Bilal ɗinne ke bata baki, domin shi dama Alhaji Mustaphn cewa yayi suje zai taho daga baya sai ya tsaya ya bada cigiyar su Suhan ɗin.
Aiko suna isa asibitin suka hango Abie zaune bisa kujerar silver ya haɗe kanshi cikin ƙafafun shi, duk isar nan ta hajiya Kubra sai gata tana gudu zuwa ga Abie ɗin, koda ta ƙara sa ba tayi wata wata ba ta ɗago yaron nata ta rungume tana mai sakin kuka da tambayar inda mafi soyuwa a cikin yaran nata yake.
Da hannu kawai ya iya nuna mata ɗakin da yake kulle, saidai zaka iya hango komai ta fari tar ɗin glass ɗin da aka zagaye ɗakin dashi.
Da hanzarin ta ta saki Abie ɗin tana mai wucewa kaman zata faɗi zuwa jikin glass ɗin, da dukkanin hannuwan ta ta sanya ta dafe glass ɗin tana mai sakin wani tsumammen kuka, hango yaron nata da tayi samɓal, an jojjona mashi wasu na'urori wuyan shi ɗaure da wani abu kaman dai ya samu matsala a wuyan nashi, jikin shi suna sanye ne da bulan yadi, kwance yake samɓal, hatta da hancin shi toshe yake da abun shaƙar iska.
Bilal ma da yake tsaye ta gefen ta, hawaye ne suke ta zurarowa daga ƙwarin idanun shi, hnakalin shi a matuƙar tashe, saidai ya sanya hanky yana sharar kwallar lokaci guda yana jan majina.
Abie ɗinne ya matso yana mai janye mahaifiyar tashi jin ta fara surutai marasa ma'ana, baya so yaji tana ba yayan nashi guda ɗaya tal mutuwa, yafi so ta bishi da addu'a.
Bilal har yanzu bai bar bakin glass ɗin a, yana tsaye hannayen shi soke cikin Aljihu, Alhaji Mustaphan ya kira wayar shi yana tambayar shi jikin Moh'd ɗin.
Sanar dashi kome ake ciki yayi, sun ɗan tattauna kaɗan Bilal ɗin ya nemi da alhakin yayi haƙuri zai kira shi anjima, hango wasu Police su uku da yayi suna nufo ta inda suke.
Suma bakin glass ɗin suka tsaya suna ɗan nazari haka kaɗan, sai kuma suka juya suka ba Bilal ɗin hannu, ganin haka ne ya sanya Mom ɗin tasowa ita da Abie.
Cewa sukayi idan ba zasu damu ba suna so a basu mutum ɗaya zasu je dashi office domin akwai ƴan binciken da suke so zasuyi.
Ba damuwa Bilal ɗin yace masu yana mai ƙoƙarin bin bayan su ne likitan ya ƙara so, shima hannu suka sha dashi suna mai bashi umurnin ya buɗe masu ɗakin zasu yi wani ɗan bincike.
Bawata gaddama likitan da yake farar fata ya shiga buɗe masu ƙofar, shiga sukayi suna ƴan dube duben su da kuma ɗauke ɗauken hotunan su, sannan suka buƙaci likitan da yayi masu ɗan ƙarin bayani dangane da ciwon na Al'ameen ɗin.
Nan ma ba gaddama ya shiga masu ƴan bayanai, duk abun nan da akeyi billa da su Mom ɗin suna cen waje suna hangen su, bayan kammalawar su ne, suka fito tare da cewa bilal ɗin ya biyo su suje.
Bayan sun isa ne suka shiga yi mashi bayanin accident ɗin da yanda ya faru da kuma kyautata zaton da sukayi cewa lallai da sa hannun wasu akaso aga bayan Al'ameen ɗin, domin dukkan abubuwan da akeyi camera ta sirri cctv tana naɗar komai, tin daga zuwan motar zata gitta har zuwa lokacin da suka ga motar ta tsaya dreban ya fito yana dudduba motar alamar matsala ta samu, da lokacin da Al'ameen ɗin ya fito daga motar yaja gefe ya tsaya, sai suka ga dreban ya matsa kusa da Al'ameen ɗin ya mashi magana, sai kuma suka ga Al'ameen ɗin na gyaɗa mashi kai yana mai duba agogon da take ɗaure wutsiyar hannun shi ƴar traveling bag ɗinshi na a hannu.
Ba suyi aune ba sai suka ga mai motar na tsaida wata taxi dreban ya fito suna magana, shi dai Al'ameen na tsaye gefe yana ta famn duba agogo, sai suka ga wannan mai taxi ya ɗaura igiya yaja taxi ɗin da Al'ameen ɗin ke ciki, sai kuma camera ta ɗauke ɗif, lokaci guda kuma ta kawo biji biji haka sai kuma ta koma normal, to fa a lokacin ne suka hango wata mota tayi sama sama da Al'ameen ɗin ta tsere, ko numb ta ba'a gani yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya faɗi ƙasa yana murmula sosai, jini duk ya wanke mashi jiki.
Salati bilal ɗin ya saki, yana mai miƙewa tsaye hannayen shi goye a bayan shi. Bai a san yana kaiwa da komowa ba, har saida ƴan sandan suka buƙaci da ya zauna.
Zama yayi yana mai sauraren su, lips ɗinshi cikin bakin shi, domin kanshi ya riga ya kulle, bai ma san wane kalar tunani zai yi ba kuma.
Nna suka buƙaci da ya sanya hannu akan binciken da suke yi, sannan ya basu haɗin kai duk lokacin da zasu buƙata gami da ƙoƙarin lalubo su victims ɗin, sannan ba zasu iya kammala bincike ba har sai Al'ameen ya farfaɗo sun ji daga bakin shi.
Haka ya koma asibitin wurin da su Mom ɗin suke, nan dai ya sake iske su, duk da dare yayi Amman likitocin sun hana su shiga, saida suka ga lallai lallai anan zasu kwana ne ya sanya suka basu ɗakin kusa da na Al'ameen ɗin da yake empty saidai zasu iya hango dukkan Abunda ke wakana a cikin ɗakin.
To koda dai suka shiga ma kasa taɓukabkomai sukayi, yayin da bilal ɗin har yanzu hankalin shi a tashe, to wanene ke son ganin bayan aminin nashi a ƙasar ta amurka da take ba baƙuwar su ba?
Mom ma saida ta tambaye shi, bai ɓoye mata komai ba, ya zayyana mata dukkan Abunda ke faruwa, wani kukan ta saki, tana mai tsine ma dukkanin mai hannu acikin son salwanta mata Rayuwar yaro
(Hmmmmmmm)
*****************************
Atare da umman tawa suka rankayo har ƙofar gidan da nake tsaye, da yake tin lokacin da naji suna shirin fitowa na ruga da gudu cikin sanɗa na fice a gidan.
A tsayn suka tadda ni, har yanzun ba wai malam ɗin ya gama yadda bane, haske ni yayi da acibalbal ɗin da take saura ƙiris ta mutu saboda iska da hunturun sanyi.
Ƙure ni yayi da ido, shi dai a gaskiya ba zai iya sheda ni ba, Maryamar kawai zai iya ganewa shima kuma ƴar kamar ce da kuma muryar, sai kuma hasken da take ɗauke dashi har yanzu, Amman gashi girma ya kama ta, ba kaman da da take ƴar matashiya ba.
"Yarinya zo mu shiga gida kinji? Nan akwai sanyi sosai" cewar malam ɗin da yake ta ƙoƙarin sai yaga fuska ta cikin ɗan hasken farin watan daya hudo, da yake tini ƴar acibalbal ɗin ta idasa mutuwa.
"Kayanmu fa baba?" na faɗa ina mai zuƙunnawa na kinkimi ƴar gana mustgo ɗin da kayan sawar mu yake ciki.
"Eh fa hakane, tau ku kwaso mu shiga daga ciki, akwai sanyi nan ba mun tsaya nan ba, banda haka ma yanzu masu farauta zasu fito, kuma akwai matsala idan suka gammu nan"
Ya faɗa yana mai zuƙunnawa shima ya ɗauki wani ƙaton ƙwali da kayan provision ɗina na makaranta suke ciki.
Jin hakan ne ya sanya jikin mu fara ɓari, tsoro ya kama zuciyar mu, da sauri muka shiga jifar kayan har zuwa cikin gidan, saida muka kwashe tas ne sannan ya maida ƴar ƙofar wacce aka yi da zallan kara da itatuwa ya saya gidan.
Tsakar gida muke tsaye, hakan ya bani damar ƙare ma gidan kallo, ƴan ɗakuna ne guda uku kaman rumbu, sai madafa da take gefe guda da bayan gidan da idan kana wanka ka miƙe tsaf za'a hango rabin jikinka.
Shi kau Malam wucewa yayi zuwa ɗakin yana faɗin "Hajjo fito ki buɗe masu wanga ɗakin da yake haka su sanya kayansu, duk da yayi ƙura a kakkaɓe shi a haka zuwa wayewar gari, bari in kaɗa masu lagwani suga haske"
Fitowa tayi tana faɗin. "To malam" Amman fa har yanzu ɗari ɗari take yi damu, ƴar dattijuwa ce itama don zata fi ummata da kaɗan amman, wucewa tayi kai tsaye zuwa ɗakin da yake gefen nasu ta fara kiciniyar buɗe shi, ga dukkan alama ma ana jimawa ba tare da buɗe ɗakin ba.
Ƴar fitilar acibalbal ɗin da ta sake kunna wa da ita tayi amfani wajen buɗe ɗakin da haska shi, duk da ba wani haske ne ya wadata ba, ga dukkan amu ma dai basa da wata fitila da tafi wannan Aci balbal ɗin.
Kayanmu muka fara kwasa muna kaiwa zuwa cikin ɗakin da sai mun duƙa zamu iya shiga, masalan ma ni da nake da ɗan tsawo.
Har yanzu dai bata tanka mana ba, da gani dai a tsorace take damu.
Ɗakin kam yayi ƙura, a haka ta koma ta ɗauko mana tsintsiya ta kakkaɓe mana muna tsaye gefe ni da ummata da har yanzu bata wani kula ni.
Ƴar yalolon tabarmar kaba ce shimfiɗe a ɗakin dagani dai ana nufin a bisa ita zamu kwana, gashi ba wani girman kirki ne da ita ba, sai ɗan yalolon filon da ta shigo mana dashi guda ɗaya a hannun ta riƙe da ƙwarya mai kyau da fura ciki wadda tasha nono kindirmo.
Zama mukayi muna bismilla, cikin mu ma babu wanda yabi ta kan furar, daf da zata fita ne ummata tace mata "Hajjo muna so muyi salla ne"
Da to tabi umman tawa tana fita, bata daɗe ba ta miƙo mana ƙatuwar buta ta tasa cike da ruwa, amsa umman tawa tayi tana mai ficewa daga ɗakin.
Zurut na tashi ina mai biye bayan ta, domin Nidai harga Allah tsoro nake ji, bata ko kalle ni ba, da yake ta san kan yanda gidan yake bayan ɗakin kawai ta nufa ta kamo ruwa gami da fitowa ta ɗaura Alwala, bayan ta gama ne ta miƙa man da niyyar nima inyi.
Amsa nayi ina mai cewa "Umma Don Allah ki jiran in gama, wallahi tsoro nakeji" bata ceman ƙala ba sai ma ja da tayi gefe ta tsaya tana mai bin ko ina na gidan da kallo da dukkan alamu dai tana fahimtar ba'a samu kowanne sauyi ba acikin gidan illa ma ƙara ruɓewa da gidan yayi.
Koda na shiga bayin, rasa inda zan zuƙunna inyi fitsarin nayi, domin ko ina ƙasa ce kwance, a haka dai na samu na raɓa nahau wani shimfiɗaɗɗen dutsi mai ɗan tudu da aga alamar wanda ake zama ne bisa in za'ayi wanka.
A kanshi na hau na tsula fitsari na, na gama na fito tare da ɗaura Alwalar sannan muka ranka ya zuwa cikin ɗakin.
Har muka gama salla babu wanda ya kuma shigowa, ganin hakan da mukayi ne ya sanya muka gane ba zasu dawo ba, sakaya ɗakin mukayi saboda sauro gashi babu maganin sauro, mu kuma namu dake cikin kaya yana cen ƙasa bama mu san ta inda zamu fara neman shi ba.
Hakanan dai muke zaune, cikin mu babu wanda yake da niyyar kwanciya, ganin hakane umman tawa ta miƙe gami da zaro wani zaninta cikin Ghana must Go ɗin tamu ta shinfiɗa mani gami da cewa idan ba zan sha furar ba in kwanta in huta.
Allah sarki mahaifiya, duk duniya babu yake, haka nan kasa kwanciya, itama ta kasa kwanciya, tana ta ƙare ma ɗakin kallo.
Cen kaman an buɗe mata baki an zaro maganar Naji tace
" *Anan fa aka Haifeki* "
Ai bansan na zabura ba na tashi tsaye, har saida Naji tace "to miye na tashi tsaye? Ni kar ku faɗo mani"
Sannan ne fa na koma na zauna, tinani fal cikin raina da tarin tambayoyi.
Ban ce mata ƙala ba, sanin halin ta da nayi, yanzu ina iya tambayar ta cibi ya zama ƙari, koma ta fasa faɗa man Abunda tayi niyya.
An kusa awa bata ƙara ceman komai ba, sai nice nayi shahadar fitowa in mata maganar karatuna ganin mun samu lokaci mu da ita.
"Umma ya maganar makaranta ta? Ki taimaka mani umma kada wannan damar ta kucce mani, bani da kowa sai Allah sai kuma ke, wannan karatun da zanyi zai taimaki Rayuwar mu ya tallamu ta ni dake baki ɗaya"
Shiru tayi tana mai nazarn kalaman nawa, cikin tausaya wa irin na uwa ta buɗe bakin ta ta shiga cewa
"Mamana, nice nan na yarda kiyi karatu, saidai kuma yanzu bana buƙatar karatun ki a waccen makarantar da suka sanya ki, dukkan Abunda ya shafe su ma bana buƙatar shi atare damu, kuma inaso kiyi mani Alfarma da alƙawalin cewa zaki manta dasu duk kansu, kuma ki binne labarin su da babinsu a Rayuwar ki"
Gabana ne ya tsananta bugu, me umma ke nufi, Amman dai koma minene tinda Naji tace zata barni inyi, ai ina tinanin zai zo mani da sauƙi
"To umma hidimar karatun fa waye zai yi mani? Kada ki manta fa, nan ba aiki mukeyi ba, ba kuma albashi ake bamu ba, umma Meyasa kika zaɓi mu baro cen gidan dukkan irin muzguna mana da akeyi, kika zaɓi muzo nan muyi Rayuwar mu?"
Na faɗa ina mai saddar da kaina ƙasa domin bansan da irin ɗauka da fassarar da zata yi ma maganar ba.
" Hauwa'u ke yarinya ce har yanzu, ba zaki gane ba, ba zaki fahimta ba, Hajiya Kubra bata da zuciyar imani, ta sanya su Hajiya Sa'a suyi dukkan yanda zasuyi mubar gidan nan, har Rayuwar mu ma zata iya Sanyawa a hallaka saboda tana tunanin ke ɗinnan zaki mallake mata yaro ne, a yayin da take kallon shi ɗin yafi ƙarfin ki ba sa'an yinki bane, ni kuma na kwammace mu bar gidan tin kafin mu nemi rasa Rayuwar mu a karo na barkatai, ki bar maganar su, dasu da Abunda ya shafe su gabaki ɗaya yanzu bana son maganar su, Alkhairin da Alhaji da Shi Ameenullahin yayi mana Mungode Allah ya saka, Amman bana kyautata zaton akwai Abunda zai ƙara haɗa mu dasu"
Tinda ta fara magana bata tsaya ba, haka kuma bani take kallo ba, hasali ma idanun ta a kulle suke gam, nikau da kwalla take shatata da zuraro mani sai faman ajiyar zuciya nake sauke wa,
Ban aune ba naji ta sake cewa
"Karatun ki Allah ne zai yi mana, Allah ne zai bamu iko da Abunda zakiyi karatun dashi, Mamana inaso ƙibar sanya ma ranki cewa dole sai dasu ne zamu iya, inaso ki sani su ɗin da Allah ya basu kuma ba zai manta damu ba, kiyi ta addu'a komai zai zo da sauƙi insha Allah, wannan halin da muke ciki zai zama tarihi da izinin wanda ya halicce mu"
"Ameen Umma"
Shi kaɗai ne Abunda bakina ya samu ya iya furta wa, duk kuwa da tarin kaman da suke cikin shi.
Kusan a haka muka kwana zaune, kowa da Abunda yake saƙawa, saidai daf da asuba ne wani nannauyan barci ya kwashe ni, cike da mafarkai masu ban tsoro kuma duk Al'ameen ne nake hangowa a ciki, koda na tashi na tadda har gari ya fara wayewa, sanin da ummata tayi cewa baccin na gajiya ne ya sanya bata tadani ba, ta bari idan na tashi nayi sallar.
****************** To kusan muce yanda su Suhan ɗin suka kwana zaune cikin ƙututun ɗaki, haka suma su Umman suka kwana, duk da ga gado ga Ac Amman hakan bisa ɗaya daga cikin su ya runtsa ba, gashi kuma Al'ameen ɗin fa har yanzu bai motsa ba, haka umma ta kwana a tsaye jikin glass, Allah ya isa dai Suhan tasha ta, domin ita a gani ta duk itace sila ko ince sanadin da ya sanya Al'ameen ɗin yabar ƙasar tashi, gashi yazo ya haɗu da mahassada masu neman ganin bayan shi, ai gara ma da ta tafi cen daga cen ayi cen insha Allahu ba dai yaron nata da wannan matsiyaciyar yarinyar ba ƴar matsiyata.
Saidai likitocibsu shiga su dudduba shi, gami da gyara mashi kwanciya su fita, Abunda ya ƙara ɗaga hankalin su shine ganin da sukayi wasu gungun likitocin kusan su biyar sun rugu a kanshi, dagani ma manyan likitocin ne da ba'a asibitin suke aiki ba kiran su aka yi.
Bayan sun gama ne suka fito su duka, fuskar su babu walwala suka ce su Mom ɗin su biyo bayan su zuwa office ɗin.
Hajiya Kubra ce da bilal ɗin suka bisu, yayin da aka bar abie nan zaune yana hango Al'ameen ɗin.
Bayanin komai sukayi masu, ai tini Hajiya Kubra ta rushe da kuka, tana cewa "wai ina Alhaji ne? Yazo yaji, yazo yaga yaron nan kada ya mutu, me ke damun Al'ameen haka da har ciwon zuciya ya kama shi har ta kumbura? Tunanin me yake yi haka? Me ya nema ya rasa? Bilal kira man alhajin kace don Allah yazo yaji Abunda likitocin nan ke faɗi.
Ai cikin hanzari shima jikin shi na rawa ya latsa number ɗin Alhajin, koda ya gaya mashi shima salati ya sanya yana mai cewa yana nan tahowa yau-yau ɗin nan kuwa insha Allahu, zai bar dukkanin Abunda yake yi yazo ya iske su a american.
Faɗa ma Mom ɗin yayi yanda sukayi da alhajin, taɓe baki tayi cikin kuka take faɗin
"ai ga irin ta nan, yaushe za'a ce maka yaron ka yana kwance rai hannun Allah kace sai ka tsaya neman wasu matsiyata marasa galihu cen, Rayuwar yaron namu batafi rayuwar su ba su duka?"
Runtse idanu bilal ɗin kawai yayi yana mai girgiza kai ya tashi ya fice daga office ɗin ma baki ɗaya, kalaman na hajiya kubra sun rasa shi, sun girgiza shi matuƙa, ko wannan kaɗai ya isa ya sanya Al'ameen ɗin ciwon zuciya, samun wannan irin uwa haka ai ba abun daɗin ne ba. Ganin yanda ranshi ma ya ɓaci ya sanya shi fita cen harabr asibitin ƙarƙashin wata bishiyar umbrella ya zauna yana mai nanata kalaman hajiyar a zuciya.
********************
Koko da ƙosai aka miƙo mana masu zafi, bamuyi ƙwaron baki ba muka sha, duk da ba wani sugan kirki ne a ciki ba, har yanzu dai tinda malam da Hajjo ɗin suka leƙo muka gaisa bamu sake ganin kowa ba, sai cen wajen ƙarfe goma ne a kintata ta, saboda waya ta ta ɗauke ba chaji, gashi kuma banga alamun wuta ba a ɗan tsukukun ƙauyen.
Ruwan wanka Hajjo ɗin tace in fito in ɗiba a cikin waccen tukunyar, irin ƙatuwar tukunyar nan ce ta ƙasa, hakan yasa na fiddo bokitin robar mu na wanka da soso da sabulu, sai dai fa da naje ɗibar ruwan na kai minti goma ina kallon ruwan nazari nake yi ta yaya ma mai rai zai iya wanka da waɗannan ruwan?
Hajjo da take tsaye daga cen ƙofar ɗakin ta ce ta ce mani. "Ki ɗiba mana, ko ba yanzu zakiyi wankan ba?"
Ban ƙasa a guiwa ba wajen juyawa nace mata "Mama waɗannan sune ruwan wankan?"
"Yo Eah mana sune, dasu mukeyin komai a nan ƙauyen mu, ko rijiya bamu da ita, sai rafi shima safko nayi naje na ɗebo, har girki dashi mukeyi, ke ko kokon da kika sha yau dashi na dama, ƙosan ne kawai aka siyo a cen bayan layi"
Baya naja da dukkanin sauri da ƙarfi na ina mai dafe ƙirji, cen kuma sai ga amai kwarara ya taho man, duƙawa nayi da sauri kada in ɓata jikina, ban tashi ba saida na amaye dukkanin abincin dake cikina, ɗan kokon da ƙosan kuwa sun dame babu kyau gani.
Nasha Wahala domin ni da kaina na dinga ƙaƙalo shi, bansan sanda hawayen wahala da tausayn kaina suka wanke mani fuska ba, ummata dake tsaye bakin ƙofa jin maganar mu da hajjon ne ya sanya ta fitowa.
A hankali ta tako har inda nake durƙushe ina mai idasa ƙaƙalo sauran kokon
"Kinga Mamana, dole fa zakiyi haƙuri, haka Rayuwar su take ciki anan ƙauyen, gwamnati ma bata san da zaman su ba duk tsawon wannan lokacin, in ma ta sani to babu Abunda take aiwatar masu, illa iyaka idan zaɓe ya tashi kiga annkawo rimfuna da sabullai ana raba masu su zaɓi wanda ya basu. Amman ruwa da wuta kam saidai in kin bar garin nan, ko ruwan rijiya basu dashi saboda suna kan tudu ne, ba'a samun damshi a ƙasan, haƙuri zakiyi ki daure har Allah ya iyakance, domin ko ɗazu ma dasu mukayi Alwalar salla, yanzun ma dasu zaki ɗauraye bakinki ki tashi hakanan ki ɗiba kiyi wankan"
Bansan lokacin da na kalle ta ba kwalla na zuraro mani, raina fa duk a dagule yake, mamadin inyi shiru sai a sake ɓarkewa da kuka da nayi, ashe cen inda muka baro muna cikin rahma ne, ashe bawa ya gode ma Allah a duk inda ya samu kanshi, hakan ma wata baiwar ce? Me yasa ya ummata jawo mu nan wurin? Me hakan ke nufi da rabo mu cikin rufin asirin mu? Duk da ada kallon muna cikin wahala mukeyi?
Sake dafa kfaɗa ta tayi cikin tausaya wa irin ta uwa, sannan ta shiga goge man hawayen tana mai cewa kinga maza ki ɗibi ruwa kije kiyi wanka kizo ki tafi makarantar taku ki gano ya zakuyi?"
Dasauri na kalle ta," Umma nan fa bansan sunan garin da muke ciki ba, bansan a wane state ma muke ba tukunna, tayaya ma zan gano hanyar da zata fidda ni daga nan surƙuƙin?
"Zaki ita Suhan, zaki iya, ke ɗin mai ƙoƙari ce akan Abunda kike so, akwai masu babura acen ƴar yara da zaki hau su fidda ki babban titi, sannan nan muna ƙauyen sunkui kenan dake cikin jihar Jigawa. (Na sanya sunan littafin ne gudun kada wasu suce na faɗo sunan ƙauyen su na aibata shi).
Ɗan murmushi nayi ina mai matsawa na ɗauko moɗar gami da zuba ruwan a cikin bokitin na wanke wurin duk da ƙasa ce, sannan na ɗauraye bakina ina yi ina runtse idanuna jin ruwan a bakina.
Sannan na zuba ruwan na shiga bayin, aiko bisa ɗan dutsen nan na haye nayi wankan, sannan har na gama ban miƙe ba, jikina kam sai ƙaiƙayi nake yi, ina zuwa ɗakin na tadda umma ta fiddo mani mantheletor na zafi wai in shafe dukkan jikina.
Haka kuwa aka yi ina shafawa Naji sauƙin ƙaiƙayin, haka umman tawa ta fice itama domin yin wankan, ina gamawa na sanya kaya na gami da shan nutri milk ɗin da umman ta ajiye mani da ragowar bredin jiya, aiko naji dam, duk da har yanzu zuciya ta tashi take yi kaman zan sake wani aman.
Saida nabari umman tawa ta gama wankan ne ta shirya ta sanya kaya, sannan nace mata zan wuce, kuɗi ta ɗauko masu ƴar dama ta bani tana mai cewa Allah ya kiyaye hanya, duk runtsi kada in bari dare yayi mani a hanya batare da na dawo ba, in kuma har ban gama ba da wuri in kwana a hostel ɗin da aka riga aka bamu Alabasshi gobe in yo sauko in dawo.
Da addu'a ta bini har ƙofar ɗakin, saida nayi ma Hajjo sallama da take zaune tana tsintar shinkafa ƴar hausa, itama cikin ƴar fara'a ta amsa mani, sannan na tambayeta kwatancen inda zai hau babur ɗin.
Wani yaro ta ƙwala ma kira da yake cen waje yana wasan ƙasa shi da ƙanen shi, dukkanin yaran jikin su gaja gaja yake da datti ga majina a hancin shi, saurin kauda kaina nayi, ina jin zuciya ta na sake tashi.
"Isa maza je ka raka wannan yayar taka ƴar yara ta hau babur ya fidda ta a hanya" da to ya bita ya ruga da gudu yana mai kaɗa ƴar tayar shi, sallama nayi masu nabi bayan yaron, yayin da umman tawa ta kai zaune bisa ƴar tabarmar kabar dake shimfiɗe ƙasa tana mai cewa "Hajjo kawo tsintar mana in tayaki"
Ba musu ta miƙa mata, sunayi suna cigaba da ƴar firar su ta yaushe gami, dagani dai yanzu ta ɗan saki jiki da umman tawa, jira kawai take yi mijin nata ya dawo daga cin kasuwa da yayi sammakon tafiya suji ta bakin Maryamar.
Nikau bamuyi wata tafiya mai nisa ba muka hango ƴar yarar, masu babur ukku ne rak a wurin kwance bisa machinan su suna ta fira, hango mu da sukayi ne ya sanya su zabura suka bukako mashin ɗin zuwa gabanmu suna cewa "Hajiya Tafiya ne?"
Ganin ɗaya daga cikin su ya fisu zaƙalƙalewa ya sanya sauran biyun haƙura suka koma suna ƙunƙuni, nikau ya juya man nahau ina mai cewa "bakin babban titi zaka fidda ni inda zan samu mota"
"To hajiya saidai fa akwai nisa, gashi hanyar bata da kyau yashi yayi yawa, sai kin riƙe mashin ɗin sosai"
Aiko na kama mashin ɗin na maƙalƙale ina mai juyawa nace ma yaron ya koma gida sai na dawo nagode
Yaron ya juya da gudu ba tare da ya jira wani ihisani daga gareni ba, saɓaninnyaran mu na yanzu ƴan cikin birni ko mun ƙanƙantar Abunda sukayi maki sai suyi maki ƙerere suna jiran ki basu kuɗi, Allah shi kyauta mana da wannan zamani.
Hanya muka ɗauka ɗoɗar, kusan tafiyar awa guda mukayi sannan muka fito bakin hanya, titi ne samɓal, nan na sauka ina mai ce mashi nawa ne?
"Jikka biyu" ya faɗa yana mai ɗaure fuska, banyi musu ba saidai na tambaye shi ƙarin bayani nawa ne jikka biyun da Hausa?
"To ai malama hausar nayi maki, saidai in baki gane ba sai ince ɗari huɗu kenan"
To nace mashi gami da ɗauko ɗari biyar na bashi, saidai bayada ko sisi a aljihun, cewa nayi ya bar shi kawai, godiya ya shiga zabga mani yana cewa "Allah ya kiyaye a dawo lafiya, ai bana tafi ba banga shigar ki mota ba hajiya"
Muna tsaye kuwa sai ga mota golf ta shararo da gudun tsiya, tsaida mani yayi na shiga ina faɗin sunan garin da zani.
Na kuwa ci sa'a suma cen suka nufa, mai mashin ɗinnan yana ta ɗaga mana hannu har muka ɓace ma ganin shi sannan ya juya, ga dukkan alamu dai yaji daɗin kuɗin nan da ya samu daga gareni.
*_Allah ka yafe mana kura kuranmu, ya sanya mu gama da duniya da iyayen mu lafiya Ameen_*
~Oum-Deedat ce~
[9/21, 12:27 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~33~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Ƙarfe uku daidai muka isa garin na Zaria, Nidai bana ce ga sunan garuruwan da muke ta wucewa ba, har Allah yayi mana isowa.
Muna sauka ne na gane inda zan dosa, mai a daidaita sahu na tare har zuwa cikin makarantar ina saɓe da ƴar jikka ta.
Bayan na sallame shi ne kai tsaye na wuce zuwa admin block na foculty ɗinmu, saidai abun da har yanzu yake ɗaure mani kai tin shigowa ta makarantar, ƴan tsirarun mutane ne suke ta kai komo, wasunsu kuma a zazzaune.
Saida na isa ne zuwa Office ɗin HOD ɗin namu ne na ganshi a kulle, kaina ya ƙara kulle wa, dole na juyo zuwa inda na hango wasu zaune ƙarƙashin bishiya, maza da mata ne zaune abun su suna ta fira da raha, duk da sun bani mamaki yanda suka saki jiki da waɗanda ba jinsin su ba, sallama nayi masu gami da tambayar su ko lafiya makarantar ba kowa har malaman?
Ƴar dariya suka saki, lokaci guda ɗaya daga cikin su ya fara bani amsa.
"Haba baiwar Allah, yanzu ke fisabilillahi duk yajin aikin da aka shiga baki sani ba? Hala ke sabuwar zuwa ce?"
Ya jefa man tambaya a ƙarshen maganar tashi, ban samu damar bashi amsa ba, saboda yanda Naji jikina yayi sanyi ko ƙafa ta ma nema take ta gaza ɗauka ta, gyaɗa mashi kai kawai na samu damar yi, sannan nace masu nagode.
Juyawa nayi a matuƙar gajiye, ga yunwa ga tashin hankalin komawa gida a yanzu, ga tashin hankalin ban samu Abunda nake so ba, ga kuma waya ta babu chagi.
A haka har na fito bakin gate duk tsawon tafiyar nan, na matuƙar galabaita jikina har ƴar kyarma yake yi.
Cen nesa kaɗan na hango mai ɗan shago yana saida provision da su lemuna, sai dougnut ɗana hango cikin bokiti. Da ɗan sauri na na isa ga inda yake zaune na fiddo kuɗi gami da cewa "A bani a haɗa mani da lemo."
Alfarma na roƙa wurin da yake zaune, akan ya tsira mani chaji na wayar ta ɗan kawo, duk da ba wai don in kira wani ba, aiko sai gashi kafin in gama cin dougnut ɗin da na shige hijab ina ta faman turawa, wayar ta samu kusan 20% da yake chargre ɗin tana da kyau.
Godiya nayi mashi gami da karɓa na wuce, shawara kawai nake yi ta yanda zan nemi komawa a yau ɗinnan gashi har la'asar tayi, kuma ban hango wurin da zanyi salla ba ma, dole a haka na nufi tasha, na tadda mota na lodi, a haka nima nabi su wurin zaman jiran sauran passingers ɗin bayan na gaya masu inda zani.
Saida dreban yace mani "Amman kinsan inda zaki cen cikin lungu ne ko? Saboda dole a hanya zamu sauke ki"
Ce mashi nayi na sani, a haka har motar ta cika muka ɗauki hanyar komawa gida.
***********************
Alhaji Mustapha sai cikin dare ya isa, har yanzu dai babu wani cigaba, duk da Bilal ya fita yayo masu take away ɗin abunda zasu ci, har yanzu babu wanda ya iya cin wani abu, saidai ruwa kawai da hajiya kubran ke kurɓa, idanun ta sunyi mata luhu luhu,ko buɗe su bata iya yi, ya zuwa yanzu kowa dake nigerian ya san da rashin lafiyar ta Al'ameen.
Isar shi ce tayi daidai da isar su Aunty Feener da Afnan, aiko suka dasa wani sabon kukan, duk da ba'a bari a shiga inda yake saidai suna hango shi ta cikin glass, duk da yanda Alhajn ke lallashin su Akan suyi shiru, kasawa sukayi, gani suke kaman sunyi bankwana da ɗan uwan nasu ne.
Tini dai Alhaji Mustaphan ya nemi da a cenza mashi asibiti mai zaman kanta inda mafi ƙwarewar likitocin suke, ba musu kasancewar sunsan yadda su Alhajn suke a ƙasar ta amurkan.
Asibiti mai kyau da tsaruwa aka maida shi, nan ɗinma kimlace shi aka sake yi wuri na musamman, saidai yanzu kam basa iya hango ta inda ma yake kwance, har yanzu bai san wake kanshi ba, hakan ya ƙara tada hankalin Hajiyna, gani take yi kaman za'a fito ace mata ya mutu, shi kau Alhaji Mustapha bai ma bi ta kan hajiyar ba, saidai afnan da take maƙalƙale dashi tana kuka, sai faman lallashinta yake yi.
Da yake an basu ɗaki na musamman akace suyi amfani dashi, duk da asibitn ba'a zaman jinya, saidai Alfarmar Alhaji Mustaphan da ya daɗe cikin ƙasar ya sanya aka basu, a haka suka kwana zaune, Bilal ne kawai ya tafi gida ganin Alhajn ya iso ga kuma su Aunty Feenar.
Tin da safe washegari sai ga Saudat da Nihal gabaki ɗayansu da mazajen su, ai fa nan sani sabon babin kukan ya buɗe, Alhaji Mustaphan har ya gaji da lallashinsu ya sanya masu idanu.
Ya san dole suyi kuka, Al'ameen ɗin ɗan uwa ne nagari, duk da kasancewar shi ba mai yawan fara'a ba ko shiga hidimar mutun, shi ɗin mai tausayi ne, mai jin ƙan na ƙasa dashi ne. Ana haka sai ga kira daga mataimakin shugaban ƙasa da sauran sarakunan sun zo ganin Al'ameen ɗin.
Kusan muce tare suka isa da Alhaji Auwalu da kaka zuwairan da ta tada rigima sai an taho da ita, haka ba yanda ya iya dole ya tattago ta tazo taga jikin jikan nata, yayin da ta baro ɗan tsoho isuhun nata a gida.
To su ɗin dai an bar su sun shiga, saboda a ranar suke so zasu juya, banda su Alhaji Auwalun da zasu zauna a nan har sai Abunda hali ya nuna.
Su kansu sun girgiza da yanda suka ga jikin Al'ameen ɗin, kaka zuwairan kam kuka ta sanya tana faɗin "su wanene sukayi maka haka Muhammadu?"
Saida aka fidda ta waje, saboda ba'a son hayaniya a kusa dashi, sun mashi Addu'a tare da bada saƙon gaisuwa da dubiya ta shugaban ƙasar, sannan suka juya suka tafi. Yayin da Bilal da Abie suka raka su har airport cikin tasu motar.
Zuwa yanzu dai kam, kowa ya sare da Al'amarin Yariman Matasan Arewan, su kansu likitocin sunyi mamakin da har yanzu bai farfaɗo ba, duk da sun dudduba gabaki ɗaya raunukan dake jikin shi sun fara warkewa, kuma komai nashi ya koma normal kawai bugawar zuciyar tashi ake so ta koma Normal.
Ya zuwa yanzu dai sai zaman jigum-jigum, daƙyar aka lallaɓa su Aunty Feenar ɗin suka tarkata suka tafi gida, Amman kuma tin da farar safiya suke dawowa su dasa zaman jiran tsammani.
A yanzu dai kam, su Nihal ɗin sun sheda Allah ɗaya ne, sun gane rai ba'a bakin komai yake ba, Amman har ya zuwa yanzu a hakan Allah bai basu ikon barin halin nasu na jin kai ba, wannan kuma sai Allah ya yaye.
Ƙawayen Hajiya Kubran ma da dangin ta na ɓangaren Mahaifiyarta duk sun zo, saidai suma jiki a sanyaye suka koma zuwa ƙasar tasu, inda Nigeria ta ɗauki addu'a daga bakunan mutane da dama akan Allah yaba shugaban Matasan nasu lafiya, masallatai makarantu da coci-coci ko ina addu'a kawai ake ta faman yi, saboda su kansu sunsan in suka rasa Al'ameen ɗin ba ƙaramin rashi sukayi ba.
**********************
Mun sha tafiya a hanya kam, har duhu yayi magariba ta soma kawo kai, a daidai lokacin ne kuma motar mu ta soma bamu matsala, hankali na fa ba'a kwance yake ba, nafi tunanin in ma yanzu aka sauke ni, to ta ina ma zan fara shiga wannan surƙuƙin lungun namu har in kai gida? Na tuno uwar tafiyar da muka sha kafin mu fito titi ɗazu da zan taho.
Tinani na yayi zurfi, kwatsam saidai Naji ana ta hayaniya a cikin motar, wasu na cewa " Wai ya haka ne? Dreba me ke faruwa ne?" yayin da dreban ko amsa masu baiyi ba, ya dai samu ya gangara bakin titi ya faka motar, ya fice domin duba meke faruwa.
Ai tini naji ƴan ciki na na yamutsawa, gamu dai a cikin dokar daji, kuma ni kaɗai ce mace, sauran mazan sai hayaniya suke yi, Dreba dai bai ko kula su ba, sai faman gyara yake yi, har duhu ya rufa ruf, kowa ya fiddo wayar shi yana haskawa, yayin da duk sauran mazan sun fice, ni kuma na takure cikin motar ina ta rawar sanyi da makyarkyata, nadama duk ta rufe ni, shin menene ma dalilina na tahowa ayau ne? Bayan na san dare ya riga yayi?
Tinani barkatai suka taru suka yi mani yawa.
Tin daga cen ɗan nesa damu muka ga an dararo mana wasu irin fitilu masu mugun haske, sai kuma ƙarar bindiga ta soma tashi, ai bansan lokacin da na ruɗe ba, har fitsarin da nake ta matse wa ya soma zirarowa, da gudu na diro daga cikin motar, hannu na riƙe da ƴar waya ta da tin ɗazu nake neman service, ko dokar ummata ce yau dai in karya in nemi Bilal ɗin tinda cen ƙauyen babu wanda zan kira babu ma mai wayar hannu saboda rashin service ɗin.
Kasheta ma nayi baki ɗaya ganin bazan samu damar kiran ba, na cusata cikin breziya, jikkata na saƙalo ta ta wuyana da hannu na ɗaya, ai bansan lokacin da na fara gudun ceton rai ba, kaman yanda naga sauran mazan duk sun fashe sun watse kowa ya kama gaban shi.
Gudu muke yi ba ƙaƙƙautawa, yayin da suka rufa mana baya, suna ta halbe halbe da faɗin "Ku tsaya kawai," tini suka fara kama waɗanda basu da ƙarfin gudu, gashi dai duhu yayi sosai, baka ganin ko gabanka sai hasken fitilun su.
Wani rami da bazan iya cewa ga zurfn shi ba, shi kawai nagani ta gefen hanya, ai bansan lokacin da na dira ta ciki ba, sai faman haki nake yi, kukan ma ya ƙi zuwa, ko ba'a faɗi ba dai na san ƴan kidnapping ne yau Allah ya haɗa mu dasu.
Abunda kake ji ana waiwai a ƙasar sai gashi yau ni Suhan nice gani gasu.
Cen ƙurya na takure kaina, sai faman kyarma nake yi, yayin da suka ƙaraso jikin ramin suka shiga haskowa, wani daga cikin su ne yace "Kaman fa nishin mutum nake ji anan ciki baba"
"Sauran ne suka ce mashi zo muje gaba dalla ai ba kowa, baka gani ba, ba zasu shiga nan ba ai, ga su shago cen sun kama wasu, mu juya kawai mu koma, watarana a haɗu"
Haka ya juya ya bisu ba don ranshi ya gamsu da babu kowa ɗin ba, saida sukayi nisa ne sosai na lallaɓa na fito da wata ƴar hanya da nagani, ina iya hango su ta cen nesa sun tattara mutane da suka kusan kai su biyar ciki harda dreban, yayin da suka chaje motar baki ɗaya basu samu komai ba, iza ƙeyar su sukayi zuwa cikin dajin.
Ban tsaya sauraren komai ba, na sake zurawa da gudu na tattare doguwar riga ta da zata kusan ma kaiwa guiwa, kaman guguwa nake falla gudu, ni Hauwa'u ban ma san ina da gudu ba irin haka sai yau.
Na gaji iya gajiya, gashi gefen titi nake bi, ina gudun shiga ta cikin dajin su sake kama ni. Tinani nake yi ya zasuyi da sauran mutanen da suka kama? Sauran kuwa tini sun ɓace ma gani na, kowa ta kanshi yake yi, basa ma ko tinanin ni mace ce bari su tsaya su taimake ni, kowa Nafsi-Nafsi.
Na gaji tuɓus, har bansan lokacin da na zube saman titin ba ina ta maida haki da numfashi, bana iya motsa komai na jikina, gashi saboda tsabar tsorata numfashi na har wani ɗauke wa yake yi, na riga na sadaƙat, yau kam tawa ta riga ta ƙare, na rasa wannan ikon Allah, hakanan kana cikin zaman zaman ka lafiya cikin ƴan awannin da ba zasu Gaza biyar ba komai ya dagule mani.
Tin daga nesa nake hangen fitila na dallowa ta inda nake yashe, na sadaƙar cewa sune suka dawo sake kama ni, yifff, mota ce tazo ta gitta ni da wani irin matsanancin gudu, kaman zata tashi sama, buɗe idona nayi a hankali ganin basu bane, da har tsoro ya sanya ni kulle idanun har sai sun ƙara so, sun tasa ƙyeya ta gaba.
A hankali na hango motar nayi ribos tana dawowa daga baya a hankali, daidai inda nake kwance motar ta dawo ta tsaya, da gudu na cikin motar ya fito yana haske ni da fitilar wayar shi daya kunna.
"Ke baiwar Allah lafiya kuwa? Da hankalin ki kike kwance nan? Zo taso taso maza"
Bai jira cewa ta ba, ya kamo ni da dukkan ƙarfin shi yayin da yaga ina niyyar miƙewa Amman na kasa, ƙofar gaba ya buɗe ya cusa ni ciki, shima da mugun gudu ya koma motar, yayin da ya fizge ta mukayi sama a sukwane.
Baice man komai ba, nima sai faman haki nake yi, cen kuma sai wani tsumammen kuka ya taho mani, aikau ban hana kaina yin shi ba, domin na san ba zan iya haɗiye shi ɗin bane.
Kuka na fashe dashi mai cin rai, ni suhan wacce irin ƙaddara ce haka take bibiyar rayuwa ta?
Me na aikata ma Ubangiji na ne da yake jarabta ta ta kowanne fanni? Shima mutumen Baice mani komai ba, har mukayi nisa sosai muka bar cikin daji muka fara ratsa ƙauyuka.
Duniyar tsit, in banda haushin karnuka da kukan tsuntsaye. A hankali ya kai duban shi gareni da naci kuka na ƙoshi ina ta sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali.
"Daga ina kika fito? Kuma ina zaki? Me ya sanya na ganki a wancen wurin kwance?
Ya jero mani tambayoyi, sannan ya kafeni da idanu ta cikin hasken fitilar motar daya sanya hannu ya kunna.
Cikin son share hawayen da tsaida kukan na fara cewa
" Daga zariya nake, naje makaranta ne, ashe yajin aiki akeyi, banda inda zan kwana ne ya sanya ni neman komawa gida, a ƙoƙari na nason komawar ne muka haɗu da ƴan kidnapping......"
"Wat?"
Ya faɗa yana mai saurin kallo na, tini wani irin tausayi na ya tsirga mashi, sake kafeni da kallo yayi, saidai baice mani komai ba saidai "Allah shi kyauta gaba, yanzu ina kika nufa?"
*"Sunkui"* na bashi amsa ina mai duban hanya, zuciya ta a cunkushe take ga hawaye dake ta faman zarya a idanuna.
Baice mani ƙala ba, ya kuma zaro tissue ya miƙa mani, amsa nayi ba gardama na shiga goge kwallar, saidai ina gogewa wata na sake ɓulɓula a cikin idanun nawa.
Daidai ya karya kan motar tashi ne, zuwa hanyar da zata sada mu da ƙauyen namu ne, sai kuma ya sake ɗan kallo na haka a gajarce, sannan ya kuma ceman
"Gaskiya kinyi matuƙar kuskure, a matsayinki na mace bai kamata ki biyo hanyar dare ba, ko ina ne ya kamata ki nema ki kwanta zuwa safe, iyayen ki zasu matuƙar yi maki faɗa, muddin suka ji abunda ya faru"
Gyaɗa mashi kai nayi, ina mai cewa "Haka ne, nima na sani, kuma nayi nadamar yin hakan, saidai ba zan kuma ba insha Allahu, nagode da taimako na da kayi"
Nan ma baice komai ba, sai ma miƙo mani waya da yayi yana mai cewa in sanya mashi number ta, in an koma yajin aikin zai kira ya gaya mani.
Amsa nayi gami da danna mashi numbobin, sannan na ƙara da faɗin
"Saidai ko ka kira ba zaka samu ba, saboda ba service a ƙauyen namu"
Ɗan shiru yayi, yana mai amsar wayar ne yake ce mani "Ba komai in an koma zanzo da kaina in faɗa maki, nima lecturer ne a makarantar da kika je ɗin, Sunana Salim Bawa. Ya sunan malamar?"
"Suhan" na faɗa mashi a hankali,
"Wow, what a nice name?" ya faɗa da ɗan murmushi akan fuskar shi, sannan yace ki share hawayen ki, insha Allah kin iso gida babu abunda zai same ki anan kuma"
Ganin mun ƙaraso ƙauyen ne, ya sanya na shiga kwatanta mashi gidan, har ƙofar gida ya dire ni, fita nayi ina ce mashi "Nagode, ko zaka kwana ne anan? Idan gari ya waye sai ka wuce?
(kaji su Suhan da ƙarfin hali. Lol)
Kallon gidan yayi, sai kuma ya ɗan girgiza kai yana mai cewa "Ah No dear, zan wuce ne, ina sauri ne, shine ma ya sanya ni tafiyar daren"
Godiya na shiga yi mashi, ina tsaye har ya juya kan motar tashi ya fice yana mamakin ace mutane ne ke rayuwa a cikin wannan kangon gida.
Yayin da ni kuma na ɗan matsar da kararen na shige, kai tsaye ɗakin namu na dosa, hannu kawai na sanya na buɗe gami da shiga, a zaune na tadda ummata tana lazimi, tabbas umman tawa mace ce mai yawan ibada, ga addu'a da maida lamirn ta ga Allah, ni kaina na san kawo mu ƙauyen nan da tayi akwai wani Al'amari mai girma ne, Amman koma menene zamu zuba ido muga Abunda Allah zai yi.
A ɗan ma makance ta taso cikin ɗan zaro idanu ta shiga cewa "mamata kece cikin tsakar daren nan? Garin yaya kika yo tafiyar dare ke da nace ma ki kwana zuwa safe kin taho?"
Kai zaune na kai ina mai sauke ajiyar zuciya mai nauyi ina cewa "To umma ai yajin aiki suke yi, hostel ɗinma a kulle suke"
"Ikon Allah, to yaya aka yi kika shigo nan? Na dai san da wuya ki samu mashin yanzu cikin daren nan, shine ma yasa nace ki kwana, kuma kinga hanya yanzu babu kyau, ɓata gari sunyi yawa"
"Umma Allah ya tsare wallahi, wani malami ne ya maido ni, a cewar shi nayi kuskure ai hanyar bata da kyau, yace ma idan an koma yajin aiki zai zo ya faɗa man tinda yaga gidan"
"Malami fa kika ce mamana, ki dai kula gaskiya, duniyar nan babu gaskiya a cikinta, Naji ma muryar ki a shaƙe ko iskan mota ce?"
"Eah umma, na gaji ne sosai, bari inyi salla sai in kwanta, zuwa safe zan faɗa maki komai"
To tace mani tana mai nuna mani buta dake ajiye, fita nayi na wanke jikina tas da fitsari ya ɓata man ɗazu, sannan na ɗauro alwala, gami da cenza kaya na tada salla.
Bayan na gama ne, umma tace mani ga tuwo idan zanci, na ƙoshi nace mata, domin ina tsammanin babu wani abu da zai iya shiga bakina a halin yanzu.
Bisa shimfiɗar tabarmar kaban namu na kwanta, har yanzu jikina ƴar kyarma yake yi, Amman ina iya ƙoƙari na kada umman tawa ta gane halin da nake ciki.
Ko minti talatin banyi ba da kwanciya baccin wahala ya ɗauke ni cike da mafarkai barkatai iri iri marasa daɗi, ciki kuwa harda na mutanen da ƴan kidnapping suka kama akan idona.
_(Masalar da ake fuskanta kenan a ƙasar tamu Nigeria, suna nan, kuma an san su, suna fitowa a lokacin da suka so, kuma su koma a lokacin da suka so, ba tare da gwamnatin Nigeria ɗin nayin wani yunƙuri na azo a gani ba, domin daƙile afkuwan hakan._
_Jinjina ga gwamnan jihar tawa ta Katsina *RT HON: AMINU BELLO MASARI* a ƙoƙarin shi nayin sulhu da ɓata garin, shi sulhu a ko'ina alkhairi ne, idan har yunƙurin nashi na kawo gyara bai yuwu ba, to hakan na nuna dole ne a ɗauki doka sosai AKANSU. _
_Haka kuma ina mai jinjinr ban girma ga *DCP ABBA KYARI* a bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen kamo ɓata garin, ba dare ba rana yana aiki, munji mun gani mun kuma yaba, Allah ubangiji ya ƙara taimaka mashi, ya kauda mashi idon maƙiya da mahassada a ko'ina yake a faɗin duniyar nan, Alherin Allah ya isar mashi, ni Oum-Deedat na sadaukar da Page ɗinnan ga mutanen guda biyu, Allah ya ƙara basu ikon jajircewa a bisa dukkanin ayyukan Alkhairin da suka sanya gaba. AMEEN)._
*******************
Yau Iyalan Alhaji Mustaphan sun tashi da matuƙar farin ciki na farfaɗowar sahibin zuciyar tasu, kuma ya tashi tangarau saidai Abunda ba'a rasa ba, kowa na matuƙar murna da farin ciki, duk sun zagaye shi, kowa kaman ya faɗa kanshi, da ɗaiɗayan suka dinga rungume shi, ita kau hajiya kubra sai faman shafa mashi kai take yi, kai ga dukkan alama soyayyar Al'ameen ɗin nata a cikin zuciyar ta, daban take harma bata iya ɓoyuwa.
Bilal ma cikin murna da farin ciki yake duban abokin nashi, sashe ɗaya kuma na ɓangaren zuciyar shi yana mai tino mashi da ɓatan su Suhan ɗin da kuma idan aminin nashi ya tambaye shi mai zai ce mashi ne?
Ƴan kankiya duk sun zo duba jikin na Al'ameen, inda Alhaji Mustaphan ne ya sanya su biyo jirgin domin suzo ganin shi, harda kaka isuhun kuwa suka taho, lallai duk wanda ke cikin asibitn nan ya shaida cewa Al'ameen ɗin ɗangata ne gaba da baya.
Tini Alhaji Mustapha ya nemi a basu sallama, Amman likitocin sun hana sunce sai nan da kwana biyu, idan ya sake gyagijewa.
A hakan ma dai murna suke yi, duk da bawai magana yake yi ba, hasali ma har yanzu baice komai ba, saidai faman ɗan murmushi da yake yi na gefen baki, ganin irin ƙaunar da dukkanin zuri'ar tashi suke nuna mashi.
Iyayen Bilal ma sun zo, harda ummin Bilal ɗin, da yake yarinya ce mai shiga rai, da faram sannan gata wayayya sosai, uwa uba mahaifan ta masu kuɗi ne sosai, ya sanya ta samu sauƙin su Saudat ɗin, duk da dai bawai shiga al'amarin nasu take yi ba itama.
Kowa dai yana tsaye, sai faman sannu akeyi mashi, shi kau sai faman binsu da idanu yake yi, yayi mamakin da yaji ance gungun Matasan kamfaninshi shi ɗin sunzo sun duba shi tin daga nigerian lokacin bai farka ba, ba'a bari a kawo ma marar lafiyan komai, asibitn sune suke ba marar lafiyan abunda suka san ya dace da yaci.
A haka suka kusan yini, dukkan su suna zaune anata fira harda Bilal ɗin da kuma sauran ƴan uwan nashi, yayin da Alhaji Mustapha ya tafi cikin gari wajen abokanan shi, tinda jikin na yaron nashi yayi sauƙi masha Allah.
Wajen ƙarfe biyar ne likitan ya shigo gami da basu umurnin su fita abar marar lafiyan ya huta, dama amfanin riƙe shi asibitin kenan.
Daf da zasu fice ne, suka ji a karo na farko tin farfaɗowar tashi yayi magana.
*"INA SU SUHAN?"*
Maganar da yayi ce ita ta sanya kowa dakatawa daga tafiyar da yake yi, a sukwane Bilal ɗin ya juyo yana mai kafe Al'ameen ɗin da kallo lokaci guda kuma ya janye idon shi ya maida kan Hajiya Kubran da take kallon yaron nata da wani irin yanayi, Tausayi ma ya bata, tabbas ta san basu bar shi hakanan ba, yaron nata maiji da ilimi, dukiya, uwa uba yanzu ga sarauta, shine mai kwallafa ranshi akan wata marar galihu a rayuwa
Buɗe baki tayi da niyyar magana, Bilal ɗin ya riga ta da sauri wurin cewa
*Suna Nan Lafiya Ƙlau, Sunma Ce A Gaidaka*
Yana gama faɗar haka ya juya ya fice sauran suka rufa mashi baya, su kuwa su Nihal kaman zasu fashe, dole ba don taso ba ta shiga bin bayan su itama Hajiya Kubran, ganin ya maida idanun nashi ya lumshe gami da sauke wata ƴar ƙaramar ajiyar zuciya.....
_ina mai ƙara bada haƙuri dai, wallahi rashin chaji ke damuna, Amman insha Allah dama samu zaku sake jina_
~Oum-Deedat ce~
[9/26, 9:43 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~34~*
_Masu kirana da masu yi mani Dm da masu comment, nagode kwarai da addu'o'in ku, Allah ubangiji ya saka da Alkhairinsa, ya kuma bar zumunci, na samu sauƙi sosai kuma Naji daɗin yanda kuka damu da rashin lafiyata, ina yinku kaman yanda kuke yina, addu'o'inku da comment ɗinku kan ƙara mani ƙwarin guiwa._
_Kyautar Page gareki @Lubabatu ta *BANFI ƘARFINTA BA FANS* Haƙiƙa damuwar ki a kaina bata misaltuwa, babu abunda zan iya cewa, saidai ince ALLAHU YABAR ƘAUNA_
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Haka dai rayuwa tayi ta garawa damu, yau daɗi gobe babu, duk kuwa da cewa irin halin takura da matsantuwa na rayuwa da muka shiga, hakan baisa mun gaza ba, ko nuna ma Allah bijirewa akan jarabawar da yake yi mana, saidai fatan Allah yasa mu iya cinye ta lafiya.
Ummata mace ce mai kawaici, da sanin ya kamata, zaman mu a gidan baisa umma ta zura idanu akan komai sai malam ɗin da matar shi hajjo sun bamu ba, ƴan abubuwan da muka zo dasu, tini umman tawa take ta fiddosu ɗauki ɗai-ɗai har suka zo suka ƙare muka cinye.
Ganin hakan ne, kullum ummata cikin tunani cikin damuwa, don watarana idan malam ɗin baiyi sa'ar kasuwa ba, mu kan kwana bamu zuba ma bakin salatin mu wani abu ba, saidai ruwan da tin inasha ina amai, a haka har na daure ma rayuwa ta.
Wannan ce ta sanya ni cema umman tawa ko zamu fiddo kayan provision ɗina na makaranta, saidai ta gane ni, a cewarta in yau aka zo aka ce in fito da me zamu siya?
To dole nima dai na haƙura, saidai fa inayi masu ɗauki ɗai-ɗai, duk da umman tawa tana kallo na, amman ta kan Gaza ceman uffan, saboda wani irin tausayi na da ya kan ratsa ta, har kwalla take yi a kai-kaice bataso in gani, saidai fa nima ɗin wani lokaci idan abun yayi yawa ya isheni nakan shige banɗaki inyi kuka mai isa ta, in wanke fuska ta in fito don kada umman tawa ta lura, amman fa ance yaro yaro ne, koda kuwa ɗan giwa ne, tana lura tsaf dani, saidai bata tankawa, saboda tasan komai mai wucewa ne.
Sana'ar wankuu ta fara yi, ta kan je bakin rafi ta wanko ta dawo gida ta shanya akan danni. To saboda ƙauyen ba wani babba bane ba, bata cika samun wankin ba, bayan haka da wani ya bada wankin gara ta auno shinkafa ƴar hausa ya watsa wake ko dawa a ciki an dafa ansha shagali.
Hakan ce ta sanya ta haɗawa da surfau, a ranar da ta fara surfau ɗin kuwa, ba irin kukan da ban sha ba, abun ka ga fara, fuska ta tayi suntum kuwa, tayi jajur, kaman ka taɓa jini ya ɓalle, tausayin ummata nake ji da irin rayuwar da muke ciki, tabbas idan guri na ya cika babu abunda zai hanani gina ma ummata gida a Abuja in ɗauke ta, muje cen muji daɗin duniya, saboda irin wahalar da muka sha a rayuwa.
Da wannan ɗan aikin da ummata take yi, nakan taya ta kullum, wani lokacin harda hajjo ɗin, saboda ƙauyen ana bala'n sarrafa dawa da gero da masara, kusan ma ince sune abincin nasu, wasu ma ko surfawa ba'a yi, a haka ake cinta datsa, wai tafi auki. To da wannan ƴar sana'ar ce muke samu mu ɗora tukunya kafin fa malam ɗin ya dawo.
Malam yana matuƙar sona, yana ji dani kaman shi ya haifeni, haka tsakanin shi da ummata sai girmamawa da mutuntawa, ya ɗaukemu kaman wasu jinin shi, duk da na kula babu abunda ya haɗa shi da umman tawa ta fannin ƴan uwantaka.
Sai ince mun samu so da ƙauna, da tattashi a inda basu dashi, basu da abun bamu, ko don saboda suma ɗin talakawa ne kaman mu? Oho...
Nima saboda haka na fara yin ɗan kitso haka, ana bani naira ashirin ko shabiyar idan yara nayi mawa, manya kuma har talatin, ko a bani sabulu ko omon wanki, ko kuka ko kuɓewa, to dai mun gode, mun i-iya dasu tinda abun kuɗi ne, muma sai mun siya. Tini kayaaa suka fara dafewa, saboda tsabar rashin kyaun ruwan wankin da sabulu, dama wuta kuwa tinda muka je ƙauyen ban ganta ba, da idanuna kuwa.
Haka muke ta ƙundunbala, rayuwa fa babu daɗi, matsatsin yayi mana yawa, a ƙauyen kowa da Hauwa yake kira na, saboda dashi Malam da Hajjo ke kirana, ita kuwa umma saidai tace man Mamana.
Da ummata hanani fita take yi, duk da bansan dalili ba, saidai nafi alaƙanta hakan da wancen zaman da ummata tayi, a lokacin da akace an haifeni, gudun tsogunguma irin na karkara ya sanya suka shawarta hakan da malam.
Saidai fa ban tsira ba, duk lokacin da na fita, haka zaka ga an hau danni ko ƴar katangar ƙasa, ana nuna ni da baki ana gulma ta, da zunɗena, har saida na samu ummata da maganar, ita kuma ta shawarce ni da kar indamu, dama dole hakan ce zata faru, saidai hakan ba wani abun damuwa bane, idan nayi la'akari da yanda aka yi aka haifeni har zuwa barin Umman tawa ƙauyen, da kuma dawowar ta katsahan..
Ta ƙara sanya ni cikin tunani mai zurfi, saidai banga fuskar tambayar warwara ba, nayi imani dai cewa ko badaɗe ko bajima dole ne komai zai fasu, dole akwai ranar ƙin dillanci, ranar da dukkanin ɓoyon da umman tawa take yi mani komai zai bayyana kanshi da kanshi...
Muna cikin wannan halin ne, wata ranar talata da sassafe, sai ga wani yaro "wai ana sallama da Suhan" tinda naji hakan gabana ya faɗi, don dai a duk faɗin ƙauyen ba kowa ne ya san da wannan sunan nawa ba.
Tin kafin in leƙa tsakar gidan, ummata da take zaune tana iza wutar ruwan kunu, tin jiya taci sa'a aka samo mata niƙan dawar da geron, da yake idan an haɗa su sunfi auki, ba ta daɗi ake ba tukun, niƙan ma da sai afi sati ba'a samo man da za'a tayar da injin ɗin ba, duk kuma ranar da aka samo, tofa ana kai wani lokaci ana niƙan saboda layi.
"Inji waye?" Ummata ta jefa ma yaron tambaya gami da tsattsare shi da idanu, domin jin amsa.
"Oho nima ban sanshi ba, wani ɗan gayu ne dai da mota, yana ƙofar gida"
Yaron ya faɗa kai tsaye, batare da ya tauna maganar ba, ko ya kula da *Yo* ɗin da yace hakan ba tarbiyya bace ba.
"Jeka abin ka" ta faɗa, tana mai zarar hijabin ta da take bisa igiya. Nidai ina tsaye bakin ƙofar ɗaki sai faman raba idanuwa nakeyi, hankalina fa duk ya tashi kar ace Bilal ne ko Ya Ameen suka gano inda muke.
Tsaye ta tadda shi jikin mota, ganin babbar mace da yayi ya sanya shi saurin isa ta inda take tahowa ya durƙusa har ƙasa yana mai cewa "Ina kwana?"
Cikin ƴar sarkin fuska jin daɗin ladabin da yayi mata, da kuma ƴar natsuwa data hanga tattare dashi ya sanya tace "Lafiya lau, wa kake nema ne?"
"Tace mani Sunan ta Suhan" ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, saidai har yanzu kanshi a duƙe yake ƙasa, ƙare mashi kallo tayi tsaf, ba manyan kaya ne ba jikin shi, hasalima ƙananan kaya ne, daidai da gani yana cikin hutu, kayan shi ma sun nuna da yanayin shi, da kuma motar da yazo a cikin ta.
Gabanta ne ya tsananta faɗuwa, tana tsoron masu kuɗi, tana gudun su, wasu kuɗin bala'i ne, wasu kuɗin masifa ne, masu kuɗin na zuwa wuta ne, lallai koma minene dole ta daƙile alaƙar nan da take shirin faruwa da ɗiyar ta.
"Yaro Suhan ƴa ta ce, saidai kuma gashi ni ban waye ka ba" ta faɗa cikin manyance da dattako irin nata.
Gaskiya yaji daɗi, ko haka aka tsaya ya fahimci tabbas yarinya ce mai gata da galihu, yarinya ce mai natsuwa, ko a sadda ya ganta wancen karon ya kula da haka, saidai ƴan matan na yanzu ba tuƙwane bane balle a kwankwasa su aji.
"Eah mama, wato nayi mata alƙawarin cewa duk sanda aka koma makaranta zanzo in faɗa mata, gashi anyi sati da komawa wani uziri ya riƙeni, ni malami ne a makarantar da take, na kula ita sabuwar zuwa makarantar ce, shiyasa gashi kuma ga dukkan alama batasan kowa ba, ko hanya ma bata sani ba, shine nazo in faɗa mata, in ba damuwa ku bani izini in tafi da ita, gudun faruwar wani abu a hanya ko kuma a cen makarantar, nayi alƙawalin cewa da izinin Allah babu abunda zai faru, Amman fa in kun amince"
Tinda ya fara magana bata katse shi ba, har ya kai aya, sannan ta jinjina kai, tana mai gyara tsayuwar ta, bayan ta ƙara nazarin shi.
Ba ƙarya ko alamar rashin gaskiya a tattare dashi, duk da yanzu mugu baya da kama a fuska.
"Tabbas ta faɗa mani hakan, kuma lallai batasan makarantar ba sosai daga nan, to saidai bana jin zan iya barin ta ta bika, alhalin kadai san ba muharramar ka bace, sannan ba sanin daga ina kake mukayi ba, kuma bamu da tabbacin kai ɗin malamin ne, saboda haka kayi haƙuri don Allah, mun gode da Alkhairin ka a gare mu baki ɗaya. Ka gaida gida"
Tana gama faɗar haka ta juya zata shige gida, shima ganin hakan ne ya sanya shi saurin shan gabanta yana faɗin
"Mama don Allah kiyi haƙuri, wallahi hanyar bata da kyau, naji idan ba zaku iya barin ta ita kaɗai ta bini ba, a haɗa ni da wani sai ya raka mu, alabasshi shi sai in sanya shi mota ya dawo nayi alƙawari"
Dakatawa tayi ga barin shiga gidan da take da niyyar yi, sai kuma ta juyo ta fuskance shi
"Kasan girman alƙawari kuwa?"
Ta jefa mashi tambaya, gyaɗa mata kai ya shiga yi, ba tare da ya iya furta komai ba, zuciyar shi nata faman duka, sai kai komo take yi. Ko ba komai ya ƙagara a barta ta fito ko ya samu sa'ida, akan tunanin da yake wuni da kwana nata.
" To shikenan tinda kace haka, Suhan zata fito yanzu ku tafi, na baka amana, kai da Allah kuma idan kaci, sannan inaso ka shige mata gaba wurin samun transfer da take so tayi, zuwa wata makarantar, ina so kayi mani wannan alfarmar"
Gabanshi ne ya tsananta duka, shi yaushe ne zai iya barin ta ta samu transfer, yana kallon ya dace ya samu daidai inda yake so, burin shi ya cika, yaushe yana kallon ruwa kwaɗo zai yi mashi ƙafa?
"Mama banyi katsalandan ba, ki gafarce ni, amman ba abune mai yuwuwa ba, duk kuwa da nake malami a jami'ar, saidai idan zaki iya faɗa mani dalilin ko damuwar, nayi maki alƙawarin zan san yadda aka yi aka kauce ma faruwar al'amarin"
Ya faɗa cike da zullumin ko zata yarda da hakan.
Saidai ga mamakin shi yaji ta fara cewa.
"Eah, duk da bansan dalilina na yarda da kai ba, inaso ne ta samu canjin makaranta saboda bana so kowa ya gane tana makarantar, kuma koda wani zai zo ya binciki inda take, ba zai samu bayanin komai ba"
Ɗan murmushi ya saki, duk da kanshi ya ƙulle sosai, to ta yaya za'ayi ace wani yaje neman yarinyar da take wannan surƙuƙin, ta yaya ma aka yi ya santa? Kenan akwai wani bayan shi? Lallai dole duk yanda za'ayi ya ture gwamnatin wancen ya kafa tashi, kai inaaaa, ai bama zai yuwu ya cire yarinyar a rayuwar shi bb,tayi mashi, kuma ya san irin zaɓin Ammin shi ce.
"Insha Allahu umma, ai bama bada wani imformation ga wani na waje a cikin makarantar, akwai tsaro sosai, kuma nayi alƙawarin yin iyakar iyawata ta a kauce ma hakan, ita kuma ta samu Abunda taje nema insha Allah"
Jinjina kai ta kuma yi tana mai cewa "Mungode kwarai, ina jaddada amana a hannun ka, marainiya ce, idan kaci amanar ta Allah ba zai barka ba kaima"
Baisan lokacin da ya haɗe hannayen shi ba don daɗi, ai tini ya fara zuba godiya, duk son ya kauce ma fiddo farin cikin shi a fili, saboda wani zargin gazawa yayi. Itama ta ɓangaren umma ta tinanin hakan ta juya ta shige gidan, zuciyar ta na ta saƙa mata wannan farin cikin da ta gani akan fuskar shi na menene? Kauda mugun tinani tayi, tare da maye shi da na alkhairi, ta cigaba da addu'a har zuwa shigar ta gidan.
A bakin ƙofar ɗaki dai ta tadda ni tsaye, sai zaro idanu nakeyi,
"Jeki shirya ki fiddo kayan makarantar ki, malamin ku ne"
Ta faɗa tana mai wucewa kai tsaye wurin tukunyar ta, da ta riga ta ta fashe tuni.
Cikin murna da ɗoki na juya zuwa cikin ɗakin, ai ko ba komai ma, na ɗaga ma wannan ƙauyen da ya zame mani ƙarfen ƙafa, ba ruwa ba wuta, ba abinci mai daɗi, ba wurin kwanciya mai daɗi.
A haka na shirya tsaf, na fidda kayan tsakar gida, ko ruwan kokon ban tsaya sha ba, saboda zumuɗin makaranta. A haka ummata ta har haɗa dubu uku da take ta maƙalo maƙalo da ita, gudun faruwar hakan, miƙo mani tayi gami da yi mani addu'a. Har tsakar gida ta biyo ni tana mai jaman kunne gani da cewa in kula.
Hajjo da malam ma da bai tafi kasuwa ba, suma sun man ihisann su, na kuma ji daɗin shi, suma har waje suka raka ni, suna mai tayani ɗaukar kayana.
Yana ganin fitowar mu, ya zabura ya buɗe mana but muka saka kayan ya kulle, ya zagaya ya buɗe man gidan gaba, na shiga gami da maida ƙofar ya kulle, shima zagayawa yayi ya shiga bayan ya gaishe da malam ɗin.
A haka motar tayi ribos, ina ɗaga ma ummata hannu da take ta faman share kwalla da bayan hannuwan ta, nima ai sai naji kwallr ta cika mani idanuwa har bansan ta fara zuba akan fuskata ba. Har motar ta ɓace ma ganin su Umman sannan suka juya zuwa gida, yayin da ni kuma na sauke hannun ina mai sake rushewa da kukan da nagaza gane ko na menene, shin na rabuwa da ummata ne? Ko na murnar cikar buri na? Ko na halin da na bar umman tawa a ciki ne? Ko kuma mikin su Ya Ameen ne ya taso mani.
(Hummm Suhan kenan)
*******************
Cikin kwana biyun kuwa da aka ɗibar mashi jikin yayi sauƙi, haka aka lallaɓa dashi aka koma gida, duk da yanzu babu abunda ke damun shi, sai rashin ƙarfin jiki.
Tin da Alhaji Mustapha yaga haka, yace zaman da su Nihal ɗin suke yi ya isa hakanan, su wuce kowacce ta koma ɗakin ta, haka duk ya tarkata su ya fafutuka su gida, ya rage daga shi sai Bilal da Abie sai Hajiya Kubra.
Zaman hakan baya mashi daɗi, ya rasa dalilin da yasa tinanin Nigeria ɗin yayi mashi yawa, kuma kullum idan ya tambaya sai ace mashi lafiya lau, idan ya tambayi su Suhan kuma ace mashi tana makaranta, wai me ke faruwa ne?
Wayar shi da number ɗin ta ke ciki kuma ta fashe kwatsa kwatsa bata ma moruwa, tin ranar da abun ya faru, gashi baiyi saving a mail ba, balle ya nemo.
A haka ya tada balli cewa, shifa zai tafi nigeria yaga ya abubuwa suke ciki, hankalin su fa ya matuƙar tashi, Alhajin ne yayi dubarar hanashi, yace Bilal ɗin yazo ya tafi ya gano komai, amman shi da barin ƙasar kuma sai yanda hali ya nuna.
Hikimar Alhajin nayin hakan kuwa shine, don Bilal ɗin yaje ya nemi su Suhan ɗin kafin komawar su ƙasar.
To shima dai Bilal ɗin ya gane hakan, wannan ce ta sanya shi tarkatawa ya koma Nigeria ɗin, wanda tare da Hajiya Kubran suka tafi, saboda ta koma ma harkokinta tinda yanzu jikin yayi sauƙi, ba abunda ke damun shi illa su shegiyar yarinyar nan, to indai don wannan ne ba kuwa zai taɓa warkewa ba, saboda yanda suka sanya ƙafa suka tafi, sun tafi ɗin kenan fa.
Bilal ya sha wahala sosai, duk inda ya san zai je yaje nema, har makarantar yaje lokacin da aka koma yajin aikin, Amman bai samu gamsasshen bayani ba, cewa sukayi har yanzu bata dawo ba, koma suce su basu sake ganin ta ba, da haka ya koma gida, tabbas ya shiga tashin hankali ba ƙarami ba, shi bama ta son da yake ma Suhan ɗin yake yi ba yanzu, ta rayuwar aminin nashi daya kula cewa lallai za'a sha darga idan ya gane cewa ta ɓata, bama asan inda za'a ganta ba, gashi kullum ya gwada layin nata akan ce mashi switche up, baya gajiyawa kullum sai ya kira ta kai sau goma.
A haka ummin shi ke sanya shi gaba da ban baki, da ban haƙuri da kwantar da murya akan al'amarin, shi bai ma san ta yaya zai ɓullo ma al'amarin ba, ko kusan alama, bai taɓa tunanin idan zai iya shiga wannan irin halin ba a rayuwa.
Ko aiki ya dena zuwa, gashi Al'ameen ya matsa akan yaje makarantar su Suhan ɗin ya bata suyi magana, ko ya haɗa shi da umma, idan ita Suhan ɗin tayi nisa.
A haka abubuwa suka taɓarɓare, ba ga aikin kamfanonin nigeria ɗin ba, ba kuma ga na cen american ba, tinda tini shi Alhaji Mustapha ya koma cen ƙasar da yake aiki, ya bar shi daga shi sai Abie.
Ƙarfe goma na safiyar litinin, Bilal ne zaune bisa kujera mai cin mutum ɗaya, ya zabga uban tagumi, ga stool ajiye gabanshi cike da kayan breakfast, so take yaci ko ya samu ya leƙa wurin aiki yau, rabon shi da zuwa office ita har ba zata iya tunawa ba, komai daga gida yake yi, ko kuma yace aje a samu mataimakin shi Peter, itama ummin zaune take gefe ta zuba mashi idanu, tabbas mijin nata yana cikin damuwa, to saidai ya zata yi dashi? Babu wani taimako da zata iya bashi a halin da ake ciki yanzu.
Kaman ance ya latso number ɗin Suhan ɗin, aikuwa sai ta fara ringin, firgigit yayi ya miƙe daga tagumin da yayi, baisan ya fara kai komo ba, yana mai cewa "Comon pick it Suhan please"
Itama ummin a zabure ta miƙe tana mai cewa "Ta shiga ne? Ta ɗaga ne?". Bai ko kula ta ba, ya cigaba da zagaye tanƙamemen falon, bata ɗauka ba, hakan ne ya sanya shi dunƙule hannu ya naushi iska dashi, gami da guntsar iska ya fesar, sake kira yayi Amman ta shiga ba'a ɗauka ba.
Da hanzari ya fice daga falon, mota ya nufa da niyyar barin gidan, zuwa zai yi ya kai number ɗin ayi mashi tracking ɗinta, koma ina Suhan ɗin take yau ce ranar da zata bayyana, baya jin idan zai iya yafe ma duk wanda yayi sanadiyyar barin su gidan gabaki ɗaya a rayuwa.
Ko ta kan ummi baibi ba, ya danna ma mai gadi horn, da gudu yazo ya buɗe mashi gate, ya ja motar a fusace yabar gidan, daidai ƙarasowar ummin da gudu tana ɗaga mashi hannu.
"Wash" tace tana mai kai hannuwan ta bisa guiwoyinta kaman zata yi ruku'u, saboda tayi gudu ta gaji, daga falon zuwa harabar gidan da ƴar tazara, hakan ce ta sanya ta gajiya, ga kuma laulayi da take fama dashi.
*Adai yi mani uziri, a kuma bini da Addu'a please*
~Oum-Deedat ce~
[10/1, 8:25 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
*Page ~35~*
*_Happy Indipendance Day To All Nigerias, Allah ya ƙara mana zaman lafiya kwanciyar hankali da wadata, yaba shuwagabanninmu ikon yi mana aiki da adalci bisa gaskiya. AMEEN_*
~Gaisuwa ga Lubabatu Funtua shima wannan Page ɗin naki ne, nagode da kulawa da ƙauna baki ɗaya~
*Aishatu Babayo Jos Mrs: Abubakar Yakubu (Ɗanjuma Master) ƴan golden pen suna yinki, ba zamu iya fasalta ƙaunar mu a kanki ba, saidai muce Allah ya bar mana ke, kiyi ta suburbuɗa mana comment Ameen*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Munyi nisa a tafiyar tamu da mukeyi zuwa makarantar, saidai ba wanda ke ceman wani ƙala cikin ni dashi,tin bayan gaida shi da nayi, lokacin da na shiga motar. Jefi jefi ya kan ɗan juyo ya saci kallo na haka, ni kuma sai in kauda kaina, tunani na yayi zurfi sosai, abubuwa da yawa nake saƙawa cikin raina, lokaci guda tunanin in sanya waya ta cikin caji a motar ganin cazar da nayi ya faɗo a raina.
Jikkata na jawo gami da ɗauko wayar, a hankali na jona ta a cikin chajin,kaman jira take yi kuwa ta ɗauka, kunna ta nayi, lokacin da na kula ta kai kusan 5% na ajiye ta kusa dani.
Har yanzu dai bai ce man uffan ba, tuƙin shi kawai yake yi, ganin hakan da nayi ne ya sanya ni janyo hijab ɗita na rufe kusan rabin fuska ta,gami da jingina kaina jikin ƙofar motar ina mai lumshe idanu, sanyin Ac na ratsa ni, haɗi da ƙamshin freshner ɗin dake cikin motar sun haɗu sun cakuɗe da ƙamshin turaren mutumen da ya kira kanshi da suna *Salim Bawa*
Ban aune ba naji muryar shi kwatsam yana cewa "Maman ki ta burgeni matuƙa, haka nake son mace mai jajircewa akan ƴaƴanta, nima haka Ammi na take"
Ɗan ɗagowa nayi a hankali, ina mai kai idanuna bisa ƴar kyakkyawar fuskar shi, sannan nace "Nagode" a hankali.
Ɗan murmushi ya sake yi, sannan ya cigaba da cewa "ya kamata ki sake sanin ko ni wanene ko? Gudun kada in sace ki a rasa inda kike, gashi ba'a haɗo mu da kowa ba"
Dam gabana ya faɗi, sake kai dubana nayi gareshi, ɗan murmushi na hanga saman fuskar shi, ga alama ma bai wani damu da abunda ya faɗa ɗin ba.
Gyaɗa mashi kai kawai nayi ba tare da na samu zarafin ce mashi wani abu ba.
Ganin hakan da yayi shima ya sanya shi sake sakin murmushi mai sauti.
"Kaman yanda na faɗa maki gaskiya sunana *Salim Bawa Bala* mahaifi na shine Alhaji Bawa Bala idan zaki iya sanin sunan?"
Ya faɗa da alamar tambaya a kan fuskar shi.
Nan ma ɗan sake girgiza mashi kai nayi, duk da har yanzu ban ɗago ba, saidai na tattara dukkanin natsuwa ta akan shi.
Jinjina kai yayi yana mai sakin murmushi da na kula hakan Al'adar shi ce, sannan ya ɗora da faɗin.
"Ni ne ɗa ɗaya tilo a wurin Alhaji Bawa Bala, da Hajiya Khaltum Bawa Bala, duk kuwa da cewa mu biyu suka haifa ni da ƙanwata Asiya da taci sunan Kakata wadda ta haifi Babana Alhaji Bawa Bala, Shiyasa muke kiranta da Suna Imtihal ko kuma mu ce Imti. Ni haifaffen garin Adamawa ne a ƙaramar hukumar Yola, ni bafulatani ne Usul, duk kuwa da kasancewa ta baƙi. A gaskiya zan faɗa maki ina da aure harda yara biyu. Aisha Sholy da Usman muna ce mashi usi. Munyi auren soyayya da matata kaman me, iyaye na kowa na ƙaunar ta, saidai kasancewar faruwar wasu abubuwa ya sanya yanzu nake searching ina so in ƙara, saboda haka ina barar ko da acikin ƙawayen ki ne masu hali da natsuwa irin taki, a taimaka mani"
Duk wannan maganar da yake yi, idanuna ƙur a bisa titi, dukkanin garuruwn da muke wucewa hankali na yana a kansu, saidai kuma kaf ina sauraren shi da kunnuwan basira.
Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya na sauke, ina mai cewa "Allah sarki, nikam bani da ƙawaye, ka gaida man da yaran idan kaje gida da maman su"
"Zasuji"
Ya faɗa a gajarce cikin wani murmushin
Ya buɗe baki kenan da niyyar sake cewa wani abu, sai kuma wayata ta ɗauki ƙara alamun kira ne ya shigo. Nima ƴar firgita nayi, ina mai sake waro idanu waje, lokaci ɗaya na yunƙura gami da wawuro wayar.
Sunan *Yaya Bilal* na gani ɓaro ɓaro a bisa fuskar wayar yana yawo.
Ba zan iya cewa ga halin da na tsinci kaina ciki ba, saidai a zahirin gaskiya na shiga matuƙar halin damuwa da firgita, ina cikin wannan halin ne har ta katse, wani kiran ya sake shigowa a lokaci ɗaya.
Nan ma ban iya amsawa ba, har ta kuma katsewa, ai kafin wani kiran ya shigo nayi saurin kashe wayar gabaki ɗaya ma, gami da zare chajin na warware wayar gami da zaro sim ɗin sannan na maida batirin gami da sake jona ta cikin caji.
Sim ɗin yana riƙe a hannu na, shawarar in jefar dashi nakeyi, ko kuma na adana, saboda kaman yanda ummata ta nuna mani a zahirin gaskiya bata so su san inda nake, ko kuma wata alaƙa ta kuma shiga tsakani na dasu.
Shiru ne ya biyo baya cikin motar, babu abinda kake ji sai ƴar ƙarar Ac da kuma saukar numfashin mu. Duk da yana lura da abunda ya faru amman baiyi yunƙurin tambaya ba, domin yana ganin ba hurumin shi bane, ko kuma lokaci bai yi ba tukunna da zai kutsa kai a al'amarin yarinyar daga haɗuwa da ita.
Daidai bakin gate ɗin makarantar yayi parking gami da ficewa ba tare da ya kashe motar ba, ba daɗewa ya dawo cikin motar hannun shi riƙe da layin Sim na Glo, miƙo mani yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.
A sanyaye na amsa gami da yi mashi godiya a hankali, lokaci guda na kuma zare chajin da har ya riga ya cika, sanya sim ɗin nayi da na kula yana da rigister already.
Har cikin makarantar da department ɗin namu muka isa, shi ya shige mani gaba wajen cuku cukun komai, sai naga ashe ma HOD ɗin namu abokin sh ne sosai da sosai, ina zaune gefe ba wahalar komai aka kammala komai.
Umurtata yayi da na bishi ya nuna mani hall ɗin da zamu rinƙa amsar lectures. Ko bayan dana fito daga office ɗin sai da ya tsaya suka sake wata magana da bazan iya cewa ga abunda suka tattauna na ba, sannan ya fito na bishi a baya har zuwa lecture hall ɗin namu da muka tarad da wani malami a ciki yana ba sauran ɗalibai lecturers, duk da na kula ɗalibai basu da yawa sosai, haka nayi sallama na shiga na zauna a kujerar da take gefe babu kowa a bisa ita. Shi kuma a daidai lokacin ya juya ya koma haɗi da yiman inkiyar yana jira na.
Da idanu na bishi, lallai mutumen ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar karatun nawa, mutum ne shi mai zafin nama da yawan barkwanci a yadda na kula, sannan ɗalibai da dama sun sanshi duba da yadda naga ana ta gaishe shi bisa hanya sannan ana bina da kallo ganin ina binshi zarai-zarai a baya duk inda yayi.
Hankali na na maida bisa kan lecturer ɗin namu dana lura sosai cewa ya iya koyarwa sosai, cikin salon turancin shi da yake fita sala-sala.
Wata ajiyar zuciya na sauke, cikin son kauda tinanin komai a raina, zuciya ta fal da zumuɗi da farin ciki yau ni Suhan ce zaune a ɗakin ɗaukar karatu ina gaban malami yana koyar dani.
*Ya Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar ta rayuwa, ka sanya hakan ya zamo mafi alkhairi a rayuwa ta, Ya Allah ka dubeni da idon rahma ka bani abinda nazo nema, ka bani ikon jure dukkan wani ƙalubale na rayuwa daka iya kutso kai a cikin rayuwar karatun nawa anan gaba*
A haka muka cigaba da ɗaukar lectures kusan yinin ranar, ban kuma neman Sir, Salim ba kaman yanda Naji student na kiran shi.
Daga Hostel ɗinmu zuwa lectures Hall da ɗan tazara ba sosai ba, hakan ce ta sanya na saki niƙab a hankali nake taka wa zuwa Hostel ɗin bayan mun gama dukkan darussan ranar.
Waya ta ce ta ɗauki ƙara, da mamaki nake kallon fuskar wayar, ganin baƙuwar number, gashi dai na san yau na sanya layin babu wanda ya sanni da number ɗin.
Ɗagawa nayi cikin siririyar sallama a bakina, daga cen ɓangaren Naji ance "Assalamu Alaikum. Idan kin gama kada ki wuce gani ta nan bayanki ina jiran ki" ɗaga wayar nayi a kunne na, gami da juyawa, ko ba'a faɗa ba na gane mai magana Sir Salim ne, shi komai nashi cikin zaulaya yake yin shi.
Ɗan juyawa nayi a hankali, cen bisa bayan boot ɗin motar shi na hango shi zaune, kallon second biyar nayi mashi, har na ɗaga ƙafa da niyyar komawa ta inda yake, sai kuma naja na tsaya. Shima ganin hakan ne ya sanya yayi ɗan murmushi gami da dirkowa ya tako cikin tafiyar shi mai sauri ya iso inda nake tsaye kaman an kafe ni.
Da murmushi ya ƙara so yana faɗin "Ya da haka kuma? Shikenan da ban ganki ba sai kuma gobe?"
Ɗan girgiza kai nayi, sannan nace "A'a dama zan kira ka ne in na shiga ɗaki" daga haka ban sake cewa komai ba.
"To ai shikenan, zan iya yin rakiya cen bakin hanya?" ya sake jefo mani tambaya cikin wani salon zaulayar
Ɗan murmushi na saki ina mai jinjina mashi kai, sannan na juya muka fara tafiya, duk da akwai ƴar tazara tsakanin mu, kuma ba mai cema kowa ƙala, illa dai ɗan kallo na da yake yi akai akai, wannan ce ta sanya duk na takura, tinda hasali ni ba sabawa nayi da hakan ba.
Har hanyar da zata sada ni da ɗakin mu ya raka ni, sannan yayi mani sallama ya juya yana faɗin zai kirani anjima idan na huta.
Naji daɗi, ko ba komai dai na samu mai shige mani gaba, na samu mai tsaya mani da kula da dukkanin motsi na, wanda in nayi ba daidai ba zai iya cewa in bari.
Da haka har na ƙara sa ɗakin da yake mallakin mu mu uku, ga dukkan alamu ma dai za'a iya ƙaro wata nan gaba mu zama mu huɗu. Waɗanda na tadda cikin ɗakin da gani dai basa da hayaniya, shiru shiru suke dan duk kansu karatu na tadda sunayi da litattafai a hannu, sallama nayi masu haɗo da yi masu sannu, sannan na hau shirya kaya na a ɓangare na, na gyara komai na kimlace. Sannan na shige banɗaki domin yin Alwala.
************************
Da matuƙar hanzarin shi ya isa ga tracking office ɗin, Allah Allah yake yi a kammala komai ya samu ya samo yarinyar nan tin kafin abokin nashi ya kuma tuburewa.
Saidai babban tashin hankalin da ya same shi, lokacin da aka sanar dashi an fidda layin a kan wayar, kusan faɗuwa yayi, saida ya dafe bangon dake kusa dashi.
A hankali ya jingina bayan shi da bangon, Ya Salam! Wannan wace irin rayuwa ce? Me hakan ke nufi? Menene dalilin su na aikata hakan? Da gangan sukayi kenan? Laifin ne suka aikata masu? Ina ita Umman take? Da hankalin ta zata ja yarinya su shiga uwa duniya inda basu da kowa?. "Huh" ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi jiki ba ƙwari yaja ƙafar shi ya bar wurin.
Koda ya shiga mota yafi minti sha biyar ya gaza tada motar, hankalin shi bai sake tashi ba, saida kiran Al'ameen ɗin ya shigo wayar tashi, kaman ba zai ɗaga ba, sai kuma yayi tunanin kada Al'ameen ɗin ya zargi wani abu kuma, tinda ya san halin shi, shegiyar ƙwalwa Allah ya bashi.
A haka ya ɗaga wayar, sukayi gaisuwa irin wadda suka saba da taɓa firar yanda abubuwa ke tafiya, har yake shaida mashi yaso zuwa Abba ya hana shi, shi ya rasa gane wannan dalilin hana shi ɗin. Kwantar mashi da hankali Bilal ɗin ya kuma yi tare da cewa yayi haƙuri har ya sake samun sauƙi.
Yau ma dai saida ya tambayi yanayin karatun Suhan ɗin da ummr, ce mashi yayi suna nan ƙlau kaman koda yaushe, umma kuma tana cikin ƙoshin lafiya.
Jin hakan da yayi ne, ya san aminin nashi ba zai yi wasa da amanar da ya bar mashi ba, ya sanya shi amincewa nan suka saki firar suka kama wata, sun kai kusan rabin awa suna magana mai muhimmanci sannan suka kashe wayar suna masu ƙaunar juna a ransu.
Bai ma jin zai iya zuwa office ɗin, don haka gida kawai ya wuce kai tsaye, koda ummin ta ganshi ba irin tambayar da bata yi mashi ba, amman yayi mata banza dole ta haƙura ta ƙyale shi.
Kwanciya yayi abun duniya duk ya ishe shi, yanzu haka rabon da ya ko leƙa gidan nasu Al'ameen tin bayan dawowar su ƙasar, to me zai je yayo? Alhaji Mustapha baya ƙasar, ba kowa sai masu aiki a cikin gidan, ko ita Hajiya Kubran ba zama take yi ba, kullum tana cen wajen harkokin ta arziƙi sai daɗa bunƙasa yake yi.
Su mama Talatu an samu Abunda akeso, ana saka ta a wala, tashin hankalin su ɗaya ita da maree da har yanzu Al'ameen ɗin yaƙi ya dawo ƙasar balle su san yanda zasuyi su shawo kan matsalar tasu na yadda zasuyi su karkato da hankalin shi, koda kuwa da ƙarfin asiri ne, wannan daular basa jin zasu iya barin ta ta tafi a ɓagas.
Tinda Hajiya Sa'a da Hajiya Laila suka tabbatas ma da Hajiya Kubran cewar, su umman fa sun tafi tafiya ta har abada ba waiwaye, sai hankalin ta ya sake kwanciya, kuɗi masu yawa ta narka masu wai tukuici, yanzu tana jin ta bata da matsala sai guda ɗaya, yayi yazo ya fidda matar daya dace ya aura kawai, ƴar manyan guda ƴar wani ƙusa a gwamnati ko ɗan kasuwa, ta yadda za'a dinga labari a ƙawaye cewa ita surukar wance ce a ƙasar ta nigeria.
Saudat basa ƙasar ita da mijin ta, Nihal ce kaɗai, itama kullum tana gida, ganin mijin ba zama yake yi ba, data dawo daga wurin aiki gida take wucewa ko gidajen ƙawayen ta, sai ta muka tasha iska sannan ta koma gidan. Hakan ce ta fara sanyawa ƴan ƙananan maganganu tashi a family ɗin mijin nata har maganar ta koma kunnen shi, duk da suke sangartattu ƴaƴan masu dashi, hakan baya mashi daɗi, ai auren ta yake yi, yana da haƙƙin duk inda zata je ta sanar mashi koda kuwa ba zai barta ba.
Sun fara samun saɓani akan hakan, inda ta nuna mashi Sam hakan fa ba mai yiwuwa bane, tana da ƴan cin da zata iya aiwatar da komai batare da ya sani ba, tinda auren ta yayi ba siyen ta ba.
A haka ya ƙyale ta yana mai ƙudurce ɗaukar mataki domin kuwa shi fa Sam ba zai iya lamunta ba, ko ba komai ai yana kallon matayen abokan shi ba haka suke yi ba, kullum suna gida ko wurin aiki kawai, Amman ace mace kullum ta fita sai taje gidan su? Wata rana ma acen take kwana koda kuwa yana ƙasar? Kuma iyayen ta na kallon ta ba tare da sun saɓa ko tsawatar mata ba? Shi a gaskiya ba zai iya ɗaukar wannan rainin wayon ba, gashi ace mace bata iya komai ba, duk tabi gida ta cika da ƴan aiki maza da mata, duk da hakan ba wai baƙon shi bane ba, amman shi sam baya da ra'ayin masu aiki barkatai a cikin gida saboda halin tsaro na rayuwa.
*****************
Cikin Hafsat ya tasa inda Sadeeq ɗin ya maido ta nigeria ɗin yace ta zauna, saboda yana ji da cikin baya son dukkan abunda zai dame shi ko ya taɓa mashi lafiyar ɗa, to itama ɗin tafi son hakan, domin yanzu idan Kaga Hafsat ba zaka ce ita bace, tayi ɓulɓul duk da dama ita ɗin ba wai mai rama bace dama cen, fatar ta ta kuma haske da sheƙi, yanzu ta samu aiki da Federal Goverment, mijin nata shi ne ya sama mata, saboda rage zaman kaɗaicin.
Hafsat tasha kuka lokacin da taji labarin ɓatan su suhan ɗin, kuma tayi imanin ba banza ba, hakanan Umma ba zata buƙaci da su bar gidan ba, a daidai gaɓar da Suhan ɗin zata tafi makaranta. Tana addu'a Allah ya bayyana su, ya kuma saka masu zaluncin da aka yi masu a koda yaushe. Bata da kaɗai ci sosai, yanzu Alhaji Awwalun da Hajiya Zainab sun tattara sun dawo gidan da dangin Sadeeq ɗin suka basu nan Abuja ɗin, kaman yanda su kuma kamfann Al'ameen ɗin suka ɗauki matasan da aka alƙauranta masu aiki daga cikin dangin sadeeq ɗin.
Hafsat ɗin na zaune da dangin mijin ta lafiya, kowa na son ta yana yabonta, to su ɗinma mutanen kirki ne, sun san haƙƙin ɗan adam, masalan ma ita da take mata ga ɗan uwansu, suna mata kallon kaman ɗan uwan nasu duk da sun kasance sun fi su Hafsat ɗin komai hakan baisa suke nuna mata sun fita ba, ko kuma wariyar launin fata.
*****************
Haka rayuwa ta dinga garawa,awanni sun shuɗe, kwanaki sun shuɗe, makonni sun shuɗe, gashi har muna fuskantar wata biyu da zuwa makaranta, karatu nakeyi ba ji ba gani, duk da yanzu na fahimci dukkan Abunda Sir, Salim yake yi mani da biyu yake yin shi, tinda sau da dama zaka ji labari na tashi wai ni budurwar shi ce, babu Abunda ke shiga tsakanin mu in ka ɗauke taimako wani lokacin da kuma ƴar fira ta barkwanci haka, to nidai ta ɓangare na babu Abunda zan iya cewa ina ji game dashi, duk da yake kasancewar shi mai barkwanci da yawan ban dariya, bayada matsala da kowa da komai, saidai Abunda na kula, ki dai baya tare da matar shi, ko kuma baya jin daɗin ta ne, domin baya yadda ya bani labarin ta, kullum dai labarin bai wuce na Ammin shi ko kuma na Sholy da Usee, to nima nafi son hakan tinda sha'ani ne na iyali.
Har da Ammin shi ya haɗa ni na gaida ta, yanda naji muryar ta mai sanyi sosai, da yanda ta amsa mani kaman zata rungume ni cikin wayar hakan yayi mani daɗi, ashe a duniyar nan akwai wanda zai soni ya tattashe ni kaman yanda Sir, Salim da mahaifiyar shi suke yi, tin kwanaki da yaje gida, sha tara ta arziƙi da kuɗi sosai ta bashi ya kawo mani, da kam bazan amsa ba, har saida ya kira ta, aiko tace ya bani wayar, ya kuwa bani ta hau faɗa, wai ashe ban ɗauke ta uwa ba, da har zata bani abu inƙi ƙarba, haƙuri na shiga bata gami da yi mata godiya.
Kewar ummata ta addabeni sosai, ji nake kaman in buɗe ido in ganta a inda nake.
Ban ƙwauron baki ba, na faɗa ma Sir Salim kaman yanda ya zama abokin shawara ta a yanzu, duk yanda zai yi ya shiga jikina yayi, ina jinshi kaman ɗan uwanka yanzu uwa ɗaya uba ɗaya, masalan da na kula dashi kamilin mutum ne, ko a makarantar kaf an bashi shaida, ba dai kiji ance yana kula mata ko hulɗa dasu ba, duk da an sanshi da barkwanci, wanda barkwancin ma ne ya sanya ni sakin jiki dashi ba tare da na kula ba.
Kaf makarantar babu wacce zan nuna ince itace ƙawa ta ko aboki ya ta, saidai wanda muke ɗan gaisa wa dasu sama sama sai kuma ƴan ɗakin namu da suma ba hayaniya ce ta sha masu kai ba, kowa karatun shi yake yi hankali kwance.
Haƙuri ya bani gami da cewa insha Allah zanga ummata very soon, nidai kawai inyi karatu, ban da matsalar kayan abinci ko kuɗi, duk Ammin Sir, Salim ta aiko mani dasu masu yawa, tin bayan daya bata labarin gidan namu, da kuma ƴar fahimtar da yayi cewa karatun dai ne nakeso inyi aman ba tare da muna da ƙarfin hakan ba.
To itama dai burin Hajiya Khaltum ɗin shine dai yaron nata ya samu ya daɗa wani auren, ko hakan zai sa Ma'un ta cenza hali, domin Sam basa jin daɗin ta, mace ce wadda zamu iya cewa rako mata tayi. Sam bata da Sirrin kanta, batasan yanda zata zauna da kowa lafiya ba, ga bala'n kishi kaman zata mutu, kasancewar mijin ta lecturer, ya sanya ta sanya ana binciken shi ta bayan fage ba tare da ya sani ba.
Masifar ta tayi yawa, saboda haka ne, ko lokacin daya koma gidan ta same shi da maganar cewa ta san dukkan Abunda yake aikatawa a makarantar na neman wata yarinya, Sam bai ɓoye mata ba, yace aure yake so ya ƙara, aikuwa masifa da bala'i babu wanda ba'a sha ba, har barin gidan nashi tayi, ta kuma bar mashi yaran, hakan ce ta sanya ya kwashe su ya kai ma Ammin shi, to ita ɗin ba mai masifa bace, ce mashi tayi yake ya lallashi matar shi, da taga ya kafe ne akan ba zai je ba, sai tace mashi ya tafiyar shi, idan Ma'un ta huce ta dawo an maida mata yaran.
Haka kuwa aka yi ya sake juyo ma da Suhan sha tara ta arziƙi daga Ammin tashi, bai ƙara so ba saida ya tsaya ya taho da Ummana domin tazo taga inda nake karatu.
Yanzu kam ta fara yarda da Al'amarin yaron, tin bayan da suna cikin mota ya haɗa ta da Ammin shi suka gaisa sosai, har tana ce mata sai ta kawo mata ziyara har gida. Murmushi ummata tayi tana sake yi mata godiya da ɗawainiya da yaron nata yake yi da Suhan, sannan tace mata sai tazo, sallama sukayi suka kashe wayar, da ɗan murmushi ta miƙa ma Sir, Salim wayar da yake cen gaba yana driving, ita kuma ita da Hajjo a bayan motar har zuwa shigar su makarantar tamu.
Kwatsam sai ga ummata daidai lokacin da na fito da niyyar zuwa masallaci sallah, aikuwa da gudu na ruga na rungume ta, kwalla na shatata a samn fuska ta, janye jikin ta tayi tana girgiza mani kai, Hajjo na gaida, gami da ɗan kallon Sir, Salim da ya kafe ni da mayatattun idanun shi, da a yanzu na fara jin nauyin su a kaina bansan dalili ba kuma.
"Zamuje ɗaki Sir, Nagode Kwarai" Abunda na faɗa kenan ina mai sauke kwayar idanuna ƙasa. Ɗan jinjina mani kai yayi yana mai juyawa ya shige motar shi gami da barin wurin bayan yayi masu umma sallama akan cewa zai je ya dawo.
Haka muka ranka ya har ɗakin namu. Ba kowa ciki duk suna wurin lectures, rasa inda zan ajiye su umma nayi, salla suka fara yi, ni kuma na fara nema masu Abunda zasu ci. Wata yarinya ce tayi sallama da manyan ledoji a hannun ta ta miƙo mani wai inji Sir, Salim.
Amsa nayi ina mai godiya gami da buɗe ledojin, take away ne manya, shinkafa ce jalop da taji kayan haɗi, sai manyan kaji guda biyu da lemuna masu sanyi, ai sai na kashe stove ɗin ba jawo plate na juye masu gami da sanya masu chokulla na ɗauko cups na shan lemon na ajiye masu.
Basu ɓata lokaci ba wajen cin abincin, so suke su juya saboda kada suyi dare. Nasiha da wa'azi da jan hankali babu wanda ban sha ba, nan umma ta kawo kuɗi dubu goma ta bani tana mai ƙara bani haƙuri, akan cewa yanzu taga wuri akai akai idan ta ɗan samu wani abu zata dinga zuwa tana kawo mani insha Allah.
A haka suka gama, na kira Sir Salim ɗin, cewa yayi yana waje yana jiran su. Kaman kar mu rabu haka naji, aiko saida bayi kuka sosai har na ƙaryar ma da ummata zuciya, itama saida tayi kwalla Hajjo ce taje bamu baki, haka na juye masu sauran naman da lemon nace ko Malam ne sa kai mawa, aiko Hajjon taji daɗi sosai ta yadda ban manta malam ba, to nikau ina zan manta mahaifi na? Tinda yanzu shine nake ma kallon uba a wuri na.
Har bakin mota na raka su, da kanshi ya fito ya buɗe ma ummata ni kuma na buɗe ma Hajjo, bayan sun shiga ne ya tsattsare ni da idanu wa alamar tuhumar kuka na menene nakeyi? Girgiza mani kai ya shiga yi, alamar kar nayi kuka, ya shiga motar yana mani inkiyar zai dawo.
A haka ina ɗaga masu hannu har motar ta fuxe daga harabar makarantar, juyawa nayi jiki ba kwari, zuwa ɗakin namu. Kuka nasha kaman ba gobe, ummata duk wahala ta sanya ta ƙara tsufa, kaman ba ita ba, Allah ya sani tausayn kanmu da kanmu ya kama ni, dole in maida hankali inyi karatu ko hakan zai zama silar fitar mu a wannan ƙangin rayuwar.
Saida ya tabbatas ya sanya su mota mai kyau ya biya kuɗin motar, sannan ya basu wani abu yace su riƙe su sha ruwa a hanya, ummata ƙin karɓa tayi, sai Hajjo ce ta sanya hannu ta karɓa, suka sake jaddada godiya, ummata ta sake bashi amana, sannan ya juyo ya dawo makarantar.
Kirana yayi na fita, nan ya shiga sake lallashi na, da yake mutum ne shi mai barkwanci, sai gashi bamu rabu ba, saida ya sanya ni dariya sosai da nishaɗi. Sannan ya kira Ammin shi da yaran shi muka gaisa yana ce masu ga Auntyn su su gaida ta suka hau tsalle suna mani gwarancin da bazan iya ganewa ba, da yake Ma'un bata koma gidan ba har yanzu, ita kuma Ammi taƙi zuwa, tace ai tinda babu abunda aka yi mata idan ta huta ta koma da kanta. A haka mukayi sallama ta kashe wayar, ƙaunar yarinyar na malala a cikin zuciyar ta, ga dukkan alamu yanzu ne yaron nata ya samu mace mai hankali da natsuwa wadda zata iya kula mashi da gidan shi da yaran shi, don ita talaucin su ba matsala bane a wurin ta, tinda ta san mai duka ne ke yin komai.
Haka rayuwa take tafiya, ɗan adam ba don ya kula ba, saidai kawai yaji shi a cikin kabari. Gashi har zamu fara semester exam, karatu ya ɗauko zafi sosai, don ma Sir Salim na taimaka mani sosai, lectures take mani a duk lokacin da muke free bama komai, kuma ina ganewa sosai da sosai, kwatsam sai ga Ma'u a makarantar mu, lokacin muna zaune ta cen baya inda ɗalibai ke zaman karatu.
Mun duƙufa muna ta karatu sai naji an ja hijab ɗita ta baya sosai kaman za'a shaƙe ni, aiko da hanzari na ɗaga domin ganin ko wacece, ganin bansan fuskar ba, sai na zare hijab ɗin baki ɗaya na sakar mata ita a hannu, gami da miƙewa na fuskan ce ta ina mai cewa "Baiwar Allah lafiya kuwa? Me na aikata maki haka da zafi da kike beman shaƙe mani wuya?"
Da hannu ta nuna mani Sir, Salim wanda ya riga ya miƙe mamaki ya kama shi har ya gaza cewa komai
"Me ya haɗa ki da mijina?"
Ta jefo mani tambaya cikin hargagi ta nayi tana jijjiga jiki.
Kallona na maida kan Sir Salim da har yanzu ya gaza cewa komai
"Au Malam? To ai gashi tsaye shi zaki tambaya ba wai ni ba" na maida mata da amsa cikin son kawar da tsoron ta daga zuciya ta.
"Au dama kece yarinyar da akace kinbliƙe mashi kin hana shi saƙat a makaranta?" irin ku dama ba karatun ke kawo ku ba, neman mazan mutane kuke zuwa nan yi.... "
" Asma'u"
Sir, Salim ya katse ta cikin ɗaga murya yayi kanta kaman zai bugeta.
Sai kuma ya dakata yana faɗin "Me kike yi ne haka? Me ya kawo ki nan makarantar? Kinzo ne ki ɗaga mani hankali ne? Ki kiyaye ni fa, da izinin wa kika zo?"
"To dama da izinin wa kake so nazo ne? Ko har yanzu da bana zaune gidan ka nema kake yi in nemi izinin ka idan zan fita?"
Nikam sun ma ɗaure mani kai wallahi, gani dai tsaye ba hijab jikina yana hannun ta duk ta cukuikuye shi, inda Allah ma ya taimake ni kayan jikina doguwar riga ce mai faɗi, sai na sanya hannu na warware gyalenta ɗana ɗaura bisa kaina.
" Eh ko da baki gidana, ai da aure na a saman kanki, idan baki sani ba yanzu ki sani, kuma wannan ita ce yarinyar da kikaji labari, kuma ki sani ba liƙe man tayi ba, ba naniƙe mani tayi ba, hasali ma nine na liƙe mata na naniƙe mata, Abunda nake so ki sani, da batasan me ke faruwa ba, batasan dalilin da yasa nake tare da ita ba, Amman yanzu kinja zata sani. Wannan ita ce Suhan wadda kikaji labarin ina nema, kuma wadda na faɗa maki cen baya cewa *Son ta nakeyi, kuma auren ta zanyi har Ammi ma ta san da zancen* "
Cikin matuƙar tashin hankali da jin kalaman Sie, Salim ga matar tashi na ɗago idanu ina binsu da kallo, ga kuma student ta duk suka zagaye mu suna kallon mu, sai ƙus-ƙus suke yi, waɗanda dama cen sun jima suna son Sir Salim ɗin murna suka fara yi, suna gode ma Allah da basu ne hakan ta faru dasu ba.
"Ai wallahi ko wacece ta san da zancen ba Ammi ba, bata da hurumi a gidana, baka isa ba, wallahi kayi kaɗan Salim, ni zaka tozarta ka wulaƙanta kan wannan ƴar abun?" ta faɗa tana mai nuno ni da hannun da hijab ɗin tawa yake kai, sannan ta ɗora da faɗin. "Wuuu Amman dai wallahi kaji kunya, inaso ka sani wallahi tallahi idan ta kuskura ta shigo gida na, sai ta kwashi kashin ta a hannu, kuma mu zuba mu gani shege ka fasa" ta faɗa tana mai maida kallon ta bisa kaina da nake tsaye kwalla ta cika man ido taf, Amman na kasa barin ta ta zuba, saboda gudun raini daga wurin ta, jefo mani hijab ɗita tayi tana mai kyasta mani yatsu alamun in kiyaye, sannan ta juya a sukwane ta nufi motar ta, ta shiga ta fisge ta da matsanancin gudu tabar wurin.
Rasa abund zanyi nayi, saidai na zuƙunna na shiga tattara litattafai na, da kayan karatu na, na ɗauki hijab ɗita da duk ta duƙunƙune ta, na juya da niyyar barin wurin.
Gabana ya sha, haƙuri ya fara bani, girgiza mashi kai na shiga yi alamun babu komai, wani tsumammen kuka yana mai taho mani, duk kunya ta gama kama ni, masalan da ma abun ya faru akan idon ɗalibai, yanzu makaran ta zata ɗauka, yanzu zan fara rashin sukuni a makaranta, ai bansan haka halin matar shi yake ba, da ko alama ma bazan yadda in saki jiki dashi haka ba sosai.
Zagaye shi nayi da ɗan gudu na, na nufi hanyar da zata sada ni da ɗakin namu, yayin da na bar shi na tsaye sororai abun duniya duk ya dame shi.
Dole ne kuwa yau yayi ma abun tufkar hanci, dole ne ya dakatar da kuma faruwar hakan, shima a matuƙar zuciye ya shiga taka wa kaman ingarmn doki zuwa wajen da motar tashi take ajiye ya shiga gami da fizgar ta kaman zai taka mutane haka yabar makarantar da matuƙar ɓacin rai.
Nasha kuka na, ƴan ɗakin mu na bani baki, lallai sunga Abunda ya faru dukan su, domin an taru sosai a wurin, saboda haka ne ma suka bani shawara da in ɗan ja jiki da Sir, Salim indai ina so in tsira da mutumci na, saidai fa har yanzu mamakin kalaman shi basu sakeni ba, yaushe ne ya fara sona har haka da har yake cewa Ammin shi ta sani? Yaushe yaje masu da maganar son aurena ni Suhan? Anya kuwa ba ɓatan kalamai yayi ba kuwa?
Da haka na zame na kwanta idanuna rufe ruf, babu abunda ke kai komo a ƙwalwa ta illa iyaka maganar da ya faɗa ma Matar tashi.
Wayata ce ta ɗauki tsuwwa, sunan Ammi na gani a bisa wayar, sai na Gaza ɗagawa, illa ma wani sabon kukan daya zo mani, gashi ummata bata da waya, koma tana da ita ƙauyen babu service da ko ita ce zan kira ta inji muryar ta ko naji sauƙi.
Daga wannan sai wannan, na rabu da cen da duk abunda ya shafi cen, sai ga kuma wata ta kunno kai nan, ya zanyi da rayuwa ta? Ya zanyi da wannan al'amari dake faruwa dani ne?
Karo na barkatai kenan da tinanin Ya Ameen ke faɗi mani a cikin ƴan kwanaki nan, tinani na ne ya tsaya cek, lokacin da Fuskar Al'ameen ɗin da yanayin shi suka faɗi mani a rai, ko yana ina?ko a wanne hali yake yanzu ciki? Ko ne yake yi? Ko ya yaji lokacin da ya samu labarin tafiyar mu? Wani abu Naji yana kwarara a dukkanin ɓargon jikina, malala yake yi zuwa dukkanin wani ɓangare na jikina.
Ai tuni na fara rawar sanyi, zazzaɓi mai zafi ya lulluɓe ni, wani Al'amari nake ji ayau dana tuna da jigkn Rayuwar tamu a da......
Ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba a haka....
~Oum-Deedat ce~
[10/2, 1:28 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
*Ahmad Deedat yana gaida duk masoya shi, da masu cewa suna so shi, da masu cewa sunan shi na burge su, da masu cewa a basu shi, da masu cewa sun kama ma ɗiyar su, da masu cewa Allah ya basu irin shi. To duka dai ina maku fatan alkhairi, da fatan nasara a rayuwa. Mungode kwarai da gaske Allah ya bar ƙauna da zumunci. AMEEN YA RAB.*
*Page ~36~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Juye juye yake ta faman yi, ya rasa abunda ke mashi daɗi a duniyar nan, shi fa gabaki ɗaya hankalin shi ya karkata zuwa ga ƙasar tashi, ga wani al'amari cen ƙasan zuciyar shi dake ta faman taso mashi.
A hankali ya sanya hannu ya ɗauko wayar tashi dake bisa side drower. Gallerry ya shiga, tini hotunan bikin su Saudat suka bayyana.
A hankali a hankali yake bin hotunan da kallo har yazo kan daidai nasu, lokacin da yake riƙe da ita ranar yinin biki.
Hoton ya ɗauku iya ɗaukuwa, sunyi matuƙar kyau kaman wasu couples, ɗan yatsan shi ya sanya yana shafa fuskar wayar, a hankali yake sauke numfashi, ya kamata ya san halin da take ciki, sai yanzu ne ya gane ashe maganar aurenta da yayi, maganar son ta da yace yanayi a cikin wasa ashe ba wasa bane, zahiri ne, shi mai yasa ma bai fahimta ba a duk tsawon lokacin da ya kwashe da ita a rayuwa.
Minimize yayi tare da shiga contact, ya san wa zai kira, ya san inda zaiji haƙiƙanin abunda yake aukuwa a rayuwar suhan ɗin dama ummata tata. Ya kula sarai da Bilal akwai abunda yake ɓoye mashi shi da Dad ɗinshi, to koma dai miye yau zaiji, yau ne ranar da ya yanke ma kanshi sanin koma meke faruwa, faɗuwar gaban shi tazo ƙarshe yau da izinin Allah.
Daidai kan sunan ta yaja ya tsaya, kiranta yake son yi, amman hannuwan shi sun gaza latso number ɗin. Shahada yayi wajen kiran, saidai zuciyar shi kaman zata tsago ƙirjinshi ta fito saboda tsabar dukan da takeyi.
Bai aune ba yana ta faman tunani, sai jin muryar ta yayi ta cen ɓangaren tana sallama.
Hankalin shi ya maida kacokam kan wayar, yana mai amsa mata sallamar da takeyi mashi
"Yaya ina kwana ya ƙarfin jiki?"
Bai ƙasa a guiwa ba wajen bata amsa, duk da kasancewar shi miskili na bugawa a mujalla, sai gashi yau yana rawar baki wajen amsa ma ƙanwar tashi.
"Jiki Alhamdulillahi Hafsat Ya Sadeeq ɗin ya kuka koma gida kuma?"
"Lafiya Lau Yaya, to Allah ya ƙaro sauƙi". Ta faɗa mamaki fal cikin ranta jin wai yau Ya Ameen ne ya kira ta a waya. Katse mata tunanin yayi wajen cewa
"Hafsat wata magana na kira ki muyi cikin sirri, amman inaso ki taimaka mani wajen sanar dani gaskiya, ke kaɗai ce na san ba zaki ɓoyeman komai ba gudun cutar da Ƙawar taki" bai jira cewar ta ba ya cigaba da cewa "Maganar ƙawarki Suhana da kuma ummanta, kwana biyu na bar jin ta, duk da Bilal ya faɗa man tana makaranta Umman kuma tana cikin ƙoshin lafiya, saidai zuciya ta ta gaza yarda da hakan, nakan gazgata shi a duk lokuttan da yake sanar dani hakan, sai nake ganin kaman akwai wani abu da yake binne mani ne shida Dad, shine dalilin da yasa ke na kira ki domin ki bani cikakken bayani, kuma ki turo mani number ɗinta saboda in nemeta"
Ɗan shiru yaji tayi ta cen ɓangaren, ga dukkan alamu dai ta shiga komar tunani ne, ga mamakin shi cen kuma sai yaji ta fashe da kuka ta kashe wayar.
Ai bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba, jikin sh na ɓari, "Hello Hello Hafsat" Abunda ya cigaba da cewa kenan, duk da ya san ba fa lallai bane ta amsa mashi ba, tinda ta riga ta kashe wayar.
A fusace yake taka wa ya shiga kai komo a tsakiyar tanƙamemen falon da babu komai ciki daga gado sai mirror da labulaye, ko sif ɗin ta cikin bango ce, ba wani hayaniya mai yawa a cikin ɗakin.
Hannun shi ya zura cikin sumar shi mai taushi da santsi yana shafa kan a hankali, yayin da gudan ya dafe ƙugu dashi a haka yake ta faman safa da marwa, idan ya gaji sai ya dunƙule hannu ya kaima iska naushi.
"Oooops Ooops Bilal why? Meyasa kayi haka? Me yasa ka ɓoye mani da matsala ne? MOOOOOOM Mom, Mom tabbas koma me ya faru da sanya hannun ki, Dad why? Meyasa ka taimaka wajen ɓoyeman komai ne? Na cencenci haka kuwa daga gareku?
Cikin hanzari ya jawo jikkar shi ya shiga ɗibar kaya daga wardroop ɗin yana cusawa, ba tare da ya tsaya ma shirya su ba.
Abie yayi ma waya akan ya baro Office ɗin yazo ya same shi gida. Da mamaki Abie ɗin ya taho akan kiran gaggawa da yayan nashi keyi mashi.
A tsaye ya tadda shi kaman zai sanya gudu, da hanzari ya ƙara so yana mai tambayar yayan nashi ko lafiya?
"Abie akwai wani muhimmin aiki ne daya taso mani a nigeria, so bana so kowa ya san na tafi har Dad da Mom kai ko Bilal bana so kowa ya sani har inje in dawo, saboda idan suka sani ba zasu barni bane" ya ƙarshe yana mai ɗaukar makullin mota gami da cewa "Muje ka kai ni Airport yanzu ka dawo da motar"
"Amma yaya jiya mukayi waya da Bilal bai ce mani akwai wani aiki ba da har zai sa ka tafi, bayan kasan Dad baya son tafiyar taka har sai ka ƙara jin sauƙi"
A sukwane ya juyo gami da dakatar da Abie ɗin ta hanyar ɗaga mashi hannu
"That Is what i said, koma minene ayau ɗinnan zan bar ƙasar nan insha Allah, idan Kaga dama ka faɗa ma koma waye ne kada kaja bakinka kayi shiru"
Yana gama faɗin haka ya sake jan jikkar shi ya fice daga ɗakin, to shima dai Abie ɗin baya da zaɓi, illa bin bayan shi yayi ya iske shi yana saka jikka mazaunin baya, gami da cilla ma Abie ɗin ɗan makullin. Caɓewa yayi sannan ya shiga shima ya zauna bayan Ya Ameen ɗin ya zauna, ya harba motar bisa titin da zai sada su da Airport ɗin.....
Bai sha wahala ba, kasancewar lokaci zuwa lokaci ana mashi renewing ɗin bisa ɗinshi, hakan ce ta sanya ticket kawai ya yanka nan da rabin sa'a jirgin nasu zai ɗaga.
Abie bai bar Airport ɗin ba, saida yaga tashin jirgin su Al'ameen ɗin sannan ya juya zuwa office zuciyar shi na ta saƙa mashi tana warwarewa, saidai yayi imanin babu wanda zai faɗa ma wannan tafiyar ta ɗan uwan nashi, kai koda kuwa ace Dad ne zai kira ya tambaya ba zai taɓ bari ya fahimci Yayan nashi baya ƙasar ba.
(To gadai su Al'ameen an nufi nigeria ko ya zata kaya kuma?)
*******************
A haka na kwana juye juye, Sam bana da walwala, ina ganin kiran Sir Salim na shigowa a wayar tawa, Amman na kasa ɗauka, so nake in kiyaye shi, bana so in sake komawa cikin wata matsala daban kuma bayan wadda na baro. Tabbas Sir Salim bai ɓoyeman ba akan cewa yana da mata, to saidai bai sanar dani halin ta ko kuma yadda take ba, bai faɗa man zata iya aikata hakan ba, tin farko ma da ban saki jiki dashi hakan ba.
Ina kallo text ɗinshi ya shigo wayar tawa, amman na kasa buɗewa balle in karanta inga abunda ya ƙunsa. A haka har gari ya waye nayi shiri na zuwa darasi, Amman jikina a sanyaye yake ƙwarai matuƙa, duk inda na gitta da kallo ake bina hakan ce ta sanya ni komawa ɗaki na ɗauko niƙab na sanya a saman fuska ta, gudun mayen kallo daga ɗalibai, kunya duk ta riga ta gama cika ni.
Ba don Jarabawar da zamu fara ba, to da bana jin ma idan zan iya zuwa wata lecture ayau saboda abunda ya faru jiya, to saidai koda ma ace na zauna ne, babu abunda zan iya taɓukawa sai tinane tinane, tinda ƴan ɗakin mu basa wasa da karatu ba wani zama muke muyi ta fira ba, karatu shine kashi 80 a cikin ɗari na firar tamu.
Har muka gama lecture ta farko muka shiga ta biyu, itama muka gama, ban kuma jin ɗuriyar Sir Salim ba, ƙarfe huɗu ne bayan mun fito masallaci muka nufi hall ɗin domin ɗaukar lecture ta 4-6. Saidai kafin in idasa shiga hall ɗin wata budurwa ta ƙara so tana tambaya ta wai nice Suhan Moh'd?
Da Kai na amsa mata, saboda magana ma yau mai ƙarfi gagara ta takeyi, da hannu itama ta nuna mani wata dunƙulalliyar mota jikin ta wata mata ce tsaye, saidai da yake da ƴar tazara tsakanin mu, bana iya shaida fuskar ta ko kuma ta maza guda biyu da suke tare da ita, sannan ta shiga cewa "Waccen matar ce tace in kira mata ke" tana gama faɗin haka ta sanya kai tayi wucewar ta.
Ɗan jim nayi kaman ba zani ba, sai kuma na juya a hankali na shiga taka wa ina nufar wurin, mota ce mai masifar kyau sabuwa dal Ash colour, matar da take jikin motar ta jingina bayan ta jikin motar, hannun ta ɗaya jikka ce da take riƙe da ita ƴar madaidaiciya, sai hannun ta da yasha jan ƙunshi cije yake taf da zobuna da awarwaron gold riƙe take da waya tana latsawa, kaf hankalin ta yana a kaina da nake nufi ta, hakan ce ta sanya bugun zuciya ta ya kuma tsananta, lura da nayi cewa Sir Salim ne yake tsaye ta gefen ta, sai wani mutum da kaman dreba ne yake tsaye cen gefe ya jingina shima da motar. Duk kansu murmushi ne ɗauke akan fuskokin su.
Hakan ce ta sanya ni sadda kaina ƙasa, matar tayi masifar kama da Sir Salim, saidai ita ɗin fara ce tas, ga dogon hanci a bisa fuskar ta, ga dukkan amu zata yi sauƙin hali.
Da sallama ɗauke a bakina na ƙarasa ina mai ɗan durƙusawa na shiga gaida ta, dukka hannuwan ta guda biyu ta sanya ta ɗagoni tana mai ƙara ni bisa jikin ta, ni sai ma Naji wani banbaraƙwai wallahi, murmushi sosai saman fuskar ta, a kunyace na maida kallona kan fuskar Sir Salim, aiko ya kashe man ido ɗaya cikin zaulaya, gami da ɗan yiman ƙaramin gwalo.
Zame jikina nayi gefe a hankali ina mai sake duƙar da kaina ƙasa haɗi da fara wasa da yatsun hannuwa na da suke samɓal farare tas dasu.
Ɗan kallon ta ta kai kan Sir Salim ɗin tana cewa "Marar kunya ka wani tsura mana idanu kana kallon mu, ku jira mu nan mu shiga daga ciki mu fito ko"
Jin hakan da nayi ne ya sanya ni juyawa ina mai nufar hanyar da zata sada mu da ɗakin namu.
Itama bina ta shiga yi daga baya, cikin tafiya irin ta ƴan gayu masu ji da kansu, jikin ta sanye da wani irin ɗanyen boyel mara zane da akayi ma aikin duwatsu dukan shi, kai kace lace ne, sai walwali yakeyi , kai da gani ba sai an faɗa maka ba yasha kuɗi, gyalen boyel ɗinne a jikin ta shima ba zanen komai sai cin bakin duwatsu da akayi mashi shima irin na kayan. A haka har muka isa ɗakin, na sanya hannu na buɗe ina mai ce mata bismilla.
Mun tadda Khadeeja Da Raihana abokan zaman ɗakin nawa, ganin nayi baƙuwa ne ya sanya suka tattara littattafan su gami da gaida ta suka wuce, cikin sakin fuska itama ta amsa da maganar ta kalar ta ƴan gayu.
Bakin gadona da yasha gyara na nuna mata, ina mai jawo kwalin lemo na ɗauko ɗaya haɗi da cup, shine kaɗai abunda nake dashi da zan iya bata a take, saboda yau banyi abinci ba, a capteria nima naci abinci ɗazu.
Sake gaida ta nayi, ga mamaki na itama a sake ta amsa mani, tana mai ɗaukar kofin lemon ta kai bakin ta tasha duk da babu sanyi, ban taɓa tinanin cewa zata iya sha ba, saboda ga dukkan alamu naira ta jiƙa matar kai bama sai ance maka ba.
Da murmushi ta fara kallona tana cewa "To Suhan ki cire niƙab ɗin ko sai muga juna da kyau, sauri nakeyi akwai maganar da ta kawo ni, gashi marece yayi ko"
A kunyace na duƙar da kai, ina mai zare niƙab ɗin daga inda nake zaune ƙasa na shimfiɗa dardumar sallah.
"Waw Masha Allah Laƙuwata Illa Billah" Abunda ta faɗa kenan tana mai tasowa ta sanya hannu ta kamoni ta miƙar tsaye, sannan ta shiga jana har zuwa bisa gadon kusa da inda take zaune.
"Ɗiyata kina da kyau masha Allah, ga kunya, yanzu ne na tabbatar Son ya samu kalar matar da yake da buri, nima nake da burin ta zama suruka ta, ina son dukkanin abunda Salim yake so, matuƙar bai saɓa ma shari'ar musulunci ba, shi ɗin yaro ne mai biyayya da kawaici, duk da yake mai yawan tsokana da wasa. Abunda matar shi tazo jiya tayi maki ne ya sanya ni tasowa takanas saboda hakan, kuma in baki haƙuri abisa kuskuren ta, kada ki hukunta yarona saboda laifin matar shi, kuma ina fatan hakan bai tsorata ki ba, saboda ita yarinya ce mai hargagi, sai daga baya tazo kuma tayi nadama, bance maki bata da sauƙi ba, to saidai wasu halayya dake gareta da bata yi daidai da ra'ayin mu ba daga ni har shi Salim ɗin, yana neman aure ne ba don ya gaza samun komai ba sai don ke ɗin ya gani kuma kin kwanta mashi, Amman yace yana buƙatar ayau ɗinnan naje na nema nashi izini a wurin mahaifiyar ki, idan ta amince ina fatan kema zaki so mu ki yarda damu kaman yanda muma mukayi maki"
Ta ƙarashe tana mai leƙen fuska ta da take ƙasa, har yanzu hannuna yana cikin nata taƙi ta sake.
Sai naji dukkanin ɓacin raina kaso 80 ya fice, har bansan lokacin da na sauke ƴar ajiyar zuciya ba, ina mai ɗan murmushi gami da jawo gefen hijab ɗita na rufe fuska ta.
Hakan da nayi ya alamta mata cewa na haƙura kuma na yarda da yaron nata.
Godiya ta shiga zubawa tana mai cewa "Masha Allah ɗiyata, da fatan zaki yafi yaron nawa da matar tashi, abisa kuskuren da suka aikata maki jiya, idan ma harda mai laifi to Ma'un ce tinda ita ta biyo ki har inda kike, kuma ni nama yi mamakin da har ta gano komai, duk da naji labarin akwai mai ɗaukar mata rahoto anan makarantar, saboda haka sai ki kiyaye, kuma kiyi duk yanda zakiyi ganin cewa wani bai shiga tsakanin ki da yaron nawa ba, shi yaro ne mai yawan kyautata ma wanda suke tare dashi, ina faɗa maki haka ne ba don yana ɗanɗa na ba, aa sai don ina maku sha'awar zama tare ne. Bari in wuce sai na kuma dawowa, daganan gidan ku wajen umman ki zamuje, acen ma zan kwana sai gobe in wuce"
Ta faɗi hakan ne tana mai miƙewa ta ɗauki jikkar ta, hankalin ta kwance, ga fara'a har yanzu saman fuskar ta, tabbas yanzu ne Salim ya samu mata ɗaya da ɗaya, yanzu ne take tunanin zai samu kwanciyar hankali da walwala a tattare dashi, tabbas ta shaida cewa kuɗi ko mulki basa sanya kwanciyar hankali muddin baka tare da iyali mai natsuwa da sanin ya kamata.
Har wajen mota na raka ta, wannan karon Sir Salim ɗin yana gefe shida wasu ɗalibai suna magana, dreban kuma ya buɗe gaban motar ya shiga sai faman gyangyaɗi yake.
Hangomu da yayi ne tafe hannuwa na riƙe cikin na umman tashi ya sanya shi sakin murmushi, sannan ya sallama ɗaliban da suka same shi akan yayi masu afuwa basu samu rubuta accessment nashi da yayi jiya ba.
Ƙarasowa yayi yana mai faɗin
"Lallai Ammi naga alama yarinyar nan rana neman ƙwace man fada, gaskiya ba zan yarda ba, da sakyal gaskiya"
Ya faɗa cike da shagwaba, ni sai a ya bani kunya, ɗan murmushi nayi na gefen baki, ina mai yima Ammin sallama da ya buɗe mata bayan motar ta zauna, tana mai miƙe mani fara ƙar ɗin emvelop, ban amsa ba, sai shine ya amsa yana mai godiya cikin zaulaya, ga dukkan alamu ya saba zaulayr Ammin tashi kuma tana ji dashi matuƙa gaya.
"Ka kiyayeni fa Son, na faɗa maka kada kayi ƙoƙarin shiga tsakani. Suhan jeki kiyi Lecture ɗinki mun sanya ki makara, sai munyi waya"
Ta faɗa tana mai jan murfin ƙofar ta rufe
Juyawa nayi ina mai mata sallama gami da ɗaga mata hannu, ban bi ta kan emvelop ɗin da ta bani ba, wadda Sir Salim ɗin ya zura ta cikin Aljihu gami da zagayawa ya shiga kujerar mai zaman banza dreban yaja motar suka ɗaga.
A haka na isa hall ɗin, raina fari tas, ko ba komai matar ta nuna mani ƙauna, ta nuna mani zallar soyayya kuma ta soni da yaron nata, ba kaman hajiya Kubra ba, mai ƙyamatar mu, mai zallan son zuciya, mai ɗaukar talaka ba a bakin komai ba, zullumi na ɗaya da tace wai gidan mu wurin ummata zata kwana, gashi ba waya balle inyi maza in kira umman tawa asamu a shirya mata wani abu ko kuma a san inda za'a ajiye ta ta kwana.
Da haka har aka tashi lecture ɗin na koma ɗaki su Raihana ɗinne masu ceman gaskiya sun yaba da kirkin matar ganin yanda ta amsa masu fuska sake duk da ita ɗin wata ce ga dukkan alamu.
Wannan ne ya sanya ranar nayi kwanan farin ciki da na rabu dayin irin shi a rayuwa da tin bayan shuɗaɗɗen lokaci a gidan su Ya Ameen ɗin. Ban kuma jin ɗuriyar Sir Salim ba har nayi bacci ina ta faman tinane tinane, yanzu fa suna nufin Sir Salim shine mijin da zan aura nan da wani lokaci ƙanƙani kenan? Ya zama saurayi na kenan a karon farko a rayuwa ta, wata irin kunyar shi ce ke kwarara a sassn jikin nawa duk kuwa da cewa baya a tare dani.
Su ma su Raihanan da murmushi suka dinga bina, ganin da sukayi ina cikin farin ciki, duk sai suka ji daɗi, kasancewar kanmu a haɗe yake babu wanda ke shiga hidimr wani gudun samun saɓani.
****************
Kai tsaye gidan hafsat ya nufa, ko gida ma baya jin zai iya zuwa har sai yaje gidan ta ta bashi cikakken bayani.
Tana zaune shirim da uban ciki a jikin ta taji ana latsa door Bell, da ƙyar ta ɓaɓɓaka ta nufi ƙofar gami da leƙa wa ta ƴar ƙofar da zata sada ka da mai latsa doorbell ɗin, to saidai bata ga kowa ba, hakan ce ta sanya ta buɗewa domin ta san ba abun cutar wa bane tinda akwai mai gadi.
Baya tayi mana zata faɗi ganin ko wanene, sanye yake cikin ƙananan kaya, baƙin wando ne, sai rigar polo kalar sararn samaniya, idanun shi daɗe cikin baƙin glass sosai, fuskar nan babu alamun walwala ko annashuwa tattare da ita, yayi fari tas ya ƙara kyau, fatar nan tashi har salƙi takeyi ga baƙa suɗik ɗin gargaza da ta samu wuri ta lafe abunta, kan nan kuwa nashi yasha gyara yayi luf dashi har ya kusan sauka ƙyeyar shi, da gani dai sumar nan tana shan gyara yanda kasan ta shahrokhan ko Omair na cikin tarkon ƙauna.
Hannu ya sanya ya taro ta, ganin yanda ta firgita har tana neman faɗuwa ga uban ciki a jikin ta.
Saida ya tabbatar da ta daidaita tsayuwar ta, sannan ya sake ta tyaa mai raɓeta ya shiga ciki zuwa falon kai tsaye.
A hankali ta maida ƙofar ta kulle, ta shiga bin bayan shi, saidai kafin ta zauna ta wuce kitchen ta haɗo mashi abun Sanyawa a baki da lemo da ruwa ta kawo mashi ta janyo stool ta ɗora bisa, haɗi da zama tana mai gaishe shi cikin rawar murya.
Bai ko bi ta kan abunda ta ajiye mashi ba, ya sanya hannu ya matsar da stool ɗin gefe, yana mai ɗan zamowa daga bisa kujerar alamar magana zasuyi mai muhimmanci, haɗi da amsa mata gaisuwar a gaggauce.
"Magana zamuyi Hafsat, tinda Naji kina kuka na san da akwai wani abu dake faruwa, ki natsu Hafsat ki gaya man dukkanin abunda ya faru bayan tafiya ta, muddin kinsan wani abu ban yarda ki ɓoye man shi ba komin ƙanƙantar shi"
Ta ruɗe ita ruɗewa, yaron dake cikin cikin ta ne ya shiga dunƙukewa yana curewa wuri guda saboda tsabar kaɗuwa da tayi, gashi kuma Dad ya hana a sanar dashi komai, idan aka ji a bakin ta yaji, ita yanzu ina zata sanya kanta
Lura da hakan da yayi ne ya shiga kwantar mata da hankali yana mata alƙawarin babu wanda zaiji cewa a bakin ta yaji, kai babu ma wanda zai san ya shigo ƙasar in ka ɗauke ta da Bilal shima idan ya kama ya sani kenan.
Saukowa tayi ƙasa haɗi da zama bisa tiles inda zata fi jin daɗi daɗi, sannan ta miƙe ƙafar ta, ko ba komai tana so ya nemo mata Suhan ɗin, tayi kewar ta sosai, tana tausaya ma rayuwar ta, bata so ta shiga wani mugun halin ko kuma yana yin da zai iya Sanyawa ta faɗa cikin wata Rayuwar, duk da kasancewar umman tata mace tsayayya.
A hankali ta shiga warware mashi dukkanin Abunda ta san ya faru bayan tafiyar shi, har kawo inda ake yanzu, kuka take wiwi tinowa da Ƙawar tata da tayi.
Tini kalar idanun shi suka cenza, wata jijiya ta taso mashi raɗau bisa kai, yayin da kanshi yake ta sa rawa, idanun nan kuwa sunyi jawur, hannun shi ya dunƙule yana bugawa a cikin gudan cikin tsananin tashin hankali, lallai aiki ja ya ganshi, duk inda suka shiga a faɗin ƙasar nan dole ne ya binciko su, ashe burin da Mom ɗinshi ta ɗauka na ganin sai sunbar gidan, bata barshi ba, Meyasa Bilal ya ɓoye mashi? Shi a tunanin shi zai nemo su ne, ya maido su ba tare da shi ɗin ya sani ba? Wannan itace amanar daya bashi? Lallai kuwa Mama Talatu zata gane kuren ta, tabbas dole ne dukkan mai hannu acikin wannan al'amari ya gane kuren shi, koda kuwa Mom ɗin tashi ce ba zai lamunci wannan zaluncin ba, yarinyar marainiya da ita ace ba za'a tausaya mata ba, har sai an koresu an raba su daga inda suke samu suci abinci.
Miƙewa yayi a matuƙar fusace da niyyar ficewa, bata san lokacin da ta miƙe ba tana mai taro shi gami da shiga yi mashi magiya akan ya rufa mata asiri.
Da dukkan hannuwan shi ya sanya ya tallabo fuskar ta, sannan ya shiga cewa
"Hafsat kar ki damu, ba zanyi Abunda zai sanya ki shiga matsala ba, hasali a yanzu ba guda na nufa ba, zan bar garin ne baki ɗaya in shiga neman su da kaina, ko Bilal bana so ki faɗa mashi nazo kai koda kuwa ace Sadeeq ne tinda kinga shi ɗin abokin shi ne"
Da alamar gamsuwa ta shiga jinjina mashi kai, tana mai zame fuskar tata ta shiga buɗe mashi ƙofar gami da cewa "Allah ya tsare hanya Yaya sai munyi waya"
Har bakin gare ta raka shi, da yake ba da mota yazo ba, har ya fice tana mai kallon shi zuciyar ta a matuƙar cunkushe, saidai ma ko menene ta san lokacin gano su Suhan ɗinne yazo, kuma tayi matuƙar farin ciki da hakan.
Saida taja ma mai gadi kunne akan kada ya faɗa ma Sadeeq ɗin Ya Ameen ɗin yazo, sannan ta juya cikin gidan tunani fal a ranta...
*******************
Ya matuƙar daɗewa a cikin makarantar, duk inda yake sa ran zai nemo wani bayani daya Ƙunshe ta ya kasa samun cikakken bayani saboda tsaro, kusan yini yayi yana zarya ofisoshin makarantar, babu wani cikakken bayani dai, rashin sani, kuma ta gaban shi Suhan ɗin ta wuce zuwa masallaci da niƙab a fuskar ta, Sam bai gane ta ba, bai fahimci komai ba, tinda bai kawo ma ranshi komai ba, itama ɗin bata lura dashi ba, tinda yana ta cikin mota ne zaune, har ya gaji yabar makarantar zuciyar shi na raya mashi cewa Suhan ɗin na kusa, kuma tana cikin makarantar idan dai har Umman tata ta barta akan ta cigaba da zuwa makarantar.
A haka yaja motar shi ya fice, zuciyar shi cunkushe, ya kusan kai kwana nawa yanzu yana shigowa makarantar ko zai dace da ganin ta, Amman babu wani labari.
Ya yanke hukuncin komawa abujan ko kuma yaje ya roƙo Hajiya Kubran akan cewa idan tanada masaniyar inda suke ta taimaka mashi ta bayyana masu, ko zasu samu su fita daga cikin halin da suke ciki tin kafin aminin nashi ya Samu labari.
Ya yanke shawarar nan da zuwa wani lokaci kaɗan, idan har bai ganta ba, to fa zai shaida ma Ameen ɗinne asan wacce za'ayi, domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa, ya gaza, ya gaza cika ma aminin nashi alƙawarin daya ɗauka, kunyar abokin nashi tana cike a cikin zuciyar shi tin kafin ma su haɗu.
********************
A tare suka isa ƙauyen da Sir Salim ɗin, da taimakon shi ma ne suka samu suka gane gidan, da kallo ita kanta Hajiya Khaltum ɗin tabi gidan, to saidai koma menene su dai sun ji sun gani kuma a haka suke so, ba kuɗi ne matsalar su indai za'a amince a basu auren yarinyar da ta kwanta mata arai fiye da duk wata ɗiya mace da ta gani tana son yaron nata.
Da sallama ta shiga gidan, yayin da tabar su Sir Salim ɗin nan jingine jikin mota.
Umma ta ce zaune tana tanƙaɗen dawa, ita kuma Hajjo tana iza wutar miya bisa murhun duwatsu da yake cen madafa.
Da ɗan sakin fuska umman tawa take amsa mata sallamar da tayi mata, ko ba'a faɗa ba ta shaida umman tawa, hango tsantsar kama dake saman fuskar tamu, da kuma sanyin dake tattare damu daya kasance iri ɗaya.
Ajiye tiren tayi ƙasa gami da yima matar maraba, duk da bata shaida ta ba, tabarmar kaba ta janyo gami da shinfuɗa mata daga gefen ɗakin namu.
Cikin mutunci suka gaisa harda Hajjo data fito, itama ganin bata shaida ta ba, ya sanya ta janyo kujera ƴar tsugunno ta zauna kaman yanda taga umman tawa tayi.
Sake sabuwar gaisuwa sukayi, yayin da Hajjon ta miƙe ta ɗebo mata ruwa cikin kofin silver sai ɗaukar ido yake.
Ga mamakin su Umman tawa, matar kafa kai tayi tasha ruwan nan a haka da yake fari fat duk laka a cikin shi, wai nan haka ma don sai sun dafa suke zubawa a randar ya kwanta.
Hajjo da umma ce suka kalli juna, saidai basu ce komai ba, har ta gama sha ruwan tayi hamdala tana mai cewa "Aikuwa Ruwan fa da daɗi gwanin garɗi"
Su dai da kallon mamaki suka bita, gata dai ƴar gayu Amman bata da jin kan masu kuɗi.
Hajjo ce tayi ƙarfin halin tambayar ta daga ina take?
Ɗan murmushi ta sake saki tana mai cewa "Eh gaskiya ba zaku shaida ni ba, kaman yanda nima yau ne karon farko ɗana sanya ku a idona har ita ɗiyar tawa, Sunana Hajiya Khaltum, kuma nice Mahaifiyar Salim Bawa, malamin su Suhan yarinyar wajen ku"
Toh fa!
"Ikon Allah, yaron kirki kuwa ɗan albarka, Allah dai ya biya shi abun alkhairin da yake yi mana, yana ta ɗawainiya da yarinyar tamu". Cewar Hajjo da yanzu ta shaida ko wacece matar kuma sai yanzu ne ta hango ƴar kamar da suke yi.
Umma ta ma saida tayi mata godiya sosai, tana mai cewa Salim ɗin ya shigo mana, ai yanzu ya zama ɗan gida, bayan Ammin tashi ta shaida masu tare suke ma.
Harda dreban Hajjo ta leƙa tace su shigo, suma tabarmar kabar suka shimfiɗa masu suka sake gaggaisawa, shi dai Salim kanshi a duƙe yake duk kunyar ummata ta cika shi, duk da har yanzu bata san me ke tafe da su ba.
Shaida ma Ammin sukayi akan cewa zasu fita cen hanya ko zasu samu Hotel ɗinda zasu kwana, kafin zuwa goben su wuce.
Da to tabisu yayin da sukayi sallama dasu umman tawa suka fice, har Hajjo ke ce masu ba zasu tsaya suci tuwon dawa ba?
A kunyace suka ce sun ƙoshi, gami da shiga motar su suka bar ƙauyen, hakan ce ta sanya Ummata da Hajjo gane cewa anan gidan matar da ta kira kanta da Hajiya Khaltum zata kwana kenan, Hajjo ce ta karɓi girkin daren, yayin da Ummata ta shiga ɗakin nata domin gyara mata inda zata kwanta daidai ƙarfin ta.
Har aka gama tuwon aka kwashe babu abinda ya tada Hajiya Khaltum sai Sallah, bayan ta gama ne ta jawo wani mai, wanda ke hana sauro cizon mutum duk ta shasshafa jikin ta, dama ummata ta shigar mata da ƴar ƙaramar jikkar ta ɗaki. A haka aka gama tuwon aka zuba mata, nan ma babu wani ƙyanƙyami taci abunta hankali kwance, harma tana zuba santin cewa ta daɗe bata ci tuwon dawa da miyar kuka da manshano haka ba.
Duk kansu sun ji daɗin sakin jikin nata dasu, gashi bata nuna masu komai ba ko ƙyama, balle har ta kasa cin abincin su.
Bayan ta gama cin abincin ne take shaida masu da akwai maganar da ta kawo ta mai matuƙar muhimmanci, wanda take so tayi da su da kuma mahaifin Yarinya Suhan.
Nan fa gaban Ummata ya shiga faɗuwa, Hajjo ce tayi ƙarfin hin cewa to su jira shi ya dawo daga kasuwa domin ko ina yake yanzu fa yana hanya ne....
Da haka suka shiga firar su ta manya da kuma halin da duniya da ƙasa take ciki, masalan na rashin abinci da kuma kidnapping ɗinnan da ake fama dashi a arewacin nigeria ɗin.
Sallamar Malam na daga cikin Abunda ya ƙara tsananta faɗuwr gaba ga Umman tawa, domin batasan ko da wacce wannan matar take tafe ba, duk da kuwa ta yaba da hankali da natsuwar matar, kuma tayi imanin bata tare da abun cutuwa ko da zai iya zama barazana ga lafiyar tata data yarinyar tata.....
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~37~*
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
*Ammin Islam Pls ki sassauta ma Hajiya Kubra, 🤣🤣ai indai kina yin Ya Ameen dole ne ki so Mom ɗinshi, kiyi mata addu'a Allah ya shirya ta. Team Sir, Salim ina gaishe ku muna mugun tare🤝🏻🤝🏻👌🏻*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Kai tsaye ɗaki malam ya shige, bayan sun gaisa da Ammi wadda bai wani waye ta ba sosai.
Sai bayan da ya kammala cin tuwon daren ne, sannan Hajjo take shaida mashi ko wacece Ammin da abunda yake tafe da ita kuma. Cewa yayi ta shimfiɗa mashi darduma zai fito suyi magana, saboda ɗakin akwai zafi.
Daga cen gefe ta shimfiɗa mashi dardumar, sannan ta shaida masu ga malam ɗinnan fitowa.
Bai wani ɗauki lokaci ba, ya fito haɗi da zuwa ya ɗauraye hannuwan shi, sannan ya koma ya zauna suka sake sabuwar gaisuwa.
Cikin salon magana irin ta manyan ƴan boko da suka iya tsara kalamai Hajiya Khaltum ɗin ke bayyana ma malam ita ɗin wacece, da kuma dalilin zuwan nata gidan.
Tsaf ya tsaya ya saurare ta da kunnen basira da kuma fahimta, ummata da Hajjo dai suna zaune basu ce ƙala ba.
Malam ne yayi gyaran murya gami da muskutawa, sannan ya fara magana.
"Ah Hajiya munji dalilin zuwan ki gidan namu, a haƙiƙanin gaskiya munji daɗi kuma mun yaba, duk wanda yayo tattaki daga nesan duniya yazo inda kake, da kuma ƙoƙon barar soyayya, kuma irin ta aure, a gaskiya ya cencenci yabawa da kuma karramawa, saboda haka ne muke cewa mun gode. To saidai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba, ban sani ba ko an shaida maki yarinyar marainiya ce? Ni ne nan nake zaman mahaifinta, wanda kuma anan gidan aka haife ta, saboda wasu dalilai ne ya sanya bata tashi a gaba na ba, wanda duk da haka na yaba da tarbiyyar da ita Maryamar ta bata, sannan kuma shima yaron na wajen ki lallai mun yaba dashi kuma munyi na'am dashi. Idan dai har kun yarda da hakan, to ta ɓangaren mu babu wani damuwa, zai iya zuwa su daidaita kansu, zuwa wani lokaci bayan sun gama fahimtar juna sai a turo manyan nashi maza domin suzo mu sake tattaunawa"
Tinda malam ya fara magana Ammi ke sakin murmushi, lallai ita kanta babu Abunda zata iya cewa da wannan zuri'a saidai fatan Alkhairi. Godiya ta shiga zubawa tana cewa wannan ai ba matsala bane, Allah ya bar zumunci kuma ya ƙara haɗa kawunan su yaran.
Nan malam ya tashi ya shige ciki ya bar su, duk da ummata ta ɗan sha jinin jikin ta, bamu sani ba ko sarakutar ce ta fara?
Da haka suma suka miƙe suka shiga ɗaki domin kwanciya, ummata ta gyara ko ina tsaf, dama kasancewar ta mace mai tsafta, sai ta shimfiɗa ma Ammi manyan barguna masu taushi a ƙasn ta ajiye mata matashin kai da kuma marar nauyi na lulluɓa.
Saida Ammi ta cenza kaya zuwa doguwar rigar bacci sannan ta kwanta, tana mai yima ummata sai da safe.
Cikin dare umman tawa ta farka domin yin ƙiyamul laili kaman yanda ta saba, saidai ga mamakin ta, Ammi ce tsaye tana salla, lamoo umman tawa tayi tana ta ƙare mata kallo duk ba tare da ta lura da ita ba.
Ta Kai kusan awa guda tana sallar sannan ta tsagaita, gami da ɗaga hannu ta dinga kwararo addu'a cikin harshen larabci da ƙanƙan da kai wajen Allah. Tabbas ta burge ummata ta ƙayatar da ita, sai taji ta sake amincewa da lamarin matar, tabbas indai haka ne abunda ta gani, Allah yayi ma Suhan ɗin zaɓi mafi alkhairi, saidai fatan nasara da dacewa.
Saida taga Ammin ta koma ta kwanta ne, sannan itama ta miƙe domin gabatar da tata, wanda itama Ammin tana kula da ita, itama hankalin ta ya sake kwanciya da auren yarinyar matar, saboda ummata mace ce mai dattako da kamala, sai taji hakan ya matuƙar taimakawa wajen ƙara amincewa da mahaifiyar yarinyar.
Washegari ma babu ƙyama ba komai aka kai mata ruwan wanka tayi, duk da har yanzu ummata bata ƙara sakin jiki da Hajiya Khaltum ba, saidai hakan bai dameta ba, tabar hakan ne a rashin sabo da basu yi ba.
Sai da tasha ruwan koko da ƙosan da aka ajiye mata ne, sannan sai ga su Sir Salim Sun dawo domin tafiya da Ammin.
Kaman kar ta rabu da gidan take ji, rayuwar tasu a sauƙaƙe ta burge ta, ga karamci ga dattako, a haka sukayi sallama harda Malam da bai riga ya fita ba, ya bari sai yaga tafiyar ta.
Tin daga murmushn da Ammin tashi keyi, ya tabbatar da nasara da dacewa a al'amarin.
Wannan ce ta sanya shi jin kunya da ta sanya dole ya dinga duƙar da kai lokacin da yake gaishe su cikin girmamawa. Sun sake saki da al'amarin ko ba komai suna kyautata zaton ƙila lokacin fitar Suhanan ne yazo daga ƙuncin da take ciki.
Basu bar wurin ba, saida aka buɗe but suka dinga shiga da kayan abinci kala kala da kayan amfanin gida, sai kuɗi da umman ta ajiye masu rafer ta ƴan 1k guda ɗaya.
Dakyal suka amsa, ummata kuwa komawa tayi gefe akan fir ita ba wannan suke buƙata ba, sai da magiya da komai ne ya sanya Hajjo amsa ta shiga yi masu godiya da addu'a
Basu bar wurin ba har saida suka ga ficewar motar su Ammin daga Layin sannan suka koma gida cike da al'ajabin wannan mata mai cike da abun ban mamaki
*********************
Saida ya gama juye juye da tunane tunanen shi, sannan ya kira waya akan a kawo mashi mota zuwa a hotel ɗin da ya sauka.
Aiko sai ga mota sabuwa dal tear ledar, mai masifar kyau, an mata glass tint sosai ta yadda ba zaka iya fahimtar wanda yake ciki ba.
Bayan ya fito ya gani ne, ya koma ɗakin shi, saboda baya so su haɗu da idon sani, labari ya bazu a gari akan shigowar tashi ƙasar, tinda shi mutum ne na mutane, gashi matasa kowa ya san da zaman shi yanzu, tin bayan da akayi mashi naɗin babu inda hotunan shi basu zagaya ba a sassan ƙasar.
Laptop ɗinshi ya jawo ya shiga bincike sosai, saidai ya manta ƙasar tamu, ba ko ina bane ba ma wireless ke shiga ba, iya binciken shi da neman shi a yanar gizo, bai iya gano komai ba, har dai ya haƙura ya ajiye ya shiga wanka.
Shiryawa yayi cikin ƙananan kaya, sannan ya ɗauko wata baƙar jacket mai hula ya sanya gami da rufe kanshi da hular, face mask baƙi ya sanya ma baki da hancin shi, sai sun glass daya ɗora ma idanun shi, Sam ba zaka taɓa shaida shi ba, in har ba kyakkyawan sani kayi mashi ba.
Cikin salon tafiyar shi ya taka zuwa bakin mirror, saida ya gama kalle kanshi tsaf, yaga ba ta inda ya kuskure wajen barin wata alama da zata sanya a gane shi, sannan ya ɗauki makullin motar tashi ya fice haɗi da jan trolly ɗin kayan shi.
Kai tsaye yabar cikin hotel ɗin, bayan ya maida masu da makullin ɗakin nasu.
(To Su Ya Ameen Ko Ina Kuma Aka Nufa?)
********************
Yanzu wata irin kunyar Sir, Salim nake ji, duk da dai nasan cewa bana jin komai game dashi, saidai kuma akwai nauyi tattare dani, yanzu dai bana da matsalar komai, har mun gama zana jarawar mu, da yake hutun semester ɗin ba mai tsawo bane, ya sanya ban koma gida ba, da taimakon kuɗin da Ammi ta bani, da kuma hidimar da Sir, Salim yake yi mani, ya sanya karatuna na sanya a gaba.
Yanzu dai na samu ummata tana da ƴar wayar hannu, itama saidai duk in zata kira ni, sai taje tabhau cen bisa wani dutsi sannan zamuyi waya, amman idan ni na kira ta bana samu.
Matsala ɗaya ke damuna, yawan text da nake samu daga Ma'un Sir Salim, tana man barazanar shiga gidan ta, saboda taji labarin cewa har aure an je nema kuma iyayena sun bada.
Har kirana takeyi a waya bana ɗagawa ne, text ɗinma in tayo mani saidai in goge kawai bayan na karanta, ban taɓa faɗa ma Sir Salim ba, kullum Ammin shi kan kirani ta haɗa ni da yaran shi mu gaisa, zuwa yanzu dai Ma'un ta koma gidan Sir, Salim ɗin, wannan ce ma ya sanya yake zuwa weak end, amman ba wani kwanciyar hankali ko jin daɗi, yaran ma duka suna hannun Ammin shi, har yanzu ba'a maida ma Ma'un su ba, to bata tsaya ta kula da kanta ba ma balle yaran?
Duk wannan abun dake faruwa bai sanya naji ko ɗar cikin zuciya ta ba, miji dai ne na samu kuma ba zan taɓa wasa wannan damar ta kufce mani ba, tinda banga amfanin zaman haka ba, bayan Allah ya riga ya kawo mani mai sona da ƙaunata da zuciya ɗaya.
Sir Salim irin mutanen nan ne masu shiga rai farat ɗaya, yana da yawan fara'a, gashi baya da girman kai duk da kasancewar shi mai abun hannun shi, sannan yana da kyauta, ga iya mu'amala da mutane, wannan ce ta sanya ko a cikin makarantar mutane da dama suke girmama ni, kasancewar ya zuwa yanzu kusan kowa ya fahimci alaƙar dake tsakani na dashi.
Dogo ne daidai misali, don zamu iya cewa yafi ya Ameen da kaɗan, yana da ƙira irin ta cikakkun maza, ba baƙi bane cen wuluk, hasken shi daidai misali, yana da haiba da dattako. Ya iya shiga kala kala, hakan ce ma ta sanya mata da yawa macewa a soyayyar shi, acikin makarantar baya da kula ƴan mata, kuma baya son wasa da karatu, dalili kenan daya sanya ya tsaya man kai da fata, wajen ganin ban samu wata matsala ba.
A wurina soyayya ba abu bace da akan iya samu farat ɗaya, saboda ƙakubalen rayuwa da nasha fuskanta, idan ma ba yanzu ɗin ba, ai ni soyayya wurin mutane uku zuwa huɗu na santa tin tasowa ta a rayuwa, ummata sai Ya Ameen, sai kuma Afnan da Hafsat, waɗannan mutanen komin yanda na kai da son in manta dasu a rayuwa ta, ba zan iya ba, saboda sun taka muhimmiyar rawa a rayuwa ta, ba kuma kaɗan ba.
Wannan ce ta sanya na Gaza manta Ya Ameen ɗin, sau da dama in muna tare da Sir Salim na kan yi imagining cewa da ace Ya Ameen ne ya zata kasance a rayuwa ta? Duk da shima Sir Salim ba baya ba a wajen komai, cikas ɗinshi ɗaya matar shi, shima kuma bana ɗaukar hakan a wata matsala tinda ba'a kanta zan zauna ba.
Ammi na gwada man tsantsar Soyayya, butsu-butsu tayo mani aike ta hannun yaron nata, kai hatta da Abban shi Sir Salim ɗin Alhaji Bawa Bala, wanda ba ɓoyayye bane a ƴan siyasar ƙasar nan, saida Ammin ta haɗa ni dashi a waya na gaida shi, na yaba da yanda yake amsa gaisuwar tawa, don ga dukkan alamu na samu karɓu wa a cikin wannan family ɗin.
*Ikon Allah kenan. Inda wani yake ƙi da yini, nan wani ke so da kwana*
Hankalin Bilal ya gaza kwanciya, masalan ma idan ya kira wayar Aminin nashi yaji ta a kashe, idan kuma ya tambayi Abie, ya kan ce mashi yana lafiya, basa tare, ko yace yana office ko yace ya fita cikin gari, ko yace ya baro shi a gida.
Ya san halin Aminin nashi sarai, ba ƙaramin ƙyalle bane, wannan duk ɓoye ɓoyen da yakeyi mashi ma, ta ita yuwuwa ya fahimci komai, wannan ce ta sanya shi shirya faɗa mashi gaskiya, to saidai ta ina? Ta yaya zai ganshi? Idan ma ya ganshi to ta ina zai fara yi mashi bayani?
Yana cike da kunya da nadamar amsar wannan amanar da ya gaza cikawa, hakan ce ta sanya shi shirya tafiya American domin yaje ya samu abokin nashi, domin a samu mafita.
Ko a cikin jirgi ma wasi-wasi yake ta faman yi,ji yake kaman ƙasa ta tsage ya shige , bai shirya amsar duk wata ɓaraka daka iya aukuwa a tsakanin shi da Aminin nashi ba, a karon farko tin tasowar su daga ƙuruciya.
**********************
Hajiya Kubra likafa taci gaba, yanzu akai akai tana zuwa cen ƙasar ta Turkiyya wajen Alhaji nata, ganin basu kuma tada mata maganar ba, ya sanya hankalin ta ya kwanta, bata da matsalar komai, yanzu komai nata sai ƙara bunƙasa yakeyi, ta zama hajiyar da duk faɗin ƙasar ake labarin ta, mafi yawan mata suna ji ace dama sune ita, yawan ma'aikatun ta, da kuma hannun jarin da take dashi a kamfanoni ya sanya kullum shaharar ta ƙara haɓaka takeyi, Alhaji Mustapha ba mutum bane mai damuwa sosai ba, balle yanzu da baya da ko yaro ɗaya gaban shi idan ka ɗauke Afnan da take hannun yayar ta, shi kuma Abie yana wurin Yayanshi acen ƙasar ta amurka.
Wannan ce ta sanya ya maida Al'amurran shi kacokam kam ƴan uwan nashi dake Katsina dama sauran garuruwa, sosai ƙasar ta Nigeria ke amfana da Alhaji Mustapha ɗin dama iyalan shi baki ɗaya. Su kaka zuwaira suna cikin jin daɗi ita da ɗan tsohon mijin ta isuhu, sai dangi da kusan duk ya sanar ma waɗanda suka gama karatu aikin yi, waɗanda kuma basu ƙarasa ba yana taimakawa wajen karatun nasu.
Hakan ce ta sanya hankalin shi bai kai kan kwana biyu da yaron nashi bai kira shi ba suka gaisa, Abie ne ke kiran shi, to shi ɗinma dai kaman yanda yake faɗa ma Bilal ɗin shima haka yake faɗa ma dad ɗin nashi, hakan ce ta sanya bai kawo ma ranshi komai ba, illa iyaka dai ya haƙura da Suhan ɗinne kaman yanda Mom ɗinshi ta buƙata, tinda shima babu irin binciken da baiyi ba, da kuma sanyawa ayi, Amman Allah bai sa an dace ba.
***************
A mota yake tafiya zuwa wasu garuruwan, photon ta dake cikin wayar shi ya sanya aka wanke mashi, matsalar dai da babu wanda take ita kaɗai saidai wanda suke tare dashi, to akan ce mashi dai ita yarinyar ba'a santa ba, amman mafi yawa sukan ce mashi ai wannan shine Yariman Matasa Arewan da akayi ma naɗi watannin baya, ya kan sha mamaki, ashe haka mafi yawan mutane suka sanshi a faɗin ƙasar tashi? Lallai tafiya mabuɗin ilimi ce, a wannan tafiyar da yayi, ya haɗu da ƙauyukan da suke matuƙar buƙatar tallafi koda kuwa ace na ruwa ne kawai, sannan ya ƙudurta a ranshi cewa zai iya bakin ƙoƙarinshi wajen ganin ya taimaka masu, muddin ya koma normal *Al'ameen Almustapha Dambulan* ɗin da yake ada.
Idan KagaYa Ameen a yanzu ba lallai ne ka shaida shi ba, shi mutum ne mai yawan tohon gashi, muddin yayi cikakken sati baiyi aski ba, to baya kalluwa, wannan ce ta sanya yanzu da yake ta faman yawon neman su, bai ko damu da yayi askin ba, indai ya samu yayi wanka ya cenza kaya, salla kuwa daman ƙasaru yakeyi, gashi sosai ya firfito mashi kaman ba shi ba, duk ya yamutse ko abinci bai damu da ya zauna zaman ci ba.
Saidai wannan haiba da kwarjini da yake dasu tin tale-tale tana nan daram babu inda taje, kome yakeyi cikin halin nan nashi da kuka sani yakeyi, hatta da tafiyar shi idan ka tsaya ka kula tsaf bata cenza ba, kuma abar kallo ce, wani lokaci a cikin motar shi yake kwana idan dare ya rutsa dashi inda babu hotel.
Ya gaji matuƙa yana so ya kwanta ya huta, yana so yayi aski, yana son aiwatar da abubuwa da dama.
Hakan ce ta sanya shi neman hotel ya kama ɗaki, tunani yake so yayi, yana so yayi tunanin ta ina zai ɓullo ma wannan yawon gararin neman nasu.
Da daddare ne bayan ya gama cin abinci yayi wanka haɗi dayin sallar shi, gado ya nema ya kwanta, duk ya zura saboda irin wannan wahalar da ba sabawa yayi da ita ba, ko zaman tuƙin ma kanshi aiki ne.
Kaman an kunna mashi redio, haka yaji labarin da hafsat ta bashi yana ta faman dawo mashi tiryan tiryan cikin ƙwaƙwalwar, idan har bai manta ba, yaji tana cewa ranar daren da zata tafi makaranta suka bar gidan, kuma idan ba wai ya manta bane, an riga an gama kammala mata komai, to kenan idan har hasashen shi zai bashi daidai, yanzu Suhan ɗin tana makarantar ta ABU zariya, muddin Umman tata ta yarda da karatun nata, to kuwa tabbas zata kasance a makarantar a daidai wannan lokacin, shine ya rubuta mata course ɗinda ya dace tayi da hannuwan shi, kuma yaji Bilal ɗin yana cewa basu cenza mata shi ba, zumbur yayi ya tashi, haɗi da ɗaukar makullin motar shi, ya ja jikkar shi ya fice, a cikin daren ya sake maida masu makullin ɗakin nasu, ya kama hanyar zariya, duk da irin halin rashin tsaro da ake fama dashi a ƙasa, duk da irin duhun daya mamaye duniya a daidai wannan lokacin, duk da irin hatsarin da yaka iya haɗuwa dashi a tafiyar shi ta wannan daren.
Wannan ba shine matsalar shi ba, wannan ba shine abunda yake ji ba, Suhan ita kaɗai ce damuwar shi, ya sanya ta a idanun shi, ya ganta koda sau ɗaya ne, ta amince mashi, koda ba zata koma gidan su bane, ta amince ta aure shi a hakanan idan hakan ta faru ya cika burin shi kaso 80 a yanzu na rayuwar shi.
Ƙarfe bakwai na safen ranar talata a cikin makarantar tayi mashi, akan idanun shi jefi jefin ɗalibai suka fara fitowa zuwa cikin makarantar, sannu kan hankali har suka yawaita, kowa na hidimar shi, zuciyar shi ce ta tsananta duka, tabbas tabbas idan har abunda yake ji a jikin shi haka ne. To *Suhan ɗinshi tana cikin makarantar a daidai wannan lokaci*
_Hmmmmmmmmmm_
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
*Laweexar ina matuƙar jin daɗin comment ɗinki, nagode Allah ya bar ƙauna. Saƙon gaisuwa gareki keda Ammin Islam daga bakin Ya Ameen, yace a sanar daku cewa yana sane daku a rayuwa, kuma watan watarana zai kawo maku ziyara shida Suhan ɗinshi, Amman fa sai bayan komai ya kwaranye idan ya samu nasarar auren ta. Lol*
*Page ~38~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Tin da na farka da safe gabana ke yawaita faɗuwa, har sai na dafe gurin nayi a'uziyya sannan nake samun sauƙi
Har dai khadeeja ta kula da hakan ta shiga tambaya ta ko ina da wata damuwar ne, da zasu taimaka mani wajen magance ta?
Gyaɗa mata kai kawai na shiga yi, ina mai cigaba da shiryawa ta. Har na kammala na fita domin zuwa hall, sai kuma na dawo ɗaki na ɗaura niƙab, gami da zura zumbuleliyar hijab ɗita har ƙasa, duk da zafin da akeyi, na kwammace hakan tinda munyi da Sir Salim akan anjima zai zo yayi mani wata lecture bayan la'asar.
Ta jikin motar ta Ya Ameen nabi na ratsa na wuce har zuwa department ɗin namu. Hatta da idanuna ba'a ganin su, hakan ce ta sanya ba kowa ne zai iya gane ni ba farat ɗaya.
Fitowa yayi daga cikin motar gami da kulle ta, Admin block ɗin ya nufa direct, ya kuwa ci sa'a ya tadda HOD ɗin namu.
Bayan sun gaisa ne, ba zai iya shaida fuskar Ya Ameen ba, saboda face mask baƙa dake fuskar shi, Amman wannan karon ya cire tabarau ɗin.
Photo na ya nuna ma HOD ɗin Mai suna Malam Sani, cikin ɗan girgiza kai bayan ya gama kallon hoton nawa ya dubi Ya Ameen ɗin.
"Wannan itace yarinyar da wani yake yawan zuwa nema a makarantar nan, kuma mu kanmu bama da masani ya a kanta, tin bayan shudedden lokaci bata kuma dawowa makarantar nan ba"
Ya faɗi haka ne saboda doka ce, kuma Sir Salim ya roƙeshi akan ya ɓoye dukkan wani abu daka iya bayyana wanzuwar Suhan ɗin a makarantar saboda wani dalili, kuma shi kanshi malam Sanin da ya kasance aboki ne ga Sir Salim, ba zai taɓa lamuntar abunda ka iya jawo cikas a al'amarin abokin nashi da matar da yake da burin aure ba.
Cikin kallon tuhuma ya Ameen ya fara kallon shi, bai ce ƙala ba, har Malam Sani ya kai aya a zancen nashi.
Yana da wata irin baiwa ta daban da Allah ya bashi, wadda ba kowa ne yaba irin ta ba, muddin ka faɗa mashi ƙarya ko abunda ba haka bane a cikin zuciyar ka, to kuwa lokaci guda farat ɗaya zai gano ka, saidai idan yayi niyyar share wa ne kawai ya share.
Ba tare da yace komai ba, ya miƙe gami da zaro complement card ɗinshi ya ajiye bisa teburin HOD ɗin.
Shima bai kuma cewa ƙala ba, ya sanya hannu ya ɗauka gami da dubawa, a ɗan firgice da kuma alamar mamaki ƙarara kan fuskar shi yake duban Ya Ameen ɗin, kaman ma dai bai gasgata abunda ya gani ba rubuce a bisa katin.
Lura da hakan da Ya Ameen yayi Ya sanya shi, zare face mask ɗin a hankali daga fuskar shi, ai tini Malam Sani ya miƙe cike da tsantsar girmamawa, hannu na rawa ya miƙa ma ya Ameen ɗin suyi musabaha
Bai ƙi ba, shima ya miƙe gami da miƙa mashi hannun, fuskar shi ɗauke da ɗan murmushi irin wanda ke ƙara ƙawata fuskar tashi.
A tare suka kuma zama, saidai har yanzu tsantsar mamaki bai saki Malam Sani ba, tinani yake yi wai ita wannan yarinyar wacece da har ake nemanta haka? Shin ma menene dalilin Sir Salim ɗin na roƙon shi Malam Sanin akan ya ɓoye labarin Suhan ɗin koda wani zai zo nema?
"Nine Muh'd Al'ameen Almustapha Dambulan. Yarinyar da nake nema ƙanwa ta ce, tayi mana ɓatan dabo ne bamu san inda ta nufa ba, ita da mahaifiyar ta, wannan ne dalilin da ya sanya kace ana zuwa nemanta nan, kuma muna da yaƙinin tana makarantar nan, shi wanda ke zuwa nan ɗin Sunan shi Bilal Amini na ne, kuma ɗan uwana, inaso ka bani haɗin kai, wajen shaida mani inda Suhan take domin mu sadu da ita da gaugawa. Mun zaɓi zuwa nan ɗinne ta ruwan sanyi, domin munsan dukkan bayanan da muke nema kana dasu"
Ya faɗa cike da ƙwarin guiwa, ƴar fara'ar dake kan fuskar shi tuni ta kau, saboda baya ko fatan Abunda kan kawo tarnaƙi a haɗuwar shi da Suhan ɗin.
Malam Sani ne ya shiga jinjina kai, sannan ya ɗora da cewa
"Tabbas Yallaɓai tana makarantar nan tamu, to saidai su da kansu ne suka nemi da muyi hakan, zan ji daɗi ace koda ka gano ta, ka nuna bansan da zancen ba, hakan shine kawai alfarmar da zan iya roƙa a wurin ka"
Cike da gamsuwa Ya Ameen yashiga jinjina mashi kai ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Miƙewa Malam Sanin yayi yana faɗin, Yallaɓai me za'a kawo maka kayi break fast dashi?
Girgiza mashi kai Ya Ameen ɗin yayi, domin shi dai burin shi ya sadu da Suhan ɗin a daidai wannan lokacin.
Komawa Malam sanin yayi ya zauna, gami da jawo wani folder ya buɗa, tiryan tiryan har yazo kan files ɗin na suhan.
Jawoshi yayi, gami da miƙa ma ya Ameen.
Cikin ƴar taƙamar da ta zama jinin jikin shi, da kuma sarauta dake yawo yanzu a jinin shi ya sanya hannu ya amsa. Malam Sani dai yana kallon shi, burge shi yake daɗa yi, abun alfaharin shi ne, ace yau kaman Ya Ameen ɗin Yariman Matasan Arewa ne zaune a office ɗin nashi, a kuma gaban shi.
Ajiyewa yayi, yana mai zaro wayar shi ya kwafi number ɗinta, sannan ya miƙa ma Malam Sani File ɗin, godiya ya shiga yi mashi kaman baya son sake magana, ya miƙe da niyyar ficewa bayan ya sake ba Malam Sanin Hannu.
Har waje bakin motar shi ya raka shi, yana gaba shi kuma yana binshi a baya, saboda girmamawa Malam Sanin ne ya buɗe mashi ƙofar motar da kanshi, wadda tin fitowar su daga Office ɗin Ya Ameen ɗin ya buɗe motar ta hanyar ɗan maƙullin dake hannun shi.
Shi kanshi motar ta bala'in tafiya da imanin shi, in ko haka ne, dole ya nemi abokin nashi Sir Salim Yayi mashi murnar ƴar babban gida irin haka da zai aura, duk da shima yana da abun hannun shi sosai, kuma ya fito daga babban gida, Amman sai yake ganin kaman wannan daya zo ya dama su ya shanye har romon nasu.
Brown emvelop ya miƙa ma Malam sanin, yana faɗin
"wannan tukuicin ka ne, saboda nuna mani ƙanwata da kayi, sai mun sake haɗuwa"
Hannu na rawa Malam Sanin ya sanya ya karɓa, bakin shi har kunne sai zuba godiya yake yi, dama gashi wata yayi tsakiya komai ya tsaya. Har saida yaga fitar motar Ya Ameen ɗin daga makarantar sannan ya juya ya koma office ɗin nashi da zummar kiran abokin nashi.
****************
Hankalin Bilal idan yayi dubu ya tashi, har saida ya dafe ɗan madaidaicin teburin da Abie ɗin yake kai, lokacin da yake labarta mashi tafiyar Ya Ameen ɗin Nigeria.
Shima Abie ɗin kwatsam saidai yaga Bilal ɗin a office ɗin nashi, aiko nan ya titsiye shi akan ya faɗa mashi inda Ya Ameen yake, sanin Bilal ɗin ko wanene a gurin Ya Ameen ɗin ya sanya Abie ɗin sanar dashi gaskiya kawai.
"Subhanallah, me yake faruwa ne Yaya?"
Abie ɗin ya faɗa cikin sauri yana mai kamo Bilal ɗin ya nufi wata sofa dake gefe ajiye ya zaunar dashi, komawa yayi ya ɗauko mashi ruwa cikin wata gora haɗi da mug fari tar, ruwan ya tsiyaya mashi ya miƙa mashi. Baiyi gardama ba ya amsa ya kwankwale, sake zuba mashi yayi, nan ma shanyewa yayi tas, ko da dai Abie ya kula kaman ruwan bai ishe shi ba, sai ya miƙa mashi gorar ruwan baki ɗaya, aiko amsa yayi ya kafa kai, saida ya shanye ta tas, sannan yayi jifa da robar gefe yana faɗin.
"Why why?"
Zanewa yayi ya kwanta, shi dai Abie yana tsaye yana kallon ikon Allah, Amman kanshi gabaki ɗaya ya kulle, tambayoyi yake son yi ma Yayan nashi, Amman ya kasa ta ina ma zai soma farawa?
Saboda haka ya juya ya koma wurin zaman nashi, gami da zama ya jawo laptop ɗin tashi ya cigaba da aikin shi.
Bilal ɗinne ya miƙe tsaye gami da faɗin "Ni zanje gida Abie, sai ka dawo" bai jira cewar Abie ɗin ba, ya juya haɗi da ficewa daga Office ɗin.
Da kallo ya raka shi, yana mai girgiza kai, dole da akwai wani abu dake faruwa ko dai yake shirin faruwa, waya ya jawo domin ya faɗa ma Dad ɗin nashi, tin kafin komai ya kwaɓe dashi a ciki.
Aiko cikin sa'a Dad ɗin ya ɗaga, tiryan tiryan Abie ɗin ya feɗe ma Dad ɗin biri har wutsiya, shima hankalin shi ya matuƙar tashi, kashewa yayi yana mai cewa bari ya nemi Bilal ɗin yaji koma menene.
To shima Bilal ɗin, koda Dad ɗin ya kira shi bai ɓoye mashi komai ba, ai abokin kuka ba'a ɓoye mashi mutuwa, in ma bai sanar da Dad ɗin ba wa zai sanar mawa?
Cikin tsantsar ɓacin rai da Alhaji Mustaphan kan daɗe bai yi ba, yake sanar da Bilal ɗin cewa kada ya sake ya faɗa ma kowa, kawai su haɗu a nigeria ɗin asan abun yi.
Kashewa yayi gami da kwanciya domin ya huta, kafin anjima ya tashi yayi wanka ya ɗauki hanyar komawa Nigeriyar.
Mama Talatu an saki jiki a gida ana zuba isa da mulki, idan Hajiya Kubran bata nan, ita ce kan gaba akan komai, ta samu yadda take so, wani lokaci ma har ita ake ba ɗan ihisanin da ake ba ma'aikata ta rarraba, sai kuma Abunda taga dama take kawowa ta basu. Ta ɗaya ɓangaren kuma Maree har yanzu tana kan bakanta na son auren ɗan masu gidan ko ta wacce hanya ce, jiran dawowar shi ƙasar kawai take yi, ta aiwatar da abunda ta ƙumso tin tini tana zaman jiran zuwan nashi.
Ita ko Hajiya Kubra ma bata ko kula da komai dake faruwa ba, su Hajiya Sa'a da Hajiya Laila sun ƙara zama mata aminnai, koda Hajiya Zainab suka koma Abujan da zama ba kasafai ma suke haɗuwa ba, shima sai dai ita Hajiya zainab ɗin taje gidan Hajiya Kubran, har dai ta gaji, ta kula cewa ita ce zata dinga zuwa gidan ƙanen mijin nata? Alhali babu abunda take nema daga matar gidan?
Sai ta haƙure ma kanta, indai wata sabgar ta haɗa su, sun gaisa, ko da yake ma ba komai ne da akeyi ba kankiyar wanda Hajiya Kubran ke zuwa, kuma a haka kowa ya sanya mata ido, to tana da kuɗi, tafi ƙarfin wulaƙanci ta kowanne fanni.
Hannun jari ta zuba sosai a kamfanin matatar mai ta Nigeriyar, arziƙin yanzu fa yaci uban nada. Ko ina kayi labarin irin shaharar Hajiya Kubran akeyi, ya zuwa yanzu ta kuma samun ƙawa da take mai irin halin ta komai da komai, kuma itama tana da masifar kuɗi, sai suka ɗinke suka zama su huɗu kenan idan kaji ana cewa 4Hajiyas to su ake nufi, ciki da bai na Abuja babu inda labarin su bai karaɗe ba, mata ne masu ji da kansu, wanda duniya take kaɗa masu gangi a tsakar ka, basu damu da su taka wanda suke so ba, su muzgunawa wanda suke so, ko wanene kai, kuma ko me kake taƙama dashi indai ka shiga shirin su 4Hajiyas to fa ka bani, ka kaɗe har buzun ka.
********************
Ƙarfe biyu muka tashi lecture ta farko, salla kawai mukayi muka koma ta biyu, sai 4 muka fito, ina fitowa ne text ɗin Sir Salim yana shigowa wayata, akan in shirya zuwa 5 yana zuwa, domin yanzu mun cenza akalar inda muke karatu, library muke zuwa domin mun fi sake wa a cen muyi Abunda zai amfane ni.
Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "Hooo Sir Salim, ba hutu kenan? Gaskiya fa kada ka fasa man ƙwaƙwalwar saboda karatu"
Da haka na isa ɗakin, wanka kawai nayi, na jawo biscuit da fresh Yoo nasha, ban cika cin abinci ba sosai, duk da kasancewa ta ba mai rama ba, jikina yunwa ko wahala baya sanyawa ya cenza daga yanda yake.
Wanka nayi gami da shiryawa, a karo na farko kenan a rayuwa ta da zan fara yima Sir Salim kwalliya, ya sha roƙo na akan hakan, ni kuma sai nake ganin ba kwalliya ko soyayya ce ta kawo ni ba.
Tsayawa nayi na tsara kwalliya mai tafiya da hankali, riga da skir na wata jar atamfa mai ratsin shuɗiya na sanya, riga da skirt ɗin sun ɗan kama ni, hakan ce ta sanya na fara tsarguwa da kaina, da tunanin ba zan iya fita a haka ba.
Su Raihana ne suka shiga koɗa ni, ganin ina shirin tuɓe kayan in cenza ne, ya sanya suka shiga yiman magiya akan in bar shi, ai hakan ma ba wata damuwa, ko ba komai ya kamata in ɗan dinga yima Sir Salim ɗin kwalliya, tinda shi dai namiji ne mai son gayu, gashi ɗan gayu, dukkan matan dake skul ɗin bai zaɓi kowa ba sai ni.
Da haka ne yasanya sukayi comvincing ɗina akan in bar su, na bar su ɗin amman nace hijab zan sanya, nan ma nunawa sukayi basu yarda ba, khadeeja ce ma mai jawo mani shuɗin gyale, harda ƙoƙarin yafa mani, Raihana na fesa mani turare.
Muna cikin wannan dramer ɗin shiryawar ne, sai ga kiran shi akan in fito yana jirana zamu wuce library.
A haka na fita, ina ta jajjan gyalena saboda rashin sabo. Gashi kaina a kwance yake, duk yanda nayi akan in rufe gashin, ɗan kwalin baya da girma, hakan ce ta sanya dole na haƙura, Amman sai na yafa gyalen bisa kaina, ni kaina na san nayi kyau, kaman wata amarya, ban ɗauke da jikka, saboda karatu zani ba biki ba, waya ta ce kawai a hannuna, sai litattafai na na text book da handout, a haka na fito har na isa ga motar.
Yana daga ciki ya sanya hannu ya buɗe mani. Shiga nayi ina mai sakar mashi ɗan ƙaramin murmushi, shima yayi kyau cikin dakakkiyar shadda mai ruwan makuba, kanshi sanye da hular ƙube, sai zuba ƙamshi yake da fara'a kaman yanda ya saba.
Jan motar yayi yana mai cewa
"Gimbiya ta barka da fitowa"
Sake sakin murmushi nayi, ina mai ɗan sunne kaina ƙasa.
Gaishe shi na shiga yi, da salon koyon magana ta ya shiga amsa mani, na daga cikin abunda ke ƙara burgeni da Sir Salim ɗin kasancewar shi mutum mai ban dariya, tin baka sakin jiki dashi, har sai ka koma kana sakin jiki dashi, har in ma baka ji ɗuriyar shi ba ka bincika, masalan in kana cikin hali na ɓacin rai.
Kai tsaye bakin library mukayi parking, littattafan ya amsa daga hannuna, muka jera har cikin library ɗin muka samu kujeru muka zauna.
Kowa dake library ɗin mu yake kallo da ban sha'awa, mun dace da juna sosai, gashi daka kalli fuskokin mu, kasan muna cikin zallar farin ciki.
Ba ɓata lokaci muka fara abunda ya kawo mu, har zuwa kusan ƙarfe shida. Littattafan muka rufe, yayin da Sir Salim ɗin ya kirawo Ammin shi video Call muka shiga gaisawa, ga dukkan alamu taji daɗin ganin yaron nata yana yaɗa manufar shi ga Suhan ɗin.
Ɗan barkwanci tayi mana tana mai kashe wayar haɗi da cewa bari tabar mu mu tattauna, ni sai ma duk ta sakar mani kunya.
Shi kaɗai ke surutun shi, nikau daga eh sai a'a sai murmushi da nake ta fama doka wa. Yaba ƙofar shigowa baya, yayin da ni kuma nake zaune ina fuskantar wanda suke shigowa, hasken fitilar library ɗin tar a kan fuska ta, masalan yanzu da marece ya soma kawo jiki.
A wayar tashi dai still ya buɗo hotunan yaran shi yana nuna mani, yaran masha Allah, farare tas dasu, kaman ƴaƴan larabawa, da gani dai wannan Hasken Ammi ne suka biyo yaran, tinda ko ita ma'un bata ko kai ni haske ba, gashi shima Sir Salim ɗin kai tsaye bazaka ce mashi fari ba, ko baƙi.
Yaran sun burgeni, har ƙanwar shi dake karatun likitanci a Sudan mai suna Asiya Saida ya nuna mani.
Amsar wayar nayi a hannu na ina kallo haɗi da faɗin
"Masha Allah, ta fika kyau, tayi maka wayau, ita ta biyo kyawon Ammi sak"
Na faɗa ina mai ɗan sakin dariya.
Shima dariyar yayi cikin wani irin salo, yana faɗin "Kedai faɗi gaskiya, ko kowa zai ce Lil ta fini kyau, ai ke ba zaki faɗi haka ba, ko kuwa?"
Ɗan jinjina kai nayi ina mai cewa "Umm gaskiya kam Yallaɓai salim"
"Wuuuuuuuuuuu"
Abunda naji kowa na faɗa kenan a library ɗin, ga dukkan alamu dai wani abu ne suka gani daya basu mamaki ko ya burge su, sai kuma naga duk suna Miƙewa mazan su da matan su.
Hakan ce ta sanya ni kai kallo na zuwa ga ƙofar da nake fuskanta, har yanzu murmushin bai bar kan fuska ta ba, bansan dalili ba yanzu indai ina tare da Sir, Salim ɗin nake tsintar kaina cikin irin wannan farin cikin.
*Dummm*
Gabana ne ya ruguje ya faɗi, ganin ko wanene tsaye ƙofar shigowa library ɗin yana fuskanta ta, a hankali ya shiga takowa cikin salon tafiyar nan tashi da bazan taɓa iya mantawa ba.
Sanye yake cikin ƙananan kaya fari ƙal ɗin wandon jins mai bala'in taushi, rigar shi ƙirar kamfanin gucci mai matsakaicin tsawo, kalar yellow ce mai masifar kyau ta ɗan sirka da orrange, hannun ta kuma gajere ne sosai, hakan ce taba damatsan hannuwan shi damar fitowa tar tar dasu.
Ƙafafun shi sanye cikin snickers masu masifaffen kyau da tsada, farare ne suma tas dasu masu adon yellow mai orrange a ciki.
Fuskar nan tashi Sam babu walwala ko annuri a ciki, hasali ma idanun nashi daɗe suke cikin wani baƙin glasa mai sheƙi da walwali.
Hannuwan shi ɗauke da makullin mota, sai kuma wayoyin shi guda biyu ƙirar Iphone 11 Pro Max.
Ni yake nufowa kai tsaye, duk takunshi ɗaya daidai yake da bugawar zuciya ta sau kusan ɗari.
Yana nufo ta inda nake zaune ne, ya shiga zare glass ɗin dake saman fuskar shi, ko da zan suma in farfaɗo, koda zan mutu inbar duniyar sannan in dawo. Koda zan shekarar annabi Adamu ban sanya shi a idanuna ba, bazan taɓa iya mance ƙamshin turaren nashi ba, ba kuma zan taɓa iya mance salo da izzar tafiyar tashi ba, ba kuma zan taɓa iya mance kalar da fuskar shi kan bada ba a duk lokacin da yake cikin matsanancin ɓacin rai.
Hannun shi marar ɗauke da komai sanye yake cikin wani silver ɗin abun hannun azurfa anyi mashi ado da ƙaton stone ɗin dymond mai masifar kyau da walwali sai ɗaukar ido yake, soke yake cikin aljihun wandon shi, yayin da gudan yake ɗauke da baƙar agogo ta kamfanin Iphone ɗin.
Ban san lokacin da na miƙe ba zunbur, ina mai dafe bakina da dukkanin hannuwa na, 🙊tsoro ƙarara da firgita suka bayyana a kan ƴar zagayayyar fuskar tawa, wayar Sir, Salim ma dake hannu na, bansan lokacin da na sake ta ba ta faɗi ƙasa wanwar.
Ganin hakan ne da Sir Salim ɗin dake ta faman zuba man surutu yayi, shima bai san lokacin da ya juya da kujerar ba, domin ganin Abunda ya firgita ni haka lokaci guda har ina sakar mashi wayar shi ƙasa.
A hankali shima ya shiga miƙewa , daidai ƙarasowar Ya Ameen ɗin ta wajen Kujerun da muke kai zaune.
Kowa ya maida mu talabijin a library ɗin, duk mu suke kallo, gabaki ɗaya attention ɗinsu ya dawo kanmu kacokam. 👀
Ganin hakan da Ya Ameen ɗin yayi ne, ya sanya shi jawo kujera ɗaya ya sanya ta tsakiyar tamu ni da Sir, Salim ya zauna yana mai ciƙa ma Sir Salim ɗin hannu alamun suyi musabaha. 🤝🏻
Jiki a matuƙar sanyaye shima Sir Salim Ɗin ya shiga miƙa mashi hannu ɗin sukayi musabaha.
"Sunana Al'ameen Almustapha Dambulan*
Ya Ameen ɗin ya faɗa yana mai sakin wani kiler smile a saman fuskar shi, ina kula dashi har yanzu da na gagara zama.
Murmushin da naga yana saki ne saman fuskar tashi ya ƙara taimakawa wajen ruɗewa ta.
Miƙewa tsaye naga Sir Salim Yayi, cikin girmamawa gami da ƴar jinjina kaɗan haka,👍🏻 hannuwan shi daidai kunnen shi, ya shiga faɗin
"Allah yaja zamanin Yariman Matasan Arewacin Nigeria"
Sake kwalalo idanu nayi,😳har yanzu fa na gagara zama, kuma ban sauke hannuwa na daga bisa bakina ba. Da hannu Al'ameen ɗin yayi ma Sir, Salim Alama da ya zauna da hannu, ba musu ya kuwa zauna.
Niko da nake tsaye sai faman tsiyayar zufa nakeyi, zuciya ta sai faman bugawa takeyi fat fat kaman zata tsago ƙirjina, har yanzu kuma gogan nawa bai ko kalli ta inda nake tsaye ba, sai ma zaro wayar shi da yayi ya shiga daddannawa.......
*Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa.*
🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣
0 comments:
Post a Comment