Kusan zamu iya cewa a tare suka sauka ƙasar. Mudi ne yaje ya ɗauko Alhaji Mustapha daga Airport, ita kanta Hajiya Kubra taji matuƙar mamakin ganin mijin nata, to sai dai isa da mulki irin nata ba zaya iya bari ta tambaye shi ba, masalan ma yanzu da harkokinta suke ta ƙara bunƙasa, ita kanta bata da lokacin kanta balle na wani mijin nata.
Bayan sun tattauna ta yanda zasu ɓullo ma al'amarin nasu ne, har zuwa yanzu dai basu samu matsayar ta yanda zasu faro ma al'amarin ba.
Bunciken komai suka fara yi, hatta dasu mudi ɗin sun shaida cewa Alhaji ƙaramin bai zo gidan ba, basa so Hajiya Kubra ta ankare da abunda yake faruwa, wannan ce ta sanya su barin binciken ta gidan, sai kuma suka koma sauran kamfanonin Al'ameen ɗin da kuma duk wanda yake da access dashi.
****************************
"Ina fatan dai ka gane ni?"
Al'ameen ɗin ya faɗa cike da basarwa, bayan ya bar latsa wayar da yakeyi, ya maida duban shi kan Sir, Salim.
Cikin kulawa sosai Sir Salim ɗin yake duban Ya Ameen ɗin duba na tsanaki, a hankali ya miƙa hannu, jawo kujerar da nake zaune kanta kafin in miƙe ya tsaye yayi.
"Zauna sweet heart"
Sir Salim ɗin ya faɗa cike da kulawa da zallar soyayya a idanun shi.
Bani da zaɓi illa zaman, domin a yanzu dai bana iya cewa ga abunda ke kai komo a cikin zuciya ta, tunani ne haɗe da mamaki da fargaba suka haɗe suka bada wani yanayi a saman fuska ta.
Ya zuwa yanzu na saki hannuwa na dukka a bisa cinya ta, saidai na kasa bari in haɗa ido da Ya Ameen ɗin, wata irin kunya ce ta taso mani ta baibaye ni, ga tsarguwa da nake fama da ita, duk da har yanzu shi gogan bai ko kalle ni ba.
Sir, Salim ne ya maida hankalin shi akan Al'ameen ɗin bayan ya sakar mani wani ƙayataccen murmushi, duk da har yanzu a cikin zuciyar tashi tarin tambayoyi ne a ciki.
Sai a lokacin ya kalli Ya Ameen gami da bashi amsa.
"Ayya Yallaɓai, Saidai fa bana da labarin ka a wajen Yallaɓiyar tawa"
Ya faɗa shima cikin son dakar da zuciyar shi, cike da ƙwarin guiwa.
Ɗan murmushi iya leɓo Ya Ameen ɗin yayi, yana mai ɗan juyo da kujerar shi yana fuskantata, turo mani wayar shi yayi bisa table ɗin yana faɗin.
"Number ɗin Umma zaki sanya mani anan. Ga dukkan alamu dai baki Iya gaisuwa ba, duk da dai ni ba wajen ki nazo ba, Umma nake son gani"
Cikin rawar baki, murya ta na sarƙewa na shiga bashi amsa
"Umma bata da waya, inda take babu network". Daga haka na duƙar da kaina zuwa ƙasa, bansan me ke shirin faruwa dani ba, amman wasu hawaye ne naji suna yankowa ta cikin idanu na, haɗa idanun da nayi dashi, sai na gaza tantance ko na menene, a hankali na shiga maida su, ina mai miƙewa da niyyar barin wurin.
"Ki bani Address" ya faɗa a gajarce cikin dakiya da son kauda zargin wani abu daga cikin zuciyar Sir, Salim ɗin.
Cak naja na tsaya, shawarar in faɗa mashi ko kada in faɗa nakeyi a cikin raina, to saidai ya Ameen ɗin ya wuce haka a wuri na, bana jin akwai wata alfarma a wajena wadda zai iya nema in kasa yi mashi a rayuwa ta.
A sace na ɗan juyo da niyyar kallon shi, idanun mu ne suka sarƙe cikin na juna, gaza ɗauke idanuna nayi, kaman yanda shima har yanzu bai janye waɗannan mayatattun idanun nashi ba akaina.
A hankali na fara janye nawa, ina mai buɗe baki dakyar cikin sarƙewar harshe na shiga cewa
"Sunkui, Jigawa State"
Ina gama faɗin haka, sai gani nayi ya miƙe gami da sake ba Sir, Salim hannu suka sake yin Musabaha, har yanzu dai ba wanda yace da kowa komai.
Juyawa yayi ya raɓe ni ya wuce gami da ficewa daga library ɗin.
Kai na a ƙasa na shiga bin shi da kallo a sace.
Ƙamshin turaren shi har yanzu bai bar wurin ba, ga wata irin tafiya da yakeyi cikin salon shi, irin na cikakken ɗa namiji.
Ajiyar zuciya na saki, daidai lokacin da na hangi tashin motar tashi, ya ja ribos yabar wurin.
A sanyaye na koma zuwa ga table ɗin na shiga tattara litattafai na, domin dai a yanzu bansan abunda zan iya faɗama Sir Salim ɗin ba, idan har ya jefo mani wata tambaya.
Shima da kallo yake bina, menene alaƙa ta da Yariman ne? Shin a taƙaice ma wai wacece ni?
Dambulan ɗin, family ne daya shahara a faɗin ƙasar, da wuya ka tara mutane goma ciki ba'a samu biyu ba da suka ce sun sanshi, ƙaramcin su, da irin yadda suke taimakon matasan ƙasar ne ya sanya da wuya kaji family ɗin da suka ce basa da tabon alkhairin su.
Miƙewa yayi ya shiga bin baya na, ganin na wuce shi ba tare da na ce mashi uffan ba, watau ma kenan bata so ta shiga motar tashi ya mayar da ita Hostel?
Sake ɗaga ƙafa yayi ganin har na gitta motar tashi da niyyar wucewa cikin sanyin jiki matuƙa.
Shiga motar yayi gami da shan gabana da motar, ya sanya hannu ya buɗe mani gaban motar.
To nima ɗin dai gudun zargi ko wani tunani daban, ya sanya ni shiga motar, ko ba komai dai Sir Salim ɗin har ga Allah bai san wanene Ya Ameen ɗin a guri na ba, kuma ko da wasa ban taɓa mashi makamanciyar maganar data shafi kaf Family ɗin Alhaji Mustaphan ba.
Kaman daga sama naji yayi parking, gami da ɗage glassan motar da suke tint, ya sakar mana Ac, a hankali naji wata ni'ima da sanyi na shiga ta, ajiyar zuciya na shiga saukewa a hankali a hankali, ina mai jingina kaina da murfin motar tashi, haɗe da runtse idanuna gam.
"Menene alaƙar ki da Yariman Matasan?"
Naji ya wurgo mani tambaya cikin bazata.
Ban ce dashi uffan ba, shima bai kuma cewa komai ba, buɗe idanuna nayi a hankali na aza su akan Sir Salim ɗin.
Wasu abubuwa naga suna yawo a cikin ƙwayar idanun nashi, kishi ne, tattare da tarin tambayoyi acikin idanun nashi.
A hankali na janye idanun, cikin ƙwarin guiwar da bansan ina da ita ba, na shiga cewa
"Yayana ne"
"Yayanki ta ina?"
Nauyi tambayar tayi mani, beside ma ban taɓa tinanin irin tambayar ba daga gareshi.
Ban da zarrar ce mashi komai, hakan ce ta sanya ni jan bakina na ɓame.
Nannauyar ajiyar zuciya Naji ya saki, sannan ya sake cewa
"Meyasa baki taɓa bani labarin shi ba?, anya hakan da kikayi yayi daidai? Ashe ban kai matsayin da zan iya sanin komai da ya shafi rayuwar ki ba?"
Maganganun shi sun yiman nauyi a zuciya, ga wani miki dake taso mani cen ƙasan zuciya ta, wani al'amari da na daɗe rabon da in ji shi a jinin jikina ya shiga taso mani.
Ban san lokacin da na saki wani tsumammen kuka ba, rufe fuska ta nayi da dukkanin tafukan hannuwa na, ina mai sauke waya ta bisa cinya ta.
Bai ceman ƙala ba, kaman yadda bai yi yunƙurin hanani ba. Bai san dalilin kukan ba, ya barta ne tayi koda zata samu sauƙin raɗaɗin da take ji a cikin zuciyar ta.
Na kai kusan minti goma ina yi, har saida na gaji don kaina na daina, tissue wadda ta ɗauki sanyin ac ɗin dake cikin motar, gami da wani ni'imtaccen ƙamshin turare ya miƙo mani.
Amsa nayi ina mai goge hawayen dake fuska ta, lokaci guda ina mai juyawa na kalle shi, sannan nace
"kayi haƙuri, na tuno da wani abu ne, tabbas shi ɗin wannan yayana ne"
Har yanzu dai ba wai ya gamsu bane, kuma koda ba komai tabbas akwai wata alaƙa tsakanin shi da ita, duk da dai ba zai iya cewa ya karanci wani abu ba daga fuskar Yariman Matasan ba.
Kunna motar yayi, gami da jan ta, fuskar nan tashi ta haɗe kaman bai taɓa dariya ba, yana da kishi, yana da matuƙar kishi, masalan ma akan abunda yake so.
Har bakin hanyar Hostel ɗin ya ajiye ni, bai ceman ƙala ba, nima bance mashi ba, na ɓalle murfin motar gami da ficewa, har waya ta tana faɗuwa ƙasa cikin motar ba tare da na kula ba.
A matuƙar sanyaye na isa Hostel ɗin namu, su khadeeja babu tambayar duniyar da basu yi mani ba, amman ban kula su ba, har wayata da na kula bata tare dani, saidai nasan tana a motar Sir, Salim na baro ta.
Daren dai a haka nayi shi cikin wani irin yanayi, dana kulle idanu na sai fuskar Ya Ameen ɗin ta bayyana a cikin ƙwayar idanun nawa.
**********************
"Wai ance ana sallama a waje"
Hajjo dake tsakar gida tana ta faman shara, yaro yayi sallama, ajiye tsintsiyar tayi tana mai gyara ɗaurin zanen ta.
"Inji waye?" ta maida ma yaron daya shigo lokacin.
"Nima Wallahi ban sanshi ba, da dai ƙatuwar mota yazo"
Ya faɗa cikin son juyawa, yana mai gara ƴar tayar shi, da niyyar ficewa.
Jin haka ne da hajjon tayi, ya sanya ta saurin tattara sharar ta juye cikin wani buhu da yake ajiye gefe.
Leƙawa tayi ɗakin Umman tawa, gama shiryawr ta kenan, da nufin zuwa wata barka da akace anyi haihuwa nan bayan gidan su.
Sanar da Umman tawa tayi wai ga Malamin Su Hauwa'u nan yazo yana waje.
Umman ce ta amsa mata, tana mai zura hijabin nata, gami da ficewa domin shigowa dashi.
Turus taja ta tsaya daga bakin ƙofar gidan.
Murna da farin cikin ganin matar fal a cikin ranshi, sannu a hankali ya shiga takawa zuwa wajen da umman tawa take tsaye.
"Muhammadu??? Kai ne?"
Umma tawa ta faɗa cikin son gasgata abunda idanuna ta suke nuna mata, gani takeyi kaman gizo idanun nata suke mata.
"Nine Umma, na same ku lafiya?"
Ya faɗa cikin girmamawa, yana mai daidaita tsayuwar shi ɗan nesa kaɗan da inda umman tawa take tsaye.
"Shigo daga ciki mana"
Abunda ta faɗa kenan, tana mai juyawa zuwa cikin gidan.
A baya ya shiga binta har zuwa cikin gidan, rana ta kawo tsakiya, hakan ce ta sanya babu inuwa ko kaɗan a tsakiyar gidan.
Ɗakin da yake nata, shi ta sake turawa tana mai ɗage labulen, sannan ta shiga gami da shimfiɗa mashi tabarmar kaba.
Shiga yayi ya zauna, yana mai tankwashe ƙafafun shi. Fita umman tayi da niyyar zuwa kiran Hajjon da ta riga ta koma ɗaki.
Da kallo ya shiga bin ko ina na ɗakin, wani irin tausayn su ne yake taso mashi cen ƙasn zuciyar shi, Meyasa suka zaɓi rayuwa a irin wannan halin? Ashe har muzgunawar da akeyi masu acen sun kwammace su zauna a irin wannan yanayin? Dubi ɗakin fa? Kalli gidan. Zuciyar shi ce ta cigaba dayin zafi, tabbas ya zama wajibi ya cire su a wannan yanayin, ya zama wajibi yayi iyakar ƙoƙarin shi wajen ganin ya inganta rayuwar su, wannan haƙƙin shi ne, alƙawari ne kuma ya ɗauka.
Har yanzu ji takeyi kaman almara, har yanzu bata gasgata Muhammad Al'ameen ɗinne zaune a ɗakin nata ba.
Ta yaya akai ya gano inda suke?
Ta ina ma yasan da wannan ƙauyen kuma har yazo? To ko dai wani ɓalli a labarin nata ya fita a duniya ne?
Da haka ta ƙarasa ɗakin da Hajjon take, ta sanar da ita tayi baƙo tazo su gaisa.
Daganan ta wuce ta ɗauko kwanon sha, ta kandamo ruwa a cikin randar ta nufo ɗakin, inda ta tadda Hajjon har sun gama gaisawa da Al'ameen ɗin cikin girmamawa da mutunta juna, duk da ba wai ya san ko ita ɗin wacece ba, ko kuma ita ta san ko shi ɗin wanene ba.
Fitowar ta yayi daidai da shigar umman tawa ɗakin, zama tayi gefen ƴar yaloluwar tabarmar dake yade gefe guda na ɗakin, da alama nan ne wurin kwanan su.
Sake gaisawa sukayi sosai cikin girmamawa, har take tambayar shi mutanen gidan da wajen su Saudat da Afnan.
Cikin son kauda komai yake murmusawa yana faɗin suna lafiya.
Ɗan shiru ne ya biyo baya, sai kuma Al'ameen ɗin ya muskuta, tare da sake duƙar da kanshi ƙasa ga matar da yake fata da burin ta zama surukar tashi. Sannan ya shiga cewa
*"Umma nazo ne takanas domin in baki haƙuri a bisa dukkanin Abunda suka faru bayan tafiya ta, haƙiƙa banji daɗi ba ko alama, hasalima dawowa ta nan ba da daɗewa ba na ji labarin barin ku gidan, nasan koma minene ya faru da sanya hannun mahaifiya ta, umma nasan kunyi haƙuri, ina mai ƙara baku haƙuri a madadin mahaifiya ta, ki taimaka umma ki dawo gare mu a karo na biyu, ina mai tabbatar maki da insha Allahu komai yazo ƙarshe, umma ki taimake ni umma, nasan ba'a kyauta maku a gidan nan, saidai ina iya ƙoƙari na ganin hakan bata faru ba. Nazo ne musamman domin in nemi yafiyar ki, sannan abu na biyu da yake tafe dani, ina so ki taimaka ki bani auren Suhan nayi alƙawarin riƙe ta amana, zan tallafi Rayuwar ta umma, zan sanya ta manta da duk wani maraici da wahala da tasha a kaf rayuwar ta umma"*
Tinda ya fara magana umman ke ɗan sakin murmushi, saidai maganar shi ta ƙarshe ya sanya gabanta rugujewa ya faɗi, da ƴar firgita ta cenza akalar kallon da take mashi.
Bata ce komai ba, ƴar nisawa tayi tana mai muskutawa a hankali ta sauke ajiyar zuciya.
Tabbas kallon shi takeyi, iyakar gaskiyar shi kenan, abunda ya kawo shi kenan, Al'ameen ɗin ba tin yanzu ba, ta riga ta sani mutum ne da baya da ɓoye ɓoye a rayuwar shi, ta san za'a rina, ta san hakan zata faru ko ba daɗe ko bajima, na daga cikin abunda ya sanya ta barin gidan kenan gudun faruwar hakan.
Amman da yake Muhammadu daban yake a cikin mutane, tinanin shi ya sha banban dana sauran, tabbas ba tantama da gaske yake wannan maganar har cikin zuciyar shi.
Nisawa tayi a karon farko kenan da zata ce wani abu tin bayan gaisawar da sukayi dashi da farko.
"Naji duk bayanin ka Muhammadu, haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki da jin wannan zancen naka, ko ba komai nasan irin ƙoƙarin da kayi a kanmu, da kai da mahaifin ka harma da mahaifiyar taka babu abunda kuka yi mana, kawai yanayi na rayuwa ne ya sanya mu cenza wurin zama, to saboda haka babu abunda kuka yi mana. Maganar Suhan kuma babu abunda zaka nema wurin mu mu Gaza baka shi, saidai yanzu haka akwai maganar wani a kanta, tana cen makaranta tana karatu, malamin ta ne, don harma manya sun shiga cikin Al'amarin, bana jin ko kai idan zaka iya bada gudunmuwar ruguza wannan auren nata, yana matuƙar sonta, kuma kowa nashi yana sonta, Kaga kai kuwa mahaifiyar ka ba zata yi na'am da wannan al'amarin naku ba, da haka ne nake mai baka haƙuri, ka bita da addu'a da fatan alkhairi, har abada ba zamu taɓa iya mance alkhairin ka gare mu ba"
Tin da ta fara magana shima kanshi yake sunkuye ƙasa.
Bai taɓa jin kalami da suka ratsa kunnuwan shi ba kai tsaye suka wuce kai tsaye zuwa cikin ƙwaƙwalwar tashi ba irin waɗannan.
Umman Suhan, ita ce yau take bashi haƙuri, da jaddada mashi cewa Suhan ɗin nada tsayayye, lallai wannan al'amari duk yanda ya kai da ɗaukar shi ƙarami ya zarce yanda yake tinani.
Jikin shi har ƴar rawa yakeyi, ƙarfin halin ce ma umman yayi "Umma nine na fara neman ta, nine farko, in ma akwai wanda ya nema to bayan nine, umma ki taimaka mani"
Itama sake girgiza kanta tayi,
"Muhammadu bana jin daɗin yanda kake mani magiya akan abunda nasan kafi ƙarfin shi a gurina, saidai sanin kanka ne cewa bakyau nema kan nema"
"Umma nine na fara nema, Umma ki tambayi Dad kiji, ya san da maganar, ya san da zancen"
Shiru tayi cike da mamaki, idan ada aka faɗa mata cewa Al'ameen ɗin zai yi magiya agaba akan Suhan ɗin, to fa lallai ba zata taɓa yarda ba, kallon shi takeyi da wani irin yanayi.
Al'ameen ɗin ba irin yaran nan bane mayaudara, hasalima ita bata taɓa jin ance yau ga budurwar shi ba, tinda take a rayuwar ta, balle ta ɗauka da yaudara yazo.
Al'ameen yaro nutsattse ɗan gayu, mai ji da kuɗi, sarauta,ga uwa uba ilimi.
Matasa da dama na fatan ina ma ace sune shi ɗin, dukkan qualities ɗin dake tattare da Salim ta san Al'ameen ya doke shi ya shanye.
Saidai bata fatan Abunda zai sanya ta karya ma Salim ɗin da Hajiya Khaltum ɗin alƙawarin data ɗaukar masu.
Ta sani cewa tuni Al'ameen ɗin ke son Suhanan, to saidai bai furta ba, koda ya furta, ita bata san da hakan ba, koda taji ƴan maganganun ta ɗauka zance ne irin na mutane da yaɗa jita jita.
Shiru ɗakin ya ɗauka na wani lokaci, kowa da abunda yake saƙawa a cikin zuciyar shi, ganin shirun yayi yawa ne ya sanya shi miƙewa gami da yima umman sallama ya fice. Itama da kallon tausaya wa ta shiga bin shi, bata da yanda zata yi, tana tsoron kaidin hajiya kubra, tana tsoron kai ɗiyar ta inda zata koma ƴar gidan jiya, hajiya kubra ba lafiya bace, duk da bata so ace Al'ameen ɗin ya nemi alfarma ba a karo na farko a duk zaman da sukayi tare ya rasa ba.
Shima dai dakyal ya isa ga motar tashi, juwa yake gani da jiri, fuskar nan ta kaɗa tayi jajur, haka ma idanun.
Biyu biyu yake gani har ya kai ga shiga cikin motar, saidai ya kasa tadawa balle ya ɗauki hanyar barin ƙauyen.
Dole ne ya nemi Dad, dole ne ya koma gidan nasu, wannan karon baya jin idan zai iya kuma haƙura, masalan ma daya ganta jiya ta ƙara kyau da wayewa, ga ilimi daya fara ratsa ta, hasken ta ya kuma fitowa fayau, sanyin ta da natsuwar ta har yanzu suna nan tattare da ita.
Kenan shine wanda ya ganta dashi jjiya?
Kenan shine wanda yake ƙoƙarin yi mashi juyin mulki?
Ba laifin kowa bane sai na Bilal, ta yaya akayi ma har hakan ta faru ba tare da yayi gaugawar faɗa mashi ba?
Kenan da yanzu bai rasa ta ba!
Wani sashe na zuciyar shi ne yake sanar dashi cewa
"Ai har yanzu baka rasa ta ba, kada ka sare da wuri Al'ameen, kai ba irin wanda zaka nemi yarinya mace bane da sunan aure ka rasa"
Ashe haka matan duk da suke cewa suna son shi da aure suke ji, a duk lokacin da ya ƙi sauraren su?
Daƙyal ya samu ya kunna motar, ya jata yana mai ficewa daga ƙauyen.
Hanyar Abujan ya ɗauka kai tsaye ba tare da shayin komai ba, Dad shi kaɗai ne last hop ɗinshi, wannan karon zai nemi taimako daga wajen mahaifin nashi, ba tare daya tsaya tunanin komai ba.
_Bayajin wannan karon idan har Hajiya Kubran zata iya zama shamaki a gareshi wurin samun Suhan ɗin tashi a karo na biyu........._
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~40~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Kai tsaye gida ya dosa, baya son abunda zai ɓata mashi lokaci ko alama.
Har bayan da yayi parkinga harabar gidan, babu wanda ya gane shi sai mai gadi da ya buɗe mashi ƙofa.
Basuyi mamakin ganin Alhaji ƙarami ɗin ba, saboda su dai sun san da wuya ace ya ɓata a faɗin nigeria ɗin.
To saidai mamakin su ɗaya sabuwar mota da suka ga Al'ameen ɗin ciki.
Mudi driver yaso ya tsayar dashi da surutu, to saidai ganin Alhaji ƙarami ɗin kaman yana cikin hali na sauri ko ujila ne ya sanya ya kyale shi har sai ya fito.
Kai tsaye sashen Alhaji ya nufa cikin takun shi na sauri da ya ƙara mashi wani irin kyau da kwarjini.
To saidai Alhaji Mustaphan basa gida shida Bilal a daidai wannan lokacin.
Sashen Mom ɗin tashi ya nufa, lallai yayi missing ɗinta ba kaɗan ba, kasan ɗa da mahaifi, saidai wannan dambarwar da ake ciki da ya riga ya san ita ce ummul aba'isi, kuma ya san suna daf da raba gari da ita, ya sanya shi kaf fara'a da walwala da sukayi saura a fuskar tashi gushewa.
Ta gaban maree da take duƙe tana matse mopper ya wuce, idanun ta kaman zasu faɗo ƙasa tsabar kallo. Har batasan lokacin da ta buɗe baki ba cikin shaƙe murya ta shiga gaida shi.
To bai ma ko kula da ita ba, koma da ya kula ɗin bana jin idan har zai iya tsayawa sauraron ta a daidai wannan lokacin.
Da gudu ta kwasa tayi sashen nasu na masu aiki, a kwance ta tadda mama Talatu tana barcin ƙalula, faɗa mata tayi bisa jiki kaman zata karyata, ta shiga sakin uhun murna.
A firgice mama talatun ta farka tana cewa"jakar uba, ke shashasha uban ne kuma ya faru?"
Bata ma ko kula da ashar ɗin da mahaifiyar tata ta ɗura ba, ta shiga faɗin
" Mama wallahi Yariman Matasa ya dawo, Ya Ameen ɗina ya dawo yanzu na ganshi har gaida shi nayi, ya kuma tsaya ya saurareni sosai"
Itama wani uban ihun murna ta saki, jin cewa wanda suke jira ya dawo, kuma ma wai har ya saurari ɗiyar tata.
Su mama Saude ne da suke tsakar gida suna aikace aikacen su, ta wani ɓangaren kuma suna ƴan gulmace gulmacen su tsakanin su, da gudu suka kwasa zuwa ɗakin, jin sautin ihuna na tashi.
Saidai koda suka je, basu ga wani abun agaishe ku ba, sufa sun fara zargin wani abu, dole tsakanin maree da mama talatun kaman akwai wata alaƙa mai ƙarfi, sannan sun kula da mama talatun yanzu da yanda take cutar su akan komai da ake bata ana cewa ta raba masu.
Juyowa sukayi suna mai sakin tsoki, koda suka koma ga aikin nasu, gulmar mama talatun suka dasa, harma da maree ɗin, yanda take fitsararra mara tarbiyya, mama talatun kuma tana kallon ta bata tsawata masu.
Su kau jin daɗin su suka cigaba da yi, suna masu tsara yanda abubuwan zasu cigaba da wakana bayan dawowar Alhaji ƙarami ɗin.
Sun shirya amsar gidan, sun shirya su gaje gidan, ta yanda babu wanda zai faɗa aji a gidan bayan su.
************************************
Kai tsaye ɗakin ta ya nufa da yake upstairs, koda yayi sallama falon babu kowa balle a amsa mashi. Kwankwasawa ya shiga yi.
Ba daɗewa ta buɗe ɗakin, da gani ma bacci take ɗan taɓawa.
Cikin mamaki ta rungume shi, tana mai farin cikin ganin yaron nata ya samu sauƙi yana tsaye a bisa ƙafafun shi.
Ɗan zame jikin shi yayi, yana mai kai zaune bisa wata haɗaɗɗiyar sofa da take ƙwalli ƙwal a cikin ɗakin, cikin ajin da ya riga ya zama jinin jikin shi,yake gaida Mom ɗin tashi.
Amsawa ta shiga yi, tana nuna farin ciki ta zalla cikin nuna isa irin tata.
Tambayar jikin nashi ta shiga yi, yana mai amsa mata, ta kula da rashin walwala da baya yi, saidai ta bar hakan da ko gajiya ce da yayi.
"Son ka ƙarasa part ɗinka kayi wanka ka huta ko, zan sanya maree ta kawo maka abinci yanzu, kaman na san kana hanya na sanya ta jiya ta gyara ɗakin."
"No mom, bana buƙatar komai, kada ki aiko ta, bana son yarinyar nan na shiga man sashe" ya faɗa yana mai miƙewa da niyyar wucewa.
"OK ita ce baka so tana shigar maka ko? Da yake ba waccen koɗaɗɗar bace ba ko?
Ta faɗa tana mai bin shi da kallo, cikin matuƙar ƙuluwa, to saidai da yake ƴar duniya ce ta ƙarshe, bata bari hakan ta bayyana ba akan fuskar ta.
Ɗan murmushin gefen baki yayi, yana mai wucewa zuwa ga fita kai tsaye. Ɗann kaɗa kanshi yake yi da makullin da yake hannun shi, yana rayawa a cikin zuciyar shi "Mom kibar ma wannan maganar ta kusa zama surukar ki da izinin Allah" ya faɗa a fili yana mai idasa ficewa daga sashen nata.
Koda ya isa ɗakin nashi, bai iya yin wankan ba saida ya kira Alhajin nasu domin yaji ko yana ina yaje ya same shi.
Da mamaki Alhajin ke tambayar Son ɗin nashi yana ina ne.?
Cemashi yayi yana gida.
Cikin mamaki Alhaji Mustapha ɗin da yake zaune a guest House ɗin nashi shi da Bilal yake ce mashi ya zauna gida gasu nan zuwa shi da Bilal.
Sai da gaban shi ya faɗi jin an ambaci sunan Bilal ɗin, amman dai koma miye zai tsaya yaji wane uziri zai bashi kuma.
**********************
Har washe gari bana da wata walwala, haka kawai sai in tsinci kaina da wata irin muguwar faɗuwar gaba.
Ban san dalili ba, sai ga hawaye na shatata a idon nawa, alhali ba wanda yace man komai, hasalima su Raihanan na lecture.
Ban ƙwari kaina ba, nayi mai isata, sannan naje na wanko fuska ta, bansan dalilin kukan ba, kuma ba zance ga dalili ba.
Wata yarinya ce tayi sallama ta kawo mani wayata wai inji Sir Salim yace tace man zai kira in amsa mashi.
Da "To na bita, yayin da ta juya tana mai ficewa.
Komawa nayi na kwanta lamo bisa gadon nawa.
Ilai kuwa sai ga wayar shi ta shigo, har ta katse ban ɗaga ba.
Sake kira yayi, cikin kasalar jiki na ɗaga kaman bana son yin magana.
" Assalamu Alaikum" na faɗa murya ta cen ciki sosai.
Daga ɗaya ɓangaren ya amsa mani.
"Good morning sweet heart"
"morning Sir"
Abunda na iya bashi amsa kenan, ina mai jan bakina nayi shiru.
"Dear ta ko baki lafiya ne? Naji muryar taki cen ƙasa"
"Lafiya ta lau"
Na bashi amsa, har yanzu muryata bata fita sosai.
"me ya hana ki attending lecture ɗita yau? Gashi har nayi accesment"
Ya faɗa daga ɗaya ɓangaren.
"Hummm" kawai na samu zarafin ce mashi. Bai gaji ba ko nuna ƙosawa akan rashin amsa mashi sosai da banayi, ya sake cewa "Sweat Heart ko nayi laifi ne?uhm idan nayi laifi ne a yafe mani, in kuma maganar nan ta jiya ce, ki barta kawai ni na janye tambayoyin nawa, bana son abunda zai kawo mana matsala a tarayyar mu, inaso ki fahimceni, ni ba zargin ko wani abu nakeyi ba, kawai dai tsabar sonki da kishin ki ne nakeyi, amman tinda kince yayan ki ne abarshi a haka, ina fatan na wanke kaina yanzu?
Ya faɗa yana mai sakin ɗan murmushi da yake al'adar shi ce
Wata irin kunya ce ta kama ni, idan ma laifi ne ni na san nice nayi, kuma nice na cencenci in bashi haƙuri, ba shine ya cencenci ya bani ba, ko ba komai babu wani laifin da yayi mani. Tabbas nuna kishi akan abunda abunda kake so ba haramun bane, hasalima hakan sunna ce mai ƙarfi. Kuma ko ba komai yanzu ne na tabbatar da haƙiƙanin son da Sir Salim ɗin yake mani.
Shikau gogan Ya Ameen isa da mulki ma ba zasu bari ka fahimci haƙiƙanin Abunda yake zuciyar shi ba, harda wani ce mani ma wai ga dukkan alamu ban iya gaisuwa ba, kuma ma wai ba wurina yazo ba, to sai kace ma kiran shi nayi.
Gashi ina zaman zama na, duk da naji daɗin ganin shi, ko ba komai na san wata waraka ce ta sake dawo mana a karo na uku a rayuwa, tinda samun Sir Salim itace waraka ta biyu da muka samu a rayuwar mu, duk da yanzu ma zan iya cewa Alhamdulillah babu Abunda Sir Salim da mahaifiyar shi Hajiya Khaltum suka rage mu dashi.
Amman gashi zuwan nashi yana neman dagula mana lissafi gabaki ɗayan mu, to ko in yaje gidan namu ma mai zai ce ma umman tawa?
Jin nayi shiru ne har yanzu bance mashi komai ba, ya sanya shi sake cewa "Hello Jaan kina juna kuwa. Ko sai nazo ne lallashi?"
Ƴar ajiyar zuciya na sauke ina mai faɗin "Ina jinka Sir, komai ya wuce, nima kayi haƙuri idan na ɓata maka"
Dariyar jin daɗi yayi, domin gaskiya jiya ko barcin kirki bai samu ba, wayar ta ita ce ma ya rungume yayi bacci, yana mai shinshino ƙamshin ta ta jikin wayar.
Koda sukayi waya da Ammi taji yanda muryar shi take kaman ba'a daidai ba, ba irin tambayar da bata yi mashi ba, amman bai faɗa mata ba, baya so taga kaman Suhan ɗin na wahalar dashi ne, kada ta fara wani tinani daban, sanin irin son da takeyi mashi, kuma bata son dukkan wani abu da zai taɓa mata tilon yaron nata.
Saidai ko da bai faɗa mata ba, ta fahimci wani abu, faɗa ne dai irin na masoya ba'a shiga, tana zaman zaman ta za'a ce mata an shirya.
Dariyar jin daɗi ya kuma saki, nan ya shiga jana da fira, da labarin ban dariya, har saida yaji na dara, na saki jiki kuma mun cigaba da fira.
Na daga cikin abunda kan ƙara sanya ni amincewa da Sir, Salim ɗin, na san banyi zaɓen tumun dare ba, komin yanda bana cikin walwala ko nake cikin damuwa, indai zan biye mashi muyi magana ta minti biyar, to duk hanyar da zai bi yaga na saki jiki, kuma na dara sai yabi, mutum ne mai barkwanci, gashi mutum ne mai sanyin hali, sam baya da damuwa, lallai matar shi ba ƙaramin asara tayi ba, irin su Sir Salim ɗinne baka fatan ya faɗa son wata, saboda komin yanda budurwa ta kai da jin kai ko jan aji idan ya fara sonta, ya san ta duk yanda zaibi ya shawo kanta, ta faɗa tsananin son shi tsundum, harma in suka samu saɓani ta shiga damuwa, saboda zata rasa wannan barkwancin nashi koda na yini guda ne.
Bai kashe ba, har saida yaji alamun na warware, kuma yaji maganar su Khadeeja a ɗakin alamun sun shigo.
To baya son yana fira dani sosai a gaban su, ko ba komai dai su ɗaliban shine, kuma ba wani sanin haƙiƙanin halin su yayi ba, gudun halin su na ɗalibai yake kada aje ana yayata shi,ko ba komai yana gudun wulaƙanci da surutai daga wurin ɗalibai.
Kuma gashi da akwai waɗanda suke son shi da jin haushin shi, jira kawai suke wani abun magana ya ɓullo daga ɓangaren shi a cigaba da yayatawa, saboda kawai yace yana son Suhan ɗin kuma da aure.
*To dama haka rayuwar ta gada, abincin wani gubar wani,duk yanda ka kai da tarin masoya dole ta ɗaya ɓangaren a same ka da maƙiya, fatan mu dai a rayuwa shine Allah yayi katangar ƙarfe mai ƙwari tsakanin mu da maƙiyan namu, ta yanda saidai su dunga hango bayan mu cen nesa dasu. Ameen*
*************************
Har yayi wanka ya shirya cikin riga fara ƙar mai samfarin amless da wando tree quater mai ruwan ƙasa sosai wanda ya ciza, yayi kyau matuƙa, kaman a ƙasar waje yake. Sai tashin ƙamshin nan nashi mayatacce yake yi.
Harabar gidan ta ɓangaren ɗaya inda akayi wani ɗan ƙaramin lambu shimfiɗe da grass carpet tsanwa shar da ita, ga wani ni'imtaccen ƙamshi da yake tashi ta jiki fulawoyin da aka yima wurin ado dasu. Zama yayi bisa wata kujera mai kyau da akayi da zallar duwatsu, harda ɗan table a tsakanin kujerun shima na duwatsu ne.
Ɗan lemon power horse ne a hannun shi riƙe yana ɗan sipping a hankali, hankalin shi kacokam na kan wayar da yake ta latsa wa. Motar tasu ta shigo gidan a guje.
Da kallo ya bita, har zuwa lokacin da tayi parking kusa daf da sashen Alhaji Mustaphan.
Bilal ne ya fito a mazaunin dreba, sai Alhaji Mustapha da ya fito daga kujerar baya.
Ɗan tsayawa yayi yana kallon yaron nashi da ya taso yana nufo ta inda suke tsaye.
Gaban Bilal ne ya cigaba da faɗuwa, ta yanda zai haɗa idanu da abokin nashi kawai yake yi.
Ƙarasowa yayi, yan mai ɗan duƙar da kanshi ga Alhajin nashi ya shiga gaida shi cike da girmamawa.
Sannan ya juya yana mai kallon Bilal ido cikin ido, miƙa mashi hannu yayi ba tare da yace komai ba.
Ko bai faɗa ba, kallon tuhuma ne yake yi ma Bilal ɗin, kuma shima ya fahimta, to saidai sanin da yayi ne cewa Al'ameen ɗin bai san komai dake faruwa ba, indai ba bayan ya dawo bane ya sani.
Amman a majiya mai tushe ai an sanar dasu cewa bai ko zo gidan ba, kenan dai ba wannan ce ta kawo shi ƙasar ba.
Alhaji Mustaphan ne ya jawo hannun shi, yana mai faɗin
"Muje ciki ka amshi hukuncin wahalar damu da kayi nida abokin naka wajen neman ka"
Duk da cikin ƴar zaulaya yayi maganar, Amman saida abun ya nasheshi a cikin zuciya, to ta yaya akayi suka san yana ƙasar da har ma suka ce ya wahalar dasu wajen neman shi?
A haka ya shiga bin Dad ɗin nashi, Bilal ɗin na bayan su har zuwa cikin tanƙamemen falon Alhaji Mustaphan daya kasance girma ɗaya ne sashen nashi ɗana Hajiya Kubra. Wanda daga baya ne aka ƙara faɗaɗa sashen Alhajin tinda ada bai kai na Hajiya Kubran ba.
Bayan sun zazzauna ne, Alhaji yace Bilal ya miƙo mashi lemo a cikin fridge.
Lemon roba na 5alive Bilal ɗin ya ɗauko haɗi da cup, ya ɗora a bisa wani ɗan trey mai kyau da ƙyalƙyali.
Saidai fa duk yasha jinin jikin shi, yanda ya kula da duk abunda yake yi hankali da idanun Al'ameen ɗin na akan shi, yana mashi wani irin kallo cike da tuhumomi kala kala.
Bayan ya zuba mashi Lemon ne ya miƙa mashi, kujerar da Ya Ameen yake kai ya koma shima ya zauna, yana mai ɗan sadda kanshi ƙasa. Ya san halin mutumen nashi sarai da shegiyar zuciya ta tsiya, ga zafafa abu idan ya faru ko da kuwa ace ba da son ran mutum ba, saidai shi zai yi ƙoƙarin ganin yayi controlling ɗin kanshi koda kuwa ace shi Al'ameen ɗin ya hau, ta yanda zasu fahimci juna, kuma su fuskanci koma menene a tare.
Gyaran murya Alhaji Mustaphan yayi cike da dattako, bayan ya kurɓi ruwan lemo da ya wadata da zallan lemon zaƙi.
"Son Meyasa kayi haka? Me yasa ka taho ba tare da ka sanar dani ba? Takamaimai ma ina son sanin abunda ya sanya ka baro ƙasar ka taho ba tare da sanar damu ba"
Ɗan guntun murmushi yayi iya leɓo, shi ba maganar da yake so ayi ba kenan. Shi ba abunda ya kawo shi ba kenan, beside ma yana ganin ya girma ya kawo ƙarfin da zai iya zartar ma da kanshi hukuncin abunda ya dace dashi, ba don ma iyaye na iyaye ba.
Bai ce ƙala ba, sai ma duƙar da kanshi da yayi ya shiga wasa da hannun shi alamun ba maganar yake son ayi ba.
Abun ka da ɗa da mahaifi, tuni Alhaji mustaphan ya gane abunda yaron nashi ke nufi, tun yana yaro wannan itace alamun da yakan yi idan baya son maganar da akeyi mashi.
Ɗan murmusawa yayi yana mai gyara zama, sai kuma ya saki gyaran murya yana mai ɗan kai kallon shi kan Bilal ɗin alamun za'a shiga daga fa!
"Al'ameen ya zuwa yanzu dai na san ka fahimci me yake faruwa a cikin gidan nan, tinda Allah ya kawo ka, Bilal yaƙi sanar da kai ne a bisa umurnina, nima kuma nayi hakan ne saboda rashin lafiyar taka da kake fama da ita, to saidai fa yanzu haka cikin binciken inda suka shiga muke, muna fatan zaka yi mana uzuri"
Bai katse Alhajin nashi ba, har saida ya kai aya, sannan ya muskuta, yana mai cewa
"Dad duk naji wannan, kuma na ga su to saidai nima ina da Alfarma guda ɗaya, wannan karon bada wasa nake ba, ba kuma zan koma nace na janye maganar ba, sannan inaso ayi dukkan abunda za'ayi cikin lokaci, sannan bana so a tsaya sauraren Mom, tinda dai nine mai yi, kuma nace zanyi ɗin."
Alhajin ne yake kallon Al'ameen cikin matuƙar mamaki akan fuskar shi.
Shima Bilal ɗin dukkanin idanun shi da hankalin shi na akan abokin nashi.
Bai tsaya sauraren suba gabaki ɗaya, ya cigaba da cewa
" Dad inaso in ƙara sanar da kai cewa inaso a nema man auren Suhan a karo na biyu, ba zan janye ba, ba kuma na faɗa bane wannan karon saboda tausayi ko wani abu ba, *Ina Son ta ina ƙaunar ta* nine zan zauna da ita, bana son Mom ta san abunda yake faruwa, saboda bana son ta rikita mana abun akaro na biyu"
Gabaki ɗayan su su biyun, babu wanda gaban shi bai ruguje ya faɗi ba, ya ana mashi maganar ba'a gansu bama, shi yana maganar a nema mashi auren ta? To ina za'a nema mashi auren? Wajen wa za'aje a nema mashi?
"Son ana maka maganar ba'a gansu ba fa, ba'a san inda suka shiga ba, amman ana kan binciken inda suke ɗin"
"Dad naji dukkan bayanin ka, kuma nace na gamsu, saidai Dad kasan garin masoyi baya nisa. Ni na gano su, na gano inda suke kuma naje har inda suke, infact ma daga inda suke nake"
Baki Alhaji Mustapha ya buɗe yana sauraren shi, sai bayan har daya kai aya ne Alhajin ya dunƙule hannu ya watsa mashi daƙuwa cikin ɗan mamaki haka, Shikau gogan sai ma sunnar da kanshi da yayi, yana mai sakin ɗan murmushi, duk da shima sai bayan daya faɗi kalmar sannan kunya ta kama shi. Saidai a fannin so, masalan ma shida yake sabon shiga a soyayyar yana ganin babu gaban wanda ba zai iya faɗa ba.
Bilal wanda bai san lokacin daya buɗe baki ba, yana mai miƙewa tsaye, Al'ameen ɗinne yayi mashi wani kallo na ai sai ka zauna ko!
Zama yayi cikin sanyin jiki da mutuwar jiki. Lallai soyayyar Abokin nashi ga Suhan ɗin daban take, kuma daga Allah ce, tausayin shi matuƙa ne ya kama shi, yana mai jin cewa wannan karon zai mara mashi baya akan komai har ya kai da samun abunda yake da muradi. Duk da shima ta ɓangare ɗaya na zuciyar shi, yana kwaɗaita mashi suhan ɗin, kyawawan halayyar ta, da tarbiyyar dake gareta sukan ƙara mashi ƙaimi wajen ganin ta zama mallakin shi. Saidai ba zai taɓa iya cin amanar abokin nashi ba, masalan ma yanzu da yaga ya tsunduma tsulundum a soyayyar ta, ya zama wajibn shi, tilas ɗinshi yaso abunda Aminin nashi keso.
Shiru falon ya ɗauka kusan na minti biyar, kowa da abunda yake saƙawa.
Sai cen Alhaji Mustaphan ya nisa yana mai cewa su tashi suje, yaji dukkanin bayan an Al'ameen ɗin kuma zai duba akan su, sannan zai shawarci Alhaji Auwalun akan komai, saboda baya yanke hukunci karon kanshi sai ya shawarci yayan nashi da kuma mahaifan shi.
(Abunda masu kuɗin mu na yanzu basa yi kenan, suna ganin tinda Allah yayi masu nasibi ko luɗifi ba zasu iya bin kowa ba, su saidai a bisu, kuma basa jin zasu iya neman komai a wurin wani, bayan ba haka rayuwar take ba, gabaki ɗayanta ita rayuwa juyawa take, idan babu masu kuɗi babu talakawa, haka idan babu talakawan babu masu kuɗin, kowa na buƙatar kowa a sha'ani na rayuwar yau da kullum)
Miƙewa sukayi gabaki ɗayan su suna mai ficewa zuwa sashen Al'ameen ɗin.
Saidai fa babu mai cewa da kowa komai, har suka shiga sashen nasu.
Ganin da Bilal ɗin yayi Al'ameen ya share shi ne, ya sanya shi jawo hannun shi, yana mai maido shi baya.
"Kai don Ubanka laifin me na aikata maka haka ne da har kake mani wani shariya? Kasan irin wahalar da nasha wajen nemo maka budurwar taka? Ko kasan har America naje in sanar da kai gaskiya ba tare da sanin Dad ba, ganin kada in biye ma Dad ka cutu, Amman shine ka dawo kana ta wani basar dani. Pls kayi mani magana mana ko Naji sauƙi"
Ɗan ɗaura mashi idanu yayi, ganin ya idashe maganar tashi cikin damuwa da take har cikin zuciyar shi.
Ɗan zare hannun shi yayi yana mai wucewa, sai kuma ya dawo da baya ya dunƙule hannu ya kaima Bilal ɗin naushn wasa yana mai rungume shi yake faɗin "Komai ya wuce Friend, ai nace na gamsu da dukkanin bayanan da Dad yayi ne, dama don inga yanda zaka yi ne don Ubanka" ya faɗa cikin yalwatacciyar fara'a da yake jinshi saƙat tinda ya samu Dad ya faɗa mashi damuwar shi da dukkanin buƙatar shi.
Shima Bilal ɗin rungume shi yayi yana mai faɗin "kaji shegen bisa, ashe dama hawan ruwana ne kake so ya tashi, to kada dai ka karya ma Ummi ni, saboda kasan fa na kusa zama Dad"
Da mamaki Al'ameen ɗin ke kallon shi, lokaci guda yana mai ɗan zare jikin shi daga Bilal ɗin, sai kuma ya sake rungume shi yana mai faɗin
"Kace mun kusa zama Dads, ƙilama kafin lokacin na angwance"
Da dukkanin farin ciki Bilal ɗin ya sanya hannu yana mai zagayo Aminin nashi zuwa gareshi sosai, yana mai jin daɗin shiryawar tasu, farin ciki fal a zukatan abokan biyu, kuma aminan da suka taso tun ƙuruciya babu mai jin kansu.......
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~41~*
*Hahaha Lol, kaji wai ƴan Team Ya Ameen har sun haɗa masu suna wai _Suhameen_ kaji fa ko daɗi babu, to mu ƴan Team Sir Saleem mu kuma munce _Suhaleem_ don Allah Fans wanne yafi daɗi nan ciki?*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Da misalin ƙarfe uku na yamma saƙon shiga yajin aiki ya iske ɗaukacin ɗaliban makarantar, kuma ana umurtar ɗalibai da su tattara su tafi gida har sai an buƙaci ganin su.
Hakan baiyi mana daɗi ba, domin duk wani ɗalibai mai kwazo da son karatu baya fatan abunda ka tsaida mashi karatun nashi.
Hakan ce ta sanya mu fara tattara komatsan mu. Kiran Sir Salim ne ya shigo wayata yana sanar dani in maza in shirya zai ajiye ni sannan ya wuce.
Ko awa ban ɗauka ba, na shirya komai nawa, sallama mukayi dasu Raihana wanda har gaban mota suka rakani, sannan suka juya suma domin idasa shirin barin makarantar.
Cikin ƴar walwala na gaida shi, ya kuwa tsare ni da idanu, domin shi a ganin shi har ya zuwa yanzu walwala ta bata koma yanda take ba ada.
"Lafiya Lau Jaan, sai kuka ji an shiga strike ko?"
"uhmm, Sir, ai mu hakan baiyi mana daɗi ba, masalan mu da muke ƙoƙarin cenza aji"
"To ya za'ayi ai sai haƙuri, gwamnatin ce bata da cika alƙawari, muma ba da son ranmu hakan ke faruwa ba, saidai fatan Allah ya kyauta kawai, ƙasar ce gabaki ɗaya sai yanda Allah yayi kawai"
Ya faɗa cikin ɗan murmushi da kan ƙara ƙawata fuskar shi.
Sir Salim mutum ne da yake da kyawon hulɗa da jama'a, Sam bashi da tsanani irin na sauran maza, hakan ce ta sanya yake lallaɓa ni kaman kwai, ko yanzu da muke tafiya shine yake ta bani labari, wasu inyi dariya, wasu inyi murmushi.
Mune bamu isa ƙauyen namu ba, sai wajen ƙarfe takwas na dare, wai a hakan ma domin lafiyayayar mota ce muke ciki.
Umma ta tayi matuƙar mamakin ganina a daidai wannan lokacin, shaida mata nayi tare muke da Malam Salim, miƙewa tayi ta shige ɗaki, haɗi da sanya hijab ɗinta sannan tace ince ya shigo, dama Hajjo batanan ta tafi gidan su da akayi masu rashi, bata dawo ba har yanzu.
Har cikin gida ya shiga, zama yayi bisa tabarmar da umma ta shinfiɗa mashi gefe, cikin girmamawa yake gaida Umman tawa, hakan na ƙara sanya ni jin daɗi, ko ba komai na san Allah ya haɗa ni da wanda ko nan gaba ba zanyi wani kuka ba a rayuwa.
Bayan sun gama gaisa wa ne ya miƙe haɗi da fita waje, saboda har yanzu ummata bata wani sakin jiki da Sir, Salim ɗin, ina jin Kunyar sarakuta ce take nuna mashi.
But ya buɗe, haɗi da ciro kayan masarufi masu yawa, shiga dasu cikin gidan ya fara yi da kanshi, ina taya shi da abunda zan iya ɗauka.
Hatta da ruwa masu yawa ya kawo mana nasha, ummata kuwa sai godiya da shi albarka take zuba mashi, domin dai ya riga ya kawo ba zata ce bazata amsa ba.
Ko bayan da na raka shi, kuɗi masu yawa ya kawo ya bani, a cewar shi, zaiyi ke wata kuma idan an koma zai zo da kanshi ya ɗauke ni.
Ƙin amsa nayi, ina mai cewa "haba abun ai sai yayi yawa"
Saida ya nuna mani tsananin ɓacin ranshi sannan na amsa ina mai ƙara mashi godiya.
Akan idanuna yaja motar tashi yabar ƙofar gidan namu.
Nima da kallo na kuma bin gidan namu, rayuwa kenan, wai ace ni da nake zaune a wannan kangon har Sir Salim ya ganni kuma ya amince da aure na a haka ba tare da yayi dubi da tsananin talaucin mu ba, har mahaifiyar shi tana iya kwana a wannan ruɓaɓɓen gidan da katangar ban ɗaki ce kawai ta ƙasa, sauran duk danni ne, domin kuwa ko ɗakin da muke kwana na bukka ne.
Babu Abunda zance da Sir Salim saidai godiya, ya so ni haƙiƙa, ya nuna mani ƙauna, kuma sun mana halarci daga shi har mahaifiyar shi, ko da zai tafi saida yana yin fuskar shi ya cenza, lallai na yadda da ƙaunar da Sir Salim ɗin ke nuna mani. A zahirin gaskiya nima na yadda da auren nashi ɗari bisa ɗari, saidai fatan Allah ya bamu zaman lafiya.
Ko dana ba ummata kuɗin, faɗa ta hau yi kaman zata burgeni, wai "bana da tunani, abun ai yayi yawa, tinda ba siyenki zasuyi ba, ko kwanaki da Ammin shi tazo ai baki ga iyayen abun alkhairin da tayi mana ba, kar in sake inga kin kuma karɓar wani abu daga hannun shi in ba haka ba sai na saɓa maki wallahi"
Nidai da kallo nake binta, yanda ta fututtuke tana faɗa, kai kace roƙonshi nayi, to abun bai ma dameni ba, saboda na san halin kayata, dole in lallaɓa ta in samu mu rabu lafiya tinda abu ya kusa saura ƙiris ya rage.
Hajjoma da ta shigo ta tadda kaya tuli tsakar gida, saida ta girgiza, to koda ummata ta nuna mata kuɗin itama faɗa ta hau yi, a cewarta itama gaskiya abar amsar abun hannun su, har sai ran da Allah yasa aka mallaka masu ni.
Hajjo mutuniyar kirki ce, Sam bata da baƙin hali, lafiya ƙlau suke zaune da ummata kaman wasu ƴan uwa, to shima malam ɗin haka yake, ko ba komai zuwan namu ya ɗan sama masu waraka daga cikin halin da suke ciki, sune yanzu harda cin shinkafa ƴar gwamnati da shan ruwan roba? Ai sai Sam barka wallahi.
A haka muka kwana firar makaranta da ummata, tana daɗa jan hankalina akan in maida hankali akan Abunda ya kai ni, banda kula ƙawaye barkatai ko samarin makaranta. Ce mata nayi wace ni? Yanda duk makaranta ta ɗauka akan cewa ni Budurwar Sir Salim ce, kuma ni ce wadda zai aura, ai su kansu ma samarin shakka ta suke yi, domin Sir Salim ɗin a makarantar Malami ne daya san Abunda yakeyi, Sam bashi da kula ƴan mata duk kuwa da barkwancin shi, samarin ma baya sake masu sai ƴan kaɗan gudun raini irin na ɗilibai.
*****************************
Basu tsaya neman abunda zasu ci ba a cikin gidan, a tare da Bilal ɗin suka fita zuwa nashi gidan, saidai duk yadda ummi ta kai da son Al'ameen yaci abincin nata, saidai ya yabuɗa, shi kau Bilal sakin jiki yayi ya kwashi girkin matar tashi, sannan suka sake fita zuwa kamfanonin su domin su duba ayyuka, duk da an tashi aiki kuwa.
Hajiya Kubra bata bi ta kan Alhaji Mustapha da yake ƙasar ba, ta sanya kai tayi ficewar ta wajen harkokin ta, su 3hajiyas ne ma suka zo suka ɗauke ta har gida. Akan idon shi suka fita, hakan ce ta sanya shi shima shiryawa ya fita zuwa wajen Alhaji Auwalu domin su tattauna akan batun Al'ameen ɗin.
To koda ya same shi akan batun, bai hana ba, domin dukkanin Abunda ke faruwa Hajiya Zainab ta faɗa mashi, hatta da halin yarinyar da nagartar mahaifiyar yarinyar, basu da matsala akan tarbiyyar yarinyar, domin haka ne ya sanya suka yanke shawarar nema ma Al'ameen ɗin ita yarinyar, alabasshi asalin nata a hankali zasu nemo shi.
Kiran Al'ameen ɗin sukayi da misalin ƙarfe takwas na dare, lokacin suna tare da Bilal a hanyar su na komawa gidan Bilal ɗin domin ya sauke shi.
Karkata kan motar yayi zuwa gidan Alhaji Auwalun, a tare suka shiga da Bilal ɗin har cikin gidan.
Hajiya Zainab suka tadda zaune a falo tana kallo, gaida ta suka shiga yi cikin girmamawa, itama amsawa takeyi cikin sakin fuska tana tambayar Bilal iyali, tana tambayar Al'ameen ƙarfin jiki.
Bayan sun amsa mata ne, ya sanya ta cewa su shiga Falon Alhajin suna ciki.
Sallama sukayi, suka koma gefe cen ƙasa suka zauna, Al'ameen harda duƙar da kai ƙasa, suka shiga gaida iyayen nasu.
Alhaji Auwalu ne yayi gyaran murya
"Al'ameen mahaifin ka yazo ya same ni akan wani batu, alal haƙiƙa naji daɗin jin wannan zance daga gareka, kuma ko ba komai muna alfahari da kai ta wannan fannin, kaf zuri'ar mu babu yaro mai tunanin manya da hangen nesan ka, saboda haka mun yanke shawarar gobe idan Allah ya kai mu, zamuje da kai ka nuna mana inda ita mahaifiyar yarinyar take, sannan magana ta biyu, kaman yanda kace baka so mahaifiyar ka taji, to ba zamu taɓa bari taji ba, sannan muna so, duk Abunda Kaga mun aiwatar ka sanya mana ido, kaidai yarinya kake so a aura maka, kuma insha Allahu zamuyi dukkan iya ƙoƙarin mu, muga ka same ta kaman yanda ka buƙata. Allah yayi maku Albarka ya sanya kufi haka, ya baku ikon taimakon na ƙasa daku a ko'ina kuke a rayuwa"
Haƙiƙa ba Al'ameen ba, har Bilal yaji daɗin wannan maganar ta wan mahaifin shi, yana matuƙar Alfahari da iyayen nashi a ko'ina yake, su ɗin masu son su ne, masu girmama ra'ayi da muradin su ne, dama ko ba komai ya san Alhaji Auwalun da mahaifin nashi ba zai taɓa samun matsala dasu ba, ga dai wadda za'a sha dabi da ita cen duk ranar da taji, saidai koma minene ya shirya ma hakan, ya shirya ɗaukar dukkan wani ƙalubale da tarnaƙi da kan iya tasowa anan gaba.
Muryar Mahaifin nashi ya tsinkaya yana tambayar shi ko da akwai wani abu kuma?
Girgiza mashi kai ya shiga yi, yana mai godiya da sanya ma mahaifn nashi albarka, shima Bilal ta ɓangaren shi, daɗi yake ji, ko ba komai yanzu ne zai shawo kan abokin nashi tin bayan shigar shi soyayyar.
Umurtar su sukayi da su tashi su tafi zuwa goben zasu wuce.
A mota ne Al'ameen ɗin ke cema Bilal ya shirya lallai fa dashi za'ayi wannan tafiyar, gyaɗa mashi kai yayi yana mai cewa "Allah ya kaimu"
Har yanzu mamakin Al'ameen ɗin yakeyi, kai idan ada akace maka Al'ameen zai faɗa soyayya irin haka zaka ƙaryata, mutumen da ƴan matan da suka kawo mashi ƙoƙon barar su, ƴaƴan masu kuɗi, ga kyau ga ilimin boko, Amman shi duk basu yi mashi ba, Suhan ita yagani tayi daidai da muradn shi, to dama haka duniyar take, duk inda tausayi yake to fa akwai soyayya a tsakani, dama shi jin abokin nashi kawai yakeyi, Amman tabbas ya san wannan lokacin ya a zuwa.
Kuma ko ba komai dai Suhan ta cencenci a sota, ta cencenci zama uwar ƴaƴayen ka, yarinya ce mai tarbiyya da biyayya da girmama na gaba da ita, duk wani namiji wanda ya san abunda yakeyi zaiyi fatan ace Suhan ɗin ta zamo uwa ga ƴaƴayen shi.
Har ƙofar gida ya sauke shi, yana mai kaɗa kan motar shi zuwa nasu gidan.
Mama Talatu da maree an sha barbaɗe barbaɗe a cikin girki, an jera ma Al'ameen a dinin table ɗinshi, wanda hajiya kubra ce ta sanya su yin hakan a cewar ta idan ya dawo ba sai ya nema ba, saidai da ta san Abunda zasu barbaɗa ma yaron nata, to da ko kusa bata fara barin maree na shiga sashen Al'ameen ɗin ba idan baya nan.
Saidai kallo ɗaya yayi ma abincin yaji zuciyar shi na matuƙar tashi, duk kuwa da irin kyawon abincin da na momin da suke cikin miyar.Iro mai ba fulawowi ruwa ya kira a waya, yace yazo ya kwashe abincin suje suci idan suna so.
Da gudun shi ya taho ɗakin na Al'ameen domin ya san cimar da za'a shirya ma uban ɗakin nasu daban ce da wadda za'a basu, balle yanzu da mama talatun take ƙwange wajen bada kayan abincin masu girkin. Duk da harda ita za'a ci Amman ta kwammace suci ba daɗi tana tara sauran a ɗakin ta, in sun taru taba maree a sace taje cen wasu ƙauyakun ta siyar a banza.
Cemashi yayi idan sun cinye su bar warmers ɗin a wurin su, godiya ya shiga zubawa yana mai ɗauka ya fice.
Saboda mugun abu irin na mutanen yanzu, shi kaɗai yaje ya ɓoye yaci abincin shi yayi ƙat, harda halshe yake sanyawa yana lashe warmer ɗin, dama Al'ameen ya san irin ƙazantar Iro, hakan ce ta sanya shi cewa yabar su a wajen shi.
**********************
Washe gari zamu iya cewa Al'ameen ɗin ya riga kowa tashi, bayan ya gama sallolin shine ya koma ya ɗan kwanta, tuni bacci mai nauyi ya sure shi, zamu iya cewa bai samu baccin kirki ba, daya kulle idanun shi, Suhan ɗin kawai yake hangowa zaune da saurayi suna fira, har tana dariya, abun ya matuƙar tsaya mashi a rai, sai kuma maganganun umma da suke yi mashi amsa kuwwa a kunne, wai wannan da ya gansu tare shine saurayin ta, wanda har an nema mashi auren ta, kuma umman ta bashi.
Sai ya tashi zaune ya jawo fulo ya matse shi kaman zai yaga shi, sai kuma ya koma ya kwanta yana mai sakin ɗan guntun tsoki.
Mamakin kanshi yakeyi, wai ashe haka soyayya take. Ashe haka kowa keji? Tin farkon asalin asali me ya sanya shi janye maganar tashi saboda wani hargagi na Mom ɗin tashi? Ai gashinan wankin hula na neman kaishi dare. A haka dai ya kwana har aka kira sallar Asubahi.
Wajen ƙarfe takwas na safe ya fito cikin shirin shi na manyan kaya, fara ƙal ɗin shadda ce gizna sai tashin ƙamshi da walwali takeyi, anyi mata ɗinkin doguwar riga kusan har ƙasa, tasha aiki Golden a jikin ta, takalmin ƙafar shi ma golden ne haɗe da hular dake bisa kanshi.
Yayi masifar kyau, idan ka hango shi daga nesa zaka iya cewa ango ne, harabar gidan ya fito riƙe da waya da ɗan ma ƙullin sashen nashi da ya kulle, domin ya kula ana shigar mashi ɗaki idan baya nan, hakan ce ta sanya tin jiya ya aika aka amso mashi makullan ɗakin wajen mama talatun.
Bilal yake ta faman kira yana sakin ɗan guntun tsaki a fili saboda rashin ɗaukar wayar tashi da baiyi ba.
Gate yaga an buɗe sai ga motar Bilal ɗin ta danno kai a guje cikin gidan. Bayan yayi parking ne ya fito shima sanye da shadda ruwan Army Green sai ɗaukar idanu yakeyi
Da ɗan sauri ya ƙara so wajen da Al'ameen ɗin ke tsaye yana faɗin
"Ran ango ya daɗe"
Ya faɗa yana mashi alamar jinjina haka cikin wasa.
Ɗan tamke fuska Al'ameen yayi, yana mashi alamun to ya tona masu asiri, ɗan waiwayawa Bilal ɗin yayi bayan su, yaga babu mai kallon su, sai kuma ya saki dariya mai sauti yana faɗin "Shegen gora, wannan kyau haka kaman yau ne ɗaurin auren?"
Sai a lokacin ya saki ɗan murmushi yana faɗin
"bana cike da iskancin ka Friend, bakaji yanda gabana ke ta faman faɗuwa ba, gashi ina ta kiran ka baka ɗaga ba"
"Ai ina ganin kiran, to na riga na kusa ƙarasowa shine nace bari kawai in bari in iso, sai inji menene?"
Sashen Alhaji Mustapha suka ranka ya, sun tadda ya shirya cikin shadda skyblue mai babbar riga, shima yayi kyau ainun, dama Alhaji Mustapha ba dai kyau ba.
A tare suka fito, mudi suka sanya ya fiddo masu wata mota mai ƙirar jeep da tun jiya Al'ameen ɗin ya sanya shi wanke ta.
Bilal ne ya shiga mazaunin driver sai Al'ameen a gefen shi, yayin da Alhaji Mustapha ya shiga baya, suka nufi gidan Alhaji Auwalun.
Shima sun tadda ya shirya, ba ɓata lokaci suka ɗauki hanya, yayin da Alhaji Mustaphan da yayan nashi suke ta firar su daga cen baya, shi kuma gogan naka ya luluƙa duniyar tunani.
**************************
Nasha baccin ƙalula yau, ba tashi da wuri tinda ba'a makaranta nake ba balle ince lecture, kafin in tashi Hajjo da ummata sun gama komai, yau tea muka sha da bredi harda wainar kwai, bayan na gama karyawa ne na fita na share tsakar gida, haɗi da gyara ɗakin namu.
Ruwa Hajjo zata je ɗebowa, hakan ce ta sanya ni ce mata ta bari idan na kammala komai nayi wanka zanje in ɗebo mana, tinda na aikin gida ne, kuma naga da ɗan saura.
Sai kuma muka zauna muna ƴar fira haka da hajjon, ummata na sanya mana baki jefi jefi, sai kuma ta miƙe haɗi da yin wanka, a tare muka fita da ita wajejen azahar zata je gidan ƴan uwan hajjon yi masu gaisuwa da yake an yi masu rashi kwanaki, shine zata koma yi masu gaisuwa, hajjon ce ta zauna gida haɗi da ɗora girki.
Muna tafe muna ƴar firar mu, har zuwa inda zamu rabu da umman tawa.
Ko da na isa rafin, na ɗebo ruwa kwatsam ina cikin tafiya, sai na kula kaman ana bina, na ɗan waiwaya sai naga wasu samari su uku, ƙara sauri nayi, sai kuma Naji ana ta faman tsayar dani.
Ware ƙafa nayi zan taka da gudu naga sun sha gabana
"Haba ƴan mata, ya ana ta maki magana kina wani share mutane kaman baki ji ba? Daga zamu taimaka maki? Tinda mun kula kinyi kwantai da sunan kin tafi wai karatu binni, Amman wa ya san abunda kike aikatawa acen ɗin?"
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil"
Shi nake ta maimaitawa, domin dai ga dukkan alamu waɗannan ba mutanen arziƙi bane ba, gashi wurin ni kaɗai ce, ga dukkan alamu wulaƙanci suke neman yi mani, gashi su uku ni ɗaya.
Tulun dake bisa kaina na saki, haɗi da tattare zani zan sake kwasawa a guje naji ɗaya daga ciki yaja mani hijab ta baya.
"Malam Lafiya? Wai minene haka ne? In na saurare ku me zance maku?"
Na faɗa ina mai tattare dukkanin dauriya da ƙwarin guiwa ta.
Dariya suka sheƙe da ita, suna mai faɗin
"Tin kwanaki muka ganki a ƙauyen nan kuma muka ji muna sonki, mun bincika sai muka gane ashe ke ƴar wannan matar ce mai nuna ita ta Allah ce, sai kuma gashi ta tura ki bunni neman kuɗi da sunan karatu, muna so dai ki bamu haɗin kai, babu wanda yaji ba wanda ya gani, kinga cen bayan bishiyar cen? Nan zamu ɗan kewaya, mintina ne ƙalilan mun gama, zamu kula dake a ƙauyen nan, duk wani mai neman shiga hurumin ki zamu kare ki"
"Innalillahi wa 'inna ilahi raji' un, la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen"
Abunda nake maimaitawa kenan, ai tuni hawaye suka shiga zarya akan fuska ta.
"Kuyi haƙuri, ku dubi girman Allah, wallahi ni ba ƴar iska bace ba, wallahi karatu nakeyi a bunni ba iskanci ba, wallahi ban iya ba, kuyi haƙuri don Allah, kada ku keta mani daraja ta"
Na faɗa cikin kuka riris, gashi sun cukuikuye mani hijab ɗita, sai faman kokowa nakeyi da guda ɗaya daga cikin su da yake neman kaini ƙasa.
Kokowa sosai ta ɓarke tsakanin mu dasu, maza ne su ba mata ba, har dai saida sukayi nasarar yada ni ƙasa cikin yashin da yake shinfiɗa ta gefen rafin.
****************************
Baisha wahalar gane gidan ba, sai gasu har ƙofar gidan, su duka babu wanda baiyi mamakin har ta yaya akayi Al'ameen ya iya shigowa nan ba, neman su Suhan ɗin, har kuma ya same su anan ɗin.
To su ta yaya ma tunanin su zai iya basu akwai wani ƙauye nan ciki haka da har mutane ke rayuwa a ciki?
Sallama suka sanya akayo masu a cikin gidan, bayan sun firfito. Shi dai Al'ameen bai san dalilin faɗuwar gaban shi ba, shi kau Bilal sai ƙarema gidan kallo yakeyi yana mai ɗan murmusawa shi kaɗai yana tunanin ƙarfin hali irin na Aminin nashi da har ya iya gano wannan wurin.
Yaron ne ya dawo yace "wai ance ana zuwa"
Alhaji Mustapha ne ya zaro ƴan dubu dubu guda uku ya ba yaron yana faɗin "an gode maza gida kaji kaje ka kaima maman ka"
Cikin su babu wanda yayi mamakin kyautar, saboda sunsan ya saba da irin haka, taimakon marasa shi, shi kau yaron ganin kuɗi masu yawa duk da ba sanin su yayi ba sosai, sai ya ruga da gudun tsiya zuwa gida yana ta murna.
Hajjo ce ta sanya Hijabinta ta leƙo wajen, ganin ƙatuwar mota da manyan mutane tsaye ya sanya idasa fitowa tana gaida su.
Cikin sakin fuska Alhaji Auwalun ya Amsa yana faɗin
"Mu baƙi ne, wajen Maryama muka zo, mune waɗanda ta zauna a gurin mu shekaru da daɗewa"
Sakin fuska sosai hajjon tayi tana masu maraba, sai kuma ta juya zuwa cikin gidan tana mai cewa su shigo.
Da yake rana ta kawo sasai, ɗakin umman ta buɗe tayi masu shinfiɗa ciki, tana mai cewa Aiko gashi Umman taje unguwa, Amman bari ta je ta kira masu ita.
Da to suka bita, cikin su babu wanda baiyi mamakin inda muke rayuwa ba a yanzu, masalan ma Bilal da Alhaji Mustapha, jinjina dalilin da ya sanya suka zaɓi suyi wannan rayuwar suke yi a cikin zuciyar su.
Al'ameen ne yake shaida ma mahaifn nashi cewa zasu koma mota su zauna, basu hana su ba, tinda sunsan a takure suke wajen ga kuma tsananin zafi da ake fama dashi.
Fitowa sukayi, saidai basu shiga motar ba, Al'ameen ke cewa Bilal yazo ya raka shi su zagaya garin suga yanda yake.
Bilal yasha tuƙi ya gaji, ga zafi yanaji, cema Al'ameen ɗin yayi ya tafi shi dai ya gaji dayawa, yana nan cikin mota yana jiran shi.
Ba tare da ya kuma cewa ƙala ba ya juya ya tafi, shi mutum ne da bai san yanda ake magiya ba, hakan ce ta sanya shi ƙyale abokin nashi, ko ba komai yayi mashi uziri, zafin ranar da akeyi kaman ana tafasa ƙwaƙwalwa.
Hannun shi soke cikin aljihun wandon shi yake ratsa ƙauyen, yana ta ƴan kalle kalle, har zuwa ƙasan wasu bishiyoyi da sukayi ma wani wuri ƙawanya, baya kyautata zaton babu ruwa a wurin, hakan ce ta sanya shi taka wa a hankali ya doshi wurin.
A zabure na miƙe, ina mai sake sakin wata razananniyar ƙara da saida wurin gabaki ɗaya ya amsa kuwwa ta.
Kuka nakeyi ina roƙon su, kaman ma ba da mutane nake magana ba, jana suke yi a ƙoƙarin su na kaini bayan bishiyar da suka nuna mani ɗazu.
Cikin sauri ya shiga taka wa har yana ssssarfa, wurin da yake jin ƙarar na fitowa yake nufa, idan ba kunnuwan shi bane keyi mashi gizo ba, sautin muryar mace ne yake ji yana fitowa, ihu takeyi, tana naiman taimako.
Sai ga Al'ameen yana ɗan gudu kaɗan haka, kaman mai four-fourty haka.
Tin daga nesa ya hange su, maza ne zarata har uku, suka rufa akan yarinya ƙwaya ɗaya tallin tal, janta suke ko ina zasu kai ta?
Tin daga nesa yake daka masu tsawa cikin wata irin murya da bansan yana da ita ba.
"Kai kai ku tsaya, ina zaku kai ta? Me zakuyi mata?"
Ya faɗa yana mai ƙarasawa inda suke tsaye, Nidai hijab da ɗan kwali sun rufe mani fuska, ihu kawi nakeyi ina "Ku sake ni ku ƙyale ni, ni ba ƴar iska baceba, kada ku keta mani haddi don Allah"
Tausayin ta ne matuƙa ya kama shi, bai san lokacin da ya kai hannu ba bisa jikin ta, haɗi da fizgota daga hannun su ya maida ta bayan shi, yana mai fuskantar su.
Nikau tinda Naji na tsira daga hannun su, sai na sanya hannu haɗi da ƙwaƙume shi matau, kaman zai tafi ya barni a wurin.
"Kai malam, ƙanwar mu ce fa, kai ina ruwan ka ne?" suka faɗa cikin zaro idanu da matse baki cikin magana irin ta ƙauraye
Daga bayan nashi nake faɗin "Ƙarya suke yi ni ba ƙanwar su baceba, wai sai na basu haɗin kai, na faɗa masu ni ba ƴar iska bace, Allah ne ya kawo mani kai da bansan halin da zasu jefa ni ba" na faɗa ina mai sake ƙwaƙume shi daga baya cikin wani irin tsumammen kuka.
Bai shaida murya ta ba, saboda wani irin ɓacin rai da yake ciki, idanun shi sun kaɗa sunyi jajawur
"Malam Kaga ka miƙo mana ita nan, gida zamu kai ta, guduwa tayi, ƙarya takeyi, kuma kai wanene da zaka zo ka katse mana hanzari?"
"OK kuna son kusan ko ni wanene?" ya faɗa cike da ƙufuluwa
Ganin yana ƙoƙarin zaro wani abu daga cikin aljihu ne ya sanya su ruga wa suna faɗin "zamu haɗu nan gaba ne ai"
Daƙyar ya sanya hannu ya jawo ni daga bayan shi, wanda na rirriƙe shi gam kaman zasu sake ƙwace ni, kuka kawai nakeyi da hamdala da Allah ya kawo mani mai ceto na.
Gaban shi ya maido ni, yana mai sanya hannu ya yaye hijab ɗin da duk ta cukuikuyeni da ɗan kwalin nawa.
A firgice ya ja baya, ganin ko wacece, sai kuma ya sake kulle idon shi ya buɗe ya azasu a bisa kaina.
Nikau kunya da ɗacin rai suka sanya ni durƙushewa a wurin ina mai sakin wani sabon tsumammen kukan.
Jin kukan yakeyi har cikin zuciyar shi, tarin tambayoyi ne kawai a cikin ranshi, Suhan ɗin da take cen makaranta me ya kawo ta nan kuma? Menene haɗin ta da waɗancen ƴan iskan?
Yana tsaye ya tsura mani idanu, sosai kukan nawa yake ratsa mashi zuciya, baya son kukan mace, macen ma wai Suhan.
A hankali ya duƙa haɗi da ɗagoni da dukkanin hannuwan shi, baya jin idan zai iya komawa da ita gidan haka gaban iyayen nashi.
Jana ya shiga yi har bakin wata bishiya da take ɗauke da wani ƙaton dutsi mai faɗi a jikin ta.
Zaunar dani yayi, sannan shima ya koma ya zauna a gefena.
Har yanzu bai ce mani ƙala ba, nima kuma na rage sautin kukan nawa sai shessheka da nake ta faman yi, da sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali.
Shiru yayi yana mai nazartar yana yin ta, har yanzu idanun shi jajur suke.
Wani bala'i kishin ta da ƙaunar tane ke taso mashi a cikin rai, wannan ne karo na farko da zai iya aikata wani abu daya san ya saɓa ma addinin nashi, saidai bayada yanda zaiyi.
Hannu ya sanya yana mai ɗan rungumoni zuwa jikin shi ya shiga bubbuga mani baya cikin sigar lallashi, idanun nashi har wani ruwan hawaye suke tarawa saboda tsananin ɓacin rai.
"Me ya kawo ki nan? Bayan kinsan akwai ƴan iska a wurin nan?
Ya jefo mani tambaya cikin salon maganar shi, da kansa inji jinin jikina ya katse ya fara gudu.
A sanyaye cikin dusasshiyar muryar da kuka ya gama cinyewa nace
" Ruwa nazo ɗiba yaya"
"Dole sai ke kaɗai ce zaki zo ɗibar ruwan anan wurin da yake ihunka banza?
Shiru nayi mashi, domin na kula ranshi a matuƙar ɓace yake. Saidai koma minene ni na gode ma Allah daya kawo mani shi a daidai wannan lokacin.
Ɗankwalina ya miƙa mani domin in rufe kaina, gashina duk ya warwatse dama gashi ba kitso a kaina, da kallo ya shiga bina ganin yanda na sanya hannu na tattare gashin duk uban yawan shi da tsawon shi na duƙunƙune shi na cusa cikin ɗan kwalin, ina mai gyara zaman hijab ɗin bisa kaina.
Har yanzu hawaye sun kasa tsayawa a idanuna.
"Yaushe kuka zo yaya?"
Na furta cen ciki, har ina kyautata zaton ma bai ji ba. Sai kuma naji ya amsa mani da cewa
"Yanzun nan, tare muke da su Alhaji da Bilal, Mun tarar umman bata nan sai kuma na shigo zaga gari, ashe ma kin dawo daga makarantar"
Dukkanin maganar da yajeyi har yanzu akwai tsananin ɓacin rai a tare dashi, fuskar nan da take fara ta kaɗa tayi ja sosai.
Duk da yanda nake gani a fuska ta, kaman ya ƙara kyau, sumar nan tashi ta kwanta luf a saman kanshi, ga fatar shi da ta ƙara murjewa kaman ka taɓa jini ya zuba, farar shaddar dake jikin shi ta ƙara fito da ainahin kyawon shi na asali.
Ya Ameen yana da kwarjini da haiba, hakan ce ta sanya ni kasa haɗa ido dashi, cikin sadda kai na shiga cewa
"Zanje na gaida su Dad ɗin"
Da sauri ya kalle ni yana mai nuna ni da yatsa
"A hakan? Ko baki san yanda kike ba? Kalli idanun ki fa"
Ya faɗa cikin wata irin murya dake ƙara sanyawa jikina sanyi matuƙa.
Miƙewa yayi yana faɗin
"Muje ki wanke fuskar ki sana"
Jerawa mukayi har bakin rafin, ta inda tuluna ya fashe muka bi, ina kallon shi yana kallon tulun, saidai bai ce mani ƙala ba, dama na san ba zai tanka ba, yau ma sa'a naci kuma na san harda tausayi na, daya lulluɓe shi.
Shi ya zuƙunna ya sanya hannuwan shi duka biyun yana mai ɗebo mani ruwan rafin ina ɗauraye fuskar tawa.
Har na gama sannan muka miƙe gabaki ɗaya, ya sanya hannu a aljihu ya fiddo hancarchip fari ƙar ya miƙo mani wai in goge fuska ta.
Ba gaddama, na amsa ina mai kai hancarchip ɗin fuska ta, saida naja dogon ajiyar zuciya, yanda ƙamshin turaren shi ɗan asali ya bugi hanci na.
Ban san lokacin da na duƙunƙune shi ba a fuska ta, in mai sake sakin wani kukan, tunowa da Abunda akayi shirin yiman yau a rayuwa ta, ni Suhan da nake daf da aure.
In ce ma Sir Saleem me? Idan duka duniya kunnuwa ne a jikin shi zai taɓa yadda dani? Me yasa wasu mazan basa da adalci ne a rayuwa? Kayi ma mace fyaɗe ko ƙanƙanuwar yarinya kaji daɗin me?
(Matsalar da muke fuskanta kenan a Rayuwar mu ta yanzu, fyaɗe cin zarafi mata, keta ma mata haddi, luwaɗi da yara maza ƙanana, ya zama ruwan dare a faɗin duniyar nan, ko saboda haka Allah ya isa ya kama mu, wallahi mu tuba mu daina, mu koma ma Allah subhanahu wa ta'ala, zamu ci riba a rayuwar mu, zamu rabauta)
Matsowa ya shiga yi a hankali ya sanya dukkanin hannuwan shi yana mai sauke man hannuwana daga saman fuska ta, ya san da ciwo, ya san ba daɗi, ko shi ya shaideta akan ita ɗin yarinya ce nutsattsa ko sutura banza matsattsa bata Sanyawa, yabar hakan a muƙaddari ne, da kuma gurɓacewar matasan yanzu a rayuwa.
Kaina ya aza bisa kafaɗar shi yana mai jijjigawa a hankali kaman wata baby.
Ban san lokacin da na kai hannu na idasa rungume shi ba ina mai sakin wani tsumammen kuka, ya Ameen ɗin Yayana ne, tin da na taso a rayuwa ta nake ganin shi, kallon Yayana nakeyi mashi, shi ɗin daban yake a cikin maza, in wani ne ba zai taɓa fahimta ta ba. Lallashi na ya shiga yi cikin shigar tausayawa yana mai ƙarfafa mani guiwa da umurtata akan in bar maganar anan wurin da gani sai shi sai Allah daya halicce mu, sannan in kiyaye koda nan gaba, tinda na kula akwai ɓata gari a ƙauyen.
Shi ya shiga jan hannuna, kaman makaho da ɗan jagora. Saida mukayi nisa ne sannan ya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo ya kalle ni sosai
"Ki daidaita Kanki Suhaaan, bana so kowa ya fahimci komai, akwai maganar da nakeso muyi kafin mu isa gidan"
Dakatawa nayi nima ina mai gyara fuska ta, na goge wasu ƴan matasan hawaye da suke sake gangaro mani.
Sannan nace
"ina jinka yaya"
Juyowa yayi sosai yana fuskanta ta, har saida Naji bugun da zuciya ta takeyi ya kuma lunkuwa, kwarjinin shi da cika idanun shi, su suka taru suka baibayeni.
Hannuna ya cika yana mai yiman kallo na sosai, sannan ya buɗe baki a hankali yana mai cewa
_*"ZAKI AURENI SUHAAN?"*_
a matuƙar firgice haɗi da bugawar zuciya lokaci guda na ɗago da dukkanin fuskanta, idanuna sun kwalalo kaman zasu faɗo ƙasa saboda tsabar firgici nake kallon shi.
Gyaɗa man kai yayi, yana mai lumshe kyawawan idanun shi da suke cike da gashin idanu Zara-Zara alamar tabbacin abunda ya faɗa shi yake nufi.
A hankali na sauke ƙwayar idanuna daga kanshi zuwa ƙasa ina mai........
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~43~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Haka muka kwana da umma, ba mai umm ba mai un-un
Washe gari tin da safe naga sun tashi ita da hajjo suna ta ƴar hada-hada.
Wajen ƙarfe sha biyu naga an fara fiddo kayan mu zuwa tsakar gida.
Kaina fa ya kulle, da idanu kawai nake binsu, har malam yau yana nan bai fita ba.
Jikin Hajjo da umman tawa yayi sanyi ƙlau, ɗan zaman da aka kuma yi ya sanya shaƙuwa mai tsanani tsakanin Umman tawa da hajjon.
Saidai a cikin zuciyar ta, bata jin zata iya barin wannan damar ta kufce mata, bata jin zata iya ɗaga ƙafa a wannan karon.
Zata ja, zata kara da koma wanene tinda yanzu akwai tsayayye a bayan ta, dama cen rashin galihu da rashin tsayayyen mai ƙarfi ne ya sanya ta ja baya, ya sanya ta yin shiru, kaman marar ƴanci.
Sun duƙar da kai sunyi rayuwar ƙasƙanci, bayan tasan komai, zaman ta a gidan dama da biyu tayi shi, yanzu kuwa bata neman wata ƙarin hujja illa ta ɗaura ɗambar neman abunda yake halalin su.
Azahar nayi naga wata irin hadadɗiyar mota tazo ƙofar gidan mu, sai kuma naji ana cewa mu fito.
Haka muka kwashi ƴan kayan namu da ba wasu masu yawa ba, dreban da kanshi ya shigar mana but, sai kuma Umman tawa ta tsaya yima su Hajjo sallama, sun ɗan daɗe suna tattaunawa, sannan suka rakota bakin mota ita da malam suna mata Allah ya kiyaye hanya.
Nima sallama nayi masu, ba tare da na kawo komai a raina ba, saidai ina tunanin inda zamuje kuma haka daganan.
Tafiya mukayi miƙaƙƙa, saidai mu tsaya salla, abinci ma take away muka tsaya muka amsa.
Hankalina bai tashi tashi ba saida naga mun shiga garin abujan cikin dare, sai kuma naga mun doshi gidan su Ya Ameen ɗin.
Toh fa!
Umman tawa da hankalin ta ta dawo damu cikin gidan nan? Bayan itace da kanta ta sanya mu barin shi da kanta?
Horn driver ɗin yayi mai gadi yazo ya buɗe mana.
A harabar gidan muka tadda Alhaji Mustapha da Ya Ameen suna zaune ga dukkan alama magana suke yi, Amman hankalin Alhaji Mustaphan gaba ɗaya yana kan ƙofar shigowar.
Da mamaki Ya Ameen ya miƙe yana kallon mu, tare suka miƙe da Alhaji Mustaphan yayin da naga ya nufo mu fuskar tashi cike fal da farin ciki.
Gaida Alhaji Mustaphan nayi, ya amsa cikin sakin fuska sosai, Abunda ke ƙara ma Alhajin Daraja kenan a idanun mu.
Sai kuma ya shiga takowa a hankali cikin salon tafiyar shi mai cike da natsuwa.
Yayi masifar kyau cikin hasken fitulun da suka haske ilahirin gidan tar kaman rana.
Daidai inda muke tsaye yaja ya tsaya, sai kuma ya shiga gaida ummata cikin girmamawa, sautin muryar shi na futa a hankali cikin wani irin amo da ya ƙara rikita ni da birkita mani tunani na.
Itama Umman tawa amsawa tayi, saidai wannan karon ba irin amsawar da nasan tana yi ma ya Ameen ba, Amsawa ce mai cike da dakiya irin ta ɗa da uwa.
A'ah
Me yake shirin faruwa ne wai?
Bai ko kalli inda nake tsaye duƙe da kai ba, ya sanya kai ya wuce zuwa sashen nashi.
Da idanu nake bin ilahirin gidan da ya wadatu da shukoki masu ban sha'awa.
Gine ginen ma kusan zamu ce an cenza su, ko ina tsit kake ji ba ƙarar komai sai na kukan tsuntsaye masu daɗin sauraro.
Alhajin ne ya kwala ma Mudi dreba kira, da gudun shi ya taso yana mai faɗin "ranka ya daɗe gani"
Kayan mu da driver ɗinda ya kawo mu mai suna Mahi ya fiddo mana ya shiga nuna mashi da hannu yana mai cewa su kwaso kayan su shigo mana dasu.
Maimakon inga mun nufi sashen masu aiki, sai naga mun nufi wani ɓangare mai kyau, wanda ada sashen Alhaji Mustaphan ne na sani a wurin.
Da makullin da yake hannun shi yayi amfani ya buɗe sashen.
"Masha Allah".
Itace kalmar da na fara furtawa lokacin da na saka ƙafar tawa cikin tanƙamemen falon da ya wadata da kaya masu masifar kyau kalar royal blue da maroon.
Umma ta na biye a bayana, itama ga dukkan alamu sashen nata ya matuƙar burge ta.
Sai a lokacin na fara dawowa hayyacina.
"wai ba dai ummata ce ta auri Alhaji Mustaphan ba" na faɗa a cikin zuciya ta ina mai kai zaune bisa wata luntsumememiyar kujera da ta wadatu da fuloli burjik kaman na gidan sarauta.
Gaba na ne ya shiga faɗuwa, Alhaji Mustaphan ne ya shiga gaba, umman tawa tana biye dashi har ɗan corridor ɗin da yake ɗauke da ɗakunan bacci guda uku.
Na farko ɗakine da yake ɗauke da kaya gwanin ban sha'awa, komai kala ɗaya ne dana falon, sai na biyu kuma shi gabaki ɗaya kalar maroon ɗinne da surkin Ash colour masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Na cen ƙurya shine yafi kowanne tsaruwa, kaya ne ƴan uban su, ba kalar na ƙasar tamu bane.
Komai na falon fari ne tas, hatta da kalar fentin upwhite ne. Kuma ko wanne ɗaki da toilet ɗinshi.
Gaskiya sashen yayi ba ƙarya, na biyun shine aka nuna a matsayin nawa, sai na farkon wai na ummata ne ɗana cen ƙurya ɗin.
Da matuƙar mamaki nake binsu da kallo, yau Ummata ita ce a matsayin amaryar Alhaji Mustapha Dambulan???
Falon muka dawo inda muka tadda ƙofofi guda biyu, ɗaya ta balcony ce, yayin da ɗayar take ta makeken kitchen ɗin da yasha carbinet mai masifaffen kyau, ba tarkace a cikin kitchen ɗin, saidai komai akwai.
Duka ɗakunan suna da Ac da manyan tagogi, sai falon shima haka, Amman shi ac ɗinshi Central Ac ce tana daga cen saƙo kusa da inda dining table da water dispenser take ajiye.
Amman sanyin ta ya wadaci falon gabaki ɗaya, harma kusan mu ce yayi yawa.
Sallama Alhajin Yayi mana ya fita yana mai cewa yana zuwa.
Da kallo nake bin Ummata ina ta raya abubuwa da dama acikin zuciyar tawa.
Ita ko ko sau ɗaya bata kalle ni ba, wata irin ƙarfin guiwa ne nake hangowa tattare da umman tawa, ta yanda naga ta shiga ƴan aikace aikacen ta hankali kwance.
Toh fa, ikon Allah saidai kallo.
Ceman tayi in tashi in shiga ɗakina inyi wanka in kwanta in huta kafin a kawo mana abinci.
A sanyaye na tashi ina mai nufar ɗakin da akace wai mallaki na ne, da ban gama yadda ba, har yanzu gani nakeyi mafarki nakeyi, nice yau a gidan Su ya Ameen ɗin da irin wannan matsayin na mallakar ɗaki sukutum.
"To amma shi ya sani kuwa?"
Tambayar da nake ta nanata ma kaina kenan, gashi naga sai wani ɗaɗɗaure mani yake yi kaman na kashe mashi uwa.
*******
Kai tsaye ɗakin Ya Ameen Alhajin ya nufa, ba zan iya cewa ga tsayin lokacin da ya ɗauka bai taka sashen yaron nashi ba.
Ba kowa falon sai Ac da take ta faman yi a hankali a hankali.
Bedroom ɗin ya tura, hango shi yayi zaune tsakiyar gado, har ya cenza kaya zuwa na bacci, laptop ɗinshi ce gaban shi yana ta faman latsawa.
Tura ƙofar da akayi ne ya sanya shi maida hankalin shi wurin.
"Dad" ya faɗa da mamaki, yana mai saukowa cikin hanzari, yana fatan dai ace lafiya, saboda tin bayan shigowar tashi ɗakin zuciyar shi ke kai kawo akan dawowar su Suhan ɗin a cikin gidan, ba zai ce baiyi murna ba, to saidai fa shi yaso ne ace sun dawo a matsayin masu matsayi a cikin gidan ba ƴan aiki ba, saboda yanzu baya jin idan zai iya lamuntr irin wancen wulaƙancin da akayi masu a Wancen zaman nasu.
"Lafiya ƙlau kake kuwa son? Naga ina ta magana kana cen kana tunani"
Dad ɗin ya faɗa yana mai jawo stool ya zauna bisa, yana mai ɗora hannun shi kan madubi da yake ajiye gefe irin na maza.
"komawa yayi ya zauna bakin gadon, yana mai faɗin" Lafiya lau dad" ai na ɗauka ka kwanta ne"
"A'a ban kwanta ba, baƙi nake so ka nemo ma abinda zasu ci"
"Baƙi kuma Dad? Su wanene baƙi?"
"Umman ka" Alhajin ya faɗa kai tsaye ba tare da wani shayi ba.
Bai kawo komai ba, yana mai faɗin "To Dad, yanzu kuwa insha Allah"
Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye haɗi da zaro jallabiyar shi ya sanya yana mai nufar ƙofa da niyyar ficewa.
"am Al'ameen, idan ka kawo ka miƙa mata sashen ta"
Ɗan dakata wa yayi daga barin tafiyar da yaje yi, sai kuma ya ɗan waiwayi yana kallon Dad ɗin nashi
"Dad ina ne sashen nata?" ya faɗa cike da mamaki
"Zo nan" Dad ɗin ya faɗa yana mai kiran shi da hannu
Dawowa yayi da baya ya samu gefen gado ya zauna, yana mai tattara dukkan natsuwa shi ya ɗora ta kan Dad ɗin nashi.
Ɗan gyaran murya kaɗan Dad ɗin yayi yana mai gyara zaman shi.
"Umman taka yanzu ai ba ƴar aiki baceba, *Matata ce* Daga yanzu kafin ta zama taka surukar ta zama uwa a wurin ku gabaki ɗaya"
Cikin sakin baki da ƴar gigita wadda Al'ameen ɗin be bari ta bayyana a kan fuskar shi ba, yake kallon Dad ɗin nashi.
Bakin shi yayi matuƙar nauyi harma ya gaza iya magana.
Jin Al'ameen ɗin bai ce komai bane ya sanya shi ɗorawa da faɗin
"Wannan shine tsani, shine matakin samun auren yarinyar a wurin ka, domin ko da muka je ma mahaifiyar da maganar ta auren naku ƙiyawa tayi, tace akwai maganar wani a kanta, to sai muka yanke shawarar hakan da Babanka Auwalu akan cewa bari in auri ita maryamar kaga alabasshi ko yaya ne ina da ɗan iko akan Al'amarin yarinyar. Amman ku fahinceni, masalan ma kai da duk dan kai ne nayi wannan abun, da kuma tausayawar da muke yi ma matar"
Tabbas ya gamsu iyaka da zancen Dad ɗin nashi, to saidai ba'a nan matsalar take ba, Mom, Mom ita ce babbar matsala, tabbas yanzu ne za'a fara tashin hankali, duk da cen ba'a yi komai ba.
Tuni zullumi da fargaba suka shiga Al'ameen ɗin, to saidai bai ce komai ba, ya shiga ɗaga ma Dad ɗin nashi kai alamar gamsuwa.
Miƙewa yayi yana mai faɗin "to Dad Allah ya sanya Alkhairi, don Allah kayi ta haƙuri da Mom saboda gaskiya za' a fuskanci wani irin yanayi a cikin gidan"
Da kallo Dad ɗin yake bin Ya Ameen ɗin da har ya fice daga cikin ɗakin.
********
Sai dai koda ya shiga motar kwalwar shi Sam ta cunkushe, rasa inda zai nufa siyen abincin yayi ba kuma wai don babu wurin siyarwa bane, tsabar tunani ne kawai da zullumi. Karkata kan motar tashi yayi ya nufi gidan Aminin nashi.
Har sun kwanta ya sanya mai gadi ya buɗe mashi ya shiga.
Parking yayi, yana mai zaro wayar tashi daga aljihu ya danna kiran Bilal ɗin.
Cikin ɗan bacci da ya fara fizgar shi, yaji wayar tashi na ruri, sunan Friend da yagani ne jiki ya sanya shi tashi zaune, sannan ya ɗaga.
Sanar mashi yayi da gashi harabar gidan shi, cikin ɗan ruɗewa ya sauko daga gadon a hankali kada ya tada Ummin da ta samu bacci ya kwashe ta ga ciki da yayi matuƙar girma a jikin ta.
Fitowa yayi daga shi sai singlet da boxer. Ilai kuwa motar Al'ameen ɗin ce fake gefe.
Ba wata wata ya shiga motar yana mai faɗin "Friend Lafiya A Daidai Wannan Lokacin?"
Ɗan shiru Al'ameen ɗin yayi idanun shi a kulle, sai kuma ya buɗe su yana mai wara su akan abokin nashi.
"Friend akwai matsala, Dad ɗina ya ƙara aure, bama wannan ce matsalar ba, Mom, Mom ita ce matsalar, idan har taji maganar ƙarin aure kuma da wadda ya aura"
Da mamaki Bilal ɗin ke kallon Al'ameen, saidai shima ya gaza cewa komai, saida aka kusan ɗaukar Second ashirin sannan ya iya cewa
"Friend gaya mani wacece ya aura? Kuma yaushe? Ya akayi kowa bai sani ba? Ko dama kai ka sani faɗa man ne baka yi ba?"
Girgiza kai Al'ameen ya shiga yi, yana mai faɗin "Umman Suhana ya aura, kuma yau ta tare, ya kake gani idan Mom ta dawo gobe ƙasar ta tadda wannan al'amari? Kadai san wacece Mom ɗita ba sai na baka labari ba, kasan halin ta kasan ne zata iya aikatawa, beside ma ina tausayin yarinyar, hakan na iya zama tarnaƙi tsakani na da ita, duk da shi Dad a ganin shi wannan ce hanya mafi sauƙi ta samun Suhan ɗin a wuri na, shi ko tunanin Mom ɗin ma baya yi, da Abunda zai iya zuwa ya dawo"
Al'ameen ɗin ya faɗa cike da ƴar damuwa a saman fuskar shi.
Ajiyar zuciya Bilal ɗin yayi, tabbas ya san Mahaifiyar abokin nashi, Sam mutumci ko karamci bai cika taba, da akan yaronta takeyi, gani takeyi kaman zasu mallake nata yaro, sai gashi abun ya juye ya koma kan mijin nata, kafin yazo ga kan ɗan nata.
Lallai akwai cakwakiya zalla a gidan nan, saidai fatan Allah ya kare kawai.
Muskutawa yayi yana mai faɗin. "Friend ka kwantar da hankalin ka, kada wani abu yazo ya same ka kawai, kayi ta addu'a, kuma kabar lamarin a hannun Abba, a shawarce kada ka sanya kanka ciki, in da hali ma, kada ka zauna a gidan gobe..."
" Bazan iya ba Friend, ko ina zanje hankali na yana a kanta, gani zan kaman wani abu zai same ta, a yanda na gani a saman fuskan ta, kaman itama bata san komai ba, Friend mafita nake nema please"
Ya ƙarashe ya mai bin kwayar idanun abokin nashi da kallo.
"To kuwa dole kayi kaman baka san me ke faruwa ba, dole ka bar zancen yarinyar for now, kada ka sake ka nuna ma Mom ɗin buƙatar taka akan Suhan, in ba haka ba kuwa abun zaiyi zafi sosai, ko da komai zai faru a gaban ka, kada ka nuna kana da intrest akan yarinyar, ka daure ma ranka, ka daure ma zuciyar ka please, komai zai zo da sauƙi, yanzu bari in zuro jallabiya muje mu nemo masu abincin"
"a'a ka bar shi kawai, zamu haɗu zuwa da safe, kana bacci na tada ka, ka koma ni zanje in nemo masu"
Al'ameen ɗin ya faɗa yana mai tada motar, fita Bilal ɗin yayi yana mai rufo mashi ƙofar ya matsa baya, har Al'ameen ɗin ya fice sannan ya koma cikin gidan.
*******
Abinci mai rai da lafiya ya siya masu, harda ruwan sha na gora masu yawa da kayan tea, sannan ya nufo gidan.
Tura ƙofar falon yayi cikin sallama ya shiga, zaune nake bisa kujera na takure saboda ɗan sanyin da yake ratsa ni, ummata kuwa tana cikin ɗaki bansan Abunda takeyi ba.
Bai ko kalli inda nake ba ya wuce kai tsaye bisa dining table ya ajiye manyan ledojin hannun shi.
Juyawa yayi da niyyar zai fice na taso a hankali ina mai kiran sunan shi cen ƙasan maƙoshi
"Yaya"
Ɗan tsayawa yayi, sannan ya juyo yana mai fuskanta ta, "Lafiya?"
Ya faɗa cikin amon murya dake nuna kaman na takura mashi.
"Yaya ina jin tsoro, bansan Abunda zai iya faruwa ba, please kaba Dad shawara a warware auren nan don Allah"
Na faɗa murya cen ƙasan maƙoshi.
Wani irin tausayin tane ya tsirga mashi, lallai ya ƙara tabbatar wa ba tare da sanina komai ya faru ba.
Takowa ya shiga yi har inda nake tsaye, duk da kaina yana a ƙasa, wasu irin siraran hawaye ne masu ɗumi ke sauka akan fuskar tawa, har ina iya juyo saukar numfashin shi a hankali.
A hankali ya sanya hannun shi duka ya ɗago fuskar tawa, wara idanu ya shiga yi saman tawa fuskar yana son gano dalilin da ya sanya ni kuka haka lokaci ɗaya.
Runtse idanuna nayi, wasu hawayen na ƙara malalowa. Da hannayen shi yayi amfani wajen ɗauke mani hawayen. "Is ok Suhan, babu Abunda zai faru sai Alkhairi kinji" ya faɗa cike da tausayawa, wata irin soyayya na fizgar shi, ji yake yi kaman ya rungume ta ko ya samu sassaucin Abunda yake ji a cikin zuciyar shi.
Ɗan girgiza kaina na shiga yi, ina mai janye kaina daga ruƙon da yayi mashi.
Sai na juya da baya da niyyar tafiya ɗakin nawa.
"suhhaaaaan" ya faɗa cikin murya siririya tana cracking
Tsayawa nayi ban juyo ba.
Ƙafa ya ɗaga taku biyu ta kawo shi ta inda nake tsaye.
Da hannuwan shi yayi amfani wajen kamo nawa.
"Nasan Mom ɗita kike tsoro, kibar jin tsoro, yanzu zaman Dad kuke yi a cikin gida nan, kuma Dad shine mai iko a gidan nan ba Mom ba, kiman alƙawarin ba zaki kuma yin kuka ba saboda haka, nasan yanda kike ji a zuciyar ki, Amman kada ki manta ina nan, Dad ma yana nan"
Ya faɗa da ɗan murmushi cikin son kwantar mani da hankali.
Ban iya zame hannuwan nawa ba, na shiga ɗaga mashi kai alamar gamsuwa.
"A'a Muhammadu kai ne?" muka tsinkayi muryar umma daga bayan mu tana tahowa.
Da sauri ya zame hannuwan shi cikin nawa, yana mai ja baya yake faɗin "Eh Umma nine, ga kayan amfani cen ku fara kafin zuwa safe muga dame dame za'a buƙata, kuna iya yo list ma"
Ya faɗa kanshi a ƙasa cike da kunya, wai yau umman ce yake magana da ita a matsayin matar mahaifin shi, Un bleavable.
Ɗan murmushi ta saki tana mai cewa "To an gode kwarai Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi"
Da "Ameen" ya amsa yana mai juyawa ya fice ko ta kaina baibi ba, itama umma juyawa tayi ta nufi inda ya ajiye kayan ba tare data ce mani komai ba.
To nima ɗin da kallo na shiga bin umman tawa, yanda take komai kai tsaye, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci umma tawa ta cenza kaman ba ita bace wadda na sani ada ba, me hakan ke nufi? Lallai akwai wani babban al'amari da yake a cikin zuciyar Umman tawa, babu shakka ko ɗar a cikin zuciyar ta?
Allah yasa koma me zai je ya dawo yazo mana da alkhairi Ameen.......
_Kuyi haƙuri da wannan a matuƙar gajiye nake wlh._
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~44~*
*Kyautar Page gareki One lurhv, ina jinjina maki a bisa soyayyar da kike mani Allah ubangiji ya bar ƙauna, ya tsole idanun maƙiya a kai, ya bamu ikon zama cike da so da amanar juna. AMEEN*
@Salamatu, Lubabatu, and Daura tnz for your personal Support, hearted u All guiz, ia ina yinku over and ove_
~_@Shalele (Raggon Miji Return) ki fita a idona in kulle fa tam, ni da One lurhv nan gani nan bari takalmin kaza, a tom_~
*Jinjina ga ƴan golden pen haƙiƙa haɗin kai da ƙaunar junan mu abu ne mai matuƙar ƙayatarwa, we are the best among the rest insha Allah, Allah ya bar mu tare*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Sama sama muka yabiɗi abincin daga ni har umman tawa.
Ƙala bata ce mani ba, ina kula da ita sai bina da kallo takeyi.
Jikina har yanzu a matuƙar sanyaye yake, amman ita umma na kula ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba wajen ƙarfafa tata zuciyar.
Kasa kwanciya nayi a ɗakina ni ɗaya ban saba ba. A hankali na tashi daga bisa makeken gadon nawa da ya wadata da katifa mai matuƙar taushi.
Ɗakin umman na ƙanƙwasa, daga ciki ta bani umurnin in shiga.
Tura ƙofar nayi a hankali ina mai shiga ɗakin, gefen gado na samu na zauna ina mai faɗa ma umma na kasa bacci ni ɗaya.
Cewa tayi in kwanta nan bisa gadon nata, zuciyar tata fal da tausayi na, ta kula yarinyar tata gabaki ɗaya kaman bata yi murna da wannan auren nata ba,tsoro ne fal acikin zuciyar yarinyar tata, saidai ba zata taɓa fuskanta ba, dalilin zaman nata a wannan gidan, da dalilin auren Alhajin da tayi duk yana da nasaba da ita Suhan ɗinne.
Ban yi baccin kirki ba, kaman yanda itama umman bata yi ba, tana kula da dukkanin juye juye na.
Saidai bata tanka mani ba, sai ma miƙewa da tayi ta dosa sallolinta.
To shima dai ɗin gogan zamu iya cewa bai runtsa ba ko sau ɗaya.
Abubuwa ne fal yake damun shi cikin zuciya. Ɓangare ɗaya Mom ɗin tashi ce ke kai komo.
Wani Al'amari irin na uwa da ɗa ke taso mashi, sai kuma cen ƙasan zuciyar shi Suhan ɗin ce tayi tsaye ƙiƙam, duk son da yayi na ya matsar da ita ya kasa.
Sai kuma tinani da taraddadin dalilin Dad ɗin nashi na son auren Umman Suhan ɗin, wanna amsar dai a yanzu kam baya da ita. Zai jira har lokacin da Alhajin nashi zai warware mashi zare da abawa.
Tin da farar safiya yayi shiri ya fice daga gidan, Bilal ya tsaya ya ɗauka sannan suka wuce.
Mu kau tin bayan munyi wanka, sai kuma muka koma zaman jigum jigum.
Nikam miƙewa nayi na koma falo, domin yana yin da nake ciki ba zan iya fasalta komai ba, cikin raina tausayin yanda rayuwa ke walagigi dani nakeyi, a hankali a hankali nakan sanya yatsa in share kwallar da take bi mani fuska, sai nayi kaman in kira Sir Salim ko zai sanya ni dariya ko da kuwa sau ɗaya ne sai na kasa.
Ina jin Kunyar ince mashi mahaifiya ta ce tayi aure, Amman kuma ya zama dole ya san inda nake ko don saboda sanin halin da makaranta take ciki.
Dirin mitoci ne ya karaɗe ilahirin gidan, sai kuma muka ji hayaniya ta ɓarke a gidan.
Miƙewa nayi a hankali na isa ga wangamememiyar tagar da take falon, leƙawa nayi, saida gabana ya ruguje ya faɗi.
Ƴan kankiya ne su da yawa, ƙwansu da kwarkwata, duk wani wanda zai iya zuwa saida yazo.
Hajiya Zainab ce gaba gaba, sai kuma Hafsat a gefen ta daƙyar take cira ƙafa saboda girman da cikin ta yayi.
Gaza matsawa nayi, ita kuwa Ummata tinda taji hayaniya ta tashi ta shige ɗaki ta barni nan tsaye ina mai binta da kallo.
Hafsat ta riga kowa shigowa, da sauri ta shigo tana mai dube dube kaman tana neman wani abu, sai kuma naga ta saki murmushi ta nufo ni, tana mai rungume ni tsam a jikin ta.
Shigowa suka fara yi, lallai suna da yawa, hannuna Hafsat ɗin taja alamun inzo mu shiga ɗaki, ganin bata san ɗakin bane ya sanya na shiga wucewa gaba, tana biye dani.
Ɗaki da yake mallakina wai muka shiga, bakin gado muka zauna, tana mai bina da idanu kaman zasu faɗo ƙasa.
Sai kuma na saki kuka mai cin rai, Hafsat ɗin ƙawa ce, aminiya ce gareni.
Bata ce komai ba sai ma sake bina da tayi da idanu.
To ita ai bata ma ga abun kuka ba anan, murna ma ya kamata inyi, Allah ya kawo ranar da muka samu ƴancin mu a cikin gidan.
Sake rungume ni tayi tana mai ɗan bubbuga bayana a hankali alamun lallashi.
"Suhan menene na kuka kuma? ko Auren Umman ne baƙya so."
A hankali na ɗago ina mai kallon ta, sai kuma na shiga ɗaga mata kai, alamun bata tabbacin Abunda ta faɗa.
"Kin jiki? To menene a ciki? Umma fa ba wuce aure tayi ba, kuma bayan haka, Babana Mutum ne da kowacce mace take fata da burin ta samu a matsayin miji, saboda yana da kirki da mutumci matuƙa. To ke menene dalilin da yasa zaki ce bakya son hakan?"
"Hafsat, Hajiya Kubra, Hajiya Kubra ba zata ɗaga mana ƙafa ba, ba zata ƙyale mu ba, ga su Aunty Nihal, da Aunty Saudat. Da cen ma da muke ƴan aiki bata ɗaga mana ƙafa ba sai yanzu da Umma ta aurar mata miji?"
Na faɗa ina mai sake matso wani kwallar daga idanuna.
Ɗan murmushi ta saki tana mai faɗin" Ke da zaki auri yaron nata ma tin yanzu kin fara karaya balle?"
Ɗan zabura nayi ina mai ce mata" Inji wa? Waya faɗa maki?"
" Mama Mana, a bakin ta naji, tin lokacin da su Baba suka je neman auren naki"
Ta faɗa tana mai ƙumshe dariya
Ohh ni Allah, ashe wancen zuwan da su Alhaji Auwalun sukayi a ranar da abun nan ya faru dani wai aure na suka je nema ma ya Ameen?
Ashe Shiyasa yace mani zan aure shi?
Kenan don kada a kirani jin ta bakina ince bana so ne ya sanya shi tara ta da wannan maganar
Gaske fa, ni dama nayi mamaki, ashe ba har cikin zuciyar tashi son nawa yake ba.
Dama wace ni da Ya Ameen??? Ai ni kaina nasan yafi ƙarfina har gaba da abada ma.
Kawai da zancen zucin da nakeyi nayi, ina mai share kwalla ta.
Ɗan duka na kai mata ina mai cewa "Banason haka hafsat, ba don babyn mu ba da sai kinji jiki"
Dariya ta saki iya ƙarfinta, sai kuma tace "Ya naga wai baki fara shiri ba? Haka zaki ci walimar?"
Da mamaki nake kallon ta ina mai cewa "Wace walima kuma?"
"Bakiga baƙi ba? Ƴan uwa ne duk suka zo za'ayi walima yau, ƴan uwan ango Dad"
Ta faɗa cikin zaulaya tana mai kanne mani ido ɗaya.
Hayewa nayi bisa gadon ina mai ce mata "A gama lafiya ƴaƴan ango"
"To ɗiyar amarya" ta faɗa tana mai wucewa gaban akwatina na da suke gefe ajiye.
Jawosu tayi ta shiga buɗewa.
Dudduba komai ta shiga yi, sai cen ta fiddo wani material mai kyau matuƙa ta ajiye ta haɗo harda gyalen da zai iya shiga dashi.
"Kinga kayan da zaki sanya nan please ƙawata, don Allah ki saki ranki, na rana ɗaya ne zamu yi tafiyar mu mu barku"
Kallon ta nake in mai taɓe baki, Ƙala bance mata ba, sai ma juyawa da nayi ina mai kulle idanu na.
Da dai taga alamun rigima nake ji da ita, kuma har cikin raina tsoron auren nan ya kama ni, sai ta miƙe haɗi da ficewa daga ɗakin.
Hajiya Zainab ma kai tsaye ɗakin ummata ta shiga, sai a na biyun ne ta hango ta zaune bakin gado.
Isa tayi suka shiga gaisawa cikin mutunta juna da ƴar firar yaushe gamo,sannan tayi mata Allah yasa Alkhairi ya bada zaman lafiya.
Bata ce ma Umman komai ba akan walimar da za'ayi, domin komai na a hannun ta ne.
Wai Ashe har mai make-up aka kira zata yi ma umman tawa, abun ban dariya.
Hajiya Zainab ce gaba gaba wajen haɗa komai, ƴan aikin dake gidan kaf saida aka kikkira su, kowanne da aikin da yake yi, duk da suma mamaki ya cika ransu fal, gashi sun san Hajiya Kubran bata ƙasar, saidai sun san duk inda take tana bisa hanya.
Canopee ne aka kakkafa manya masu kyau, anyi masu ado sosai, sai kujeru da aka jejjera.
Daga wani eatery aka dinga shigowa da abinciccika suma duk jejjera su aka shiga yi, ƴan kankiya ma har sun zazzauna.
Kowa ya sha kwalliya daidai gwargwado, nima daƙyar Hafsat ta lallaɓa ni na sanya kayan, Amman fuskanta babu wata kwalliya, ko kwalli babu daga mai sai farar powder.
Bamu kai ga fita ba, saidai ance da anyi sallar azahar za'a fara gabatar da walimar cin abincin, kafin a gabatar da Umman wurin ƴan uwa.
Ma'aikatan gidan sai ƴan maganganu suke yi, saidai ba damar a faɗa fili, duk da har yanzu cikin su ba wanda ya san abunda ke faruwa sai mudi ne kawai ya sani, shima da yake ba surutu gareshi ba yaja bakin shi ya tsuke kada aji maganar sarki a bakin shi.
************
Yana tsaka da aiki wayar tashi ta soma ruri, saida ya kai kallo sashen da Bilal yake zaune shima yana latsa laptop.
Sai kuma ya ɗaga yana mai sallama ganin Sunan Mom ɗin nashi yana yawo a bisa screan ɗin, saida gaban shi ya faɗi.
Sallama yayi cikin dakiya da son kauda komai a cikin ranshi kada ta fahimci ko yana da damuwa.
"Son na dawo kazo ka ɗauke mu a airport yanzun nan"
Ta faɗa cikin bashi umurni kai tsaye.
Miƙewa tsaye yayi yana mai tattara wayoyin shi bayan ya kashe wayar.
"Friend akwai matsala"
Ya faɗa cikin wani irin yanayi mai nuna alamun ya kusa sarewa.
Cikin ƙarfafa guiwa Bilal ɗin yake tambayar abokin nashi.
"Mom ce ta dawo yanzun nan, kuma wai ni zanje in ɗauko su in kaisu gida, may be ita da ƙawayen ta ne"
"Toh fa! Menene abun matsalar a ciki? Friend mahaifiyar ka ce fa"
Ya faɗa yana mai ɗan tallafe kanshi da hannuwan shi.
"Anyway, bari inje in gani ko zan samu in dawo da wuri in idasa aikin nan"
Ya faɗa yana mai wucewa cikin salon takun tafiyar shi mai ɗaukar hankali.
Koda ya isa lallai hasashen shi ya zama gaskiya.
4Hajiyas ne cikin shiga ta alfarma sai zuba ƙamshi suke yi, tin daga nesa zaka iya hango isar su da hamshaƙar su.
Cikin murmushi irin na ɗa da uwa ta shiga taka wa tana nufar inda yake doso su kai tsaye.
Ɗan rungume shi ta shiga yi, tana faɗin "I missed you My Lovely Son"
Ɗan murmushi yaƙe ya saki yana faɗin "Mee Too Dear"
Motar suka ɗunguma gabaki ɗayan su bayan ya gaida ƙawayen Mom ɗin nashi.
Cikin Murmushi da ban sha'awa suka shiga amsawa, ko ba komai suna matuƙar alfari da yaron Ƙawar tasu kuma hamshaƙiyar tasu.
Tin da suka doshi gidan gaban shi ke faɗuwa, cikin mamaki take kallon shi, hango motoci da tayi ƙofar gate ɗin gidan nasu, gashi kuma ita batasan abunda akeyi ba, kuma ko da safe sunyi waya da Alhaji Mustaphan Amman bai ce mata ana yin wani abu ba.
Ɗan kallon shi ta shiga yi, alamar son ƙarin bayani.
Janye idanun shi yayi yana mai runtse su, Abunda zai je ya dawo a daidai wannan lokacin yake gudu, ina ma ace yabi shawarar abokin nashi wajen barin garin ma gabaki ɗaya.
A hankali ya shiga gangarawa cikin gidan, bayan mai gadi ya wangale masu gate.
Tsabar mamaki tsantsa ne a kan Fuskokin 4Hajiyas ɗin, tin kafin ya idasa parking Hajiya Kubran ta ɓalle murfin motar ta fito, gyalen ta saman kafaɗa guda ɗaya, sai ƴar mitsitsiyar jikkar dake hannun ta kaman ta wasan yara, da tafka tafkan wayoyin dake hannuwan nata riƙe
Abokan nata ne suka shiga mara mata baya. Kusa da Canopee ɗin taja ta tsaya, tana iya hango ƴan kankiyar a cikin runfar, walima akeyi, abinci ake ci mai rai da lafiya, kowa sai hidimar shi yake yi, duk da sun kula da ƙarasowar ta wurin.
Waiwayawa tayi tana mai kallon Al'ameen ɗin da yake tsaye bakin motar tashi, ya gaza ɗaga ƙafa balle yabar wurin.
Sai kuma ta maida kallon ta kan mutanen da suke cikin rumfar.
Wata kujera mai matuƙar kyau, ruwan gold ce ajiye gefe guda ba kowa a kanta, sai kuma kanta ya ƙara ƙullewa.
Ta rasa wanda zata tambaya, gashi tana son tambayar Amman isa da mulki sun hana ta tambayar.
Hajiya zainab ce kan gaba, sai Goggo Aisha da Goggo Fatima a bayan ta, sun sanya wata mata tsakiya. Tasha ɗanyen leshi mai matuƙar tsadar da tasan kuɗin shi sun haura ma naira dubu ɗari biyar, wara idanu ta kuma yi sosai, daga sashen da Alhajin yace mata nashi ne aka fito da ita, kanta lulluɓe da mayafi mai kyau da walwali.
A bayan ta yara ne guda biyu, ta shaida Hafsat da take cira ƙafa daƙyar, sai kuma gudar da ta kalle ta a fige ba tare da ta shedata ba, saboda hankalin ta ba'a kanta yake ba.
Kai tsaye kujerar da take ajiye suka zaunar da ita.
So take taga fuskar matar, hankalin ta in yayi dubu ya tashi, ƙawayen nata ta maida kallon ta wurin da suke tsaye suma cike da tsabar mamaki.
A hankali ta shiga takawa har gaban matar da aka zaunar bisa kujera, hannun ta duka ta sanya ta ɗage gyalen da yake lulluɓe saman fuskar Umma tawa.
A matuƙar zabure taja baya, har tana shirin faɗuwa.
Wa take gani haka?
Maryama ce zaune bisa kujerar tasha kwalliya har ta gaji, wuyan nan nata cike da ɗanyen gwal ɗinda kuɗin shi saidai a kira miliyoyi, hannayen ta kaf cike suke da awarwaro na gwalagwalai
"Ayuririririririri"
Taji wata mayyar guɗa ta saki guɗa cike da ƙwarewa matuƙa, sai kuma taji an shiga faɗin
"Uwargida ke nan a wurin Alhaji Mustapha Dambulan ɗin, ita ce da kanta ta siyi wankan da Amaryar tata tayi ayau domin faranta ran dangin mijin nata. Ayau Allah ya kawo mu shagalin bikin Amaryar ta Alhaji Mustaphan Farar mace alkyabbar mata, Uwargidan ki na tsaye a gaban ki tazo kawo gaisuwar ban girma da yi maki maraba da shigowar taki gidan nasu da yake cike da ɗumbin wadata da arziƙi haɗi da soyayya da zaman lafiya."
Gabaki ɗaya muka waiwaya domin ganin wacece wannan zabiyar haka?
Wata mata ce tafe jikin nata sanye da atamfa mai matsakaicin kuɗi, da gani dai zabiyar ce da gaske, to ko wa ma ya gayyato ta kuma? Oho!
Hajiya Sa'a ce ta matsa haɗi da kamo hannun Hajiya Kubran da ta tabbatas tayi mutuwar tsaye ne, idanun ta sun firfito kaman zasu faɗo ƙasa, ita kuwa umman tawa murmusawa kawai takeyi cikin ƴar kwalliyr da akayi mata Light mai ban sha'awa, ashe haka Umman tawa take da kyau masha Allah.
Bata da zaɓi illa ɗaga ƙafa ta shiga bin abokiyar tata, ƙafafun ta har suna harɗewa, to sanin da kowa yayi akan halin hajiya Kubran ne ya sanya basu kawo komai ba, sun ɗauka isar tata ce ta motsa, kuma gashi babu wanda tayi ma magana.
Ya Ameen da yake gefe, nannauyar ajiyar zuciya ya saki, yana mai kai idanun shi bisa fuska ta da take tar babu ko ɗigon kwalliya bisa, hakan ne yasanya haskena ƙara fitowa, da idanuna suka yi ɗan ja saboda kukan da nayi gashi kuma babu kwalli a jikin su ko ɗis.
Kallona yayi na tsawon Second goma, sai kuma ya ɗaga ƙafa cikin sauri ya nufi sashen nashi, yana mai ɗan sauke ajiyar zuciya ganin Mom ɗin tashi bata saida hali ba.
*************
Suna shiga sashen nata, ta fizge hannun ta daga na Hajiya Sa'ar, sai kuma ta shiga kai komo.
Cikin wani irin yanayi na tsantsar ɓacin rai, zuciyar ta kaman zata tsago ƙirjin ta ta fito, ga wani irin ja da farar fuskar tata tayi.
Kai komo ta shiga yi cikin falon da ya wadatu da kayan alatu.
"Ni?? Ni?? Ni???"
"Ni Alhaji zaiyi ma haka? Ni Alhaji zai cima amana? Ya rasa wadda zai aura sai ƴar aikin gida na tsawon lokaci? Ƴar aikin ma wadda nafi tsana a rayuwa ta? Ƴar aikin ma marar galihu da asali irin Maryama?"
"Niiiiiiiiii???"
Ta faɗa tana mai zama bisa kujera ta shiga dafe kanta, sai kuma ta miƙe ta wawuro wayar ta ta shiga danna kira.
"Hello Saudat, kinji Abunda mahaifin ku yayi? Aure yayi, kuma ma wannan shegiyar ƴar aikin marasa asali, Eh ki kira Nihal yanzun nan kuzo ku same ni a gida"
Sai kuma ta kashe wayar tana mai danna ma Ya Ameen kira.
Gabaki ɗaya ta fita kamannin ta da hayyacinnta, lallai ma Alhaji ya zubar mata da ajin da mata dayawa suke ganin ta dashi.
Yana ganin kiran nata ya kasa ɗauka, ya san abunda zai faru, zama yayi yana mai dafe kanshi da dukkanin hannuwan shi da yake jin kaman zai tsage mashi.
Hajiya Laila ce ta amshe wayar a hannun ta
"Hajiya Kubra ki tsaya muyi magana, ki zauna mu nemi mafita"
A zafafe Hajiya Kubran ke kallon ta, sai kuma ta shiga cewa
"Duk laifin kune Laila, ku kuka ja mani, wane irin kuɗi ne ban ba ku ba akan a ɓatar dasu a cikin ƙasar nan? Kuma kun mani albishir ɗin sun tafi kenan? Ta yaya zasu dawo mani cikin gida, kuma ma wai a matsayin matar gida? Kunci amana ta Laila da Sa'a kunci amana ta bazan taɓa iya ɗaga maku ƙafa ba har abada"
Ta faɗa cike da hargagi tana mai watsar da tukwanen plowers ɗin dake ajiye bisa wata pula gefen falon.
Kaman zata yi hauka haka take ji, ta watsar da gyalen da jikka harda wayo yin nata, abun kunya ne a wurin ta ace kaman ta mijin ta ya auri ƴar aikin ta.
Hajiya Sa'ar ce zata fara magana ta shiga dakatar da ita.... "Kiyi mani shiru Sa'a, har maci amana ma irin ku zaku iya bani uzirin ku? Amman nasan mai laifi, ba kowa keda Laifi ba asai Al'ameen, shine ya fara bijiro da maganar Aure a gidan nan, zai zo ya iske ni, sai na ci mashi mutumci wallahi zai tadda ni.
Mai gadi ne ya shiga buɗe gate ɗin gidan, a guje motar ta shigo haɗi dayin parkin kaman zata murje mutanen dake gurin tsaye.
A fusace suka fito suna yima kowa kallon banza, Nihal ce da Saudat ɗinda aka ci sa'a sunzo ƙasar ita da mijin nata.
Fuuu suka shige cikin gidan, kowa da kallo ya bisu yana mai girgiza kai haɗi da Allah wadai a cikin zuciya.
A sukwane suka isa wurin da mahaifiyar tasu take ta faman safa da marwa tana sakin ajiyar zuciya sukayi.
"Mom me kike faɗa mana haka a waya? Taron me akeyi cikin gidan nan haka?
Nihal ɗin ta faɗa cike da rashin kunya da tsiwa.
Hajiya Kubra ce ta kuma zaburo mata, ji takeyi kaman tayi hauka fa yau.
" Na faɗa maki Dad ɗinku ne yayi aure, Maryama ƴar aikina ya aura don cin amana"
"What Mom? Waɗannan Talakawan faƙiran? Me Dad ya gani ya burge shi jikin su?"
Umman ce ta kuma matsowa jikin Saudat ɗin kaman zata kai mata duka.
"Yo me kuwa ya gani banda asiri? Asiri suka yi mashi, da sun yima Al'ameen basu ci galaba ba, shine yanzu suka koma kan Dad ɗinku mai gaba ɗaya, to wallahi ba zata taɓa zama gidan nan ba, ba zan lamunta ba, ai kiran ku nayi ku gani da idanun ku"
Ta faɗa tana mai kwasawa ta nufi hanyar waje kaman zakanya.
Su Hajiya Sa' a basu nemi hana ta ba, saboda uwar watsin da tayi masu yanzu, duk jikin su yayi sanyi, dama ita sabuwar Ƙawar tasu ba'a sanya ta ciki ba, bata ma san meke faruwa ba, duk da itama cike take da ɗinbin mamaki.
Rufa mata baya sukayi suma, saidai daga bakin part ɗin nata suka ja suka tsaya, su kau su Nihal har bakin rumfar suka isa.
Ja tayi ta tsaya cike da isa tana yima kowa kallon wulaƙanci, harda yayyen mijin nata da suke ta sha'anin su ba tare da sun kula ta ba ma.
"To taron maciya amana, taron kwaɗayayyu, taron ƴan kuci ku bamu, ku kuma ku rasa auren da zaku zo mawa sai wannan auren na maciya amana? Auren ha'inci? Auren da bana da masaniya akan shi? Ta faɗa tana mai bin su da idanu gabaki ɗayan su.
Goggo Fatima ce ta buɗe baki da niyyar bata amsa, sai Goggo Aisha ta zunguro ta alamun tayi shiru.
Hakan ba ƙaramin ƙona ran Hajiya Kubran yayi ba, sai kuma ta shiga cewa
"Ba dole kuyi mani shiru ba, anci amana ta an zalunce ni? An auran mani ƴar aiki? Ke kuma na dawo gareki, ki sani baki kai matsayin da zan iya haɗa miji dake ba, wallahi saidai yazo ya zaɓa ko ni ko ke, cikin ɗaya ayi biyu. Dama munafuntata kike yi zama gidan nawa da kika yi ashe? Gaskiya naji na tsane ki, da anso a liƙa ma yaro na wannan koɗaɗɗiyar ɗiyar taki Allah ya tsallakar dashi, ashe kince dole dai ki zauna a gidan bayan barin nashi da kikayi kaman gaske, ashe wani tsafin akaje aka ƙullo? To wallahi ahir ɗinki kurwa ta kur data mijina data ƴaƴana"
Umman tawa tinda Hajiya Kubra ta fara magana take ta fama doka murmushi abun ta, Sam hakan bai ɓata mata rai ba, bai kuma bata mamaki ba, wannan ƙaramin abu ne akan wanda ta shirya ma gani, saidai koma minene ba zata taɓa sarewa ba, wannan shine mafari ma, wannan shine masomi, zama daram kaman ɗuwawu.
Nikau tinda ta fara magana hawayen da nake ta faman riƙewa suka soma zarya akan fuska ta, wannan shi nake gudu, wannan shi nake tsoro, ina gudun abunda zai je ya dawo, inda Allah ma ya so mu babu wanda ya tanka mata duk wulaƙancn da takeyi, hatta da su Goggo Aishan sun haƙure ma kansu.
***
Tin da ta fara sonsomin bala'n ta yake tsaye ta taga yana kallon ta, gabaki ɗaya kalar fuskar shi ta sauya, me Mom ɗin tashi ke nema a rayuwa? Wane irin abu ne takeyi a haka? Gashi kaman sun maida ta mahaukaciya tsaye ita kaɗai tana ta zuba bala'i? Ina ta baro isar tata yau? Ina ta ajiye girman kan? Da rashin son maganar?
Juyawa yayi a hankali yana mai sakin labulen ɗakin ya koma ya zauna bisa sofa, kanshi yake ji kaman zai tsage biyu, Gaza zama yayi sai kuma ya tashi ya koma bakin tagar yana hangen komai tar.
Hangota yayi ta tashi cikin ɗan gudu ta nufi sashen nasu, da alamu dai kuka takeyi sosai, sai kuma yaga Hafsat ta ɓaɓɓaka ta bita daƙyar.
Runtse idanun shi yayi yana mai sake sakin labulen ya zarce zuwa bedroom ya kwanta rigingine yana kallon POP ɗin da yake fari tar saman rufin ɗakin da ya wadatu da fararen ƙwayaye tas.
Wayar shi ya jawo haɗi da kiran Bilal ɗin, yana mai ce mashi yabar ko me yake yi yazo ya same shi please.
Runtse idanun shi ya kuma yi, idan duk duniya farin ciki ce, zai iya cewa shi yau baƙi ƙirin yake gani tsabar ɓacin rai.
Ranshi gabaki ɗaya a dagule yake, ya san ba zai taɓa fita ba, ya san zasu kai ruwa rana da Mom ɗin tashi, tinda yaga kiran ta ya san kwanan zancen Shiyasa ma bai ko iya ɗagawa ba.
Baiyi gigin kiran Dad ɗin nashi ba, domin a yadda Mom ɗin tashi keji da bala'i, ko Alhajin ne yazo a daidai wannan lokacin zata iya yi mashi, kishi da baƙin ciki na cin ta tsanta.
Ganin ba wanda ya kula ta ne ya sanya ta juyawa cikin ƙufula da hassala ta koma sashen nata.
Cikin ƙawayen nata babu wanda ya iya ce mata komai, suma su Nihal mara mata baya sukayi, ransu a matuƙar dagule ga wani kallon tsana da suke bin ummata dashi, Abunda ya kuma ƙara ɓata masu rai shine murmushi da suka ga tanayi, kenan ma ta maida su sakarkaru kenan.
Cikin minti Goma sai ga Bilal ɗin ya bayyana sashen Abokin nashi, duk mutanen da suke harabar gidan haka ya ratso su cikin sauri.
Kwance ya tadda shi yana dafe da kai.
"Al'ameen Lafiya kuwa?"
Ya faɗa yana mai hawa gadon haɗi da tallafo kan abokin nashi.
"Ba lafiya Bilal". Al'ameen ɗin da ya buɗe idanun nashi daƙyar, sun cenza kala sun koma kaman garwashi, ya aza su bisa kan fuskar Bilal ɗin da yake tallafi da kanshi.
"Friend nace maka ka sanyaya zuciyar ka, babu Abunda zai faru insha Allahu, ka dena tunani Mom ba zata yi wani abu.......
" She has done it"
Abunda ya iya faɗa kenan ya maida idanun nashi ya kulle.
"What?" Bilal ɗin ya faɗa cike da kaɗuwa. Muryar Al'ameen ɗin ya tsinkaya a hankali yana faɗin
"Am sick Friend ka kira mani doctor, kaina zai tsage"
Cikin bala'n firgici ya diro daga bisa gadon, jikin shi har rawa yakeyi ya zaro wayar tashi daga Aljihu ya shiga laluben number ɗin doctor ɗin.
Ya san matsalar Abokin nashi, ya san da uwar shi, dole kuma ya shiga wani hali na tashin hankali, damuwa dole ce, to saidai shi da yake da matsala bai kamata ya sanya ma ranshi damuwa har haka ba.
"Cool your mind friend, nothing will gonna happen insha Allah" Abunda Bilal ɗin yake faɗa kenan da ƙarfi yana mai girgiza Al'ameen ɗin da idanun shi suke daɗa kullewa a hankali har suka idasa rufewa kirif.......
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~45~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Cikin minti goma sha biyar Dr.ya ƙaraso.
Ta ƙofar baya Bilal yaje ya buɗe mashi, saboda gudun jawo hankalin mutane.
Duba shi sosai yayi, yana mai kwantar ma Bilal da hankali akan cewa ranshi ne ya ɓaci, kuma ba'a son haka, saboda ga alamu nan har yanzu jikin nashi bai ida warwarewa ba, ga kuma stress da ya sanya ma kanshi, gaskiya a kiyaye abunda ke ɓata mashi rai haka nan da nan.
Ruwa ya ɗaura mashi haɗo da allurai, yana mai bada shawarar a bar shi ya samu bacci sosai kaman na awa biyu.
Sai a lokacin hankalin Bilal ɗin ya kwanta, jin matsalar ba mai yawa bace.
Wai me yake faruwa ne haka? Wa zai tambaya, ashe abokin nashi bai bi shawarar tashi ba? Ko dayake ba lallai bane yanzu ya dinga bin shawarar tashi ba kai tsaye.
Nan ɗakin ya zauna yana watching abokin nashi, gashi gidan kuma da ƴar hayaniya, duk da bata cika damun su ba kai tsaye da yake da ƴar tazara haka kaɗan daga inda suke.
***********
"Suhan kiyi shiru hakanan, kiyi haƙuri don Allah, bana so inga kina kukan nan, aure dai an riga an ɗaura, saidai muyi Addu'ar Allah ya basu zaman lafiya, ya kauda duk wata fitina dake neman kunno kai, ita kuma Mom Kubra Allah ya shirya ta."
Hafsat ɗin wadda ta zauna gefen gadon nawa, tana mai & ora hannun ta kan gadon baya na da nake kife ina mai rusa kuka haiƙan.
Abunda nake guje ma Umman tawa kenan, cin mutunci a gaban kowa, har yanzu ban gano dalilin wannan auren ba.
Ɗagowa nayi ina mai kallon ta haɗo da cewa
"Hafsat wannan wane irin aure ne? Auren da yake barazana ga kwanciyar hankalin mu, wancen karon ma wace Allah cika? Balle yanzu da ta auran mata miji? Wane irin zama kike tunanin zamuyi a cikin gidan nan? Hajiya Kubra na da kuɗin da Ummata da bata da komai ba zata iya ja ko karawa da ita ba..."
" Suhan mace fa bata auran kanta, kuma na tabbata Umman ba itace ta bijiro ma da Dad maganar auren nan ba, ƙila akwai abunda ya hango tattare da umman ne, kasancewar ta mutuniyar kirki, ga sanin ya kamata, kuma Abunda nakeso dake ki sani shine, kowa a zyri'ar mu yayi na'am haɗi da farin cikin wannan auren, har su kaka zuwaira, kasancewar Dad na buƙatar mai taimaka mashi da kula dashi, saboda irin hidindimun shi, da kuma ayyukan shi, kinga kuwa ita Mom Kubra business ɗinta ya fiye mata tsayawa da kula da Dad, hasalima idan ta sanya ƙafa ta bar ƙasar sai an ganta, gashi taƙi yarda ta zauna dashi acen Istanbul ɗin, saboda haka babu wanda ya soki lamirn auren nan, share hawayen ki ƙawata kiyi farin ciki, babu Abunda zai faru insha Allah in ba alkhairi ba, kuma itama Mom Kubra insha Allah zata yarda kuma ta amince."
Ɗan runtse idanu nayi, wasu hawayen na daɗa zirara a idanu na, Hafsat ɗin ba zata taɓa fahimta ta ba...
Wayata da take ajiye bisa gadon ce ta ɗauki ruri.
Number ɗin Sir Salim ce naga tana kai kawo a bisa fuskar wayar tawa.
Kafin in kai hannu Hafsat ɗin ta kai hannun ta ta ɗauko gami da duba mai kirana, saboda ita a zaton ta ko Ya Ameen ne, saboda tin da suka shigo da Haj Kubra bata ƙara ganin shi ba, amman dai ta kula yana cikin gidan.
Kallon tuhuma ta bini dashi tana mai miƙo mani wayar.
Tashi nayi zaune sosai, sannan na amsa ina mai matsawa na jingina bayana da makarin gadon.
"Assalamu Alaikum"
Na faɗa cikin siririyar muryar da tasha kuka ta gaji.
Daga ɗaya ɓangaren akan amsa mani cikin muryar da ayanzu nafi muradi da inji ko zan samu sauƙin Abunda nake ji cikin zuciyata
"Wa'alaikumussalam my Jaaan, ina kika shige ne haka? Naje Sunkui ance kun tashi, gashi ina ta kiran wayar taki, sai yanzu Allah ya sanya ta shiga"
Ya amsa mani cikin salon kwaikwayon murya ta. Ɗan murmushi nayi kaɗan har sau tina ya fita haka, sai kuma na shiga ce mashi.
"Sir Ina yyini"
"Ba zan amsa ba, sai kin faɗa mani kina ina ne haka?"
"Please Sir answer me First"
Na faɗa nima cikin ƴar shagwaɓa, a ƙoƙari na na in manta damuwar da nake ciki.
"Lafiya Lau Jaaan, baki ko nema na for Godsake, haka akeyi?"
Shima ya faɗa cikin barkwanci irin nashi, har ina iya jiyo sautin murmushn shi.
"Yauwa Sir, Ya labarin makaranta?"
"wayo kike son yiman ko? Ki faɗ aman kina ina? An koma makaranta ɗaukar ki ma naje yi na tarar bakwa nan"
Cikin ɗan zullumi da faɗuwar gaba nace mashi "Abuja" da mamaki yake sake tambaya ta. "Abuja kuma?"
"Cen kuka koma? Gaskiya Jaan na gaji hakanan, su Abba zasu zo ayi magana, in ɗauke ki kawai in huta da wannan jan ajin Naki"
Ƴar dariya na saki ina mai cewa "haba dai Sir, sai kace ƴar babyn roba? Wai ka ɗauke ni"
Na ƙarshe ina mai sakin dariyar da bansan nayi ba.
Idan una ne suka sauka akan Hafsat dake ta faman bi na da kallon tuhuma, fuskar nan tata tamau.
Maida hankali na nayi akan shi, jin yana cewa "To me ai you are a baby kid, kinga kaman babyn robar ce, yanzu dai ki faɗa mani inda kike insha Allah gobe zan zo mu tafi makaranta"
"Nooo Sir, na hutar da kai, yanzu ina inda ba wahalar samun mota, don haka zan taho insha Allah ko zuwa jibi haka, ko nan da kwana uku"
"To ban yarda ba"
Ya faɗa kai tsaye cikin ɗan ɗaure murya irin serious ɗin nan.
"Sorry Sir, Please akwai ƴan abubuwan da zan kammala ne Shiyasa.."
"To zanzo in taya ki, kinsan bana so ma kike wahala"
Cikin ɗan kaɗuwa na shiga bashi haƙuri akan ya bari idan mun koma zamuyi magana, tubure mani da yayi lallai fa shi sai yazo ko ya turo su abba kawai ayi a wuce wurin, Ammi ma ta matsa, tace ta ƙagara ta ganni a matsayin suruka wai.
A haka muka rabu akan cewa anjima zai sake kirana, tinda yanzu ana samu na, ai yanzu fa sai na gaji da wayar shi.
A hankali na sauke kan wayar, ina mai ɗan bin hafsat da kallon gefen ido.
"Dena satar kallo na malama, bayani zakiyi mani wanene wannan mutumen wai wani Sir Saleem ko?"
Ta faɗa cikin gyara zama, har yanzu fuskar ta a ɗaure take.
"Malamin mu ne, shi ne wanda maganar ahi take akai na"
Na faɗa mata kai tsaye nima, ba tare da damuwar komai ba, jin zata kawo mani wata magana daban kuma.
"Bamu san da zancen ba mu, kin dai san ba'a nema kan nema ko?kuma kinsan babu kyau me yasa zakiyi haka? Me yasa zaki kula wani bayan kinsan akwai wanda ke son ki tin tini?
Da mamaki na kuma kallon ta. " Wa kenan?" na tambayeta nima ina mai ɗan ɗaure fuska.
Ba shayin komai tace mani "Ya Ameen ɗinmu, na dai san duk nagartar shi wannan ɗin bai kai Yayan namu ba, kuma kin sani wallahi saidai in wulaƙanci kika shirya yi mana, duka yanzu shi wannan ɗin watan ku nawa tare dashi? Da har zaki wani ce maganar shi na akan ki? Yaushe akayi haka kuma?..... "
Katse ta nayi da cewa
" Shi yayan naku ne bai samu shiga ba, beside ma bana tunanin miskilan ci zai bar shi yin soyayya, balle har ya soni, bayan ni dake mun sani sarai irin tulun ƴan matan da ke cewa suna sonshi masu aji da kyau, bai soau ba ma balle ni? Kada ku yaudari kanku mana please"
Da mamaki Hafsat ɗin ke bina, yaushe na sauya har haka? Kodai soyayyar Wancen ta rufe mani ido, saidai duk da ba ganin shi tayi ba, Tasan har ga Allah da wuya ya iya zarta ɗan uwan nata.
Suhan yaushe kim zama haka?mu a haka muka gani muka ce muna so, kuma ba tin yanzu ba Ya Ameen ya shigo da buƙatar auren ki, tin lokacin da akace mu fidda mazajen aure, shi kuma ya ce ke yake so, wallahi kiji na rantse"
Da mamaki na ɗaga ina kallon fuskar Hafsat ɗin da take cike da gaskiya da kuma ƙwarin guiwa.
Ɗan ware idanu nayi akan ta ina mai cewa "Hafsat ya she kika zama ƴar campaign haka ne ban sani ba?"
"Suhan ba maganar Campaign, ki yadda dani, kowa ya san fa Ya Ameen na sonki har ranshi, kawai dai bayyanawa ne baya son yi, gudun ja maku matsala a wancen karon, kuma lokacin bikin namu, kowa ya shaida haka, kawai dai su Dad ne suka ce ya bar maganar zuwa wani lokaci"
Ta faɗa tana mai kamo hannuwa na duka gami da marairaice mani, ta koma kalar tausayi harda wani karyar da kai gefe.
Zare hannuwa na nayi cikin wani tashin hankalin, ina mai sauka daga bisa gadon na shiga takawa a hankali Uwa ga jikin tagar.
Hannu na sanya gami da yaye dukkanin labulen da ya sha ƙawa jikin tagar zuwa gefe, wata sanssanyar iska ce ta kaɗa ni a fuska, bansan lokacin da na shiga sauke numfashi da ajiyar zuciya ba a hankali,a hankali.
Itama Hafsat ɗin, tasowa tayi daƙyal tana mai dafa kafaɗu na a hankali ta shiga cewa "please Suhan ki amince damu, ki bamu wani yanki a cikin damar ki, insha Allah zaki faɗa da bakinki cewa babu wanda ya iya nuna soyayya sama damu please"
Na buɗe baki ne da niyyar in ce mata wani abu, sai muka jiyo hayaniya ana shigowa sashen namu, ga dukkan alamu dai an gama walimar ne, da yake yau zasu tattara su wuce Gidan Alhaji Auwalu, zuwa gobe su wuce Katsinar.
Juyawa nayi a hankali ba tare da nace mata komai ba, na shige toilet ɗin, haɗi da kunna fanfon sink na shiga watsa ma fuska ta ruwa, ko zan farfaɗo daga dogon suman mamakin da na tafi.
Itama ganin hakan, a hankali ta shiga cira ƙafa tana mai barin ɗakin nawa, zuciyar ta Ƙunshe da abubuwa, tayi ma kanta alƙawarin taimaka ma Ya Ameen ɗin wajen kafa kanshi ga Suhan ɗin, tinda ta kula shi yana yin soyayyar tashi ce take haka, ga kuma miskilanci da rashin ba soyayyar muhimmanci.
*********
Ina zaune gefen gado, har yanzu maganar Hafsat ɗin baya bar cikin zuciya ta ba, ga shi ina ta tunanin to wai zaman ne zanyi a cikin gidan ne? Me zan tsinta banda tashin hankali? Kawai gobe in wuce in komawa ta school kawai, saidai wata zuciyar na tunatas dani cewa "Hakan zaki tafi ƙibar umman ki a cikin irin wannan halin?"
"Huh" na faɗa a hankali ina mai fesar da isa daga baki na, gami da ɗan girgiza kai na a hankali ina mai cewa "Ai haka ta zaɓa, ban da yanda zanyi da ita"
Turo ƙofar akayi aka shigo, Hajiya Zainab ce gaba, sai Hafsat dake binta a baya, tana cira ƙafa daƙyar.
Tashi nayi tsaye saboda girmamawa, har saida ta zauna gefen gadon.
Ga mamaki na, kamo hannu na tayi ta zaunar dani gefen ta.
Sai kuma tayi ma Hafsat alama da ta zauna.
Tini jini na ya tsinke ya fara gudu, kar dai ace Hafsat ɗin taje ta faɗ ambata wata kalma ne akan maganar da mukayi da ita yanzu, duk da nasan ba halin ta bane ba.
Katae mani zancen zucin da nake Naji tayi wurin cewa
"Suhana mun gama komai zamu tafi gida yanzu, saidai ina son inja hankalin ki kaman yanda naja na Umman ki, kuyi ta haƙuri dai, auren nan muƙaddari ne, kuma muna fatan Alkhairi ne insha Allah, naga kina kuka ɗazu akan Abunda Kubra tayi, to ina so ki sani, insha Allah itama zata koma kan hanya mafi daidai, zata gane zuwan Maryama gidan nan alkhairi ne, kuyi ta haƙuri da duk abunda zaku gani, insha Allahu mai wucewa ne, kada ku biye mata duk Abunda zata yi Nidai ina mai daɗa ƙara jan hankalin ku akan haƙurin nan"
Tana mai gama faɗar haka ta miƙe, haɗi da cema Hafsat "Taso muje Hafsat"
Miƙewa tayi, ba tare da ta ko kalli inda nake zaune ba itama, ga dukkan alamu taji haushin abunda nayi mata ɗazu kenan, na ƙin amsa ma maganar Ya Ameen da nayi, aikau ta gaji ta sauko wallahi, ni ina ni ina bala'n hajiya Kubra? Ai da sai ta sanya mashi ta tsire mu a cikin gidan.
Haka suka fice ina kallon su, a hankali a hankali na jiyo sautin hayaniyar na raguwa, har zuwa lokacin da naji gidan ya sake ɗaukar tsit.
Zamewa nayi a bisa gadon na kwanta rigingine, hannuwa na kaf dasu nayi amfani wajen tallafe kan nawa.
Ƙarfe shidda daidai Umman tawa tayi sallama a ɗakin nawa.
Ta sake wanka tayi shar abubta, sai walwali takeyi kaman ta fara amarcin ne.
Janye idona nayi akan ta, ina mai tashi zaune haɗi da gaida ta.
Kai zaune tayi gefen gadon tana mai amsa mani gaisuwar da nayi mata, sai kuma ta buƙaci in natsu da zamuyi magana.
Hankali na duka da natsuwa ta na tattara akan ta, ina mai wasa da hannuwa na, fuska ta har yanzu jajur take saboda tunani da kukan da nasha bayan tafiyar su Hafsat, har yanzu zuciya ta ta gaza natsuwa ko amsar wannan auren da zamu iya kiran shi na ƙaddara akan mahaifiyar tawa.
Ga wani zancen kuma da yake neman kunno mani kai ya dagula mani lissafin a, Ya Ameen ɗin namiji ne har da rabi, ya zarce mace ɗiya mace ta kalle shi ta ƙi amsa tayin soyayyar tashi, ko da ya faɗa mani ban kai da gasgata ba, sai gashi ɗazu Hafsat ɗin na ƙara tabbatar mani, na tabbata ba zata taɓa yiman ƙarya ba, kenan in haka ne, Al'ameen ɗin shine na farko da ya fara bijiro da maganar auren nawa kenan? Gabaki ɗaya zuciya ta ta cunkushe, a ma'auni ɗaya nake aza Ya Ameen ɗin, da Sir Salim, saidai na gaza banbance wanda yafi nauyi daga cikin su.
Muruar Umma na tsinkaya lokaci guda tana mai cewa
"Suhan tunanin me kike yi ne?"
Da mamaki nake kallon Umman tawa, kirana da Suhan da tayi kai tsaye yau, hakan ce ta sanya ni maida hankali na akan ta.
"Nasan har yanzu ba wai kin amince da aure na bane, kuma nasan zaki dinga yi mani wani kallo na daban, wala alla kema ki ambata ni da mai kwaɗayi ko mai son abun duniya, ko wadda ta shigo gidan Alhaji Mustapha da wata manufa ne, Amman ina so ki sani duk ba haka bane, zamana a gidan nan yana daga cikin ɓari na ƙaddara ta da kuma ke tin bayan aurena na mahaifin naki, da ƙaddarar da ta sanya ya rasu, da ƙaddarar da ta sanya nabar gidan namu da kuma ƙaddarar da ta sanya na haife ki a ƙauye, da ƙaddarar da ta sanya ni zama a gidan nan a karo na farko a matsayin ƴar aiki, duk kuwa da ba aikin ne takamaimai zamana a wancen lokacin ba, sai gashi ƙaddarar ta juye ta zama wata aba daban a yanzu. Zan ja hankalin ki ne akan haƙuri, ki bani haɗin kai, inaso ki sani nan ba da jimawa ba, zaki san ko ke wacece, zaki san ko ji wacece, Amman ina so ki sanya zakiyi zama ne anan gidan, zaman haƙuri da dukkanin Abunda zai je ya dawo, ko me kika gani ki kauda idanun ki, ke ba wadda ta cencenci wulaƙanci bace ga dukkan wani mutum dake rayuwa a ƙarƙashin rufin gidan nan bace. To saidai akwai wani abu ɗaya. Muhammad Al'ameen, kada ki kuskura in sake ganin ki dashi tsaye ko kuna magana, wannan alaƙar na datse ta, indai ba kina so wani sabon abu ya kuma bijirowa bane nan gaba, kwanaki mahaifin shi sunzo sun same ni akan maganar auren ki dashi, to saidai ban bada dama ba, saboda wasu dalilai na, inaso ki sani, mahaifiyar shi ba zata taɓa lamuncewa ba, kina da mai sonki da gaskiya shine Saleem, na bada dama ya turo mahaifn shi a koda yaushe ne, Amman maganar Al'ameen ban yarda da ita ba, bana kuma jin zan yarda da ita koda anan gaba ne kuwa."
Cikin matsanancin furgici na ɗago ina mai kallon Umman tawa, to saidai ba bakin yi mata magana a yanzu, yanda nake jin zuciya ta na halbawa, ga kuma wani irin abu dake taso mani cen ƙarƙashin zuciyar tawa.
Ina ji ina kallo ta miƙe, har ta fice ɗakin ban iya ce mata komai ba, bana da wannan ƙwarin guiwar, bana da wannan zarafin.
Hawaye na sulalowa a saman fuskn tawa, da bansan ko na menene ba, Nidai nasan bana jin komai dangane da Ya Ameen ɗin, to saidai kukan ne nakeyi? Gashi umman t a mani albishirin zanin ko ni ɗin wacece, kuma ta faɗa man ni ba wulaƙantatta baceba, to mi ya sanya ni kuka? Minene na damuwar kaina?
Tattara dukkanin kayan makaranta ta na shiga yi, ba zan zauna a gidan ba ma, balle har in shiga wani hali na ɓacin rai, saidai wani ɓangaren na zuciya ta, Ya Ameen shine mutumin da yayi mani kaka gida a cikin ilahirin zuciyar ba tare da na san dalili ba. Ya Allah ka dafa mani a al'amari na, ya Allah ka dubi maraici na, ya Allah ka tallafa mani a kowanne yanayi.
*************
Kaman an masu mutuwa, gabaki ɗaya ilahirin hankalin su baya cikin jikin nasu, Mom kuwa kaman zata fashe, sai faman jinjiga ƙafa da takeyi tana daga zaune, Su Hajiya Sa'a tuni suka fice suka bar gidan, ba yanda ba suyi ba da ita, akan ta saurare su, amman fir taƙi ko kula su, sai kai komo takeyi, da ta gaji ne ta koma ta zauna.
Gashi tin ɗazu taje kiran Al'ameen ɗin yaƙi ɗaga wayar, me yake nufi ne? Saudat ta aika akan taje ta gano mata ko yana ɗaki, zuwa tayi ta tadda baya lafiya, komawa tayi ta sanar da Mom ɗin tasu, Amman saboda bala'i da yanda take ganin hadda hannun shi akan wannan cin amanar da akayi mata ya hana ta ko taje ta gano shi, jira ma takeyi ya samu sauƙi ta huce haushn ta akan shi. Shi yanzu har ya zaɓi ƴan aiki akan ta? Ashe duk ƙaunar da suke ma juna ta tashi a banza, ya fifita ƴar aiki da ɗiyar ta akan ita da ta zuƙunna ta haife shi..
*****
Ƙarfe huɗu Ya Ameen ɗin ya farka, da salati ɗauke a bakin shi, sai kuma ya ɗaga hannun shi da ƙarin ruwan ya ƙare Bilal ya cire mashi Amman bai zare canula ɗin ba, bisa kanshi ya ɗora shi yana mai dafe kanshi haɗi da ƙoƙarin tashi zaune.
Bilal dake zaune gefe yana latsa system ne ya taimaka mashi ya zauna, yaji daɗin ganin jikin abokin nashi da ƙarfi ba kaman ɗazu ba.
"Ina Mom?"
Abunda ya fara faɗa kenan.
"Tana part ɗinta" Bilal ɗin ya bashi ansa.
"Zanje in ganta Bilal"
"Nooo Friend, yanzu tana cikin wani hali, ka bari sai ta huce sannan, ba zaka taɓa fita ba a wurin ta, zata ga kaman da kai aka haɗa baki, masalan ma da baka sanar da ita ba"
"Bilal bana jin daɗin Abunda takeyi a cikin taron mutane....."
"Dr. Yace ka daina tunanin komai friend, zaka jawo ma kanka wata matsalar ta daban, ka bari sai zuwa dare muje mu same ta"
Komawa yayi ya kwanta ba tare da ya kuma cewa komai ba. Saii kuma ya tashi a daddafe ya shige toilet ya ɗauro alwala duba da yayi lokacin an kammala sallah.
Bayan ya kammala ne ya koma ya zauna gefen gadon, yaji sauƙi sosai, masalan ma wannan sallar da ya ƙara yi.
Tashi yayi gami da cire kayan nashi ya sanya bathroob ya shige toilet haɗi da sake yo wanka.
Bilal dai bai ce mashi komai ba, sai a aikin shi da ya cigaba da yi, wanda wata kwangila ce Federal Goverment ta basu aproval akan ta, shine suke ta faman aiki a kanta.
Shiryawa yayi cikin ƙananan kaya, samfurin ƙasar Holand, kayan sun amshe shi matuƙa, sai agogo da turare da ya fesa.
Fuskar nan tashi fayau, kaman wanda ya shekara yana ciwo, baƙin sajen dake fuskar shi ya sake fitowa raɗau akan fuskar, saidai babu wata walwala ko annuri a jikin ta, kaman wanda aka sanar dashi mutuwar kowa nashi.
Falo ya koma ya zauna, haɗi da kunna dstv ɗin dake falon.
Duk da kallon yakeyi , amma Sam hankalin shi ba'a tattare dashi yake ba, so yake yayi tunanin abubuwa da dama.
"Suahana, yanzu a wanne hali take? Umma, itama a wanne hali take? Mom......
Ɗan tsoki yaja yana mai tashi ya shiga zagayen falon, hannayen shi goye a bayan shi.
Da gudu yaji an shigo haɗi da ruƙunƙune shi ta baya.
Cikin hanzari ya juya domin ganin ko wacece, saboda ya san duk duniya yarinya ɗaya ce keyi mashi hakan.
Ilai kuwa ita ce. "Afnan! Yaushe kuka zo? Ina Aunty Feena?"
"Ɗan ja kaɗan tayi tana mai ƙare mashi kallo
" Yaya are u sick? Naji jikinka da ɗan zafi, me ya same ka? Ta faɗa tana mai bin dukkanin jikin nashi da kallo, sai kuma ta ɗora idanun ta akan fuskar shi.
Kamk hannuwan ta yayi dukkanin su, yana mai ja ta zuwa bisa Sofa.
Zaunar da ita yayi yana mai zama shima.
"Afnan am fine, yaushe kuka zo?"
"Yanzun nan yaya, ko cikin gidan ban shiga ba, Aunty Feena ta wuce ciki, na ƙagara in ganka ne"
"Afnan yanzu ba lokacin hutu bane, ya akai na ganku kuma?"
"Yaya Dad ne yace muzo yau, tin jiya ya faɗa mana, so tin jiya ma da daddare muka taso ai"
Da mamaki yake binta da kallo.
"Me ya faɗa maku? Yace anyi wani abu ne?"
"Kai yaya Wannan duk tambayar ta mecece? To nidai banji Aunty Feena tace komai ba, kawai dai tace in shirya zamuje gida ne cikin gaggawa"
ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke yana mai cewa
"Afnan Go inside am coming now insha Allah"
"To Yaya am waiting for u"
Ta faɗa tana mai Miƙewa ta fice.
Ƙarfe takwas Alhaji Mustapha yayi parking a harabar gidan nashi.
Mai gadi da dukkanin sauran ma'aikatan maza suka taso suna yi mashi barka da zuwa.
Suma mamakin shi suke yi, duk da sunsan tsaye yake a gidan nashi, to saidai ba suyi tunanin zai iya ƙara wani auren ba, duk da har yanzu basu kai ga sanin wacece amaryar ba, domin ba'a basu damar hakan ba, tin bayan dai da suka gama jera komai aka sallamesu har matan ƴan aikin kuwa.
Kai tsaye sashen nashi ya shiga, bayan ya ɗaga waya ya kira Al'ameen.
Saida suka jira shi ya gama wankan, sannan ya umurce su da su ɗungumo har sashen Hajiya Kubran kuwa, harda Bilal.
Gaban su dai faɗuwa yake yi yayin da suka bishi a baya, shi kau da yake namiji ne tsayayye ba tare da shayin komai ba ya durfafi sashen da uwargidan nashi yake mallakin ta cikin takun shi irin na tsayayyn namiji a faɗin duniyar.....
A falon suka tadda su jigum jigum, har Feena da Afnan ɗin da uwar ta gama karanta masu komai, duk da hankalin su ba wani tashi yayi ba, a ganin su ai hakan ba wai abun tada hankali bane, ko ba komai Mom ɗin ta samu abokiyar zama wadda zata na kula da komai idan bata nan.
To saidai uwa da ƴaƴa sai Allah, ganin yanda Mom ɗin tasu ta tada hankalin ta, da bala'n da take ta faman yi tin ɗazu ya sanya jikin su sanyi.
Bama kaman Feenar da duk ta fisu hankali da sanin komai, ko ba komai ta mallaki hankalin kanta, kuma Tasan halin Mom ɗin tata, tana gudun Abunda zai je ya dawo masalan akan ƙanin nata mai bi mata da ta fuskanci shima Mom ɗin tasu cike take dashi.
Waje ya samu ya zauna, duk suka shiga gaida shi, amsa ma kowa yayi cikin fara'a da sakin fuska.
Ita kuwa Afnan wajen da yaje zaune ta ƙara sa3ta zauna haɗi da ɗora kanta bisa jikin shi, tana mai ɗan rungumo shi take faɗin
"I missed u Dad"
"I missed u auta"
Ya faɗa shima cikin jin daɗin zuwa kiran da yayi masu.
Nasreem ce ta ɗan gangaro da ɗan Gudu irin nata, sai ya sanya hannu ya cafe ta, yana mai ɗaga ta sama yake mata wasa
"Afnan je ki kira mani Umman Suhan"
Ya faɗa ba tare da ko ya kalli ɓangaren da Hajiya Kubran take zaune ba tana ta zuba isa.
"To Dad" ta faɗa tana mai ficewa.
Tin da su Al'ameen ɗin suka shiga falon take aika mashi da wani irin kallo.
Nan fa hankalin shi ya ƙara tashi, Amman da yake namiji ne, sai ya aro dakiya, juriya da natsuwa ya yafa ma kanshi.
Bai ma ko sake kallon sashen da take ba, saboda guje ma irin kallon da take binshi dashi.
Shima Bilal yana lura da ita, Amman bai ce mata ƙala ba, har su Afnan ɗin suka shigo tana riƙe da hannun Suhan ɗin kanta a ƙasa.
Shigowar Umman ce ta ja hankalin kowa dake falon ya maida hankin shi kanta.
Sanye taje da atamfa, anyi mata ɗinkin riga da zani. Sai hinabi a kanta, fuskar ba kwalliya ko ɗis, sai zallar kyau da Allah ya mallaka mata.
Cikin taku irin na kamala take tahowa har zuwa bisa wata kujera mai zaman mutum ɗaya da tafin kusa da ita.
Zama tayi bismillan ɗauke a bakin ta, hakan ne ya ƙara ƙular da hajiya Kubran, ya faranta ran Alhaji Mustapha da Bilal da abokin nashi.
A hankali ta shiga gaida Alhaji Mustaphan cikin girmamawa, sannan ta maida akalar gaisuwar tata ga uwargidan tata.
Fuskar nan tata babu wani abu dake nuni da alamun tsorata ko fargaba ko ɗin a cikin zuciyar Umman.
Duk da Hajiya a kubran bata amsa ba, sai a wani wulaƙantacccen kallo da ta bita, sai bai da wata ba, ta juya wurin da Feena ɗin take zaune, haɗi da gaida ta ba tare da fargabr komai ba, haɗi da yi mata sannu da zuwa.
Sai abun ya ba Feena kunya haɗi da mamaki.
Ya matar da ta girme ta nesa ba kusa ba, gashi kuma tana matsayin matar mahaifin ta zata gaida ta? Lallai ba mai zafi baceba, ba irin wadda Mom ɗin tata ke faɗi bace, bata fahimce ta bane, amman ko a yanayi da yanda fuskar ta ta nuna ita ɗin ba mai zafi bace.
Kowa dake falon ya gaida Umman tawa, banda Saudat da Nihal suma da suke bin mu da wani irin kallo na tsana.
Nikau da nake zaune cen ƙasa gefen Afnan ta kama hannuna ta matse taƙi saki, nima jikina da hijabi, fuskata tayi luhu luhu, Allah ya sanya lokacin da afnan ɗin ta shiga kirana Salla na gama ba kukanba, saida tayi ihun murnar ta mai isar ta, na jin daɗin gani na, sannan ta faɗa mani saƙon Dad ɗin nasu.
Kallon shi gabaki ɗaya da hankalin shi yana kanta, yana kula da yanayin ta, watau tasha kuka kenan bayan wanda yaga ta tanayi ɗazu.
Saida Bilal ya zungurobshi sannan ya iya janye idanun nashi a kanta, wanda har Hajiya Kubran ta lura da Kallon da yake yi ma a Suhan ɗin.
Gyaran Murya Dad ɗin yayi, yana mai muskutawa ya fara buɗe taro da addu'a
Sannan ya fara jawabi kamar haka.
"Na tara ku ne anan ba don komai ba, sai don in gabatar maku da abokiyar zaman mahaifiyar taku, daga yanzu wannan itace a matsayin abokiyar zaman Mahaifiyar taku, ina fatan zaku yi mani biyayya wajen bata girman ta, da kauce ma duk wani abu da zai kawo saɓani. Ku sani yanzu ba matsayin ta na mai aiki take ba, matsayin matar mahaifin ku take,kaman mahaifiya take a wurin ku, ku girmama ta kaman yanda zakuyi ma mahaifiyar ku nan da take zaune, sannan ki darajta ta, ga Suhan nan, ku ɗauke ta matsayin ƴar uwa, bana so inga wani banbanci a tsakanin ku, masalan ma ku Saudat Da Nihal, ina fatan zaku kiyaye.......
*"Alhaji dakata"*
Hajiya Kubran ta faɗa cikin kashin murya, tana mai zaburowa daga inda take zaune bisa Sofar.
*"Ni ba abokiyar zaman ta bace, kuma ita ba kaman mahaifiyar ya rana bace ba, ni a wuri na maci amana ce, kuma ina sonka sani daga yanzu har yaumuttanadi ba zan taɓa amsar ta ba a matsayin kishiya, san amshe ta ne a matsayin aiki wadda taje zaune a gudana cikin rigar alfarma ta, tana cin dukiya ta da nufin ta kare kanta daga Raɗaɗin talaucin da take fama dashi tin shekara da shekaru, muddin tana zaune a ƙarƙashin rufin gidan nan nawa, ba zata taɓa amsa sunan matar guda ba, saidai ƴar aikin gida, tinda wannan auren babu Abunda yake cikin shi sai cin amana da mugunta kawai*
Ba Alhaji Mustapha ba, hatta Afnan da Feena, Bilal da uwa uba Al'ameen da suke zaune a falon saida maganar tata ta Dakar masu zuciya.
Cikin tsananin furgici Al'ameen ɗin ya ɗago kai yana mai ƙure Mom ɗin tashi da idanun ta ya rufe ga kallon gaskiya yake yi.
Shi kau Bilal saidai sauke kanshi ƙasa yayi yana mai ɗan girgiza kai, yayin da Feenar take kallon Mom ɗin nata da wani irin kallo kaman ta nutse ƙasa.
Ni kau tare da Afnan a lokaci guda muka kai kallon namu a bisa fuskar Umman tawa, domin ganin yanda ta karɓi maganar Hajiya Kubran.
Ga ɗin bin mamakin mu, murmushi ne kwance bisa fuskar Umman tawa, har kana iya hango fararen haƙoran ta, a lokaci guda na janye idanuna na maida su kan su Saudat ɗin da farin ciki fal a zuciyar su kaman zasu taka kan jariri....
_Ku godewa Allah fa, nima na fara koyon ƙyuyar typing, tinda kuma kun iya ƙyuyar comment. Sai kuma sati na sama_
0 comments:
Post a Comment