*Aslm Alkm.Fans da fatan duk kuna cikin ƙoshin lafiya. Sabili da yawan ƙorafe-ƙorafe da nake samu daga gareku, da yawan roƙo na, da masu kirana a waya, da masu mani Dm da masu bina Pc akan in taimaka inyi typing, na yanke shawarar baku koda kaɗan ne ba yawa, ba don na kammala uziri na ba, ba don ayyuka na sun koma normal ba, sai don in faranta maku rai, haƙiƙa har kullum masoyi yafi maƙiyi, Rubutun nan dan ku nakeyi, domin jin daɗin ku ne, domin idan babu ku, tabbas fa babu mu, Amman sai wasu daga cikin readers su kasa gane haka, su sun ɗauka idan kace zaka yi rubutu baka da aikin yi ne (Jobless). To inaso ku sani ba haka abun yake ba, kawai dai sa kai ne wanda yafi bauta ciwo. Masu yawan damuna akan nayi typing wannan Page ɗin naku ne har abada, kuyi yanda kuke so dashi. Daga ƙarshe ina mai roƙa ma sister ta lafiya a wurin Allah, ina so kuma ku taya ni da addu'a, duk da nai nasan kuna yi, inaso ku ƙara sosai my fans. Allah ya barmu tare Abadan da'iman. Ina sonku tsakani da Allah. Ngd*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Babu wanda ya katse ta har ta kai aya, haka babu wanda ya tanka har kawo yanzu da falon ya ɗauki shiru.
"Kubra ke ba zaki cenza ba ko? A gaban yara kike faɗar irin waɗannan kalaman? Maryam dai matata ce, itama auren ta nayi kaman yanda na aure ki, kuma ba ƴar aiki bace ma a yanzu kaman yanda kika faɗa, Amman wannan ba irin maganar da zamuyi bace a gaban yara, ki kiyaye hakan ko don gaba"
Muka tsinkayi muryar Alhj Mustaphan yana mai maida ma Hajiya Kubra maganar tata.
Ƙara duƙar da kan namu mukayi ƙasa, yayin da su Saudat jin haushi ji suke kaman su rufe Dad ɗin nasu da duka, zunɓura baki suka hau yi sun murguɗe murguɗen baki.
Umma ta dai har ila hazar yanzu bata ce komai ba, sai dai ɗan murmushi da take ta faman yi, babu ko alamun damuwa akan fuskar ta.
Ita kanta tasan abunda tayi ba daidai bane, ta sani abunda tayi don Hajiya Kubra ta kira shi cin amana ba laifi bane, kowa ma zai iya kiran shi hakan, muddin yaji yanda abun yake. To saidai bata jin wannan dalilin ya isa daƙile nata dalilin da take dashi cikin zuciyar ta.
Alhj Mustaphan yayi maganganu masu daɗi da fa'ida, ya kuma ja hankalin Haj kubran da yaran nata akan su haɗa kansu, baya so su kawo mashi wani tashin hankali a cikin gida, duk wanda ya samu da hakan, zai mugun saɓa mashi.
Sannan ya umurce mu da mu tashi kowa ya koma part ɗin shi, yayin da ya buƙaci Hajiya Kubra da Umman akan su su zauna yana da magana dasu.
Sannan yace Ya Ameen ɗin kada yayi bacci yana son ya ganshi idan ya kammala da iyayen nashi.
Haka muka tashi da niyyar ficewa.
"Suhan yaushe ne zaki koma makaranta?"
Muryar Alhaji Mustaphan ce ta doki dodon kunne na daidai lokacin da nake ta faman sauri domin barin falon, da nake ji na kaman a ɗaɗɗaure, yawan aika mani da harara da Hajiya Kubran takeyi.
"Gobe idan Allah ya kaimu"
Na faɗa kaina a ƙasa, bayan na dakata daga tafiyar da nakeyi,ina mai ɗan waiwayawa na kalle shi.
"To Allah ya kaimu"
Ya faɗa yana mai nuna alamun da in tafi. Cikin matuƙar sakewa kaman kaman yanda yake yi ma yaran nashi.
Da hannu ya yafuto ya Ameen da bai kai ga miƙewa ba shi.
Inda yake ya isa, gami da ɗan russunawa domin sauraren Dad ɗin nashi.
"Kuje ka kai ta tayo shopping ɗin komawa makaranta, zuwa gobe ka maida ta makarantar da kanka, bana so a haɗa ta da driver"
Ya faɗa ta yanda ba wanda zai iya jin me ya faɗa, gudun wata fitinar ta daban.
A hankali ya miƙe yana mai faɗin "to Dad."
Da hannu yayi ma Bilal alamun da suje.
Shima a hankali ya miƙe yana mai yima su Dad ɗin sai da safe.
"Bilal zamu je mu kai yarinyar cen shopping inji Dad"
Ya Ameen ɗin ya faɗa daidai lokacin da suke barin sashn mom ɗin tashi.
"Kai bros, kuje kawai wallahi bacci nake ji, ina so in ƙara sa gida ne, Kaga Ummi ba lafiyar kirki"
Ya faɗa cikin son kauce ma rakiyar, yayi hakan ne saboda kada ya shiga haƙƙin masoyan.
"Muje sai mu sauke ka"
"To ai shikenan, ina jiran ku a mota", ya faɗa yana mai amsar key ɗin motar a hannun Ya Ameen ɗin.
Yayin da Ya Ameen ɗin ya juya kai tsaye ya nufi sashen su Suhan ɗin.
A falo ya tadda ni, tsaye nake na juya baya, hijab ɗita na a hannu na da na riga na fidda tin shiga ta sashen.
Zuciya ta cunkushe, bana so Haj Kubran ta ƙara ci ma Ummata zarafi a kalaman ta, in da son samu na ne, ƙafata ƙafar Umman muyi dawowar mu a tare, domin nasan dukkan Abunda Alhaji Mustaphan zai faɗa ma Hajiya Kubra ba wai ganewa zata yi ba.
Ya ɗan jima tsaye daga baya na yana ƙare mani kallo. Hannayn shi duka soke cikin aljihun wandon nashi.
A hankali ya shiga takawa yana nufar inda nake tsaye.
Jin takun tafiya daga bayana, ba ƙaramin tashin hankali da tsoro na shiga ba.
A firgice na juyo da niyar kwarara ihu, domin Nidai nasan babu kowa a sashen namu, gashi naji takun tafiya, kuma yanzu na baro ummata Sashen Hajiya Kubra.
Cikin azama ya sanya hannu gami da toshe mani baki na duka, yana mai ɗan tallafo ni zuwa jikin sa kaɗan, ganin kaman nayi baya zan faɗi.
"Matsoraci ya"
Abunda ya faɗa kenan, yana mai bin duka fuska ta, da idanuna da wani irin kallo, da na gaza fassara ko na menene.
Ajiyar zuciya na sauke, ina mai ɗan matsawa baya kaɗan daga jikin nashi.
Sai kuma na koma bisa kujera na zauna, ina mai dafe kaina da har ya fara sa rawa, tsabar tsorata.
Da kallo yake bina har yanzu, ganin bance komai ba, sai kuma ya fara takawa zuwa fita daga falon
"Ki shirya ki same ni mota yanzu, zan kaiki kiyi siyayyar makaranta"
Bai jira cewa ta ba, ya idasa ficewa daga falon.
Nima da kallo na bishi, oooh Ya Ameen, mai hali baya barin halin shi, komai nashi da yake aiwatar wa, cikin miskilanci yake yi kaman ma baya son yi, a hankali na miƙe ina mai zura hijab ɗita zuwa cikin ɗakin domin na duba fuska ta.
A mota ya samu Bilal ɗin yana ta faman jiran shi.
"Friend ya dai? Hankalin ka yayi gida wajen ummi ko?" ya faɗa cikin ƴar zaulaya da ya kan yi idan ya so, yana mai zama cikin motar, ƙafar shi ɗaya a waje bai kullo ƙofar ba.
"wallahi friend tana jin jiki ne, ni ina ma tunani ko gida zan maida ta, domin a kula da ita sosai, nauyi take ji sosai yanzu na jikin ta"
"Gaskiya kam Friend, idan kana ganin ba matsala, You can allow her to go, Kaga kai ba isasshen time ɗin zama gidan ke gareka ba"
"ehhh kuma....."
Ƙarar buɗe motar ne ya sanya su juyawa gabaki ɗaya.
Ƙamshin turarn ta ne ya fara yi masu sallama, kafin kyakkyawr ƴar madaidaiciyar zagayayyar fuskar ta ta bayyana cikin motar.
A tare Bilal da Ya Ameen suka kalli juna, sai kuma ya Ameen ya janye tashi yana mai gyara zaman shi, gami da maida ƙafar shi cikin motar ya rufo ƙofar motar.
Nima rufowa nayi ina mai gaida ya Bilal ɗin, saboda lokacin da muka haɗu sashn Hajiya Kubra bamu samu damar gaisawa ba..
Amsawa yayi cikin sakin fuska, yana mai ɗan zaulaya ta da cewa na ɓoye.
Ɗan murmushi kawai nayi mashi, ina mai wasa da yatsun hannuwa na.
Sai kuma motar ta ɗauki shiru, na tsawon wani lokaci har muka ƙara sa bakin gate ɗin gidan na Bilal.
Ya Ameen na ƙoƙarin danna horn, mai gadi yazo ya buɗe ne Bilal ɗin ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Kaga malam ajiye ni nan, ya isa, kada kuyi dare fa"
Dakatawa yayi ba tare da yace komai ba, saida Bilal ɗin ya fita ya zagaya ta ɓangaren shi, sannan sukayi musabaha tare da yin sallama.
Nidai kallon su kawai nakeyi, Amman ƙaunar junan sun na matuƙar burgeni, duk duniya banga wanda Ya Ameen ke sake wa da sakin jiji dashi ba kaman Ya Bilal ɗin.
Haɗuwar jini, ƙauna, abota daga Allah.
Har ya shige gidan muna iya hango shi, rufo ƙofar gidan ce tayi daidai da sauke ajiyar zuciyar Ya Ameen ɗin. Sai kuma Naji yace
"Dawo gaba"
Da ɗan mamaki nake kallon shi, sai kuma nace "I am comfortable here"
"Am not asking you dear, i am jst commanding you, ko kin manta ni ba driver bane?"
Ɗan murmushi na sauke, yau ya Ameen ne da yin faɗa har haka? Ji yanda yaje magana kaman ana karanta mashi...
Sauke kaina ƙasa nayi, bana da niyyar ma ko motsawa.
Ji nayi ya kawai kashe motar. Sai kuma ya jawo wayar shi haɗo da kunna data, yana mai ɗan kwantar da kujerar sit ɗinshi ya cigaba da latse latsen shi.
A hankali na ƙure shi da idanuna ta bayan motar, hasken wayar tashi ba mai yawa bane, amman duk d a haka zan iya hango farar fatar fuskar tashi, da take cike da siririn sajen da ya kwata luf akan fuskar, gashin idanun shi Zara Zara, sunyi ma kyawawan idanun shi, masu kama da yana jin bacci kyau, girar nan tashi kaman an zizara mata kwalli, ta tsaru iya tsaruwa.
A hankali na janye idanuna, ina mai sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, ganin ya kashe hasken wayar yana mai lumshe idanun nashi tare da ɗora Zara zaran yatsun hannun shi bisa fuskar shi.
Mu biyu haka acikin mota mai duhu? Ga Ƙamshin turaren shi, da ya haɗe da Ƙamshin humra ta da sanyin cikin motar ya saukar mani da wata irin kasala.
A hankali na ɓalle murfin motar, ina mai ficewa daga cikin motar naja na tsaya, ina mai jingina baya na da ƙofar motar.
Duk motsin ta yana kula dashi, ganin ta fice ne ya sanya shi tashi zaune, yana mai sakin ɗan murmushi na gefen baki.
Wato ita taurin kai zata nuna mashi, ko kuma jan aji ne irin na mata? Tinda ya furta mata yana sonta, ya kula da wani shasshare shi da takeyi da ba zai iya cewa ga ko na menene ba.
Shima ɓalle murfin motar yayi ya fito.
Cikin takun shi mai ƙara kada mani gaba ya iso ta inda nake tsaye.
Sai kuma ya ja ya tsaya, hannayen shi zube cikin aljihun wandon nashi, idanun shi dukan su bisa fuskar tawa da hasken farin wata ya haske.
Sai kuma ya zaro hannun yana mai duba agogon dake ɗaure bisa wutsiyar hannun nashi.
Baice mani komai ba, sai naga ya sanya hannu ya buɗe sit ɗin gaban, yana mai nuna mani da in shiga.
Sake ɗauke kai nayi, nima bansan menene haka ya shiga kaina ba yau, Amman jina nakeyi a sama, kaman wata sarauniya mai mulki.
Ban aune ba naji ya kamo ni duka na, yana mai saka ni cikin motar gabaki ɗaya na, sai kuma ya rufe yana mai danna key.
Zagayawa yayi shima ya shiga motar, ba tare da ya ko kula ni ba, ya fizgi motar kaman zai tashi sama, har yanzu fuskar shi bazaka taɓa cewa ya taɓa dariya ba.
Har muka ƙarasa daidai super market ɗin ba wanda yace da kowa komai.
Ɓalle murfin motar yayi yana mai ficewa kai tsaye, nima ban da wani option illa na fitowr.
Gaba yayi ina biye dashi a baya.
Na ɓata mashi rai na sani, Amman hakan ba shi ke nuna nice mai laifin ba.
Tsabar girma da jin kai nashi, shine abu na farko dake ɗawainiya da Ya Ameen ɗin.
Wato shi yana da kuɗi, yana da kyau, yana jin cewa dole abi umurnin shi ko? Ga miskilanci yana fama dashi.
A haka har muka ƙarasa ciki.
Nuni yayi mani da ɗan ƙeƙen da ake zuba kaya. Alamun in ɗauka in ɗebo kayan.
Kenan dai ba zaiyi mani magana ba yake nufi?
Ɗan murmushi nayi ina mai wucewa kai tsaye ga zaɓen kayan.
Yayin da cikin girmamawa aka sanya aka ajiye mashi kujera ya zauna daga gefen accounter ɗin.
To nima dai ba komai na ɗina ba, kasancewr abincin ma ba damuna yayi ba, kuma ni ban iya almubazzaranci ba, nasan idan ummata taga siyayya da yawa ma, faɗa zata yi.
Haka na turo keken wani gulu gulu, har zuwa wajen accounter ɗin.
Da kallo ya shiga bina, ganin na taho ina turo keke duk da kayan basa da yawa, amman kaman zan kife.
Miƙewa yayi yana mai bina da kallon tuhuma.
Sai kuma ya ƙara gimtse fuska tamau.
"Wuce mu koma"
Ya faɗa cikin wata irin murya, da gani har yanzu yana cike dani sosai.
Ba musu na sake juyawa, ina mai wucewa.
Hannuwan shi naji kwatsam a bisa nawa, yana mai kama handle ɗin keken.
A hankali na zare nawa ina mai ɗan ja da baya.
Me ke damun shi ne wai? Ɗabi'ar turawa na neman yin tasiri a Al'ada da addinin nashi.
Gashi dai mutum mai addini, ga yawan ibada, Amman bai ɗauki haɗa jiki dani ba a matsayin komai.
Ji na da yake yi kaman Afnan, ai ni ba Afnan ɗin baceba. Kenan ma yana ganin don Mahaifiyata ta auri mahaifin shi hakan ke bashi lasisin haɗa jiki dani a koda yaushe kenan?
Ban ankare da har yayi nisa ba, sai hango shi nayi cen nesa dani.
Yana ta ɗaukar abubuwan amfani cikin salon shi mai ban sha'awa
Haka na cigaba da bin shi, har yanzu bai ko juyo ya kalli inda nake ba.
Ba ra'ayi na ko zaɓi na yake bi ba, saidai na kula dukkan abubuwan da yake ɗauka masu matuƙar amfani ne.
Har ya gama ya cika keken taf, har wasu suna zubo wa.
Haka na sake bin shi har teburin accounter.
ATM card ɗinshi ya miƙa masu, zasu, zasu cura ta Pos
Sun matuƙar yi mashi discount, saboda Alfarmar dake gareshi a garin.
Sannan aka zuba mana su sit ɗin baya.
Har yanzu bai ko ceman ƙala ba, ya shiga motar.
An cika sit ɗin baya, ba damar jan magana. Hakan ce ta sanya ni buɗe sit ɗin gaban na zauna, nima ina mai basarwa tare da shassharewa.
Zama a kusa dashi ko a tare dashi, ba ƙaramin abu yake jaza man ba.
Kuma ni ba wai zan iya cewa ga abunda nake ji ba.
Haka muka shiga tafiya zuwa gidan babu mai kallon wani.
Saidai lokaci zuwa lokaci na kan muskuta in gyara zama, daga baya ma sai na jingina kaina jikin makarin kujera ina mai ɗan lumshe idanu.
Kaman ance in buɗe idanu na, idanun nashi na bisa fuskar tawa tar dasu, bai ji kunya ba, kaman yanda bai ɗaga idanun nashi ba.
Sai nice na janye fuska ta, ina mai maida ta bisa titi ganin yanda yake tafiya a hankali kaman wanda yaba so mu isa gidan da wuri.
Mai gadi yayi ma horn yaje ya buɗe mana, har muka sulala cikin gidan ba wanda ya tanka ma ɗan uwan shi.
Fitowa mukayi mu duka.
Ganin ya zagayo ta inda nake ne ya sanya nayi tunanin ko kayan zai fiddo mani ne.
Miƙo mani makullan motar naga yayi, sannan yace
"Idan kin gama kwashe kayan ki rufe mani motar, ki shirya da wuri da safe Dad yace in kaiki kamarantar da kaina. So kun katse mani ayyuka na, bana so kiyi keeping ɗina delay ok?"
Amsa nayi ina mai cewa "To yaya"
Sai kuma Kunyar abunda nayi mashi ta shiga kama ni.
Mutum ne mai ƙoƙarin kyautata ma duk wani wanda Allah ya haɗa shi zama dashi.
Da kallo na bishi, ganin ya juya ya nufi part ɗin Dad ɗin nashi, ya bar mani makullan motar a hannu na
Ya Ameen mutum ne mai matuƙar sauƙin hali.
Miskili ne, Amman yana jin haushn kiyi mashi miskilanci.
Da kallo na kuma raka shi.
Har gobe na rasa abunda zance yana burgeni tattare da Ya Ameen ɗin, saidai zan iya cewa shine mutumen guda da ko bacci nakeyi tunanin shi baya saki na.
Har ya shige part ɗin idanu na suna a kanshi, a hankali na saki ajiyar zuciya ina mai fara sauko da kayan zuwa ƙasa sannan na kulle motar.
Cikin part ɗin namu na nufa, sai kuma naja na tsaya ƙirjina yana dukan uku uku, ko a wanne hali zanje in tadda Umman tawa? Ko ya sukayi da Alhaji Mustapha da Hajiya Kubran?
A kasalance na ɗaga ƙafa na shiga takawa a hankali har zuwa cikin part ɗin namu......
_Kuyi manage, wannan ma squizing nayi na maku typing_
*Muna tare My Fans*
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~47~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
A falon na tadda Umman tawa zaune, kayan kallo a kunne suke, amman Sam hankalin ta baya kansu, har na ƙara sa inda take zaune na shiga ajiye kayan.
Bance mata komai ba, saida na juya na gama shigo da kayan, sannan na zauna kusa da ita ina mai kamo hannuwan ta nace
"Umma lafiya kuwa?"
Sai a lokacin ne ta ɗan firgita ta dawo hayyacin ta. "Lafiya ƙlau mamana, kun dawo?". Ta faɗa cikin son kauda wani zargin daga zuciya ta.
Ɗaga mata kai nayi, ina mai cewa "eh Umma, ga kayan da Ya Ameen ya siyo mani nan"
Ɗan kallon kayan tayi kaɗan, sai kuma tace "baki dai takura mashi ba ko?"
"a'a Umma, shine ma ya zaɓo da kanshi, wai waɗanda na zaɓa sunyi kaɗan"
To Mamana aikuwa an gode, je ki kaisu ɗaki kizo zamuyi magana dake.
Sai da gabana ya faɗi jin Abunda ta faɗa, hakanan na daure na miƙe, gami da kwasar kayan na nufi ɗaki.
Sai da na kwashe su duka, sannan na koma inda taje na zauna ƙasa ina mai cewa "gani Ummana"
"Taso ki hau kujera, banson kina zama ƙasa mamana, nan sashen Umman ki ne"
Haka ta faɗa cikin wani yanayi da na Gaza fahimta.
Sai da na miƙe na hau kujerar, sannan ta sake kallon a sosai tace "Mamana inaso ki bani aron hankalin ki sosai, akwai maganar da nakeso muyi dake, kinga dai dukkan abunda ya faru, ba sai na faɗa maki komai ba, zama a cikin gidan nan abu ne mai wahalar gaske, masalan ma gareki, da za'a dinga maki kallon agola, kiyi haƙuri da Abunda na faɗa, amman zaman ba zai iya cigaba a haka ba, Shiyasa nake so da ki faɗa ma Saleem yayi gaugawar turo da manyan shi, akan azo a tsaida lokacin biki, shima ba wani lokaci mai yawa za'a sanya ba, saidai kafin hakan dole ki toshe kunnen ki, zaki iya fuskantar matsaloli ta ko ina, maganar Muhammadu ki ajiye ta gefe, ban hana ki auren shi da wata manufa ba, na tabbata babu mahaifiyar da zata samu suruki kaman Muhammadu ta ƙi shi, to saidai abubuwan da zasu iya biyowa baya, da kuma irin matsaltsalun da zaki shiga bayan auren, wannan ne dalili na naƙin amincewa, mahaifiyar Saleem mutuniyar kirki ce, tasan darajar ɗan adam, zaki samu sauƙi zama da ita, shima kanshi Saleem mai ƙaunar ki ne, don haka kiyi biyayya, kibi umurni na, insha Allah zaki ci nasara a rayuwar ki. Ki tabbatar kin gama haɗa komai da wuri don Alhaji yace shi Muhammadn ne zai maida ki, amman ina so ki kula, babu komai tsakanin ku, in banda yana matsayin yayanki a yanzu. Kuma don Allah ina so dukkan Abunda zakuga anyi mana acikin gidan nan ki toshe kunne, ki kauda kai, insha Allahu komai mai wucewa ne"
Da idanu kawai nake binta, sai dai na rasa irin fassarr da zan yi ma maganganun nata, ban dai san me ke faruwa ba, illa iyaka dai na tsinci kaina da gangarowar hawaye a saman fuskan tawa.
Me kalaman Umma suke nufi, tabbas nasan Saleem shi nake so, shi ne muka shirya Rayuwar aure dashi, to saidai duk lokacin da ta furta ko ambata mani rabuwa da Ya Ameen na kan ji wani irin dafi ya soke ni a ƙahon zuciya ta, bansan dalilin hawayen ba, amman na ta'allaƙa abun da maganar aure, da rabuwa da ita ne data sako mani a yanzun.
Girgiza kai na fara yi, ina mai cewa "To Umma insha Allahu, zaki same ni mai biyayya gareki, kuma in Allah ya yarda ba zan baki kunya ba kaman yanda kika buƙata"
Ɗan murmushi tayi tana mai shago kaina kaman ƙaramar yarinya, ni kuma ganin hakan sai wani irin kuka yaso ya ƙwace mani. Zamewa nayi ina mai kwantar da kaina bisa cinya ta, share kwalla nake ta faman yi, Amman bana so ta gane, saidai na riga na makaro, tini ta fahimci hakan, saidai bata so wannan hawayen nawa ne ya ɗore har ƙarshen rayuwa ta.
Mun kusan kai ƙarfe sha biyu anan zaune, ƴan labaruka take bani masu daɗi, rabon da in samu sake wa da Umman tawa kaman haka, har na manta, ina so in tambayeta yanda sukayi da Hajiya Kubra, wata zuciyar na garbaɗi na, ai ba hurumi na bane, saboda haka naja bakina nayi gum abu ba, kada ƴar fara'r da na samu takeyi mani in kauda ta da kaina.
Sai lokacin ne ta miƙe tana mai cewa "Mamana je ki haɗa kayan ki, kinga da wuri zaku tafi, kada ku tafi kuma kina jin bacci.
Da haka muka miƙe ina yi mata sai da safe, kowa ya shige ɗakin shi, bayan ta kullo ƙofar shiga falon.
****************
" Wai ni kuwa kunsan Abunda ke faruwa ne a cikin gidan nan kuwa?"
Mama saude ta furta cikin tsabar mamaki.
Suna zaune su duka ma'aikatan a ɗakin mama talatun da bata lafiya duk sun shiga gaida ta, sai kuma aka buɗe sabon babin gulma.
Da mamaki suma sauran suka kalle ta
" Me ke faruwa ne?" Cewar Uwani da take zaune gefen katifar mama talatun
"Maryama mana, wallahi ina jin fa ita ce tayi auren cin amana, ita ce amaryar da Alhaji fa ya aura, wadda kuka ga anyi walima jiya"
Cikin tsanann mamaki, firgita da kaɗuwa su duka suke kallon ta.
Mama Talatu kuwa bata san lokacin da ta tashi zaune ba, tana mai wara idanu kan mama Sauden
"Ke Saude kice Allah kin tuba, wannan ma Hajiya babba ta jiki ai wallahi sai kin bar gidan nan, ba fa ita bace, matar da ba'a san inda take ba ma a halin da ake ciki? Na fa ganta, ita waccen wata mata ce mai kyau, jiya saida na sai jiki naje ganin kwam wallahi, gaskiya ba ita bace... "
Cewa Uwanin da har yanzu mamaki ne fal a fuskar tata.
" Ke Uwani wallahl azim ita ce, ai na ganta, kwalliya kawai akayi mata, kuma dama kinsan Maryama da kyaun ta, kawai wahala da babu ne yasa kika ga ta koma wata tsohuwa guda, yo Alla na tuba Suhan a ce fa kawai ɗiyar ta, ita kanta Suhanan dududu nawa take? Wallahi dai to ita ce, nima na daɗe ina mamakin yanda wannan al'amari ya juye haka"
"Ke Saude kin tabbata da Abunda kike faɗa?"
Cewar Mama Talatun da kamar ta sanya kuka take ji saboda tsabar baƙin ciki
"Wallahi kuwa shugaba, ai nima nayi mamaki, Amman muna nan daku zakuga Abunda zai biyo baya, ai Hajiya Babba ba kanwar lasa bace ba, hakan ma da dauke zaune wace Alla cika balle yanzu dataci amanar ta? Kuɗi zasuyi mata aiki yanzu don wallahi kunsan ba ƙyale ta zata yi ba sai ta hukunta ta"
Mama Talaun bata samu zarafin cewa komai ba, sai a komawa da tayi ta kwanta, jikin ta duk yayi sanyi, ashe hassada ga mai rabo taki ce? To ita yanzu da wane irin ido zata kalli Maryama a matsayin matar Alhaji? Bayan duk irin abubuwan da sukayi mata a baya?
Lallai sunyi wauta, sunyi kuskure, baka raina ɗan adam duk min yanda yake, sai gashi su Alhajin bai kalle su yace yana so ba, su da suke cikin gidan, sai ita da ta sanya ƙafa tabar gidan shine yaje ya nemo ta ya aura, lallai akwai dabi, zasu sanya idanu suga yanda Al'amurra zasu kaya, Amman ita kanta tabbas tasha Alwashin ba zata taɓa ajiye makaman yaƙin ta ba, sauƙin ta ma ɗaya da maree bata nan taje ƙauye ai da yanzu ta ɗaga mata hankali.
*********
Washe gari kuwa tinda na tashi sallar asuba, ban kuma komawa ba, saida na shirya komai nawa sannan nayo wanka, mai kawai na shafa ma fuska ta, sai kuma na koma na kwanta.
Misalin ƙarfe takwas na sake tashi, a gaggauce na wanko baki na, gami da zura kaya na, hijab na sanya har kusan ƙasa, babu kwalliyar komai a fuskar tawa.
Ina daga ɗaki na jiyo shigowar shi, suna gaisawa da Umma ta da take falo
Saida gabana ya yanke ya faɗi, jiyo muryar shi da nayi, sai Naji duk jikina yayi sanyi, bansan ko menene dalili ba.
A haka na jawo akwatn kayan nawa na fito.
Yana ɗan zaune bisa kujera, hango fitowa ta daga ɗakin ne ya sanya shi miƙewa yana mai nufi ni da niyyar amsar akwatin daga hannu na.
Ja nayi na tsaya, ya masifar yiman kyau, fuskar nan tashi tar kaman wata ɗan daren sha huɗu, da mayatattun idanun shi, masu kama da yana jin bacci yake kallo na, ɗan bakin nan gum dashi kaman an ɗisa mashi, sai dogon hancin da ya ƙara ƙawata fuskar.
Ƙananan kaya ne jikin shi, baƙar riga sosai mai rubutun C-Blue a jiki an rubuta *Be my love* sai kuma blue ɗin wandn jeans mai kyau sosai, ƙafar shi soke cikin tomps masu masifar kyau suma C-Blue ne. Kai masha Allah 🤝 Ya Ameen mutum ne mai kwarjini da haiba, ga cika idanu.
Hakan ce ta sanya ni sauke kaina ƙasa, kama ni da yayi dumu dumu na shagalta da kallon shi.
"Ina kwana?" na faɗa daidai lokacin da ya ƙara so ya amshi akwatin.
Ban jira amsawar shi ba, na juya na shige ɗakin da niyyar kwaso wasu.
Ɗan bin baya na yayi da kallo, sai kuma ya juya yana mai fita zuwa motar tashi, bayan yayi ma Umma ta sallama.
Cikin sakin fuska matuƙa ta amsa mashi, ita kanta tana yi ma yarinyar tata sha'awar Muhammadun, yaro ne nutsattse, ga kamala da girmama na gaba dashi, Sam baya ɗaukar kanshi a wani ko wanda Allah ya mallakawa dukiya har haka.
Kwaso kayan na shiga yi ina mai kaiwa bakin motar inda naga ya ajiye akwatin, saidai fa baya wurin bansan ina ya nufa ba.
Umma ta ce ke cewa in tsaya ko tea in kurɓa saboda yunwr safe.
Girgiza mata kai nayi, Umma ba zan iya cin komai ba, kinga doguwar tafiya zamuyi insha Allah da mun isa zan nemi wani abu inci.
Da to ta bini, sabida Tasan dama bana iya karyawa tin da safe, sai ma inyi amai, har bakin motar ta rako ni, daidai lokacin da na hango Alhaji da Ya Ameen ɗin sun fito daga sashen Alhaji Mustaphan
Ƙarasowa sukayi inda muke tsaye da Umman, cikin Wasa da ƴar zaulaya Alhajin yake tambaya ta har na shirya?
Sauke kaina nayi ƙasa ina mai gaida shi, haɗi da yi mashi godiyar ɗawainiya.
Kuɗi masu yawa ya miƙo mani wai in riƙe a hannu na, kasa amsa nayi, har yanzu kaina a ƙasa yake, ina matuƙar jin Kunyar Alhajin tin da cen ma, balle yanzu da ya zama miji ga mahaifiyar tawa.
Ɓata rai yayi yana mai miƙa ma Ya Ameen, "Tunda ni ba zata amsa a hannu na ba, gashi kai ka bata idan kun isa cen, ku kula Al'ameen, banda gudu sosai, Allah ya tsare hanya"
Gidan baya ya buɗe ya saka kayan nawa, wasu kuma ya zuba a boot, sannan ya zagaya ya shiga, nima sallama nayi ma Umman tawa, miƙo mani wani abu tayi a cikin keda, ina kyautata zaton dai kaza ce gasassa, "amshi wannan kunci a hanya, tinda kin ƙi tsayawa ki karya" amsa nayi, jikina a matuƙar sanyaye sannan na shiga motar tana mai ɗaga mani hannu har muka fice daga gidan, sannan ta juya ita da Alhajin suka nufi sashen nata.
"Ba wanda ya tanka ma wani, sai a kunna ƙira'ar sudais yayi a hankali a hankali ƙira'ar ke tashi, jawo hijab ɗita nayi na rufe fuska ta, wani irin bacci ne ke fizga ta, ga sautin ƙira'ar da yake ratsa ni, ina mai nishaɗantuwa, jingina kai na nayi jikin kujerar, wani irin bacci na fuzga ta.
Ban san lokacin da baccin ya kwashe ni ba, haka shima bai san yanda akayi ba, sai gani yayi na gyara zama na, ina mai sauke kaina bisa ka faɗar shi da take kusa gani.
Ɗan waiwayowa yayi yana mai ƙare mani kallo, sai kuma ya saki murmushi, ganin da tayi bacci na nakeyi bilhaƙƙi da gaskiya, ba tare ma da na san na kwanta bisa jikin nashi ba.
Mun kusan tafiyar awa guda waya ta ta ɗauki ruri, a hankali na buɗe idanun nawa, kina kwance sosai bisa jikin mutum ya sanya ni ɗan wara idanu na, ina mai tashi zaune, kunya ta baibaye ni, wai ashe bisa jikin shi nake baccin, haba gaske naji baccin yayi daɗi, ga kuma wani ni'imtaccen ƙamshin turare da yake dokar mani hanci na.
Bai ko kalli inda nake ba, nayi tsilli tsilli dani, kaman in buɗe motar in fice saboda kunya.
Sunan Sir Saleem da nagani yana yawo a saman fuskar wayar, ya sanya na saci ɗan kallon shi haka kaɗan.
Har wayar ta katse ban ɗaga ba, na gaza saboda wani irin kwarjini da Ya Ameen ɗin yayi mani, ga Kunyar shi, wai yau nice kwance bisa jikin shi ina bacci.
Wayar ce ta sake ɗaukar tsuwwa, kallon wayar kawai nakeyi ina tunanin ta ina ma zan fara ɗagawa, kada yaga kaman naci mashi fuska ne, ina amsa wayar wani a gaban shi.
"Ki amsa mana"
Naji ya faɗa ba tare da ya ko kalli inda nake ba, hankalin shi da fuskar shi na akan titi.
A hankali na ɗaga ina mai karawa a kunne
"Assalamu Alaikum"
Na faɗa a hankali, daga cen ɓangaren ya saki wani sanyayyen Murmushi, sannan ya amsa mani da "Wa'aikisalam my Jaan, kina ina ne haka ina kira baki ɗagawa?"
"Ina hanya Sir" Abunda na iya faɗa kenan
"Wow my dear, shine baki jirani inzo ba, kika taho? Allah dai yasa ba motar haya kika hawo ba?"
Ya faɗa cikin son ƙarin bayani.
Sai da na kuma satar kallon Ya Ameen sannan nace "A'a Yayana ne zai kawo ni"
"OK tou zan jira ki insha Allahu, sai kun iso, take good care my Jaan"
Yana gama faɗar hakan na latse wayar na kashe, sai kuma na ɗan juya na kalle shi, bai ce man ƙala ba, daidai lokacin da muka isa Kaduna, naga ya ɗauki wata hanya ta daban.
Ƙofar gidan wani abinci mai matuƙar kyau naga mun tsaya, bai ceman komai ba, ya ɓakke murfin motar ya fita, sai zuwa cen kuma gashi ya dawo, ya ɓangaren da nake zaune ya zagaya gami da buɗe mani ƙofa yana mai cewa "Fito muje"
Ban mashi musu ba, saboda bana iyawa, har yanzu Kunyar shi bata gama saki na ba.
A hankali na shiga bin bayan shi, har zuwa wani ɗan ɗaki mai kyau sosai, dining table ne ƙwara ɗaya a ɗakin, sai kujeru guda huɗu, an ƙawata ɗakin da flowers vase masu kyau sosai, sai ƴar ƙaramar tv plasma, da sinc na wanke hannu a gefe guda, ga dispenser.
Ɗakin yayi matuƙar kyau, bamu jima da zama ba, waiter tazo da list na kayan abincin da suke dashi.
Amsa yayi yayi ma kanshi ticking sannan ya turo mani ɗan littafin
Ɗauka nayi nayi ticking ɗin lipton kawai, sannan na miƙa mata book ɗin, tana mai juyawa ta fice.
Ɗan shiru ɗakin ya ɗauka yana mai ta faman latsa wayar shi, da kallo nake binshi, lallai Ya Ameen ɗin miskili ne sosai, wato ya kwammace ya latsa waya, kaman ma bai san ina zaune ba a wurin, tabɗi a hakan ne zamuyi soyayyar da ya buƙata kenan?
Wata ƴar budurwa ce ta shigo hannun ta ɗauke da serving tray mai kyau, bisa plate ne ƙwara ɗaya, shi ta sauke ma ya Ameen a gaban shi, sannan ta koma ta sake shigowa da mugs guda biyu bisa ceremics, shima ta ajiye mashi guda ɗaya nima ta miƙo mani guda ɗaya.
Green tea ne, a cikin nashi, yayin da ni kuma lipton ne kawai, juyawa tayi ta fice, bai ceman ƙala ba, ya jawo plate ɗin shi ya shiga cin abincin shi, sandwitch ne kaɗan sai cocumber da take falle guda biyu a saman plate ɗin.
Da kallo na shiga binshi, yanzu don Allah ta yaya mutum zai ci wannan ya ƙoshi?
Ganin naja mug ɗina ne na fara sipping ya sanya shi ajiye sandwitch ɗin da ya riƙe da tissue ya shiga mani kallon tuhuma
"Ina abincin? Ko dama shi kaɗai kika buƙata?" ɗan ɗaga mashi kai na shiga yi.
Haɗe fuska yayi tamau
"Banson sakarci fa, wannan shine zai riƙe ki?" Ya faɗa cikin cin serious, bance mashi komai ba, sai ma sauke kaina nayi ƙasa ina mai wasa da tea spoon ɗin hannu na.
Turo mani plate ɗin nashi yayi yana mai cewa "have it"
Da mamaki nake kallon shi, sai kuma nace "Na ƙoshi fa Yaya"
"Ai ba tambayar ki nayi ba, cewa nayi kici, bana son jin wani uziri naki" ya faɗa cikin ƙara haɗe fuska
A hankali naja plate ɗin gaba na, ina mai fara ɗan gutsiri haka kaɗan ina ci.
Baya yaja da kujerar shi, yana mai ɗaukar Mug ɗin nashi, ya shiga shan tea ɗin shi hankalin shi a kwance.
Kaman dole haka nake ta tura sandwitch ɗin, ban ci cocumber ɗin ba, gashi daƙyar nake turawa.
"Na ƙoshi yaya please"
Na faɗa cikin ƴar shagwaɓa
Ko bai faɗa ba, yanda nayi maganar na burge shi, bai ce mani ƙala ba, ya kuma jan plate ɗin gaban shi, ya shiga cinye sauran da na bari.
Da mamaki nake kallon shi, ya Ameen ɗinne ke cin sauran abinci na ayau?
Tabɗijam, lallai kuwa, namiji saidai a bar shi, watau duk yanda naso in zayyana halin Ya Amee kullum sabuwar sanin shi nake komawa.
A haka muka gama, ya muƙe gami da nufar inda ake biyan kuɗi, ni kuma na isa bakin motar ina mai ɗan jiran shi.
A haka ya ƙara so ya buɗe motar, shiga nayi ina mai zama, shima ya shiga ya zauna yaja motar muka cigaba da tafiya.
Ƙarfe sha ɗaya da wani abu muka isa makarantar, ba wata fira da mukayi cikin mota, Shiyasa Naji zaman ya gundureni, saɓanin Sir Saleem da ko baka tanka mashi, sai ta jan fira da kai ne, har sai ka saki jikin shi da naka.
Muna yin parking shine mutum na farko da na fara hange, bansan lokacin d ana saki wata irin dariya ba, har sauti na yana fita a hankali, ganin inda nake kallo ne, ya sanya shi kai idanun shi wurin.
Zaune yake bayan mota ƙarƙashin wata bishiya, yana duba wani littafi,amman hankalin shi gabaki ɗaya yana kan hanyar shigowa.
Tin da motar tamu tayi parking hankalin shi ya ɗauku gareta, hango ni da yayi na fito ne ya sanya shi ɗan dirowa, sai kuma ya nufo wurin da muke.
Shi kau Ya Ameen tinda ya kalle shi sau ɗaya sai kuma ya ɗauke kai, ya buɗe boot yana sauko mani da kaya na, sannan ya dawo gidan baya yana fiddo sauran.
Ƙarasowa yayi yana mai sakin murmushi sosai, shi ya ma mantatare da wani nake, hakan ce ta sanya shi faɗar
"You are welcome my Jaan, ta hanya? Ya su Umma?"
Wata sabuwar kunya ce ta lulluɓe ni, ganin ko bai kula da Ya Ameen da yake sauke kaya ba, ko kuma ya ganshi salo ne irin na ɗa namiji?
"Ga Yayana Sir, zaku gaisa"
Na faɗa cikin son kauda tashi maganar
Sai kuma ya sake sakin wani murmushi, yana nufar inda ya Ameen yake tsaye jingine da motar yana fuskantar ƴan makaranta.
"Assalamu Alaikum" Sir Saleem ɗin ya furta, yana mai miƙa mashi hannu daidai lokacin da ya ƙara sa ga Ya Ameen ɗin.
Shima ɗan basarwa yayi, yana mai ɗan sakin guntun murmushi iya leɓo, tare da miƙa mashi nashi hannun sukayi musabaha.
"Ya hanya Yayan mu?" cewar Sir Saleem
"Alhmdllh" cewar Ya Ameen yana mai ɗan kauda kai gefe ya wulla mani wani irin kallo mai cike da ma'anoni.
Sauke kaina nayi ƙasa.
Hoooo Sir Salim, gaskiya yana neman bani kunya, shi totaly haka rayuwar shi take, sauƙin kai, da zaulaya haɗi da fara'r shi har sun so suyi yawa.
Zagayowa ya Ameen ɗin yayi ta inda nake tsaye, cikin salon tafiyar shi, inda nake yaja ya tsaya, yana mai zaro kuɗin da Dad ya bani, haɗi da miƙo mani.
"nagode" na faɗa ina mai amsa.
Gyaɗa mani kai yayi ya zagaya ya shiga motar yana mai faɗin "Take care"
Sir Saleem ne ya duƙa ta cikin motar yana miƙa mashi hannu, nan suka sake yin musabaha yaja motar shi da wani irin gudu yabar harabar makarantar.
Da kallo na shiga bin motar, lallai ranshi ne ya ɓaci, to ji banma ga abunda akayi na ɓacin rai ɗin ba.
Wasu ƴan mata Sir Salim ɗin ya kira suka kama mani kayan muka nufi Hostel ɗin namu.
Da murmushi ya shiga bin baya na, har muka ɓace ma kallon shi, yana mai faɗin zamuyi waya.
Wani irin mutuwar sonta ne yaji ya ƙara kashe shi, lallai samun Suhan ɗin a gareshi ba ƙaramin nasara bace a rayuwar tashi.
Sanyin hali, girmama na gaba ga kunya da biyayya, na ɗaya daga cikin Abunda suke ƙara rura wutar soyayyar tata a zuciyar shi.
Su Raihana ma sunyi matuƙar murna da dawowa ta, khadeeja ce mai faɗin "Ai na Ɗauka sai munje mun taho dake Suhana" da dariya duka na bisu, kwanciya nayi in ɗan huta gajiya, in samu in ɗan yi tunanin Abunda akayi ma ya Ameen ɗin da ya ɓata mashi rai.
********
Yana fita daga school ɗin ya samu wuri yayi parking.
Kanshi ya ɗora bisa steary yana mai zurfafa tunanin shi, lallai yarinyar ga dukkan alamu soyayya suke ita da malamin nata, kenan dama shine Umma ke faɗa mashi akwai maganar shi akan ta?
Ta ina zai fara ne? Baya jin idan ma zai iya haƙurewa da auren nata.
Dole ne yayi wani abu, dole ne ya san ta inda zai ɓullo ma lamarin, sai yanzu yake jin haushin kanshi da bai tsaya shima ya nuna akwai wani abu tsakanin ta dashi ba.
Ɗan runtse ido yayi, yana mai ɗan dukan kujera haka dashi.
Yana rasa tunanin da zaiyi, a haka yaja motar tashi yabar wurin, idanun nan nashi masu kama da na mai jin bacci, sun rikiɗe lokaci guda sunyi jawur dasu.
***********
Wajejen ƙarfe huɗu ne na yamma, Sir Saleem ɗin ya kira ni, akan wai inzo yana jira na.
Dama na sake yin wanka, hakan ce ta sanya ni ɗaukar hijabi ta na zura, kai tsaye inda muka saba zaman karatu na nufa.
Cen na hango shi zaune, a hankali na gangara ina mai zama ɗan nesa kaɗan dashi, na shiga sake gaida shi.
Ji yake kaman ya haɗiye ni tsabar so, da fara'a sosai ya shiga amsawa yana mai tambaya ta gida da su Umma. Duk lafiya ƙlau na faɗa mashi.
Sai kuma ya shiga cewa "My Jaan dama dalilin da yasa nace kizo shine, Ammi ta matsa akan in maki magana za'a tura manya, shine nace mata ta bari yau zaki dawo, to ɗazu ma ta sake kira akan maganar, shine nace bari in tuntuɓe ki domin in sanar dake."
Ɗan shiru nayi ina mai sauke kaina ƙasa, sai cen kuma nace" To Sir, nima Ummata tayi mani maganar, ba damuwa Allah ya kaisu Lafiya, amman wannan karon ba cen ƙauyen za'aje ba, Abuja ne, gidan Alhaji Mustapha Dambulan"
Da mamaki yake kallo na, ganin hakan ne ya sanya ni gyaɗa mashi kaina, sannan na shiga faɗin
"Eh, shine Mijin Ummata a yanzu, don haka shine wanda za'a nemi aure na a wajen shi, haka ummata tace"
"To shikenan Jaan ai wannan ba matsala bane, su Abbu ma ai sun sanshi sosai, don haka zan faɗa mata insha Allahu, nasan zuwa gobe ne zasu je, sai ki kira Umman ki sanar da ita"
Cikin sanyin jiki na amsa mashi da "to" nan ya shiga jana da fira, a ƙoƙarin shi na son ganin na saki jiki dashi, tinda ya kula kaman dawowar nan da nayi har yanzu a darare nake dashi.
Sai kusan 6 mukayi sallama na koma hostel ɗin namu, nan na kira Umma na faɗa mata yanda mukayi da Sir Saleem.
Cewa tayi "To masha Allahu, insha Allah zan tuntuɓi Alhaji da maganar, sai musan yanda za'ayi. Ina so in tambayeta Ya Ameen ya dawo? In ajin nauyi da kunya, kar tace banji maganar ta ba, hakan ce ta sanya ni share wa, mukayi sallama.
Facebook ɗina na hau, nayi searching sunan Ya Ameen ɗin, ai kuwa sia gashi na gani, direct Massage naje na rubuta mashi na ban gajiya, ina mai shaida mashi yayi haƙuri ban kiraa ba tin ɗazu ne saboda bani da number ɗinshi. Nagode
Haka na kwana juye juye ranar, tin da safe na tashi da faɗuwar gaba, wai ni Suhan yau nice za'aje neman aure da Sir Saleem ɗin.
Komai nakeyi haka nake yin shi a kasalance, har kai lokacin da Sir Saleem ɗin ya kira ni yana mai shaida man iyayen nashi sun nufi Abujar yanzu yanzun nan....
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~48~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Sai a lokacin kuma dukan da gabana yakeyi ya ƙaru.
Saboda haka ne ma, ko da naje lecture ba abunda nake ganewa, har dai lecturer ɗin namu ya gama ɓaɓatun shi ya fita, ban iya fahimtar me yake nufi ba.
Saboda haka ne ma na tattaro na dawo ɗaki, ganina da su khadeejan sukayi ne wani iri sukuku, ya sansu matsanta tambayar gareni.
Bani da zaɓi illa iyaka kawai shaida masu anje tsayar da magana ta da Sir Salim ɗin.
Aikuwa nan suka hau uhun murna, rai hana ce harda maƙalƙale ni, wai suna taya ni murna nayi miji ɗaya da ɗaya, abun muradin ɗaukacin student mata dake makarantar.
Nidai kawai da yaƙe nike binsu, na gaza ma ko cin abinci.
Haka na lalubo waya ta, ina mai kiran Umman tawa duk da ban san me zan ce mata ba.
Har saida ta ɗauka, sai kuma na Gaza ce mata komai, tin bayan gaidatan da nayi.
"Hello Mamana, kina jina kuwa?"
"Eh Umma, nace ya gida, wai kuwaaaa... Umm um nace Ya Ameen kuwa.. Kinji ɗuriyar shi kuwa.. Tin dai daya kawo ni ban ki... ra shi ba nayi mashi ammm an ban gajiya"
Na ƙarashe cike da in'ina, saida na dire ne kuma sai tunanin kada tace na damu dashi ne, ya sanya na kira ta ina mata maganar shi.
Kafin tace komai sai kuma nayi saurin cewa "Umma gani nayi ya kamata in kira shi inji yanda ya koma ko?"
Na ƙarashe da alamun tambaya.
Bata kawo komai a ranta ba kuma, ba kaman yanda na tsammata ba.
Sai kuma naji tace "Eh mamana, aikuwa Muhammadu ya shigo ko da safen nan ya gaida ni, Amman fa kaman baya da lafiya nake gani, don ko da Alhaji yayi mashi maganar ya shirya guest House nashi ce mashi yayi baya jin daɗi,to ban dai sani ba ko jikin ne ya kai shi ga kwanciya, saboda ban kuma jin ɗuriyar shi ba, tin dai lokacin, gashi kuma har baƙin sun tafi, amman da yake dai ko shi Alhajin bai kai da ƙarasowa ba"
Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauke, wani abu na tsira mani cikin zuciya, na Gaza tantance ko menene.
"To Umma ayi mashi sannu in ya shigo, ina gaida Dad ɗin...." na ajiye maganar a hankali, sai kuma na sake tarar numfashin ta.
"Amm.. Umma nace ko zaki turo man number ɗin Ya Ameen ɗin, dama wani abokin shi ne da ya hango shi jiya, kafin ya ƙara so har ya tafi, shine yace mani in bashi number ɗin, nace bana da ita, shine fa yake mamaki yace in samo mashi to.."
Cikin yanko ƙarya duk fa na zage ina yi ma ummata wannan bayanin, saidai ni kaina bansan dalilin da ya sanya ni neman number ɗin ya Ameen ɗin ba, kuma wai wurin Ummata, bana ma ko tunanin ta zargi wani abu.
Ta ɓangaren Umman tawa, murmushi kawai ta saki irin nasu na manya, sai kuma tace "to bari in Alhaji ya shigo zan amsar maki wurin shi, don dai ni a yanzu bana da ita gaskiya"
Ɗannjinjina kai nayi, kaman tana gaba na ne, sai kuma nace "To Umma, ina gaida Dad in ya shigo"
Sallama mukayi, kowa mamaki fal a cikin zuciyar shi, Umma tana mamakin wai ka haifi yaro a cikin ka yace zai yi maka wayo, ni kuma ina mamakin saurin amincewar Umman tawa da wuri haka, akan batun turo number ɗin.
Ni me ma ya sanya ni cewa ta turo man number shi? Me zan mashi? Ko hakanan zan ajiye a cikin waya ne?
Ajiye wayar nayi bisa cinya ta, ina mai sakin ɗan murmushi, ko dai Umman tawa ta gani wayon da zanyi mata ne? Ya sanya bata turo mani ba?
Khadeeja ce ta kalle i cikin ɗna mamaki haka a saman fuskar ta " *Suhalim* wanene kuma Ya Ameen? Mu bamu san shi ba? Ko dai ko dai? Naga zaki ce a baki number ɗin sai kwana kwana kike yi, gaskiya mu bama son haka, kada fa ayi mana snatching"
Raihana ce ta amshe maganar da cewa "Kinji ki Khadee, yo wane ƙwace kuma magana har taje kunnen manya? Wayyo Allah, zamu raƙashe a bikin mu, ke har Adamu zango, da Umar M. Shareef, da Ado gwanja zamu kira, ke ranar fa kamu Shahrokhan na gidan biki zamu kira ya haɗa mana jugunannen hall, bani mu kashe, wai na ganni a bikin Sir, Salim, gaskiya kun bala'i dace da juna, Allah dai ya nuna mana lokacin"
Da "Ameen Khadeen ta bita, tana mai miƙa mata hannu suka kashe.
Nidai da kallo nake binsu, har kusan ƙarfe huɗu suna zaune suna ta soki burutsun su, yayin da nikau jikina sai daɗa sanyi yakeyi ganin har yanzu Sir Salim ɗin bai kira ni ba.
Ina cikin tunanin ne kuwa, sai ga kiran Sir Salim ɗin ya shigo waya ta. Tsam na tashi ina mai ficewa daga ɗakin.
Ina jiyo su Khadee na sanya shewa, wai kaji fa salo na masoya, shine ba za'a zauna ayi zancen gabanmu muji ba?
Sai da na ɗan juyo ina mai tulla masu daƙuwa sannan na idasa ficewa.
A bisa wani slao mai ɗan faɗi da tudu, inda mafi yawan cin student ke zama suyi wanki na zauna, kasancewar yamma ta kawo jiki, ga kuma ƙarancn ɗalibai a wurin, Shiyasa na zauna ina mai amsawa gami dayin sallama cikin ƴar siririyr muryar da zullumi ya kusa cinyewa.
"Hello my Jaan, kina lafiya ko?"
Ɗan murmushi na saki ina kai cewa
"Lafiya Ƙlau Sir, ina wuni?"
"Lafiya Lau, my Love, wai ni sai yaushe ne za'a dena ce mani wannan Sir ɗin ne?" ya faɗa yana mai sakin wani irin killer smile, wanda ke ƙara taimakawa wajen rusa plan ɗin ƴan mata.
Nima ɗan murmushn na saki, ba tare da nace komai ba.
Sai kuma ya sake cewa" Koda yake saurin me ma nakeyi? Saura kaɗan fa, wannan Kunyar zan cire ta ne,kinsan bana so bikin nan namu ya ɗauki lokaci mai tsawo insha Allah, don haka ki zaɓi suna mai daɗi da zaki dinga kirana dashi bayan munyi aure, kuma ki shirya, ba zaki kuma zama cikin makaranta ba, ina da gida cikin zariya babba mai kyau, nasan zai burge ki, acen zaki zauna, sai ki dinga zuwa kina komawa, ko in kawo ki da kaina ko kuma in siya maki mota"
Wani murmushin na sake saki.
Nasan idan har Allah yayi aure na da Sir Salim ɗin, matsala saidai Saura kawai, saboda shi mutum ne mai girmama mace, mai girmama ra'ayin mace, yana da kula sosai, da plan, duk Abunda zai sanya ni insha wahala na kula baya so.
Ban san lokacin da nace mashi "TO Sir, as u wish, duk yanda kace, Allah dai ya kaimu lokacin"
Wata irin dariyar jin daɗi ya saki, har sautin shi na fita sosai a wayar, sai kuma yace, "Kinsan me? Ammi fa ta kira ni, tace duk Abunda nake in baro shi yanzu in taho, saboda magana mai muhimmanci su Abbi suka dawo da ita, so bata yuwuwa a waya, saidai naje kawai, nasan dai bai wuce maganar date, Shiyasa gani ma har na shirya zan wuce, kiyi mani addu'a idan na isa zan kira ki, insha Allah"
Samun kaina nayi da jero mashi addu'a sosai, shi kuma sai Ameen yake amsawa cikin jin daɗi, da godiya ga Allah daya bashi mata kaman Suhan ɗin.
A haka mukayi sallama, yana ta faɗi mani zaiyi missing ɗina, kada in kashe waya, komin dare zai kira ni.
Da to na bishi, domin dai nasan ai yana da wata matar cen, da wuya ace ya samu ya kira ni cikin dare, saidai ni ɗin ba mace bace mai musu, ya sanya ni amsa mashi kai tsaye.
To ba ta matar tashi nakeyi ba, ai kuma na riga da naga lagon ta, Tinda tin kafin in shiga ta iske ni, na kuma ga salon ta, da kula kalar haukan tata, da dai ace shiru Naji, ban san kalar ta ba, sai inyi shayin yanda zan tadda ta, acikin gidan, ko tana da wani matsayi ne na daban, Amman yanzu kuma ai ta ɓarar da garin ta ƙasa, da wuya kam idan zata iya kwashe shi duka.
Muna gama wayar, saƙon Umma ya shigo cikin waya ta, Number ce kawai ba tare da tace mani komai ba.
Na kai tsawon wani lokaci ina mai shawarar in kira ko kuma in haƙura, kada ya ɗauka da wata manufa kuma.
Shahadar kira nayi, waiting call aka sanya mani, sai kuma ban jira ba na sake danna wani kiran.
Still dai waya yakeyi, Amman wannan karan kiran ya shiga wayar tashi.
Bai amsa ba, har saida na fidda rai, ina mai miƙewa da niyyar shiga ɗakin.
Sai kuma ga kiran nashi ya shigo waya ta.
Ƙarar wayar ce tayi daidai da rugujewar ƙirji na ya bada wani irin sauti.
Ban san lokacin da nayi kwana ba, na miƙe tiryan tiryan ba tare da nasan inda zan dosa ba, tafiya kawai nakeyi.
Sai da ta kusa katsewa, sannan na iya ɗagawa.
"Cikin wata irin sassanyar murya, mai cike da kwarjini da haiba Naji yace.
" Assalamu Alaikum, Sunana Muhammad Al'ameen Dambulan, ko zan iya sanin da wa nake magana?"
Kuttttt
Wannan dogon bayanin fa? To ai nasan wanda na kira, saida na cire wayar a kunne na, na Harare ta, sannan na mayar ina mai cewa "Suhan ce"
Kaman ma cikin tsiwa nayi maganar, sai kuma naji kaman ban kyauta ba, sannan nace "Yaya Ina wuni?"
Murmushi iya leɓo ya saki, cikin son basarwa kaman ma bai gane wake magana ba ya shiga cewa "Suhan!? Suhan? Wace Suhan kenan?"
Wayar na cire a kunne na, ina mai sake kallon number ɗin, lallai dai, daidai na rubuta ta, gashi kuma har ya faɗa man sunan shi, kuma. Ma dai beside, wannan muryan ko a cikin bacci na jita, zan iya shaida ta.
"Yaya Suhan fa ta Umma ta"
Na faɗa cikin salon ƴar shagwaɓa kaman zanyi kuka.
Murmushi ya saki mai sauti, ita dariya ma ta bashi, Amman da yake dariyar ba ɗabi'ar shi bace, a cewar sa murmushin ma kawai ya isa, sai kuma ya shiga kwaikwayon irin maganar tawa.
"Nifa ban gane ba malama, kiyi cikakken bayani mana"
Zaune na kai, bisa wata grass carpet mai ban sha'awa, tayi tsanwa har abun tt,ina mai cewa "Kai Yaya, Allah kuwa ka gane, gashi ma Naji kana murmushi"
"Suhan fa kika ce ko? Yaushe kikaji nayi murmushi? Ko dai aljanna ce ban gane ba? Kinga sai anjima tinda ba zakiyi bayani ba.
Ya ƙarashe yana mai ɗauke wayar a kunnen shi kaman zai kashe, sai kuma yaji nayi saurin cewa
" tsaya, tsaya yaya, to nice Suhan ƙanwar ka, da take makaranta Zaria"
Wannan karon dai dariya ta bashi sosai, kuma saida ya ɗan dara kaɗan yana mai cewa
"Oho, to ai haka zakice, Yarinya ta girma, ina saurayin naki?"
"Kai Yaya, wane irin saurayi kuma?"
"Oh baki ma gane shi ba?"
"Uhummm". Kawai na iya faɗa, kaman ina gaban shi, ya saukar mani da kunya kaman in nutse ƙasa nake ji na.
Cen na tsinkayi muryar shi yana cewa "Ya na barki to? Fatan dai kina karatu? Naga massage ɗinki ɗazu, ina wani abu ne yasa banyi maki reply ba, am sorry"
Nan ma ban iya cewa komai ba, wai dama haka Ya Ameen ɗin yake? Ɗan zaulaya ne? To me yasa ma tun tuni ban kula ba?
"kina jina kuwa?" na sake tsinkayo muryar shi, cikin salin maganar shi mai burgewa.
"Eh yaya, na kira in maka ya gajiya, nagode da ɗawainiya, Allah yabar zumunci"
"Ba komai ƙanwata, nagode kiyi karatu lafiya"
Abunda ya faɗa kenan ya datse wayar, ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Da mamaki na sauke wayar ina mai binta da kallo.
Wani salo kuma
Wai ƙanwata, hummm
Sabun na yaya fa har ya fara bani tsoro, na zaton zaiyi mani maganar baƙin da suka je gidan, sai kuma naga ya share bai ceman komai ba, kuma dai bana tunanin zai ce bai san da zuwan nasu ba.
Sauke kafaɗa nayi, cikin ƴar basarwa na miƙe, sai lokacin ne na fuskanci irin tsawon tafiyar da na shawo.
Tabɗi, lallai ma ni Suhan, to da ina zani da na kawo kaina nan na zaune? Duk da akwai tsirarun student, Amman banyi tunanin tafiyar har ta kawo nan ba.
Jikina a mace na kama hanyar ɗakin namu, ina ta saƙe saƙe a cikin zuciya ta, na kuma ƙagara Sir, Salim ya kira ya shaida mani yanda akayi da magabatan nawa.
***********
Da yake cikin dare ya isa sosai, sai bai takura wajen zuwa gidan nasu ba, gidan shi kawai ya zarce, kaman yanda ya tsammata, Ma'un bata yi wani shiri na tarbar shi ba, baccin ta ma ya tadda tana shaƙa, da makullin hannun shi yayi Using ya buɗe gidan, har ya saka motar shi bata ji ba, ko kuma taji share shi ne tayi oho?
Da yake yaran na gidan su wurin Ammi ɗinshi, sai bai ma ko bi ta kan Ma'un da take ta kwasar bacci ba.
Kai tsaye ɗakin nashi yayi ma dirar mikiya, saidai fa ɗakin gashi yaji ƙura, kaman anyi yaƙin badar a ciki.
Haka ya shiga kakkaɓewa, ya share duk cikin daren, sannan ya gyara gado.
Duk da tana jin motsi, Amman bata yi niyyar tasowa ba, wai a haka mijin ka ya dawo kenan daga doguwar tafiya, kai Allah yayi wadaran naka ya lalace.
Wanka ya shiga, saida ya fito ne ɗaure da tawul ya isa ga water dispenser dake falo ya matso ruwan zafi ya jefa lipton.
Sannan ya koma ɗaki, bakin gado ya zauna ya sha lipton ɗin, sannan ya ajiye mug ɗin yana mai zura kayan bacci ya saki ac a hankali a hankali ya kwanta.
Tunowa yayi da yace zai kira ta, sai kuma yayi tunani ai ba ita kaɗai bace a ɗakin, kada ya takura su, gashi kuma su ɗin ɗalibai ne, wasu ɗaliban basa raina abun magana da yayatawa.
Text kawai ya tura mata, ya jawo blanket ya lulluɓe ƙafafun shi, yana mai furta addu'ar barci
Da yake yayi doguwar tafiya, ai tuni bacci ya kwashe shi, ba tare da ya an kare ba.
*********
Yana sauke wayar, murmushi ya kudce mashi, wai sai yaushe ne Suhan ɗin zata bar wauta a rayuwar ta?
Na daga cikin Abunda ke ƙara sanya ta burge shi kenan.
Ji wai, shi zata yi ma shagwaɓa.
"Hummm"
Ya furta a fili, yana mai sakin wata ajiyar zuciya.
Zaune yake bakin swimming pool, hankalin shi na akan ruwan da take garai garai kaman kasha, lokutta da dama, idan yanayin marece ya kawo jiki, wurin ya kan je ya zauna, iskar ruwa haɗe da sanyin lambun da yake gefe yana buso mashi.
Murmushi yake saki akai akai, tin bayan da ya sauke kiran wayar nata.
Muryar Mom ɗinshi ya tsinkayo tana tahowa inda yake, cike take da taƙama da izza kaman yanda kowa ya santa, babu abunda ya ragu daga cikin halin ta.
Kujera taja ta zauna, rana mai fuskantar shi.
"Mom barka da gida"
Ya furta mata cikin girmamawa, tare da soyayya irin da ɗa da mahaifi.
"Yauwa Son, barka da hutawa" itama ta furta, cike da duniyanci.
Shi kanshi yayi mamakin ta, sai kuma yaga ta sake kallon shi cikin ƴar dariya ta izza tana mai cewa "Son ina so ne ka kai ni unguwa"
"Unguwa kuma Mom? At this late hours?"
"Eh ba daɗewa zanyi ba, gidan Hajiya Sa'a zaka miƙa ni"
Da mamaki yake kallon ta, Hajiya Sa'r da tayi ma uwar watsi? Yanzu kuma me zata je yi gidan ta?
Da mamaki yake kallon ta, har ta miƙe, tana mai miƙa mashi makullin motar ta, ƙirar pomatic.
Amsa yayi ba tare da yace komai ba, ya miƙe gami da nufar motar da take ajiye gefe.
Yana kallon ta, saida ta wurga ma sashen Umma harara, sannan tayi kwafa ta wuce.
Mamaki yake, da addu'ar Allah ya shirya mahaifiyar tashi, domin dai shi bai ga wani abu da Umman tayi mata ba, wanda ya saɓa ko ya kauce ma shari'a, balle har take iƙirarin taci amanar ta.
Hum.
Ba zai iya fassara yanda abubuwa zasu wakana ba, muddin taji lamarin auren nashi da Suhan, Abunda har ta riga ta sanya ma ranta cewa an wuce wannan babin.
***********
Sai da ya gama baccin shi sosai, misalin ƙarfe tara na safe ya farka, wanka ya fara shiga, sannan ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda gizna Ash colour, yayi matuƙar kyau, dogon namiji alkyabbar maza.
Ɗakin Ma'u ya leƙa, bacci take ta shaƙa, ga plate cen gefe kan gado, tare da mug na tea, ya tintsira, ga Alama ma karyawa tayi ta bar kwanonin bisa gado.
Ɗan ƙaramin tsoki taja, yana mai ficewa daga gidan, kai tsaye gidan Ammin shi ya nufa.
Da gudu kyawawan yaran nashi suka rugo suka maƙalƙale Sir Salim ɗin suna faɗin "Oyoyo Oyoyo ga abbanmu"
Da ɗaiɗai ya shiga ɗaga su, yana mai miƙa ma kowa ledar tsarabar da yayo mashi,
Da gudu suka haura sama suna dariya da godiya.
Da kallon farin cikin ganin yaran nashi ya bisu, yana mai faɗin "Kuce da Ammi na shigo"
Sai gata kuwa yaran na shiga da tsaraba.
Mace mai yawan fara'a, ga kamala, kyakkyawa da ita, fara tas.
A hankali take saukowa tana faɗin wannan saukon fa haka malam?
Ɗan zamkwa yayi daga bisa kujerar da yake zaune, lokacin da take zama ne ya shiga gaida ta cikin girmamawa.
Amsawa tayi itama, tana mai rage fara'r dake saman fuskar ta.
Ina Ma'un?
"Bata tashi ba na baro ta Ammi"
"Amman dai Tasan ka dawo ko?"
"Ammi tana jina fa tayi banza dani ta ƙyale ni, ni kuma ban mara magana ba na fito, ki sanya a kawo man break fast nan, yunwa nake ji, ko jiya lipton kawai nasha"
Cikin wani irin kallo take faɗin
"Salim ka dena zama da yunwa, nasha faɗa maka" ta faɗa tana maibƙwala ma mai aikin ta kira.
Sai fata kuwa, cikin girmamawa ta gaida Salim ɗin.
"Ki kawo mashi breakfast, kada ki cika suger a tea ɗin"
"To Hajiya" mai aikin ta furta tana mai juyawa.
Ba'a daɗe ba kuwa sai gata ɗauke da tray, cike da kayan abinci.
Tashi yayi tsaye ya amsa, yana mai ajiyewa ƙasa, ya sauko bisa carpet ɗin, yana mai cire hula ya ajiye, sannan ya zare links ɗin, yana mai kalmashe hannun riga.
Miƙewa yayi yana mai wa ko hannu cikin sink da yake ajiye gefen falon tare da gogewa da towel, sannan ya dawo ya zauna.
Sai da yaci ya ƙoshi, sannan Ammin ta sake kiran mai aikin tazo ta kwashe, sannan ya sake miƙewa ya wanki hannu ya dawo ya zauna.
Tattara dukkan natsuwar shi yayi kan Ammin tashi, yana mai faɗin "Ammi gani, kince inzo kina son ganina"
Itama ganin ya bata dukkanin hankalin shi, ya sanya ta gyara zama, tana mai fuskantar shi, cike da tausaya ma yaron nata, akan abunda zata faɗa
"Salim, yarinyar nan kayi ta addu'a, idan rabon ka ce sai kafa Allah ya baka ita"
Gaban shi ne ya yanke ya faɗi, cikin tsananin firgita yake kallon Ammin tashi, idanun nashi har sun cenza kala.
"Ammmii bann.. Fahimta.. Ba, wani abu ne ya faru kuma?"
Ya tsinci kanshi cikin in'ina yana mai jefa ma Ammin tashi tambaya.
Tsam ta miƙe daga inda take, tana mai dawowa bisa kujerar da yake zaune, sai kuma ta kamo dukkanin hannuwan shi.
"Wato jiya Su mahaifin ka, da su Alhaji Basheer (Wan mahaifin shi) su je cen Abuja gidan Iyayen yarinyar nan, to Amman dai su abunda sukace, yarinya dai sunyi mata miji, Amman dai idan basu daidaita kansu ba, to zasu neme mu"
Cikin tsananin firgita ya miƙe yana mai sauke hular dake kanshi, salati ɗauke a bakin shi yake furta
"Ammi anya kuwa cen suka je? Suhan fa na ƙauna ta, kuma mahaifiyar ta da bakin ta tace maki ta bani, yanzu kuma ya zasu ce haka? Ko dai ba cen suka je ba Ammi?"
Kamo hannuwan shi tayi duka, tana mai cewa "Zauna Salim, zauna, ya zaka ce ba cen suka je ba Alhaji Mustapha Dambulan ɓoyayyu ne a ƙasar? Kana sane da mahaifin ka ma ya sanshi tin da daɗewa ko? To dai haka suka ce, sannan Baffan ka ma ya riga ya yanke hukunci, yake ka haƙura, su ba ƙananan mutane bane da zasuyi magana biyu ba, kuma ma banda abun ka, ai ba mace ke bada aure ba ko?"
" Ammi ki roƙe su su koma, ina cikin wani hali please Umma, Suhan ita kaɗai ce zata iya gyara mani gida na, da tsaftar ta, da kawaicin ta, da biyayyr ta, da haƙurin ta, Ammi ki taimaka mani don Allah"
Ya faɗa cike da kaɗuwa, yana kuma ƙoƙarin sake miƙewa.
Amman Ammin tashi ta damƙe hannun nashi kam, ta yanda ba zai iya kuma miƙewa ba.
"Nima Salim naso ka da yarinyar nan, na maka sha'awar ta, tarbiyyar ta, da hankali da natsuwar ta ta burge ni, saidai har yanzu ban fidda ran bazaka same ta ba, ban kuma fidda maka ran ko ka rasa ta, ba zaka samu wadda ta fiye maka ita ba, ina maka addu'a Salim, kuma zan cigaba da yi maka Addu'a, Allah ya shirya maka matar ka, sannan ya baka wadda zata kawo kwanciyar hankali a cikin gidan naka. Wanna shi e fatana a gareka a kida yaushe."
Ta ƙarashe maganar tata itama cikin ƙunar zuciya.
Har ga Allah bata ji haushin Umman a Suhan ba, saboda ita uwa ce, har kida yaushe zataso ta Aurar da ɗiyar ta ga wanda take so, to saidai itama kanta ƙarƙashin wani take, dole ne tayi biyayya, komin yanda take son abun, addu'a ita kawai zasuci gaba da bin yaran nasu da ita.
Rabon ko da taga Salim ɗin yayi hawaye an daɗe, duk yanda yake shan wahala da azabe zama da Ma'un baya damun kanshi har haka, Salim mai barkwanci, Salim mai yawan fara'a, Salim bai fidda wasu daga damuwa da zaulayar shi, tau sai ga Salim na hawaye gaban Ammin shi.
Guiwoyin shi duka ya sauke ƙasa, har yanzu hannayen shi na cikin na Ammin nashi, Tunowa yakeyi da wayar su ta ƙarshe da ita, Tunowa yakeyi da kallon shi da ita na ƙarshe, Tunowa da Kunyar ta, da yawan son karatun ta, yanzu shikenan ta tashi ba'a mallakin shi ba? Anya kuwa zai iya haƙura kaman yanda iyayen nashi suka buƙata?
A sanyaye ya miƙe tsaye, yana mai faɗin "Ammi zanje gida in kwanta, kaina yana yi mani ciwo"
"Ba inda zaka Salim, shiga ɗaki na ka kwanta, zuwa anjima sai ka tafi."
Ba musu ya fara taka matattakalar upstairs ɗin, yana mai jin kanshi yana wani mugun sara mashi.
Wanene wannan? Wanene wannan mai sa'ar da har zai iya mallakar yarinyar daya ƙwalkafa rai a kanta? Yarinyar da ya tsara yanda zaman gidan nashi zai kasance da ita? Shin tana ma son shi kuwa? Zata yarda da auren itama kuwa? Saidai yasanta, yarinya ce mai kawaici da biyayya, ba zata taɓa bijire wa umurnin iyayen nata ba.
Koda ya isa ɗakin, ciki ya tadda yaran nashi, suna ta faman wasan su, hankalin su kwance, ga kayan ciye ciye daya kawo masu, sun baje bisa gadon kakar tasu Ammi, sai cin abun su suke suna wasa.
Haka suka sake hawa kanshi, kowa da abunda yake faɗa, kowa ƙoƙarin bashi biscuit yakeyi yaci, hakan na burge shi da yaran, Amman sai gashi yau yana ture su, yana faɗin suje ƙasa suyi wasa kanshi ke ciwo.....
Hhhhmmmmmmmm
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~49~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Tin dai da naga text ɗinshi da daddare, sai na kawo ma raina ba zai kirani ba sai zuwa safe.
Hakan ce ta sanya, banyi gigin kiran shi ba, har kusan ƙarfe goman safiya.
Ya kamata ace ya kirani, ko don inji yanda akayi da maneman auren suka je.
Ban dai kira ba, amman zuciya ta na ta saƙa man in kira shi inji halin da ake ciki.
Har yanzu gabana bai bar duka ba, sai kuma hankalina ya fara tashi, gashi munyi waya da Umma da safe itama bata ce man ga yanda ake ciki ba.
Hakan ce ta sanya ni kiran Hafsat, saidai muka gama gaisawar da ita Amman itama bata ce man komai ba.
Ban iya tambayar ta ba dai, kunya nake ji sosai, tun da dama nasan ita bata ra'ayin abun a cikin ranta, ɗan uwanta kawai take so.
Haka nayi shahadar kiran Sir Salim ɗin.
Kira na sau biyu amman ba'a ɗaga ba.
Kasaƙe nayi da waya riƙe a hannu, ga su khadee suna ta tambaya ta wai ko an sanya bikin ne?
Rasa abunda zance masu nayi, saidai na miƙe tsaye ina mai ficewa daga ɗakin, wayata riƙe a hannu.
Sake jaraba kiran nashi nayi, wannan karon ma ta shiga, saidai tana fara ringing aka katse.
A'ah me ke faruwa ne?
Sake kira nayi, amman sai ba'a katse ba, aka barta ta cigaba da ringing, har said ata gaji ta katse don kanta.
Gashi dai ina jin kunya, bana iya kiran Ammi, hakan ce ta sanya dole na koma ɗaki na kwanta, nan na tarar su Raihana sun tafi lecture.
************
Baya jin zai iya ɗaga kiran nata a daidai wannan lokacin, hakan zai iya ƙara karya mashi guiwa.
Muryar ta kaɗai yake da muradin ji, Amman idan ya tuna da hakan ba zai wani amfane shi ba, mallakn wani ce, sai ya runtse idon shi ya sake buɗewa, har yanzu dai wannan abun da ya tattaru ya dunƙule mashi a maƙoshi ya kasa wucewa.
Har Ammi ta gama tattara yaran nashi ta shirya masu zuwa makaranta, driver ya ɗauke su, yana nan kwance bisa gadon nata, shi ba bacci ba, shi ba ido biyu ba.
Babu sauran kuzari ko walwala tattare dashi, yana tuno farko haɗuwar shi da ita.
Sanyin ta, tarbiyyar ta, duk waɗannan abubuwan idan ya tuna wai ya rasa su, sai yaji kanshi ya ƙara yi mashi nauyi.
A haka Ammi ta shigo ɗakin ta same shi.
Bakin gado ta kai zaune cikin sanyin jiki itama, ƙura ma yaron nata ido tayi, har yanzu tana iya hango irin Abunda take gani a cikin idanun shi, aduk lokacin da ya nemi wani abu ya rasa, tin yana yaro, saidai da yake shi ɗin mai haƙuri ne, tasan zata iya shawo kanshi da izinin Allah.
"Salim" ta faɗa a hankali.
Ganin hakan da yayi ne ya sanya shi tashi zaune, yana ƙure Ammin tashi da kallo irin na ban tausayi.
A take tausayin yaron nata ya kuma tsira mata.
Duka hannuwan shi ta kamo.
"Salim Abban" sunan da take yawan kiran shi kenan duk lokacin da rashin irin wannan ya same shi.
Da gefen baki ya ɗan murmusa mata, irin yadda shima ya kan yi mata.
Hakan ne ya ƙara mata ƙwarin guiwar ci gaba da abunda take da niyyar faɗa.
"Nasan ba daɗi Salim, to saidai bamu da yanda zamuyi, dole ne kuyi biyayya ga iyayen ku, masalan ma ita da take mace, ba ita zata aurad da kanta ba, wannan yasa nake matuƙar so ka taimaka mata wajen yin biyayyr ga iyayen nata. Ba zan ji daɗi ace ka koma mata ba a yanzu, inaso ka sanar da ita dukkan abunda ke faruwa, sannan ka yanke duk wata alaƙa ta soyayya dake tsakanin ka da ita, ina maka addu'ar Allah ya baka wadda ta fita"
Da idanun shi da suka cenza kala yake daɗa bin Ammin tashi da kallo.
"Ammi ina son Suhan matuƙa, nayi rashi Ammi, ya zanyi? Naso ta shigo gidana, ko da hakan zai zama silar samuwar haske a cikin gidan nawa, nima in zama mai gida kaman yanda sauran maza keyi, Ammi ita kaɗai ce zata iya..."
Girgiza mashi kai ta shiga yi.
"Salim kada ka sare, da izinin Allah zaka samu wadda ko bata fita ba, itama ba abunda zaka nema a wajen ta ka rasa, insha Allah"
Sauke ƙwayar idanun shi yayi ƙasa, ji yake kaman ya saki kuka, ko ya samu maƙoƙon da ya tokare mashi ya wuce.
A hankali yake haɗiye wasu irin miyau masu zafin gaske.
"shikenan Ammi, ki cigaba da taya ni addu'a, nagode ƙwarai, ina alfahari da samun uwa ta gari, nagartatta kaman ki, ki faɗama su Abba cewa *Na janye kaman yanda suka buƙata* Allah ya zaɓa mana Abunda yafi zama alkhairi, ya sanya hakan shine alkhairi gare mu baki ɗaya"
Cikin tausayawa take bin shi da kallo, ita kanta tasan tayi rashin suruka ta gari.
"Ba komai Son, Insha Allahu zan cigaba da yi maka addu'a, ita kuma Ma'u Allah ya shirya mana ita, ya sanya ta gane gaskiya, kuma ya bata ikon yin aiki da ita, ko yanzu ka kawo wadda kake so, a shirye nake da na mara maka baya ka same ta Salim, sannan inaso idan kaje makarantar ka haɗa ni da Suhan ɗin zamuyi magana"
Jinjina mata kai ya shiga yi, ko ba komai ya ɗan samu relief, wani sashe na zuciyar shi yayi sanyi, Ammin tashi mace ce wadda ba kowa Allah yaba irin ta ba, a matsayin Uwa, samun ta kaɗai a rayuwa ya gamsar dashi. Shiyasa a kullum yake daɗa alfahari da ita a rayuwar shi.
Zuro ƙafafu shi yayi daga bisa gadon a hankali yana mai miƙewa, sannan ya maida kallon shi kan Ammin tashi, da ta riga da ta saki hannun nashi.
"Ammi Abban fa? Bamu gaisa ba, gashi ina so in wuce, ban ɗauki excuse ba"
"Ayya, Gashi kuma tin safe ya wuce majalisa (Senate) saidai ko ka kira shi, yace ne suna da muhimmin Meeting ta yanda za'a shawo kan matsalar wannan ƙarin harajin da gwamnati tayi, sannan da rufe boder"
Ɗaga mata kai yayi alamun gamsuwa, sannan ya fara takawa zuwa sauka down stair.
A baya ta biyo shi har suka sauko tana mai ƙara yi mashi nasiha akan yadda da ƙaddara.
A bakin ƙofa ya tsaya, yana mai kamo Ammin ya manna mata peck a goshi, sannan ya fice tana mashi fatan Allah ya kiyaye hanya.
Ba Abunda zai koma gidan yayi, hakan ce ta sanya shi ɗaukar hanyar zariyar kai tsaye ba tare da ya kuma bi ta kan Ma'un ba.
********
Sanye yake cikin dakakkiyar shadda, ruwan bula, sai hula daya aza bisa kan nashi itama bula ce.
A hankali yake takawa zuwa sashen amaryar tashi.
Ƴan aiki sai kallon shi suke yi, suna kuma gaida shi, haɗi da jinjina irin jajircewar Alhajin ta fannin tsaya ma gidan nashi, gashi dai kowa yayi tunanin wata fitinr zata ɓullo ta fannin Hajiya Kubra, Amman ga mamakin su, duk sai suka ji shiru kuma, kaman ma babu abunda ya faru a cikin gidan.
Ba kowa a falon, sai kayan kallo da suke ta aikin yi, da kallo yabi sashen, ko ina tsaf-tsaf, ga ƙamshin girki da yake tashi, wanda ya haɗe da na room freshner da ta fesa a ɗakin ta Naseem.
Duka ɗakunan ya leƙa bata ciki, hakan ce ta sanya shi nufar kitchen.
Ta gama soya dankalin ta lafiyayye, ta haɗa coleslow da ƴar stew ta anta da kwai, sai tea data haɗa wanda ya sha lemon grass da kayan ƙamshi.
Ta juye kenan zata fito sukayi kiciɓis.
Da murmushi a saman fuskar ta, sai kuma ƴar Kunyar shi da har yanzu bata gama sakin ta ba.
A hankali taja baya tana mai gaida shi.
Cikin murmushi ya sanya hannu ya amshi plate ɗin, ita kuma sai ta koma ta ɗauko Mug ɗin tea ɗin da wani fork.
Gaba ya shiga tana bin shi a baya, har bisa dining table ɗin.
Kujara yaja ya zauna, itama tana mai zama, ƙara gaida shi ta yi, ya amsa cikin sakin fuska da walwala irin ta dattawn arziƙi.
"Alhaji bismilla mana, ka karya don nasan dai da wuya idan kaci wani abu, don naga ka fito da wuri yau"
Ta faɗa a kunyace irin tasu ta manya.
Da kallo yake binta, tayi kyau, duk ta cenza abun ta, kaman wadda ta shekaru a cikin hutu.
Atamfa ce jikin ta, an mata ɗinkin zamani mai kyau, sai yake ganin kaman ma bata taɓa haihuwa ba, balle ace ta ajiye kaman Suhan.
"Kin bani ne? To wa zai bani idan ba ke ba?"
Ya faɗa cikin zaulaya.
Itama dariya tayi a hankali, tana mai tura mashi Mug ɗin tea ɗin gaban shi.
"Afuwa Alhaji, to gashi, ai bansan yanda tsarin yake ba, naga duk tare kuke cin abinci ne cikin gidan, Shiyasa nayi tunanin ko ka karya"
Bai ce ƙala ba, in banda murmushi da yake yi, yaja cup ɗin gaban shi, yana mai ɗaukar cokalin ya fara cin abincin.
Ba sabon abu bane a wurin shi, cin abincin nata, to saidai yau yake jin kaman abincin nata ya ƙara daɗi, gashi dai ba wani tarkace a ciki, Amman ɗanɗanon yayi mashi daɗi a baki.
"Magana nazo muyi dake Umman Suhan, to Amman dai kafin nan kije ki haɗo naki tea ɗin, tinda na ƙwace maki wannan"
Itama murmushi ta sake saki, tana mai tura kujerar baya, sannan ta miƙe ta nufi kitchen ɗin.
Da kallon jin daɗi ya bita, yana ayyanawa a ran shi, yanzu ne aure ya tabbata a gareshi, ko bayan hakan ya samu natsuwa da kulawr da yake da muradin samu a wurin Umman, wanda tun tuni yake fatan ya samu, masalan idan yaga yanda matan abokan shi ke ba mazajen nasu kulawa, kai ko Alhaji Auwalu da ya fishi manyanta, kuma itama Hajiya Zainab ɗin tafi hajiya Kubran Manyanta, Amman kulawar da suke samu Sam bama a haɗawa.
Bata daɗe ba sai gata ta fito, hannun ta ɗauke da madaidaici Mug ɗin itama.
Zama tayi, tana mai sake sakin murmushi, sannan ta sauke kanta ƙasa, suka ci gaba da karyawar, duk da dai a matuƙar takure take.
Ta riga Alhajin ajiye cokalin ta, sai bayan da ya gama ne shima ya tattara dukkanin hankalin shi a kanta.
"Maryam Magana nake so muyi dake ta fahimta, ina fatan kuma zaki bani dukkanin goyon bayan ki, a matsayi na na wanda yanzu na tashi daga mutumen da kuke ma aiki, na koma mijinki mai gidan ki, ina fatan kin fahimta?"
Gyaɗa mashi kai ta shiga yi, cikin girmamawa da mutuntawa.
Hakan ne ya sanya shi jin daɗi, gyara zaman nashi yayi bisa kujerar yana mai fuskantar ta, da yanda zata so maganar ko kuma yanda zata fahimce shi, har ta ɗauki al'amarin.
"Maganar Auren Suhana dai ce, jiya maneman aure sun zo daga Adamawa, kaman yanda kika sani, to saidai ban samu sanar dake yanda mukayi dasu ba, saboda muna shawara wani al'amari ne da yaya Auwalun tin jiyn. Amman alal haƙiƙa bamu amsa masu ba, daga ni har Alhaji Auwalun, dalili kuwa shine, yaron ki Al'ameen tin farko tin kafin ma ta shiga makarantar da suka haɗu da shi wancen yaro, shi Muhammadun shine ya fara zo mana da buƙatar auren Suhanan, to Amman saboda wasu dalilai acen baya, ya sanya muka dakatar dashi, sannan muka hana shi bayyana maku, har sai lokaci yayi, to kafin lokacin ne duk Abunda ya faru, ya faru. Saboda haka, inaso ki bani damar ba Muhammadu izinin neman ita Suhan ɗin, idan Allah yasa sun daidaita kansu, tana sonshi to falillahil hamdu, kinga ai gida batanƙoshi ba ba'a kaiwa dawa. Har ga Allah ni dai na yarda, kuma na amince da tarbiyyar da kika bata, hakan ce ta sanya kuma bana tunanin har zaki iya bijire wa wannan buƙatar tawa, nasan zaki ce Hajiya Kubra ita mahaifiyar Muhammadun, to inaso ki sani, ke babu ruwanki a wannan maganar, ki bar komai a hannu na, yanzu dai amincewar ki muke buƙata"
Da tsananin kallo take bin Alhaji Mustapha ɗin, saidai kwarjini, girma haiba tashi, ba zasu iya barin ta bijire wa buƙatar tashi ba, kaman yanda ya furta.
Ƙasa ta sake yi da kanta, tana mai jinjina wannan al'amarin, anya kuwa hakan zata yuwu? Ko ba hajiya Kubra ba, ai duniya sai ta zage su, sai ace son abun duniyar nasu yayi yawa, gashi dama har yanzu ta kasa fita waje balle su haɗu da su Mama talatun.
"Ko in baki lokaci ne kiyi shawara?" Alhaji Mustaphan ya faɗa cikin son jin ba'asi.
Tabbas Al'ameen yaro ne nutsattse, duk wani abu da ake buƙata wajen ɗa namiji ya tattara su, kusan ma zamu iya cewa idan ana zartarwa to shi fa ya zarta, Amman Hajiya Kubra ba lafiya bace...
Miƙewa Alhaji Mustaphan yayi, har yanzu da sauran murmushi a kan fuskar tashi, Allah sarki, dattijon arziƙi kenan.
"To shikenan ni zan fita, muna da Meeting da shugaban ƙasa, kiyi shawara da zuciyar ki, Amman inaso ki sani *Ni Alhaji Mustapha Yusuf Dambulan, ina nema ma yaro na Muhammadu Al'ameen Mustapha Dambulan, auren yarinyar ki Suhan* da fatan za'a amshi ƙoƙon barar namu da hannu bibbiyu."
Yana gama faɗar haka ya sanya kai ya wuce, yana mai faɗar "Nagode da abinci, lallai yau kada ki sanya in ta bacci a office ɗin shugaban ƙasa"
Miƙewa tayi itama, tana mai sakin fara'a, raka shi tayi har bakin ƙofar fita daga sashen nata, daga nan ta tsaya tana mashi a dawo lafiya hannun ta ɗauke da briefcase ɗin tashi tana miƙa mashi.
Amsa yayi yana mai sanya mata albarka, har ya juya zuwa ga motar tashi, sai ga mota ta shigo cikin harabar gidan.
Ɗan dakatawa yayi da shiga motar da driver ɗin nashi ya buɗe mashi ƙofa, domin ganin ko su wanene.
Hajiya Zainab ce ta fito daga cikin motar, Sanye take da tsadadden lace, hannun ta ɗauke da jikkar ta, cikin mutun ta juna ta isa ga motar ƙanin mijin nata, yayin da shima ya fasa shiga motar ya nufe ta suka shiga gaisawa.
Sai bayan da suka gama gaisawar ne sannan ta nufi sashen Umma dake tsaye tana iya hangen su.
Ɗan runguma juna sukayi, alamun gaisawa sannan suka rankaya cikin falon gabaki ɗaya, yayin da motar alhaji Mustaphan ƙirar Range Rover 2019 fara ƙar ta sanya kai ta fice daga cikin tanƙamemen gidan.
Hajiya Kubra da take tsaye jikin window ɗinta ta ɗaki daga upstair ta saki labule tana mai komawa baya, cikin ƙutawa take faɗin "ayi dai mu gani maciya amana"
Bayan ƴan gaishe gaishe irin na mata, Umman tawa ta buƙaci ta kawo ma Hajiya Zainab ɗin kayan breakfast, Amman sai tace a'a wlh sauri takeyi zata wuce ne. Dama akwai Abunda ya kawo ta ma yanzu.
Cikin kulawa Umman tawa take kallon ta.
"Umman Suhan, akan maganar yaran nan ne, ina roƙon ki da girman Allah ki amince masu su auri junan su, shi Al'ameen ɗin yaje mani da maganar wai kin hana, saboda mahaifiyar shi, haba Maryama, mahaifiyar shi ce zata zauna da ita ko shine zai zauna da ita? Ba'a aure ita aka aure ta? Ina ce itama ita taga Alhaji Mustaphan ta nuna tana son shi? Don haka ni banga abun hanawa anan ba, yara dai suna son junan su, ba tin yanzu ba, tin lokacin da aka fara kawo maganar auren su Hafsatu shima yace Suhanan yake so, aka dakatar dashi, wanda tin lokacin ni banji daɗi ba, tinda yaro yace aure yake so, kuma ga wadda yake so ba sai a bashi ba? Ko yarinyar ce tace bata yi?"
Ta ƙarashe da jefa ma umma tambaya.
Ita dariya ma abun ya bata, gaskiya ba abunda zata iya cewa da waɗannan mutanen sai godiya, ƙauna dai sun nuna mata ita, ita da yarinyar ta, har wani lokaci ta kan ji babu abunda zasu iya nema a wurin ta, ta kasa basu.
"To Alhaji Auwalu ne ya turo ni, yace inzo da kaina, kuma saƙo ne, muna neman auren Suhanan, don Allah ki bamu asamu ayi a wuce wurin, duk abunda zai biyo baya a shirye muke da mu ɗauka, indai mun samu anba yaron namu"
Da murmushi Umman ke kallon ta, sai kuma ta shiga cewa "A hajiya Zainab ya da haka kuma? Ba komai Allah ya shige mana gaba, Allah kuma ya zaɓa Abunda yafi zama alkhairi, ai Muhammadu yaron kirki ne, kuma yaro ne nutsattse Sam ba don komai na hana ba, sai don gudun zagin mutane, da kuma siya ma ita Suhanan mutunci, bana so ta sake shiga wani halin ƙunci kuma anan gaba, Shiyasa ma na amsa ma Wancen yaron malamin su, Amman tinda anyi haka Allah muke roƙo da ya shige mana gaba."
Farinciki fal a ran Hajiya Zainab ɗin take cewa" Yo wace irin maganar mutane kuma? Mutanen yanzu da idan kika biye ma faɗar su babu abun ariziƙin da za'a ƙulla, ki ƙyale su duk wanda bai zaga ba, bai shirya bane" sai kuma ta miƙe tana faɗin" yauwa ko ke fa ƙanwata? Allah ya basu zaman lafiya, kar ki wani damu, insha Allahu auren nan alkhairi ne a tattare damu baki ɗaya, nabarki lafiya, bari in leƙa sashen Kubra ɗin sai in wuce"
Itama Umman miƙewa tayi tana faɗin "to ko in raka ki ne?"
"a'a wallahi yi zaman ki, bari inje ai sauri ma nakeyi, itama dai don kar ace nazo gidan ne ban shiga ba mun gaisa"
Duk da haka har saida ta raka ta ƙofar falo, sannan ta koma ciki, yayin da Hajiya Zainab ɗin ta wuce sashen Hajiya Kubra.
Bakin gado ta koma ta zauna, tana tunano halin karamci irin na Ammi, gashi bata da wayar ta balle ta kira ta ta bata haƙurin yanda al'amari ya juye lokaci ɗaya, su duka ta tausaya masu, masalan ma shi Salim ɗin da ta kula yana ƙaunar Suhanan da zuciya ɗaya.
Runtse idanun ta tayi, tana mai kwararo ma Suhanan addu'ar zaɓin Alkhairi a cikin Al'amarin.
Ta daɗe tana sallama a sahen, sai cen ne Afnan ɗin ta fito, ga alamu ma bacci takeyi, don kayan bacci ne a jikin nata.
Cikin fara'a ta ƙara so tana gaida Hajiya Zainab ɗin.
Sai kuma ga Aunt Feena ɗauke da nasreem, jaye da Ayan, itama gaishe ta ta shiga yi cikin girmamawa.
Cikin jin daɗi Afnan ɗin take ce ma hajiya Zainab ɗin, bari taje ta kirawo Mom ɗin tasu.
To tace mata, tana mai zama ta ɗauki Nasreem tana mata wasa, tana ce ma Ayan mijin da babu cefane kyaun shi bola
Cikin fara'a suka shiga ƴar fira da Aunt Feena ɗin, ita mace ce da abubuwan duniya basu cika shan kanta ba, bata cika kula da abubuwa ba, saidai wani lokaci halin Mom ɗin tata kan ɗanyi tasiri a kanta, shima ba wai yarda takeyi ba duka, saidai halin ɗa da mahaifi, wasu abubuwan idan Mom ɗin ta cika faɗa kan yi mata zafi, duk da itama wani lokaci bata mara wa Mom ɗin tata baya.
Afnan ce ta sauko tana mai faɗin "Tace tana zuwa"
Da to Hajiya Zainab ɗin ta bita, itama zama tayi suna ɗan fira, har ake zancen Hafsat, suna so ne zasu je gidan nata kafin su wuce.
Har kusan rabin awa, Hajiya Kubran bata sauko ba, har Hajiya Zainab ɗin ta miƙe cikin ƙunar zuciya, tana mai cewa su gaida Mom ɗin tasu idan ta sauko, sai kuma gata, cikin takun ta na isassu take saukowa daga bisa matattakalar.
Bisa wata kujera mai cin mutum ɗaya tayi ma kanta mazauni.
Hajiya Zainab ɗince ta fara gaida ta cikin sakewa.
Cikin shan ƙamshi take amsawa kaman wadda akayi ma dole.
Sai kuma ta maida kallon ta kan su Aunt Feena ɗin da suke zaune, alamun su bata wuri.
Cikin mutuwar jiki su duka suka miƙe suna mai ficewa harabar gidan, basa so Mom ɗin tasu ne ta yima Hajiya Zainab ɗin wani abu, ko ba komai dai gaba take da ita, kuma Hajiya Zainab ɗin ba mace bace mai yawan damuwa da al'amurran kowa ba, tana da matuƙar sauƙin kai, sannan ga girma da ya fara kama ta, duk da cewa wani lokaci hutu baya bari a gane.
Mom ɗin ce ta maida kallon ta kan Hajiya zainab ɗin da take ƙoƙarin miƙewa.
"Dakata Hajiya Zainab, bana son sake ganin ƙafar ki cikin gida na, haka duk wanda ya dangance ki, kun yi ma Alhaji aure cin amana kun ji daɗi? , saidai ina so ku sani, Abunda zai biyo baya ba zai taɓa maku daɗi ba, kunyi matuƙar kuskure, kun manta wacece Kubra ne, ba wanda ya isa yaja dani ko ya taka ni, don haka bana son munafunci ki kiyaye shigo mani gida... "
Murmushi Hajiya Zainab ɗin ta saki, tana mai gyara zaman gyalen ta bisa kanta, sai kuma ta shiga takawa a hankali har gaban Hajiya Kubran da take zaune bisa kujera.
" Kubra kenan, ba zance ma Hajiyar ba, kin manta ne, kin manta nan gidan ƙanen miji na ne, kin manta nan ba gidan ki bane, kaman yanda nake da masani yar babu ko sisin ki acikin ginin gidan nan, ke baki isa ki hanani shigowa gidan nan ba, saidai idan kika ce kada in shigo sashen ki, wannan bana da ja akai, saboda mallaki ki ne, kuma ki sani dama cen ba don ke nake zuwa gidan nan ba, saboda mijin ki, Ayanzu kuma zan shigo ne saboda mutum biyu *Mijinki da kuma Kishiyarki* a domin haka, ki sani shigowa yanzu ma na fara, kiyi Abunda kike ganin zaki iya yi, kin manta bana neman komai a wajen ki ne, kin manta duk Abunda kike taƙama dashi baki kai mai gidan naki ba, Amman shi haka kika ga yanayi? Saboda me yasa baya yin haka? Saboda shi ya san kima da darajar ƴan adam, kuma ya san ba shine yaba kanshi ba, kuma kema yanzu baki wuce ya ƙwace ya ba ma wanda kike ganin bai kai ba, ko bai isa ba. Kince mun ma Alhaji Mustapha aure, eh lallai aure fa anyi, kuma nan gani nan bari, ba abunda kuka isa kiyi, da ana tausaya maki, ashe ke ɗin ba abar tausayi bace, mu ba mune muka ce kada ki tsaya ki kula da mijin naki ba, kina nan zaune, Maryama zata ƙwace Alhaji da duk wanda yake tare da Alhaji ki rubuta ki ajiye. Amman shigowa gida yanzu ne ma muka fara, tinda yanzu ne zamu san munje gida ba kango ba"
Kuttttt
Hajiya Zainab yau ita ce ta zage tana zuba ruwan bala'i haka? Lallai mai haƙuri bai iya zuciya ba.
Da mamaki ita kanta Hajiya Kubran take kallon ta, ita dai a iya zaman ta da ita, ba zata taɓa cewa ga ranar da taga tayi faɗa ba.
Tana gama faɗar haka kuma ta juya tana mai saɓar jikkar ta, ta nufi ƙofa da niyyar ficewa.
"Ke kika ɗauke ta a matsayin kishiya, bata isa ta mallaki mijina ba, na auren saurayi da budurwa ba ta zauna lafiya, wallahi zaku san dani kuke yi dukanku"
Ta faɗa daidai lokacin da Hajiya Zainab ɗin zata fice daga sashen nata.
Itama bata ce komai ba, ta idasa ficewa tana sakin dariya.
Afnan dake shilla Ayan a shillo, yayin da Aunt Feena take zaune ɗauke da Nasreem da har tayi bacci a jikin ta, bisa wani ɗan dandamali da akayi da zallar kankare, hankalin ta yana a kan sashen Mom ɗin tasu, don tasan komai zai iya faruwa, har yanzu Mom ɗin tasu bata huce ba, tinda gashi tin ranar ta kankara masu worning akan zuwa sashen Umman, duk yanda Afnan ɗin taso akan taje, tin kafin ma Suhan ta koma makarantar, Amman dole ta haƙura, koda suka sanar da Dad ɗin ma cewa yayi, su dakata har sai komai ya koma normal sun dinga shiga.
Hango Hajiya Zainab ɗinne, yayi sanadin tasowar Aunt Feena ɗin, ta nufo ta tana mai mata magana.
Bata share ta ba itama, haka suka jera har zuwa bakin motar Hajiya Zainab ɗin, har ta shiga motar ta tabar gidan cike da tausaya ma ƴaƴan Hajiya Kubran, masalan ma Al'ameen, Feena Afnan da Abie da yake cen american ɗin.
*********
Hankali na fa ya tashi matuƙa, gashi tun ina kiran shi tana shiga, har ta koma ma tabar shiga, a'a wai meke faruwa ne?
Haka su Khadeen suka dawo suka tada ni jiki a mace, tambaya ta suka shiga yi, banda zaɓi illa shaida masu, ko ba komai ina buƙatar wanda zamu tattauna dashi.
Suma hankalin su ya tashi, Amman sai suka shiga kwantar mani da hankali.
Jinsu dai kawai nakeyi, Amman bana cikin natsuwa
Waya ta ce dake saman cinya ta ta ɗauki tsuwwa, alamun saƙo ya shigo, da sauri na wawura in gani ko shine.
Saƙon MTN ne, hakan ya sanya nayi wurgi da wayar bisa gado, aikin banza ma kenan, su MTN ɗinnan basa gajiya da shirme, sai a lokacin da kake tunanin ganin alert ko wani muhimmin saƙo ne zasu ke damun ka da ture turen banzan su.
Miƙewa nayi ina mai ficewa daga ɗakin, komai ya dagule mani, gabaki ɗaya duniyar ta mani ƙut, ya kamata ace ko ba komai Salim ɗin ya ɗauki waya ta.
Magriba ta riga tayi, dole na shiga ɗakin na ɗaura alwala, yau fuska ta ko mai bata gani ba, tin dai bayan da nayi wanka na zura kaya na shikenan, ban tashi daga bisa sallayar ba, har aka yi isha'i.
Saida na gabatar da duka salloli na, sannan na miƙe ina mai naɗe sallayar, wanka na shiga, watsa ruwa nayi, koda zanji sauƙi.
Su khadee an duƙufa da karatu, sai gashi cikin sa'a akwai wutar nepa kuma.
Suma basu kuma ceman komai ba, sai karatun su da suke yi, ganin bana cikin Mood ne ya sanya suka ƙyalenin, har in warware sana.
Kwanciya nayi ina mai jawo littafi na, saidai babu abunda yake shiga kwalwa ta, hakan ne ya sanya ni ajiyewa na shiga jan bargo na lulluɓe jikina duka.
Wayata na jawo da niyyar kashewa, sai na hango ɗan akwati maƙale saman wayar, alamun ina da saƙo, kaman in share, sai zuciya ta ta gaza daurewa "Idan Sir Salim ne fa?" zuciya ta ta raya mani.
Buɗewa na shiga yi a hankali.
Yana yin tsarin Rubutun, da kyawun shi ne suka ɗauki hankalina, na gaza wucewa ban karanta ba.
Rubutun turanci ne a tsare, cikin grammer mai kyau, ga words ɗin sun tsaru iya matuƙa.
Ga Abunda ya rubuta.
_"Zuciya ta bata laƙanta man son abu, muddin tasan ba zata samu ba, ina mai yi maki albishir da cewa Alhaji, Umma da kowa da kowa sun yarda sun amince da auren namu. Ki shirya ma karɓar soyayya ta a koda yaushe, salon ta daban ne, kaman yanda ke ɗin kike daban a cikin zuciya ta. Ina alfahari da samun ki a matsayin uwar ƴaƴana. Kiyi bacci cikin natsuwa, ina fatan zakiyi mafarki na"_
Wuuuuuuuuu
Ai bansan lokacin da na duro daga bisa gadon ba, Sir Salim ne, Sir Salim ya turo mani saƙo, Su Dad sun yarda.
Abunda nake faɗa kenan, ina tsaye tsakiyar ɗaki kaman wadda akayi ma allurar tsayuwa.
Dukansu litattafan nasu suka ajiye, suna mai tasowa domin duba saƙon, sannan suka rungume ni suna mai faɗin
"wow Suhan, waɗannan zafafan kalamai haka? Wallahi sun tafi da imanin mu, dama haka Malam ya iya kalamai?"
Komawa nayi bisa gadon, ina mai zama, cikin tsabar farinciki, gashi gabana dai bai bar faɗuwa ba, amman murnar da nake ciki ta hana ni kula ko ankara.
Ba da numb shi ba kenan yayo mani saƙon.
Abunda zuciya ta ta raya mani kenan, ƙoƙarin kiran layin nakeyi, Amman ana faɗa man ba zai iya shiga ba. Layin shi na ainahi na kira, ya shiga Amman ba'a ɗaga ba, ban damu ba, sai ma sake sakin murmushi da nayi ina mai cewa "Ƙila wani abu yake yi."
A haka muka zauna muna ta fira mai daɗi da su Khadeen da suka kula ina cikin farinciki.....
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~50~*
_Kai gaskiya *masoyan banfi ƙarfin ta ba* ina matuƙar farin ciki daku, ba zan iya lissafi sunayen ku ba da ɗaiɗai, Amman in kinsan kina ciki, tau bansan irin godiyar da zanyi maku ba, ina ganin ruwan comment, kuna ƙayatar da Oum-Deedat. Nagode kwarai Allah ya saka maku da alkhairi, ya bar ƙauna, fatan za'a dinga faɗa mana kura kuran mu, saboda shi ɗan adam a ko'ina yake ajizi ne, tara yake bai cika goma ba_
*Gaisuwa ga ɗaukacin ƴan golden pen Writers Association, da bazarku nake taka rawa a ko'ina kuke a faɗin duniya. Allah ya ƙara haɗa kawunan mu, ya kauda idon maƙiya da mahassada. Ameen ya Rab*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Bacci fa mai daɗi na kwashe shi yau, har saida su khadee suka tada ni.
Ko bayan dai da na tashi walwalar bata bar fuska ta ba, haka nayi salla nayi wanka, da yake muna da lecture ɗin safe, tea kawai na iya kurɓa na fice ɗauke da tsantsar farin ciki.
Ina hanya ne wani text ɗin ya sake shigowa.
Ganin number ɗin jiya ce, ya sanya ni dakatawa daga tafiyar da nakeyi
A hankali na ƙara hasken waya ta, ta yanda zan iya ganin komai tar. Sannan na buɗe
_Abubuwa biyu ne suka assasa man barci mai daɗi a daren jiyan, amincewar Umma da Dad, yanzu kuma abu ɗaya ne zai raya wannan hasken ranar ta yau a gareni, ganin fuskar tauraruwar tawa, ki shirya ma zuwa na a koda yaushe. Take care with my love_
Cikin tsabar murmushi, har ƴar siririyar wushiryata ta bayyana, nake kallon wayar.
Saida na kuma tusa karanta abunda ya rubuta, sannan na samu bisa wani block na zauna, jikina duk ya mutu tsabar farin ciki.
Ta ina Sir Salim ya iya waɗannan kalaman tun tuni bai taɓa yi mani irin su ba sai yanzu.
Kenan Sir Salim ɗin zai dawo ayau kenan?
Cikin hanzari na kuma miƙewa na isa ga hall ɗin namu, Allah ma ya taimake ni lecture ɗita 8-10 ce sai kuma 12-2.
Ina da isassshen lokacin da zan iya komawa ɗakin ma har inyi wanka, don dai nasan sai marece yake zuwa shi.
Yau kam na fahimci lecture ɗin sosai, abokiyar zaman tawa mai suna Sumy itama kuwa ta fahimci hakan, har take tambaya ta minene sirrin fara'ar tawa ta yau, murmushi kawai nayi mata bance da ita komai ba.
Har muka gama kaf lecture ɗin tamu, sannan na nufo hostel.
Daf da zan ƙarasa hanyar da zata sada ni da ɗakin namu ne na hango tsayawar motar tashi.
To fa, ashe da wuri zai zo?
Kallon jiki na na sake yi, atamfa ce jikina ɗinkin riga da skirt, sai hijab ɗita kalar atamfar, Amman ba mai tsawo bace sosai, domin da kaɗan ta wuce hannuwa na.
Ba kwalliya ko laƙo a saman fuskar tawa, to saidai ba sabon abu bane a wajen Sir Salim ɗin ganina a haka, saboda ko lokacin da ya ganni ma yace yana sona, bai ganni da kwalliya a fuska ba.
Ja nayi na tsaya jikin wata bishiya haka mai ƴar inuwa.
Tafe yake cikin shadda saƙar gizna, na kula yana bala'n son shadda gizna, ba yabo ba fallasa yake nufo inda nake tsaye bayan ya kulle motar.
Ɗalibai sai gaishe shi suke yi, Amman da hannu kawai yake iya amsa masu.
Haka ya ƙara so inda nake tsaye, sadde da kaina ƙasa, ko ido ma na kasa bari mu haɗa, bansan dalili ba, yau Kunyar tashi da nake ji a jikina, ta linka wadda nake ji ada cen baya sau kusan goma.
Wai wannan shine wanda zan aura? Mijina uban ƴaƴana, kalaman da ya faɗa jiya ne suka sake dawo mani, sai kuma wanda ya turo mani ɗazu da safe.
Gefen hijab ɗita na jawo ina mai ɗan rufe fuska ta, haɗi da ɗan juyawa haka.
Da mamaki yake binta da kallo, Kaman ma fa bata san Abunda ke faruwa ba, muryarta ya tsinkayo tana mai gaishe shi.
"Sir Ina yini? Ya hanya? Ya su Ammi?"
Duk ta jero mashi tambayar, Amman fuskar ta har yanzu a rufe take, duk iya yanda zaiyi su haɗa idanu taƙi bashi wannan damar.
"Suna lafiya Suhan, Ammi tace a gaida mata ke sosai, ina so ne zamuyi wata magana, ina sauri ne zan wuce"
A ɗan mamakance na juyo ina mai kallon shi, to ai dole inyi mamaki, Suhan fa ya kira ni kai tsaye, kuma wai yana sauri, ba kasafai yake faɗa man haka ba, wani lokaci har nice ma zan ƙagara ya tafi saboda in samu inje in huta.
Gashi Sam wannan zaulayar, da walwalar da na saba gani a saman fuskar tashi, yanzu duk sun kau, babu ko ɗaya a cikin su.
Tsayuwa ta na ɗan gyara ina cewa "To Malam"
"Muje ko?" ya faɗa yana mai nuna mani wasu ƴan kujeru da take na zaman student saboda karatu, ƙarƙashin wata bishiya.
Kunya duk ta kama ni, yanzu a tsakiyar makaranta zamu zauna mu tattauna ɗin?
Saidai ban mashi musu ba na shiga bin bayan shi.
Zama yayi, yana mai ɗan tura mani kujera ɗan nesa kaɗan dashi.
Ja nayi na zauna, ina mai tattara dukkanin natsuwa ta a kanshi.
Ganin hakan, sai bai ɓata ma kanshi lokaci ba ya shiga kora mani jawabi.
"Watau Suhan iyaye na sunje gidan ku, sun samu mahaifan ki, Naji daɗin yanda komai ya faru, basu yi wani ɓoye ɓoye ba suka shaida masu cewa sunyi maki miji, saboda haka suna mana addu'a da fatan alkhairi..."
A firgice na ɗago ina mai kallon shi, lokaci guda kuma ina mai ƙoƙarin tashi daga zaunen da nake, ji nayi kaman an buga mani guduma a tsakar kai.
Da hannu yayi mani alamun da in dakata, sannan yace" koma ki zauna, ai ban gama ba"
"a zahirin gaskiya Suhan na soki, na ƙaunace ki, saidai ina ganin hakan shine yafi alkhairi, domin dama kullum zaɓin alkhairin muke addu'a, banso rabuwa dake a wannan yanayn ba, saidai bana da yanda zanyi, bana son shiga tsakanin ki da mahaifan ki, bana kuma so a dalili na ki bijire ma umurnn su, don haka kiyi biyayya, indai nine Salim, to *Na anye maganar aure na dake* saidai bana fata hakan ya shafi zumuncn mu, ko da yaushe kike buƙatar taimako a makarantar nan, ƙofa a buɗe take, kizo ki same ni, insha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na magance maki ita, don Allah Suhan ki amshi zaɓin iyayen ki, wata ƙila shine mafi Alkhairi a gare ki. Ammi tace in bata ke a waya zakuyi magana"
Ya faɗa yana mai zaro wayar shi, ya shiga kiran layin Ammi ɗin.
Nidai kawai zaune nake kaman mutum mutumi, to kenan ba shine ya turo mani text ba jiya, kenan wanda suka zaɓa mani ne? To ta yaya? Ta ina ya samu layi na?
Cen na tsinkayo muryar shi suna gaisawa da Ammi ɗin, sai kuma ya shiga cewa "to Ammi gata"
A hankali na miƙa hannu na ina mai amsa na kara a kunne, sai kuma na fashe da kuka, shiru Ammi tayi tana mai saurare na, saida nayi mai isa ta, Allah ya soni ma an shiga lecture ɗin 2,ɗaliban ƴan tsuraru ne suke wucewa, suna ɗaga ma Sir Salim ɗin hannu, wanda shi hankalin shi ma Sam baya kaiwa kansu.
Sai da nayi mai isa ta, sannan na tsagaita, bansan ko kukan menene ba, idanuna sunyi jawur, haka fuska ta, kaman wadda aka faffalawa mari, abun ka da farar fata.
"Ya isa hakanan Suhana ta, yi shiru goge hawayen muyi magana"
Ammi ɗin wadda take zaune a tanƙamemen falon nata bisa wata sofa mai kyau, ta faɗa.
Share hawayen nayi, ina mai jan majina a hankali, sai kuma nace "Ammi ina yini?" cikin karyayyar murya da tasha kuka.
Saida ta ɗan runtse idanun nata, kukan nawa ya taɓa mata har cikin zuciya, wannan ke tabbatar mata da cewa Salim ɗin ya faɗa man komai, kuma hakan ya ƙara tabbatar mata da nima ina son yaron nata.
"Suhan haƙuri zakuyi ku dukanku, ƙaddara ta riga fata, dama cen Allah bai rubuta ke matar Salim bace, Allah ya sani mun soki, mun ƙaunaceki da zuciya ɗaya, tin jiya naso in kira ki, nayi tunanin gara ki fara ji daga bakin shi, kinsan zuciya bata da ƙashi, mun san ba laifi ki bane, haka kuma mun san ba yaudara bace, ke ɗiya ta ce Suhan, ko baki auri yaro na ba, inaso ki ɗauke ni a matsayin uwa, zan zame maki gata Suhan, zan zame maki kaman Umman ki insha Allahu, a koda yaushe muna tare dake a rayuwa, yanzu abunda nake so dake shine, ki amshi zaɓin iyayen ki, kada ki sake kice zaki bijire masu, saboda soyayya, kada ki sake ki rabu da iyayen ki akan ɗa namiji, su kansu wani lokacin basa da tabbas, koda yake ɗanɗa na, ba zan iya bada shedar shi ba 100% saboda batare dashi nake kwana nake tashi ba, saidai zan iya bada shaidar wasu daga cikin halayen shi, kasancewa ta uwa a gareshi, uwa kuma mai kula da al'amurran yaran ta. Suhan insha Allahu ba zaki yi nadamar zaɓin iyayen naki ba. Don haka nake baki shawarar da kibi Allah kibi iyayen ki, kiyi haƙuri kibar kuka, Allah zai baki wanda yafi Salim komai da izinin Allah"
Ta tsagaita cikin tausasawa, sai kuma itama zuciyar ta ta karye, bata bari na fahimci haka ba, ta shiga ƙara kwantar mani da hankali, har saida taji ina mai ɗan sauke ajiyar zuciya cikin wayar a hankali a hankali.
Mun ɗau tsawon lokaci tana bani baki, har saida na gaji da riƙe wayar a kunne na.
Sallama tayi mani, bayan na shiga zuba mata godiya, ina ƙaunar matar har cikin zuciya ta, baya ga Ummata banga matar da take mani ƙauna irin wanna ba, bayan bamu haɗa komai da ita ba, sai soyayya da ɗanɗan nata.
Cewa tayi in bashi wayar.
Miƙa mashi nayi, ina mai ƙara share hawayen da har yanzu sun kasa tsayawa a fuskar tawa.
Amsa yayi shima, kamar ya zuba kuka, ganina da yayi gaban shi, gashi ina kukan rabuwa dashi, hakan sai ya ƙara katse mashi jijiyoyi, ji yake kaman yace bai yarda ba, ji yake kaman ya tashi yaje gidan namu da kanshi ya samu Umman tawa, duk da dai ya san iyayen nashi ba zasuyi mashi ƙarya ba.
Shima sun ɗau tsawon wani lokaci suna waya sannan ya katse wayar yana mai maidata aljihu.
Yanzu na ƙara tabbatar wa, saƙon jiya da na yau ba shine ya turo mani ba.
*Zaɓin iyaye na* shine ya turo mani saƙon kenan, wanda zan iya kiran shi da *ɓoyayyen masoyi*
Hankalina na maida kanshi, ganin ya miƙe saboda ɗalibai da suka fara fitowa daga lecture suna kallon mu.
"Suhan zan tafi, Allah ya haɗa kowa da rabon shi na Alkhairi, don Allah ki ɗauke ni a matsayin yayanki uwa ɗaya uba ɗaya a makarantar nan, bana so ki ɗora ma kanki laifi da damuwa har hakan ya shafi karatun naki. Ina sonki har cikin raina" yana gama faɗar haka ya juya ya nufi motar tashi,ba tare da ya bani damar cewa wani abu ba.
Saidai ya kasa tashin motar tin bayan shigar shi ciki.
Kanshi ya ɗora saman steary, wani irin ƙululun abu ne yake jin yana mashi sama da ƙasa a cikin maƙoshi, ɓacin rai zalla, sai yanzu yake jin wasu ɓoyayyu hawayen soyayya na tsattsafowa daga kwarmin idanun nashi.
Yana iya hango ta, ita kanta har yanzu ta kasa tashi daga wurin, lokaci zuwa lokaci takan sanya hijabin ta tana share kwallar ta, da yake university ce, saidai a kalle ta a ɗauke kai, waɗanda suke tsaye suna kallo na basu da yawa.
Ganin an fara taruwa ne ya sanya ni miƙewa jiki a sanyaye da niyyar barin wurin.
Wasu jibga jibgan mktooci ne suka yo shigar burgu zuwa harabar makarantar a guje, ƙurar su kawai kake iya hangowa, saidai daf da zasuyi parking sai kuma suka rage gudun su, zuwa a hankali a hankali.
Ban iya cewa ga sunan motocin, saidai ni kaina nasan a irin fina-finan ƙetare ne kawai nake ganin irin su.
Motoci uku ne, guda biyu watau ta gaban da ta bayan dukan su farare ne sal, sai kuma ta tsakiyan da ta kasance ɓaka wuluk, a tare suka yi parking a kuma jere, da gudu naga wasu irin bodyguard suna fitowa zuwa jikin baƙar motar domin su ba mai fitowa daga ciki kariya da kuma tsaro.
Sai wasu mutane masu saye da rigunan fadawa suma riƙe da bulalai irin na dorina, sai zare idanu suke yi.
Kallo fa ya koma sama.
Anyi cirko cirko zaman jiran wanda zai fito daga cikin wannan motar da ta riga ta tafi da imanin kowa dake faɗin makarantar.
Sai da na kusa faɗuwa, gani wani bodyguard guɗa ɗaya, da hannun shi ke riƙe da ƴar bindiga ya sanya hannun shi ya buɗe bayan motar.
Ganin wanda ya fito daga cikin motar ne, ya sanya ni ƙara wara idanu na akan shi.
*ya Ameen* na furta cen ƙasan maƙoshi, ina mai ƙara ƙwalalo idanu na, kaman zasu faɗo ƙasa, lokaci guda litattafan hannuna suka sulale zuwa ƙasa.
Sanye yake cikin wasu irin baƙaƙen suit, hatta da takalmin da yake ƙafar shi cover shoes baƙaƙe ne, sai ɗaukar idanu suke yi da walwali.
Fuskar shi Sanye take da wani irin baƙin Sun Glass, da baka iya hangen kwayar idanun nashi.
Hakan ce taba farar fatar shi daman sheƙi da walwali.
Gashin kanshi kwance yake luf luf,har zuwa saman wuyan shi, duk da kan nashi babu aski saidai gyaran fuska, kai in ka kalle shi sai kace ya haɗa iri da fararen Larabawa ko kuma indiyawa.
Kai tsaye idanun shi bisa ni suka sauka, hakan ce ta bashi damar fara takowa a hankali kuma cikin ɗan sauri sauri da zafin nama irin na cikakken namiji.
"wow, wow, Al'ameen dambulan, yariman matasa"
Abunda naji wasu ƴan mata dake kusa dani sun faɗa kenan, suna mai zuba mashi dukkanin idanun su.
Shima Sir Salim dake zaune cikin mota, y kasa tuƙawa balle ya bar wurin, hankalin shi ne ya kai kan motocin tin shigowar su, gabaki ɗaya an rubuta *Yariman Matasa* a jikin number ɗin motocin.
Kallon shi ya sake kaiwa inda nake zaune, domin ko ba komai ya san wurina suka zo, tinda ƴan gidan mu ne.
Ga mamakin shi nima tsaye nake, ga litattafai na a ƙasa yashe, har kai lokacin da Al'ameen ɗin ke takawa yana nufar inda nake tsaye, watau inda Sir Salim ɗin ya barni zaune.
Bodyguard guda biyu ke biye dashi, sai fadawan da suke biye dashi da ɗan guntun gudun shi, da niyyar su isa su gyara mashi wurin da zai zauna, hannun ɗaya daga ciki riƙe da wata irin kujera da ake naɗewa kaman keke mai masifar kyau.
Har yanzu dai da kallo nake binshi, bakina a sake, kaman gaula, ya koma mani Ya Ameen ɗin da na sani tin cen baya.
Wannan comvoy ɗin duk na menene? Ƙila hanya ce ta kawo shi, shine ya biyo ya ganni, to amman duka yaushe ya kawo ni? Duka yaushe muka rabu?
Bansan ya ƙara so inda nake tsaye ba, sai ƙamshin mayataccen turaren shi Naji a kusa dani.
Fuskar nan ba yabo ba fallasa, duk da har yanzu tana ƙunshe cikin Glass ne.
Kujerar suka warware haɗi da ajiye mashi suna mai matsar da tawa kusa da wadda suka ajiye.
Da hannu ya dakatar dasu, yana mai faɗin "you can go"
Baya sukayi su duka, suna mai komawa jikin motocin, hadda dogarawan kuwa.
Sai kuma abun ya ƙara ba student mamaki, ai su duk a tunanin su wajen VC yazo, sai kuma suka ga ya dakata a wajen da nake tsaye.
Su kuma sun san alaƙa ta da Sir Salim, kuma ga shi cen tsaye bakin motar shi, yana iya hangen dukkan abunda ke faruwa.
Ai sai suka zuba mana idanu, kunsan ƴan makaranta da gulma, gashi kusan ƙarfe huɗu duk sun firfito.
Hatta dai da su Raihana da Khadeejan tsaye suke suma sun zuba ma sarautr Allah idanu.
Kujerar da suka ajiye mashi, ita ya ɗauka ya ajiye mani, sannan ya duƙa ya shiga tattara mani litattafai na da suke ƙasa, ya aza su bisa ɗan table ɗin, yana mai jawo kujerar da suka ajiye mani ya zauna.
"Zauna mana malama, ko Soja ce ban sani ba? Kina wani kallo na kaman kinga baƙon ki"
Ya faɗa cikin basarwa, kaman ba shine yayi maganar ba.
Banda zaɓi illa zaman.
Kaman sauna dai, haka kuma nake kallon shi, ga idanuna da sukayi luhu-luhu tsabar kuka.
Wayar shi ya zaro yana mai latsawa, kaman ya manta dani a wajen.
"ina yini?
Na furta a hankali kaman wadda bata son yin maganar.
Bai bar latsa wayar ba, haka ma bai amsa mani gaisuwar da nayi mashi ba.
Sai cen ne naji yace " ai na ɗauka baki Iya gaisuwa ba"
Da mamaki nake kallon shi, au Shiyasa bai amsa mani ba?
Sadda kaina ƙasa nayi ina mai ɗan sakin ajiyar zuciya.
Ganin ba zan tanka ba, sai ya ajiye wayar bisa ɗan teburin dake gaban mu. Sannan ya maido hankalin shi a kaina.
"Bakiga text ɗina ba jiya da yau?" ya furta yana mai zare Glass ɗin idanun shi.
"Na gani Yaya"
Na faɗa nima a hankali.
"Meyasa baki yi mani reply ba? Ko bani da amsa ne? Ke yaushe ne zaki bar ƙauyanci ne?"
Ya faɗa still shima dai kaman ba shine yayi maganar ba.
Ɗan kallon inda student suke tsaye nayi, kunya duk ta baibayeni.
Sai kuma na maida kallo na kan Sir Salim da yake tsaye jingine jikin mota, kaman an dasa shi, mu kawai ya zuba ma idanu.
Ganin inda nake kallo ne, ya sanya shi shima maida idanun shi wurin.
"Oooh! Wancen shine saurayin naki da aka je nema mashi auren matata jiya?"
Ya faɗa cikin I dont care tune.
Sadda kaina na kuma yi ƙasa ba tare da nace mashi komai ba.
Salon da yayi ya matuƙar burge ƴan matan dake tsaye, kowacce tana fata da burin ina ma ace ta mallaki ya Ameen ɗin.
Tsaye sukayi suna mai more ma kallon shi, wanda suke gani a gidajen talabijin yau shine a zahiri a cikin makarantar tasu.
Tsam naga ya miƙe yana nufar inda Sir Salim ɗin yake tsaye.
Hannu ya miƙa mashi sukayi musabaha.
Sai kuma yace "kaman naso in gane ka ko?"
Da mamaki Sir Salim ɗin ke kallon shi, lallai jin kan wannan gayen ma yayi yawa, watau haka dai yake kenan ko a zahiri, lokacin da suka haɗu dashi a library bai kamata ace har ya manta shi ba, da kuma duka yaushe ne suka gaisa dashi ya maido Suhan ɗin makaranta?
"Eh kwarai kuwa ka gane ni, ba kai ne yayan Suhana ba?"
"Eh kwarai kuwa nine. Malam ko?" ya furta cikin salon muryar shi da ba mata ba kaɗai har maza burge su takeyi.
"Sosai kuwa nine"
Al'ameen ɗinne ya sake bashi hannu suka gaisa, kowa da Abunda yake ƙunshe cikin zuciyar shi.
Juyawa yayi ya koma inda ya tashi, baki sake nake binshi.
Lura nayi da dogarawan sun fara korar ɗaliban da suke tsaye suna kallon mu, wanda wasu daga ciki har sun fara fiddo waya suna haska Ya Ameen ɗin.
"Nace zanzo ki shirya ma zuwan nawa, sai gashi kuma na tadda ke a haka? Me ya same ki? Kaman ma kinyi kuka ko?"
Ya faɗa cikin tsattsareni da idanun shi da suke sanya jikina ƙara sanyi.
Ɗan kallon jikin nawa na kuma yi a karo na biyu.
Sai kuma kunya ta kama ni, Amman sai na share ina mai cewa" Yaya daga lecture fa na fito yanzu, to wacce kwalliya zanyi kuma?" na faɗa cikin ɗan narkewa alamun ƴar shagwaɓa.
Da kallo yake bina. Na matuƙar burge shi.
"Bana son Yayan nan, ya zuwa yanzu nasan kin fahimci matsayi na a wajen ki, so don haka ina buƙatar a cenza mani suna"
Ni dariya ma ya bani, Amman bari ayi mashi boko, mugani idan zai iya kubce wa.
"Wanne matsayi kenan yaya? Ban fahimta ba? "
Na faɗa cikin wayancewa.
"au baki gane ba?kina so inyi abunda saisa kowa ya tabbatar da matsayin nawa ne? "
Shima ya faɗa cikin wani salon na basarwa.
Kai tsaye nace mashi "Eh" ban ko rufe baki ba, naga ya nufo fuska ta da fuskar shi, fuskantar Abunda yake niyyar yi ne ya sanya ni ja baya, ina mai faɗin "Nagane yaya, Allah na gane"
Yar dariya ya saki yana mai ɗan wayancewa ya kauda fuskar yana mai faɗin "Matsoraciya kenan, ai naso ki bari har shi Wancen saurayin malamin naki ya fahimta, duk da yanzu nasan ya riga ya janye, mai wuri yazo ai dole mai tabarma ya naɗe"
Da kallon mamaki nake binshi, wai Ya Ameen ɗin da na sani ne da kuwa?
Kaman ba shine ya saki jiki yana zaro maganganu haka ba.
To ada ma idan ance man ya iya magana haka ai bazan iya yarda ba, yo to ai ni kallon miskilanci nake mashi, ashe ba kowa yakeyi mawa ba? Ashe ba a ko'ina yake miskilin ba.
"Anyway ya kamata inyi Abunda ya kawo ni, don naga kin faɗa komar tunani."
Ya faɗa yana mai gyara zaman shi, sai kuma ya ɗan haɗe fuska, alamun maganar ba wasa a cikin ta.
Bai bani damar magana ba, sai ma cigaba yayi da cewa *"All the way from Abuja na taso yau, ba don komai ba kuma sai domin in ganki, bana buƙatar sake tambayar ki amincewa akan batun auren nawa, Amman All what i want is your Love. Soyayya nakeso mai tsafta, Soyayya mai ƙunshe da ƙauna, bana son ƙauyanci fa, zaki ajiye wannan Kunyar taki ne a gefe, saboda ni ban ganin abun Kunyar indai har muna son juna, we have to show it and prove it a gaban kowa, hakan ne zai sa iyayen mu su yarda mun amince da juna. Maganar soyayyar ki tada, ki mance da ita, ki ajiye ta gefe, salon zai cenza ne a wannan karon, I am Al'ameen Almustapha Dambulan as u know, so ba lallai ki iya ganewa ba, Amman zan iya ce maki bansan micece soyayya ba sai akan ki, bansan ya ake yin ta ba, na ɗauke ta shirme ce, na ɗauka sai marasa abun yi ne suke wata abu wai ita soyayya. Amman yanzu duk ba haka bane, na fahimci kuskure tunani na, tin shigowar ki rayuwa ta. Ina Sonki Suhan, zan aureki, kuma zan kasance tare dake a kowanne hali. Da fatan zaki bani goyon baya kema, zan bari kiyi tunani a koda yaushe zaki iya ganin na dawo, domin a yanzu na fahimci cewa garin masoyi baya nisa ko ina yake a faɗin duniya"*
Tabɗiiiiiiii
Ya Ameen ne yau zaune a gaba na, a gaban ɗumbin mutane haka yake faɗa mani irin waɗannan kalaman? Ina miskilancin? Ina sarautar? Ina haɗuwar? Ina izza da kuɗin?
"Duk ya ajiye su a gefe."
Wata zuciyar ta bani amsa.
Idanuna cikin nashi, hakan ne ya sanya ni saurin janye nawa idanun.
Ya Ameen ya haɗu iya haɗuwa, hatta da fuskar shi ba zan iya jure ma kallo ba, balle kwayar idanun nashi.
Kallona na maida wajen da motar Sir Salim take.
Baya wurin, kaman yanda ban ma ji ko tashin motar tashi ba.
A hankali na sauke kwayar idanuna gefe, sai kuma na saki wata nannauyar ajiyar zuciya kaman wadda aka shaƙe sannan aka saki.
Yakai tsawon minti biyar yana kallo na, har saida Naji kallon yayi mani yawa, ga kwayar idanuna tana yawo a ƙasa, kaman wadda take ƙoƙarin gano wani abu.
Wani Ya tafi wani Ya zo.
Ikon Allah kenan.
Lallai rayuwa tana garawa dani kaman garin tayar yaro.
Miƙewa tsaye naga yayi, yana mai ɗan sakin murmushi iya gefen baki, wanda ya ƙara ƙawata mashi fuskar tashi, lokaci guda yana mai ƙoƙarin saka glashin idanun nashi.
"Muje ki raka ni ko?" ya furta a hankali cikin wata irin salon murya, kai kace da wata sarauniya yake magana.
Ban miƙe ba, kaman yanda ban kalle shi ba.
"Kada kisa inyi Abunda zai baki kunya fa"
Ya furta cikin wani irin salo, na san zai iya aiwatar da Abunda ya faɗa ɗin.
Zumbur nayi na miƙe, ina mai kwasar litattafai na, sannan ce "To yaya muje, yi haƙuri"
Ƴar dariya ya saki, muka fara takawa a hankali yana mai ƙara gaya man wasu kalaman da ni fa ina tunanin saida ya rubuta sannan yayi haddar su.
Kai idan ka hango mu sai kace irin masoyan nan ne da suka shekara biyar suna soyayya har aka sanya masu rana.
Ko ba komai ni a wajena jerawa da Ya Ameen ɗin muyi tafiya a bigire ɗaya abun alfahari ne a wuri na, saboda haka sai na dayaye kawai, gudun kada ƴan tsogumi su fahimci halin da ake ciki.
Har bakin motar na raka shi.
Ni na buɗe mashi bayan motar, bai zauna ba, saida ya kalleni da wani irin ƙayataccen murmushi alamun ya gode, sannan ya shiga motar ya zauna yana mai kallo na.
"Nagode Gimbiya ta" ya faɗa cikin salon da ya ƙara sanyaya mani jiki.
Ɗan baya naja a hankali, har yanzu fa mamakin shi bai sake ni ba, Allah gani nakeyi kaman mafarki nakeyi, a hankali ya ɗan ɗaga man hannu alamun bye, sannan yayi salute ɗina, daidai lokacin da motocin suka juya a hankali suna mai barin cikin makarantar.
Tsaye nayi kaman wadda aka dasa, da kallo nake bin motocin har suka ɓace ma gani na, daidai lokacin da su Khadee suka ƙaraso inda nake tsaye khadeen ke faɗin
"wow Suhan wannan gayen kuma fa? Yariman matasa ne fa! Dama kin sanshi ne? Wallahi gayen ya haɗu, ya tafi da imani na, please ki haɗa ni dashi, wallahi lokaci guda son shi ya kama ni, ina yawan ganin shi a instagram, gayen yana da followers sosai wlh ga kuma naira"
A hankali na juyo ina mai maida kallona kan khadeen dake faɗin wannan kalaman.
Ga mamaki na kuma, sai kalaman nata suka bani haushi.
Bance mata ƙala ba, na shiga zagayesu ina mai wucewa kai tsaye zuwa ɗakin namu.
Zuciya ta a cunkushe, saboda na rasa ma tunanin da ya kamata inyi.
_Na tafiyar Sir Salim_
Ko
_Na zuwan Ya Ameen?_
~Toh Fans ga Suhn fa ta shiga ruɗu, ku bata shawara please~
_Please Share_
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~51~*
*Salamatu wannan Page ɗin naki ne, kaman yanda na alƙauranta, kiyi yanda kike so dashi, kuma a dinga karantawa oga shima. Nagode Allah ya bar ƙauna*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Kai tsaye ɗaki na zarce, jina fa nake kaman na wani zauce,Ya Ameen? da kanshi?
Bakin gado na samu na ɗan ɗosana.
Sai kuma me?
Tafiyar Sir Salim ke mani kai komo.
Sai kuma hango tahowar Ya Ameen with full confidence.
*"Huh"*
Na saki wani irin huci mai tare da ɗan sauti.
Daidai shigowar su Khadee ɗin.
Gani na da sukayi zaune dafe da kai, ya sanya suka nufi inda nake.
Tsakiya suka saka ni, Khadeen ce ta ruƙo mani hannuwa,sannan ta fara cewa
"Suhan kiyi haƙuri, naga kaman kinji haushi don nace ina son Yayan cen naki, Nidai nasan ba wani abu tsakanin ku, tinda maganar Sir Salim ta riga taje gidan ku, kuma ni ina ganin wannan ba wani abu bane, wanda yace yana son naka ai kai yake so, wallahi ganina dashi na farko naji ya kwanta mani, tin kafin ma in ganshi a zahiri, duk da nasan cewa yanda yake da masoya, sannan gashi da kyau uwa uba yana da kuɗi, kada kiyi tunanin dalilin da yasa nace yayi mani kenan, a'a wallahi ko ɗaya, so ne na tsakani da Allah ya kama ni a take, ki taimaka mani koda number ɗinshi ce, insha Allahu ni zan ganin nayi ƙoƙarin na kafa kaina, duk kuwa da cewa ni kaina nasan ya wuce da ajina. Amman hakanan nake sonshi, koda kuwa zai wulaƙanta ni, haka kuma koda yana da mata uku, wallahi na yarda zan shiga a ta cikon huɗun"
Ban kalle ta ba, saidai tabbas nasan kalaman ta suna ratsa zuciya ta, wani kumbura naji zuciya ta nayi, sai kuma Naji kaman ƙofofin hancina na ƙara buɗewa, kaman iskan da nake shaƙa tayi mani ƙaranci.
Raihana ce ta maida kallon ta kan Ƙawar tata, ita mamaki ma take bata, daga ganin bawan Allah sai ki ruɗe har haka a kanshi?
"Khadee ki dena faɗar haka, sanin kanki ne cewa Al'ameen dambulan har Samira ɗiyar shugaban ƙasa tace tana sonshi ya ƙiya, ke shaida ce, ko a Instagram ma mata faɗa suke akanshi, ke wallahi akwai matan auren da naji suna cewa muddin Al'ameen zai kalle su yace yana so, zasu iya kashe auren su su koma mashi, Khadee kin daɗe kina wannan maganar tin ma kafin ki ga Al'ameen a zahiri, sannan tin ma kafin kinsan yana da alaƙa da Suhana, to don Allah kibi komai a hankali, tinda yanzu kin samu link ɗin haɗuwa dashi, insha Allahu komai zai zo maki dasauƙi"
Har yanzu dai zaune nake dafe da kaina da hannu ɗaya, yayin da Khadeen ke riƙe da ɗayan.
Ganin bam tanka ba ne, ya sanya Khadeen cigaba da magana.
"Raihana kin fi kowa sanin na daɗe da ƙaunar Dambulan acikin raina, ke shaida ce, nasha gwada yi mashi magana a kafafen sadarwa amman ko dubawa ma baya yi, nasan kuma ba ni kaɗai bace, muna da yawa. Suhan please ki taimaka ma Ƙawar ki, wallahi ina cikin wani hali"
Sai a lokacin na ɗaga idanu na na kalle ta, duk tabi ta koma kalar tausayi, lallai soyayya banzar abu ce, raɗaɗin rabuwa da Salim ɗin bai sakeni ba, gashi Khadeen kuma tana tara ta da wata magana ma marar amfani.
To koni dai daya ce yana so ban gama gasgatawa ba, gani nakeyi kaman yana da wani ƙudirin daban, ƙila so yake sai Mom ɗinshi ta yanka ni, ta kakkatsa namana sannan. Ummata ma da tayi aure a gidan don bani da yadda zanyi ne.
Daƙyal na buɗe baki na da yayi mani nauyi na fara cewa.
"Khadee kiyi haƙuri don Allah, ni yanzu ba wannan ne a gabana ba, Al'ameen da kike magana kuma Sam bashi gabana, saboda bana fatan kai kaina inda Allah bai kaini ba, kuma ko ba Salim bana tunanin zan iya yadda da Al'ameen, domin kuwa ni nasan yafi ƙarfi na"
Da mamaki duk kansu suke kallo na, masalan ma Khadee da bata kai ga fahimtar inda zancen nawa ya dosa ba.
"Excuse me Suhan, wai me kike nufi ne da wannan maganar taki? Bamu fahimce ki ba fa"
Cewar Raihana da tsabar mamaki ya cika ta.
Maida kallona nayi kanta.
"Eh Raihana, ina nufin iyaye na basu yarda da maganar aure na da Sir, Salim ba, Al'ameen shine wanda suka zaɓa mani, shine suke so in aura, kuma suna fatan ace nayi masu biyayya, ko wannan zuwan da Al'ameen ɗin yayi, yazo ne wai ya bayyana mani soyayya, Abunda bana tunanin kuwa mai yuwu wa ne"
Zumbur Khadeen tayi ta miƙe daga kusa dani.
"What?, me? Me kike faɗa ne Suhan? Dambulan ne wanda zaki aura? Are u sure? Shine yazo bayyana maki soyayya kika tsaya kina tarabbabi?"
Tana gama faɗar haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice a sukwane.
Raihana ce ta maido hankalin ta kaina, tin bayan da muka raka Khadeen da kallo.
" Masha Allah Suhan nayi maki matuƙar murna, baki buƙatar wani tunani, ki amince, Al'ameen ba irin mazan da zasu ce suna son mace bane ta tsaya masu yanga ko jan aji, wasu ma neman irin tasu soyayyar suke da kuɗi basu samu ba, ƙaramn musali ki kalli Khadee, yanzu ta zama abun tausayi, ta daɗe tana dakon soyayyar shi, maganar ce dai bamu taɓa yi ba, gashi yau da ta ganshi a zahiri ji take kaman ta bishi, kaman tayi hauka, kinsan da inda kuke zata je ta same ku? Nice na hana ta? Kiyi haƙuri Suhana kibi zaɓin iyayen ki, shi kuma Sir Salim Allah ya bashi daidai shi, Amman wallahi baki buƙatar sai na faɗa maki kunfi da cewa da Dambulan"
Itama kuwa kalaman nata sun ratsa ni matuƙa, to saidai....
Kallon ta nayi, ina mai cewa "Raihana please ki gaya mani ni ba mace bace? Ban kai a soni ba? To ta yaya zai ɓullo da kalmar soyayya a gareni da niyyar cimma wata manufa tashi?"
Da mamaki take kallo na.
"Shi wa?"
Ta tambaye ni.
"ya Ameen" na bata amsa kai tsaye.
Girgiza kai ta shiga yi.
"Ke kanki Suhan kinsan idan ba don soyayya gaskiya bace, to da babu Abunda Dambulan zaiyi dake, kiyi haƙuri ba cin zarafi bane"
"Kin fi kowa sanin irin matan da suke rububi da faɗa akanshi.Sai gashi duk ya tsallake su, ya kawo kanshi gareni, so bana tunanin ma idan har zaki wani tsaya ɓata lokaci wurin amsawa"
Har yanzu fa ina tababa.
Ga wani irin mugun tausayn Sir, Salim dake ratsa mani zuciya.
Bance mata komai ba, na jawo waya ta na shiga neman number ɗinshi.
Bugu uku ya ɗaga, cikin sanyayyar murya yake ce mani
"Suhan baƙon naki har ya tafi ne?"
Ban iya bashi amsa ba, sai ma rumtse idanu da nayi.
Da mamaki Raihanan ke kallo na, bata kai ga fahimtar wanda na kira ba, saida taji ina cewa.
"Am sorry Sir, wallahi ba laifi a bane, kayi haƙuri don Allah"
Cikin wani irin yanayi, shima tausayin ta yake ji, duk da yasan cewa wanda Allah ya bata, ya fishi komai, infact ma ko abota ya samu yayi da Al'ameen abun alfaharin shi ne.
Cikin wata irin murya ya shiga cewa
"I understand Suhan, please dont burder your Self, let the bygone be gone please, bama da zaɓi illa hakan"
Bai kai ga ƙarasawa ba wani irin kuka ya ƙwace mani.
Kashe wayar nayi, ina mai faɗa wa jikin Raihana. Rungume ni tayi tana bubbuga bayana alamun lallashi.
Shi kau ta cen ɓangaren kashe wayar ma yayi baki ɗaya, ko zai samu salama acikin zuciyar shi.
Ba daɗewa dama Ammi ta kira shi ta ƙara kwantar mashi da hankali.
A haka Khadee ta dawo ɗakin ta same mu, Raihana nata lallashi na, da kallon idanun ta kuka tayi, ko ba komai tasan ta rasa Al'ameen ɗin kenan, ashe ma tana rayuwa da wadda zata zama matarshi a ɗaki guda, ba tare da ta san hakan ba. Bata ce mana ƙala ba ta haye gadon ta ta kwanta.
*********
Ƙarfe takwas a gida tayi masu, kai tsaye sashen Mom ɗinshi ya nufa, saboda duk yau basu gaisa ba, ba wanda ya tadda, su Afnan ma basa nan, sun je gidan Nihal amman driver yaje ɗauko su.
Hakan ce ta sanya shi hayewa saman zuwa ɗakin Mom ɗin kai tsaye.
Kwankwasawa yayi, daga ciki ta bashi izinin shiga.
Ita kanta bata ɗauka yaron nata bane.
Tana zaune bisa wata sofa ƙwaya ɗaya tal, da table a gaban ta, lissafi take ta faman yi, saboda busness ɗinta yanzu yanda take ta sake haɓɓaka.
Bakin kujera ya zauna kai tsaye.
Barin abunda takeyi tayi ta taso. Kusa dashi ta zauna cikin murmushi ta kamo hannun nashi tana faɗin
"Son barka da shigowa, daga ina kake haka? Naga kaman ka gaji.
Shima ɗan murmushn ya saki iya leɓo, sannan ya kamo hannuwan ta yana mai ɗan basu peck haka kaɗan
" Mom wallahi kaman kin sani, wata ƴar tafiya nayi, gashi na gaji shine kafin in kwanta nace bari inzo in ganki"
Ya faɗa a gajiye sannan da ƴar sha-gawaɓa irin ta yaran masu kuɗi.
"Ayya Son, gashi ko abinci baka ci ba kana maganar kwanciya, bari in sanya Maree ta kai maka abincin.."
"Mom! Sau nawa zance banson kina barin yarinyar nan na shiga man sashe wai? Baki ga yanda take ba? Ko tsabtar kirki fa bata da, please Mom, ina Afnan ne? Taje ta kai mani mana"
Ƴar dariya ta saki, wai wanda ke son Ƴar aiki, shine yanzu yake nuna yana ƙyamar ƴar aiki.
"Afnan basa nan, sun je gidan Nihal da Feena, Amman suna hanya, na tura driver yaje ya ɗauko su, idan ta dawo sai ta kawo maka, kada fa kayi bacci Son"
Miƙewa yayi yana faɗin "Better Mom, Good night"
Bai jira cewar ta ba, ya fice abinshi, yana mai sauka daga saman ya nufi part ɗinshi kai tsaye.
A harabar gidan ne yaci karo da Maree ɗin, sake ɗaure fuska yayi, domin ya kula yarinyar tana neman shisshige mashi, Amman soon zaiyi maganin ta ne"
Ita kuwa Maree tsaye tayi galala, kai in banda so ma yana shashasha, ita kanta tasan gayen ya wuce da iyawarta sau million ma ba sau dubu ba.
********
Saida ya gama komai, wanka da duk Abunda zaiyi, wajen cin abinci ne ma ya ɗan ɓata lokaci, saboda Afnan data zo ta tsare shi da surutu, anan ne har take ɗan faɗa mashi Hajiya Zainab tazo gidan jiya, kuma tana tunanin Mom tayi mata wani abu marar daɗi.
Sam bai ji daɗin labarin ba, komai akace Mom ɗin tashi tayi, ba zai musa ba, ya san halin ta sosai, fata dai yake yi Allah ya shirya mashi Mom ɗin tashi, domin yana matuƙar ƙaunar ta, ko dan irin yanda take nuna mashi so a fili muraran a ko ina kuma, don dai wasu halayya nata da baya so kwata kwata.
Har saida ya kulle ko ina, ya sallami bodygurd ɗin nashi da ya basu wani ɗan ƙaramn flat kusa dasu, duk da baya so yanda suke binshi ko ina zai je, Amman Mom ce da Dad suka matsa akan dole ya samu masu kula da lafiyar shi, gudun sake faruwar abunda ya faru dashi a America.
Yau kiranta yayi niyyar yi, baya jin idan text kawai zai iya bayyana mata saƙon zuciyar tashi.
Wani irin shauƙi yaje jinshi a ciki, tin bayan barowar tashi wurin ta.
Shi kaɗai sai ya samu kanshi da sakin murmushi akai akai, abunda ba halayyar shi ba kuma, koda cen idan yaga Bilal ɗin ya zage soyayya da Ummi a waya, sai ya ɗauka kaman baya da abun yi ne.
Yau gashi shine ya faɗa komar son Suhan ɗin *Abun kamar da wasa* yarinyar da ta taso gaban shi, yarinyar da yake ma kallon kaman Afnan, Saudat, ko Nihal, yau ita ce wai yake so, yana jin wani tiririn sonta na dakar mashi zuciya.
Ko bayan da ya ɗauko wayar, ya daɗe yana jujjuya ta a hannun shi, shawarar yake ko ya kira ko ya ƙyale ta, kada ta raina shi, ko taga kaman ya cika takura ne, bayan gashi ya san yaune ranar da ta rabu da Saurayin nata, kuma bata da tabbacin cewa bata sonshi, Amman duk dai yanda zaiyi ya kafa tashi gwamnatin sai yayi, shine fa Al'ameen Dambulan, matashin da kowa ke ganin ya kai, to ta yaya zai nuna gazawar shi akan abunda yake so?
A hankali dogon ɗan yatsan shi ya sauka kan number ɗinta.
Bai yi mata saving ba, saidai ya haddace number ɗin tin lokacin da kiran nata ya shigo wayar tashi a karo na farko.
Tayi ringing kusan sau shidda ba'a ɗaga ba.
Har ya ynke ma kanshi cewa ko tayi bacci ne?
Cen cikin murya mai kama da ta wadda ta gaji, ko tayi bacci ta ɗauka yaji ƴar siririyar muryar ta tana mashi sallama.
Saida illahirin jikin shi ya amsa, lumshe ido yayi yana mai sake buɗe su, daidai lokacin da yaji ta kuma doka mashi wata sallamr.
Wai dama haka soyayyar take? Shiga takeyi cikin jiki tayi gunduwa gunduwa da sassan jikin mutum?
Ta yaya akayi ma tuni bai shaida cewa tana da zaƙin murya har haka ba?
Ashe dai ilimi, kuɗi kyau ba sune abunda ake kallo a jikin mace ba ace ana sonta.
Sai gashi shi, yarinyar da kowa ke mata kallon bata kai ba, shi ita ce zuciyar shi ta naƙalta mashi sonta har haka, kuma yake ganin ta kai ɗin a idanun shi.
Yaushe ne ma ya faɗa cikin rububn son nata har haka bai sani ba?
Jin zata kashe wayar ne ya sanya shi saurin cewa "Hold on dear"
Wayar na cire a kunne, na sake kallo, lallai number ɗinshi ce, to ya san bacci yake ji kuma ya kira ni? Kallona na maida kan Khadee da take riƙe da littafi Amman ba karatun takeyi ba, kaf hankalin ta yana a kaina.
Samun kaina nayi da sake narkewa, bansan dalilin nawa nayin haka ba, illa iyaka dai kaman ina son in ɗan ba Khadeen haushi ne ko yaya ne,kaman yanda ta bani ɗazu itama.
"Shine kanaji ina ta sallama kayi mani shiru?"
Nima na samu kaina da faɗa cikin ƴar shagwaɓa.
Murmushi ya saki mai aji, kai kada fa yarinyar nan ta zauta shi.
Tashi yayi zaune yana mai jingina bayan shi da makarin gadon.
"Please wake magana ne? Naga ana ta kira na da wannan number ɗin tin ɗazu, please ko zan iya sanin wa kike nema?"
Cikin mamaki na ƙwalalo idanu,😳 nice ke kiran shi tin ɗazu,🙄 to yaushe ma na kira? Nasan nidai tinda ya tafi ban kira shi a waya ba. To ko na latso ne ban sani ba?
Minimize nayi na shiga call log, saidai babu wani alamun kiran da nayi ba tare da na sani ba.
Maida wayar nayi a kunne, shikau jin nayi shiru, sai ya cire wayar a kunne ya danne mouse ɗin ya shiga ƙyalƙyala dariya.
Yau sai ga Ya Ameen ɗin bisa gado, har yana ƙyaƙyatawa da kuma yin jifa da fillow alamun jin daɗi.
Jin ina magana ne ya sanya shi maida wayar a kunne.
"Ya Ameen ni fa ban kira ka ba, ni yaushe ma na kira. Bayan nace bazan kira ba"
Na faɗa cikin suɓutabbaki.
Sai bayan da na faɗa ne, sai kuma na ankare da kasassaɓar da nayi.
Cikin ƴar dariya da zaulaya ya shiga cewa.
"faɗi gaskiya yarinya, ko baki kira ba ai kina zaman jiran kiran nawa, Shiyasa ma bakiyi bacci ba ko?"
Turo baki nayi kaman yana gabana.
Sai kuma na shiga cewa "ni Allah ma sai na kashe wayata, sai zaulaya ta kake yi" na faɗa cikin shagwaɓa sosai, wadda ko Umma ma ban taɓa yi mata irin ta ba.
"Yi haƙuri, yi haƙuri my dear, wasa nakeyi" ya faɗa yana mai ɗaga hannu kaman ina gaban shi.
"Ban gaji da ganin ki ba dear, please ya za'ayi, tinda na taho sai nake jin kaman nabaro maki gabaki ɗaya zuciyar tawa my wife"
Ɗan murmushi na saki, ina mai komawa na kwanta.
Cikin ƙwaƙume fillow ɗin da bansan nayi ba nace "Kai Yaya, kana sani ina jin kunya fa"
"Huh". Ya saki ajiyar zuciyar da har saida Naji fitowar hucin ta a cikin wayar.
"Video my dear wife please"
"Bangane ba Yaya"
"Au baki cenza sunan ba ko? Dont ever call me Yaya please. On your data"
Ya faɗa yana mai katse wayar.
Da kallo nabi wayar, ina mai ɗan satar kallon Khadee da ta juya mani baya, ban iya hango fuskar ta, Amman yanda take motsi ya tabbatar mani da ba bacci takeyi ba.Hannu na sanya kaman wadda akayi ma dole na kunna datar.
Ban gama tunanin ba naga kira ya shigo waya ta ta application ɗin We-Chat.
Ban san ya yanayin fuska ta yake ba, balle gashi ma nayi kuka ɗazu, duk da dai nayi wankan kafin in kwanta.
Gaza amsawa nayi, Nifa har yanzu ban yarda Ya Ameen bane wannan.
Wani kiran ne ya sake shigowa wayata.
A hankali na ɗaga, ina mai tashi zaune.
Tar nake kallon fuskar yi.
Hasken shi har wani koɗa koɗa yakeyi, duk da dare ne, saidai Hasken farin glop ɗin ɗakin nashi da yake tar, ya taimaka wajen ganin fuskar tashi fes a idanun nawa.
Sajen shi ya sake kwanciya luf a saman fuskar, kaman an zana mashi shi, gashi baƙi wuluk gashin kuma gazar-gazar.
Bakin nan nashi kaman ya shafa Light pink ɗin lipstick, har wani walƙiya yakeyi.
Gashin idon nashi Zara-Zara, kaman zai tsole mani idanu, ni da nake ta cikin wayar.
"Kallon me kike mani haka?"
Ya faɗa, cikin hura ma screan ɗin laptop ɗin tashi iska, kaman yana a gabana.
Sai kuma naji kaman da gaske iskan ta fito a gaske.
Ɗan lumshe idanun nayi ina mai kauda fuska ta.
"Ya kika kauda fuska my wife?, please ki kalle ni mana"
Ya faɗa shima cikin wani irin salo da ɗan rage girman idanun nashi, alamun yana cikin tsabar soyayya. Hakan ya sanya yayi masifar kyau, har dimple ɗinshi na loɓawa
Ɗan waigowa nayi, ina mai kallon shi ta gefen ido.
Jan Laptop ɗin yayi kusa dashi, yana mai kwantawa a ruf da ciki,ya kara fillow mai taushi a ƙasn haɓar shi. hakan ya sake ba fuskar shi damar fitowa ta cikin screan ɗin.
Wani irin duka naji gabana yana yi, kaman yana a gaba na.
Dukka hannuwan shi ya sanya yana mai tallafo haɓar shi dasu.
Idanu ya zuba ma ni, waɗanda suke taimakawa wajen ƙara rikita ni.
A hankali na janye idanun nawa ina mai faɗin "Ya hanya?"
"Ki bari sai in ke kika kira, sannan ki tambaya, ba kince ba zaki kira ba? Kin cika wauta Suhan"
Ya faɗa yana mai son ganin yanda zanyi da fuska.
Har yanzu na kasa kallon shi, cen na tsinkayo muryar shi yana mai cewa "Baki jin zafi haka kike zaune da hijab? Duk da dare yayi, gashi kuma ku kaɗai ne a ɗakin"
Bansan lokacin da na kalle shi ba.
"Ai yanzu da kwai maza"
Na faɗa cikin ɗan tura baki.
"maida bakin, kafin inyi abunda zai baki kunya. Ina mazan suke?"
Ya faɗa cikin ɗan ɗaure fuska, saboda ya kula da abunda nake so ince.
Da hannu na ɗan nuna shi, ina mai faɗin "Gakanan"
Ɗan waiwaya wa yayi yana mai faɗin
"ban ganshi ba fa"
Ya faɗa alamun yana neman wani abu.
Bansan lokacin da na ƙara turo baki gaba ba, sai ji nayi yana cewa "zaki bar wannan al'adr ta turo baki gaba, don duk lokacin da kikayi shi a gabana hum...."
Ya faɗa yana mai ɗan kanne ido ɗaya.
Kunya ya bani sosai, har saida na kife wayar a kan cinya ta.
Khadee ce ta juya ta sake kwanciya, ta yadda zata iya gani na kai tsaye.
" Yaya bacci nakeji" na faɗa, bayan na ɗaga wayar.
"Saidai kuma ni gashi ban gaji da ganin wannan ƴar kyakkyawar fuskar ba"
Ya faɗa kai tsaye, yana mai ɗan ɗaure fuska.
Bance komai ba, illa sauke kaina da nayi ƙasa.
"In faɗi wani abu?"
Ya faɗa cikin salon tambaya, sannan da ƴar zaulaya.
Kai na ɗaga mashi, ba tare da nace komai ba.
"tashi yayi zaune sosai, ya ɗauko laptop ɗin zuwa bisa cinyar shi.
"Suhan na dawo lafiya, saidai na taho tare da matuƙar kewar ki, ban ƙi ba ace gobe ne za'a ɗaura mana aure dake, banaso kina mani wani kallo daban, illa kallon masoyn ki, mijin ki, kuma uban ƴaƴanki, ina ƙaunar ki har cikin zuciya ta, wanda bansan lokacin da hakan ya fara faruwa ba a rayuwa ta. Suhan ki yarda dani don Allah, nayi maki alƙawarn kulawa dake da rayuwarki fiye da yanda nake kulawa da rayuwa ta, da kuma kaina, amincewar ki nake buƙata, insha Allahu gobe zan samu Dad da maganar ayi bikin mu kwana kusa, saboda Na ƙagara inga na mallake ki a matsayin mata, ko ba komai shekaru na sun fara ja, ina buƙatar mace a kusa dani, ina da abubuwa da yawa da nake buƙatar mataimakiya a kusa dani, ba wadda naga ya dace, ba wadda naga ta cencenta, *Sai ke* kece daidai ni Suhan, ke nagani kuma nace *ina so,* don Allah ke zan aura Suhan, ba zan iya cenza wata a madadin ki ba, ki amince mani Suhan"
Ya faɗa cikin wani yanayi, wanda dab zuciyar shi take kusa da tsinkewa saboda tsabar wata irin wutar soyayya dake azalzalar zuciyar shi.
Ajiyar zuciya muka sauke kusan a tare.
A hankali na ɗago kaina ina mai kallon fuskar shi.
"Talk Suhan" ya faɗa cikin alamun roƙo.
Bana iya jure kallon nashi, a hankali na kuma sauke wata ajiyar zuciyar.
Sai kuma nace "Ya Ameen Allah ina jin Kunyar ka, kaifa *Yayana* ne"
"Stop Suhan,Stop, better Stop please; mubar maganar kunya or something like that, ki amince kawai nake buƙata, I promise u, zan sanya ki manta da wata abu wai ita kunya a tsakanin mu, ki bani kwana uku rak Suhan, Amman fa duk da haka zan tuntuɓi Dad da maganar zuwa safe insha Allah"
A hankali na shiga ɗaga mashi kai, alamun na yarda, cikin wata irin kunya dake daɗa malalowa a cikin zuciya ta.
"Yessssss" ya faɗa, yana ɗaga hannu kaman wanda yaci wasan kwallo, sai kuma yace "Thanks u my Love nagode Allah ya barmu tare my Wife"
Ya faɗa cikin tsabar farin ciki, ni sai ma ya bani mamaki.
Kaman ba shine ya Ameen ɗin da yazo ba ɗazu, kaman ba shine ake tsaron lafiyar shi ba, kaman ba shine ake ma kirari ba ɗazu. Sai gashi yanzu zaune yana zuba man zallar kalaman soyayya, sai gashi bisa gado shi kaɗai yana ƙure ni da kallo iyakar gaskiyar shi, sai gashi wai ni Suhan yau ni Al'ameen ke bayyana ma Sirrin zuciyar shi. anya kuwa..... Har yanzu na kasa yarda da haƙiƙanin gaskiyar wannan al'amari, dole ne zuwa gobe in kira Umman tawa inji abunda yake shirin faruwa, idan Abunda yake faɗa gaskiya ne, ya labarin Hajiya Kubra?
"Wife ki kwanta kiyi bacci, but make sure u dream with me" ya faɗa cikin wani salo.
A hankali na sauke hannu na kan screan ɗin da sauri ina mai faɗin "Nagode Yaya, i will" ko kafin in kashe wayar ya manna mani wani irin hot peck, yana faɗin "I Love U With All My Heart Wife" ya faɗa yana waving ɗina da hannu.
Zamewa nayi na kwanta, bayan na tura wayar a ƙarƙashin fillow.
Gabaki ɗaya na rasa yanda zan fasalta wannan al'amari, anya kuwa Umma tasan da wannan zance? Kaddai ace shi kaɗai ke kiɗinshi, kuma yana rawar shi.
A hankali idanuna suka kuma sauka kan Khadeen.
Tausayi ta bani, duk maganganu da yake faɗa tana ji fa, kada ma taga kaman saboda cin fuska ne nayi.
A hankali na tashi daga bisa gadon nawa ina mai nufar inda take kwance.
Zama nayi kusa da ita ina mai dafa jikin ta.
"Khadee tashi muyi magana"
"Bacci nake ji Suhan, ki bari sai da safe"
Ɗan jim nayi, sannan na miƙe ina mai cewa "To Khadee as you wish"
Komawa nayi bisa gadon nawa, ina mai zare hijab ɗin na kwanta, cikin ɗinbin mamakin abubuwan da suka faru duka tsawon yau ɗin.
*****
Tin bayan da ya rufe laptop ɗin, sai kuma ya faɗa kwance bisa gadon, shi yau jin shi yakeyi sakayau, kaman ba shine ya gaji ba, kaman ba shine yake jin bacci ba. Kwana uku rak ya ɗaukar ma kanshi, kafin nan insha Allahu sai yasa ta fara kiran shi da kanta.
Blanket ya jawo, yana mai ɗaukar remote ɗin Ac ya ɗan ƙara ƙarfin gudun ta, yana mai kwanciya ƙwaƙume da fillow, assuming yakeyi dama ace Suhan ɗince.....
Wani irin farin ciki da annashuwa ce ke shigar shi, yau Al'ameen Almustapha Dambulan ya faɗa soyayya.......
*Allah ya kauda idon waɗanda zasu kawo cikas a al'amarin*
_Share Please_
~Oum-Deedat ce~
0 comments:
Post a Comment