Bismillahirahmanir raheem,ina rokon Allah yabani ikon rubuta Alkhairi ya kuma sanya ku amfana da abinda zan rubuta,Allah ya kareni daga sharrin maheranta yakuma sanya na gama da iyayena da duniya lapia Ameen...
Kaunar ku agareni me yawan gaske ce amintattun haske Allah ya kara hade kawunanmu ya dauke idon maqiya akan mu.
Wannan littafin sadaukarwa ne ga kawata Hafsat ilham.
01
Tafiya takeyi tana faman had'a gumi iya gajiya ta gaji,tafiya tun daga agege har owodé tafiya ce me nisan gaske sabida fitane daga ckin garin lagos zuwa wani country na daban,btada kdin hawa brt tun daga agege har zuwa can,gashi tafiyar ta zame mata dole dakyar taga ta isa,tun asba ta fito daga gida amma sai karfe daya saura ta isa wurin,batare da bata lokaciba ta bude bakin buhun da tazo dashi tashiga tattare shinkafar da masu durawa a buhuhuwa ke zubar wa awurin yayin aunawa,tafi awa biyu tana tatre wa,ba laipi ta tara yafi kwano goma kasancewar ba wani wanda ya damu da wacce ta zube din kowa aikinsa yake,kwara babbiyar nokia torch light dinta ta janyo daga cikin zani tga har uku ta gota,wannnan ya sanya ta dakata tayi salah sannn taci gaba,ganin hudu ta gota yasanya tayi hanyar gida,bus tafara hawa ta sauketa wani station sanan ta hau brt ta sauketa a agege inda ta hau adaidaita zuwa zango...da salama ta shiga gidan nasu ba kowa a tsakar gidan nasu tamkar anyi shara,kai tsaye daki ta wuce ta tarar mahaifiyar ta nata kwasar kuka,da sauri ta karasa inda take ta durkusa murya na rawa ta furta
"Umma lapia me kuma ya sameki haka?" Dagowa tai ta kalli yar sannan tace
"Amal Auwal ne shine yazo" zaro ido tayi waje ta dafe girji tace cikeda fargaba
"Kaddai wani abin ya aikata agareki Ummie?" Gyaran zamanta tayi tace cikeda d'acin rai
"Amal yamun komai ma,Auwal so yake ya kasheni ya huta sam wannan yaron bashida kirki,kaf abincin dake gidannan ya gama tattarashi ya gudu,a haka jawaheer tafice tana kukan yunwa banmasan inda ta nufa ba" dafe kai Amal tayi cikeda k'unan rai tace "Subhanallah oh ni Aisha se yaushe Auwal zeyi hankali ne wai? Kiyi hakuri Ummie bara nayi sallah nazo na gyara wannan shinkafar tunda da kasa aciki inyaso nakai gidan iyan hadi su siya se nayi cefane muci abinci tunda inaga yafi kwano goma wannan" kwanciya Ummie tayi tana me sakawa Amal Albarka yarinyar gwanin ban tausayi akwai kokari mace sekace namiji tana mata fatan Alkhairi.. A wahalce ta mike taje ta dauro alwalan la'asar ta gabatar sannan tafara aikin ta....
Da azama kameel ya shigo gidansa iya yunwa ya kwaso yunwa,yana shigowa parlor ya tarar tana kwance Ameer yayi kashi a saman tile se jagwalgwalashi yakeyi tana zaune tana shan rake abinta tana kundu ma masa zagi
"Tsinannen yaro me shegen kazantar tsiya ka rasa inda zaka mun kashi se'a parlor wlhy sena kammala shan rake na sannan zan kulaka ka karasa kazantar taka" to she hanci kameel yayi cikeda bacin rai yace
"Haba Hauwa wannan wane irin mugun kazantane haka,gida se wari yake yaro yayi kashi kin zauna kina faman shan rake" mikewa tayi ta gyara daurin zanin atamfarta wanda asaman bingilalliyar vest dinta ta dora shi tace tana Sosa kunne
"Kaga kameel ni karkaga laifina fa Ameer shine sarkin kazanta,banda iskanci yaro yasan yace zesha ruwa,Umma tee zansha,Amun wanka amma ya zauna ya tiqa mun kashi a kasa sannan kace laifina zaka gani?" Tsaki yaji cikeda kosawa yace
"Yaronnan fa Hauwa ko wando baki saka mishi ba,ga uban sanyi ana kwad'awa amma kibarshi tsirara ko kunya bakyaji" tsaki taja ta dauke yaron kurun tayi ciki dashi tsabar haushi kasa karasawa ciki yayi ya juya abinshi zuwa gidan maryama,besha wahalar shigaba kasancewar me gadin yasan da zamansa tun a kofar parlor din wani dadda dan kamshi ya tarbeshi,lumshe ido yayi ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cira hannu cikeda kasala yai knocking,bude masa kofar maryama tayi a lokaci daya ta rungumoshi ya fado jikinta,Sumba ta manna masa a wuya sannan cikeda shauqi ta kirsa tace
"My kameel kamar kasa ina wanka ina tunanin ka jiya bakazominba dukna damu" kura mata ido yayi ba komai ajikinta se towel wanka tafito jikinta duk ruwa,amma se tashin kamshi takeyi tamkar wacce tayi wanka da shagon turaruka,kurawa fuskarta ido yayi cikeda kauna,gashin girarta yacika da ruwa ya kwanta lufluf ba karamin kwanciya gashin yayi ba kuma ya mar kyau matuka,janyota yakumayi jikinshi ya saka harshe ya lashe mata ruwan na duka giran biyu yace
"So much miss yhu Deena na,Kinyi kyau se tashin kamshi kike,gidanma sekace kamfanin sarrafa tuararuka" Murmushi tayi tace dashi tana tafiya tana jujjuya duwawuka "My honey bara nasaka kaya nabaka abinci I'm sure kanajin yunwa" wuri ya nema ya zauna a daya daga kujerun parlor din har takai kofar dazata sadata da walkway dashima ze leading nata zuwa dakin ta juyo a shagwabe tace
"Honey ni bazaka tayani saka kayan ba?" Murmushi yayi ya mike ya karaso kusa da ita dagata yayi gaba daya yana fadar "Baby dee mezai hana nashirya abata" wani narkewa tayi a jikinshi tace "Honey kona tayaka wankane mu shirya dukkanmu" direta yayi yace "sure mana baby dee ragemun kayan nauyinnan" matsawa tayi daf dashi ta Shiga balle botiran rigarsa cikeda shagwaba da salo irinna bariki,ahaka tamai zigidir itama kuma ta cillar da towel na jikinta da fada jikinshi sungumarta yayi ya direta a cikin ruwan me kanshin da ke cikeda bahon wankan shima ya fada aciki...wal iyazu billah Allah ya shiryi zuri'a.
Kallon Mansoor Amal tayi tace dashi "Mansoor kana ganin lokacin dazamuyi auren yayi dududu fa watanin mu hudu da haduwa,ina ma mukayi zaman da muka fahimci juna da har zamu fara zancen aure?" Kallonta yayi damuwa dauke a fuskar sa yace
"Haba my Amal? Tayaya zancen aure yashafi watanni nawa mukayi atare fata daya ne munasan junan mu" langwabar da kanta tayi sannan cikeda shagwaba daya zame mata dabi'a tace
"To ai ni banasan rabuwa da Ummie na da khairiyyah kuma kace wai Kano zaka ajiyeni" rike hannunta yayi yace "zan kular miki dasu my Amal,kisani bayanda zanyi ne daba yanda za'ayi nayi nesa dake,kumama daddy yace zai mayarda ni kampaninsa dake Kano so kinga bata yanda za'ayi na ajiyeki anan" Murmushi tamasa cikin dabara ta zare hannunta domin sam batasan yake tabata kuma ta kula hakan d'abi'a ce agareshi
"Ba damuwa yaa Mansoor Allah ya sanya shine mafi Alkhairi zanwa Ummie maganar inyaso tasanarwa da baba gambo sena maka waya" block compartment nashi ya bude ya janyo wata waya kirar tecno cs ya mika mata,kin karba tayi ta tsaya kallonshi sanda ya daura kan cinyarta "yaa Mansoor me haka kuma"
"Waya na siya miki mana kalli Nokia dinki Amal duk roba aiba girma na bane Matana na rike wannan wayar" langwabe kai tayi kamar zatayi kuka tace "amma yaa Mansur abin beyi yawaba kalli fa dawainiyar daka gama dani yanzu" lakuce mata hanci yayi
"Kinga malama Bafa ruwanki da abinda nayiwa Matana ehee" Murmushi tayi me sanyi
"Allah ya saka da Alkhairi yaa Mansur Allah kuma yabar kauna"....har ran Amal tana kaunar Mansoor tarasa dalilin daya sanya wasu lokutan takan ji faduwar gaba duk sanda ta tuna da zancen auren su.
Sosai kameel da Deena suka barje ayarsu a gidan Deena,sai wuraren karfe goma na dare yayi shirin tafiya gida,har sunzo kofa ta wani narke " Honey wai yanzu zaka tafi bazaka kwanamun ba" Sumba yafara manna mata yace "kiyi hakuri my Deena gobe zanzo kinji" kuka tasaka dakyar yalallab'ata ya tafi....Koda yazo gidanshi Hauwa na zaune a parlor tana cin farfesun kazarta me karnin gaske kota damu da ficewarsa dayayi dazu ce cewa tayi dashi
"Kameel dazu kanna fito wanke wa Ameer kashi harka juya,nace wata sabga ta samu kenan" Kallonta yayi da muguwar shigarta kitson kanta yafi one month yace "E" a takaice ya shige abinshi.
Mom nuaiym
[10/12, 7:57 PM] billygaladanchi: HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡
Billy Galadanchi
HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.
02
Kallon Amal Ummie tayi tace da ita "Amal anya kuwa zan bari kiyi nesa damu? Ki duba dai kigani haryau su jawaheer shekarun su sha hudu,sannan Auwal bashida hankali ni kam narasa mesa banasan aurenki sa Mansoor dinnan sam banasan kimun nisa" langwabar dakai Amal tayi sannan ta sadda kanta kasa tace cikin sanyin murya
"Zan sanar masa ra'ayinki Ummi idan ya yarda ze barni anan shi kenan idan kuma dole se kanon ma hakura da zancensa" shiru sukayi na yan dakiku kan Ummie tace "Karki dauka banasan farin cikinki Amal sam ba haka bane,kisani banida wani karfi ajikina,wannan hawan jinin bawai barina zeyi ba sannan yayanki yazama sakarai khairiyyah da jawaheer dukkansu yarane kanana ba wacce zata kula da kanta Idan yau na fad'i na mutu a hannun zasu zauna?, Rabi ce dai kinsani ba karbarsu zatayi ba ita kanta tata bataliyar ta isheta,ga Abbanku ko wanda yataba ganinshi kojin labarinshi bamu ganiba" hawayen datake tare wane suka gangaro daga kuncinta tace "sarai na fahimceki ummi gani nayi Yanzu ina cikin shekara ta ishirin da shida fa ba miji,yanzu Allah ya kawo ahaka ze tafi a wani bangaren kuwa na sani kin fini gaskia wannan dalilin kadai yasanya kikaga ina kuka wlhy" shiru Ummie tayi tana tausa yawa yar tata tasani koba komai lokacin bukatar namijine akusa da ita yanzu...
"Yaa Mansoor ka fahimci ummi basuda wani gata fa,nice kadai nake tallafa musu,idan namusu nisa me kake tunanin zeje yazo?" Nisawa yayi yace "Hakane zancen Ummi my Amal, kema kinsan tafimu gaskia gashi rashin lafiya nta ya tsananta gakuma yara,abinda yafi shine kawai zanje na wa dad magana,ya barni anan,idan yaso seya tura wani kanon,harga Allah bazan iya hakura dakeba my other half,gwaramun na rasa komai nawa akan rashin ki,zan iya sadaukar da farin Cikina matukar inhar zaki dauwama a naki" murmushin ta me sanyi tamasa sannan tace "Nagode yaa Mansoor Allah ya barmin kai" Murmushi yamata shima ya janyota jikinshi,janye nata jikin tayi tace cikin murya kasa "yaa Mansoor kadena tabani ba kyau fa" kura mata ido yayi kan yace "kiyi hakuri Aisha bazan kuma ba" da haka suka sha hirarsu suka koshi kan daga bisani suyi sallama.
"Hauwa" wai meye Hakane? Breakfast dinma bazaki tashi ki bani ba ko ruwan tea fried egg da break ai ya isheni" kara mimmikewa tayi akan gadon batada niyyan tashi tsaki yaja ya wuce kitchen din kai tsaye,kallon tulin wanke wanken dake kitchen din yayi da alama yafi sati ana tarawa,ya duba kaf ba inda ze koda fasa kwai ne store din se warin albasa yakeyi tsaki yaja nanma,ya juya kawai harya bar gidan baccinta takeyi ita da Ameer,daga office gidan ya koma koda yaje tana zaune tana kallon film din makaryaci tana kwasar dariya,kurawa parlor din kallo yayi ko ina kaca kaca,nisawa yayi yaje ya zauna kusa da ita yace cikin dakiya
"Hauwa saka pause a film din nanan magana zamuyi" kallonshi tayi tace cikeda kosawa "Haba Babban Ameer yanzu duk zaman damuke a gidannan baka San lokacin dazamuyi magana ba se yanzu danake kallo na?" Murtuke fuska yayi yace
"Maza ki nutsu magana nace zamuyi ko kuwa?" Shiru tayi yaci gaba "Dama game da zancen wannan kazantar taki ne,ni abin ya isheni wlhy idan kinsan aikin gidannan yamiki yawa munemo yar aiki kawai" a fusace ta fara banbami tana daura zaninta harta kai tsaye "wlhy kameel Kayi kadan,Wato salon ta kwace mun miji Aini da yar aiki har abada,kuma wacce kazantar nayi? Duk iyakar kokarina baka gani?" Kasancewar kameel ba me San rigima bane yasanya cikin sanyi yace "Allah ya huci zuciyarki ya zancen abincina?" Sosa kanta tayi
"Aikam dai tun safe naketa kallon hausa films dinnan dana Aro sabida haka banma daura girkinba wlhy,kona daura maka taliya da manja da yajine?" Kura mata ido kurun yayi ya mike ya je ya watsa ruwa a toilet dinshi dayake wanke wa da kanshi kuma ya kulle abinshi dan kuwa Hauwa ko flushing kashi batayi setaga dama kuma setayi wata biyu bata wanke ban dakiba,siyisa yakanyi wata fiye da uku be leqa sashen taba,a gurguje ya shirya ya bar mata gidan zuwa gidan maryama Deena....wani karamin yaro yayi karo dashi yafito daga gidan yabi shi da kallo harya bacewa ganinsa,komawa yayi wurin me gadin yace dashi "Dan buba waye wancan yasaba zuwa nan gidanne dama?" Gyaran zaman hularsa yayi yace "yallabai inaga fa tare yake da qawar Hajiya lokaci zuwa lokaci sukanzo tare" gyada kai kurun yayi yashige ciki,a parlor ya taradda Kawar ta maryama me suna huda,batada banbanci da tsirara,dauke kanshi yayi yace cikin dakiya
"Dan Allah maryama fa?" Tasowa tayi cikeda kirsa ta zo daf dashi "Deena taje shopping me kake buqata ne na maka,juyawa yayi kurun da zummar barin gidan ta rungume shi gaba daya" Haba mana kameel,nikan ji labarinka abakin qawata cewar kaidin jaru mine, plss kamora daga ni'imomina mana" tureta yayi cikin tsawa yace "Danla malama ke kam bakida hankaline haka kawai tsabar hauka zaki mun wannan shashancin bakauya dake" shiru tayi yaci gaba da banbami ahaka maryama ta tadda su,Kallonta tayi cikin fusata tace "huda me haka kuma menene kikewa kameel yake daga murya haka?" Shiru tayi simi simi tawuce dakin Deena,bata fuska yayi yace
"Baby dee ina wannan Kawar taki ce nakejin labarin cewar lesbian ce? To wlhy ba ita ba karna kuma ganin yan iskan qawayenki a gidannan kuma ki sani duk randa ita dinnan nakuma ganinta nida ke har abada" zaro ido tayi arude tafara mai magiya domin kuwa Deena tana kaunar kameel shiyasa dashi kadai take mu'a mala,dakyar tashawo kanshi ya sakko yayinda tayiwa huda korar kare.."
Cikin dare Amal acikin baccinta taji gurnanin mahaifiyarta karti ne tagani susu biyar tsaye a kanta, mari dayan ya wanka mata yace "kina yunkurin yin ihu zan fasa kanki da harsashi wlhy" shiru tayi jiki na bari ta Shiga kuka,tana kallo daya daga cikinsu ya zaro wuqa,yace da d'ayan "rufe mana idon ta" tanaji tana gani aka saka kyalle aka rufe idonta,da karfin Allah ya cakawa Ummie wukar a makogaro,atake ta mutu, ya saka wukar ya cire nonuwanta duka biyun sannan aka cire idonta na hagu nan suka wurgar da gawar suka bar gidan da gudunsu,hauka cewa Amal tayi sanda ta kunna fitilar dakin,taga uwarta haka ta tashi kannenta sunaso su kira makota sunajin tsananin tsoro hankulansu atashe seda asuba suka ruga suka sanar mutanen unguwa se alhini suke kuma ga tsoro daya shigesu...Amal tayi kuka tamkar ranta ze fita da wannan wulakncin kisan da aka aikata ga mahaifiyarta gashi batasan ina Auwal yashiga ba se ita da jawaheer da kuma khairiyyah yara kanana gwanin ban tausayi...
*Bayan sadakar arba'in*
My Amal nifa hankalina be kwanta ba kuke zama a gidannan kuku kadai,kawai a daura aurennan mu wuce Kano" rausayar da kanta tayi cikin kuka tace "yaa Mansoor ina zan ajiye jawaheer da kuma khairiyyah? Bamuda wani gata sena Allah fa" kallon ta yayi yadan bata rai "Dolene muje dasu ainine ubansu kuma yayansu Amal,keda kanki kin fada baba gambo ma takanshi yake baze iyaba" sosai tamasa godiya suka wuce wurin...
*Bayan daurin aure*
Auwal yazo gida yayi bakin jin abinda aka aikatawa ummien shi ko gafararta be nemaba,shine ya saka yan haya agidan nasu,su kuwa dungu rungum suka wuce Kano. Tun zuwansu gidan suke mamakin wannan katafaren gidan ace wai duk na mutum daya ne,dakanshi yamusu umarnin Shiga dukma sassan gidan amma banda wani d'akin guda daya daya tabbatar musu har Amal be amincewa Shiga cikiba,ba wanda ya kawo komai aranshi kasancewar dakin ma abayn gidan yake,gidane tsararre wanda yaji komai,zamu iya cewa duk inda kajuya madubine a gidan tun daga gate,mutanen unguwar ma suna kiran gidan da gidan mirror,sosai Amal ta tsorata da wannan uwar dukiyar amma ta dake a haka suka shirya komai,daki daya ta bawa kunnen nata yayinda sauran sunkai bakwai suka zama mallakinta wannan kenan...Daren farko daya fara kusantarta tasha wuya sosai ya mulketa San ranshi bako sallar godiya wa Allah kazalika baccinshi yashaqa bashi ya farkaba se azahar juyin duniya tayi yatashi yayi sallah amma sam yaqi,koda azahar ma wanka kadai yayi yaci abinci yafice bataga alamun sallah atare dashiba. Tun daga ranar fa sam Amal bata ganin Mansoor se cikin dare,idan ma sun kwanta tare sedai tafarka taga wayam,sam batasan ina yake zuwaba,se gabanin asuba yake dawowa,abu daya tasani yana matukar kulawa da ita haka mahaifirshi mutuniyar kirki tana matukar kaunarta,wannan ne yasanya take d'an jin sanyi aranta,yasaka su jawaheer a ss1 wata makaranta me tsada itama kuma ya sanyata a poly Kano, wannan yasanya hankalinta ya kwanta,damuwar ta daya lura datayi yana da raunin addi ni sannan kuma baya sallah ranar juma'a ko d'aya amma sauran ranakun jam'i baya wuce shi indai yana gida,abin na damunta sedai ta kula ranar juma'ar idan dare yayi baya fita kwana yakeyi yin sallah,harga Allah Amal takasa gane kan mijinta...
*Bayan watanni takwas*
Promotion exam su jawaheer keyi wannan yasanya takiyin bacci tana bitar litattafanta,motsi taji na alamun mutum,kuma taji cewar a dakin bayane fitowa tayi domin ganin waye ganin cewar karfe daya ta gota,daga can ta hango Mansoor ne,ganin ya bude dakin yasanyata juyawa ta koma, shi sam be gantaba,a yan wayannan Kwana kin kuwa ta kula daidai karfe daya yake zuwa dakin ko wane dare,sam zuwa yanzu hankalin jawaheer yafara karkata akan son sanin meke kaishi d'akin daya hana kowa zuwa kuma cikin Dare! Wannan dalilin yasanya jawaheer ta kudurta aranta cewar Daren gobe juma'a seta masa labe,ga mamakinta har gari ya waye be fito ba sam!!!!
Hmm Masu karatu waishin Wanne Mansoor? Wane irin sirri ne yake boyewa a wannan dakin? Shin meye sana'arsa? Menene tushen su Amal? Kuma miye makomarsu agidan mirror? Waye kameel kuma mecece ainahin alakarshi da maryama Deena?" Muje zuwa dai...amsoshin tambayoyinku na tare da alkalamin maman Nuaiym
Loves you.
[10/13, 8:46 PM] billygaladanchi: HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡
Billy Galadanchi
HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham
03
Ba karamun karkata hankalin jawaheer yayiba akan san sanin menene ke cikin wannan dakin me kuma yake yawan kai Mansoor aciki duk daren duniya mesa daren juma'a ne kadai baya zuwa? Wannan abin na damunta tanaso ta manta da wannan amma sam ta kasa cirewa aranta,yau a school bayan sun kammala exams an tashi a school suka fito abakin gate na school suna jiran isowar driver gidan mirror wanda shine dama yake kaisu yake kuma daukarsu idan sun tashi,har after 3 be zoba gashi sun fara jin yunwa,kallon khairiyyah jawaheer tayi tace cikin kosawa
"Khairiyyah dan Adam be saba yin haka ba kuma nifa yunwa nakeji,ko naje can shop din na karbo mana cock?" Gyada mata kai kurun tayi kasancewar ta bamesan yin magana ba sam,tsallakawa tayi tashiga cikin karamin shopping mall din ta dauko chocolate cookies da cock da kuma wasu chocolate tazo domin biyan kudin bayan an gama bugawa kudin se yaron ya kalleta yace da ita
"Haj basai kin biya ba, yallabai ne yace komai tarin kayan dakika dauka kar a karbi kudinki" kallon mamaki tamasa tace
"Waye kuma yallabai kuma ce masa nayi banida kudi dazai biyamun Kokuwa yawon bara yaga alamun inayi ?" Kallonta yaron yayi "maida wukar Haj bani nakar zomonba rataya aka bani,kuma Nima Bansan shiba,Yaune kadai naganshi awannan shagon,kuma kayanki 2300 kacal dubu goma ya bayar ungo ga canjinki,danshi ya fice tuni" mamakinta ne ya kasa b'oyuwa tace dashi "bani dubu gomar da daya baka duka,da kudina zan biya wannan kayan,ungo kudin" beyi musuba ya karbi kudin yabata dubu goman da canjinta dari bakwai dayake 3000k tabashi,kallonshi tayi tace dashi muje waje koda zaka ganshi ka nuna mun" ba musu ya bita ilai kuwa koda suka fito yana jingine jikin wata mota kirar Mercedes Benz 2017 black se sheqi takeyi yasha dakakkiyar shadda fara k'al dinkin hannu da hularsa black ta kalminshi black agogon hannunshi ma black,daga inda take hango shi tana jiyo tashin kanshin turarenshi daya mamaye ilahirin wurin,waye yakeyi yana dariya ilahirin kefen kumatunsa lobawa sukeyi ga tsararriyar wushiryarsa dake bayyana a duk sanda yayi dariyar,nuna mata shi yayi da hannu yace "Gashinan ni zan koma kan aikina" godiya tamasa taje ta tsaya akanshi harya gama wayar,mayarda dubanshi yayi zuwa ga reta yace cikeda izzah
"Yan mata any problem why are starring @ me like that,how may I help?" Dayan hannunta daba komai ta saka tarike kugunta tace cikeda tsiwa
"Yallabai aka ce dani kake kowa oho dai,zuwa nayi na mayar maka da kudin ka tunda ba rokar ka nayiba,Kokuma ka sanar dani idan alamun bara kagani ajikina dazaka biyamun kudin abinda na siya har dan raini zakace Abani canji" kura mata ido yayi na wasu yan dakiku,kan ya mika mata hannu,kallonshi tayi da rashin fahimta amma batayi magana ba,cikeda yanga yace "Bani kudi na malama,kin wani kafeni da ido" sosai taji haushin kalamanshi,mika masa kudin tayi a wulakance ya kalleta ya tab'e baki yace "Haka yakamata kina baiwa Babba abu bawani girmama wa?" Hawayen datake tare wane ya silalo har ranta taji zafin kalamanshi duk tsiwa irin tata se taji nauyin sake hada ido dashi gashi lokaci daya ya mata kwarjini,sadda kanta tayi k'asa ta kasa mika masa kudin,sanda yace
"Bani kudina mana?" Cikeda kasala tace tana me mika masa a ladabce "Kayi hakuri raina ne a bace" bece da ita kanzil ba ya karbi kudinsa ya shige mota ya tayar,har yabar wurin tana tsaye,a center mirror ya ke Kallonta,aranshi yana mamakin tsiwa irin tata dakuma saurin yin laushi datayi,har ranshi gwadata yayi yaga koda itama tanada mugun hali nasan abin duniya. Gwiwa a sace ta karasa wurin khairiyyah ta ajiye kayan tace da ita,Kici kawai ni cock din ta isheni, dama khairiyyah batada yawan magana,shiru tamata kurun ta soma cin cookies din,wasa wasa fa har karfe biyar dan Adam be zoba ga basa zuwa da waya school, kuma Aunty Amal sunsani yau se shida zata dawo bata masan basu koma ba balantana tazo daukarsu,ga yaa Mansur ya gargadesu akan hawa adaidaita,tsakin da jawaheer taja kuwa yafi hamsin,ganin yamma nayi yasanya ta kalli khairiyyah
"Kinga mufara traking Nagaji da zamannan wlhy" mikewa kurun khairiyyah tayi suka fara hanya,har shida saura ba dan Adam ba labarin sa,wata jar mota ce kirar kia I robot ce tasha gabansu,azatonsu d'an Adam ne yazo da wata motar dukda yake sunsan agidan mirror ba irin wannan motar,tsayawa sukayi ma mallakin motar ya bude ya fito cikeda yanga se tashin kamshi yake,sanye ajikinsa shirt ce hadaddiya fara kal se blue jeans takalminshi da komaima blue har mudubin dake idonshi gilasanshi blue, mamakine ya kama jawaheer ganin yallabai ne na dazu,sadda kanta tayi kasa ta rike hannun khairiyyah, kallonsu yayi ya sakar musu Murmushi sannan ya kalli jawaheer yace
"Yan makaranta lapia dai har yanzu baku tafi gida ba?" Rausayar da kanta tayi idonta harya Cika da kwallah tace
"Toba d'an Adam bane ba tun daya da Rabi muka tashi amma bezo ya daukemu ba kuma yaa Mansur ya hanamu hawa a daidaita ko taxi" dariya ya kwashe da ita domin kuwa harga Allah rashin hakuri irin nata da yanda tayi maganar tamkar zatayi kuka ya bashi dariya,itakuwa kara kular da ita yayi,take kukan datake rikewa ya kwace mata,kasama magana tayi se khairiyyah ce cikin sanyinta tace "Haba juju ke da girmanki amma komai kankantar abu sekin yi kuka ni kina bani haushi wlhy" Banza tamata shikuwa yace "matsalar kuma jujun bata karbar kyauta dana baku lift na saukeku agida" kallonshi khairiyyah tayi tace
"Kayi hakuri mu dama Bazamu Shiga motar wanda bamu saniba" Murmushi yayi yace "Dan Allah kibani number din sister dinki mana inaso idan kun isa nakira naji saukarku lapiya" kallon jawaheer tayi tace "kinji me yace ki bashi mana da kanki ina kema kinada baki" Banza jawaheer tamusu ana haka suka hango d'an Adam yana nufosu,da sauri suka juya jawaheer taja hannun khairiyyah suka wuce abinsu, bayansu yabi har suka isa gidan,ganin anshiga dasu katafaren gidan mirror dake unguwar kuntau yasanyashi furta cikin mamaki "gidan mirror?? " a hankali ya gangara yayi parking a gefen gidan me gadin gidan yawa sallama sannan yace dashi
"Dan Allah Mlm so nake kamun magana da d'an Adam, ka sanar masa yanada bako a waje" kallon sheqeqe ya masa yace yana fesar da hayaqin sigarin daya zuqa yace "Yallabai a nawa?" Murmushi yayi ya zaro dubu biyu ya mika masa,take ya shige cikin gidan se gashi sun dawo tare da dan Adam,mamaki dan Adam yayi ganin shine dayagansu tare dazu,matsawa yayi ya dan rissina yace "sannu yallabaii"
"Yauwa sannu d'an Adam ko?" "Ea nine lapiya dai?" Zaro kudade yayi ha irga dubu goma ya mika masa,yace dashi "zan baka irinsu har so hudu su zama dubu hamsin inhar Kayi kokarin samomun number din yarinyar danaji ankira da juju,acikin yaran daka dauko daga school yanzunnan" Sosa keyarsa yayi yace "yallabai ai indai wannan ne angama yafi komai sauqi,bara na zura taka lambar inyaso namaka alkawarin gobe da sassafe zan aiko da ita" godiya yamasa suka rabu akan se washe gari,goben kuwa yana daukarsu yace "Jawaheer kinga jiya ina kani kawa har yamma bkuna makaranta, nayi magana da hajiya tace ke jawaheer kibani lambar wayanki kuma ki rika zuwa da taki wayar makaranta idan irin hakan ta faru sena kiraki inyaso seki sanar mata ita tazo ta daukeku"
"Ba damuwa zan baka anjima"
"Haba kekuwa idan wani matsalar yafaru yaudin kuma?"
"Koda wata matsalar ta faru ni ban fito datawa wayar ba" Sosa keyarsa yayi
"Dukda haka kibani na ajiye" tsaki taja sannan ta karanta masa yayi saving, take ya aikawa Hilal,shikuwa ya bukaci number din acc nashi atake kuwa yamai transfer.
Rungume Kameel yake da Deena se narka iyayi takeyi,adole tafiyan dazeyi Abj seyaje da ita,sosai ta saka yaji baze iya hakurin sati daya basa tare ba,da wannan yace ta shirya su tafi,dukkuwa dayake yagama sanarwa Hauwa cewar tare zasuje,koda ya dawo gidan yasanrwa Hauwa Abinda ya faru wai tafiyar ta sauya domin kuwa ogansu yace koda sunje da matansu bazasu samu lokacinsuba,wawiyar se hamdala tayi wai dama tanada bikin kawarta " tsaki yaja domin harga Allah yanasan Hauwa kuma kullum yanajin tsanar kansa akan abinda yake aikatawa amma yazeyi,yana bukatar kulawar mace,Hauwa kuwa daga kazanta se bacci.
Da dare wuraren karfe tara na dare jawaheer na zaune a babban parlor itada Amal wayarta tashiga ruri janyota tayi taga number bakuwa,dagawa tayi adaidai lokacin datake yunkurin barin wurin,a wahalce cikin muryan wahala tace "waye yake magana ne?" Gyaran murya yayi yace "Yallabai ne" jin muryarshi kadai ya kayar mata da gaba tace cikin sanyi "Banfa gane ba malam" Murmushi yayi tamkar tana gabanshi yace
"Nine dana sakaki kuka jiya har sau biyu,wanda muka hadu a shopping mall" gyaran tsayuwarta tayi "Mlm nifa Banganeba ban kuma hadu da wani a mall ba sam,hasalima ni jiya daga school se gida" sarai ya gane da gayya take masa Murmushi yayi
"Sunana Barrister Hilal Mahmoud Auwal,inasone muke gaisawa idan ba damuwa" takasa gane mesa taji wani farin ciki daya kirata tunanin ta bemaje wa neman sanin inda ya samu digit nata ba,langwabe kai tayi tace "Ba damuwa amma ina karatu yanzu goben inada exam ne" Murmushi yayi shima jin bata Musa masa ba yace "Bakida matsala Allah ya taimaka seda safe" ahaka ta ajiye wayar tana ta murnar da batasan dalilin taba.
Bacci ne ya sureta batare da saninta ba, ita kuwa khairiyyah karatu nta takeyi gobe wasan aljanu ne dasu Wato mathematics gashi dama bata wani iya lissafi ba,motsi taji wanda ya ja hankalinta zuwa kofar dakin nasu dayake a bude,tsayawa tayi ganin yaa Mansoor dauke da wani yaro dabaze wuce shekaru huduba,kuma tabbas ta hango yaron ba kunnayenshi duka biyu,kasa jurewa khairiyyah tayi tabi bayanshi sadaf sadaf har zuwa sanda yashiga dakin daya hana kowa Shiga,kanta karasa harya rufo kofar d'akin daidai kofar d'akin taje,ta kara kunne nta amma bata jiyo komaiba,har zata juya taji muryar karamin yaro yana cewa "Wayyo mama na ki taimakeni ze yankani da wuqa,dafe kirji tayi ta Wato ido,a haka tajiyo yaron ya rangad'a kara harya mace,juyawan dazatayi taci karo da mopping stick,yafadi a kan tile gashi kuma na karfe ne, daga dakin taji ance " waye Anan?" Da sauri tashige kitchen tayi store ta rufo kofar, Mansur kuwa ya tabbatar yaji motsin mutum kuma yasani duk iya gudunka baka isa wuce kitchen ba sabida yafi kusa,dakin matarshi yajuya yatarar tana baccinta sannan yafito, tabbas yasani akwai wanda yamasa label,dakin su jawaheer yashiga yatarar jawaheer tanata baccinta ga fitila a kunne se littafi a kusa da ita,juyowa yayi yana fitowa yaci karo da khairiyyah sadaf sadaf zata shige daki!
Mom nuaiym
[10/15, 10:26 PM] billygaladanchi: HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡
Billy Galadanchi
HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.
04
Sosai khairiyyah ta saisaita nutsuwarta tace cikin dakiya
"Yaa Mansur Kaima kaji ko?" Dan Ajiyar zuciya ya sauke a boye ya kara tamke fuska yace "Naji me?" Dafe kanta tayi tace "Ohh Allah wlhy yaa Mansur inaga Aljanai ne suke bibiyata,tunda nafara karatun darenan kullum sena rika jin wani motsi,yanzu kuwa ina karatu kawai senaji kamar kukan yaro,can kuma senaji kamar karan wani abu ya fad'i shine Nafito induba kuma Banga kowaba banmaga meya fad'inba kuma har kitchen na duba" sosai yaji wani sanyi jin cewa ba label tamasa Ba, yace cikin fad'a
"Idan kuma wani mugun abinne seya kashe ki ko? Tsabar wowta seki fito kuma ke kadai,me zaki gani? Keda ya kamata ace kin datse dakin Ku inma Hakane, to daga yanzu nice zan rika rufe dakinku ta waje se asuba zanna rika bude Ku,wlhy bazan yadda wani abu yasa mekuba kuna marayun Allah,kukan yaro kuma inaga makota ne,sabida haka Karki kuma yawon dare,maza shige kuma kibani key zan rufeku ta waje kar wani abin ya sameku" jiki na bari ta Shiga dakin ta miko masa,ya rufe yana me sauke ajiyar zuciya kai tsaye dakin ya koma!.
Kwance take tana karatun littafin hausa a wayarta tana jin dad'in labarin sosai,wayarta ta soma ringing, tsaki taja ganin sunan yayan nata rad'am yaa Mansoor,dagawa tayi cikeda faduwar gaba tace "Hello yaa Mansur ina wuni?"
"Amma shine kina ganin ina kiranki Deena bakya dagawa,tayaya aikinki dakikeso akansa yayi tasiri bayan bakya kwawo mana abinda mukeso,kuma sanin kanki ne ina matukar San farin cikinki,gashi har yanzu bema furta Kalmar auren kiba" bata fuska tayi tace
"Haba yaa Mansoor, wlhy nafika San kasancewar wannan al'amarin, sati daya fa kawai ne ban kawo ba,kuma ina tsoron ya fahimci wani abin,gashi ni sam wannan zunubin ya isheni kuma nasani Umma na ta damu da rashina matuka" nisawa yayi ganin yarinyar naso ta basu matsala gashi dodon makuba yafara korafi,yace cikin sigar rarrashi
"Ai Deena shiyasa nake so muyi mu kammala ki dawo gida hakanan,Allah Umma ta damu,Nima kuma ba sona nakeyi kina zama kamar wata karu waba,gashi kullum kina yawo cikin nikabi tamkar wata munafuka,dan Allah yau kiyi kokarin samo maniyyinnan na kameel sora kadan mu kammala" nisawa tayi tace "Ba damuwa Yaya Mansur dama ko yanzu shi nake jira zanyi kokarin samowa inshaa Allah"
"yauwa my sister se munyi waya zuwa dare" a haka sukayi sallama Deena name kosawa da wannan rayuwar da yayanta ya tsunduma ta aciki"
Wayewar gari koda su khairiyyah sukaje school kasa sukuni tayi,exam dinma haka tayishi jiki a sanyaye har jawaheer ta fahimci wani abun,Kallonta tayi bayan an tashi tace da ita "khairii wai me yake damun kine,naga alama sam bakya cikin wal wala" narai narai tayi da ido,sannan cikin zumudi ta kwashe komai ta sanar mata tace "jawaheer tsoro nakeji kar Nima ya kashe ni wlhy juju naji da kunnena kuma na gani da idona sam mijin Aunty Amal dan yankan Kaine ba mutumin kirki bane" nisawa jawaheer tayi,dukda yake kananun yarane dasuke da shekaru sha biyar da watanni shida be hanasu yin dogon nazari ba,tace "khairii ba tun Yauba nake zargin wani abu game da yaa Mansur,amma ki nutsu ki saisaita kanki Karki kuskura ki nuna masa wani abin,kazalika Karki nuna wa Aunty Amal komai,babban rufin asirin da zakiwa kanki kuwa shine dauke idonki akanshi,sam Karki kuskura ki kara masa labe,ke komai girman motsin da kikaji cikin dare karki kuma fita,mu bashi lokaci muga iya gudun ruwansa" gyada kanta tayi cikeda gamsuwa da bayaninta,daga ranar kuma bai kuma barin kofar su a bude ba sannan kuma yarage yawan yawon dare,amma kuma wasu lokutan yakan kwana ba'a gida ba seya sanarwa Amal meeting na company ne daddynshi bashida wannan lokacin da rana"
Awara jawaheer ke toyawa a kitchen tana shan waka a wayarta tana yar rawa wayanta ya soma ringing dauka tayi tace a sarari "Barrister Hilal" sannan cike da sanyi ta daga tace "Assalamu Alaikum" a daya bangaren ya ansata "Amin wa Alaikumussalam, jawaheer kina lapia" dan gyaran tsayuwar ta tayi sannan ta kashe cooker din tace "Ina lapia ya aikin?"
"Alhamdulillah kwana biyu ina kiranki wayanki a rufe"
"Ea na kashe wayar ne sabida ina exams yanzu kuma na kammala"
"Oh that's very good of you my juju" dariya tayi har yana jiwo sautinta tace "oh ya ilahi Kaima ka iya irin wannan sunan ba,ka biyewa khairiyyah ko?" Murmushi shima yayi yace "sunan yanamun dadi sosai Wlhy,idan na haifi yata ta fari sunan zan saka mata" yar dariya taku mayi "kana nufin baka da 'ya har yanzu?"
"Kalar tsofaffi namiki ne,ni ko aure ma banba fa"
"Kai tsoho ne mana,yakamata kanada yara goma yanzu" dariya sosai yayi yace "Naji nidin tsoho ne amma ki yarda dani sekin rigani tsufa" itama dariyar tayi "kanada ban dariya Barrister" dan bata fuska yayi tamkar tana ganinshi
"Ni yayanki ne so ki kirani yaa Hilal kawai banasan wani Barrister"
"Toshi kenan,zannan rika kiranka da wannan sunan"
"Jawaheer yaushe zanzo na ganki ne idan ba damuwa" Murmushi tayi "Bana tunanin Yaya nada wata damuwa dan kawai zezo ganin kanwar sa" shima din murmusawa yayi yace "Nagode sarakan tsiwa zanzo gobe da yamma inshaa Allah" sallama sukayi sannan ta juyawa awararta.
Barrister Hilal zaune tare da abokin shi Al'ameen Galadanchi suna tattaunawa game da matsalar damutane ke samu a duk lokacinda suka tsinci Kansu a cikin gidan mirror, nisawa Barrister Al'ameen yayi yace "Ba shakka wannan abin akwai mamaki Barrister Hilal family Kusan biyar suka rasa rayukansu acikin wannan gidan na mirror, nifa aganina mutane sudena baiwa Mansoor mirror auren 'ya'ya yensu,shine kadai mafita" gyaran zama Hilal yayi yace
"Ai Al'ameen wannan karon da matar kurun yazo,ba wanda yasan ina ya aurota,a binciken danayi kuwa yaran duka kannenta ne kaga kuwa akwai babbar matsala,abu d'aya na tabbatarwa Kaina shine zan nunawa Mansoor iyakar sa wannan karon sena saka ya shaida cewar hannun jiminar ma kala biyu ne,Akwai naci akwai na zubarwa,kuma ninan nine jiminar domin kuwa ko k'arfe na had'iya seya narke, na dad'e da burin tallafa wa bayin Allah dake Shiga hannun shi,balantana kuma yanzu danake tsananin kaunar jawaheer, wlhy se inda karfina ya kare,zan ari rigar daba tawaba in zama dan jarida sena tattaro muhimman information's ta hannun ta" Murmushi Al'ameen yayi ya daki kafadar abokinshi yace "Nima zan tayaka wannan aikin dan uwa".
Yau Amal ta tashi da zazzab'i sosai alamomi sun nunar mata ciki ne da ita,waya takira Mansoor ta sanar masa batajin dadi,da kanshi ya kawo family doctor ya dubata cikine da ita da watanni hudu da mamaki batasan dashiba se yanzu,sosai Mansoor yayi murna,take yabata kyautar miliyan biyar wai taja jari,kallon shi tayi tace " Yaa Mansoor nikuwa me zanyi da Ku dinnan ? Mena nema na rasa kawai sabida inada ciki zaka bani wannan kyautar?" Dariya yayi "ke kinsan billion nawa wannan cikin naki ze kawo mun kuwa? Lallai ma yarinya kina wasa,zan kawo miki tukwuici ma idan kin haihu" da mamaki ta kalleshi tace "Billions kuma yaa Mansur daga ina?"
"Ahaf daddy yace idan na kawo masa jika ze bani kamfunnansa duka biyu dake Lagos,kinga kuwa zanyi kudi da kyautar ki Kokuwa?" Murmushi tayi harga Allah ta gamsu da baya ninsa tace "seka fara adu'ar saukana lapia" Murmushi yayi yace angama.
Washe gari da yamma barrister Hilal yaje wurin jawaheer, a babban parlor aka saukeshi,suna tsakiya da gaisawa Mansoor yashigo gidan,kallon kallo suka tsaya yi shida Mansoor, cikeda faduwar gaba barrister Hilal ya mika masa hannu su gaisa,sam baiso suka hadu yanzu ba,ba wannan lokacin yakamata ya bayyana kanshi ba.....
Mom nuaiym.
[10/16, 8:06 PM] billygaladanchi: HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡
Billy Galadanchi
HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.
Allah ya baki lapia other half, Allah yasa kaffara ne.
05
Murmushi Mansoor ya sakarwa jawaheer yace cikin sigar wasa "Au kaddai jawaheer siriki na kika kawo mun?" Rufe fuskarta tayi da tafukan hannayenta tace "Laa yaa Mansoor bafa haka bane fa Yaya nane kurun" dariya yaku mayi "Ba waninan naganoki,kaikuwa dan samari kasani bana aurar da kanwata setayi digiri ta digirgije" dariya Barr. Yayi yace "Amin afuwa dai yallabai gwara Abani" zama Mansoor din yayi yace da Barr.Bismillah ka zauna mana" zama Barr. Yayi suka gaisa cikeda karamci sannan ya mike zuwa ciki,kallon ta Hilal yayi yace cikin sigar wasa "Wato kinga fin bobo zaki makalemun,Wama ze auri bakar mace,kin taba ganin fari ya auri baka" dariya tayi zuwa yanzu tafara sabawa da salon wasannin Brr Hilal, tace "Amma kasani koda nake blacky nafika kyau,nifa ko'a turai samun fata me lapia irin tawa se an tona,beside ko makaho ya laluba fuskana yaga black beauty irin totally en nan" sosai Barr Hilal yayi dariya,yace "ni banga wata kyakyawa ba anan kina fama ta manyan hakwara ga kuma dinple daya sekace kin roka" dariya ya bata harga Allah tace "kai tunda kake ka taba ganin inda kyakyawar ba indiya ko balarabiya take ba manyan hakwara? Duk wata kyakyawa acikin su hakwaranta na gabannan guda biyu dai manya ne,so abin kyawune,dimple kuwa da kake magana kasani wlhy shi ake yayi,sabida yanzu side pic ma akeyi,ko kawai sabida kanada biyu me ake da namiji da dimple sekace mace" dariya yayi har da kwallah,
"Kedai na kula sam bakya barin bashi,kanki dai akeji yanzu" ahaka yayita janta da wasanni cikeda hikima kasancewar yanasone ta saki jikinta dashi sabida yasamu tattara muhimman information's ta hannunta,Mansoor ne yashigo da sallamar sa ya kalli jawaheer ya mika mata wani tsadadden agogo da kwalin turaruka guda biyu wanda tsadar agogon kadai yafi 150k yace da ita "ki baiwa bakonki ni zan fita" godiya tamasa sannan sukayi sallama ya wuce,da Barr Hilal ze tafi kuwa jawaheer tabashi wannan kyautar yamata godiya ya tafi!" Mansoor na barin gidan ya nufi gidan su,a parlor ya taradda mahaifin shi yana karatun news paper ya gaidashi cikeda girmamawa sannan yace "Daddy wata dama ce ta samu fa" a jiye jaridar daddyn yayi ya washe baki yace "Mansoor kaikadaine ka gajeni har halayena ina yabawa jarumta irin taka,sanar dani menene sa'ar?" Murmushi yayi yace "Ai daddy inaso ne mu samu wurin sirri ko Umma bata nan ne?" Gyaran zama yayi yace "Batanan taje taron yancin mata" gyaran zama shimdin yayi yace
"D'aya daga cikin kannen Amal ne tasamu saurayi kuma inaga zamu samu nasararsa kasancewar sa me kwadayi,harna bashi turarukan da agogon se washe bakinshi yakeyi" sosai daddyn yaji dadi sannan yace
"Ka rabu dashi zuwa yanzu kuma wannan sam bajinishi ake bukataba dan kungiya zamu mayar dashi indai muddin muka bashi kyautar kudi ya karba yaku mayi amfaninshi dasu toko tabbas yazama dan kungiya kaga tunda garbati ya mutu ba mafedin fata" gyad'a kanshi yayi alamar gamsuwa yace "Hakan za'ayi Daddy Allah de ya taimakemu"
"Wanikam Mansoor ya labarin Deena ne? Inafa tsoron sanda mahaifiyar ta zata hadu da ita garinnan,bayan na sanar mata tana Canada kuma na hanata amfani da waya sabida tasamu tayi karatu,kaga zargi ze Shiga aciki"
"Ai daddy matsalar saurayin Nagane,sam wannan kameelun baya amfani da duk abinda tabashi,bincikena ya bani ma kyautar dasu yakeyi baudadden mutum ga rikon addini sallah bata wuce shi"
"To Allah yamana jagora idan hagu taqiya semu juya wa dama ai,tashi katafi Allah ya maka albarka".
Koda barrister yafita daga gidan yashiga mota kurawa agogon idon yayi yace a sarari yana Murmushi " Mansoor dan gidan mirror kana sha'aninka Aini bazaka rudeni da wannan kyautar nakaba,kuma da yardar Allah bazanyi amfani dasu ba,yana cikin tafiya yaji wayarshi na ringing dagawa yayi yana Murmushi yace "Blacky pentyn Allah" dariya tayi tace "wanda ba'ayi da burushi ba" dariya yayi yace "kinga kyakyawa kin makale menene kuma zaki rangada min kira daga rabuwar mu?" Langwabe kai tayi tamkar yana gabanta tace cikeda shauki
"Yaa Hilal plss karkayi amfani da wayannan kayan da yaa Mansoor yabaka" cikin mamaki yace
"Mesa haka Juju? Sabida me zakice karnayi amfani dasu,bayan yayan kine da kanshi yabani?" Cikin rada tace
"Karka yawa ita bincike indai kana sona to karkayi amfani dasu,banasan warin turaren ne kuma ni agogon bemun kyau ba" Murmushi yayi yace "To bazan yi amfani dasu ba amma karki zata dan wani inasan kine nifa banayi da blacky akai kasuwa" dariya tayi tace "Naji nidai karkayi using plss" haka yace mata bazeyiba ya ajiye wayar aranshi yana mamakin maganganunta,Kodai ta fara shinshi no wani abinne daga wurinshi,koma dai menene Allah shiya barwa kansa sani"
A bangaren jawaheer kuwa haka kawai takasa yadda da wannan kyautar daya yiwa Hilal,musamman idan tayi la'akari da yanda ya murtuke fuska @first daya shigo,sosai ta hango yak'e acikin dukkanin kalamanshi da dariyarshi sam yanzu kome Mansoor zeyi basa yadda dashi ita da khairiyyah abu daya ne yake kashe musu jiki shine yanda yake masifar kaunar Amal,wani bangaren na zuciyoyin dukkansu kuwa basu yadda soyayyar Allah da annabi yake mata ba musamman da yayi gargadi wa Dukkansu wai ba'a Shiga makota kazalika makota basa shigowa gidanshi.
Kwanaki sun tafi kamar yanda watanni suka shude cike da tafiyar lokaci,cikin Amal yanzu watannin shi tara tsaf,haihuwa suke jira ko yau ko gobe, a bangaren Barr Hilal shakuwa me tsanani tashiga tsakaninshi da jawaheer ya kasance kwakwaran awoyi uku daya baya iyayi batare da yaji muryar dan uwansaba,amma sam Barr. Baya barin su hadu da Mansoor hasalima baya zuwa gidan se in Mansoor din yayi tafiya....Yau Mansoor ba inda yaje yana zaune gida abinshi kasancewar yaga Amal batada lapia alamomi sun nuna haihuwa ce amma bayaso ya kaita asibiti sabida wasu yan dalilai dasuka shafi aikinsa....dakinshi yaje yashiga ya kulle kofa yakira waya,
"Kai Baba kabari kawai wlhy inaga yau Amal zata haihu,Yaune Dodo ze bani dauwa mammen Arziqi mara qarewa, kasanfa cewa yayi baya maso araba cibiyar jaririn da mahaifar shi so shiyasa ban kaita asibiti ba ina tunanin yanda hakan zata kasance cikin sauqi" dariya ya kwashe da ita yakuma cewa "Sekace shine na farko ai yara shida akace kuma shine na karshen daze janyo min arziqi banbancinsa d'aya sauran shine shi ina kaunar uwarsa bazan iya kashe taba,amma tsab zan badashi wlhy" jawaheer dake daidai bayan window din dakin tana kwashe shanya jikinta ya soma bari zufa tako ina tsatsafo mata yakeyi a rude tashigo cikin gidan tana zare ido,d'akin Amal tashiga taje kusa da ita inda take zaune ta zauna
"Sannu Aunty Amal baida lapia kaman ko?" Murmushin karfin hali tayi tace "banida lapia wlhy juju,gashi Mansoor yahana zuwa asibiti kumafa inaga nakuda ce dandai wlhy da azaba sosai" gyaran zamanta tayi cikeda damuwa tace "Eyyah Adda Amal sannu Allah ya saukeki lapia kinji,sedai kam nasha mamaki ko a kauye andena cewa ba'a zuwa asibiti komeye dalilin shi na hanawar oho" cikin azaba tace "wlhy kam rashin zuwa asibiti ko kauye sun denashi gashi bako wata tsohuwar dazata taimaka min" shiru kawai juju tayi tana tunanin mafita jiki ba kwari tabar d'akin taje ta kwashe komai ta sanarwa khairiyyah, take khairiyyah ta ce tasan abinyi suna zuwa parlor suka tadashi zaune ya kurawa TV ido khairiyyah ce tace
"Yaa Mansoor anya bazaka nemowa Aunt Amal tsohuwaba ta kula da ita,ranar kan ummien mu tarasu da babbar yayarmu tarasu wurin haihuwa jinayi ance wai sabida tana nakudar Baccine ba ungozoma sabida irinta se tsofaffi ,sabida daga wannan baccin suke mutuwa harsu har cikin basama haifeshi,gashi kuwa naga Adda Amal ma hakan takeyi tunfa dazu seta fara bacci seta farka a firgice" zabura yayi jin cewar zata iya mutuwa musamman da yaron cikinta yace
"Ahaf shine baku sanar munba da wuri maza ku kula da ita zanje nazo tsohuwar" to suka ansa a tare shikuwa yajuya yafita. Jawaheer tafara koyon mota,da Kansu suka sakata amota suka kaita asibiti,dakyar aka karb'eta kasancewar ba'anan take awon ba,basu dade ba kuwa ta haihu yaronta namiji santalele sak ubanshi,aka yanke cibi aka kuma wankeshi tas aka shirya yaron a had'adden kaya....koda Mansoor yadawo gidan da tsohuwar yaga wayam bakowa hankalinshine yatashi yashiga kiransu suka masa Banza,seda ta haihu sannan jawaheer sarakan rashin tsoro takirashi
"Ke jawaheer gidan ubanwa kukaje?" Wayan cewa tayi
"Laa yaa Mansoor karka daga hankalinka ta sauka lapia anan sabitin Aminu Kano ansamu baby boy me matukar kama dakai" cikin gidama yace
"Anyanke cibi?" Cike da mamaki kamar bata fahimci shiba tace "Laa Mansoor katab'a jin inda aka haihu ba'a yanke cibiba yaro ai mutuwa yake an rabashi da uwar tuni gashi ma a hannun khairiyyah yasha kayan sanyi abinshi" kara gigicewa Mansoor yayi
"Amma ke jawaheer ban sanar muku bansan Aje asibiti ba ubanwa ye yace kuje?"
"Yaa Mansoor bakaga ba kadan yarage ta mutu wlhy kuma munga ka dade ne" tsaki yaja ya kashe wayar ya sallami tsohuwar ya durkushe anan yana kuka,aranshi yace asarar dasuka masa zasu ganene wlhy duk seya kashesu,yanzu mezaice da dodo ance karya kuskura araba jaririn da mafarin cibiyar sa....gaba daya Mansoor ya rude gudun kar asirina ya tonu yasanya yaje asibitin ga mamakinshi kallo daya yayiwa yaron yaji yana masifar kaunar sa har ranshi bama yanda za'ayi yawani badashi wannan itace haihuwa tashida amma be moraba....
Durkushe yake agaban Dodo yana bashi hakuri,cikin wata razananniyar murya yace "Kaga Mansur karigada ka bata wancan shirin, yanzu me zamu maka,kasani ni Dodon makuba aikina najini ne kuma munrigada mun shirya aikin da jinin ta,abu daya cikin biyu zaka zaba da dole Kayi shine, Kodai kabaiwa dodo jinin matarka yasha ya huce Kokuma ka tara da daya daga cikin kannenta harta samu ciki ta haihu kamayar mana da asarar daka mana kaima Kayi arziqi nahar abada" godiya yazabi tarawa da d'aya daga cikin kannen nata kota wace hanya ce dan yanason matarsa,da ace suna San haihuwa tabiyu dase yace su jira haihuwar Amal tabiyu tosu dole sabuwar mahaifa sukeso,cikin lokaci kankanin ya shirya yadda zeyi da Jawaheer...... Da safe ranar asabar suna zaune suna breakfast ya kalli jawaheer yace
"Jawaheer kinga gobe suna,kuma hajiyata na bukatar taimako,kije ki tayata atyukan ke kuwa khairiyyah ki zauna ki taya Amal nata" kallonshi tayi tace "Waze kaini nawa driver magana ne?"
"Driver duka biyun sunje cefanen abincin suna,sabida haka ungo dubu uku ki Hau taxi" batayi magana ba ta karbi kudin kawai,tana zuwa daki ta tarar Barr Hilal ya kirata,kiranshi tayi back take sanar mai inda zataje tana sauri ne idan ta isa zasuyi magana... Tana tsakiya da taron adaidaitar wata mota me bakin glass ta sha gabanta gashi tagaji kasancewar unguwar tasu tsit kantayi wani yunkurin se gani anbude motar wani ya fito ya cizgeta da karfi,suka bar unguwar da ita....wani parlor aka ajiyeta se kuka take gashi sun kwace mata wayar hannun ta,tana tsakiyar kukan taji muryar shi yana magana a razane ta dago ta kalleshi!!!!
0 comments:
Post a Comment