Barr Hilal ne ya kalli Amal yace,
"Amal ke har Yanzu yarinya ce naga Alama,bakya ganin bata wannan hanyar yakamata ki bulo musu ba,su yara ne ba lallai bane su hango abinda ke kika hango,wannan ba ita bace hanya data dace Kibi,sabida haka ina me baku shawara ku je kuyita hakuri,zan lallaba Matana na nusar da ita,shima kameel ze kwatanta nashi,amma zaki ruguza kyakyawan zumuncn da kika dade kina ginawa idan har kika biyewa zuciyar ki akan tafiya da garaje....... Nisawa tayi tace " Na fahimci manufarka Hilal nakuma gane inda na kuskure zan gyara da yardar Allah" godiya ska musu daga nan suka bar gidan,Kallonta Mansur yayi yana dauke da Muhammad yayinda take tuki,acikin kwayar idonta yana hango rudu da tashin hankali,dayan bangaren kuma yana hango kaunarsa kwance a ranta,hankalinsa ya tattara zuwa gareta ya kira sunanta a hankali tajuyo ta kalleshi yace
"Amal nagode" yafada cikin sanyin murya,dan langwabar dakai tayi tace "Yaa Mansur wlhy ina cikin rudu,gani nakeyi tamkar yaranna sun fini gaskia,anya bazamu hakura da juna ba kuwa" sauke kanshi yayi yaci gaba da kallon Muhammad batare da yayi magana,jin bece komaiba ya sanya ta juyo ta kalleshi tace cikin sanyinta
"Yaa Mansur bansan dalilin daya sanya dukda nasan Kaine ka kashe mun mahaifa naba,na kasa hakura da kai,banida damar hanawa zuciya ta tunaninka,ada har haushin kaina nakeji yanda a rayuwa na sakaka araina,banji na tsaneka ba seda kayiwa khairiyyah abinda ka mata,kuma na kasa yarjewa kaina ka aikata abinda ka aikata din, yanzu kuwa da duniya ta shaida cewar bada San ranka ka aikataba se naji tausayinka matuka har kuka namaka,wannan tausayin nakane ya rikida zuwa zallar soyayya mara adadi,dan Allah kamun halacci karka yaudareni" sakin hannun Muhammad yayi ya damko nata cikin Nasa yace
"Amal banida burin daya wuce saka miki da Alkhairi akan halaccin dakika nunamin,sam a tsarina ba cutarwa dama ba halina bane,karkuma kiga laifin khairiyyah lallai ne setaji ta tsaneni fiye da shed'an ma kasancewar na wulakantar da ita ga azabtarwa...." Murmushi Amal tayi taje ta saukeshi agidan shi dama acan ta daukoshi daga nan ta wuce gidan Ummie kai tsaye.....
Bayan sun gaisane ta daddage ta rerowa ummi jawabi abinda ke yafe da ita dan gane dason komawarta gidan Mansur,suna haka daddy ya shigo Mamie ce ta fayyace masa komai da ake ciki, nisawa yayi sannan a fusace yace
"Wlhy Amal lallai kina da kuruciya ke sam ba hankali a kanki tayaya ma zaki ce zaki komawa makashin iyayenki,koda a fagen yaqin annabawa ne se an girgiza miki, wannan wane irin rashin sanin ciwon Kaine,wlhy kinji narantse na dauki matsayina na ubanki yau ,ranar asabar ta jibi zan daura aurenki da Alhaj sammani nagano sam ba hankali a kanki,yaje can da tubansa amma dai bazaki koma masa ba tunda ba zuciyar karnuka ne dake ba,kuma ke Mamie kuje tare gidanta ta tattaro kayanta,bazamu zura mata idoba tana zaman kanta wannan zaman datake yasanya take gani tamkar ta ishi kanta aikin Banza aikin wofi,kafarki kafarta karki barota ita daya ku dawo tare" daga waya yayi yakira baba gambo,shaida masa komai yayi sannan yace dashi
"Zan turo maka da ticket number na jirgi guda hudu,kai matarka,kanwar mahaifiyarsu dakace ze Auwal,lallai Kuzo nan gobe jibi asabar agama komai dama shi sammani ya matsan tamun..." Ahaka suka yi sallama,hannunshi ya mika mata yace "Bani wayarki da mukullin motar ki " ba musu ta mika masa cike da ladabi yace cikin fusata
"Haj wlhy ki kula da Amal naga alamun ba hankali akanta,ko wayanki karki bata karta kirashi yace zezo ya manna mana hauka anan" shiru hajiyar tayi domin harga Allah bataga laifin Matakin da Alhj ya dauka ba,aganinta ma ba zuciya sam a zuciyar Amal,shasha ce mara wayau,itama yana fita ta hau banbami,Amal se kuka take,gashi ko zasu kasheta bazata iya musu musuba,a haka driver ya kaisu ta ebe kayanta duka dake Gidan dana Muhammad se sha'aninta take tana kuka suka bar gidan.....
Khairiyyah rungume ajikin kameel tana kuka ya dago da kanta ya kalleta girgiza mata kan yayi sannan ya sanya hannayenshi duka biyu ya taffo fuskarta,harshensa ya saka ya lashe mata hawayenta tatas,sannan ya cura bakinsa a nata,saqonninshi Masu zafi yashiga aika mata dasu tun tana dan janyewa har itama ta cuta yan yatsunta cikin uwar sumar daya tara a kanshi, tafara shanye yajin dayake bata,sun jima suna wasaninsu sannan ya saketa yace
"Khairiyyah menene na kuka kuma?? Kinsani bana San yawan kukannan naki ko kadan,bazan goyo bayan ki yarjewa Amal komawa auren Mansur ba kamar yanda bazan goyi bayan ki sake aikata mata rashin kunya ba,banj dad'i n yanda kika yiba dazu so karki kuma kinji sahiba ta?" Gyada masa kanta tai cikeda shagwaba tace
"Bazan kuma yaa kameel" mikewa yayi yace "dts very good of u princess" hannunta ta riko ya juyo ya kalleta,shagwabe wa tayi yace "ya akayi yan matan kameel?" Murmushi tamasa tace cikeda shagwaba "yaa kameel zansha" dawowa yayi ya kwanta itama ya kwantar da ita ya raba jikinshi da nata yana a saman ta yace cikin murya kasa kasa "yan matan kameel sanar dani me zakisha? " hannayenta ta saka ta rufe fuskar ta,janye hannayen nata yayi yace
"Gaya mun mana Yanmata na I'm all urs fa" cikeda jin nauyin tace "Alawar dake cikin harshenka zan tsotsa" dan cakulkuli yamata sannan ya matso daf da ita ya tura mata harshensa waje,kankameshi tayi sannan a hankali ta turo bakinta ta cafko harshen Nasa ta lumshe idonta lokaci daya suka suke ajiyar zuciya kamar yanda shirun wurin yakoma numfarfashi a hankali,sunfi 30 mnt suna wasa da ba kunan junansu cikeda kwarewa sannan dan kanta tayi pulling out cikeda kasala, kurawa juna ido sukayi shikuwa ya lumshe nashi a hankali ya bude su ya sauke akanta wanda ita har yanzu kallonshi takeyi,iska ya hura mata cikin ido take ta lumshe manya manyan dara daran idonta yace..."Yan Mata na kadan ya rage ki cire mun harshena yau dinnan" Murmushi tamasa tace
"Yaa kameel ba kadanba nake shagala idan ina kallon dan bakin kannan me dauke da pink lips da madaidaitan hakwara ajere farare tas,idan kuma naga harshenka a waje se ka kashe mun jiki ba abinda nakeso na tsotsa sama dashi" laquce mata hanci yayi yace murya can kasan makoshi
"Yan mata na wlhy bakin kinan yafi nawa zama attractive, wasu loktan idan kina magana se Inga tamkar ba wannan dan tsurut din bakin naki bane ke furta wayannan kalaman,bana gajiya da tsotsar shi,shiyasa duk bayan minti daya sena tsotsa" dariya tayi tace "kai dama gwanine wurin fasawa mutum kai ai,kafi shahara a wannan fannin yanzu dai kawo kunnen ka kaji" mika mata kunnen yayi ta rike kanshi ta hura masa iska me cikeda d'imi sannan ta zura harshenta me tsawo da taushi tafara masa wasa,anan ya mace ya kasa koda kwakwaran motsi se lumshe ido yake yana budewa,yana fesar da wata iska me zafi a bakinshi gashi ya gama shanye yajin gidan da surutanshi.... Sanda dan kanta ta sakeshi,juyowa lumsassun idonshi yayi yace " Ban koshi ba y'an matana" itama da lumsassun idon nata tamkar mejin bacci ta budesu ta kalleshi
"Mene baka koshi ba yaa kameel?," rugomota yayi sosai yace " wannan wasan dakikemun mana yan matana" kara yin kasa tayi da lumsassun idonta takara lumshe su "yaa kameel koshi fa,se kace wani tuwo" Murmushi ya mata ya manna mata kiss a forehead nata,suka tsunduma faranta tan junansu,Ummie Aisha se faman rikeni take mu tsaya gulma,nace ni billy ba daniba.....
Yau dai kam abin ya kure ma Jawaheer, tsakani da Allah ta gaji kullum seya tayar matada Sha'awa seya wani barta hakanan,kitchen taje ta shirya masa chicken n egg da fried spaghetti with cabbage and liver souce, ta had'a hadadden zobon ta se tashin kamshin karan fari yakeyi da citta,wanka taje tayi ta karkade duk wata kunya tayi taje ta sanya wata yaloluwar riga pink iya karta gwiwa,ta d'ameta tsam, agaban rigar akwai wata igiyar da ake zugewa ga juju masha Allah akwai yalwar Heeps da ababen zama, lallausan gashinta ta zubo asaman bayanta wanda ya sauka sosai, dining tawuce ta ga komai normal sannan ta wuce dakinshi,yana zaune da tulin takardu a gabanshi ga laptop yana dannawa,sallama tayi cikin zazzakar muryarta ya dago ga ansata,rikicewa yayi ya kasa dauke idonshi akanta,a yangace ta karaso wurinshi,duk motsi daya tana tunawa da Bahijja matar malam jabir #Wani haske,na Ummie Aisha, kusa dashi ta tsaya yace yana Murmushi
"Blacky nane haka yau dinnan zoki zauna anan mana" wani shagwabe fuska tayi ta marairaice
"Allah ni baran wani zauna ba,bakada wani lokaci Sena wannan laptop da tulin takardu,Ni yanzu nagano Sune kishiyoyina" mikewa yayi matsa wurinta ya tallafo kafadunta yace
"Haba my beautiful black girl,menene kuma na rikici kiyi hakuri na karasa sena zo mu tafi" doddoka kafa tashigayi tana kuka sharshar
"Ni Allah yaa Hilal yunwa nakeji kazo muci abinci,idan bakazoba bazan ci abinciba yau gaba daya" Kallonta yayi yanda ta juya masa baya tana doddoka kafanta mazaunanta sai jijjiga suke,yanda suke jijjiga haka jikinshi ma keyi gaba d'aya.... Rikota yayi gaba daya ta fado jikinshi sannan ya daga ta cak zuwa dining se wutsilniya take da kafafu,be dire ta ko inaba se can, abincin ta zuba masa itama ta zuba nata ta zaga ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa....loma biyu yayi ya dauki cup na zobon data tsiyaya masa ya kurba,cikin sigar wasa yace
"Hmm su blacky an kware fannin girki da kayan kwadayi,ni tunda nake a rayuwa ban taba cin kalar wannan girki ba,ga wannan zobon tamkar a ingila,Allah ya miki Albarka" cikeda ta karfin hali tamkar wacce ke jira tace
"Ya zanyi ba dole nayi girkiba me gamsar wa,tunda na fahimci aikina kenan a gidannan" da mamakin kalamanta ya kalleta "Ban gane aikinki kenan agidan ba?" Tsuke dan guntun bakinta tayi kan tace "Idan ka kula kusan watana daya da sati Biyu a gidannan kaga ina wani aikinne bayaga dafama abinci me gamsarwa,kaga nifa naje islamiyya kuma acan an shaida mana cewar ya wajaba ga remu mu sauke dukkanin haqqoqin mazajenmu akanmu,kamar yanda kuma ya wajaba ku sauke namu haqqoqin,to ni I'm just following ur footsteps ganin kana bani kulawa da dukkanin haqqo qina yasanya Nima nake kokarin sauke naka,kar lahira na rasa bakin magana" sosai ya fahimci kalaman ta,yakuma gane yarinyar a takure take,shi aganinshi yana tausaya mata amma a yau ya kudiri niyyar sauke mata wannan tsiwar dake kanta....,kasa cewa da ita komai yayi suka gama cin abincin ya wuce dakinshi itama tayi nata....a dakin ya sameta yace
"Jawaheer zonan,sameni a Dakina" haka kurun taji gabanta ya fadi domin baya kiran sunanta se idan babban abune,mikewa tayi jiki ba kwari tabi bayanshi,a saman gado ta sameshi tace,"Yaya gani" Kallonta yayi ya dauke kanshi yace "kashe wutar dakin Kizo ki kwanta" a dirirce tace "banajin bacci"
"Aiba tambayarki nayi ba,ko kinji nace Kizo ki kiyi bacci" ganin ba wasa a maganarsa ya sanya ta aikata abinda yace,can karshen gadon ta takure,yaje ya matseta ta bayanta ya rada mata a kunne
"Babyna yada bani baya haka,wasa nakeso muyi " so tayi tace masa "katayarmun da Sha'awa ka barni a uku ko" se kuma tayi shiru tana jinsa yafara aika mata da saqonni Masu muhimmanci,a take ta biye masa,suka shiga wasanninsu ,koda yazo shiga jikinta bata matsa masaba kasancewar khairiyyah tace mata da dadi,danna kanshi na farko tafara salati "yaa Hilal dan manzan Allah Kayi hakuri wlhy da zafi" dan tsayawa yayi ya kalleta acikin duhun, yace "Kiyi hakuri so nake na sanar dake abinda malamanku Na islamiyya basu sanar mukuba,kuma wannan ma ai yana cikin aikinki a gidannan" kuka ta fashe dashi,ya soma rartashinta yana mata wasanni harta saki jinta,koda yasoma kokarin shiga kuka sosai ta saka Amma be saurara mata ba, tana yakushinsa akan azaba bekobi ta kanta ba yaci gaba da abinda yake,seda ya samu nutsuwa sannan ya kula mutuniyar bata motsi,da sauri ya kunna fitila,ananfa ya hango ta cikin jini kaca kaca,gigicewa yayi yace aranshi "mekenan na aikatawa yar mutane.....
Ranar asabar din kuwa aka daura auren Aisha Amal da Alhj sammani,wanda tana kukan wannan abin da daddy ya matane ta ji wani mugun labari wai yan fashi sun shiga gidan Mansur dake rijiyar zaki sun masa yankan rago...wannan labarin ba karamin tayar mata da hankali yayiba....
Mom Nuaiym[11/6, 9:26 PM] billygaladanchi: HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡
Billy Galadanchi
HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.
22
Da sauri yaje ya ebo ruwa a cup yazo ya Shafa mata a fuska,sauke ajiyar zuciya tayi ta bude idonta a hankali,kallonshi tayi se kuma ta rufe idon ta saka masa kuka,ajiye cup din yayi ya tallafo kanta ya manna mata Sumba agoshi,a hankali yake magana
"Sannu Jawaheer Allah yamiki Albarka,wannan dalilin yasanya nake kauda kaina a kanki,tausayinki nakeji matuka,nasani juju my beautiful black wife yarinya ce karama,idan namiki wannan Zakisha wahala,amma ki kwantar da hankalinki bazaki kara jin zafi da yawa haka ba" har ya karasa maganganunshi batasan ma yanayiba,tashi yayi yashiga toilet yafito,dagata yayi cak ya nufi bathroom da ita batace masa komaiba har lokacin idonta a rufe yake,ruwan zafin daya hada mata ya saka ta a ciki ,wata uwar kara ta kwallah ta kankameshi
"Yaa Hilal zafi wlhy da zafi azaba nakesha ka tausaya mun ka fitar dani dan Allah" cikeda tausaya yace
"Wannan shine laifin malamanku na islamiyya sun kasa sanar muku cewar wannan abin da kukeso da zafi a farko,kiyi hakuri blackyn ya Hilal,wannan kadai ze taimakeki" tana kuka tana yarfe hannaye har samu sassauci,wanka ya mata da kanshi tanata nonnkewa sannan ya dawo da ita dakin,kan doguwar resting chair ya direta kasancewar kadon a hargitse yake,ya tattare komai da kanshi, sannan ya shirya ta ,jawaheer ankai karshen tsiwa domin kuwa ba kinnan ya mutu mututus anji maza lolxx.... Daddy Ne yakira Hilal a waya dasu akayi daurin auren sannan kuma suka ji mutuwar Mansur mara dadin ji hankulan su ya tashi kuma ya basu tausayi ainun..... A ranar aka kai Amarya,ba laifi angon datake tsammani tsohone Ba tsohone,sam baze wuce shekaru 42 ba anan zamu iya kiranshi natashi,se washe baki yakeyi,bayan yan kai Amarya sun watse seya zauna a kusa da ita yace
"Amal nasani ban miki adalciba, kasancewar ban bayyana kaina agarekiba har zuwa wannan lokacin,haka Allah ya tsara kuma ina fatan zaki yarda da kaddara ki rikeni hannu bibiyu,ki yarda dani Amal ba cutarwa a tsakanina dake,matana Allah ya mata rasuwa kuma bani wata matsala,Muhammad kuma zancen mutuwar mahaifinsa ya riskeni,namiki Alkawari bazeyi maraiciba indai ina Raye,nine nan zan zame masa gata na duniya da lahira Inshaa Allah, dan Allah Amal ki saki jikin ki" kasa cewa dashi komai Amal tayi kawai dai ta sadda kanta kasa ne sabida kunya,wanna ne ganinta dashi na biyu kuma a ganin farko sam bata kalli koda inda yake ba,kuma wannan ganin,data masa lokaci daya setaji ya kwanta mata arai matuka,matsawa yayi daf da ita ya rungume ta yace "Amalus na yada kunya haka? Nifa mijin kine ko sena cire wannan kunyar zaki fara mun magana?",nan ma batayi magana ba Banza ta masa......sosai Amal tayi mamakin yanda sammani ya tafiyar da ita cikeda kwarewa ga wasanni Masu daukar hankali kuma na ban mamaki komai nashi ya gama burgeta da kyawun fuskarsa dana surarsa da sanyin halinsa uwa uba kuma shekaru kadai ze nunawa Mansur amma sammani ya kere Mansur a komai ma har nagarta da kamala.....washe gari Amal a kunyace ta tashi yanda ta dage ta biye masa a daren jiya,wanka ta tsala ta caba ado da riga iya gwiwa ash color an mata adon stones jajaye ba dankwali a kanta ta tufke lallausan gashin kanta a tsakiya,ba wani makeup tayi ba amma tayi kyau ainun,kitchen ta fada ta duba available abinda ke akwai ta daddage ta hada breakfast najin dadi,a can ya sameta yana sanye da gajeren wandon jeans iya gwiwarsa da yar shirt fara me tambarin Playboy, bata San da zuwanshiba ta bayanta yayi hugging nata ya manna mata Sumba a wuya,kasa koda kwakwaran motsi tayi ya rada mata
" my Amarya is the best wlhy,kinga yanda kika yi kyau kuwa? Ba'a ma magana wlhy" Murmushi tayi sannan cikin sanyi tace
"Good morning my charming prince" be taba tsammanin jin wannan daga bakin taba,tallafota yayi gaba daya ya juyo da ita "Morn beautiful how was night?" Murmushi tayi idonta kasa tace
"It was really romantic, all thanks to you" sosai yaji ya kara kaunarta,matseta yayi sanda tayi kara sannan ya sassauta rungumar ta yace " Baby Amalus trust me ur just the best u really made me feel alive,keta dabance my Amal ban taba haduwa da macen data kaiki ba a komai ma,kuma tukwicin daren jiya na nan na ajiye miki" Murmushi tayi tace "Aika rigada ka bani tukwici charming,tun jiya na gano da banbanci na kuma dauki wannan matsayin tukwici babba" dagata yayi gaba daya be direta ko ina ba se farfajiyar gidan,nuna mata wata mota yayi kirar kia I robot ash color yace "Baby kinga tukwicin nan wannan motar,dama ke nasiya wa waccen motar tayiwa matana kadan sosai wacce kike hawa" kallonshi tayi kwallah har yacika mata ido,ta matso daf dashi ,hannunta duka biyu ta dora a jikinshi,dayan ta zagaye kugunshi dayan kuma ta sakala shi a wuyanshi tace hawayen na gangara a kuncinta,cikin sanyin murya
"Kai Alkhairi ne,wlhy kai Alkhairi ne Prince Charming,nazata rayuwa ta gama rugujewa,nazata tawa ta kare,nazata banida sauran amfani a duniya,Ashe gaskiyar daddy dayace kaidin masoyine na haqiqa Allah ya kara maka budi,ya daukaka mijina,ina alfahari dakai" murmushin shi me kyau ya mata yace "wlhy Amal idan kikamun halacci sena baki mamaki, zan shayar dake mamaki mara misaltuwa,fatana kawai ki soni dan Allah ba dan komai ba" ahaka suka wuce cikin gidan Kansu tsaye dukkaninsu cike da farin ciki.
Jawaheer kuwa koda dare yayi kasa girka komai tayi,Hilal yazo ya sameta yace "Jawaheer zomuje Dakina mu kwanta" da sauri ta zaro ido waje se kuma hawaye shaaa,murmushi yayi yace "blacky me aka miki na kuka kuma?" Langwabe kai tayi "yaa Hilal dan Allah kamun rai wlhy na tuba bazan kara ba" dariya yayi ya karaso cikin dakin ya sungumeta yace "ina yarinya ai wlhy Kinyi kadan se kin dauki darasi ina a islamiyar taku ba practical se zallar theory, Toni nan ba'a fini practical ba har theory dinma,dama sun barmun filin koyar dake practical ai" Jawaheer sosai take kuka,ni kuwa nace ohhh ni Wato dai Hilal ba tausayi kenan...
Mom Nuaiym
[11/8, 7:19 PM] billygaladanchi: HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡
Billy Galadanchi
HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.
23
*Bayan shekara daya*
Zamane na Amane tsakanin gidajennan guda uku cike da kaunar juna,bangaren Haj juju dai juna Biyu ne harna tsawon watanni biyar,yayinda Amal take da nata kusan 6 month, amma fa khairiyya shiru shiru har yau ba labari abin kuma yana damunta ga rigimar Hauwa kazama kullum ta yau daban na gobe daban,yauma kamar kullum a parlor suke zaune ita da Khameel tayi Matakin kai da cinyar kameel yayinda yake watsa da kananun kitson da aka yarfa mata,dan d'agowa tayi cike da shagwaba tace "Yaa kameel dan Allah kabari muje asibiti wlhy na damu" ran kwafowa yayi ya saukar mata da Sumba a goshi, "Baby haihuwa fa ta Allah ne bazamu janyo ta da karfin tuwo ba dole ne semun jira har sanda me bayarwa ya bamu" dan tsuke fuska tayi tashiga yarfe hannaye tna shura kafa "Allah ni yaa kameel so nake muje,kaga fa juju da adda Amal nikadaice kumama bansan mesa kake haka ba baka ma wani damuwa" dagota yayi gaba daya "yan matan kameel ki fahimceni ba wai bana so bane ina sone ki riqa yarda kaddara" shiru tayi tana nazarin kalamansa batada lavarin an sanar masa dawuya ne ta kara aihuwa tun a asibiti kasancewar a wancen lokacin sun zata shine mijinta acewar Su an dakawa mahaifarta wani abu kuma ta huje abune mawuyacin abu ta kara iya daukar ciki,be sanar wa kowa ba,Wannan dalilin yasanya bayaso suje asibiti kar ta gane,a hankali ta kalleshi,tace "yaa kameel dan Allah da manzan sa kabarni inje Inji takameme meyake damuna inaji ajikina cewar banida lapia,Idan har kanasan kwanciyar hankali na ka barni naje" tausayinta ne ya kamashi yace "ki shirya gobe muje kinji yan matana" makalkale shi tayi Sega Hauwa a Kansu
"Banza jaka dakika gama wofintar da yayanki atitim ? Wlhy keda haihuwa har abada Banza jaka,ayi dai mugani Idan tusa zata hura wuta" Idan da sabo tariga ta saba kallon shi tayi tayi kokarin danne damuwarta da shagwaba tace
"Yaa kameel en matanka zata kwanta ka kaini daki plss" Murmushi yayi yana yaba jarumtarta ya tashi ya ciccibeta aikam basu ankare ba se ganin Hauwa sukayi har janyo kujerar dining daya,da karfin tuwo ta bugawa kameel a baya da sauri ya ajiye khairiyya yana kokarin kareta Amma ina sanda Hauwa tayi nasarar kwala mata a cikinta,take ta zube a wurin hauwa se banbami takeyi
"Ni zaku nunawa lalata yayan iska Shegu wlhy baku isaba" juyawar dazeyi yaga jini nabin kafafun khairiyya, dagata yayi yaga sam bata motsi yace..
"Hauwa wlhy duk abinda ya faru da yan matana sena wulakanta ki wlhy wawiya kawai jaka kazama" daganan yayi waje da khairiyya
"Ba yan matanka ba yan mazanka Banza na mamajo" Banza ya mata,asibitin data haihu can yakaita koda suka duba cikine da ita na watanni Biyu kuma yana ta zubewa duk iya taimakon dazasuyi sunyi amma ina seda yafita,ga Wannan abin ba karamun kara bata mata mahaifa yayiba,kwananta Biyu bata san inda kanta yakeba,koda ta farfado ma ba lapiya daga nan aka fara zancen cire mata mahaifa inda asibitin sukace Idan ba'a cire ba ze iya zame mata cancer!!!!! Kameel yayi kuka lokaci daya ya sallami Hauwa saki daya,jin Wannan maganar ya furgitar da karamar yarinya khairiyya har yau shekarunta basu kai sha takwas ba,kameel da aka baiwa takarda ya sanya hannu zaman dirshan yayi ya saka kuka dakyar dadynshi ya lallabashi ya sanya hannu, bayan Kwana Biyu aka Shiga da ita tiyata ana shirin farawa wani doctor abokin daddy dake London yace kar ayi azo masa da ita London ze yi gyaran mahaifar,hakan kuwa akayi batare da bata lokaciba aka shirya tafiyar visa ce kadai ta tsaidasu,suna samu kuwa suka wuce,ita da kameel kawai suka tai Alhamdulillah anyi aikin successfully komai ya dawo normal,soyayya ce me karfi akaci gaba da zubawa a London itada kameel,wanda basu dawo gida ba se da ciki karami dan wata wanda basu masan dashi ba ajikinta murna fal aran kowa,koda suka diro se ganin sashin Hauwa sukayi abude Ashe daddy ya dawo da ita,dama ya kudirta hakan aranshi,be nuna komai ba yaje gareta ga mamakinshi gidan qalqal an gyarashi ga kamshi gashi kuma an musu girki,haka dai zamansu yaci gaba da kasancewa ka daran kada han...... Amal ta sauka lapia ta samu yaronta kyakyawa aka saka masa suna kabeer,mahaifinshi naji dashi sosai da uwarshi....
Hilal Na kwance yana sharar baccinsa nakuda ya tashi juju, madam duk da kasancewar ta me tsananin raki seta kasa koda kwakwaran motsi taso sosai ta tasheshi sedai kamar yanda bakinta ya mutu haka bayanta ma ko kadan kasa motsi tayi Allah ne ya taima keta rigar baci kawai ce acikin ta aikam wata azabace ta ziyarceta me tsanani jitayi tamkar ta mutu gashi kamar za'a tsaga mata mara haka taji wani yunkuri tayi zata mike Sega baby ya fado tare da uwar lokaci daya yaro ya cancara uwar kara a razane Hilal ya farka a zatonsa mafarki yakeyi,fitila ya kunna a gigice yaga Wannan abin ficewa yayi ba shiri ya kwankwasa wa Hauwa gidan kameel daya,aikam akayi Sa'a kameel na gidan itace ta yanke cibiba da kanta yaro sak uwarshi blacky dashi,kuma ko tear bata samuba gwanin burgewa,Hauwa da Khairiyya ne suka gyara gidan tsaf da wurin tun da asuba Sega Amal Sallah kawai a ka idar,murna awurin Hilal ba'a magana yama rasa me zeyi....a daki ya tadda jawaheer tafito wanka bushewa yayi da dariya yace
."blacky wai kinga katon hancinki kuwa duk kin wani kara hawa,gashi kuma baki kamar zunubi" Murmushi tayi tace "Ga blacky nan Allah ya baka zan nuna maka bolar da ake kai baqaqe seka kaishi" dundu ya d'aka mata a baya yace "Dan gwal din kike cewa nakai bola,cikin shawaga ba tace
" Asshhh yaa Hilal da zafi wlhy" Murmushi yayi yace "yau dai Su madam anji practical ba theory ba,to sannu da kokari Allah saka da alkhairi ya baki lapiyarki yakuma raya mana Al-ameen" Murmushi tayi tace "Ameen abokinka kayiwa takwara kenan?" Murmushi kurun yayi yace "Aminina zakice"......ranar suna an darji naira ba laifi,kasancewa khairiyya tasha jikila gashi bata masan da cikinba yasanya tafara bleeding dole aka kaita asibiti take suka bata bed rest,ahaka taci gaba da rainon cikinta har lokacin haihuwar shi yazo, cikin ikon Allah ta sauka lapia baby girl sosai take kamada kameel se murna yake,matsala daya ne dole sanda aka cire mahaifar gaba daya Wannan lokacin kasancewar barinta a jikinta babban matsala ne. Dolensu suka rungumi kaddara,yanzu Hauwa ta zama ta gari zamansu suke lapia lau,bayan shekara daya kameel ya kara auro Deena,khairiyya bata saka komai a ranta ba ta dauki Wannan amatsayin tsarin Allah kuma mijinta na sonta gashi maryama Deena tana ganin girnan khairiyya sosai,a haka Hauwa tazo haihuwa awurin haihuwa Allah ya mata rasuwa,tabar yaro namiji Su khairiyya sunsha kuka komai ya dawo musu ba dadi,a haka suka dauki kaddara suka ci gaba da zaman aminci dajuna,khairiyya ce ta shayar da yaron da hauwa tabari.
Tammat bi Hamdilla.
Ina godiya agareku
Duniyar makaranta
Taskar billy Galadanchi
Hanjin jiminas fans
Sophe G novels
Mimei bee novels group
Huguma novels group
Haske writers Association
Pherty zahra novels
Hajja ce novels
Littafan hausa zallah
Da sauran daban anbaci sunayensu ba,nagode da dinbin kaunarku ga Wannan book din.
Mom Nu'aiym ce.
0 comments:
Post a Comment