Juyawa tai da sauri ta koma office d'in Habib.
Ammar ne ya tsaya kallan Habib cike da mamaki yace " yaya waye waccan d'in?"
Habib ya juya baya yace " bakaji abinda Seemah tacemai ba? Shine wanda takeso, bakuma soyayya ta wasa ba harda maganar aure take nufi."
Dariya Ammar yai yace " haba yaya kamar bakasan kanwata ba? Na sani guy d'in daya fita yana da cikar zati da kirar jikin da maza ke so, amma kanwata bata damu da wannan ba, wanda takeso shine wanda zai kula da ita, wannan kuwa kana ganin yanda yaganta ya wani d'auke kai?"
Habib ya matso kusa dashi ya rik'e hannayensa yace " Ammar, Dad fa nacikin tsananin damuwa bansani ba ko shine dalilin ko kuma da wani abun."
Ammar yace " Dad kuma? Nifa na kasa fahimtar abinda kake nufi? Kanasan kacemin yaran nan shi Seemah keso.................."
Da karfi sukaji an bud'e kofar, suka juya atare Seemah ce tsaye fuskarta a had'e, ta karaso kusa da Habib ta kalleshi ido cikin ido tace " Yaya mai kawa Deen?"
Habib ya had'e rai shima yace waye wani Deen?
Ta kara had'e fuska, tace " Jalal, mekamai?"
Ammar da mamakin abinda yake gani yace " Seemah waye waccan d'in dahar zai sa ki zo ki tsare yayanki da kike girmamawa?"
Idanta ne ya ciko da kwalla ta kalli Ammar tace " Ya Ammar na rasa dalilin dayasa akemin haka, na d'auka kowa yana da right d'in dazaiso abinda zuciyarsa take so?"
Ammar kam yama kasa furta wata kalma, haka kawai yaji ransa na b'aci, me yarinyar nan take nufi? Bai ankara ba kawai yaga ta tsugunna tare da rufe kanta da hannu tana kuka, cikin kukan take cewa" Ya Habib please karku rabani da Deen, yanzu gashi ya tafi bansan ya zanyi ba."
Habib haushi ya kamashi kawai yai waje da sauri duk da yanajin kukan kanwartasa har cikin ransa.
Yana fita Ammar ya tsaya kawai yana kallanta, Jin idanunsa suna neman kawo ruwa saboda kukan datakeyi yasa ya matso ya zauna shima kusa da ita a hankali ya jawo kanta ya kwantar akan kafad'ar sa.
Kwanciya tai lamu, ta fara share hawayenta, Ammar cikin sanyin murya yace " Seemah do u love him that much?"
Kai ta d'aga sannan tace " yaya bansan ya zanyiba yayi fishi dani?"
Ran Ammar yakara b'aci sai dai ya d'aure yace " Seemah kinsan me? Ta girgiza kai, yace" Falling in love is so easy but keeping that love is very difficult., bansan yaushe harkika fara soyayya haka ba, but karki bari soyayya da kikeyi tajawo fad'a tsakaninki da iyayenki da kuma 'yan uwanki."
D'agowa tai ta kalleshi ta kara share kwallarta, sannan ta kalli idanunsa da kwalla ta taro murmushi ta saki, tace " yaya please please kar ka k'i abinda nakeso, in har kaima kak'i Deen it will make it difficult for me. "
Murmushi ya kakaro wanda kana ganinshi kasan a iya leb'ensa suke, ta mik'e tace "yaya kataimaken please kaji?"
Yace name fa?
Tace ka k'ira Jalal a wayarka kacemai yai hakuri duk dabansan me ya Habib ya mai ba.
Ammar ya kalleta cikin mamakin gaske yace what? Me? Kai ta d'aga cikin halin ko in kula tace " kaine best bro d'in na kaikad'ai nake tunanin zakamin abinda nake so kuma, kaji yaya please? "
Kallanta yake da mamaki, sai dai haka ya sabar mata bai iya ce mata a'a ba akan duk abinda tace, wayar ya mik'amata tai tsalle tare da ansa tasa number tai dialling.
Jalal kam yana fita waje yai kawai tafiya yakeyi, zuciyarsa taf take da tunani kala kala, yarasa meya kamaceshi, sai dai abinda yafi bashi takaici kud'in da Habib ya bashi, me ya d'aukeshi? Jin karar waya yasa ya zarota daga aljihu ganin number ne yasa sai data kusan katsewa ya d'aga tare da Sallama, Seemah naji sallamarsa tai saurin mekama Ammar waya, Ammar ya mik'e tare da ansa duk da ransa bayaso, ya amsa tare da cewa "Yayan Seemah ne da muka had'u a office d'in Habib yanzu."
Ran Jalal ya kara b'aci yace " Wani kud'in kaima zaka kara bani akan in rabu da Seemah ko me?"
Sai a lokacin Ammar ya gane abinda ya faru, amma saboda bayaso Seemah tagane yace" Hmm da Alama wannan saurayin na kanwata yanada zafin rai."
Jalal ya kara had'e rai kamar Ammar na ganinshi yace " Ya akai to?"
Ammar yai ajiyar zuciya tare da kallan Seemah data rik'e hannunsa tana rokonsa, ajiyar zuciya ya sakeyi yace " Kanwatace tace in k'ira in baka hakuri."
Jalal yace " me kace?"
Ammar ya kara kufula yace " Kanwata ce ta damu da yanda taganka shine takeso naji ko komai lafiya."
Jalal yace " kana nufin saka tai ka k'irani ko me?"
Ammar ya had'e rai sai dai yazaiyi? Yace " gata tana san magana dakai." Yana kainan ya mik'ama Seemah wayar yai waje da sauri.
Seemah na amsa tace " My Deen ka sauko?"
Jalal yace " wannan yayankine?"
Tace " eh special brother na ne." Ya d'an tab'e baki kad'an yace" shine kikasa ya k'irani? Yama za'ai ya biye miki? Kuma ce miki akai in kika k'irani bazan d'auka ba?"
Turo baki tai tace " menene d'an nasashi yamin abu? Ni duk abinda nace masa inaso yimin yakeyi, sannan yanda naga kayi shine yasa nai tunanin bazaka d'aga ba."
Murmushi Jalal yai a ransa yace lalai an sangartata dayawa, a fili yace naji, zan k'iraki a wayarki anjima.
Tace zan jiraka fa? Yace eh zan kira.
Sunyi sallama ta kashe wayar tare da sakin murmushi.
Jalal ma yabi wayar da kallo ya saki murmushi.
Ammar kam yana fita toilet ya shiga yai ta watsama fuskarsa ruwa, kalaman Jalal ke dawomai, mirror d'in toilet d'in ya kalla sannan ya goge fuskarsa ya fito.
Habib na fita daga office ya nufi gidan Abba, ba yan sun gaisa da Zahra ne ya tambayeta mahaifiyarta, tace " taje Suleja d'azu da safe."
Habib yace wani abun ya faru ne? Zara ta girgiza kai tace " wlh bansani ba Yaya naga dai da safe Abba ya k'irata tana dawowa tace suleja zata."
Habib ya d'aga kai sannan yace" Abba fa?"
Tace yana falonsa kaje, Habib ya tura kai b'angaren Abba.
Yai sallama Abba ya amsa tare da bashi izini, Habib ya shiga, a zaune yaganshi kamar yanda ya saba da jarida a hannunsa, bayan Habib ya shigo ya ninke jaridar tare da kallansa, Habib ya karasa ya zauna a kasa tare da gaidashi.
Abba ya amsa yace " Habibu daga ina haka?"
Habib ya d'ago yace " Abba wani abu ke damuna." Abba ya kalleshi da mamaki.
Habb yace " d'azu naje gun Dad na ganshi a wani yanayin da bazan iya fad'a ba, Abba abin nan ya dameni ya hanani sukuni, da farko nai tunanin ko Saurayin da Seemah takeso ne bayaso, amma yanzu kaina ya kulle, bansan menene ba."
Abba ya gyara zama yace, saurayin da Seemah takeso? Kamar ya? Akwai wanda takeso ne?"
Habib ya d'aga kai yace " eh tasanar mana ni da Dad jiya."
Abba yai shiru, wato wannan ne dalilin dayasa Dad yake tunanin abubuwa kala kala? Yanzu gashi ganin seemah da Hajiya tai dakuma zuwan Dad dayai yasa ta takwanta d'an ciwonta ya tashi.
Habib ne ya katseshi yace " Abba ya za'ayi?"
Abba yace " zamuyi magana da Isma'el d'in sai dai inaso kaima inkaje gida ka kwace wayar Seemah ka kuma hanata fita harsai mun gama yanke hukunci da Mahaifinka."
Habib yace " to Abba amma Seemah zata yarda kuwa? Tanasan yaron....."
Katseshi Abba yai ya mik'e yace " Seemah gwal ce? Kai meyasa kaida mahaifinka halinku yake d'aya ne? In kasan abinda mahaifiyarta taja mana bazaka tab'a bin bayanta ba."
Habib ya kalleshi da mamaki yace " bangane mahaifiyarta ba? Ba Maman mu bace ta haifeta kake cewa ko me?"
Sai a lokacin Abba ya tuna, Habib da Jalal da babban d'an Abba Jafar tare suka kaisu karatu tun suna yara yan 15yrs da Habib da Jafar, junaid kuma 12yrs aka kaisu England gun Kanwar mahaifiyar Jafar dake zaune acan, Abba shiya had'asu ya biya musu karatunsu, a lokacin da abin ya faru suna can, Ammar ne kawai a gaban mahaifiyarsa lokacin yana d'an shekara 5.
Habib ya sake cewa" Abba bakace komai ba?"
Juya baya Abba yai yace " wani abune a raina, sam hankali na yana gun, kaje ka aiwatar da abin da nasaka kawai."
Yana kai nan ya juya yai d'aki, Habib ya bishi da kallon mamaki, me Abba yake nufi? Daga yanda Abba yai maganar yama za'ai ya yarda wai badashi yake ba? Shidai a iya saninsa Seemah mahaifiyarsu tana haifarta tabar duniyar, wannan shine abinda suka sani kuma dashi suka taso, to amma me Abba yake nufi da kalamansa..........?
❓❔❓❔❓❔❓❔da alamar tambaya......injini😂
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 3⃣2⃣
Ammar ne ya fito daga toilet, a bakin kofar toilet d'in ta ganshi yana fitowa ta d'aneshi, tace "yaya godiya sosai, thanks to you munshirya da Deen."
Ammar ya had'iye wani bakin cikin sai dai ya kakaro murmushi yace " are you that happy?" Kai ta d'aga sannan ta d'ago ta kalli Ammar tace " yaya inasan Deen sosai, kasan me?"
Kallanta yai zuciyarshi kamae ta fashe duk yanda yaso ya b'oye bakin cikin dake ransa ya kasa, Seemah tai murmushi tace " amma kasan wani secret yaya? Na kasa tantance wayafi matsayi tsakaninka da shi a guna."
Ammar ya kalleta jiyai zuciyarsa bazata juri ganin ta ba, shi zata had'a da wani bare da ko wata da had'uwa basuyi ba? Juyawa yai ya fara tafiya batare da ya tankamata ba, da sauri tasha gabansa ta rangwad'ar da kai tace " Ohhhh my bro ba dai haushi kaji ba?" Idanunsa ya runtse saboda bazai iya fad'a mata magana mara dad'i ba, gashi bai san ya mata magana, cewa yai" Seemah matsa mu wuce, Dad nake san gani."
Ya matsa kad'an daga kusa da ita, hannunsa ta kamo tace " wasa nake yaya." Juyowa yai ya kalleta tai murmushi tace " yaya inasan Deen sosai amma yama za'ai in had'ashi da kai? Ko kamanta ne? In na kwanta zazzab'i saboda shakuwarmu kaima sai ka kwanta?"
Tai murmushi sannan ta cigaba" tsokanarka kawai nakeyi, Deen soyayyar macen dake bala'in san saurayinta nake mai kai kuma soyayya ce ta jini yama za'ai ka had'a?"
Murmushi ya saki sosai ta had'a yanayenta biyu ta tafamai tace " yauwa my dear bros yanzu kafimin kama da yayana."
Ajiyar zuciya yai, yace " Seemah nima bansan meyasa naji haushin ba d'an kin had'ani da wani, na sani sarai soyayyar jini dake tsakaninmu."
Ta furzo iska ta sa hannu a goshinta tace " oh God my bros sai yaushe zamu dauka ne?"
Dariya yai, ta kalleshi tace " ji kafar yaya kamar wanda bata aiki?" Yace ni d'in? Gwalo tamai ta ruga da gudu, binta yai da gudu shima, suna gudu suna dariya.
Jalal kam jin yanayin jikinsa ba daidai ga magrib takawo kai yasa ya wuce d'akinsu ya bud'e, abin haushi 'yan d'akin suna zaune sun kure radio, jiyai kansa na juyawa haushi yasa shi ya fita tare da zama a waje, sanyin dake ratsashi yasa ya tabbatar zazzab'i keneman rufeshi, waya ya d'aga abin haushi ya rasa wama zai k'ira? Sagir ne ya fad'omai hakan yasa yai dialing number, ringing 2 Sagir ya d'aga tare da cewa " Jalal kaga Chairman d'in?"
Yace " Eh amma sagir please kana ina?" Sagir yace ina gida ya akai zaka zo ne?
Jalal yai shiru, Sagir yace " please kazo tun yaushe nake rokanka? Har cewa nai ka dawo gidanmu mu d'inga zama a d'akina ka k'i bansan meyasa kake haka ba.
Jalal kam sai nishi yake jiyake kansa na wani irin sarawa, ka karar disco duk ta isheshi, a hankali ya firta Sagir please kazo ka d'auken a wajen d'akinmu kaina...........
Jiyai kansa yayi kinkirikim, hakan yasa ya sauke hannunsa, Sagir ya saki kiran sunanshi, jin shiru yasa ya zari makulli da sauri ya fita.
Da gudu ya zuro motarsa, yana zuwa yaga Jalal a waje ya jingina da jikin bishiya, da sauri ya karasa kusa dashi, yanasa hannu ajikinsa yaji kamar wuta, da sauri ya d'auke hannunsa yace " Jalal meke damunka haka? Ya za'ai kanajin zazzabi haka bazaka gun likita ba, Jalal ya d'ago ya d'an saki murmushi yace " Sagir ka iso? Nagode fa."
Sagir ya kalleshi cikin tausayi, yace Jalal tashi muje asibiti, kai ya girgiza mai yace " muje chemist kawai, ina sha magani zai tafi."
Sagir ya amince da shawararsa, nan ya nemi taimaka mai Jalal yai murmushi yace " me kad'auken Sagir? Zan iya tafiya da kaina, is not a big deal."
Sunje chemist nurse d'in ya kalli Jalal yace " ya kamata kaje asibiti gaskiya, jikinka na burning dayawa."
Jalal yace bani magani kawai, nan ya bashi magani yana mamakin taurin kai irin na Jalal, Sagir ya kallu nurse d'in yace " haka yake indai Jalal ne."
Sun fito suka shiga mota Jalal sai kallan wayarsa yakeyi, da alama k'ira yake jira ko kuma yakesan yi.
Sagir ya kalleshi yace " ka tabbatar ba matsala?"
Jalal ya d'aga kai, Sagir yace " amma maganar me kukai da Chairman d'an da alama ba maganar aiki bane."
Jalal yai d'an karamin tsaki yace " banasan ma tunawa amma Sagir wani irin mutum ne Chairman?"
Sagir yai murmushi yace " mutum ne mai mutuncin gaske sai dai yanda na ga alama yana tsananin san family d'insa, yana girmama mahaifinsa sannan yanasan kanwar nan tasa."
Jalal yad'an tab'e baki, Sagir yace "amma maganar me kukai?"
Jalal ya maida kanshi jikin window baice komai ba.
Dad yana zaune a wajen gidansa, motar Habib ta shigo, mamaki yasa ya kalli motar har Habib ya karaso ciki, yai parking, Dad ya kalleshi kallo d'aya zakamai kasan akwai abubuwa dayawa a zuciyarsa.
Yana karasowa ya gaida Dad, Dad ya amsa tare da cewa " na d'auka Ammar ne zaizo."
Habib yace " anan zai kwana yace, nasan anjima zaizo suna tare da Seemah ne."
Dad ya d'aga kai tare da murmushi yasani ai, da za'abar Ammar da a gidan Habib zai kwana.
Habib ne ya katseshi da cewa " Dad ina da tambaya?"
Kallansa yai yace tame fa?
Habib yace " Ummi mahaifiyar mu, ita ta haifi Seemah?"
Gaban Dad ne ya fad'i ya kalli Habib cikin tsananin mamaki, yawo ya had'iya sannan yai saurin kauda kai, yace " wani irin shirme kake fad'a? Bansha sanar daku sanda Maryam zata rasu ba tana haihuwar Seemah ta rasu? Ko so kake inyi ta tisa maganganu na?"
Habib ya dawo ta gaban Dad ya kalleshi, yace " a'a Dad akwai wani abun bayan abinda muka sani, akwai abinda kake b'oyewa bayanan."
Dad ya had'a rai kamar me, yace " karka kara tunanin ba mahaifiyarku d'aya da Seemah ba, inba sokake ranka ya b'aci ba."
Yana kai nan yai saurin yin haryar ciki, sai dayai nisa ya juyo yace ka gaidata in ka koma, sannan kace mata nayi missing d'inta.
Yana kai nan ya karasa ciki.
Daga yanda Habib yake kallan Dad zakasan bai aminta da kalaman da Dad ya fad'a ba, dole dole akwai wani abun da ake b'oyewa kod'an yanda dad yake saurin katse maganar in an fara.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 3⃣3⃣
Jalal har sun d'anyi nisa sam haji hankalinsa ya kasa kwanciya juyowa yai ya kalli Sagir yace " Sagir please d'an taimaka ka ajiyeni anan, akwai inda nakesan zuwa."
Sagir ya girgiza kai yace " Kai Jalal, baka da lafiya na d'aukama zaka yadda na wuce dakai gidanmu, ina kuma zaka?"
Jalal yai ajiyar zuciya yace " gidan su Chairman akwai wacce nakesan gani."
Mamaki yasa Sagir yai baki sannan ya juyo cikin namaki yace " ban gane ba?"
Jalal ya juya kai yace " I don't know why but I feel that I must see her."
Sagir ya kalli Jalal yace " jalal me kake nufi da kalamanka? Wazaka gani? Ko ince wa kakesan gani?"
Jalal yai shiru, sagir yace badai Seemah ba ko? Jalal yace " Sagir bari na sauka nagode sosai."
Dasauri Sagir yace " a'a bandai san meke faruwa ba amma bazan iya barin ka katafi kai kad'ai ba."
Jalal ya kalleshi tare da cewa tnx alot.
Sun fara tafiya kad'an Seemah tak'irashi.
Murmushi ya saki tare da d'agawa, tace " My Deen!"
Jalal yai ajiyar zuciya tare da cewa " kina ina?" Tace gida d'azu muka dawo da ya Ammar.
Yace ganinan zuwa, yanajin karar datai tace " haba? Dagaske? Wayyo naji dad'i, ka kusa isowa?"
Murmushi yai yace " nad'auka zakice mezan zo yi?"
Tace "wa? Ni? Kaima kasan ko kullum zamu had'u bazan ce haka ba."
Yace " tsokanarki nakeyi bari inzo shaf shaf in ganki."
Sagir kam tuki yake amma gaba d'aya hankalinsa na kan Jalal meke faruwa? Soyayya suke ko me? Anma anya Seemah ce? Kodai wata ce a gidan?
Suna isa suka parking a gefen gidan, Jalal na mata flashing kafin wayar ta katse yaga ta fito, kamar irin tana waje tana jiranshi d'in ne.
Kodayake hakan ne d'an suna gama waya taji hankalinta ya kasa kwanciya, gyara fuskarta tai tad'an fesa turare ta sauko, a falo taga farida ta tambayeta Ammar tace ya fita yanzun nan inaji ya tafi, ta fito ta tsaya a waje.
Sagir ya fita daga motar ya kurama Seemah ido itakam dayake hankalinta baya kanshi bata na kula dashi ba, kawai juyawa tai tana neman Jalal, murmushi Jalal yai sannan ya fito daga motar tare da d'aga mata hannu, murmushi ta saki sannan ta karaso inda yake, Jalal ya kalleta ya saki murmushi itama murmushin tai tace " yau meya sameka? Nemana na ba zata haka?"
Ya kalleta yai ajiyar zuciya yace " meya sameni? Ahhh ni kaina ban sani ba, ko d'an d'azu bamu rabu ta dad'i bane? Kawai nakejin kamar ina tsananin san ganinki."
Murmushi tai sosai tasa hannu a kirjinta tace " wow naji dad'i sosai for this honour."
Tad'an rangwab'ar da kai tace " amma kamar numfashinka yana fita da sauri."
Murmushi yai yace " kawai maybe ko d'an kaina na ciwo ne."
Ai batasan sanda takai hannu goshinsa ba jin zaffin zazzab'i mai karfi yasa ta rik'ice, tace " My Deen ya haka? Meya sameka?."
Hannunta ya zare daga goshinsa yace " Don't worry ba wani abun bane, bari mu wuce."
Kallanshi tai idanunta sukai raurau kamar me shirin kuka tace " My Deen kaji jikinka kuwa? Yama za'ai kacemin karna damu?"
Kai ya kwantar a jikin kujera yace " karki damu in nasha magani komai zai dawo normal."
Sagir kam mutuwar tsaye yai, kawai kallansu yake, basu ankara ba kawai sukaji cikin muryar fad'a sosai ance " Seemah uban me kike anan?"
Da sauri ta juyo jin muryar Ya Habib, Sagir ma ya juya da sauri, Habib ya maka mata harara cikin zafin rai yace " ba magana nake miki ba?"
Jalal ya fito daga motar tare da kallan Habib yace " Chairman what do you mean by me takeyi anan?"
Habib ya had'e rai sosai wanda yasa cikin Seemah ya d'uri ruwa, ta kalli Jalal sannan ta kalli Habib tace " Yaya Deen bashu da lafiya please kamai a hankali."
Ran Habib ya kara tuzura yacw yace" kin wuce gida ko kuwa? Me yadaman da abinda ke damunshi?"
Zatai magana Jalal yace " Sorry Yaya zata shigo amma nan da minti 5."
Habib yace " what?"
Jalal yai murmushi yace " ban fahimci me kake nufi da metake yi anan ba bayan kafi kowa sanin meke tsakanin mu, bana tunanin kana zargin wani abun datake anan da ya wuce ganina."
Habib yace " mene?"
Jalal ya matso kusa dashi yai murmushi yace " yaya ka shiga ciki, yanzu kanwarka zata shigo sallama kawai zamuyi nima sauri nakeyi."
Habib sai hucci yakeyi ransa ya gama b'aci, lalai ma Jalal d'in nan, meya d'aukeshi?
Jalal ya juya kusa da Seemah ya rangwab'ar dakai yace " da alama dole muyi sallama yanzu, naga kamar yayanki jiranki yake."
Ta kalleshi hawaye suka zubo mata, kai ya girgiza mata yace " banasan kukan nan please. " ta kalli hannunsa tace " agoggonka?" Tai maganar cikin raunaniyar murya, da sauri yasa hannun a aljihu, idannunta suka sake zubar da kwalla, meya sami agoggon mu? Jalal ya kalleta yace " karki damu."
Share hawayen tai tana kallansa, yace ki shiga gida.
Habib ganin rainin hankalin yafara yawa kawai ya matso tare da fizgar hannun Seemah, tafiya suke da Habib anma kaba d'aya ta juya fuskarya kallan Jalal kawai take tana hawaye, shima shi kad'ai yasan me yakeji.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 3⃣4⃣
Ammar gidan Dad ya wuce kai tsaye, saboda ganin yanda Dad yai ta k'iransa, ya dade yana knocking kafin Dad yazo ya bud'e mai, yana ganin Dad yace " Dad saura kiris in b'ata ai gashi na iso a gajiye amma ka k'i bud'e min kofa."
Dad ta d'an hararesa sannan ya kamo kunensa da karfi ya jawo shi ciki, Ammar ya saki kara tare da cewa " Dad so kake d'an saurayin d'an naka ya rasa kunne daga nan ya rasa matar dazai aura?"
Dad yasa hanunnsa a hab'arsa ya d'an karkata yace " Wato tun safe daka iso sai yanzu zakazo ganin mahaifinka ko?"
Ammar ya dariya tare da cewa " Dad kasani kaima inda nake ai, balle na d'ade banganta ba, kasan me?"
Bai jira amsar Dad ba yacigaba" wlh yanzun ma gudowa nai ban bari munyi sallama ba ina tsoron kar inmuka kara had'uwa in kasa tahowa."
Dad ya girgiza kai yana wani murmushin farin ciki yace " Alhamdulila nasani ko yanzu na mutu Ammar bazaka bari swthrt d'ina ta wulakanta ba."
Dariya yai yace " yanzu dai ka huce kenan?"
Kara kama kumnensa Dad yai ya jashi cikin falon, Ammar ya rik'e kunnen yana cewa Dad yanzu in na kawo matar dazan aura taga anamin haka ai rainani zatai.
Dad ya sakeshi tare da cewa " ka kusa kawota ne? Na d'auka bakada wacce ta kwanta maka?"
Ya d'anyi kasa dakai yace " Dad anya lafiyata kalau kuwa? Narasa meke damuna, duk macen dana gani wlh sam bata birgeni, har addu'a nake Allah yasa in samu wacce zata dinga birgeni ko kwatan yanda Seemah take birgeni ne."
Dad ya kara sakin murmushi baice komai ba amma a zuciyarsa fal take da farinciki.
Ammar ya kalli Dad yace "Dad nasani abu kakesan fad'amin ko?"
Dad yai ajiyar zuciya yace " eh Ammar amma kuma ina tunanin, maganar nan dole sai Habib yana nam za'a yita, ka k'irashi kaji in zai saku damar zuwa to, inkuma sai gobema dai to duk d'aya ne."
Ammar yace ok bari na k'irashi, waya ya d'aga ya k'ira number Habib.
Habib kam bayan ya shiga da Seemah cikin gida, bai saketa ba sai da suka shiga d'akinsu ya saketa ta zauna a bakin gado tare da turo baki tace " Ya Habib wai meke damunka kwana biyu ne? Ko ka daina so nane?"
Had'e fuska yai yace " Seemah bawai san ki bane na daina sai dai bazan yarda kiyi abinda zai ja miki dana sani ba har karshen rayuwarki."
Cikin rashin fahimta ta kalleshi tace " San Jalal ne zai ja min dana sani? Ko kuwa me?"
Had'e fuska ya sakeyi yace " bani wayarki?"
Da sauri ta mik'e tsaye tace " ban fahimta ba?"
Habib yace " ki bani wayarki nace ko?" Seemah ta mik'e tare da turo baki gaba cikin shagwab'a tace " Ya Habib kasan dai bazan iya rabuwa da wayata ba ko?"
Matsoyai kusa da ita tare da fizge wayar yace " kanwata ajiye miki zanyi, sannan gobe kishirya mu fita yawo."
Yana kainan yai hanyar waje, zubewa tai a kasa tafara kukan shagwab'a tana bubuga kafa, tasani indai tafara wannan kukan to kome takeso sai an mata shi koda kuwa ba'a san yi mata, sai dai mamakinta yau Habib ko juyowa baiyi ba, duk da kasan zuciyarsa kukan na tab'ashi sosai sai dai bazai bari rayuwarta ta salwanta ba saboda yarinta ba.
Yana shiga d'aki ya kashe wayar ya bud'e drawer ya sata sanna ya zauna a bakin gado yana tunanin mezai wa Seemah dazai sa ta manta wani Jalal.
Wayar Ammar ce ta shigo ya d'aga wayar kamar bayaso, Ammar yace " Dad ne kesan magana da kai amma yace in akwai abinda kake ka bari......."
Katseshi yai da sauri da cewa ganinan zuwa yanzun nan, yana kainan ya katse wayar tare da yin waje da sauri, tunaninsa d'aya "Dad ya sauko zai sanar dashi komai."
Da sauri ya fito falo yai hanyar waje, Farida data fito daga kitchen rik'e da tire ta yanka kayan marmari aciki, ganin ya fito da sauri yasa ta shiga k'iransa sai dai inaaaa hankalinsa yayi waje sam bai kula da ita ba.
Ajiyar zuciya tai sannan ta koma kitchen d'in.
Habib da kanshi ya shiga mota ya fara driven ya fito yabi inda da Jalal ya tsaya da wani kallo ganin basanan yasashi yin tsaki.
●●●●●●●□□□□□□□●●●●●●●●●●●□□
Jalal kam bayan Seemah ta shiga gida Sagir ya shigo motar tare da kallansa yace " Jalal sam ban fahimce meke faruwa ba, dan Allah kamin bayani."
Kansa ya rik'e dayakeji yana sara mai ya juyo a hankali yace " muje Sagir zan fad'ama."
Nan Sagir ya tadda mota suka d'au hanya, sunyi tafiya mai nisa kafin Jalal yace " Sagir ina san Seemah." Juyowa Sagir yai ya kalleshi sannan ya maida kansa titi yace " Jalal amma kasan........
Wani irin murmushin kafin hali Jalal yai yace " I am not worthy ko?"
Sagir yace ba haka bane, ni a guna you are far much more worthy sai dai su a gunsu.........
Jalal ya kwantar da kansa yace " Nasani Sagir, su sunfisan 'yarsu ta auri wanda yake the same class da su."
Yai ajiyar zuciya sannan yace " Sai dai abinda ban fahimta ba shine, na d'auka in mace da namiji suna san junasu shikenan, na farko ita yarinyarnan tasan banida hali kuma a hakan ta aminta dani, na biyu yarinyar nan tana sona, so ni ina tunanin kamar abinda akeyi baya dacewa."
Sagir ya d'an kalli Jalal yace " haka ne Jalal abinda kafad'a haka yake sai dai yanzu rayuwar da ake ciki kenan."
Jalal ya furzar da wata iska sannan cikin kakkausar murya yace" Sagir kasan me? " sannan ya saki murmushi yace " a farko nayi tunanin kamar da wahala a barmu tare da Seemah sai dai d'azu zuciyata ta sanar dani wani abu, bazan rabu da Seemah ba duk tsanani da abinda zasu ce, sannan bazan yarda su wulakantani ba, wannan alkawari nama zuciyata."
Sagir ya kalleshi yace " Jalal please nidai shawarata d'aya shine ka hakura da yarinyar nan, ni yaushe ka fara soyayya haka dakake jin zaka jure komai na abinda za'a maka? "
Jalal ya maida kallansa jikin window yace " yanzu nafara shiyasa nakeji kamar nafi kowa kamuwa da soyayya."
Dariya sosai Sagir yai yace lalai Jalal.........
Nima nace Lalai.............
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 3⃣5⃣
Habib yana isa gidan da sauri ya bud'e mota ya fita ko kofar bai rufe ba, yai cikin gidan da sauri, bayan ya shiga da Sallama suka amsa mai yasamu guri ya zauna, Ammar na kasa kusa da Dad yana daddana waya, Habib shima ya karasa bangaren dake kallan Ammar ya zauna.
Ammar ya kalleshi tare da cewa "Yaya ka iso?" Habib ya d'aga nasa kai alamar eh yamaida kallansa kan Dad dayai shiru, a zuciyarsa kam addu'arsa d'aya ce Allah ya taimakeshi akan abinda yake shirinyi.
Habib ganin Dad yayi shiru yasa yace " Dad kayi shiru?"
Ya sauke idanunsa akan Habib sannan yamaida kallansa kan Ammar yai gyaran murya tare da cewa " inaso ku bani aran hankalinku nan."
Gaba d'ayansu suka maida kallansu kanshi, Dad ya had'iyi wani abu sannan yace " abinda nake shirin sanar daku shine......."
Duk sun zak'u gashi maganar Dad ta katse bai karasa ba, jin shirun dayai yasa Ammar yace " Dad yaka tsaya?"
Dad yai shiru sannan ya sauko tsakiyansu ya zauna tare da dafa Ammar idanunsa taf da kwalla yace " Ammar kasani inasanka ko?" Murmushi Ammar yai yace " haba Dad harsai ka fad'i haka?"
Dad ya kakaro murmushi sannan ya mik'e tare da takawa gaba dasu kad'an ya hard'e hannayensa ta baya, ya juya musu baya ya cigaba " lokaci yayi daya kamata in sanar daku wani sirri da baku tab'a sani ba, Ammar banaso ka sa wani mugun abu a ranka dalilin dayasa na yanke shawarar sanar daku shine Ammar nakeso ya auri Seemah."
Ba Ammar ba hatta Habib mik'ewa yai a zabure, Dad kam idanu ya runtse, Ammar da Habib a tare suka had'a baki suka ce *What?* Ammar ya cigaba da magana " ban fahimci me kake nufi ba Dad, ni in auri kanwata? Me kakesan fad'ane Dad?"
Habib ya amshe maganar da cewa " Dad me kake nufi da kalamanka? Wani irin zance kakeyi haka? Kana nufin akwai aure a tsakanin Ammar da Seemah ko me?"
Dad ya d'aure tare da share hawayen da suka kwaranyo ta gefen idanunsa, ya juyo tare da cewa " haka ne Habib akwai aure a tsakaninsu domin kuwa Ammar ba d'ana bane."
A tare suka kara cewa *what?* gaban Ammar ya fad'i zubewa yai kasa tare da kallan Dad cikin wani irin rud'ani, Habib ma ya kalli Ammar sannan ya kalli Dad yace " ban fahimceka ba Dad kanasan kacemin Ammar kanina ba kaine mahaifinsa ba?"
Dad ya d'aga kai tare da cewa " nasanar dakune saboda inasan had'shi aure da Seemah shiyasa na aika yazo kasar nan."
Girgiza kai Ammar ya shigayi da sauri ya mik'e yai waje da gudu, Dad ya runtae ido shikad'ai yasan meyakeji, Habib ya matso kusa da Dad, ga mamakin Dad gani yai Habib ya saki murmushi yace " Dad do u expect me to believe that? Mene? Ammar ba d'anka bane? Banda tsananin kama da kukeyi? Da muma mukeyi dashi? Me kakesan cewa dad?"
Dad yai saurin juya baya tare da cewa " kanina da nake tsananin kama dashi shine mahaifin Ammar yana haifarsa sunyi tafiya sukai hatsari shida matarsa wannan dalilin ne yasa na anso Ammar tare da alkawarin kula dashi kamar d'ana."
Habib yai shiru tare da jinjina kai yace " ayya meyasa baka tab'a fad'amin ba Dad?" Ganin Habib ya yarda da kalamansa ne yasa Dad ya juyo yace ba wannan bane da muwar da ya kamata muyi yanzu, Seemah kana tunanin zata rabu da waccen banzan yaron? Habib yai shiru sai can yace " Dad Allah ne kawai ya sani, amma yarinyar nan sai anyi da gaske wajen rabasu, har kud'i na bashi d'azu akan ya bar aikin dayake a company d'ina ya bar garin nan amma yak'i, Dad yaron nan yanada taurin kai."
Dad yai tsaki tare da cewa duk taurin kansa ai baifi karfin iyayensa ba, su kuma iyayen nasa nasan basufi karfin kud'i ba,ka bincikomin garinsu zanje har gidansu in basu kud'i su sa d'ansu yabar aiki a company d'inmu.
Habib ya jinjina kai yace " wannan ma is a good idea."
Dad yace " naso in d'auketa mubar kasar amma kuma sai nai wani tunani, inaso kafin mu koma ai baikonsu da Ammar inyaso daga baya sai ai auren."
Habib yai shiru bai amsa ba, shidai tana mamakin wannan al'amarin.
Nan yai sallama akan gobe zai turo address d'in gidansu Jalal.
Jalal kam da kyar ya lallab'a Jalal suka wuce gidansu, sunje shiga gate d'in gidan Yaga k'iran Abba, da sauri ya d'auka tare da saisaita murya ya gaida shi, Abba ya amsa tare da cewa " Ashe ka koma?"
Jalal yace " wlh k'ira na akai na gaggawa."
Abba yace " ba wani abu dama na k'iraka ne na sanar dakai na yanke hukunci ranar Juma'a rana ita jiya kenan, za'a d'aura maka aure da Zainab, ka kuma tabbatar ka iso da sassafe."
Cikim razana Jalal ya bud'e murfin mota ya fita tare da cewa " Abba ban fahimci me kake nufi ba, bangane Aure ba?"
Abba ya had'e rai yace " na yanke hukunci kuma baka isa ka bijirema hukuncina ba kafi kowa sanin hali na, sannan bazan yarda da wani shirmenka ba."
Jalal yace " Amma Abba......."
Cikin fad'a Abba ya katseshi da cewa karka kuskura Jalal kace zaka d'inga musu dani, kai ko kumya bakaji ba? Yarinyarnan tun tana karama take taimakon mahaifiyarka da kanwarka, kai kana tunanin dabadan Allah yasa tana nan ba wani abun ai mahaifiyarka bazata iya jura ba."
Jalal zai kara magana Abba ya kara katseshi da cewa " ka kuma tabbatar ka zo ranar juma'a da wuri d'an intanine gobe ma za'a d'aura auran sa'a kaci mahaifiyarka ta nemi izini zuwa juma'a." ABBA nakainan ya katse layin.
Bin wayar Jalal yai da kallo meke faruwa? Dasauri ya danna number Umma sai dai lokacin tana zaune kusa da Abba hakan yasa tak'i d'aukan wayar d'an umarnin Abba ne kar kowa ya d'auki k'iran Jalal.
Ganin taki d'auka yasa ya k'ira Zainab tana zaune akan sallayar datai salla tana lazimi, ganin k'iran Jalal yasa tai murmushi sai dai data tuna me ya mata da kuma umarnin Abba yasa ta canza fuska ta koma kalar tausayi, sai dai inaaaaa bazata iya ganin wayar Jalal ta katse ba tana zaune, saura kiris ta katse ta d'aga tare da sallama, Jalal ya amsa tare da cewa " Zainab meke faruwa? Ban gane aure wani satin kai tsaye ba?"
Zainab tai kasa da kai a hankali tace " Yaya bansan nima meya faruba gaskiya kawai tun sanda Abba ya fita d'in nan, inaji gidan mu yaje, d'an bai dawoba sai daf da magrib, bansan meya faruba kawai yacemin inyi hakuri lefe da wani sha'anin biki ayi daga baya in inaso amma wani satin za'a d'aura mana aure amma anan zan zana kafin ka samu gida."
Jalal yaja dogon ajiyar zuciya tare da cewa " it can't happen." Yana fadar haka ya katse wayar tare da neman number Seemah, sai dai duk yanda yake k'ira layin a kashe yake matar take sanar dashi.
Hannu yasa ya shafi kansa sannan ya furzar da wata isa tare da naushin jikin bango da hannunsa, yaji zafi kwarai sai dai baikai zafin da yakeji a zuciyarsa ba.
Sagir ne ya matso ya dafashi, baice mai komai ba.
Seemah kam taci kuka harta gaji, Aisha sai dariya takeyi, d'an karma tai lallashi yasa taki shiga d'akin, gani take gwara a saita mara kunya da sakalci.
Farida kam shigarta uku tana bata hakuri amma inaaaaa seemah taki hakura sai kuka takeyi itadai a bata wayarta.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
No. 3⃣6⃣
*Washegari*..........
Seemah na kwance tana bacci Dad ya karaso gidan, bayan sun gaisa da Habib da matarsa da 'ya'yansa kasancewar yau lahadi kowa na gida, Farida ta kwashe su Ra'isa suka barmusu falon, Dad ya kalli Habib yace " yaya ka nemo gidan?"
Kai Habib ya d'aga tare da cewa na nemo Dad dama na tab'a tambayar abokinsa Sagir a wani gari Jalal yake shine yacemin Birnin/gwari, to shine nasa akamin bincike a garin, ya fada tare da mik'amai takarda.
Habib ya kara kallan Dad yace " Amma Dad kana ganin hakan ne ya dace?"
Dad yai murmushi yace " Habib kenan, ban tab'a ganin yaran ba amma tunda kar baiji kunyar kallan Seemata ba yace yana so hakan ya nunamin he is stubborn sannan iyayensa ne kad'ai zasuma tufkar hanci."
Habib ya gyad'a kai alamar gamsuwa, Dad ya amshi takardar tare da cewa yauwa Habib nagode, sannan ina so anjima ka shirya kaje Suleja ance jikin Hajiya ya tashi.
Habib ya amsa ta to, tare da cigaba da cewa " Amma Dad ya maganar Ammar?"
Dad yai murmushi tare da cewa "karka damu yana Nordic Villa, sai wajen 1 na dare dana dameshi da waya shine yamin text."
Habib yai kasa dakai yana tausayin kanin nasa, Dad ya mik'e tare da cewa ina baby na?
" Tana d'akinsu mayb bata tashi ba."
Dad yai hanyar d'akin kai tsaye a raina nace lalai rayuwar turai ta zauna muku amma mu anan yaza'ai uba ya wuce cikin gidan d'ansa kai tsaye? ?????
Yana isa kofar d'akin daidainan Aisha ta fito daga d'akin,, ganin Dad yasa tai saurin risinawa ta gaida shi, Dad ya amsa fuska a sake yace " Seemah fa?"
Ta kalli d'akin tace " tana bacci."
Bai amsa mata ba ya tura d'akin tare da sallama, a kwance take tama baccinta zama yai gefenta yana kallanta, ba shakka tana tsananin kama da mahaifiyarta, sai dai ko d'an shi kansa bai san uban bane???? Hannu yasa ya shafi gefen kanta a hankali Seemah ta bud'e ido ta saukeshi akan Dad, murmushi ta saki cikin abin bacci tace " My Dad yaushe ka iso?"
Yanzun nan ya fad'a yana kallanta.
Ta mik'e zaune tare da rik'e hannayensa, tace " Dad please kad'aukeni mukoma gidanmu kaji?"
"Bakyasan gida Habib d'in ne ko me?"
Sake hannun Dad tai ta turo baki tace " banaso Dad ni Yanzu nama daina san Ya Habib, Dad please mukoma kaji? Gani gaka ga ya Ammar hakan yafi dad'i."
Dariya Dad yai yace " Seemah kinsan ba mace a gidan dazata d'inga girki da sauransu."
Ajiyar zuciya tai tace " Nidai to banasan gidan nan"
Dad ya mik'e tare da kallanta yace " Amma yanaga idanunki haka?"
" banacr maka banasan gidan nan ba? Dad dan dai bakasan me ya Habib yamin bane, yanzu ko waya ma bandashi, narasa meyasa bayasan Deen bayan ni zan........."
Wani kallo da Dad ya maka mata yasa tai shiru tare da cewa " ni duk kun daina sona ma ina Ya Ammar d'ina?"
Dad ya saki fuska yace " yauwa dama abinda nazo fad'a miki kenan, Ammar bayajin dad'i shiyasa nakeso kije gunsa."
Dirowa tai daga kan gado tace " me ya sameshi? Jiya fa lafiyarsa kalau."
Ganin yanda ta rud'e yasa Dad yai dariya yace " Yana Nordic villa kishirya kije."
Da sauri ta zari towel d'in wanka tace " Dad nayi nan."
Dariyar farinciki Dad yai yanasan yanda sukesan junan.
Fitowa yai sukai sallama da Habib da kuma Farida ya fad'a motarsa driver ya jashi sai binin gwari.
Jalal kam sam jiya kasa barci tai saboda bayasan takurama Sagir yasa ya kwanta kamar mai bacci harsai da yaga Sagir yafara bacci sosai sannan ya mik'e ya d'auro alwala ya fara sallah a neman mafita agun Allah sai wajen karfe 3 bacci ya d'aukeshi akan sallar.
Da safe bayan sunyi wanka Sagir yabashi d'aya daga cikin kayansa yasa, nan ma dakyar Jalal ya yarda, Sagir ya nunashi da yatsa yace " gaskiya Jalal bansan irinka ba? Meyasa ne sam bakasan kai amfani da abin wani?"
" Sagir tun ina karami haka na taso, Hali nane, banasan amfani da abinda ba nawa ba ko neman alfarmar wani ko kuma bari kud'i su nemi cin galabata."
Kai Sagir ya jinjina yace " shiyasa kowa yake respecting d'inka, wlh ko ni ina bala'in ganin girman ka."
Murmushin dabai wuce iya leb'e ba Jalal yao sannan ya d'aga waya ya kara k'iran umma sai dai yanzun ma bata d'aga ba, ajiyar zuciya yai tare da kallan Sagir yace " tunanin zuwa birnin gwari nakeyi."
"Yanzo? Ba jiya ka dawo ba?"
Ido Jalal ya kankance ya kurawa wani gun ido baice komai ba.
Sagir ya daga kafad'ar sa yace " Calm down Jalal."
Kallansa Jalal yai yace " how can I? In this situation? Ga nakasa samun Seemah?" Sagir zaiyi magana yaga Jalal ya mik'e tare da cewa " Inaji gidansu Seemah zani."
Zaro ido Sagir yai yace " Jalal meke damunka wai? Yaushe kazama haka wai? Taya za'ai kaje gidan da inagani a ido ba sanka ake ba in fact ni tsorona ma karka rasa aikinka."
Jalal yasaki wata dariya yace " I wish zasuyi tsautsayin korata daga aiki, dana nuna musu shayi ma ruwa ne."
Sagir ya kalleshi da alamar tambaya yace " kamar ya?"
Jalal ya had'e hannayensa ya fara takawa yace kai kana tunanin in suka koran daga aiki ban musu laifin komai ba zan barsu haka? Takarda zan tura harsai sun sanar dani menai dana cancanci kura, in ba haka ba su amsa k'iran hukuma."
Sagir yasa dariya tare da tafi yace " Jalal kenan u are really smart suma nasan bazasuyi wannan gangancin ba, amma dai duk da haka ka kula."
Jalal ya juyo yace " nagode Sagir amma please in ba inda zaka aramin motarka yanzu zan dawo.
Sagir ya mik'amai batare da yace komai ba, Jalal ya amsa tare da godiya ya fita.
Seemah ta isa inda Ammar yake, sunje shiga daidainan wani babban mutum ko ince d'an siyasa babba, ya fito tare da mutanensa da 'yan goya kai baya, Seemah ta kalleshi baifi sa'an dad ba amma ko ba'a fad'a ba kasan d'am siyasa ne, idanta ta d'auke daga kansa sai dai maganar dataji ne yasa ta maida hankalinta da kallanta gun.
D'an siyasan nan taji yana fad'a kamar zai yanka mutanen dake gun, mamaki abin ya bata ta kara dubawa dawa yake fad'an? Wani dattijo tagani a tsugunne yana rokarsa jitai mutumin yace " wai ku mutane wasu irin dakikai ne? Sau nawa ina sanar dakai za'a baka kud'in gidan ka? Nifa banasan hauka kuma wlh karka kuskura ka kara zuwa inda nake, in banda darajar kai tsoho ne da tuni nasa an d'aureka."
Tsohon sai hannu yake had'awa alamar ban hakuri, sam Seemah batajin ke yake cewa da alama ma baya iya magana da karfi saboda tsufa, tsaki tai tace " na tsani mutane irin wannan dabasu san darajar tsofaffi ba aikin banza kawai......
Ta juya wasu 'yan jarida ne suka shigo cikin harabar hotel d'in securities na cemusu su tafi amma ina....sai da suka karasa gun wannan mutumin, Seemah ta juya ta kallesu, da mamaki ta kara kallan gun me zata gani? Wannan mutumin daya cima tsohon nan mutunci tagani ya kama hannun tsohon yama bashi hakuri, ga 'yan jarida nata d'auka, da mamaki ta kara kallansu, mutumin taji yace " Baba kayi hakuri munanan muna kok'arin yanda zamuyi kud'inku su fito amma ga wannan, batasan nawa ya mik'a ba amma tasan kud'ine masu kauri, mutumin taga ya kara kankame hannun babban harda kwallarsa wai Baba ka yafe mana, mukanmu mumajin tausayin halin da kuke ciki, ko bacci bana iyayi saboda tausayi.
Seemah dariya tasa tace " what? Me nake gani? Wannan wani irin mutum ne? 2 face? Ahhhhh yau naga abinda ban tab'a gani ba, harara ta maka mai duk da baimasan tanayi ba ta karasa ciki, tana tafe itakad'ai tama masifa.
D'akin da Ammar yake ta jarasa tare da danna kararawa, bata dad'e ba Ammar yazoya bud'e d'an ya d'auka masu aikin hotel d'in ne, ganin Seemah yasa ya tsaya kawai yana mata kallan mamaki, itama kallam mamaki take mai ta sa hannu akan fuskarsa yace "yaya menene haka? Meya sameka?"
Ammar bai amsa mata ba ya koma ciki tare da komawa karshen bango ya zauna, kamar yanda yake d'azu, Seemah da sauri ta karasa kusa dashi tace " yaya menene hakan?"
Bai ko kalleta ba bai kuma amsa mata ba, Seemah mamaki ya kara kamata ganin yanda duk ya canza a daren jiya yasa ta matso gabanshi tasa hannayenta akan fuskarsa idanunta suka ciciko tace " Yayana menene?"
Kallanta Ammar yai sai dai duk yanda yaso ya mata magana ya kasa, hawaye ne suka sauka a idanunsa, itama hawaye suka zubo mata tace " yaya wani abun ne? Please ka fad'amin."
Tafad'a tare da kallan d'akin, da alama ko kan gadon bai hau ba gashi kuma kamar abincin ma da aka kawomai d'azu ma bai ciba.
Kallansa tai da mamaki, bata tab' a ganin Ammar haka ba, mutum mai barkwanci? Mik'ewa Amnar yai kawai ya shiga toilet ta bi bayansa da kallo tare da share kwalla, wayarsa tagani akan gado da sauri ta k'ira Dad sai dai bai d'auka ba, ta kira junaid yace mata zai kirata yana aiki ne, haushi ya isheta gashi ita bazata k'ira Habib ba, da sauri tasa number Jalal.
Jalal kam har ya iso gidan yana shirin fita daga mota wayarsa tai kara ya d'aga jin muryar Seemah yasa ya koma ya zauna tare da cewa "Meemah ina kika shiga nakasa samun layinki? Do u know how worried am I?"
Ajiyar zuciya tai sannan taxe " My deen ina nan Nordic sai dai narasa meke faruwa da Ya Ammar yak'imin magana gashi duk ya canza."
Duk da Jalal baiji dad'i ba amma sai ya daure yace " ahh ina my cute Meemah ta shiga ne? Wacce kesa mutum dariya ko bai saba ba?"
Murmushi tai tace " let me try."
Yace " amma I want to see you ya za'ai?"
Ajiyar zuciya ta kara saki ta kara rik'e wayar tace " My deen ni kaina inasan ganinka ga ba waya a hanuna, kawai nanda 20mins kazo nan sai in fito."
Ya saki wani sanssanyar murmushi yace " ok see u later."
Tai murmushi tare da katse layin, wani energy ne taji ya zo mata ta mik'e tsaye tare da karasawa bakin toiler d'in da Ammar yake.......
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 3⃣7⃣
Seemah ta shiga knocking d'in toilet d'in Ammar na tsaye jikin kofar tunaninsa d'aya ya ya zai kalli Seemah yanzu? A matsayin me? Ganin yaki bud'ewa yasa Seemah ta zame ta tsugunna a jikin kofar tare da cewa a hankali " Yaya nice fa? Nad'auka tsakanina dakai babu 'yar haka, ko me ya faru ya kamata in sani indai har abin ya shafeka."
Ammar shima ya tsugunna a jikin kofar ta ciki yana sauraranta, Seemah tai ajiyar zuciya tare da cewa " yaya please ka bud'e muyi magana? Please? "
Ammar ya motsa baki har zaiyi magana kuma ya fasa, Seemah ganin yayi shiru yasa tace " yaya kasan me? Ni yanzu na daina san Yaya Habib d'an haka mu koma kawai gidan Dad ni dakai muzauna."
Nan ma shiru yai sai dai yanda na kalleshi naga fuskarsa tad'an saki, Seemah tai murmushi sannan ta cigaba " yaya amma in muka koma wazai d'inga mana abinci? Kasan ban iya girki ba."
A hankali murmushi ya bayyana a fuskar Ammar, Tab'e baki tai ta cigaba " yaya nasan dai kaima ba wani abinci ka iya ba, to ya zamuyi?"
Murmushi sosai Ammar yai, jiyai zuciyarshi tayi haske, Seemah kam ganin yak'i kulata yasa ta mik'e tare da cewa " yaya nasan kanaji na amma tunda kak'i kulani, shikenan bari nai tafiyata."
Jin alamun ta mik'e yasa Ammar ya fito daga toilet da sauri, yana zuwa ya rungumeta ta baya, a hankali tace " Yaya?"
" wait for a moment please." Ya fad'a cikin wata murya dayasa Seemah tasha jinin jikinta, Ammar ya dad'e a haka kafin a hankali ya saketa, juyowa tai ta kalleshi tace " Yayana meke damunka wai?"
Murmushi yai tare da cewa Seemah.......wayar sa ce ta katsesu da kara, da sauri Seemah ta d'aga wayar ganin number Jalal, cemata kawai yai yazo, tace ok, sannan ta juyo ta kalli Ammar tace " yaya my Deen yazo bari in d'an fita waje ina zuwa." Bata jira amsarsa ba tai waje da sauri, Ammar ya bita da kallo zuciyarsa ba dad'i.
Seemah kam tana fitowa ta kara kallan inda taga wannan mutumin sai dai ganin ba kowa yasa tai tsaki tare da fita neman inda Jalal yake.
Jalal kam daga nesa ya ganta, murmushi ne ya bayyana a fuskarsa ya bud'e motar ya fita, kansa ya samu da d'aga mata hannu, tana ganinshi itama ta saki murmushi ta karaso a hankali cikin tafiyarta, tana zuwa kusa da shi suka kalli juna suka saki murmushi a tare kana ganinsu kasan suna tsantsar farinciki na ganin juna, Seemah ta kalli Jalal tace " My Deen ya jikin naka?"
Yace " Ahhh!!!! Ni sam na manta ma banda lafiya a jikina."
Da mamaki tace " ban gane ba?"
"Zuciyata tana rashin lafiya wazai damu da ciwon dake gangar jiki?"
Dariya Seemah tasa sannan ta rik'e hab'a tace " tooh? Oh ni? Yaushe my deen yazama malamin kalamai? "
Hararta yai yace " bawani malamin kalamai abinda ke damuna na fad'a"
Zagayawa tai ta shiga mota, shima ya koma ya zauna tare da juyowa yace " ya Ammar d'in?"
Tai ajiyar zuciya tace " I don't know, haryanzu bai cemin komai ba."
Jalal ya d'an matso da fuskarsa kusa da ita yace " ko dai bayasan ya fad'a miki ne? Ko sirri ne?"
Ta murgud'a mai baki tace " ba wani sirri tsakanina da yayana."
Jalal yace " naji, amma meyasami wayarki?"
Ta had'e rai tare da cewa " ba yaya Habib bane ya kwacemin waya."
Jalal ya koma ya zauna jikin kujerar, sannan ya daure yace " because of me?"
Ta kalleshi idanunta suka ciciko, tace " karkadamu Deen komai zai zo da sauki, ni takace, kaji?"
Murmushi yai sannan ya matso tare da d'anjan kumatunta, kai ta karkatar tace " ya kukai a Birnin gwarin?"
Jalal ya kalleta tare da neman zare hannunsa, da sauri ta rik'o hannun sa tare da kura mai ido, murmushi ya kakaro yace " karki damu kinji?"
Daga yanda yai maganar tasan akwai wani abun, sakeshi tai tare da cewa " Deen ina tsoron kar a rabamu da......."
Ya tsarsa yakai bakinta yace " please Meemah karki karasa, ba abinda zai fari sai alkairi."
Hawayen da take boyewa ne suka zubo, yasa hannu ya share mata sannan yace " banasan ind'inga ganin idanun dana fiso a duniya suna zubda hawaye, abin takaicin kuma nine nake sasu zubar da hawayen."
D'agowa tai ta kalleshi tare da girgiza kai, Jalal jiyai kamar shima hawayen zaiyi, da sauri ya bud'e motar ya fita, Seemah ta bishi da kallo, tare da kokarin fita, vibration d'in dataji wayarsa nayi yasa ta kalli wayar *ZAINAB* abinda taga ya fito a jikin wayar kenan kawai sai ta samu kanta da d'aga wayar, Zainab kam kai tsaye tace " yaya ya zakayi? Su Abba fa da gaske suke d'azu ya fita kaiwa abugo Iv na d'aurin aure, da alama next week d'in nan za'a d'aura."
Jikin Seemah ne ya shiga rawa, batasan sanda ta yarda wayar ba, duk bata hankalinta, bud'e kofar tai tafito, Jalal na ganinta ya taho, sai dai ko kallansa batai ba tafiya kawai take, ganin haka yasa Jalal yasha gabanta yace Seemah menene? D'agowa tai ta kalleshi, jitai kamar tasa ihu, matsawa tai gefensa ta cigaba da tafiya, Jalal ya riko hannunta ta baya yace Seemah? Janye hannunta tai kawai tasa gudu ta koma cikin hotel d'in, binta yai da kallo sannan shima yai ciki, sai dai inaa, sam bai ganta ba, securities sukazo sukace ya fita.
Dad ya isa Birnin gwari lafiya, bai sha wahala sosao ba wajen neman gidan, saboda unguwar kusan duk sunsan gidansu Jalal, tunda ya fara shiga lokon da kafa ransa yake a b'ace, mamakinsa amma lalai Jalal d'in nan yagama raina musu hankali, sai ma daya isa gidan, ba gate bane kawai koface ya d'an bubuga jiyai ance ana zuwa, ba'a dad'e ba wata yarinya budurwa sanye da hijabi tazo ta bud'e tare da mai kallan mamaki, sai kuma can tai saurin cewa " ina kwana?"
Lafiya dad ya fad'a tare da cewa nan ne gidansu Jalal? Kai ta d'aga tace " nan ne amma bayanan."
Dad ya kara kallan wajen gidan yace " nasani iyayensa nake nema." Zuciyar zainab ce ta buga, badai laifi yai ba ko? Ahankali tace shigo, Dad yasa kafa cikin gidan, yabi gidan da kallo, Umma ce ta fito tare da cewa sannu da zuwa, ya kalleta yace yauwa, tace shigo, wani kallo yakarama gidan sannan yace
" basai na shiga ba dama zuwa nai akan ku jama d'anku kune, yasan matsayinsa, 'yata Seemah namata miji ya fita daga harkarta tun kafin rai yazo yana b'aci gwara ayi magana a mutunce."
Jikin Umma yai sanyi, tace " bawan Allah kayi hakuri mu kanmu kaga wace mukeso ya aura kuma ma wani satin za'ai auran, d'an haka ka kwantar da hankalinka."
Dad ya matso tare da ajiyema Umma envelope yace " nagode da fahimtarku, ga wannan kyautace ba yawa, ku bawa d'anku shawara d'an masani shine ya makallewa 'yata."
" ka koma d'an kuwa kayi zuwan banza."
Da sauri Dad ya juya jin furucin daga bayansa, juyawa yai ya kalleshi harzai yi magana sai kuma ya kura mata ido sosai, shi kanshi Abba kalansa yakeyi, a hankali Dad ya karaso kusa da Abba, Dad yace " malam kamar na sanka ko?"
Abba shima da mamaki yace " nima kamar na sanka,"
Dad ya d'an juya kai yace ya sunan ka? Da mamaki yace Ahmad.
Idanun Dad ne suka rik'ed'e cikin wani yanayi ya riko wuyan Abba ya jashi zuwa jikin bango, yace Amadu mai shago?
Idanu Abba ya zaro, Umma da zainab mamaki ya kamasu menene hakan.
Cikin tsawa da fad'a Dad yace " Amadu ne? Kai ne?"
Abba ya kara zaro ido yace " Isma'il?"
Matsashi sosai Dad yai har numfashin Abba ya fara rawa, da sauri Umma da zainab suka matso sunamai magana, Dad cikin masifa yace " Amadu? Kaine? Yama za'ai in mantaka? Mutumin dakajazama rayuwata, ka lalatamin rayuwata."
Umma najin haka tafarayin baya baya tana jijiga kai, idanunta na zubar da ruwa, zainab kam ganin yanda Abba yakeshan wahala yasa tai saurin tsugun nawa ta rik'e kafafun Dad.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 3⃣8⃣
Dad ganin Abba na kakari yasa ya sakeshi sannan yace " me kakeyi a nan?"
Kafin Abba yai magana Zainab tayi saurin zuwa kusa dashi tace " Abba sannu." Hakan yasa ya gane wato gidan sa ne, cikin tsananin mamaki da takaici Dad yace " Jalal d'anka ne?"
" Eh" zainab ta fad'a sannan ta cigaba" amma malam menene hakan?"
Wani kallo Dad ya mata yace " dama ina 'ya'yan Amadu zasuyi tarbiya? In ba haka ba yaza'ai yarinya dake kid'inga shiga maganar manya?"
Da sauri tai kasa dakai itakanta batasan ya akai tai magana haka ba, jitai Umma tace " Zo ki wuce ciki."
Simi-simi Zainab tai ciki, Abba ya d'ago yace " Isma'il!!!" Dad ya nunashi da yatsa yace " karkaga wai na maka magana ka d'auka wai na yafe maka abinda kamin ne a shekarun baya, Amadu kaine mutum na farko kuma na karshe da bazan tab'a yafema ba, alhakina dama Fatima shine yasa ka kasa ci gaba, kuma wlh kaji na gaya maka kayi gaggawar fad'a ma d'anka ya barmin 'yata tun kafin na aikashi prison. "
Yana kainan Dad yai hanyar waje, Umma ce da sauri ta matso ta tsugunna a bayansa hawaye na zuba a idanunta sosai, tace " Malam d'an Allah kayi hakuri ka yafe mai, na sani......."
Dad bai jira ta karasa ba yasa kai ba bar gidan, yana fita waje ya juyo ya k'ara bugawa gidan kallo, sannan yai gaba.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Jalal kam a waje ya tsaya ya rasa meya faru da Seemah ta canza lokaci guda haka, to amma yazaiyi? Sun hanashi shiga, wayar sa ya d'aga kawai ya k'ira number Ammar sai dai tanata ringing ba'a d'aga ba, cilla wayar yai gefen kujera ya shafi goshinsa tare da cewa Ya Allah!
Seemah kam tana shiga d'akin ta tadda Ammar a tsaye ta jikin window da gudu ta karasa ta rungumeshi ta saki wani irin kuka mai tab'a zuciya, Ammar kamar ta sosa mai inda yake mai kaik'ayi shi kansa so yake yai kuka kamar haka, jiyai idanunsa ya shiga kawo ruwa, d'an kukan gar zuciyarsa yake tab'awa, Sam ya kasa cewa tai shiru sai ma shima kukan da yakeyi, sunfi minti 10 a haka kafin cikin kuka Seemah tace " Yaya ya zanyi?" Ta karasa maganar tare da d'agowa ta kalleshi, ganin yana kuka shima yasa ta shiga girgiza kai tana hawaye tace " yaya me yake damunka please? " hannu yasa ya goge hawayen yace " fad'a kukai da Deen d'in naki?"
Baya ta juya ma Ammar tace " yaya shikenan, rayuwata tazo karshe."
Da sauri Ammar yadawo tagabanta ya rike kafad'arta yace " Seemah me kike fad'a haka?"
Hawayene ya zubo mata tace " yaya aure za'amai nextweek."
Ta karasa maganar da fashewa da wani kuka, Ammar ya kama hannunta ya zaunar a kan gado, sannan shima ya zauna a gefenta ya juyota setinsa yace " Seemah?" Kallansa tai da mamaki jin yanda ya kararra gurin k'iran sunan, yace " Seemah!!" Tace " yaya inaji menene? Ka tsoratani."
Fasa fad'ar abinda yai niyya yai ya wayance da cewa "Seemah ki rage wannan soyayyar da kikema Jalal bana tunanin yana sanki kamar yanda kike sansa."
Hawaye ta share tace " kaima haka kake gani ko yaya? Na sani yaya, nasan nafi sansa akan yadda yake sona, in fad'ama gaskiya yaya ni na fara cewa ma ina sanshi."
Ammar ya juyo ya kalleta, hawayenta suka cigaba da zuba, tace " amma yazanyi yaya? Ina sanshi sosai, kome nakeyi yana raina, in ban ganshi ba ji nake zuciyata kamar zata fashe, in muna tare kuma ji make kamar kar mu rabu."
Tai ajiyar zuciya tace " ya Ammar banaji zan iya rayuwa ba Deen."
Ammar duk da kalamanta sun mai zafi a zuciya amma bai nuna ba murmushi ya kakaro ya matso kusa da ita yace " Seemah yaushe zuciyarki ta kamo haka?" Tace " ban sani ba Ya Ammar ni kaina ban sani ba." Ta karasa tare da sa kuka, jawota yai jikinsa yana shafa bayanta alamun lallashi.
Jalal ya dad'e agun ganin Seemah tak'i fitowa yasa ya juya gidansu Sagir, yai parking motar yashiga gun Sagir, d'akin a bud'e yake sai dai ba kowa a ciki, shiga yai ya hau kan gado ya kwanta tare da d'aura hannayensa akan goshinsa, tunanuka sun mai yawa a hankali hawaye suka ziraro ta gefen idanunsa, sam bai ji sallamar Sagir ba, sai da yaji an dafashi, kallan Sagir yai sannan ya mik'e zaune yace " Sagir ina kaje?"
"Ummanmu ce zasu fita shine na musu sallama"
Jalal yace " Amma bansan sunanan ba dana gaidasu ai."
Dariya Sagir yai yace " kana cikin tension ina zan fad'ama?" Ya cigaba " amma ya? Ka ganta?"
Kai Jalal ya d'aga alamar eh, Sagir yace " Amma kamar baka farin ciki, fad'a kukai?"
Ajiyar zuciya Jalal yai yace " nikaina bansani ba, da alama Seemah hard to get take neman yimin, sai dai ni a wannan lokacin batasan banasan muyi fad'a ba sam d'an ni kad'ai nasan me nake ji."
Sagir ya kwashe da dariya yace " Lalai Mr Romeo."
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♢♡♢♢
Habib ya isa Suleja sai dai jikin Hajiya ba dad'i sosai kusa da ita ya zauna, ya kalli Kawo yace mu wuce Abuja kawai kawo a kaita asibiti, kaga Abba da Dad duk suna can, Kawo yace haka ne wannan ma shawara ce.
Hajiya ya kalla ya rik'e hannunta, jiyai itama ta kama hannunsa da karfinta tace " Isma'il bakasan mahaifin yarinyar nan ba kai kanka, taya za'ayi ka nemi had'a zuri'ata da jinin da bamu sani ba."
Idanu Habib ya zare da jin kalamanta ya kalli Kawo a zabure me Hajiya take fad'a? Da sauri kawo ya d'an matsar dashi ya zauna kusa da Hajiya yace " Amina kalle ni nam ba Isma'il bani Habibu ne me kike fad'a haka?"
Jikin Habib ne yafara rawa ya mik'e tsaye a rud'e yace " Kawo me take nufi da kalamanta?"
Kawo ya kalleshi cikin tsoron furucin da Hajiya tai, yanzu me za'a ce?
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 3⃣9⃣
Habib ya matsa kusa da kawo ya tsugunna agabansa idanunsa sunyi jaaa yace " kawo meke faruwa wai? Nine babban d'a agun mahaifina meyasa zaku d'inga b'oyemin abu? Gaba d'aya kun birkita min lissafi ance ba mahaifiyarmu d'aya da seemah ba? Dad yazo yace wai Ammar ba d'ansa bane, yanzu kuma Hajiya tana maganar ba'asan mahaifinta ba, in maganar mace takeyi da Seemah kenan take, gaba d'aya na kasa fahimtar abinda ke faruwa."
Kawo yai kasa dakai yace " Habibullah maganar da ake b'oyema........"
Amman da Hajiya ta shiga kwarawa ne yasa maganar ta tsaya, gaba d'ayansu suka mik'e suka nufi gun, hajiya amai takeyi sai dai da alama ba komai a cikin ganin yanda take kak'aro aman, Habib da sauri ya d'agowa yace kawo tayani mu kaita mota, nan suka d'auketa d'an ta galabaita sukai mota da ita, kawo ya zuba musu kaya a jaka suka ja gida suka rufe suka shiga mota.
A hanya ba wanda yai magana d'an Hajiya numfashi kawai take saki.
Dad kuwa harya kusa fita daga birnin/gwari wata magana ta Hajiya datamai randa yaje ta fad'o mai, lokacin har yaje fita daga gidan yaji muryar ta tace " Isma'il kasan ma mahaifin yarinyar ne? Itadai bazata tab'a yarda da yarinyar da ba'asan mahaifinta ba."
Tunano kalaman ne da Dad yai yasa ya kalli drivern sa yace mukoma inda muka fito nayi mantuwa.
Nan driver ya juya da kan mota suka koma, Dad sai tunanin abinda yafaru a baya yakeyi, bai tab'a tunanin zai had'u da Amadu ba, abinda yafi d'aure masa kai wai Jalal d'in da Seemah takeso d'ansa ne.
Ya zarfafa cikin tunani bai san ma harsun iso ba, sai da driver d'in yace " Alhaji mun iso. " lungun gidan Dad ya kalla ransa na kara tunzura d'an bakin ciki, haka ya daure ya fito daga mota ya nufi gidan.
Abba kam tun bayan tafiya Dad ya zauna a waje shi da umma sai dai ba wanda ya iya yima wani magana a cikinsu, sai can Umma ta daure tace " Malam ne dana mahaifin yarinyar da Jalal keso?" Abba ya had'iyi wani abun bai iya ce mata komai ba, tacigaba " mun shiga uku malam yanzu in Jalal yasan..........wani kallo da Abba ya buga mata ne yasa tai shiru, sai dai abinda ke zuciyoyinsu na da yawa.
Jin an kwankwasa kofa ne yasa Umma ta d'aure ta mik'e ta nufi kofar, ta bud'e ganin mutumin dake tsaye ne yasa ta fara ja da baya da baya, tare da cewa Malam? Abba dake zauna ya taso tare da cewa "ke kuma menene inaji da......" ganin Dad ne yasa shi yin shiru, Dad ya makamai wani mugun kallo yace " inasan ganinka." Yana fad'ar haka ya juya.
Abba ya kalli Umma itama cikin tsoro tace " Malam mun shiga uku." Takalmansa ya d'auko ya fita sai dai kana ganinsa kasan ta maza kawai yakeyi anma a tsorace yake.
A d'an gaba da gidansa yaga Dad ya karasa gunsa, yace " Isma'il gani." Juyowa Dad yai ya kalleshi cikin d'aure fuska yace " tambaya ta karshe nazo in maka, daga wannan in har ka sake min karya wlh kaji na rantsema wannan karan ba kamar da bane dazan kyaleka, wlh sai nasa an d'aureka."
Abba ya kalleshi a tsorace, Dad yace " Wayama Fatima fyad'e?"
Gaban Abba ne ya fad'i ya kalli Dad sannan ya had'iyi yawo bakinsa na rawa yace "Malam Isma'il!"
Dad ya d'agamai hannu yace ba abinda nazo ji kenan ba, ka fad'amin abinda na tambayeka ko kuma wlh zakasha mamaki.
Abba yace " Malam Isma'il alokacin wlh ba asan raina......"
Dariya sosai Dad yai sai dai kana gani kasan ta tsabar bakin ciki ne, yace " Amadu kenan, karka sake tunanin zan yanda da kalamanka, kalma d'aya nakesan ji daga gareka, waye ya k'etama Fatima mutuncin ta?"
Abba ya kalleshi idanu a zare, Dad ya karkatar da kai yace " Don't tell me kaine?" Da sauri Abba yace " Me kake fad'a? Ni kuma? Akan me? Kaima kasan ba hali na bane."
Dad yai murmushi yace "a shekaru masu yawa kenan nai tunanin ba halinka bane amma daga baya na gane babu babban munafikin dana tab'a gani irinka, sannan dama na sanar dakai wannan shine tambaya dazan maka ta karshe, yanzu sai ka jira d'anka d'an inaji shi kad'aine zai iya jin amsarka."
Dad nakainan ya juya ya tafi, Abba ya rikice, sai dai kafin ya dawo hayyacinsa Dad har yayi gaba.
Da sauri ya koma gida ya tadda Umma a tsaye tana jeka ka dawo, tana ganinshi ta rike hannayensa tace " ya kukai?" Abba yace " ya tafi yace Jalal zai fad'ama."
Zubewa Umma tai a kasa jin haka tace " Malam meke damunka? Kataba tunanin in Jalal yaji maganar nan abinda zai yi?" Ta mik'e tace "Ko dai nima kana b'oyemin wani abu ne? Indai har abinda ka fad'amin shine gaskiya meyasa bazaka fad'ama Malam Isma'il ba? Karka manta abinda ya faru da shi da iyalinsa saboda kalma d'aya daka furta."
Abba ya kasa magana sai zufa kawai yakeyi, ya kalleta yace " Ban b'oye miki komai ba, kema kinsan haka." Yana kainan yai waje da Sauri....
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM.*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣0⃣
Zainab kam tunda ta shiga d'aki hankalinta ya kasa kwanciya, ba shakka wannan wulakancin da aka ma Abba ya k'ona mata rai, bata fiya fishi ba haka take sai dai in ranta ya b'aci bata ganin komai, wayarta ta d'auko ta danna number Jalal, ringing uku Jalal ya d'aga tare da sallama ta amsa sannan tace " Yaya dama akwai lokacin da zaizo har ka fifita soyayya akan iyayenka?"
Cikin b'acin rai Jalal yace " ke Zainab meke damunki? Ni kike fad'ama wannan banzan zancen?"
Zainab rai b'ace tace " meye ma bazan fad'ama ba yaya? Akwai abinda yafi b'acin rai irin a wulakanta iyaye? Mahaifinta Har da shake ma Abba wuya? Sannan kai kuma anjima kazo kace kana santa ko me?"
Jalal ya mik'e tsaye idanunsa suka kad'a sukai jaaa, cikin fad'a yace " me kika ce?" Shiru tai bata amsa ba, tsawa ya daka mata yace "ME KIKA CE?"
Nan tai ajiyar zuciya ta shiga fad'amai abinda akai a gabanta, cilli naga yayi da wayarsa kan gadon Sagir, dama Sagir baya nan, wani hucci ya shiga saki ni kaina sai dana tsorata alk'alamin dake hannuna sai daya fad'i, tun yana karami ko a wasa bayasan irin zagin nan na yarinta da ake, d'an shi ko kad'an baya san a zagi iyayensa, bari har me?? Shakemai wuya?.
A zuciye naga ya fito daga d'akin ai da gudu nai gaba nikam kar a huce akaina.....
Ammar kam tunda Jalal ya tafi yake faman lallab'a Seemah sai dai dakyar ya samu tai bacci, sai dai kamar wata yarinya tana bacci tana ajiyar zuciya, Ammar dake tsugunne saitin fuskarta ya saki murmushin ganin yanda take ajiyar zuciya, a hankali naga fuskarsa ta koma ta damuwa, ya matso da fuskarsa saitinta ya kwantar, ya k'ura mata ido, a hankali ya furta " Seemah wani irin so nake miki?
Na jini ne?
Ko kuwa na 'yan uwa ne?"
Ko kuma soyayya ce ta d'a namiji?"
Shiru yai kawai yana kallanta can baisan sanda zuciya ta d'aukeshi ba, a hankali yakai bakinsa kan kuncinta ya sumbata, motsin datai ne yasa ya mik'e tsaye da sauri tare da sa hannu a bakinsa, jiyai d'akin yamai zafi duk da A.C da kuma sanyin da akeyi, bakin window yaje ya tsaya yana firfita da hannunsa.
♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧
Habib kam suna isowa Abuja yai asibiti da Hajiya, suna shiga akai emergency da ita dan gaba d'aya bata hayyacinta, kawo duk ya rikice hakama Habib, dakyar Habib ya lalubo wayarsa ya k'ira Abbansu Zaid sannan ya k'ira Dad, Dad dake hanya jin mahaifiyarsa ba lafiya yasa ya rikice, ya kalli driver yace kara gudu hajiyata ba lafiya, nan ya amsa da to tare da kara gudu.
Habib na kashe wa ya k'ira Ammar, Ammar yana kallan wayar sai data kusa katsewa ya d'aga ba tare dayace komai ba, Habib yace" Ammar kazo Asibiti Hajiya ba lafiya."
Da karfi Ammar yace " me ya sami Hajiyar?"
Seemah dake bacci ta bud'e ido, tana kallan Ammar, Habib ya cigaba " bansani ba nima Ammar gata dai a emergency tana jin jiki."
Ammar yace " *Inalilahi wa ina ilaihi raji'un* bari muzu yanzu." Yana kainan ya katse.
Juyowa yai ya kalli Seemah dake zaune akan gado, ta kalleshi tace "yaya me ya sami Hajiyar?"
Kai ya girgiza alamar a'a yace "Seemah bansani ba ki tashi dai muje."
Da sauri ta sauko ta gyara d'ankwalinta ta yafa mayafi suka fita.
A asibiti kuwa Likitoci sundai yi nasu k'okarin sai dai su kansu sunsan inaaaa, ganin dai ta dawo hayyacinta yasa aka bata d'aki, kawo ya zauna kusa da ita, ya rik'e mata hannu, yace " Sannu Hajiya!! Bakiji yanda naji ba nad'auka kema mutuwa zakiyi ki barni kamar yanda sauran matan nawa sukai."
Hajiya tai murmushin karfin hali tace " Isma'il fa?" Kawo yace " yana hanya."
Habib ne ya shigo shi dasu Abba da mami, da sauri Abba ya karasa kusa da ita, yace " Hajiya?"
Ta kakaro murmushi tai tace " D'an nan kaima tasoka akai?"
Sannu hajiya abinda ya fad'a kenan, ta d'aga kai sannan ta kalli Mami dake mata sannu, tace yauwa Allah ya muku albarka, sukace Amin.
Abba ta kalla zatai magana sallamar su Ammar ta katseta, suka shigo shi da Seemah, Ammar ya kalleta duk ta rame yace " matata ya banje gaidake ba sai in ganki akan gadon asibiti?" Tace " yaushe ka shigo?"
Murmushi yai sannan ya gaida kawo dasu Abba, Seemah ma ahankali ta gaidasu, sai dai mami ce kawai ta amsa, Ammar ya kalli Abba da kawo yace" wooo yanzu kanwar tawa mai tsada tana gaidaku shine kukai shiru?"
Kawo ya kalleshi yace " Ammar kana nan dai yanda kake." Hajiya kam tunda Seemah tai gaisuwa ta kafe ta da ido, Abba ganin haka yana tsoron kar ciwonta ya tashi yasa yace " Seemah d'an fita waje, Habib dake tsaye ya kallesu, ba shakka matsalar daga Seemah ne ba Ammar ba.
Seemah ta d'ago ta kalli Abba, tsawa ya daka mata yace "bakiji me nace ba,"
Duk ta rikice tama rasa hanyar fita, Ammar ne ya jawota jikinsa yace " me kakeyi hakan Abba? Yaza'ai yarinya tazo gaida kakarta ka nemi korarta?"
Abba yace " Ammar ina wasa dakai ne?"
Ammar yai ajiyar zuciya yace " yahkuri in na b'atama rai Abba sai dai ba inda Kanwata zataje inkuma anaso ta fita to sai dai ku fita tare."
Yana kainan ya jata sukai waje.
Seemah duk ta rikice kawai hawaye takeyi.
Jalal kam a sukwane yaje gidansu Habib sai dai mai gadi ya sanar dashi yanzun nan motar Farida ta fita suna asibiti, hakan yasa da sauri yasa mai machine d'in yabi bayan motar.
Sun isa asibitin, Farida ta fito da sauri tai ciki, shima ya bita, a harabar gun ya kallo, wata kamar Seemah, hakan yasa ya tsaya yana kallanta, Seemah kam hannun Ammar ta rike kam dan jikinta duk rawa yake, ganin haka yasa Ammar ya jawota jikinta ya rungume, Jalal dake tsaye yaji ransa yayi mugun b'aci, karasa wa yai inda suke Ammar ya d'ago ganin kafar mutum ya kalleshi, da mamaki yace " Jalal? Me kake anan?" Seemah najin sunan tai saurin d'agowa ta kalleshi.
Idanunsa sun kad'a sunyi jaa dama ga bakin cikin abinda aka mai ga kuma wani sabon salo, babban yaya namiji ya kama rungume kanwarsa, Seemah ta kalleshi da idanunta dake hawaye tace " My Deen?"
Kallanta yai yace " Meemah me kike anan?"
Ta kalli Ammar sannan ta kalli Jalal, Ammar yace " kai ya kamata kabada wannan amsar, mu tinda ka ganmu anan ai akwai dalili, Jalal yace " Dad nake nema."
Ammar ya jinjina kai sannan yace " tunda Dad kake nema bayanan." sannan ya kama hannun Seemah zai koma cikin asibitin da ita, da sauri Jalak ya kamo d'ayan hannunta, ta juyo ta kalli Jalal ta lumshe idanunta, Jalal ya sakar mata murmushi sannan ya kalli Ammar yace " sry yayan Seemah inasan magana da ita."
Wani kishi ne ya kama Ammar ya bugamai wani kallo, Jalal mamaki ya kamashi, ba shakka wannan kallan ba kallan yaya bayasan shi bane kallan kishi ne, amma......Ammar ne ya katseshi da cewa " ka manta me ka mata?"
Jalal da sauri ya kalli Seemah, meya mata? Nan Seemah ta tuno kalaman Zainab, a hankali tai fara baya, tana kokarin zare hannunta, jisukai ance " *Me kukeyin hakan?*
Da sauri suka juya dukansu, Dad ne a tsaye rai a b'ace.
0 comments:
Post a Comment