Seemah zaune take kawai, a rakub'e a jikin gado, sai kallan y'an uwa take suna zuwa gaisuwa, sam ko magana batayi bare cin abinci, duk ta rame ta canza a kwana d'aya.
Tana zaune tana jan carbi taji sallama, jin muryar yasa ta d'ago da sauri, Junaid ya kalleta tare da sakar mata murmushi, kuramai ido tai a hankali hawaye suka zubo mata ya matso kusa da ita tare da cewa " Kanwata ai saura kiris in kasa gane ki, wace irin jinya kikai haka?"
Kallansa tai kawai ga mamakinsa sai yaga ta fashe da kuka, kallanta yai da namaki, sai kuma can yace " Seemah mutuwa fa ba'a san a d'inga mata irin wannan kukan, bare Hajiya da batasan kuka addu'a kawai zamu mata."
Seemah ta d'ago a hankali tanasan mai magana, yace " anma wani irin cinwo kikai haka?"
Zahra ce ta shigo ganin Mutum yasa tai kasa dakai tare da gaisheshi, Junaid ya d'ago ya kalleta yace" Badai badai ba?"
D'agowa tai tare da nuna shi tace " yayana?"
Kallanta yai yad'an kanne ido yace " badai badai ba?"
Tace " badai yaya bane wannan?"
Dariya yai yace " na d'auka kin manta inkiyar tamu."
Tai murmushi tare da matsowa tace " yayana yaushe a gari?"
Yace "d'azu na shigo ya hakurin mu?"
Tace " Alhamdulila"
Kallan Seemah yai yace " Kanwata mey........"
Da sauri Zahra ta katseshi tace " tashi yaya muje ka gaida Mamie."
Ya mik'e tare da kallan Seemah, nan sukai waje, Seemah ta share kwalla Allah sarki rayuwa, a da tad'auka 'yan uwanta ne na jini yanzu kuwa ta gane ashe bata da alaka da dukansu, itafa? Inane cibiyarta? Suwaye 'yan uwanta?.
Jalal yayi sa'a a kofar gida yaga Abba, da sauri ya karasa gunsa, Abba ya kalleshi yace " Jalal kai nake jira ai, na shiga ciki aka sanar dani ka iso."
Jalal ya kalli Abba tare da cewa " Ina Kwana?"
Abba ya amsa tare da rik'o hannun Jalal yace " Nagode Jalal da baka bani kunya ba kazo tun kafin ranar bikin, nagode kwarai, Zainab ta koma gidansu acan zasuyi taron su."
Jalal kallan Abba kawai yakeyi, can yace " Abba inada magana mai mahimmanci dakai."
Kallansa Abba yai yace " Jalal wace magana ce haka da bazaka bari sai bayan biki ba?"
Jalal ya girgiza kai yace " Abba banajin zan iya runtsawa sai naji abinda ke faruwa."
Gaban Abba ne ya fad'i ya kalleshi cikin tsoro yace "Jalal me kakesan ji?"
Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace " Abba meye tsakaninka da Dad d'in Seemah?"
Da sauri Abba ya juya baya gabansa ya cigaba da fad'uwa, Jalal ya kalleshi sannan ya matso ta gabansa, yace " Abba bai kamata ka cigaba da b'oyemin wani abu ba, me ka musu suka tsaneka haka? Meye tsakanin ka dasu dahar suke tunanin kafisu sannin abinda si basu sani ba?"
Abba ya had'iyi yawu sannan cikin tsoro yace " Jalal banasan maganan nan na kuma hanek da karamin."
Ga mamakin Abba kawai gani yai Jalal ya tsugunna a gabanshi, yace " Abba d'an Allah ka fad'amin bakasan yanda nakeji a zuciya ta bane a wannan lokacin."
Abba yai ajiyar zuciya yace "naji zan sanar dakai abinda yafaru amma da sharad'i sai ka min alkawari."
Zuciyar Jalal ta matsu taji komai yace " na ma Abba koma akan menene."
Abba ya kalleshi idanunsa sunyi ja, yace " tun ranar da Isma'il yazu gidan nan nasan sirrin nan dole ne ya bud'u, in har kuma kanasan insanar dakai sai kamin alkawari tsakaninka da Allah cewar ko menene tsakanin mu bazai hanaka auren Zainab ranar Asabar ba."
Jalal ya d'ago da sauri ya kalli Abba yace "Abba me kake nufi?"
Abba yace" bazan sanar dakai ba har sai ranar da aka d'aura muku aure da Zainab."
Jalal ya mik'e a zabure yace " Abba d'an Allah......"
Abba ya katseshi da cewa " In har kanasan kaji to sai ka jira ranar auranka, alkawari na maka kaima kamin, haka ya kamata mu barshi."
Abba na kainan ya wuce cikin gida, Jalal bai kula bane amma hannun Abba rawa yakeyi.
Jalal ya naushi bango da hannunsa yana huci ya rasa mai zaiyi.
Wayar Sagir ce ta katseshi, ya d'aga da sauri tare da cewa " Sagir ya Seeman?"
Sagir yai shiru, Jalal yace Sagir ya kai shiru?
Sagir yace " Jalal kakarta ta rasu."
Jalal yafara " *Inna lilahi wa ina ilaihi Raji'un*"
Nan ya kashe wayar tare da silalewa ya zauna a dandaryar kasa, hannu biyu yasa ya rufe fuskarsa zuciyarsa na k'una, wani hali Seemah take ciki? Ance in tambayi Abba mahaifinta shikuna yace sai na auri Zainab, idanu ya runste sai ga hawaye sun zubo, Seemah ya zanyi?
Mutane sai wucewa suke suna kallansa.
Ya dad'e a gun kafin ya mik'e ya fara tafiya, wayar Ammar ya d'aure ya k'ira, daga gun Ammar dake zaune gun amsar gaisuwa ganin k'iran Jalal yasa ya mik'e yai gefe tare da d'agawa, Jalal yai sallama Ammar ya amsa, Jalal yace " Ammar ya hakuri? Ya kuma jikin Seemah? Tanacin abinci kuwa?"
Ammar yai shiru can yace" Jalal baka fahimci abinda muke nufi bane? Ko kuwa idanunka ne suka rufe?"
Jalal yai shiru, Ammar ya cigaba " abu d'aya muke buk'ata agunka ka tambayar mana mahaifinka waye mahaifin Seemah shikad'ai mukesan ji daga gareka."yana kai nan ya katse wayar, tare da kasheta gaba d'aya.
Jalal ya samu wani dakali ya zauna kamar maraya, kalaman Ammar kawai yake tunawa........
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣2⃣
A goggon dake d'aure a hannunsa ya kalla, sannan ya jawo wayarsa dake gefensa, number Seemah ya kurama ido, ya bude gun da nufin aika mata da sako, sai dai sam ya rasa mai ma zai ce mata, a goggon wayar ya kalla karfe 1 na dare, ya runtse ido da nufin yai bacci sai dai inaa, sam ya kasa sai ma wani irin ciwo dakan ke yi masa, zama yai, yaji zaman ba dad'i ya mik'e tsaye can kuma ya kwanta, tunawa yai ashefa daren jiya baccin awa d'aya da rabi ya samu.
Shawara d'aya ya yanke, a yanda yakejin San Seemah a ransa yana tunanin zai iya sadaukar da farincikinsa ita ta samu, indai har auren shi kad'ai ne mafitar da zaisa Seemah ta san mahaifinta ta kuma yi farinciki da ganinsa, to ba shakka zai iyayin abinda ya fi wannan, sannan shi yasani bai isa ya take hukuncin mahaifinsa ba, sai dai a da yaso gwadawa ya rok'eshi akan ya hakura da auran sai dai bukatar Seemah yasa bazai iya tambayar hakan ba.
Ya rik'e kansa dake rad'ad'i tare da rufe ido, ya dad'e yana tunani kala kala kafin Allah ya taimakeshi bacci yai gaba dashi.
Washegari.........
Ranar Alhamis kenan ya kama kwana d'aya da rasuwar Hajiya sannan a d'aya b'angaren kuma yau ne ake shagalin kamun Zainab, sai dai itama Zainab ba wani farin ciki take sosai ba ga kawayenta sai tsokanarta suke, wai basuga tana waya da angon ba bare ma har yazo ganinta, murmushi kawai takeyi a ranta tace " inafa zanganshi bayan ba nice a ransa ba?"
Jalal kam da bacci ya d'aukeshi sai karfe 10 ya tashi, shi kansa yayi mamakin ganin karfe 10, da sauri ya mik'e Alhamdulila yaji ciwon kan ya tafi, ya fad'a toilet yai wanka sannan ya zura kaya ya fito, yayi mamki daya shiga cikin gida ya taddasu suna ta hidimar su ta biki, wasu kuma suna shirin wai tafiya gidansu Amarya, Jalal ya had'e rai sannan karasa ya gaidasu Goggo ta kalleshi tace " Ango anya ma kuwa kaje ganin Amarya?"
Ya d'ago ya kalleta yace " Goggo sai kace ban santa ba? Ganinta kuma name?"
Goggo ta shiga tafa hannu tace "lalai wannan shine bagidajen, kai an fad'ama ko a kauye ana haka ne?tsaya ma anya kuna d'an tab'a wayar nan kaji matsalarta?"
Jalal ya kalleta yace "Goggo kenan, wace matsala zata samu yarinyar dake gidan iyayenta?"
Goggo ta shiga salati sannan tace " oh ni yau me nake ji haka? Ni ko d'akin da aka gyara muku ma banga kaje ka gani ba."
Jalal ya kalleta zaiyi magana karar wayarshi ta katseshi, Manager d'insu ne hakan yasa ya mik'e tare da cema Goggo yana zuwa, yana fita ya d'aga wayar, Manager yacemai "Jakal ya? Ka tura takardar kuwa?"
Jalal yace " oh God wallahi na manta amma bari na musu sending yanzu."
Ran Manager ya b'aci yace " Jalal wai me ke damunka ne? Sam ka daina maida hankali akan aikin ka sannan yanzu kayi tafiya ba rubuto takarda nakasa fahimtar ka yanzu."
Jalal yai kasa dakai baice komai ba, ganin haka yasa Manager ya katse wayar.
Komawa yai kan dakalin kofar gidan ya zauna, Umma ta aiko yazo yaci abinci, ya kalli d'an aiken tare da cewa " banajin yunwa sai dai anjima."
Daga bayama mik'ewa yai ya tafi can bayan gari ya zauna shi kad'ai.
Rana bata karya, a yau ne ranar asabar uku ga mutuwar Hajiya haka kuma a wannan lokacin ne aka gama d'aurama Jalal aure a massalaci, kana ganinsa zakaga ya rame sosai, sannan sam ya canza Umma kam harta gaji da fad'an rashin cin abincinsa, ana gama d'aurin aure ya wuce gida ya shiga d'akinsa, abokai 'yan uwa da iyaye sai cigiyarsa sukeyi a d'au hoto sai dai an nemishi an rasa, shikam yana kwance cikinsa na mai wani irin ciwo, agoggonsa kawai yasa a gaba yana kallo.
'Yan d'aurin aure sun watse, Abba ya taho gida shikanshi farincikinsa ragaggene d'an yana tsoron abinda zai faru a yau tsakaninsa da Jalal.
Yana isa kofar gida kuwa yaga Jalal a tsaye, kallan mamaki yamai yace " Jalal meye hakan? Kasan dole ne a nemeka amma shine kayi tahowarka gida ko?"
Yai kasa da kai yace " Yahkuri Abba banajin dad'i ne."
Abba yamai kallan tausayi duk ya canza, Jalal yace " Abba jiranka nakeyi, akan alk'awarin dakamin."
Abba ya d'ago a tsorace yace "Jalal!!!."
Jalal yace " Abba d'an Allah na rok'eka daka cika alk'awarinka na fad'amin d'in dakace zakai."
Abba yai shiru sannan yace " muje d'akinka."
Nan suka juya suka shiga soro inda d'akin Jalal yake.
A b'angaren Seemah kuwa tunda ta tashi da asuba, taketa maimaita wannan ranar a ranta, lungun gado ta samu ta rakub'e duk yanda Zahra tai da ita inaa abin yaci tura ga maza duk suna gun karb'ar gaisuwa, agoggon hannunta ta cire tare da rungumeshi a kirjinta, idanunta sun kad'a sunyi jaa.
Kalma d'aya ke yawo a ranta " *Deen an d'auramai aure da wata.*"
Daga karshe Zahra da Aisha sai zuba mata ido kawai sukai.
Jalal zaune a kasa, Abba nakan katifarsa dayake kwanciya, Jin kwankwasa kofar yasa Abba yace " Shigo."
Jalal yabi kofar da kallo, Umma ce ta shigo rik"e da tire, da samiru d'aure a kai, ta ajiye a gaban Jalal, Abba yace " Jalal bismilla."
Kallansa Jalal yai yace "Abba amma ni......"
Abba ya katseshi yace " in har kanaso kaji sai kaci abinci, bansan inkaci wannan abincin kuma sanda zaka karacin wani ba."
Jalal ya kalleshi da mamaki, Umma ta zauna a gefen Abba tare da bud'emai kwannon shinkafa da miyar da akai, nan Jalal ya fara cin abinci sai daya cinye tass sannan Abba yace " Habiba kema ki zauna ."
Nan Umma ta zauna Abba ya kalli Jalal cikin tausayawa sannan yafara bashi labari tun daga farko........................
Har sai da yazo kan ranar da Fatima tazo shagonsa, Jalal hawaye kawai yakeyi na tausayawa Fatima.
Abba yai ajiyar zuciya yace " Nafita kiran Isma'il ne a lokacin dana bar d'ana a shagona shida Fatima akan su jira ni, na fito naga maza guda 5 sun nufo shagon, karasawa nai kusa dasu tare da cewa d'an Allah ina sauri ne amma in kunje akwai d'ana a shagon sai ku bashi kud'in.
Sai a lokacin na kuka da kamaf abu suke sha, jin warin abin ma yasa na gane wiwi ce, na d'an ja baya sannan nace " hmm kuyi hakuri nad'auka shagona zaku.
Ogan cikinsu dana kula shi bayashan komai ya matso kusa dani yace " Amadu Tambaya, Fatima wai na shagonka?"
Na kalleshi sai a lokacin na gane Chairman d'in garin mune wanda ake tunanin nad'awa a satin, kuma yaron gidan da Fatima ke aiki, kuma mijin da zata aura nan da kwana biyu. na kalleshi nace " Chairman nemanta kake?"
Yace " Eh yanzu abokaina sukace tun d'azu suka ganta a shagonka." sam har kasan zuciyata na d'auka ko k'iranta ake ko kuma shi ke san ganinta ko saboda wani abu, na kalleshi nace " Chairman kayi hakuri yanzun nan zata koma gida......."
Kafin na karasa maganata naji an kifamin mari, da sauri na kalli wanda ya naren d'aya daga cikin abokan Abdul d'in ne nace " Kai meye hakan kuma?"
Wanda ya maren d'in yace " Wai Abdul kai wani irin mutum ne? Ya za'ai kana Matsayin Chairman ace wani banza mai shago har zai kalleka yad'inga ma tambayar banza? Banace ka barni nai handling d'in komai ba? Kobakasan ka d'ana ne?"
Abdul ya kalleshi ga mamakina kamar me tsoransa naga yaja baya, daidai nan cikin rashin sa'a ashe d'ana na kallanmu d'an muna kusa da shagon, ganinsa mukai yazo tare da kallan wanda ya maren d'in yace " Malam me Babana ya maka?"
Wata muguwar dariya ya saki sannan yace " Good haka nake so."
Ban kawo komai a raina ba kawai sai gani nai an cafke min d'ana, an kuma samai wuka a wuya, nan fa ya shiga kuka.
Na rikice sosai, kuka yakeyi sosai nima na shiga rokonsu,dariya suka samin na d'azun da ko sunanshi ban sani ba ya cilla ma wani d'an nawa tare da matsowa kusa dani yace " karkuma kai tunanin wannan ne kad'ai matarka tana hannunmu, ahh abin tausayi ko?"
Sannan ya kalli Abdul d'in yace " kayi tafiyarka ko itama tafi karfin ka?"
Abdul ya girgiza kai yace " ai ko d'aureta ne sai nayi, ina gani ya nufi shagona ina ihu akan karyayi.......
Kallansa nai duk na gana rikicewa nace d'an Allah kuyi hakuri, karku lalata mata rayuwa. Naga tashin hankali a lokacin kuma abin da yaban mamaki ba wanda yazo wucewa, gashi kamar sun tambaya, ba wutar nefa gashi dama a lokacin ba gen ake kunnawa ba.
Dariya suka samin dashi sannan aka kwad'ama d'ana k'otar wuka a goshi wani ihu yasa kawai sai ga jini kankace mai......
Kuka nake sosak, suka cemin matarka da alama bata ma da lafiya ko? Na d'ago da mamaki d'an ko ni ban sani ba, suka kwashe min da dariya sukace dataji azaba cemana tai wai muyi hakuri karmu bari abin cikinta ya zube.
Nan na matso tare da rik'e kafafunsu, tashin hankali ne ya karune a sanda suka fito da bindiga, suka nunani sannan suka nuna d'ana sannan sukace " kaje ka k'ira ma Fatima wanda take jira kayi sauri kafin Abdul ya mata ila."
Na d'auka tausaya mata sukai hakan yasa da sauri na wuce na tadda ana fitowa daga masallaci nan na gyara fuskata na shiga cikin masu fitowar, Isma'il na gani na d'aure na sanar dashi Fatima na nemansa na gaggawa.
Mun taho gabana sai faduwa yake, muna zuwa zan shiga sai naga sun min alamar inzo, hakan yasa Isma'il ya shiga shi kad'ai ni kuma na je gunsu, sukamin tafi sukace yauwa ka kyauta.
Na kallesu nace d'ana fa? Mugun ya tab'e min baki sannan ya kalli Abdul da nima sai a lokacin na kalleshi yanasa wando, zaro ido nai nace " meke faruwa?"
Hoton D'ana aka nunomin an saitashi da wuka sannan matata ansaita ta da bindinga, sukace abu d'aya zakai ka cecesu.
Kuka nake sosai ina rok'onsu, ban farga ba kawak naji karar mutanen gari, sukace cewa kawai zakai Abokinka Isma'il shiya mata fyad'e.
Girgiza kai na shigayi ina kuka, mugun yace " to shikenan ka taimaki abokimka in yaso matarka da d'anka, da wanda ba'a haifa ba kwa had'u a lahira.
Abba na zuwa nan yai share hawayensa, Umma ma haka, Jalal kam kukan ya kafe kaf kawai Abba yake kallo wani irin kallo daban fahimceshi ba ni kaina.
Jinai cikin wata irin murya Jalal yace" Saboda tsoron kar ama matarka da d'anka ila yasa ka ce Amininka ne ya mata fyad'e?"
Abba ya kalli Jalal sannan ya kara goge kwalla yace " Akan d'ana ba abinda bazan iyayi ba, ina ganin ansama d'ana wuka za'a yankashi mezai sa inkasa fad'ar kalma d'aya?"
Jalal ya mik'e ya shiga jijiga kai sannan ya kalli Abba sai a lokacin wasu zafaffen hawaye suka fara zubo mai, Abba ya matsu tare da kokarin rik'e hannunsa Jalal yayi baya.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM.*
*Gaisuwa ga duk Masoyan littafin nan ....I Luv u Ol*❤😍😍
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_*This Page is Dedicated to you 🅿herty😍 wish u ol the best in ur Exams..... Thanks once again*_
No. 5⃣3⃣
Jalal jikin bango ya jingina a sulale ya tsugunna hawaye ke malala a kuncinsa, Umma dake zaune itama tana kuka ta taso ta matso kusa dashi tace Jalal! Wani irin kara yayi da duk sai da suka tsorata kuka ya wuce da shi kamar wani karamin yaro, Umma tsoro ya fara kamata ta kalli Abba tace " Meyasa ka fad'amai? Yanzu in wani abu ya sameshi fa?"
Abba ya kalleta cikin wani yanayi, yace " daga sanda Isma'il yazo gidan nan nasan ban isa in b'oye sirrin nan ba, da wani a waje ya fad'amai mahaifinsa yaci amanar Amininsa gwara ni dakaina insanar dashi. "
_Nikaina Ayusher yanda naga Jalal na kuka sai da naji hawaye ya zubomin a hankali nayi waje d'an bazan iya zama ba._
A b'angaren Seemah kuwa bayan mutane sun ragune Ammar ya shigo d'akin, ya kalleta a rak'ub'e a gefen gado, tausayinta ya kara kamashi ya matso inda take tare da d'agata, kallanshi tai kamar wacce hankalinta baya jikinta tace " Ya Ammar am d'aura ko?"
Kallanta yai idanunsa suka ciciko, hannu yasa a kafad'arta yashiga jijigata yana cewa " Get hold of your Self Seemah, please. "
Ya d'ad'e yana jijigata kafin ta kalleshi tace " Yaya ya zanyi?"
Yace " Seemah England zamu koma ranar bakwai inajin shi kad'ai ne zai sa ki manta komai."
Ta d'aga kai tace " na yarda Yaya ni kaina haushin kaina nakeji."
Nan ya mike yai waje, bai dad'e ba sai gashi ya dawo rik'e da plate na abinci, Zama yai kusa da ita tare da d'ebo abinci a cokali da niyyar ba ta, ta kalleshi sannan ta amshi cokalin tace " Zanci da kaina Oppa."
Murmushi ya mata sannan ya mik'a mata spoon d'in, ta fara ci, yace " Matar Dad tazo ta dubaki?"
Ta d'an tab'e baki har zatai maganar rashin kunya ta tuna ashefa ta fita matsayi yanzu, tai kasa dakai tare da cewa " Ta l'eko d'azu."
Ammar yai d'an karamin tsaki yace " bansan ya akai Dad ya aureta ba, sam batada kara."
Seemah tai shiru can tace " Ka manta Yaya? It is all my fault, bakaji Dad nacewa saboda ni ya aureta ba? Na sani saboda yanaso akula da......."
Kasa karasawa tai saboda hawaye, Ammar ya kallera yai murmushi yace " Oh yazanyi da wannan kanwar tawa mai saurin kuka?"
Ta kalleshi tare da share hawayenta tace " Yaya?"
Yad'an rangwab'ar dakai yace " Seemah rufe idonki."
Ta kalleshi tad'an turo baki kad'an, sannan ta rufe, hannu yasa a aljihunsa, sannan yace "bud'e."
Da sauri ta bud'e tanasan ganin menene, kwalin waya ya mika mata, ta kalli wayar Iphone 6 ce, tace " yaya inafa da waya?"
Yace " Dad ne yace kar abaki waccan."
Tai murmushi sannan ta amsa tace " Thanks Bro."
Yai murmushi shima yace " Ahhh naji dad'i kinyi murmushi, sannan kinci abinci."
Ta kalleshi tace " saboda Deen ne ba'asan abani d'ayar wayar?"
Ammar ya kalleta bai amsa ba, ta kara murmushu tace " karkadamu yaya, yama za'ai in sake ganinshi? Sannan bazan bari effort d'inka ya tafi ba yanda kasa naji zuciyata tayi sanyi ba."
Ammar kallanta kawai yake, ta kara sakar mai murmushi sannan ta hure mai ido tace " Yaya kallan fa?"
Mik'ewa yai da sauri tare dasa hannu a aljihu duk ya rikice yace " Ehem dama dama fita zan d'anyi, nan zafi ko bakya ji?"
Batasan sanda tasa dariya ba, tace " Zafi kuma yaya? Nan d'in?"
Kallanta yai yace " Seemah just now dariya kikai ko? Badai hallucination na gani bako?"
Tai kasa dakai tana murmushi tace "kai yaya kai d'in ne wai zafi."
Kallan yanda take murmushi yasa ya farajin zafin na karuwa, da sauri yai waje, yana fita daga d'akin ya fara furzar da wata iska yanacewa " Cool down Ammar."
Can kuma yace " meke damuna?"
Junaid ne ya dafashi yace " Ammar agidan gaisuwar ba kunya kake soyayya?"
Kallan Junaid yai a tsorace, Junaid yai murmushi yace " Ya Habib ya fad'amin komai karka damu."
Ammar yai ajiyar zuciya sannan ya kuma kalleshi da mamaki yace " ban gane soyayya ba kuma?"
Junaid yace " in ba soyayya ba me kake a d'akin?"
Ammar ya kalleshi da mamaki yace " What? Seemah ce fa a d'akin."
Junaid ya d'an jinjina kai yace "ai sanin Seeman ce yasa na fad'a, Ammar ka nutsu ka tambayi zuciyarka, wacce irin soyayya kake mata?" Junaid na kainan ya juya yai gaba yabar Ammar da binsa da kallo.
Jalal kam bayan su Abba sun fita yana nan dai a gun da yake, ya dad'e agun kafin ya daina kukan, yafara cewa " ya zanyi Seemah?"
Jin ba amsa yasa yai shiru can yace " Abdul?"
Cikin zafin nama ya mik'e yai waje, a waje yaga Abba, Abba na ganinsa wani dad'i ya kamashi da alama harya sauko kenan, Jalal ya kalleshi cikin d'aure fuska yace " Abdul d'in yana ina yanzu?"
Abba ya girgiza kai yace " Jalal ka rufamin asiri d'an Allah wannan mutumin yafi karfin mu bani ba har Isma'il d'in dayake da kud'i."
Jalal ya kalli Abba yace " Abba ina Abdul d'in yake yanzu? Dole ne ya nemi yafiya agun Seemah da iyayenta, kaima kuma Abba dani dolene mu nemi yafiya, duk da ba lalai a yafemana ba, wayasan wace irin rayuwa suka shiga akan kalaman nan guda d'aya?"
Abba ya kalleshi a tsorace yace " Jalal ninaji zan bada hakuri ko mai za'amin bazan damu ba amma Jalal ba ruwanka da harkarnan, dama tun farko baka san komai ba, d'an haka yanzun ma ka nuna bakasan komai ba."
Jalal idanunsa suka ciciko yace " Me kace Abba? In nuna bansan komai ba? Taya zan iya?"
Hawaye suka zubo mai yacigaba " akan Mahaifiyar Seemah ne fa da kuma Wanda ya rik'eta kamar 'yarsa Amininka kuma."
Yai ajiyar zuciya sannan yai d'an murmushin yake yace " Tunda naji labarinnan nasan ban cancanci auran Seemah ba, ko da kuwa iyayenta zasu amince dani, Ammar shine ya dace da ita koda har karshen rayuwata zan kasance cikin tsananin begenta bazan kuskura inkara gangancin cewa ina santa ba."
Kalaman Jalal sun ratsa zuciyar Abba shima ya share kwallarsa yana kallan Jalal, cigaba da magana yai da cewa " Shiyasa nakeso ko ban aureta ba insamu in mata wani abinda zaisa ta rage tsanar datamin hakan ne zaisa ta manta dani."
Ya kara share kwalla sannan ya kalli Abba yace " Abba kataimakeni inma Seemah abu guda d'aya a rayuwar duniyar nan."
Abba bai san sanda ya rungume Jalal ba, yace " Jalal a koda yaushe ina alfahari dakai, kafi wannan mahaifin naka tunani mai tsawo."
Jalal idanu kawai ya runtse, shikad'ai yasan rad'ad'in dayakeji a ransa.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣4⃣
Jalal ya d'ago ya kalli Abba yace " Shugaban kasa ne shi ko me?"
Abba ya kalleshi yace "Jalal Sanate ne yanzu wanda kuma ake ji dashi haka kuma mutane na sanshi, ina tsorace maka abinda zai biyo baya."
Wata muguwar dariya Jalal yai wacce sai da abin ya tsorata Abba, sannan ya tsagaita yace " mene? Sanate? Wasu mahaukatan ne suka zab'eshi? Kuma shi ko kunya mutumin dabai san darajar d'an Adam ba harya iya cigaba da siyasa?"
Abba yai ajiyar zuciya yace " nidai yanzu kabar komai kaga gobe za'a kawo Zainab."
Jalal ya kalli Abba shi harya manta da wani auren Zainab, ya juya kai batare dayace komai ba.
Ganin haka yasa hankalin Abba yad'an kwanta, mutane mak'ota ne suka fara zuwa halan yasa Jalal ya koma ciki, shiru yai yana tunani can ya d'auko wayarsa yafara duba senate na kasa, kan wani yazo *ABDULLAHI UMAR*
Ya kalli hoton mutumin dakyau gabansa ne ya fad'i ba shakka wannan shine mahaifin Seemah bawai kama sukai sosai ba sai dai in har ka kalleshi ka kalli Seemah zakasan akwai alak'a ta jini sannan ga tarihinsa daya karanta, ransa yakai k'oluluwar b'aci sanda yaga yanda ake ji dashi da kuma yanda mutane ke masifar sanshi wasu har so suke ya tsaya a matsayin shugaban kasa na zab'e ma gaba.
Haushi ya ishi Jalal ya cilar da wayarsa kan gado sannan ya mik'e cikin zafin rai kawai wayarsa ya d'auka ya fita.
Tasha ya nufa kawai ya shiga motar abuja, sam idanunsa sun rufe.
Dad da Abba da kuma kawo ne zaune a d'aki, Abba ya kalli kawu yace "Wani hukunci ka yanke?"
Dad yai saurin cewa " Kawu nidai dan Allah kadawo nan da zama me zakayi a suleja yanzu? Dama can ba garin mu bane."
Kawu yai shiru cam yace " naji amma dai kai Isma'il kaima ina fatan kadawo nan da zama kenan?"
Dad ya d'ago ya kalli Kawo sannam ya kalli Abba jikinsa yai sanyi, Abba yace " gaskiya kam ya kamata kaima ka dawo kazauna anan."
Dad a hankali ya furta "karatun Seemah fa? Ina tunanin yimusu baiko itada Ammar sai in koma can inyaso in ta gama karatun sai mu dawo gaba d'aya."
Abba yai shiru can kawu yace " naji bayananka sai dai nima na yanke nawa hukunci na."
Ya kallesu sannan yace " In akai bakwai d'in marigayiya nakeso wahsegari ai baikon Junaid da Ammar, in yaso sai ka d'auki matarka ku koma England har zuwa sanda zata gama karatu, da zarar ta dawo za'a had'a ayi auren."
Dad ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan can ya kalli Abba sannan ya kalli Kawu yace " Amma junaid yanada budurwa ne?"
Nan Abba ma ya kalli kawu da mamaki, Kawu yai murmushi yace " ba wani taro za'ai ba saboda rasuwar da akai mana kawai dai za'asa rana ne a kuma bada kud'in gaisuwa."
Abba ya kalli Kawu yace " amma kawu......"
Kawu yai murmushi yace "Mahaifiyarku babban burinta bai wuce tayi had'in aure a tsakanin 'ya'yan ku ba, tunda shi Ammar yanada Seemah shiyasa nake tunanin had'a auren Junaid da Zahra."
Kallan juna Dad da Abba sukai, Kawu yace " na amince da auran Ammar da Seemah sai dai kamar yanda mahaifiyarku tace dole ne kafin ranar auren asan mahaifinta."
Dad yai murmushi tare da cewa gaskiya ne naji dad'in had'in nan, Abba ma yai murmushi.
Jalal sai bayan magrib ya iso Abuja, wayar Umma ce ta shigo sai alokacin ma yai tunanin ashe bai fad'a musu ba, da sauri ya d'aga wayar yace " Umma?" Tace " Jalal kana inane? Tun d'azu ana nemanka."
Jalal ya kalli cikin garin Abuja yace " Umma kiyi hakuri d'an Allah wani uzuri ne ya tasomin ina Abuja yanzu."
Tace " Abuja kuma?gobe fa za'a kawo Amarya."
Jalal ya runtse ido jin an anbaci Amarya yace " kiyi hakuri Umma."
Tace " naji amma ka tabbatar gobe ka dawo da wuri banasan mutane su fara zargin wani abun."
Yace "insha Allah." Nan suka kasje wayar.
Yana sauka yai sallah sannan ya nemi d'an machine yace " kasan gidan Sanate Abdullahi?"
D'an machine d'in ya kalli Jalal daga sama har kasa sannan yai dariya yace " kasan me kake cewa kuwa?"
Jalal ya had'e rai yace " mahaukaci ne ni dabazan san me nake cewa ba ko me?"
D'an machine yace " A'a muje inkaika." Aransa yace ko mai aiki ne a gidan?
Sun isa wata had'ad'iyar unguwa manyan gidajen dake gun da kuma tsarinsu zai tabbatar maka da guri ne manyan mutane.
A kofar wani had'ad'an dank'araren gida yai parking, Unguwar shiru kamar ba mutane, d'an machine ya juya yatafi bayan ya cemai nan ne gidan.
Jalal yabi gidan da harara yace " Dama irinkune masu hana kasar mu cigaba, kun tara zunubai a kanku kuma kunzo d'an yaudarar mutane."
Kofar Gate d'in ya karasa tare da tunanin ta inda zai fara, wani security ne ya fito tare da kallansa yace " me kake anan?"
Jalal ya kalleshi yace " Gidan Sanate Abdullahi ne?"
Mutumin ya kara had'e rai yace " eh amma kai waye?"
Jalal ya d'an daure tare da sa hannu a aljihu yace " nemansa nakeyi."
Security d'in ya jara kallansa yace "baka da hankali ne? "
Jalal yace " what?"
Nunashi da bindiga yai irin doguwar nan yace " waye kai?"
Nan fa idanun Jalal sukai tsuru tsuru, husur security d'in ya hura nan da nan wasu securities d'in suka fito, ya kalli Jalal yace " a dubashi da kyau ban yarda da shiba."
Jalal haka suka ririk'eshi suka shiga lalubamai jiki kamar yai ihu d'an bakin ciki, suna gamawa suka sakeshi tare da cewa " nothing suspicious Sir."
Ya kalli Jalal yace " tashi ka kara mai karkuma insake ganinka anan."
Jalal ya dake zuciyarsa yace " ganina kuwa dolene d'an bazan tafi ba harsai naga mutumin gidan nan inkuwa kuka hanani to sai dai ku fita da gawata."
Mutumin ya kalli Jalal yai murmushi yace " I wish kayi karatun Soja da anyi jarumi."
Jalal ya juya kai, mutumin ya cigaba sai dai inhar baka tafi ba zakuwa a fita da gawarka.
Jalal ya kara dakewa tare da jingina da katangar gun, ran mutumin ya b'aci ya d'aga kasan bindiga zai bugama Jalal, sai sukaji karar horn, da sauri suka jeru aka bud'e gate, motoci uku ne suka shigo Jalal ya kalli motocin har sukai parking sannan wata yarinya ta fito daga motar sanye da riga da wando sun matseta, tana tafe tana jijiga kai alamar rawa, Jalal yaja karamin tsaki yace "Allah ya shirya."
Juyowa tai d'an taji alamun kamar ana kallanta caraf suka had'a ido da sauri Jalal ya d'auke idanunsa, d'an takaici aransa yace "yanzu wannan kanwar Seemah ce fa ko?"
Baisan tazo kusa dashi ba sai jiya tace " waye wannan?"
Securitin ya kalli Jalal yace " Sorry madam."
Yanda take magana ma ya tabbatar ma Jalal ba'a hayyacinta take ba, ta nuna Jalal tace " Kai."
Jalal ya kalleta tare da girgiza kai yarinya karama dabata wuce shekara 18 ba amma.......
Zata sake magana taji daga saman beni ance "Me kikeyi anan?"
Da sauri Jalal ya d'aga kai, baban mutum ne da dukda baikai su Abba ba amma kasan baba ne, Jalal ya kara cusa ido ya kalleshi tabas mutumin da yake nema ne.
Dabara ce ta fad'o mai,
Yarinyar zatai magana Jalal da karfi yace " Sannu Dad dama cewa tai inzo gunka akan maganar soyayyarmu."
Securities suka kalleshi da mamaki itama ta juyo duk da a bige take ta nuna shi sannan ta nuna kanta, murmushin rainin hankali ya mata yace " Ko Sweety?"
Kai ta d'aga sannan ta kalli Mahaifinta wanda ransa yai mugun b'aci yace ku shigo ciki.
Jalal yai wani murmushin rainin hankali sannam ya kalli Securities d'in yace " Sorry bansanar daku da wuri ba."
Fatan Alkairi gareku " _*MUM HAMRA, MOM FARHAN, FRESH, AGRA, RAHANCY DA MOM FAROUK*_ "
Hope anyi weekend lafiya.......😍😍
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
*This page is for you Ramalurv......*😍😍😍😍
No. 5⃣5⃣
_I am really sorry jiya da shekaranjiya kun jini shiru, wani uzuri ne ya hanani typing. ......luv u ol_
Jalal ya kalli yarinyar ya mata wani murmushi yace " muje ko? Ta kalleshi sai dai idanunta nuna mata wani guy datakeso yake, hakan yasa ta d'aga kai da sauri tare da natsowa tana k'okarin kamamai hannu, Jalal yad'anyi baya tare da cewa "kiyi gaba ina binki."
Tad'an tab'e baki kafin tai gaba, wani tafkeken falo ta bud'emai ya shiga da sunan falon baki sai dai duk dakiya irin ta Jalal sai da jikinsa ya amsa d'an kyan falon ya wuce inda mai karatu zaiyi tsamani, ta nuna mai kujera, Jalal ya zauna tare da karabin falon da kallo, sam ya shagala baiyi tsamani ba yaji mace ta zauna kusa dashi tare da sakalo hannunta, zabura yai ya mik'e cikin mamaki yace "me kike yi hakan?"
Ta tab'e fuska kamar zatai kuka, jitai ance tashi ki shiga ciki, atare suka kalli mai maganar, ta mik'e tana layi tai ciki shikuma Jalal ya sake kuramai ido.
Har mutumin yazo ya zauna tare da kunna tv Jalal na tsaye sai da yace " zauna mana."
Sannan Jalal ya farga tare da zama a kasa, yace "Ina wuni?"
Mutumin bai amsa ba yabi Jalal da wani kalan wulakanci sannan yace "kaine kesan Huda?"
Jalal a ransa yace Huda sunanta?
A fili ya d'ago ya kalleshi, zaiyi magana taji yace " Naji dad'i dana ganka haka, dama nafisan talaka wanda yake nema, yanda duk abinda na gindaya mai dole ne yabi, d'an haka ka sanar da iyayenka d'an nima na gaji da wannan iskancin nata da jamin magana datakeyi, a d'aura muku aure sai in turaku Australia kuje can kuzauna har karshen rayuwarku."
Jalal ya d'ago ya kalleshi da tsananin mamakin kalaman fayake furtawa a matsayinsa na mahaifinta.
Daurewa yai tare da cewa " niba saurayinta bane sannan ni maganar danazo ma da ita......."
Jiyai an katseshi da cewa " what? Kaikasan ko ni waye zaka rainamin hankali? Da kace gunta kazo yanzu kuma me? Ko dama ba da aure kake santa ba?"
Ya mik'e yana kare ma Jalal kallo, Jalal ya dake tare da d'agowa ya kalleshi yace" akan maganar d'aya babbar 'yar taka nazo."
Kallan mamaki yamai yace " Da alama bakasan ma mai kazo yi ba, bayan huda ragowar kannanta maza ne guda uku sai karama yanzu wacce ko shekara 4 bata kai ba." Cikin takaici ya fara kokarin juyawa.
Jalal gani haka yasa yai saurin cewa " Ka manta Fatima ne? Ta garin birnin/gwari?"
Da sauri ya juyo ya kalleshi idanunsa suka kad'a da sauri ya dawo kusa da Jalal ya d'agoshi tare da rik'emai kwalar riga cikin fad'a yace " Who are you? D'an jarida ne kai?"
Har zuciya Jalal yaji tsoro sai dai da ya tuno Seemah sai ya dake yace " Ni ba d'an jarida bane, Sunana *JALAL* D'an gidan Amadu mai shago dake garin birnin/gwari."
Sakeshi yai sannan yace " What?"
Jalal ya gyara tsayuwarsa, yace " 'yarka tananan lafiya agun mutumin da kuka ma sharri ya rik'eta, sai dai ko bata fad'a ba nasan itama tanasan ganin mahaifinta."
Wata mahaukaciyar dariya Jalal yaji an fara mai kallan Abdul yai cikin tsoro, Ya dad'e yanayi kafin ya tsagaita yace " What?'ya ta?" HA HA HA HA
Ya cigaba " ko a da ba 'yata bace banga dalilin dazaisa yanzu ta zama 'yata ba."
Jalal yai ajiyar zuciya tare da komawa ya zauna a kasa, yace " ka manta Fatima fa wacce kuka ketama......."
Tsawa ya dakamai yace " na keta mata ko Isma'il ya keta mata?"
Jalal ya d'ago cikin mamaki yace " me yasa kana babba kakesan take gaskiya? Me yasa bakajin kunyar karyata abinda kasan tabbas shine gaskiya?'
Ya kalli Jalal yace "in ma turo ka akai ko d'an kanka kazo sai ka kama hanya ka fita, duk duniyar nan banga wanda zaizo ya wargazamin harkar siyasa ta dana shiryata da gumi na ba, dan rainin hankali sai da nakai wani matake sosai ina shirin kara hawa sama shine zakazomin da zancen banza d'an kasamin bak'in jini gun mutane? Da can bakuzo ba sai yanzu?"
Ya nuna Jalal da yatsa yace " Wallahi kaji ma fad'ama ba 'yataba? Ba kuma matata ba ko mahaifiyata bata isa ta kawomin cikas a harkar siyasa taba in kyaleta bare kai da wata yarinya daban ma santa ba, in kud'i takeso kaje kace ta fad'i ko nawa ne, Ni Abdullahi nad'au alkawarin ba ta."
Jalal wani irin kallo yake binsa dashi na tsananin ban mamaki da kuma tsoron furucinsa, wani irin mutum ne wannan? Siyasa ce ta maidashi haka ko kud'i ne? Ko kuma dama can haka yake?"
Kafin Jalal ya k'okarta yai magana haryakai bakin kofa, Securities ne suka shigo suka kalli Jalal sukace " fito ko mu fitar dakai."
Jalal ya kalli mutumin cikin takaici ya dake ya matso kusa dashi kad'an yace " Wallahi kaji na rantse maka in dai ina raye sai ka tsuguna a gaban Seemah ka nemi yafiyarta da abinda kama mahaifiyarta, idan kafi karfi na ai bakafi karfin hukuma ba, Allah kuma na tare dani kajira ka gani."
Dariya Abdul yai tare da zaro 'yan bandir d'in dubu d'aya ya mik'amai yace " Daga kai har yarinyar har hukumar bakufi karfin wannan ba."
Jalal cikin takaici yake kallansa ya kakaro murmushi yai sannan yace " in kafi karfin hukuma ai baka fi ta Allah ba."
Yana kainan yai waje.
Ko securities d'in bai kula ba ya fita, kafa kawai yake sawa, yana tafe yana mamakin abinda idanunsa suka ganemai, kuma kunnensa suka jiyemai, a hankali wasu kwalla suka zubo mai, a fili yace " Seemah ya zamuyi?"
Seemah kam tana zaune a kan gado rik'e da waya, tarasa abinda ke mata dad'i, d'azu Zaid yazo yace mata wai za'a sanya musu rana da Ammar, itakam ta rasa mema zatayi, motsin bud'e kofa ne yasa ta kalli kofar, Dad ne ya shigo tare da sallama, ta amsa tana neman kakaro murmushi, ya karaso kusa da ita ya zauna tare da kamo hannunta yace " me kikeyi anan bayan kowa na falo?"
Tai kasa dakai batare da tace komai ba, yai murmushi yace " Kinji labari?"
Da sauri ta d'ago ta kalleshi tace " name fa Dad?" A ranta kuwa addu'a take Allah yasa ba zancen Zaid yake nufi ba.
Dad ya sake murmushi tare da shafa mata kai yace " burina ya kusa cika Seemah, babban burina bai wuce inga kin auri d'aya daga cikin 'ya'yana ba, na sani kuma kowa ya sani Ammar ne yafi dacewa dake, shiyasa nakesan ki daure kicire san Jalal a ranki."
Seemah jitai kafarta na rawa da sauri ta hawuda ita kan gado kar Dad ya gane, ta kakaro murmushin yake sannan tace " Dad nasani ya Ammar zai kula dani sosai. "
Dad yasa dariyar farin ciki yace " ko? Ashe kema kinsani, shiyasa muka yanke za'a samuku rana sai mukoma ki karasa karatunki sai ai auren."
Tai murmushi tare da cewa hakan yayi Dad, burina bai wuce inga nasanyaka farinciki ba."
Takarasa maganar cikin rawar murya.
Dad ya jawota jikinsa yana lalashi, yace "kicire komai a ranki ki koma yanda kike da nakuma gode sosai da amincewar da kikai."
Ta d'ago tare da girgiza kai tace " nice da godiya Dad koda ace zan bauta maka har karshen rayuwata banaji zan biya kwatan abinda kamana nida mahaifiyata."
Dad cikin wasa yace "oh ni Seemah yaushe zaki daina maimaita abin nan?"
Tai kasa da kai tana murmushi ya mike ya fita ta bi bayanshi da kallo tare da cewa "Deen yazanyi?"
Jalal tsaye a kofar gidan Abba yanaso ya musu gaisuwa sai dai inaaa kunyar ma shiga yake in ya tuna abinda ya faru, gani yai an dalleshi da fitila, hannu yasa yad'an kare fuskarsa, a hankali mai fitilar yazo kusa dashi ya nuna shi da yatsa tare da kwashe wa da dariya yace " I am right kaine." Yafad'a tare da nuna kansa alamar naushi.
Jalal ya kalleshi sannan yai 'yar dariya yace" ashe baka manta ba."
Zaid yace " ya za'ai in manta bayan an nemi a gurd'eni?"
Jalal yace " Kayi hakuri time d'in....."
" baka hayyacinka ne saboda kishi ko?"Zaid ya karasa mai.
Jalal yai murmushi baice komai ba, Zaid ya rik'e hannunsa yace " muje ciki kuyi sallama da Seemah an kusa sa mata rana."
Bawai baiyi tsammanin ranar zatazo bane, bawai kuma tsoron hakan yake bane, bawai kuma baisan hakan a faru bane a'a shi aganinsa hakan ne daidai sai dai jin kalmar ya sa ya ja burki ya tsaya, gabansa ne yashiga fad'uwa, idanunsa suka canza kala, Jalal ya daure yace " dare yayi mubari sai gobe nazo."
Zaid ya haska agoggon hannunsa yace "karfe 8 da rabi shine dare? Tab lalai inbaka gantaba yau banaji zaka kara samun wani lokacin."
Jalal ya kalli Zaid sannan cikin sanyin murya yace " muje."
Yana tafe yana " *_INALILAHI WA INA ILAHIHI RAJI'UN_*" har yai sa'a gaban nasa ya daina fad'uwar.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣6⃣
Jikin Jalal yai sanyi haka suka shiga gidan, Zaid yace " ka ga ka nausheni ashe kaima gaba kai za'a nausa?"
Jalal yai murmushi yace " hakane dama, to amma karfa mu shiga cikin gidan ka d'inga cewa na nausheka."
Dariya Zaid yai yai alamar zip a bakinsa, Jalal yai murmushi, sun shiga falon mami, mata me 'yan uwa a zaune, nan Jalal ya tsugunna kansa a kasa ya gaishesu, suka amsa suna kallansa, ya musu ya hakuri, Zaid ne ya kalli mami yace " mami kin ganeshi? Jalal d'in........"
Kafarsa Jalal ya mintsina da karfi, Zaid yai 'yar kara tare da kallan Jalal, da sauri ya mik'e yace " Sai da safenku."
Ya fad'a yana kallan Zaid, muryar mami suka ji tace " Ka kaishi ya gaida su Abbanka."
Jalal ya kalleta jiki a sanyaye, da alama ta ganeshi tunda sun had'u a asibiti, Zaid ya kalli Jalal yace muje ko?
Nan suka wuce falon Abba, a hanya Jalal ya kalli Zaid yace " d'azu mai kake san fad'a?"
"AUUUU wannan? Hmm dama cewa zanyi Jalal d'in Seemah in na fad'a za'afi ganewa."
Jalal ya kalleshi cike da mamaki yace " mene? Jalal d'in Seemah?"
Dagewa yai ya takamai kafarsa da karfi Zaid sai da yai 'yar kara yace " Wai ni menai?"
Girgiza kai Jalal yai yace " lalai Zaid mema kai kake tambaya? Da alama........."
Ammar ne ya karaso gun yana cewa " Zaid meye hakan?"
Ya fad'a yana kallan wanda ke tsaye, kalan kallo suka shiga yi, Jalal ya daure tare da mik'a mai hannu, Ammar ya mik'amai shima suka gaisa.
Jalal ya kalli Zaid sannan ya kalli Ammar yace " Gaisuwa nazo."
Gyad'a kai yai alamar gamsuwa sannan ya nuna mai kofar falon yace " muje?"
Nan suka shiga su uku tare da sallama, Abba, Dad, da kawu suna zaune a falo ga Junaid a kasa da alama nasiha ko fad'a ake mai, jin sallama yasa suka amsa, Junaid ya kalli Kawu yace " Zan rik'eta amana insha Allah."
Yana kainan ya maida kallansa kansu Ammar, Zaid ne ya fara shigowa, sai Ammar sai Jalal a baya, dukansu suka canza fuska shikam Junaid kallan Jalal yai nan suka karasa suka zauna a kasa.
A hankali Jalal ya gaidasu, suka amsa kamar basa so, ya musu ya hukuri, nan ma suka amsa kamar d'azu, sunyi shiru a falon kafin Junaid yace " daga ina?"
Jalal ya kalleshi suna kamada ya Habib hakan yasa ya gane shine d'ayan yayan Seema, mik'ewa yai a hankali ya dawo sautinsu Dad a hankali yakai gwiwowinsa kasa, kallan mamaki suka mai, idanun Jalal suka cicoko ya d'ago a hankali ya kalli Dad yace " Nasani banida bakin magana, bankuma san da wacce kalma zan fara ba, da ace abin bai faru bane shine zan sami karfin gwiwar yin magana." Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba" na sani dani da mahaifina bamu da bakin da zamu nemi yafiya daga gareku, sai dai.......sai dai....."
Hawaye ne yafara zubomai hakan yasa ya kasa karasa maganar, kansa ya durkusar a kasa yana hawaye sosai, dukansu tausayinsa ya kamasu, Junaid ma ya gano shine Jalal d'in, Dad yanasan Jalal tunsanda aka haifeshi, ganinsa cikin wannan yanayi yasa shikansa yaji idanunsa sun ciciko.
Ammar mik'ewa yai yaje kusa da Jalal a hankali yace " Tashi mu tafi."
Jalal ya runtse ido, ba tare da ya motsa ba, Ammar ya kalleshi cikin tausayawa, Zaid ne ya mik'e shima ya kalli Jalal yace " Katashi ka tafi Jalal."
Nan ma bai motsa ba, Zaid ya kalli su Dad cikin b'acin rai d'an shi baisan meya faru ba, yace " Abba shiya muku laifi? Me yai? Meyai muku da zai tsugunna yana neman yafiya amma dukanku ku shareshi? Bayan yarinyar dayakeso take sanshi kun......"
Da karfi kuma cikin tsawa Jalal yace *ZAID* kowa sai da ya kalli Jalal, Zaid a zuciye yai waje, a zahiri shikam ya kasa gane menene dalilin dazai sa a hana yarinya yaron da takeso.
Jalal yai ajiyar zuciya tare da kara share hawayensa ya kakaro murmushin da kana gani kasan na bakin ciki ne ya kalli Dad yace "Dad an d'auramin aure."
Kallan sa sukai su dukansu, ya sake murmushi sannan ya kalli Ammar yace " Ammar ina tayaka farinciki, naji an kusa sa rana."
Ya sake wanni murmushin tare da goge kwalla ya maida kallansa kansu dad yace " Dad Allah yasanya alkairi, naji dad'i."
Hawaye suka kara zubomai, yace " Bakomai in har zuciyarka bazata iya yafemin ba, na sani wannan wani gyambo ne da ke zuciyarka, tunda Amininka ne ya cuce ka."
Yai murmushi har hakoransa suka fito, ya share hawayensa sannan yace " Amma nikam a kasan zuciyata nayi tunanin wani abu guda d'aya, naji dad'i daya kasance kaine ka raini Seemah har kawo wannan lokacin, da Allah ne kad'ai yasan wace rayuwa zatayi a gidan wannan mutumin da zuciyarsa ba imani."
Ya share kwalla sannan yace " in na duba abin ta fuskar daya kamata sai inga Allah ne ya taimaki Seemah......."
Dukansu tausayin Jalal ya ratsasu sosai, dan Dad sai daya kauda kai ya share kwalla a fakaice, Junaid ma idanunsa sun ciciko, Ammar kam shima hawayen yakeyi, a hankali Abba yace " Kasan mahaifinta ne?"
Jalal ya kalli Abba yana hawaye yace " nasanshi, sai dai ba amfani a sanin nashi."
Dad ya mik'e yazo kusa da Jalal yace " Me kake nufi?"
Jalal yai murmushin takaici yace " Dad karka damu, bazan iya fad'a muku ko waye a wannan lokacin ba, sai dai nama Ammar alkawari, kafin a d'aura masa aure da Seemah sai mutumin nan yazo da kansa yaba Seemah hakuri koda kuwa hakan shine zai zamo abu na karshe dazanyi a rayuwa ta."
Dad ya kalleshi cikin tsananin tausayawa, Ammar ya share kwalla ya kalli Jalal yace " kar ka kuskura kayi abinda zai jama matsala a rayuwa da sunan alkawari."
Jalal yai murmushi, ya mik'e yazo kusa da Ammar ya dafashi, baice komai ba yai hanyar kofa.
Zaid kam yana fita gun Seemah yaje, tana zaune da waya tana rubuta sunan Jalal sai ta goge, ta sake ta kuma sake gogewa, tafi hour 1 tana abu d'aya, Zaid ya shigo ya kalleta yace " Seemah albishir?"
Kallansa tai batace komai ba, yace " Jalal yazo yana gunsu Dad gwiwowinsa a kasa."
A zabure ta mik'e ta zauna tare da cewa " Deen?"
Deen?
Deen d'i.....?
Zaid ya d'aga mata kai, fita tai da sauri d'an ko mayafi ta manta bata d'auka ba, sai datakai kusa da falon ta tuna ashe fa sun rabu, hartayi alamar juyawa taji motsin bud'e kofar falon, tsayawa tai cak ta baya gabanta na dukan uku_uku, Jalal shima yana fitowa daga d'an nesa kad'an ya kalleta, gabansa ne ya fad'i a hankali Seemah ta juyo, cikin tsoron wanda zata gani, Jalal ma idanunsa na kanta.
Tana juyowa suka kafe juna da ido, dukansu idanunsu ya ciciko da kwalla, Seemah jitake kamar taje ta rungumeshi, a hankali Jalal ya fara takowa, suna kallan juna, har yazo kusa da ita kad'an, ya fara kokarin maida kwallarsa tare da kakaro murmushi ya rasa me zaice mata, itakam kallansa kawai take.
Can ya dake yace " Long time?"
Ta kalleshi tare da share kwalla tace " ka rame"
Yai murmushi yace " kema."
Ta d'an d'auke idanunta, a hankali yace " bantab'a tunani zan ganki ba."
Ta d'ago ta kalleshi tace " nima bansan ya akai nazo nan ba."
Murmushi mai cike da tausayin juna sukama kansu, ya kalleta yace " an kusa ko?"
Kai ta d'aga mai, yace " Congrats. "
Itama tace " anyi ko?"
Shima kai ya d'aga mata, ta share kwalla tace " I see."
Shiru sukai suna kallan juna can Jalal yace " bakya cin abinci ko?"
Ta kalleshi batace komai ba, yace " do you not resent me?"
D'agowa tai ta kalleshi, ya jinjina kai yace " dole ne ko?"
Kallansa kawai take batace komai ba, yace " bazan nemi yafiyarki yanzu ba, sai na cika alkawarin dana d'auka."
Ta bud'e baki zatai magana, taga Ammar ya fito daga falo, cak ya tsaya daga nesa kawai yana kallansu, itama kallanshi takeyi, hakan yasa Jalal ya juya...........
Ruguntsemi sai ran sallah🎧 Ruguntsemi sai mata🎹 ranar bikinmu akwai shagali Ruguntseminmu da nairori🎧😂 oh ni Ayush ina ganin haka kawai ma tuno wakar daa.......
© *THE MEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣7⃣
Jalal ya kalli Ammar sannan ya juyo ya kalli Seemah jikinsa ya kara wani yin sanyi, murmushi yama Seemah sannan a hankali cikin wata murya yace " Nagode Meemah da duk abinda ya faru bai hanaki ganina ba, nagode sosai." Yana kai nan ya fara tafiya ya wuce Seemah, Ammar na tsaye ganin Jalal ya fara tafiya shima jikinsa yai sanyi, har Jalal ya d'an wuceta kad'an Seemah tace "Deen?"
Tsayawa yai cak batare daya juyoba sai idanunsa da suka kara cicikowa, wato haka dama rabuwa take? Seemah ma bata juyaba tace " In ka tafi yanzu shikenan kuma ko?"
Idanu Jalal ya runtse zuciyarshi ta shiga k'una, sai dai ya kasa amsa mata, kuma ya kasa wucewa, Seemah can ta kalli Ammar daya juya baya ta fara takawa ahankali har ta isa inda yake, sannan ta juyo ta kalli Jalal, daidainan shikuma yaji shirun yayi yawa ya juya d'an ya ma ta sallama, gani yai bai ganta ba nan ya shiga dubata, daga nesa ya hangota da Ammar, juyawa yai da sauri d'an zuciyarsa na wani irin zafi, a hankali ya d'inga takawa har ya fita.
Seemah kam Ammar ta kalla tace " Yaya?"
Juyowa yai a hankali d'an baiyi zatan zai jita a kusa ba, ta kalleshi ta mai murmushi tace " Kayi hakuri na........"
Girgiza mata kai yai yace " Kar kice komai, naji dad'i ma da kika fito daga d'aki, d'an nagaji da ganinki kullum a d'akin nan."
Tai kasa dakai tana neman abin cewa can tace " yaya ni ban ma san......."
Hannu yasa akan leb'enta yace " karkice komai."
Ta kalleshi kawai batace komai ba, a hankali tad'an juya baya ta zata yananan, gani tai ba kowa agun, ga mamakinta jitai Ammar yace " Ya tafi."
Da sauri ta kalleshi jikinta yai sanyi tace " nifa ba wanda nake nema."
Yai murmushi yace " nasani, kin tambayeshi mahaifinki?"
Idanunta ne suka ciciko ta d'ago ta kurama Ammar ido, yace " Seemah?"
Share hawayen daya zubomata tayi tace " Banasan sanin ko waye shi."
Zaiyi magana sukaji ana tafi,juyawa sukai suka kalli Junaid.
Ya karaso yana dariya yace " iyee? Abin ma ba kunya a kofar falon Abba? Da alama kun kosa a d'aura." Yai maganar cikin zolaya.
Ammar ya kalleshi yace " Kai fa meza'ace?"
Junaid yai dariya tareda karasowa yace "ne nai ni kuma?"
Kallan Seemah yai yace " Kanwata kema bakya mamaki? Ace wai Junaid an had'ashi aure da Zahra amma ko meta baiyiba sai ma farin ciki dayake?"
Seemah tai dariya tare da kallan Junaid tace "Gaskiya ne yaya nima ina wannan mamakin, itakanta Zahran da na d'auka kai takeso, amma da akace mata Ya Junaid za'a bata na d'auka zatai kuka sai naga kamas."
Dariya sukai su dukansu, Junaid yace " Wato kukuma 'yan sa ido kenan ko?"
Seemah ta kalli Ammar tao murmushi, ido ya kura mata yana mata wani irin kallo, Junaid ya rik'e hab'a zaiyi magana yaji Ammar yace " Farin cikina bai wuce in ganki kina cikin farin ciki ba."
D'agowa tai ta kalleshi, batare datace komai ba ganin yanda yake mata wani kallo yasa tai saurin d'auke idanta tare da kallan Junaid ta wayance da cewa " Ya Junaid ina Ya Zaid?"
Hakan yasa Ammar ya d'auke idansa, tare da kallan Junaid, tai sa'a yace " bazai wuce wajen gate ba."
Ta juya da sauri ba tare da tace komai ba, kallo kawai Amnar ya bita dashi.
Jalal kam har yakai waje zuciyarsa ba dad'i, yana fita gate ya samu gefen gidan ya zauna, idanunsa ne suke gano mai Ammar da Seemah, da sauri yasa hannayinsa biyu yad'an bubuga fuskarsa yana cewa " Wake up Jalal me ke damunka? Kamanta alkawarinka? Katuna abinda mahaifinka yamata ta dalilin cetanka fa?."
Wata nanauyiyar ajiyar zuciya yai tare da cewa " Gaskiya ne, nasani kuma Ammar ne yafi cancanta da ita."
Ya dad'e a zaune kafin ya mik'e ya tafi, sam ya mantada cikinsa wanda tun d'azu yake kara, gidan Sagir ya wuce.
Bayan sun gaisa Sagir ya kalleshi yace " Mutumin yaushe a gari haka?"
Yai murmushi baice mai komai ba, Sagir ya dafashi tare da cewa " duk ciwon soyayyar ne yasa ka rame haka?"
Murmushi Jalal yai yace " Sagir sorry zan d'an takurama kad'an."
Ya fahimci me yake nufi, ya d'an harareshi yace " Jalal me yasa kake min haka?"
Hannu biyu Jalal ya had'a irin na ban hakurin nan suka shiga d'aki, gado Jalal ya fad'a Sagir ya matso kusa dashi yace "daga ina kake haka?"
Jalal yai shiru, hakan yasa Sagir yace " Jalal ba dai......"
Katseshi yai da cewa " yau fa aka d'auramin aure."
What? Me kake nufi?
Jalal ya juya baice komai ba.
Sagir ya mik'e tare da sa hannunsa a kafad'ar Jalal irin na tausa ya fita.
Jalal ya hard'e hannayensa tare da zarfafa cikin tunani, abinda mahaifin Seemah ya fad'a yafi komai tada mai hankali, dama akwai uban da bazai so ganin 'yarsa ba? Shi ya d'auka inyaji zancen hankalinsa ne zai tashi ya kuma nemi ganin 'yar tasa cikin gaggawa bayan laififukan daya tafka.
Wata iska mai zafi ya furzar tunaninsa d'aya tayaya zai sa mutumin nan ya shiryu?
Sagir ne ya shigo, ya zauna kusa da Jalal yace " tunanin me kake?"
Jalal ya mike da sauri ya fuskanci Sagir yace " Sagir kasan Senate Abdullahi?"
Sagir ya kalleshi da mamaki yace " kai kuma ina kasanshi?"
Jalal yai shiru, Sagir yace " Amaryarsa kanwar Ummana ce."
Jalal ya d'ago yace " What?"
Sagir yad'an tab'e baki yace " hmmm ni sam mutumin nan ba wani burgeni yake ba ita kanta Aunty tun bayan auransu da wata 2 ta fara kawo kara."
Jalal yai tsaki yace " ai da alama, amma ita mai yakaita auransa? Ba'ai bincike bane?"
Kallan mamaki Sagir yama Jalal yace " lalai Jalal, mutum kamarsa wanda yakeda kud'i ga mulki shine kake tunanin za'ai wani bincike? Ita kanta Auntyn ai kud'in ne ya rufe mata ido."
Jalal yai shiru, Sagir ya dafashi, yace " ka ga ka raba kanka da mutumin nan Jalal, a yanda Aunty take zancensa sam..."
Kai ya girgiza kawai, Jalal yai shiru ya shiga tunani, Tayaya zaiyi yasa mutum kamar Senate yaba 'yarsa hakuri kafin auranta?
Dafashi Sagir yai, Jalal ya kalleshi zai yi magana cikinsa yai wani kara, murmushi Sagir yai yace " Bari in kawo ma abinci." Ya fita yana dariya.
Jalal ya dad'e yana tunanin mafita kafin bacci ya d'aukeshi.
Washegari ya shirya ya koma Birnin/gwari.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣8⃣
Sagir na dawowa daga raka Jalal mai gadi ya mikamai wata takarda, kallan sa yai yace " nameye?"
Mai gadin yace "d'azu da zaku fita wanda kuke tare ya bani yace in kun dawo in baka."
Sagir ya amsa yana mamakin takardar miye acikin envelope?
Yana shiga d'aki ya fito da farar takarda, abinda idanunsa suka fara gani nai ya kad'ashi, letter of resignation an yi rubutun da manyan harufa ankuma ja layi, wasik'ar barin aiki?
Hannu yasa a aljihu ya kira Jalal, Jalal kam sun d'au hanya ya d'aga wayar, Sagir yace " Jalal me nake gani haka? Ban gane wasik'ar barin aiki ba?"
Jalal yai shiru, Sagir yace " Jalal menene hakan?"
Numfashi yad'an ja kad'an sannan yace " Please kamin submitting d'in takardar, bazan iya zuwa dakaina bane."
Cikin rashin fahimta Sagir yace " aiki ka samu? Ko me?"
" ba wani aiki akwai babban dalilin dabazai sani na cigaba da aiki a company d'in ba."
Sagir ransa ya b'aci yace "saboda soyayya zaka hallaka rayuwarka ko me? Jalal wai me yasa kek neman barin soyayya ta rufema ido?"
Jalal ya d'anyi murmushi inama ace soyayyarce kawai ba wannan babban al'amarin bane? Ya daure yace " Sagir kenan."
Haushi ya kama Sagir ya kashe wayar tare da jefata kan gado, shikam yana mamaki ace wai mutum yabari soyayya ta nemi hargitsamai rayuwa?
Zahra ce ke ta shiga d'akuna tana kaima mutane abincin safe, ta taho da flask d'in abincinsu Junaid tai d'akin, takalman dake bakim kofa ta kalla, takalmin Zaid ne kawai hakan yasa tai sallama tare da tsayawa a kofar d'akin, Junaid dake kwance ya amsa a kasalance, zuciya d'aya ta shiga tana cewa " kai dai ya Zaid kaji jiki ace kowa ya tashi amma kanannan akwance kamar ba namiji ba."
Junaid jin maganarta yasa ya fara murmushi tare da kara shiga bargo, ta matso cikin tsokana tafara jan bargon daya rufu dashi, Junaid ya zaro ido tare da kallan kayan jikinsa, vest ce sai gajeran wando, da sauri shima ya ja bargon nan suka fara jaye_jaye, tana ja tana cewa " Allah yau sai ka tashi kai ko kunya bakaji Yaya?"
Junaid ya kara jan bargo, hannu ta hard'e tare da sa kafarta a kan gado ta kamo bargon da karfinta, ai kam ta fizgo bargon, Kallan mamaki tama Junaid tare da bud'e baki cikin mamaki, Junaid ya fizgo bargon da karfi, itakuma gaba d'aya nauyinta nakan bargon, ai kuwa tabi bargon ta fad'a jikinsa, Ta d'ago ta kalleshi cikin mamaki murmushi ya mata na karfin hali dan shima kunya yaji, yace " Zahra kece?"
Mik'ewa tai da sauri tare da juyawa tai waje da gudu, Junaid ya bita da kallo fuskarsa na wani irin murmushi, Zahra d'aki ta fad'a da gudu tare da sama d'akin makulli ta matso kusa da Seemah dake zaune rik'e da agoggon Jalal, Zahra ta fado kusa da Seemah kamar mai shirin kuka tace " Seemah an kashe ni?"
Seemah ta kalleta tace " an kashe ki kamar ya?"
Zahra ta mik'e ta fad'a gado tai rufda ciki tare da rufe fuska tace " Seemah naga Ya Junaid da vest."
Tana fad'a tare da tura kanta jikin katifa, dariya Seemah ta kyalkyale dashi wanda rabon datai dariya haka harta manta, dariya sosai tai sai data tsagaita tace " Haba? Kuramai ido kikai?"
Zahra ta bubuga kanta tace " Eh mana?"tafad'a kamar mai kuka.
Seemah ta kara sa dariya tace " lalai Zahra wato ba kunya? Kika kuramai ido?"
Zahra ta mik'e zaune tace " wayyo wlh ba da sanina bane nifa bansan shi bane."
Seemah ta guntse dariyarta tace " kyama fad'i gaskiya da alama ma dama haka kika so, yanzu Zahra ko kunya? Hmmm"
Zahra ta mik'e da sauri ta matso gun Seemah ta rik'e hannayenta tace " Seemah yazanyi? Shima zaiga kamar banda kunya ko? Nashina da wani idon zan kalleshi?"
Seemah ta kara guntse dariya tace " gaskiya kam wannan kam fitsira ce."
Zahra kula datai Seemah cinnata takeyi yasa ta kalli Seemah tace " tsaya! Shi yayan naki waya ce yaki fad'amin shine? Ai ni banida laifi."
Seemah tai dariya tace " ahhhh gaskiya ba laifin yaya na bane a dai duba."
Haka tai ta tsokanar Zahra.
Jalal kam har ya isa zuciyarsa ta rasa bashi mafitar alkawarin daya d'auka, yana isa gida yaga mutane a cike, shiga yai duk da ransa ba so yake ba, nan suka shiga gaisawa da jama'a wasu 'yan uwan Zainab ne wasu nashi, yana gama gaisawa ya wuce d'akinsa ya kwanta, Abba ne ya shigo d'akin ya tsaya a bakin kofa yace " Jalal?"
Jalal bai juyaba yace " Naam"
Abba yai shiru cikin sanyin jiki yace " kaga Abdullahin?"
Jalal yace " eh amma...."
Sai kuma yai shiru, Abba ya kalleshi yace " Jalal mutumin nan ba mutunci gareshi ba ka karfi na dukiya da mulki dayake dashi bana tunanin kanada hanyar dazaka sashi abinda baiyi niyya ba."
Jalal yai shiru, tabbas yasan haka abin yake, Abba ya cigaba " Kai ba Lawyer ba, ba kuma D'an jarida ba mai zaka iyayi? Bayan ko shari'a yafi karfinta?"
Da sauri Jalal ya mik'e ya yace "d'an jarida? Lawyer?"
Kallansa nai nima cikin mamaki mai yake nufi?
*HUSSYLURV, BILLY, AENART, AMAL, HADIJA, ZEE BALA, UMMU NAFISA, RAMBI. DAFATAN KUNYI WEEKEND LAFIYA.*
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_Ina kara ba masoyan littafin nan hakuri na jina shiru da kukai kwana biyu, a min afuwa ina cikin taro ne.......Nagode kwarai da kulawarku da kuma kaunar da kukema littafin nan_
No. 5⃣9⃣
Abba ya kalleshi shi kanshi bai fahimci mai Jalal ke sakawa a ransa ba amma mamaki ne bayane a fuskarsa ganin Jalal na murmushi.
Daurewa yai yace " Jalal kazo ka fita gun abokanka anjima kad'an za'a kawo amarya."
Ya kalli Abba yace " yanzu Abba inza'a kawo Zainab gidan nan har sai na fita? A gidan nan take da fa, sannan ni gun wa zani kasan ba abokai garan ba."
Abba yace " Al'ada ce hakan yaza'ayi akawo Amarya kuma Ango na cikin gidan? Ai sai daga baya zakuzo siyan baki da abokanka."
"Siyan baki? Bakin wa kuma zan siya?" Yai maganar cikin mamaki.
Abba yai murmushi yace " Jalal ya akai bakasan komai na aure ba? Ai in aka kawota sai kunzo kun ba kawayenta kud'i sannan su tafi."
" Ah wannan ba siyan baki bane, neman kud'i dai kawai."
Abba yace " Haka dai akeyi d'an haka kazo ka fita sannan ga wannan." Ya mik'a mai bakar leda an d'an nad'eta, Jalal ya amsa yana kallan Abba.
Abba ya cigaba " 'Yan uwanka ne suka tara maka, sai ka ciri wani abun kaba 'yan siyan baki sannan a ciki ka siyo kaza da madara ko yogurt ko lemo, na fad'ama su Kafilu suzo su rakako anjima."
Jalal ya irga kud'i dubu 20 ne cif, ya kalli Abba yace " Yanzu Abba meyasa akasa su tara kud'i haka?"
Abba ya sake Murmushi yace " ba wanda ya sasu, dama haka akeyi, had'awa akeyi kowa ya kawo nawa yai niyyar bayarwa."
Jalal yai shiru yana kallan kud'in, Abba ya juya tare da cewa, kai wanka kasa sabon kayanka kazo ka fita.
Jalal yace to, sannan yace " Amma Abba baka tambayeni......."
Abba ya juyo ya kalleshi yace " nasani Jalal, amma daga baya mayi maganar."
Yana fad'a yai waje.
Kallo yabishi dashi sannan ya zauna a bakin gado, shifa sam baiyadda wai shine akama wani aure ba, shi da yad'auka in mutum aka mai aure wani farin ciki ne ke mamayeshi, to shi ya yake jinsa ba wani farin ciki? Sai ma wani bakim ciki na mahaifin Seemah dake nukurkusar sa? Ga zafin rabuwa da abinda zuciya da gangar jiki ke bege."
Ya zaiyi?
Haka dai ya mik'e yai wanka ya zura shaddarsa sabowa da Umma ta d'inkamai ya fita, cikin gida ya kara shiga ya musu godiya sannan ya fita.
Waya ya d'auko ya kira Sagir, shikam Sagir haushin Jalal duk ya isheshi, da kyar ya d'aga wayar, Jalal yace " Sagir d'an Allah tambaya, a tsakanin Lawyer da d'an Jarida wanne yafi d'aukan lokaci wajen gama karatunshi?"
Haushi ya kara kama Sagir yace " Au bama zancen aikinka ka k'ira kamin ba?"
Jalal ya saki Murmushi yace " Sagir d'an Allah kabani amsa."
Sagir baice komai ba ya katse layin.
Jalal ya girgiza kai fuskarsa d'auke da murmushi, jiyai am dafashi ta baya, ya juya Kafilu(d'an gidan goggo) ne da abokansa, Jalal ya kara sakin fuska yace " Kafilu?"
Kafilu yasa hannu a hab'a dayake shi mutum ne mai barkwanci, yace " Haba tun dana karyo kan lungun nan nake ganin haske d'an nima hasken na d'inga bi, abin mamaki hasken ya d'ireni anan."
Jalal ya kalleshi yace " Au nine nake haskem kenan?"
Dariya Kafilu yasa yace "Sosai ma, abinka da sabun shiga, saurayi zaiyi sabon aure."
Ya fad'a yana kallan abokansa, Dariya dukansu suka kwashe mai dashi, har Jalal d'in.
Ya cigaba " ni gashi ina shirin kara ta uku amma kai sai yanzu zakai d'aya gaskiya dai anji kunya."
Kallan mamaki Jalal yamai yace " Kafilu? Ka rufa mana asiri ina zaka kai mata uku?"
Dariya suka sakeyi Kafilu yace " ah to kaidai ba d'an boko ba sai kayi ta zama ni ai sai na ciki hud'un nan rass."
Jalal ya girgiza kai yace " Lalai abin naka babba ne, kaje kana kwance a kwarama ruwan zafi."
Suka kara sa dariya, Kafilu yace " tab, ai sai dai suyi ta fad'a akaina ni kuma inzauna akan kujera ind'inga kad'a kafa."
Jalal ya kalleshi cikin mamaki yace " Allah ya shirya, wato kai fad'an ma dad'i yake maka."
"Sosai ma."
Sun dad'e suna hira suka d'anje yawo.
Seemah kam duk motsin datai sai ta tuna, Shikenan Jalal ya zama ba nata ba, yana can yau za'a kaimai matarsa, wani sabon kishi da takaici ne ke nukurkusarta, kwankwasa kofar dataji ne yasa ta mik'e tare da bud'e kofar, Ammar ne ya kalleta fuskarsa d'auke da murmushi ya bud'e mata hannayensa yace " Suprise! !!! "
Ta kalleshi tare da matsamai, Ammar ya shiga yana cewa " Kodai in koma? Kamar wannan kanwar batai farin cikin ganina ba."
Seemah ta shiga ciki batare data amsa ba, a kan kujera ya zauna tare da nuna mata kusa dashi, ta karaso ta zauna, ya kalleta ya d'an langwab'ar dakai yace " ko in tafi?"
Kai ta girgiza mai, alamar a'a yace " in bakyasan na tafi to lalai ki saki fuskarki."
Ya fad'a tareda had'e fuska, Seemah ta kalleshi cikin shagwab'a tace " Fuskata fa a sake take."
Ya juyo yai murmushi sannan ya mik'e ya dawo gabanta ya tsugunna, ta kalleshi tare da yin murmushi ganin yanda yake kallanta, tace " Yaya kallan fa?"
Ya kara kafeta da ido yana mata wani kallo yace " Seemah bansan ganinki cikin damuwa kema kinsan haka."
Ta d'auke idanunta da sauri tare da juyar dakau tace " Yaya?"
Ya mik'e tare da juyawa ya fara tafiya, jikin gado yaje ya tsaya, ba tare da ya juyo ba yace " na sani Seemah, soyayyar da kikemin ta 'yan uwantaka ce bawai ta saurayi da budurwa ba, a da na d'auka nima wannan soyayyar nake miki, amma bayan sanin ba jinin mu d'aya ba na gane cewa soyayyar danake miki kala biyu ce."
Ya juyo ya kalleta idanunsa sunyi jaa, yace " in har bazaki iya aurena ba wani abu, ni zan iya hakura koda kuwa sanki zai kasheni zan jure, abinda bazan iya jurewa ba shine inganki cikin bakin ciki."
Seemah hawaye suka gangaro mata, ta kalleshi cikin tausayi, sai dai ta kasa magana juyawa yai yafara takawa, da niyyar barin d'akin, mik'ewa Seemah tai da sauri ta zo ta rungumeshi ta baya (abinka da rainon da ba na kasar nan ba, bare sun taso tare basu d'auki hakan komai ba.)
Cak Ammar ya tsaya, tare da had'iyar wani abu, idanunsa na neman kawo ruwa, Seemah cikin kuka tace " Ba haka bane Yaya, ba haka bane."
Hannunta ya zare tare da juyowa saitinta, hannu yasa ya share mata ta tsugunna a kasanshi tasa kuka tace " Yaya ya ya zanyi? Ni kaina haushin kaina nakeji, banasan abinda nakeyi, tayama za'ayi zuciyata ta kasa tsanar wanda mahaifinsa shine sanadiyyar wulakantar mahaifiyata, kila ma shine sanadin rasa rayuwarta?"
Ta kalli Ammar idanunta na zubar da kwalla abin tausayi tace " Yaya inaji bana cikin hankali na, a da nad'auka ko ganinsa bazan nemi sakeyi ba, amma da kaina na fita gunsa, kuma na kasa ko tambayarsa bare inyi masa masifa, yaya anya mahaifiyata zata yafemin?"
Ammar ya share kwallarsa shima, ya tsugunna kusa da ita tare da rike hannayenta, ta cigaba da kuka sannan tace " Yaya ka taimakeni kasa na manta da Deen d'an Allah, in daina mafarkinsa da tunaninsa, banasan na........"
Hannu yasa ya rufe mata baki, ta kalleshi hawaye na cigaba da zubowa, har kan hannunsa, baice mata komai ba, sun dad'e a haka, Kafin a hankali Ammar ya zare hannunsa daga kan bakinta ya kalleta yace " Ya isa kukan haka, banasan ki zubarda hawaye koda kuwa akainane bama akan wani ba, hakan nasa zuciyata shiga wani hali."
Kallansa tai ta kasa magana, yace " bari naje masallaci."
Ta d'aga kai a hankali, ya mik'e ya fita, ta bishi da kallo, jikinta ya kara sanyi, taya zata ki jinin Dad, a yanda takejinta koda Dad wani can talakan gaske ya d'auko yace Seemah wannam nakeso ki aura, bataji zata bijire masa bare Ya Ammar? Mutumin datasan bazai tab'a barinta ta wulakanta ba bare yasata kuka, jinin Dad, sannan a 'ya'yan Dad d'in ma wanda tafi shakuwa dashi tafi kuma sansa? To amma meyasa take neman b'ata masa rai saboda Deen? Meyasa?
Wani sabon kuka ne ya kara zuwa mata........
An kai Amarya, mutane sun cika a gidan Jalal su kafilu a gaba suka sashi aka siyo kaza da lemon kwalli da hollandiya mai sanyi, Kafilu sai tsokanarsa yakeyi, sunje shiga gida Kafilu ya kalleshi yace " Jalal sai naga kamar farincikinka baikai zuciya ba."
Kallansa Jalal yai baice komai ba, Kafilu yai dariya yace " ko duk ka kosa ne kayi......."
Harara Jalal ya dokamai yace " kai wannan ya dama mai iyalai."
Kafilu ya kalleshi yace " Kai!!!!! Ai abin ne....."
Jalal ya kara makamai wata hararar yace " bamasan jin sirrinka uban 'yan surutu, Allah ya shiryeka."
Nima nace Ameen, d'an kuwa fad'ar sirrin aure babbar illa ce......Allah yasa mu kiyaye Ameen.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
⛹🏻♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_I Sincerely dedicated this page for you *ASY KHALEEL*._😍
No. 7⃣0⃣
Sun shiga cikin d'akin, nan Kafilu ya samu abinda yake so wato hira, shikam Jalal ko kallan Zainab dake lullub'e cikin mayafi baiyi ba, Sai can d'aya daga cikin abokin Kafilun ya tab'ashi yace " ya kamata mu yafi fa."
Nan suka ba kawayen Amarya dubu biyar kud'in siyan baki sannan akai addu'a suka fita.
Toh fa!!!! D'aki ya rage daga Zainab sai Jalal, zaman dukum sukai wato zaman kurma har na wajen minti talatin, kafin can Jalal ganin zamanshi anan bashi da amfani ya mik'e ya kalleta, yace " Zainab?"
"Naam"ta fad'a cikin sanyin murya.
Yace " bud'e fuskarki mana muyi magana."
A hankali ta zare mayafin idanunta a kasa, tasha kwalliya d'an kuwa tayi kyau, sai dai wanda akai dominsa baimasan tayi ba, kallanta yai yace " ungo wannan." Ya fad'a tare da mika mata leda, hannu tasa ta karb'a tana kallansa.
Yace " Abincine ki samu kici, inadai kinyi Sallah?"
A hankali ta furta " eh, amma kai yaya kaci abincin ne?"
Ya d'an juya kai yace " ni na koshi, kedai kici abinci sannan ki shiga d'aki ki kwanta d'an nasan kingaji."
D'agowa tai ta kalleshi, duk da dai itama tasan ba santa yake ba amma bata tab'a tunanin abinda zai ce mata kenan ba.
Kai kawai ta d'aga, yai cikin d'akinn, dama d'aki d'aya ne da toilet a cikin d'akin sai falo, toilet d'in ya shiga yai alwala yai sallah a d'akin.
Itakam dakyar ta iya cin cinya guda d'aya sai yoghurt d'in data d'an kurb'a tai shiru tana tunanin wannan abu, kawayenta jiya sun bata labarin yanda maza ke kula da mace ranar da aka kaita, yau gashi ita taga wani abu.
Jalal bayan yayi addu'oinsa ne ya fito falon tare da kallanta yace " kinci abincin?" Ta d'aga kai, yace " Good, kishiga ki kwanta."
Ta kalleshi tare da mik'ewa tai d'aki, har takai bakin kofa tad'an juyo, ganinshi tai ya kwanta akan doguwar kujera, tace " yaya kaifa?"
Ya kalleta kad'an tare da cewa ni inanan.
Kallan mamaki tamai sannan tace " yaya."
Jalal ya had'e rai yace " to so kike inshiga mu kwanta tare?"
Shiru tai tana kallansa, yace " ki wuce kije ki kwanta karki damu dani."
Shiga tai cikin d'akin ta zauna a bakin gado tai shiru, ta rasa ma me zatai, shikam Jalal waya ya d'auko yai tai binciken abinda yasa gaba wato sanin harkar karatun law dana mass com.
Yana cikin binciken ne yaga wata kungiya masu bada scholarship na PTDF sun bud'e a fara siyan form.
Nan fa ya sai katin yana fatan Allah yakaimu gobe ya tafi cafe yaje ya cike.
Haka rayuwa ta cigaba, 'yan taron biki sun watse, sai dai tsakanin Jalal da Zainab, intai abinci ta bashi ya ci sai kuma gaisuwa, kamar yanda ta saba kullum tana cikin gida kamar da, wannan ne ya rage mata kewa da kuma sanya abin aranta.
Hmm rana bata karya, yau tun safe ake ta shirye_shirye a gidan Abba kowa ya shiga hidima, kowa murna yake yi banda Seemah wacce kwai yake take yima kowa, tana tsaye a kitchen d'an Mami tasata kullum ta d'inga shiga kitchen tana ganin yanda Zahra da mai aikinsu ke girki, yau dai ita kad'ai ce a kitchen d'in tana dafama Dad indomie babban burinta Dad yaci abincin ta, Ta dage tana ta aiki sai kace mai dafa sakwara duk ta b'ata kitchen d'in, ji tai an rufe mata ido ta baya, tai murmurishi tace " Ya Ammar ka tashi?"
Sakinta yai tare da juyowa saitinta yace " Seemah ya akainkiga ganeni?"
Ta d'an harareshi kad'an tace " lalai ma Yaya, tambayar dazakamin kenen? Inada hanyoyin sanin kaine dayawa."
Ya kalleta cikin jin d'adin kalamanta, ta kalleshi tare da cemai "yaya yau Dad nakema girki."
Ammar ya hau saman kanta daga gefe ya zauna tare da cewa " lalai duk wannan d'in na dad ne kenan? Bama a tuno da ni?"
Ya d'an matso ta da fuskarta kusa dashi yace " ur husband to be."
Kasa tai dakai da sauri sannan ta d'ago ta d'an kankance ido tace " oh ni yaya yaushe ka zama haka wai?"
Murmushi yai sannan ya nunata da hannu yace " yazanyi tunda kanwata ta maida ni haka?"
Ta d'an juya kai tace " gobe dai zan tafi ai."
Yad'an bata rai yace "gaskiya ji nake kamar zan biki, bansan ya zanyu ba inkika tafi MEEMAH."
Da sauri ta d'ago ta kalleshi gabanta ya fad'i, idanunta yaga sun ciciko, cikin tsoro yace " SEEMAH? Menene?"
Ta share hawayenta tare da saurin maida kanta kan girkinta tace " please yaya karka kara cemin Meemah."
Ammar da mamaki yace " meyasa? Naga kinasan sunan?"
Ta kara goge kwallar vata amsa ba kawai ta cigaba da yanka albasa, aranta tace" sunan da Deen ke kirana dashi ne, na rabu dashi ina fatan zuciyata ta manta dashi sai dai banasan wannan sunan ya fito daga bakin kowa sai shi, tunda mun rabu dashi wannan sunan inasan ya zama tarihin daya rage tsakaninmu."
Ammar kallanta kawai yakeyi, har ta gama nan ya tayata gyara kitchen d'in.
A ranar da yamma aka sanya ma Ammar da Sewmah sannan Junaid da Zainab ranar aurensu nan da shekara 2 daidainan Seemah ta gama karatunta a hankali ta dawo sun karasa shiri, itama Zahra ta gama nata.
Washegari Seemah da Dad da matarsa suka calla England.
Jalal kam yayi sa'a ya samu wannan scholarship d'in murna kamar yai me, nan ya fad'ama Abba shima ya tayashi murna duk dadai a kasan ransa yasan manufar Jalal, nan fa yafara shirin tafiya dan kasar Germany ya cike karatun d'an Jarida, d'an yaga a can shekara 2 ne an gama.
Yagama komai shima sannan ya calla kasar Germany d'an yin nasa karatun.
0 comments:
Post a Comment