*Bayan sati daya*
Duniya tayiwa Gwamma zafi sosai abubuwa sunyi Mata yawa ta rasa yarda zatai ga Malam ya kafa mata Doka.Abinci sai Jummai tayi ake yafa Mata ga Malam ya daina kulata baya shiga Dakinta.
Yau ma data Ke kaikawo don neman mufita Abu yaci tura ga d'aci da ranta keyi, sabili da ganin Malam da Jummai a zaune suns Hira.
Malam na bata Labarin wata tafiya daya yi da dad'ewa da irin Gwagwar mayar da suka sha sai dariya take.
Da sauri ta d'au Buta ta shiga band'aki ta fito ta Koma d'aki gashi tana San fita Amma ba dama ta zauna Ke nan taji Malam nace wa:
"Ai Hansai so nake ace ta gama Makaranta. Amma Allah baiyi zata gama ba, tunda bikin saura wata Hudu."
Jummai tace "tabbas haka ne Malam" .
kiran Hansai yayi datake d'aki ta fito ita da Dije 'yar Gwamma .kallon Hansai yayi yace "aji nawa kike.?
Sunkwi dakai tayi tace "ajina Uku".
Hamdala yayi yace "ko a hakan kika tsaya ai kin samu .
Jummai tace "Malam ai se a saka Dije ma tunda kaga tayi Girma".
Malam yace "anya ba'a bari ta kai goma ba ,ko bakwai."
Da gudu Gwamma ta fito "wallahi kar wanda yakaimun yarinya makaranta".Malam ya d'aga Mata hannu "waya saka dake ehe?,meye naki aciki? nayi maki tsakani damu don haka Ke 'yar kallo ce, idan kinga bazaki iya ba,ga k'ofa nan abud'e take".
Jiki a sanyaye ta Koma.Haka dai rayuwar ta kasance a yanzu hankalin Jummai da Hansai ya kwanta, har k'iba sukayi.
Hansai kuwa soyayyar su ta dad'a ninkuwa itada muntari domin bala'in son Junan su, suke d'aya baya son rabuwa da d'aya ,arana sai muntari yazo gun Hansai so uku ga Shi komi yagani sayya sayo mata ,duk da shima ba sana 'a yake ba. Amma yana zuwa gona,tun Bayan gama Secondary d'in sa yana son cigaba .Amma tunda baiji Maigari yayi magana ba shiisa yayi shiru .
Hansai kuwa ta b'angaren iLimi sai nace Masha Allah ,duk k'auyen ayaran Mata,domin ta dage kullum Malam na k'arfafa Mata Gwiwa Musamman na Addini sai san barka.
Sam bazaka ce Hansai daga K'auye take ba,tun Bayan da malam ya dakatar da Gwamma sai ya ce Dije ta Koma gun Jummai haka Dije ta fara nutsuwa ,gashi Hansai Ke koya Mata karatu Sun saba sosai ,sab'anin da sai de ta tsaya k'ofar d'akin su tana hararar Hansai duk da yarinya ce mai Shekara Hudu.
Gwamma kam tana gani ba damar magana don Malam yace duk randa takarya doka inta bar Gidan to har abada bazata dawo ba. shiisa tai shiru saboda tana k'aunar zaman Gidan domin tabbs tasan Malam yana da kyautatawa da yawa.
Matan k'auyen na surfe sukam Malam bai bari suyi gashi har kud'in kashewa yake basu ,wad'an nan dalilan su suka sa Gwamma tayi lamfa.haka dai rayuwa tayi ta tafiya har su Hansai suka zana Jarabawar Junior Secondary school,ayanzu Hutu suke.
BAYAN WATA UKU Bikin hansai da Muntari yana ta k'aratowa ayanzu saura wata d'aya,nan gari ya d'auka saboda an Dad'e ba ai biki gidan maigari ba ga kuma Hansai da ake ganin ta dad'e.San nan gashi soyayyr su mai Asali wadda ta kaisu ga Shekara hud'u da rabi kenan shiisa kowa Ke zumud'in Bikin.
(Bari mu waiwayi Lawandi muga wane waina aka toya tun lokacin shigar sa gun 'yan Sanda).
Bayan da suka tafi dashi dama suna da case dashi sai direct suka kaishi cell saboda dama andad'e Ana neman sa, bisa dalilin satar da sukayi wa wani D'anfulani ,sai lefin nasa ya zama biyu gana satar yarinya gana kayan D'an fillo ,kawai sai aka sashi cell na wata uku ba beli .
To ayanzu wata ukun ya cika ya samu ya fito . Zuwan sa gun kaka lokacin tayi fishi dashi tace ya bar Mata gidan ya Koma gun Dangin Maman sa kaka sai kuka take hakan yasa ta d'akko wata Jikarta suke zama tare Shi kuma Lawandi ya had'a kayan sa ya cale Lagos neman kud'i ,acewar sa sai kaka ta neme Shi .
kaka tace "nikam nayi nan kayi can .Allah ya bada sa a can yayi tafiyar sa.
Al amuran Gwamma kuwa tayi ladaf din k'arya don har ciwon karya tayi domin ta jigata matuka. Malam na zaune tazo ta zauna sai matsalar k'walla take "Malam kayafeni na tuba bazan K'ara ba na jigata tamkar a Kurku ku nake ,ka taimake ni ba donni ba.
Malam ya kalleta "Ashe har kin horu" Gwamma tace "na horu Malam."
"To kije na janye. Amma idan sab'anin hakan ya kuma faruwa zanyi mai gabad'aya."
"Malam aina saduda".
Tashi yayi ya fita domin Shi kam yasan tuban muzuru Gwamma tayi.
*Bayan sati daya*
Kud'in da Malam Ke tarawa dama na bikin da wasu awakan sa daya sayar ya had'a jumulla dubu d'ari dashi za yiwa Hansai siyayyr kayan d'aki.
Wajen k'arfe 9 na dare ya shiga d'akin Jummai lokacin ta na zaune ,ya zauna gefen tabarmar ya kalleta.
"Jummai kinsan dai bikin Hansai ya matso yau,saura sati daya ko! to shine Allah da ikon sa ga kud'in da za'a sai Mata kaya, yanzu sai kuje keda iro har kano sayo Mata duk abinda ya samu."
Godia Jummai tayi itama ta d'auko nata ajiyar, nan duk suka had'a, Hansai na kwance tana bacci d'an tashin datai taji suna maganar, kuka takeyi A hankali tabbas babu wani sarki sai Allah mai had'a bayin sa duk inda yaso, gashin ya had'ata da Mutane masu kyautayi, tana daga kwancen ta rok'i Allah ya bata abinda zata rama d'umbin Alherin da sukai Mata.
Duk maganar Kud'in da sukai akunnen Gwamma nan hankalin ta ya tashi ta kasa tsugun komawa d'aki tayi ta rafka tagumi.
"Lalle nayi sake D'an zaki ya girma ,dole na san abinyi kud'in ma ba za asadani ba lalle dole na tashi tsaye" ,haka taita Sumbatu tana jira safiya tayi ta San abinyi.tooohhh muje zuwa dai.....
*By Queen meemi*
.
[4:00pm, 17/01/2017] 👑Meemi🔸: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣12❣
*JAN 2017*
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
*Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's*
_TUNATARWA_
_Ya 'yar uwa ko d'an uwa, ka/ki kiyaye harshen ka/ki, domin shine wakilin Zuciyar ka/ki.Kuma shine hallakarka/ki take jikin sa, karka/ki rik'a sakin sa,sai akan Alkhairi ko abinda Zai Amfaneka/ki_
**********
Haka kuwa akayi washe gari da sassafe kuwa Jummai da iro suka tafi can kano don siyayyr kayan d'akin.
Misalin k'arfe 11 Gwamma kuwa Bayan fitar Malam itama ta fita, dama ba tambayar sa take ba,bata zarce ko ina ba sai Gidan Maigari .
Da Sallama ta shiga, Ladidi tana zaune tana hira da bak'uwa tacee "Ah! lale da Gwamma" dariya Gwamma tayi tace "wallahi kuwa" nuna Mata waje tayi suka kuma gaisawa, haka sukai sallama da bak'uwar ta tafi, nan ta juyo gun Gwamma tace "yasu Dije da Jummai" ta amsa da Alhamdlh gyara zama tayi "Ladidi dama magana nazo da ita kan Hansai.
Ladidi tace "Eyyya ya shirye- shirye?" tab'e baki tayi batace komai ba, d'an juyowa tayi ta fuskanci Ladidi tace "wato ranar wanka ba a b'oyen cibi dole idan kaga za acuci Mutum ka sanar."
Ladidi tace "ban gane maganar da kike ba,"tace "ai In gaya miki Hansai de ba 'yar gidan mu nan bace."
"Asalin ta tsintar ta malam yayi, ba asan iyayen ta ba ,to ku kam kwaso had'a iri da ita.?
Ladidi tace "haba dai Gwamma idan kikaji wani na maganar nan ai seki kwab'eshi ,nasan Hansai ai 'yar k'anin Malam ce". Gwamma tace "wa din? to wallahi aga bana ya shigo da ita,kinsan badai zan miki k'arya ba."
Shiru Ladidi tayi tace "tabdi Amma wan nan magana da mamaki! zan sanar da Maigari nan Gwamma tace karde kice nice na fad'a don Allah"
Ladidi tace "haba dai sai kace wata yarinyaa."
"Yawwa bari na tafi."
Haka Gwamma ta tafi,tana tafiya tana maijin dad'i.
Da misalin k'arfe Hud'u Maigari ya shiga gida Bayan ya huta Ladidi ta zo mai da maganar da Gwamma rltazo da ita, Murmushi yayi "wan nan ai magan- ganun Mutane ne" ita wan nan Matar dama bata son Yarinyar ,don haka abar Maganar kar ma kowa yaji."
Haka Ladidi ta hak'ura tabar maganar Amma abin na ranta.
k'arfe shida su Jummai suka dawo ba laifi sun sayo kaya da yawa, k'aramar motar d'aukan kaya da gado aciki na katako duk k'auyen Hansai ce Malam ya fara yiwa, duk a wanda akaiwa aure ba masu irin sa duk da wan nan d'in ma bamai tsada bane can,lalle ta cika yar gata littafin( Miemei bee) Malam yayi farinciki ganin kayan .
Gwamma kuwa sai dariyar Mugunta take ganin ta had'a gurmi, haka dai sukai ta shirye- shiryen su.
Bayan sati d'aya Gwamma taji shiru ba alamun cewa an fasa auren, sai ma shiri data ga anayi a irgen da tayi yau saura Sati Uku bikin,hankalin ta ya tashi. Yau ma da takasan ce ranar Laraba Gwamma na zaune ta rafka ta gumi zumbur ta mik'e cike da wani tunani, ta yafa mayafi ta fice bata zame ko ina ba sai Gidan Delu,ta shiga Delu na zaune tana cin Zogale ta taso tace "lalle daga ganinki ta ciyoki."
Gwamma tace "sosai ma ai mufita nake nema."Delu tace "ai Labarin Bikin Hansai ya karad'e K'auyen nan ,ina zaune a nan nace kinyi sake".
Gwamma tace "yo ai lokaci bai k'ure ba."
Delu tace "tabbas yanzu kawaii kizo muje Gidan Boka na gaban K'auyen nan, da Zafi-Zafi akan bigi K'arfe.
Gwamma tace "yo ai matsalar ta Kud'i ce."
Delu tace "ai ba damuwa kije ki had'a su Kud'ad'en ki ,sai muje.
Gwamma tayi shewa "shiisa nake sonki Delu haka kawai yarinya ta zame min sai kace 'yar kishiya"! haka suka gama Gwamma ta tafi.
Fafutukar samo Kud'in Gwamma tashiga yi ,kurd'a- kurd'a, kullum tana yawon rancen Kud'i har wata Akuyarta, ta sayar nan ta had'a dubu Goma ,ta shiga kuma neman cuko dak'yar da Sid'in Goshi ta had'a Kud'in a sati d'aya ,hakan yayi dai- dai da Sauran Bikin Hansai sati Biyu.
Da sas safe Bayan Malam ya fita ta fita ,dama bata tambayar sa unguwa, ba bata zame ko ina ba sai gidan Delu tana zuwa suka tafi Gidan Boka.
Sunyi tafiyar Awa d'aya San nan suka hau Mota ta aje su adede Dajin da zai kaisu Gidan Bokan, Surk'uk'in Daji ne gun. Amma haka suka Shiga.
Sallama sukai boka ya daka tsawa yace "ba ai masa Sallama( saboda tsabagen tab'ewa irin ta Boka) haka suka shiga Gwamma tace "Boka dama akwai wata Yarinya ce da mijina ya tsinta tunda tazo na shiga Matsala ayanzu hakan D.an Maigari zata Aura ,ni kuma ban so ,dalilan daya sa nazo ne akan a rusa Auren karya yiwu ,San nan Kishiya ta sai abinda nace Mata, shima Mijina ayi min abinda kome nayi bazai ga laifi na ba."
Dariya ya kwarara "tabbas kina da sa a azzaluma mai son kanta, wan nan Aiki Sam bashida wahala,Amma fa kin cika muguwa ki tuba" dariya ya kurma yayi surkulle nan Hayak'i ya fuuuu ! ya d'auko wani Garin Magani yace "gashi ki yi abinci kitabbatar Kishiyarki da Mijinki sun ci .
San nan kuma Aiki akan auren can Zanyi shi .Godiya sukai ya kwarara ihu "ba aimun Godiya tab'ab'b'u kawai, ni ai na gama shiga ha'ula'I gashi kuma kun biyo Layi ,dariya ya saka .(meemi tace sakarkaru kawai Allah dai ya kiyashe mu tab'ewa ya shiryi masu hali irin na Gwamma).Aje Kud'in sukayi suka tafi... .kubiyoni
*By Queen meemi*
.
[3:58pm, 18/01/2017] 👑Meemi🔸: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣13❣
*JAN 2017*
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
_*Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's*_
.
_TUNATARWA_
_Ya 'yan uwa ,Mu yawaita neman gafara awajen Allah domin Allah gafururr Raheeem ne.Mu yawaita tasbihi domin samun kusanci ga Allah_
************
Tun komawar Gwamma gida sai ta tsiri faran-faran da Jummai Malam kuwa har wani canja Ladabi tayi mai da yake itace da girki bata sha wahalar bad'a Maganin ba.
D'aki ta koma tana Murmushi "sai ni Gwamma mai Mugunta ba dalili" can sai ta yatsine fuska "haka kawai ai sai inda mai na ya k'are."
Washegari kuwa Gidan Maigari Ladidi ta damu da Maganar can k'asan ranta taji bata k'aunar Auren (Da alama Bokan Gwamma yayi tsiya)sai kai-kawo take tasa aka kira Mata Muntari Lokacin yana can Gidan da zasu Zauna da Amaryar sa yana Gyarawa,haka nan yazo Ladidi ta tareshi.
"Muntari nikam wai kai bakasan Hansai ba 'yar Gidan nan bace?"
Gabansa ne ya fad'i yace "haba Gwaggo kidena damuwa da jita- jita."
"Kai Muntari ba wani Jita- Jita sai Gaskiya.
Dai -dai Lokacin Maigari ya shigo ya tarar da su a tsaye nan ya tambayi ba'asi Gwoggo tace "Malam nikam ayi bincike kan auren nan nifa Gaskiya ina juya maganar Gwamma ,shiru yayi baice komi ba can yayi gyaran murya yace "nima kawai ji nake bansan Auren gabana har fad'uwa yake. Amma yau zan samu shi Malam d'in akan Maganar.
*Bayan Awa Hud'u*
Malam ne tsaye Shida Maigari suna Magana, idan ka kalli fuskar Malam tsab zaka Zakulo razanar dake kai .Amma sayya dake yace "wato ranka ya Dad'e Maganar Gaskiya Hansai ba 'yata bace nan ya gaya mai Asalin Had'uwar su San nan yace "Kaga kuwa mai Asalice Rabuwa ce kawai Sanadin daya sa bata tare dasu iyayen nata, idan akai duba da yanda abun ya faru, ayanzu nine matsayin uban ta."
Maigari yace "Lalle Abin tausayi ce .Amma zan gayawa ita Mahaifiyar yaron aji ta bakinta.
"Toh! toh! ba damuwa" inji Malam.Jikin sa asanyaye ya shiga gida .
Shikam Maigari yajewa da Gwogg Maganar nan tayi tsalle ta dire kan D'anta bazai Auri wanda ba asan iyayenta ba, shima Maigari d'in baya so Amma kunyar Mutane yake ji, nan suka k'ark'are kawai Afasa Auren.Turk'ashi! wata Sabuwa kenan inji 'yan caca.
Washegari kamar k'arfe Goma na Safe Malam na shirin tafiya Gona akai sallama dashi ya fita, Yaron Maigari yagani saida K'irjin sa ya buga, nan Yaron ya gaidashi sa'an nan yace da Malam Maigari na neman sa, tare suka jera nan sukaje Maigari na Zaune kan tabarma Asoron Gidan sa, ya shiga suka gaisa .
Sai da yayi tsai San nan ya tashi ya Zauna yayi Gyaran Murya yace "wato Malam komai dama Muk'addari ne daga Allah, Matar Mutum Kabarin sa, kayi Hak'uri Auren nan abarshi, tunda uwar Yaron tace bataso, haka 'yan Uwa da Azo daga baya Ana kace nace! .Gwanda A Hak'ura.
Dumm!! Malam yaji akansa Idon sa yayi ja "yace bakomi dama Matar Mutun kabarin sa, Allah ya had'a kowa da rabon sa".
Maigari yace "Amin ,Amma aimin afuwa" Malam yace "Haba de wanda baisan k'addara ba shine zai damu" .
Haka ya fita yana tafiya a Hanya yana Magana har yaje tsakar gidan sa, Gwamma na gefe tana shara Jumma na d'aki kawai sai ya zauna bakin Bishiya ya dafe kai.
Gwamma ta taso "Aa Malam ya na gan ka haka?" Shikan Malam yace "An fasa Auren nan, Maigari yace ba zasu Aura wadda bata da Asali ba".
D'ora Hannu tayi a ka kamar zata kurma ihu Malam yace "Aa meye haka? sai kace wanda akai Mutuwa". Gwamma data juya ta yi dariya ganin hak'an ta ya cimma ruwa tace "Allah sarki Hansai .
Nan Jummai ta fito tana Malam Lafiya haka?"
Gaya yayi take ta hau kuka, "shike nan na shiga uku yanzu abinda Zasuyi mana kenan! yau saura kwana takwas wayyo Allah" .
Hansai dake shigowa Gidan da leda A Hannu ta aje da sauri ta tari Jummai tace "Inna Mayya faru?".
Jummai tace "an fasa Aurenki da Muntari". Hansai taji kanta na yuuu saboda Mamaki. Luuu tayi k'as Asume.
Da sauri sukayi kanta Gwamma kam D'aki ta Shige tana rawa, yay yafawa Hansai ruwa sukayi take ta Farfad'o da kuka, nan Jummai ta shige da ita D'akin ta, ta kwanta tana Mata nasiha ita kam Hansai son Muntari ne taji ya nunku kuka ta fasa.
Can kwa Gidan Maigari Muntari shima Kukan yake saboda tsananin son da yakewa Hansai da shak'uwar da ke tsakanin su, Shekara biyar kenan daya k'wallafa ransa akan ta ,haka sukai ta lallashi shikam yace haka yake sonta koda bata da kowa d'aki ya shige ya kulle ,suka bishi suna bugawa Amma yak'i ya bud'e.
Haka dai wad'an nan rayukan masu tsananin son juna ,suka rayu a kwana biyun nan cikin k'unar Rai ga gari ya d'auka ai Hansai bata da iyaye an fasa Auren ta, ko ina Maganar abuga k'auye.
"Jummai inaga zanyi huce Haushi kawai domin duk Lokacin Dana sa Auren baza a fasa ba, sai a d'aura da Mudi".
Fit Gwamma ta fito "Aikuwa badai a Gidan nan ba, wai abada Auren D'ana da wan nan abar, to sai de ko Bayan Raina".
Malam yace "to sai de Muga ni dake Waye yafi iko da shi."
Buga k'afa tayi "Ai wallahi sai de wani Amma ba Mudi ba,don kaga Yarinya ank'i Aurar ta, shine zaka Lak'abawa Mudi, haka kawai yo dama Mutum mai Hankali ina zai yadda D'ansa, ya Auri Hansai ba asali,gashi d'ai-d'ai shekarar ta goma sha biyar ace ba Aure"
Malam yace "ya ishe ki haka Gwamma! domin zan huce akanki wallahi,kisani Hansai babu K'ashin tsiya agareta kawai haka Allah ya shirya,kuma in banda ke da bak'in cikin ki,Abinni Akwai Mata 'yan talatin 30 basi Auren fari ba Amma dan anan Anayi Masu aure da wuri shine zaki takurawa yarinya ,to wallahi gwamma ahir d'inki Aure ne sai anyi da Mudi ki fad'i ki Mutu shashashar banza" Afusace ya fita.
Gwamma tace wallahi ba zan yardaba" ta kalli Jummai tace "Almunafum-fum kawai " ta juya ta shige band'aki
Ita kanta Jummai bata son had'in domin tasan Mudi basu dace da kamilalliyar yarinyar irin Hansai ba, cutar ta kawai zaiyi .
Duk wan nan budirin da ake Hansai na d'aki tana sharar Hawaye domin son datakewa Muntari jitake kamar yana k'aruwa gashi taji Ana zancen had'ata da Mudi.
Malam da kan sa ya shiga dakin Jummai Bayan da ya sake shiga gidan,ya zauna kusa da Hansai yace "kiyi hak'uri 'yata komi Muk'addarii ne daga Allah ,dama Allah haka ya shirya ,kiyi hak'uri kinji sai de bansa ni ba idan na miki katsalan dan Arayuwa wadda nake ganin shine kad'ai zai sa na Huce haushi na had'aki da Muntari, duk da nasan bakya son sa."
Dumm!! taji k'irjinta ya buga ta d'ago tace "tabbas Baba basai nayi tunani ba, ni ai ikon ka ce kayi duk abinda ya dace dani ka cancanci hakan Insha Allahu zanyi Biyayya agareka".
Dad'i ne ya kashe shi ,yace "Allah yayi miki Albarka Hansai, ya Baku zama lafiya, tashi yayi ya fita Ita kam Hansai ji take Numfashin ta na gudu tana kamo Shi.......
Auren nan zai yiwu kuwa??
ya Rayuwar Hansai zata cigaba da kasancewa?
Anya Hansai da muntari zasu Hakura da juna kuwa?.
Gwamma fa !!kudai cigaba da bin Queen meemi da sannu za muje inda muke San kaiwa.
*By Queen meemi* .
[1:04pm, 19/01/2017] 👑Meemi🔸: .
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣14❣

_Ban kanta daku ba *Nana* *fiddy, Husy, Maryam* *Ahmad,Neesah,Maman Ramlat ,Maman Rahma,Feedoh 'yar ficika*_
***********
Haka Nunfashinta yayi ta neman kufcewa ta Kwanta Ahankali ta Sami nutsuwa har bacci ya kwace mata. A b'angaren Muntari kuwa tunda ya rufe d'akin ya Kwanta kamar Matacce sai tunanin Rayuwar su da Hansai yake Zumbur ya mik'e lokacin karfe 9 na safe ya fita .
Gwoggo na ganin sa tace Muntari ,bai waiwayo ba sai ma K'ara Sauri da yayi bai zame ko ina ba sai bayan Dutsen da suka Saba had'uwa da Hansai nan ya k'urawa wani gun da Hansai ke zaama.
"Yace tabbas bazan iya rayuwa babu ke ba Hansai" kamar wani k'aramin yaro yana Magana "ya za'aimin haka! maisa sai dana sa rai dake, za a hanani ke, wallahi ina sonki" haka yayi ta Magana kamar zautacce.
Mudi kuwa wajen 1O ya shiga Gidan da sauri Gwamma ta tareshi "Zonan d'an Gwamma" nan ya bita d'aki suka zauna tace "abinda zan gaya maka ka saurareni, kasan kuwa Malam yace zai had'aka Aure da Hansai"?.
A mik'e ya tashi "kamar ni ace zan Auri Hansai bazata sab'uba." Gwamma tace "yawwa haka nake sanka ,ina zaka iya da ita ,yarinya da ba asan Usuli ba, ko da Malam ya maka Maganar kace baka son ta."
Ganin wuce war Hansai Mudi ya bita da kallo shikam yasan Hansai nada kyau ga jikinta na birgeshi, wani tunani ya canja ya juyo "to Mama ki bari kawai na Auretan mana"! ai ba damuwa.
Gwamma ta d'aga kai "Lalle kacika shashasha "to wallahi sai nayi maka baki akan hakan, kai me zakai da Yarinyar da ta gama tambad'a" .
Mudi yace "to Mama ba damuwa nima dama ba wani sonta nake ba kawai don Naga baba yace dole ne."
Tashi yayi ya fita suka had'u da Hansai Asoro yace "ke zo nan!"
Zuwa tayi ya Nuna ta da Yatsa "kifa gane ni ba sa anki bane nai miki zarra, me zan dake Gwanda ma kicewa Baba bakya Sona ,don in ba haka ba wallahi zaki gane kurenki."
Hansai tace "idan ba biyayya ba nima me zan dakai, wallahi darajar Baba kaci zan Aureka ne kuma wallahi bazan tab'a cewa bana son Auren ba."
Kai Mata hauri yayi tayi baya tana kuka,dama da Hijab d'inta ,kawai se ta zarce Bayan dutsen su tana zuwa ta zauna da abin busa d'inta, tanayi idon ta na b'ulb'ulo da hawaye ,domin ta tuno Muntarin ta, kamar Amafarki yaji sauti .
Firgigit ya mik'e daga baccin daya kwashe shi,tsai ya ganota durowa yayi daga kan Bishiyar ya je kusa da ita ya tsaya, yace "Hansai an rabamu ko?
Da sauri ta juyo suka had'a Ido tace "Muntari yanzu shikenan Mafarkin mu ya zama ba Gaskiya ba?". Muntari yace "nikam bazan iya babu ke ba".
Hansai itama tace "nima haka Muntari .Amma ba yanda muka iya". Kuka ne ya kubce Mata da gudu tayi baya ya bita, suka tsaya yace "har abada Hanasi kece Masoyiyata, ina Sonki Sona Gaskiya dama zasu Amince da Auren namu".
Tace "Muntari mu fawwalawa Allah shine zai iyar mana" haka sukai ta hira. Suka rabu cike da k'unar Rai.
******** Bayan kwana 2 anyi rigingimu a Gidan inda Gwamma ta kek'ashe baba ma ya kafe .
Yauma da take tsaye tana tunani "yo wai ni ko Maganin da boka ya ban baya Aiki ne? Naga Malam baya yarda da Magana ta" nan Taje ta duba kwanan ajiyarta,Mamaki ne ya cika ta Ganin Maganin da Bokan ya bata ,tace "kodai bashi na zuba ba!". "Lalle dole mana Malam yana min musu" da sauri ta d'auka Mayafinta,ta fita Gidan Delu, zuwanta ta Sanar da ita, Shine Delu tace "yanzu Shikenan kin b'ata Aikin ki da kanki".
Gwamma tace "to ni yazanyi ,yanzu?" Delu tace "ki kawo wani Kud'in na koma ya had'a wani Gwamma tace nikam wallahi ban da kud'i sai dai ki ran ta Min".
Tace "ba Matsala zan baki" nan suka K'ark'are zata je anjima haka ta tafi tana Surutai A hanya.
Wajen k'arfe 8 na dare sai ga Delu har taje gun bokan. Gwamma suka kule ad'aki tace "gashi Boka yace ki tabbatar ayau da daddare kin amfani dashi Hayak'i Zakiyi kamar turare, inde suka shak'a kin samu kansu."
Da rawar Jiki Gwamma ta boye a zanin ta,sukai Sallama da Delu ta tafi. Bayan Dan Lokaci ta turara Hayakin duk suka shak'a .
Washegari kuwa Malam ya tsare Mudi yace "kaga yau saura kwana 2 D'aurin Aurenka." Mudi ya kada baki yace "Baba ni bana son Auren nan".
Gwamma dake d'aki tace "yawwa".
Baba ya sunkwi da kai "yanzu kai bakaji kunyar gayan Maganar nan ba na ko?! ai shike nan dama ai babarka tace bata so kuma nasan ita ta kitsa ma. Amma komi Mutun yayi Shi za ayi mai.
Mudi kam wata jakar bagkoy ya d'auko, ya tsaya "ni na tafi Lagos neman kud'i baba dama yau na tsara tafiyar".
Gwamma ta fito "Yawwa mudi yau ka biyani". Baba yace "ni kam ina Umartar ka A matsayina na Mahaifinka kar kaje duk da nasan ba ka Maidani komai ba." Gwamma tace "wallahi Sayyaje". Mudi ya d'uri jaka yace acan zan hadu da Lawandi ya fice.
Gwamma tayi shewa "Ahayye yaraye nanaye"
Kuka hansai keyi saboda tausayin Baba, tace "Baba kayi hak'ur. Baba yace "bakomi Hansai ina Alfahri dake Allah ya baki miji na gari" ya tashi ya fita.
Haka Malam duk ya sanar an fasa auren nan nan gari ya hau tsogwami anata Gulmace- Gulamace ko fita Hansai tayi sai a fara ga Hansai mai bak'in Jini "da kuka take dawo wa, sai da Malam yaje yayiwa tufkar hanci ,San nan aka sakar Mata Mara.
K'anin Maigari ne dake zaune a kano yazo mai suna Alhaji Salisu, Shi ya tashi a hannun k'anin Babar su Maigari to ita abirni take Aure shiisa ta d'auke Shi ya tashi yayi Boko ,yanzu hakan yana aiki A NNPC Manager ne, yana da 'ya'ya da Mata Biyu.
Zuwansa Gidan ya tarar Ana tak'addama akan Muntari kan ya kafe bazai Auri wata Lantana da Gwoggo ta kawo ya Aura yace tunda anraba Shi da Hansai ba 'yar da zai Aura, to ganin hakan Alhaji Salis yace zai tafi dashi can Birni ya cigaba da karatu ,Jin an ambaci karatu yasa ya Amince zai bishi. bankwana .. .
*BY QUEEN MEEMI* .
[12:55pm, 21/01/2017] 👑Meemi🔸: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣15❣
*JAN 2017*
*Queenmeemi.WordPress.com*
*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's_*
_TUNATARWA_
_'yan uwa muna hak'uri da rayuwa aduk yanda tazo mana,hak'uri maganin zaman duniya ne ,komai ya sameka mujarrabi ne daga Allah_
******
*Misalin k'arfe 9 na safe*
Shirin sa yayi tsaf ya had'a Jakarsa tunani yayi dole yayi bankwana da Hansai, hakan ya tashi ya tafi gidan su, ikon Allah adai-dai Lokacin Hansai ta fito, turus tayi suka K'urawa Juna Ido nan yace "zo muje bayan Dutse."
Haka kuwa akai ta bishi a baya har suka je ,nan ya zauna yace "Hansai birni zan tafi" dafe kirji! tayi ta Mik'e "na shiga uku." Muntari yace "gwanda na tafi Idan na zauna ina ganinki Zuciyata zata iya bugawa."
Saboda nasan an raba mu soyayyarki tana nan a Araina kece ta Farko Dana keso."
Hansai tace Rabuwa da kai Shine Sanadin cin Fuskar da na ke fuskanta daga gun Mutane da Ammana Aure da hankalina kwance,ba wanda zai min."
Kuka ta kuma fashewa "Wallahi bazan so kowa ba sai kai" Shima da k'walla ya fito mai yana jin Zuciyarsa kamar zata fashe. "Hansai da inada dama da sai na gudu muyi Aure. Amma ba dama San nan nama fasa tafiya Birnin ma, Zan Zauna na Jajirce har su yar da subani ke ko."
Hansai ta mik'e tsaye Muntari karkayi hakan ka tafi kawai. "Allah ya k'addara Saduwarmu."
Kollonta Yayi da Siraran Hawaye suka Zubo yace "Idan da rai da rabo.Hansai inde da rabo a tsakanin mu gaba zami Aure."
Murmushi tayi "Allah yasa"
Nan suka tafi a tare sun zo kwanar su yaga Maigar da Alhaji Salisu an saka Jakar sa a Mota kuka ne ya Kubcewa Hansai.
Maigari ya kwad'o Mai kira tafiya yayi yana waiwayon Hansai .Maigari yace Au gurin "Yarinyar can kaje? Iyayen naci ai gwanda ka tafi Birnin kowama ya wuta Soyayya ba Alkunya." Dariya Alhji salisu yayi yace "Zamani ne ai, Amma mai yasa Baku basi Auren ba.?
Maigari yace "Yarinyar ce ba usuli .
Dai-dai Lokacin Muntari ya K'araso Maigari yace "tafiya zakuyi." Idon sa yayi ja yace "baba na fasa" Maigari yace "saboda kaga 'yar Gwal ko? to dole ka tafi" sharshar hawaye ke sauka ya tashi ya Shiga gida don sallama da Gwoggo. Wata Takarda ya d'auko da wata Leda , bayan sun sallama da Gwoggon. D'ahiru kanin sa ya bawa ya kaima Hansai.
Tana nan tsaye inda ya barta can ta tusa Hijab Baki tana Kuka saida ya tsaya ya k'ura Mata Ido ya share Hawaye ya shige Motar ,Maigari yace "Allah ya kiyaye ya bada sa' a ".
Ganin an tada Motar Hansai ta durk'ushe agun tana gurshek'en kuka. Tamkar ance Baba ya Mutu Muntari, yana ganota ji yake kamar yayi tsalle ya kamota, D'ahiru zuwa yayi ya mik'a Mata "gashi inji yaya" da sauri ta karb'a sai da taga tafiyar su San nan ta tashi kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki ta shiga gida.
Gwamma na d'umamen tuwo tace "ke zo nan.? ko kallonta batai ba ta Shige d'akin Jummai. Zazzabi Mai zafi ya rufeta. Allah sarki Soyayya.
Saida Hansai tayi kwana 2 tana ciwon love Hankulan su Malam atashe. Allah da ikon sa ta samu sauk'i .
Hakanan Gwamma ta bud'e shafin Cusgunawa Jummai da Hansai. tunda yanzu ta Shanye Malam baya iya katab'us a gidan, koya ga Abu baiyi ba ,da yayi Magana zata hayayyak'o mai.
Hansai kuma ad'an Lokacin nan ta gane shayi ruwa ne don azabtuwa da take domin Gwamma ta bud'e Mata huta. Yauma data tasheta tana bacci "k!e ke! tashi kizo ki min talllan zogale."
Mutsitstsike I'do tayi. Gwamma tace banza Gansai ni tashi ki tafi."
Hansai tace "talla kuma! ni aiban iya ba."
Gwamma ta kai Mata duka yaran gari dake yi finsu kikai?
Tashi Jummai tayi ta Shiga d'akin "Haba Yaya wane talla kuma? ai kinsan ba'ai agidan nan."
Gwamma tace "to kan Hansaai za a fara, haka ta taso ta agaba wata Jibgegiyar Langa ce ta d'ora mata. Malam ne ya fito Jummai tace "Saboda Allah Malam ace kamar Hansai za a aiketa Talla?.
Malam yace "haba dai ai baidace ayi ba Gwamma tace "wallahi bazan asara ba dole taje" Malam yace "to shike nan. Hansai Allah ya kiyaye kiyi hakuri ya fita Jummai na Mamakin canjawar Malam kwanakin nan Sam kamar tsoron Gwamma yake baya tanka mata.
Haka dai rayuwa tayi ta tafiya yau Fari gobe Baki Acikin hakan ba irin taskun da Hansai bata shiga ba, saboda Malam yanzu bai fiya Magana ba ,hakuri ne yazamo tushen Rayuwar Hansai.
BAYAN SHEKARA DAYA
kudakace ni fans ga wan nan ba yawa saboda Banda caji.
*By Queen Meemi*
[12:31pm, 22/01/2017] 👑Meemi🔸: .
. .
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣16❣
*JAN 2017*
*®NWA*
_*Queenmeemi.WordPress.com_*

_Cikakkiyar Nutsuwar Ruhi ta tabbata ga Mutuncin da Tunanin Laifukan sa ya hanashi hangen laifin wani ,'yan uwa mu daina aibata 'yan uwan mu, mu guji yi da wani da aibata Shi, batare da hak'k'in sa ba._
*Abuja*
Sumy ce tsaye tana jijjiga "ke kandala" ta k'wala kiranta a karo na 2 Jikinta na rawa ta tawo "gani Anty Sumy" tsaki taja "wato na baki wanki baki ba, ina kika tsaya?"
"Mopin nayiwa Antyn mubrk" Sumy tace "awajenta kike ko gun Umma?"
"Aa gun umma"
"To kar na k'ara ganinki acan, gashin can kije ki wanken Under Wears d'ina a Washing Machine" Jiki da b'ari ta tafi ita kam Sumy side d'in Anty Rabi taje, tana zaune tana karanta Novel ta tsaya "Anty sako daga Umma tace adaina arar Mata 'yar Aiki, course ba ke kika d'auka ba, Anty Rabi ta had'e rai to mara kunya naji".
Sumy ta fita tana k'unk'uni "inbanda Shima Dady da aure- aure Anty Rabi ai sa'ar Ruby ce" mtwss taja tsaki tayi side nasu.
Anty rabi kuwa inda sabo ta saba nan ta k'uduri Aniyar Dady na dawowa zata sanar mai itama zata d'au 'yar Aikin.
Haka kuwa akai A round 6 :pm tajiyo dirin motar Dady data guards din sa ,Zuwa tayi ta fesa wanka da kwalliya San nan ta tafi.
Mama da Umma ta gani kowacce a Hakim ce agefen sa Murumushi ya sakar mata "mum's Boys y gida" zama tayi tace "fine Dadn Boys".
Mama tace Alhaji kenan idan an girma ai a sani tashi Sukayi suka fita, dayake girkin Rabia ne Hug ya bata, nan ta fara hidima da shi bayan ya kimtsa tace "Dady dama inason nai samu 'yar Aiki Saboda Shiru Side D'ina kuma gashi kowacce nasa sai a ce ba aso ka kira.
"Mum's boys ba damuwa ki nema" Dad'i ne ya kashe ta tace tana zuwa.
After Some Minutes Rabia tayi dialing layin Maman ta ,bugu d'aya aka d'auka nan tace "Mama dama ina son Mai Aiki ne" daga can Mama tace "ba damuwa zan baki Nomber din Lami ki kirata, bari na turo miki" cike da jun dad'i ta kashe kirr sai ga Msg ya shigo.
Nan ta buga Layin din Lami daga can ta d'auka suka gaisa tace "Rabia ce 'yar Maman kano" Lami ta washe baki "ranki ya Dad'e" nan suka gaisa tace tana son mai Aiki. Amma me D'an girma ba k'arama can ba." Lami tace babu damuwa Insha Allahu za asamu nan suka kashe.
***********
Bayan kwana 2 lami ta tafi gidan k'awarta shiga da sallama ta amsa "Aa Rai kanga Rai" nan suka b'arke da hira Lami tace to nikam Ana neman mai Aiki kin San ni k'anana nake kaiwa 'yan 11 zuwa 12 to tace 'yar me girma nake so" Delu tace tooo Zan Bincika miki ba damuwa."
Bayan tafiyar Lami Delu tayi tunanin kawai taje Gidan Gwamma.
Bayan kwana d'aya da Maganar. Delu taje Gidan Gwamma .nan hira ta b'arke na yaushe Gari zance har ya kai kan Hansai nan Delu tace :
"Hmm haba da Sake ta yaya za'ace ki Zauna da katuwar Budurwa bakya Morarta.
Kibani ita Mutafi Abuja ta nemar miki kud'i ko Samira kya sai mata, sai kace ba Inna Gwamma ba mai Mugunta ba Dalili" .Ta bata hannu suka tafa tareda shewa
"Waima ina Hansai en take ne"? Delu ta tambaya.
"Na aiketa rafi d'ebo tafasa cewar Gwamma
Dede lokacin Hansai tashigo ta tsaya tsaye
"Gashi Mama".
Gwamma ta kalleta "ke Hansai baki ga Delu bane? kin tsaya gansai ba gaisauwa. Mai suffar Munafukai waima waya baki izinin dad'ewa?
Jummai ta fito daga d'aki "ni nace tabiya ta sayo kuka"
Gwamma tace na gaji da Gulmarki Jummla tam".Ke kuma Hansai Algunguma Nagaji da Zamanki haka tafiya Dole ce ki nemar mun kud'in hidimar Bikin Dije inya tashi ehe.
Saura naji kingayawa Malam nida kene tayi k'wafa Shige ki ban Guri."
ta shige sum -sum tai Daki Delu k'awar Gwamma tace
"Kai Mutuniiyata ,wan nan baza Umarni haka?"
tafawa sukai "ke to ni ta wasa ce ai barni da Munafukai sun isheni nafisu na fiso dagani sai 'ya 'ya na....
Tana shiga D'aki tasaki kuka tana Surutai tana cewa narasa mena tsarewa Inna Gwamma wannan tsana haka tayimin yayi yawa dame zanji ya Allah ka kawomin D'auki takwanta akan karauni tabarmar dake D'aki Dakin kamar kurkuku babu daban kasa Saman sa sai A zara ga cinnaka ba k'warin dababu aciki ga Shirgi,duk wan nan Gwamma ce tayi bayan ta zama mai fada aji agidan tasa Hansai ta koma d'akin shirgin.
*****
Acan tsakar Gidan kuwa Bayan tafiyar Delu ,sun gama K'ark'are Maganar Gobe za a kai Hansai Aiki
Taa baje A K'ark'ashin Bishiya ana ta yiwa Jummala Habaici inda Sabo Jummala tasaba jin wannan dan haka tak'i kulata taci gaba Aikinta na had'a Danbu A Zuciyar tana cewa Allah ya shiryata Mata kamar Shed'an bata da Magana sai
ta sharri bayan ta gama taraba ta bayar aka kaiwa Malam Gona ta.
Jummai ta faki ido ta shiga D'akin Hansai ta tarar da ita tana ta kuka abun tausayi Ta tasheta tace "haba Hansai meye abin kuka? sai kace saban abu kullum fa kinsan sai Anyi haka a Gidan nan tashi kici Abinci miyi Magana dak'yar ta tashi kan ta nasara Mata Kamarya tsage tafara ci Hannu baka Hunnu baka Hannu k'warya tas ta cinye Rabanta da Abinci tin na safe Gashi yanzu kusan La'asar bayan tagama tasha ruwa tadawo D'akin Jummala tace "Abinda zan gaya miki.
Kinga tunda wannan Matar tafara wannan Maganar ta kaiki aiki to sai tayi ki tsare mutuncinki. Yadda Matar nan takeso taga wani abin kunya yasameki ki kula
Da Sallah da Addua Allah ya tsare ki da ina da iko da na hana Amma ko Malam bai isaba bareni zan dinga yimiki Addu'a Allah yakare.
Suna cikin Magana sukaji Ihun Dije nacewa "Mama suna ta Zaginki ."
nan Gwamma tayin kukan kura ta tashi tace "barni da Shegu yau zasuga tijara agidan nan ta Dauko ittace taiyo,D'akin a fusace tana zuwa tad'aga ice zata Makamusu Malam yayi Sallama da Gudu ya zo ya kwace ice yace "haba Gwamma kullum kebaki da Aiki sai fad'a kishiyar da Yarinya."
Tace "dalla can "Malam matsa kabani guri sahurami kuma wallhi sai na suburbud'i Hansai a Gidan nan ko tai bacci Zatasan sunhad'u suna zagina."
Jummai tace "wallhi ba Zaginta Mukeba".
Allah sarki Hansai tini tarude sai Rawar Jiki take saboda tasan Gwamma da Mugunta Dije
sai Gwalo take mata .
Malam yace "baki isa kidake taba ba wallhi babbar
banza Mara Girma saina Jiki."
Gwamma tana kad'a jiki Malam yace jummai kama Hansai kuje d'akinki".
Gwamma tace Malam "Gobe Hansai zan kaita Aiki har min Magana da Lami za akaita Abuja."
Cak! Malam ya tsaya baice komai ba Yace "Naga yanda za ai taje Allah ya kaimu goben."
*By Queen meemi*
.
[7:08am, 23/01/2017] 👑Meemi🔸: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣17❣
*JAN 2017*
*NWA*
*Queenmeemi.wordpress.com*
*_This page Dedicated to Anty Maijidda Musa Tnz A a lot_*
_TUNATARWA_
_yawai ta istigfari Awurun Allah ,yana saukaka Samun biyan bukata_
******
Washegari kuwa da Asubayin fari Gwamma ta fito da Hansai ko gama wartsakewa batai ba ta tulo Mata wankin ta tace tai maata na k'arshe kan Rana ta gama fitowa, ga sanyi hakan tayi sai 7 ta gama.
K'arfe Goma Hansai ta gama Shiri sai kuka take Malam ya fito "Gwamma nadai gaya Miki Yarinyar nan baza taje ba, wallahi in taje ranki sai ya b'aci."
Gwamma tace sai de ya b'acin ,haka kawai Ga hanyar samu sai na zauna tunda ita ba Aure dole ta nemar mun kud'I. Don baka ga Laran Gidan Toka ba sai busha sha Suke da Kudin Aikin nata."
Malam yace "to ki kai Dije ,Amma ba Hansai ba tunda ba ' yarki bace, Hansai Jeki maida kayan nan." Cike da D'oki da Jin Dad'i ta koma D'akin ,Shi kuma ya Fita Gona."
Bai dad'e da tafiya bada ,sai ga Delu ta Shiga gidan. Da Zumud'i Gwamma ta tare ta,nan taje ta fito da Hansai "fito Algunguma komai Malam zaiyi saide yayi sai kinje."
Jikin Jummai a sanyaye ta kalli Hansai tacea "Hansai ki Rik'e Allah ki kiyaye Mutuncin ki ki Zauna Lafiya dakowa, Allah ya karemin ke" Rungume Jummai tayi "Inna banason tafiya"
"Fito ko na zo na makeki da duka" cewar Gwamma Jummai tace "Amma dai Malam ai ya hana. Gwamma tace "tafi can wayake take" nan ta kalli Hansai "ke kuma d'auki kayan nan ki D'ora akai, wallahi idan kiyaje bakya Aiki sosai sai kinci na Jaki.
Delu tace sai kizo mu tafi" kuka Hansai take tamakar taci babu da k'yar ta tafi, Jummai ma kuka suna fita Gwamma Tai shewa "wayyo Ina daga zaune kud'i suna zuwar min."
Delu kuwa suna tafiya sai hantarar Hansai take har sukaje Gidan Lami dama Jiran su ake yara ne su biyu Hansai ta uku .Amma duk ta fisu Girma Lami na ganin Hansai tace "Yawwa kinga wan nan zata dace da Alama zatai tsafta". D'ari biyar ta kawo ta bawa Delu "ga Ladanki" nan sukai Sallama har ta tafi ta dawo "Yawwa Lami kinga Hansai sai kin Jamata kunne domin bataji.". Lami tace "yo ai dama duk 'yan Aiki sai na Jamusu kunne" sai wajen k'arfe Goma Shabiyu suka tafi,in Banda kuka ba abinda Hansai keyi.
Malam kuwa yana komawa Gida yaga Jummai na kuka ya tambaya tace "Ai antafi da Hansai." zama yayi yace "Amma Gwamma Allah sayya yimin sakayya duk abinda kike Allah zai saka mana" Jummai muyiwa Hansai Addua, Allah yasa hakan Shine mafi Alheri agareta ,Allah ya bata kwanciyar hankali" Jummai tace "Amin."
Sunje tashar mota suka shiga fuuu Mota taja sai kano ta Dabo Tunbin Giwa kodame kazo Anfika ,sai la' asar sukaje nan Lami taje duk Gidan dake bukatar Yaran takai musu ta k'arbi Kud'in sallama Dana kowo su.Hansai ce ta k'arshe ta kaita Gun Maman Rabia dake kanon tamfatsetsen Gidan suka shiga Hansai nata Raba Ido shigar su Falo yayi dai-dai da fitowar Mama tace "Aa Lami kece da Yamman nan!" Lami tace "wallahi."
Au! har an Sami 'yar Aikin Lalle Lami agaishe ki" nan ta zauna tacii Abinci San nan tai shirin tafiya nan ma mama ta bata Kud'in kawo wa ta fita
Idan Hansai ne suka kawo ruwa Lami ta kirata tace "ke hansai wallahi karnaji karna gani Banda sata da k'azanta zan zo d'aukanki Ganin gida in kikai watanni "nan tayi tafiyar ta.
Mama kam Umartar Hansai tayi data yi wanka hakan kuwa akai ta kirawo iya mai Aikinta tace ta duba kan Hansai nan ta tsefe mata wajen 8 na dare aka wanke kan tayi wanka sosai ta ci Abinci tayi Sallah ta kwanta bacci.
*washegari*
Da safe Hansai ta karya da breakfast mai Dad'i nan iya tayi Mata kitso Mama na kan kujera Rabia ta bugo waya tace "an samu! Mama tace "gata nan kuwa Masha Allah, an samu" yanzu sai ki turo driver yazo ya d'auke ta, Rabia tace "to Mama Amma sai gobe, saboda yau yana da uzuri" Mama tace "ba matsala" nan ta kashe .
Ta kalli Hansai tace "ni meye Sunanki na Gaskiya ne? Hansai tace "Hansai Shine na Gaskiya" iya tayi Dariya "Hansai ai ba Sunan Gaskiya bane" Mama tace "A toh".
Amma kinayin Makarantar Allo Acan? Hansai tace "Eh ina Makarantar Allo, Nayi Izifi Arbain" Mama tace "Masha Allah.Boko fa" iya tace ai kinsan k'auye basu damu da boko ba,Na Addinin Ma wasu ko ansasu basa yi" Hansai tace "Nayi boko Ajina uku a Secondary" Mama tace Lalle ki Godewa Allah.
Bayan an agamai Mata kitson Mama ta kuma sata tayi wanka nan tace kinga Abuja za'a kaiki kina tsafta ,duk da naga balaifi." Hansai tace "to" Hansai kuwa duk bidirin nan zuciyar ta na kukan tuno inna da baba haka tayi yinin nan har ta dad'a fes ba Tsangwamar Gwamma.
Washegari kuwa wajen 12 sai ga Ashiru driver bayan yaci Abinci nan Hansai tasaka kayanta bayan motar suka d'au Hanya sai Birnin Tarayyya.
Bari na D'an huta kan su Hansan su sauka.
Sister's kuyi Hkr ba kullum zakuna jina ba saboda matsalar ba wuta ngd.
*By Queen Meemi*
[9:52am, 26/01/2017] 👑Meemi🔸: . . .
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣18❣
*JAN 2017*
*Queenmeemi.WordPress.com*
*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_*
_Sakon ku ya iso gareni masoyana na gode da kulawa❤_
*****
Sai wajen k'arfe 6 dai -de su Hansai sukaje Lokacin taci bacci ta k'oshi Hon din da Ashiru nayiwa Maigadi ne ya tashe ta ta bud'e Ido tayi tozali da k'awataccen Gida juya baya tayi taga duk Layin da suka shigo kusan hakan Gidajen su ke .Maidadi ne ya tashi ya bud'e zirif Ashiru Driver ya shiga yayi parking a gurin adana Motoci ne Reras a ajiye, ahankali ta fita Ashiru ya fito Mata da kayanta daga bayan Motar, nan tayi Duru- Duru sai kallon gidan take wanda ada tana ganin na Maman Kano mai kyau ,sai taga ko Rabin kyan wan nan be kaiba da Girma da k'watuwa.
Ashiru ne yayi gaba tabishi suka danna door bell da dad'ewa wani Namiji yazo ya bud'e ya basu Hanya suka Shiga ya cigaba da goge -gogen sa y Mamaki k'arara akan fuskar Hansai,Masha Allah ta kira azuciyar ta Sakamakon Tozali datayi da had'ad'd'en falon wanda dukan sa acircle yake Ashiru ne ya tsaya can sai ga Anty Rabi ta fito daga Part nata da D'an saurin ta d'auke da Murmushi saman fuskar ta ,tace "Aa Sannu Ashiru kunsha Hanya!" Alamar russuna Mata yayi yace "eh Wallahi Maman tace agaishe ki" nan ya juya ya fita Rabia ta kalli Hansai "muje ko" zungi zungwi ta bita sai kallon waje -waje take tana Mamakin tsaruwar Gidan Ahankali ta furta "Aljannar Duniya"
Jikake ta guum! ta k'ume da k'ofar Shiga paty d'in Anty Rabia da Hanzari Anty ta jiyo "Aa kiyi ahankali fa" nan suka shiga b'angaren Antyn baki sakin baki Hansai tayi ganin wani falon wanda yafi kyau ,nan tayi ta k'auyancin ta zama tayi gefen kujera ta kafawa Tv Ido tana kallon film d'in da ake ga sanyin Ac na hurowa had'e da sanyayan turaren wuta zo kuga yanda Hansai ta langwab'ar da kai gefen kujera kamar tai bacci.
Anty Rabia kam dawowa tayi d'auke da Khalil a Hannu ta zauna tace "ya Sunanki ne?" Hansai ta sunkwi da kai Sunana Hansai .
Anty tace "Madallah Garinku fa?"
Tace "Bunkure".
kina Makarnta tace "eh Ajina Uku a secondary" (oh su Hansai Ana ji da Aji ukun din nan da akai)Anty tace "Madallah, tom kinga yanzu Aiki kikazo na Farko banason k'azanta na Biyu Banson Gulma kinga da 'yan Aiki wajen biyu A Gidan nan Kamar ki da tsohuwa ga Namji mai Goge -Gogen Babbann falo, ki Kame kanki,Banda shiga inda ba hurumin ki ba, Zakina min Renen boys D'ina Mubarakh da khalil ,San nan Zakina Wanke- Wanke da Gyaran kitchen, nan falon Zakina Shareshi da Goge kujera ,zakina Goge kayansu Tv vedio ,center Table su Dining Teble duk kiyi sai ki Moping tile d'in da D'an abinda baka rasa ba. Shine kad'ai iya Aikin ki, Maganar kud'in Aikin ki Kuma dama Munyi Maganar da Lami."
Dadi ne ya kama Hansai Jin Aikin bame yawa ba don ak'auye wanda take ya ninka wannan ,nan ta d'ago "Insha Allahu Anty zanyi abinda kika ce finsa Ma" Anty Rabia tace "yawwa yanzu kije zan nuna Miki toilet kiyi wanka duk da ba anan Zakina kwana ba akwai Shashin Masu Aiki" Hansai tace "tam Anty."
Dai-dai Time d'in aka kira Sallah nan ta tashi tayi gaba ta bita suka fita Daga part d'in suka koma Ainihin Big Falon, San nan sukayi wani dan sako daga Arewa nan suka Shiga wani korido San nan suka shiga wangamemen daki da Madaidaitun katifu Guda Hud'u aciki,Gefe ga wasu akwatin Katako Babba Doguwa kayan su ne aciki.
Kande ce da Karime suna Alwala a Band'akin dake Cikin D'akin Anty tayi Magana nan suka fito duk suka Zube.
Anty tace "ina kuke kwance? wacce katifa ce Empty Kande tace "waccen ta Lokon e babu ,wan nan ta Tsakiyar nice akai sai ta Gefen Karime waccen kuma ta iya Abu ce sai ta Lokane ba kowa."
Anty tace "ok naji ke Hansai kije waccen nan zakina kwana ki aje kayanki Acikin Wan nan doguwar Kwatin tunda nasan akwai inda babu komai aciki, Bayan haka yanzu ki fara wanka kan ki sallar tunda ba a tayar ba." Idan kinyi Sallaar kizo side Dina."
Hansai tace "to" nan ta fita zuwa kuwa tayi ta aje kayan nata Acikin akwatin ta zauna kan Luntsumar katifar San nan ta tashi tashiga band'akin tayo Wankan ta fito .
Lokacin su kande na zaune sai hira suke ta canja kaya tayi Sallah San nan ta kalli su Karime tace "Sanunku" sukace "yawwa" suka D'an tab'a hira San nan ta tashi ta fita.
Sai hanyar ta kauce Mata ta Manta part din Anty tarasa ina yake sai zagaye falon take duk girman Shi, take nan tayi part din Dake Gabanta b'angaren Hagu Alhalin ita Anty tana side na Dama shiga tayi a hankali ta Danyi sallama ta shiga Zuby ce ta d'ago "waye?.
Hansai tace "nice" sai Lokacin ta gane ba gun bane Zuby tace "ke daga ina?".
Hansai tace "nayi Makuwa ne!! gun Anty Rabia zani."
Zuby tace "oya get out ,ba nan bane."
Haka ta juya sai Lokacin ta gano gun ta shiga da Sallama Anty na Sallah ta d'au Khalil tana mai Wasa sai Dariya yake bayan gama Sallar Anty tace "Jeki kitchen akwai abinci ki d'auka" ta nuna mata.
Tashi tayi tabi ta Gefen Dining ta yi kitchens d'in sakin baki tayi tana kallo nan ma kamar ba Kitchen ba ga had'uwa ga Girma sai kalle -kalle take San nan tadauka ta fita, tace Anty na d'auko"
Anty tace "ok."
Hanyar fita tayi tace "dawo ki Zauna anan kici nan ta zauna tana ci Dad'i ya cika kunnen Hansai sai Hamdala take ,nan ta tuno Inna da Malam tad'an Share hawayen da suke neman zubo Mata,tas ta cinye takai kwanon Kitchen.
Ta fito tace "Anty ina Omo zan wanke kwanukan" Anty tace "habade! kije kawai ki kwanta ki huta."
"Hansai tace Anty bari nayi kawai" nan ta shiga ta nuna Mata sinck ta nuna Mata inda zata matsu Ruwan San nan ta fita .
Cikin Mintuna ta wanke komai ta kife ta fita ta tsugunna tace Anty "na gama" Anty tace "to Hansai ki je ki Huta."
Nan ta fita bata b'ata ba Saboda ta Gane gun yanzu sai Hira su Karime, suke nan ta Zauna Lokacin Iya ta shigo Iya tace "Aa Kande kuce Sabuwa Muka Samu?"
Hansai tayi Dariya ta Zauna Iya tace "to Sannu da zuwa 'yata Hansai" tace "yawwa" Nan da nan tabi su Karime sai hira suke kamar sun dad'e da Sabo dama 'yan aiki in sunga Juna akwai Saurin Sabo wan nan ke nan.
kubiyo ni
*By Queen meemi*
[12:16pm, 27/01/2017] 👑Meemi🔸: . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣19❣
*JAN 2017*
®NWA
*_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_*
_My fecebook fans ina miko gaisuwa gunku nagode da kulawa_
********
Yau kwanan Hansai uku haryanzu agajiye take yauma sai wajen 9 Hansai ta tashi taga d'akin wayam duk basu Kande da Sauri ta tashi tayi waje Part dinsu tayi tana shiga taga Anty na breakfast tsugunnawa tayi "Anty kiyi hakr na Makara."
Da Murmushi Anty ta juyo "Ai nasan baccin gajiya ne ,yanzu sai kiyi" da sauri ta mik'e tai kitchen ta fara Aiki sai wajen 11 ta gama San nan tayi break tafita nan taga iyalan gidan a big falo nan Gabanta ya bada Ras! tazo zata wuce Umma ta kirata taje duk suka zubo Mata ido, tace "ke 'yar Aikin Anty ce? tace eh Mama tace Gata kwa kyakkyawa Sumy ta tab'e baki ta kafa uban d'auri da alama school zata "yauwa ke ya sunanki? ta fad'a Sumy tace "biyoni" salo -salo ta bita ta Shiga d'akin su ta dauko mata under wears da bra ta wanke ta kalleta "kifa wanke tas bansan Almundaha na" tace "to Anty" k'was- k'was ta fita Hansai ta mik'e tayi part d'in Anty tana zaune tana bawa khalil tea ta tsugunna "kinga Anty d'aya daga cikin 'yann Gidan nan tace na wanke Mata" tsaki Anty tayi "oh wad'an nan yara ba kunya Bra ma din sai an wanke musu duk gayun tsaki tayi, ni sun hanani Kula nasu Amma bakomi je kiyi."
Nan ta tashi taje can D'akin su ta tarar da karime na ninke kayan ta tace karime don Allah ina ake wanki karime tace acan bayan D'akin nan ne bari na Nuna miki nan ta tashi ta fita ta bita ta zagaya da ita ta nuna Mata hakan ta zauna tad'au wani boket ta zuba tana wankewa tas ta wanke ta shanya.
Ta koma D'akin su tayi wanka Bayan awa uku Sumy ta fako motar ta ta shigo dai de Sady ma ta fako Tata ta shigo Hansai Lokacin na zaune a kusa da flowers Sumy tace "ke d'ebon kayan" shaf ta manta da gudu ta tashi tayi bayan nan taga duk sun fad'i k'asa sun b'aci tsaki tayi ta d'auka takuma wankewa.
San nan ta koma ta shiga d'akin nasu birjik kowacce daga ita sai shimi tace Anty na wanke Amma na koma kayan duk sun b'aci ran Sumy ya baciallema 'yar Aikin nan! ni zaki b'atawa kaya" ji kake kauu ta kai Mata Mari Ruma tace kai Sumy me tai miki kin fiya zalinci" Murgud'a baki tayi Aiki nasa ta ta b'atan."
Nan ta kalleta "Get out kona Mauje ki Stupit kawai" kuka Hansai take tafita gaanin Anty Rabia zaune a big falo yasa ta D'an kawar da fuskar ta nan kwa ta ganta "tace zo nan" taje ta tsugunna meya sameki nan ta gaya Mata cikin b'acin Rai Anty taja Hannun Hansai suka tafi d'akin ta shiga tace "ke Sumy me yarinyar nan ta miki?.
Sumy tace "Aiki nasa ta."
Anty tace "ke tsaya kiji karma wanda ta kuma sata Aiki tunda Baku kuka d'auke ta ba."
Sady ta turo lips "Dady ne ai ke biyan Albashin ta, don haka dole musaka ta."
Anty tace "Nadai gaya muku" ta fita afusace Dariya Sumy Sady da Zubo suka saka "Lalle Matar nan zamusa k'afar wando d'aya da ita."
Ruby tace "ni bakuga bana shiga harkar ta ba don gani nake sa'ata ce."
Zuby tace "yar Aikin nan munafuka kullum tana Sanye da Hijab sai kace Matar Liman."
Sumy tayi tsaki "zan San ya zan ,dole a bamu 'yar Aiki d'aya kuma wan nan yarinyar muke so tana mana wankin k'ana nan kaya, inga Anty sai ta mutu"
Sady tace "Good idea tawan."
Yaya Babba Ruma tace 'kukam Anyi banzaye ace har sai me Aiki ta wanke muku su bra Anji kunya" ,Ruby tace "haba Anty Ruma Lokacin Abu ayishi."
*Bayan wata d'aya*
Hansai tad'an Saba da Gidan har D'an K'iba tayi Skin colour d'in ta yafara fitowa sai tayi kyau dama wahalar Gwamma ce ta dafar da ita ,tana zaune agefen kujerar falon Anty tana kallon wani Film BARAUNIYA sai Dariya hansai ke ga Mubarak agefe shima yana taya ta kallon tunda ba School yau weekend.
Anty ta fito cikin Shiri oya Hansai tashi Mutafi Hjab dinta ta saka ta dau khalil suka fita.Mubrk na Dan tsalle- tsallen sa don zasu Unguwa ba kowa a Big falo duk suna d'aki bacci.
Nan su Anty suka fita harabar Gidan inda d'aukacin Motocin Gidan ke suka doshi motar Anty duk suka shiga ta bata wuta suka fita daga Gidan tun zuwan Hansai sai yau ta Lek'o wajen wata d'aya kenan sai kalle- kalle take ganin yanda garin yayi Mata kyau .
Wani Supermarket suka je zuu suka tsaya a harabar kantin suka fito Anty tace "Hansai fito Mana" nan ta fito suka shiga nan k'auyancin Hansai ya Motsa sai Duru-Duru take Anty tace "kifaa nutsu Hansai."
kayan aka jidarwa Hansai irin yan kantin nan masu iri d'aya masu siket manya San nan aka d'ibar Mata atamph,da bra su pant da body spray wajen biyar masu kyau akai counting Anty ta biya suka fito nik'i nik'i da kaya.
Direct wurin wani tailor d'inta taje ta bada a d'inkawa Hansai nan ya Gwada ta yace 1 week zai gama sai wajen 1 suka dawo gida a gajiye saboda gajiya Anty tace Ashiru ya gyara Mata parking d'in Motar suka shiga.
Sumy ce da Sady sai tirk'ar Shoki suke a tsakiyar falon suna kwaikwayar yanda na tv d'in keyi kowacce da jins da tsht , domin vedio din suka saka. Anty ta tab'e baki sukai side dinta.
Hansai kuwa d'aya daga cikin kayan da Anty ta sayo mata ne Anty tace ta saka ta daina sa wadanda tazo dasu daga k'auye zo kuga yanda sukai dab'as ajikin Hansai dayake Allah ya wadata ta da hips me d'aukan hankali Anty tace "dole kinasa hijab kici gaba da sawa shine dai-de."
Hansai tace "to" nan ta d'auko mata wani k'aramin Hijab d'inta tace duk ta daina sa wad,ancan kan a d'inko Mata Sabbi .Hawayen Dad'i ne suka zubo Mata tace "Anty na gode" tace "no ke Amana ce agareni."
Da zumudi ta tashi ta tafi b'angaren su, kande da karime nata hira ta zauna "kuuu! zo kuga kayan da Anty ta sai min" ta yaye musu Hijab tace kunga d'aya ta bud'e Leda tarik'a zaro su wajen kala biyar, San tace kuma akwai d'inkin wasu."
Kande tace" Lalle kin cab'a dama nice gun Anty" karime tace "hmm mu kam ba wacce ta tab'a saimana kaya daga Sallah sai Sallah sai kuma kwancen su Sumy."
Hansai tace "kunsan kowa da irin kyautar sa."
Karime tace "Hansai kin sanme? Hansai tace sai kin fad'a! tace "ina zuwa" nan ta Lek'a kudu da Arewa bata ga kowaba ta dawo....
*Queenmeemi.WordPress.com*
*By Queen meemi👑*
.
[12:16pm, 28/01/2017] 👑Meemi🔸: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣20❣
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*********
"A 'ya'yan Gidan nan wallahi kinga Sumy wuta ce Saboda sa Aikin ta da fad'an ta, Zuby kuma isah Ruby kuma Zuma ce ga zaki da Harbi Anty Ruma kuma" Shiru tayi ganin yanda Kande ke karkarwa Hansai kuma Tai k'asa da kai ad'arare Ta juya Zuby ce tsaye tana kallon su ta saka wani Material me Blue da Pink fuskar nan sai k'yallin Make up take sai tashin kamshi take tace "Lalle karime kinsamu sake kinji jar miya kin Tara su kina Gulmar mu ko? dole nay punishment dinki next bazaki ba."
kuka take "kiyi hkr" tafiya ta fara ta kalli Hansai "ke zo ki min Aiki" Jiki na rawa ta mik'e ita kam tsallan kwad'o tasa karime acan waje, itakam Hansai d'akin baki Zuby ta kaita tace ta dad'a gyara shi ta sa Room fresh haka ta fara ko ina sai data goge ya dawo fes sai wajen 4 ta gama taje d'akin su Zuby tace to "Anjima zan bak'o Idan yazo karki bari nai Magana kije kitchen ki had'o Drink da Cup da Cincin kingane" tace "eh Anty ,zan iya tafiya?"
"well zaki iya" fita tayi ta tafi Bangaren Anty .
Bari mu leka b'angaren Su Gwamma muga wai nar da suke toyawa
*MANGALU*
kuka Gwamma keyi tace "Amma kuwa Delu kin badani akan bashi shine zaki taran Mutane!" Delu tace "eh na Tara lokacin da kike so na baki har Gida kikaje don biyan buk'atarki Amma don ke dama taurin bashi gareki yau wata d'aya kenan ina son ki bani kink'i, to wallahi yau sekin bayar".
Gwamma ta share Hawaye bazan bayar ba, kinjiko,Delu duk abinda zakiyi kiyi."
Nan ta koma gidan ,Delu ta bita suka tsaya tsakar gida tace baza fa ta sab'u ba, ki bani kud'i na, uzuri gareni."
Ke kika sani Amma wallahi Delu bazan bada ba sauke Mayafi Delu tayi tasha damara tace "yo kinyi Asiri kin Raba Masoya kin had'a gurmi amfasa Auren shine zaki ce haka ko, da komai ya kammala."
Jummai dake d'aki ta dafe kirji dama Gwamma ita ta Raba Hansai da Muntari tashi tayi ta fita lokacin Gwamma da Delu sun kaure da fad'a Jummai tace "Subhanallah! ya da abin yara?"
Cizo Gwamma ta akaiwa Delu tace "Lalala kika cijen?"
Dayake Delu Jibgegiya ce tafi Gwamma girma ta naka ta da k'asa ta hau kan ruwan cikin ta tana duka sai ihu Gwamma take Dije ta fito tana dukan Delu ta baya nan ta hamb'areta.
"ki bani kud'ina Idan ba haka ba wallahi sai kin gane ban da kyau" Gwamma data Jigata sai kitan Malam! Malam!! take .
Jumma tace "Delu kiyi hkr"
Delu tace "ke yimin shiru wallahi Idan bata ban Kud'in nan ba sai na kaita gun 'yan sanda." Adai-dai time d'in Malam ya shigo "Me zan gani haka nan, Delu ta mik'e
Gwamma ta Jigata ko Hannu batta iya d'agawa yace Meye haka nan da Girman ku ba yara ba."
Delu tace "kudina zata biya ni bashina" yace "Nawane? tace "dubu Goma" ya jin-jina kai a "yanzu da ake wiyar Rayuwa Gwamma kika ciwo wan nan bashin? to ita ku sai kibiya ta."
Gwamma ta tashi ta face Hanci wallahi kin daki Kud'in ki Koni ko ke."
Delu tace mu zuba D'an Halak ka fasa Jarababbiya afusace ta fita Gwamma ta shige d'aki tana huci Jummai ta fasa dariya tare da cewa "Allah ya kara" ni meemi bace "Ameen"
Ga wan nan ba yawa fans Sakamakon hannu na dake ciwo shiisa banyi da yawa ba.

0 comments:
Post a Comment