Tunda Dady ya Yanke Hukunci Zuby ta shiga Matsala saboda tsagwaran san datakewa Fawwz kullum suna Manne awaya abinda ya dada sadda da Rashin gamsuwar ta ga Mijin Da aka bata sabili da zuwan da yayi Sam sai taga kamar batai mai ba yana basarwa had'e da nuna isa.
Agabanta yayi waya da Budurwar sa wacce yakeso bai wani nuna naam da ita Zuby ba La akari da tai watakil shima dole akai mai tundaga nan Jikinta yayi sanyi kullum kuka inda taje ta Samu Hajiya kan Maganar tace sai de tayi hkr.
Bangaren Ruby kuwa ba yabo ba falllasa sun dai-daita kansu Mutumin nada 'ya'ya biyu ba wani Babba ,ne sosai da Alama yayi Mata ,itama tayi mai tunda yaganta d'agwas- d'agwa kaji abin Manya k'warya tabi k'warya .
Itakam Ruma nata Suga Dady ne Babba ne yana da manyan yara Baban d'an sa ya Girme mata,itama tayi Naaam don Biyayya inda Shi kuma gani yake ya samu dami akala sai b'arin Naira yake wan nan kenan.
Shirye- Shirye ake inda Manya aka saka Ranar 22 ga watan March 2017 inda shine d'aurin Auren.
Zuby sai kuka take tana zaune ta D'ora kan ta akan cinyar Mama tace "na shiga uku Mama nifa wulak'anci yake min da Alama ban masa ba, kuma nima bai mun ba ,ki taimakeni."
Mama tace "kiyi Biyayya ki hkr" ba yanda ta iya ko waya ya bugo Mata sai de yayi tsaki yace ykk ba yanda ta iya tace Lafiya ahakan har aka suke waya.
Yauda suke zaune anata tsara Bikin ita kam Zuby kanta ke ciwo Ga Soyayyar Fawwz dake nuk'urk'usar ta kullum damuwa Sede su had'u dashi a School.
Zaune take Adaki taci kuka, bakin ciki ne yayi Mata yawa ta fita wajen Garden tana kuka kiran wayarta ne ya motsa ta dauka daga can Dan Sanata yayi tsaki "idan bazaki Magana ba zan kashee."
Haushi ya isheta "ka kashe mana Waya damu da kai ,duk abinda kake tak'ama dashi nima hakan" yace "bana Sonki don haka ki Sanar da Parents naki" kit ya kashe.
Tunani ta fara Lokacin da wani kb ke sonta da sukaje Jigawa k'ark'ari ta Dinga cewa bata Sonsa har kuka yayi agabanta ,ta Buda kasa a idonta tace bata Sonsa face to face, sai yanzu taji Ciwon abin ashe haka kb yaji? duk da ita tasan bata san Dan Sanata Amma taji d'acin kalmar na Bai Sonta.hmm Abinda kai Shi za ama.
Komawa Gida tayi tace Hansai ta dafa Mata kunun Gyada saboda bata iya cin Abincin.
*Bayan Sati 2*
Zuby ciwon so ya kwantar da ita itace har Asibiti nan hankalin Mama da Dady ya tashi kai kowa ma na Gidan, direct bayan treatment dinta da Doctor yayi ya kira Dady inda yace "ranka ya Dade 'yarka hawan Jini ke neman kama ta saboda damuwa da yawan tunani ya kamata ta samawa kanta salama."
Dady yace "okay ba matsala" yau kwanan ta 3 a Hospital Su Dady shida Mama na zaune Dady "yace yanzu Zuby kan na Rabaku da Fawwz shine Sanadin Sa damuwarki har ta ke nema ki jawa kanki ciwo?
Mama tace "Aa yarinyar nan fa D'an D'anata baya Santa koni wani Zuwa da yayi na zo zan fita naji yana gargaya Mata Magana kullum kuma sai tace min ga abinda yace Mata to ga Wanda takeso an Rabasu haka kuma Shi Wanda ake son had'asun yana yimata hakan Dole damuwa tai Mata yawa."
Shiru Dady yayi "yace ba Matsala zami Magana da Sanata d'in kan Maganar .
Satin Zuby D'aya aka sallamota duk ta fige Dady kuwa sunyi Magana da Sanata ya sanar mai abinda yake faruwa Sanata yace "ay 'ya'yan zamani sai ahankali, yanzu tunda abin yazo da hakan mu Janye had'in kawai, Allah ya had'a kowa da Raban sa, Amma wani hanzari ba gudu ba Minister ya kamata ku dai-dai da Baban Fawwz domin koba komai Gaba ba kyau kodan ka ceci Rayuwar 'yarka ,Amma ni da kaina zanje har can wajen nasa insha Allahu." Dak'yar Dady ya hkr.
BAYAN Sati D'aya Da k'yar da sid'in Goshi Baban fawwz ya sakko duk da dama Dady ke Gabar dashi ,ba yanda zai yi haka ya hkr yace Ayi daman shima Fawwz din duk ya rikicemai wan.nan shine Silar shiryawarsu nan akai maganar Auren aka Maida kan Fawwz Nan shirin ya kuma kankama.
Zuby ba Wanda yakaita jin Dad'i Auren Masoyi akwai dad'i su Dady an Rikice sai barin Naira ake komai daga waje ya wayar ai order Su ,ya'ya sun Samu irin Mazan da yake so.
Sumy anci K'uzun Bikin nan, Mama kuwa Mutanenta kowa Nason zuwan sa haka Umma to Bikin 'ya'ya Uku wasa ne! hansai ba abarsu abaya ba wajen son Zuwan Bikin Wanda Jikinta ke bata tabbas wani Burinta zai cika agun Wanda yayi dai-dai da Saura Wata d'aya cir.
Bari na tsagaita Anan .
By
Queen meemi
Queenmeemi.wordpress.com
. . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣32❣
*JAN 2017*
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION_
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
***********
Gida kowa shirin Biki yake kai hatta su Hansai ba abarsu abaya ba an musu kaya da yawa kowa ne event da za agabatar suma an musu nasu kalar anko da su head din su duk iri d'aya .
ABangaren su Sumy Da Dady kuwa ba a cewa komai domin kaya na gani na fada suka dinka duk na event .
Amare kuwa ba a cewa komai. Lokaci na tafiya Bikin na dada K'ara sowa Ankawo Lefen kowacce aciki set 24 tamkar had'in baki kaya turmus kamar abude kanti .
D'aki d'aya aka ware musu nan aka d'auko 'yar Maiduguri tana Getta su masha Allah kowacce sai kyau suke ,yau da akewa Zuby Sady ta shiga Tace "Anty Ruma ya Za'a ai preparation na frnds event d'inku sa frnds naku?"
Zuby tace "no wan nan ai akwai masu yi ki bari kawai" Sumy ta shigo "wow gaskiya dole ai mini nima don na Rikita Nazi." dariya Ruma tasa "tab! nikam keda nazin nan kuna ban Dariya."
Sady ta tashi tana waya tafita don karbo dinkin ta hatta gidan sai da aka getta su duk an canja wasu kayan yau ta kama saura sati d'aya Bikin Hajiya ta duro da sauran Dangin Dady ,haka Dangin Maama da Umma suma suka duro. Anty kuwa k'annen ta ne zasu zo Amma sai anfara Event.
Nan fa Dida ya kacame Dangi kota ina Dady sai barin Naira yake tunma ba A faraa Bikin ba ,ga Gift da yake karb'a gun Abokanan Siyasan sa.
Shi kanshi katin Rabo kala -kala zaka ganshi Amare kuwa ko Giftawa sukai sai kaji kamshi kai gashin kansu ma ba abarsa ba ya ba wan nan kenan.
Ranar Talata shine Ranar fara Biki inda za ayi Dinner da dare wajen k'arfe 7 dai- dai aka fara talle Amare cikin wata me makeup ce tazo ta yimasu kwalliya me kyau kamar dawisai haka suka fito A tsadaddun Amare, kowacce taci latest gwan inda wani shegen matrial ne me d'aukan ido da less ajiki abu na manya idonka Shi zai tantance maka yawan kudin sa, Golden ne da red akai adon sa kuma dukkan su iri d'aya suka saka, sai de Head d'in Ruma red ne ,nasu Zuby da Ruby Golden.
Angwayen ma haka suka saka D'anyar Shadda Golden ,Ana gamawa aka fara kwasar su Frnds Na Amare ,Su Sumy da Sady kuwa Su Suka kwashi nasu frnds d'in a motocin su, Shigar nasu yayi kyau kamar Ka sace su ka gudu sun Balain kyau sai iyayi suke kowacce da hadaddun frnds nata.
Hango Hansai nayi ita dasu Kande sun kafa head masha Allah sunyi kyau musammn Hansai kyanta ya fito kayan sun karbi jikinta hakan aka dunga daukansu Ana kaisu tafkeken hall din da za a Gabatar haduwar gun da fadar sa Sayya b'atan Lokaci.
Cool Music ke tashi ga k'amshi ma na tashi nan MC ya fara Aikin sa,ko ina ka kalla wal -wal wan nan na wane wan can haka aka ci aka sha aka taka rawa aka gama aka Raba Atampah Super Holland da Calender dake manne Pictures d'in Amare.
Washegari Ranar Laraba shine Mothers Day nan fa Su Mama karfe 3 Aka fara inda Mama da Umma da Anty sukayi Ankon kaya iri d'aya me makeup ta yi masu duk sunyi kyau sunkafa head Sai tarbar Manyan mata suk.
Amare kuwa shigar wani kwantaccen Less sukai mai Manyan flowers da Stone Pink ne da ratsin Green inda Ka nad'a musuu head Green me adon pink suka saka wani a kafad'ar su ,Buba ce da zani sunsa wani hil Shoes Green sun Balain kyau Lokacin da suka fito ai nan da nan Masu vedios da Masu Photo suka fara Aikin su, Flower Girls suka? rakasu wajen zama wajen ya k'ayatu Su Sady ma sunyi kyau Sai tar bar frnds suke.
Mawak'in Nan Audu Gwanja ke watso wakar sa yauma Hansai sunyi kyau kamar ba 'yan Aiki ba.
Wajen 4 Pm Wata Sumammiyar Mota ta faka a harabar hall d'in.
Wata Had'add'iyar Matashiyar Budurwa ce ta fito bayan ta kashe Motar ta kulle akalla zatai 21 yrs bugaggiyar wayar ta ta fiddo a Jakar me kyau,tayi shigar wani material Ash tayi balain kyau, dole ka kalleta ka Kara gani nan ta danna kiran Sady tace tana harabar Hall ta fitoo Su shiga.
Kamar 3mint saiga Sady ta fito duk sokeken shoe da ke k'afarta besa ta tawo aguje ba inda suka Rungume Juna da Budurwar "wow Suhaima kin ganki kuwa!" Suhaima tace "ke ni k'yaleni Ina Anty? Sady tace "ke Anty banganta ba tana cikin mutane , ban d'auka zaki zo Mana ba Lokacin da na fada miki ai kuna Landonn ,yaushe kuka dawo daga Landon din? Suhaima tace "ke ni kyaleno muje kawai."
Karo Sukayi da Hansai nan Jakar Suhaima ta fad'I ,Head d'in Hansai ya fad'i Sady ta wanka Mata Mari "bakida hankali ne bakya ganin ina tare da bak'uwa?
Hansai tace "kiyi hkr banganku ba."Dallah Matsa Fool Gal kawai,ki bata hkr kona kuma Mazge ki Saida Gaban Hansai ya Fad'i tace "kiyi hkr" tare da share Hawaye Suhaima da taji hansai ta birgeta kuma ta bata tausayi, tace "bakomi."
Da sauri Hansai tayi gaba Sady taja Hannun Suhaima sukayi Gaba.Biki yayi Biki Gwanja sai samun naira yake ya rikice sai watsowa Amare wak'a yake yan Mata kuwa sai cashewa suke k'arfe bakwai dai de aka gama.
Sady ta rako Suhaima nan sukai sallama da Sady , "Suhaima tace banga frnds namu na Secondry ba! ,Sady tace "nakai musu inaga ko sai na gobe" suhaima tace "okay nikam ina yarinyar dazu? Sady tace Wan nan Dirty Gal din 'yar Aikin Gidan mu ce fa!
Suhaima tace "yarinyar she's so beautiful kawai naji ina sonta", Sady tace "ke rabani da wan nan ai kema me kyan ce ,Zaki zo goben?"
Tace "eh kinsan fa Gidanmu duk suna Landon nima Hutu Nazo Saboda na samu Hutun School nima Ina Gwarinfa Gidan Kanwar Mami Aikinga kuwa dole nazo,yanzu ma inason zuwa Bakery ne kicewa Anty ina gaisheta Gobe zamu had'u,nan sukai sallama ta tafi.
By
Queen meemi
*Queenmeemi.wordpress.com* .
. . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣33❣ . *FEB,2017*
®NAGANTA WRITERS ASSOCIASION(NWA)
_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's_
_Sak'on gaisuwarki ya iso gareni *MAMAN SAFYAN*nagode da kauna da kuma bibiyar book dina ,da duk masoya masu turon da sako NGD.❤_
*********
Washegari Alhamis shine ranar kamu inda wajen k'arfe Hud'u Atafkeken filin Gidan su akai Decoration na Gargajiya su kwarya ,tum-tum,su Ludaya ,Fai-fai da sauran kayan Gargajiyar yayi kyau don masu tsara irin gun aka d'auko ga Masu kid'an k'warya ne da yan Gad'ar su aka dauko nan suka zo, yau duk shigar Gargajiya sukayi inda Amare Suka sa Super Sharaton Babbar Aka d'aura musu Gwaggwaro(head)da Atampar rigar akai Buba suka dora zanin akan Rigar sunsha Makeup sunyi kyau kamar ka D'auke ka gudu Amma yau kowacce da kalar tata Sai d'aukansu Vedio ake idan DJ ya kada sai mai kid'an k'warya tabuga.
Su Sady Kamar kai ya tsinke ko ina ka kalla sai walwali yake Ga yan Gada sai yi suke su Mama sai liki suke wa Hajia dake tsakiyar fili da Sauran Dattijai sai rawa suke , ko ina wadace da kayan motsa baki kowanne tebur.
Dai de an fara Kamu Ana ta zuba Uban guda wayar Sumy ta buga nan ta d'auka Nazi ne yace yana kofarar Get ta fito zai bata sak'o,tafita sai yauk'i take kugun nan yasha Murjani ,tana zuwa ta tsaya "my Nazi How far?" yace "fine dear ya Biki?" tace "Alhmdlh."
Nan ya mik'o Mata Gift Ga "wan nan ki bawa Sisters namu Gudunmawa, Dad'i taji tace 'oh! dear Sun Gode" yace "they diserve more" Murmushi tayi "Jirani na dawo" Juyawa tayi tana Mirgina Ukwu binta yayi da Ido ,kamar ance ya Juya Hansai ta fito daga Mak'ota da wani Makeken flaks akai da sauri ya fito zuciyar sa kamar ta fad'o wani irin Bugawa datayi tayi fat! fat!, "Hansai" taji ankirata cak! ta tsaya juyawa tayi Ya kafa Hula yayi shigar Abuja Boys ,yace "ke ya Biki?" Jiki na rawa tace "Lafiya"
Dariya yayi yace "ke bakya sona ko? dara daran idanuwanta ta d'ago ta zuba mai "I can't love you"
Shafa gemu yayi "Lol Yarinya kinfara Jin Speak ashe ,Harara ta watsa mai ta tafi ,ya rik'o maya finta, dai de Lokacin Sumy Ta fito rik'e da flaks da kayan take Away.
"Tab jar Ubban can!" tsawa ta dakawa Hansai "me kike anan? Jiki na rawa tace bkmi Anty" harara ta kaiwa Nazi yace "Sorry Princess tambayarta nake."
Mari ta kaiwa Hansai har da bugu ta dumata Dundu abaya, Durk'ushewa tayi tasa fasa kuka Nazi ya had'e rai "wait Sumy ki daina dukanta."
idonta yayi ja saboda kishi tace "ya zaka zo kana nuna Mata so bayan kasan banso wallahi hansai sekin ganekuren ki, in banda son matanka me zakai da hansai ,Ai se Nuhu maigadi, ki sani wild duk randa Na kuma ganin ki dashi sai kin koma kauyen ku."
Wani kallon masifa Tayiwa Nazi karma kazo kana ban hkr domin bazan Saurareka ba.A fusace Nazi ya shige Mota da Gudu taje mai take away a gaban motar afusace ya ja nan ta dawo kan Hansai "tashi banza ko yaushe akanki nake samun matsala da Nazi rankwashin ta tayi mai zaiyi dake adauri kashi ko abata Igiya."
Motar Suhaima ce ta Danno kai ta yau ba irin ta jiya bace motar hon tayi ganin Gidan cike ba Space yasa ta Dan matsa gaban Gidan tai Parking Motar ta fito Yauma tayi kyau kana ganin ta kasan hutu ya ratsa yau kuma shigaright Purple tayi, tayi Masifar kyau.
Sumy ce ta ganota "Oyoyo Sis Suhaima Welcm" idanuwan Suhaima ne suka sauka kan Hansai tayi Murmushi "meya faru yau kuma?" Sumy tace "Rabani da wan nan banzar 'yar Aikin tunda Saurayina ya k'yalla ido ya ganta Raina ke b'aci Agabana yake nuna Mata so bazan iya d'aukan kowane irin Nonsense ba wallahi."
Tausayin Hansai ne ya kama Suhaima tace "Sorry Aiba Lefinta bane" Sumy tace ai sena renama Nazi hankali.
Kamo hannun Hansai Suhaima tayi Ta d'aga ta ta mik'e nan ta dau flsk din Ta kalli Suhaima "Nagd" Duk yayin da ta kalli Suhaima se gabanta ya fad'i nan suka shige Gidan .
Biki yayi Biki gud'a ko ta ina nan aka bawa Suhaima Mazauni Lemo kawai tasha Sady Tazo ta jata Gun Frnds nasu sai yau shegamo suke domin An dade ba ahadu ba, sai kiran wayar Anty take ta nan sukai waya ta tashi ta doshi cikin Gidan Direct side d'in Anty tashiga.
Anty yau bata fita ba sakamakon kanta dake ciwo Da dugu Suhaima ta Rungume Anty tace "I mssd u Anty" Dariya Antyn tayi "Saukar yaushe? dama kuna Nigeria? Suhaima tace "no Anty hutu Nazo" duk Family suna can Amma Suma zasu zo hutun."
"To Allah ya kawo su cewar Anty."
Suhaima tace "nikam Anty akwai wata 'yar Aiki tun jiya Naganta yauma Naganta." Anty tace "wake nan? Kin san suna da yawa."
Tace "Kinga wata 'yar fara haka yar Doguwa bacan ba mai Manyan Ido da dogon hanci ,tana da Gashin Gira Da yawa harda Wushirya."
Dariya Anty tasa "Tamkar kanki kike Suffan tamin ai"
"Aa walh Anty aikin ga ni Banda wushirya kawai de haka take."
"Kode Hansai kike Magana?" kamar da had'in Bakin Hansai ta shigo da Khalil A hannu yana kuka .
Suhaima tace "yawwa kin ganta" Anty tace Au Hansai ai 'yar Aikina ce"
Suhaima tace "tana Birgeni Ga hankali saide ko yaushe saina ci karo ko Sady da Sumy na dukanta."
tace "ai haka suke sai hkr" .
wurin Bikin suka koma Haka akayi akagama aka watse
Washegari ta Kama Friday inda Amare da frnds Nasu suka hada lunching Nan ma ba a magana Na chase Inda Nura m inuwa yayi barin Wak'okin Bakin.
*Washegari Ranar Daurin Aure*
Nan ma Washegari Ta kama Saturday aKa D'aura Auren *RUMASA'U DA ALHAJI MUSA*
*RUBAYYA DA MUSTAPHA*
*ZUBAIDA DA FAWWZ*
Aka shaida Akan Sadaki Lakadan ba ajalan ba Kowacce dubu Dari Biyu.
Lalle burin Dady ya cika domin garin Abuja sun san Ana Bikin, ko ta ina mutane.
Su Mama kuma Suka Zarce Da yini Nan ma Faty Niger ce Tazo ta wak'e Amare.Haka akai biki Lafiya aka Gama sai fatan Zaman Lafiya.
Washegari Ta kama Ranar Sunday Aka fara shirin Mik'a Amare Zuby Anan Abuja Gidan ta Yake Haka Ruma ,Ruby ce zaa Mika ta Lagos ita se Washegari.
Amare sunci kuka sunkoshi kowacce akai musu Nasiha aka mika ta Had'dden Gidan ta.
Litinn Da safe aka tafi kai Ruby,Sai de muce Allah ya bada Zaman lafiya.
kudakace ni Fans sai kuma gobe In kowa ya huta da gajiyan Biki.
By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com
. . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣34❣
*FEB,2017*
_®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASSION_
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
**********
Gida an Gama Biki an watse sai su Hajia da sai tayi Sati 2 san nan zata tafi ,sai su Sady sai hutun gajiyar biki suke haka su hansai keta aiki ko ina agidan saboda harkar biki sai an bata gu,Hajiya da Umma da Mama ke break fast A babban Falo tace "ku yanzu bakuji Dadi ba! jin kamar kun sauke Wani nauyi da Allah ya D'ora muku,musamm idan.mace ta isa Aure kuyi Mata inde ta isa Dan Sauke Nauyin Da Allah ya D'ora maka."
Mama tace "Wlh kullum sai nayi wa Allah Godia Saboda min sauke wani nauyin ." Umma tace kedai Bari Allah dai ya bawa yan baya maza na gari."
Hajiya Tace "Ameen".
*Bayan wata D'aya*
B'angaren Amare kuwa sai san barka Musamm Zuby Soyayya suke kwasa da Fawwz Dan sun tafi Honeymoon Dubai,haka Ruma tana zaune Lafy da Alhaji Musa Saboda Gidan ta da ban kuma sun fahimci Juna, sai B'angaren Ruby ma hakan take.
Sady ce zaune ta kafawa waya I'do tace "Sumy wlh inada damuwa! kin san wan Handsome din nan Wanda muka had'u dashi a Bikin Futha 'yar Minister ,wlh na Kamu da Sonsa."
Sumy ta d'ago da gud'a "yirrrrr! Lol Amma nayi farin ciki yanzu duk Irin Mazan dake sonki duk basi maki ba se yanzu nikam Zanso Naga wan nan Guy."
Sady ta FarFara Ido "ai suma zakiyi Idan kuka had'a Ido, keni fa Numfashina har neman sark'ewa yake yayin da na kalle shi ki,ba abinda ke Birgeni dashi sai basarwa d'in nan."
Sumy ta tab'e baki "ayi dai Mugani."
Hansai ce ta shigo da Mopper ahannu zatai Guga Sumy ta Harareta "Get out" Juyowa tayi ta koma Sumy tace "ban san Yarinyar nan Cuz duk ta Birkitan Nazi."
Sady ta k'yalk'yale da Dariya "tab! Amma Sumy kin fad'o kina Big Gal, Amma ace tsami Hansai zata kasa ki koda yake tafa kile yanzu, ahakan ma bata son sa kenan."
Sumy tace "Barni kawai kin san Nazi yanzu se yayi me gaba d'aya!"
Sumy tace "to ni wai kinsan Sunan shi Saurayin da kike so? tace "Aa"
"Aa! kinada Wahala sai ki dage."
Sady tace "Futha zan tambaya kawai!"
tace "daya fi maki," wayar Sady tayi K'ara ta d'auka Ganin number waje yasa ta daga "Aa Suhaima!" tace "naam"
"kin koma ashe!" tace "eh hutun ya k'are ai se kuma nan da 3 Month zan kammala Degree zamu dawo da har su Dady". Sady tace "Allah ya kawo ku,"
"Ina Hansai kuwa? tsaki Sady tayi "ke kin Mak'alewa 'yar Aikin nan tana can tanayi"
Tace "Okey ki Gaida" ta nan sukayi Sallama.
*8:Pm*
Nazi ne a d'akin wani Abokin sa suna kallo "yace Khalid kasan Sumy?"
yace "eh man!
yace "to Gidan su akwai wata Yarinya wlh ban d'auka Sonta nake da Gaske ba, kwanakin nan duk ta dabaibbayeni,kuma matsalar batta sona."
khalid yace "haba naga Sumy ce Budurwarka! yace "eh Dan so ina son Sumy, Amma Soyayyar Yarinyar nake sosai."
Yace "tab! zaka had'a Jalala kasan ba yarda Sumy zatai ba"
yace "sosai so nake kaban Shawara," shuru Khalid yayi kawai ka hak'ura da d'aya"
"Nida Sumy zata hkr ai nafison hakan" yace "Haba kai ma kasan Dadyn ka bazai so had'a iri da 'ya'yan talakawa ba ,naji kace 'yar Aiki ce ma"
Nazi yace "ni ba ruwana da wan nan inde akwai so is okey" khlid yace "my Fnd kawai ka rik'e Sumyn ka so me sonka" yace "zan Gwada."
* After 2 Weeks @4pm*
Juyi Sady keyi adaki don kuwa duk ta tashi hankalinta Domin Sosai take son Dream Guy nata Ganin ba sarki sai Allah yasa ta watsa kiran Futha
Ta dauka "Amarya bkya Laifi" tace "ya San Ranki" D'an Jimm tayi "nikam Futha a Bikin ki ai Naga wani Handsome Guy duk Samarin gun sai de Subi bayan sa wajen haduwa"
Tab'e baki Futha tayi "Banda Mijina dai!" Sady ta sa Dariya "haba dai Futha ai ko Mijinki Al barka, Pls kin san Shi ?"
Tace "ke ni ta ina zan sanshi" nan tayi taimata kwatance bata gane ba tace "aidama bazakii gane ba" tace "eh naji" nan suka kashe.
Kande ce ta shiga D'akin tace "Anty Sady wai kin bak'o awaje" tab'e baki tayi "naji" mikewa tayi ta Dan fesa turare tayi waje sai cuno baki take ta fita.
Yana zaune akan 'yar Rumfa a kusa da Parkin Space Tsaki tasa tace "Dan naci kaine? d'agowa yayi haba "Sady meye Laifin me sanka?
kaga! Hannu ta daga "kai Faruq ka fita way D'ina don bana Sonka haba adauri kashi ko a bata igiya? na farko Bakada Naira na biyu ba Good Dress ko mota bakka da ita."
Murmushi yayi "haba Sady ni inada rufun asiiri, ni Dan kaduna ne Aiki nake a Abuja din nan kuma kin san ai aganka da Aikinka ai yafi baki san inda Rana zata fadi ba."
Hansai ce ta fito da Roba ahannu k'walla kiran ta tayi taje "oya zauna kuyi hira da Shi , da ita kuka dace ni nayi nan" juyawa tai suka bita da ido .
Gaidashi Hansai tayi tace "kayi hkr Aiki nake" yace "ba Matsala dama tafiya zan ma nide ki tayani Addua Allah ya ban Sady" tace "Amin."
Nan suka Rabu ta koma Gida cike da mamakin wulakncin da Sady kewa Samari kowane yazo sai tace bata son sa haka dai Rayuwa tacigaba da tafiya har... .........
By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com
. . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣35❣ . *FEB,2017*
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION(NWA)
_Sadaukarwa ce Ga Basher Usman Family's_
***********
Rayuwa nata tafiya da k'alubalai masu Buri suna son ya cika ,wasu kuma suna cikin bakin ciki haka Rayuwar take yau Baki Gobe fari .
Yau Me d'aukan su Kande da Karime tazo tafiya dasu da yake gari daya suke. "Mama ta kalli Kuluwa Tace yanzu tafiya zakiyi dasu?
Tace "wlh Aure za a musu" Umma Tace "ai ma wad'an nan sun Dad'e kisan k'auye basa barin yara sukai har sha takwas ba Aure".
Kuluwa Tace "wlh kuwa yanzu duk ba sa'anin su,suma Dan sun Samu nan ne shiisa,baga sunan sunyi fes dasu ba." Nan aka had'a musu kud'in Aikin su tare da shatara ta Arziki .kuluwa na Jadda da musu kan zata kawo musu wasu 'yan Aikin.
Acan Farfajiyar waje suka had'u da Hansai tana kuka zuwa tayi ta Rungumesu "Shekara Biyu muna tare Mun shak'u yanzu zaku tafi ku barni."
Kande ta Matse k'walla zamu had'u bamu Rabu ba ,ki bamu Number D'inki kinga bamu da ita idan Munje zami samu waya Mi miki nan ta bata,karime kuwa ta kasa magana.
Kuluwa tazo "se kuzo mu tafi Garinmu da nisa fa," da k'yar suka rabu Suka tafi da Abin Arziki da yawa, wan nan kenan.
Suk'uk'u Hansai ta dawo Bayan tafiyar su, sai da iya kad'ai suke hira kawai kamar Mara Lafiya,nan ta hau tunani jitayi Gidan yayi Mata rashin dadi side din Anty taje Ta shiga tana zaune tana waya ta juyo tayi ma Hansai Iso data zauna .
Zama tayi Anty ta d'ago tace "Jiya Uncle Abbas ya kawo Mini Result naki" Mamaki ne ya kama Hansai tare da Murna tace "wayyo Dadi"
Tashi tayi ta fito da Result din ta zaro ta nuna Mata Gashi 8, Credit kika samu saboda Dadi kuka ta saka Hawaye shab'e -shab'e ta daga hannu sama "Allah na Godema" Anty tace "kawo na adana miki nan ta mik'a mata
Anty tace sai Abinda zan gaya miki ki dawo nan kawai kina kwana wan cen D'akin.
Kinga iya k'aramin D'aki zata koma itama ,can yayi Girma tunda Su karime sun tafi." Dadi ne yayi ma Hansai yawa tace "to Anty."
Can waje ya fita ta zauna sai washe baki take tana kad'a kafa tace burin Baba kenan da Muntari Abinda sukeso nayi kenan Wayyo Allah Nagode maka kasa na had'u da Muntari."
Haka tayi ta magana ita kad'ai nan ta Lula tunanin irin Soyayyar da suka zuba da can Allah ka kawo min Muntari Dariya tayi kamar wushiryarta yafito tamkar tana tare dashi.
Tana nan A zaune Get d'in Gidan ya bud'e Sady ta danno Hancin Motar ta a Fusace ta fito daga Motar a 360 idan ta na tsiyayar Hawaye ta kalli Hansai ta wulla Mata key "dalla Gashi kaiwa Ashiru ya wanken mota" da sauri Hansai ta D'auka tana Mamakin Sady.
Da gudu Sady ta Fad'a kan Bed ta fashe da kuka Sumy dake kwasar Sleep ta, Mutstsike Ido ta mik'e tace "Sis meya faru?"
kuka ta kuma fashewa dashi Ta tashi zaune ta zauna "Sumy."
"Ehen ina Jinki meya faru?" Sady ta Lank'washe k'afa kamarni Sady wai Namji zai yan k'wana Impossible."
"Ke in zaki gayan Ki gayan" Sumy ta fada Sady tace "wai kin san Handsome d'in nan na gani a 212 yana Zaune Acikin Motarsa irn na fito na gano shi Lokacin ya fito sai na bige ban saniba yana D'agowa Yace wai ina dubawa ina kallon hanya na bashi hkr ya tab'e baki."
Sumy ta sa Dariya "Weldon kinga ai yanzu Kayi hkr dashi ,tace "no nifa Shi nakeso wlh ,yan zuma kawai na fada miki ne Amma bana jin haushin sa kawai tsananin sonsa ne ke sani kuka." tace Allah dai ya kyauta" Sady tace "yanzu number d'insa nake nema wlh."
Sumy kam Daria ta yi "nikam da zaki bi ta tawa da kin hkr da Samarinki Ki zabi d'aya aciki."
"Kai Sumy kinsan Dady bai son Talakawa kun manfa yanda akai dasu Zuby ne! don haka wan nan guy din ta koina yayi."
"Be a Lady mana haba karki bada Mata kina Jan Class." Sady tace "sekiyi kuma" nan ta mik'e ta fad'a toilet don wanka.Haka itama Sumy ta shiga Dayan Toilet don Nazi zai zo.
*5:30*
Hansai kuwa yau tsimin son Muntari ya motsa haka ta d'auko dogon abin Busar ta tun na k'auyensu tana Dan busawa tana tunano irin Soyayyar da suka sha da Dalilin Rabuwar su, hawayenta ne keta diga kan cinyar ta, Mangaron dake Garden din taje tadan tsinka ganin ya nuna tazo tana Goga Shi a hannun ta.
Dariya taji a bayan ta tajuya
da sauri sukai Ido hud'u da Nazi Shida Sumy ne zaune kan kujeru Ta fesa uwar kwalliya sai kwai nane take. shikam Hansai ya kafawa ido Sum sum Hansai ta mik'e tazo ta wuce a hankali ya furta I luv u babe" Tsawa Sumy ta dakawa Hansai ta tsaya tace "come"
Nan tazo ta tsaya ta kalli Nazi "ka kalleta san Ranka wlh akanta zan huce" Murmushi yayi "Madam Sumy in kika dake ta ai kamarni kika daka." K'ululun taji na bak'in ciki tace "Nazi ka dai na mun irin haka! haba banso ,ke Hansai ayau agabana inaso Ki ce bakyason Nazi yaji."
Dago Kai tayi ta ce "nifa Anty inada Miji akauye kawai ni bana sonsa,Ki daina damun kanki ma." Murmishi tayi "kin fanshi kanki yarinya don bana son raini Bar nan ."
Asalub'e ta Juya Nazi ya bita da ido ,Sumy tace "yanzu Nazi agabana kake son wata haba watan ma 'yar Aikin Gidan nan yanzu ace ita kake so Alhalin kasan Maganar mu dakai har ta Kai ga Manya dama baka sona ko!?" ta share Hawaye.
Yace "Sorry Sumy ina Sonki But!
"But what? Nazi plss nifa akan hakan wlh sena hk'r dakai na dole, don ban san Yaudara."
Yace "sorry Daga yau na dena"
Dariya tayi "okey" nan suka cigaba da hirar tasu.
BY
👑Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.
. .
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣36❣
*FEB,2017*
®NAGARTA WRITERS ASSOCIASION(NWA)
_Sadaukarwa ce Ha Basher Usman Family's_
*************
Da k'yar da sid'in Goshi Sady ta samo Number d'in Handsome agurin Futha domin damun ta data taimata Mata yasa ta tambayi Mijinta ganin bata gane ba yasa tace Sady taje gidan nata.Acikin vedio na Bikin ta nuna shi nan Mijin Futha yayi Mata kyautar Nomber din sa, taji D'adin Karba tace ya gaya Mata sunan sa Yace Aa ganin ta samu Number yasa ta hkr.
Tunda ta amshi number din sai Abin ya zamo kamar me kullum ta kira a kashe. kamar ta kurma ihu yanzun ma kira take tayi Amma Shiru.
Abin Haushin ma ta d'ora Number din a whtsup taga ma ba'a tab'a bud'eta A whtsup ba, kamar tayi kuka
Tana kwance Hansai na Gyara mata farce ta kira wayar k'irrr ihu tasa Jin ta shiga ta kalli Hansai "Get out anjima Kya k'arasan" sai datayi kira sau wajen 10 san nan aka d'auka daga can Mace ce tayi Magana "plss yana Aiki ne a office Later Kya kira" tsaki Sady tasa Tasan sakatariya ce ta d'auka nan ta juya baya tayi mai text msg ta aika.
Haka fa take ko yaushe cikin Msg ko kira, so daya ya taba d(auka bayan Sallama ta fad'a A kwainane "Yace plss I'm so sorry don Allah Ki daina kirana" d'if yakashe. kamar ta fashe a wan nan saboda Haushi ,time faruq ya kira tayi tsaki tama kashe Phone din agaba d'aya.
*After 2 month*
Fad'a sosai akai tsakanin Nazi da Sumy Shi ya nace kan yana san Hansai don har Dena d'aga kiran Sumy yayi, da yake Sumy nada fad'a yasa ta biye mai sukayi kaca-kaca Yace bazai kuma zuwa gunta ba hakan itama tace inde hakan ne sede su Rabu domin bazata yarda yana kunya tata ba, dama ta san Mayaudarin ne yau satin su d'aya kenan.
********
Wan nan damar ce tasa ya saki jiki ya juya akalarsa Bangaren Hansai ,har saida ya samo Number dinta,haka ya tasam ma kiranta ba dare ba rana, yawan kiran Hansai da yake a waya yasa take sata a silent domin ta rasa inda ya samu sai dare yake kira tsoro ke cika ta domin tun d'aukan da tayi daga farko ta gane shine bata sake ba ,hakan sai karaci kiraye -kirayensa ya Hakura.
Umma Mama Sumy da Sady duk suna suna zaune a babban falo inda suke hirar Amare su Zuby watan su Shida da aure suna kallo Suna hirar su. Anty ma ta shigo ta zauna Anayi da ita.
Hansai kuwa tsaye abayan Sady agefe tana yi mata tsifar kai wayatar ta dake sak'ale a bakin zanin ce ta tayi k'ara, ta zaro ta sai kiran ya d"auke,ganin ya katse sai ta aje a bakin kujera.
Wani kiran ne ya kuma shigowa Sumy kam a kusa da wayar take nan idon ta ya kai kan Screen din 'yar k'aramar wayar nan tayi tozali da Number d'in Nazi domin ta hardace ta tsaf wani tashi tayi har ipon dinta ta fadi k'asa.
"Ke Hansai wan nan number waye?" cike da tsoro Hansai ta hau in ina ,"ba dake nake talk ba?" Hansai tace. "Nima ban sani ba."
"Uhum baki sani ba me idona ke gani ehe?"
Hansai tace "Yi hkr wlh bansani ba, Don contacts 6 ne A wayana Daga na Anty sai Baba sai taki da ta Sady da Uncle" wani Zazzafan mari ta bawa Hansai,karamar k'ara tasa ta D'urk'ushe akasa tana kuka.
Anty tace "me tayi maki Sumy? Mama ta juyo "haba Sumy me tayi maki?"
Ragwaf Sumy ta zauna tace "Mama tun Randa Nazi yaga Hansai yake min A binda ya gaya dama,yanzu kusan watan mu d'aya da B'ab'ewa, dalili Yace wai dole yana son Hansai nikam ba irin Fadan daba mi dashi ba kan hakan Tun kan bikin su Ya Tuna,ni kam bazan iya had'aka da itaba na Rantsa."
"Shiisa yanzu Naga ya daina kirana Ashe Sun had'e yana bugo mata."
Umma ta Had'e rai "ke Hansai har wuyanki yayi kauri da zaki had'a kafad'a da Sumy har kinyi Gogewar da zaki k'wace Saurayi! to wlh Ki kuka da kanki Ki tsaya inda Allah ya barki domin bakida wani gata kina "yar aiki."
Ran Anty ya b'aci tace "ke Hansai gayan Gaskiya tace "wlh Anty ban san cewa Shi bane kullum Ana kirana da Number ban tab'a d'auka ba kuma ban san cewa Shi bane kuma bana Sonsa."
Sumy tace "shut up! me Nazi zai dake to wlh Ki kuka da kanki."
Anty tace "Tashi muje"
Nan Hansai ta mik'e tana kuka.
Umma ta bisu Galala da kallo "yo dama 'yar aiki in Banda Sangarta har da waya ita da Aka kawo Aiki!
Anty ta juyo "Umma kenan sai kuma akace 'yar Aiki ba Mutum bace ,ba fa Wanda yafi wani, face mafi tsoron Allah."
Mama tace "ku bar Maganar, ke Sumy ku shirya kawai tunda su Dady basu san cewa bakwa tare ba."
Umma tace "yadai kamata."
*Bayan satittika*
B'angaren Nazi kuwa ya rasa yanda zeyi Saboda kin D'aukan kiran Hansai duk ya fita Hayyacin sa gashi harga Allah yana missn Sumy sede fad'anta ke hadashi da ita. Amma dole ya kulata domin yasan Dadynsa bai san Sun b'ata ba.
dama Ummansa keso yayi Aure ko ya Dena shigar Swag,tabbs yasan Auren sa da Hansai ba mai yuwuwa bane tunda batta sonsa gashi kuma yar talakawa Amma tabbas yana son ta.
K'ara kiran ta yayi jiyayi ta dauka farin ciki ya samu kansa ciki ,siririyar Muryar ta ta doki kunnen sa ya lumshe ido.
Nan Ta fashe da kuka "Don Allah kadena kirana ,sabili da kana had'ani da Mutan Gidan mu,kana cutana kadena banso kayi hkr ka rike wadda ke sanka ni na gayama inada Miji ku ni ba yar kowa bace face yar talakawa, pls ba donni ba don Allah kadena kirana Ngd da soyayyarka gareni." kit ta kashe wayar
Tsai yayi da wayar a hannu ya daga kai sama idon nan yayi ja sosai.yadan mike dole nabi Shawarar Abokina na koma gun sumy mu shirya, Bazan so A dinga k'untatawa Hansai akaina ba, domin so mai sonka, son maso wani kuwa k'oshin wahala ne.
hakan kuwa akai ya nemi wayar Sumy Sam taki d'agawa.
Wajen Kwana 2 yana Try Amma bata d'auka da kyar da Sid'in goshi Abokinsa ya shirya su ta hak'ura suka koma Soyayyar su kamar da.
By
Queen meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[5:52pm, 23/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣37❣
*FEB,2017*
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION(NWA)
_Sadaukarwa ce Ga basheer Usman Family's_
***********
RANAR MURNA
Wajen K'arfe 12 na Rana Lami ta dira A abuja Hansai na Tsifar kai A kusa da Fulawowi Ta gano Lami nik'i da kaya ta shigo da sauri Hansai ta je ta Amshe ta tana Murnar Ganin ta. Lami tace "ja'ira to tafiya nazo nayi dake."
Tsalle ta daka "haba Wayyo Dadi" Nan suka shiga side din Anty itama tayi Mamakin Ganin Lami tace "Aa Lami kece haka da tsakar rana kinsha hanya" zama tayi Wallayi kuwa tafiyan Gaggawa ce ta same Ni Shi Baban Hansai da kansa yaje guna yace amaida ita za'ai Mata Aure wlh kuwa,shiisa kika ganni."
Jikin Hansai ne yayi sanyi hakama Anty.
Bayan taci ta huta tayi Sallah Anty tace "Amma inaga sai de Gobe zaku tafi kinga yau Alhaji be sani ba" Lami tace "bakomi yau da Goben Ai duk dayane."
Hansai kuwa suk'uk'u ta dawo Jin cewa za'ai Mata Aure Sam se taji bata san komawa bata san wa za'a Aura Mata ba Amma ta basar.
har ta gama karfe 5 dai -de Iya tayi mata kitso me kyau.
Washegari Misalin k'arfe Bakwai suka gama Shiri Anty ta fito da kayan tsaraba hili Atamph, Shadda su Takalim kaya de turmus da sarka k'aramar Akwati tayi Mata tace taci Biki dasu .
Kuka sosai Hansai take taje sukai sallama da Umma da Mama su ma suka bata Atampha kowacce, taje gun su Sumy da Sady ma sukai Sallama sabo akace turken wawa koda ba zaman Dadi suke da itaba sunji rashin tafiyar ta .
haka dai duk sukai Sallama Anty ta bada kudin Aiki 200k san nan ta bawa Lami Dubu Goma da kudin Mota su Mama suka bawa Hansai dubu Biyar,da kuka ta tafi .Anty suka tafi Driver ya tafi kai su tasha.
Shekara uku kenan da zuwan Hansai Abuja yau Gashi zata koma don Ai Mata aure ,to muje zuwa.
*Mangalu*
Sai wajen 2 suka Shiga Mangalu A gajiye taxi ta aje su a k'ofar Gidan Suka Firfito da kayan wasu yara suka daukar musu suka shiga ciki, tun A soro take Jin Maganar Jummai tana Maraba ganin yara na shiga da kaya da gudu Hansai ta Rungumeta har da kwalla.
Jummai tace Lami "kede sannu ya hanya?" nan Lami ta fito da 200k "ga kudinta Ni dama tun acan aka ban nawa, ta dauki wasu kayan tace na tafi domin so nake nake gida na huta."
Jummai tace to "angode Lami Allah ya saka da Alheri d'awainiyar da ki kai da Hansai" tace "Amin."
Bayan firar ta Jummai tace "naji Dadin ganinki fes Hansai kamar dama can A birnin kika rayu, sai k'amshi kike" Dariya tayi suka shiga daki .
Tayi sallah taci Abinci suna hira da D'an Jummai da ya dawo daga Boko Jummai ce ta shiga d'akin Lokacin Hansai nata fito da kaya.
Tace "inna wai ina Baba Gwamma ne? Nasan dai Baba ba yanzu zai shigo ba.wai Da gaske Aure Za aimin?"
Jummai tace Eh Haka dai naji Malam ya gayawa Lami Amma de Anjima maji Dalili."
Zaunawa tayi "Lalle Hansai na yarda Dan Adam ba abakin komai yake ba,duk iskancin Mutum to akwai ranar kin dillanci ,wato Ranar da hajjar Maigari ta cika,duk zalincin Mutum Karshensa bai da bai kyau."
Hansai tace "Gaskiyane Inna"
"Ai In gaya miki tun Lokacin da Larura ta samu Mudi na fadan da sukai da. Abokan sa, da suka yayyanka Shi, Gwamma ta tashi hankalin ta gani take kamar Ni nayi mai Asiri har abokan suka samu dama akan sa, akan hakan ta sai da Akuyar ta taje gun boka, wai ya bata Maganin da zata samun don na nakasa ,duk wan nan Abu da take bata san nasan Abinda take ciki ba, domin da kunne na naji tana Gayawa Mudi dake kwance yana jinya kan sai ta dau fansa akaina."
"Hakan tayi Abinci ta zuba min duk don naci nikam tana kawo wa na zubar , tun tana zuba ido ta ganni daram nan ta dada tsangwama ta nikai Addua naketa zubawa kan Allah ya kawon Dauki."
"Bayan kwana biyu Mudi ya warware ya koma gun shedanin A bokansa sati biyu tsakani fad'a ya kaure kan kud'i inda mudi Yace bazai bada na wajen sa ba,domin bai dena Halin nasa ba na bunsu sace-sace, nan suka tasar mai Yace kudin nagun Maman sa."
"Washegari sai gasu kuwa! Lokacin bakowa Gidan Dije ta tafi Tallah ,nima na fita Malam baya nan sai Gwamma kawai ,suka shiga Mudi ya kasa ta ya tsare Gwamma Daga d'aki ta dinga d'uro musu Ashar wai ba zata bada kud'in ba ta cinye in na karfi ne su kwata."
"Da yake su 'yan zamani n,e sukace idan ba zata bayar ba se Sun illata ta, mudi Yace ta bayar kawai ya hkr, domin yasan halin su, Gwamma har da buga tsalle tace ba zata bayar ba tana zagin su kan kace me! Sun zaro Adda da wuka nan suka hau fada da Mudi .Gwamma har da d'auko tab'arya ta kwad'awa wani akai, kan ya fashe Jin zafi ya Shammaci Gwamma ya Lafta Mata Adda a hannu da k'afa dayan ya yanki Mudi a hannu ganin Gwamma ta Fad'i k'as kamar mara yasa suka arce."
"Ba adade ba, aka kaiwa Malam Labari ya dawo aka kai ta Asibitin cikin gari."
"Satin ta d'aya suka dawo duk ta fita Hayyacinta mai hali baya fada halinsa, tana cikin ciwon ma bata daina Rashin kirki ba, hakan ta cigaba da yiwa Malam abinda ta ga seda tayi wata daya san nan ta warke ,nan ma ta kuma sai da akuyar ta wadda ita kadai ta rage mata ta tafi gurin boka."
"Adalilin zuwan ta gidan Boka ne, Mota ta Bigeta m wan war tayi atiti, badon ta da nisan kwana ba data shura,nan aka kaita Asibiti,gashi wanda ya buge tan ya gudu, ganin yanda k'afarta daya data dagargaje aka yanke taci kuka ganin tadawo Gurguwa."
"Satin ta Daya da fitowa A Asibitti ,Malam ya zaunar da ita yana Mata fad'a,kan tayi hankali ta dawo Matar kirki, tashin farko ta Lailayo Ashar ta danna mai tare da Ambato babarsa da ta Dade a kushewa ta zaga, Harkuka yayi shikam Yace inde Itace Autar Mata ya saketa bazai iya zama da ita ba."
Ta b'ata tarbiyar 'ya'yanta Dije duk kauyen nan ba Wanda take shayi ga fada da maza ko ita Gwamma din ce tai Mata magana zaginta take.Duk halin gwammar ta kwashe sarai.Malam so biyi yana sata makarnta tana cire akanta,Mudi kuwa yazama Abinda ya zama baya kwana agida ma,ba irin fadan da Malam be mai ba kan kin karatu da sana a yaki har kaishi gun bakanike yayi don Ya dinga koya yaki ,duk sa aninsa Sun san me suke wasu ma sunyi aure,To ta Riga ta bata musu Tarbiya."
Hansai taja Numfashi "Allahu akbar Wanda yadau Duniya da zafi haka zata zo mai."
Jummai tace "yo ai Duniya tafi bagaruwa iya jima. Wanda Yace tukunyar wani bazata tafasa ba to nasa ko dimi bazaki ba."
Hansai tace "to yanzu tana ina?"
"Jummai tace "tana Gidan iya sema kin ganta abin tausayi ga ba k'afa duk ta Rame, iya kam sai hantara ce ke shiga tsakanin su ,Dije kuwa ko kallon ta batai balle ta taimaka mata sai de yawo.wataran Haka zata zauna da yunwa,se Iya ta samu take bata."
Hansai tace "Allah y kyauta."
Adai-dai time din Baba ya dawo yayi Murnar ganin Hansai, don Hansai har da kuka Tayi saboda aganin sa.
Baba ya zauna Yace "Allahu k'adirun Ala man yasha 'u tabbas abinda Allah ya shirya babu makawa tsaiya faru.
ya kalli Jumaai jiya bangaya miki Dalilin dawo da Hansai ba ko? to Dama dalilin dawo da ite shine Anga iyayenta na Asali."
Jummai ta mik'e tsaye tare da dafe k'irji! "da gske Malam? kai Alhamdlh."
Ita kam Hansai suman zaune tayi.
By
Queen meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[10:38pm, 25/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣38❣ *FEB,2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*Fans kunjini Shiru ko? whtsup nawa ya samu Matsala ne shiisa Amma yanzu Normal ,hope kuna fyn,thanks for support nd care,😘*
***********
Kusan mintuna ta d'auka san nan ta d'ago kai cike da Hawaye tace "Allahu Akbar" Baba Yace "ki godewa Allah."
Hansai kan cinyar Jummai ta dora kanta tana Matsar Hawaye.
Jummai tace "Malam to ya abin ya kasance? taya aka same su?"
Dariya yayi "aike dai Jummai bar ikon Allah,Shekaran Jiya Sarkin kasuwa Yazo mani da Maganar, ina Gona yaje can da yake kinsan Ni bana zuwa kasuwa.
To ya zo mani da Maganar wani bawan Allah da yazo dai+ dai Babban Titin nan me kud'i dashi yana kuka Acikin motar sa kuma motar baud'e, su dai Sun rasa dalili yasa sukaje suka same shi.sarkin kasuwa Yace Alhaji meya faru?
Juyowa yayi Yace bakomi bawan Allah kawai wani abu nake tunawa anan hanya, Malam ban mantawa da wan nan Hanya Domin shekara Aru- Aru hanya tace duk shekara sai naje wani kauye gaba nan Dan tai makon bayin Allah Marasa k'arfi."
Akwai wata shekara da Tsautsayi ya afka Bomb ya tashi da Tsautsayi nazo wucewa dani da Matata da yarana Biyu to anan ne muka rasa D'aya har ila yau da nake maka Magana bamu sake jin D'uriya ba shiisa koyaushe nazo wucewa sai na koka saboda tunowa da Gudan Jini na.
Jin hakan Sarkin kasuwa ya shiga tunani na tsawon Lokaci nan ya tuno da ita Hansai dake guna yace zai Gwada sa a ko Allah yasa adace ,shine fa Mutumin ya Gigice Yace akaishi gun Mutumin, haka muka gama Magana kan cewa nan da kwana 3 zasu zo don tantancewa.
Yanzu dai Shi muke jira watak'il Gobe ko Jibi."
Jummai tace "Allah kasa su zamanto cewar shine iyayen nata da nafi kowa jin Dadi Malam Yace "wlh nima haka."
Hansai kuwa kuka take mai tsuma rai kamar ranta zai fita "Baba Yace Hansai keda zaki godewa Allah kuma kike kuka."
Ta d'ago "baba kayi hk'r Ni kune iyayena bana son Rabuwa daku." dariya Jummai tayi ai mu dake mutu ka raba ,Amma hankalin mu zai fi kwanciya in muka gansu Hansai,yau kiyi ta Addua Allah ya tabbatar da Alheri."
*8pm*
Hansai da Jummai na zaune sai hira suke ga Baba agefe yana cin Tuwo Abdullahi yana bacci Hansai ta fito da kud'in hannun ta dama ita suka d'amkawa ta mik'awa Baba tace "Gashi Baba kayi Jari dasu."
Baba Yace "haba Hansai kije ki wahalar Aiki mu daci"
Dariya tayi "Aini ba abunda zan dasu" Jummai tace "naki ne fa! nan baba Yace to ba matsala Angode" Hansai tace "baba ka daina Godiya Saboda Ni na cancanta na Maida muku da Alkhairi da kukai mini domin kun Nunan duk-kan k'auna."
Baba Yace "Allah ya miki Albark" Hansai tace "Amin."
Kamar An wullo Dije ta shigo Baba ya daka Mata tsawa "me kike awaje yanzu?"
Turo baki tayi "banjin bacci" Baba Yace "Allah ya shirya" tashi tayi zata kuma komawa "baba Yace "ina kuma zaki?"
Tace "Innarmu."
Hansai tace "haba dije Baban Kike gayawa Haka? gashi kinga dare ne fa!
"Eh to ina ruwanki ,naji inna tace na koma me zan tunda ba uwata agidan."
Ta fita tana gatsina.
Malam ya aje kwanon cike da damuwa Yace "Gaskiya Gwamma ta cucueni, duk ta batan tarbiyar yara yanzu ace ina magana Dije bata ji?" Jummai tace "sai hkr fa da Addua."
Gidan iya Dije tayi ta shiga d'akin da Gwamma ke ciki k'afarta da aka guntile na ciwo tace "Dije zo ki rik'eni zan mik'e"?"
Tace "nifa Bazan ba karki takuran."
Gwamma tace "Ni kike gayawa haka?sai kace sa arki." ko magana bata kumai ba tayi zamanta.
Gwamma ta matse k'walla halin da take ciki kenan ba mai Kula da ita kowa ya gujeta hatta iya hantarar ta take gashi yayanta ma nayi mata saboda rashin Tarbiya.
Mudi ne ya shiga yana fito Gwamma tace "Yawwa mudi, kayiwa Dije fad'a kan abinda take min."
Ya juyo "Nifa Gwamma ba ruwana da harkanku abin Babana ya ishen."
Kuka ta saka da k'yar ta mik'e ta shiga Band'aki. iya ta fito "yanzu ke Dije uwar taki kikewa haka?"
Dije tace "nifa banyi komai ba."
Iya tace Aa kyace baki komai mana tunda baki da tarbiya."
Nan Gwamma ta fito "yawwa iya ki gayawa mata ko taji."
"Yo Gwamma ai dama duk uwar dabata bawa yaranta tarbiyya ba ,tace 'ya'yanta sukad'ai ne 'ya'ya to wallahi abin kanta zai dawo, kede Gwamma kin b'ata Rayuwarki data yaranki,uban yara ya sasu Makaranta ta Allo ma kin hana, ba abinda suka sani haba kin musu Tarbiyar banza, ai wlh kad'an ma kika gani kin d'auka ban san bin Bokayen da kikai ba,kika mallake Miji da kishiya ko,har 'yar ruk'on nan ma haka kikai ta zalintar ta, ke 'ya'yanki ne yara miji an maida Shi hotiho, to ai ga irin ta nan ki fara tuba ga Allah tunkan ki kaiga kushewa."
Gwamma cike da haushi tace "to naji."
Iya tace "ai baki horu ba.
Ke kuma Dije uwarki komai rashin kirkinta to ki bita domin Allah ne Yace abi iyaye."
Nan ta juya ta shige D'aki.
Gwamma ta zauna da Guntulalliyar k'afarta zuciyar ta na danasani Amma Girman kai bazai barta ta nuna ba.
Domin aganin ta ta fad'o (lalle Gwamma baki horu ba).
*Washegari.*
Tun safe su Malam ke Tsammanin zuwan baki Amma shiru duk Jikinsu yayi sanyi waya ya bugawa sarkin kasuwa ko Sun zo yace mai Aa.
Haka aka wuce Ranar Amma shiru ba Labari sai kuma Hansai Jikinta yayi sanyi sai kallon Hanya take har dare ba Labari,cikin sallar ta sai rokon Allah take Allah yasa burin ta ya cika.
Cike da Jimami ta kwanta.
*Washegari Da karfe goma Ranar Laraba.*
Hansai tayi wankanta tayi kwalliya tayi kyau kai kace zuwa k'auyen tayi ta Tambayi gun Jummai zata je ta D'an zaga gari.
Tafiya take Ahankali tana tuna irin Rayuwar da tayi baya ak'uyen Muntari ne ya fad'o Mata kawai sai tayi Hanyar bayan Dutse wurin nan kamar yanda yake sai sassak'e wasu dutsunan da akai.
Zama tayi tana ta tunani da Murmushi ga iska na kad'ata ,tayi kusan Awa d'aya a zaune yasa ta mik'e don ganin Dad'ewarta tayi Hanyar Gida.
Daga can nesa ta gano wasu shimfid'ad'dun Motors guda 2 ak'ofar Gidan su,Badon tayi zaman Abuja ba, da sai ta tsaya ta Lailaya su.
Gaban ta ne let dukan uku- uku har taje daf da Motar ta tsaya bakowa aciki yasa tayi hanyar shiga Gidan a sanyaye.
Tun shigar ta taga Mutane Birjik a Babbar tabarmar Baba dake zama Asoro.
Cak! ta tsaya tare da k'arewa Mutan gun kallo har tazo kan wata d'anyar D'aby wadda taga kamar ita.
Kuka taji an fasa "Wallahi ko ban ga shaida ba wan nan Baby Husy ce!" kallonta ta maida kan me Maganar taji wani irin Fad'uwar gaba.
BY
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[11:19pm, 25/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣39❣ *FEB,2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*************
Rungumeta tayi ta d'ago hab'ar Hansai tace "tabbas wan nan itace" dai de Lokacin kyakkyawar Budurwar ta shiga Gidan Dady yace "Daga d'auko Album kin zauna ko?"
"No Dady ke ne ban gani ba Amotar sai dana duba."
Juyawa Hansai tayi sukayi Ido hud'u da budurwar Suhaima tace "You!" nan ta yar da Album d'in data d'auko ta Rungume Hansai "Mum wlh itace wadda nake baki Labarin suna kama da Arif wadda na ganta a gidan Anty."
Jummai ce ta fito rik'e da wata leda ta tsugguna ta aje Gaban Malam da smSarkin kasuwa, nan ya d'auko ya bud'e hoto ne guda biyu Daya ajiki Hansai ce da Malam aka d'aukesu a Ranar da aka tsinceta sai D'ayan kuma ita kadai ce nan ya mik'awa Dady ya karba Yace Allahu Akbar."
Nan ya d'auki Album ya duba sak! itace ce ba makawa Hansai 'yar su ce .Domin shigar Jikinta an Musu hoto ita da Hassanar ta.
Malam ya d'ago wato 'yan biyu ne kenan!"
Baba yace "tabbas twins ne" .
Sarkin kasuwa yace "mun godewa Allah."
Nan Dady ya kalli Suhaima yace "wan nan itace first Born dita Suhaima, sai su Twins Hassana Da Hussaina,sai kanin su Arif gashi nan."
Hansai dake bunsu da ido tana sharce k'walla sabida Jin wani sonsu da take.
Mum (Fatima) shine sunan ta ,ta d'ago ta kalli Suhaima tace "Amma ace kije Gidan Anty ki kasa gano kamar da suke da Hassy haba Suhaima."
Suhaima tace "Mum wlh tunda Naganta naji ina kaunar ta Sam abin bai kawon ba,don naji Ance ta Mutu."
Dady yace Aikin san dama su basa kama da Junansu, sosai Hussaina tafi kama da Mahaifiyar ku, ita kuma hassana da ni shiisa."
Baba yace "Masha Allahu komai de Daga Allah ne."
Nan Hassy ta zo ta k'urawa Hansai Ido ta d'an tab'a Hancin Hansai ta Rungumeta tana Hawaye I Missd u dear ,I luv u my Twins sis."
Itama Hansai ta Tungumeta ta na Tsiyayyar Hawaye "Me too sis."
Nan aka zauna sai Maida zance ake Hansai sai kallonsu take A ranta tana yaba su dukkansu Masu kyau Ashe wan nan finest Baby din Yayata ce Arif kuwa D'an Lukuti sai satar kallonta yake ,Mum Ma sai satar kallon Hansai take Ganin kamar da suke da ita.
Dady yayi gyaran Murya "yanzu yaya Sunanta? Malam yayi dariya sunan mu na k'auye take karb'a."
Jummai tace "Hansai
sunanta" dariya Arif yasa
hassy ta zungureshi, Hansai tayi Murmushi ganin yanda suka Birgeta ashe itama haka take ta yan uwa Masu kyau had'ad'd'u.
Mum tace "dama ba acanja masu suna ba,Hassana da Usainar su ake ce masu Sai mu da muka tak'aita muke cewa Hassana Hassy."
Malam yace "itama 'yar tawa tunda ga sunanta Wato Husaina sai Ana cemata hakan."
Dariya suka saka dukkansu.
Dady sa bakinsa yak'i Rufuwa yace "ai Malam karkaji irin dad'in da nakeji da ya zamanto irin ruk'on da kukai mata kun zame yan uwa domin Husaina 'yar kuce."
Sarkin kasuwa yace "Masha Allah ai tun Lokacin b'atanta mukai ta bada cigiya shiru."
Dady yace "ai A lokacin Bama hayyacin mu, domin duk asume muke Direct kano aka wuce damu sai da Mukayi 3 weeks akwance Domin Hassana ma mun d'auka Mutuwa zatai itama domin mun Saddakar Husaina ta mutun, Amma duk da Hakan bayan warkewar mu sai da Mukazo munka bada cigiya sai aka cemana ai da dama yara Sun mutu dai Muka hkr.
Amma Mahaifiyar su kullum Maganarta ai na hussaina na raye da yake Munfi zama a Landon to duk Lokacin da Mukazo Nigeria sai na biyo hanyar nan domin ina tunawa da ita."
Malam yace "ikon Allah domin shike k'adarta k'addara Allah abin godia."
Nan sukayi sallar azahar se kuma suke shirin tafiya.
Malam yace Hansai ta had'a kaya ta bisu nan tasa kuka dum da farin cikin dake gareta,Jummai ma kuka take tace "Hansai kibi iyayenki ai bamu Rabu ba.
Mum tace "iyayenki ne suma ai" Dady yace "lalle me iyaye hudu" aka sa Dariya nan taje iban kayanta Mum tace ta bar su a bawa wadanda basu dashi.
Haka Suhaima da Hassy suka k'an-k'ame Hansai Arif na gefe yana binsu Mum da Dady suka tsaya ya fito da check ya Rubutawa Sarkin kasuwa 1million, Malam kuwa check na 2million ya mik'a mai duk suka k'i karb'a k'arowa yayi ya Rubutawa Jummai na 500hundredk haka sukace su bazasu karb'a ba domin Hansai 'yar su ce komai sunyi ne don Allah da k'yar da sid'in goshi suka karb'a."
Dady Yayiwa Wani Driver din sa Magana kan ya karb'i check din yaje ya ciro musu.
Shamsu yace "oga driving din fa?"
yace "no Madam ta tuk'a, ka tsaya koba yauba har zuwa Gobe in Sun shirya sai kuje tare kacire Musu."
Da k'yar aka B'anb'are Hansai daga Jikin Jummai tana kuka tana kiran Baba da Jummai dak'yar tayi ta saduda suka fita.
cin-cirindon Mutane ne cike a awajen Motocin kan al' ajabin cewa wad'an nan First class d'in sune Familyn Hansai haka Hansai Da suhaima da Hassy da yasir suka shiga mota d'aya Driver yaja.
Mum da Dady suna Mota d'aya itake tuk'a su Jummai da baba sukai ta D'aga musu hannun da Alk'awarin dawowawr Dady gun Baba kan wani Aiki da zai Sama mai.
Fuuu! Motocin suka fita daga k'auyen Mangalu suka mik'a kan Titin Bunkure suka santali Hanyar kano.
Note -Hansai yanzu ta koma Husaina Husy ,don haka zakuji Ana cemata Husy.
By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.
.
. [11:25pm, 26/02/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣40❣
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
*_Wan nan page din naki ne @Ngileruma Tnz for ur luv nd care❤_*
*********
Direct Gidan Maman kano sukaje wajen k'arfe Biyar Jikin Husy yayi sanyi game da Mamakin meya kawosu Gidan Maman Anty Rabia.
Tana zaune Ita da Dan Autanta suna hira Suka shiga Falon Maraba tayi Masu, tace kuce da Ibrhm d'in kuka Mum tace Eh wlh Mama,nan dukkan su sukabo lafiyar kujeru, tace Aa Arif Dan lukuti har yanzu kanacin kayan fulawar ne?"
Dariya yayi , Tsai ta tsaya da maganar tace "to Hansai yana ganku tare ikon Allah sai naga kin saje kuna kama dasu ,keda akace Aure za'aimiki kodai Gidan Aiki kika canja?"
ba Wanda yace kala sai da suka zauna suka huta.
Dady ya kallai Maman kano yace "ikon Allah Husaina ce yar wajena data b'ace da dad'ewa wadda akace ta mutu."
Tafi Mama ta dunga Amma naji kunya yarinyar nan so biyi tana zuwa gidan nan inde za a kaita Aiki abuja ko za a maidata kasan gun Rabia tayi aiki.
Ashe ni nan Jinina ce ban sani ba ,shiisa nake k'aunar ta mana,koda yake ai duk mun Sadak'ar ta mutu ne shiisa Sam ban kawo ba
ikon Allah hansai zo nan Naji d'iminki."
Arif yace "no Maman kano yanzu sunan ta Husy not Hansai." Dariya aka saka dukka nan ta kamo Hussaina tace "wlh se yanzu nake ganin kamarta da Arif ikon Allah Ashe ba baya ba kike da kyau kunya ce ta kama Husy."
Haka sukai ta Maganar anan ta d'au waya ta Sanarwa Anty Rabia har da kuka tace Mama wlh shiisa nake k'aunarta har Raina Ashe Jinin mu ce."nan mama ta bawa Husy (hansai) waya suna ta waya tana tambayarta su Mubarak.
Bayan sun gama wayar Mama tace ni din nan da kike ganina Husaina Mahaifinki K'anina ne Uwa da d'aya Uba daya.
Mu 'yan Asalin nan kano ne Fulanin Garko Amma iyayen mu duk anan cikin kwaryar kano muke.
Kinzo cikin Arxiki Domin dukka familyn mu kowa nada Hannu da Shuni.
Babanki ya rik'e muk'amai A Nigeria irin Lucky Man din nan ne tun yana yaro shiissa tashi d'aya yazamana Done ku kanku a Landon aka haifeku acan kuke da zama yanzu hakan Ambassador ne na Nigeria to London,kuma yana kasuwanci Akwai taimakon ma kasa dashi ,Allah yasa kuyi koyi da Halin sa na taimako.
Mahaifiyar ki kuma ita Asalinta 'yar Adamawa ce fulanin can ce iyayenta Malamai kuma suna da abin hannu kakanninki duk suna nan na gun uwa Amma na Dady kuma saura Kaka mace Mahaifiyarki nada kirki da son jama'a batta k'yamar talaka kinga an raba ke kike kama da ita Hassy da Dadyn ku."
Dariya suka saka Dady yace kai Maman kano duk wan nan bayani haka?"
Tace yo Meye aigwanda na sanar Mata tunda ya zama dole.
tace yanzu dai sai an kwana 2 kyaje ki ziyarci Dangi."
Dady ya mik'e to ni na tafi Masallaci,Bayan fitarsa dukkansu sukayi wanka Saboda gajiya wajen k'arfe 9 na Dare kowa yayi bacci Abinsa na gajiya in Banda Hansai dake ta Sallah tana kai Godiyar ta ga Allah.
Sai Suhaima dake waya da Saurayinta.
*Washegari*
Hassy da Hussy na zaune sai D'an hira suke,Hassy ta ce ki saki Jikinki Tweeny"
Suhaima dake gefe tana taje kai tace "nikan Husy kinyi School ko?"
Tace "eh mana nayi Junior Class sai natafi Aiki Amma acan Anty ta d'aukon me Lessn har seda nayi Waec."
Hassy tace "Weldone Amma banso kikai Aiki ba",Husy tace "sis Ai ba yanda Mutum zai kaucewa k'addarar sa"
Suhaima tace "tabbas" "Hassy plss ban phone naki zan duba wani abu"
hassy tace kai "Ya Suhaima chatin nake"
"Ok dama bakya gajiya ai"
Hassy tace "sorry sis take it"
Husy sai kallonsu take sun bata sha'awa .Mum ta shigo tace "Oya kowa ya shirya 9 zamu tafi" haka kowacce ta shirya Hassy ta d'auko wani Material me kyau da tsada me ratsin Pink ta bawa Husy itama ta dauko wani ta saka cif sukai Ma Husy da yake kusan Jikinsu iri d'aya ne Suhaima tayiwa Husy kwalliya Hassy tace "wow my twin sis kinyi kyau"
Murmushi tayi "thnks Sis"
Hassy tace " Oya zomi Selfie🤳🏻 nan Hansai ta tsaya Hassy ta saita Ipon dinta ta daukesu sunyi balain kyau sai kamar su ta fito Rad'au.
Direct ta dora su kan Instrgram tana she's my twin sis.
Sai Dariya suke Arfif ya shugo yace wow "kunyi kyau Amma ya Suhaima Ai Husy tafi Hassy kyau ko?"
Hassy tace Lallema Lil Bro nidin?"
"No Hassy ai gaskiyane kefa bakki da Wushirya" Gwalo yayi mata.
Hassy tace komai NO Mr No kawai"
Yace "Naji tadai fiki kyau"
"Ai sekayi tayi"
Suhaima tace "zancen Gaskiya husy tafi ki kyau."
Hassy tace "Wayyo koma dai me zakuje Tweeny Dina ce munfi kusa kano da
Jigawa."
Ita dai Husy Dariya kawai take yi sai kallonsu take. Nan duk suka fita sukayi Breakfast Dady ya kalli Husy yace ya kika kwana My Lovly douter?"
Tace "Alhamdlh Dady" Mum ta kamo ta zo nan my Twin" nan Husy ta agida ta.
Hassy tace "shikenan ta k'wacen fada" dariya Arif yasa dama Dan adawar tane yace "sede ki hkr."
Dady yace "haba keda ita ai duk d'aya ne nan suka gama suka d'au Damarar tafiya Mama ta Rungume Husy "Allah yayi maki Albarka" ta bata wani Leda nan suka tafi.
Direct Gidan Kakan nin su suka tafi nan ma Sai ganin Husy ake yar dangi kakarta kuwa harda kuka tamkar ta Maidata ciki sai wajen 12 suka dau Hanyar Birnin
Tarayyya,hansai ta kunshe kai tana kukan tuno su Malam da Inna Jummai.
Muje Zuwa Dai
0 comments:
Post a Comment