Tafiya akace yankin azaba hakan su Husy suka yi tayi har suka je Abuja direct Osokoro sukayi ainihin Gidan su Wani Babban Gida suka dosa Hon sukai Maigadi ya wangale gate Nan Motocin suka shiga da gudu mai bawa Fulawowi Ruwa ya bud'e Musu "Barka da dawowa Oga" Dady yace "yawwa."
Su Hassy ma duk suka fito Husy tasbihi tayi Azuciyarta domin ganin Gidan tamkar ya fad'o kansu saboda Girma da kyau tamkar da kwali akayishi,duk haduwar Gidan su Sady sai taga yazama Mara kyau akan wan nan ,Lalle kafi wani wani yafika.
"Twinny tawo mana!" sai Lokacin ta dawo da kanta kansu Arif yace "idi kaga Husainar Hassy" zaro Ido yayi "haba ikon Allah ko itace wadda ta bace ko?"
Arif yace "yeah"
Nan Maigadi ma ya tawo yace "ikon Allah gashi kuma kamar su d'aya" nan suka yiwa Mum da Dady barka suka koma.
D'uruwa sukayi cikin Gidan Husy ta kuma sandarewa domin falon ma kamar ba a Nigeria ba, Matatta kalar bene 2 ne a falon Wanda kowanne da Decoration din sa Dady da Mum sukai d'aya su Suhaima kuma sukayi d'ayan Husy ta bisu a baya suka hau, nan taga d'akuna Ajere Guda Hudu a gefen kowane d'aki Flower ce Masu kyau Jikin bangon kuma wasa Frames ne masu kyau, can gefe kuma Dan karamar Dining table ne me kyau Black me kujeru 3 nan Arif ya shige nasa D'akin, haka Suhaima Har ta shiga ta fito.
"Sis Husy Bari na nuna miki d'akin ki don tun jiya Dady yayi waya aka shirya Miki shi."
Nan suka shiga bud'e baki tayi don duk haduwar d'akunan su Sady wan nan ya zarce nasu (sawun giwa ya zarje na Rak'umi ) wani gado ne Purple madai-daici da Cover da Mudubi Fentin d'akin ma purple ga Decoration masu kyau. Nan Hassy tace "nikam tare da Husy zamuna kwana ki dawo dakina kawai."
Husy tace "Nima dai Nafison mu kwana mu 2"
Suhaima tace ai gadon daya ne can sai de akoma da komai naki can." Mum ce ta lek'o My husy d'akin yayi maki ko a canja?"
Tace "Aa Mum yayi" Hassy tace "Mum so Muke akomar da komai nata d'akina na munfi son mu biyu."
Tace "Okey ba damuwa tunda dama d'akin nada Girma zai cinye."
D'akin Suhaima suka shiga Mum ta kira masu had'a Funiture waya yace nan da awa d'aya zai zo.
Husy sai kallon D'akin Suhaima take ko ina Hoton Suhaiman ne Lik'e a bango Gaban Mirrow kwa kayan Makeup ne turmus nan duk suka zube a gadon ta Suna hira.
Wajen kamar k'arfe 6 ya zo su 2 kamar injina suka Fidda kayan dakin zuwa dakin Hassy suka jera yayi kyau na Hassy Pink nata Purple 7 suka gama suka tafi.
Nan suka koma dakin Hassy tace "wow yanzu ma yafi kyau" husy kam Godia take ga Allah kan Niemar da yayi mata, nan sukayi Sallah tare da wanka Hassy ta bude wardrobe d'in Husy gefe abaya ne da Pakistan sai Atamph da shaadda su Materials wanda ba d'inkakku ba, ga takalma da Jaka nan duk suka fito da Jakunkunan da takalmin suka kai su Mazauni .
Hassy tace "Twieeny yanzu Gobe sai muje akai din.kunanki" husy tace "ok sis.
Arif ya shigo "food is Ready."
Garam ya koma.
Dariya suka saka dukan su suka fita, Suhaima ma ta fito "hi sisters."
Sukace "ya gajiyar tafiya sis?"
Tafe "fine"
Itama tayi wankanta nan suka jera suka sauka k'asa.
K'amshin Girki ne ya doshi hancinsu sai lokacin Husy ta kalle Falon tas iya had'uwa ya had'u tv 2 ce aciki sai Aiki suke ga wani Gabjejen hoto na Art work Dady ne da Mum sai Suhamina Hassy da Arif akasa sunyi bala'in kyau me Art d'in ya iya. Murmushi Husy tayi suna Lura da ita Dady yace "Lovely Douter kema za 'a yi maki za'a dauke wan nan Ayi sabo wanda hardake."
Dariya tayi tace "Ngd Dady" Suna tacin abincin su har suka gama Dady yayi Gyaran Murya "Godia ta tabbata ga Allah Wanda ya k'addara Rabuwar da gudan Jinin mu gashi kuma ta dawo to ku zama Tsintsiya Mad'aurin ku d'aya ku zama Masu san Junanku da Girmama Juna kai Arif Banda raini ku kuma ku soshi Banda Wulakanta Mutane."
Mum tace "ai yaran nawa sai san barka Musammn Husyna."
Dady yace "Husaina ya batun karatu kinyi Secondry ne?"
Tace "eh Dady nayi acab Anan Abuja na karasa."
Au kinyi Zaman Abujan nan?"
"Eh Dady nayi Aiki Gidan Antyn Maman kano"
Nan yace Rabia Matar Alhaji tanko?"
Yace "eh."
yace "ikon Allah."
Mum tace "Allah Sarki 'yata Husaina, d'an bamu Labarin Rayuwar ki."
Husy ta sunkwi dakai kamar zatayi kuka nan ta fara basu Labarin tun bud'e idonta a Mangalu har yau.
Kuka Suhaima da Hassy keyi na tausayawa Rayuwr Husy idanuwan Mum yayi tana matsar hawaye hakan idanuwan Dady ma yayi ja.
Hassy tace sis Duk da *RABUWA CE SANADIN* shiga Hali wannan dalilin ne yasa duk kika shiga wancen wahalar, da ace kina tare damu dabaki shiga haka ba."
Dady yace "Hassana karki d'auka Rabuwa damu ne yasa haka! to Daga Allah ne shiya tsara hakan don Gwada imanin mu da ita Husaina Dana wanda suka riketan, koda tana gaban mu ma hakan sai ta iya faruwa, wani abun shine Sanadin wani dama ita Rayuwa yau bak'i gobe fari,kin gane?"
Tace "eh Dady"
Suhaima tace "Nikam wan Nan Gwamma ke ban haushi wlh Muguwa ai gashi nan taga k'arshen Mugunta,kuma hakan ma bataga komai ba."
Arif yace "ni kuma su Sumy da Sady ke ban haushi Mugwaye don tayi aiki Gidan su."
Hassy tace "hmm Tweeny da tuni fa kina da Aure da Muntari."
Husy batace komai ba sai sunkwi dakai tayi jin gabanta ya Fadi
Suhaima tace "Aikuwa Su Sady sai na Raina musu hankali."
Arif yace "Amma wan nan Lawandin Mugu ne Allah ya kareki, wai Shi wan nan bad Mudi din shine harda wani wulak'antaki wai yafi k'arfin ki,Arif yace kece Ma ai kika fi k'arfin sa." Arif ya sunkuyar dakai cike da Haushi.
Hassy tace "nikam wlh duk nafi tsanar Gwamma."
Suhaima tace "Baba da Inna kuwa Muna k'aunar su sun so Jininmu."
Dady ne yace "ya isa hakan komai yawuce kud'au komai k'addara kuma duk wani Mugu k'arshen sa baya kyau."
Mum tace "hakane Ku manta da komai" ta kalli Husy "sannu Husaina Allah yayi maki Albarka da dukkan ku" suka ce "Amin."
Dady yace "yanzu kan karatun Husaina zan samar mata."
Mum tace saura fa 3 Month mu koma London!ko Anan zatayi?"
Dady yace "Aa" acan d'in nake nufi" tace "maddala."
Sai wajen 10 kowa ya koma side din sa,da tunanin Labarin Hansai (Husy)
*Washegari*
Suka mike Sukayi wanka Husy ta sauka kasa ta shiga kitchen Mum ce tsaye tana yiwa Dady Farfesu nan Husy ta gaisheta ta hau taya ta don karasa breakfast.
Mum tace "Husy Kin ganni nan banida masu dafa Abinci nike Yima Dady."
Husy tace "Yawwa Mum ki kawo ina mana"
Mum tace "haba ai Dalilin daya sa ban d'au yan Aiki Masu Girki ba kenan Saboda su Suhaima su koya, kinga mu ba Mazauna bane shiisa ma ban d'auka ba sai Mai goge-goge kawai kullum tare da Suhaima Da hSsy Muke Hada breakfast."
Husy tace "Mum Tunda Gani Yanzu kawai koba zamanki muna yi kawai."
Mum tace "Yayi kyau douter."
Suhaima ce da Hassy suna suka shiga Suna kirchen din Nan suka saka hannu sunayi suka gama aka kai Dining sukaje suna breakfast.
Wajen 10 suka mike kowacce suka sake wanka suka fesa Makeup,Mum sai kallinsu take Musammn Husy tana godewa Allah.
Falon Dady duk sukaje Arif Na danna computer Suhaima tace zasu Kai dinkin Husy kuma zasuyi Mata shopin .
Nan yace Suhaima ta tuka bai san tukin Motar Hassy saboda tana da Tsoro,sai nan da 1 yr kin dada k'warewa"
Dariya Arif Yasa "Dady wallahi koni na fita iyawa"
Harara ta kaimai "Oho dai Mr No kawai."
Dady yace Hussaina ma Zan kawo Motar ta Sai afara koya mata"
Kudi ya zaro ya basu yace "kuje ku taya Husaina shopin" jin Hakan Arif Ma ya Bisu Nan Suka Lodu a Benz din Suhaima ta kwashe su Gwanin sha'awa,Kyawawa dasu.
Haka sukaje Shoprite suka jido Mata kaya san Ransu suka biya ta gun tailor dinsu Suka jidemai kaya kan Suna san yayi masu express ya gaya masu kudi suka bada deposit,suka biya suka sha icecream san nan suka koma Gida agajiye wajen 1.
Kowanenn su yayi sallah sai bacci Husy kuwa Sabuwar Wayarta ta Kurawa Ido wayar data ke ganin ta hanun su Sady Ashe itama da Raban ta riketa.Murmushi tayi har Wushiryar ta ta fito ta kwanta kan Luntsuman Gadon ta,nan ta kira Inna dama ta bata wayarta sanda zasu tawo.
Daga can ta dauka nan Husy ta fasa kuka "inna Jummai"
Tace "Allah sarki munyi kewarki Husaina"
Tace "ina baba?"
Jummai tace "ya fita?" tace "Dan Jummai fa"
Tace "yana Allo kullum sayya yi kewarki"sun dade suna Waya san nan ta kashe.
Gadon Hassy ta kalla taga sai kwasar bacci take nan itama Batasan sanda ya d'auketa ba cike da farin ciki.
By
Queen Meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[11:00pm, 01/03/2017] 👑Meemi💋: . . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣42❣
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
*Ban manta kuba wan nan page naku ne@ Maryam Oumiey,Juwairiyya, Ummen Yusra & Aysha Maman Umayma❤*
*********
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta wurin Hussy domin Rayuwa take cikin 'yan uwanta cike da 'yanci da walwala Uwa uba soyayya gaya ake nuna Mata sosai. ko tari tayi sai suce meye sis, ko meye Douter wan nan sakewar yasa Husy ta fito ta kara kyau fatar ta tayi kyau hatta gashin ta yasan ta samu canji shima ya dada kyau haka ta sake tsakanin su ta ware dasu komai nasu iri daya ita da Hassy abin sha'awa.
Ganin tana son computer Dady ya d'auko wani ya koya mata nan ya sai mata laptop kirar Apple Already dama su suhaima nada ita ga dalleliyar Motar ta mekyau Red cikin 2 weeks ta iya Rayuwa kenan.
Yau Dady ya sanar ma Mum gobe zasu d'aga Landon don Hutun su Arif ya k'are shida Hassy, dake Yniversty acan dama ita Suhaima ta gama.
Nan suka hau shiri wajen 1 sai ga driver Anty nan yazo zo kuga Murna gun Husy Rungume Anty tayi tareda yaranta.
Anty tace "lalle Hansai!" Husy tace Anty "ai wan nan Old name ne"dariya Anty tasa tace "wlh naji dadi Husy tace wlh Anty nayi missn naku tace ai dole.
Nan Hassy ma tazo suka gaisa dasu Arif suhaima ce bata nan ta tafi saloon.
Hassy tace "Yawwa Anty karki gayawa su Sadyn nan Husy yar uwarki ce ki barsu kawai zami basu Suprise" tace to ba Masala hakan sukayi ta hira har Dady ya dawo suka gaisa sai dare Anty ta koma gida.
*Washegari*
Da Asuba kowa ya gama shirin sa k'arfe 9 duk sun gama komai shi duk sun kulle Gidan Sukai sallama da Maigadi Suka d'uru A Family Motor Driver yaja suka tafi 10 sunje Abuja International Airport Dady ya Juya baiwa Idi sak'o kan ya je Bunkure ya kaiwa Malam.
Husy taso ace taje sunyi Sallama da Su baba da Inna Amma ganin ba time ta kyale nan jirgi ya d'aga dasu Sararin Samaniya.
*Gidan Alhaji Tanko*
Sumy ce tsaye kan Sady A Runfar wajen aje motoci kuka take sosai sumy tace "haba sis yanzu kan Shi Handsome d'in kike kuka ai wan nan abun kunya ne."
"Sumy kina ganin Na buga mai waya yayi man Wulakanci wai baison mace Mara kamun kai,Wai nadena kiransa."
Tsaki Sumy tayi "ai sekiyi tayi dama D'an nacinki ne yazo faruq yanzu Dana fito nan Maigadi je gayan na can waje a waje."
"Bazani ba Cuz I hate him"
Zubaida ce ta shigo da Mota Adaide Lokacin Tayi faka tafito rik'e da Baby boy a hannunta Dan 3month data haifa.
Gano su tayi yasa ta je wajen ta kalli meya sameki Sady?"
Sumy ta gaya Mata ta kalle ta "lalle Sady kina son kiyi Saki na dafe great man irin Faruq ga kyau meye aibun Faruq Kodan kinga Dady na cewa sai masu Naira."
"Hmmm wlh wani Auren me kudin wahala ne azamanin nan ki Auri me sonki da yawa Shi yafi domin wani Namjin wallahi komai kudin babanka sayya taka ka,Naga ishara akaina."
Sady tace "Nifa sis bana sonsa, haba ya k'yaleni kofa Mota baida ita meyaci meya bani,gashi bai iya dressn ba."
ta kalli Sumy ke yanzu bagashi da Nazy kike luv kuma ba kinsan baban sa me Naira ne,ba wlh bazan taso a wadata ba Kuma nakoma talauci"
Zuby tace "Dalla shut up ur Mouth ,ke naki Baban ba mai kudi bane ba, haba wlh Nikam na dawo daga rakiyar wai sai me Naira wallahi ka samu mai sanka shine."
Akwai sirri da ban tab'a gayawa kowa ba wlh kun ganni nan kunsan dai Auren so mukai da Fawwz ko, ina balain sonsa to sai da Mukayi Auren na tabbatar nafi sonsa domin da Gangan yake mini abu yasan son danake mai da wuri zan huce, wataran se mi 3 days muna fushi dole ni zan bashi hkr yana basar dani,himm wlh ina baki shawara ki Auri Wanda ya fi sonki domin Faruq Masoyi ne kusan fa shekara kenan kina mai wulakanci!"
Sumy da Jikinta yayi sanyi tace Zuby "Nikam na kad'e."
Zuby tace "akan me?"
"Maganar da kika fad'a mana don alal hak'ik'a Madam nasha wahala gun nazi dole na canja salo tumma ba ai auren ba."
Zuby tace "atoh ki zauna kina hauka akansa."
Sumy tace Wlallahi Sady ki rabu da wani Handsome karki ki 2 -0
Tashi tayi a Fukace ta fita Zuby tace Allah ya kyauta "iska na wahalar dame kayan kara." nan suka mike sukayi cikin gida.
*LONDON*
Sun sauka a katafaren Gidan su ma can bayan sun huta yan Nigeria Mazauna Landon sukazo Sunaima Ambassador nasu barka da dawo wa.
Husy tasha kallo bata tab'a zaton zata bar Nigeria ba Lalle ikon Allah yau gata A landon.
Nan ma Husy da Hassy daki daya suke kowa ya kwanta baccinsa na gajiya.
*Washegari*
Bayan sunyi breakfast Arif ya tafi Makarantar su inda yake SS1 Hassy ma ta shirya Driver ya kaita Cumpus na su.
Haka Suhaima ta shirya zata shiga School karb'o wasu Ducument nata Harta fito Mum tace ta tsaya Husy ta rakata saboda kar abarta ita daya Agurguje ta shirya suka fita.
Dady ma ya fita Office sai Mum kad'ai agidan ta kishingida Bacci.
Acan kuwa Suhaima kuwa Cumpus dinsu tayi don ba School Nasu d'aya da Hassy ba ,turawa keta wucwa Wanda suka Santa suna Hi Suhaima Har sukaje office Husy ta tsaya abakim Bishiyaa sai k'ikkifta ido take.
wani siririn Saurayi ne yazo ya tsaya gabanta "Hi Baby".
Ko kallonsa batayi ba,wani abokinsa shima yazo wucewa ya d'aga murya "Bobby come here!"
What Wrong frnd?
"See beauty" ya nuna mai Husy nan ya matsa kusa da ita Jikinta sai rawa yake neman kai hannu Jikinta suke Suhaima ta k'araso ta harare su.
Dariya suke suka bar wajen Husy tace "sukuma haka suke dama ance fararen nan 'yan iska ne!"
Suhaima tace "no koda ba Musulmai bane Amma ko ina akwai na gari dama wad'an nan basu da kirki kin san me sis duk abinda kika ga Namji yayiwa mace ita ta bada dama suma sun sani kuma su Al adarsu ba wani abu bane su rike mace don haka inkin fara zuwa School karki sakarwa kowa fuska tunda Al adunmu da nasu ba daya ba."
Husy tace "Gaskiya ne inasha Allah zan kiyaye."
Bayan ta gama komai taja su suka tafi gida suna komawa suka shiga taya Mum Aikin Girki.
Suna zaune Husy tace "nikam ya inason layi zan kira Nigeria" nan Suhaima ta bud'e wata Jakarta tace "ga wani Empty" ta karb'a tayi Godia don so take ta kira su Baba.
"Ya Suhaima Nikam ban san yayan namu ba" kashe ido daya Suhaima tayi tace "lol bari na bashi ku gaisa."
Nan ta kira domin acan Nigeria kusan dare ne nan ya d'auka tace "my safwan ga Twin din Hassy zaku gaisa"
yayi mamaki tace mai "ai ta dawo" karba husy tayi.
"Yaa Safwan ina maka barka da dare" yace lafy k'anwata, Inaga sai na biyoku Landon ganin ki" tace "Aa ahakan ma yayi basai kazo ba"
Suhaima takarb'i wayar tace "ko na bugo maka ta Imo ka ganta?"
yace "eh."
Nan ta buga mai ta Imo Lokacin yana zaune kan kujera yana Shan tea Husy tace "ya Suhaima nima zai ganni kamar yanda nake ganin sa?"
Dariya tasa "kai husy yan zuma Ai yana ganin ki"
karbar wayar tayi Suhaima tasa dariya.
Dak'yar ta bud'e har da Dan sunkwi dakai ta gaidashi yace "Lahhhhh kaiii zankadaziyya ashe k'anwar tamu ta kudi ce."
Dariya tasa haka sukai ta hira yana kallonta tana kallonsa nan tabawa Suhaima Suka cigaba.
Bayan ta gama Husy tace "ya Suhaima Allah yasani kunya" tace "haka yakema Hassy ma D'an shaftane."
Husy tai Dariya Wushiryar nan ta fito tace "Amma kundace."
Suhaima tace Tnks sis, Wai kuma fa so yake asaka Rana."
Husy tace "ai gwanda Musha Biki Dan kallonta Suhaima tayi "lalle sis Kema A ce."
Sai 5pm Hassy ta dawo agajiye.
*Washegari.*
Dady Bayan sun gama break Dady yace Monday husy zata fara zuwa cumpus din su Hassy" tsalle sukayi itada Hassyn cike da murna .
*4:30*
Kowacce tasha Makeup Husy da Hassy sun saka wata Riga da siket ,Rigar Red ce haka Siket din black sai suka dora Top black,sun nad'e kansu da Red d'in Gyale sunyi kyau sosai Manyan takalma suka tsikara.Dak'yar Hussy ke takawa saboda tsinin sa tunda ba sabawa tayi ba sai da Hassy ta koya mata.
Nan Suhaima tasa wata bak'ar Abaya Anyi shape din ta tad'an bazo da gashinta gaba ta na nada Mayafin abayar Akanta gashin yadan fito ,tasa no Respect Glass ta kwashe su suka fita zaga Gari.
Sunje Super Market suka D'an siyo abun Motsa baki end suka je gurin shak'atawa suka Shimfid'a Carpet sai Selfie suke suna Dan ciye- ciye da drink.
*BAYAN WATA DAYA*
Hassy ce ke Zaune a 'yar Runfar Gidan su ta shak'atawa sai Murmushi take ita kad'ai Husy ta d'ago d'aukeda Fruit Salad A cup ta zauna tana sha tana kallon Pictures a instr .d'agowa tayi ta kalli Hassy .
" Tweeny" ta dago "Naam sis."
Tace "ya naga sai Murmushi kike ke d'aya."
Tace "kin san me sis? wallahi ba abinda yakai so dadi Musammn in ka samu wadda ke sanka kake sansa."
Hussy tace "tabbas" Hassy ta matso Dan gaba tace "bantab'a gaya miki inada Saurayi bako? to ina dashi .
Husy ta tasa dariya "ya Sunansa?" tace sunan Yasir"
tace "kai yanzu yana Nigeria ne? tace" Nop a Cumpus namu yake Last yr yayi Graduation yanzu one yr kenan da fara Soyayyarmu farkon shigana School."
Husy tace "Wayyo Amma nayi maki Murna, ki tayani da Addua Allah ya had'amu da Muntari na domin yazama heartbeat dina,Allah yasa ya rike Amanata duk da rabamu akayi tayiwu yayi aurema.
Share Hawaye tayi Hassy ta taso ta Rungumeta ta baya.
tace "ai insha Allahu zaku had'u Ameen"
Haka rayuwa take gudana ga wad'annan Family' kowa nasan Dan uwansa fans in kunga Hansai to sai kun tsaya kun sake kallonta tamkar wadda akaiwa wankan inji ta kile ta sake wayewa ga kwalliya su Hassy duk sun koya mata tun sanda ta fara shiga school.........
*fans Caji yayi tsiyar ya kare banzo inda nake san tsayawa ba Amma dai ku biyo ni.*
By
Queen meemi
Queenmeemi.worldpress.com.
.
[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣43❣ *FEB,2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
_*Wan nan Page naku ne dukkan 'yan NAGARTA WRITERS ASSOCIASION onluv❤*_
*********
Bayan wata Uku da fara zuwan Husy School Aka saka Ranar Suhaima Nanda 3 Month Lokacin su Husy sunyi hutu Alokacin zasu tafi Nigerian don gudanar wa Murna gun su Hassy ba Magana Sai shiri suke abinda Hankali kwance.
Husy da Hassy ke zaune a Garden na School suna karatu Wayar Hassy tayi K'ara ta d'aga Ganin Sunan Yasir yasa ta d'aga da wuri "haba kazo Landon ne."
"Ok sai kazo."
Juyowa tayi ta kalli Husy "kinsan me? Husy ta dago "Aa" tace "to Yasir yazo tun jiya Yanzu zai zo ya ganni kinga dama kina son ganin sa."
Husy tace "ai kuwa domin hirar sa Harta isheni Hassy tace yau kwa zaki Ganshi wallahi Mundace."
Bayan kamar 1 hour Kiran sa ya K'ara shigowa "Yawwa kazo?" yace "eh"
Nan tayi mai kwatance da suna Garden, direct yasan wajen dama ya tawo Hassy harda d'an Goga Powder Shigowa yayi Garden d'in daga can ta gano Shi ta tashi tana Murmushi.
Yana Jingine kusa da Wata bishiya sumar nan tasha k'yalli yasa tshrt black da farin wando sai agogo fari da shoe black wani d'igon sonsa ne ya motsa Mata sallama tayi ya juyo suka yiwa juna Murmushi yace "I Mssd u dear na" tace "me too."
"Oh ina Tweeny namu ne inason mugaisa" ya tambaya, tace "woo ai itama kai take son gani tare muke tana can zaune."
Anutsue suka jero Husy kanta na sunkuye tana karatu ,har sukazo inda take hassy tace "Tweeny ga yasir."
Dago kai tayi Eyes nasu suka had'u a razane ta kafa mai ido shima sakin baki yayi yana kallonta kallon Hassy tace "dama shine yasir din?" Hassy tace "eh kun san juna ne?" Husy tace "no"
Da kyar ya bude baki yace "Amma kunyi kama" kirjinsa ne yaji yana bugawa sabili da jin wani irin Abu tabbas yasan Hansai din sa ce Mamaki ne ya isheshi taya haka ta faru bayan Malam yace Aure za amata, Jiiyayi kamar ya cire kansa saboda zafi da yayi .
Husy kuwa Hawaye ke neman zubowa tayi saurin tare su, ba yabo ba fallasa ta gaidashi, tace "Tweeny bari na tafi Ana jirana zami Lucture in kun gama kimin waya sai na fito mu tafi."
Binta yayi da ido cike da Razana akan face nasa.
Bayan class taje ta tsaya sai kuka take harda d'ora hannu aka tana kuka "wayyo ashe Tweeny Muktar ne saurayin nata" can Wata zuciyar tace Mata kefa wan nan sunan sa yasir nan taji hankalinta ya kwanta kanta har ciwo ya fara ta fito ta ta shiga class.
Sai wajen 3 ta fito Lokacin Hassy na jiranta suka tafi.
***********
Yau kwana 2 kenan sa had'uwar su ya kasa Sukuni domin tabbas yasan Hansai ce yana Mamakin meya kawota Landon kuma yaji Hassy na cemata sis dinta to dama Hansai ba yar can bace duk wan nan tambayoyin ya rasa amsarsu.
Duka gwiwowinsa yayi ya dau phone dinsa yana tunanin wazai kira a Nigeria,k'anin sa ne ya fad'o mai da yake shima yana Secondary yanzu yasan yana da waya kuma yana Aiki.
Nan ya buga mai yace "wai ni na tambayeka? ya Labarin Hansai ta Gidan Malm tsohuwar budurwata da aka fasa auren mu ? Tana ina ne wai?"
Daga can Musa yace "ai yaya kwanakin baya naji Labarin anga iyayenta har Sun tafi da ita abuja ashe ba yar gidan bace" Dam! gaban Muntari ya fadi.
Yace "ok ba matsala" kwanciya yayi a kan gadon sa ,yana dafe kirji kansa duk ya daure
Husy kuwa kwana biyu duk tayi suk'uk'u zuciyar ta takasa sukuni zuciyar ta na gaya Mata shine domin tabbas ko da cikin duhu zata nuna Shi duk da yayi D'an kiba da tsawo Amma kuma taga sunan sa yasir .
Tana zaune tana Latsa waya cike da k'unar rai Hassy tashigo "Tweny na" ta zauna "yanzu muka gama waya da yasir baijin dadi gaban husy ne ya fadi tace "eyya Allah sarki" "wallah hussy duk na damu Domin Soyayyr dana kewa Yasir daban ce domin shima yana sona sosai saboda yasha gayan wai ina kama da wata first lov dinsa shiisaa yake balain sona.
Husy tai dariyar takaici domin wan nan Maganar ta sa ta dad'a tabbatarwa shin Amma kuma dole taji daga bakinsa tace "haba Tweeny yanzu bakya kishin saboda kamar ku daya da wata yake sonki?"
Hassy tace kai Tweeny to meye ai dama badole sai ya dade da itaba."
Suhaima kam duk ta zama busy sai shirin yanda zata gudanar da bikin ta take suna zaune kan kujeru dake kewaye a falon Mum na kallon wani film .
Husy ta shigo da Gudu ta fad'a kan Mum tana kuka hankalin Mum ya tashi tace "meya faru?" kuka take na fitar hankali tace "wai ke meye? tace Mama su baba nake missn Dariya Mum tayi kai Husy shagwab'a.
Tace "karki damu ai saura wata biyu bikin yayarku kinga Idan muka rankaya can sai ki je bayan gama biki."
Husy ta kwanta jikinta tana maida zuciya domin son Mukhtar ne ke dawainiya da ita ga kuma yanda Hassy ke san sa tabbsa tasan da matsala.
Suhaima ce ta shigo da Album "mum kinga irin kayan nan nakeso" Mum tace "kai suhaima ba kunya agabana" sunkwi dakai tayi "yi hkr mum" .
Dariya tayi bakmi ai gwanda ki zabi irin kayan da kikeso" ,Arif ya shigo yana neman Hassy Mum tace tana bedroom bacci.
*BAYAN SATI D'AYA*
Husy ce zaune a Garden din da ta Saba karatu domin yau Hassy bata da lucture Ganin Mutum tayi agabanta ta d'ago.
Muktar ne ya zauna daya kujerar kauda kai tayi .
Yace Hansai ashe zanganki a Rayuwa?
Kallonsa tayi kawai sai ya koma Mata Muntari k'auye kuka tasa harda shashsheka sai datai mai isarta.
Muktar yace kiyi hkr idon sa shima yayi jan "abubuwa Sun faru.Muktar tayaya kasan ja suna? kuma yaushe har ka manta dani ka fara soyayya ni ina ta Dakon son ka!"
"Am so sorry Husaina"
Bayan Rabuwar mu kinsan dai kano na koma gidan kanin Hajiya to anan na zauna nafara sana'a sosai daya yana legs yace zai mani cuku cuku don cigaba da karatu"
"Dalilin Sanja suna na kuma shine:
Hatsari ya faru dani da Dan Alhaji mai suna yasir Lokacin zamu wani gwaji da za ai mana duk credentials D'ina da nasa na tare to nawa yana hannu na nasa na jaka, Munyi hatsari sai Allah yayi mai Rasuwa saboda motar ta kone ni kuma fad'owa nayi Asume waje.
To abinciken Motar ne sai aka gano takardunsa a jaka Allah yasa bata kone ba. komai nawa ya kone to wan nan dalilin ne yasa kikaga na canja suna Sabili da duk da komai nasa Alhaji yayi Mani cuku- cuku na samu Scholarship na tawo nan karatu shine nake amfani da sunan yasir anan."
To karshen shekarar da zan gama ne muka had'u da Hassy ita lokacin Zata shugo ,nayi Mamakin ganinta irin kamar da kuke da ita komai naku iri d'aya yananyi dukka sai de abinda dai bambancin kadan ita yar Birni ke k'auye."
"Soyayyr da nake miki ce ta darsu naji ina son ta.
Ban kulataba har saida na koma hutu Nigeria Naje Bunkure har gun Malam naje na tamaye ki yace ai an kaiki aiki kuma ma Aure za'amiki da jin hakan nasan Malam be manta abinda akai maki ba,haka nai jinyar Rashin ki na hkr"
"Wan nan Dalilin ne yasa na hkr ,Amma Still kina Raina domin True Love Never end.
Ganin kamar kun yasa nace inason Hassyy saboda ganin ta nake tamkar ke."
Kiyi hkr Amma wlh kece Araina domin ance kama da wane ba wanen back.kuma ganin ki yanzu yasa Soyayyrki ta dada ninka da naji bazan iya ba."
Kuka Husy keyi sosai domin tasan tabbas bai da Lefi kallonsa tayi cike da k'auna tace "kayi hkr Tweeny blood Dina ce abinda take so ina son sa don haka na barka da ita kucigaba."
Domin bazanso abinda zai shiga tsakanin mu ba Muktar yau na tabbatr Rabuwarmu itace Sanadin Abubuwa da dama ni gashi na samu iyaye na ta hakan ma na samu ilimi.
Juyowa yayi burinmu ya cika husy saura Daya domin bazan iya rabuwa dake ba"
Ya zakayi da Tweeny to kasan hakan bazata sabuba?
kansa ne yaji ya d'au zafi ji yayi bashida mafuta.
Sallama yayi mata ya tashi yayi ya tafi.
Tace "OMG! Matsala tabbas ta tunkaro ni,domin tasan yanda Hassy ta mato kan Muktar.
By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣44❣ *FEB,2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
*NWA*
*Nagode Waheeda da kulawa Allah yabar zumunci👍*
***********
Tunda abun ya faru Husy ta shiga neman yanda zata Manta Muntari sai de hakan ya faskara daurewa kawai takeyi.
B'angaren Muktar kuwa har wani Dan rama yakeyi saboda rad'ad'in da zuciyarsa ke ciki domin koda Hassy ta buga mai waya bai dauka aganin sa yanzu ya zama dole ya yakice ta.
Ammawata zuciyar na tunatar dashi inyayi hakan kamar zata ha yaudarar ta yayi.
Yauma d suke zaune suna hira ad'akin su Hassy tace kin san me sis? na rasa mai yasa yanzu Muktar yake shareni"
Hussy taji gabanta ya fad'i tace 'kiyi hkr tayiwu ko yana Busy Hassy tace Allah dai yasa."
Tunani hussy ta hauyi tabbas dole na San yanda zan don bazan so sis taji ba nan tad'au wani layi ta saka ta awayarta ta d'au Number din sa a wayar Hassy Direct tayi mai text Msg kamar haka:
_"Muktar ka manta dani saboda hakan Allah ya kaddaro akanmu balalle sai mun zauna inuwa daya ba wato aure, kadaina wulak'nta sis Dina plss ,kuma karka bari tasan mun tab'a soyayya karka nuna mata kaine muntari na idan ma ta sani to sai kun aure ,ka kyaleni kawai dama ba komai Mutum keso ya samu ba ,Matar Mutum kabarinsa wani baya Auren matar wani Bye"_
Yana gaban Computer yana wani project sak'on ya shiga nan ya d'auka ya karanta ji yayi kansa na bugawa ya daki Bench na gaban sa .
"Tabbbas kece farin cikina bazan iya babu keba Amma zan d'au shawarar ki na daina kin d'aukan wayar Hassy Amma ki sani ke tawace"Shi kad'ai yake Maganar kamar da wani.
Ita kuwa tana gama tura.Msg din ta cire Layin ta Maida nata,da Gudu Hassy ta shiga "Tweeny!"
zo kika wani d'anyan Material da Dady ya sai mana" nan ta nuna Mata "wow Amma sunyi kyau",Suhaima da Arif suka shiga nan suka baje kowa yana fad'ar irin Bikin da za a gudanar.
*Bayan 2 weeks*
Su Hassy Exams suka fara tukuru haka Hussy ma ta bangaren Hassy kuwa hankalinta yad'an kwanta ganin Mukhtar na kiranta yanzu,damma ya koma Nigeria domin fara shiga office Aikin daya nema ya samu.
Yau suka Gama Exams dukkansu cike da samun nasara,nan fa suka fara shirin tafiya inda suke ta siyo lates kaya Wanda zasu ci biki dasu, Ranar Asabar itace ranar da suka d'aga kasarmu ta Gado wato Nigeria.
Sun sauka Abuja da misalin 6 na yamma Mota 2 ke jiran isowar su suka kwashe su suka je gida Agajiye duk suka zube don Gajiya.
**********
Yau saura Sati biyu Bikin Suhaima, dinki kawai suke kaiwa Ana musu tsaddadu abinka da yaran manya.
Ganin da sauran sati hakan yasa Hassy ta damu zata Bunkure .
Dady shida Mum na zaune a falonsa suna hira ta shiga ta gaidasu Ta zauna Dady yace "Douter da Magana abakin ki" tace Dady ina son zuwa Bunkure ne?" Mum tayi dariya "ai tun a Landon harda su kuka zata" yace "ki shirya gobe Idi ya kai ku keda Arif."
Hassy kuma zata taya Suhaima rabon kati ,kema sati d'aya zakuyi ku dawo saboda Biki."
Dad'i ne ya kamata nan ta sanar da Arif yace ba Matsala Amma Shi ba sosai yake son zuwa k'auye ba harara ta kaimai ,"dole kaje yaro."
*Wshegari*
Hussy ita da Arif Idi driver ya tafiwkaisu da tsaraba Jingim musalin k'arfe 5 suna Bunkure.
Tun shigar su garin sai kalle kalle take ganjn wani gun ya canja sai 5:30 suka k'arasa Mangalu,tsayiwar su ak'ofar Gidan Husy tace Baba idi ka manta Gidan ne? yace "Aa nan ne ai" Mamaki k'arara afuskarta ganin yanda gidan ya koma Ginin bulo yaci fenti.
Abdallah ne zai shiga gida tace Dan jummai Juyowa yayi shikam bai gane ta ba Arif ma ya fito suka shiga gidan.
Nan ma taga yasha gyara dakuna Shima harda tile an canja tsarinsa, Jummai ta fito itama har dan kiba tayi "wa nake gani kamar husaina?"
Tace "nice inna" zama tayi tace "naga gida ya canja?"
Inna tace "kedai bari Dadynki ne da wan nan Aiki wlh ai sede godia domin Malam ma yana cikin gari kantin kayan Masarufi yake siyar wa."
Husy saboda dad'i harda kuka.
Inna ta kalli Arif "Dan lukuti ba magana kayi shiru" Murmushi yayi ya gaida ta.nan ta bud'e ciki da rumfa ne da malam nan aka budewa Arif Rumfar ya shiga.
Tsaraba husy ta fito da ita duk ta warewa kowa nasa "gana Baba wai yana ina?" Jummai tace "ai Malam sai 7 zaki gansa."
Gidan aka shigo aguje Dije ce ke rusar kuka tace ku taimaka Mama zata mutu."
Sam bata gane Hansai ba ganin kamar an canja ta inna tace "to Husaina Dan jeki ni kinga ba damar fita tunda Malam baya nan." bin Dije tayi tana tafiya Anutse Suka shiga Gidan, d'akin Gwamma sai tashi yake k'afar da aka Guntule ke ciwo Sai kuka take ga iya agefe suka shiga.
Jin k'amshin turaren Husy yasa suka d'ago dafe k'irji Gwamma tayi "wa nake gani kamar Hansai!"
Tace "nice"
kuka Gwamma ta fara "don Allah kiyi hkr kan abubuwan Danai miki, nasan na zalunceki gashi nan ina Girba yau wata biyu kenan k'afata ke ciwo har Ruwa take futar wa, ga bak'in cikin Mudi se yayi wata baya lek'oni, Ga Dije ko Samari Sun Dena zuwa gunta kowa bai sonta, saboda rashin tarbiya da fada da Maza,don Allah ki yafeni domin naga izina ba irin gorin Aure da ban maki ba, gashi na ga ishara ga 'yata domin ita akwai Wanda ma ya kusa yi mata Fyad'e irin Mazan da takewa rashin kunya koda bai Matan ba ya Cuceta dalilin da yasa kenan ba mai zuwa Gunta kowa cewa yake ta gama lalacewa. Malam yace bashi ba ita, Nasan nice sila domin ni na b'ata taribyar su, dama ance kak'i naka Duniya taso shi Hakan ka soshi Duniya ta kishi."
Iya tace "ke yimana shiru duk wanda yaja ruwa ai shi kan doka."
Hussy tace "ba komi na yafe" Gwamma tace "yanzu kece kika dawo haka! tamkar Balarabiya.Ashe! ke yar Manya ce."
Hussy tace "yanzu insha Allahu Gobe za a kaiki Asibiti."
Dije kuwa bin Hussy tayi ta Rakata ta dawo tana murnaa.
Husy shigarta kuwa Malam har ya dawo nan yayi Murna sosai da ganin su Arif na gefe yana Latsa waya, haka sukayita hira har ta mai zancen Gwamma yace Shi ba ruwan sa da Gwamma ,Husy tace Baba kaban izini na taimaka Mata" kallonta yayi yana cewa dama 'yar sace ta cikinsa,Amma ahakan ma yana Alfahri da ita matsayin 'ya yace "ba komai 'yata ai Rama Alkhairi ga Macuci."
*Washegari.*
Wajen goma aka taro taxi aka tafi kai Gwamma Asibitin ciikin Garin kano wani k'anin iya ne ya kai ta.kudi Hussy ta ciro a Accnt nata aka kai ta akace sai am Mata aiki a k'afar inda hali ma asaka Mata k'afar Roba.
Da yake duk wata Dady na zuba masu Hussy kowa dubu d'ari a Acccnt yasa Hussy ta bud'e bakin Accnt nata akai wa Gwamma Aiki aka sa Mata k'afar roba.
Tun daga nan Dije taji tana k'aunar Husy sai hkr take bata kan abubuwan data yi mata tace bakomi, ta bata shawarar zuwa islamiyya Harta bokon ma.
Jummai da Malam sai San barka suke da ita Sam bata duba sharrin da Muguntar da Gwamma tayi Mata ba, gashi ta rama tayi Mata Alkhairi.
(Shiiisa akeso ka rik'e Mutum tsakani da Allah Musamm irin Matan dake rike D'an kishiya suna Musguna mai kod'an ruko, 'ya'yansu sune 'ya'ya to bakasan wa zaka Mora ba ba Lalle ka mori d'an cikin ka ba ,sai dai ka Mori na wasu, shiisa akeso ka Maida D'an wani na naka, Domin Masu iya magana nacewa D'A NA KOWA NE Allah yasa agane)
*Ina busy ne fans ga Wan nan ba yawa.*
By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣45❣ *FEB,2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
_*Wan Nan page din naki ne Surayya ngd da kaunarki agareni ngd sosai nima ina kaunarki ngd da support❤*_
*********
Yau suka shiga sati a Mangalu nan suka had'a inasu inasu sukayi Abuja.
Tunda suka koma basa zama kullum suna kai d'inki da rabon kati kuwa duk Sun gama inda sukaje aka fara Gyaran Jiki ,ba Amarya ba hatta Husy da Hassy an musu Amma kwana biyu Sun fito kamar taurari Amarya kuwa kullum na kunshe Ana Gyara ta .
Wasu frnd nata su 2 suka zo suna tayata don su yauta Mata,Mum kuwa wasu k'annenta su 2 daga Adamawa sukazo sauran Dangi duk sai ran laraba zasu zo ,Ga Anty Rabia ita kullum tana gidan don gudarwa abubuwan tunda su basu da yawa.
Gidan su Ango ma ba abarsu abaya ba, shiri suke sosai Dady ma shiri yake su Masu mutane komai atsare ake ma'aikata ne aka d'auko duk wani Prepartion su ke gudanar wa .
Hassy kwa koyaushe suna mak'ale a waya da Muktar kullum Maganar sa d'aya abasa Husy su gaisa shima yayi Alk'awarin zuwa.
******
Yau data kama Ranar Alhamis aka fara Gudanar da Kamu da Walima wajen k'arfe hudu da rabi aka kwashe su zo kuga kyanda Amarya tayi.
Tayi shigar Golden Colour abinka da me kyau sai ita da kayan suka haska Juna ga k'wararriyar me Makeup ta tsantara Mata .Ango ma shigar Light golden shadda yayi.
Su hussy kuwa shigar wani Black nd Red Less sukayi sunyi buba da zani Sun dora zanin kan Rigar Sun balain kyau Me Makeup ta matso masu kyan su ,haka Arif ma yayi shigar sa black nd Red shadda combination yayi kyau shida yaran kanen Mum nan aka kwashe su.
Fati Niger ce ta wak'e su ko ina sai san barka Musammmn su hussy duk inda suka Gifta sai an kallesu.
Haka aka gudanar aka watse.
*Washegari*
Ranar Jumaa shine aka gunar da Mothers Event Manyan mata kuwa in banda kece less ,less da Manyan atampopi da Tsaddun Materials ba abinda suke, wan nan na Wace wacccan kowacce ka kalla zabba ne fal ahannun ta matan Ministoci Sanators nd others duk sune gun, wuyan nan yasha english fasion ,Indian, etc duk sunci Gwara Gwarai duk k'awayen Mum ne da 'yan uwanta.
Lokacin da Amarya ta shigo kallo ya koma kanta domin ta had'u ta hade ga Twinss agefen ta sunyi shigar Ash colour kamar ka sace ka gudu haka, Arif ma yasa Ash colour na shadda da wasu bayan su Frnda din suhaima ne Dana hassy suka rako su.
Husy sai kashe selfie suke da Hassy Musammn da frnds na Suhaima don Sun basu sha'awa.
Mum ke kiran Husy tazo fita Sai idonta ya gano mata Mama da Umma Matan Alhaji tanko suma ita suke kallo Musamm ganin Twins ne .
Umma tace "kai Yarinyar nan tamakar mai Aikin Anty Suna kama dande wannan tafi haske ne da wayewa.Mama tace wlh tun dazu nake kallonta cikin sani.
Murmuahi Husy tayi ta zata wuce ta sunkuya ta gaaida su ta wuce don shigo da bak'i.
Arif kuwa tsakiyar fili ya shiga sai Rawar shoki suke shida frnds nasa nan kallo ya koma kansa sai sakar Musu Lik'i ake Amarya ma ta fito tana mai Liki don ya Birgeta ga Hassy na d'aukansa video, sai da Mum tazo ta fidda shi.
Haka akayi akai ciye-ciye akasha aka watse.
*****
*Washegari*
Ranar Asabar kuma aka gudanar da Dinner kwalliyar yau da akayi masu dukkansu sunyi kyau Amarya tasa Blue Dark tayi balain kyau Gwan din kamar ka dauke saboda tsaruwa an adon Ash ajiki sai walwali take .
Shi kuma Ango yayi shigar Light blue shima yayi kyau.
Su Hassy kuwa shigar wani Materls sukayi Light pink sukayi duka an musu adon Dark pink hakan head nasu ma, Arif shima yasa Ligh Pic D'anyar shadda anyi mai dede Shi sunyi balain kyau Musammmn husy.
Frnds din Amarya kuma Sun shigar ankon su mai kyau Material Brown sukayi abokan ango kuma sukayi Brown shadda wow sunyi kyau .
K'arfe 7 Manyan motoci suka kwashe su aka kaisu hole da za a gudanar.
Husy ce ke Driving sai Hassy a gaba sai Arif a baya da wasu 'ya'yan yar Anty maza su 2 .
Shigar su Filin hole din Motoci ne Birjik fitilu sai walwali suke ,Big gals ne da had'addun Maza keta shiga,Husy ta tsaida Motar .
Hassy tace "ke kalli can ga wad'ancan 'yan Matan pls ba sune su Sady ba?"
Hussy tace "eh sune" hassy tace wlh nasan Motar nan taki ta tafi dasu kin san fa Motarki tafi tawa kyau ,jibi tasu irin Tsohuwar ta ya Suhaima ce data canja."
Husy tace "hmm Tweeny kede ki yishiru ki k'yalesu" Hassy tace "to ai ba Magana zan masu ba kawai ina son kima canja tafiya nasan zasu gane ki." Dariya husy tayi kawai
Arif yayi tsaki "ni ku bud'en plss!" Hassy tace "anki kaji kid'a ka rikice."
Atare suka fita Hassy na yatsina Husy kam kawai fitowa tayi suka jera.
Sady ta kallli Sumy "ke dama Hassna twnss ne? Sumy tace "ke dalla bakya ganewa wai bama ki ga kamar da suke da Hansai ba?"
Sady tace "haka kuma fa."
Hassy Sun gifta su tace "Hi" Sady tace "yaran fa Sun Birgeni wai ni,Kinga motar su irinta fa nace Dady ya saimun wai tayi tsada, Sumy duk had'uwar ka kana ganin ka kashe kala in kazo gun biki sai kaji d'ar."
"Babies din nan na kill me wallahi sun balain kyau",Sumy tace "agidan su fa ake Bikin."
Allah ko ba agidan su ba,nasan Sun kai mak'ura
Ni bama wan nan ba dama twnss ne ?"
Ke ni kije ki tambayesu kindamen zo Mishiga ai Anty tazo sai mu tambaye ta."
Nan suka kulle Motar suka tafi wata mota ce Black ta danno hancinta cikin farfarjiyar.
Sady tace "ke wlh Handsome ne amotar can wow yau Nazo a sa'a" Sumyn tace "bada kanki dai!"
Janta tayi sai waiwayen sa take ganin ya sako k'afarsa waje alamun zai fito wani dafe k'irji tai "I luv dis Man wallahi" .
Ak'ofar shiga sukaga Hassy na waya Alama kwatance take suka shige.
To fah!
By Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.
[6:21pm, 08/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣46❣
*March 2017*
*NWA*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*_Godia marar adadi masoyana masu kirana awaya da text msg sakamakon jina shiru, hakan ya faru ne Wayana samu Matsala amma yanzu komai normal,ngd da soyayyarku gareni Allah yabar zumunci❤❤_*
********
Anutse yazo ya wuce wani Bugaggen k'amshi ke tashi nan ya shige ciki waje ya tsaru ko ina ka wulga had'ad'd'un Mata ne. Sady tunda ya shiga take kallon sa, aganinta ba ishi aduk Mazan wajen.
MC ne yad'au Lasfik'a ya fara Magana kan Amarya da Ango su fito tsakiyar fili nan suka fito take waje aka hau Ruwan Naira sai takawa suke ganin Handsome ya tashi Danyin Lik'i Sady tayi wuf ta mik'e tana tafiya har taje filin nan ta hau rawa ta gefen sa tana lika sai satar kallon sa take tana sane ta d'an bige Shi ta d'ago "oh Sorry" yace "no Problem" Dadi ne ya kamata ganin yayi Mata Magana sajen sa ne ya tafi da ita bak'i Sid'ik sai shek'i yake komawa yayi ya zauna .
"Shuriem" wani abokin ango ya kira sunan sa.
Waigowa tayi cike da D'an Murmushi akan face nata "wow nyc name" komawa tayi ta zauna ganin Amarya da ango sun koma daga can ta k'ura mai Ido Wanda bai san tanayi ba sai basarwa yake .
"Sumy kinji sunan Handsome kuwa?"
"To 'yar wahala ya sunan sa?"
tace Shuriem tab'e baki Sumy tayi dole ki Mato kan Saurayin don k'arshe ya had'u Amma duk had'uwar sa ki kame kanki keda kike mace ce."
Sady tace "oh wa azi zakimin kenan! ko?"
hmmm tsaki Sumy tayi
Ganin Anty yasa Sady tace "Anty wai waccen Lady ta nuna Husy dama twins ne imean kannen Suhaimaa" dariya Anty tayi "eh mana ba adad'e da ganin ta ba kunsan b'ata tayi."
"Wai ku ce Baku gane ko Wace ba?"
suka ce "eh"
tace "tab! to Hansai na ce wadda tayi mani aiki."
Safe kirji sumy tayi "Hansai kuma?!
"Haba Anty wan nan 'yar k'auyen!"
Dariya suka sa itada Sady "gane min hanya."
Dariya Anty tayi "to wlh Hansai nace now ta koma Husy."
Sady kam kamar Mutum Mutumi ta dawo sai nanatawa take Anty ta kirawo Husy ganin ta tawo suka k'ura Mata ido yanayin tafiyar ta duk sai sukayi kamar sun Raina kansu.
Ta k'araso hatta lafuzzan bakinta ta yanda take furta Magana ya canja tace "Anty Sumy ya kuke.?"
Da in ina suka ce "Lafiya" tace yayi kyau Anty tace ."kun Gasgata ko? sady tace "hmm ni da wushiryar ta na gane" Anty tace "to anan kwa gane D"an Adam ba abin wulak'antawa bane kowane irine bakasan waye shi ba."
Aduniya ma kenan kinga duk abinda kuke tak'ama tana dashi wani ma ya zarce naku to inaga in Lahira idan ka wulk'anta Dan adam kana ganin sa a wulak'ance baka san Darajar da Allah ya yi mai ba to Sai ku Gyara."
Nan ta tafi Sumy tace "kaji Anty da wani abu sai kace wani abu Mukai."
Sady tace tab! gaskiya nayi Mamaki Jibi Hansai ce wai takoma haka wlh Jinai duk na Raina kaina."
Sumy tace "hmm wai har tazo tana sanya kayan da ya zarce namu,koda yake Dadyn Suhaima fa yafi Dadynmu kud'i."
Haka sukai ta zan tuka da Jin haushi Da hassada. Mc ya kira twns k'annen Amarya da Arif kan suzo su taka yasa suka Mai da hankulansu gun.
Hassy Mazari ta kamo Hannun Husy dak'yar ta mik'e domin kunya take ji tun kan su k'arasa Hassy tace a samusu kujerar tsakar Gida domin tace batta san wan nan Cool Music d'in chasewa zasuyi don tana balain son kujerar tsakar Gida.
Nan Mc yasa Ga police band na buga kid'ansu suma suka tsaya tun ahanya ta fara Rawa har sukaje filin dai deokacin Muktr ya iso Caraf idanuwansa suka sauka kan Hassy da Hussy
Itakam husy ta kasa Rawar kawai sai D'an takawa take.Shuriem dake zaune nan yaji Husy ta tafi da Ruhuinsa cuz yana son Mace me kunya Murmushin ta yake kalla ganin sai K'ara kyau take Dan jingina yayi yana kallonta daga nesa.
Daga can Muktar ita yake kallo,duk gani yayi itada hassyn ba bambanci Amma husy dabance.
Nan Ango da Amarya suka hau musu lik'i da sauran 'yan uwa ahakan ta zare Jiki ta fita ta koma wata kujera can baya ta zauna don jitai kanta na ciwo saboda kid'a.
Tsam ya mike Sady na Kula da motsin sa nan ta kurawa tafiyar sa ido ganin ya wuce yasa ta juya direct gun husy yayi yaja kujera d'aya ya zauna.Hausawa sukace Abari ya wuce.
Atsorace ta d'ago Manyan idanuwansu suka had'u nan gabansu ya hau fad'uwa Itakam kwarijin yayi Mata da kyawunsa .
Yace "sannu ko" tace "Yawwa."
"Number ki nakeso"
Gabanta ne ya fad'i tace "no bana bada Number."
Murmushi yayi ya shafa gefan fuskar sa, so pls Bani idan kina da ita ,ni bana takurawa Mutum kan abinda baiso."
Nan kawai tai shahada ta bashi Murmushi yayi yace "tnks" ya mike cike da k'asaita ya tafi.
Duk abinda suke idanunwan Sady na kai yayi Jajawur kamar ta Fashe da kuka ganin ya fita waje inaga tafiya zai yasa ta mik'e itama ta fita.
Muktar kuwa sai Laluben Husy yake be ganta ba da k'yar ya ganota tana ganin sa ta b'ace don batta so yazo yayi Mata Maganar so Hassy taji.
Can Waje Husy ta fita ta shiga Motar ta ta zauna Sady ce tsaye sai yarfe hannu take domin kan tazo Hansome ya shige Motar sa yabar Gun . Ganin Husy yasa tai waje afusace ta lek'a ta window d'in Motar tace "Lalle Hansai kin kile."
D'agowa tai galala tace ba sunana Hansai ba kin gane."
Sady haushi ya kamata tace ai kan Mage ya waye "to wallahi kinga Saurayin nan wlh na wane ba naki ba don haka ki fita harkarsa."
Dariya husy tasa kin san ni sai dai kazo badai na kai kai ba.in banda abinki aibacewa yayi yana sona ba."
Rufen baki maidani gaula ko banga kin bashi no ba!"
Husy batta san fad' a Amma dole ayita kare ta d'ago "Anty Sady idan game ki keso abuga to mu,zuba aga wazai Wining."
"Okey haka kikace ni sady wlh sai na fad'o dake k'asa ko mai de cigaban Mutum sai dayayi Aiki agidan mu."
Husy tace "badonn k'addara ba ai kin san nafi k'arfin Gidanku,kuma bana bak'in cikin yanda Rayuwa ta ta kasance wai don na samu niema ayanzu,domin nasan rayuwata agun Allah take",tana gama fadar haka tasa karatun Qur ani Tana ji ta Rufe Ido.
Ido Sady ta k'ura Mata tace "dani kike zan-cen."
Afusace ta koma hole din tamkar ta fasa ihu Sumy tace "ina kika je? tace "kizo mu tafi plss zan iya fasa ihu anan."
Tashi tayi suka fita suka zarce mota.
******
Husy na tssye a jikin Motarta Gefe Hassy ce da muktar Harara Hady takai musu Hassy ta yatsine fuska Nan suka shige Motar Sady taja aguje tabar wajen.
Hassy ta Maida kallon ta gunsu Muktar ne ya kurawa Husy Ido Juyowar Hassy yayi saurin kauda kai ,kirrr aka kira wayar Hassy nan tayi cikin hole d'in hakan ya bawa muktar dama yace:
"Yanzu husy ni kike guda? karki manta nine first luv naki wani furzar da iska yayi why Husy??"
D'ago kai tayi "Am so Sorry Mukatar u ar my luv ,kuma kai nakeso kai nake burin Aure tunda kaine first luv dina ,Amma wani abin na kore wani dole na d'au hkr saboda adalilina bazan sa sis Dina a damuwa ba."
"Mun rabu ka fara Soyayya da ita to ganina be dace a ganina kace zaka dawo ba."
Dafe kai yayi ya Jingina da Motar asanyaye karki Manta Soyayyrmu a baya nine Masoyinki na hak'ik'a kodan kinyi sabon Saurayi!"
Hawaye ta share don kawai daurewa take Musammn inta kalli kwayat idonsa tasan tabbas da damuwa tace "na sani bazan iya son kowa bayan kai ba Wanda kake kira Saurayina yau na fara ganin sa."
Muryarsa ce take rawa ganin tana kuka yace plsss karki haramta mana abinda Allah ya halattta plssss husaina I can do with out you."
"Muktar *RABUWA CE SANADIN" karka manta rabuwan mu ce dukka wan nan da ace bamu rabu ba da tuni muna inuwa daya Amma karka Manta Rabamu akai kan ba ason ka aureni ,haka muka hkr Allah sai ya had'a ka da Hassy komai fa bayin kanmu bane daga Allah ne."
"Shut up Husaina Wlh dole na Aureki an Rabamu yanzu kuma mun hadu don haka ba gudu ba ja da baya,yana gama fadar haka yayi hanyar Motar sa ya fita.
Tsugunnawa tayi gun tana ta kuka ganin kiran Hassy yasa ta mike.
Karfe 10 aka tashi kowa ya watse tun komawarta gida taketa kuka domin toilet ta shige tasha kukanta ta k'oshi san nan ta fito.
Bacci k'auracewa idanuwanta yayi kowa sai sharar bacci yake duk 'yan biki sai hasken wayar Hassy dake ta doka tsaki jin hakan yasa Husy tace "Tweeny meye matsala ne? Naga sai tsaki kike"
Tace sis wajen 10 missd call muktar bai d'auka ba na kuma fa ko sallama bai mun gun Dinner ba, na rasa dalili k'arshema sayya kashe wayar."
"Sorry siis Inaga ko bai da caji gobe ai sai ki kiji Dalili ba."
Tace "hakane kuma Good nyt.
Asanyaye Husy ta kwanta tana tunani.
Can b'angaren Handsome Shureim kuwa yana zaune sai buga Murmushi yake shima ya kasa bacci Number din Husy ya d'auko ya gwada kira k'irrr yaji ta shiga jin and'auka ya zauna
B'angaren Mukhtar kuwa kai kawo yake don zafin daya kejia mind nasa Hotunan Husy ne tun na k'auye yake kalla kamar yayi kuka.
Hmmm Sady kuwa kuka take ci kamar me don ta kasa bacci itama adai-dai lokacin ta buga wayar Shureim taji busy nan ta sadakar da Husy yake waya.
Allah Allah take Washegari tayi ta d'au mataki.
To wata sabuwa kenan.
Sunan wani book badakala( Na Kwaiseh Maryama).
Kudai biyoni.
By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[4:33pm, 09/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣47❣ *March ,2017*
Sadaukarwa ce Ga Bashir Usman Family's
_*Wan nan page din naki Zahra Abdullah ngd da soyayyrki agareni❤*_
**********
A sanyaye ta d'au wayar cike da sallama wani sanyi yaji ya ratsa Shi yace "wasslm" Shiru sukayi gaba d'aya, "dawa nake magana" Husy ta fada.
Gyara kwanciya yayi "ur husband mana."
"Toh!"
Nan yayi dariya "so kina waya da shuriem,na karb'i number dinki a hannunki dazu gun Dinner."
"Oh na gane" cewar Husy yace "ok finest fatan za a bani masauki" dan dariya tayi batace komai ba.
Muryarsa ke ratsa kwanyar ta tace "ba damuwa zanyi tunani" ,bari na barki idan kinyi tunanin sai ki gayan "uhubbiki finest bye."
Bin wayar tayi da ido wani irin Abu take ji a jikinta nan ta kwanta.
Shuriem kuwa komai na Babyn na Birgeshi ji yayi bazai iya babu itaba komai nata Birgeshi yake dama atsarinsa bai son budurwa mai hayaniya.
*Washegari*
Ranar Asabar aka d'aura Auren Suhaima da Safwan akan sadaki dubu d'ari.
D'aukacin Jamaa suka shaida.
Nan mum ta zarce da yini inda da yamma aka hau shirn kai Amarya tasha nasiha kan zaman Aure kuka sosai su Arif da Hassy suke na shak'uwa.
Husy ma haka duk da ba wani shak'uwa sukayi ba Amma tana son Suhaima su uku suka k'ank'ameta dak'yar aka tafi kaita nan kukan Husy ya zarce da biyu.domin tinowa da Matsalar ta da tayi.
Haka gida ya watse tas kowa ya koma inda ya fito nan gida ya dawo tsit suna ta Missn Suhaima.
Yau kwana sati d'aya kenan da gama Biki Hassy da Hussy na tafiya A mota zasu Gidan Suhaima Shan gaban su akai da sauri Hassy ta taka Birki Sady ce da wata k'awarta suka fito dai de windown da Husy take, ta tsaya "ina dad'ai miki kashedi wallahi bake babu Shuriem kin gane."
Hassy ta cika ta batse "ke Sadiya shiga hankalin ki mu ba sa'anin ki bane kin gane."
k'awarta tace "See dis gal ke a ido ai kin san mu yayunku ne ko a Girma don haka zamu baku Mamaki" su Sady harda dungure kan Husy.
Fauu kikeji Hussy ta bawa Sady Mari Mamaki ta saki Husy tace "kad'an kika gani da da yanzu ba d'ayaba wlh kifita hanya ta atoh."
Tazo Ramawa Hassy ta rik'e hannun Sady "be carefull" nan ta ture hannunta.
taja su suka bar gun.
Sady tace tab! wlh saina rainawa yarinyar nan hankali" K'awar tace "ai Naga sakacinki."
**********
Zuwa tayi ta aje k'awar agida itama ta koma gida domin bakin cikin abinda su Hassy sukayi mata.
Faruq ne zaune kusa da Maigadi yana jiranta tayi tsaki kayi ka gama.
Da gudu Maigadi yaje ya tareta Sadiya Ga bak'o can na jiranki" cike da haushi tace "wai bana ce a daina kirana in Wancen abun yazo ba?"
Ayi hkr yar Dady juyawa tayi kamar ta tashi sama
Bata dad'eba ta dawo nan ta hau da ruwa a jug tana zuwa ta juye Maj ajiki d'an naci Wanda baida zuciya wallahi ni ba sa' ar auren ka bace nafi karfin ka ka kalle sama da kasa na wuje ajinka."
zazzagamai Masifa take san ranta tare da bala'i.
Kamar yayi kuka domin yasan shiya kawo kansa kiyi hkr Sady pls ki soni"
"Wallahi faruq bazan so kaba saboda baka daga cikin Wanda nakeso" hkr yake bata kamar Ana zugata "don Allah ki soni Bani na sa soyayyarki A raina ba plss" tsaki tayi ta koma cikin gida.
Maigadi duk najin abinda tagama yimai yazo ya dafa faruq "kai kuwa kaiwa Allah kaiwa Annabi ka k'yale yarinyar nan ai inde yarinya ta nuna bata sonka ka hkr domin ba Amfani."
Ngd Baba maigadi insha Allahu daga yau bazan K'ara zuwa inda take ba Amma ni saboda Allah nake santa na rabu da ita insha Allahu"
Yawwa ka sai wa kanka mutunci yaro"
kudi ya zaro ya bawa baba Maigadi ya tafi.
**********
Su kuwa su Hassy suna zuwa gida suka dire a d'aki sai tsaki Hassy take tace "sis wai meya had'aki da wan nan sadyn ko duk tsanar da sukai miki ne?"
"No sis kawai don a Dinner ya Suhaima wani mutum yayi mani Magana har na bashi no D'ina to tun data gani ta dinga yarfan tsiya tun awajen inaga ko sonsa take ne da alama ko bai sonta, shine fa duk wan nan tsiyar."
Hassy tasa Dariya "Lallema wan nan ai sis kawai wan nan hanyar zaki rama kawai ki Amince da Soyayyr Mutumin kodan ki bak'anta Ranta."
Husy tayi tsai zuciyar ta na zugi tace "to sis hakan za ai."
*Bayan Sati 2*
haka Shuriem yake kiran Husy har suka saba domin itakam husy ta danne soyayyr data kewa Muktar domin tasan San sa ajininta ne Amma dole ta koyawa kanta son Shuriem domin in had'uwa ne yafi Muktar nesa ba kusa ba,kuma ganin sanda Hassy take ma Muktar yasa ta saki jiki da Shuriem don ta manta Muktar.
Yau Shureim ya buk'aci yana son zuwa Gidan su Husy kamar wadda laka ya fashewa ajiki domin bata san amsar da zata bashi ba Domin zuciyar ta har lokaci tana a muktar.
5 dai de yana k'ofar Gidan su cikin Motar sa, yayi kiran wayarta d'auka tayi tareda sallama yace "finest nazo fa" tace "okey."
Nan ta Umarci Arif daya bud'e falon bak'i, pink abaya tasa ta Lining kanta simple Makeup ne a face nata, nan ta d'auki wayarta tafita gun Mum don ta tambayi izini.
K'amshin Turaren sa ne ya bugi Jancinta tareda Ya gauraye da AC dakin.
Zama tayi a daya da kujerun suka gai sa D'an dagowa tayi ta kalleshi yau shigar k'anann kaya yayi.
Tsaf yayi Mata kyau dago idunawan sa dake fad'ar Mata dagaba yayi ya dora kan nata caraf suka had'a ido.
Tayi saurin d'aukewa
Murmushi yayi "finest yau dai inason amsana."
Tana Mamakin yanayin Maganar sa d'ai- d'ai kuma a takaice,ji tayi ya birgeta
"Finest"
Sunan yana Mata Dad'i inya fada yace "plss tell me"
Murmushi tayi wushiryar ta suka fito tace
"Allah yasa alkairi a tsakanin mu."
Aje cup yayi "Weldone Finest."
Wani kallo yayi Mata take wanda taji ya tafi da ita.
Agogo ya duba "Okey ni zan tafi zan lek'a office d'auko wasu takardu."
Mik'ewa tayi t "Okey"
yace "yanzu sai yaushe?" tace "sati biyu."
Murmushi yayi yace kina so Ambulance ta d'auke ni ko?"
Dariya ya bata tace "sai Minyi waya."
Ido ya kura Mata wani irin sonta dake ratsa shi badon yaso ba ya tafi.
Koma warta daki taga Hassy na kuka tace "me ya faru.?"
Hassy tace "Mukatr namin wulak'anci yanzu ban san me nayi mai ba yanzu tunda ya koma kano ya shareni."
Husy taji gabanta ya fad'i wato ni yana yawan kirana Amma ita baya kiranta. tace "Sorry sis kiyi hkr" .
"Haba husy ya zakice hakan wlh ina son sa saida ya koyan so san nan zai gujeni dama maza Mayaudara ne."
Husy tace "karki damu" nan ta tashi ta shige d'aki ta dau phone nata ta tura Text Msg kamar haka:
haba Muktar ban cancanci haka daga gareka ba! Mayyasa zakana wulak'anta sis d'ina? Ai yaudara ce wan nan haba, idan danni kake hakan nace ma da matsala"
.
Ganin text d'in ya maida Mata Martani "ke nakeso" kawai ya tura mata.
Harta cire kayaa Msg ya shigo dafe kay tayi ganin abin da yace,tunani ta keyi yanda zata warware Matsalar Amma ta kasa.
Ku dakaceni fanz ga wan nan ba yawa.
By
Queen meemi.
.
[5:27pm, 10/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣48❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*********
Bayanda ta iya domin abin yafi k'arfinta ganin Msg d'in sa kamar tayi Kuka itaba k'awa balle ta gayawa Mata ta bata shawara,ba wacce ta fad'o Mata sai Suhaima nan ta d'au phone dinta ta Latso Layin "Hello ya Suhaima?" daga can Suhaima tace "yadai Husyna."
Kuka ta Fashe dashi "Sis ina cikin Matsala Amma Maganar bata waya bace gobe Zanzo muyi Maganar."
"Okey kizo fa da wuri Aamma wan nan kukan ya kamata kidaina","Yawwa sis ngd" sukayi sallana ta kashe ta kwanta.
*Washegari*
Wajen k'arfe 10 na safe Ta Shirya Mum da Dady na break fast Arif da Hassy ma haka.
Mum ta kalleta "Aa Husyna ina zaki haka? ko karya wa! kamar tayi kuka ta gai da Dady da Mum d'in,tace "zani gidan ya Suhaima ne kuma can zan karya"
"Aa ko kewarta ne ya tashi? cewar Dady dariya tayi "eh Dady yace to "adawo lafiya."
"Tweeny zaki?Husy tace da Hassy tura k'wai tayi baki "no tweeny kije my regard to her." Dadi husy taji tace "bye Mum da D'an sauri ta fita Direct Motar ta shiga ta faka Maigadi ya bud'e Mata ta fita.
10:30 ce ta kaita k'ayataccen Gidan Suhaima da sallama ta shiga Suhaima na zaune itada Safwan suna break tareda yar Soyayyr su.
"Oyoyo my sis" Murmushi tayi "Safwan Aa sis namu se yau a gidanmu?" tace "Alhmdlh sun D'an tab'a hira dashi ya tashi ya fita nan taje Dining ta karya san nan suka shige d'aki itada Suhaima.
Zubewa sukai kan Bed Suhaima tace "ina Jinki sis meya faru ne?"
Dan Matse Hawaye tayi "sis kin san na gaya miki na tab'a Sauryi a k'auye ko."
"Eh na tuno"
"To shine suke Soyayya da Hassy kinsan dama mun rabu to wai sun had'u da Hassy a landon a school ganin kamar mu daya yasa ya fara Soyayya da ita shine fa yanzu ganina ya dawo wai ya komo da tsohuwar Soyayyr sa kuma wai ba gudu baja da baya sai ya Auren, yanzu wulakanta sis yake kuma banso ta sani.Ayanzu hakan nan nayi Sabon Saurayi kuma na amince da soyayyr sa ,nikam bazan iya haka ba sis nason sa amma so yake ya samu a Matsala aganina ai wan nan salon yaudara ne da ace basu fara luv da tweeny ba da zan amince."
Suhaima taja Numfashi "lalle matsala nasan bakisan Hassy ba wlh shegen k'wak'wa ne da ita wlh adalilin hakan zata iya kwanciya domin in tasa abu arai da tana da wuyar cirewa."
Tabbas hakan da kikai shine dai de,shikam Muktar kamar Yaudarar Hassy yayi indai yayi hakan kuma wallahi saide yayi biyu babu."
Husy tace "kinga Hoton Shireim" karb'a Suhaima tayi "kai charkwad'i! wan nan ai yama fi Muktar had'uwa nesa ba kusa ba duk da banganshi ba Amma dai ruwa biyu ne ko?"
"Sis ban sani ba tunda bamu dad'e ba."
"To ni dai shawarata agareki tun da abin yazo da hakan ki lallab'a Shi, Shi Muktsr din saboda inde baki Lallab'ashi ba Hassy zata iya sani kuma inta sani cewa zatayi ta bar miki abinki Amma kuma abin na ranta sai de kiga tana ta rama ni nasan ta ciki da bai."
"Ai sis tun tuni na cire Muktar a zuciya nasan da Matsala."
Haka sukayi ta hira tana bata shawarwari har wajen shida takai agidan ta tafi.
Ahanya ta tsaya agefen Titi ta d'auko wayarta sai kiran Layin inna take shiru da alama ba Ntwrk sosai tunda k'auye ne 10times tana kira dak'yar layin ya shiga "hello inna!"
daga can tace "naam Husaina" bayan sun gaisa ta gaya Mata dalilin kiranta.
Haushi ne ya kama inna tace lallema to karma ki soma amincewa ko kin manta iyayen sa su sukace bazai aureki ba! Sai yanzu kuma ya dawo duk da nasan ba laifin sa bane yaron nada kirki alal hakika nasi ya aureki.Amma tunda yanzu abin yazo da haka dole daya ya hkr."
"Eh inna ai dama ban aminceba kinga kuma a ganina inyayi hakan bewa sis adalciba yawwa hakan Shi yafi nan sukayi sallama ta kashe wayar taja Motar tayi gida.
**********
yana zaune a tangamemen Office d'insa sai k'amshi yake.
Yana Jingine jikin kujerar sa yana kurb'ar Copee knockin Door akai yayi Dan guntun tsaki "yes".Sakatariya nan bata san aikinta ba.
Cike da karairaya ta shiga office din Left hand nata sak'ale da jaka direct kujera taje ta zauna bai d'ago kai ba saima limshe Ido da yayi ya kalli sama.
Wani D'an small Dream Sady ta tafiyi ganin gata ga Shureim suna zuba yar soyayya suna ciyar da juna.
"Me kike so?" firgigit ta dawo daga k'warya-k'waryar Mafarkinta cike da Murmushi a kwance kan face nata ya kalleta kamar yasan face din sai ya basar.
Sady tayi ta maza dama naji labarin garabasar wan nan Company ne yasa nazo abani ga takarduna nan ta zaro su, Amma b'angaren computer nakeso saboda nayi diploma akan computer yanzu kuma ina degree ina a Level 400."
"Well ! Amma bata nan ake fara neman aiki ba sai kin bi wasu offices na kasa idan takardunki sunyi kyau sai a baki ,Amma waya baki izinin shigowa ta nan direct?. tsaki yayi ya hau kiran Sakatariya da gudu tazo ban hanaki barin kowa shigo min office ba?"
"Sorry sir na shiga toilet ne shiisa."
"Ok last warning,domin kinada sakaci."
Nan ya kalli Sady "oya muga takardun naki" cike da d'oki da zumudi ta mika mai Dan dubawa yayi yace ok da wuya in d'aukeki Aiki domin mun rufe dauka"
Tsugunnawa tayi tamkar saliha "kayi hkr ni don Allah" har dasu hawaye tausayi ta bashi kawai yasa yace ok zakina min Typin kullum hope kin iya?" da sauri tace "eh" ganin ta samu dama.
Nan ya nuna mata Wata computer yace Tomorrow zaki fara zamuna baki Albashi kamar tayi tsalle tace ok." Amma sir ina yin Lucture 12 kullm tab'e baki yayi koma yaushe ne idan kina son Aikin sai kiyi da wuri ki ware."
Tamkar ta Mak'al-k'aleshi takeji wani,shauumin Murmushi tayi da sannu zan kafa gwabana tina kuma na goge alak'arka da Waccen banzar.
Tashi tayi "Ngd sir" nan tafita kamar ta yi tsalle don Murna.
Ni meemi nace lalle Sadi kin daukota da zafi ayi dai mugani in sabulu zai toya kosai.
By
Queen meemi
[5:34pm, 12/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣49❣
*March,2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
_*Masoyana wlh banda word din dazan gode muku kun nunan kauna Musamm Ummu Khadija,Halima sadiya,Aysha Nuhu Zahra Abdulla ,Surayya,maman Shureim da 'Yan group na Maman Shakur ,da sauran wadanda ban fado ba duk kuna raina.Godia ba adadi Lv u so much❤*_
*********
Tunda ta fita take daga office d'in take Murmushi "tabbas ni mai sa'a ce" bayan ta koma gida taga Gidan acike su Ruby duk sunzo zama tayi "yau gidan namu da kyau" duk sunyi birjik afalo suna Lunch Sumy dake tsakiya tace "yawwa sisters kuyiwa Sady fad'a ta nacewa wani saurayi yanzu kullum itace buga mai waya yayi ta Mata wulaknci ga Faruq dake santa Allah har kuka yake mata Amma indan ku kaga irin wulak'ancin data keyi mai saikun tausaya mai jiya Maigadi har gaya mini yayi ta watsa mai ruwa a jiki."
Sady tace "ai kin san bana failure nikam innace inason abu,ba makawa saina samu"
"Lalle Sady kin d'aukarwa kanki wahala cewar Ruma wallahi Mazan yanzu ba irin na da bane wlh tun Ana zuwa sai kinzo an Dena zuwa, jibar ni duk da Dady ne ya hana alokacin tun Samari na zuwar mun har suka zo basa zuwa kuma ban tab'a wulak'nta kowa ba asali ma Dady ke korar su Amma kinga k'arshe ba zab'ina na Aura ba sa'an Dady ne. Amma ke yanzu baki da Aiki sai wulak'nta samari kin k'wallafa rai ga Mutumin Dabe San dake ba haba ki hankalta Mana."
"Ya Ruma duk masu zuwa Guna fa wlh basu da naira haba adauri kashi ko abata igiya ai yanda nake yar gaye sai Dan gaye mai nera dan kwalisa Wanda zai kashen be jimami ba"
Zuby tace hmm wlh Sady ki karatun ta nutsu atoh, domin ni yanzu wlh kowacce Mace kallonta nake idan ma Rawar kai kike kidena.
Ruby tace "karma tayi ga Mata nan birjik a gari ke din wa.Allah yasa ma kar Faruq din ya dawo wa gari ya waya" ta kai Mata harara.
Ruma ta kalli Sumy "kefa? sumy ina Nazi d'in ??"
Hmmm kawai tace San nan ta tab'e baki "ai ya Ruma ban san haka maza suke ba sai yanzu kiga yanda nakeson Nazi Amma Shi kaco kam ashe yaudarata yake sai da Umma tace ace ya fito yace ba yanzu zai aure ba Alhalin duk masu sona da Auren duk ya kore Jibi case din da mukai dashi kan Hansai (yanzu data koma husy) amma wai ni zai tulawa k'asa a ido,yanzu ma baya kasar."
Zuby tace "tab! Ai ni dama nasan Nazi Mayaudari ne tun time da muna cumpus son Mata gareshi da yaudara ba agabanmu yace yana son Hansai ba! nasha gaya miki Alokacin kina mayen son sa baki gane ba."
Sumy tace "ai last week Wani abokinsa ke gayan Sabuwar budurwa yayi"
Dariya Ruma tasa "Amma kwai D'an iska Nazi yanzu kenan baki da kowa???"
Sumy tace "gamu nan dai Muna nema."
"To Allah ya kawo na gari."
Zuby tace "ke bani Labarin Jansai d'in naji kince ta koma Big gal garin yaya bayan 'yar k'auye ce".
Hmmm "Zuby kin san dai Suhaima Beauty 'yar yayan Babar Anty ta nan gidan ko?" tace "eh"
"to yarsa ce wan nan Ambassador Nigeria to London."
Ruby tai sak'alo tana ji "to garin yaya hakan?"
Nan ta gaya Mata iya abinda ta sani Wanda Anty ta gaya musu.
Zuby ta sauke ta gumi "tabdi jam! lalle in daranka kasha kallo D'an adam ba abin wulak'ntawa bane."
Sumy tace "ke kinganta yanzu tab! Wlh duk gayuna ta kereni kinsan Suhaima beauty badai Gayu ba Ga Hassanar ta ,ai dole ta waye acan london din ma fa take karatu! Kinga Motar da takeja duk nan ba wadda take hawan irinta,ina irin wadda sukace Dady ya sai mana yace Tayi tsada!"
Zuby tace "eh nagane ta"
"to wlh ita take ja."
Kunsan Karin wani haushin ma wai saurayin Hansai Sady ke Mutuwar so,Shi kuma Hussyn yake so"
Ruma ta tafa hannu "Amma kuwa Sady kin fad'o ai bakida sauran fangima wlh Gwandama ki dawo hayyacinki."
Sady tace "Nifa ak'yaleni Naga zan iya cire wando taka! haba dadyma ya bani Go ahead na kawo Wanda raina keso."
Zuby tace "ayidai mu gani,Agabanki ba irin feleken daba mi ba mu sai kaza Amma gashi yanzu sai manage Sady bakisan life ba sai kin aure."
Haka sukayi ta bata shawara Amma ko ajikinta.
**********
Zaune Husy take ad'akinsu tana Chatin da Shuriem domin yanzu zuwa luv suke kamar me,k'irrr wayar hassy tayi k'ara lokacin tana toilet da sauri ta fito ta d'auka "hello dea!"
"Plss mai sa kake basar dani ne? bata san me yace ba ta kashe. Juyowa tayi ta kalli Husy "Muktar ne wai zai zo gobe" husy tace Allah y kaimu.
Shikuwa Muktar acan so yake yazo ayita ta k'are domin bazai zauna yana gani a 2 times ya kuma rasa Husy ba.
Jikin hassy in banda b'ari ba abinda yake, "Tweeny mai zanwa dea na tarba ne?" husy tace "sis pls don Allah kina basar dashi Mana! kefa Mace ce ,hakan da kike ne yake basar dake."
Hassy tace "ni kaina tweeny wlh bansan hakan da nake kawai daurewa nake don wallahi sonsa yayi mani yawa."
Husy tayi Murmushi koma dai meye kina Jan class domin samun mazauni ni na gaayamiki Allah da kanshi zai dawo yana nemanki Amma bawai ki shareshi ba kawai de ki daina nuna damuwar da yawa agabansa" tace" to sis."
Husy da tausayin hassy ya kamata tace "wlh duk son da yake min bazan aminceba domin farin cikin Tweeny.
*Washegari*
Da wurwuri Sady ta mik'e k'arfe takwas tayi Mata a Companyn su Shuriem taje k'ofar shiga Sakatariya ta tsaida ita "kina da Appointment ne? Sady tace "yh kije ki tambayeshi" da sauri sakatariya ta shiga Lokacin bai dad'e da zuwa ba nan ta dawo "yace ki shiga."
Gyara Mayafi tayi ta gyatta d'aurin ta, ta bud'e Jakarta ta fito da Powder ta dada fente fuskar ta maida duk abinda take sakatariya na kallonta domin ta saba ganin irin 'Yan Matan insun zo suna hakan,ta d'auko turare ta fesa.
Da karairaya ta shiga sai girgiza take wani shocking taji a jikinta ganin yanda yayi balain kyau yaci fararen kayansa komai fari fuskar sa tayi fes wow ta ambata a hankali.
"Good Morning sir"
Nan ya dago "Morning 2" zama tayi kan kujera nan ya mik'o Mata wasu takardu hada Ido sukai ta saki mai fari kauda kai yayi ta koma ta zauna.
Tana yi tana satar kallonsa komai nasa Birgeta yake bak'in Glass dinta ta d'auko ta kafa a ido don taji dad'in kallonsa ,Shi kuwa sai aikin sa yake .
Wajen awa d'aya batai Aikin kirki ba,Dan tsaki yayi ya Mike ya d'auko wayarsa Murmushi yayi ganin test msg na husy. Kiranta yayi bugu wajen 3 times bata d'auka ba duk abinda yake tana satar kallonsa can sai ga kiran ya shigo ya kashe ya kira ta.
"Oh my finest ina kika shiga ne??
Kin san ina missn voice naki" Murmushi yayi love u so much babe."
Da alama yana jin dadin hirar.
Murmushi yayi tareda shafo sumarsa "finest anjima zanzo ganin ki domin samun sukuni a Mind d'ina."
Tamkar ta kurma ihu don ta gane da Husy yake waya D'ora hannu tayi aka da k'arfi ta buga bench d'in .
Waigowa yayi Mata kallon raini nan Jikinta ya saki ya dad'e suna waya San nan ya kashe.
"Ke idan bazaki iya aikin nan ba U can go bansan Matsala."
"Sorry sir"
Nan ta fara ko rabi batai ba ta d'ago "12 tayi sir time na Lucture yayi"
"Are u finished?"
"No sir."
"Okey to ya?"
Fari tayi da ido dan samun shiga "bari na k'arasa" nan ta tayi sai 12:30 ta gama ta tafi.
Tana shiga mota ta kifa kai kan sitiyari da Dan tsaki
Fushi taji mai tsanani ji take kamar ta kauda Husy tunani take yanda zata b'ullo sanda taje har an fita daga lucture daga nesa ta gano lubna janta tayi sukaje bakin bishiya.
K'awa "Handsome yak'i saurara ta plssss say Something na rasa idea."
Dariya Lubna tayi "hmm kawai ki sanar mai" Sady tace "so kike ya koreni daga office nashi?"
"Ke dalla zauna nan garin kallon ruwa.....ai abari ya wuce Shike kawo da rabon wani.Sady tace "nifa ban san hakan domin namiji yace yana sonka ma ya Allah ya cika,balle kace kana sonsa."
Lubna ta tab'e baki "nikam itace shawarata" Sady tace "Okey to ta yaya?"
"Kimai text msg tunda yanzu nasan yasan Number d'inki in kuma bai sani ba ki k'ok'arin karb'a ki kirasa ya gane kece wadda ke aiki gunsa kamar one week haka saiki samar mai."
"Good idea lubna" Dadi ne ya kamata suka tafi.
*******
K'arfe Biyar Mukatr na gidan su Hassy suna zaune kusa da flowers kan kujeru suna hira yana son tambayar ta Husy Amma ya kasa sai kallon kofa yake.
Hassy na lura dashi "yadai Muktar? yace "no problem" kurb'ar lemu yayi San nan yayi ta maza ina hussina ne?
"Tana cikin gida tana shiri.cuz bak'onta ne sai zo" dam! yaji gabansa ya fadi .
Kamar da 30 mint haka Maigadi ya wangale gate had'addiyar Motar sa ya danno ta cikin farfajiyr fitowa yayi yau yayi shigar white din jins da tshrt white sai black din shoe sai agogo black can kamar Mintuna sai ga Hussy ta fito cikin shigar Red tayi bala'in kyau wani kwantaccen Murmushi ke fita daga bakinta wushiryarta na K'ara Mata kyau.
tsayawa tayi wani kallo yabita dashi don ta rud'ashi kunyarsa taji tace ina zuwa.
Nan tayi wajen su hassy wani Mahaukacin kishi ne ya kama Muktar zuwan taa yasa ya sunkwi da kai "Tweeny ga Shuriem su gaisa da Muktar" k'ura Mata idanuwa yayi dai de Lokacin shureim ya k'araso gun ya mik'awa Muktar Hannu kamar ya naushe Shi ya keji idanuwansa sunyi ja da k'yar ya mik'a mai Hannu suka gaisa kallon Hussy yayi cikin ido ta d'auke kanta suka bar wajen.
Hassy kuwa da Mamaki take binsa da kallo kamar me domin ganin ya canja mata,cup d'in lemo ya d'auka jikinsa har wani rawa yake cup din ya fadi kasa ya fashe ,rikicewa hassy tayi wai Muktar Menene? Akaro na 2 ta tambayeshi kamar da tsawa yace ta k'yaleshi k'arshema yace zai tafi haka sukayi sallama ba yabo ba fallasa zuciyarsa na tuk'uk'i.
Hassy Asanyaye ta koma gida domin abin yayi Mata ciwo koma meye yake b'oye Mata zata sani.
Husy kuwa ranta yad'an baci duk sai Jikinta yayi sanyi.Shureim kuwa jifanta yake da mayataccen kallon sa Wanda ke d'imauta ta tana Son salon Shureim saboda ko bai Magna ba yasan yanda zai aika sakon sa cikin salo da k'warewa.
"Finest"! ta d'ago "naam"
"wai yaushe zamu zama inuwa d'aya ne ki bani dama Manya su shiga ciki mana" Dariya tasa "har yaushe daren yayi?" Murmushi yayi ashe kin iya magana haka to ai mu Soyayyarmu ta da ban ce bazamu cinye soyayyr awaje ba sai kin zama wife d'ina."
"Nida nake karatu ai sai na gama."
"Anya finest?"
K'ayataccen murmushi ta saki batace komai ba
"Gaskiya finest kina da kyau"
"Har nakai ka?"
"ina wani kyau a namji" tace "hmm haka dai kace.Amma ai kafini kyau."
Satar kallon sa tayi taga yana kallon ta tare da "Lumshe ido finest bakya iya dagowa na kalleki sai de ki ta zuban kalamai ta k'asa ko?
K'unshe kai tayi a gyalenta ta kasa d'agowa tana jin heat nata na fat -fat.
K'arar Msg ne daya shigo wayarta, ya dawo da ita daga duniyar data tafi wayar ta duba k'irjinta ne ya buga ganin abinda ya k'unsa kamar haka:
_Ki sani ba gudu ba ja da baya_
_nayi dakon sonki tun kina k'arama sai wani daga baya zai zo ya k'wacen ke domin ni nake miki true luv ayanzu hakan zan turo iyayena ayita ta k'are_
_Ur husband Muktar_
Kashe wayar tayi gaba d'aya ta d'ago suka had'a Ido da Shuriem "Subhanallah Finest meya faru! Naga idonki hawaye?
Shafawa tayi bata San sun zubo ba "Aa abune ya fad'an ido" "sorry angel" Handkerchief ya zaro ya mik'a Mata ahankali ta karb'a k'amshin sa ya bugeta taji wani sanyin dad'i ta share yace "finest bari na tafi na barki ki huta kinji?"
Tace tam wani sansa taji ya k'ara shiga ranta afuskarsa taga damuwa sai data shigar sa mota ya d'ago Mata hannu San nan ta tafi.
Bata taba sanin zata so wani bayan Muktar ba sai gashi ahankali son Shureim ke shigarta ,da gudu ta shige gida ta haye saman bene domin taga ba kowa afalon k'asa d'akunasu ta shige tayi ruf da ciki tana kuka kamar me.
Hassy ce ta shigo itama idanuwan ta yayi ja da sauri ta k'arasa "sis meye? husy ta dago "bakomi dear ke ma meyasa kike kuka" hassy tace kinga abinda Muktar yayi mani ko nikam inaga zan hk'r dashi ba dole dama wasu Mazan Mayaudara ne."
Gaban Husy ne ya fad'i "tweeny nima abinda ya sani kuka kenan domin ni dake d'aya ne abinda ya faru dake tamkar dani ya faru" Rungume juna sukayi suna kuka.
Bayan sun tsagaita
Hassy tace "sis na tafi Mum na kitchen" tace "nima gani nan."
K'arar Ringtone na wayarta ne ya buga nan d'auka ta duba taga sabuwar Nomber ce Da sallama ta amsa wayar. "Yar aikin gidan mu ki sani Karona dake bazaiyi kyau ba wlh, ko ta halin k'ak'a sai na rabaki da Handsome saboda dani ya dace wlh na dai gaya miki."
Kan tayi magana ta kashe Tabbas tasan Sady ce sai Duk barazanar da zatai bata tsoro ba,ayanda takeji bazata iya ba Shuriem ba kuma in ta rabu da Shuriem kamar ta bawa muktar k'ofa ne ga kuma Tweeny dole ta shiga damuwa wullar da wayar tayi cike da haushi domin ji take kamar tasa ihu.
*Waye Shuriem*
Shuriem d'ane a gidan Alhaji Kabeer da hajiya Khadija. Alhaji kabeer shahararren D'an kwangila ne wanda yake samu ta hakan ,inda kuma yake kasuwanci ya tab'a rik'e Muk'amai a gwabnatin tarayyya San nan yana da Company anan Abuja da sauran Jahohi ayanzu hakan yayi ritaya shureim shike gudanar da duk harkokin sa.
Shureim shine d'a na biyu a Gidan su, inda yake da yaya Mace Maryam dake Aure a lagos sai k'anwar sa Nawwara itama tana Aure anan Abujar sai Autansu Sadiq dake karatu.
Yayi karatunsa a Oxford University inda ya karanci Accounting bayan ya kammala ne sai Mahaifinsa ya bashi Ragamar komai nasa ganin ba irin nan ya karanta ba, bai San wasu kasuwancin ba, yasa yayi wani Course a uniAbuja kan Bussness.
Allah ya bashi farin jinin Mata sai de duk basi mai domin Shi bai san mace tace tana sonsa ,shiisa ma duk masu sonsa baya kulasu don basi masa ba.
'Yan Mata da yawa wasu har gida suke binsa wasu office Musamm Mata masu kwad'ayi ganin yana tashen Naira wasu kuma don kyansa.
Shuriem yana da son tsafta ga da son turare da son Fararen kaya bai da Magana sosai sai Murmushi kad'an kenan daga Shuriem.
Tunda Muktar ya koma kano yake cike da damuwa duk ya canja ganin hakan yasa yatafi Mangalu domin zuwa gun Malam don ya taimaka mai
To fa muje zuwa.
by Queen meemi👑
.
[2:04pm, 13/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣50❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce Ga basher Usman Family's_
_*Wan nan page din naku ne Maman haneef ,Maryam oumey, Ameera Mahmoud,Maman rahma,Rabia Alhasan, Nana fiddausi, Muhfaz,Maryam Ahmad,nabila ladan,Maman yasmeen & Zeenat tukur. Tnz❤*_
******
*Mangalu@11am*
"Ya kamata ace kayi Aure haka Muntari" cewar Goggo "ai Goggo da Maganar nazo ma shiisa nazo ma ayita kare."
"Hakan shine dai-de Muntari gashi nan duk sa aninka da yara a ina yarinyar take ne?"
"Ai gogga kinma Santa Hansai ce fa" Goggo ta zaro ido haba idan d'a ya manta ai uwar d'a bata manta ba kamanta baya yanda mukai musu mukace bata da asali ai yanzu muka je sai ace don ance iyayenta masu kud'i ne kwad'ayi ya kaimu."
"Goggo ataimaka" suna cikin Maganar Maigari ya shigo "Aa Muntari hira kuke ne? gogg tace aifa kajimin d'a wai Hansai yakeso anema mai Aure ai da kunya mukoma."
Maigari yace "too nikam bazan shigema gaba ba sai de in wata ce Amma ai da kunya."
Kamar yayi kuka ya tashi ya fita sai gaisawa suke da tsofffin abokansa nada sai sha'awarsa suke suna dama suma sunyi karatu bai Zame ko inaba sai gidan Malam,yana k'ofar gida tsaye suna hira da wani Mutum.
Dan tsayawa yayi suka gaisa kan Mutumin ya tafi Malam yace "Muntari Kaine a gari?" "eh wlh Malam dama magana nazo da ita kan husaina."
"to wata matsalar ne?" Muntari ya sosa kai "dama Aurenta nake so akaro na biyu." murmushi Malam yayi masha Allah amma ai Muntari ai an bar Maganar tun abaya ko ka manta maigari yace Aa, ai maganar bai dace ka Taso da ita ba domin ni inada taka tsan- tsan balle yanzu ma kaga ba a guri na take ba ,ina Baka shawara ka hak'r ka nemi wata tunda kaga ba'ai Auren ba to ba Alheri duk wacce kake so zan shige ma gaba."
Tunda Malam ya fara magana Yake zufa kamar me idon sa yayi ja yace "Malam ngd Allah ya saka" akasalance ya mik'e ya tafi Malam ya bishi da kallo cike da tausayi.
*Abuja@ 4:00pm*
Tsaye Husy suke itada hassy zasu Super Market goslow ne ahanyar yasa suka tsaya da yake yau weekend duk Motoci na fita wasu zasu visiting Akusa da motar su Sady ce itada Lubna. Lubnan ce ta fara ganin su Ta nunawa Sady alokcin aka bada hand nan suka fafara Sady ta bisu abaya har sukaje Super Market d'in.
Firfitowa sukai shiga iri daya sukai nan suka shiga Sukayi side na makeup da perfumes,yana tsaye yana duba wasu lates agogwaye wajen yana gefe.
Shiya fara ganinsu wani k'ayataccen Murmushin sa yasaki.Hankulan su Husy na kan d'aukar abinda sukeso ji tayi kawai an k'arfe basket ta d'ago suka hada ido atare suka sakar wa juna Murmushi "Finest da nasan zakuzo siyayya ai Dana Zo na d'aukeki ban san kowa yana gane wan nan fuskar."
Murmushi tayi "Habibi kenan barka da yamma." "bana amsawa sai yanzu ma zaki gaidani." "Kaina bisa wuyana habibi"
Murmushi yayi ahankali yad'an sunkuyo kamar zai d'au Abu iluv u Swt finest."
Lokacin Hassy ta k'araso gurin perfumes din ta gama da Makeup site Dan dariya ta saki "Aa kice da Masoyin aka hadu."
Su Sady kuwa sai A lokacin suka k'araso suma suka shiga karaf idanuwan Sady yakai kan Handsome dake rike da Basket na husy wani Mahaukacin kishi ne ya deb'ea taje ta wanke Hussy da mari mai zafi.
'yar k'ara ta saki saboda zafi da sauri ta kalli wacce ta mareta ganin Sady yasa ta matso kan ta rama taji an wanke Sadyn da mari.
itama an bata wani dagowa tayi sukai ido hudu da Handsome yana wuci "ke kina da Mental problem ne?"
Zaki zo kimare ta d'an karamin tsaki yayi bansan problem wlh. Hassy kuwa sai harare harare suke da Sady "anji kunya ba ason mutum ya nace ."
Jan hannun lubna Sady tayi ta kalli hassy "dani kuke zancen."
har sun fita Lubna ta dawo tayi side da Shuriem yake don itama yana birgeta Amma tunda k'awarta ta rigata dole ta basar.wani kallon Shureim tayi Tace Sady me k'aunarka ce domin babu wacce takaita sonka kuma sai inda mammu ya k'are",da sauri tafita don ganin yanda yake huci.
Hanunn sa ya daka ganin yanda husy ke zubar hawaye "sorry My Queen" da k'yar ya lallasheta yayi counting suka fito sai day aga tafiyar su San nan ya shiga Motar sa ya tafi.
*Monday @ 8:09*
Da k'yar Sady ta shiga office d'in cike da tsoro burki taja domin yau shigan da yayi yafi na jiya abinda ke dada rudarta gashi kenan akwai tsafta da ado.
"Morning sir"
Bai d'ago ba sai ma D'an.Rubutunsa da yake yana waya ta dad'e a zaune ganin hakan yasa. Tayivta maza tace "sir aikin."
Wani wulak'antaccen kallo yayi Mata tare da Murmushi ta gefen Lips nasa yace "ke!
Get out of my office"
"Sorry sir wlh bazan kuma ba wlh dama tsautsayi ne wlh."
Kuka ta fara shab'e -shab'e plss sir bazan kuma ba kallonta kawai yake yana juya kujerar sa ,da mamaki fal zuciyar sa wai sonsa take sai yanzu ya gane dalilin neman aikin ta D'an tsaki yasa I said get out of my office yaune last da zan K'ara ganin ki a office na kin gane."
Jakarta ta tad'auka "pleaes sir!"
"Security"
Da sauri yazo nan Shureim ya nuna Sady "fitar da wan nan karka barta har sai kaga tabar harabar Companyna."
Da gudu ta fita Sucurity na binta ta galla mai harara "Malam sai ka k'yakeni haka ko! Tunda ba maula nazo ba" nan ta shige Motarta ta kwasa aguje.
Tana ta fiya tana kuka gefen titi ta tsaya tana dukan sitiyari tayi "wlh dole ka soni Shuriem bazan barka ba akan wan nan kile war kwanan nan zakana wulaknta ni, ke kuma husy sai kin gwammace kid'a da karatu.
*************
Kwana 2 hassy ta rage neman Muktar don Jan ajinta .yau ma suna zaune Dady ya shigo duk suka mai barka da zuwa "yawwa dama ke husaina da hasna inason sanar daku ba daku za a koma London ba saboda Na dawo da karatunku nan abuja a uniAbj saboda Suhaima kar mu tafi mu barta ita daya duk da ga Anty . Mum naku kawai zamu tafi da ita sai Arif."
Hassy kamar zata sa kuka "Dady yanzu mu kad'ai zamu zauna a wanga memen gidan nan! Yace habadai Goggo zata zo Ita zata zauna daku( k'anwar Maman sa ce)akwai dalilai ne Amma idan be muku ba sai mu tafi ke Hussyna me kikace?"
"Dady zamu zauna d'in Allah yasa hakan yafi Alheri" "Yawwa 'yar Dady."
Mum tace nima fa nafi san zaman nan Dady yayi Mata wani kallo Wanda shiyasan ma'anarsa kauda kai tayi "to my twinss ku Kula banda shirmen k'awaye ku zama masu kula kun gane?,bamu yarje muku kawo ko wane saurayi yazo zance gunku ba, illah ke Hassy Muktar ke kuma husy Shuriem su na sani suna zuwa.ban yarda ku tsaya da wasu ba bayansu suma din ku kiyaye."
Sukace "tam Mum."
Dady yace kowaccen ku level data ke shi zata cigaba ke Hassy dake level 2 nan zaki shiga haka ke Husy dake 1 Kema nan zaki shiga."
Arif dariya yasa yana musu gwalo harara suka kai mai ya gudu Dady yace "sarkin tsokna.Yanzu jibi zamu tafi Gobe Goggo zata zo ga Idi nan kun san dai amanar dake tsakanin mu dashi tamkar Dan gida duk wani babban abu da kuke so kwa bashi yana sayo muku ,zai dawo nan suna kwana a boys quaters saboda tsaro." Nan duk ya sallamesu suka haye sama.
*Washegari @12am*
Sai ga Goggo ta iso da murna suka tare ta tace kai ni karku karya ni ina kakarku" Mum tafito Aagogoji kece? Sannu da zuwa" zama tayi kan d'aya da kujerun.
Wani saurayi D'an kimanin shekare 23 ya shigo da tulun kaya "Aa harda kamilu akazo?" goggo tace "ai k'afata kafar sa saboda bakowa gidan."
Hassy tace "kai duk girman sa!" kamilu yace "aini d'an Auta ne" suka dariya.
D'akin dake kusa dana su Haassy aka bata komai akwai aciki su funiture.
Shi kuma kamilu aka bashi dakin dake k'asa empty gado ne aciiki zai wardrobe mai 2 sai toilet duk suka shigar da kayansu.
Washegari kuwa su Mum 7:00 Am suna Airpot da kuka su Haassy suka saki itama bata san barin su ba yanda ta iya ne haka suka Rungume Dady da Arif suna nan tsaye Jirginsu ya d'aga asanyaye suka koma gidan.
Gidan yayi masu fadi sai da Goggo ta jawo su kasa suna kallo suna hira har kamilu nan suka sake da take kamilu Dan shafta ne nan sukai ta hira.wayar Hassy ce tayi K'ara ganin sunan Muktar yasa ta kauda kai Husy tace "meye tweeny?" "wan nan Muktar dinne mana."
Dariya husy tasa "lalle sai da dare ki ishemu kina.missn sa ko?" ganin kamilu da goggo na kallonsu yasa ta dauka tayi sama .
"Helo" daga can ya amsa nan yace Mata zai shigo kamar bataso tace to Jikinsa yayi sanyi kit ta kashe.
Yana zaune ya tashi yana zagaye daki zuciyarsa na mamaki taya zan samo kan husy ne kode hk'r zan na rike Hassy no huusy itace life dina msg ya tura Mata kamar haka: _ya tauraruwta ki sani amincewarki itace zata bani damar aurenki domin malam yace akaro na 2 sai kin amince domin pls ki taimakeni ya tura mata_
Dariya suke sha itada su Goggo kan wani Labari data basu d'aukan wayar tayi jin karar msg Murnushin jin dadi tayi don kin Amincewar malam,tabbas Tasan dole ya maida hankali kan Hasssy hakan take fata.
Martani ta Maida mai Muktar ka sani Bafa komai Mutum keso ke samu ba ka yaki zuciyarka kamar yanda nayi da tawa duk son da mukema juna domin Bakomai mutum keso ke samu ba,idan kuma amincewa kake nema to nikam bazan aminceba tunda baka tausayin sis nawa,tamkar ka yaudareta ne"
Tashi tayi ta fita tace Goggo ina zuwa can garden taje ta zauna bakin bishiyar Mangwaro tana kuka domin duk son Shuriem da zuciyarta keyi har yanzu Muktar na ranta yana bata tausayi bayan ta gama kukan kiran Shuriem ya shigo nan ya mantar da ita bacin ran data ke ciki.
0 comments:
Post a Comment