Yau ta kasance Monday Husy suka tafi Lucture da yake duk time d'aya yau suke da ita tunda su kaje kowacce ta tafi nata Fuculty bayan kamar awa 2 Husy suka fito. Bakin wani bishiya taje da kujera irin ta dutsen nan ta zauna tana duba littafanta.kamar daga sama taga Sady akanta da wasu Frnds nata 5 tafa hannu tayi "wajen zaman namu shine kika zo?
Bama wan nan ba dama da tamu dake akanki an Mareni ko? to wlh akanki zan rama" kallon k'awayen tayi kun san "duk kyann yarinyar nan da wani bud'awar da take wlh tayi aiki agidan mu. Ummi wata daga ciki tace kai Sady ni kam ban yar daba haba ai wadda tayi aiki ma tafita daban." Lubna tace "ku wlh da gaske ne yanzun ma cigaba ta samu ne sauran 2 din sukace "tab! ke ai baki da fangima."
kallon su tayi ta tab'e baki Ummi tace "ke yar aiki" nan duk suka kwashe da dariya Sady ta tuje Mata D'an kwali "wlh idan baki rabu da Hansome ba sai nai k'asa -kasa dake" haushi ne ya kama husy ta bugawa Sady Mari ta daura Dan kwalinta tace "samu yafi iyawa if Allah say yes. No body can say no.
Ku kalleni sama da k'asa kunsan duk cikin ku na zarce ku ba yabon kai ba in banda ma shirirta kufa kun Girmen kamatayi kuja girman ku, ke kuma Sady wlh kin d'auko Roman dafa kanki ki sani wlh da ina tunanin hkr da Shureim Amma wlh yanzu kin sama sai na Aureshi kuma wlh sai na k'unsa miki bak'in ciki idan neman miji kike kizo zan miki hanya useless jobless kawai" nan tabar wajen.
Da mamaki suka bita da kallo suka saki dariya Ummi tace Ammafa yarinyar ta hadu inafa tantama da kikace yar aiki ce" Sady kuwa k'wafa tayi tace "kuzo mu tafi, wallahi koni ko ita kunsan dai ko aschool bana missn abinda nakeso"
Husy kuwa Motar ta ta shiga ta zauna ta kifa kai tana kuka dole ta takawa Sady birki Murmushi tayi ta latsa kiran Tweeny daga can ta d'auka tace gata nan kamar 30 mint sai gata nan ta shiga Gaban motar suka ja.
Hassy tace "tweeny muje musai icecream Husy tace "Okey dea" sunje sun saya suka zauna suna sha husy tace hassy "dama School namu Sady take? "Nima bansani ba kinsan bazata wuce nan din ba" husy ta cije leb'e "Hmmm yau taso tozar tani agaban k'awayenta ni bansan me natare mata ba" hawaye ta share.Hassy tace tweeny kin Mata kafa ne tanasan saurayinki shiisa ta takura miki so take ki bar Mata Shuriem."
Husy tayi dariya "nikam wlh bazan bar mata ba." Hassy tace "Weldone dea kodan hakan ma ki dage har ai Aurenku da shi domin sai mun bata mamaki" husy tayi Murmushi nan suka gama suka tafi gida.
Suna zuwa kamilu ya ta resu hannnu duk fulawa Husy tace "bro meye hakan?" yace "Gogggo ke D'an wanke shine fa nake taya ta mai nake toyawa" Hassy ta rik'e ciki "wayyo Namji da suna Hajara" kamilu yace "se kunzo kuna Lashe hannu" koma wa kitchen yayi ya d'auko su tumatur da Albasa yana yan kawa Gogggo na saki.
Wanka suka je sukayi suka fito suna Goggg abamu d'an wake tace "yara Musammmn ke Hassy ba Saba ci kikai ba, yanzu zaku coi Dad'i zama sukai aka zubo musu Aka matsa leman tsami da yaji suna ci sai santi suke Hassy tace "Goggo za musa rana kina koya mana girkin Gargajiya irin wan nan Lagwada haka,duk da nasan Husy ta iya wasu tana Mangalu" kamilu yayi dariya sis santi kike fa! Kin ganni nano ba abinda ban iyaba ba Bording nayi" suka saka Dariya Hassy tace "Allah Goggo saboda kinga Husy ta iya nikam zaman waje mukai se Aslow, sai de girkin gayu muka iya." Goggo tace "yo ai dole nane so nake Na kai ku d'akunan Mazajen ku kowacce ta k'ware akan girki, nima sai kuna nunan na zamanin." haka suna hira da raha suka gama suna santi.
***********
Bak'in ciki ke cin Muktar yana Office Amma ya kasa tab'uka komai dalili Husy taki daukan wayar sa har Hassyn ma, tsaki yayi komai ta fanjama- fanjam yau ze sanar da Hassy shine Muntarin Husy yasan zata hak'ura ta barwa husy din, da wan nan shawarar yayi ya gama ya koma gida.
Text msg ya aikawa Hassy ta email adresss ya tura Mata yasan ya yiwa Huusy lefi Amma bazai zauna ya cuci kansa ba.
Hassy na zaune tana game candy crush taga sak'o na email ya shigo nan ta bud'e gaban ta ne ya fad'i nan Hawaye suka fara zarya.tashi tayi ta fita tana k'wala kiran hussy Suna zaune suna kallon wani film sai dariya suke kwasa Goggo tace "Aa yaya dai da wan nan kiran?" hassy taja hannnun husy sukayi sama suna shiga ta kulle d'akin.
"Haba sis ashe kin san Muktar shine Muntarinki kuka barni cikin duhu wan nan dalilin ne yasa yake mun wulak'nci" kuka tasa "haba sis Keda abinki me kike tunani daga yau na bar miki abinki,domin bazan Auri Wanda baya sona ba! kuma duk sonda kukayu dacan atsakanin ku baici na cigaba da kasancewa da shiba saboda kece aransa."
Husy tace "tweeny ina kika sani? tace shiya gayan nan ta nuna Mat a sakon daya turo mata. wayar ta karb'a ta karanta .Zama tayi bakin gadon tana kuka ka karya Alk'awair Muntari maisa ka canja hali daga Muntarinkana asali haba."
D'agowa husy tayi "sis ai ya Riga ya wuce domin Munrabu tunda kuma kinga yanzu inada saurayi ke kuma kun fara Soyayy sai Naga kamar yaudararki zaiyi."
Hassy tace "no sis bazan so farin cikina na danne naki ba, nasan kina san sa na hak'ura dashi kawai."
fita tayi aguje tana kuka datan d'akin ta shiga husy ma kukan take nan ta buga wayar Muktar yana kwance yaga kiranta ya washe baki.
Da hanzari ya d'aga.
"Yanzu muktar kayi mani adalci kenan? ba haka mukayi da kai ba fa! haba yanzu me kake so sis ta d'aukeka ka yaudareta bakajin tausayinta to wan nan dalikin ba zaisa na Aureka ba bawai don munyi soyayya abaya ba yanzu kace dole sai mun koma, ba haka Rayuwa take ba don haka ni bazan Aureka ba. se kayi hk'r tunda har ka iya yaudarar sis nawa k'it ta kashe phone din.
Wani sandarewa yayi ya kama kai " OMG!"
Husy Ta tashi tabi bayan Hasssy kuka ta ganta tanayi tace "sis bazan kuma luv da Muntari ba kai duk wani namji ma don mayaudara ne wasunsu, dama Muntari naki ne kiyi hkr ki yafen" husy ta ce "sis ya kikeso nayi da Shuriem ko kin manta artabun dake tsakanin mu da Sady kuma kin san ba hkr zai ba sis ke kike ban karfin gwiwa na Auren Shuriem yanzu ban san ya zan ba plss sis."
Hassy tace "tweeny koda ba zaki Auri Muktar ba toni kan na Rabu dashi har abada Allah ya gani dana san shine Muntarin ki da ban bari sonsa ya mini illaba."
Kuka suke husy tace "wlh Hassy bazan Aureshi ba Shuriem na keso danke aka haliccci Muktar shiisa Allah bai k'addara auren mu dashi ba tun abaya. duk wan nan k'alubalen ya faru ne kawai saboda haka Allah ya tsara."
Hassy tace "na sani sis Amma na hk'r da shi" ke kuma yanzu sai ki zab'a koshi ko Shuriem Amma ba hakan na nufin wai Mubar Sady ba sai inda manmu ya k'are. Ke Allaurar ruwa ce mai rabo ka d'suka."
Haka sukai ta kukan su suka gama san nan suka koma k'asa.
*Bayan Kwana 2*
Shi kuwa Muktar duk ya tashi hankalin sa domin dukkan wayar tasu inya buga baya samu duk ya fita Hayyacinsa duk ya kod'e ya Rame ganin ba mafita ya fita gari don zaga yawa ak'arshe yaje gun abokin sa da sukayi karatu tare.
Lemo ya kurb'a. Yace "Aboki ina cikin Matsala na rasa gane kaina plss help me."
Mahmud yace "meye matsala ne? nan ya kwashe komai ya fad'a mai Mahmud yace "tab! Amma kanaso ka had'awa kanka xafi fa domin abinda ya wuce ya riga ya wuce da kasani ka rike ita hassanar tunda kaga ita hussainar dalilin kana Soyayya da Hassy din tace "Aa" kasan tunda blood siaters ne dole ka samu problem to tunda abin yazo sai ka hkr da ita husaiina kadau kaddara ka rike hassana."
Muktar yace "wlh baksan sanda nakewa yarinyar nan bane! na kasa cireta araina idan nace zan tsaya don kamarsu d'aya to zan cuci kaina wlh domin kama da wane bata wane Matslar yanzu duk kan su sun juyan baya."
Mahmud yasa dariya to badole ba Jana neman zauta yara, sai ka nemo wata bayan ga mata nan agari kyawawa. Muktar yace ni ai in ba itaba sai Rijiya."
Mahmudu yace "so da dama Mutum yayi ta hak'ilon abu ba shine alkairi agaresa ba. Shawara kayi istikhara wato neman zab'in Allah idan zaaka so akwai wani Malami da yake istikhara sai yayi ma idan kai baz akai ba sai ya baka wata shawarar ma tareda addua."
Jikin Muktar ne yayi sanyi yace "ni bansan zuwa gun Malaman nan 'yan duba fa!" Mahmud yace "wlh wan nan Malami ne kawai addua yakeyi koya baka kayi da kanka bisa koyar war addinin Musulunci, kai de kazo muje."
Muktar yashafa kansa yace "yau ina busy Amma gobe sai kayi mani waya after na dawo daga aiki sai muje......
By
Queen meemi👑
[3:10pm, 16/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣52❣
*March2017*
*®NWA*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
_Ummyn Khadija agaskiya banda bakin Da zan gode miki sai de nai miki fatan Alheri tnz da kauna❤_
*********
Washegari kuwa bayan komawar Muktar daga Aiki Mahmud ya kira Shi kan zuwan sa, nan yace ya sameshi a gida Direct gidan yaje lokacin har yayi Wanka suka rankaya Unguwar Mandawari.
Zuwan su kuwa ba kowa A gun sai Malamin yana karantar da wani yaro ganin su yasa ya sallameshi,Mahmud suka gaisa Malam yace "mahmud kana nan dama?" yace "eh walh Malam yauma abokina na kawo" ya nuna Muktar Malam yace "Masha Allah Meke tafe daku."
Mahmud ya gyara zama "."Malam mas'ala ce akan neman Aure Shi wan nan abin yazo masa abai-bai nan ya sanar wa Malam san nan ya d'ora Da ya naso ayi mai istikhara ta Aure neman zabin Allah.
Malam yace "MASHA Allah hakan shine dai- de hakan ko yarwae Manzon Allah ya uwarcemu kan mi istikhara a sha'anin Aure sai kaga Mutum yayita bulayi kaga Abu ba alkhairi ne gareshi ba. Nan ya tambayi sunan sa ya ce sudawo nan da 3 days zaiyi Istikhara wanda Annabi ya koyar(duba littafib hisrul muslim akwait aciki).abinda naa gani zan sanar dak Godia sukayi suka aje kudi yace Aa suje yayi don Allah ne da k'yar ya karb'i d'ari biyu.
********
Tunani take Amma tak'i bari husy ta gane Da sun hada ido zata basar Husy na kula Da ita.
Tashi tayi taje wajenta ta zauna kusa Da ita "sis ya kamata ki dai na tunani komai yayi zafi Maganin sa Allah nasan kina k'aunar Muktar kawai b'acin rai ne yasa kika ce kin hk'r Amma nasan yana manne aranki,Amma ta wani sashin ni nafiso ki nuna b'acin ranki kan abinda yayi maki ki nuna kema macece" Hassy tace "hakane na d'au shawarark kuma na dena tunani" tace "yawwa sis akanme wani namiji zai saki kina tunani? ai yanzu an dena hakan" dariya Hassy tayi "kaji husy kamar kece yayata ko,sai wani karyar dakai kike wai irin big yaya din nan, Allah sai yaso nice babba" dariya itama tasa "yo meye Marabar dambe da fad'a".nan ta mantar Da ita suka shiga hirar duniya Da yake yau ba lucture.
******
@4:pm
Sady kuwa tana zaune sai tunanin irin abinda za taiwa Husy take Amma ba idea sai kwancewa take tana sakawa. Sumy dake taje kai tace "dama wani d'an adam d'in shike d'orawa kansa wahala." Sady tace "baruwan mutum Naga zan iya ne"😏
Sumy tace "ayidan mugani dai-de lokacin wata mai Aiki ta shigo "wai Ana sallama Da Antysady" tsawa ta daka Mata Da sauri ta fita ,sumy "tace Abari dai ya wuce, wlh kiyi amfani Da damarki kan ta kubce miki atoh!kalleni nan yanzu cizon yatsa nake mistake danai yana damuna bamai lek'o ni danma ina zuwa school to kazo ka gama ba mashin shini wanda da can Allah ya baka kayi wasarai rai dashi Allah Nazi ya cuceni duk shi yasa na kore samarina masu sona Da gaske kan zai auren Amma she nan kwa shine Mayaudarin Allah bazan yafe ba."
Sady tace "ke dani not desame don haka ba lalle yanda ta faru dake ba ni ta faru dani."
Nan ta mike don fita ganin Wanda ke sallama Da ita tun daga k'ofa tayi tsaki dan nacin yaki hkr wlh yau senai mai wulak'ancin Da Shi akacee ya ganni ahanyama bazai kulani ba.
Zuwa tayi ta tsaya "Faruq gani" yace "ya gida" lfy" san nan tace "yanzu don naci ba zaka rabudani ba ? Wai nikad'aice mace a Abuja n?"
Yace
Bawan nan bane ya kawo ni nasan ina sonki Dan so tunda kin k'ini dole na hkr domin son maso wani koshin wahala, tuntuni na hkr kawai de zan sanar dake daurin aurena next week don na samu nima mai kaunata" Nan ya zaro Iv ya bata yace "Allah ya k'addara saduwarmu ya baki wanda kike so" nan ya juya ya tafi.
Kallon katin tayi ta tab'e baki "da ya fi maka don ni ba tsarar ka bace tayiwu kucaka ce irin sa" mtsww tayi tsaki ta shige gida ganin Sumy afalo tace "ke ashe wai faruq Aure zaiyi har Da kawon iv" Sumy tace tab kinyi saki na dafe amma" tace "ke ni ba sonsa nake ba sai Handsome" tab'e baki Sumy tayi tace Allah ya kyauta.
*********
Bayan kwana 2 su Muktar suka koma gun Malamin yayi masu bayani kan istikharar Da yayi yace "agaskiya lamarin nan kan ita wadda kake so tabbas ba Alheri agareku Da ita hatsaniya ce sosai, sai de ita dayar Naga kamar Da sauki abun naku Da ita a tunanina ya kamata ka hkr Da ita husaina saboda kwata -kwata ba Alheri a tsakanin ku. Duk wata Soyayyar ta da ka keji ka fawwalawa Allah domin shike tsara lamuran mutum don ya jarabashi so Da dama abinda ka keso ba shine Alheri agareka ba, sai kaga Wanda bakaso din shine domin Allah shine Masanin gai bu shiisa Annnabi S. A.w ya koyar damu wan nan istikhara din.
Shawara Da zan baka ita hasanar ka koma wajenta ku sasanta idan Da rabon amAure a tsakanin ku sai kaga anyi san nan kayi ta Addua kan Allah ya cirema soyayyr dake ranka domin ba Alheri atsakanin ku."
Tunda Malam ya fara magana yake zufa sai Mahmud ne yace Nalam "mungode kuma insha Allahu zamu bi abinda kace Da shawarar daka bamu."
Malam yace "madalla kai Muktar kayi hkr haka Allah yaso Matar Mutum kabarinsa idan baka samu wan nan ba sai kaga Allah ya baka mafi alheri agareka Mahakurci Mawadaci Allah yana k'aunar masu hk'r" nan yace "ga adduo I zan baka kaje kanayi na samun nutsuwa aranka" nan ya basu takarda sukayi godia suka tafi.
Tun a mota yake share kwalla Shi kansa Mhamud Muktar ya bashi tausayi domin bai taba ganin irin azamanin nan wanda keson budurwar sa kamar yanda Muktar keson husy haka ba yayi ta bashi baki ,Muktar yace "tabbas Allah shine sarki mutum bai san komai ba insha Allahu zan k'ok'arin cire husaiina duk Da nasan santa ajini na yake .Zan k'ok'arin Maida shi kan Hassanar Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi" Mahmud yace Ameen haka yaje ya sauke Mahmud agida shima ya koma gida agalabaice d'akinsa ya shige ya kwanta kamar mai bacci kamar mara lafiya.
*Bayan Sati daya*
Satin Muktar d'aya yana ciwon so Da k'yar da ban bakin Da Mahmud kemai Da kuma adduoi Da ya keyi yaji zuciayar sa ta samu nutsuwa.
Yau yana office ya gwada kiran Hassy sai ring take bata d'auka ba daga karshe ma aka kashe dafe kai yayi shikansa ya rasa mesa yake kaunar su nan yasa aniyar gobe sai je Abuja don ayita face to face.
Washegari kuwa k'arfe 12 tayimai a Abuja ya sauka inda ya Saba sauka in yazo sai kamar 4 san nan yayi wanka yayi fes mike ya tafi Osokoro.
Maigadi ne ya ganshi suka gaisa kamilu dake gefen Maigadi shima suka gaisa nan ya rufe gate din muktar ya fito daga motar sa ya cewa kamilu ya sanar Da su Hassy yazo nan kamilu yaje.
Suna zaune Goggg na basu Labarin wani buzu mai saida shayi kamilu ya shiga "yaufa saurayin d'aya yazo yana nemanku." kallon juna sukayi Hussy tace "nikam bami da Shuriem zai zo ba, kode Sabon smSauryain ki ne Hassy ?"
Dariya Hassy tayi "ai yace zai zo nace Aa kinsan bansanar Da mum ba." Gogg tace kudai je ba dadi haka nan suka saka hijab suka fita.
Kujeru 3 kamilu yakai musu wata yar rumfa me kyau Hassy na ganin sa ta had'e rai zata koma Husy tace "sorry sis zo muji dame yazo"haka sukaje sai kallon su yake suka zauna kamar me in ina sai de yayi ma Hassy kyau Amma bata nuna ba, yace "nasan nayi katob'ara Amma ku yafeni domin wlh abin ne yayumin yawa. ya kalli husy na janye Maganata Husaina na yarda Da kaddara Allah dama beyi zamu aureba an bani shawara na dauka." San nan ya juya kan hassy "yace kiyi hkr wlh ba asan raina nayi ba insha Allahu kulawa Da Soyayyata zan tattarasu akanki." Dadi ne ya isheta Amma a fili ta tab'e baki Murmushi yayi yace "Husy ki bata baki ta yafeni"
Husy Da taji komai yayi Mata sauk'i taji dadin matslar ta tafara kaucewa tace "karka damu insha Allahu komai zai daideta kaima sai kayi hkr kan abinda zatai ma domin tayi zuciya."
Yace ngd Husaina nan ta tashi tace "na barku lafiya".d'an binta Da kallo yayi then yadawo Da kallonsa kan Hassy dake latsa waya ta hade rai..
By
Queen Meemi👑
.
.
[4:21pm, 18/03/2017] Queen: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣53❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
**********
Sun zauna Jigum-Jigum magana yake Mata amma kanta na duk'e sai latsa wayarta take ,d'an shiru yayi ya sunkwi dakai d'an satar kallon sa tayi ya d'ago ta juya da sauri murmushi yayi ta tab'e baki "am Hassy kiyi hkr bisa abinda ya faru tabbas bazan miki k'arya ba naso Hussy Amma naga abun bamai yiwuwa bane haka Allah ya tsara.But now kece nake so dalili dama can ina kallon ki a Hussy pls mu dawo luv na mu."
Dakatar dashi tayi tace "wato ma ba zaka soni don Allah ba sai ta dalilin sis ko? wan nan dalilin ne ma yasa kaga na hkr dakai nikam ka kyaleni" fuuuu ta tashi zuciyarta na tuk'uk'i Da haushi d'an tsayawa tayi gefen fulawa ta saka kuka Allah ya gani tana son Muktar Amma tayi Dana sanin sanin sa tunda sis natane aransa kawai zai Manage da ita as Hussy da gudu ta shige gidan har tana bangaje Kamilu dake tsaye afalon binta da kallo yayi haka ma Goggo dake zaune sai Husy dake karanta Jisnul muslm mikewa tayi zata bita sai kuma tayi waje yana zaune ya had'a kai Da gwiwa tana zuwa tace "muktar" d'an d'agowa yayi yace "hussy ban san meyasa take fushi ba."
"Hmmm ai dama sai da na gaya maka karka fad'a kace kaine Muntarin da mukai Soyayya dama nasan za asamu wan nan matsalar,shiisa Amma kaki."
"Hussy tun lokacin Da malam ya bani addua ta istikhara bayan yayi mani tasa nima ai naje inayi alal hak'ika idan nayi game da alakar mu da hassy ina jin nutsuwa araina Amma kinga sai da aski yazo gaban goshi komi ya baci.domin ni yanzu na daina Zurfafawa akan komi domin kama taka ne Allah na nashi."
Husy tayi murmushi "hakane maganar ka Amma karka damu komai nada sila Matar Mutum kabarin sa karka damu zan tattausheta." juyawa tayi ta tafi yace nima na tafi d'an tsayawa tayi ta kalleshi na scan shima haka nan ta girgiza kai jitayi kamar zuciyarta ta karye ahankali ta fada "RABUWA CE SANADIN koma meye daba a rabamu ba da duk wan nan bata faru ba,sai de komi nufin Allah ne" shigewa ciki tayi direct saman benen ta hau gunjin kukan Hassy taji tana shiga ta zauna kusa da ita.
"Haba hassy kiyi hkr mana tunda ya nuna yayi maki lefi kuma ya hak'ura sai ki yafe duk maisa ba zaki duba Rayuwata bane tun farko kinga na abinda yayi silar rabuwa ta da iyayena na fada wani hannun sai Allah ya had'ani da masu sona da kuma wadda ta azzabi rayuwata kinga duk wahalar da nasha rabuwa da iyayena ne ya jawo Amma kinga haka Allah ya tsara kuma nayi hkr lokacin Dana san gaskiyar wace ni,san nan Soyayyr mu da Muntari munyi kamar ba zamu rabu ba munci burin Aure to Allah bai k'addara zamuyi Aure ba rashin yiwuwar Auren mu yasa Shi yabar garin ya tafi karatu,ni kuma kinga har cewa akai na Auri mudi alokacin bana sonsa amma saboda Biyayya yasa na amince hakan ya gudu ganin bai so na ta dalilin hakan yasa na kuma shiga damuwa da k'unci da wahala Wanda aka kaini aiki kinga Sanadin hakan Naga iyayena daba don duk wad'an nan abin da suka faruba ai nasan da tuni da Auren Muntari akaina toin Allah bai nufa ba,kuma tun rangini ran Zane."
Numfashi ta d'aanj san nan ta cigaba mak'sudin zan cen nan kuwa! Allah yayi kinga Muntari bazai Aurenba Amma kinga Allah sayya sa kuka hadu Wanda kinga tsatson mu d'aya kinga ni dake twins ne shiisa Allah ya saka masa sommu .Allah mai girmaa mai shirya lamura yanda yaso kiyi hkr Muktar yana da matsayi aguna ko badon so ba ya taimaken abaya plss ki hkr."
D'agowa Hassy tayi "naji zan cen ki sis na gane insha Allahu zan gyara" rungume juna sukai. hassy tace "amma fa sis dole naja class saboda yad'an famin wulakanci" Husy tace kija kad'an don karya tsinkei" dariya tasa suka tafa sukai san nan suka sauka k'asa.
Goggo tace "oh ni "yasu! wad'an nan yara sautari d'aya daga cikin ku sai tahau sama tana kuka amma sai ku sauko kuna shewa" Hassy tace "Gogg ai kin san twnis akwai had'in head." dariya tayi tace "ja'ira randa za akaiku gida jenku Naga yanda zakuyi"
kamilu ne ya tawo da Wata 'yar roba ya mik'awa Gogg lallene ya kwab'o mata rik'e baki husy tayi "kaide kamilu komai ka iya!" Goggo tace "kamilu kenan ai nida Shi agida muna aiki muna hira ai shiisa ki kaga ko ina k'afata k'afarsa" hassy tace ai dama na mamajo ne lokacin da zai Aure naga yanda zaki."
Kamilu ya d'ago muna tare domin duk kudin dazan yi to inna tashi gina gida da shashin Goggg agidana" Goggo tace "Allah sarki Autana."
Husy tace "yawwa juya Dady yayi waya da Mum lokacin kina bacci Goggo sunce agaida ke" Goggo tace "ina amsawa"
Hassy tace "sis ya kamata fa gobe muje muyi k'unshi ko bak'i ne da Saloon" tace "oke sai goben."
Washegari weekend ta kama Saturday basu da lucture a Round 3 suka tafi CUTE ZAHRA BEAUTY SALOON & HENNA shago ne Babba suna Saloon gyaran jiki k'unshi, da dai sauransau 'yan mata ne wajen 5 awajen ko wacce da abin da ake mata suna shiga dama matar Musulma ce ta tawo "welcome my special customer" murmushi sukayi ta kalli hassy long time ina Suhaima Amarya? kun b'uya" tace "wlh bama nan ne Amarya kuma sun tafi Honeymoon itada mai house nata."
"Eyyya! wan nan sister naki ce ko ? Hassy tace "eh" nan ta tambayesu mai za amusu su kace k'unshi da Saloon nan Zahra ta kirawo wata daga cikin yaranta tace ta fara musu Saloon hira suke kad'an- kad'an suna 'yar dariyar su. Jin k'ararar taunar cingum sukayi kas! kas! fus! fus! suka juya Sady ce da Lubna suka Shigo zama tayi Sam bata kula dasu ba sai da Zahra ta tawo "welcm Sady" me za'ai miki? tace "Steaming" nan idonta ya sauka akan husy taja wani wawan tsaki.
D'an kauye yazo birni" suka sa dariya itada Lubna.
Hassy ta had'e rai suka basar wata ce tazo dan shafa Mata man da ake steaming ta Zame d'an kwalinta kan nan ba tada gashi su hassy suka kwashe da dariya gwi da yara kenan!.
Sady ta k'ulu sosai don tasan da ita suke don dama bata da gashi.
Bayan kamar 1 hour aka gama musu Saloon aka fara k'unshi yayi balain kyau abinka da farar fata,k.k'irr wayar Husy ta kama ruri ta d'auka a slowa ganin Handsome ne a wani yanayi tace "Husby" Sady ta d'ago gabanta na fad'uwa ganin yanda husy ke waya tabbas tasan da Shuriem take nan taji kamar ta shak'e husy.
Jitayi husy tace "oh dear I missd u ,i want see u" Dan Murmushi tai "Okey dea i'm waiting" ta kashe wani d'an fari tayi tace "tweeny yanzu Shuriem zai zo ya ganni wai dama yana kan titin nan zai koma gida" Hassy tace "Weldone dear"
Sady ji tayi zaman ya isheta Allah Allah take agama mata ta k'addamar wa da Husy tsiya.
5:00 aka gama musu sunyi kyau lokacin Shuriem ya k'araso suka mik'e wayarta tayi K'ara "okey dea gani nan" mik'ewa tayi ta kalli Sady tai murmushi ta fita.
Afusace Sady ta mik'e "Zahra ina zuwa plss "tace oke
Tana fita taga Shuriem shida Husy a farfajiya Shagon tsaye sai yaba kyan fulawar yake, gani tayi sun juyo alamar zata koma shagon ,yana wan nan tafiyar tasa wadda ke fusgar Sady.Zahra ce ta fito zata aje abu Shuriem ya tabmbayeta list d'in abunda za'abiya ya tambayi Zahra tace "oga ai an sun biya tun damu" Sumar sa ya shafa "no karbi na baki kyauta ne don naga Amarya ta ta fito sosai" washe baki zahra tayi "Thank u oga" ta koma ciki Tace "Hassy ur Sister agaskiya tayi sa'ar boy frnd gashi handsome ga kyauta."
Hassy tace "eh wlh Zahra ai shiisa Mata ke sonsa Shi kuma yace sai sis Hussy ko garin ba kowa." Zahra tace "ai Sis naki tana da kyau sosai har ta fiki kyau fa!" hassy tace "kai zahra ai kamar mu d'aya."
Sady kamar ta kurma ihu Lubna ma haushi ya isheta afusace ta futa taje ta bayan Hussy ta juyo da kafad'arta 'yar k'ara Husy ta saki don jin kafadarta tayi zafi domin da kyau taja. Juyowa tayi taga Sady na Jijjiga tana harar ta idanuwan ta sunyi ja.
Shuriem kuwa wani banzan kallo ya bita dashi da mamaki akan face nasa irin k'arfin halinta yana huci...
My fans ga wan nan ba yawa abubuwa sun min yawa shiisa bana post kullum..
By
Queen Meemi.👑
[5:32pm, 19/03/2017] Queen: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣54❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_
***********
Zuciya ce ta d'ebi Sady ta kai hannu zata Mareta. Jitayi an rik'e hannun nata da k'arfi an kai mata mari juyawa tayi sukai ido biyu da Hassy fusge hannun ta tayi zatai magana hassy tace "ba kida word da zaki fad'a domin komi akai miki ke kika janyo."
Husy dake sosa wajen ta wurgawa Sady harara itama ta wulla mata tace "wlh duk me zakiji sai de kiji domin Shuriem yayi maki nisa nawane kibi wani sarkin domin nawa ya miki nisa,dafa da yanzu ba d'aya ba karki k'ara saka dirty hand naki ki tab'a ni, ko ki dakeni haba! kizama mace me class mana, ai wallahi da nice ke sai de son Saurayi ya kasheni dana nuna mai ballan tana ina hauka agaban sa wai don ya soni Mutunci ai madara ne,don Allah ki gane mana mutum na k'ara girma yana shiga dawa."
D'aga hannu tayi zata mareta tace "kul! Ahir dinki karki K'ara kai hannu Jikina kingane don naga ke saurin hannu gareki."
Sady tace "ke ki sani wlh sai na rabaki da Shi koda bazan Aureshi ba domin kwata -kwata bai dace da yar kauye irinki ba." dariya hassy da hussy suka saka san nan suka tafa hassy tace "ai baby kinyi sake d'an zaki ya girma ,domin wlh d'an hakin daka raina shikan tsone ma ido gashi kuwa tweeny ta tsone idanuwanki,koda yake hausawa sunce samu yafi iyawa.'
Shikam yana jikin motar sa cike da takaici wani wulak'ataccen kallo ya yiwa Sady domin bai da time d'in magana da ita sai de dole ya taka Mata birki gurin Hussy yace "finest ni zan tafi wacceen yarinyar ta b'atan rai plss kema kubar wajen don zan iyayi Mata kwaf d'aya inta kaini end."
Daria hassy tasa hankali taiwa Sady gwalo.
Hussy tace "Okey dear semin waya" motar sa ya hau ya figa haka hassy ma taja hannun husy suka fad'a tasu motar suma suka ja.
Kamar gunki Tai atsaye ta kasa motsi huci kawai take lubna tazo ta dafa ta "frnd ya da ajinki kina biyewa wadan nan yaran banso kikai magana ba, domin bada kanki kike agaban sa hakan fa bashi zai sa ya soki ba kinyi kuskure don ba kiga yanda 'yan matan can suka fito ba suna kallo haba sai dariya suke suna cewa gaki big gal amma kina abin yara, har cewa suke Husy tafi birgesu."
Sady ta fashe da kuka ban san kalmar da zan miki explain domin sonda nake ma Shuriem wlh ban san ya zan ba , kishi ke cikani duk yayin dana gansu tare plsss help me."
Liubna tayi dariya "kece ance tun-tuni ga Simple way farat daya zasu rabu kin zauna waike mumina kibar komi ahannuna ko kin mantani ne hmmm."
Sady ta tsaya tace "koma meye ayi wlh sedai ayi biyu babu domin da narasa Shuriem gwanda ko wama ya rasa." da k'yar taje aka karasa musu suka tafi gida.
**********
*Bayan wata daya*
Rayuwa sai dad'a tafiya take komai na wakana daki- daki inda tsakanin hasssy da Sady akoda yaushe husy ke wining sady taci alwashin saita Rabasu ita da lubna sai shige da fice suke Wanda ni ban san meye ba sai de mungani.
Ayau su Husy suka gama first semester exams,shiri suka shiga yi domin tafiya k'auye hutu sun bugawa Dady da mum suna son zuwa Bunkure nan Dady ya turo musu da Kudi ta accnt don suyi tsaraba domin Washegari rankaya wa za suyi har su Hoggg inda zasu sauka a kano su kuma awuce dasu.
Washegari da safe misalin karfe 10 suka d'au hanyar kano basu su kaje ba, sai 2 bayan sun sauke su Gogg da kamilu sunyi sallah driver ya wuce dasu Mangalu.
K'arfe 5 sukaje K'ofar gidan malam suka tsaya suka fir-fito suka shiga driver ya bisu da trolley nasu da tsaraba bayan yayi Sallah ya kama hanyar komawa kano.
Jummai ce kad'ai atsakar gidan da gudu husy ta Rungumeta Jummai tace mutan Abuja sai yau tace hassana ya kika tsaya runfar ta suka shiga harda kayan kallo lalle su Jummai anci gaba ko ina fes fes hira ce ta b'arke a tsakanin su da gudu Dan jummai yazo ya samesu yana oyoyo husaina ta rungumeshi suna dariya basu dad'e ba akai kiran sallah sukaje sukayi suka ci abinci kafin isha malam ya dawo yayi murnar ganin su husy taji dad'i ganin su kowa fess don malam har babur ga reshi nan duk suka firfito da tsara suka basu don har ta gwamma da Dije suka bayar hassy tace "yaude zanga muguwar nan" Jummai tace ay yanzu ta zama abin tausayi hussy tace tab! Allah ya kyauta hassy tace "ke gobe muje muga k'wak'waf hussy tasa dariya "kai hassy."
Itama dariyar tayi "yo koma meye ai ita ta jawo" Jummai tace "wlh kuwa hassana."
Washegari wajen 11 sukayi wanka suka fita d'an zaga gari Sun wuce ta gidan su Muntari husy tace "yauwa ga gidan surukanki hassy" dariya tayi "to meye saima na shiga" husy tace "ai kuwa da kin bar abin fada".sunje gidan iya suna ta sallama shiru daga can suka jio kamar magana sai suka shiga d'akin iya ce kwacr da alama bacci take taji sallamar su ta tashi "wanake gani kamar husaina" tace "nice iya" tace sannu 'yar albarka suna d'an tab'a hira Husy tace "ina kwa gwamma" iya ta tabe baki kede yar nan kina da kyan zuciya har kike nemanta, ta tafi Bara kin san tunda ta rasa k'afarta shikenan kuma ta tsiri Bara cikin bunkure suke shiga suda sauran mabaratan."
Jusy tace "Allah yayi mana mekyau" nan ta aje turmin atampha guda 2 da kudi tace na gwamma haka ta bawa iya ma sai godia take tace duniya kenn.
Suna fita hassy tace "ke dak'yar nake hadiyar miyau gaskiya suna kazanta" husy tace "ai dama gwamma nada k'azanta hassy tace inna jummai kuwa wlh kamar ba akauye take ba,ga tsafta ga iya girki. Amma naso ganin ta wan nan Gwammar muguwa." husy tace "ai kan mutafi zaki ganta."
Sun koma gida suka zauna husy tace "ashe Bara gwamma keyi? jummai tace tun yaushe wataran ai da dije take tafiya." husy tace Amma "ai Naga dije na zuwa Makaranta. Jummai tace ke tadena taki" "to ina mudi" jummai tace "ai Mudi yayi aure da kyar malam ya sashi agaba dole sai da ya nemo matar,tunda akai auren kullum cikin sulhu malam yake har saboda fad'a kamar kaji ai ni se yanzu nasan ilimi nada amfani domin wlh da ace mudi yayi duk bazai na irin hakan ba har dijen ma ai samun maslaha yanzu tare da malam suke tafiya kasuwa domin Mahaifinki wani zuwa da yayi ya tarar da fad'an duk dama rashin sana'a ne ya bashi jari" husy suka kalli juna da hassy "dama Dady na zuwa? Jummai tace "ai yana yawan zuwa ko yayi aike kafin su koma ai mukam ba abinda zamuce Sai godia." hassy tace "mune da godia."
Husy tace "to yanzu inna Mudin sun Dena fad'an?" tace "eh man yanzu ai yana sana'a sede abinda ba'a rasaba...
Wayyo Battery low fans ga wan nan ba yawa
By
Queen meemi.
[4:44pm, 21/03/2017] Queen: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣55❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*******
Tunda Muktar yaji labarin zuwansu Mangalu shima ya tarkato ya tawo, tun da yazo bashi da aiki sai aukin lallashi yake gun hassy har ya samu ta saki jiki .yauma da suke zaune a soron gidan gidan Malam suna hira Muktar yace "Hassyna kafin ku tafi nake son turo magabata na, kawai ayita ta k'are." katsahan taji Maganar tace "haba de?" yace "wlh da gaske don an matsan agida" ta juyo suka had'a ido yace "ki amince" tace "senai shawara domin kasan su Dady basa nan" yace "na sani Amma ai akwai 'yan uwanku kosu sa karb'a" murmushi tayi "dear kabari nai musu waya duk abinda sukace I wll tell u" yace "tnx babyna."Bayan ya tafi ta shiga ciki lokacin har inna Jummai ta sauke dambun da suke itada Husy da gudu taje ta rungume husy tace "albishirunki tweeny" tace "goro" Dan dariya takumai "yau de Muktar yace zai aiko maganar auren mu" husy tace "ke dan Allah!" nan Jummai ta d"ago "me ake cewa ne?" nan suka sanar Mata tace "hmm lalle Matar Mutum kabarinsa Allah yayi bada Husy bace." Nan husy tace ay inna dama komai nufin Allah ne, yanzu sai agayawa su Dady aji mai zasu ce ko?" Hassy tace "nima haka nace mai. Bayan sunci sun sha Husy ta bugawa Mum waya ta d'auka nan ta sanar mata tace abari nan da 1 week zasu dawo domin Arif sunyi hutu Dad'I ma haka yace. husy dake mak'ake da waya ta daka tsalle "Allah ya kawo ku lafiyya" tana gamawa tace "tweeny Mum tace abar maganar next week zasu dawo sai ayi" Jummai tace "hakan ma yafi kuwa."
*Bayan sati daya*
*******
Su Dady suka sauka A Nigeria sai da sukai kwana biyu Wanda yayi dai-de da saura kwana d'aya biyu hutun su Hassy ya kare san nan suka zo Mangalu malam yayi masu tarbar arziki, bayan sun huta Dady yayi maganar Wanda ke san ita Hassy nan ya umarceta data bugama Shi Muktar d'in waya hakan kuwa akai tayi mai waya bai ma Dade da zuwa garin ba. Direct gidan Malm yaxo asunkuye ya shiga ya ga idasu sun yaba da shi yayi masu bayani Dady ya kad'a baki yace "naji yace shidan me garin nan ne inace shine wanda aka kusa Auren sa da husaina abu bai yiwuba" malam yace "shine" Dady ya had'e rai "Sam ba zata sab'uba" ya kalli Muktar "yaro kayi hkr domin kaga tun farko babanka yace baya so, kaga yanzu idan yaji 'yar uwar d'ayar ce bazai yarda ba" zufa ce take ta karyowa Mukatr wan nan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa Malam dafe hannu yayi domin dama yasan za'arina a sanyaye Mukatr ya tashi ya fita kamar zaiyi kuka Hassy kuwa tana d'akin Jummai tana kuka domin taji yanda akayi sai hkr husy ke bata tace insha Allahu zai sakko.
*****
Shirin komawa Abuja sukayi suma su Hassy suka bisu su Malam sun yi kewar Su ,sunkai dai de titin da zai fudda kai babban titi husy taga Gwamma da taron mata suna bara nan tace wa Dady Adam tsaya zata bada sadaka tunkan su tsaya su Gwamma sun cika gun, ta zaro 1k ta mikawa Gwamma suka had'a ido Motar su taja. Gwamma sai kuka take tana domin tayi danasanin rayuwar datai abaya.Tafiya akace yankin azaba sai wajen k'arfe 7 suka je Abuja Hassy wani k'aramin zazzab'ine ya rufeta.
Ab'angaren Muktar kuwa hankali tashe yaje gida Goggon sa na zaune ta Ganshi abirkice tace "yadai?" yace "Goggg kunga ni ko! da tun farko ba ai haka ba wlh da Dadynta bazai hanani ba" tace "wai meye ne? Kake abu kamar zararre" zufa ya Goge "yace bazai ban Aurenta ba saboda da ance bazan Auri bazan auri husaina ba don ba tada Asali yace tunda Jininsu daya,shima bazai had'a iri damu ba sedai nai hkr." Goggg tace "hmm matsala ni na rasa mesa kake san wad'annan mutane wai to yaran nan su kadaine mata? Haba ga 'yar yayata nan Aliya tana sonka kana watsar da ita." Muktar yace "haba Goggo yarinyar da karatun sallah ma Inaga bata iya ba,bafa ta zuwa makaranta" tab'e baki tayi 'kai nifa ba ruwana domin ai da kunya ma muje muce abaka Auren 'yarsu bayan da munce bama kaunar dayar ai sai suce kwad'ayi ne, sai de ka bari Yabanka yaje" ji yayi garin yayi zafi ya tashi ya shige d'aki kamar mara lafiya.
By
Queen Meemi
[5:20pm, 21/03/2017] Queen: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣56❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
********
Kwana biyu duk ya zabge domin son Hassy yaji na shigar shi, ganin hakan ya dage da Addua kullum Sallahr neman zab'in Allah kan idan Auren nada alfano Allah ya tabbar .Amma kullum ji yake yana dada san abun,da k'yar ya koma kano cike da k'aunar Hassy ji yake duk kaunar da yayiwa husy shafar mai ne kan wan nan ,jikinsa na bashi muddin ya rasa ta to zai iya shiga wani hali.
Ta b'angaren Hassy kuwa kullum kuka yauma da take kwance ad'aki tana aukin kukan Mum ta shiga "yanzu ke hassy kan ance ba zakuyi aure ba shine kike kuka karki manta fa Dady yace kar ya kuma jin ambton sa abakin ki." husy ta shigo da Panadol Suhaima abayan ta da tsohon ciki suka zauna Suhaima tace "mum ni ina gani kawai da Dady ya hkr" husy tace "eh wlh Mum ni nasan ta dalilina ne abun ya faru Amma kunga ita da ban ni da ban .Misali da ayanzu ne ai nasan ba zasu k'i Auren ba ,tunda kinga da Usulina Mum ki taushi Dady." Suhaima tace "mum kin san Hassy da sa Abu arai wlh yanzu seta fige" Mum tace "kusan Babanku da wuyar sha'ani musammm aka tab'oshi amma zan taushe Shi" nan ta fita husy tace hasssy ga Magani kisha" dai de lokacin wayarta tai k'ara sunan Muktar ne akai Husy tace "ga shi kuyi magana" jiki asanyaye ta karb'a ta kara akunne can yace Hassyna I missd u so much wlh, u are on my mind & in my heart ban san word dazan miki explaining ba,yanzu hakan gani Banda lafiya, plss meye shawara." Hassy ta share hawaye saboda jin dadin kalamansa "yanzu muyi ta addua" yace "ko jiya saida Babana yaje gun Malam shima yace baruwar sa" Hassy tace "insha Allahu zai sakko" Nan sukayi sallama ya kashe.
**********
Kwana 2 tsakani su Malam da Maigari suka tafi abuja domin muktar ya damu kansa, kullum zarya gun Malam kan ya shige mai gaba ya dawo kamar mara lafiya don har zazzab'i yayi ganin hakan yasa hankulansu ya tashi musamman Maigari sukaje gun malam sun bada hkr kan abinda ya faru da malam yace sai de suje Abuja a sami Maslaha wan nan dalilin ne yasa suka tafi k'arfe 11suna can sabida da wuri suka tafi yau ne farkon zuwan Malam gidan su husy tabbas sun san Dady ko a masu kudin ma gwaska ne , musammn Ganin irin gidan. ya Tare su a mutunce nan sukaci abinci mai rai da lafiya san nan. Malam ya fara da ban hak'uri ya gayamai mak'sudin zuwan sa. Maigari yace "Alhaji muna neman afuwa da abamu Auren yarinyar nan, domin munsan munyi kuskure bisa rashin sani yanzu hakan yarona yana nan ba shida lafiya duk akan hakan." Dady yace "banji dad'in abunda akaiwa jinina ba ,duk da labari akaban Amma naji haushi sosai m;Malm yace Alhaji ayi hkr koni nan abin yayi min ciwo domin ba irin k'alubalen sa bamu shigaba ba Amma tabbas nasan Matar Mutum kabarinsa dama haka Allah ya tsara shiisa nima na sakko na hkr." Dady yace tabbas Malam kai me iya bayar da auren yarana ne domin kimar ka da girmanka da nake gani saboda hakan na amince." .Maigari yace "mungode Allah domin ku kun nuna girma wanda ada ni ban nunaba ngd Allah ya saka" Nan sukayi haramar tafiya husy ta fito suka gaisa da Malam tana murnar ganinsa sunyi hira da Malam san nan ta tafi inda Dady yasa driver ya tafi kaisu.
***********
Farinciki da walwala da samun kwarin jiki Shi ya wadatu a jukkunan wad'an nan masoya, nan duk suka ware suka cigaba da harkokin su inda dangin Mukatr Wanda ke zaune akano wato inda Muktar yayi karatu suka kai kayan Mungani Munaso gidan kakan ninsu Hassy tare da tarba ta arxiki.Nan fa hankulasu suka huta suka cigaba da zuba Soyayyar su Nan Dady yayi Umarni da itama husy saurayinta ya motso, bataji d'ar ba alokacin da Mum ke gaya Mata domin tasan Handsome kullum maganar sa yaushe zai turo ,nan ta cewa mum cike da kunya "ai dama ko yaushe yana mun Maganar, Amma idan ya kumai mun! zan gaya mai" Mum tace "tom 'yar Mum .da hayaniya Hassy da Arif suka shigo falon "kinga kibani ipon dina" tace "bazan bayar ba sai na ga wani abu" haushi yaji yace "ai gwandama duk ku k'ara gaba dama kun cika mana gida" Husy tace "ka gaji damu ko? sai muntafi zakai missn d'in mu" Mum tace "atoh sai de yayi ta bin gidajenku."
B'angaren Shuriem kuwa...
By Queen Meemi👑
[5:44pm, 24/03/2017] Queen: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣57❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*_Fans kuna hkr wlh wutar muce take lalacewa shiisa bakwa ganin ina typin kullm amma in aka gyara komai zai nomal .Da tuni mana gama book. Godia nake masoyana Masu support Dina Allah yabar kauna.❤❤_*
*********
B'angaren Shuriem kuwa yana zaune a office aiyuka sun hade mai yana so ya kira husy ba dama, nan yayi sauri ya gama ya mik'e cike da kasala ya umarci sakatariya data getta gun Da sauri ya fita dai -de lokacin Sady na cinno hancin Motar ta, ta glass ta gano Shi yana k'ok'arin shiga motar sa da sauri ta fito amma kafin tayi magana yaja motar sa @360 yabar gun.
D'an tsaki tayi ta shiga tayi ribas tabi bayan sa, b'at ya b'ace mata nan tad'au wayarta ta kirawo shi ganin ring yayi tsaki yak'i d'auka don yasan 'yar nacin ce. ganin bai d'auka ba yasa ta kirawo Lubna daga can ta d'auka "helo Sady" tace "k'awas da matsala fa wlh Sam munyi sab'ani kinga yanzu ina dialling no d'insa baya d'auka." Lubna tace ba akwai whtsp ba? ki tura mai tanan tunda akwai a wayarki dayan ba matsala bace gobe ma rana ce" Sady tace hakane dea shisa nake sonki ngd" nan suka kashe a tare.
********
Direct gidan su ya tafi da mMaminsa yaci karo tace "yawwa D'an halak kaji ambato yanzu muke maganarka nida Dadynka kande magaanr aure yace "Momi har guda nawa neke" tace "tafi can" murmushi yayi ya zauna "me kuka dafa yau mami?" "ba irin cimarka bace Alala nayi" yace Mami bani naci I'm feeln hungry" kallon sa tayi "kaine ance kayi Aure ka zauna ruwan ido ga 'yan Mata na sonka kojiyan nan wasu sunzo gaisheni suka ce kai ogansu ne nikam nasan da biyu" Shuriem yace "Mami suwaye?" tace "kaini rabani idan zaka fito da mata kayi domin kaga azumi ya kusa nafiso ace da aurenka." Dan sosa K'eya yayi "mum lokaci kawai nake jira amma na samu yarinyar anan Abuja take." Mami tace "Allah yasa dai domin in bakai Magana ba sai de kaga Amarya ad'akin ka." Dariya yayi san nan ya mik'e ya shige bedroom nasa, tunani yake yaya ma za'ace wata tazo shidai yasan ba finest bace saboda tana da tarbiya da kunya amma yana tunanin ko Sady ce Dan tsaki ya saka "dis gal na da problem wlh" k'arar Msg ne ya shigo aka rubuta kamar haka: ka bud'e whtsp naka kaga abin mamaki.bai kawo komai ba ya bud'e msgs suka shishshigo can yaci karo da wani picture daya razana shi bai Gasgataba sai daya kuma k'ura ido tabbas itace amman Sam ya kasa Gasgatawa take kansa ya fara ciwo nan ya tura Ma husy hoton ak'asa yasa husyna meye wan nan? dama yaudarata kikeh? Bayan ya turamata ya tashi yana kai-kawo idansa yayi ja tare da dafe kai abincin da baici ba kenan.
********
Dariya suke k'yak'yatawa da alama sunji bauri domin wani Film suke kalla na Comedy k'arar msg d'inne ya shigo kan wayarta Wanda alarm d'in Special ne ta sawa Shuriem nata da sauri ta bud'e taga yace ta bude whtsp bud'ewa tayi na d'an mintuna ya shigo d'an baya tayi ganin Hoton nan hankalinta ya tashi. d'aka Mata duka hassy tayi "kinga kalli nan" jin batai magana ba yasa ta juyo taga tana hawaye husy tace "hassy kinga me akaimin?" Karb'ar wayar tayi taga Hoton Hassy ne itada wani saurayi Wanda ma bata san shi ba ya mak'alk'aleta hannunsa na cikin rigarta ja da baya tayi "tweeny plss kece kuwa?" husy tace "nasan kin trust Dina kin san ba ni bace wlh sharri ne" ta fashe da kuka hassy tace "ba mamaki sis domin duniya ta b'aci tabbas za 'aiya abinda yafi hakan domin nasan aikin Sady ne to wlh ba zamu yardaba ai wan nan b'ata suna ne." sai huci take ta karb'i wayar hussaina ta lalubo number din Sady k'irr ta d'auka Wani wawan tsawa hassy ta yiwa Sady "ke hawainiyarki ta kiyayi ramarmu! duk makircin ki wlh ba ki isa ba ,macuciya me farutar saurayi." dariya Sady tasa "ai na riga na gama da ku domin Shuriem ya barta kenan" kafin hassy tayi magana ta kashe dab'as ta zauna kan gadon ta dafa bayan Husy "dama nasan Sady ce to wlh dole mud'au mataki" husy ta share hawaye "ni na rasa ma tayaya Naga hotona sai de kayan ne kin san bamuda irin sa Amma mayafin jikin kin san ina da ita kuma ga face dina nice" nan ta kuma fsshewa da kuka ta kirawo Shuriem ya dauka husy ta fashe da kuka har ransa yana jin kukan amma bakin ciki ya hana yace komai "wlh bani bace sharri ne yanzu Sady ta gayan confusing ya shiga cuz ga face nata b'aro- b'aro duk da awaye yake yasan tabbas za'a iya had'awa Amma bakin ciki da kishi yake inyaga hannun gardin a rigarta sayyaji haushi sai yaga kamar husyn ce duk da ya santa da tarbiyya bece komi ba ya kashe.
**********
Kuka tasa "shikenan ta gama dani ta cucen haba" hassy tace "barta idan tasan wata aiba tasan wata ba,wlh sai mun nuna mata ita k'aramar 'yar Air ce" haka dai sukayi ta fesa maganganun inda hankalin husy ya tashi.
wajen 8pm husy na zaune kowa na hira itakam ta kurawa tv ido kawai Wayarta tayi K'ara ganin Sady ce yasa tayi maman bene ta d'auka afusace "ke mara kunyar k'arya karki sake kirana" Sady ta fashe da dariya "ai kadan kika gani badai zaki takara dani ba! hmm ke clean din kwanan nan ma, balle ni da acikinsa na tashi, to wlh akan Shuriem sai de komai ya faru ,kuma ki sani saina watsa hotunan a media kowa yayi tir dake." husy da jikinta ya hau rawa "idan baki fasa ba bakya k'aunar Allah da Annabi, ga fili ga maidoki" kit ta kashe ta fashe da kuka. dai-de lokacin hassy ta hawo ta tsaya husy tace "kiji wai zata watsa a media" hassy ta dafe kirji "tab! wlh dakwa ta jangwalo" Nan suka shige daki sunfi awa suna maida zance .Mum ce ta shigo ta tarar husy na kuka tace "meye?" nan suka kalli juna da hassy tace "bakomi mum idona ke ciwo" tace "kuma shine kike kuka?" "Aa momi hawaye ne" juyawa tayi zata fita "sai gobe da safe kuje adubaki" tace "to momy."
Shuriem kuwa kishi ke d'ibarsa kamar ya kurma ihu tabbas zuciyar sa yasan ba husy bace amma jikinsa ya kasa aminta domin daya gano hannun gardin nan sayyaji wawan haushi,duk da yasan ba ita bace wayarsa ya dauka ......
By
Queen Meemi
.
[5:32pm, 25/03/2017] Queen: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣58❣
*March 2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*********
Bayan kwana biyu duk abu ya dagule domin Shuriem ko husy ta buga bai d'auka itama sai ta share Amma zucciyar su na manne basa daina tunanin juna,tana cikin bacci k'arar shigar msg ya shigo ta dauka ta duba Shuriem ne ke shaida mata anjima zai shigo, bai ji mai zatace ba ya kashe Amma ya matsu yaji voice nata.
5:00 Shuriem ya cinno hancin motar sa cikin gate din ,ganin wani saurayi yayi a d'an nesa da gate din gidan ya basar da sauri saurayin yazo yana k'ok'arin yi mai magana ganin hakan ya tsaya yace "wa kake nema ne?" Yace "nazo wurin husaina ne" "meye alak'arku juyawa yayi "gal frnd nawa ce" Shuriem yaji mamaki ya kamashi bai sake magana ba yabi k'aramin gate ya shiga inda suka Saba zama kamar mintuna sai ga tanan ta fito ya k'ura Mata ido santa da kishi ya kuma kamashi kanta ak'asa ta zauna saboda kunya da k'yar take magana yace "husy nasan bake bace Amma xuciyana ta kasa hkr wlh wani kishi nake" dagowa tai ta kalle Shi "am so sarry dea" yace "nasan wan nan joblesss yarinyar ce Amma karki damu ina sane da ita duk ta gama shirmenta zan maganin ta" nan da nan suka manta batun suka hau hirar su maidadi.
********
Hayaniya suka ji Maigadi da wani nan. husy ta daga kai ganin kamar kokawa yasa ta kira mai gadi ya tawo tace "meye? yace "yar Dady ai wani ne yazo wajenki wai ni kuma ba aban list da Shi ba" Dan shiru tayi tace "ka koreshi saboda ban San shi ba",Shuriem yace "no barshi yazo don tun d'azu na ganshi sa gudu mai gadi yayi ya koma yace ya shiga gyara riga yayi ya shiga farfajiyat gate din ganosu da yayi yasa yadan murmusa ya fito da wata wayar sa ya kira wayar husy nan ta fara ring @ten times yana kira tana kashewa don bata daukan no daba ta sani ba,Shuriem ne ya kalleta "finest ki daga mana" nan ta d'aga "waye? yace "juyo ki ganni ina kallonki" jikinta na rawa ta juya tare da kashe wayar Shuriem ya jingina da kujera baice k'ala ba, ganin hakan saurayin ya k'araso yace "Aa sweat heart tun a school nake kiranki kin share haba kodan kinyi sabo shine zaki watsar dani" husy ta mike tsaye "niii! Ta ina na sanka,pls kace ban sanka ba plsss ka fitar mana agida." murmushi yayi "husaina kenan! ba kyau yaudara don kin samu wancan had'ad'den to nima ai ba baya ba ,duk tsiya dai munyi luv sosai don haka ga pictures da muka d'auka duk da kince bakyaso dan gulma nan ya fito dasu ya watsa a kan table ya kalleta beauty sai minyi waya" ya juya ya tafi. Hannu tasa aka wlh ni bansan Shi ba sharri ne d'aya bayan d'aya yake kallon hoton kala -kala wasu rungume da shi wasu suna kallon juna Shuriem kuma Afusace ya mik'e ya watsa Mata pics d'in zatai magana ya dakatar da ita "bana son any word da zata fito daga bakinki, saboda komai na gani da ido na" juyawa yayi ya fita ransa adagule.
*********
Da gudu ta shige gida ta haye bene tana kuka lokacin hassy na aiki kan laptop ta fad'a gadon tana kuka hassy tace "meye?" nan ta nuna Mata hotunan San nan ta kwashe duk yanda akai ta gaya Mata hussy ta fara huci "lalle sady kinyi kuskure."dafa husy tayi tace kiyi hkr gobe zan San yanda zanyi don rana tayi yau."k'aramin zazzabi ne ya rufe husy wan nan kenan.
*Washegari*
@12am
Hassy ta mik'e tsaye tace "zo muje sis nasan inda zan kai atabbatar min da hakan" husy cewa tayi ba zata ba nan hassy ta cewa mum zata karb'o books nata take ta zari motar ta wani had'ad'den studio taje tana shiga suka gaisa da wanda ke bakin wajen nan ta zauna ta tambayeshi yanda ake had'a picture idan a rabe suke misali mace da namiji da yake sun saba dama dashi nan ya bar aikin ya d'auko wata computer yana nuna mata sample har da zata nuna mai pic d'in sai kuma ta fasa don bata so aga face na 'yar uwarta. Hotuna ne birjik na Mata da Maza sunyi kyau a gabanta yayi editin ya cire kan wani ya sa akan wani saurayin sai kace shine haka ya nuna mata kallonta yayi "kin gane yanzu" tace "eh" nan ta d'an zauna sai tace "nikam ban Naga pics din Naga style masu kyau" mika Mata laptop d'in yayi ta dinga gani zaro ido tayi ganin saurayin da aka had'a pics nasu da Husy kuma ga budurwar agefe wadda aka cire kanta aka sawa Husy hannunsa cikin rigarta wani wawan nishi ta saka tayi murmushi Alhmdlh nuna ma salihu tayi tace ya tura Mata pic d'in a waya hakan kuwa take ya tura maata ta bashi 1k ta tafi tana murna.
********
Da gudu ta shiga d'akinsu husy na zaune tana aikin dube duben waya sai lek'a groups take tana dubawa Allah yasa kartaga hotunan nan domin tasan Halin Sady zata iya watsawa hamdala tayi ta kashe data k'ululin bak'in ciki ne ya kamata don tunda jiya Shuriem yazo da abinda ya faru ta kasa sukuni ta rasa wane mataki zata d'auka jitake kamar tace ta fasa auren Shuriem din ,kuma da mamakin inda saurayin ya santa da fata tayi ta dago kai "tun dazu naga kina tunani ai kisani komai yazo end na samo bakin zaren" ta zaro wayarta ta lalaubo Gellary "kalli nan" da sauri ta karba tace "ke kuwa ya akai kika gano? hasy tace "haba yanda take da ilimi haka muma" zuwa tayi akai editin aka cire kan wan nan ladyn aka saka naki ai duk ya nuna ke bakya ce anyi wani abu ba" "Amma Allah ya isa wlh ban yafewa Sady ba." nan ta fashe da kuka "gashi Shuriem yana fushi tun abun fa ya faru jiya ai wallahi sai Allah ya sakamin,ni bansan taya ma akai saurayin jiya harda no dina ya kira fa." Hassy tace kede yanzu kawai musan yanda za'ai na nunawa Shuriem ya tabbar da Gaskiya, bayan hakan zamu gano waye wlh bazamu yardaba,kuma dole ta hakura sa Shureim" husy tace "kyaleshi tunda har ya yarda , ni na hkr na barmata Shi bazan iya jidalin nan ba" Hassy tace "kiyi hkr kin san fa makirci dole yaji ba dadi .Amma batun wai ki bar mata Shi bata tasoba saide in shine yace ya fasa" nan ta mike "bari naje nai wanka don na dauko rana duk da a mota nake amma ina dan jin zafi,tsunduma kogin tunani husy tayi wanda bata san bacci ya kwasheta ba tare da mafarkin abin sonta.
By
Queen Meemi.👑
.
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣59❣
*March 2017*
_*Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's*_
*********
Washegari kuwa wajen 10 sai ga Sady a office d'in Shuriem yana zaune yayi shigar shadda hartin da wando farare k'al -k'al ya turo hularsa gaba yana ta Rubuce -Rubuce tura k'ofar tayi ta shiga tana karai raya sai kace tarwad'a kujera taja ta zauna bai d'ago ido ba, tadade a zaune san nan tace "Shuriem kaga abinda nake fad'a ko? kaso mai sonka don hussy ba sonka take ba, domin da idona a sch nake ganin ta da wan nan saurayin" nan ta zaro pic ta aje agabansa. "saurayinta ne sosai kowa ya sani don haka ni Sady ni ce mai sonka kayi tunani idan kayi Accept you can call me" da sauri ta mik'e har taje k'ofa yace "wait" nan ta tsaya yace "zoki d'auke haukanki kuma ki saurari Punishment dina san nan nace maki bana yinki, plss ki je gun masu sonki su aureki maana! Domin duk wani makircinki sai de ki gama amma mutu karaba nida fines kingane"
Murmushi tayi ta fita Amma ak'asan ranta kamar ta kwanta k'asa tayi birgima haka taje gida. Sumy na had'a wasu kayanta ta Sady ta zube a gado "sumy nayi-nayi ba irin abinda banba handsome ya kasa ganewa ya nace wa waccen fool gal d'in dame tafini? dame Allah ya rageni? harda zai na min hakan"nan ta fashe da kuka Sumy ta tab'e baki "ai dama duk Wanda yasai Rariya yasan zata zubda ruwa kuma duk abinda kayi za'aima, karki manta irin wulak'ancin da ki kaiwa faruq wlh nasan ko rabin sa Shuriem bai maki ba, nadai gaya miki kiyi karatun ta nutsu kin dace kinada farinjini ma don Naga wani kamal na sonki yana zuwa shima kina wulakanta shi to kiyi ahankali tun kan dare yayi maki."Tsaki Sady tasa ta tashi tace "naji kuma ban d'auka ba" "jiki magayi ai" cewar sumy.
********
Husy kam da safe data tashi sukayi break suka tafi School itada Hassy domin lucture safe ce dasu. Kamar k'arfe 11 Hassy na zaune a Captaria tana try Number d'in Shureim 3 missd call san nan ya d'auka suka gaisa tace "don Allah kazo Cumpus namu akwai wani Abu da zan gaya maka da zaka san gaskiya plss." "Okey hassy zan zo after 2" nan ta kashe ta tafi Lucture.
@2:00 Shuriem ya shiga school din ya faka bakin Bishiya ya kira Hassy dama ta dad'e da fitowa ta fito tazo inda yake ta gaida shi san nan tace "Shuriem hak'ika duk abinda ya faru wlh sharrin Sady ne, domin da bakinta ta gaya mana duk plan ne donta sameka haka saurayin da yazo jiya shima plan ne plss ka gane. bari kaga" nan ta d'auko Pic ta nuna mai ya karb'a yaga asalin pics d,in yace "to na jiya fa? tace shima duk had'inta ne, kaga kenan baruwan husy bai kamata ka d'ora laifi akanta ba" jikinsa yayi sanyi."Hassy ina son sisi naki ne shiisa nake jin kishinta, wlh duk da nasan ba gaskiya bane Amma na samu hujja insha Allahu zan maganin ita Sady." nan tace "yawwa Shuriem." Dai de lokacin Hsusy ta tawo sanye da dogon hijab bata kalli inda yake ba shikam idansa na kanta wani Birgeshi tayi wani d'an Murmushi ya saki ta kauda kai tayi gaba ta shiga motar su .Hassy tayi mai sallama suka tafi ya dade a tsaye yana Murmushi ya shiga Motar sa ya d'auki hanyar fita.
Hasyy dake kwarara gudu a Mota ta kalli Husy tace "yanzu komi Normal, kiyi hkr nasan zai taushi zuciyarki, itakam Sady daga wan nan ta daina domin zami maganin ta".husy tayi murmushi "nifa kaina yau ciwo yake" Hassy tace "ba wani ganin na k'arfen ne ya birkita lissafinki" .Dariya suka saka 3:00 suka shiga gida.
**********
Shuriem kuwa adai-de layin da zai shiga gidan su yaga saurayin nan da yayi pretending as saurayin Hussy nan ya sha gabanshi Saurayin ya fito zaiyi bala'i yaga Shuriem nan ya sandare don ya ganeshi, a nutse Shuriem ya tako ya tsaya yace "wato han baka kud'i ake ka kashe aure ,ko ka b'ata da d'ad'diyar soyayya ko? to kayi na farko kayi na k'arshe" nan ya d'auko hotunan ya mik'a mai, "kaine ko zakace ba kai bane na asalin kuma kazo jiya" nan ya dabirce take Shuriem ya bugawa Police dake kusa domin ya damk'e hannunsa ya kasa kwacewa, ba'a dad'e ba sai gasu nan yace atafi dashi anjima zai zo....
Sai da Shuriem ya koma gida yaci abinci yayi wanka yadan matse barcinsa gajiyar sa duk tabi jiki san nan wajen karfe 5 :00 ya mik'e ya tafi police station zuwan sa Sauryain nan ya gaji ga yunwa nan ya zauna yayi wa DPO bayani kan abinda saurayin yayi don ai musu tsakani, yace ayimai hukunci nan suka tambayeshi dalili ya fad'a kan Sadyce ta saka Shi yayi aikin ta biyashi.ya d'ora da cewa suyi mai rai domin Shike dawainyar gidansu
Nan DPO yace "yi mana shiru kune masu d'aurewa karya lasisi" yace ya a kirawo ta nan saurayin yayi kiranta kan tazo ya samu wata idea, 6 dai -de motar ta ta k'arasa Station d'in tana shiga suka gaya Mata abinda ke faruwa nan hankalin ya tashi suka tambayeta sunanta ta gaya musu. DPO yace "wato ke 'yar gidan Alhaji tanko ce ko shine kike haka, lalle kuwa zan sanar mai" jikinta yayi sanyi Kudi ta zaro ta aje ma Wani kurtu sukace Aa Wanda ya kawo case Babba ne sai de tai hkr.Shuriem ya shigo wajen suka gaidashi ya zauna gefen da Sady take ya kalleta "yanzu sai kibi wani sarkin don husy ta miki nisa." DPO yazo yace "ya sunan yarinyar da sukaiwa haka ,nan ya fad'a Sunan ta dana babanta hankalin DPO ya tashi yace "wait itama 'yar manya ce ashe!" ya kalli Sady "dole mahaifinki yaji."nan ya dauko zai kira tace "plss kayi hkr karka fada" "dole na fada domin idan sukace basu yarda ba fa?"
Dady na zaune dawowar sa kenan wajen 7 DPO ya kirashi ya sanar mai cikin tashin hankali ya tashi yace "yanzu zai zo Umma ce dama a d'akin tace "meye?" yace "kinji Sadiya ce ta cangwalo wai suna hatsaniya da yar Ambassado,r komi ya kaita l yanzu Shi saurayin ita yarinyar wai ya kaisu station ita da saurayin da tasa yayi ma dayar sharri, wama ya bata izinin fita da dare?" nan tace subhanallah tashi yayi ya tafi driver din sa ya mika shi.
**********
Sady ido ya raina fata domin Abun kunya ne agareta .DPO ya umarci da Shuriem yace itama Husy tazo Ana nemanta. Shuriem yace basai tazo ba ga shaida duk agunsa. zuwa Dadyn sady duk aka gaya mai aka nuna mai abinda tayi agun ya wanka Mata mari ,yace "ni zaki kunyata da girmana! wato ki b'ata wa wata suna ko? akan son zuciya kuma 'yar Ambassador to ki sani afagen mulki ma yana sama dani donni yanzu bana cikin mulki don haka dole na baki Punishment" "Dady Kayi hkr" yace "yi min shiru" ya kalli Saurayin kai-kuma anyi Sahorami da za'a baka kudi kayi shirme" nan yace wa DPO itama asata a cell d'in kya k'ara hankalta .
Shuriem cike da girmamawa yace "ba za'ai haka ba, kawai de ta saka hannu nima na saka bani ba ita, kuma ba ita ba husaina domin tana yawan Cusguna mata don haka ai musu Tsakani." DPO ya kawo Paper ta cike tana kuka shima haka Shuriem ya cike shima. Saurayin kuma akai mai afuwa kan ya kuma sai yayi watanni acell nan duk suka tafi. Dady kuwa kamar ya cinye Sady fad'a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.
Saurayin kuwa da gudu ya fita yana mai dana sani domin sun wulakanta shi bai tana zuwa police ba kan wani lefi ba. Shuriem kuwa dad'ine ya kamashi domin yasan ya rabu da naci .
Muje zuwa.
By
Queen meemi👑
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣60❣
_Sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_
This page 4 u Anty sis much luv❤
*********
Tafiya suke amota ta inda Dady yake shiga bata nan yake fita ba,fad'a sosai yake mata har driver yayi parkin a k'ofar gidan su ta fito,itakam sharb'ar kuka take kamar me d'akinsu direct ta zarce Sumy na danna waya tace "meya faru sis naganki kina kuka" ta d'ago "na rasa Shuriem wlh ba zan iya rayuwa ba shiba" dai -de lokacin mama ta shiga d'akin fuskarta atamke tace "sai kuje Dady na kira" jikin Sady ya fara rawa duk rashin kunyartaa tana tsoron Dady ,direct falonsa suka shiga yana zaune sai fad'a yake kumayi Umma azaune tana bashi hkr .
Tsawa ya kuma dakawa Sady Sumy tayi gefe suka zauna ya kallesu "wato Dan kunga na sakar muku ko! shine kuke abinda kuke so Musamm ke Sady Naga kanki rawa yake, yanzu inbanda lalacewar zamani har Sady ta santa had'a tuggu akan saurayi dan zubar da kima, kina binsa yana gudunki, wato har ma sharri kikewa Wacca yakeso ko? to Anyi na farko duk cikinku yanzu kuna lvl 4 ko? to ya isa kowacce na bata 2 week ta fito da Miji in ba haka ba zan mummunan sab'a muku" ya kalli Sady "shashar banza da hofi tashi ku bani gu. Asanyaye suka mik'e suka fice. Umma tace "Amma Dady a sauk'ak'a" ya d'aga Mata hannu "dama ku ke sakar musu suyi abinda ransu ke so to ya kau! wlh duk waccen ta sab'awa Umarnina za taga hukunci bazan zauna yarinya ta janyon abin fada."
*****
Tunda suka shiga d'aki Sumy hankali atashe ta kalli Sady dake kuka "ni bansan ya zanba babu Wanda fa ke zuwa guna" Sady ta d'ago "nifa inba Shuriem ba bazan Aureba" Sumy tace "ke bakya jin magana kin faye taurin kai, ni kam dama kinga Uzaifa na sona nice dai nake tsoron sakar masa Saboda yaudarar da Nazi yayi mani sai nake gani kamar shima haka ne. Amma kinga yanzu zan kulashi." Sady ba tace komai ba, tayi shiru abin duniya na damunta .
******
Ab'angaren su Hassay kuwa yanzu hankalinsu ya kwanta domin Shuriem y bawa husy hkr sun shirya inda yake shaida mata manyan sa zasu so ai magana, tayi murna ta sanar da mum .Suna zaune suna hira Wayar Husy tayi K'ara taga sunan miji Suhaima nan ta d'auka yake sanar mata Haihuwar Suhaima wani ubn tsalle ta daka ya shaida Mata an Samu Baby Boy dukkansu kowa ka kalla farin ciki wajen k'arfe 2 suka je asibitin lokacin Suna shirin tafiya don an sallamesu hassy ta k'an-k'ame Jariri Mum ta roki Safwan da yabar Suhaima tazo gida wanka, bai musa ba don yasan za'afi kula da itaa agidan,kafin yamma Dangi kota ina don jin haihuwar musammn b'angaren Safwan. Hassy da hussy kamar suke jegon yauma suna zaune Ana shirya baby wayar husy tayi K'ara ta dauka "my husby" yace "ba wani nan!! kin manta dani ko? tace kasan munyi d'a dole kai hkr" yayi dariya "zan kamaki ne tunda bakya missn dina." "Anjima zanzo barka" tace "to."
Da yamma sai ga shinan yazo yauma fararen kayan ne jikinsa ya dade azaune sai ga husy rik'e da Baby ta shiga d'akin baki yana ganin ta ya tashi ya karb'i Babyn yace "wow Masha Allah Amma babyn me kyau dashi" tace "agabana!" yace "to meye kema next yr da naki" ta rufe fuska "haba dai aini sai na dad'e" dariya yayi yana yaba babyn wata leda ce babba shak'e da kaya ya mik'a Mata "gashi abawa Maijego." Hussy tace "lalle harda hidima!" "To meye yiwa kaine" haka ya gama ganin baby ya tafi.*Washegari*
Su Anty da Mubarak suka zo husy tayi murna suna zaune suna hira. Suhaima na gyara baby hassy tace "Anty ina wan nan Sadyn?" tace "tana nan" suka tuntsire da dariya .Hassy tace "ai bata da kirki kin san me taiwa husy kuwa!" Anty ta girgiza kai "sai kin fad'a" nan suka gaya mata tace "biri yayi kama da mutum, ashe shiisa Naga Dady ya kafa musu doka" hassy ta tashi danjin gulma "ai gwanda" tace "ai cewa yayi duk sufito da miji nan da 2weeks" dariya suka sa "Ai maganinta kenan! ba ita mugunta ba" Anty tace "ai Sady sai ahankali kinga da dasu Zuby nanan duk itace ba ruwanta. Amma Ana musu Aure taga fili ta fitsare." husy tace "eh nima.nayi mamaki donfa muna shiri da ita lokacin dana zauna gidansu." Hassy tace "ita ta sani saita tafi neman miji ai" Suhaima tace "bar 'yar banza ai ni yanzu ba sosai muke wurd'aba duk kan abinda take muku."Anty tace "Allah ya kyauta."
***********
Sati ya za gayo akai suna yaro yaci suna Muhd nan suka cigaba da taya suhaima jego.
Ranar Asabar iyayen Shuriem maza suka zo lokacin Dady na nan su uku akai musu iso nan suka nema Dady ya amince atake suka zaro 200k aka bada kud'in mun gani munaso wato engaged. zo kuga murna gun Shuriem da husy ,nan Dady yayima Mum bayani tace "Aa kace auren yara 2 zanyi to Allah ya kaimu" Dady yace "Ameen" tunda Sady taji zan-cen kawo kud'in Husy gun Anty yasa ta kuma tashin hankalinta harda su Zazzabi ga Dady ya addabesu su. Hassy kuwa kowacce yanzu Normal suke dame santa suna zuba soyayyrsu inna Jummai taji dadi wan nan kenan.
*Bayan Sati biyu*
Yau satin da Dady ya dibarwa su Sady ya cika. nan ya kirawo su kowacce ta zauna ya kalli Sumy tace "Dady akwai wani Uzaifa mun dai-daita da shi" yace "to umma" tace "amma sai de fa bashida kudi sosai" Dady yace "ai anshani na warke yanzu ga Zuby kullum bani ke taimakonta ba! duk kuma kud'in sa fawwz dana babansa kin san ya zama matsolo baya wadata ta,ni yanzu kawai inde yaro na da mutumci zan bashi kuma zai iya rik'eta" yace "ke Sumayya na gama dake saiki ce ya aiko." ya kalli Sady wacce ido ya firfito "ke kuma fa? ta saka kuka "Dady wlh ban tsayar ba ,don Allah kayafen! nan da wata daya zan samo" da yaki yarda sai da su mama suka sa baki ya amince, nan ta mik'e suka tafi daki Sumy tace "kinga abinda nake gaya miki ko! gashi nan ba shureim ,ga Faruq yayi aurnsa tun-tuni sai kamalu Allah yasa dai baki koreshi ba shima" Sady tace "ke ni ki kyaleni" sumy tace "ki bugawa Kamalu "muji mana"! ganin Sumy ta dameta yasa ta bugamai ta dade tana ring San nan ya d'auka "ya dai lafiya?" tace "Aa dama kwana 2 na jika shiru ne" yace "ba komi kawai naga bakya sona ne ni kuma bana jurar wulakanci shiisa na hak'ura yanzu haka na samu wacce muka dai- deta an kusa engaged ma Allah ya hadaki da rabonki." dama a hands-free tasa nan Sumy tace "wata sabuwa kingani ko dama na fad'a yanzu baki ga tsuntsu ba tarko" Sady tasa kuka "wayyo wlh ni banso Dady ya had'ani da kowa" Sumy tace "ta baya ta rago dai dama ranar Dana sani ake tsoro ga mara daukan shawara."
By
Queen Meemi👑
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣61❣
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
********
Haka Rayuwa tayi ta tafiya inda har an samu wata uku cir da maganar da Dady yayima Sady Amma shiru ba mashin shini domin duk samarin dataiwa wulaknci duk sun samu masu sonsu,kuma basa zuwa, kullum sai -de ta rok'i Dady daya k'ara Mata lokaci ak'arshen satin nan ne yace mata nan da sati zai yanke hukunci akanta.kwana biyu tsakani Sady duk ta tashi hankalin ta domin tsoron kar Dady ya had'ata da wani tsohon don yanda yaji haushinta ba lalle ya saurara mata ba.yauma tana zaune wajen k'arfe hud'u itada Sumy suna kallo azahiri ba kallon take ba sai tunani wanda ya Zame Mata tamkar me Sallama sukaji Anyi sallama.Lubna ce ta shigo tana murmushi da gudu Sady ta Rungumeta "Oh! my Frnd I Mssd u lubna" tace "nima haka" nan suka hau hirar yaushe gari Sady tace "ya katsinan" tace "Alhmdlh nafa kusa Aure" Sady tace "ke Dan Allah wazaki Aura? Ashobe ta zaro "gashi anko nan da 3 month sunan mijin Kamalu Sady tace "nunan pics nasa" nan ta zaro waya ta nuna mata dafe kirji sady tayi "me zangani! cin amana" lubna tace "name fa?" "Amma kinsan dai saurayina ne sonawa ina mai wulknci agabanki bayan ke kike ma zugani" lubna tace "lol to don tsohon saurayin kine sai akace ni na wulak'anta Shi alokacin kina mayen son wanda bai sanki shiisa kika kasa gane masu sonki" Sady tace "amma kin asara lubna Allah ya isa muguwa" Tabe baki tayi Amma Sady baki da wayo dame Allah ya ragi kamalu kika watsa mai kasa a ido nikam yayi min don haka kinga tafiya ta in kinga dama kiyi ankon" nan ta aje taai hanyar k'ofa Sady tabita "wlh lubna bani bake, muguwa Allah saiya sakan." Lubna tace wlh sai de ya tsaya akanki domin bance ki wulakanci ba waike gamai farin jini to ai ga irinta nan" ta fita tana juyi da gudu Sady ta koma gida Sumy dake jin duk abinda suke tace "lalle duniya budurwar wawa ai yanzu kyayi hankali Sady,kisan irin kawayen da zakina yi",ita kuwa kukanta take sha na bak'in ciki.
*************
Yau aka saka ranar Su hassy da hussy wata biyu nan fa Murna kamar me su hassy aka hau shiri ta b'angaren mazan kuwa Muktar yayi ginin sa akano shi kuma Shuriem yayi gininsa dank'arere A nan Abujar . Lefe kuwa kannen maminsa suka tafi dubai inda aka had'o akwati saiti 24 wane kyau domin tamkar a bud'e kanti mami kuwa ta tama bikin Shuriem bangaren Mum din su Hassy kuwa duk ta shiga busy domin kullum suna kano Sayen kayan k'awa komai 2 take saya domma Suhaima itama sati mai zuwa zasu tafi dubai da hassy da husy don sayo kayan fitar biki da wasu sauran kayan.
Bayan Sati d'aya suka d'aga dubai su uku sun sayo kaya na gani na fad'a na manyan mata domin Dadyn su ya saki kud'i domin daga su bazai kuma aurarwa ba kaya suke jibga musamm husy mai son abubuwa komi ta gani sai ta saya wan nan kenan.
Sai da sukai sati biyu San nan suka dawo Dan ma an musu huutu shiisa abin yazo da sauki.
Suna azaune mum na ganin kayan "kai My twins gaskiya kun iya zab'e wan nan kaya haka lalle" suhaima tace "ai mum komi suka gani sai sun saya musammn kayan kitchen" mami tace ai yarn nawa sun horu da girki shiisa suke saya" hassy tace mum ai dady "yafa bamu kudi sosai" Suhaima tace "yanzu ku Ana zancen auren naku kuke saka baki" husy ta rufe ido "kai Sis Suhaima" hassy tace "hmmm! siis suhaima lokacin bikinki fa! komai ke kika zab'a" mum tace "ku tashi kuje kuyi girki don yanzu dole ku dada k'warewa" nan suka tashi.
***********
Husy ce zaune da Shuriem suna hira inda suka Saba zama Dan kallonta yayi da murmushi d'auke akan face nasa 'Amaryata nan da one month kina gidana" sunkwi dakai tayi "angona Kenan" yace "ki gayan meye bai miki ba agidan a gyara" nan ya bud'e tsaleliyar wayarsa yana nuna mata masha Allah kawai take ambata tace "nikam husby ko ina yayi wlh ai wan nan na zama yar gata" yace "baby kinfi haka ma" haka suka gama hirar su ya tafi.
*Bayan sati daya*
Dangin su Shuriem suka kawo Lefe Motoci ne manya manya ke. fakawa a farfajiyar gidan su hassy. manyan mata keta fita inda katti ke d'aukan jakun kuna suna shiga dashi cikin gidan ma dank'am yake da mata nan aka hau gud'a kota ina Masha Allah aketa anbata "lalle yarinya tayi goshi" su maman kano da goggo duk sun zo nan aka basu tukwici na 200k da Snaks kala- kala amutunce suka gama suka tafi inda aka saka date On 30 April.bayan tafiyar su akaita san barka hassy ta haye d'akin su tace "tweeny gaskiya kinyi goshi kinga kaya! Amarya kenan." Husy ta dago "kema ai hakan wai yaushe mukatr zasu kawo" tace "shima a dis week" nan suka zauna suna ta shirya yanda event sai wakana.
***********
"Kai muktar yanzu wan nan shirgegen Lefen Shi za'a kaiwa yarinya d'aya ai wan nan sai an kaiwa yarinya Goma in a k'auyen nan ne! Ai dama nasan su Antyn kano su lefen karya zasuyi don sunga yar birni ce shiisa ba akawon na gani ba saida ka gama haba muktar! kodan yar manya ce" muktar dake durk'ushe don tunda aka fara hada lefen ya hada abinsa da tainakon su Antyn kano (inda yake) Su gaggo tun ganin su da lefen suke maganganu kan yayi yawa shiisa ma har yanzu ba'a kaiba.Muktar yace "haba gogg kinsan dai gidan Dana d'auko aure dole komai ai na bajinta kuma falilkahil hamd inada Halin yi."daka tsalle tayi "wallahi sai an rage" nan ta d'ebi wasu atamfofi ta aje agefe da mayafai "haba aje lefe saiti goma sha shida zaka kaiwa mace d'aya wlh sai an rage" kamar yayi kuka don ya dade yana shirinsa. shigowar maigari ya tarar da tak'ardama yace "meye?" nan ta sanar mai yace "kinga ban san haka! ke kinga inda ya samo auren ne? kibarsa kawai tuwon girma miyarsa nama,duk damu k'auye bamu san wan nan k'aryar ba ,to shi abirni yake yanzu dole tunda 'yar can ya samo dole yayi masu tunda yana da hali" nan ya dauke duk kayan ya maida a fusacce ta d'au wani atamph "wlh Banda wan nan" muktar yace "gogg kinga fa akwatinki can da kaya keda baba na ciko muku don fitar biki ga kuma dubu hamsin akai." nan ta washe baki "yanzu naji magana, Amma de duk da haka sunyi yawa" yace "don Allah Gogg kiyi hkr don Allah!" tace "to bkmi Allah ya sanya Alkairi kaga ranar Asabar sai akai" yace "yawwa goggo na." "Inaga su Antyn su zasu kai kayan ko?" yace "eh Gogg" murmushi tayi Allah ya amfana .
By
Queen meemi👑
. . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣62❣
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
_This page for u my lovers fans❤_
********
Ranar Asabar gidan su Muktar suka kai lefe Abuja da ance akarb'a agidan maman kano sai suka ga dacewar sukai Abujar. nan Marik'an Muktar na kano suka yankara suka tafi kai lefen suma sun kawo an yaba akwati saiti sha shida duk da bai kai kyan na hussy da yawa ba Amma itama nata an kashe kud'i lefe yayi kyau sai san barka da zasu tafi aka basu tukwici. 100k tare da Snaks da Drinks abu yayi kyau duk sunyi goshi nan duk aka tsaida date dai-de dana hussy Muktar bayan tafiyar su sun waya da hassy yace kaya sunyi tace "haba dai Muktar ai kaya sunyi wlh" nan yaji dad'i sosai suka taba hira abinsu. Haka fa duk suka shiga Busy ko yaushe suna tafe gurin kai d'inki da shirye -shiryen su,bangaren angwaye ma duk sun shiga busy da yake ma duk suna da abokanan da suke taya su shiri.
********
Can kuwa a mangalu su inna Jummai ne keta shirin tafiya bikin daya ke saura sati d'aya shiisa malam yace suje,hakan kuwa akayi malam yace Dije ma ta shirya tabisu da zumudi ta shiga shiri. Gwamma kuwa taso zuwa malam yace meye had'inta d a ita dama zuwa tayi ta sameshi a rumfar sa lokacin sun dawo daga bara ta sami gefe ta zauna "Malam dama magana biyu ke tafe dani" nan tayi mai zancen zata bikin yace basu da had'i don haka ta hkr Dije taje hakan ta hak'ura, har ta tashi ta dawo "yawwa malam dama ina rok'anka Allah da Annabi ka maidani d'akina," wani kallo yabi ta dashi "gwamma ai yanzu bamu da wani sauran zama ko kin manta saki uku nai miki! kije kiyi hk'r kawai" kuka tasa ta tashi tana cangala kafa ta tafi da dana sani fal aranta. su kuwa yau suka tafi wajen karfe biyar suka sauka amAbujar tun zuwan su suka tsinke da ganin gida Dije kam k'auyancin tane ya fito fili suna zaune misalin k'arfe 7 na dare Jummai ta fito da kayan kad'i kaloli da tasa aka daka mata da yawa irinsu kuka,karkashi,kub'ewa bushasshiya,Daddawa da kayan k'amshi duk ta daka ta mik'awa mum gashi kayan kad'i ne duk na amarre ko zasuyi tuwo" mum tace "tuwo ai dole ne wlh kuwa na gode nima zan dib'a kinsan anan abuja wahala suke ga Dadyn na son su" nan ta fito da wasu samiru masu adon blue irin nada d'in nan wajen saiti goma masu biyar- biyar tace "wan nan kuma gudunmawar malam ne" mum tace "oh bakwa gajiya! ai kuwa kinga ajera musu akitchn" wani buhu ta zaro "wan nan kuma na wane dama munyi magana da husy tace tana son kaskon wuta" mum tace masha Allah ubangiji yabar zumunci mun gode, ta kara janyo wata babbar leda wan nan kuma su Mubirgi ne da mara su fai-fai da k'warya su Ludayi da sauran kayan gargajiya" mum ta murmusa Amma fa jummai kin burge yaran naki kinga sai ai musu kitchen kala 2 daya kayan zamani daya na gargajiya ,kinsan irin kayan nan yanzu zamani yazo Sam bakya ganinsu a kitchen amare iyayen anbar al' ada sukuma yaran basaso .Allah ya biya" jummai tace mune da godia ai"
*********
Su kuwa Amare suna daki kullum basu fita domin yau,kwana biyar kenan da farai musu dilka (halawa) inda Maryam Alk'ali (mamu) ke musu domin ta k'ware tun daga sokoto aka d'aukota abubuwa kala -kala take musu,jin dadin ma sun saki kudi gurin masu d'inki domin da kansu suke kawo musu idan sun dinka.
Bayan sati d'aya kenan ya kama sati biyu Ana kwaskware su husy hatta magana da yanda zasunaa fidda lafuzza saida mamu ta koya musu cikin salo na daukan hankali kai gaskiya idan kana da kyau ka K'ara da Wanda domin idan kukaga yanda su husy suka dawo sai kun kalla kun k'ara kallo,nan aka sallami mamu da kyauta mai tsoka da alk'awarin zata lek'o bikin tunda tana Abujar lokacin.
*SHAGALIN BIKIN*
Ranar laraba gida ya cika dank'am da 'yan biki.
Ranar Alhamis aka fara da kamun Amarya inda aka d'auko Maryam Ramat wadda za tana kwalle musu fuska k'arfe hud'u ta gamai musu kwalliya masha Allah sunyi kyau domin fad'ar kayan da sukai b'ata time ne, duk sunci Material black nd ash sun bala'in kyau sun dora wata abaya ne kamar Alkyabba baka ,dangin Shuriem suka zo nan aka gudanar aka akayi kamu aka raba kaskon wuta dasu lalle harda humra me k'amshi adan wasu dogwayen roba sukaci suka sha aka watsae.
Washegari Ranar Jumaa aka gudanar da dinner da dadare misalin k'arfe 7 dai de angama kwalliya carkwad'i hussy da hassy sun bama Mara d'a kunya domin kayan jikinsu ma abin kallo ne sai walwali suke Jummai harda kuka lokacin da taga yanda husy takoma nan Suhaima tai ta daukan su hoto da hassy sun saka wani blue green d'in material mai kama da less da golden ajiki tamkar ba yaran hausawa ba, sai kace yaran larabawa haka Arif ma ya had'e da frnds naasa Suhaimaa ta gaji da haduwa itama ita da babynta. Angwaye ma sun had'e suma shigar su iri d'aya suka debe su suna zuwa kallo ya koma kansu Sady da Sumy na gani sunje Sady hawaye ta fara ganin Shuriem da husy sunyi match sun had'e tabbas husy tayi wining akanta,ganin yanda Shuriem ke watsawa husy wani kwantacccen kallon yasa Sady tabar gun domin ji take kamar ta shak'e husy haka akayi aka gama akai rabon calendar me hotunan su key da Atamph Super aka watse.
Ranar Asabar shine mothers event kai gaskiya anyi gayya nan ma k'arfe hud'u angama makeup don mum tace bata son African Time,yauma sunyi kyau tamkar jiya twins ko ina sukai sai an kallesu kowacce sai doka domin tamkar dawisu suka koma don kyau,k'awayen mami duk sun hallara ,da kawayen Amaryar waje yad'au d'imi kowa yana yaba Dan uwansa ga k'awayen suma sunyi kyau,wayar hassy keta ruri a hannun khadija wata frnds nata ta kaimata lokacin ango na musu selfi tace "ga wayarki Ana kira" ganin sunan miss hafcy yasa ta d'auka hello kawas tace gafa writers sun zo kinsan fa dama da duk nakai musu iv"
"haba ba naga yawan cinsu su kowacce da garin da take ba? miss hafcy tace "yap kinsan Ana bikin wata writer frnds nasu kinsan su da zumunci shiisa duk sunzo wasu daga ciki." "Nayi farinciki sai kun k'araso" nan biki yad'au colour ko ina ka kalla kowa na wasa da kaji ga drinks kaloli a time din lokacin writer suka k'araso irin su ,feenat jaafar ,miemie bee ,maman shakur, batul ,Maman hanef sady jegal,Amra, Zahra Bb,bena zir chucu ammani,lubie phty Bb,sodangi,biebi isah,Auta,pyar ,rufaida omar, yar ficika.da dai suaran wadanda ban fad'a ba ,take akai musu big masauki Anty sis ,da Anty maijidd ma duk sun hallara haka akayi biki cikin farin ciki kowa ya watsae.
***********
Ranar Lahadi aka d'aura Auren HUSAINA DA SHURIEM,HASSANA DA MUKTAR Kan sadaki dubu d'ari lakadan ba ajalan ba waliyai da shaidu suka shaida aka shafa fatiha nan marok'a suka fara aikinsu inda suke wak'e Amare da Angwayensu manyen mutane ko ta ina marok'a kam sun Sami abinda suke so,zo kuga bakin Shuriem da Muktar tamkar gonar Auduga Alkawari ya cika,nan suka zarce da reception.
Mum kuma da danginta suka cigaba da yinin su mai kid'an k'warya tun daga kano maman kano ta dauko su ,suna tayi har wajen 5 aka fara shirin mik'a husaina (husy gidan angonta Shuriem ,ita kuma hassy sai gobe za'a mikata kano hmmm Ranar rabuwa kuka suke ta tasha tsakanin hassy da husy Arif ma kamar me sai kuka yake ita kanta mum matsar kwalla take,lafaya aka nada mata Dady yayi Mata nasiha mai ratsa jiki dakyar aka banbareta jikin jummai da suke kuka aka shigar da ita mota hassy na kusa da ita don zata rakata motoci suka ja tunda aka tafi take kuka har kaje hadaddenn gidan ta maitsari iya tsaruwa gidan mai bene ne falonta na kasa am mai adon golden komai ya tsaru abinka da 'yar manya, da daki 2 sama ma da wani falon Shi kuma adon red akai mai shima mai daki 2 koina cike da kaya wane zeezee yargata,kitchen daya mai kayan zamani daya mai na gargajiya tsayawa fad'ar sa bata lokaci ne,Nan aka aje Amaryar kowa yayi haramar tafiya da kyar hassy suka rabu da juna aka barta ita daya (Aure yakin mata)kan ango yazo.
Washegari gari misalin karfe 11 d'aya su maman kano suka rankaya da hasssy harda Jummai don zasu koma mangalu aka tafi da ita,k'arfe 3 suka isa direct gidan marik'an Mukatr akayi da ita Dangin su ne fal agidan akaiwa amarya nasiha su maman kano suka bada Amanarta san nan aka d'auketa aka kaita gidanta dake Shagari quaters itama gidan ta ya had'u sosai Amma ita flat house ne a tsakiya zai kod'a gidan ake,duk irin kayan dake gidan husy shine agidanta komai ba bambanci k'arfe 6 dai de kowa ya watse aka barta ita daya tana kuka kamar ranta zai fita.
By
Queee Meemi👑
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣63❣
_Sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_
**********
Bacci take d'irka na ga jiya bata sanma rana har ta fito ba. A hankali ya bud'e d'akin wani k'amshi ya buge shi ya zauna gefen gadon ya d'ora hannun sa dai-dai beauty face nata yana shafawa tare da godia ga sarki Allah daya mallaka masa farin cikinsa .Bayan ta ya shafa nan tayi mik'a ta juya Murmushi yayi ganin yanda take bacci gefen mayafinta yasa yana d'an sawa akunnen ta nan taakai hannu tare da bud'e ido murmushi ya saki "my finest wake up! kinga fa rana ta fito tun jiya bayan kawo ki kike bacci abokaina ma sai sallamar su nayi" sunkwi da kai tayi cike da kunya ganin yanda yake kallon jikinta bargo ta janyo da yake rigar bacci a jikinta tunano wa tayi jiya bayan ankawo ta kowa ya tafi kafin ya shigo tayi sallahr isha ta kwanta don jiran sa,bata san baccci ya d'auketa ba. Murmushi tayi ta kalli agogo da sauri "wayyo banyi sallar asuba gashi ba har 6 :30" Shuriem dake kallonta tana bashi shaawa yace duk bar diriricewar nan jeki sallah don jiya na shigo na ganki sai kwasar bacci kike ai inaga na shigo d'akin nan yakai so goma na dauka ma mutuwa kikai,.da Asuba kuwa na tashe ki na fita na dauka ma kinyi" da gudu ta fada toilet tana magana "ai nagaji fa wlh tunda a ka fara bikin nan bana samun sleep" dai- de lokacin ta fito ta shimfid'a sallaya ta tada sallah shikam Shuriem yayi d'ai d'ai kan gadon yana shak'ar kamshin ta daya manne a zanin gadon. Bayan ta idar ta yiwa Annabi salati tayi karatun Al'Qurani ta nad'e sallayar.haka kawai kunyar sa takeji ta kasa hawa gadon sai kawai tayi hanyar waje zata bud'e taji ya kamota ta fad'a k'irjinsa ya riketa gam nan suka shiga wata duniyar yace "husyna zo ki koma baccinki anjima sai mu tashi" juyawa tayi "break fast zan mana" d'an hararta yayi "waya gaya miki Amarya na girki? tace "to meye nidai Amaryata ba zata shiga kitchen yauba kizo mi bacci mami zata sa akawo" janyo ta yayi tana sunne kai suka kwanta Wanda baccin gajiya ya debe su Basu suka tashi ba sai k'arfe 11 na safe ita ta fara mik'ewa ta shiga toilet tayo wanka ganin ba kayanta ko d'aya ad'akin yasa ta fita ta dayan d'akin masha Allah ta ambata domin naira tai kuka ad'akin wardrobe ta bud'e sabbin kayanta me jeras tasan aikin hasssy ne nan ta zabi wata vaila Atamph red tasa ta kashe d'auri jikin nan sai tashin kamshi yake. ta sauka k'asa domin yunwa ta fara kwasarta.manyan flaks ne da kalolin abinci dai- de lokacin Shuriem ya sauko shima ya shek'a wankansa yasa jins da t- shart rungumata yayi ta baya "kinyi kyau finest" ta juyo tamai fari "kaima haka handsome" janta jikinsa yayi yana shakar kamshi. Suna manne da juna ya ja musu tebur tayi saving nasu sukai break fast.
Bayan sun gama suka dinga bin d'akunan suna kalla su kitchen daga sama har k'asa Shuriem yace "yanda kike da kyau haka gidan ki ma" tayi dariya "haka angon ma yake" ak'arshe suka dire a wani k'aramin garden shuke-shuke ne duk wan nan tsarin husy ne don tana son green ganye sun dad'e agun suna soyewarsu san nan suka koma cikin gidan suka zube afalo Shuriem yana saita musu Tv.
B'angaren Amarya Hassy kuwa kuka tak'i dainawa domin ganin ita gata wani garin bata san kowa ba dadin tama ga maman kano,dirin motoci taji yasa ta dad'a k'unshewaa hayaniya taji afalo Muktar ya shigo "Amaryata ta" ko ihim bata ce ba yaje ahankali ya yaye Mayafin ta rufe idonta gam alamar bata sann bud'ewa dariya yayi "kyama bud'e yad'an ja hancin ta idon arufe tayi dariya ya d'agata "kinyi kyau fa! ga abokanai can zasuyi siyan baki juyawa tayi kasan Banda k'awaye taya Za" shafa sumar sa yayi "baby kawai addua za'ai" mayafinta ta d'auka suka jera abokan su uku suka hau mai tsiya musammn mahmud yace "Lalle dole kace sai twins din nan ashe ba abanza ba" muktr yace "yimin sharri" suka sa dariya nan sukai D'an nasiha suka aje manyan leda sukai musu sallama suna fita hasssy ta shige d'aki shima ya bita da leda "baby ga kaza nan da fresh milk kici nasan kinajin yunwa" tad'an turo baki "nifa nak'oshi" yace tab! "yau kuwa sai kinci ko d'ure sai na miki" "Nifa bacci nake ji wlh am so tired" yace "I know dear! kici kad'an saiki kwanta" dan zamo wa tayi ta sakko kan capet suka juye kazar a filet sai tiriri take ya d'auko cup ya tsiyaya musu cinya ta d'auka ta gutsira ahankali kamar bata san taunar. shikam ci yake yace "lalle wan nan aiba ci kike ba" tsam ya tashi ya koma bayanta ya d'an janyota jikinsa "oya open ur mouth" dariya ya bata tad'an bud'e ta gutsira ahakan suka gama ci yace zai je toilet nasa yayi wanka yayo alwala, yace itama tayi kan yayo.'yan mintuna tayi ta fito ta saka kayan bacci da zumbulelen hijab lokacin ya shigo ya jasu sallah sukai nafila ta godia ga Allah . kokarin tashi take ya kalli k'unshin k'afarta "wow dea wan nan k'unshin yayi mani kyau" ya shafa k'afar taji yarr! Ajikinta ya tashi shima itakam tuni tayi flat a bed taja bargo saboda Ac dake hurowa sosai sai take jin d'an sanyi.kwanciya yayi yana d'an janta da hira sai magana take can kasa "yace hassyna k'arfe tarafa! yanzu ki tashi mi hira Dan mik'ewa tayi suna dan hira harda dariya yana nuna mata pictures na bikin su wayarsa. Nan da nan ta ware taji baccin ma ya tafi hirar su suke ta soyayya yanayi yana shafa gashin ta daya sha gyara d'an abubuwa ya farai mata nan suka fara shiga wani hali kissn dinta yake take jikinta ya fara rawa shima haka Nan na bar dakin Asuba ta gari Amarya da Ango
By
Queen Meemi👑
. .
⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣64❣
_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_
*******
Husy na zaune tayi filo da Shuriem yace "gaskiya kunsha gwagawrmaya finest kamar ba za'ai auren nan bafa!" ta d'ago ta kalleshi "dear donma bantab'a baka full labarina ba da sai kayi mamaki" tashi yayi "my love bani mana" murmushi tayi "to sarkin jin labari" yad'an yi kayatacciyar dariyar sa yace "ai dole indai hira daga bakin kine aida dad'i" lumshi ido tayi tana jin sonsa aranta Shi kuma yana wasa da hannunta nan ta fara bashi tun daga farko har k'arshe tashi yayi ya matseta tsam ajikinsa "lalle na yarda let rabona ce tabbas tsantsan rabone ya had'amu amma nayi mamakin muktar ke dashi bakwa nunawa" tace "to ai kaga komai nada sanadi" yace "Muktar ya kara girma a idona saboda yabar min hear beat dina" Dan dukansa tayi na wasa "dama can dan juna akayi mu" yace "tabbs baby na ilove u so much tace luv u too" ganin karfe shida dai de ta mik'e dea bari nai mana jallof mai dadi janyota yayi ta fad'a jikinsa ba yau ba har yanzu fa ko 3 days baki ba." Dan ya mitse fuska tayi "dea kabari nayi plsss wlh sha'awar yimaka girki nake" ganin tana alamar shagwab'a ya mik'e "muje finest" suka shiga kitchn nan ta bashi yankan albasa ya dage sai yi yake ita kuma ta had'a 7 dai de tayi sukaje sukai wanka suka fito suna ciyar da juna wani irin nishadi ke shigar su duk yayin da suka kasance atare da kaunar juna. ko can da nan basa san fita ga Shuriem yasan salo- salo na rikita ta nan da nan suka dada shak'uwa D'an jingina tayi yace "finest yaude gajiyarr tabi jiki ko?" ta kalleshi ta sunkwi da kai domin tasan kanun zancen tashi tayi zata gudu d'aki yadam k'ota ta fad'a k'irjinsa zuciyoyinsu sai fat -fat suke k'amshin ta
Ke rikitashi ga kayan data sa sun mata kyau sun fito da kyanta cak! ya d'auketa sai dakinsu ya bud'e jaka ya dauko Mata hijab sukai alwala suka gabatar da sallah sukayi adduoi na godia ganin yanda yake zumud'i yasa tafara d'ari dari,kalamai masu dadi yake gayaa Mata suke shiga kanta duk jikinta yayi sanyi .gashi ya rikitata da salonsa take hawaye suka zubo mata ganin tana kuka yace "sorry dea iluv u so much nayi laifi ko? tace "no dear bansan daliliba"tashi yayi ya kashe masu fitila suka fada duniyar masoya Asuba ta gari Hussy shureim.
********
Haka Amaren nan suka bud'e shafin soyyayya angwayen su ko fita basa yi ga girki mai dad'i da suke kwasa don mum batai wasa da koya masu girki ba musammn Shuriem da yake san na gargajiya yauma suna zaune husy na game a waya Shi kuma yana kallo ya juyo "zo nan finest" ta noke kafad'a don tasan ramuwa zayyi tsam ya tashi ya zare wayar ya b'oye .fillow ta dauka tana Dan dukansa alamar kuka "ni kabani Allah zanyi kuka" yace "yauwa yi mugani dama ina son ganin hawayen ki" harar sa tayi "Allah nafasa yin wan nan hadin me dadin nan!" yace "ai na iya bari ma ki gani" tashi yayi yaje yad'au kan-kana da ayaba yayi blandin dinsu suka zama drinks yad'an sa sugar yasa afirj don yayi sanyi ya fito tana zaune ta rufe baki tana dariya "wa yaga kwab'a" yace "finest ai har na fiki iyawa, bari naje na watsa ruwa kafin nan yayi sanyi" yana shiga kuwa taje ta dib'a tasha ta boye saura tana son hadin domin tun agida takeyi tunda yasha yaji dadi yanace mai.,kitchen ta shiga tana yan wake- wakenta tana musu girki tafiyar kasaita yake ya bude firj zai sha yaga wayam da gudu ta fita waje nan ya gano ta ya bita sai zagaye suke afalon yana finest inna kamaki saina cije wan nan lips din" ta tsaya tana girgiza tace "gani" kafin yayi taku ta arce suka kuma kasa tsere caraf ya kamota take yahau cizon lips nata ahankali kawai suka zarce sai numfarfashi suke yace "wa kika shanyewa?" "sorry dea bari naimaka wani ta" kadamai ido ta tashi ya bita da kallo yana mai nishadi.
********
Su muktar kuwa hatta waya kulleta yayi acewarsa bai san damu kwasar luv nasu suke san ransu yau satin su d'aya Goggo babar muktar suka zo gidan hassy da itada wasu tsoffi. suna zaune muktar yana ma hassy tausa a kafa ta dan ji ciwo suka shiga. yana ganin su ya dirirce Goggo ta gani hassy ta tashi tana musu sannu da zuwa suka amsa. muktr yazo "sannunku da zuwa" Gogg tace "lalle muktar ka samu wan nan yarinya haka aidole ta maidaka haka Naga har tausa kake Mata" kunya ta kamashi "Goggg ciwo taji" tace "ayyo" Hassy ta shigo tana k'arai musu sannu da zuwa ta aje try da lemo ga dambun kaza agefe. Gogg sai tauna take ashe ta iya girki "husaina ki kula dashi kaima ka Kula da ita ku zauna lafiya nasan ka muktar banda biyewa mace musammn wan nan Naga yar gayu ce" kunya ya keji ganin tana magana sun d'an jima suka tafi ta had'a su da turare da aTampa bayan ya rakasu ya dawo suka cigaba da hira wan nan kena. Bayan wata d'aya da bikinsu Dady ya biya. Musu zasu tafi Spain daga can suje Saudi suyi Umara har sai azumi ya kare amatsayin gifts dande suji dadi haka suka d'unguma Hassy da hussy da mazajensu
*************
Kuka take sosai kamar ranta zai fita. "Sumy wallahi ina tsoron wanda Dady zai bani kinga yanzu duk Samarin sun gujeni" Sumy tace "sai hkr" "kinsan yau zai kirani" suna cikin magana Anty ta leko "Sady kixo inji Dady" jiki na rawa ta mik'e ta shiga kanta akasa ta gaidashi yace "wato Sadiya na baki lokaci yau wajen wata hud'u amma ba magana ko? to yau na yanke magana zan had'aki da Dan gidam kawu wato Bello" da sauri ta d'ago kai alamar zatai kuka zatai magana ya d'aga mata hannu ta tashi ya daga mata hannu gama magana nan da 2 month za ai aure."
Da gudu taje gun Sumy "wayyo Wai kinji bello zan aura!" Sumy tace "tohh to ai Naga bakya sonsa" Sady tace eh mana, kin manta ya tab'a cewa yana sona nace be min ba, saboda Allah ina zan kai Bello tuzuru dashi ni bemun ba" sumy tace "hmm kidaiyi hkr kawai ai tunda ma ya tab'a cewa yana sanki da sauk'i" Sady ta fashe da kuka "ina zan kai k'aton bakin sa jibeshi fa ko kwalliya bai iya ba tamkar bagidaje" sumy tasa dariya "kidaiyi ahankali kawai matar mutum kabarin sa" gun Mama taje tana kuka umma ta kalleta "sai ki hkr domin baki da kaico ,naga yanada ilminsa har masters gareshi ga ilmin addini kawai Dan baya kwalliya saikice meye, cewar da kike mummuna ne ai ba daura Shi akafa zaki ba.ke kika cuci kanki ba irin samarin Daba su soki ba kike wulakanci,kuma kinsan Dadin ku baya magna biyu sai ki hkr." kuka ta cigaba dayi "wlh bana sonsa" jin tafiyar Dady yasa ta shige d'aki aguje ta b'uya ya shiga ya kalli mama "na bawa Sady bello domin dama ya dad'e yana sonta ta nuna bata yi dashi ,ban san wani zance na gama magana zati na sama za asaka rana" ya tashi ya fita.Aguje ta fito "mama wlh bana sonsa ko d'aya baida kyau" mama tace "ai har yanzu baki karatun ta nutsu bako? Meye dashi gashi Dan uwanki kawai ki hkr Allah yasa hakan shiyafi alkairi."tashi tayi ta fita tana ihu kamar me.
By
Queen Meemi👑
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣65-66❣
_Sadaukarwace Ga Basheer Usman family's_
_Page din naki ne Maijidda musa Nagode da kulawa❤_
******
kuka take kamar ranta zai fita hardasu birgima jin sallama yasa ta mike tai cikin d'aki zuby ce da Ruma sai Ruby hankalinsu ne ya tashi ko b'angaren iyayen nasu basu je ba suka zarce inda take. Sumy ce ke ta bata baki amma kamar k'ara volume take tamkar karamar yarinya, zama sukayi Ruma tace "sis meya faru? wan nan kuka haka! kamar ance mama ta rasu" tsagaitawa tayi "sabida Allah an kyautamin ace wai bello zan aura! Tuzuru dashi ga bai iya wanka ba ga bashida kyau" dariya suka saka ganin yanda tai mici- mici da ido Ruma tace "to saime! ba mutum bane?" Sady ta harareta "Amma dai kinsan bana sonsa kawai ace Shi zan aura" zuby tace "wai to meke faruwa? sady duk samarinki ya akayi haka ta faru?" sumy tace "ai duk ita taja" nan duk ta sanar musu Ruma tace "kinyi wawta ai Allah da kansa ya karrama D'an Adam meya kaiki wulaknta masu sanki,haba gashi Shi Wanda kikeso yayi auren sa ma, ita kuma hussy har kika iyai mata sharri" sumy tace "kudai gaya Mata ba irin shawarar da ban bata bata ba! ta biyewa lubna suka sako husy agaba gashi ta kaiki ta baro ta aure saurayin datai ta zugaki kuna masa wulaknci wlh maza sunkai 4 Wanda tayiwa wulaknci ai shima bellon tayi mai" zuby tace "ina lefin ma in bakasan mutum kabashi hkr Amma sai ki hau wulaknci gashi Allah ya nuna maki karshen me wulaknci don haka ki saki jiki ki rik'e Bello da kyau domin yana sonki kinsan Dady bai magana 2 atoh kuma ki dage ki koyi girki domin Naga k'alubale akansa duk soyyayyar da muka sha da fawwz rashin iya girkina yasa yake mun wani abubuwan, kin san mu nan Sam sede masu aiki suyi girki wallhi duk ciikin mu nan ba wacce ta wani kware sai yanzu da muke zuwa koya, don haka ku dage" Sumy tace "ai dole,lefin su mama ne da basu koya mana ba ai" Ruma tace "ai saiki dage ki koya yanzu" Sady ta tabe baki "aini ba sansa nake ba balle har na dage na koya" Ruby tace "ke kika sani dama aike bakya d'aukan shawara." nan duk suka fita daga falon suka tafi shashin su mama suka barta tana zancen zuci tare da danasanin wulakanta masu sonta da aure da tayi gashi dalilin rashin su za'ai Mata auren dole acewarta.
******??
Rayuwa suke shimfud'awa mai rai da lafiya har sukayi sati biyu a spain san nan suka tafi saudia umara har sai bayan azumi zasu dawo.kullm suna cikin ibada rayuwarsu abin sha'awa muktar da Shuriem sun zama abokai komai atare,yauma suna zaune sunje wani kanti zasu d'an sai sweat wata balarabiya sai kallon Shuriem take da alama ta d'asa. husy ta gano ta kishi ya turnuk'o ta taje ta bangajen matar hassy na kula da ita husy ta had'e rai tana hararta ba shiri matar tabar gun Shuriem ko in Banda dariya ba abinda yake ganin yanda ta had'e rai kamar zatai kuka yace "ashe babyn tawa akwai kishi" hassy tace "ai kadan ma ka gani"Mukatr yace to ai duk sammakal keda itan" nan gama siyayua suka bar wajen. haka dai rayuwar su take wakana cikin so da kaunar juna wan nan kenan.
*************
Yau a kazo saka ranar Sady da yake abin na gida ne kowa san abin yake Sady kuwa d'aki ta kullle tana birgima bello sai kiranta yake awaya ta d'aga "pls ka daina damuna na gaya maka wlh kabari akai auren kashinka ya bushe" dariya yayi "sorry sister tuba nake" ya kashe taja tsaki "aikin banza mutum kome zakai mai baijin haushi" haka aka saka kowa ya watsae Sady har k'aramin zazzabi tayi da dare Dady ya kirata yayi Mata nasiha kan biyayya san nan yace "ban k'wareki ba na baki dama. Sady kika take dama amusulunce uba ke zab'awa yaransa miji ina mai baki hkr matar mutum kabarinsa" ya sallameta kuka take yi tare da Dana sani sai yau take tuno Hashim Wanda har kuka yake Mata amma haka take cimai mutunci. ta tuno faruq mai hkr kullum yana tafe ba irin wulakncin daba tamai har ruwa ta watsa mai ta jikashi amma ya nace ta jin-jina kai ta tuno kamalu shima ya sota k'arshe yaga bazai iyaba ya ware. kuka ta kuma fashewa sai yanzu take dana sani "kaico na gashi zan auri Wanda duk suka fishi komai da komai" haka ta koma d'aki tana koke- koke.Washegari bello yazo ba laifi ya d'anyi fes amma sai aslow sai dare baki yake kamar ta fasa ihu ba damar yi masa wulak'nci don Dady yace in tamai bai ya feba shikuwa sonta yake sosai kamar me sai hararar sa take yana Allah ya huci zuciyar Gimbiya. haka ta juya ta koma yayi murmushi ya tafi itama Sumy ansaka ranar sai zaman jiran Lokaci.
*Bayan wata d'aya*
*******
Yau ale kamun su. Sady kuwa sai gursheke take tace "Wayyo D'an hakin Dana raina gashi Shi zan aura" sai lokacin ta bawa su zuby tausayi suna ta bata hk'r da lallashi ganin tayi kukan har ta gaji yasa ta daina magana sai kallo suna zaune misalin Tara na dare. Sady tayi lamo ajikin ruma kanta dake ciwo,Ruma tace "kinsan yau Dady ya bawa bello mota da babban gida! duk Dan ya faranta miki ki dage kimai biyayya" Shi kuwa bello Dan uwanki ne kuma masoyinki" bata ce komi ba ta d'aga kai Ruma tace san nan shawara kinsan mace na iya canja namji? to ina baki shawara daki fara canjashi wajen shashi yana irin kwalliyar da kikeso kai duk wani abu wlh da kanki sai kin gode min" kuka ta fashe "na shiga uku" Mama ta shigo "haba sady ke bakya yarda da k'addara ne? haba! kiyi ta addua Allah zai sanyaya ranki" tace "to mama." Mama tayi dariya "keda kikema 'yar gatan Dady har fa mota ya canja miki" su zuby sukace yawwa ai kodan faranta miiki da yake kyamai biyayya" had'e rai tayi domin gani take kawai an cuceta.
*******
Haka aka shiga biki gadan- gadan itada Sumy tayi kyau. Sady kam duk tak'i kyau ma saboda yawan kuka don agun dinner data ga yanda bello ke washe hak'ora sai da taji kuka domin kome zai bai burgeta. Shikuwa duk wani abu dayake Dan ita yake.haka aka gama biki lami lafiya kowacce aka mik'a ta gidan mijinta. Sady kamar k'aramin hauka take saboda ihu sai da Dady ya daka Mata tsawa yace "ki Kula sady ayanzu duk abinda ki kaiwa mijinki zunubi ne" kuka ta kuma fashewa tausayinta yaji ya sauko yana Mata nasiha k'arshe yace "ki hkr kinji Allah yayi miki albarka ya damk'a Mata muk'ulln Sabuwa motar mata suka mikar da ita suka tafi.
Tnz reader for support me luv lodi .
Loading..end
By
Queen Meemi👑
.
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣67-70❣
_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_
*KARSHE*
***********
Tunda aka kaita take tsiyataku kala- kala bello sai d'ari -d'ari yake domin har tsoron fad'anta yake. yau sunyi sati d'aya Amma ko kallo bai isheta ba da yake mai hkr ne haka yake sharewa komai ya samu sai ya kawo Mata ko bataso kyautatawa kala- kala idan 'yan kirkin nanan zata kulashi Amma in basa nan kallo bai isheta ba, komi Shi yake ganin Agidan harsu shara domin ko tsinke bata d'aukewa a gidan.yanayin hkrn sa yasa ta d'an fara sakin jiki haka dai zaman nasu ke wakana ta b'angaren sa yanzu har jins da t -shrt yake sawa duk Dan ya birgeta tana kwance zai Mata break fas ya kawo tana ya tsina haka zai ta lallashi irin kulawar da yake bata yasa ta fara d'an tausayin sa take masu girki duk da ba iyawa tayi ba Amma haka yake ci kuma ya yaba komai rashin dad'in sa gashi ko yaushe ya fita sayya zo mata da gift ganin hakan yasa ta dan sassauta.
*********
Lokacin azumi ya k'arato cikin nan jamaa aka fara azumi su hassy cike da jin dadi suke gudanar dashi bautar Allah suke tuk'uru da Adduar neman samun zaman lafiya mai d'orewa.
Ta b'angaren Sady kuwa sai aslow yau data ta tashi da rashin lafiya ko hannu bata iya d'agawa bello duk ya rikice ko aiki daina zuwa yayi shike Kula da ita yawan ciwon kai take sunje asibiti an bata magani Amma indai ciwon kan ya motsa sai tayi ta kwarara amai haka zata yi a ko'ina bello Shi zai gyara wajen ba k'yank'yami har cikin dare intayi haka zai ta kai kawo yana taimakonta wataran har kuka yake idan yaga tana kuka saboda tausayi,cikin ikon Allah aka samo magani wani maganin gargajiya take sha nan ta fara samin sa ida tun bayan warkewarta ta daina mai rashin kunya ganin yanda yayi d'awainiya da ita gashi ko kad'an bai san b'acin ranta d'ari -d'ari yake haka ta sakko suka fara zaman lafiya sai alokacin ta gane bello irin mutanen nan ne da basa nuna soyayya a waje sai anyi Aure soyayya yake nuna mata kalar wadda take so cikin salo take nunamai irin yanda take so ya dinga gudanar da kwalliyar sa da tsaftar sa sai gashi yayi fes bataji sonsa ba .Amma zaman lafiya suke gudanarwa kullum cikin yawo da ita yake don taji dadi ga cima sai wadda takeso ko ihim tayi sai ya rikice,cikin wata daya suka sake sai ga Sady duk an manta baya ji take da bello Dan yanzu ya dawo irin wanda ta keso hatta turare sai k'amshin da takeso yake sakawa domin da turare baidameshi ba haka kaya komai ma shi kuwa farinciki ke kamashi domin ya samo kan abarsa.
Wani zuwa da sukayi gida dukansu suka ga Sady tayi kib'a nan suka hau tsokanar ta cewar kika ce bakyaso dama gulma ce " tace "ai Anty zuby "sai yanzu na gano dawan garin mace zata iya canja namji kuma ka auri mijin dake sanka yafi domin don bakiga yanda yake min ba ,shiisa nima na sauko nake Kula dashi ,kinsan meye wlh manyan mazan nan sunfi rik'e mace gam musamm Wanda ya dad'e bai aure ba" tafawa sukayi sumy tace Alhmdlh k'ananan ma suna rik'ewa kaide ka samu mai sonka da gaskiya kaima ka rikesu da amana kuskure Ada munyi amma yanzu komai lafiya sai kuma kyautatawa" Sady tace ai nikam na godewa Allah wani hanin ga Allah baiwa ne ,so nake na fara zuwa gidan kayan girki ma" Ruma tace "ba gashi kinyi biyayya kinga sakamako ba Allah dai ya inganta" wan nan kenan.
******
Yau ake azumin karshe su husy sai shirin dawowa suke. washegari kuwa suka sauka a Nigeria watansu 2 acan sun dad'a kyau kai bakace su husy daga Nigeria suke ba kowacce sai murmushi ,suka saukaa gidan su mum sunyi murna sosai Dady ma yayi farin cikin ganin su nan duk suka bada tsaraba da yake azumi ne husy ta tafi gida da wuri .hassy kuma sai gobe zasu tafi saboda sallah.
Washegari su muktar jirgi kuwa sukabi jya sauke su afilin jinrgin malam aminu kano direct gida suka wuce nan 'yan uwa da abokan Arzuka sukai ta musu barka da zuwa,nan aka gama azumi aka shiga bikin salllah cike da farinciki.
Sinasir husy tayi mekyau da lafiya da miyan agusi me bushashen kifi da naman kaza sai k'amshi take da drinks kala- kala ta bawa Shuriem yakai abincin sallah gidansu gun babrsa hade Dana mumyn ta.shima ya kwaso abokansa 2 suka kwashi girki domin ba karya itada hassy sunyi iya girki mum batai wasa ba domin girki shine mace wan nan dalilin yasa ma mazan keji dasu tamkar kwai. Sati daya da sallh husy na zaune taci uwar kwalliya tana ta kallo taji Ana knockn mik'ewa tayi da mamaki a fuskarta "mezan gani kamar su karima da Sahura" dariya sukayi suka zauna akan tiles tace "haba ku hau kujerar mana" sai kallonta suke tace "ashe zan sake ganin ku!" suka ce "wlh munje mangalu akace ai kina abuja kuma kinyi Aure kinsan daya muke aure da sahura, shine mukace mukam sai munxo wlh muka saida awakan mu kazo gidan su zuby yau kwanan 2 ashe! sady ma sun aure" Husy tace "niban ma san tayi aure ba yau satinmu daya da dawo nigeria kum kuwa k kyauta wlh kun rike alk'awari ta" kalli yaran dake hannunsu wad'annan 'ya'yannku ne?" sukace eh kowacce yaranta biyu" tace masha Allah nan ta basu abinci fa lemo sukaci suka sha karime nada waya ta bata number suna gaisawa suka mik'e zasu tafi ta hadosu da turare da turmin atamph dai dai sai kwancen kayanta wasu ma so 2 tasa.wajen kala biyar biyar ta basu ta had'a musu da tsarabar makka sukai ta godia. lokacin Shuriem ya dawo ta sanar dashi ya basu dubu goma -goma saboda dadi harda kukansu suka tafi husy taji dadin ganinsu sai rayuwar da sukai lokacin suna aiki ke dawo mata wan nan kenan.
********
Wata daya ga sallah suka tafi mangalu Shuriem zai gaida su malam sunje lafiya aka karb'esu lokacin suka aje musu tsarabar da sauran abubuwa. suka tarar Ana bikin husy dije ta bada gudun mawa Kwana 2 sukayi da zasu tafi Abdullah ya nace zai bisu dama Shuriem cikin garin kano ya tafi ya dawo daukan husy ya tarar da hakan .malam harda dukan Abdallah Shuriem yace "baba ka bamu Shi mutafi can dashi sai yayi makarnta acan husy tace "tunda anan wataran kin zuwa yake ba!" Dad'i jummai taji malam yace "zai d'ora muku nauyi fa!" Shuriem yace "haba malam "wane nauyi husaina fa ku kuka rik'eta ai abdallah matsayin k'aninta yake" malam yace "to Allah yayi albarka nan suka tafi dashi suka yi sallama suka tafi.
Komawar su da kwana 2 aka sashi wata primary me kyau da tsada.
*Bayan shekara 2*
Husy d, hassy ne da Suhaima suke birthday din first born din ita suhaiman na 3 yrs lokacin sunyi kyau husy da hassy kowacce da babynta masu kyau turare tas dasu husy namiji shakur hassy da yarta Rauda duk watan su goma am musu kwalliya sunyi kyau su hassy ma sunk'ara kiba su kara kyau cakes ne guda uku za a yanka sai daukan photo suke suna zaune wasu yara yan makotansu bazafi 3 din ba aka kawo su nan aka yanka musu suna ta jin dadi ko ina baloons .
Sallama akai Suhaima tace "Sady ashe zaki zo! su husy duk suka juya itama tana rike da babynta mace nan suka gaisa dasu husy suna ta hira Sady ta kalli husy "duk abubuwan da suka faru abaya kiyafen min na dade ina son had'uwa dake Amma ko yaushe bakwa kasar sai yau. husy tace "bakmi fa!ni nama manta ai ya wuce" sady tayi murmushi "inaso mu cigaba da zumucnci" hassy tace "okey ba matsala" haka akayi aka gama kowacce ta tafi.
Husy da Shuriem na tafiya a mota ga babyn su abaya Shuriem na waya driver ya dauko abdallah daga school an tsaya round about sukaga wani gu a hargitse alamar Ana fad'a duk an had'a goslow suna tsaye suka ga Dan sanda ya fito da wani za'a turashi mota sai ihu yake bashi bane. husy tace "wlh lawandi ne! to meya kawo shi abuja!" tace "husbyna ataimakeshi" ya bud'e motarsa yaje wajen D'an sandan na ganin sa ya sunkuya ya gaidashi domin da yawa an sanshi garin Abuja saboda companynsa dake ci ya tambayi ba'asi Dan sanda yace "gudun gacganci yake a babur ya bigi motar wani shine mutimin yace bai yarda ba sai an gyara mai mu kuma muka kamashi saboda gudun ma da yake na ganganci." Shuriem yace "fito dashi aka fito da lawandi fuska shab'e -shab'e domin yasan wahalar da yake agunsu bayau d'aya ba aka kamashi yace "wlh bani bane wani ne ya bige motar ya gudu ni kuma lokacin na tsaya abun ya wad'a kaina kuma babur din arone" nan Shuriem ya bada ten thousand kan mutumin yayi hkr ya bada card nashi kan yakai motar inda ya kwatanta a gyara mai duk a ljihun Shuriem. take aka saki lawandi sai godia yake har ya biyoshi bakin motar caraf idonsa ya sauka akan husy ya nuna ta da yatsa duk da tak'ara girma da haske amma ya ganeta yace "hansai kece mijinki ya taimaken? dama na dade ina nemanki" shureim yace "kai nutsu kaji" nan ya sunkuya yace "don Allah kiyafemun nasan da hak'kinki" ma tace "na yafe Amma yakamata ka nutsu mana duk rashin ilmin ne ka koma makarntar yaki da jahlici" nan ta zaro dubu goma ta bashi Allah ya kiyaye suka ja motar su ya bisu da kallo,da kudiri aransa na gyara rayuwan sa.
Haka rayuwarsu ta kasance dai husy na kwance kan 3 seter shakur na wasa akanta shureim ya shigo da gudu suka mak'alk'aleshi ya cafe shakur yana kissn kumatunsa ya kamo husy "finest Allah yayi muku albarka keda little boy namu,ina sonki matata ta" dagowa tayi tai fari nagode angona yakai Mata peck agoshi dai -de lokacin Abdallah ya shigo yana jss 1ya ya gaidasu yayi fes dashi.ya shiga dakinsa dake kasa.
jansa tayi ta tayashi yayi wanka yaci abinci me dadi nan ya janyota jikinsa.
wani agogo Shuriem ya zaro duk an rubuta sunan husy da ruwan zaiba ta ciki amma ya samata ahannu yace "Allah ya Kara mana dankon luv" tace ameeen ya hadasu shakur agefe yana papa itama adayan side din ya sakar musu selfi sunyi kyau. happy family.
Tammat bihamdlh.
Anan na kawo karshen wan nan book nawa mai suna Rabuwa ce sandi inda nayi kuskure Allah ya yafen inda nayi daide kuma Allah yasa ni amfani da fadakarwar dake ciki . domin nobody is ferpect. Allah ya kara mana kaunar Sayyadi Rasulillah.
Godia ga d'aukacin groups din da suke bibiyar wan nan book nawa ngd Allah ya bar kauna.❤
Fans Dina kunmin komai kun nunan kauna da book dina ina sonku sosai kamar yanda kuke sona.👍❤
GODIA Ga Kungiyar NAGARTA WRITERS ASOOCIATION Allah ya barmu tare.
Wasalllahu Ala nabiyur rahmati wa hali wa sahbihi ajmaen.
Ni Queen Meemi👑 Anan na aje alk'alamina sai kuma Allah ya Kara sadamu daku ga wani sabon book din wanda bankai ga samasa suna ba Allah ya taimakemu Ameen.*fans kuyi follow Dina on Wattap@Queen_Meemiluv*
❤❤❤❤❤
.
0 comments:
Post a Comment