*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣1❣
*©Mymounerh Basheer*
*®NWA*
*littattafan marubuciyar*
*soyayya gamon Jini*
*Raheena*
*kishiyoyina*
*habibullah*
*noor ala noor*
*Na Aminta dake*
*gimbiya maimunatu*
*Akan kaskon suya*
*Zeenatu*
*Ashe haka so yake*
*Queenmeemi.WordPress.com*
***************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*_k'aramar hukumar bunkure,dake jihar kano_*
Babban titin dake garin bunkure wanda ya cika da d'aukacin jama'a kowanne ka kalli fuskar sa arazane yake wasu kuma gudu suke ci,ga wasu a kwance dai-dai kusa da wata Babbar mota na gano yarinya
Yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniyaba a zaune kusa da wata mota sai ihu take,Jikinta sai karkarwa yake kukan natan Sam baya fitowa sabili da taci kukan harta k'oshi.
Daamm!!! k'ara ce ta kuma tashi, take mutane suka hau guje-guje yarinyar da Bacci ya fara d'ibanta ta tashi firgigit ta k'wala k'ara ba wanda yasan tanayi gudu ta hauyi irin Na yara bawanda ke Kula taa kowa ta kansa yake ,ke sai kiran momy take da dady ,wata mota ta gano gurin tayi aguje
taje aguje tana bubbugawa dady! dady! neman iyayenta take Amma ko alamarsu Babu ga wajen ya hargitse kowa takansa yake Saboda tashin bomb din da akaji wanda yazamo tamkar wata jaraba gun wani mutumi ta yi ta baya da gudu tayi wajensa tana dady.
juyowa yayi a tsorace yayi arba da ita , yana shirin magana k'arar bindiga ce tafara tashi tas! tas! tas! tas! kakeji nan da nan waje ya kuma hark'ewa hayak'i ko ta ina.
yarinyar da duk Jikinta yajike da fitsari ga bakinta Na jini ,mutumin nan ya falfala yafara gudu ,yarinyar tabiyoshi dady! dady! sojojine suka tawo aguje suna harbi nan da nan mutumin yai wata kwana yarinyar tabishi tana ihu inda ya b'uya taje ta tsaya ta dafa shi "dady momma" hankad'eta yayi yace "Yau naga jaraba ke ina iyayenki? ana wann nan tashin hankalin don sakaci", tureta yayi yace ta bar wajen, tafiya tayi da gudu tayi wani waje tai kwana tana sangal-tangal saboda ciwo dataji a k'afa wani yaro ne ya arto yana haki yai ciki da ita ta fad'i k'asa d'agowar da Zatai akai harbi Allah ya taimaketa ba aharbeta ba Amma tsoro yasa ta suma ganin hakan tausayi yakama mutumin ya fito Daga mab'uyar sa ,yazo ya d'auketa ya
runtuma aguje yana gudu seda yayi nisa yaje motar sa dake ajiye ya ajiye ta agaban mortar dayake motar d'aukan kayace yara su hud'u ya ganni a bayan motar sai ihu suke ya kallesu yace " ina iyayenku"? D'aya ne mai wayo yace "nan mukazo muka b'uya",Sauran kwa ba wanda yayi magana sai kuka duk jikinsu k'ura da d'an Jini-jini ajikin su,jin- jina kai yayi kawai ya shiga motar.
************
*K'auyen mangalu*
Jan motar yayi ya fafara aguje nan yiyi hanyar k'auyensu tafiyar awa d'aya da rabi ya kaishi k'auyen mangalu wanda yake a k'ark'ashin k'aramar hukumar bunkuren, Bayan yaje k'auyen nasu su, take bai zarce ko ina ba sai tasha,ya bud'e motar ya fita yaran yad'ebo, ya sauke su gaban motar yaje don d'auko yarinyar wayam ya nemi yarinyar ya rasa neman duniya yayi bega yarinyar ba mamaki k'arara afuskarsa "kode aljana ce tsuka yaja inajin Aljana ce
sede ko sauka tayi",nan yayi ta dubawa bai ganta ba
Sarkin kasuwa ne yazo aguje "Malam lado me nakeji ne agari wai cikin gari bomb ya tashi da Gaske ne kuwa"?
"Tabbas! hakane Sarkin kasuwa Ni kaina wallahi abun yaban tsoro, lodi fa nake zan kai kaya kasuwa kawai mukaji k'arar tashin bomb ai Wallahi munga tashin hankali don an mutu agun ,dak'yar Na sha,kaga kuwa abin tausayi harda wata yarinya dana gani
agun sai karakaina take tana neman iyayenta kawai sai yarinya ta dinga bina tausayinta yasa Na d'auketa abin mamaki munzo nan Daga sauka din na sauke yaran can na duba bangan taba".
"Allahu Akbar Allah ya k'ara kiyayewa" sarkin kasuwa yafad'a Yaran nan su hud'u malan lado ya mik'awa Sarkin kasuwa da bashi dubu d'aya kan akaisu Police station da ke cikin garin bunkuren ko za asamu iyayensu , sarkin kasuwa yace wa wani d'ahiru ya rik'e yaran ya basu abinci shida MLM lado suka hau dube-duben neman yarinyar nan ,Amma basu ganta ba ,nan suka dawo lokacin yaran Sunci Sun sha MLM lado ya deb'e su sarkin kasuwama ya shiga motar .
Sun fita titi caraf idon sarkin kasuwa ya gano masa yarinyar nan gefen titi da Rabin bread a hannu tana ci tana kuka,yace "hala dai ita ce waccan"? Malam lado yace "ita ce" direct motar ta tsaya suka fita abin tausayi
jikinta zafi zau suka d'auketa,sunje police station suka bada yaran kan b'atansu a dalilin tashin bomb d'in ,sunayensu a ka d'auka da hotuna,da yake gidan sarkin kasuwa anan yake yasa aka bar yaran a gidan nasa,su kuma 'yan sanda suka hau sanarwar neman iyayensu. malam lado ma ya tafi kan duk yanda akai Skasuwa ya Sanar mai.
*by Queen meemi*
. . January 2017 Queen meemi
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣2❣
*©Mymouner Basheer*
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
wajen yamma MLM lado ya je gida a gajiye shigar sa gida ya Tarar da gwamma na tsinkar zogale d'agowa tayi tace ''MLM Yau kayi nisa da yawa" ,ruwa ya d'ebo a randa ya sha San nan ya zauna atabar mar da gwamma ke kai,yace "ai Yau munsha da k'yar nan ya labar ta Mata dafe k'irji tayi "kai Amma ka auna arziki' ,dama naji labarin birni bai shiga ta Dad'i, gashi yazo garin nan yanzu" alamar jimami ne fuskar sa,yace "ai kede bari gwamma Allah ya kyau ta dai" kallonta ya kumayi "wai Ni ina jummai ne"? tab'e baki gwamma tayi "ai kasan ayawoma ce Sam bata zama agidan nan muddin kasa k'afa ka fice".murmushi yayi don inda sabo ya Saba da halayen gwamma wajen yiwa jummai sharri,sallamar jummai ce ta katse musu hirar da harara gwamma ta sauki jummai da murmushi d'auke a fuskar jummai ta tsugunna tace "malam Barka da dawowa ,naje gidan kaka ne gaida ita Batada lafiya" nan yace bakomi jummai nasan da dalili ai " gwamma tace "tab! Lalle malam ka sakarwa jummai da yawa ace Mata ta fita bada izininka ba, Amma bazakai Mata fad'a ba,ita ga matar so" tashi jummai tayi ta d'auko kwanon abincin malam ta aje mai da ruwa daya ke itace da girki Yau, nan ya hau ci dama yunwa ce ke cinsa.
*BAYAN SATI D'AYA*
MLM lado na zaune a soro yana jin radio domin tun lokacin da bomb ya tashi bai koma cikin gari lodin kaya ba, don yaji labarin wajen ansa masu tsaro , kuma gashi saboda tsoron karyaje tsautsayi ya afka dashi, sallamar sarkin kasuwa ce ta katse mai jin radio d'in da yake da fara'a ya zauna suka gaisa mudi D'an MLM lado mai kimanin shekara goma ya kawo mai ruwa,sarkin kasuwa yace "wato MLM lado yaran nan cikin ikon Allah duk anga iyayen su biyu a asibiti akaga nasu iyayen sauran kuma duk yan uwan su ne suka karbe su duk ta dalilin faruwan tashin bomb dinne yara suka bata ,kuma duk Daga wani garin suke,wani hanzari ba gudu ba ,yarinyar nan Sam! ko alamar wanda ya Santa ba agani ba balle su zo",gaban MLM lado ne ya fad'i cike da tausayi yace "ikon Allah yanzu ya za ai ke nan sarkin kasuwa yace ai police sunce mu rik'eta agunmu zasu cigaba da dubawa gashi Ni kuma zan tafi garin gabas jibi" ,mlm lado yace "to ai ba matsala ka kawota gurina muga yanda Allah ya yi ,haka sukai sallama ya tafi.
*WASHEGARI*
wajen k'arfe goma sha d'aya saiga sarkin kasuwa nan da yarinyar suna tsaye sai ga Shi ya fito musabaha sukai da Shi nan yace "to MLM lado gata nan godia malam lado yayi mai ya tafi Shi kuma ya d'auketa suka shige ciki.
gwamma na hura ice jummai kuma na tankad'e MLM lado ya shiga kallo suka bishi da shi ,murmushi ne Akan fuskar sa gwamma tace "malam wan nan yarinyar fa"? ,kallonta yayi yace "Dad'i na dake wutar ciki, to 'ya na samu" nan ya kwashe duk yanda abun ya faru ya gaya musu jummai harda kuka saboda tausayin yarinyar gwamma kuwa tace "to rik'eta zakai kenan"! MLM lado yace "to ya zanyi Allah ne ya had'ani da ita" nan ya kalli jummai yace "ga 'ya na kawo miki ki na Kula da ita, kafin Aga iyayenta,da murna ta karb'eta dama bata da yaro tun lokacin da yarta hansai ta mutu har yanzu bata K'ara haihuwa ba,kallon yarinyar tayi tace "ya sunan ki ,batai magana ba sai D'an motsa baki da tayi,malam yace "kinga jummai kisa Mata suna na wucin gadi sai ana kiranta dashi kan Aga iyayenata".
"MLM zan ce Mata hansai sunan marigayiya",gwamma tace "Amma ke kan jummai anyi solob'iyo ayi dai mu gani Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i" MLM lado yace" kinga gwamma ban San neman magana tunda bake na bawa ba baruwan ki" tab'e baki tayi ay ba tun Yau nasan kafisan jummai dani ba ,me zanyi da tsintacciyar mage, nan ta buga cinya ke kuma jummai dani kike zancen".......
*By Queen meemi*
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣3❣
*Jan 2017*
*©Mymouner Basheer*
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
haka jummai ta d'auki hansai ta shigar da ita d'aki ta fito ta D'ora Mata ruwan zafi tayi Mata wanka San nan ta wanke kayan ta ta shanya, d'akin nata dake d'auke da azara ta shiga da hansai ta ajeta, tana na zaune tayi zuru nan ta d'aura Mata zani ta bata abinci ta ci,gwamma ce ta shiga d'akin "to gulmamma sai ki fito ki tuk'a tuwon da miyar" jummai ta d'ago "to yaya gani nan" madafar taje ta duba kayan kad'I bata ga kuka ba, nan ta fito tace "yaya ina mudi yazo ya sayo kuka" gwamma tace "ke bazafa ki ta kurawa yarona da aike-aike ba,yanda kika Saba fita sai kije" haka jummai ta d' au mayafi ta shiga Mak'ota siyaowa
bayan fitar ta, gwamma ta shiga d'akin jummai, hansai na tsugunne tana rawar d'ari tsayuwa tai ta k'ura Mata Ido "oh malam da kwashe -kwashe ko ina ya kwaso wan nan yarinyar oh" d'aga kai hansai ta kalle ta gwamma tace "ke Maida idon ki k'asa wa yasani ma ko mayya ce ke" wani kwano ta dauka ta fita dai-dai lokacin jummai ta dawo nan ta D'ora girkin ta shirya hansai.
*MALAM LADO*
malam lado asalin sa d'an nan garin bunkuren ne yana zaune anan mangalu d'in ne tun iyaye da kakan ni ,su uku ne agun iyayen su, Daga Shi sai k'anin sa sai k'anwar su wanda duk suna garin suma da iyalansu,yana sana'ar tuk'in mota yana lodin kaya zuwa gari- gari,gwmma itace matar sa ta tafari haladu shine d'ansa na farko da ita Amma Allah yayi masa rasuwa sai mudi da aka haifa bayan haihuwar sa da shekara uku ya auro jummai, zaman lafiya suke yi farkon kawo jummai Amma bayan samun cikin jumman, sai gwamma ta uzzura Mata ta tsangwameta ,Allah yayi gwamma da fad'a ga San girma da son komi ace itace a kai ga k'yashi ,batak'i ace jummai tana mata biyayya ba don ma malam tsayyye ne shiisa take D'an ragawa jummai bayan haihuwar jummai shekarar 'yar ta hansai d'aya aduniya tace ga garinku, tun Daga time d'in bata kuma samin ciki ba.
wan nan dalilin ne yasa gwamma ke shuka Mata tsiya Musamman wajen aike sai dai taje da kanta badai ta aiki mudi ba, hakan yasa take lullub'i ta tafi da kanta ,inkwa aka samu mudi yaje aiken to sai ta bashi kud'i wan nan ke nan.
*bayan wata d'aya*
*karfe 8:00 da safe*
hansai ce tsaye bakin famfo jummai na k'ok'arin dafa Mata ruwan zafi saboda sanyin da ake ga kuma koko da take San damawa gwamma ce ta fito ta bud'e tukunyar ta kamfaci ruwan jummai ta d'ago "yaya fa ruwan wankaan hansai ne fa ,kuma Dana koko".
gwamma ta juyo da harara Akan fuskar ta, "na d'iba d'in mudi ne ke San wanka Yau kwanan sa hud'u bai ga ruwa ba, don zakiwa wan nan figaggiyar yar shine zaki magana kan na d'ibarwa D'an gida,koko kuwa dole ki dama" tsaki tayi afujajan ta yi hanyar band'aki.
jummai bata ce komai ba sai ma d'aukan hansai tayi ta Goya ta ,malam dake fitowa da buzu ahannunsa zai je soro ya tsaya yace "kaga jummai da yar ta" murmushi tayi tace "wallah MLM gata da hak'uri sai dai tana yawan cewa wai mamma da dady" ,alamar tausayi ne a idon malam yace "Allah sarki, wallahi kullum naga yarinyar nan sai naji k'walla a idona saboda nasan duk inda iyayen ta suke basa hayyacin su" ,jummai tace "Allah dai ya sa agansu. MLM yace "ameen" nan ya fita ,sai wajen 11 hansai ta samu wanka.
lokuta sunja haka watanni Yau kimanin watan hansai shida, Babu amo ba labarin iyayen hansai haka malam yace yaji ya Gani zai rik'e ta amana son yarinyar yake kamar me komai ya samu itace nan ta koma cemai dady duk ganin sa take shine ba banta haka jummai tamkar 'yar cikin ta nan tace tana ce Mata inna sosai - sosai yarinyarta ware,ganin irin kulawar data ke samu nan gwamma ta kuma tsanar hansai ko gunta bata San zuwa da taje zata kwad'eta tace tafi can tsintacciyar mage mudi kuwa cin zalinta yake shiisa bata zuwa inda yake.
haka dai rayuwa taci gaba da tafiya da k'alubale da dama Yau ga hansai nada shekara bakwai ahanun goma a hannun malam lado wanda in aka had'a da shekaukun ta shekarar ta goma kenan,hansai ta zamo yar da suke so kullum tashin duniya MLM ya kalleta sayya ji kamar yayi k'walla, (haka ake San bawa mai yawan tausayi) wanda ta zamo jinin jikin jumai da mlm.
Sallama hansai tayi ta shigo da Allo ahannunta ta dawo Daga makarantar Allo ta dawo ta yamma. Nan taci karo da mudi take ya kai Mata mari wasu wuta ta Gani nan ta durk'ushe tana kuka gwamma dake b'arar gyad'a tana watsawa abaki tace "kayi min dai- dai ita ba Mara kunya ba, wai waccen munafukan marik'iyar taki itace ke zugaki har Kina had'a hanya da mudi" ,jummai tace "Haba yaya yanzu ai bai Dace ba kamar mudi yayi Mata wan nan Marin,saboda ai kwarin su d'aya ba", gwamma tace rufen baki mai rik'on wahala tashi tayii ta janyo hansai ta mik'ar da ita, had'a Ido sukai da gwamma nan ta yiwa hansai dak'uwa, "daina kallona da Ido kamar gujjiya".
d'aki suka shige jummai tace "hansai ki hak'r kinji mamanki gwamma ba wai sanki ne batai ba, kawai haka take" ,hansai ta jin-jina kai "ai inna na sani" Amma azuciyarta Sam tarasa mesa gwamma ta tsane ta.
Zama tayi tana tilawar karatun ta, jummai ce ta shigo rik'e da rubutun tsari tabawa hansai ta shanye wanda kullum sai an bata ko Tai Mata tofi aruwa ta sha ,yanzu izifin hansai arba'in, domin malam ma yana da sani dai de gwargwado yana koya Mata.
Akwai wata makarantar boko a bayan gari ita hansai ke tafiya tana aji d'aya 2 na fimamare duk da yaran garin basa zuwa karatun, a ajin nasu basu fi su goma ba domin wataran ma a bakin bishiya suke zama ahakan hansai ke dagewa domin wataran malam shike takawa da k'afar sa ya kaita San nan ya dawo ,yana so tayi karatu koda secondary ne daya ke malam nada wayewar ilmi sabili da yawan tafiyar sa ,mudi kuwa Sam baya San karantun shiisa inaga shekara d'aya kawai yayi yana zuwa ya daina Shi isa MLM ya turashi gona da yake malam yanzu baya tuk'in motar shiisa ya koma gonar.
hansai kuwa duk lokacin da jummai Keda girki to tare suke yi, tana koya Mata shiisa jummai bata da damuwa kokad'an, ga tsafta sabili da jummai na da tsafta shiisa hansai ma ta tashi cikin tsaftar Sam bazaka ganta futu-futu irin sauran yaran kauyen ba,sai ka d'dauka sune asalin iyayen ta saboda kulawa.
ganin hakan yasa gwamma ta bud'e huta kan sai hansai ta dawo hannunta, jummai bata iya fad'a ba, Amma aranar tace Sam bazata bawa gwamma ba ,malam dake shiga gidan ya shiga yace "Haba gwamma yada haka bakya tunanin lalurar dake jikin ki" nan ta fasa kuka ,"ai MLM dama nasan kafi San jummai shiisa ganin hakan yasa ta samu damar yimin habaici,wai tana da yar huce takaici lo bata haihuwa" don na rok'eta kan hansai ta dawo hannuna saboda cikin dake gareni yanzu ban iya komai shine ta bud'e min wuta" .
jummai kuwa in Banda kuka ba abinda take saboda tasan k'arya ta Mata. MLM yace "duk hakan bata taso ba, naga hansai ko agunwa take, wata zata iya sata Aiki, to meye abin tashin hankali" gwamma tace "nikam malam ka bani hansai kawai idan ana San zama lafiya ta dawo guna kawai" . Malam yace "Haba gwamma ki zama mai adalci mana sai da kika ga yar ta fara zama mutum San nan kizo kice a baki? bayan ga wanda taci kashin ta".
gwamma ta shige d'aki tana kuka jummai tace "malam na yarda ta koma tunda nasan ba rabuwa Mukai ba", k'ank'ameta hansai tayi ni inna nafi San gunki". MLM yace hansai 'yata ki koma gun ta kinji kan ta haihu Kinga k'ani zaki samu", saida jummai ta lallasheta San nan ta yarda.
da gudu taje soro tana kuka innar ta kawai take so Sam bata san gwamma Amma ba yanda zatayi dole ta koma
tunda ma suna tare.
*BY Queen meemi*
.
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣4❣
*©Mymouner Basheer*
*®NWA*
*Queenmeemi.wordpress.com*
_Salamu Alaikum fans masoya littafina ina mik'o gaisuwa gunku,na gode da kulawarku_
*Sati biyu da komawar hansai dakin gwamma*
komawar hansai d'akin nan gwamma ta shiga takura Mata da tsangwama. kullum cikin aiki ada hansai Sam bata zuwa rafi Ko yo itace domin jummai bata saka ta koda deb'o ruwa ne Amma gwamma da gayya zata aiketa deb'o ruwa Ko ita cen sabili da malam baya so.
yau ma da ake rura uban sanyi wajen k'arfe takwas na safe,hansai na kwance tana barci gwamma ta d'akawa hansai duka tare da kai Mata hauri ,firgigit ta tashi tana zare Ido, da k'arfi ta fad'a "inna" jummai dake zaune tana gyra ta mik'e ta fito tsakar gidan a tsaye ta tarda hansai,na rawar d'ari da botiki a hannu,gwamma ta fito "ke hansai tafi rafi" jummai tace "haba yaya ina hansai ina zuwa rafi" .
tsaki gwamma tayi "to munafun- fun yara nawa suke zuwa rafin, su dama suke "yan gida balle ita tsintacciyar mage daba galihu gareta ba" ,tsawa tayiwa hansai tace "shige muje Ke Kuma," haka suka yi hanyar soro gwamma tace saura ki Dad'e ga su tsahare can za su je".
nan ta dawo ciki har lokacin jummai na tsaye nan ta kalli gwamma tace.
"Amma yaya kin San dai hansai tafi k'arfin tsintacciyar mage Wlh hansai agarin nan bata da maraici, malam da zai tafi rano sai daya jaddada kar a Aiki hansai rafi Amma kikayi sabili da kinsan gurin ba tsaro".
"lalle jummai wuyanki ya isa yanka, ina fad'a Kina fad'a Ko? ,to kisani yanzu hansai ba a hannunki take ba sai yanda na yi da ita Wallahi".
jummai tace "yaya hansai 'ya tace domin jinta nake har b'argo na don haka ina nan bazan bari ta cutu ba, domin Amana ce awurin mu .
tsaki gwamma tayi tace "JUYA Kawai"littafin Feenaat ja afar) San nan ta shige daki jummai da rai sakato ta juya cike da jin haushi sa b'acin rai na kalmar juya data kira ta.
*Hansai*
tun fitar hansai take kuka nan taja birki kusa da wata bishiya ta zauna ba yaran data ga ya fita iyan zu sai ita, saboda yanda ake sanyin nan, ga rafin da nisa tashi tayi ta hau gudu cak! ta tsaya ganin cakau sunan wata akuya ce mai tunkuyi a garin k'ahonta cako- cako data ga yara Mata zata bisu tana tunkuyi, jikin hansai bai Dena b'ari ba gudu tasa akuyar ta hau binta.
Muntari dake tawo wa ya tsaya cak! take ya kori akuyar ya kalli hansai yayi murmushi "kema tsoron cakau kike"? "Eh wallahi agaba na ran nan ta fasawa d'ahiru hannu" murmushi yayi keba k'anwar mudi bace"?
"eh nice" ta fad'a a tsorace .
"Ina zaki"
"rafi zani d'ebo ruwa"d'aga kai yayi yace "kai da sanyin safiyar nan, duk yaran ma ban ga kowa ba ana sanyi fa.
muje na rakaki"haka suka je ya d'ebo ruwan ya d'auko mata suka juyo yana rik'e da botikin har ya kaita k'ofar gidan su ,San nan ya koma.
tana kai ruwan ta koma ta fara hura wuta gwamma nadaga d'aki tana Shan koko yunwa duk ta ishi hansai sai data gama San nan ta bata koko da k'osai biyu tasha ,gyangyadi ne ya kama gwamma nan hansai ta sulala tayi d'akin jummai(inna) tana zuwa ta kwanta kusa da ita suna ta hira ta K'ara Mata abincin taci.
ji tayi an kai Mata shuri gwamma ce tsaye tace "Ke hansai wancen wankin nawa wazai miki ehe"?
idon hansai ya kawo ruwa tace "mama gwamma bazan iyaba sunyimin nauyi"
dundu ta kai mata "Dan gidanku a banza zamu na baki abinci ina lefin rik'on da ake mike, tashi kona masge ki" hansai dake shiga rud'ani duk lokacin da gwamma tace Mata rik'on ta suke, Ko tace Mata tsintacciyar mage,sai taita tunanin kodan tsanar da rai Mata ne yasa take Mata hakan, tashi tayi tana matse hawaye,
jummai ce tace "yaya kawo wankin nayi saboda hansai bazata ita ba" .
"oho can ta matse miki jummai nidai Naga kaya awanke dan me nace ta dawo d'aki na" .
wani uban wanki ne ta tulo jummai ta jin-jija kai tace azuciyan ta, ran nan inaji mudi yace bazai Mata wankin ba ,Amma da zalunci yarinya k'arama ace ita zatayi wan nan uban wanki, haka tayi wankin nan tayi ta shanya .
*Washegari*.
washegari malam ya dawo,sunyi murar dawowar sa yayi farin cikin ganin hansai da dare yana zaune suna hira ya fito da wani takalmi me kyau irin na roba me ado ya bawa hansai yace "ga tsarabar ki" nan gwamma tace "ina na mudi" kallonta yayi "haba gwamma ya kike haka ne? inaga mudi saurayi ne mai zan bashi in Shi bai bani ba? hansai kwa yarinya ce"
tabe baki tayi tace "ayi dai mu gani"
tunda malam ya dawo ta daina aiken hansai rafi sai de aikin gida duk ta fige ta rame ran nan malam ya shiga gidan yaga hansai na wanke kayan gwamma kwalla kiran gwamma yayi ta fito yace "yanzu don rashin imani har hansan nawa take da zata wanke manyan kayanki, ina mudi ai shi ya kamata yayi" gwamma tace "ita nayi niya haba! sai kace 'yar gwal ba dangin iya ba na baba".
malam yace d'a de ai na kowa ne hansai de 'ya tace ina k'aunar hansai har raina kamar yanda nake son mudi, don haka karki Kuma sata Aiki me wahala . k'walla kiran hansai yayi yace taje gun jummai ta zauna Ko taje waje tai wasa da tsahare.
Ahankali ta fita taje can waje ta zauna tana ..kubiyoni.
*by Queen meemi*
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣5❣
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
_*sadaukarwa ce ga Bashir usman family's*_
_sis Marwa Phart bb ,Anty maijidda ,Nazifa Ngd Ngd sosai da kaunar book nawa,San nan 'yan group Dina na QUEEN MEEMI FANS ina godia da kaunarku agareni sosai kuna nunan kauna nagode Nima ina sonku luv u_
*****
tana zauna tana kuka Muntari dake tawo wa Daga can ya ganota yazo kusa da ita yace "hansai meya sameki"? da sauri ta share hawayen daya zubo Mata Babu komi ta fad'a juyar Dakai yayi tabbas yasan da matsala can k'asan zuciyar sa yana tausayin hansai Ko acikin yara bata da kuzari ,"kina jina? kiyi hakr kinji yanzu ya makaranta?" ya tambayeta bata bashi amsa ba sai ma d'agowa da tayi ,yace "Ko bakya zuwa kema? kin zama su tsaharen?" da sauri tace "Aa ina zuwa ajina 4 a firamare Yawwa hansai ki dage Kinga Matan garin nan basu damu da zuwa ba, har mazan ma, ki dage kina zuwa ki zama gwania acikin su," tace "to" yace "San nan kullum kina zuwa gun sahura (kanwar sa) ina koya muku karatu," Dad'i ne ya kashe ta tace "to" mangwaron dake ledar hannun sa ,ya zaro ya bata ta amsa tana mai murmushi.
Muntari D'ane agurin mai garin ,garin mangalu a gidan su shine d'a na uku a ciki yayansa duk Mata ne sai maza kannen sa da Autar su mace,matashin saurayin k'auye ne D'an shekara goma sha takwas Allah yayo Shi da San karatu duk gidan su Shi kad'ai Ke zuwa, har ya kammala firamaren sa ,ya shiga secondary ta maza yana aji biyar ,duk k'auyen Ko acikin Samarin ya fisu ilmi ga kirki,tun ganin sa da hansai yake jin tausayin ta haka kawai ba don komi ba, hakan shine farkon alak'ar su da hansai.
Bayan kwana biyu a tsakani yau ma MLM ya fita gona gwamma ta aiketa rafi wajen k'arfe hud'u na yamma ta d'au botikin ta tafi ,da d'an nisa sosai haka taje zuwan ta rafin taga yara birjik.Daga gefe ta tsaya tana d'iban nata ruwan ,wata Daga cikin su tazo taja kan hansai "Ke waya baki izinin d'iba,? bayan Kinga ana fad'a" hansai tace "to ni meye ruwana daku" fitsararriyar yarinyar tace "to duk nan na Riga kowa zuwa Kuma ba wanda zai d'iba sai ni" ,hansai tace "tabdi" kande tace "hansai sahura fa yar gidan mai gari ce fa!".
hansai bata saurare su ba ta d'iba ta juya, jitai an jefar da botikin juyowarta, taga sahura na huci hansai zatayi magana sahura ta kamata da fad'a ,da yake sahura tafi hansai k'arfi ta jefar da ita a k'asa ,santsin k'asar gun taja ta tajita cikin rafi ,tinjim! kake ji k'arar fad'awar ta,Yaran gun duk suka saka ihu idanuwa sahura suka Rena fata,hansai kuwa sai ihu take duk tasha ruwa dai-dai lokacin Muntari ya taho yana zuwa yace "Ke sahura haryanzu aikenne? ga inna can na nemanki,"ganin suna kuka ya tambaya dije tace "sahura ce ta wulla hansai rafi" a kid'ime ya yi wajen ya ganta har ta daina motsi cikin ruwan ya shiga ya d'auko ta, ya fito da ita gefe yaran duk suka zagayeshi ya danna cikin hansai ruwa sai fitowa yake Amma duk da hakan bata farfad'o ba. haka ya d'auketa yaran suka bishi abaya duuuu.
malam dake zaune sai fad'a yake "bana ce adaina aiken hansai rafi ba,? haba gwamma mai sa bakyaji ?gwamma dake zaune ta had'e rai "haba mlm "wai duk yaran garin nan tafi su ne? da za'ace bazata ba",mlm yace "eh tafi su ,ace tun k'arfe hud'u har yanzu shida dai- dai Babu alamar ta" ,jummai tace "malam Nima hankalina bai bani lafiyaya ba" .
Sallama aka doka mlm ya amsa Muntari ya shigo da hansai a hannu jummai tace "la haula ,mai ya sameta Muntari ? yace "ai fad'a wai sukai a bakin rafin itada sahura, shine ta fad'a rafi" kuka jummai tasa ta k'ank'ame hansai, mlm yace "Muntari na gode sosai" bayan fitar sa ya dawo kan gwamma "Kinga ABINDA AKE GUDU (littafin batul mamman) ko, gashi kin gani dai Ko"! d'aki ya shinga ya fito da magani yasa a raunin hanun ta da k'afar nan yasa jummai ta D'an gasa jikin hansai ,haka dai sukayi ta treatment d'inta sai wajen k'arfe Tara ta farfad'o tana kuka yau a d'akin jummai ta kwana.
Washegari dak'yar ta taka, saboda yanda k'afarta Ke ciwo ,sai da aka gasata da ruwan zafi San nan ta samu sa'ida ,muntari ne ya shiga shida sahura da leda a hanun yayi ya jikin hansai, San nan ya umarci sahura data bawa hansai hak'r badon Taso ba, suka tafi.
yau 3 kwana kenan, kullum Muntari sayya zo duba hansai Kuma yazo ya jata da hira shak'uwa ce sosai ta shiga tsakanin su sosai bayan warkewar ta sai Muntari Ke zuwa yana biya Mata karatu irin su hadisi sira ,kawa'idi,alkurani,da tauhidi. (da yake da da yake D'an karami Dan shkear goma ankai Shi makarantar almajirai yayi shekara daya sai aka dawo dashi ya shiga boko Kuma daya dawon ya cigaba da d'aukan karatu gun malamin makarantar Allon su hansai).
haka ya fara koya Mata da amincewar mlm, ba haka gwamma taso ba, don yamma k'arfe 4 yake zuwa asoron gidan su hansan,yana da k'wak'walwa sosai haka ya Farai Mata harda na bokon, kullum Kuma sayya zo da kayan k'walam ya bata .Daga baya ma sai sahura tazo shima ya had'asu yana koyawa,haka dai rayuwar hansai ta kasance yau fari gobe baki,cikin wata safiyar laraba gwamma ta haihu ta samu mace tunda ta haihu bayan anyi suna yarinya taci suna khadija suna kiranta dije, sai ya za mana duk wani Aiki hansai akeyi wanda ma yafi k'arfin ta ga yawan dukanta da mudi keyi yayi tai Mata wasan banza sai de inta ganshi ta gudu d'akin jummai.
*BAYAN SHEKARA HUDU*
wani busa Ke tashi a tsakanin duwatsun dake wajen hansai Ke busa Shi tana murmushi taci irin kwalliyar su ta k'auye Masha Allah hansai ta K'ara girma kyanta ya dad'a fitowa duk da ban tab'a suffanta muku ita ba .
hansai 'yar farar yarinya ita ba irin gau d'in nan bace, ita Kuma ba za a kirata bak'a ba tsaka -tsaki ce'yar lawai-lawai bata da kib'a sosai sai de Allah ya horema ta kuturi(hips tun ma bata K'ara girma ba Ke nan ,shiisa jummai take bata hijab tasa domin tasan tana da baiwar da daukacin Mata Ke so,Kuma hakan shine ya kamace ta duk da yaran k'auyen kamar ta wasu basa yawo da mayafi.
Sam hansai in ka ganta bazaka ce zatayi k'arfi ba komai a sanyaye ta keyi, siriryar fuskarta wadda Allah ya wadata ta da Dan dogon hanci siriri da bakinta madaidaici sai gashin Ido da suke gazar -gazar dogwaye tamkar tasa eye lashes ,idan ka kalli jikinta duk gashi ne ajiki sai de bata dayawan gashi kai tana da de na fakin Amma gaban goshin ta cike yake da gashi a kwance luf-luf hansai Ke nan😉
Muntari dake saman bishiya yana murmushi Shi kad'ai ya d'ago da idon sa, "Anya hansai duk k'auyen nan A kwai me kyanki kuwa"? dariya tayi "haba dai ka dad'a bincika yace to ni dai masoyiya ta tafi kyau,tun bayan shekara d'aya kenan suka fara soyayya shida hansai wanda kowa ya sani agarin, kullum nan ne wajen hirar su cigaba tayi da busa usur d'in .D'an dogo wa tayi ta kalli saman bishiyar lokacin muntari ya juya, kallon Muntari tayi azuciyar ta tana sonsa, domin ya taimaketa arayuwa, ya Sanar da ita ilmi da yawa ya taimake ta sosai, magana yayi firgigit ta dawo Daga duniyar data tafi tare da jin kunya da gudu tayi hanyar gida .......
*By Queen meemi*
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: . . .
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣6❣
*JAN 2017*
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usaman family's_*
*ABUJA*
A fafare Zuby ta shigo da motar ta ta faka a tafkeken filin gidan su.
Ruby dake bayan motar ta fito a zafafe suna hararar juna kowacce d'auke da jaka sukai ainihin cikin gidan wanda Ke d'auke ta kafcecen falo, wanda Ke d'auke da K'ofar shiga part guda hud'u falon dake tsakiya wanda yake a circle ga manya manyan kujeru na leda masu D'an karan kyau, d'aukacin falon an kewaye Shi da labulaye masu kyau, ga wani site dake yamma da falon an k'awata gun tafkekeiyar plasma ce awajen tana ta aiki,ga wani kuku na k'alk'ale tile d'in falon.
Shigar su Zuby da Zuby kowacce tayi part nasu .Ko wacce ka shiga part d'in nasu wani falo ne shima again d'auke da kujeru lintsuma- lintsuma ga decoration me kyau a falon, sai plasma tv da dining area da kitchen San nan jerin d'akuna guda uku,kowanne part haka yake duk gidan,d'akin mama. Tashiga ( hajiya khadija) tana zaune bakin tamkeken gadon ta, wanda ya malaye Babban d'akin ta zauna kusa da ita ,Mama tace "zuby har kun dawo"? "eh wallahi Mama gashi yunwa nakeji, sai de Kuma raina a b'ace yake" tayi tsaki ,"wallahi Mama wataran saina fasa bakin Ruby" Mama tace "haba Ke Bakya rabo da fad'a, Ruby ai kin San bada fad'a, dama Sumy kika ce ne da saina yarda".
"Mama wai akan driving yarinyar nan zata min rashin kunya, dan taga itace babba,Allah ni banso dady ya had'ani mota da ita ba" ,dai-dai lokacin Sady ta shigo tana rawa mama tace "har abada dai Sady bakya rabo da shirme" sady tace "mama wallahi wak'ar ce da dad'i ,nan ta kalli Zuby tace "ya zuby mai naji kina cewa ne? inde zan cen mota ne wallahi mu had'u muje ga dady Kowa a sai mai dai -dai, ta yaya za ace kamar mu Kowa sai ace su biyu ne a mota d'aya. jiya fa haka sai da Sumy ta lalato motar ta, bayan na hau tace ni na lalata har sai da umma tayi min fad'a"
Zubi tayi tsaki "gaiskiya Ya Ruma ta huta ita kad'ai da motar ta" ,mama tace "to sai kuyi hakr, ai ruma dai yayar kuce dole abata girmanta". D'an fita zuby tayi ta tafi Babban falo ta zauna tana kallo Rabia ce ta fito Daga nata falon itama ta zauna, Zuby tace "Anty Rabia ina gajia" batai mamakin jin yadda Rabia ta gaisheta ba tamkar ba matar baban su ba, "lafiya tace" ,da dai- dai da d'ai-d'ai Matan gidan da 'ya'yan suka fito sukai birjik a falon, gidan Alhaji tanko kenan. .
Alhaji tanko Babban Dan siyaya ne, da yayi shura yana zaune a garin Abuja,yana zauna A maitama yana da kud'i na fitar hankali ,yana d'auke da muk'amin minister na kudi ,yanzu hakan yana da matan aure guda uku Hajia khadija itace matar sa ta farko ,tana da 'ya'ya da Shi Rumasa'u (Ruma) itace babba sai Zubaida (zuby) San nan Sadiya(sady). Wan nan sune na b'angaren ta San nan Hajiya Karima itace matar sa ta biyu, itama tana da 'ya'ya da Shi Rubayya(ruby) itace babba awajen ta sai sumayya (sumy) itace Ke binta wan nan sune iya 'ya 'yanta, sai Amaryar sa daya auro shekara 5 kenan tana da 'ya'ya da Shi khalili shine babba sai Mubarak, duk a gidan Ruma ce babba mai shekara 25, sai Ruby mai 23 San nan Zuby mai 22 sai sumy da sady sa'annine suna 20 sumy ta bawa sady wata biyu,sai khalil Dan 4 yrs San nan mubarak Dan 2 'yan gata ne sosai suna jin d'ad'in su San ransu ga gadara
*MANGALU*
Shigar Hansai gida yasa gwamma ta kwad'o mata murfn kwano a k'afa take ta dafe gun tana kuka gwamma tace "wallahi Hansai zamusa k'afar wando d'aya dake, kin gansame agari ba mai aurenki, duk sa aninin ki an aurar ,hatta ita tsaharen ankaita d'akinta bara Amma Ke. Kina nan shekara goma sha hud'u god'ai god'ia dake duk ba sa aninnki sai wanda kika girma,kullum sai aukin sa hijab tamkar matar liman,Ke ga malam ya tsaya miki wai sekin gama makarantar gaba da furamare ake cewa kome, to ayi Dai mu gani duk ran da aka fara saka ki A wak'a ai maji,ni b'acen da gani kar na ballaki ki,na k'arashe k'afar, je ki min wanki",tana d'ingishi ta tafi jummai ta fito lokacin itama Allah ya bata ciki ta kusa haihuwa tace "haba yaya hansai fa tana k'ok'ari miji Kuma ai lokaci ne Kuma ai D,an gidan mai gari ne Ke Santa, kin ga kuwa ai lokaci muke jira" gwamma tace "ayi Dai mu gani ba" dije ce ta shigo 'yar shekara hud'u gwamma ta kamo ta tace 'yar lele ina kika je ?tace "rafi kamo kifi" ,da sauri ta rufe bakin ta jin muryar malam dake k'ok'arin ya shigo ,tace "Ke yi shiru kin san malam baya so yi maza shige d'aki.
Hansai da kafar ta keta jini wajen da gwamma ta wulla Mata murfi,Daga gefe sai kuka take ga wunya dake d'ibar ta tace "mama gwamma zan d'auraye k'afata jini" tace "Dan k'aniyar ki sai da kikaga malam zaki ce haka to bazaki wanke ba gulmammiya kawai" jummai dake kusa da ita tace hansai zo na d'auraye miki sai kici abincin," da gudu gwamma ta taso "Ke karki tab'a ta domin Salam munafinci",Malam dake shigowa yace "Aa meye haka nan kukayi cirko -cirko.
*by Queen meemi*
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: . . . . .
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣7❣
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
*_sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_*
_happy birthday *MIEMIE BEE 👄*Wish u more years ahead ,GOD bless u🎉_
****
Sun tsaya cirko-cirko Malam ya k'araso yana tambaya da sauri gwamma tace "Aa magana muke kawai" hansai da kanta na sunkuye gwamma na harar ta MLM yace "Ke Kuma meye kike d'ingishi"? jummai tace "ai bigewa tayi" yanki ya d'auko ya bata ta d'aure gun yace ta koma gefe ta tafi tana d'ingishi,gwamma haushi tamkar ya kasheta ga wankin da bata k'arasa ba kenan, domin tasan malam bazai K'ara fita ba tun daya shigo, haka ta duk'ufa tana K'ara sawa.
Washegari da jummai ta fita asibitin cikin gari Malam ya fita gona sai hansai da gwamma kawai ganin,hansai da uniform gwamma tace "Ke bazafa ki je ba, kizo ki d'eban ruwa"hansai tace baba gwamma yunwa nake ji" "baza ki ciba ki fita kawai wallahi" haka ta aje jakar buhun dake hannun ta,ta d'au botikin ta fita sai sauri take har taje rafin, ba kowa agun sai wasu mitsi-mitsin yara acan gefe suna wanki d'iban ruwan tayi ta d'ago kenan ta ci karo da lawandi k'irjinta ya bada dam! tayi gefe, bin ta yayi yace "Ke hansai"! taki tsayawa sai sauri take fit! taji ya ja hijab d'inta nan ta tsaya yace "Ke hansai don baki da rabo ina maki magana Amma bakiji don ina sonki kikemin wulak'anci.
tace "kayi hkr inada masoyi" yace k'arya kike da kina da Shi bazaki zauna Ke kad'ai a gari ba duk kamar Ke an aurar sai kace mai bak'in jini, koda yake wa zai auri yar tsintuwa" da sauri ta juyo "kadaina jifana da munanan kalamai saboda da iyayena dariya".yasa dariya "tafi can ki farka tun dare bai miki ba" ,don ma zam taimakeki duk kyan nan naki ace ba mashinshini" tace "wallahi karya ne da iyayena malam da inna dariya yayi "kinsan dai ni abokin mudi ne, don haka ya gayan Kuma nasan bazai miki k'arya ba"
fuu ta juya ya zata tafi ya cafko ta nan tahau ihu yace "bari na kwashi rabona tunda kince baki sona" k'ok'arin cire Mata hijab yake ta k'walla ihu dama kowa yasan lawandi a k'auyen bashi da mutunci shammatar ta yayi ya fisge hijab d'in ,kuka take sosai "kayi hk'r na tuba" jinjina kai yayi ya turza k'afafuwan sa a k'asa "gaki da kyan jiki Amma kullum arufe" hannun sa ya kai jikinta yaji an mauje hannun, Muntari ne Ke huci ya nuna lawandi "ka shiga taitayinka iskancin ka bai tsaya ba har akan budurwata, to wallahi duk k'auyen nan za'a jimu Kanmu" mazga ya kaiwa lawandi take shima ya rama suka nan suka hau naushe -naushe da gudu hansai ta juya ta yi hanyar gida tana kuka
shigarta gidan ta tarar da jummai na tsintar shinkafa,lokacin bata Dad'e da dawo wa ba sai ta shige d'akin jummai tana kuka, cike da jimami jummai tajata tace "meya faru hansai"? nan ta fad'a Mata abinda lawandi yace da ita ,hankalin jummai ya tashi ta tuno lokacin da Malam Ke shaida Mata karta bari hansai ta San basu ne suka haifeta ba to waya gayama lawandi nan tayi ta lallashin hansai tace zata gayawa Malam .
Makarantar daba taje ba kenan ,gwamma ta shiga d'akin jummai tana masifa "bafa zan d'au asara ba dole a biyani botiki na" ,hansai tace "kiyi hk'r tsautsayi ne yasa ya fad'i ,fizgo ta tayi ta fito da ita waje ta hau jibga hansai na ihu jummai ta janye ta tana haki "wallahi karki Kuma dukanta gwamma don Kinga Banda lafiya shiiisa kwanan nan kike dukan ta" ,gwamma tace "jummai dani kike zancen wallahi sai kun gane kalata ta kwanan" nan tayi k'wafa ta fita. jummai ta kamo hansai suka shiga d'aki tana bata hkr.
Muntari da Lawandi kuwa sai da suka ji jiki San nan suka rabu lawandi yace saiya ga bayan Muntari inde akan hansai ne. Hatsaniya sosai sukayi har wajen mai gari ina waje d'aya ya Tara su lawandi da muntari na agaban maigari yace "kaga kai D'ana ne Muntari, kai Kuma lawandi kai Nike jagorantar ka meya had'a ku"? .
Lawandi ya furzar da huci yace "yarinyar dana keso wai ita yake so" maigari yace "wake nan"? Lawandi yace "Hansai ta gidan Malam". Maigari yace "ayyo na gane" nan ya juya gun Muntari yace "haba Muntari na san ka da hankali ya da fada akan yarinya"? Muntari yace "baba wallahi tin hansai na shekara goma muke tare, atambayi Malam ma da ita Hansai d'in.
nan maigari yace aje akirawo malam , yana gona akaje kiran sa ya tawo suka gaisa a soron gidan maigari d'in, yagan su nan maigari yace "Malam ya maganar 'yar wajen ka hansai"? cikin lawandi da Muntari wake Sonta malam yace "Allah ya gafarta Malam ai Muntari na sani tun da dad'ewa".
"To kai kaji lawandi cewar maigari sai kayi hkr, karna K'ara jin wani tashin tashina anan" .Lawandi dake tsuke baki ya tashi ya fita yana mai k'wafar kota Halin k'ak'a sayya samu Hansai
*ABUJA GIDAN ALHAJI TANKO*
Sady ce da Sumy sukayi shawarar zuwa gun dady .yana wangamemen falon sa mai d'auke da kayan K'awa ,Anty Rabia taci uwar kwalliya tana gefe tana had'a mai tea zuby ta zauna daga gefe haka Sumy ma suka gaidashi " dady dama muna da complain akan mota wallahi yakamata ace kowa nashi dai-dai aka sai mai ,sady ta cafe "eh wallahi dady kullum baama jin Dad'i da sake wa ga frnds" har dariya suke mana A school" dariya dady yayi "har kun manta, Amma kafin na sai muku wan nan motoicin ai da kowa tasa yake hawa yawan yawonku ne yasa na had'a ku mutum 2 a daya".
Sumy da alamar zaak'uwa tace "dady pls wallah zamu gyara ,kamar mu big girls a School Ace muna had'akar motor" Anty rabi ta kalle su lalle su Sady sai na ga hakan yafi dacewa" Sumy tace ni fa bansan sa ido don dai ba su khalil aka ce bane Shi isa mutum zai sako eyes" tsawa dady ya daka musu Dan baisan atab'o mai rabi saboda sonda yake Mata yace "inde rashin kunya zakuyi to ba wacce za a canjawa" Sady tace sorry Anty tab'e baki Rabia tayi ta fice nan suka bashi hkr yayi musu alk'awarin kowa d'ai- d'ai sabbi .
da gudu suka fice direct public room d'insu dake Babban falon gidan ,inda nan suke zama da rana ,da rawar shoki Sady ta shiga Ruma da Ruby suna Aiki kan computer Zuby na checking phone d'inta, Sumy tace "yau sharr muke dady yayi alk'awarin new car kowa dai-dai take kowacce ta how murna.
Zuby tace "wallahi saina rainawa su ramla hankali inde nayi sabuwar mota don aranar da dadyn ta ya bata new car har wani d'agan head take" "Allah yasa masu zafi zai bamu" inji Sady, Sumy tace "ai uploadin zan yi a Instr su gani na basu surprise" tsaki Ruma tayi tace "ku yaran nan abinda ya dame ku kenan ko"? Ruby tace "barsu 3 month fa da canjamana mota Amma sun koma don tsabar k'arya" dariya suka sa dukan su.
*by Queen MEEM*
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣8❣
*_Sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_*
*®NWA*
*Queenmeemi.WordPress.com*
*******
Misalin k'arfe goma na safe.Hansai na gefe a zaune tana dafe da cikinta dake k'ugi kallon d'akin jummai tayi taganshi da kwad'o don tasan ta tafi Asibiti.
gwamma ce Ke can gefe tana wak'e -wak'e sallama akayi delu ce Daga bakin k'ofa tace "gafaranku dai" .Gwamma ta washe hak'ora "dele ce yau agari!.Gaskiya kinyi nisan kiwo",delu tace "wallahi sai jiya na dawo daga D'an lasan," zama tayi kan tabarmar suna hira ,d'umamen tuwo ne sai tururi yake ta Matso Mata dashi. kuka Hansai tasa,gwamma ta juyo tace "au barin aikin kikaii"? sunkwi dakai tayi,nan suka cigaba da cin d'umamen da ita da k'awarta delu suna ci suna shewa hansai ta tashi tace "mama gwamma cikina murd'awa yake yunwa nakeji".
Delu tace "tab lalle 'yar nan kin samu sake ,gwamma ai Naga saka cinki " "to ya zanyi bayan malam shike tsaya Mata" tulun wanke-wanken ta nuna Mata "jeki wanke min banza gansama mai bak'in jini" kuka tasa "au bazakiyi sauri ba! ,Salan malam ya dawo ya hau fad'a" cigaba da shewar su sukayi.
haka ta hau wanke wanken ,cikinta na hautsina sai Misalin12 ta gama lokacin ta gama galabaita ,San nan ta bata ragowar tuwon nasu. Delu tace "wai ni har yanzu ba Aga iyayen ta bane"?,gwamma ta tab'e baki gata nan, waya sani ma ko bata da iyayen". Delu tace "kede ki tashi tsaye don yanda Naga take taken sa sayya iya bata gado tun bai mutu ba, ai kina ban mamaki gwamma,duk kin sakwarkwace".
Loma biyu hansai tayi duk tana jiyo su.Amai ne ya biyo baya haka taita kwarara amai gwamma tazo ta tsaya kanta "munafuka kawai ,kima tsiyayar da kayan hanjinki, ni bai shallen ba,shaidaniya ai wallahi ko zan yawo tsirara sai kin bar gidan nan, har akanki malam bai damu da dije ba,da mudi"dundu mai rai tayi Mata hansai ta durk'ushe.Delu tazo zata fita tace "gwamma sai na jiki".
Wajen azahar jummai ta dawo.Hansai na gefen d'akinta a kwance tana kuka tana ganin ta ,ta rungume ta tace "inna ku gayan so biyu Ke nan Ana cemun Banda iyaye. don Allah ku sanar dani ,kuka ne ya kubcewa jummai ta bud'e d'akinta suka shiga .
Zazzabi ne ya rufeta ta kwanta, sai bacci sai wajen la 'asar ta tashi tayi sallah ta fito tsakar gidan, taga Malam na Jan carbi da alama Sallah ya idar, da kuka taje ta sameshi "baba don Allah wai dagaske ba kune iyayena ba? kuka take saosai, jummai ta fito "Malam na rasa Inda hansai taji" ,hansai tace "mama gwamma ce Kuma ba yanzu ba, tun da dadewa,lawandi ma sai daya gayan,don Allah ku gayan ko na samu saida" ..Malam da idon sa yayi jajawur alamar bacin rai ya d'ago idon sa cike da tausayi ya kalli hansai,"tabbas bamu ne iyayen ki ba" tana zaune ta kwanta,nan ya cigaba bomb shine Sanadin rabuwar ki da iyenki "nan ya labar ta Mata duk abinda ya faru, luuu hansai ta fad'i alamar ta suma.
Nan suka yayyaafa Mata ruwa, ta farfad'o tana kuka ta rungume jummai tace "baba har Ababa kaine babana Gaskiya samun irinku sai an tona, baba ka nunan k'auna kaida inna insha Allahu zan cigaba da yi maku biyayya ,Wan nan rayuwar danayi daku itace dama wadda Allah ya shirya min,nikam banyi maraici ba. Amma tabbas Nagd wa Allah daya wad'o dani cikin ku nagode inna da baba" cike da tausayi baba yace "hansai Allah yayi miki Albarka "jummai ce taja ta suka tafi dakin ta.
fakam- fakam gwamma ta shigo gidan malam ya dakatar da ita,yace "ki koma Inda kika fito gwamma tunda kin zamo mai karya Alkawari ,kin b'atan rai kije sai na neme ki,".Salati ta hau "yanzu akan yar tsintuwa shine zaka ce naje gida to ai shike nan zan dawo ai",nan ta d'aga murya" jummai wallahi kin tab'o gwamma sai na yi miki rashin mutunci,nasan Ke kika had'a gurmi".
*BAYAN WATA UKU*
Bayan wata 3 dangin gidan su Muntari suka zo aka tsaida auren Muntari da hansai zo kuga murna gun hansai da muntarin duk tsiya hankalinta ya kwanta dalilin gwamma bata gidan. kuma gashi ta cigaba da zuwa makarantar ta,yanzu tana aji biyu na secondary dake cikin garin bunkure ,acan take zuwa ta dawo duk nisan ga muntari na k'arfafa Mata gwiwa.
kwatsama cikin daren ranar juma'a jummai ta haihu ta samu d'a namji zo kuga murna gun hansai ranar suna aka samai suna Abdullahi ,suna kiran sa d'an jummaii,lokaci yana ta tafiya. Har jummai tayi arbarin hansai Ke Kula dashi tana jin k'aunar sa.
Washegarin Arba'in d'in jummai sai ga gwamma ta dawo inda da k'yar da sid'in goshi malam ya maido ta. Ganin yanda hansai tayi kyau abinta ya bak'anta ran gwamma, dama taji labarin auren su da Muntari nan ko ta d'au damarar yak'i da hakan muje zuwa.
*BAYAN KWANA 2*
*da yamma*
Tafiya hansai keyi tana sauri zata gidan sahura k'anwar Muntari ,lawandi ta gani agaban ta ,da sauri ta kauce lawandi yace "ki tsaya mana!, da gudu ta arta ya bita Allah ya ci da ita taga wasu mutane akan jakai take lawandi yayi baya hamdala tayi ta tafi.
*k'arfe goman safe*
washegari mudi na zauna a d'akin gwamma se yau ya ya shigo,satin sa d'aya bai lek'o suba ,gwamma tace "ai ni yanzu burina wan nan yarinyar tabar gidan nan",mudi yace "Yawwa ni akwai wani abokina lawandi yana Santa,kwanaki ai har fad'a sukai da muntarin" ai da hankali na bazan bari ta auri muntari ba,haka kawai saboda banso ta samu rayuwa mai kyau, kace gobe lawandi yazo" mudi yace "ba matsala".
da yamma hansai na soro itada munatari yana Mata K'arin karatu gwamma ta fito da botiki ,cike da ruwa ta kwarawa Muntari tace "kai kam anyi Mara rabo, shikam dayake tsaye jiki na d'igar ruwa ,hansai kuma na gefe jikinta na rawa ta kalleta, tace "wuce muje 'yar banza" nan ta bita da dundu ,ta dawo kan Muntari tace "to kai yanzu karasa wa zaka aura sai 'yar tsintuwa 'yar daba asan iyayenta ba"?.
"Amma ka bani mamaki ,kasan dalilin dayasa tak'i auruwa kuwa? to cikin shege tayo aka rufe a bun" idanuwan Muntari kam sunyi ja yace "haba mama gwamma yada jifanta da irin kalaman nan Sam ban yarda ba" "to baka yar daba kenan? to wallahi da gaske nake" kansa ne yaji ya fara juyawa ya dafe shi yana waswasi.
*by Queenmeemi*
*Queenmeemi.WordPress.com*
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: . . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣9❣
*JAN 2016*
*Queenmeemi.WordPress.com*
*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_*
Nagode da bibiya @* *ummu yusra*, *Amiener* *Ngileruma ,Maryam* *Shettima,Ummie* *Maryama Niger*
*khadija lagos &Ashnur tnks* ❤
Muntari baice komai ba sai ma waje daya yi gwamma
"tace tafi can wallahi sai na rabaku".
komawa ciki tayi tahau wak'e- wak'e .
Mudi kam Bayan ya gayawa lawandi sak'on gwamma baiyi wata -wata ba sai gashi da sassafe .Bayan malam yafita yazo gwamma ta fito soro suka gaisa tace wa lawandi "ka ce kana son Hansai ko"? yace "eh to karka samu damuwa Amma kafin nan sai na saka ka Aiki. kuma kayi a k'arshe zaka ga yanda komai zai tafi dai- dai lawandi yace "ai ko ba so tsakani zan iyayi miki" nan tace "so nake ka d'auke Hansai kaje can wani wajen ka b'oye ta,kana jina"? murmushi yayi lallai fad'uwa tazo dai de da zama, ya d'ago yace "to yanzu yaushe za ai,? tace "ko yau ma, kaide wajen uku kabi hanyar rafi zan ai keta yo jida".
Sallama sukayi ya tafi Misalin k'arfe uku gwamma tace wa hansai tazo tana zaune a bakin d,akin jummai ,goye da D'an jummai, gwamma tace "Ke jeki sauke wan nan bushashen yaron," Hansai taje ta sauke Shi ta Koma wani k'aton buhu ta bata, "gashi so nake kije ki yo mini jida a gonar Malam kalla".Jummai na d'aki ta fito "haba gwamma kinsan wajen da nisa, kuma jida har me zata samo Bayan duk an gama", gwamma tace "bari kiji ko jiya saida lantana 'yar wajen larai taje yo kalen Dan baki ga gyad'ar data samo ba ,don haka dole Hansai tayo mini jida ,wallahi ko na kileta". Jummai tace bafa "zata je ba, gwamma tace "dani dake aga wa zai bi wani" wawuro ice tayi tabi Hansai aguje tayi waje da buhu a hannu .
Haka Hansai ta santali hanya tiryan- tiryan, tana tafiya hawaye na bin kuncin ta,sai wajen hud'u da rabi taje ta hau kale Babu komi da k'yar ta samo kad'an tayi kwana tana sauri saboda gajiyar da tai ,ji tayi kawai an sure ta K'ara ta k'walla buhun ya fad'i ,wani dutse ta d'auka ta kwad'awa lawandi, tace "Amma kai kayi asara, ka rabu dani nace," binta yayi ta hau gudu ita da zatai hanyar rafi sai tayi wata hanyar da k'yar takai wani gida ta tsaya tana haki,ji tayi an rufe bakin ta' an d'aga ta sama sai ihu take Amma baya fitowa ,Mari lawandi ya faska Mata sai data ga wuta d'if ta some nan lawandi ya tafi da ita.
K'arfe bakwai dai de malam da jummai ne tsaye suna neman hansai, ba inda ba a duba ba. Amma ba alamar ta .Jummai kam kuka take hankalin malam idan yayi dubu ya tashi ,komawa gida yayi yace da gwamma "mai yasa ne kika aiketa kale? haba sai kace bamu da abin sawa abaka" malam sai hak'uri, Nima tun d'azu hankalina atashe yake" .
Wajen takwas na dare sai ga Muntari ya zo zance ya gun hansai da wata leda a hannun sa, zuwan sa k'ofar gidan, ya tarar da malam a tsaye nan suka gaisa malam yace "D'ana Muntari ko kaga Hansai"? a fargaba ya d'ago "Aa malam miya same ta", malam yace "ai tun k'arfe 3 ta fita wai kale har yanzu shiru ba labari" da jimami Muntari yake magana a gigice, "ina zuwa" malam ya sanar da Muntari ya shiga ciki shiga ciki .
gwamma dake lab'e ta fita soron tace "amma kwa Muntarii anyi sahorami, yanzu ba kaji abinda na gaya ma jiya ba ko? ka d'auka k'arya ne ko"? Muntari yace "Ni ai ko ma mene Hansai tayi koda ta da wani batare da aure ba ita nakeso kuma zan aura kuma haka nake santa ko da duk kowa zai ce baya sonta".Gwamma tace "ka rabu da hansai Muntar", "mama gwamma hansai fa kamar 'yar ki take kina yi Mata zaton Alheri"
"lalle Muntari ka fitsare ko girmana baka duba ba ,kake gayan wanga magana ,dani kake zancen dole ka rabu da ita" muntari da ya share zufa duk sanyin da ake alokacin Amma gumi yake saboda zafin da gwamma ta had'a mai yace*_"rabuwa da Hansai ,tabbas zai iya zame min matsala,haka Sanadin Rabuwa da ita zai jefami a mawuyacin hali wallahi Ita nake k'auna _* gwamma tace "tab! anya kana da kai, lalle dole ne na Ke gidanku" .da sauri ta fice don jin da yayi kansa na juyawa. Ledar da ya shigo da ita ,ta d'auka ta duba taga soyayyan kifi, "hmm da wan nan cimar zan k'yale Hansai ta aure ka ,inaji ina gani Hansai ta auri d'an maigari ta shiga daula ,ai dole na tashi tsaye ,ai idan yasan wata bai san wata ba.Juyawa gidan tayi ta shiga d'akin ta suka ci ita da dije.
. haka Muntari yayi ta yawo baiga inda take ba ba inda baije ba, har wajen 9 na dare yana yawon nema harda k'walla don yanda yake jin Hansai a ransa.
****** Al amarin hansai kuwa, bayan da lawandi ya sace ta bai zame ko ina ba sai wani gida wanda ba kowa a ciki sai wata tsohuwa ,aje ta yayi a d'akin tsohuwar ya d'ago yace "kaka ga ajiyata nan" dafe kirji tayi!" kai D'an nan yau ma jafa'in ka jawo? har ka fara satar bil adama". Lawandi yace "kede kaka ba ruwanki ki sa Ido kawai" fit ya fice daga gidan.
Bayan fitar sa ,Hansai ta farfad'o ta hau kalle- kalle kuka ta kuma sawa, "na shiga uku wayyo baba, wayyo inna" ,tsohuwa tace "yarinya mai ya had'aki da lawandi"? Hanai ta kalleta "wallahi iya ,ya nace yana sona Alhalin an saka min rana da wani ,in dai zan fita sayya biyo ni, yau ma tsautsayi yasa naje jida ,shine ya d'auko ni don Allah kaka ki taimakan".
tsohuwa tace karki samu inaga Allahu gobe zan bud'e ki tafi,ina kike" ta tambaye ta ,Hansai tace a mangalu"tsohuwa tace "ai bamu da nisa ma" dadi taji tsohuwa tace ta tashi tayi Alwala haka tayi ta dawo ta zauna.Tai tsuru-tsuru tana jimami.
tsohuwa tace "ai lawandi kwai tak'adari wallahi tunb yana shekara goma nake fama, jika nane ni na haifi baban sa,babar sa tazo haihuwa ta mutu baban sa kuma ciwo yayi ya rasu, sai rikonsa ya dawo guna neman fada doke doke ba irin wanda bai ba daya fara girma ya tsiri dauke -dauke, har ya girma bai nutsu ba sai ma janyo fada wanda ya sha kwana gun masu kayan sarki('yan sanda) har yanzu sai adda'a domin kullum sayya yi wani abun rashin da'a,tun da nace ya samo Mata nai mai aure kowa nutsu ,shine ya satoki ko? kiyi hak'uri gobe- goben nan, zan saki a hanya ki Koma mangalu" Hansai tace "iya dama cikin gari ya kawo ni"? iya tace "ai nan cikin garin bunkure ne".kuka hansai tasa kaka na bata hak'uri.
*By Queen meemi*
.
[12:02am, 15/01/2017] +234 903 281 0350: . . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣10❣
*JAN 2017*
*Queenmeemi.wordpress.com*
*dedicated this page to sis marwa &sis Ameener*
_jinjina gareku, *Anty maijdda* *Anty sis,Anty sadyjegal* *LubieD*, *Hapsert NM, Kursiyya* *yusha'u ,Aneesaty*, *respectable* *& Princess Amra*da sauran wanda ban fad'o ba duk kuna raina_
Washegari da sassafe sai ga lawandi nan tunda dama ba kwana yake a gidan ba ,kokon da kaka take sha ya d'auke ya d'ad'd'aka. Hansai kuwa rakub'ewa tayi a gefe ya kalleta .Hansai gani gaki sai yanda nayi dake zaki raina kanki keda ba gata gareki ba ,kaka tace" kai lawandi tsiyar ka da rashin da'arka ya kaini bango wallahi zan sab'a maka" lawandi yace "to kaka bake kika ce na samo aure ba, don haka ga Mata na samu" harara Hansai ta galla mai tashi yayi ya fita.ya rufe k'o far ta baya .
Hansai tace "kaka yanzu zan tafi "kaka tace "bakya ganin ya rufe", kuka tasaka ta tashi ta fita tsakar gidan ta ta zaune shikwa Lawandi yana waje ya kasa ya tsare don yasan dole hansai zata nemi guduwa.
Acan gida kuwa hankulan malam da jummai atashe yake ganin har safiya ba labariin Hansai yanzu ma da suke zaune jummai kamar Mara lafiya tace "yanzu shike nan 'yar da na k'wallafa rai akanta ta bata"? .Malam yace "ki daina kuka ai na sanar da Maigari yanzu anjima za naje ,kuma ina addua sabida tamkar amana ce Allah ya bani" gwamma dake d'aki tayi tsaki "kwayi kwa gama ai, kunyi bankwana da hansai ".
Wajen k'arfe 11 Malam ya fita gona, sai da ya fara biyawa ta gidan Maigari ya kumai mai tini kan maganar San nan ya suce gonar.
Al a' amarin Muntari kuwa yana d'aki yak'i fita sai matsaar k'walla yake, Maman sa ladidi sai karakaina take don ya karya don tun jiya takula bashida kuzari da abinci jiyan ma baici ba,da k'yar yaci ya fita nai man hansai har gun su da suka Saba zama yaje bai ganta ba ya Dade a gun San nan ya kuma nausa neman ta.
Hansai kam durfafar k'ofar fita tayi ta sakace ganin ba lawandi agun ta kalli gabas da arewa nan tayi gabas tafara tafiya kenan ta k'unshe hannunta a cikin hajib sai ga lawandi yasha gaban, ta yace "Ke hansai koma"! tace bazan Koma ba", nan yace ai kinshigo kenan dole ki soni, kuma sati mai zuwa za a d'aura aure".Wallahi bana sonka muntari nake so shine jarimina" hannu yakai zai damk'o ta tace "karka k'ara tab'ani! domin Naga kai baka San dokar musulunci ba",wata siririyar wuk'a ya d'auko a gefen wandon sa ya nuna ta da ita ki Koma ,konai miki kwale a fuska ,duk kyan nannaki ya b'aci" hawaye ta fara ganin ya nufota ta juwa ta shige gidan, kaka na zaune tace "Ahh! ya kika dawo?...Hansai tace "ya k'i bari na na wuce har wuk'a ya nunan" kaka tace "barshi sai na nuna mai b'acin raina".
*Bayan kwana 5*
Maigari ankai report guron 'yan sanda dake cikin garin bunkure ,saboda ganin yau kwanan hansai shida ba labari,jummai har zazzab'i tayi saboda sabo akace Turken wawa Shi kansa Malam d'in daure wa yake haka akaita nemanta.
*RANA DUBU*
_*(Hausawa na cewa rana dubu ta b'arowo rana d'aya ta mai kaya)*_ yau lawandi wajen 12 ya fita don zuwa wani waje kaka tana sane ta kirawo hansai tace "yauwa hansai ga naira D'ari ki tafi kiyi sauri kan ya dawo ko ya rufe k'ofar ki jijjiga ta " godia tayiwa kaka ta fita.Allah da ikon sa sai gashi k'ofar abud'e saboda ya sakankance hansai ba zata gudu ba, da sauri Hansai ta fita tana kalle- kalle gudu ta hauhi,ganin wasu mutane taje gunsu tace "don Allah wane ina zanyi ya kaini titi "nan suka nuna Mata wata hanya haka ta yi ta gudu har taje , nan tana tsaye kan titin taga wucewar lawandi ai sai ta b'oye don kar ya ganta, wata mota ce Ke shiga mangalu duk sati taji Ana ambatar mangalu! mangalu! ai da gudu ta shiga akaja,cikin ikon Allah wajen k'arfe 1, sai ga hansai a mangalu godia tayiwa Allah,ta yi hanyar gidansu.
Gwamma na tankade tana wakar _ahayye yaraye_ hansai tayi sallama tashi gwamma tayi tana tafa hannu "Ke 'yar nan sai yau kika dawo daga yawon tambad'ar? oh ni! gwamma duk k'auyen nan ace Ke kad'ai ce ba aure duk sai k'annen ki ai dole ki yawo".Jummai ce ta fito tazo ta kama hansai tace "Hansai ina kika shiga"? kuka ta saka Jummai ta jata d'aki.
gwamma kuwa mamaki tayi yadda akai hansai ta tsallake rijiya da baya, Malam ne ya shigo da sauri Jummai ta fito tace Malam sannu da zuwa, ga Hansai fa"! da sauri ya bita d'akin Hansai na zaune na kuka yace Hansai ina kika shiga"? eh ransa a b'ace yake maganar tace "baba lawandi ne ya sace ni ya kaini cikin garin bunkure gidan kakar sa, wai sayya aureni" tafa hannu Jummai tayi tace "baide miki komai ba ko" ?tace "eh" ran Malam abace ya fita A fusacee bai zarce ko ina ba, sai gidan maigari suna soro a zaune yaje ya nemi izini akayi mai Iso,nan ya sanar da dawowar hansai da sacewar da lawandi yayi mata, ran maigari ya b'aci yace tabbs sai na b'atawa lawandi bazai rikitan gari ba,yace dole 'yan sandan za a gayawa". Haka kuwa akai .Washegari aka sanar musu dama sosai suke da case da lawandi nan suka hau neman sa.
Zo kuga yadda gwamma ta tashi hankalinta domin lokacin da malam ya Koma yana ta fad'a agabanta yake maganar an sanar da 'yan sanda nan ta shiga rud'ani ta San dole asirin ta zai tonu,haka taita kaikawo tana habaice -habaice "haba ko dije a ka d'auke ai Malam bai ci kai wan nan gigicewar ba, Amma kan 'yar tsintuwa duk ka d'imauce" ,haka taita surutan ta.
Cikin sa'a aka kamo Lawandi sai da suka zo gun maigari .Maigari yace "kai yanzu lawandi abinda kayi yadace ne? haba! ai nayi maku tsakani da Hansai ko to kuma har da d'auketa ko"? ,lawandi ya tsuke baki ranka ya Dad'e nasan ina son Hansai, Amma banyi niyar saceta ba, sani akai".Maigari yace "waye ya saka? yace "gwamma matar malam". Malam dake durk'ushe ya d'ago tabbas matar nan ta rainani , duk sai yaji kunya ta kamashi. Maigari yace "ai sai Malam kai ne zaka hukun ta ta, kai kuma lawandi sai atafi da kai". haka kuwa akai masu kayan sarki suka tafi da lawandi .
Afusace malam ya shiga gidan, gwamma ya k'wallawa kira saida hanjin cikin ta suka bada k'uuuuu !ta fito "Malam gani tace "yada wan nan kira haka"? yace "kin tozarta ni, kin badani acikin wanda Ke ganin mutuncina, gwamma kin addabeni kije ni a yanzu bazan ce ki je gida bako wani Abu kawai na datse alak'a ta dake ba ruwanki da hansai ko jummai, nima karki shiga tawa ki zauna agidan nan Amma saina waiwayeki ,abinci kawai na baki izinin ci shima sammaki zan" kuka tasa "yanzu Malam duk sosyyyar dake tsakanina dakai akan hansai kake min haka"? ,afusace ya juyo yace "Ke ko akuya Kikaiwa haka saina hukunta ki Ballan tana Mutum" dije ta fito tana zumbure baki jin anawa gwamma fad'! duk gwamma tana koya Mata halayen ta Malam yace "Ke dije je ki d'auro d'ankwali zunb'uro baki tayi tak'i tafiya, malam yace "kinga halayenki ko! gwamma gashi kin koyawa yarinya,Allah ya shirya" .gwamma sai fatar hanci take tana kuka ,Jan dijen tayi suka shige d'aki....
Muntari kuwa dad'i ne ya kashe Shi ganin hansai ta dawo ,cikin gari ya shiga ya sayowa hansai hijab guda 2 yazo gidan su hansai ta fito sunkuye da kai harda d'an murmushin ta na ganin muntari zama sukayi yayi ta tambayar ta tana bashi amsa duk yanayin data shiga a sacewar da lawandi yayi Mata.Muntari yace "hansai tabbas kin fita da yaran kauyen nan shiisa nake sonki kina da nutsuwa dad'in dad'awa kullum jikin ki arufe sab'anin sauran yaran dake yawo gandak'ai.Murmushi tayi "innace tace na dunga sawa, ai yanzu ni na sabama" mik'a Mata leda yayi to ga wasu a K'ara sakawa" haka sukai ta hira yanai Mata K'arin karatu wan nan Ke nan..kubiyoni
*By Queen meemi👑*
0 comments:
Post a Comment