*P*....1⃣↪2⃣
Kwance take atakure a wata yagal galalliyar taburma wanda duk ta tattare dan tsufa ko kyawun gani babu dakin ƙasa ne take kwance aciki wanda duk ba'rin dakin ƙasar ya zube agefe kuwa tumaki ne suke kwance atare
Yanda ta kwanta da ka ganta kasan sanyi takeji domin kuwa lkcn sanyi ne babu abin rufa dogon rigan jikinta fadin yanda yake bata lkc
Tana cikin baccin wahalan takeyi ne taji sauƙan bokitin ruwan sanyi ajikinta afirgice ta tashi tana raba idonuwanta manya dasu farare tass masu kyawun kallo
Duka duka bazata wuce 14years ba
Batayi auni ba taji sauƙan mari da sauri ta dafe wajan gami da sakin kukan wahala ta durqusa ƙasa
Dan Allah *YADIKO* kiyi hakuri me zan miki
Yadiko tace eh lallai *SHUHADA* kin samu guri harda kwanciya bacci ai baki da sauran wata hutu
maza kitashi ki ɗauki tulu kije rafi ki dibo ruwa kina dawowa ki share gidan nan tas ki ɗaura sanwa kafin mu farka a bacci nida Shalele ta da kuma ɗana idan ba haka ba wallahi wallahi wallahi kinji na miki rantsuwa sau uku ko to na lahira ma saiya fiki jin dadi shegiya karuwan yarinya kawai
Yadiko ta koma dakin su tabar shuhada durqushe tana kuka mai cin rai
Yanzu a wannan tsohon dare zata fita diban ruwa rafi akalla yanzu karfe uku na dare gashi ƴan ƙauyen su da lalata yan mata barinma ita da suke kawo mata hari
Yadiko ta leko tace wlh shuhada idan baki tashi kinfita ba idan kika bari na sake fitowa sai naci ubanki agidan nan na babballaki naga mai ceton ki duk faɗin kauyen nan
Da sauri shuhada ta tashi ta dauki tulu tafita tayi hanyar rafi tana kuka tana adduan neman tsari bakajin komai kafa duk ya ɗauke ƙauyen tsif kowa yana cikin gidan sa yana bacci domin ance dare mahutan bawa
Haka shuhada taci gaba da tafiya cikin tsoro tana addua Allah ya kareta sannan Allah yakawo mata karshen wannan baƙar azaban da take sha awajan yadiko da ƴaƴan yadiko
Da haka harta isa rafin ta dibo ruwan kafin tadawo an kira sallan assalatu
Tulun ta ajiye ta hau sharan gidan tanayi tana addua domin kuwa shuhada hafizan Al'qur'ani ce tayi sauƙarta shekara uku da suka wuce tun tana da 11years kenan
Bayan ta gama sharan ne ta fita neman icce da ƙirare tazo ta ajiye kafin nan har lkcn sallar asuba tayi dan anshiga masallaci alwala tayi ta koma ba'rin dakin su ita da awaki ta share tukunna ta tada sallah tayi nafilolinta da farillah sannan ta ɗaura da addu'o'inta dan kullum bata rabuwa dasu abakinta da kuma zuciyarta
Hura hutan tayi ta ɗaura ɗumamen tuwon dawan datayi jiya wanda ko rabin loma ba abata taci ba dan kwanonta daya ne agidan kullum
Ita zatayi girki amma baza abata taci ba
Sai wanda ya bushe sai a haɗa mata da ƙanzo ace taci idan kuma taci to ba ita ba sake cin wani abun sai washe gari wani lkcn ma haka zata wuni ta kwana bataci ba
Saidai idan Allah ya taimake ta taje makaranta sai aminiyarta yar gidan mai gari ta kawo mata abinci taci
haka zata zauna taci uban aiki sannan ta wuni da yunwa ko kuma ta kwana da yunwa
Bayan ta gama tumamen ta juye musu a langa suna can suna baccin asara babu wanda yafito balle yayi sallah
Basu tashi ba kuwa saida rana tafito gal asaman kwano tukunna suka fito suna wangale baki suna hamma babu ko rufe baki
Shuhada shirin zuwa makaranta tayi uniform dinta duk sun koɗe sun sha ruwa ga uban pachi ajiki
Dama jiran su takeyi su tashi zataje makaranta domin kuwa bata isa taje batare da sun tashi ba idan tadawo jikinta ne zaiyi tsami
Durqusawa shuhada tayi tace yadiko ina kwana
Mtsww munafukar banza lpy
Shuhada ta juya ta kalli *Sale* wanda yafito yanzu shima yana wangale baki
Yaya sale ina kwana
Harara ya aika mata dashi yace da ban kwana ba zaki ganni shegiya mai kama da aljana
Ya ɗauki buta ya shiga kewaye
Yadiko tace dan ubanki bakiga shalele bane da bazaki gaisheta ba ?
Shuhada ta kalleta tace *NURATU* ina kwana
Nuratu tace iya ki gani fa atsaye take gaisheni kuma ku tacemin anty saboda raini ta raina ni
Shuhada ta girme nuratu da shekara daya da rabi
Shuhada batayi auni ba taji sauƙan rankwashi akanta da sauri ta duqa sale yace idan bazaki gyaru ba ki dinga gaisheta a tsugune sannan ki kirata da anty ba wlh kin dinga shan ran kwashe awaje na ya faɗa yana shigewa dakinsa
Yadiko tace dallah ɗauko mana abin karin kumallon mu shuhada ta tashi da sauri ta ɗauko takawo musu tace yadiko dan Allah ki taimaka min da ko loma daya ne naje makaranta wlh yunwa nakeji
Ahasale yadiko ta miqe tayi kan shuhada
Da gudu shuhada ta fita tabar gidan tana kuka
Yadiko tace dama kin tsaya kiga loma daya yau kije wajan koyan iskancin naku da kumburaren fuska shegiya karuwa kawai
A hanya shuhada tana tafiya tana hawaye ga yunwa tanaji sosae har wani zazzabi takeji na shirin kamata
######
*zan dakata anan saina ga yadda kuka karbi littafin daga nan muci gaba da gashi*
*ta hanyar comments dinku da dogon sharhin ku zan fahimce book din yasamu karbuwa ngd mah ppls*🥰
*P*......3⃣↪4⃣
Da haka har taje makarantan tana kuka wani malamin su ne yaganta tana kuka ya kira ta shuhada zo nan
Tana zuwa yace bana ce kice wa baban ki ya canza miki uniform ba ?
Sun kuyar da kai ƙasa tayi domin shuhada akwai kunya da biyayya tace malam bani da mahaifi Allah ya masa rasuwa
Mamar ki fa ?
Malam mahaifiyata itama Allah ya mata rasuwa bani da mama bani da baba
To baki da yaya ne ?
Malam ina dashi amma ko nace ya siyamin bazai siyamin ba
Malam rabiu ya girgiza kai yace Allah ya kyauta duk makarantan nan kinfisu ilmi duk da a ƙananun shekarun ki kina ss3 amma kuma uniform dinki
Tunna primary skull ga uniform din da rashin kyan gani gashi kullum sai kinyi latti abinda yasa ma ba a dukan ki latti sbd kokarin ki da ilmin ki da biyayyar ki
Nan malam rabiu ya dinga mita dan shi bai jima da zuwa makarantan ba dan haka bai san halin da shuhada take ciki ba nan dae ya gama faɗar sa shuhada ta duqa kasa tace malam kayi hakuri ba laifi na bane nake yin latti
Malam rabiu yace tashi kije
Bayan tashiga class jitayi anya yau din nan zata gane karatu kuwa sbd yunwa kalle kalle tafara ko zata hango hindu yar mai gari kawarta amma da alama yau hindu batazo makaranta ba
Haka dae aka fara musu karatu tun bata fahimta da ta tuno karatun nan fa jigon rayuwarta ne hasken rayuwarta ne domin kuwa ilmi haske ce kuma burin mahaifiyarta ne tana so tayi karatu domin ta taimaki jama'ar kauyen su tana son zama likiti
Nan tadinga tunanin innarta ta manta ma a makaranta take jitayi ana taba ta firgigit tadawo daga duniyar tunanin da ta lula
Taga ba kowa a class din alamun anfita break ne tace hindu yau ina kika tsaya?
tace hummm kedai bari shuhada yau nazo da wuri malam rabiu ya tare ni wai ilmi na bai kai na yan ss3 ba shine fa wai na koma primary ni kuwa nasa kuka nace wlh ina yar mai gari bazan koma primary ba da kyar aka mai dani js1 dan kawai yaba assignment ba kasa yamin tmbya nakasa amsawa shikenn fa nikam ba dabadin ke ba aradou bani ba wata karatu na allon ma tunda nayi rabi Allah ya isheni haka Allah ya amfana
Shuhada duk da batajin ddi sosae amma mgnr hindu yayi matukar bata dry dan haka ta hau dry hindu kuwa tacika tayi fam dan ita ta tsani dry zata fita da sauri shuhada ta riqota haba kawata yi hkr mana nabari bazan sake ba
Dawowa tayi ta zauna tace to wlh kibari idan ba haka ba kuwa mu bata dake na sati daya
Shuhada tace haba hindu ina murna kece kawai mai sona idan kika bata dani ai mutuwa zanyi
Hindu ta zaro ido waje tace tab lallai kibar mgnr mutuwa ba yanzu ba
Murmushi shuhada tayi tace ai dole nayi zancan mutuwa ina innata ina babana ta faɗa tana hawaye ya gangaro a idonta sosae hindu ta tausaya mata tace kiyi hkr shuhada wata rana sai lbr gashi kina da ilmi da natsuwa na tabbata a wannan ƙauyen namu mijin da zaki aura sai angani insha Allah yadikko sai taji kunya domin zakiyi abinda ba ataba yinsa ba a ƙauyen tanko
Gashi na taho mana da abinci innata ta dafa shine na juyo mana ita a leda amma kici kawai idan na koma gida zan kara ci tunda kafin nazo ma naci
Da sauri shuhada ta karba ta hau ci tana kuka hindu tana tayata
Hindu zata girme shuhada da shekara daya domin ita shekaranta 15 ne shuhada kuma 14
Hindu bata jin mgn ko kadan kasan cewarta yar gidan mai gari haɗuwar su da shuhada kuwa abakin rafi ne taga shuhada nan taji tana sonta da kawa duk yan mata ƙauyen suna son yin kawance da hindu sbd hindu tana da kyau daida gwargwado sannan tana haske
abunta bai rufe mata ido ba tana da kyauta ga neman tsokana
Hindu bata da hkr idan kayi mata abu tofa saita rama haduwarsu da shuhada ne yasata ta koyi hakuri
Akan kawancen shuhada da hindu
Nuratu bata so ba dan ita tafi dacewa tayi kawance da hindu ba shuhada ba
Akan wannan kawance saida shuhada taci dan banzan duka
Wannan dukan kuwa har gaban mai gari
********** *wacece shuhada*
Shuhada mlm amadu isa shine cikakken sunanta
Mahaifinta malami ne haifafen dan AZARE acan cikin wani kauye mai suna kauyen tanko nan iyaye da kakanni suke na mlm amadu
Mlm amadu yafara auren laure wato(yadiko) kwata kwata laure bata son kishiya ko da kuwa a maƙota ne balle ace kuma ma ita za akawo mawa
Mlm amadu bai san halin laure ba ya aureta ga ƙazanta dan wasu halayyan nata saidai sukayi aure take fitowa dasu da haka harta haifi ɗanta sale
Sale harya shekara 7 amma laure bata sake haihuwa ba
Sale yaro ne wanda baya jin mgn dan kullum iyayen yara sai sun kawo karansa wajan babansa
mlm amadu daya gaji ya bugama sale keji yana kullesa aciki dan yafi masa salama
Babu kalan bala'i da laure batayi ba akan an tsani ɗanta sale akauyen amma ko kulata mlm amadu bayayi sbd shi mutum ne baya son hayaniya
Mahaifiyar shuhada kuwa ba yar azare bace bafulatanan TILDE ce bikin kawarsu sukazo a ƙauyen tanko dake cikin azaren tunda mlm amadu yaganta yaji ta kwanta masa arai
Da haka dae yayi ta tmbya har yaje tilde yagana da mahaifin iklima wato mahaifiyar shuhada
Ba tare da bata lokaci ba mahaifin iklima ya amince da mlm amadu aka ɗaura aure
Laure bata sani ba wata kawarta ce talatu wanda halinsu yazo daya da laure tare suke kashewa su binne ta kawo mata jawabin ai mlm amadu yayi aure tana nan sake da baki acikin gida
Ranar babban hauka mlm amadu yagani awajan laure.haka ta dinga fasa tulunan ta da langa tana timasu da ƙasa
Mlm amadu bai bi ta kanta ba yasa aka sharewa amarya daki aka kawota
Tunda iklima tazo gidan sam batajin dadin zaman gidan bawai da mijinta ba aa saidai laure da ɗanta sale sun hanata sukuni
Da haka a daddafe har Allah yabata ciki ba ƙaramin wahala take sha ba haka laure tadinga azabtar da iklima
Ko abinci bata bata
Ranar haihuwa kuwa iklima tasha wuya kamar bazatayi rai ba. Laure tana kallonta yanda take juyi tana salati tana kiran sunan laure ta taimake ta amma laure tana zaune tana shan rake abunta har iklima ta suma
Malam amadu ne yashigo gidan da wata kanwarsa mairo basu shiri ko kadan da laure tsakaninsu saidai kallon banza
Da gudu mairo tayi kan iklima tana jijjigata gashi babu asibity a ƙauyen tanko sai sunje kauyen gangare.
Hnkln su yatashi matuƙa
Suka rasa yanda zasuyi mlm amadu yace bari naje gidan mlm sabitu yabani aron amalanken sa saimu kaita asibityn ƙauyen gangare mairo tace to yafita da sauri
Duk wannan bidirin da sukeyi laure ta hakimce a tsakar gidan tana kallonsu ga dan kwalinta gaban goshi tana shan raken ta
Haushi ne ya kama mairo tazo gabanta ta fizgi raken ta jefar ta ɗaga hannu da niyyar kai mata mari ta tuno da mgnr babbar yayarsu dan haka mairo ta fasa marin laure ta nuna ta da tsaya tana mgn
Laure baki da hali baki da tausayi kisani ita rayuwar duniya makaranta ce duk abinda kikayi to ina gaya miki zaki tarar da sakamakon sa ko bajima ko ba ɗaɗe
Laure tace hoohoo hoo naji din wlh dukkanku atafin hannuna kuke kar nake kallon ku gabaki dayanku zanyi maganin ku ita kuma wancan shegiyar Allah ma yasa ta mutu
Mairo zatayi magana taji muryan yayanta dan haka bata bi ta kan laure ba suka ciccibi iklima suka sata a akori kura
Gudu sosae sukeyi a hanya duk kansu sunji jiki kafin suka iso
Aka karbi iklima bayan awanni da wahalhalu ta haifo yar'ta mai kyawun gske wanda kamar ka taba ta jini ya fito mairo murna takeyi tasa hannu ta karbi yarinyar
Mlm amadu yace ya ita mahaifiyar yarinya
Bayani suka farayiwa mlm amadu cikin fada akan cewa suna da sakaci domin sunyi jinkirin kawo iklima domin kuwa tasamu matsala babba
Salati kawai mlm amadu da mairo sukeyi
Kafin mlm amadu yace wani irin matsala ne haka
Likita yace cutar shanyewar barin jiki ga kuma yoyon fitsari
Kuka mairo tace tana salati
Mlm amadu saida idonsa tayi ja amma baiyi kuka ba
Satin iklima 2 a asibity aka dawo da ita gida
Mairo ke kula da ita da yarinyar
Iklima da kanta tacewa mlm amadu yayiwa yar'ta huduba da sunan *SHUHADA* domin tana son sunan
Har tsawon wata uku mairo tana.kula da iklima da shuhada domin mairo tana son iklima ga shuhada yarinya ce mai shiga rai
Watan shuhada 7
Laure ta samu ciki
Kafin laure ta haihu
Shuhada tana da shekara daya daya da rabi
Babu kalar azaba da wulaqanci da mlm amadu da iklima da kuma yar'su shuhada basu gani wajan laure
Kuma mlm amadu baya iya tsawatar ma laure saide shima idan abun ya damesa yayita hawaye
Shuhada tana da shekara 7
Babu aikin da batayi laure tayi mata duka agaban iklima tayita kuka gashi bazata iya tashi ta kwaci yar'ta ba
Idan laure wulaqancin ta yatashi ta dinga zagin iklima kenn wai miskiniya
Ranar wata jumma'a shuhada ta gama yiwa mahaifiyarta komai zata tashi
Ta kira sunanta a hankali
*shuhada*
Gabanta ne taji ya fadi dan haka ta dawo da sauri tace naam innata me kikeso
Murmushi inna tayi tace duk rintsi duk wuyan rayuwa shuhada ki riqe mutumcin kanki shuhada ke yarinya ce amma kina da hnkln manya
Shuhada karki bar zuwa makaranta kiyi karatu kizama likita ki taimaki al'umma shuhada kina da hakuri da juriyar wahala amma inaso ki qara akan wanda kike dashi
Shuhada kiyiwa yadikko biyayya tamkar ni duk abinda zasu miki shuhada kibarwa Allah
Domin innallaha ma'assabireen
Kinji ko shuhadata?
Shuhada kuka take ta rungume innarta
Inna tace kibar kuka shuhadata
Duk wuyan rayuwa karki bar karatu domin ilmi haske ce jahilci kuwa duhu ne
Duk da shuhada shekarun ta bakwai amma tasan rayuwa
Tace insha Allah innata na miki alkawari zanyi karatu sosae na zama likita
Inna tayi murmushi tace Allah ya miki albarka shuhada Allah yasa ki zama abin alfahari Allah ya raya min ke Allah yabaki miji nagari wanda zai jikanki ya so ki sosae
Ameen shuhada tace
Inna tace shuhada jeki kawo min ruwa nasha
Shuhada tana dawowa da ruwan taci karo da babbar tashin hnkl
Mgnr take yiwa inna
Amma shuru kuka tasa tahau jijjiga inna tana cewa ga ruwan amma shuru
Ihu shuhada tasa daidai lkcn da mairo ta shigo gidan da gudu tayi kansu tana tmbyar shuhada mai yafaru
Cikin kuka tace gwaggo mairo innata
Mairo taba iklima tayi tace innalillahi wainna ilayhirrajiun kullu nafsin za'ikatil maut rufe idon iklima mairo tayi da zafi
Taja hannun shuhada Suka fita
Mairo tana kuka shuhada ma tana kuka har gona sukaje ta fadawa yayanta mlm amadu
Shi karan kansa saida yyi hawaye ga tausayin yar'sa shuhada
Haka akazo akayiwa iklima sutura su gwaggo mairo ne suka mata wanka
Agaban shuhada aka fita da innarta a makara sumewa tayi jama'a suka taro akanta sosae suka tausaya mata
Duk wannan abun yadikko bata gida
KO da tadawo taga mutane cike tam agidan tasan akwai abinda ya faru
Cikin ranta tace Allah dai yasa shigiyar nan mutuwa tayi da sauri tashige cikin gidan
Tasamu mata anata bawa shuhada hakuri tare da lallashinta
Tmbya tayi.akan mai yafaru ?
Akace mata kanwarki ce Allah ya karbi abunsa
Kukan munafurci yadiko tasa ta zube kasa tanayi ana bata hkr amma fa ga wanda basu san halin yadikko ba
DA haka aka gama zaman makokin iklima
Tofa daga nan kalar zaman yaqara canzawa
Shuhada tana da shekara 11 tayi saukar al'qur'ani mai girma mahaifinta yaji ddin sosae
Har wajen mai gari yaje yayi masa mgn akan cewa dan Allah yanaso ko bayan ransa shuhada ta cigaba da makaranta kar laure ta hanata
Mai gari yace haba mlm amadu ai cuta ba mutuwa bace yace nasani ranka shi dade amma inaso dan Allah kamin wannan Alfarman mai gari yace ba damuwa mlm amadu insha Allah
Bayan Haka da sati uku mlm amadu shima yace ga garin ku
Sosae shuhada taga rayuwa
Gwaggo mairo kuwa cutar makanta tasamu wanda anyi maganin har angaji amma abu ba labari
Yadiko taso shuhada tadaina zuwa makaranta amma mai gari yace sam sai shuhada ta kare makaranta kaf
Wannan shine ataƙaice tarihin rayuwar *shuhada*
Cigaban labari
Muje zuwa dai
Bayan antashi karfe biyu
jerawa sukayi da hindu yayinda gaban shuhada ke dukan uku uku domin duk lkcn da zata koma gida ji take kamar prison zataje
Har suka rabu da hindu tayi hanyar gida
Shuhada tana shiga gidan da sallama tasamu yadiko zaune akan turmi ga wata zabgegiyar bulala ahannunta ga nuratu agefe sai kaɗa ƙugu takeyi tana aika mata kallon banza
------------dan Allah kuyi hakuri wlh banjin dadi ne dan ko editing baiyiba
Nasan dolene aga kuskure but dan adam ajizi ne
Ina bukatar adduarku plss
more comments more typing
Share
*P*......5⃣↪6⃣
Gaban shuhada ne yashiga bugun dari dari gabaki daya hankalinta yatashi ganin bulalan dake hannun yadiko
Daurewa tayi ta durqusa nesa da yadiko tace ina wuni yadiko
Tashi yadiko tayi tana cewa dan ubanki da ban wuni ba zaki dawo ki sameni zaune iyee ?
Kin dawo daga wajan iskancin naki
Kuka shuhada tasa gamida cewa wlh yadiko ba wajan iskanci naje ba wajan karatu naje
Nuratu tace iya wlh wnn shegiyar taki rabuwa da hindu
To kema shalele ki rabu da hindun nan mana tunda kina da wasu kawayen
Turo baki nuratu tayi tace wlh nidai iya har kwanan gobe inason hindu da kawa
Yadikko tace haba shaleleta idan ba sokike a kulle uwarki ba ya kamata ace kin hakura da hindu nan fa agaban ki akazo aka tafi dani mai gari yamin kashedi akan karna sake taba shuhada
KO kin manta lkcn dana mata shegen duka akan ta rabu da hindu amma kamar sake manna su nayi
Kuka nuratu tasa yadiko ta koma rarrashinta ita dai shuhada tana tsugune awajan
Dan kullum sai sun ƙwaƙulu laifi domin kawai su jibgeta kamar jaka addua takeyi Allah ya kaɗarwa yadiko da tunani karta daketa ta juma awajan tana tsuguna amma yadikko ta koma lallashin nuratu da take kuka da hawaye shabe shabe kukan da ba dalili saboda dadi ya mata yawa
Da taga su shiririce ta miqe ahankali tashige ba'rin dakinta da awaki canza kaya tayi tazo ta hau shara da wanke wanke
Tana gamawa ta ɗauki tulu tayi hanyar rafi domin ta dibo ruwa ta ɗaura girki kar dare yamata
A hanya sai kallonta ake domin kuwa duk kauyen tanko babu yarinyar da takai shuhada kyau
Hakan ne ma yasa farin jininta kadan ne awajan yan mata yan uwanta
Domin yawancin samarin kauyen sunce sai shuhada
Wasu kuma ba don Allah suke sonta ba don kyawunta suke sonta
Tafiya take tana tunanin rayuwa
Allah sarki ni shuhada anya zanyi farin ciki kuwa arayuwata
Masifan yau daban na gobe daban Anya zan iya cika burin innata kuwa
Saurin istigfari tayi data tuno fa komai na Allah ne sannan dukkan bawa da kalar kaddaran sa
Lumshe ido tayi ahankali tace ya Allah kabani iko da karfin gwiwan cinye wannan jarabawan da kamin ya Allah karka samin gajiyawa ko kuma na kauce hanyar daidai haqiqa ina farin ciki da jarabawata bana baƙin ciki da ita Alhamdulillah ala kullee halin
Harta isa rafi jitai ana mata sallama abaya da sauri ta juyo tana kallonsa gabanta na faduwa
Afili tace yakubu lpy ?dan Allah ka rabu dani karka jamin sharri
Murmushi yakubu yayi yace shuhada nidai bazan gajiba ina sonki
Tashi shuhada tayi da sauri ta dauki tulunta tayi gaba
Yakubu dan wani mai kudin kauye ne amma ba akauyen tanko yake ba yana kauyen yar'tsami ne amma sbd shuhada yake zuwa kauyen tanko kullum sbd akwai abokansa
Ranar suka hadu da nuratu a dandali nurata tana ganin yakubu taji duk duniya babu wanda take so kamar shi
Amma shi shuhada yakeso kuma auranta yake sonyi
Shiyasa shuhada takejin tsoron kula yakubu sbd agabanta nuratu take fadawa yadikko tana son yakubu
Da sauri ya bita yana mgn yace shuhada dan Allah ki tsaya kabani minti biyu kacal
A hnkl shuhada ta juyo tace kayi hkr yakubu
Yace naji shuhada mgn nake so muyi
Tace sauri nakeyi zanje na ɗaura sanwa
Yace to yau zakizo dandali na jira ki ?
Waige waige shuhada takeyi dan karta hango nuratu
Domin nuratu bata iya zama wajen daya yanzu zaka ganta nan ka ganta can
Sbd kawai yakubu yabarta tace eh yakubu zanzo sai muyi mgn a dandalin
Yakubu yaji dadi sosae yace to shuhadata
Hawaye taji domin innarta ce ke kiranta da hakan
Da sauri ta wuce tana goge hawaye
Tana zuwa gida ta cigaba da aikinta
Har gefen magriba nuratu ce ta shigo gidan da waka ko sallama babu
Tabarma tagani a shinfide ta zauna ta hau kwalliyar zuwa dandali
Shuhada tana ta fama da wutar murhu taqi kamawa tunda ba siyan icce yadikko takeyi ba
Kwalliya sosae nuratu tayi ta kalli kanta a madubi ta kalli fuskan shuhada
Wani ƙololon baƙin ciki taji
Duk da tayi kwalliya amma ko tafin kafar shuhada bata kai kyau ba tsaki ta hau jerawa gamida yiwa shuhada kallon banza shuhada bata san ma tanayi ba
Har nuratu tagama ana sallar magriba ta fice abunta girgiza kai shuhada tayi tace Allah ya kyauta
Bayan ta gama girki inna ta lodo mata kayan wankinta dana nuratu wai ta wankesu yau
Shuhada gashi tagaji yau dabadin hindu ta kawo mata abinci a makaranta ba ai da tajima da sumewa domin babu abinda yadiko tabata asunan abinci
Yadiko tace dan ubanki bakiji me nace ba ?
Ahnkl shuhada tace naji yadikko amma naga dare yayi shiyasa kuma fa ana cewa rafin akwai aljanu da daddare
Yadiko tace yo kedin miye marabanki dasu ai kaman ki daya dasu
Idan nasake magana kikamin musu wlh saina lahira yafiki jin dadi domin idan namiki wani dukan sai kinga yan'wuta suna tsintar wake ta juya fuuuu tayi daki
Tagumi shuhada tayi ta lumshe ido a hankali tace Alhamdulillah ala kulli halin
Nuratu ce ta shigo gidan da gudu da ihu tana kira iya!iya! Iya! Kina inane kizo zan mutu da gudu yadiko tafito adaki babu ko zani ajikinta
Sale ne ya shigo shima ya kalleta yace ke kuma miye haka ihun ki har kan layi me aka miki meya faru?
Cikin kuka nuratu tace yakubu ne wai baya sona shuhada yake so duk da kwalliyar danayi masa amma wai shuhada tafini kyawu wai ko silpas din shuhada yafini kyau bayan ko silpas din ma bata dashi wai fuskata kamar tabo amma fuskar shuhada kamar wata taci gaba da kuka
Ran yadikko yabaci ta juya ta kalli shuhada wacce tayi sumar tsaye
Yadikko tace inyee lallai kam wato wannan jinsin mayun yakeso ba keba
Sale ya gwadawa shuhada rankwashi da sauri ta duqa kasa sbd azaba
Yadikko tace ai wlh wannan fuskar taki yau dinnan zan canza masa launi
Hanyar murhu tayi ta ɗauko icce daya wanda yake ci da wuta tace sale nuratu ku riqemin shegiya yanzun nan zan babbake mata fuska
Kuka shuhada ta hauyi tana basu hkr
Sale da nuratu suka riqeta yadikko ta dososu da wuta ....
Kuyi manager wlh har yanzu banajin dadi
Comments
An
Share
By Mmn ahlan✍🏻
[29/01 à 08:22] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*StөЯҰ ѠЯЇttЄҋ БҰ*
*Z⃡a⃡h⃡r⃡a⃡ A⃡b⃡d⃡u⃡l⃡ (m⃡o⃡m⃡y⃡n⃡ A⃡h⃡l⃡a⃡n⃡*
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
__________________
*GSKY YA KAMATA ACE MASU YIMANA POSTING* *MUDINGA NUNA FARIN CIKINMU AKAI TA YADDA ZASUJI DADI DOMIN YAU ACE SUN DAINA MU AKARAN KANMU BAZA MUJI DADI BA PLSS YAN UWANA WRITER'S MU GYARA*
🙄 *ATK* *AƘARA HAKURI*
_____________
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*ALHAMDULILLAH*
*A GSKY FANS BABU ABINDA ZAN CE MUKU SAI DAI ALLAH BAR KAUNA*
*NAGA KULAWA DA WANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKA MIN MGN TA PRIVATE SUKA MIN YA JIKI GSKY HAKAN YAMIN DADI SOSAE*
*HAKAN NE YASA NAJI DADI SOSAE NA DAURE NA MUKU TYPING*
*SANNAN NA DAUKI PAGE DIN NA MALLAKA MUKU HALAK MALAK*
*SON SO NAKE MUKU MAH FANS*❣
_________________
*P*.....7⃣↪8⃣
Kuka shuhada takeyi kamar ranta zai fita tace yadikko wlh Allah malamin islamiyyan mu yace ba kyau horo da wuta Allah ne kawai yake horo da wuta dan Allah yadiko karki ƙona min fuskata
Sosai shuhada tashiga kokuwan kwace kanta daga hannun su sale da nuratu
Yayinda yadiko tazo tana kokarin manna mata wuta a fuska
Shuhada data ga tabbass yadiko zata ƙonata ne yasata buge hannun yadiko da iya karfinta saiga wutan a fuskan yadiko
Wata uwar ihu yadiko tasa da karfi ta zube kasa tana birgima kamar ƙaraman yarinya
Tana wayyo fuskana wayyo fuskana
Da gudu sale da nuratu sukayi kanta
Shuhada ganin haka yasa tafice da gudu tabar gidan
Tayi gidan gwaggo mairo
Gwaggo mairo tana zaune a dakinta taji an banko kofarta da sauri ta rarimi sandarta tana cewa waye ne wannan ?
Da gudu shuhada ta faɗa jikin gwaggo mairo tasa kuka
Shuhada? gwaggo mairo ta kira sunanta domin taji muryan ta
Kasa mgn shuhada tayi sai kuka domin tasan yau kashinta ya bushe
Rungumeta gwaggo mairo tayi ahankali ta fara mgn
Shuhada kiyi hkr tun tasowar ki baki san komai ba sai wahala gaki yarinyar ƙarama gaki da hnkl da natsuwa ga tarbiyya
Shuhada baki san miye so ba tunda baki rayuwa da iyayenki cikin soyayya ba rayuwar wahala kukayi ahannun laure
Ɗagota gwaggo laure tayi tace shuhada ɗago ki kalleni duk dani bazan iya kallonki ba sbd laluran dana samu
Ɗogo idonta tayi wanda sukayi jajazur sbd kuka
Ta sauke su akan gwaggo mairo wanda bata gani
Gwaggo mairo tace shuhada lkc yayi da zaki karbi yan cinki agidan ubanki domin kema ƴace kuma kinada gado agidan amma duk laure tayi ƙam dasu ita da yaranta
To shuhada inaso ki sani tsoron Laure babu inda zai kaiki sai halaka lkc yayi da zaki daina tsoron laure da ƴaƴanta
Ki zage duk wanda ya miki ki rama
Amma ki zauna nuratu kanwar ki ta raina ki haba shuhada ya isa haka karki ƙara ragama kowa tunda basu nemi hakan ba
Gaban shuhada ne yashiga bugawa da sauri sauri
Tana tmbyar kanta anya zata iya kuwa
Murmushi gwaggo mairo tayi tace shuhada naji kinyi shuru karki ce baza ki iyaba yanzu dai tashi ga abinci can da yar uwarki haula takawo kici saiki kwanta gobe ki koma gida
Domin na lura laure bata son zamanki agidan ne kuma wlh tayi karya dan zama dole tunda gidan ubanki ne
Shuhada tace gwaggo mairo yau fa ƙona min fuska zatayi shine na buge hannunta wutan ya zube mata afuska idan na koma gida wlh yaya sale da nuratu zasu kasheni nikam gsky gwaggo bazan koma ba
Sanda gwaggo mairo ta ɗauka zata kaiwa shuhada
Da sauri ta matsa
Gwaggo mairo tace kinci gidan ku
Kenan duk abinda nace miki baki ɗauka ba kenan lallai kam
Zaki mutu lkcn ki baiyi ba domin laure kashe ki take son yi wannan makantar tawa ma nikam zarginta nake
Shuhada ta miqe ta ɗauko abincin ta zauna ci har lumshe ido takeyi tace wlh gwaggo mairo anty haula ta iya girki gsky yaya shamsu yayi sa'ar mata domin antyna ba baya ba
Dry gwaggo mairo tayi tace eh lallai kin iya santi
Nan dai suka dinga hira
Da washe gari
Anty haula tazo kawowa mamarta abinci taga shuhada riqe baki tayi tace shuhada yau kece
Dry shuhada tayi ta rungume antynta tace wlh anty ina son zuwa gidanki yadikko ce bata barina ga kuma aiki
Tsaki haula tayi tace aini ko kofar gidan baba amadu bana son bi sbd yadiko sam bata da hali
Nan dai suka gama hiransu yayinda yawancin hiran akan shuhada da yadiko ne
Tashi haula tayi tace nikam bari na koma gida
har gidanta shuhada ta rakata
Tasa shuhada tayi wanka ta bata wasu kayanta tasaka tace mata tadaina sa wancan
Sannan ta wuce gidan su gabanta na dukan dari dari
Yadikko kuwa jiya su sale fama suka dingayi da ita
Suka kaita gidan mai magani Allah yasota ma wutan bai wani ƙonata sosae ba
Ahankali shuhada ta shigo gidan kamar munafuka
Tana so tayi shirin makaranta sallama tayi
Ta sami nuratu da yadiko zaune akan tabarma fuskan yadiko ta kalla gefe daya a ƙone
Dry ne yaso kwace mata amma ta ɗaure
Da sauri nuratu ta taso tayi kan shuhada tana auna mata buhun zagi da ashar harda cewa yar gidan miskiniya
Sosae shuhada taji zafin mgnr nuratu
Tana jira ta isota
Ɗaga hannun nuratu tayi zata kaiwa shuhada duka riqe hannun shuhada tayi jikake tass!tass!tass! Ta saukewa nuratu afuska gefe daya
Da sauri yadiko ta miqe ta ɗauko muciya tayi kan shuhada ganin haka yasa shuhada itama ɗaukan tabarya tace wlh yadiko kina matsoni zan zubar dake ƙasa
Sosae yadiko da nuratu suka tsorata da lamarin shuhada
Dan haka suka saffe suka koma gefe suna kallon shuhada
Uniform tasaka tafice abunta tayi hanyar makaranta tana jinjina kalar abunda tayi dan batayi tunanin zata iyaba kuma da batayi ba da taji jiki
Ko da sale yadawo basa lbrn abinda shuhada tayi musu yadiko harda kuka wai shuhada ta kwankwaɗa mata tabarya
Sale yace bari ta dawo saina ci ubanta agidan nan
Shuhada sun tashi a makaranta kamar kullum suna tafiya da hindu tana bata lbrn abinda yafaru hindu mai zatayi inba dry ba
Tace wlh shuhada kin burgeni saura sale
Shuhada tace humm kedai bari hindu wlh tsoro nakeji dan nasan sai sun gaya masa
Hindu tace ah kema ai kinsan wannan jazaman ne
Amma karki tsorata shima kici uwarsa wlh sale wani karfi ne dashi sai shegen uban kurin bakin tsiya kiyi masa ragaraga wlh
Suka saka dry harda tafawa
Hindu tace yauwa kawalliyata namanta ban fada miki ba kinsan me?
Da sauri shuhada ta girgiza kai tace aa saikin fada menene? Dan naga fuskan ki da annuri kodai ta samu ne ? Ta fada itama tana murmushi
Rufe fuska hindu tayi tace dan mai garin gangare ne ya aiko da wasika wai yana sona
Da sauri shuhada ta rungumo hindu tace dan Allah da gske kikeyi
Hindu tace wlh ingaya miki
Shuhada tace to ya maganar karatun ki kuma fa ?
Murmushi hindu tayi tace kinsan fa shima yana karatu yace ba matsala Zai barni naci gaba da karatu na
Shiyasa ma na amince dan kinsan ya hadu fa gayen
Suka sa daria gabaki dayansu gamida tafawa
Sallama shuhada tayiwa hindu tace humm bari naje gida
Hindu tace inafa kara tuna miki wlh karki sake kiji tsoron sale
Shuhada tayi dry tace to zan gwada nagani ko zan iya
Hindu tayi dry
Suka rabu kowa yayi hanyarsa gida
Ahankali tayi sallama agidan tashiga ba kowa a tsakar gidan dan haka tashige dakinta da awaki duk sun bata mata shi da kashi
Saida ta share tukunna ta canza kaya tayi sallah ta hau aikace aikacen ta wanda takeyi agidan
Jin shuru yasata cewa azuciyarta inaga fa basu nan
Dan haka ta ɗauki tulu tayi hanyar rafi
A hanya ta haɗu da yakubu da sauri ta shigesa sai mgn yake mata taqi kulasa harta dibo ruwanta
Shan gabanta yakubu yayi yace dan Allah tauraruwar mata ki tsaya meyasa kike wahalar da zuciyata ne kam shuhada kinsan fa ina sonki
Hade rai shuhada tayi tace kaga yakubu kafita harkata kayi hkr karatu nakeso kuma shi nakeyi dan haka babu mgnr soyayya agaba na yanzu kayi hkr ta wuce tatafi abunta
Yakubu kamar zaiyi kuka sai bin shuhada yakeyi yana mgn kamar mahaukaci
Har akaxo kofar gida da sauri tashige gidan
Sanwa ta ɗaura tanayi harta gama ta zuba musu a langa itama ta zuba nata a kwano zataci kenan suka shigo gidan ko sallama babu
Yadikko tace inyee lallai kam sale zo kagani shigowa sale yayi yana aikawa shuhada harara
Gaban shuhada ne yashiga dukan dari dari amma tayi fuska ta dake abunta cin abinci tafarayi wanda takejin sa kamar magani
Tayi loma daya zata kai na biyu
Taji sauƙan rankwashe ihu tasa tayi tsalle ta miqe ta shaƙo wuyan sale
Kuyi manager da wannan
Amma gsky Ku qara yawan sharhi idan ba haka ba wlh zaisa nakasa muku typing
Ina Kara gode muku akan kulawarku agareni my fans ngd
Comments
And
Share
[29/01 à 08:23] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*StөЯҰ ѠЯЇttЄҋ БҰ*
*Z⃡a⃡h⃡r⃡a⃡ A⃡b⃡d⃡u⃡l⃡ (m⃡o⃡m⃡y⃡n⃡ A⃡h⃡l⃡a⃡n⃡*
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
__________________
*GSKY YA KAMATA ACE MASU YIMANA POSTING* *MUDINGA NUNA FARIN CIKINMU AKAI TA YADDA ZASUJI DADI DOMIN YAU ACE SUN DAINA MU AKARAN KANMU BAZA MUJI DADI BA PLSS YAN UWANA WRITER'S MU GYARA*
🙄 *ATK* *AƘARA HAKURI*
_____________
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*ALHAMDULILLAH*
*A GSKY FANS BABU ABINDA ZAN CE MUKU SAI DAI ALLAH BAR KAUNA*
*NAGA KULAWA DA WANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKA MIN MGN TA PRIVATE SUKA MIN YA JIKI GSKY HAKAN YAMIN DADI SOSAE*
*HAKAN NE YASA NAJI DADI SOSAE NA DAURE NA MUKU TYPING*
*SANNAN NA DAUKI PAGE DIN NA MALLAKA MUKU HALAK MALAK*
*SON SO NAKE MUKU MAH FANS*❣
_________________
*P*.....7⃣↪8⃣
Kuka shuhada takeyi kamar ranta zai fita tace yadikko wlh Allah malamin islamiyyan mu yace ba kyau horo da wuta Allah ne kawai yake horo da wuta dan Allah yadiko karki ƙona min fuskata
Sosai shuhada tashiga kokuwan kwace kanta daga hannun su sale da nuratu
Yayinda yadiko tazo tana kokarin manna mata wuta a fuska
Shuhada data ga tabbass yadiko zata ƙonata ne yasata buge hannun yadiko da iya karfinta saiga wutan a fuskan yadiko
Wata uwar ihu yadiko tasa da karfi ta zube kasa tana birgima kamar ƙaraman yarinya
Tana wayyo fuskana wayyo fuskana
Da gudu sale da nuratu sukayi kanta
Shuhada ganin haka yasa tafice da gudu tabar gidan
Tayi gidan gwaggo mairo
Gwaggo mairo tana zaune a dakinta taji an banko kofarta da sauri ta rarimi sandarta tana cewa waye ne wannan ?
Da gudu shuhada ta faɗa jikin gwaggo mairo tasa kuka
Shuhada? gwaggo mairo ta kira sunanta domin taji muryan ta
Kasa mgn shuhada tayi sai kuka domin tasan yau kashinta ya bushe
Rungumeta gwaggo mairo tayi ahankali ta fara mgn
Shuhada kiyi hkr tun tasowar ki baki san komai ba sai wahala gaki yarinyar ƙarama gaki da hnkl da natsuwa ga tarbiyya
Shuhada baki san miye so ba tunda baki rayuwa da iyayenki cikin soyayya ba rayuwar wahala kukayi ahannun laure
Ɗagota gwaggo laure tayi tace shuhada ɗago ki kalleni duk dani bazan iya kallonki ba sbd laluran dana samu
Ɗogo idonta tayi wanda sukayi jajazur sbd kuka
Ta sauke su akan gwaggo mairo wanda bata gani
Gwaggo mairo tace shuhada lkc yayi da zaki karbi yan cinki agidan ubanki domin kema ƴace kuma kinada gado agidan amma duk laure tayi ƙam dasu ita da yaranta
To shuhada inaso ki sani tsoron Laure babu inda zai kaiki sai halaka lkc yayi da zaki daina tsoron laure da ƴaƴanta
Ki zage duk wanda ya miki ki rama
Amma ki zauna nuratu kanwar ki ta raina ki haba shuhada ya isa haka karki ƙara ragama kowa tunda basu nemi hakan ba
Gaban shuhada ne yashiga bugawa da sauri sauri
Tana tmbyar kanta anya zata iya kuwa
Murmushi gwaggo mairo tayi tace shuhada naji kinyi shuru karki ce baza ki iyaba yanzu dai tashi ga abinci can da yar uwarki haula takawo kici saiki kwanta gobe ki koma gida
Domin na lura laure bata son zamanki agidan ne kuma wlh tayi karya dan zama dole tunda gidan ubanki ne
Shuhada tace gwaggo mairo yau fa ƙona min fuska zatayi shine na buge hannunta wutan ya zube mata afuska idan na koma gida wlh yaya sale da nuratu zasu kasheni nikam gsky gwaggo bazan koma ba
Sanda gwaggo mairo ta ɗauka zata kaiwa shuhada
Da sauri ta matsa
Gwaggo mairo tace kinci gidan ku
Kenan duk abinda nace miki baki ɗauka ba kenan lallai kam
Zaki mutu lkcn ki baiyi ba domin laure kashe ki take son yi wannan makantar tawa ma nikam zarginta nake
Shuhada ta miqe ta ɗauko abincin ta zauna ci har lumshe ido takeyi tace wlh gwaggo mairo anty haula ta iya girki gsky yaya shamsu yayi sa'ar mata domin antyna ba baya ba
Dry gwaggo mairo tayi tace eh lallai kin iya santi
Nan dai suka dinga hira
Da washe gari
Anty haula tazo kawowa mamarta abinci taga shuhada riqe baki tayi tace shuhada yau kece
Dry shuhada tayi ta rungume antynta tace wlh anty ina son zuwa gidanki yadikko ce bata barina ga kuma aiki
Tsaki haula tayi tace aini ko kofar gidan baba amadu bana son bi sbd yadiko sam bata da hali
Nan dai suka gama hiransu yayinda yawancin hiran akan shuhada da yadiko ne
Tashi haula tayi tace nikam bari na koma gida
har gidanta shuhada ta rakata
Tasa shuhada tayi wanka ta bata wasu kayanta tasaka tace mata tadaina sa wancan
Sannan ta wuce gidan su gabanta na dukan dari dari
Yadikko kuwa jiya su sale fama suka dingayi da ita
Suka kaita gidan mai magani Allah yasota ma wutan bai wani ƙonata sosae ba
Ahankali shuhada ta shigo gidan kamar munafuka
Tana so tayi shirin makaranta sallama tayi
Ta sami nuratu da yadiko zaune akan tabarma fuskan yadiko ta kalla gefe daya a ƙone
Dry ne yaso kwace mata amma ta ɗaure
Da sauri nuratu ta taso tayi kan shuhada tana auna mata buhun zagi da ashar harda cewa yar gidan miskiniya
Sosae shuhada taji zafin mgnr nuratu
Tana jira ta isota
Ɗaga hannun nuratu tayi zata kaiwa shuhada duka riqe hannun shuhada tayi jikake tass!tass!tass! Ta saukewa nuratu afuska gefe daya
Da sauri yadiko ta miqe ta ɗauko muciya tayi kan shuhada ganin haka yasa shuhada itama ɗaukan tabarya tace wlh yadiko kina matsoni zan zubar dake ƙasa
Sosae yadiko da nuratu suka tsorata da lamarin shuhada
Dan haka suka saffe suka koma gefe suna kallon shuhada
Uniform tasaka tafice abunta tayi hanyar makaranta tana jinjina kalar abunda tayi dan batayi tunanin zata iyaba kuma da batayi ba da taji jiki
Ko da sale yadawo basa lbrn abinda shuhada tayi musu yadiko harda kuka wai shuhada ta kwankwaɗa mata tabarya
Sale yace bari ta dawo saina ci ubanta agidan nan
Shuhada sun tashi a makaranta kamar kullum suna tafiya da hindu tana bata lbrn abinda yafaru hindu mai zatayi inba dry ba
Tace wlh shuhada kin burgeni saura sale
Shuhada tace humm kedai bari hindu wlh tsoro nakeji dan nasan sai sun gaya masa
Hindu tace ah kema ai kinsan wannan jazaman ne
Amma karki tsorata shima kici uwarsa wlh sale wani karfi ne dashi sai shegen uban kurin bakin tsiya kiyi masa ragaraga wlh
Suka saka dry harda tafawa
Hindu tace yauwa kawalliyata namanta ban fada miki ba kinsan me?
Da sauri shuhada ta girgiza kai tace aa saikin fada menene? Dan naga fuskan ki da annuri kodai ta samu ne ? Ta fada itama tana murmushi
Rufe fuska hindu tayi tace dan mai garin gangare ne ya aiko da wasika wai yana sona
Da sauri shuhada ta rungumo hindu tace dan Allah da gske kikeyi
Hindu tace wlh ingaya miki
Shuhada tace to ya maganar karatun ki kuma fa ?
Murmushi hindu tayi tace kinsan fa shima yana karatu yace ba matsala Zai barni naci gaba da karatu na
Shiyasa ma na amince dan kinsan ya hadu fa gayen
Suka sa daria gabaki dayansu gamida tafawa
Sallama shuhada tayiwa hindu tace humm bari naje gida
Hindu tace inafa kara tuna miki wlh karki sake kiji tsoron sale
Shuhada tayi dry tace to zan gwada nagani ko zan iya
Hindu tayi dry
Suka rabu kowa yayi hanyarsa gida
Ahankali tayi sallama agidan tashiga ba kowa a tsakar gidan dan haka tashige dakinta da awaki duk sun bata mata shi da kashi
Saida ta share tukunna ta canza kaya tayi sallah ta hau aikace aikacen ta wanda takeyi agidan
Jin shuru yasata cewa azuciyarta inaga fa basu nan
Dan haka ta ɗauki tulu tayi hanyar rafi
A hanya ta haɗu da yakubu da sauri ta shigesa sai mgn yake mata taqi kulasa harta dibo ruwanta
Shan gabanta yakubu yayi yace dan Allah tauraruwar mata ki tsaya meyasa kike wahalar da zuciyata ne kam shuhada kinsan fa ina sonki
Hade rai shuhada tayi tace kaga yakubu kafita harkata kayi hkr karatu nakeso kuma shi nakeyi dan haka babu mgnr soyayya agaba na yanzu kayi hkr ta wuce tatafi abunta
Yakubu kamar zaiyi kuka sai bin shuhada yakeyi yana mgn kamar mahaukaci
Har akaxo kofar gida da sauri tashige gidan
Sanwa ta ɗaura tanayi harta gama ta zuba musu a langa itama ta zuba nata a kwano zataci kenan suka shigo gidan ko sallama babu
Yadikko tace inyee lallai kam sale zo kagani shigowa sale yayi yana aikawa shuhada harara
Gaban shuhada ne yashiga dukan dari dari amma tayi fuska ta dake abunta cin abinci tafarayi wanda takejin sa kamar magani
Tayi loma daya zata kai na biyu
Taji sauƙan rankwashe ihu tasa tayi tsalle ta miqe ta shaƙo wuyan sale
Kuyi manager da wannan
Amma gsky Ku qara yawan sharhi idan ba haka ba wlh zaisa nakasa muku typing
Ina Kara gode muku akan kulawarku agareni my fans ngd
Comments
And
Share
[29/01 à 08:23] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*ᔕTOᖇY ᗯᖇITTEᑎ ᗷY*
*z̸a̸h̸r̸a̸ a̸b̸d̸u̸l̸* ( *m̸o̸m̸y̸n̸ a̸h̸l̸a̸n̸*)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*
_________________
Alhamdulillah Mah fans Ina qara gode muku sosae Allah yabar zumunci ameen
_________________
*karo na farko da zance idan kinsan zaki min comments da tnxx ko stickers*
*ki riqe abunki bana buqata*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*P*.......9⃣↪🔟
Da iya karfinta shuhada ta shaƙe sale wanda yake mutsu mutsu domin ya ƙwaci kansa daga hannun shuhada amma yakasa
Yadiko da nuratu tsoro ne ya kamasu sosae sai ihu sukeyi suna neman jama'a taimako domin ayanzu kam sun gama yankewa shuhada fa aljanune da ita da gudu nuratu ta fita neman agaji wa yayanta dan kar shuhada ta kashesa
Sale yasha wahala sosae a hannun shuhada dan ba karamin shaqa tayi masa ba saida sale yayi lakwas numfashinsa da kyar yake fita
Tukunna shuhada ta sakesa ta koma gefe tana zare manyan idanunta farera wanda suka koma jajur kamar an daka barkono ne aka zuba mata a idon ya zama haka saika rantse ba acikin hayyacinta take ba
Nuratu ce ta shigo da wasu maza uku wanda da kyar suka biyota dan ba kunya nuratu take dashi ba
Duk girman ka duk tsufan ka ba shi zai hana nuratu zagin ka ba
Suna shigowa shuhada ta rarimi tabarya tayi kansu dashi tana cewa kuna kara sowa zan sumar daku
Ai adari da saba'in suka ruga da gudu suka bar gidan
Yadikko ma gudun zatayi shuhada tace wlh kina fita saina fille miki kai da tabaryan nan
Ku ukun nan kar wanda yafita
Nan suka duqa ƙasa yadikko sai wuqi wuqi takeyi da idanu nuratu harda fitsari
Yadikko tace dan Allah shuhada kiyi hakuri wlh bazamu sake ba bamusan kinada aljanu masu karfi haka ba
Cikin tsawa shuhada tace kimin shuru kona banbare miki haƙwaran gaba yanzun nan banson jin komai daga wajenki azzaluma kawai
Daga yau duk wanda yaqara takurawa shuhada mune nan maganinsa
Keeeeeeee!!! Nuratu
Da sauri nuratu taɗago amma bata kalli idon shuhada ba sbd wani tsoron shuhada daya ziyarci zuciyarta
Jikinta na rawa tace na'am anty shuhada
Dry ne yaso kwacewa shuhada amma idan tayi plan dinta zai wargaje dan haka takara hade rai sosae tace ashe ma kinsan kece ƙarama to maza tashi amatsayinta ta yayarki ina umartanki ki tashi ki dibo mata ruwa arafi kizo ki haɗa wuta kisa mata ruwan wanka zatayi wanka kuma kunga wannan abincin data girka din nan bazakuci ba yau kuma da yunwa zaku kwana kuji ko da dadi
Ke kuma yadikko tashi kiyi jinyar ɗanki
Nuratu tafara kuka tace wlh anty shuhada ban iya zuwa rafi ɗibo ruwa ba bantaba zuwa rafi ba dan Allah anty shuhada ki taimaka min wlh ban iya komai ba
Eh tabbas kam ba ki iyaba amma koya zakiyi kuma idan har kika jima baki dawo ba kinsan sauran
Tashi nuratu tayi tana sheshshekar kuka ta ɗauki tulu
Tafita
Yadikko kuwa sale da ciccibesa da kyar takai shi dakinsa ta dibo ruwa tahau yayyafa masa da kyar yasaki ajiyar zuciya mai karfi
Yana bude ido ya koma bayan yadiko da sauri yana cewa wlh iya yarinyan nan ba ita kadai bace dan Allah iya ki ceceni karta kasheni wlh aljanu gareta
Yadiko tace kayi magana a hankali karta ji domin tana tsakar gida sale riqe bakinsa yayi sai wulli wulli sukeyi da ido adaki
Shuhada kewaye tashiga tahau kyalkyala dry kamar ranta zai fita tace yau ina zanga hindu na bata wannan labarin itama tasha dry
Tana cikin kewayen ne tana kan dry taji kukan nuratu fitowa da sauri tayi ta hade rai tace meya faru?
Daidai nan yadiko da sale suma suka fito sale sai maqalewa yakeyi bayan yadiko
Cikin kuka nuratu tace tulun ya fashe
Shuhada tace shine kike wannan ihun ? To ai ba matsala dama tulun hudu ne kin fasa daya saura uku dauki wani kije ki dibo ruwan nan
Nuratu tace anty shuhada dare fa yafarayi kuma inaso naje dandali
Shuhada tace yau babu wanda zai fita agidan ban dan haka ko ki ɗauki tulu ko kuma jikin ki ya gaya miki
Nuratu tana kuka tace iya ki taimaka min kina fa kallon abinda take min yaya sale kaima kayi magana mana
Tsawa shuhada tayiwa nuratu wanda ba nuratun ba hatta yadikko da sale saida suka tsorata
Tace maza ki ɗauki tulun nan ki fita kafin na shaqo ki ba shiri ta ɗauka tana kuka ta fita shuhada tace kuma wlh nuratu idan har kika sake fasa tulun nan nida ke ne ina gaya miki
Dakin innarta ta share ta koma ciki yadiko ko uhum takasa cewa
Da kyar nuratu ta kawo ruwan
Wajan haɗa wuta saida akasha drama
Shuhada ta tsala wankanta fuskarta babu komai amma sai kyalli takeyi kyawun fuskarta yasake fitowa sosae ta ɗauki hijab dinta tasa ta fice abunta yau karo na farko kenan da zata fara zuwa dandali
Kafin taje dandalin saida tafara biyawa gidan gwaggo mairo ta bata labarin abinda ya faru dry sosae gwaggo mairo tayi tace eh lallai kam yau anyi maganin laure da marasa kunyan yaranta sun dan taba hira daga bisani kuma shuhada tayiwa gwaggo mairo sallama tace zataje gidan antynta haula daga nan zata dan leqa dandali kafin ta wuce gida
Gwaggo mairo tace to Allah ya tsare hanya shuhada ga kwanon antyn naki can ki ɗauka ki tafi mata dashi wanda takawo min abinci ne yau bata dawo ta ɗauka ba
Shuhada tace to
Kwanon ta ɗauka tafice
Gidan anty haula tayi kai tsaye taje sun jima suna hira da anty haula shuhada ta bata labarin draman su dasu yadiko dry anty haula takeyi har tana zubewa ƙasa tace wlh kunyi kyau kai ko ba komai zaki sake ki wala yanzu agidanku dry shuhada tayi suka cigaba da hiransu
Saida shuhada tayi sallan isha kafin tayiwa anty haula sallama kai tsaye dandali ta nufa
Tana zuwa kallo ya koma kanta
Waige waige takeyi ko zataga hindu
Amma bata ganta ba kallon da ake mata ne yasata tashi domin ta tsani kallon azuciyarta tace bari naje gida tunda hindu yau batazo dandalin ba
Yawancin samarin duk sun ruɗe da sukaga shuhada
Wasu harda rige rigen yimata mgna
Amma taqi kulasu
Wasu kuma sukace ko yar' gidan waye oho
Da haka tatafi gida abunta dan bata saba zuwa dandali ba gashi bataga hindu ba
Ko da ta koma gida su yadikko suna daki yunwa ta addabe su amma sunajin tsoron ɗaukan abincin suci
Aljanun shuhada suci ubansu
Suna jin shigowarta suka ƙara lafewa aɗaki
Shuhada akwai tausayi dan haka ta ɗauko langan abincin ta zuba nata sannan ta kira nuratu ta miqa mata sauran da sauri nuratu ta karba ta koma dakin
Sukaci
Da washe gari
A makaranta shuhada ke bawa hindu labarin abinda ya faru hindu dry take harda hawaye tace amma fa wlh kawata kin burgeni
Shuhada tace humm ai naɗan samu lafiya dan harma na share dakin innata na koma ciki da zama
Hindu tace da kyau wlh hakan da kikayi yayi daidai
Nan dai suka cigaba da hiran su amma yawancin hiran akan karatun su ne
*bayan sati biyu*
Abubuwa dayawa sun faru harda samun yancin shuhada kuwa agidan ubanta dan yanzu yadikko bata shiga hidimarta sale ma yafita tsabgarta nuratu ma haka amma kuma duk da haka dan wani aikin na gidan tanayi harda girki amma wani lkcn tana tilasta nuratu suyi tare amma itama bata shiga hidimarsu kuma hakan yafi mata salama
Yau ta kama asabar
Shuhada tana gida babu makaranta sunata shirin exams
Zaune take akan tabarma gefenta kuma books dinta ne tana dubawa
Masifa taji yana tashi kafin ashigo gidan yadiko tafito daga daki wata mata ce ta shigo sai fizgar yar'ta takeyi tana ruwan bala'i
Miqewa tsaye shuhada tayi dan tasan matar
Yadiko tace lpy kuwa?
Innar lilo tace ina kuwa lpy ina sale?
Yadiko tace baya nan yafita mai yafaru ne kam
Cikin masifa innar lilo tace ina kuwa lpy ɗanki sale yayiwa yarinyata ciki
Zare ido shuhada tayi tana kallon lilo
Yadiko kuwa ƙugu ta riqe ta turo ɗan kwali gaban goshi tace lallai ma innar lilo sharri zakiyiwa ɗana duk tsanar da kuka masa lkcn yana ƙarami da sharrin da kuke kulla masa yana ƙarami bai isheku ba to wlh tun wuri kisan wanda yayiwa yar'ki ciki amma wlh badai ɗana sale ba
Ana cikin wannan hayaniyar ne saiga wata ma tashigo da ashar tana cewa ina dan iskan yaron yake dan akuya wlh bai isaba an isa atabani azauna lpy wlh yau sai gaban mai gari
Yadiko tace ke kuma lpy zuwaiba? Waye kuma kike kira da dan akuya
Zuwaiba tace waye kuwa bayan ɗanki sale yayiwa ya'ta ciki
Nan fa gida ya hargitse da hayaniya
Shuhada tattara books dinta tayi ta fice tabar gidan
Gidan gwaggo mairo taje ta kwanta gwaggo mairo tace lpy kuwa shuhada?.
Guntun tsaki shuhada tayi tace wlh gwaggo mairo yaya sale ya zama abinda ya zama yanzu fa na baro musu gidan suna hayaniya yaya sale yayiwa yar' gidan baba zuwaiba ciki da yar'gidan innar lilo
Salati gwaggo mairo tasa tace wlh ko kadan albasa batayi halin ruwa ba laure kin cucemu domin ko kadan sale da nuratu basuyi halin yaya amadu ba
Nan dai suka dinga jajinta lamarin shuhada kuwa bata koma gidan ba sai dare
Ko da ta koma bata gansu ba
Ashe mai gari yasa an kulle sale ne nuratu kuwa ba aganta ba shine yadiko tafita nemanta
Washe gari
Yadiko abin duniya ya mata yawa
Shuhada ce ta fito tana kiran sunan nuratu yadiko tace nuratu bata gida tun jiya muke nemanta
Hankalin shuhada ne yatashi domin duk abinda yasamu nuratu ya sameta tunda ƙanwarta ce ubansu daya
Fita tayi cikin tashin hankali tana neman nuratu ahanya suka hadu da hindu
Tace ke kuma yana ganki wujiga wujiga haka ?
Cikin tashin hankali shuhada tabawa hindu labarin abinda ya faru sannan tace nuratu kuma ba aganta ba tun jiya
Tsaki hindu tayi tace shine kuma duk kika bi kika tayar da hankalin ki haka? Wlh na tabbata yau ace kece aka nema aka rasa wlh yadiko ko nuratu ko sale bazasu nemeki ba
Shuhada tayi murmushin yake wanda yafi kuka ciwo ta girgiza kai kafin tace duk lalacewar naka nakane
Hindu wlh ko kadan banajin haushin hakan
Nidae kawai zo muje ki tayani neman kanwata hindu ta tabe baki tace muje
Babu kalar neman da shuhada da hindu basu yiwa nuratu ba amma basu ganta ba
Har karfe uku hindu tace nikam shuhada gsky nagaji wlh kizo muje gida ko tadawo
Gida sukaje suka tadda yadiko zaune ta rafka tagumi shuhada tace yadiko nuratun bata dawo ba ?
Yadiko tace eh bata dawo ba nima ban jima da shigowa gidan ba
Har akayi sallar la'asar ba nuratu balle labarinta
Sosae hankalinsu yatashi duk kawayenta an tmbye su sunce basu ganta ba
Saida nuratu tayi kwana2 kafin tadawo gida babu kalar tmbyar duniyan nan da yadiko bata yiwa nuratu ba akan inataje kwana2 amma nuratu taqi magana akarshe ma cewa tayi itakam akyaleta gidan saurayinta taje
Har duka shuhada tayiwa nuratu amma abanza
Bayan sati daya
Yadiko taje gidan kawarta talatu take bata labarin halin da take ciki
Talatu tace ai muddin shuhada tana gidan nan tofa kema kinsan al'qadarin ki zata karye dan haka ya zama dole ki ƙaɗa shuhada tabar ƙauyen tanko gabaki daya
Nazari yadiko tashiga yi kafin tace tabbas mgnrki gsky ne amma tayaya zan kori shuhada ?
Talatu tace ai gun boka zamu koma
(Wa iya zubillah)
Yadiko tace to yanzu mubari sai gobe kenn
Talatu tace wani gobe tashi zakiyi yanzun nan muje ai yau kar shuhada ta qara kwana a kauyen tanko haka suka shirya suka wuce kauyen kuka domin nan ne inda bokan nasu yake
Shuhada sun tashi a makaranta sun jima suna hira da hindu kamar yau ne suka hadu da kyar suka rabu domin da sunzo rabuwa zasu sake ɗago wata hiran
Harta koma gida
Shuru taji alamun ba kowa agidan
Dan haka ta canza kaya tayi sallah tayi wanke wanke da shara ta ɗauki tulu taje ta dibo ruwa ta ɗaura sanwa
Da kyar takeyi sbd wata ciwon kai daya zo mata lkc daya
Su yadiko kuwa boka ya musu alqawari kafin suje gida shuhada tabar kauyen tanko
Haka kuwa akayi domin bayan tagama girki taji kanta da kafafunta suna mata ƙaiƙayi da gudu tabar gidan
Tayi tasha ta fada mota batare da sanin inda zataje ba
_________________
*rashin sharhin Ku ne zai sani dakatar da littafin nan so plss agyara bcox nima inada abunyi wlh*
________________
*kambala'i wlh duk wanda ya siyarmin da littafi ko kuma ya canza min wata kalma ALLAH YA ISA ban yafe ba wlh duk wanda ya cire sunana ko yamin editing haka kawai ai bawai anfini son kudin bane kowa ya qirqiri basiransa bawai ya saci na wani ba*
Comments
And
Share
0 comments:
Post a Comment