*P*...2⃣1⃣↪2⃣2⃣
Wata budurwa ce tsaye a parking space na hospital fuskarta ɗauke da murmushi
Bazata wuce 19years ba sanye take da atampa riga da siket wanda dinki ya karbi jikinta kaman dama ajikinta aka dinka kayan
ta naɗa veil akanta asaman atampar lobcourt ne na likitoci tym to tym takan duba agogon dake ɗaure ahannunta zuwa can anjima wani saurayi ya fito da sauri shima hannunsa ɗauke da labcourt din kallon sa tayi tace yaya fauzan sai yanzu
Murmushi yayi yace eh *shuhada* muje mu ɗauko su mihik da shukra a skull
Mota ya shiga itama ta shiga ya tada suka ɗauki hanyar *nadabo university Kaduna* fauzan yace gsky yau kinyi matukar kokari ko da yake ma kullum kinayi kinsan wannan doctorn dayazo daga Dubai dinnan wlh saida yasha mamaki wai shekarun ki 19 amma wai kina da degree sbd bai taba tunanin yan' nigeria suna da wannan hazaƙan ba
Murmushi kawai shuhada keyi tana tuna baya lumshe ido tayi tace yaya fauzan turawan nan sun raina mu dayawa wlh
Yace haka suke ai hira suke danyi sama sama dan shima fauzan din bawani magananne bane har suka isa waya fauzan ya ɗaga ya kira mihik yace sufito ko minti uku basuyi ba suka fito duk sun zama big girls jida kansu kawai sukeyi suma yanzu yan'mata ne za adama dasu yan matan university basu kula kowa balle mgn da mutune wasu har cewa suke yaran familyn gidan kawu baba akwai girman kai duk mgnr da zasuyi basu saka sunan yarinya daya domin sunsan halinta sarai ba kauwar lasa bace tunda yanzu an girma amma babu abinda ya canza
Motar suka shiga suka gaishe da yaya fauzan ya amsa shuhada ta waigo tana murmushi tace sannun ku ya lecture din yau akwai dadi?
Mihik tace ina kuwa dadi saidai kawai Allah yasa mudace
Suka amsa da ameen shukra tace ya hospital kashe ido daya shuhada tayi kafin tace Alhamdulillah
Nan motar ya ɗauki shuru
*waiwaye adon tafiya*
*****************
Tun lkcn da shuhada ta cigaba da karatun ta ta cire duk wani abu mai sunan wasa ta ajiyesa agefe karatu kawai takeyi burinta kawai ta zama likita domin cikar burin mahaifiyarta da ita karan kanta ga kuma yaya fauzan agida yana nunnuna mata wasu abubuwa wani lkc ma har exam yake mata agida kuma tayi winning sosae basirar ta ke aiki afannin abinda take karanta tunda tabasa mahimmanci harta family house ta daina zuwa hira sai ranar asabar kawai take zuwa
Awannan shekaru biyar din ba qaramin nasarori shuhada ta samu ba lkcn da aka nemi iyayenta da suzo shuwagabannin makaranta suna son ganinsu batare da bata lkc ba abbi da ammy suka shirya sukaje
Aranar ne akabawa shuhada mukamin dalibai kusan 358 ranar shuhada tayi kukan farin ciki haka ma abbi da ammy domin basuyi asaran kudin makaranta ba sosae aka taya shuhada murna binayya kamar ta mutu haka taji yarinya qarama da ita amma akwaita da nasibi
Shuhada tana da shekara 15 tayi candy gama secondary skull tayi farin ciki kamar mai
Hankalin binayya bai sake tashi ba saida taji lkcn da zatayi graduation na degree taji ance shuhada ma zatayi a lkcn shuhada tana da shekara 18 ita kuwa a lkcn tana da shekara 23 sannan ko awajan graduation din shuhada tafi karban kyauta domin harta mai girma governorn kaduna saida yabawa shuhada kyauta domin ya yaba da kwazonta da hazakarta hakika ilmi ma baiwa ce har kuka binayya tayi alkcn da mai girma governor yace yabawa shuhada kyautar mota qirar benz hot 127 su ra'eena ra'eesa zeeyadat shukra mihik saida suka shirya party agida suka cashe
Yaya fauzan kullum idan sukayi waya da yaya burleey saiya basa lbrn shuhada
Haka kawai yaji yana son ganin yarinyar gashi duk wannan tsawon lkcn bai taba bude pics dinta yagani ba wa inda yaya fauzan yake tura masa
Da haka fauzan ya fara janta zuwa asibityn da yake aiki *ramhar clinic hospital* ranar zuwanta na farko ta karbi haihuwar wata mata wanda wasu nurses suka kasa ko a ranar shuhada ta samu kyautar girmamawa
Wannan kenan
*************
Suna isa gida direct tayi ɗakin ammy dan haka ya zame mata jiki kullum idan suka dawo saita fara zuwa taga lpyr ammy sannan idan tayi wanka taci abinci taje ta gaishe da momma da mamy kafin ta wuce family house taje gaishe da kawu baba da hajiya kaka
A zaune ta iske ammy abakin gado da wasu takardu ahannunta tana dubawa cikin natsuwa tayi sallama ta shigo ammy ta amsa tana qara murmushin fuskarta har ƙasa shuhada ta duqa tace barka da gida ammyna
Yauwa barka dai my doter ya hospital din ?
Murmushi tayi tace Alhamdulillah ammyna
Ammy tace kije kiyi wanka kici abinci ki huta tashi shuhada tayi tace to ammy Jounalist da dr ra'eena basu dawo bane ammy tayi dry tace Jounalist tadawo amma dr ra'eena bata dawo ba shuhadan ma dry tayi tafice tana cewa nabarki lpy ammynmu
Ammy tabi bayanta ta kallo tayi murmushi haqiqa shuhada ta shige can ƙasar zuciyarta gashi wani lkc idan tayi magana kamar burleey
Tun kafin shuhada ta shiga ɗaki tana haya upstairs din dakinsu taji wani irin kiɗa natashi sai kace a club domin yanzu dakinsu daya ne su uku
Da sauri ta qarasa ɗakin ta tura kofa ra'eesa ce a tsakiyar gado tana tsaye daga ita sai gajeran wando da vest sai ɗikar rawa takeyi har tana zufa sai kace ansata
Da sauri shuhada ta kashe dvdn ta hade rai tana hararan ra'eesa juyawa ra'eesa tayi cikin rashin mutunci taga waya kashe mata kiɗa dan ra'eesa bawai canzawa tayi ba tozali da shuhada tayi ta haɗe rai hakan ne kawai sai yabata dry tace kai dr shuhada miye haka dan Allah ? look nifa bana son takuran kin nan ki barni na more quriciyata aha ta sauko agadon taje da niyyar sake kunnawa shuhada ta riqota tace haba ra'eesa ya kamata ace kisan cewa yanzu kin girma kin wuce wannan shafin
Bai kamata ace inkinyi gaba kiyi baya ba dan Allah kiyiwa kanki karatun ta nutsu yanzu miye amfanin haka ? da abbi ne yazo yaganki ahaka kuma fa amadadin ki ɗauki littafi kidinga dubawa kwace hannunta tayi ta zauna abakin gado tace kai haba inaa bazai yuba nikam na kashe kaina a karatu ba nifa bazan iya zama kamar ke ba ina kika fito karatu ina zaki karatu gida basu yaya burleey ba yaya jb ai sai na sakata na wala naji dadin rayuwata girgiza kai shuhada tayi tace to Allah ya shirye ki amma dan Allah karki sake kunna kiɗan nan dry ra'eesa tayi tace to naji bazan kunna ba
Tashi shuhada tayi ta shiga bathroom domin tayi fresh up
Bata jima sosae ba ta fito ɗaure ta towel ta samu ra'eesa tana zaune tana shan chapman
Shuhada tace sannu yar hutu dry ra'eesa tayi tace yauwa inaso na fada miki ma anbude wani sabon waje anan bayan bypass din nan ana koyar da makeup girki kala kala ɗaurin dan kwali and others kuma fa a 2wks zaka iya komai harna karbo mana form din mu bakwai cikewa kawai zamuyi yaya rayyan da yaya anwar sunce zasu biya mana
Tabe baki shuhada tayi tace ni kuma wani kwalliya zanje koya?
Kallonta ra'eesa tayi ta kwashe da dry tace ayyo wato babu ruwanki da kwalliya sbd kina da kyawun fuska amma ai dr shuhada masu iya magana sunce idan kana da kyau ka qara da wanka kuma fa wlh harda kayan kamshi
Jinjina kai shuhada tayi tace to shikenan Jounalist amma naji kince mu bakwai naga kuma mu shida ne ko anty binayya ce ta bakwai din?
Ra'eesa tace ina kuwa auta ce tasa rigima wai itama asa sunanta shine yaya mashkur yace asa da itama murmushi shuhada tayi tace Allah sarki my sabah tana inane
Ra'eesa tace tana gidan abbu nan dai suka cigaba da hiran su zuciyar shuhada cike da tunanin gwaggo mairo da antynta haula da aminiyarta hindu ko anyi auren hindu oho
Ko da shuhada ta fadawa yaya fauzan akan cewa zasu fara zuwa training na 2wks yace ba damuwa dan haka taɗan dakata da zuwa asibity sbd girki ma adon mace ne
Ba tare da bata lkc ba suka fara zuwa training sosai kuma suke ganewa masha Allah tun a kwana goma aka zabesu amatsayin gwanaye barin ma shuhada
Ranar da aka yayesu ma ansha shagali
Zaune suke adaki dukkan su suna hira zeeyadat tace amma fa wlh anty sarah din nan tana da kirki mihik tace sosai ma ki gafa harda bawa sis shuhada kyautar kit ra'eena tace ai haka akeso wlh gashi dai mun karbi first class
Shukra tace aifa kam dazu kunga kallon da anty binayya take bin shuhada dashi kuwa mihik tace ni kuwa nagani narasa gane wani irin kalar kiyayya anty binayya take yiwa shuhada ba murmushi shuhada tayi tace ba komai fa kawai dai inaji banyi mata bane tsaki mihik tayi tace saika ce ita tayiki kinga dai yaya burleey baya son mgn ko wasa baya dry ko hayaniya amma baya da girman kai kullum sai yayiwa anty binayya fada akan halinta
Tabe baki shuhada tayi ta ɗago kai ta kalli ra'eesa wanda duk wannan hiran da akeyi ko uhumm bata ce ba hankalinta kwata kwata baya wajansu
Ta bata shuhada tayi amma shuru saida ta girgiza ta tukunna afirgice tadawo hayyacinta tana kallonsu idonta harya dan canza kala
Hankalinsu atashe suka hau tmbyarta meyake damunta domin duk abinda zaisa ra'eesa shiga damuwa ba qaramin abu bane
Ra'eena harta fara hawaye tana cewa dan Allah yar'uwata ki fadamin abun dake damun ki
Kuka ra'eesa ta fashe dashi tace na shiga ukuna zuciyata bata min adalci ba rungumeta ra'eena tayi tana lallashinta tana tayata kukan
Cikin tashin hankali zeeyadat tace wai dan Allah ra'eesa sai kinga dukkanmu mun fara kuka kafin ki fada mana abinda ke damunki idan har baki fada mana ba kina da wa inda zaki fada musu sama da mune dan Allah kibar wannan kukan ki fada mana meya faru
Shuhada ta riqo hannunta itama hawaye takeyi cikin sanyin murya tace plss ra'eesa tell us what's wrong with u pls?
Ra'eesa ganin gabaki daya hankalinsu yatashi ne yasata fara mgn cikin muryarta harta dashe sbd kuka
Dana sani da ban fara zuwa wajan koyan makeup dinnan ba dana san zuciyata zata min rashin adalci da ban cike tawa form din ba dana san cewa zan hadu da *khalid* harya furta min kalmar *so* da banje ba
Cikin tashin hankali ra'eena ta saketa atare suka miqe tsaye dukkan su amma banda shuhada suka hada baki gami da cewa *Allah yasa dai ba tarkon soyayya kika faɗa ke da bare ba*?
Cikin kuka ra'eesa tace wlh na faɗa son khalid wanda bansan lkcn da hakan ta faru ba
Mihik tace lallai kam kin ɗauko dala ba gammo kin san al'adar wannan familyn namu ba auren bare lallai akwai babbar matsala
Itadai shuhada ta kasa mgn
Zeeyadat tace ai kiyi gaggawar cire khalid aranki na tabbata kwanan nan za afara mgnr auran damu kinsan tsaurin kawu baba shida yayunsa da ƙannansa da yan uwansa abbu ko abbi ko abba babu wanda ya isa ya canza wannan aqi'dar saida nace miki tun farko karki kulasa amma kika cemin wai wulaqanci ba kyau akazo karban number nace miki aa amma kikayi kunnan qashi to ai yanxu ga irinta nan
Nan suka dinga zuzuta mgnr saida shuhada ta dakatar tasu tace haba dan Allah dame zataji kubarta taji da abu daya mn nan shuhada ta dinga lallashin ra'eesa tare da kalamai masu dadi na kwantar da hankalin har tabar kukan ta koma ana hira da ita amma jikinta duk yayi sanyi
Shuhada acikin ranta tace tofa anayinta kenan
Yau ta kama weekend dukkan su suna family house harda su ammy momma mamy abbu abbi abba
Dasu brother's gabaki daya anata hira ana raha
Kawu baba ya kalli shuhada yace matar mai kama dani akasa dry hajiya kaka ai saidai mai kama da kai din
Kawu baba yace ai nima tana kama dani zan bata mamaki
Abba yace su adeel sunce zasu dawo acikin sati amma basu fadi ranar ba kawai dai sunce acikin sati
Nan family aka hau murna yayinda gaban shuhada ya buga haka kawai taji tana sonyin tozali dashi dan ko a pic bata taba ganinsa ba
Kawu baba ya kalli shuhada yace matan kishiya ne zai dawo kar akasani fa
Aka kwashe da dry binayya kuwa tashin hankali ta shiga jin kalaman da kawu baba yake fadi badai yana nufin zai hada wannan shegiyar mai kama da ya'ya'n aljanu aure da yaya adeel ba lallai kuwa da antaro masifa dan yaya burleey nata ne ta jima tana rainon soyayyarsa acikin zuciyarta
Haka aka gama hira aka watse
Bangaren su burleey kuwa shirye shirye suke zasu dawo gida domin sunyi missing din family shekara biyar fa ba wasa ba
Jb ne tsaye yana kallon akwatyn sa wanda ra'eesa tayiwa aiki domin yana nan bai manta ba kuma ya mata tanadin horo mai tsanani ranar da. Allah ya saukesu lpy agida
Bangaren ra'eesa kuwa ita harga Allah tama manta da ta yaga wasu kaya
************
Yau ta kama laraba
Tsaye suke a babbar airport din garin kaduna ko wannen su yasha jarket idanunsu sanye yake da black shadow sun rataya jaka abayan su ahankali suke taku cike da izza da jin kai wani irin farin ciki sukeyi wanda baya misaltuwa
Basu tsaya kiran mutanen gida ba suka tari taxi acewar su suna so ne suyi musu bazata kayansu suka loda abayan both suka Shiga suka cewa driver yakaisu unguwar. _malali_
_________________
Comments
And
Share
*by Mmn ahlan*✍🏻
[29/01 à 08:29] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*ᔕTOᖇY ᗯᖇITTEᑎ ᗷY*
*z̸a̸h̸r̸a̸ a̸b̸d̸u̸l̸* ( *m̸o̸m̸y̸n̸ a̸h̸l̸a̸n̸*)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*P*...2⃣3⃣↪2⃣4⃣
_a unguwar malali_
agate din family house driver yayi parking jb sadam suka fito suna murmushi amma jb wani murmushin nasa harda mugunta
Sadam ya leqa ta window yacewa burleey kai bazaka fito bane ?
Ahankali burleey yafara zura kyawawan kafafunsa akasa yana fitowa sadam yayi gaba burleey nabinsa abaya jb yacewa drivern ya jera musu kayan su awajan za azo ashiga musu dashi driver yace to jb ya sallame shi yabi bayan yan uwansa
Mai gadi yana kallon su aransa yace to wasu baƙin labarawa kuma yau mukayi agidan bai gama tunaninsa ba sadam yace barka da wannan lkcn baba sambo
Da sauri ya miqe domin yagane muryan sadam nan ya shiga yimusu sannu da dawowa suka amsa gamida gaishesa shima ya amsa yana cewa gaskiya munyi kewarku ba kadan ba sadam yayi murmushi yace muma haka munyi kewarku dan Allah baba sambo kayiwa su nasiru da kamalu magana a shiga mana da kayan mu sannan agyara mana parts dinmu
Baba sambo yace to ba damuwa yafice shi kuma yabi bayan yan uwansa domin tuni suka yi gaba abinsu
Hajiya kaka dake zaune a parlour tana kallon tv sukayi sallama jin muryan su tayi wanda ko a bacci taji zata gane mazajenta ne suka dawo da gudu ta tashi har tana tuntube ta rungume su tsantsan murna da farin ciki bakin ta ya qi rufuwa kira ta hau kwalawa masu aikin gidan ta juyo taqara qura musu ido kawai saita fashe da kuka burleey ya riqo kafadarta yace haba matar mene kuma abin kuka sadam ya hau share mata hawayen cikin tsokana yace ashe dai zamu dawo mu taddaki baki wuce ba ina kawu tsoho dry tayi tace ja'iran yara ba saiku kashe mu ba ai harta ya'ya'n ku sai mun gani zo nan ku zauna
Taja hannun su tana cewa ina sadam ?
Gani nan matar ya fada yana dry da sauri hajiya kaka taje yimasa oyoyo shima duk sun qara zama wasu haziƙan samari daidai nan kawu baba ya fito dan jin hayaniya duk yan family house an fito an zagayesu maza da mata ana murnan dawowar su kafin kace me anjere musu kayan maqulashe agaban su rungume kawu baba sukayi dukkan su suna dryn farin cikin kai gaskiya family sunyi indai akwai hadin kai to ba shakka akwai kwanciyar hankali gaishe da kawu baba sukayi atare kawu baba ya goge hawayen farinciki masha Allah Alhamdulillah shine kawai abinda kawu baba yake iya nanatawa yana shafa fuskokinsu nan suka gaishe
Da sauran yan uwa iyayen su da wasu yayunsu
Jb sai ware ido yakeyi inda zai hango ra'eesa har wani cije baki yakeyi
Yana saka da warwara domin abinda zai mata saita gwammaci kiɗa da karatu
Sadam yace ina yaran nan suke na tabbata yanzu kam sun girma hajiya kaka tace suwane kenan ai naga suna dayawa yace ok hakane fa ina nufin su twins din ammy dasu zeeyadat dasu mihik
Hajiya kaka ta kwashe da dry tace ayyo wasu sunje makaranta wasu kuma sunje aiki
Jb yace kai tsohuwa wannan yaran ne za ace wasu sunje aiki ? Duka duka nawa suke da zakice sunje aiki wama zai ɗaukesu aiki ? dama dai makarantar kawai kike ce
Hajiya kaka ta riqe baki tace suwaye kake kira da yara iye mai gidan ? saida ya yatsine fuska kafin yace suwaye kuwa idan basu zeeyadat da shukra ba ? Sadam yace to ina kabaro mihik ai itace karaman su
Hajiya kaka tace tab lallai ma dan baku gan yanda suka zama yan mata bane shiyasa ai ko sabah yanzu baza ace mata yarinya ba jb yace ai wlh na tabbata ko da kowa zaiyi hankali ya natsu har yaje aiki to banda wannan yarinyar ya faɗa yana cije baki hajiya kaka tace wacce yarinya kenan?
*ra'eesa* ya fada atakaice hajiya kaka tace tab yar'jarida zaka ce ra'eesa da take zuwa aiki yanzu fa ita yar'jarida ce karku raina min jikoki daga zuwan ku ku bari sudawo ku ganewa idanuwan ku
Kawu baba yace wato har yanzu bazaku tambayi matata shuhada ba ko ? gaban burleey ne ya buga tun shigowar su yake wulla ido ko zai ganta amma bai ganta ba ko da yake ai fauzan ya fada masa suna zuwa asibity tare maybe suna can tunda ko su fauzan din ma basu gida to ma nasanta ne ? ko na taba ganinta ne? to ai da zanga bakuwar fuska shi kadai yake mgnrsa acikin zuciyarsa to ma meyasa zan damu mtswww yayi tsaki
Kawu baba yace kai kuma burleey mutane suna hira ana dry amma kai sai wani yatsine fuska kakeyi miye hakan to harda kuma tsaki ?
Wata kasalalliyar murmushi yayi ya taso yazo kusa da kawu baba ya zauna ya ɗora kansa akan kafafun kawu baba yace tsoho mai ran karfe nagaji ne wlh ko mgn bana son yi kawu baba yayi dry yace to ai shikenan hajiya kaka tace kai dai burleey ka shiga uku wlh tashi yayi domin idan bai tashi ba yanzun nan zata fara yimasa sababi
Hanyar fita a parlorn ya ɗauka kawu baba ya dakatar dashi ina kuma zakaje?
Batare da ya waigo ba yace nayi missing din mommana da mamyna tare da ammyna zanje na gaishesu ne naga lpyrsu lafin su abbi sudawo kasan shekara biyar ba wasa ba jb ma da sadam miqewa sukayi domin iyayensu suna yimusu alkunya wai sbd sune ya'ya'n farko suka bi bayan burleey kawu baba yayi dry yace kinga yanda suka zama saika ce masu mata ?
Hajiya kaka tana murmushi tace ai yakamata yanzu ace anfara mgnr aure tunda sun dawo kawu baba yace na gama yanke shawara akan su su duka hajiya kaka tace tame kenan ?
Murmushi yayi yace idan lokaci yayi zaki gani
Saida suka fara shiga gidan abba suka gaishe da momma sannan suka shiga suka gaishe da mamy kafin sukayi gidan abbi suna shiga suka samu sabah tana zaune tana kallon tv sallama sukayi sabah ta tashi da gudu tana cewa oyoyo gasu yaya ammy !ammy ! da gudu sabah ta rungume sa tace sannu yaya adeel ya hanya juyawa tayi tayiwa yaya sadam da yaya jb oyoyo
Sadam yace kai auta kece kika dawo haka a shekara biyar? rufe fuska tayi jb yace eh lallai kam sabah an girma shekaran ki nawa ma yanzu ? cikin dry tace am 12yrs old now burleey yayi murmushi ya shafo kanta saiga ammy ta sauko tana dry ah ah ah lale marhaban da yan'ƙasar Indonesia shine ko ku fada mana muyi muku girke girke kala kala ?
Rungumeta sukayi gami da gaisheta ammy ta amsa tana dryn farinciki tace ah bari na shiga kitchen na shiryawa ya'ya'na special food
Yanzu ra'eesa zata dawo saita tayani muyi muku girki burleey yace yanzu ma mamy da momma suka ce zasuyi mana girki mukam dai yan' gata ne sadam jb suka miqe tsaye suna cewa ammy bari muje mu watsa ruwa ammy tace to afito lpy kar dai ku dade jb ya duba agogon hannusa yace oh my god gashi har karfe 6 fa sadam yace kawai mu bari idan akayi sallar isha'i sai muci abinci gabaki daya jb yace inaga hakan zamuyi ammy idan angama duka kawai akai family house ammy tayi murmushi to my son's lkcn ma kowa yadawo sai ayi hira sukayi dry sannan suka fice sabah tace yaya adeel wlh ka qara kyau sosae murmushi yayi ya shafo sajensa yace kedai har yau kina nan da surutun ki ko
Tashi yayi yabi bayan ammy wanda tashige kitchen zuciyarta cike da farin cikin ganin babban ɗanta wanda takejin sonsa har can maqogoron zuciyarta sallama yayi a kitchen din ta waigo ta dubesa fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa kwantar da kansa yayi akan kafadarta ammy i miss u so much haqiqa duk wanda ya rasa uwa yarasa babbar masoyiya i luv u very very much ammyna
Murmushi ammy tayi ta shafo fuskarsa cike da shauki tace i miss u more my son Alhamdulillah kun dawo gida lpy Allah ya albarkace ku Allah ya sanya alkhairi a ilmin ku Allah yasa ku zama abin alfahari wa al'umman Annabi S,A,W
Sosae yaji dadi yace insha Allah ammyna ameeen bari naje na watsa ruwa tace to afito lpy kaga magrib ya kusa karka juma yafice yana cewa to ammyna
Bayan ya fita da minti biyar ra'eesa tayi sallama a parlorn fuskarta ba walwala domin yanzu ta rasa meke mata dadi soyayya yasakota agaba kullum wutar son khalid ruruwa yakeyi acikin zuciyarta amadadin ta ciresa amma sai qara shiga zcyrta yakeyi
Sabah ce ta tashi tana dry ra'eesa tace lpyr ki kuwa? Wannan dry haka
Sabah tace su yaya burleey sun dawo
Wani wawan faduwar gaba taji nan take takardun dake hannunta tare da handbag dinta suka fadi ƙasa ta dafe qirji ta zare ido tace su yaya burleey dai ?
Sake baki sabah tayi tace ehmana anty ra'eesa baki murna ne ammy ce ta fito daga kitchen tana cewa yawwa ra'eesa kin dawo jeki cire kaya kizo ki tayani girki kafin ra'eena da shuhada su dawo yayunku sun dawo kinga yanzu za a kira sallar magriba
To ta amsa dashi asanyaye kafin ta gaishe da ammy
Ammy tana amsawa tana komawa kitchen
Sama ta haura ta cire mayafinta ta ɗauki wata doguwar riga marar nauyi tasa tasaka hula ta fito kenan saiga sabah ta ɗauko mata handbag dinta da takardunta data zubar dasu a parlorn bata ɗauko ba tace ayya sannu auta namanta ne ban ɗauko ba murmushi sabah tayi ta shige dakin ita kuma ta wuce kitchen wajen ammy suna girki
Saida aka kira sallar magriba tukunna ra'eena ta shigo agajiye kamshin abinci taji dan haka tayi hanyar kitchen ta samu ammy da ra'eesa suna girki ra'eena tace sannu ammy ina wuni yagida?
Lpy lau dr ra'eena ya skull din ? Murmushi tayi Alhamdulillah ammy yau abbi zaiyi baqi ne ?
Aa yayun ku ne suka dawo
Shagwabe fuska ra'eena tayi tace kai ammy yau kuma su yaya fauzan da yaya mashkur ake yima wannan abinci haka ?
Ammy tace su adeel da sadam da alh ƙarami dai tsalle ra'eena tayi tace sun dawo ? Ammy tayi dry tace eh sun dawo dazu nan itama ta hau tayasu domin sun kusan gamawa bayan sun gama ammy ta kalli ra'eena
Tace ra'eena meke damun ra'eesa?
Ba ra'eesan ba harta ra'eena saida gabanta ya fadi cikin inda inda da in'ina am eh um oh am ammy kinga wani abu ne ? tsura musu ido ammy tayi tana musu kallon tuhuma duk sun gama ruɗewa da kyar ra'eesa ta kwaqulo murmushi tace babu abinda yake damuna fa ammyna girgiza kai ammy tayi tace kuje kuyi sallah ai da sauri suka fita a kitchen din bin bayan su da kallo ammy tayi ta girgiza kai lallai akwai abinda yake damun ra'eesa sannan dole ra'eena tasani
Sai da akayi isha'i tukunna shuhada suka dawo ita da yaya fauzan faduwar gabanta ya tsananta suna shiga sukaga ana fita da kulolin abinci kala kala shuhada azuciyarta tace to ko anyi baki ne ta tambayi kanta
kamar yanda ta sa ba kullum dakin ammy taje ta gaisheta taga yau tana cikin walwala ammy tace sannun ku yau kun jima shuhada tace wlh ammy aikin yau din nan sai ahankali
Gabaki daya agajiye nake ammy zatayi magana yaya fauzan yace sannu raguwa ammy tayi murmushi da tace aa wlh shuhada ba raguwa bace karka sake cewa yarinyata raguwa
To bazan sake ba ammy ina wuni
Lpy lau ya hospital din ?
Alhamdulillah
tashi shuhada tayi tana cewa nabarki lpy ammyna
To my doter ahuta gajiya yaya fauzan yace ammy naga masu aiki suna wucewa da abinci anyi baqi ne? ammy tace su burleey ne suka dawo da sauri fauzan ya tashi shuhada kuwa burki taci gabanta na faduwa ammy tace shuhada lpy kuwa ?
Da kyar ta tattaro natsuwarta tace eh ammy ta fice da sauri
Adaki ta samu su ra'eena ra'eesa suna rigima akan abu daya sallama shuhada tayi ra'eena tace yauwa sis dan Allah kizo kiyi mata magana wlh ammy harta fara ganowa
Shuhada tace bari nayi wanka nikam agajiye nake baku san aikin danayi bane wlh likitoci suna mugun kokari ta ajiye handbag dinta
Ta shige toilet
Wayar ra'eena ce ta ɗauki ruri tana dubawa taga sunan *lvly zeedi* ɗauka tayi zeeyadat tace wai kuna inane kam mu fa tun daxu muna family house dukkan mu ra'eena tace gamu nan zuwa zeeyadat ta katse wayar
Kayan bacci suka saka suka sa hijab har ƙasa haka kawai ra'eesa gabanta sai faduwa yakeyi jb kuwa yana can yana jiranta domin agabansa kanwarsa ta kirasu raeena tace gasu nan zuwa ita kuma ra'eesa ta manta da tayi ba'rna
Tsaye suke suna jiran shuhada domin ammy ta shigo tace su fito su abbi ma sundawo har sun tafi family house ammyn ma ta wuce
Shuhada tana fitowa tagansu atsaye tace yana ganku tsaye kunsha hijab ra'eena tace kiyi sauri ki shirya muje family house
Haka kawai shuhada taji bata son zuwa a raunane tace kuje zanzo ra'eesa ce tafara yin gaba qirjinta na dokawa ra'eena ta kalleta tace karki jima dan Allah nasan sai kawu baba ya tambaya idan yaganmu bai ganki ba tace to kafin ra'eena ta fice adakin itama
Zama shuhada tayi akan kujeran dreesmirrow ta saki ajiyar zuciya mai nauyin gaske ta lumshe ido tarasa dalilin dayasa taji bata son zuwa bodylotion ta shafa tayi sallar isha ta kashe light din dakin ta kwanta ta lumshe ido tana son ganin yaya burleey dinnan amma bazata jeba tunda yadawo ai dole zasu hadu
***********
A family house kuwa an cika aparlorn kawu baba domin duk gidan parlornsa yafi girma banda hayaniya babu abinda kakeji natashi kaman gidan biki
Sallama su ra'eena sukayi da sauri jb ya ɗago idonsa ya ɗaurasu akan fuskar ra'eesa wanda kanta yake sunkuye cije baki yayi
Gaishe da jama'ar parlorn sukayi ra'eena taje kusa da yaya sadam ta zauna tana murmushi shima murmushin yakeyi tace yaya sadam sannun ku da dawowa yaya jb ya hanya brox adeel ya hanya
Adeel yace lpy lau sister jb ma ya amsa da lpy lau sadam ma haka yatsine fuska ra'eesa tayi tana cije baki ta gaishesu jb ya tashi da sauri ya kamota oyoyo my ra'eesa ya rungumeta duk parlorn ansha mamaki wasu kuma dry suka kwashe dashi ra'eesa kuwa suman tsaye tayi saketa yayi yaja hannunta suka zauna yana murmushin mugunta nan aka cigaba da hira
Binayya ce ta shigo taci uban kwalliya saika ce zataje gasar kwalliya ko kyau makeup din bai mata ba tunda lkcn dasu shuhada ke zuwa ita girman kai ya hanata zuwa farin fatar ta ce kawai ta rufa mata asiri sai wani taku takeyi cike da yauqi har gaban burleey taje ta zauna tana wani fari da ido yaya adeel dina sannu ya hanya gasky nayi kewarka sosai jb yace mu kuma daba kiyi tamu ba kice mu koma mana juya ido tayi cike da kilbibi tace ni binayya na isa yi hakuri broz dina shi dai burleey tunda yace lpy yayi shuru da bakinsa ya kau da kai sai rarraba ido yakeyi ko zaiga shuhada amma bai ganta ba
Binayya kuwa ba qaramin dadi taji ba da bata ga shuhada ba har addua takeyi Allah yasa kartazo
Kawu baba ya juya ya kalli su ra'eena yace ina matar take?
Aqufule binayya tace wace ? ai naga duk family gamu anan saidai ko bare ake tambaya
Wani banzan kallo kawu baba ya wurga mata a tsawance yace karki sake kiranta da suna bare na gargadeki *shuhada* tafi karfin bare acikin wannan family
Mahaifin binayya ne yayi magana yace kawu baba kayi hakuri ke kuma binayya karki sake domin kawu baba bai taba tunzura haka ba ran binayya idan ya kai dubu yagama baci wata sabuwar kiyayyar shuhada ce ta taso mata tana hadiyewa mai mugun ɗaci
Kawu baba yasake tambayarsu ra'eena ina *shuhada* asanyaye ra'eena ta bude baki tace da tare zamuzo sai tace mufara gaba zata zo bansan me ta tsayayi ba
Burleey aransa yace to meta tsayeyi?
Yaya fauzan yace ko ta kwanta ne dan wlh yau tasha aiki a asibity ammy tace bari naje na dubata kawu baba yace aa abarta idan tazo shikenan idan ma batazo ba akwai gobe
Jb ne ya tashi ya kama hannun ra'eesa yace my sweet kanwa zo muje na taho miki da tsarabar ki muje ki karba mamy tace to bazaka bari sai gobe ba meyasa dole sai yau ko yanzu?
Kawu baba yace ah mutum da kanwarsa
Momma tace aidai naga ba ita kadai bace kanwar tasa gama yar uwarta nan ra'eena amma zai kama yajata ita kadai
Murmushin gefen baki jb yayi yace momma ita tata ta musamman ce muje my sweet ya fada yana kashe mata ido daya banda faduwar gaba babu abinda zuciyar raeesa keyi
Suna fita kawu baba yayi wata murmushin da shi kadai yabarwa kansa sani
_________________
🌚🌚🌚dan Allah karkuce komai makaranta ya sakoni agaba gashi ina zango mai wahala ku tayani addua plsss
__________________
Comments
And
Share
_by mmn ahlan✍🏻
[29/01 à 08:32] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*ᔕTOᖇY ᗯᖇITTEᑎ ᗷY*
*z̸a̸h̸r̸a̸ a̸b̸d̸u̸l̸* ( *m̸o̸m̸y̸n̸ a̸h̸l̸a̸n̸*)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*P*...2⃣5⃣↪2⃣6⃣
Part dinsa direct ya wuce da ita kai tsaye har cikin bedroom yana shiga yasawa kofar key ya sake hannunta ya juyo yana kallonta ya haɗe rai sosai kujeran dake dakin nasa ya zauna yana cigaba da kallon fuskarta
Ita dai ra'eesa tana tsaye kamar gunki
Muryarsa a daqile ya mata nuni yace bude wancan trolley din kayan tsarabar taki suna ciki
Atsorace tana ɗari ɗari taja trolleyn ta bude afirgice ta miqe tsaye tana ja da baya sai yanzu ta tuna lallai idan ba guduwa tayi ba yau kam tasan kashinta ya bushe tayi hanyar kofa ta hau jijjigawa sbd tashin hankali domin yanda taga ya haɗe ran nan tasa ubanta zataci
tsawa ya daka mata idan kike sake kika balle min kofa to wlh abinda zan miki sai yafi haka tunda ke baki da mutunci tashi yayi fuuuu amatukar fusace yayi akanta kafin ya karaso ta duqa awajan ta fara kuka tana basa hakuri
Gashin kanta ya damqa da iya karfinsa jitake kamar ranta zai fita saura qiris ta saki fitsari sbd azaba murya a tsorace tafara basa hakuri dan Allah yaya jb kayi hakuri wlh bazan sake ba tsautsayi ne
Murmushin gefen baki yayi ok tsautsayi ko ? kin jima kina min bar'na nida adeel sbd idan kinyi laifi muna miki hukunci saboda ki gyaru amma shine kika raina mu dama inaji da haushin fasa min glass din mota da kikayi da kuma sace min tayar motar abokina duk tara ki nakeyi shine bai isheki ba kayana dana shirya zanyi tafiya kika yage mun su tas da almakashi sbd ke baki da kunya to yau zanyi maganin rashin kunyar taki ta yadda idan kinji ana mgnr kayan jibril zaki bar wajan da mugun gudu
Wayarsa ya ciro ya kira zeeyadat tana dauka yace
tashi acikin mutane tashi tayi ta koma gefe sannan yace idan har aka tambayi ra'eesa kuce tayi bacci adakin ku kusan yadda za ayi kar agane tana dakina idan kuma kikamin ko kuma nace kukamin abinda ba haka ba wlh wlh wlh kinji na rantse ko to jikinki ko jikinku zai gaya muku yana gama fadin haka ya katse wayar ya juya yana kallon ra'eesa wacce take rusan kuka tun baikai ga yimata hukunci ba
Zare da allura ya ɗauko ya miqa mata yace alfarma daya tak zan miki shine yadda kika zauna kika yage kayan nan haka zaki zauna ki ɗinka su tsaf inba haka ba ra'eesa saina miki dukan da bazaki moru ba
Cikin kuka tace yaya jb taya zan dinka su ?nida ban iya ɗinki ba
Ta yadda kika yagesu haka zaki ɗinka su ok lokacin da kike yagamin ko nace lokacin da kike bar'na bakiyi tunanin zaki gyara su ba ? kinyi tunanin tunda zanyi tafiya kin yage banza ko? to ban manta ba oya maza fara ɗinka kayan nan yanzun nan kafin raina yaqara baci
Zama zatayi ya dakatar da ita ta hanyar cewa No No karki kuskura ki zauna a tsugune zaki ɗinka kayan nan idan kika zauna ai ma ban hukuntaki ba kenan ra'eesa ta juya ta watse masa harara dan tagaji da wannan abun nasa goge hawayenta tayi tace
Wlh nidai bazan tsuguna ina ɗinka kaya da zare da allura ba haba dan Allah wannan wani irin mugunta ne dan na yaga maka kaya ai kai ka fara ana gobe yaya burleey zaiyi tafiya ya zane ni kaima kuma ana gobe zaku tafi ka rankwashe ni bayan ni babu abinda nafi tsana sama da rankwashe shiyasa nima na rama ta qarasa tana murguda masa baki
Wani wawan mari taji ya sakar mata abakin kafin tadawo hayyacinta ya sake ɗauketa da wata marin nan ta zube kasa saida taga stars sun gifta mata a ido bakinta ya fashe sai jini
Belt ya zaro ya ɗaga ya zuba mata daya biyu ihu raeesa tasa wayyo jama'a zai kasheni zagaya dakin suka hauyi dataga tabbass zata ji jiki tunda ta tunzura shi ta hau basa hakuri
Dan Allah yaya jb kayi hakuri wlh zan ɗinka kalli fa ka fasa min baki ka kumbura min jiki karka min illa wlh zan ɗinka ka dubi Allah da Annabi manzon Allah S,A,W kabarni zan ɗinka
Jefar da belt din yayi domin duk horon da zai mata shi bai cika son ya daketa ba amma duk yadda kayi da raeesa sai tasa ranka yabaci toilet ya shiga ya barta nan tsaye tana matsar hawaye ga jikinta namata raɗaɗi leqowa yayi yace wlh idan kika sake na fito baki fara ɗinke kayan nan bako hummm sunan ki sorry kuma a tsaye zaki ɗinka su yana gama fadin haka ya koma toilet
Da sauri ta dauki kayan ta hau ɗinkewa tana kuka duk da bata wani iya ɗinkin ba
Ai mugunta ne zai ce mata ta dinkasu da hannu gashi kuma a tsaye har ya fito wanka ɗaure da towel a kugunsa daya kuma a hannun sa yana goge jikinsa kallon sa tayi suka haɗa ido tayi sauri rufe nata idon yace kin taimaki kanki yarinya
ya wuce yaja stool ya zauna ya shafe jikinsa da mai ya ɗauki pajamas dinsa yasa ya feshe ilahirin jikinsa da pefurm yafice adakin ya kulleta dan karta gudu parlor yafito ya tada sallahn nafila harya idar
yadawo ya sameta tana tsaye tana ɗinka kayan kafafunta sun gaji zogi kawai suke mata har wani layi ta fara gadon sa ya wuce ya kwanta yabarta awajan ko kallonta ma baiyi ba
Tace yaya jb dan Allah ka taimaka min naje na kwanta gobe saina qarasa
Ɗaga kai yayi ya watso mata harara kafin yace lkcn da kika yagasu a lkc daya kika yaga ko kuma kinfara ne da washe gari kika qarasa ? Shuru tayi tana zazzare idonta da suka ciko da kwalla murmushin mugunta yayi ya tashi ya ɗauko wata zabgegiyar bulala yazo gabanta ya damki bakinta ya matse tayi qara yace idan har kika sake na tashi da asuba baki gama ɗinke kayan nan ba wlh kinji na rantse ko hummm saina miki dukan da bazaki qara gane suwaye suke kanki ba yana gama fadin haka ya ajiye bulalar akan dressmirrow ya koma ya kwanta
Haka ra'eesa ta cigaba da ɗinka kayan tana kuka gashi wayarta ta barsa agida balle ta kira akawo mata agaji kuma tasan halinsa sarai idan har bata tsaya ta dinka ba tabbas zataci na jaki abanza haka ta cigaba da ɗinka kayan tana guntun kuka tana kallonsa ya lumshe ido yafara bacci
Bangaren su zeeyadat kuwa ta fadawa shukra yadda sukayi da yaya jb dan haka tun kafin agama hira sukayi sallama da mutanen family house sukayi gida gabansu na faduwa
Itama mihik tashi tayi tacewa sabha ta tashi su tafi gobe akwai skull domin sabah tare suke kwana da mihik suma dai sallama sukayiwa yan family house suka wuce gida
Ina tunanin me ra'eesa tayiwa yaya jb har ya jata zai mata hukunci ? Shukra tace ai wlh tunda naga take taken yaya jb harda yiwa ra'eesa oyoyo da jan hannunta wai tazo ta karbi tsaraba nasan cewa akwai matsala ita kuma da shike batan basira ya kamata alokacin saita bisa zeeyadat ta kuma cewa eh nikam mu rufawa kanmu asiri muyi abinda yace inba haka ba wlh yaci ubanmu domin har rantsuwa yayi shukra tace humm Allah ha fitar dake raeesa amma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kece kika jawa kanki Allah ya kyauta dai cewar zeeyadat ta kwanta tana tunani
Bangaren ra'eena tajira ra'eesa harta gaji mamy ta hau fada tun dazu ina alhji karami ya tsaya da ra'eesa mamy har kiransa tayi awaya lkcn harya fara bacci ya tashi y sameta ta zauna tana kuka saida ya toshe mata baki tukunna ya dauki wayar mamy tace wannan wani irin iskaci ne kaja yarinya ga yar uwarta tana jiranta zasuje su kwanta kasan gobe akwai aiki ra'eena kuma tana da skull
A kasalance yace mamyna tun dazu fa ra'eesa tabar dakina nikam ma fa harna fara bacci saidai ko a tambayi su zeeyadat ko suna tare mamy batare da tabasa amsa ba ta kashe wayar ta kira zeeyadat tana ɗauka mamy ta hau tambayarta akan cewa suna tare da ra'eesa ne cikin rawar murya zeeyadat tace eh suna tare har tayi bacci ma mamy tace atasota ga raeena tana jiranta cikin zeeyadat ne ya ɗuri ruwa gabanta ya fadi shikenan ta mutu muryan kawu baba taji yace aa abarta tunda tayi bacci nan zeeyadat tayi hamdala
Ra'eena da ammy da abbi suka koma gida ra'eena taje ta samu shuhada tana bacci hankalinta kwance girgiza kai tayi itama ta kwanta akan gadonta
Ra'eesa kuwa batayi bacci ba gashi duk ta sossoki hannunta da allura yatsunta sun kumbura sunyi ja wani ma har jini yakeyi idonta ma haka harta fuskarta saida yatashi kafafunta ma duk a kumbure suke sbd tsayuwa atakaice dai ra'eesa wahala taci da asuba daya tashi yaganta yayi banza da ita saida yaji an shiga sallah tukunna ya kira zeeyadat da shukra
Yace suzo yanzun nan ai ko sai gasu a 3mnts
Suna zuwa suka ga ra'eesa atsaye idanunta sunyi luhu luhu kafafunta ma sunyi fushi jb yace ku jata kubar min nan wajan ahankali raeesa ta hau jan kafarta Wanda suke mata zogi jitake kamar basu gangar jikinta juyawa tayi suka haɗa ido aranta tace dabadin bazan iya gudu ba to da saina maka Allah ya isa mugu horror kawai kuma ka rubuta ka ajiye saina rama azaban da kamin dabadin su zeeyadat sun riqeta ba aida ta fadi suna shiga daki ta zube akan gado ta saki kuka Allah isa mugu horror kawai wlh saina rama mutum gashi da haske amma zuciyarsa baqi
Sudai zeeyadat ido kawai suke binta dashi tunda basu san meya faru ba shukra ce ta hada mata ruwan zafi tayi wanka ta gasa jikinta sannan tayi sallah
Zeeyadat taba ta
paracetamol tasha ta kwanta sbd zazzabin dake taso mata batajin zata iya zuwa aiki yau
Bangaren su shuhada kuwa da washe gari shuhada tana shirin zuwa hospital ra'eena ke bata labarin abinda ya faru a family house jiya abinda binayya ta fada da amsar da kawu baba yabata atsawace
Allah ya kyauta kawai shuhada tace taja bakinta tayi shuru domin taga alama nan gaba kadan binayya zata iya korata agidan ma gabaki daya
Ammy ce ta shigo dakin take cewa ra'eesa bata shigo bane suka ce eh bata shigo ba
Ammy tace to bazata je aiki bane yau ko yayane ?
Ra'eena tace bari naje na dubata ammy tace aa barta kawai ai tafimu son aiki
Ko da shuhada ta gama shirinta na zuwa aiki basu hadu da burleey ba dan haka yaya fauzan yana fitowa suka shige mota suka tafi
Ra'eesa zazzabi ne ya kamata wuni tayi tana bacci saida ta tashi taqara shan magani harda na gajiya ta sake watsa ruwa tukunna taji jikinta yamata sauki mamy sai jera mata sannu takeyi domin su zeeyadat sun tafi makaranta tun safe
Saida suka dawo da yamma kafin suka rakata gida nan take basu labarin abinda tayi masa da abinda yamata jiya sannan taqara da cewa baza tabarsa ba saita rama zeeyadat tace baki da gaskiya acikin wannan maganar karki manta fa su yaya jb yayun mu ne bamu muke binsu ba kafin ni akwai yaya anwar shekara nawa yaya anwar yabani sannan yaya jb shekara nawa yake bawa yaya anwar karki manta fa yaya jb shine gaba da yaya burleey ma shin ke aganin ki daidai kikeyi ?kidinga yimusu rashin kunya yanzu fisabilillahi kafin yayi tafiya kika fasa masa glass din mota abokansa sunzo kika sace musu tayar mota ke anaki ganin daidai kike aikatawa ko ? kawai kiji da abinda ya dame ki ma yanzu na soyayya da baren da kika afka wanda bazaiyi lasting ba ko kadan
Shukra tace wlh baki kyauta ba saika ce bakije islamiyya ba ki kama ki yage sutura
Sutura fa raeesa
Ta bude baki zatayi magana taji wayarta na ruri da sauri ta ɗauko ta duba taga sunan *part of my lyf* ya bayyana wani murmushi tasaki kafin ta ɗauka wayar ta kara akunnata ta kwanta ta lumshe ido magana ya fara mata haba my happiness idan wani laifi nayi ai sai afadamin na bada hakuri jiya na kira ki yafi sau dari amma baki ɗauka ba yau ma na kira ki bila'adadin baki ɗaga ba hankalina yayi matuƙar tashi my luv ajiyar zuciya tayi kayi hakuri my lyf wlh nima ba ason raina nayi hakan ba jiya wani mugun yayana ne suka dawo wanda nace maka suna kasar Indonesia shine fa dan yamin abu na rama kafin yatafi ashe bai manta ba ni kuma namanta shine yajani ya tabani azaba jiya da daddare gashi dama da zanje family house dinmu banje da wayar ba duk atunani na bazan jima ba amma nima ai na azabtu da rashin jin muryar ka
Ajiyar zuciya yayi yace gaskiya dabadin yaya bane danayi masa hukunci sbd ya hora zuciyata da yawa murmushi tayi tace kamanta dashi kawai muryan ka ta kori komai nan suka cigaba da hirar su ayayin da yake cemata dan Allah karta bari a rabasu
Zeeyadat da shukra haushi ne ya kamasu sbd taurin kai irin na ra'eeesa kwata kwata ra'eesa batajin magana balle taji shawara cikin bacin rai suka tashi suka tafi
Bangaren burleey ji yayi ko ya tashi yaje asibityn ne ya ganta sbd da yashiga gaishe da ammy da abbi yake tambayar ammy akan cewa fauzan ya fita ne ammy tace sunje hospital mana shida shuhada kuma dama shi ai ba dan fauzan din ya tambaya ba kawai baya so ya tmbayi shuhadar kai tsaye ne ammy tayi tunanin wani abun to meyasa zuciyarsa takasa samun sukuni dole saiya ganta ? ya tambayi kansa
Amsar da zuciyarsa tabasa shine sbd fauzan yana baka lbrn ta tana da natsuwa da tarbiyya ilmi biyayya sannan ance kuna kama da wannan amsar ya gamsu shiyasa ya takura kansa dole saiya ganta
Da daddare dasu shuhada suka dawo raeesa ke basu lbrn abinda ya faru tsakaninta da yaya jb nan shuhada ta hau mata fada sosai akan ta nutsu
Tare da nasiha da lallabata ta janye mgnr saita ɗauki fansa da kyar shuhada tashawo kanta tace ta hakura
Wasa wasa saida shuhada ta kwashe kwana uku basu hadu da burleey ba harta family house din ma tadaina zuwa kullum sai kawu baba ya tambaya tana ina kawai sai a danganta hakan da tagaji ne tunda yanzu basu dawowa da wuri sai dare burleey kuwa ya damu sosai kodai yasa akira masa ita ne to idan tazo yace mata me kawai salon ya jawa kansa raini ai tun tana gidan shima yana nan zasu hadu ai da wannan tunanin ya hakura da son ganin nata
Yau ta kama weekend saturday musamman yan matan gidan suka shirya fita shan fresh air domin hutu sun tambaya an barsu sun kai su goma sha biyar dan harda wasu daga cikin ya'ya'n yan uwa na family house
Kwance take akan gado ra'eena da ra'eesa kuwa shiri sukeyi sunci uban makeup sunyi kyau gasu dama model ne doguwar rigar abaya suka saka iri daya nan suka fito asalin twins dinsu zeeyadat da shukra ma kaya iri daya suka saka abaya mihik da sahbah ma kaya daya suka saka sunyi kyau sosae
Ra'eena tace dan Allah sis shuhada meyasa kikace baza kije ba? Ɗago kai tayi ta kallesu tayi murmushi tace kuje wlh banajin dadin jikina ne gashi na tabbata idan aka fitan nan sai ankai yamma kafin ku dawo ni kuma banajin zan iya zuwa wlh muje kawai na rakaku family house nabi na gaishe da mijin da kishiyar ta tashi ta ɗauki hijab dinta ta saka suka fito atare
A gate suka hadu da yaya rayyan shida yaya anwar nan suka dinga tsokanar su wai wannan kyau haka my sisters kai gaskiya gidan mu akwai flowers zo nayi muku selfie Yaya rayyan ya kalli shuhada yace matar tsoho mai ran karfe yake naganki da hijabi raeesa ta shagwabe fuska tace yaya rayyan tace ita bazata je ba
Yaya anwar yace meyasa baza kije ba shuhada? murmushi tayi tace wlh yaya's bana son fita ne idan ba skull ba ko hospital nafi son na zauna agida abuna yaya rayyan yace ai su kam kafar yawo garesu hakan ma wai ana taka musu burki ya fada yana jan hancin raeesa tayi qara wai zai bata mata makeup raeena tace mujen ku dan Allah karmu maqara yaya anwar yace eh lallai raeena wato raeesa ta koya miki yawo ko? Dry ta hauyi tafara tafiya tace wlh ba haka bane kawai dai kawai dai dry su ma sukayi kafin suka shiga mota suka fice su shuhada sukayi family house
Sallama sukayi a parlorn nan aka shiga tsokanar shuhada wai tayiwa kawu baba saki biyar cikin dry tace inaa na isa na sake mijin guda hajiya kaka tace wai ma meya kawoki shuhada tace nazo ganin lpyr mijina da kuma kishiyata akasa dry ta gaishe da kawu baba da hajiya kaka da yan uwa
Cikin wasa kawu baba yace nayi fushi ai ta hau basa hakuri yace to na hakuri ai na ɗauka za ayi min shigo shigo ba zurfi ne aka kwashe da dry nan dai suka dan taba hira su ra'eena kuwa jip biyu sukayi kawu baba yace banda dai kula samari sukace to
Shuhada tun shigowarta taga binayya kwance a dogon kujera tana danna waya itama yanzu ta tattara ta ta watsar hajiya kaka tace ke kuma binayya yan uwanki sunfita amma meyasa kikace bazakije ba ? Saida ta yatsine fuska ta watsawa shuhada kallon ƙasƙanci tukunna tace bazan iya fita da yara bane hajiya kaka anjima idan adeel dina ya tashi zamuje tare dashi lokaci daya shuhada taji abu ya tokare mata qirji sbd abinda binayya ta fada amma ta ɗaure kawu baba yace kefa matar meya hanaki zuwa ?
Murmushi tayi tace wlh mijin bana son fitan ne kawai yau ranar hutu ce gwanda na huta abina miqewa tsaye tayi tace ai yau zanzo da dare bari nadan koma bacci kawu baba yayi dry to a koma lpy atashi lpy matar tace to mijin Allah yasa kishiyar sai anjima hajiya kaka tayi dry tace karki sake ki dawo
Harta kai kofar fita ta juyo tana dry tace ai dawowa ya zama dole hajiya kaka ta miqe shuhada ta fice da gudu tana dry ran binayya ya sake baqanta lallai wannan shi ake kira bako yazo yafi ɗan gida dole ta takawa shuhada burki ta tsaya amatsayinta ta bare
Gida ta koma taji gidan ya mata shuru domin ammy ba bata nan sunje unguwa dasu momma da mamy
Dakinsu ta wuce ta kwanta taji tanajin yunwa cire hijabin ta tayi english wear's ne ajikinta na dogon. riga yamata kyau sosae kuma ya kamata dan karamin veil ta ɗauko ta ɗaura akanta tafito harta zura kafarta zata taka step kenan sukayi Karo zata gangara yayi saurin janyota ta fada qirjinsa ɗan ƙaramin veil din da ta ɗaura akanta ya since ya fadi kasa gashin kanta ya zubo ya rufe mata fuska kamshin turaren su ya gauraye dana juna wani irin shock sukaji tunda ga zuciyoyinsu har izuwa gangar jikinsu take kuzarin dake tattare dasu suka nemesa suka rasa yana rungume da ita aqirjinsa yanabin gashin kanta da kallo ahankali shuhada ta sauke ajiyar zuciya wanda burleey yajita har can ƙasan ransa saida ta saita natsuwarta tukunna ta tashi daga qirjinsa kanta a sunkuye gashi ya rufe mata fuska rabawa ta gefensa tayi zata wuce yayi sauri riqo hannunta yadawo da ita gabansa suna fuskantar juna hannu yasa ahankaki yafara kwashe gashin dake fuskarta ya qura mata ido banda faduwar gaba babu abinda zuciyar shuhada keyi harya gama yaye gashin kyakkyawar fuskarta ta bayyana take bugun numfashinsa ya qaru ahankali itama ta ɗago ido ta kallesa take zuciyoyinsu ta shiga harbawa saida ta samu natsuwarta tukunna ta qarasa tattare gashinta ta ɗauki veil dinta araunane tace ina kwana? ta juya zata koma daki da sauri ya bude baki kamar baya son yayi magana yace inasu ammy dasu ra"eena batare da ta juyo ba tace su ammy sunje unguwa gaisuwa su ra'eena kuma sun fita shan iska tana gama fadin haka da gudu ta shige daki da kyar burleey yaja kafafunsa ya koma part dinsa ya kwanta ya lumshe ido shuhada kawai yake kallo tare da zazzaqar muryan ta itama bangaren ta hakan ce ta kasance domin ta tabbata ko tantama babu wannan shine yaya burleey ko ba a fada mata ba gsky guy din ya hadu shafa fuskarta tayi tace muna kama da kai to menene sirri ta fada tana danna kanta acikin pillow
*********
Da misalin karfe 2 na rana yana zaune a parlorn ammy shuhada kuma tana daki a hankali ya kira mai aikin ammy bara'atu ta amsa ta fito daga kitchen yace dan Allah hau sama kicewa shuhada tazo bara'atu ta amsa da to ta haura upstairs tana zuwa kofar ta tura tayi sallama shuhada tana kwance ta amsa bara'atu tace anty shuhada kizo inji yaya adeel gabanta yabada dumm ta dake tace to muje atare suka sauko kanta a duqe tace gani saida ya kai kusan minti biyu kafin yace ki dafa min indomie plss kinga su ammy dasu raeena basu nan banci komai ba tun safe cikin natsuwa tace to ta juya tayi hanyar kitchen ya bita da kallo ya jingina bayansa da kujera ya lumshe ido yana tmbyar kansa wai meke damunsa ne haka
Bata wani jima ba ta dafo masa indomien ta hada masa mango juice tasa a trey ta fito dashi tunda ta fara tahowa yasake zuba mata ido zata wuce ta kai masa dinning yace no kawo nan kawai
a carpet zan zauna naci ba tare da tayi magana ba ta nufo sa gabanta na faduwa durqusawa tayi ta ajiye a gabansa ta juya zata koma daki ta tsinkayo muryan sa *ASHSHUHADA* bakiyi serving dina ba dawo kici ka ladar ki
Shuhada ta kai kusan minti biyar tana tsaye sbd yanda ya kira sunanta wai *ashshuhada* gabaki daya saida tsiqar jikinta ya tashi ahankali ta dawo ta zauna agefen sa cike da natsuwa tafara zuba masa kamshin indomien kadai ma wani abun burgewa ne tana gama zubawa ta ajiye masa agabansa ta hau tsiyaya masa juice din bata gama tsiyaya masa ba suka ji ashar da sauri suka ɗago kai binayya ce ta ci uban kwalliya fuskar nan cabe cabe da powder abinka da mutum mai haske ba kyau ba sai yayi wani iri bauu
Da sauri ta qaraso tayi kan shuhada gadan gadan miqewa shuhada tayi zata gudu ganin yadda binayya ta tunkarota burleey cikin hanzari ya cafko hannunta yace ina zakije ?
Juyawa yayi ya watsawa binayya kallo ya hade fuska tamau wanda yasata tsorata ta tsaya cak tana hura baki da hanci yace lpy ? kuka take so tayi amma bata son shuhada ta raina ta dan haka tadinga hadiye kuka da haushi da baqin ciki da kishi
Tasan halinsa sarai dan haka tace yanzu dan Allah yaya adeel meyasa baka kirani nayi maka girkin ba kasan fa ina kishin ka
Tsaki burleey yayi yace inaga watakila ina wasa dake ne ko?
Ya kalli shuhada yace zauna ba musu ta zauna shima ya zauna binayya tace yaya adeel dama fa nazo nace maka zamu fita shan iska ne
Wani banzan kallo ya aika mata dashi yace ok gani drivern ki ko ?
Zama tayi kusa dashi harda kashe murya ni na isa nace kai driver na kawai dai inaso muje shan iska tare ne
Yace amma dai naga alama baki da hankali duka duka yau kwana na uku da dawowa ban gama hutu ba balle na fita sannan da kike maganar cewa muje shan iska nace miki inajin zafi ne ?
Binayya tsantsan baqin ciki da haushi da wulaqancin da adeel ya mata agaban wannan shegiyar mai kama da ya'ya'n aljanun kasa magana tayi da kyar tace yanzu duk wannan makeup din danayi baka gani ba so kake naje na wanke ? kosawa yayi da maganar tata dan ba son mgnr yake ba yace idan kinason fita ai akwai driver saiki je ya kaiki murguda baki tayi ta gefe bai gani ba tace ai dan kai nayi makeup dina ba dan driver ba kallon fuskarta yayi yace dama kinje kin goge fuskar nan ko kuma kije ki wanke dan wlh bakiyi kyau ba
Da sauri binayya ta tashi da gudu ta fita tabar parlorn kai tsaye gida ta wuce tana kuka dan bazata iya juran cin mutuncin da adeel yake mata agaban shuhada ba
Ita kuwa shuhada dry ce ke cinta amma bata isa tayisa ba ganin yadda ya haɗe rai saiya sake yimata kwarjini ganin binayya ta fita yasata tashi itama zata koma daki dan atakure take amma me cewa yayi ta koma ta zauna bai bata ikon tafiya ba saiya gama cin abinci babu yanda shuhada ta iya haka ta dawo ta zauna abincin ma ayangace yakeci shuhada azuciyar ta tace amma lallai fa wannan bawan Allah akwai fi'ili tabbass kaci sunan ka burleey din
Da kyar dai ya gama ci ta kwashe trey din kafin tadawo baya parlorn dan haka da sauri tayi daki
Haka ta wuni agidan su ammy sai karfe uku suka dawo su raeena kuwa sai gefen magriba
Suka dawo da kayan ciye ciye suna ta bata lbrn inda sukaje jinsu kawai takeyi tana amsawa da kai amma hankalinta da tunaninta yana wajan adeel abinda ya faru dazu yake mata yawo akai har akayi sallar isha'i suka tattara suka tafi family house hira nan fa aka dinga barkwanci ana dry burleey ya zo ta zauna amma bai kula kowa ba baiyi mgn da kowa ba lkc zuwa lkc yana satar kallon shuhada da take hira da kawu baba da hajiya kaka agefe kuwa raeena ce itada yaya sadam suna hira yana bata lbrn Indonesia jb kuwa ko kallon raeesa bayayi itama haka duk ta kwashe sa ta zubar dashi gefe daya bata kallon kowa inba khalid ba tarasa taya zata fara fuskantar ammy da wannan mgnr haka dai ta bari aranta amma tayiwa kanta hisabi itafa ko da kasheta za ayi sai khalid
Suka gama hirar su kowa ya kama gabansa
Da washe
Burleey kwance adakinsa fauzan ya shigo yace ɗan uwa yadai ? burleey yace yauwa bro dan Allah kacewa yarinyar nan ta dafa min indomie
Fauzan yace raeena ?
No ba itaba shuhada da mamakin fauzan ke kallon sa kafin ya kwashe da dry yace kodai kodai burleey yayi tsaki yace kodai me ?fauzan yace kodai da ita za ayine
Asibityn su adeel dan haka su fauzan ma zasu koma can da aiki yan uwa fatan Alkhairi sukayi
Agurguje
Bayan wata uku abubuwa dayawa sun faru daga ciki kuwa harda soyayyar da burleey yakewa shuhada itama haka amma babu wanda yasani bata fada masa ba shima bai fada mata ba kuma har yau basu wani mgn saidai gaisuwa ko kuma yace mata tayimasa girki
Har angama asibitynsu adeel sadam da jb ana neman sunan da za asakawa asibityn kowa ya kawo nashi ace baiyi ba harta binayya ta fadi nata akace baiyi ba shuhada tana zuwa tace asawa asibityn suna *FAMILY HOUSE .J.BURKA CLINIC HOSPITAL* ai nan aka hau mata tafi ana cewa sunan yayi murmushi kawai adeel yayi abbi yacewa fauzan gobe idan yaje asibity ya fadawa ogansa zai koma nasu asibityn da aiki fauzan yace to abbi insha Allah
Ko da fauzan ya fadawa ogansa bai so ba domin shine gawatartun haziƙan likitoci shida shuhada gashi basa latti
Babu yanda ya iya yace to ba damuwa amma dan Allah zasuje *azare* gobe anyi kiran gaggawa suna bukatar taimakon kwararren likitoci dan haka kaida shuhada zakuje dan Allah ku taimaka fauzan yace ba komai insha Allah zamuje
Da yaje gida yacewa shuhada ta shirya gobe zasuyi tafiya ba tare da ta tambaye sa ina bane tace to tunda ya mata jawabi taimakonsu ake bukata
Da washe gari da safe suka kama hanyar azare kuma sun isa da wuri
Tun shigowar su garin shuhada gabanta ke faduwa
Nan suka fara gudanar da abinda ya kaisu ta fito da sauri jikinta sanye da kayan likitoci taji an riqe mata riga juyawa tayi taga wani yaro wanda ko amafarki bazata taba manta mai irin fuskar yaron ba dry ya hau mata yace momy ina kwana yaron bazai wuce shekara hudu ba
Murmushi shuhada tayi tashafo fuskarsa tace Masha Allah fyn boy how are u? Yana dry yace fyn momy
Mom din boy din ne ta hau kiran sa tana cewa *shuhad*!!! *shuhad* gaban shuhada ne taji yana tsananta faduwa
Idonta ya cicciko da kwalla
Da sauri ta juya wazata gani *HIND*....???
____________
🤒🤒🤒🤒. Gaskiya wlh yau nasha typing idan har banga ambaliyar sharhi ba ko hummmm baku da typin yasin
____________
Ina qara gode muku masoyana wannan page din nakune LUV urs kace kace
_____________
Comments
And
Share
*by mmn ahlan*✍🏻
[29/01 à 08:33] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻
*ZAHRA ABDUL* ( *m͞͞o͞͞m͞͞y͞͞n͞͞ a͞͞h͞͞l͞͞a͞͞n͞͞*)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻
*sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
___________________
🤣🤣
*_wayyo Allah cikina bari na fara sanar muku da wuri zan saki novel dina mai cike da.......hummm ba adai bada labari kuma karku bari abaku labari kudai ku fara tara kudi #200 ne🤣🤣 kar ayi baku aha_*
*__________________________*
*بسم ا لله ا لر حمن ا لر حيم*
*_________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*________________________*
*P*...2⃣7⃣↪2⃣8⃣
Kallon juna sukeyi jikin su na rawa a hankali suka matso kusa da juna domin kaman nin su bai bace ba saidai kawai kyau din da shuhada ta ƙara kamar ka tabata jini ya fito tayi bul bul da ita
Shuhada ce ta shafi fuskar hindu ayayinda itama hindun fuskar shuhadan take shafa domin su tabbatar wa kansu ba mafarki sukeyi ba
Cikin matsinacin kukan da sukeyi da kyar shuhada tayi jarumtar fara haɗa kalmomin sunan hindu
Hin..hind...hindu..ke....ke..kece ? nan take suka rungume juna suna kukan kewar juna da kukan farin cikin sake ganin juna arayuwar su domin ita hindu harta cire rai zata sake ganin shuhada tasa aranta kawai shuhada ta mutu tunda an ɗauki lokaci kamar haka
Shuhad ganin mom dinsa tana kuka yasa shi juyawa da gudu domin ya kirawo dadynsa (mijin hindu) atare kuwa suka dawo hannunsa ɗauke da wani jaririn wanda bazai wuce wata 7 ba har yanzu kuma suna manne da juna suna rusan kuka jama'a ancika ana kallonsu masu saurin kuka kuma sun hau taya su suna hawaye duk da basu san menene sanadin kukan nasu ba
Yaya fauzan ne ya fito yana neman shuhada ganin jama'a yayi ancika awajan kofar fita reception nan yadinga ƙutsa kai acikin jama'a shuhada ya hango suna rungume da wata suna kuka harda sheshsheƙa
Zuwa yayi yasa hannu zai ja shuhada hindu ta sake riqeta gam tana cewa dan Allah shuhada karki sake tafiya dan Allah ki tsaya wayyo Allah na ni hindu karku tasheni awannan baccin dadyn shuhad wlh shuhada ce itace tasake sakin kuka mijin hindu ya janyeta yace ku nutsu dan Allah ku kwantar da hankalin ku tunda Allah yasa yau kunga juna ku kalli fa yanda ku ka tara jama'a kuna sharban kuka kuma kunsan cewa nan asibity ne akwai marasa lpyr da basu son tashin hankali ko hayaniya ku zo muje gefe daya ko kuma muje gida kin ga ma sha'ib yana kuka ya karasa mgnr yana miqa mata yaron amma taqi karban sa
Shuhada ma sambatu take yiwa yaya fauzan daya riqeta
Wlh yaya fauzan itace itace hinduta aminiyata dan Allah yaya fauzan ka kyaleni karka rabamu na jima ina mafarkin sake ganinta ita da gwaggo mairo da anty haula duk ranar duniya dasu nake wuni azuciyata dan Allah yaya fauzan ka sakeni
Mijin hindu ne ya kalli fauzan yace yallabai idan bazaka damu ba kaxo muje gida na ba nisa kajata sai muje amma idon jama'a yayi yawa anan kaga sai kallon mu akeyi tunda bazasu bar kukan ba fauzan yace ok ba damuwa
Ko awajen shiga mota sunqi su shiga daban daban suna manne har aka isa unguwarsu hindu dake cikin garin azare mai suna g,r,a bauchi road
Ashe duk kukan da sukayi a hospital kadan ne nan da suka shiga parlorn hindu suka dasa sabuwar kuka luqman yacewa fauzan zo mu koma asibity
mu kam fauzan yayi murmushi ya girgiza kai ya fice luqman kuma ya ajiyewa hindu sha'ib akan cinyarta shuhad ya zauna agefenta kafin ya fice shima yabi bayan fauzan
Suka bar musu gidan
Sun kai kusan minti talatin a haka kafin hindu tace shuhada meyasa kika gudu meyasa kika barmu meyasa bakiyi tunanin halin da zamu shiga ba ni da gwaggo mairo da anty haula kinsan barin ki kauye saida anty haula tayi ba'rin ciki sau biyu sbd tunanin halin da kike ciki kullum bamu da kwanciyar hankali shuhada nakai kusan sati ina kwance adaki bana fita ko nan da can sbd tunanin awani irin yanayi kike ciki shuhada kin min Alƙawari cewa duk abinda yadikko zata miki bazaki taba barin kauyen tanko ba amma sai gashi naga akasin haka sbd bakiyi tunanin halin da zamu fa'ɗa ba haba shuhada haba shuhada meyasa hakan meyasa meyasa mey......takasa karasawa sbd kukan dayaci karfinta
Ɗaukar sha'ib shuhada tayi tana kuka sosai tace hindu labari ne mai tsayin gaske halin dana shiga bayan nabar gida amma kafin nace miki komai inaso ki gafarceni ko kuma nace ku gafarceni wlh ba yin kaina bane yasani nabar kauye haka kawai na tsinci kaina a tasha amma dan Allah inaso ki fadamin gwaggo mairo tana nan lpy itada anty haula?
Hindu ta numfasa tace gwaggo mairo da anty haula suna nan lpy
Ajiyar zuciya hindu tayi tace Alhamdulillah yadikko da nuratu da yaya sale fa ?
Tabe baki hindu tayi tace nikam ki bani labarin abinda yasa kika bar kauye
Hawaye shuhada ta goge tafara magana
Lkcn da muka rabu dake bayan mun tashi a makaranta naje gida nayi duk abinda ya kamata haka kawai naji kaina ya saramin natashi na fita ko hijab ban ɗauka ba sai tasha nan dai ta dinga bata labari da kalar wahalar data sha tare da qalubalen data fuskanta daga hannun bala hannun hajiya kila har izuwa rayuwarta ahannun su ammy da kula da itan da sukayi harta samu ta cika burinta
Kuka sosai hindu keyi ta rungume shuhada tace tabbas shuhada Allah ba azzalumin bawansa bane saidai bawa ya zalunci kansa yadikko ce duk tayi sanadiyyar komai wlh bazanyi kaffara ba yadikko ce dan ban yarda da itaba lkcn da muka rabu dake haka kawai naji hankalina bai kwanta ba na fadawa inna zanzo duba ki har inna tana cewa ba yanzu muka rabu ba nace aa dai bari naje na dubo ki
To ko da nazo na samu yadiko da talatu suke cemin wai yadiko ce ta aike ki kauyen yar'mai dille ashe duk karya ne da washe gari haka nayita jiran ki amakaranta ko zakizo amma shuru shine fa da aka tashi naje gidan ku banga kowa ba nayita sallama harna gaji na juya zan tafi kenan saiga nuratu nake tmbyarta cewa kina ina sai take gayamin ga abinda yadikko tace mata jiya itama bata san inda kike ba wai an tura ki yawon duniya shuhada haqiqa kece da riba domin barin kauye ya zamo miki alkhairi dama wani hanin ga Allah baiwa ne wlh shuhada karkiso kiga yadikko da kanwarki nuratu da sale suka zama banda wahala babu abinda sukeyi in takaice miki zance nuratu ya'ya'n ta biyu banda wanda yadiko ta zubar dasu sale yaransa biyar dukkansu kuma ya'ya'n shegu domin akan kwararo aka samesu sai gashi ke da aka tura domin kiyi bariki sai Allah yaqare ki ya hadaki ahannu nagari sbd baki da haqqinsu kuma insha Allah su yadiko basu gama ganin karshen su ba
Banda kuka babu abinda shuhada takeyi tace yanzu inasu gwaggo mairo hindu ta numfasa tace suna kauyen tanko cikin ƙoshin lpy kuma kinsan wani abu wlh babu wanda yasake tada zancen ki a kauye ni abun ma har mamaki yabani nan dai hindu tadinga bawa shuhada lbrn abubuwan da suka faffaru bata rage mata komai ba tace sahura ma har yau ba asan inda take ba
Shuhada tace wacece sahura?
Sahura dai yar gidan talatu riqe baki shuhada tayi tace innalillahi wainna ilayhirrajiun to kuma ita ina taje hindu ta tabe baki tace Alhaqi wasa ne ai haqqin wani ba wasa bane ahankali dai kowa saiya ga karshensa indai junin mutum mugunta
Nan dai suka dinga jajanta lamarin
Shuhada tace ita kam kauye zataje yau bazata bari sai gobe ba hindu tace kibari sai gobe sai muje tare da kyar dai ta amince suka hau hiran yaushe gamo hindu tana bata lbrn karatun ta shuhada tace ke sai yanzu kike university? Hindu tayi dry tace to ina laifi ma na ɗaure na cigaba da karatun suka kwashe da dry shuhada ta hau bata labarin nasarorin da tasamu harda kyautar da mai girma gwamnar kaduna yabata nan hindu ta dinga murna harda labarin burleey shuhada tabawa hindu
Cikin dry da tsokana hindu tace kodai dashi za ayi dan naga soyayyarsa a kwayar idonki nan da nan shuhada fuskarta ta sauya tace bazan boye miki ba hindu ina mutuwar son adeel amma saidai kash...shuru tayi bata karasa ba tafara hawaye hindu cikin damuwa tace akwai matsala ne shuhada?
Kwarai kuwa akwai babbar matsala domin su familyn su basu auren ba're
Zare ido hindu tayi tace bangane ba basu auren bare fahimtar dani
Saida shuhada ta numfasa tukunna tace haka al'adar familyn tasu take sunada matuƙar kirki fiye da yanda kike tunani fiye da yanda nabaki labarinsu amma basu auren bare sannan yar'gidan bazata auri bare ba.shima dan gida bazai auri bare awaje ba
Yanzu haka akwai wata yar uwarsa wacce take masifan sonsa inaga kuma watakila da ita za ayi sunanta *binayya* kwata kwata bata sona bansan dalili ba kodan taga yaya adeel yana shiga hidimata ne oho
Hindu tace kamar ya? Shuhada tace yakan kirani yasani aiki nayi masa girki harna kai masa part dinsa wani lkc ma idan na kai masa sai yahani tafiya harsai ya gama ci ko kuma yasani gyaran bedroom da toilet dinsa ke wlh wani lkc harda gyaran wardrobe dinsa fa
Hindu ta kwashe da dry tace wlh shima yana sonki
Yatsine fuska shuhada tayi tace bana tunani haka kawai dai akwasa da fi'ili ne
Hindu tace ajure zuwa rafi wata rana dole tulu zai fashe
Shuhada tayi dry tace haka fa kanwarsa raeena tasani agaba ranar itada yaya fauzan wanda mukazo nan garin tare dashi wai na fada musu gaskiya me yake tsakanin mu da burleey wai basu gane ba ni kuma bansan me zan gaya musu ba
Hindu tace da alama dai kun dace da wannan burleey din zanso nagansa
Humm kedai manta da wannan mgnr juyawa tayi ta kalli shuhad da yayi bacci tayi murmushi ta tashi ta gyara masa kwanciya ta kwantar da sha'ib dan shima yayi bacci tace hindu tun yaushe kikayi aure?
Tab ai nakai shekara kusan biyar da aure dan shuhad ya kusan shekara hudu sha'ib kuma watan sa 7 shuhada tace Allah sarki kawata shine kika saka masa suna shuhad?
Eh na saka masa sunan shuhad ne sbd ke shuhada naso ace in samu mace amma Allah bai bani mace ba shiyasa nasawa ɗana na farko shuhad sbd wani lkcn idan na kirasa jinake tamƙar kece na kira lkcn fa su baba suka gani ina neman fita hayyacina shine kawai baba yayi magana da mai garin gangare shine akayi biki ko hankalina zai kwanta kinsan ai yace zan cigaba da karatu na har yanzu ina skull of nursing
Murmushi shuhada tayi tace alhamdulillah Allah yabarmu tare hindu tace ameen hira kawai suka dinga yi har aka kira sallar magriba tukunna shap shap suka shiga kitchen sukayi girki
Da badin luqman ya kira ba da basuyi girkin ba
Sai bayan sallar isha'i luqman da fauzan suka shigo gidan yaya fauzan yana dry ya kalli shuhada yace angama kukan?
Itama dry tayi tace eh yayana mun gama nan suka zauna suka ci abinci fauzan yace na fadawa ammy abinda ya faru dazu amma abun akaina ya qare fada tayita min
Sauya fuska shuhada tayi ya koma kalar tausayi tace meyasa ?
Dry fauzan yayi yace bafa wani abu bane ammy tana sonki wai akan meyasa nabar yar'ta tayi kuka tace dan Allah na kula dake
Shuhada tace ayya ammyna ina sonki sosai yaya fauzan gobe inaso zanje kauyen mu zanje naga gwaggo na da antyna plss
Shuru fauzan yayi yana nazari yace ki fadawa ammy tukunna asanyaye ta amsa da to
Fauzan ya miqe yace nikam zan koma asibity itama tashi tayi tace muje sallama sukayi da hindu kamar karsu rabu amma bisa alƙawarin gobe suna tare har wajan mota suka rakasu luqman. ya miqawa fauzan hannu sukayi sallama suka shige mota
Ahanya shuhada ta kira ammy take fada mata akan cewa tana so taje kauye gobe ammy tace to my doter ba damuwa sai kuje da fauzan burleey dake zaune agefe yacewa ammy karta je aje kawai ataho dasu gwaggon akawo su azare fauzan ya nema musu gida
Yanda yayi maganar cike da kishi ransa bace ne yabawa ammy mugu mugun mamaki yana gama fadi kuma yatashi ya fice yabar parlourn fuuuuuu
Ammy tace to kinji abinda mijinki ya fada sai ki kirasa ki tambayesa nikam ba ruwana ammi ta katse kiran
Shuhada ranta yabaci dan ita tana son zuwa kauyenta
Sai kace wani ubanta ko mijinta juyawa tayi ta kalli yaya fauzan tace dan Allah kabani numbern yaya adeel ɗauka wayarsa yayi ya ciro mata numbern yabata ta ɗauka domin yana driving
Gabanta na faduwa. ta shiga kiran layin nasa a karo na farko kenan
*************
Yau dai bari mu waiwaye su yadiko
Yadiko zaune nuratu tana gefenta sai hamman yunwa sukeyi yaran sale sai ihu suke suna buge buge da fashe fashe su yunwa sukeji yaran.nuratu kuwa dambe sukeyi
Yadiko ta hau kutuntuma musu ashar ta tashi ta zari. Mayafi tayi gidan talatu
Talatu zaune abun duniya yamata yawa ta rafka tagumi
Yadiko ta shigo ta zauna itama ta zuba hannuwanta duka a kumatu sunkai kusan minti15 ahaka
Kafin yadiko tace wai meke shirin faruwa ne haka
Talatu tace boka yace aikin daya mana zai iya wargajewa sanadiyyar wargajewar shine idan har *SHUHADA* ta sake taka kafarta a kauyen nan gashi boka yace yarinyar yanzu taci dubu saidai ceto
Yadiko tace to ta yaya ma shuhada zata dawo balle asirinmu ya tonu
Talatu tace humm kedai kawai gwanda musan inda zamu bullowa lamarin
Yadiko tace shuhada kam har abada da kauyen nan
Dan ko zan mutu ba shuhada ba kauyen tanko
______________
Shin burleey zai bar shuhada taje kauyen tanko?
Gashi ance duk ranar da taje karyewar asirin su yadiko. Yazo to abun yakenan?
Wannan amsa duk sai mun hadu a next page
_______________
Comments
And
Share
*_by mmn ahlan_*✍🏻
[29/01 à 08:33] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻
*ZAHRA ABDUL* ( *m͞͞o͞͞m͞͞y͞͞n͞͞ a͞͞h͞͞l͞͞a͞͞n͞͞*)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻
*sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*S̶O̶N̶ S̶O̶ N̶A̶K̶E̶ M̶U̶K̶U̶ M̶A̶H̶ P̶P̶L̶S̶ S̶H̶A̶R̶H̶I̶N̶ K̶U̶ Y̶A̶N̶A̶ S̶A̶N̶Y̶A̶N̶I̶ N̶I̶S̶H̶A̶D̶I̶*😘
*بسم ا لله ا لر حمن ا لر حيم*
*_________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________*
*P* ..2⃣9⃣↪3⃣0⃣
Ta kira sa ya kai sau biyar amma bai ɗaga ba har suka isa hospital tana kan kira amma yaqi ɗagawa bawai kuma bai ga kiran bane aa dan bai san number bane shiyasa yaƙi ɗagawa
Fauzan yayi parking ya juya ya kalleta yace yadai? hawaye ne ya zubo mata tace yaƙi ya ɗauki wayar fauzan ya girgiza kai ya ɗauki wayarsa ya kira sa ringing huɗu adeel ya ɗaga yasa akunne kafin fauzan yayi magana adeel yace ammy ta fada maka sako na?
Fauzan ya numfasa yace aa wani sako kuma ?ammy bata cemin komai ba, na kira ka ne nace maka shuhada tana son magana da kai tanata kiran ka baka ɗaga ba
Bai jira amsar sa ba ya miqawa shuhada wayar ya fice a motar yabata key din yace idan kun gama kika fito ki kulle motar ta ki sameni aciki , gyada masa kai tayi ba tare da tayi mgn ba sbd hawaye takeyi
Fauzan ya juya da sauri yayi cikin asibiti domin akwai abinda zaiyi
Wayar ta kara akunne tayi shuru shima yayi shuru bata san me zata ce masa ba sai ajiyar zuciya kawai take saukewa
To ma me za tace ? wannan ai rashin kirki yake son mata wai kar taje maganar ma ko tsari babu sai kace mijina ko ubana
Da kyar tayi sallama cikin zazzaƙar muryarta
_Assalamu alaykum_
Ajiyar zuciya ya sauke domin sallamar ta daki kwakwalwarsa ya kai minti uku yana jan iska kafin ya amsa
_wa'alaykissalam_
_ina wuni_
_lafiya_
Shuru ta kumayi tana zare ido shi kuma yana jira yaji me zata ce masa da kyar dai ta tattaro jarumta tace
_zanje ƙauye na harna fadawa ammy amma kace bazan je ba meyasa_?
_mtswww keee ina wasa dake ne da zan fadi umarni har zaki kirani kina tambayar ba'asi to banyi niyyar kije bane fauzan yaje yataho dasu gwaggon sai a nema musu gida a azaren amma karki sake kije_,
kamar zatayi kuka tace
_yaya fauzan bai san ƙauyen ba fa_,
_okay naji bai san ƙauyen ba amma ai ana iya masa kwatance idan kuma kin dage sai kinje to kibari kawai ku dawo sai muje tare karki kuskure kije nadai gaya miki_
Kasa magana shuhada tayi kawai ta saka masa kuka runtse idon sa burleey yayi domin yanda sautin kukan nata ya daki dodon kunnensa da kwakwalwarsa da zuciyarsa shuru yayi yana sauraron kukan nata da yaji bazai iya jurewa bane yaja dogon tsaki ya kashe wayar yana busar da iska mai zafi abakinsa tunani kuma yafara ya kirata ya lallasheta amma kuma karta gane sonta yakeyi nan ma yasake jan tsaki domin ya rasa mafita baya son kukan ta sannan kuma baya so taje
Shuhada kuwa kuka taci sosai daga baya ta share hawayenta tana cewa wlh saina tafi saidai duk abinda zai faru ya faru amma tafiya dole dan ni banga dalilin ka na cewa karna je gida ba fitowa tayi a motar ta kulle ta shige asibitin suka haɗu da sauran likitoci yan uwanta suka cigaba da aikin su na taimakon jama'a
**********
Da washe gari bayan fauzan ya gama abinda yakeyi a asibiti ya shirya zuwa kauyen tanko domin ya tambayi mijin hindu yayi masa kwatance
Shi kadai zai tafi domin burleey ya kirasa yamasa gargadin akam karya sake shuhada tabisa ko tace zata je karya tafi da ita fauzan yadinga dry yace ba damuwa yanda kace haka za ayi
Hindu ta shirya tsaf zasuyi tafiya harta fadawa mijinta kuma ya amince yace amma fa kuma fauzan yace banda shuhada hindu ta kwashe da dry tace nasani ta fadamin jiya brothern sa ne yace kar taje amma ni banga dalilinsa na hanata zuwa ba dan haka kawai ka bamu kudin mota ka kaimu tasha
Luqman yace ke momyn shuhad banson irin haka fa tunda yace kar taje to ta hakura mana
Kar yazamo matsala
Hindu tace aa wlh nidai muje kaimu tunda ai ba mijinta bane bata aure sa ba tukunna balle harta taka masa umarni ta shiga wuta kishi yakeyi tun bai furta mn kalmar so ba, ai ba haka akeyi ba
Luqman yace to maganau naji muje na kaiku amma nikam ba ruwana hindu tana dry ta kama hannun mijinta da ɗanta tace eh munji ba ruwanka
A hanya suka ɗauki shuhada luqman ya kaisu har tasha yabasu kudin mota yamusu Allah ya kiyaye hanya ya juya ya tafi
Bangaren fauzan kuwa ya nemi shuhada harya gaji bai ganta ba ya kira wayarta a kashe haka shima ya juya ya kama hanya sai kauyen tanko tunda baiyi tunanin zata tafi ba ya ɗauka tana gidan hindu ne
*********** *ƘAUYEN TANKO*
Tunda suka fara shigowa gaban shuhada ke tsananta bugawa hindu tace ina zamu tsaya gidan gwaggo mairo ko gidan anty haula ko kuma mu wuce faɗar mai gari shuhada tace duk inda muka sauka ma daidai ne
Shuhada tace amma fa har yanzu ba asami wata cigaba ba a kauyen tanko ,hindu tace gsky kam ba asamu wata cigaba ba
Ko da suka sauka a mota shuhada ta ɗauki sha'ib hindu kuma taja hannun shuhad suna tafiya jama'ar kauyen tanko kallon shuhada kawai sukeyi sun shaida hindu amma basu shaida shuhada ba samari sai lashe baki sukeyi, ita kuma yar'gidan mai gari ina ta samo balarabiya haka cewan wasu samari da yan'mata
Shuhada tsaki tayi tacewa hindu har yau dai samarin kauyen nan basu daina yiwa yan mata kallon qurillah ba
Hindu tayi dry tace yo ina kuwa zasu daina barin ma ke ai dole akalle ki
Harta yan mata ma sai sun kalli shuhada bama samari ba yadda take tafiya tana haskawa ga kyau ga ilmi
Sunata tafiya abubuwa dayawa take tunawa ji take kamar bata taba rayuwa anan ba gabaki daya komai na kanta jitake ya tsaya mata tsak, a ƙauyen tanko aka binne cibiyarta aƙauyen tanko aka binne uwa da ubanta amma sai gashi rana daya tazo tabarta wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ,
Hindu tace shuhada dan Allah ki manta da komai ki dubi gaba, murmushi shuhada tayi tace hindu wahalar dana sha nake tunowa ni ake aikawa rafi tsakar dare ni ake kamawa a jibgeni kamar jaka hummm Allah sarki rayuwa duniya kenan mahaƙurci mawadaci ne , shakka babu ba gashi ba yanzu kinyiwa jama'ar kauyen nan zarra dan ba mai ilmi ki
Karki damu komai zaizo karshe wani abu kuma sai ranar da muka kai ki dakin burleey ta qarasa da dry
Shuhada kuwa tsoro ne ya kamata dan ita harta ma manta da yace mata wai kar taje ajiyar zuciya tayi aranta tace am so sorry burleey bazan iya jurewa ba
Saina zo hankalina zai kwanta tayi murmushi
Hindu tace inyee wato na kira sunan masoyi shiyasa haƙorin ki suka qi rufuwa ?
Shuhada zatayi magana kenan suka iso fada hindu ta duqa ta gaishe da mahaifinta da jama'ar wajen sannan. Shuhada ta gaishesu suka amsa sunawa hindu kallon tuhuma
Hindu tace baba baka gane ta ba ko ko kuma nace baku gane ta ba ko?
Aka haɗa baki akace eh , hindu ta kalli mahaifinta tace baba dan Allah ka aika akira gwaggo mairo da anty haula
Umarnin da mai gari yabayar kenan yace aje akirawo gwaggo mairo da matar mansur
Ba ajima ba suka taho tare suna isowa shuhada ta miqe tsaye tafara ambaliyar kuka anty haula sumar tsaye tayi tace ..shu..shuhaa..shu..ha..da... Rungume anty haula tayi ta fashe da matsinacin kuka tuni al'ajabi ya ƙauraye fadar mai gari sun sha kuka kafin shuhada tazo takama kafaɗar gwaggo mairo tana kuka gwaggo mairo itama kuka hindu tana tayasu saiga innar hindu domin tuni shuhad ya shiga gidan ya fadawa kakarsa sunzo da wata kyakkyawar momy
Innar hindu ma tayi farin cikin ganin yanda shuhada tadawo bayan angama koke koke mai gari yabada umarnin a zauna
Bayan an zazzauna aka fara tambayar shuhada inda taje tsawon lkc haka
Nan ta shiga basu lbr jama'a sai tausaya mata sukeyi ga mutane ancika maqil a fadar mai gari wasu shuhadar kawai suke kallo ai da suka gane shuhada ce nan lbr yadinga zagaye ƙauyen tanko shuhada tadawo
Labarin har kunnan talatu shuhada ta dawo cikin tashin hankali talatu ta fita taje gidan yadiko tana kwance tana bacci yaran sale sunyi kace kace da gidan yaran nuratu kuwa dambe sukeyi
Talatu ta kallesu tace dan ubanku da uwarku ku baku iya komai bane sai bar'na ku kuma baku iya komai bane sai dambe ?
Daya daga ckin ɗan sale ne ya durqusa yaja kafar talatu ta fadi timmm da ƙasa
Suka kwashe da dry suka fita da gudu aka bar talatu zaune sai ruwan ashariya takeyi sai kace tanayi da babban mutum
Tashi tayi fuuuu ta shiga dakin yadikko zarnin fitsari ya daki hancinta har saida cikinta ya juya da iya karfinta ta ɗakawa yadiko duka afirgice yadiko ta miqe zata fita da gudu talatu tace ina zakije? Wannan daki ai bazan iya bacci ba wannan zarnin fitsari haka ,
Yadiko tace wlh shegun yaran nan ne da rana suka tashi iskancin su haka zasuzo su tsula fitsari atsaye su ruga da gudu yanzu dai meya kawoki naganki wujiga wujiga haka tafada tana sosai kai hannu bibbiyu dan Jitake kamar an zuba mata ƙarara akan sbd ƙaiƙayi
Talatu tace shahashar banza ba dole ki ganni haka ba kina nan kin kwanta kin sake baki kamar injin patari kina bacci
To *SHUHADA* tadawo kauyen tanko
Tsallen yan bori yadiko tayi ta zube daf da ƙasa wata sharab tace ni laure kai talatu ban son irin wannan wasan
Talatu tace tashi muje fada ba shiri yadiko ta zari mayafinta suka fice
Duk inda suka gitta sai anbisu da kallo ana musu kallon mahaukata
Suna zuwa fadar mai gari sukaga jama'a ancika sai kace ana rabon kudi daidai nan fauzan ya iso yace dan Allah yana neman fadar mai garin tanko nan aka masa kwatance yace ya gode sai kallon kauyen yakeyi ai ko amafarki aka ce masa anan kauyen aka haifi shuhada zaice karya ne
Atare suka isa yadiko tayi kukan kura tayi kan shuhada da sauri fauzan ya fito a mota ya shiga tsakani nan jama'a aka hau tare tare ana tare yadiko
Wani irin ihu gwaggo mairo ta saki ta zube ƙasa tana murza idonta da sauri jama'a akayi kan gwaggo mairo yadikko tahau cewa nice ajalinki mayyar yarinya shikenan zata karya min asiri kizo kibar kauyen nan dan uwarki da ubanki shegiya yar kutumar uba ta karya min asiri boka yace duk ranar da kika dawo asirina ya karye to saina kashe ki ta sake yin kan shuhada fauzan da ransa ya gama baci yaɗaga hannu ya wanke yadiko da maruka biyar masu rai da lafiya saida taci ƙasa network dinta ya ɗauke na wucin gadi talatu kuwa ta hau dry tana nanaye awajan tana tafa hannuwa tacire ɗan kwalinta ta jefar dashi mayafinta kuma ta ɗauresa a kugunta tana ta shewa tana cewa yau ranar tonon asiri ne
Hahahahha nice nan na batar da innar garba shekaru goma shabiyar da suka wuce nice na asirce mijina na hanasa katabus
Nice na raka laure wajen boka aka makantar da mairo nice nayi kaza nayi kaza faɗe faɗe tayike tare da sambatu kala kala
Banda salati babu abinda ke tashi afada anayiwa su talatu da laure Allah wadai da halinsu
Nuratu ce tazo da gudu tasamu yadiko tana fizge fizge itama da sauri shuhada tazo ta rungumeta tana kuka nuratu ta tureta tace wacece ke? Shuhada tace nice fa yar uwarki antynki shuhada ,sun kuyar da kai kasa nuratu tayi tana kuka
Malam liman ne yasa aka kawo masa ruwa yayi tofi aciki yabawa gwaggo mairo tasha tayi ajiyar zuciya ahankali tafara bude idanunta da suka rufe kimanin shekaru kusan goma tar ta budesu tana kallon jama'ar dake faɗa
Wani kururuwa yadiko tasa ta zunduma da gudu talatu tabi bayanta shuhada zata bisu fauzan ya riqota yace karki bisu duk wanda yayi nagari zaiga da kyau idan kuma kayi akasin haka zaka gani atafin hannunka kuka nuratu takeyi ta juya tayi hanyar gida
Shuhada kukan tausayin nuratu takeyi da yaya sale da yaransu
Bayan yan nasihan da mai gari yayi da kuma bada umarni da doka agarin sa daga nan aka rufe fada da adduah
Fauzan yayiwa mai gari jawabin zai tafi dasu gwaggo mairo cikin garin azare bisa tallafin yayansa zasu zauna acan garin azare nan yayiwa mijin anty haula mgn akan ya maida Sana'arsa azare tunda dama shago suke dashi murna sosai yaya mansur yayi yadinga zubawa adeel albarka
Mai gari yace amma su bari sai gobe su kama hanya fauzanu sai akaika gidan saukan bakina fauzan yayi murmushi yace ba damuwa gdy nake
Haka suka wuni suna yawo akauyen shuhada tana nunnuna masa kauyen ta yace waima yaushe kika taho burleey yace karkizo shine kika rigani tahowa to wlh nikam ba ruwana domin yace zaki koma ki samesa ne ,murguda baki shuhada tayi itakam abarta ma da abinda ya dameta
Haka suka wuni suna yawo sosai yan mata kauye sai yabawa da kyawun fauzan sukeyi
Shuhada tace yan matan garinmu fa kai suke kallo fauzan yace idan sukaga burleey zasu suma kenan shuhada tayi dry fauzan yace kema gashi sai haɗa go'slow kikeyi nan ma dry tayi
"""""""""
Da daddare taje gidansu ta samu nuratu da sale abun duniya ya musu yawa ga yara suna ihun yunwa masu dambe sunayi
Shuhada kuka sosai tayi amma nuratu da sale sun kasa kallonta da kyar sale ya nemi ya fiyanta nuratu ma haka
Shuhada tace najima da yafe muku ko.ba komai ku din jinina ne Allah ya yafe mana gabaki daya ta ciro dubu goma ta miqa musu gamida alƙawarin zata dawo domin harta yanke wata shawara azuciyarta
Da washe gari da safe suka bar kauyen tanko sai cikin garin azare
Fauzan yayi dukkan abunda burleey ya umurce sa da yayi, dan ya tura masa kudi masu yawa ya budewa mijin anty haula shago ya nema musu gida sosai shuhada taji dadi.tadinga zubawa yaya fauzan gdy yace bawani zakiyiwa gdy ba wa burleey zakiyiwa gdy kuma yana nan yana jiranki ki koma tunda yace karkiyi kikayi itadai bata ce komai ba dan burleey yasake samun babbar fada azuciyarta
Sosai yanzu hankalin shuhada ya kwanta duk abinda yake faruwa su ammy suna sane kullum kuma sai sunyi waya dasu..hardasu kawu baba da hajiya kaka
Satin su 2 suka shirya zasu koma kaduna shuhada tasha kuka kamar karta koma haka suka kama hanya sai yamma suka isa fauzan yayi horn ana wangale musu gate suka yi ido hudu da burleey ya hade rai fauzan yana parking ta fito kamar wanda kwai ya fashe mata aciki domin tagama tsorata da kallon da burleey yake mata
Afusace ya tashi yayo kansu ba shuhada ba harta fauzan ya tsorata fizgo hannunta yayi sukayi part dinsa .....
*******tofa
sai mun haɗu a next pg
Cmmnts
An
Share
0 comments:
Post a Comment