*P*...3⃣1⃣↪3⃣2⃣
Shuhada a tsorace take dashi ganin yanayin sa gashi sai fizganta yake sai kace ya samu kaza ,suna shiga parlornsa ya haɗeta da bango idonsa yayi ja
_mene ce miki ? Cikin daga murya ,banace karkije ba shine dan kin rainani kika kama hanya kika tafi sannan ko ki kira ni sbd kin mai dani abokin wasan ki_?
Ƙiris ya rage shuhada tasaki fitsari tsananin tsoro
_Muryan ta na rawa tace kayi hakuri bazan iya jurewa bane saina je naga ƙauye na shiyasa na tafi amma kayi hakuri ngd sosai da taimakon ka agareni harna mutu bazan manta ba Allah yasaka maka da mafificin Alkhairi_
Sosai yaji dadin adduarta ,
Zamewa tayi ta gefensa ta raba zata wuce
Yace ina...tsayawa tsak shuhada tayi naji gabanta ya fadi juyowa tayi suka haɗa ido suna kallo juna
_ina....inaa...ina..dafe goshin sa yayi sannan yace ina...so daga yau idan nace bana son abu kidinga kiyayewa kinji ko_?
Asanyaye ta amsa da to sannan ta fice, tabbas ba abinda yayi niyyar fadi ba kenan yaso ya fada mata yana sonta ne zubewa yayi akan kujera ya lumshe ido oh Allah ka kawo min agaji nida nake fari bazan so yarinya ba sai gashi son shuhada yana neman zautar dani ya dafe qirjinsa dake harbawa da sauri sauri
Tana shiga parlor ta samu ammy atsaye tana ta mita fauzan yana zaune yana dry raeena raeesa zeeyadat shukra mihik sabah duk suna zaune
, haba wannan wani irin abu ne daga dawowarta saiya wani jata bari abbinku yadawo yaxo ya fadi menene matsalar sa da shuhada daya takurata haka bari naje na dubota dan naga alama wani lkc ba imani yacika ba yanzu sai yace zai daketa
Shuhada tace ammyna gani fa ,
Juyowa ammy tayi tace my Doter, da gudu shuhada taje ta rungumeta ta saki kuka ammy tace badai dukan ki yayi ba raeesa ta yatsine fuska tace indai yaya burleey ne zai aika ,yaya fauzan yace ki iya bakin ki dan yau naga a wuya yake yanzu zakiji yamiki rubdugu, su zeeyadat suka kwashe da dry
Ammy ta shiga lallashin shuhada tana bubbuga bayanta a hankali ,ammy ta kuma tambayarta adeel ya dakeki ne?
Girgiza kai shuhada tayi taɗago fuskarta tana share hawayenta da bayan hannu tace ammy babu abinda yamin nayi kewarki ne kawai ,ammy tayi murmushi ta shafo fuskarta tace nima nayi kewar yarinyata jeki watsa ruwa kizo kici abinci
Shuhada ta juya ta kallesu tace sister's nayi missing dinku wlh tashi sukayi suka rungumeta duka, sabah tace anty shuhada wlh kin ƙara kyau dry shuhada tayi tace ngd , juyawa tayi ta kalli yaya fauzan tace ahuta gajiya saurayi mijin yan matan kauyenmu su zeeyadat me zasuyi inba dry ba fauzan ya miqe afusace ta haura sama da gudu tana dry ta juyo tamasa kwalo yayi kwafa ya fice domin yaje ya samu ya watsa ruwa shima
Gabaki daya suka haura sama shuhada ta shiga wanka
Ta fito ta shafa lotion tasa dogowar abaya marar nauyi raeena taje ta kawo mata abinci taci ,suka kafa dandalin hira shuhada tana basu lbr sai mamaki sukeyi daga karshe kuma sukace Allah ya rabamu da son zuciya suka amsa da ameen raeena tace dan Allah kujifa wani abun kamar a shirin film mihik tace shuhada kefa kawai an haifeki ne acan amma mune familynki shuhada tace kamar ya? Shukra tace haka kawu baba ya fada ranar ,
Zeeyadat tace kawu baba yana can yana jiranki yayi kewarki harta hajiya kaka kullum saita addabemu yaushe zaki dawo shuhada tayi murmushi tace Allah sarki mijin da kishiyar bari muyi sallar isha'i sai mutafi family house din
Zeeyadat tace naji kawu baba yace akwai mgn bansan wani mgn bane yace abari yaya fauzan ku dawo tukunna ,shuhada tace to Allah yasa muji alkhairi suka amsa da ameen
Shuhada tace raeesa yanaga kin rame haka? Murmushi tayi batare da tace komai ba tausayinta ne ya kama shuhada aranta tace nidai wlh raeesa banga wani abun so ba awajan khalid duk da ya hadu so kenan mai sa mutum yafita daga kamannin sa da da akwai yanda zanyi danayi kin auri khalid amma bani da wannan ikon Allah dai ya zaba mana abinda yafi Alkhairi
Mihik tace ai yanzu raeesa an koma salihatu suka kwashe da dry ta bude baki zatayi mgn wayarta ya ɗauki ruri tana dubawa taga my lyf ɗaukawa tayi ta fice daga dakin dan idan ba haka ba yanzu zasuyi fada dasu zeeyadat da shukra
Hira sosai sukayi bayan sallar magriba suka fita sukaje gidan momma shuhada ta gaisheta momma da fara'anta tace doter ina tsaraba shuhada tace kwantar da hnklinki mommana zan kawo miki gobe ,momma tace to shikenan doter inajiranki fa suka yi dry suka fice suna cewa zasuje wajen mamy daga can zasu wuce big house momma tace adawo lpy sai munzo ,
Gidan mamy suka shiga mamy tayiwa shuhada sannu da dawowa tace dazu fauzan yazo ai nake cemasa ina yabaro min ke wai yabarki a azare nace masa ashe zai koma yanzu da dogoyen kafafunsa kenan , shuhada tayi dry tace yaya fauzan da zolaya nadawo mamyna ,mamy tace ai da kuwa da gske ne bama niba kawu baba zaisa shi ya koma suka sa dry
Saida sukayi sallar isha'i kafin suka fito duka zasuje family house har sun kai gate raeesa tace wayyo nayi mantuwa kuje zanzo suka ce to ita kuma ta juya da gudu bata lura ba taji ta bangaje mutum da sauri taja burki tana kallonsa haɗe rai yayi ,keee ba ki ganin gabanki ne murguda baki tayi tace sai fa hakuri domin idanuwana abayan ƙeyata suke kaga kuwa ai bazan iya kallon gabana ba kai da kake da ido agaba aida saika matsa ka bani hanya na wuce
Cikin bacin rai jb yasa hannu zai kaiwa bakinta kopɗa da sauri ta matsa sannan tayi cikin gidan da gudu mamy tace ah ke baki tafin bane waya koro ki da gudu kuma,? Eh mamy na manta da waya nane ɗauka tayi ta fice tana cewa mamy kinsan akwai horror agidan ,a gate din taga su shuhada suna tsaye dasu yaya anwar yaya mashkur yaya rayyan da kuma yaya fauzan tace au baku tafin ba shukra tace brother's ne suka tsaida mu
Yaya mashkur yace matar tsoho aka akwashe da dry shuhada tace eh naji nice nan ku faɗi da ihu ku kara da wayyo sai kawu baba hira sukeyi abin sha'awa atsaye awajan
Yaya anwar yace mutafin ku mana, dukan su suka ɗunguma family house
Sallama sukayi yawanci jama'ar gidan suna. Zaune parlorn kawu baba da gudu hajiya kaka ta tashi tana cewa oyoyo shuhada rungume juna sukayi suna dry
Hajiya kaka tace wlh bansan haka nake sonki ba saida kikayi tafiya shuhada tana dry tace wlh nima nayi kewarku sosai
Gaban kawu baba taje tana cewa hajiya kaka dan Allah kishiyar karki sakeyin gudu kamar haka kinga dai ni ba likitar ƙashi bace balle idan kika karye na gyaraki
Riqe baki hajiya kaka tayi tace eh ba dole ba ja'irar yarinya tunda kinga nayi miki oyoyo daban rakaki da sanda ba akasa dry
Kawu baba yayi murmushi ya shafi kan shuhada yace sannu da dawowa matar gaishesa tayi ya amsa yana fara'a sannan ta gaida kowa na gida nan aka hau hira zuwa can anjima burleey sadam jb suka shigo aka ɗaura dasu amma burleey da jb basu mgn dan sune yan'shan kamshi
Kawu baba yayi gyaran murya yace masha Allah isyaku hafeezu ismaeel ina alfahari daku amatsayinku na ya'ya'na sannan ga jikokina masha Allah
Sannan duka nan ba bare gabaki dayan mu family ne kum....kawu baba bai gama mgnr sa ba wuf binayya tace aa fa tsoho kadinga cire harafi daya akwai bare mutum daya
Kawu baba yace eh tabbas akwai bare kuma inaga nin ba kowa bace face keee domin duk familyn mu babu marar kunya sama dake ina magana da ubannin ku ne wanda na haifesu suke ganin girmana wanda zansa suyi sannan suyi nace abari sannan subari
Idan kuma shuhada ce kike kiranta da bare to shuhada ta sha gaban bare kiji na fada miki tun ranar da shuhada ta taka gidan nan na maida ita ahalina shuhada bazata auri bare awaje ba *SHUHADA ƊAN GIDA ZATA AURE ACIKIN FAMILYN JIBRIL BURKA*
Binayya ki kiyayeni zanyi mugu mugun saba' miki ran kawu baba yabaci sosai domin azuciye yake magana
Ahankali binayya ta tashi tana qunquni har tana buga cinye daga gani kasan alwashi take sha ,ta fice a parlorn kawu baba ya juya ya kalli mahaifin binayya yace nayiwa binayya miji domin naga albasa batayi halin ruwa ba mahaifiyarta tace kayi hkr kawu wlh binayya zugin kawaye take ɗauka sam bata jin mgn ta
Nan aka dinga bawa kawu baba hakuri
Kawu baba ya cigaba da jawabinsa ina so ne yaran nan tunda sun kai munzalin aure to su duba acikin yaran yan uwan anan ko a niger ayi musu aure nabasu nan da wata daya tak suyi abinda yadace idan kuma basuyi ba ni zanyi
Alh kawu ƙarami (jb) adeel sadam fauzan mashkur rayyan anwar ...............kiran sunayensu kawu baba yayi dukkan su samarin dake wajen yace duk ku zaba gasu nan nabaku wata daya kul ko da wasa kuma kuzo min da rainin hankali abba abbi abbu suka ce insha Allah kawu baba zasu duba idan ma basu duba ba duk hukuncin da kayi daidai ne
Raeesa hankalinta a tashe yake so take tayi mgn amma tanajin tsoron rubdugun da za ayimata haka taja bakinta tayi shuru amma jikinta amatukar sanyaye yake har aka gama hira aka watse bata ce komai ba duk da yau ba wata hira akayi mai nishadi ba
Burleey kallon shuhada yakeyi wacce ta sun kuyar da kai ƙasa hawaye takeyi batare da kowa yasani ba amma burleey yasani hankalinsa kuma yatashi yana so ya tambayeta amma babu hali
"""""""""""""""""""""
Da washe gari basuje asibiti ba suna gida angama asibitin amma har yanxu akwai abinda ba agama sakawa ba
Raeesa taje aiki su raeena kuma sun tafi skull shuhada ita kadaice kawai
Shiryawa tayi cikin riga da wando karo na farko data fara sa wando kenan domin ko dasu raeena raeesa suka saka ita bata sawa haka kawai ta tsinci kanta da sakawa yau
Rigar ya kai mata har gwiwa daga ƙasa yana da fadi da kuma igiyoyi tayi simple makeup,
Wow masha Allah haka fa furta ta ɗauki ribom ta tufke gashinta ta yafa ƙaramin veil ta ɗauki awayarta ta zauna tana tunanin shawaran data yankewa zuciyarta wani documents tagani wanda suka dawo dashi daga azare tace lahh wannan fa dr sagiru yace nabawa yaya fauzan gashi namanta
Tashi tayi ta ɗauka ta fice tana cewa yauwa daga nan saina fada masa yabani shawara
Burleey dake zaune akan Farar kujera kusa da parking space kamar ance ya ɗago kai ai kuwa da ita yayi tozali kallonta yakeyi ko kifta ido babu aransa yace ina zataje haka ga mamakinsa yaga ta shiga part din fauzan wani mololon abu ne yaji ta tokare masa maƙogaro ya hadiye sannan yake tambayar kansa me yake tsakanin fauzan da shuhada ne kam ? Lumshe ido yayi yaji zufa harta fara ɗiga masa, ohh Allah na shuhada don't kill me pls
Tsawon lkc yana jira yaga fitowarta amma shuru ji yake yatashi yaje yaga me sukeyi amma idan yaje yaga suna soyayya zuciyarsa bazata iya ɗauka ba nan dai yadinga saƙa da warware
Shuhada kuwa a parlor ta samu yaya fauzan da system akan cinyarsa bisa alama aiki yakeyi tayi sallama fauzan ya amsa yana cewa ah ah matar burleey
Ina zuwa haka fatan dai yaga wannan adon ? Tayi murmushi tace kai yaya fauzan kai da raeena baku gajiya da zolaya zama tayi agefensa tace gashi dr sagiru yace nabaka wlh namanta ne ,ya karba yace ok zan duba anjim, jim tayi kadan ya juyo ya dubeta yace yadai akwai matsala ne naga akwai mgn abakin ki , tace eh yayana shawara take so muyi
Ajjiye system din yayi agefe yace inajinki ,saida ta numfasa kafin tafara mgn ,am dama cewa nayi wannan motar tawa.mai zai hana asiyar da ita tunda dai nidai ba iyawa nayi ba inaso ne dama....sai kuma tayi shuru fauzan yace sisterna feel free ki fadamin me kikeso , saida ta sun kuyar da kai kasa tukunna tace inaso ne agida asibiti agarinmu ba asibiti kwata kwata garin ba asamun cigaba rashin asibiti shine yafara ɗaqilewa mahaifiyata rayuwa hartayi burin nazama matsayin danake da ita ayanzu wato DR ,
Fauzan ya numfasa yace ok to amma kinsan idan abbi da ammy sukaji wannan mgnr bazasuji dadi ba ko ? Harta kawu tsoho bazaiji dadi ba karki damu zan samu abbi da ammy da mgnr sannan nayiwa adeel mgnr asan yadda za ayi kinji ?
Murmushi mai hawaye tayi tace ngd sosai Allah yasaka muku da gidan aljanna fauzan yace bana son kina fadin wannan mgnr yawwa kin sanma miye kuwa?
Ta girgiza kai tana share hawayenta ,yayi dry wai fa ranar dr sagiru yake cemin wai dan Allah nayi masa hanya sonki yakeyi ni kuma nace masa aa familyn ba ba'a yarda mu auri bare ba harna nuna masa hoton burleey nace masa shine mijinki
Shuhada turo baki shike da shagwaba tace yaya fauzan meyasa kake hadani da yya adeel bayanni ko mgn bamuyi
Fauzan yace ai mukam mun gano komai tashi tayi tana murmushi,Allah babu abinda ku ka gano haka ma raeena kullum saita titsiyeni
Tashi shima yayi yace tunda kin katse min aikin dana keyi muje ki dafa min indomie irin wanda kike dafawa burleey domin kinsan ance ƙannin miji shima mijina atare suka fito suna hira suna dry wanda duk hiran fauzan akan adeel yakeyi
Izuwa wannan lkc burleey zuciyarsa ce kadai bata fito waje ba sai jeka ka dawo yakeyi a parking space hannunsa duka aqirjinsa
Hankalinsa bai kara tashi ba saida ya hangosu sun fito suna dry
Ai baisan lkcn da yayi kansu ba fuuuuu ya sha gabansu idonsa sun kaɗa sunyi jajur sbd tsananin kishi
Atakaice yace ki sameni a part dina fauzan yace ikon Allah yallabai abu zata min ahasale adeel ya juyo ,kai fauzan ka kiyayeni fa abunda ni zatamin yafi naka mahimmanci itadai shuhada ido ne nata sai wulli wulli takeyi dasu ,fauzan ya kwashe da dry yace my love muje kinji ,adeel ya fizgo hannunta yayi part dinsa da ita a idon *binayya* wacce ta shigo yanzu take son zuwa wajen ammy an aiketa tazo tayi mummunar gani
Suna shiga parlornsa ya saketa ,ya juyo yana kallonta fuskar nan babu annuri
_uban meke tsakaninki da fauzan_?
_Cikin tsarkewar murya tace bangane ba_
_okay ni abokin wasan kine da zaki kawo min rainin hankali ya fada yana sake fizgota_?
Da iya karfinta itama ta kwace tace
_menene kuwa a tsakani na da yaya fauzan banda shakuwa_?
Maƙureta yayi da bango yace _bari kiji na fada miki idan ma soyayya kukeyi ke da fauzan to kiyi gaggawar ciresa aranki domin nayi miki miji_
Wata kasalalliyar murmushi shuhada tayi dan abun burleey yafara mata yawa
Ahankalin tafara mgn
_yaya adeel karka manta fa yaya fauzan mun jima dashi yaya fauzan yana da matuƙar kirki tun farkon zuwana gidan nan yake jana ajikinsa wannan matakin dana taka harda gudumawar yaya fauzan muje aiki tare mu dawo tare sannan awajan aiki mu wuni tare sannan kuma ace baza aganmu amanne ba? Hummm idan ma soyayya mukeyi da yaya fauzan ai mun caccanta kuma ma ai...._ bara karasa ba ya ɗauketa da wata gigitacciyar mari wanda bai san lkcn da hakan ta faru ba
Shuhada marin ya shigeta sosai amma tabbas ta tabbatar adeel na sonta dan haka ta juyo zata bar parlor ya sake dawo da ita murya aharzuqe yace gobe karki sake kibi fauzan ki jirani mutafi tare kisan kuma irin mgnr da zai dinga fitowa abakin ki sannan ya sake mata hannu ta fice da gudu ya buge hannunsa da karfi abango hannun da ya mareta dashi
Bata zarce ko ina ba sai daki tana zuwa kuma ta samu wata matsalar binayya kwance shabe shabe daka ganta kasan rashin mutunci yana cinta
Hankali ta taso dazo gaban shuhada tana mata banzan kallo kafin tafara mgn kamar bazatayi ba
Shuhada kike ko wama da suna? Anywhere ba sunan naki bane agabana karki sake ki miqe kafa kinaji nan familynki ne nan ba gidan ubanki bane inaso ki fita harkan adeel idan ba haka ba wlh saina batar dake dama ance tsintattiyar mage bata mage to indai adeel ne yarinya kwalelen ki shashasha yar gidan matsiyata wacce bata gaji arziki ba ba qaramin maganganu binayya ta gangasawa shuhada , shuhada tana tsaye tamkar gunki takasa ko da motsi da yatsar hannunta har binayya ta gama ta fita
Shuhada ta kai kusan minti 30 ahaka kafin da kyar taja kafafunta ta shiga toilet tasakarwa kanta shower da kaya ajikinta sanyi yana ratsata tasaki kuka mai tsanani harsu raeena suka dawo tana tsaye jin shurun yasanya su bude kofar toilet din suka ganta tsaye ruwa yana zuba akanta jikinta jaqab da ruwa idonta daga fari sun rikide zuwa ja
Tashin hankali shuhada meyasa meki da gudu raeesa taje ta kira ammy
Akayi tambayar duniyar nan amma shuhada taki ta bude baki balle tayi mgn ammy da kanta ta cire mata kaya raeena takawo wani akasa mata sannan ammi ta kwantar da ita ta lullubeta tacewa su raeesa su fita itama fita tayi
Bangaren burleey kuwa baƙaramin drama sukayi da fauzan ba , fauzan sai qara cinnasa yakeyi yana masa dry adeel ya kai wuya ,fauzan ko ajikinsa dan shi harga Allah yana so adeel ya auri shuhada ,domin shikam tun kafin kawu bba yayi magana yayi zabensa ba kowa bace ya zabo face *zeeyadat* burleey yace karka sake tafiya wajan aiki tare da shuhada nadai gaya maka ya fice yabar fauzan sai kwasan dry yakeyi saikace sabon kamu
""""""""""""""""
Shuhada bacci tayi bata tashi ba sai gefen magriba lkcn taji tadawo daidai amma kalaman binayya yana nan yana dawo mata domin ba qaramin cin mutunci ta mata ba
Wanka tayi kafin tayi sallah taje kitchen tasamu su ammy dasu raeena raeesa suna aiki nan suka dinga tmbyrta amma fir tace ba komai batasan abinda ya sameta ba itama
Haka suka hakura suka gyaleta ,
Yau ma bataje family house ba
"""""""""
Da washe gari bayan tagama shirinta ta fito bata samu yaya fauzan ba yatafi abunsa sai burleey tagani kallo ya watsa mata baiyi mgn ba amma ta fahimci abinda yake nufi dan haka ta shiga suka kama hanya bamai kula dan uwansa ko a asibiti bataga fauzan ba har suka dawo gida sai dare da ta sauko tagansa zaune parlor tace yaya fauzan ina kaje yau nayita neman ka
Ya hau dry yace na isa na sake jiranki burleey ya ballani nan yabata lbrn yanda sukayi da adeel, tabe baki tayi suka dan taba hira kafin yatashi yamata saida safe
******* haka rayuwa take tafiya bata zuwa family house sosai yanzu ko taje ma bata iya sakin jiki hakan kuma ba qaramin tayarwa da kawu baba hnkl yayiba
*******
*bayan wata biyu*
Tsaye take a aharabar asibiti tana waya wani saurayi yama sallama ta juyo tana kallonsa tace ah dr nasir yakeki?
Murmushi yayi yace ina lpy ba lau ba shuhada ,
Dan Allah ki taimakeni ki canza min matsayi azuciyarki ,bata kai ga bashi amsa ba sukaji amsa na tashi abayansu
_SAIDAI NI NA CANZA MAKA WAJAN AIKI DAGA WANNAN ASIBITIN ZUWA WATA_
dr nasir yace yallabai meyasa menayi?
Atsawance yace shut'up bance ka fita hanyarta ba?
Kee kuma wuce mota da sauri shuhada ta shige sannan ya kalli nasir yace kajira sakamako gobe yawuce fuuuu ya figi motar da karfi
****
Da daddare kawu baba ya tarasu yace nabaku wata daya amma gashi. Yanzu kun shuɗe wata uku dan haka na yanke hukunci
Fauzan yace zeeyadat yakeso dan harma sun daidaita kansu mashkur kuma yace mihik yake so suma kuma sun daidaita kansu, rayyan kuma yace shukra yakeso suma masha Allah haka sun daidaita nan kawu baba yadinga lissafin wa'inda suka daidaita kansu
Sannan ya kalli su jb dasu sadam adeel raeesa wanda izuwa yanzu zuciyarta ta kusan fitowa waje sbd tashin hnkl
Kawu baba yace yanzu dai nagama yanke hukunci ba gudu baja da baya
Zan hada *shuhada aure da adeel* zan haɗa *sadam aure da raeena* zan haɗa *kawu ƙarami(jb) da raeesa* ai tuni parlor ya hargitse ihu raeesa tasaka ta zube akasa tana kuka binayya ma haka
Wayyo Allah na nashiga uku an kasheni da raina yanzu fisabilillah da horror za ahaɗani kumin afuwa wlh inada wanda nake so *khalid* nakeso
Kawu baba yace waye kuma khalid agidan nan
Raeesa tace *wayyo nashiga ukuna ba ɗan gida bane bare ne* nakeso zan mutu
Da sauri su ammy abbi kawu baba hajiya kaka kai kowa ma saida ya miqe tsaye
Kawu baba yace *what*........
**********
Atareni a next pg muji ya zata qare familyhouse ya rigice
Comments
An
Share
*by mmn ahlan*✍🏻
[29/01 à 08:34] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻
*ZAHRA ABDUL* ( *m͞͞o͞͞m͞͞y͞͞n͞͞ a͞͞h͞͞l͞͞a͞͞n͞͞*)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻
*sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*بسم ا لله ا لر حمن ا لر حيم*
*_________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________*
*P*...3⃣3⃣↪3⃣4⃣
Kawu baba yace what bare ? Ra'eesa kina da hankali kuwa , to ba awannan familyn ba
Babu ke babu auren bare gwanda ma ki ciresa aranki domin aure ke da kawu ƙarami(jb) babu fashi, ke ma kuma binayya wannan gurnanin da kikeyi aure ke da nura babu fashi dan gobe ma zaizo daga niger dan auren bazai wuce wata daya ba ,kuma lkc daya za ayi bazan dauki sakaci da lalaci ba
Binayya ta miqe tsaye , wlh nidae ba yaya nura nake so ba yaya adeel nake so, gaban adeel taje ta kamo hannunsa dan Allah yaya adeel kace kana so na kace nice ka zaba kace ba wancan baren ba dan Allah kayi magana wlh kai nakeso , mamarta ce tazo ta fizgeta da karfi suka bar parlor'n. aka bar raeesa da kuka ta zauna shabar a kasa tana magiya kawu baba yace nariga dana gama mgn kunsan halina bana mgn biyu magana daya nakeyi dan haka duk ku tashi ku bawani waje ,raeesa taƙara rikiciwa ta durqusa tayi rarrafe ta riqo kafafun kawu baba tana kuka sosai harda majina da sheshsheƙa har numfashinta na shiɗewa
Kawu baba ka taimaki rayuwata ka rabani da horror wlh mugu ne na bugawa a jarida wlh bana sonsa khalid nake so dan Allah kawu baba ta kuma sa kuka mai tsanani ta rungume kafafun kawu baba kowa na parlorn tausayinta yake amma idan suka tuno abinda takeyiwa wannan haukan to fa nan take zasu nemi tausayin su rasa domin tun tahirin kakanni babu wacce ta taba auren bare atarihin burka
Jb ya kasa ma mgn sbd tashin hankali sai maimaitawa yakeyi wai raeesa za abasa amatsayin matarsa ta sunna uwar ƴaƴansa kai inaaa bazai yuba gasky kawu baba bai duba masa ba yarasa da wacce zai hadasa sai raeesa innalillahi wainna ilayhirrajiun ai da yasan wannan ɗanyen hukuncin kawu baba zai yanke da ya zaba da kansa akan ahaɗasa da raeesa yo ma gwanda ma ahaɗasa da raeena ba akan raeeesa zufa kawai yakeyi
Kowa yana so yayi mgn amma ba hali kawu baba ganin abunda raeesa takeyi yayi yawa ne afusace yace ke kam gobe goben nan zan haɗaku aure da kawu ƙarami sauran kuma nan da wata daya yana gama fadin haka ya bar parlorn raeesa taje ta rungumi ammy tana kuka , Dan Allah ammyna kisa baki kar ahaɗani da horror wlh bana sonsa wannan wani irin al'adace haka naga shima khalid din wata rana zai zama ɗan gida, abbi da kun basa aure na yafita asahun bare dan Allah abbi ,abbi baiyi mgn ba ya juya yafita dan babu wanda ya isa yacanza wannan al'adar shekaru aru aru
Jb ji yake kaman ya shaƙo raeesa yamata shegen duka sbd baqin ciki idan kuka ne ai shiya kamata yayi kuka ba itaba dan shi aka cuta yarinya sam bata da kunya to ma wani irin kalar zama zasuyi a matsayin ma'aurata
Ammy taja hannun raeesa tace raeena shuhada kuzo mu tafi gida ,
Ahankali aka dinga watsewa a parlorn
Jb kasa tafiya yayi saida sadam yajasa burleey kuwa tuni ya fice dama, dan bazai iya da wannan hayaniyar ba maman binayya tana jan binayya ya fice abunsa murna yakeyi kamar mai dan jiyake duk yafisu dace gaskiya kawu tsoho yana sonsa kamar yasan abunda yake ransa shuhada
Ammy dakinta tayi da raeeesa tadinga lallashinta tana bata hakuri tare da kwantar mata da hankali amma ina raeesa ta birkice taqi sauraran ammy sunan khalid kawai take ambata
Ran ammy yabaci ta hau balbalar ta da masifa tashi raeesa tayi da gudu tabar dakin ammy ta tafi dakinsu ta samu shuhada da raeena sun buga tagumi hannu biyu
A haukace ta shigo dakin ko sallama babu ta bude wardrobe dinta taja trolley dinta tahau tattara kayanta tana sawa aciki
Riqota raeena tayi tana kuka dan tun dazu takeyi ganin halin da yar uwarta ta shiga lkc daya duk ta fita hayyacinta
Haba raeesa me kikeyi haka dakike tattara kaya ina zakije me kike nufi ne kam Dan Allah ki tsaye ki saurareni
Amma fir raeesa taqi sam batajin mgnr kowa da karfi ta fisge hannunta daga na raeena tana cewa wlh bazan zauna agidan nan ba tunda ba asona wlh tafiya zanyi bazan iya rayuwa da kowa ba saida khalid , taja akwatynta zata fita da sauri raeena tajata ta wanketa da mari wanda yasata sakin akwatyn ba shiri ta ɗago kai raeena tasake kifeta da mari saida ta duqa
Sannan ta tunata da yatsa ta fara mgn bakinta da jikinta suna rawa ,kin ban mamaki sister ashe soyayyar wani banza na rana daya zai saki ki manta soyayyar familynki na shekarun da bazasu qirgu ba suka miki ashe soyayyar rana daya zata sa ki tafi kibar *ammy* wacce ta ɗauki nauyin wahalar cikinki na tsawon wata tara sannan tasha wahalar haihuwarki bata gajiya ba ta shayar dake kina rungume ahannunta da qirjinta harna tsawon shekara uku sannan zaki ɗauwama acikin zuciyarta har abada amma soyayyar wani namiji rana daya yasa kin mance da hakan ya zakiyi da *abbi* wanda ya tufatar dake yabaki ingantacciyar ilmi ya kula dake shima wannan kin manta raeesa sbd wani khalid ko?. Family sun miki komai amma duk kin manta, shi wanda kike ikirari kina so dame yafi dan uwan naki na jini ? Yaya jb dai jininki ne idan kika so shi kinso kanki idan kuma kika qisa kinki kanqi
Rayuwar ki ce shawara ta rage gareki ki zabawa rayuwar ki abinda yafi dacewa da ita
Raeena tana gama fadi ta juya ta shiga toilet tabar raeesa durqushe tana kuka shuhada ta kasa mgn dan jitake duk ba dadi babu wanda ya kula kowa
Har raeena ta fito daga toilet bata kalli inda raeena take ba tagama shirinta ta kwanta tabarsu itada shuhada
Can zuwa anjima shuhada ta ɗago raeesa ta hau bata baki tana lallashinta cikin sanyin murya da kwantar da kai tace raeesa duk abinda raeena ta fada miki gsky ne kiyi hkr karkija dasu kawu baba sannan ina tabbatar miki bazakiyi danasanin auren yaya jb ba
Tana hawaye tace sis shuhada yaya horror mugune bazaku gane bane
Shuhada tayi murmushi tace wata rana zai so ki amma fa sai inki so yaya jb mutum ne wanda duk mace zataso ta samesa kidaina yiwa yaya jb rashin kunya kigani ko bazai fara sonki ba kiyi hkr kifitar da khalid azuciyarki sannan ki dage da adduah sosai shuhada tadinga lallaba raeesa
Raeena tana jinsu tayi shuru
Har suka gama suka kwanta
"""""""""
Da washe gari
Kamar wasa babu wanda yaje family house da misali karfe biyu na rana su yaya fauzan yaya mashkur yaya rayyan yaya anwar suka shigo lkcn su shuhada suna parlor dan yau basuje asibiti ba sai yamma zasuje
Ammy data fito daga kitchen tagansu tace ahh ku kuma daga ina haka gashi kunsha shadda sai kace wanda zasuje ɗaurin aure ?
Yaya mashkur yace ammy ai ɗaurin auren akayi yanzun nan
Ammy tace auren wa?
Yaya fauzan yahau dry yace masha Allah ammy an ɗaura auren *RA'EESA TARE DA HABIBINTA JIBRIL*
Wani zabura raeesa tayi ta ɗaura hannu aka ta kurma ihu na shiga uku ashe kawu baba da gaske yakeyi a auremin horror
Ammy tace Alhamdulillah Allah ya sanya alkhairi aka amsa da ameen ko kallon raeesa ammy batayi ba raeena ma haka dan tun jiya basu mgn shuhada ta sun kuyar da kai yaya fauzan cike da tsokana yace saura na burleey da shuhada wanda za adaura gobe ammy tayi dry tace Allah ya kaimu
Ahankali shuhada ta tashi tabi bayan raeesa wacce ta shige haura sama. tana kuka lallashinta shuhada taje ta hauyi tana bata baki tare da cewa kidinga nanata kalman innalillahi wainna ilayhirrajiun komai zai dawo daidai zakiyi farinciki da wannan auren bazakiyi dana sani ba ki kwantar da hankalinki dan Allah kibar wannan kukan karya yamiki ciwo
Bangaren jb ma haka sadam yadinga fama dashi jb yace haba sadam raeesa fa wlh idan har tamin rashin kunya jikinta ne zai gaya mata
Sadam yace haba jb raeesa dai kanwar kace yanzu kuma matar kace ,...
Mtswww dan Allah kabarta amatsayin kanwar wai matata abun ma ko dadin fadi babu meyasa ma kawu baba bai haɗaku ba sadam yayi dry yace wlh kuwa da zan riqeta na koya mata sona tsaf zaka iya zama da raeesa harta maka biyayya ta so ka ta haifa maka yara amma fa idan ka so jb yayi tsaki yatashi ya fita sadam yahau dry yace nikam anjima ma zanje zance wajan my raeena ,jb yana jinsa yayi banza dashi
Da yamma shuhada ta shirya ta fito ta samu adeel yana jiranta awaje zasu tafi hospital batare da ta kulasa ba ta shiga mota ya tada suka bar gida suna zuwa asibiti yana yin parking zata fita yace tsaya ....dakatawa tayi batare da ta juyo ba yace idan kika sake naganki da wani wlh wlh ranki saiya baci ke zaki ma koma office din kusa dani batare da tayi masa mgn ba ta fice tana murmushi hali irin na adeel takasa gane wani irin mutum ne
Agida kuwa ammy ta hana raeesa fita ko nan da can
Da misalin shida saura ta lallabo ahankali ta fice kofar gida a gate ta samu khalid jingine da motarsa yana ganinta ya saki murmushi ..ita kuma ta fara hawayen tausayinsu
Ahankali tazo inda yake yace my luv yana ganki haka lpy kuwa? Tun jiya inata kiran ki amma naji shuru Allah yasa lpy
Kuka tasaka tace kayi hkr nan tabasa lbr abinda ya faru sannan ta qara da aurenta da aka ɗaura yau tace kayi hkr bazan iya mantawa da kai ba kaddara tariga fata ta juya da gudu zata koma gida yasha gabanta cikin tashin hnkl daidai nan jb yafito da mota
Atake yaji ransa yabaci ƙarasowa yayi wajan su sannan ya fito a motar yazo inda suke tana ganinsa taji gabanta ya fadi dan yanzu tsoronsa takeji
Hannu yasa ya janyota jikinsa hannunsa aqugunta yana murmushin mugunta yana cije baki yace ohh my wife meyasa kika fito baki sanar dani ba kinzo ki fada masa cewa mu danginmu basu auren bare hahah am sorry dan uwa aduba agaba watakil adace amma yanzu wannan ta zama mallakin kawu karami ya fada yana qara matseta ajikinsa khalid saura qiris ya hadiye zuciya sbd kishi da baqin ciki raeesa kuwa tazama hoto janta jb yayi suka shiga mota sannan yayi horn mai gadi ya bude masa ya shiga awajan suka bar khalid tsaye kamar gawa raeesa sai waiwaya wa take tana kallonsa tana hawaye (rabuwa da masoyi zafi)
Yana gama parking ya fito sannan ya fito da ita tana ganin sun ɗauki hanyar part dinsa tafara tirjewa amma takasa kwacewa suna shiga parlornsa ya zauna ya ɗaurata akan cinyarsa raeesa tuni jikinta ya ɗauki rawa
Jb ganin yanda take bari ne yabasa dry yace yau ina bakin rashin kunyar yake? shuru tayi tana zare idanunta da suke zubar da hawaye yace ban. Wayarki ba musu ta miqa masa yace da kyau good girl tun bakizo gidan nawa bama kin fara hankali ashe,
inaso ki bude kunnenki da kyau ki saurareni kiji irin kalar zaman da zakiyi agidana idan har kikace zaki dinga min fitsara da rashin kunya wlh saina miki dukan da bazaki sake gane kowa ba kinaji na?
Ta gyada kai yace gud girl sannan babu ruwanki dani dan ikirarin da kika dingayi baki sona tunda har baki sona babu ruwanki da hidimata sannan harda kirana horror ko? Da sauri tahau girgiza kai ya cije baki yana kallonta , na tanadar miki abubuwa kala kala agidana daidai nake da zamaninki tashi ki fita ki bani waje harta kai kofa yace saura kuma nagara ganin wannan mai wuya kamar zariyar wandon kiga abunda zan miki
Ta fice da gudu yace marar kunya na ɗauka zakimin ne wlh jikinki yabaki bayani yanzun nan
A hospital kuwa adeel ya hana shuhada saqat yau kwata kwata ma ya hanata mgn da likitoci maza har aka fara qananun mgn anya babu abinda yake tsakanin dr adeel da dr shuhada kuwa? Wasu suce anya kuwa kanwarsa ce kawai, wasu kuma suce soyayya suke kowa da abinda yke fadi
"""""""""""""Agurguje bayan sati biyu an tsaida bikinsu adeel
Binayya kuwa an tattarata ankaita niger acan za adaura nata auren sbd haukan da tadingayi harda bin shuhada da wuka ranar da kyar adeel ya murdeta ya kwace wukar shiyasa kawu baba yace a tattarata ta koma niger ayi bikinta acan
Shirya shirya akeyi sosai dan ba ataba aure dayawa haka ba abbu abbi abba sun tayarwa yaransu gidaje masu rai da lpy nagani na fada domin an zubar da wani abu mai suna kudi acan wajan zaria road kafin g,r,a
Adeel zaune shida fauzan yana basa lbrn yanda sukayi da shuhada ranar akan tanaso ayi asibiti a kauyensu adeel yace to ba damuwa nima abbi ya min mgn fauzan yace eh nina gayawa abbin ai adeel yace eh amma yace abari agama hidimar bikin nan tukunna fauzan yace to ba damuwa
Shuhada kwance suna waya da hindu sai zolayarta hindu keyi
Amarya amarya ba gashi ba dama ai na fada miki
Shuhada tace hummm hindu wlh har yau baice yana sona ba sai masifar bani umarni idan yaganni ina mgn da wani ko a asibiti ne sunana sorry hindu ta kwashe da dry tace shi kuma irin tasa salon soyayyar kenan amma dole ya furta damu yake zancan zai shigo hannunmu ke bari ma kiji yana fadi yana kuka
Shuhada ta kwashe da dry tace lallai ma hindu yaushe zakuzo hindu tace sai nan da sati daya
Ok Allah ya kaimu hira suka cigaba da yi hindu tana ɗaura shuhada akan network yadda zatayi da adeel
"""""""""
Har yau raeena batayiwa raeesa mgn
Raeena tadawo daga skll ta samu raeesa kwance dan bata zuwa ko ina jb ya hanata zuwa aikin ma duk ta zama wata shuru shuru da ita abin tausayi
Kallo daya raeena tayi mata ta kauda kanta gefe raeesa ta taso ta kama hannunta tace sister gaba kikeyi dani ?kiyi hakuri wlh banajin dadin shareni da kikeyi ta karasa hawaye na zuba a idonta
Itama raeenan hawaye ta share sannan ta rungumeta tace yawuce ni ba gaba nakeyi dake ba so nake ki fahimci gaskiya amma nima ba inajin dadin hakan bane
Tun daga lkc raeena suka dawo daidai da yar uwarta amma raeesa mgn ma yanzu wahala yake bata
Ammy ta dauko mai gyaran jiki daga maiduguri sosai ake musu gyara barin ma shuhada tawani qara kyau da qiba sai sheqi takeyi tana maiqo
Ranar zasuje asibiti burleey ganin irin kyawun da tayi yace mata ta koma tasa hijabi haka ta juya taje tasa hijab din ta fito yace ta koma tasa liqab tace bata dashi yace to daga yau babu ita babu zuwa aiki sannan ya fice yabarta tsaye anan kamar tayi kuka ko da ta koma cikin gida ammy tace ah baku tafin ba kuma ?shuhada ta sunkuyar da kai kasa dan yanzu kunyar ammy takeyi kamar me tace ammy yace bazanje ba
Ammy tace eh dama yakamata kam yanzu ki hkr da zuwa asibityn nan tunda amaryace likita matar likita
Shuhada tayi murmushi tana sosa ƙeya cike da kunya ta haura sama ammy ta girgiza kai tana dry dan ta fahimci yanzu shuhada bata sake da ita kamar da
********
Yau saura sati daya biki ayau ne kuma su anty haula da gwaggo mairo aminiyar kwarai hindu suka diro garin kaduna tun daga gate hindu take yaba gidan numfashinta bai tsaya ba saida suka shiga cikin gidan
Su gwaggo mairo da anty haula a family house aka tarbesu an karramasu sosai hajiya kaka sai jan gwaggo mairo takeyi da hira
*******
😞🤒🤒 kun matsa gashi nan to
Comments
An
Share
By mmn ahlan✍🏻
[29/01 à 08:34] Indon Birni: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠
*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻
*ZAHRA ABDUL*( _momyn ahlan_)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
__________________
*masha Allah alhamdulillah ina tayaki murnan kammala book dinki _rasheedat usman (ummu nasma)_ wato _sara da sassaka_ darasin dake cknta Allah yabamu ikon amfani da ita kuskurenki kuma Allah ya yafe miki up up up aminiyata Allah yaqara basira da daukaka yasa kigama mn indo abirni lpy*
__________________
*_jinjina da gdy ga masoyana na nesa dana kusa da wanda na nasani da wanda bansani ba wannan pg din na kune kuyi yadda kukeso dashi ina muku ftn Alkhairi yan grp din SHUHADA FANS inayinku ina sonku barin ma masu suburbudomin cmmnts_*
Na gaisheku kamar haka
_DOTER SURAYYA_
_ANTYN AHLAN_
_TEEMAH FASHION_
_DR HERPSERT_
_UMMU FU'AD_
_MAMAN ABDUL🙊_
_ITZ DEEJEH_
_MOM TWINS_
_MRS FAROOQ_
_UMMU BILAL_
_MUNAYAH_
_HABIBTYNA احلم_
_MMN HAFSAT /BB_
_UMMYN FADEE_
_NAJA YARKWARAI_
_UMMAKULSUM_
_AMATULLAH_
_MAMANASMEE44_
_KHADIJA IBRAHIM_
_XEA SAEED_
_DEAR FATIMA BINTU SAGIR_
_CAPPA_
_MAMAN ISMAEEL_
_HIDAYA KABIR_
_MAMAN MUSHPIQ_
_NANAH XANNAH_
_Kanwata NAFEESAH_
_AYSHAT IBRAHIM_
"""""""""""""""
*mamies luv fans club wlh gabaki dayanku inayinku ina sonku ina qaunar ku*
*_MASOYANA ALLAH YABARMU TARE SON SO NAKE MUKU DOMIN ALLAH_*💘
__________________
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*P*...3⃣5⃣↪3⃣6⃣
Family house ancika sosai ba ma tsaka tsinke sbd jama'a wasu ma kuma basu zo ba sun tsaya a niger tunda acan za ayi bikin binayya
Shuhada hindu raeena raeesa suna zaune adaki ammy ta shigo da babbar trey tace oya maza maza sauko kuzo ku cinyesa duka shuhada ce ta fara tashi kafin raeesa ,raeena tace ammy nifa wlh nagaji da cin wannan abun ta fada tana yatsine fuska ,ammy tace ungo nan naki maza zaune kafin na makeki hindu tayi dry tace ammy zataci ai dolenta ma, ammy itama dryn tayi tace yawwa hindu idan basu ciba ki ɗura musu ,hindu tace to ammy angama
Ammy ta fice suka zauna dukkansu suna ci suna dan taba hira sama sama amma banda raeesa dan ta koma silent kwata kwata bata son mgn yanzu
Bayan sun gama suna zaune shuhada ta tashi ta dauki hijabi,hindu tace ina zakije ?.
Tace zanje wajan zeeyadat ne akwai abinda nakeso ta turamin ne, nayi mata mgn ta whatsapp tun jiya bata cemin komai ba ,bari naje yanzu zan dawo ,hindu tace da dai kin hakura kinga fa waje akwai maza bai kamata ki fita ba wlh ,yatsine fuska tayi ta tabe baki kafin tace aidai naga ba a daura auren ba balle a qudunduneni ,eh amma ai za adaura tunda yau saura kwana biyar dan Allah shuhada karki fita ,hijab din tasa tace wlh saina fita harta kai bakin kofa hindu tace Allah yasa kina fita ki hadu da adeel, cikin gatse tace ameeen
Raeesa ta girgiza kai dan rabonta da fita idan bata manta ba tun ranar da aka daura mata wannan kaddararran auren
Raeena tace ai kuwa harna tausaya mata idan suka hadu hindu ta kwashe da dry, nan suka cigaba da hira da raeena ,raeesa kuma kwanciya tayi ta lumshe ido data fara tunanin khalid zatayi sauri ta bude ido tace astagfirullah
""""""""
Shuhada tana fita ta hango jama'a maza birjik gashi gabaki daya sai kallo ya koma ganta duk da hijabinta har kasa ne amma fuskarta tana haskawa
Ido yamata yawa hakan yasa jikinta fara bari da anganta za ace ga matar adeel can
tana zuwa bakin gate kenan ana budewa burleey gate ya danno motarsa ya hangota tana tafiya ahankali wani burki taci sakamakon tozali dashi da tayi yawani hade fuska tamau mazan wajan ya kalla duk da yan uwansa ne amma saida idonsa ta rufe har wani zufa yakeji amadadin yashiga yayi parking sai ya koma da baya da motar yayi parking dinta awaje ya fito yana taku cike da izza wanda dakagani kasan azuciye yake ranshi bace ko kunyar mutanen wajan baiji ba dan idonsa ya rufe so yake ya tambayeta uban abinda ya fito da ita mai gadi ya kalla yace rufe gate din nafasa shiga sannan ya fizgi hannun shuhada wacce take tsaye kamar bishiyar da aka dasata
Waje yayi da ita inda bar motarsa ya bude yasakata sannan ya zagaya shima ya shiga
_gidan uban wa zakije bance karna sake ganinki awaje ba dan iskanci da wulaqanci kin kama hanya kinfito sai kyetarawa kikeyi cikin maza suna binki da kallo suna qare miki kallo kema harda canza kalar tafiya sai kace tsutsa kina qara rausayawa agabansu ? Duk sauran suna daki a zaune amma shine ke kika fito dan kin rainani bakijin mgnta ban isa nace ga abunda nakeso kibi ba ko *Ashshuhada*,ina zakije nace ?ya fada afusace_
Shuhada da numfashinta ke barazanar barin gangar jikinta sbd tsoron daya dabaibaiyeta tace am..na..na..um...dama ...damaa. ...inaso ne naje..wajen..zeeyadat ta turamin abu ne, bansan da maza da yawa haka ba da ban fito ba kayi hakuri zan koma yanzu
_ok baki san da maza dayawa haka ba yayi kyau_
Motar ya figa da karfi basu zarce ko ina ba sai kasuwa yace ta zauna a mota karta sake ta fita tace to yadan jima kadan kafin yadawo da leda ahannunsa yabata yace gashi maza kisaka yanzun nan karba tayi ta bude ledar taga liqab da safa turo baki gaba tayi tace _haba dan Allah yaya burleey ina kuma zanje da liqab da safa_ taqara ashagwabe fuska
Da sauri ya juye yana kallonta yace what yaya wane kikace?
Da sauri itama ta riqe bakinta tashiga girgiza kai alamun ba haka take son fadi ba jikinta na rawa tace dan Allah yaya adeel kayi hakuri ba burleey nake son cewa ba subutar baki ne plss kamar zatayi kuka
Ya wani hade rai amma azahirin gaskiya sunan yamasa dadi abakinta kamar yace ta sake fadi amma kuma saiya fuske yaja motar suka koma gida saida tasa liqab da safan tukunna ya rakota har upstairs
Bai damu da mutanen wajan ba sai tsokanarsa sukeyi amma kasancewar sunsan halinsa na kyaliya da rashin son mgn shiyasa basu damu daya tanka ba
Ko da ya koma part dinsa yasamu su sadam fauzan jb da mashkur suna zaune suna tattaunawa amma banda jb dake amfanin da system
Fauzan yace yauwa adeel kawu baba yace babu wani bidi'ar da za'ayi da an daura aure za ayi walima shikenan ,adeel yayi tsaki to ina ruwana nifa duk wannan abun ba damuna yayi ba dama ni ba gayyar hayaniya nake so ba ,so that i don't care,
Nan suka cigaba da tattaunawar su
Shuhada tana shiga daki hindu ta hau dry tace Allah yaqara saida nace miki karki fita amma kikace sai kin fita gashi yanzu kindawo ninja raeena ma ta hau dry itama tace antynmu matar yayanmu gasky kalar love dinku yana burgeni ku naku daban ne dan Allah ku koyamin nadinga yiwa yaya sadam
Shuhada tace wlh wannan yayan naku au yayanmu karkije ki fada masa naboni gashi ni bai barni naje inda nake son zuwa ba yawani kaini kasuwa ya siyamin liqab ko waya nuna masa wajan oho ,hindu datake dry kamar ranta tace haba tunda yaje kasuwa ai zaiyi tambaya yasamu ta tabe baki ta dauki sha'ib tace ina shuhad? Hindu tace yana can family house dinku yasamu yara yan uwansa suna wasa
******
Duk wani shirye shirye da akeyiwa ya' idan za akaita gidan miji babu wanda ba ayiwa amaren nan ba, gida angama jere babu abinda ba asaka ba
Ammy momma mamy sun gyara yaransu ba kadan ba ayayinda akayi musu dinkin fitar biki
Tun ana saura kwana uku biki suka fara shan makeup
Jikinsu yayi bulbul barinma shuhada har wani maiqo maiqo takeyi
""""""""""""""""""
Ranar daurin aure masha Allah
Haka aka dinga daura aure dama shi jb an riga da an daura nasa dan haka yau saida aka daura na adeel shida shuhadarsa kafin aka daura na sadam da raeena sai fauzan da zeeyadat , haka aka dinga lissafin familyn jibril burka su goma sha uku jama'a sai barka ake musu ana tayasu murna da ganin kokarin wannan family dan sun nuna bajinta auren yara dayawa haka
Adeel yau ji yake babu wanda ya fisa duk da fuskarsa baya dry amma daka gansa kasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa
Da yamma akayi walima inda aka gayyato malama juwairiyya isa tazo tayiwa su amare wa'azi akan haqqin miji akan matarsa da kuma haqqin mata akan miji
_yaku yan uwana mata idan har kukaji ance miji ana nufin majibancin lamarinki na rayuwa gabaki daya aljannarki tana ƙasar tafin kafarsa saiya ɗaga miki zaki samu dama wucewa mata muji tsoron Allah yar uwata aduk lkcn da miji yake miki mgn ki kasance mai duqar da kai agaresa karki daga masa murya ,yar uwa idan mijinki ya miki laifi ki kasance mai yafiya agaresa ki kasance mai yiwa mijinki adduah tare da taimakon sa yar uwa karki dinga yiwa mijinki rashin kunya yace kiyi kice bazakiyi ba sannan yace abari kice bazan bari ba hakan babban hatsarine ga neman aljannarki karku manta annabi S,A,W ) yamana bayani sosai akan babbar matsayin da miji yake dashi yamana bayani akan haqqin miji yan uwa muji tsoron Allah mudaina daukar aure abun wasa da kashe sha'awa aure rahma ce aure sunnar ma'aikin Allah ne aure kwanciyar hankali ne ,amma hakan bazata samu ba sai kin kasance mai hakuri ladabi da biyayya juriya da tawakkali tsabta iya girki iya kalamai masu dadi karki fiye yawan fushi_
Sosai malama juwairiyya ta sanyaya jikin amaren nan, ai kuwa suka dinga kuka barin ma raeesa lallai zataje tabawa yaya jb hakuri dan karta shiga wuta
Sai magriba aka watse
Da daddare aka kwashesu aka kaisu family house nan yan uwa da abokan arziki aka dinga yimusu nasiha
Kafin aka kaisu dakin kawu baba lkcn ya gama yiwa mazan nasiha nan yayiwa matan kafin yace afita abar masa shuhada
Bayan anfita kawu baba ya dafa kanta shuhada kuka takeyi sosai tarasa gane farinciki takeyi ne ko kuma akasin haka iyayenta kawai take tunawa ahalin yanzu addua take musu aranta
Shuhada !!! Kawu baba ya kirata a sanyaye ckn kuka ta amsa yace alhamdulillah haqiqanin gasky shuhada tun ranar da kika shigo familyna na maidake ckn ahalina fatan zaki zauna da adeel har abada sannan ban zaba miki abunda zai cutar dake ba?
Ckn kuka tace kunmin komai arayuwa kun maidani mutum yanzu kuma kun sake haɗani ackn ku ni kuwa me zance daku wanda yawuce Allah ya sanya ku agidan aljanna
Kawu baba yace masha Allah ,Allah yabaku zaman lpy da zuri'a dayyiba
Tana kuka a kunyace ta amsa da ameeen
Bayan ta fito adakin kawu baba gwaggo mairo da hajiya kaka ma suka yimata nasiha sosai anty haula ma ba abarta abaya ba
Wata yar uwarsu wacce tazo daga niyar mai suna anty suwaiba taja shuhada nan tadinga tsorata ta, kinga shuhada saikin daure gaki yarinya ce kuma wlh daga ganin adeel ba qaramin jarababbe bane zaki sha wuya maganganu sosai tadinga fada mata har saida aka fara kiran shuhadar kafin ta rakota hajiya kaka ta hau sababi tana cewa wananan wani irin iskaci ne duk antafi da sauran amaren amma anbarta burleey dallah azo afice ,suna fita kuwa hajiya kaka ta hau kuka dan tasan zasuyi kewarsu tunda ba unguwa daya bane
Masha Allah ko wacce an ajiyeta acikin gidanta
Hindu ta kalli shuhada tace dan Allah kibar wannan kukan ya isa haka yakamata ki godewa Allah lkc daya rayuwarki ta canza yanzu ki kalli wannan gdn duk girmanta da fadinta naki ne mai hakuri shike da riba kibi mijinki kiyi masa biyayya sosai hindu tadinga bawa shuhada shawara ,amma ina anty suwaiba ta dagula mata lissafi
Har wajen karfe goma suna tare hindu tana lallashinta dan jitake ma kamar ba itaba ,wayar hindu yayi ruri taga mijinta ne dauka tayi tace ok to gani nan fitowa , ta tashi ta dauki mayafinta da sha'ib wanda yayi bacci dama shi shuhad yana tare da gwaggo mairo
Shuhada ta riqe hindu tana kuka dan Allah hindu karki tafi kibarni,hindu ta hau dry tace eh lallaima kowa da haka aka tafi aka barsa yarinya sai hakuri dan yau inaji saki qara tabbatarwa eh lallai sunan mijinki burleey ta kwashe da dry tace saida safe ta fice abunta aka bar shuhada ita kadai sai tunane tunane takeyi
Yau itace tayi aure sannan acikin wannan gida tashi tayi sannan tayi alwala tayi sallah ta jima tana addua tare da gdy ga Allah da kuma iyayenta sannan ta canza kaya ta kwanta abunta
Can wajan karfe sha biyu saura taji motsinsa take gabanta ya fadi ta tashi da sauri ta diro daga gadon neman wajan boya take ,kafin ta hango ƙarƙashin gadonta wanda yaji flower ta shige. Da sallama dauke abakinsa ya shigo dakin amma wayam bai ganta baiyi tunanin komai ba ya ajiye ledojin da ya shigo dasu yafice dan a tunaninsa tana toilet
Saida yaje ya watsa ruwa ya canza kaya zuwa kayan bacci kafin yadawo dakin nan ma bai ganta ba toilet din yaje ya bude nan ma bata nan hankalinsa ne ya tashi yaje har wajen mai gadi yana tambayarsa dan ta duba duka dakunan bata nan ,mai gadi ya tabbatar masa eh lallai fa tana ciki bata fito ba ,ciki ya koma ya zauna adaki harya gaji ya tashi ya koma dakinsa ya kwanta yana tunanin inda ta boye
Shuhada kuwa yana fita ta dauki pillow ta koma ta kwanta akasan gadon
"""""""""""
Bangaren raeesa ma haka jb ya kawo mata ledojin kaza yasata agaba taci tadinga lallabata ita kuma ta kasa sakewa dashi gashi kunyarsa ma takeji tana so tabasa hkr amma takasa
Shi kuma jb umarnin mamy yake bi domin mamy tayi masa tatass akan raeesa shiyasa yayi alkawari zai kula da ita ko da tayi masa rashin kunya bazai mata komai ba sabanin da da yayi alkawarin saiya ballata idan tayi masa abun da ba haka ba
""""""""
Ta bangaren sauran amare kuwa komai yayi daidai
Allah ya qara bada zaman lpy
Da washe gari haka shuhada suka dinga wasan boya ita da adeel har ya fitan yabar gidan bai sakata a idonsa ba
Su hindu sunzo nan suke cemata sunzo mata sallamane ta hau kuka anty haula tace kee bana son shirme miye kuma abin kuka,hindu taja shuhada suka shiga bedroom dinta tace ke yanaga haka? Ckin rashin fahimta shuhada tace me fa me kika gani?
Hindu tace naga tafiyarki bai canza bane kodai baki bada kai bori yahau bane?
Mtswww wlh hindu bansan lkcn da kika zama marar kunya ba to ma ina ruwanki?
Hindu ta kyalkyale da dry tace to ai gwanda nasan dalili keda raeesa akwai ayar tambaya akanku domin duk saida muka biye gidajensu kafin mukazo nan raeena ma kam bata iya miqewa tana can zazzabi yakamata abin tausayi ,ai nan shuhada tasake tsorota, afili tace to al'mufuffuki ni jaruma ce shiyasa , anty haula tahau kiran hindu akan ta fito su kama hanya luqman yana jiransu
Har waje shuhada ta rakosu suna dan taba hira suna dry kamar daga sama ta hangosa saida gabanta ya fadi ganin kallon da yake mata ,yana qarasowa ya miqawa mijin hindu hannu suka gaisa ya gaishe da anty haula suka gaisa da hindu kafin ya kalleta yace koma kisa hijabi da liqabi anty haula da sauri ta shige mota tana cewa to suwaye agidan bayanku hindu tace haba ango kwantar da hankalinka yanzu zamu tafi , yadan saki murmushin gefen baki batare da yayi mgn ba hindu tace to amarya da ango mun wuce sai mun zo suna insha Allah adeel yace ok mun gode sosai Allah ya kiyaye hanya ,ya juya ya watse mata harara da gudu tayi ckn parlorn kafin ta haura sama tashiga daki harya shigo
Ganinsa yasa hanjin cikinta suka kaɗa ahankali ta juya zata hau saman ..yace ina abinci na ,juyowa tai tace yana kan dinning su hindu ne suka kawo daga family house ,,,,,ok ni kikeso nayi serving din kaina ?girgiza kai tayi sannan ta dawo ta wuce dinning area ta fara zuba masa abincin yana zaune a parlor bai taso ba harta gama haɗa masa komai tace nagama ,batare da ya ɗago ba yace kawo min nan daukowa tayi tazo ta jere masa agabansa ta tashi zata tafi....dawo ki zauna ,,abinda ya furta kenan ,dawowa tayi ta zauna tana turo baki ,kinci abincin ne ke? Tace aa ni sai anjima zanci
What sai anjima mtsww tashi yayi yaje ya dauko mata spoon yace maza zonan muci , babu yanda ta iya haka tazo ta zauna sukaci tare duk atakure take dan takasa sakewa dashi har suka gama
Ta koma dakinta shima bai damu daya bita ba tunda yaga gudunsa takeyi
Bayan biki da sati daya sukaje family house ranar wata jumma'a ai kuwa da suka hadu suka dinga murnan ganin juna hajiya kaka sai nan nan takeyi dasu sbd farincikin ganinsu kawu baba ma haka sai murna yakeyi babu wanda baya murna
Bayan sun gama hira a family house suka wuce gida shuhada sai kallon raeesa takeyi yadda tayi wani qiba da haske kasa hakuri raeeena tayi tace sister wannan qibar ina zaki kaita haka ? Zeeyadat tace wlh gata nan duk tafimu auki mihik tace dama mukam ba jikin garemu ba
Abin mamaki amadadin ta basu amsa saita fara kuka ,sosai hankalinsu ya tashi suka shiga tambayarta menene?
Saida ta tsagaita tukunna tafara mgn,,,, wlh sister's duk yadda nake tsoron auren nan ashe ba haka bane babu abinda yaya jb yakemin banda zallar. Kula dani dayakeyi idan banci abinci ba shima bazai ciba danayi motsi zai cemin me nakeso nan tadinga basu lbr abun kirki da yake mata zeeyadat ta kwashe da dry tace tofa to yanzu miye abun kuka? Kodai kin fara son yayanmu ne ?
Raeesa tace eh inajin wani abu ajikina dangane dashi idan na kwanta bacci yanzu mafarkinsa nakeyi sabanin da da nake mafarkin khalid
Shukra tace to ai mai sauki ne wannan soyayya ya kamaki,,,,, shikenan saiki rungumi mijinki ku zauna lpy
Raeesa ta girgiza kai tace baya shiga hidimata ,,shuhada tace kmr ya baya shiga hidimarki ?
Hawaye ta goge tace sbd ikirarin dana dingayi bana sonsa shiyasa yace babu ruwansa dani,,zeeyadat tace ai ga irinta nan duk kece kika jawo yaya jb yake miki abinda yake miki dabadin rainasa da kikayi ba wlh daba haka ba ,,,shukra tace haba zeeyadat yanzu gyara mukeso kidaina janyo abinda ya wuce mu fuskanci gaba ,,,kallo shuhada sukayi sannan raeena tace anty shuhada plss kinga ke matar yayanmu ce ki bata shawara ,,, shuhada azuciyarta tace tab wai nabata shawara nima akaran kaina ina bukatar shawaran da har gobe akasan gado nake kwana
Amma afili tace daki daya kuke kwana? Raeesa ta girgiza kai shuhada harda gyara zama ita gata adole matar yaya tace to yau ki je dakinsa ki kwana duk korar da zai miki karki tafi waima ke ba mace bace ai ba sai ance miki komai ba suka hau dry
Mihik tace anty shuhada anya ba ciki ne dake ba ?shuhada ta zare ido tace asati dayan?
Suka hau dry suna cewa ahto abu na Allah waya sani
Shuhadan ma dry tayi tace saidai ko ku ne kuke da cki amma bani ba hira sukayi sosai kamar karsu rabu
Sai bayan sallar isha'i ko wanne miji ya dauki matarsa suka kama hanyar gida
Da misalin karfe sha daya da rabi raeesa taci wanka na daukar hankali tasa wasu arnakun kayan bacci wando da riga
Wandon da kadan ya wuce cinyarta rigar kuwa iyakar cikinta ya tsaye turarukan da mai gyara jiki ta basu sai yau ta dauko nata ta mulke jikinta dasu ta daure kitson kanta da ribom ta fito gabanta na faduwa ta dauki hanyar dakinsa bisa shawarar anty zubaida wata yar uwarsu a family house
Ahankali ta tura kofar dakin tayi sallama ckn sanyin murya da sanyin jiki
Jb dake zaune kan gado da system acinyarsa yana kallon film take gabansa ya fadi sbd turaren da tasaka mai dauke wuta, hankalisa bai gama tashi ba saida ya hangota tsaye a kofar ita bata shigo ba ita bata koma ba
Harna tsawon minti10 aransa yace wannan yarinya yau me take nufi dani ne?
Ahankali ta qaraso garesa ta zauna ta duqar da kai jikinta na rawa ,,jb da kyar ya tattaro sauran jarumtarsa ya hade rai sannan yace meya kawoki dakina? baya kince baki sona kin tsanen...mgnr maqalewa tayi abakinsa sakamakon shigewa jikinsa da tayi ta saki kuka ,jb kasa motsin kirki yayi sbd wani bakon yanayin daya tsinci kansa aciki ,,,, dan Allah yaya jb kayi hakuri da abinda nace giyar soyayya ce ta dibeni amma yanzu nagane kuskure na ,kuma ance idan kana fushi dani zan shiga wuta ,,ɗagota yayi daga jikinsa yana kallon fuskarta karo na farko daya fara ganin kyawunta yace kina so na???
Kanta a kunye sbd kunya tadan rausaya kai ,,yace no amsa zaki bani kina so na ? Ta gyada kai nan ma yace aa ta fadi da bakinta idan harda gaske takeyi tana sonsa kuma ta cire khalid aranta ,,,saida ta turo baki tukunna tace i love u!!! Murmushi jb yayi ya rungumo ya hau bata hot kiss ta ko ina
To daga nan fa nima na fice da gudu har ina tuntube
Tun daga rana zama ya canza tsakanin jb da raeesa tana yimasa biyayya shi kuma yana kula da ita sosai
Bangaren *ashshuhada* kuwa babu abinda ya canza tsakaninta da adeel
Har yau waje. Kimanin watansu biyu da sati daya da aure
Harya koma aikinsa su raeena sun koma skull harta raeesa ma jb yabarta ta koma aiki
Amma shuhada adeel ya hanata zuwa ko da bakin gate ne
Zaune take a parlor da yamma tana kallo tv ta kamo tashar sunna tv baya sun gama waya da hindu
Ta maida hankalinta kan tv sakamakon wa'azin da taji anayi akan matar da take qauracewa shinfidar mijinta ko kuma take gudunsa ai nan take hankali shuhada ya tashi takasa zaune ta kasa tsaye
Har dare tana safa da marwa adakinta shima yanzu burleey ya tattarata ya watsar, ya zuba mata ido yaga iyakar gudun ruwanta
Da daddare ta kasa bacci barinma idan ta tuno ance mala'iku suna tsine mata ai ba shiri ta tashi ta duba agogo taga karfe 12am ahankali ta fito ckn sanɗa ta turo kofar dakinsa ta shiga burleey kuwa idonsa biyu dan bai jima da kwanciya ba aransa yace to yau kuma meya korota
Bakin gadon tazo ta kwanta agefensa ta juya masa baya, bada jimawa ba kuwa bacci ya sureta ,saida ya tabbatar tayi bacci tukunna yasa hannu ya janyota jikinsa ya rungumeta sosai ya lumshe ido yace Allah ya shiryamin ke *ashshuhada* dama duk gudun ki nasan zaki dawo saketa yayi ya qura mata ido yana kallon kyawun da Allah ya mata idonta ya kalla da suke lumshe ya shafosu yace idonmu iri daya ne nisful hayatina bakinta ya kalla ya hada da nasa yahau tsotsa idonsa a lumshe wanda hakan ne yayi sanadiyyar bude idonta ganinta tayi acikin jikinsa gabaki daya ,,so take ta kwace bakinta amma inaa yaqi barinta sai qara matseta ma da yayi
Shuhada tayi iyakar yinta amma ranar karya ya qare
Da washe gari wata sabuwar soyayya da tattali tagani ya gyara gidan ya mata girki ya kawo mata daki sai lallabata yakeyi taci amma taqi har yamma tana kwance takasa motsin kirki Allura yazo mata nan tace bata san da zancan ba abunma dry yabasa dan haka yahau darawa aranta tace dama ashe kana dry,,,,yace lallai fa ke kina yima wasu amma kice ke baza amiki ba karya ma kenan
Zama yayi ya ɗagota gabaki daya ya riqeta tana ihu amma saida ya mata ,har dare tana kwance takasa tashi ,nan fa hnklnsa ya tashi gashi bataci komai ba
*ashshuhada* ido ta bude tana kallonsa ,,yace kiyi hkr ki taimake ni kici abinci idan har kika cutu nima zan cutu ina sonki ....da sauri taɗago tana kallonsa ya jinjina mata kai *yes i luv u my ashshuhada*
Rungumesa tayi tace i luv u too my burleey saketa yayi yace kifa kiyayeni da wannan sunan,_ tayi murmushi ,,yace to kici abinci ki sha mgani
Kadan taci abincin,,,,da kyar tasha maganin dan ba so takeyi ba
Masha Allah zama yayi dadi agidan wa innan ma'auratan
Har yau kuma hanata zuwa aiki kwata kwata tayi roqon harta gaji ta kyalesa
""""""Agurguje bayan wata 7
Zaune take tana fama da cknta na wata biyar, ya fito ya kalleta yayi dry yace gobe ki shirya zamuyi tafiya batare da ta tambayesa ina bane tace to Allah ya kaimu ya amsa da ameenn
___________
Comments
And
Share
0 comments:
Post a Comment