A hnkli Afeefah ta dago kai tana kallonsa ta ga black coffee dinsa kawae yake sha, ta kuma sunkuyar da kai, bayan kusan minti uku ta kai mug din baki a hnkli ta kurbi coffee din ta ji yyi mata ddi ssae, hada ido suka yi tayi saurin ajiye cup din murya can tace "na koshi" wani kallo yyi mata yace "In xubar knn kike nufi?" Bata ce komae ba ta kuma daukar mug din, fiddo wani foil paper dake cikin basket din gabansa yyi ya bude ya ga cake ne ciki ya ajiye gefe snn ya dauki wani textbuk ya shiga dubawa, rabin mug Afeefah ta sha coffee din snn ta ajiye tace "thanks sir na koshi" ya kalli mug din yace "Its beta ki shanye don baxan xubar ba" kmr xata yi kuka tace "Sir ya isheni" kallon da yyi mata ya sa ta dauki mug din ta kuma kai wa bakinta bata kuma ajiyewa ba sae da ta shanye ta ajiye a kunyace tana goge bakinta, bayan kusan minti biyar ta Mike tsaye ganin hnklinsa na kan textbuk din gabansa murya can kasa tace "ngd sir" sae a snn ya dago Kai yana kallonta yace "Welcm" sunkuyar da kai tayi tace "can I go" yace "yes but dnt ever come to my class absentminded again" a hnkli tace "OK sir" snn ta juya xata fita yace "gashi ki tafi da wnn," juyawa tayi ta ga yana mika mata cake din dake cikin foil paper, xata yi magana ya daure fuska yace "take dis!" karasowa tayi ta dan risina ta karba tayi masa gdya snn ta nufi kofa ta fita daga office din. A bakin lecture hall dinsu ta hadu da Maryam da wasu yan matan class dinsu, Maryam tace "ina kika je ina ta nemanki Afeefah" Afeefah tace "Dr Sharif ne ya kira ni" Kallon juna duka yan matan suka yi amma bbu Wanda yace komae, Maryam tace "wae to tunanin me kike a class ana lecture" Afeefah tace "ni ba tunani nake ba" tana Kai wa nn ta shiga class abunta. Daga masallaci Maryam da Afeefah suka nufi cafeteria, xaunawa suka yi inda suka saba xama Maryam ta gaida matan da taga sun kafa masu ido da alama yan 300lvl ne, bbu yabo bbu fallasa suka amsa ta, Afeefah kam xama tayi abunta Maryam ma ta xauna tace "Me xa a kawo maki?" Girgixa mata kai Afeefah tayi tace "ni a koshe nake" Maryam tace "me kika ci?" Afeefah tace "Dr Sharif ya bani coffee a office dinsa, kuma kin ga cake din nn ma shi ya ban, kawae ki siya drink sae ki sha da cake din." Maryam ta saki baki tana kallon Afeefah tace "da gske?" Afeefah xa tayi magana ta ga yan matan da suka samu a cafeteria tsaye kansu, daya daga cikinsu tace "dama mun xo maku kashedi ne a kan ku fita hanyar Dr Aliyu Sharif, idan kuma ba hka ba duk me ya sameku ku kuka siyan ma kan ku wllh wllh" daga Afeefah har Maryam sake baki suka yi suna kallonsu, Maryam tace "ikon Allah, to a kan wani hujja ko dalilin xa mu fita harkansa yana lecturer dinmu ku ma hka" Daya daga cikin yan matan tace "to idan ku kun cika yan halak ku ci gaba da mu'amala da shi wllh sae kunyi da kun sanin xuwan ku makarantar nn" Maryam ta mike a fusace tace "sae de kuyi da kun sanin xuwan ku bayero ba dae mu ba, har mu ance maku muna da lkcn gantalallu irin ku, mu ba abinda ya kawo mu ba knn, kila ma wnda kuke dan shi bae san Allah yyi ruwan ku a bayero ba yan wahala" da mamaki suka ce "mu kike gaya ma hka?" Maryam tace "yes!" mikewa Afeefah tayi har hawaye ya cika idonta tana kallon yan matan tace "don Allah don Annabi kuyi hkuri...." Turata Maryam tayi tace "kada Allah yasa su yi din mana" xage xage suka soma yi har ana neman dambe, Afeefah tuni ta fashe da kuka tana rokon Maryam su wuce, Xuwa ynxu duk an taru ana kallonsu, masu cafeterian ne suka ce duk su fita su je waje suyi kadda su korar masu customer, Afeefah ta ja Maryam da kyar suka fita da cafeterian suka nufi faculty dinsu Maryam na huci tace "ke daga yau Afeefah ki daina sa baki idan ina abu bbu ruwan ki, idan kuma kina jin kuka to ki dinga fita ko kuma ki matsa daga inda nake ki je kiyi kukan ki," Afeefah dae bata ce komae ba sae share hawayenta take. Karfe uku saura ta ce ma Maryam da ta wani share ta a class tun bayan abinda ya faru a cafeteria xata wuce gida, Maryam ta ajiye littafin hannunta tace "baxa kiyi tutorial din bne?" Afeefah tace "um gida xan wuce" Maryam tace "ba tare ku ke tafiya da su Anty Jidda ba" Afeefah tace "na daina jiran su ynxu" Maryam tace "to shknn Allah kai mu gobe" Afeefah ta Mike ta dauki jakarta snn ta fita daga class din, a hanya ta hadu da Dr Sharif da alamar shi ma gidan xae wuce, ta kasa wuce sa bata gaishesa ba kmr munafuka kanta a kasa tace "ina yini" kallonta ya tsaya yi ta dago jin bae amsa ba kuma bae wuce ba, ya sauke idonsa kasa daga kallonta yace "y are yhu crying?" Wasu sabbin hawayen ne suka xubo mata lkci daya ta fashe da kuka, a dan tsawace yace "ba kya ji na ne?" Ganin student sun fara kallonsu yasa yace "follow me," snn ya bar wajen da sauri, ta shiga binsa tana hawaye har lkcn, motarsa ta ga ya nufa ya jingina jikin motar yana kallonta yace "answer my question" a hnkli tana wasa da fingers dinta muryarta na rawa tace "dama ni da Maryam ne mun je cafeteria sae wasu mata suka xo suka same mu wae daga yau kar mu sake kula ka, idan ba hka ba ni bn san me xa su mana ba, shine sae Maryam ta kula su suka fara fada shine..." Kasa karasawa tayi ta shiga rusa masa kuka kmr an aikota har da shessheka, kallonta kawae ya tsaya yi ta daga kai ita ma tana kallonsa tana ci gaba da kukanta, can ya dauke kai yace "kin san matan?" Girgixa masa kai tayi tana share hawayenta.
Eeshatullah Goni 😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸
A true life love story
By *Ashmaad*
19.....
Shiru Dr Sharif ya dan yi kmr me naxari snn daga kai yana kallonta yace "ina xa ki ynxu" A hnkli tace "gida" ya ce "yayyinki fa?" ta make kafada tace "ni baxan jira su ba" yace "OK cry no more, I will fish out those galz, su nawa ne?" Tana kallonsa tace "su biyu ne" yace "gud!" Yana kai wa nn ya xaga ya shiga motarsa ita kuma ta nufi main gate. Da daddare Afeefah na xaune falo da yayyinta da su Sumayya suna kallo Abba ya shigo Aliyu na biye da shi a baya, duk suka yi masa sannu da xuwa ya nufi sama, Aliyu ya dawo kusa da Afeefah bayan ya amsa gaisuwar kannin nasa yana kallon idonta yace "Me aka maki" bata fuska tayi tace "a sch ne mana" yace "hado min coffee ki kawo min" yana kai wa nn ya nufi stairs, ta Mike ta je tayi abinda ya sa ta snn ta haura sama don kai masa coffee din, yana xaune yana waya ta karaso ta ajiye masa ta xauna tana kallonsa, yana gamawa ya ajiye wayar yace "Mami ce ko" girgixa masa kai tayi tace "a sch ne mana, wasu mata...." Shiru tayi da sauri ya daga kai yana kallonta yace "wasu Mata me?" Kmr xata yi kuka tace "su ke son min dariya a sch" harara ya watsa mata yace "shine kike masu kuka wawiya kawae, ke baki da bakin masu dariyar ne" hawaye cike idonta tace "ina masu ni ma ae" tsaki yyi ya dauki coffee dinsa ya soma sha, ta wara manyan idonta da ke kyalli da hawayen ciki tace "yayanmu ashe dama coffee na da ddi?" Ba tare da ya kalleta ba yace "da baki sani ba" tace "wllh ban sani ba sae da na 'dan dana daxu kuma har da madara ya sa min, yyi ddi ssae" cire cup din yyi daga bakinsa lkci daya yana kallonta yace "wa ya bakii?" Xaro ido tayi kmr warce ta tuna abu tana kallonsa a dan tsorace ta fara inda inda, ya ajiye cup din hannunsa ya murtuke fuskarsa yace "nace wa ya baki coffee," kuka ta fara yi tace "yayanmu siya fa muka yi ni da Maryam" tsawa ya daka mata yace "yaushe kika fara karya Afeefah? OK gobe xa ki kai ni inda ku ka siya coffee din" ta xaro ido a tsorace tace "wayyo yayanmu kayi hkuri, wani lecturan mu ne ya bani..." Tsit tayi ganin irin kallon da yake mata, ya mike ya xabga mata mari mai lfya yace "ki ka ce wa ya baki" kuka ta fashe da ya daura hannu lebbansa alamar tayi shiru, lkci daya ta hadiye kukan, fuskarsa a daure yace "wani lecturer ne wnn?" Ta hadiye sauran kukanta tace "A makaranta" ya kai mata wani marin a fusace yace "fita ki ban waje, doluwa kawae, " mikewa tayi da sauri ta toshe bakinta da hannunta ta fice daga dakin da gudu ta afka dakinsu ta xube gabansu Jiddah ta dinga rusa masu kuka, harkan gabansu duk suka ci gaba da yyi bbu Wanda ya kalleta bare ya ji me ya sa ta kuka sanin irin halinta. Ta gaji da kukanta ta Mike ta nufi gado ta kwanta lkci daya bacci ya dauketa.
Washegari da safe Afeefah ta je gaida Abba bayan tayi shirin sch kmr ynda suke yi duk safiya, xaune ta tadda duk yan gidan a falon Abba bnda Mami da ya Aliyu, ta xauna gefen su bayan ta gaishesa ya amsa fuskarsa a daure, Mami ce ta shigo snn ya Aliyu, Afeefah ta ki bari su hada ido da ya Aliyu, sae wasa da fingers dinta take, sunanta taji Abba ya kira, ta dago kai da sauri yace "Wani lecturer ne a sch kike xuwa office dinsa yake baki abu ki ci?" Xaro ido tayi a tsorace tana kallonsa, Abba ya daka mata tsawa "ba magana nake maki ba kike kallona hka, meye tsakanin ku, kuma a ina kika san shi? Kin mance doka na ne" Kuka ta fashe da tana kallon Aliyu da ya wani hade rae, Abba ya mike a fusace yace "au kuka xa ki yi min don kaniyar ki don ban sa an xane min ke ba?" Sunkuyar da kai tayi ta hadiye kukan da sauri, Abba yace "today shud b d first nd last day da za ki sake kula lecturer a sch, na hane ki da sake kula ko wani namiji a makaranta, hka kika ga yayyinki suna yi, to na sake jin hka sae nayi mugun Saba maki wllh, tashi ki ban waje sha shasha kawae" mikewa Afeefah tayi da sauri ta fice daga falon da gudu. Abba ya juya kansu Jiddah yace "ku kuma ban ga amfanin ku ba a tare, ku tashi ku ban waje" sum sum suka fice daga falon su ma.
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸
A true life love story
By *Ashmaad*
Dedicated to my kawalliya romon jaa6a(khaleesat haiydar) 😘😘
20....
Afeefah bata yi wani break din kirki ba tsabar kukan dake cin ta ga shi bbu daman yi, Mami da ya Aliyu na falo, bbu abinda take sae jujjuya Fork din hannunta, Da kyar ta iya yi ma Mami sallama don har wani rawa muryarta yake, ya Aliyu kam ko kallonsa bata yi ba, driver na barin gidan ta rushe masu da wani matsanancin kuka cikin mota, Driver yyi parkin da sauri yana kallonta da mmki yace "kai! me ya faru" tsaki su Jiddah suka yi suka ce "Da' alla baba mu je iskanci ne kawae" har suka isa makaranta bbu Wanda ya kalli inda take, Duk suka nufi faculty dinsu, ita ma ta nufi faculty dinta, Bakin lecture Hall ta ga Maryam tsaye suna magana da wasu yan ajinsu, Maryam ta saki baki tana kallonta har ta karaso snn tace "Ni kam kina bn mmki Afeefah, bbu ranan da xae wuce baxa ki yi kuka ba, kukan ma mara reason? Haba ki dinga maintain mana, ke fa ba yarinya bace don Allah ki bari, ni baxan boye maki ba gskya haushi kike ban, abu kadan kuka kmr wata yar shekara uku" tabe baki tayi ta ci gaba da xancenta da yan matan ajin, Afeefah tayi tsaki ta bar wajen ta koma karkashin bishiya tayi xamanta. Har lecturer su ta iso Afeefah bata shiga aji ba, yan ajinsu da dama sun yi mata mgna lecturer fa na class sae dae ta ce ta sani, Tun daga nesa ta hangosa yana tahowa, gabanta yyi mugun faduwa taji kmr ta tashi ta falla a guje amma ta kasa, wasa da hijab dinta ta shiga yi gabanta na faduwa, dago ido tayi suka yi ido hudu da shi, ta sunkuyar da kai da sauri, har ya wuceta bae ce komae ba ita ma bata gaishesa ba, mikewa tayi da sauri ta bar wajen kmr munafuka. Da yamma tana xaune cafeteria ita kadae amma ba wnda suka saba xuwa ba, kwata kwata ranan bata shiga lecture ba a cafeterian ta yini, ko Maryam bata san inda take ba, juyawa tayi jin student din cikin cafeterian na gaisuwa don ganin Wanda suke gaisar wa gabanta ne yyi mugun faduwa ganin sa da tayi ya shigo cafeteria, tayi saurin sunkuyar da kai ta jawo hijab dinta ta dan rufe fuskarta, kujerar dake kallon nata ta ga ya ja ya xauna, mikewa tayi da sauri xata bar wajen yace "if I shud slap yhu! Koma ki xauna" kallonsa ta tsaya yi ya watsa mata harara yace "sit" komawa tayi ta xauna ta sunkuyar da kanta, fuskarsa a daure yace "me ya hana ki shiga lectures yau?" Kin dago kai tayi bare ta basa amsa, waiter din dake cafeterian ne ya ajiye ma Dr Aliyu soft drink a table da pack din straw, ya xare straw daya snn ya bude chill coke din gabansa ya saka straw din yyi sip din kadan snn ya dago kai yana kallonta yace "Answer my question B4 i slap yhu" kin dago kanta tayi, a dan tsawace yace "Zainab!" Dago kanta tayi lkci daya hawayen da ke makale idonta ya gangaro, yyi mata mugun kallo yace "oh kuka kike min?" girgixa masa kai tayi ta share hawayen da sauri, ya hade rae yace "me ya hanaki shiga lecture yau" a hnkli kanta a kasa tace "an min fada a gida ne" jin yyi shiru bae ce komae ba yasa ta dago kai tana kallonsa, ta ga wani mugun kallo yake mata, ta dauke kai, a nutse yace "fadan me aka maki?" Shiru tayi bata ce komae ba, ta ji yace "Zainab!" Kallonsa tayi snn tace "Ni ma bn san me nayi ba" Maryam ce ta shigo cafeterian da alamar Afeefah take nema, hango hijab dinta tayi ta karasa table din da sauri tace "kin kyauta Afeefah daga na fadi maki gskya shine har da wani kin shiga lecture...." Harara Afeefah ta watsa mata tace "ehh ban shiga ba" tana kai wa nn ta mike ta fice daga cafeterian sae a snn Maryam ta lura da Dr Sharif da ya bi Afeefah da kallo, ta dan kirkiri murmushi tace "sir ashe kana nn, ina yini" yace "lfya lau" ta juya kmr munafuka ta fice daga cafeterian. Mikewa Dr Sharif yyi ya ciro kudi ya mika ma waiter din snn ya fita, parking space ya nufa ya shiga motarsa yyi reverse ya nufi main gate, tafiya kawae take tana share hawayen idonta taga mota ya tsaya daga kusa da ita, ya bude motar ya fito yana mata mugun kallo yace "yhu walked out of me ina maki magana koh?" Xaro ido tayi tace "Sir Maryam ce..." Dakatar da ita yyi yace "meet me at my office yanxun nn" yana kai wa nn ya bude motarsa ya shiga ya bar wajen.
Eeshatullah Goni 😘😘🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
21....
A hnkli Afeefah ta tura kofa ta shigo bayan tayi sallama ta karasa kusa da table dinsa kanta a kasa tace "am here sir" jin bae ce komae ba yasa ta dago kai tana kallonsa, hararanta taga yana yi, yace "Sit" ba musu ta xauna tana kallonsa, yace "Me aka maki a gida?" A hnkli tace "yayanmu ne ya gaya ni da Abbanmu" kallonta yake yace "Me kika masa?" Girgixa masa kai tayi kmr xata yi kuka murya can kasa tace "wae don nace ka bani coffee" shiru yyi yana kallonta gnin hka yasa ta soma wasa da fingers dinta, "me yasa kika gaya masa na baki coffee?" Dago kai tayi ganin hawaye idonta yace "kar ki min kuka" gyada masa kai tayi ta mayar da hawayen snn tace "Dama yace in hado masa coffee ne da daddare shine da na kai masa daki nace masa ashe coffee yana da ddi ban sani ba sae yace eh mana, sae nace masa har da madara ka sa min....." Murmushin da taga yana yi yasa tayi shiru tana kallonsa, ya ce "ina jin ki" shiru tayi har lkcn, yace "go on!" Sunkuyar da kanta tayi tace "shine sae ya mareni, kuma ya gaya ni da Abbanmu ana ta min fada" muryarta na rawa ta kare maganan tana kallonsa, a hnkli ya daura fingers biyu kan lips dinsa yace "kar ki min kuka" ta gyada masa kai tare da hadiye kukan, murmushi ya kuma yi yace "meyasa kika gaya masa na baki coffee?" Girgixa masa kai tayi tace "ni ma ban sani ba" yace "beside gani nayi kina kallona ranan shi yasa na baki Zainab" xaro ido tayi tace "sir ni ban kalle ka ba wllh" murmushi kawae yake ya jawo foil papern dake desk a gabansa ya warware ya dauki table knife yyi slicin cake din ciki ya soma ci a hnkli yace "ya sunan yayan naki?" Sauke idonta tayi daga kallonsa tace "Ya Aliyu!" Ya dan wara ido yace "uhhn Namesake dina ne knn" Bata ce komae ba, bayan kusan minti uku ta dago kai tana kallonsa jin bae ce komae ba, suka hada ido don kallonta yake tayi saurin sunkuyar da kanta, cake din gabansa ya dauka ya mika mata yace "Take" ta girgixa kai da sauri tace "Thnk yhu sir" hararanta yyi yace "Shine kuma kike kallona?" Kmr xata yi kuka tace "ni ban kalle ka ba wllh" a dan tsawace yace "C'mom take this" har wani rawa hannunta yake ta karbi cake din da yake mika mata, yace "Eat" tace "Sir...." Kallon da ta ga yana mata yasa ta kai cake din bakin ta shiga ci a hnkli yana kallonta, rabi ta ci tace "Sir na koshi wllh" ba tare da ya kalleta ba yace "In xubar kike nufi, yhu had beta finish it right away," kmr xata yi kuka ta karasa cin cake din ya mika mata table watern da ya fara sha, ta karba a hnkli ta bude ta sha snn ta ajiye sauran, wayar ta dake jaka ne ya soma vibrate ta bude jakar yana kallonta ta fiddo wayar, xaro ido tayi sae kuma ta mayar da wayar da sauri yace "feel free, pick yhur cal" girgixa masa kai tayi da ganinta kasa a tsorace take, a nutse yace "wa ke kira?" Da kyar ta iya cewa "Yayanmu" yace "To dauka mana" bude jakar ta ta dauko wayar da ya katse a lkcn, kuma kira aka yi, ta daga kai tana kallon Dr Aliyu kmr xata yi kuka, yyi murmushi yace "pick" daga kiran tayi ta kara a kunne tayi shiru, ya Aliyu yace "Baki gama fushin ba Afeefah" turo baki tayi tace "Eh" yar dariya yyi yace "Srry Angel, nayi laifi baxan sake ba...." Make kafada tayi ta fashe da kukan karya tace "bana so, kuma ni bbu ruwana da kai kar ka sake min magana bbu ruwana da kai" Kallonta kawae Dr Shariff yake, ya Aliyu yace "ohh Haba yar Kanwata, I said am srry, yhu caused everything" ta kuma saka kukan karya tace "ni ka kyaleni joor" lallashinta kawae ya Aliyu ke yi yana mata promises kala kala, lkci daya ta fashe da dariya tace "yhu Promised fa yayanmu" yace "Allah Kanwata I mean it" dariya take sosae tace "ohk byee na hkura" katse wayar tayi ta mayar cikin jakarta ta dago kai tana kallon Dr Aliyu da ya kafa mata ido, wani kunya ya rufeta ta rufe fuskarta da tafin hannunta da sauri tana yar dariya tace "Sirrr" murmushi yyi yana kallonta har lkcn, hkn yasa ta cusa kanta cikin Hijab dinta tana dariyar jin kunya.
Eeshatullah Goni😘😘
🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
Dedicated to all my fans.... Luv u all❤❤
22......
Gajiya tayi da boye fuskarta ganin bae ce mata komae ba ta bude fuskar a hnkli ta mike ba tare da ta kallesa ba tace "Sir am goin home" Yace "ashe bayan kuka ma har da dariya kika iya hka?" Boye fuskarta ta kuma yi da sauri ta fara wani sabon dariyar kmr an aikota, murmushi yyi yana kallonta, can ya mike ya dauki makullansa ya fice daga office din ta bi bayansa. Ba tare da ta kallesa ba yana kulle office dinsa tace "Sae gobe sir" yace "OK Allah ya kai mu" Main gate ta nufa ta samu adai daita da xae kai ta har gida. A falo ta samu ya Aliyu da Mami ta gaida Mami shi kuma ta 6alla masa harara xata haura sama Mami tace "ina su Jiddah" Tace "Mami sae shidda fa xa su gama lecture ni kuma tun uku na gama" Mami bata ce komae ba Afeefah ta haura sama, Aliyu ya dan saci kallon Mami snn ya Mike ya bi ta. Bedroom dinsu ya sameta ta bata fuska tace "ni ka tafi" Dariya yyi yace "ba kin ce kin hkura ba Kanwata" juya masa baya tayi yace "To ki shiriya mu fita yawo da daddare," tsalle ta doka ta rungumesa tace "Yeehhh thanks yayanmu, wllh na hkura" dariya yyi yace "toh ina jiran ki downstairs ki xo mu yi kallo," juyawa yyi ya fice daga dakin, ta shiga cire kayan jikinta snn ta fada bathroom don yin wanka. Da daddare Ya Aliyu ya fita da ita kmr ynda yyi mata alkawari, yawo suka yi ssae snn ya biya da ita shoprite don siya mata ice-cream da kuma shopping da ta ce xata yi, Shopping ta fara yi duk abinda tasan tana bukata ta dinga diba yana tura mata trolleyn, bangaren Ice-cream suka nufa daga karshe bayan ta gama siyayyanta tace "yayanmu mu dan siya ma su Anty Jiddah da Sumayya kar su ji haushi na koh? Ka ga suna ta fushi da xa mu fita" Yace "to xa mu siya masu" ice-cream robobi Shiddah suka siya snn ta kuma sa shi ya siya mata Wanda xata sha a hanya aka sa mata scoop biyu na vanilla da chocolate, juyawa tayi da sauri ba tare da thinking twice ko akwae mutum a bayanta ba taji ta fada jikin mutum kusan rabin ice-cream din hannunta ya xube jikinsa, da sauri ta koma baya, ta xaro ido ganin duk ta juye masa ice-cream din ta daga kai tana kallonsa feelin guilty, sae kuma hkurin da take shirin fara basa ya makale ta kafa masa ido, murya can kasa tace "Sir!" Kallonta shi ma yake, ta cire dankwalin kanta da sauri ta shiga goge masa ice-cream din chest dinsa bayan ta dafa shoulder dinsa duk da ynda ya fi ta tsayi tana cewa "Am srry sir bn san.... Kayi hkuri plss sir" kallonta kawae Dr Shariff yake, kanwarsa ce ta bullo da trolley tana ganin abinda ke faruwa ta karaso da sauri tace "ya aka yi yaya, bata gani ne," Afeefah dake goge masa jikinsa har lkcn da dankwalinta tace "Mistake ne bn sani ba" kmr xata yi kuka ta kare maganar tana kallon yarinyar, Dai dai nn ya Aliyu ya karaso gun da trolley ya tsaya kallon Afeefah da mamaki yace "meye hka wat happened?" Kmr xata yi kuka tace "ban sani ba na buge sa yayanmu shine sae ice-cream ya xube jikinsa" Karasowa Aliyu yyi ya fixge dankwalin hannunta yana mata mugun kallo, snn ya karasa goge ma Dr Sharif jikinsa ya danka masa dankwalin ba tare da ya lura da na Afeefah bne fuskarsa a daure yace "srry" snn ya ja ta suka bar wajen, waigawa take tayi tana kallon Dr Sharif da ya bi su da kallo kafin su sha kwana ta daga masa hannu alamar _bye bye_ tare da yi masa murmushi, shi ma ya mayar mata, biyan kudin kayansu yyi yana janta har lkcn fuskarsa a daure suka fita ya tura ta cikin mota cikin tsawa yace "don kin xuba masa ice-cream shine xa ki kama gardi kina goge masa jiki? Kina da hnkli kuwa?" Girgixa masa kai kawae tayi, yyi tsaki ya xaga driver seat ya ja motar a fusace ya bar wajen. Sae da suka isa gida yyi parkin snn ya kamo hannunta a hnkli yace "am srry sweet sis, me yasa kike taba namiji" sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, hkuri ya shiga bata don yyi mamakin rashin kukan da bata yi ba, daga karshe ta dan yi murmushi alamar ta hkura, shima murmushin ya sakar mata ya ja kumatunta yace "ko kefa yar Kanwata," a hnkli tace "dankwali na yayanmu" yace "yana ina?" Ta dan yi shiru snn tace "ka bar masa" wara manyan idonsa yyi yace "meyasa baki ce min naki bane? Ohh yi hkuri xan siya maki wani atamfar me kyau kin ji" murmushi tayi da ya bayyana beauty point dinta da ke gefen kumatunta na dama tace "thnk yayanmu" ya bude motar ya fita ya fiffito mata da kayanta ya kira su Jiddah su xo su kwashe.
Eeshatullah Goni😘😘🌸👩🏻 'Ya mace Kyautar Allah 👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
23/24....
Da sallama Afeefah ta shigo office din ita kadae rike da coke din da straw ta karasa table dinsa ta ajiye tace "Sir ga shi" ba tare da ya kalleta ba yana ci gaba da danna wayarsa yace "Thnk yhu" ajiye masa change dinsa tayi ta nufi jakarta ta dauka xata fita ya dago da sauri yace "Ina maryam din?" Juyawa tayi tana kallonsa tace "tana waje tana jira na" yace "OK, ku baxa ku sha coke din ba" ta girgixa masa kai tace "Aa mun sha daxu" yace "OK" har ta isa kofa yace "Zainab!" Juyawa tayi tana kallonsa yace "Waye ku ka je shop rite da shi jiya?" Ta wara ido tace "Shine yayanmu ae" gyada mata kai yyi yana kallonta yace "Cousin brother koh" ta girgixa kai da sauri tana dariya tace "lah Abbanmu daya wllh fa Sir" shiru yyi yana kallonta snn ya gyada mata kai, ta juya ta fice daga office din.
Ana gobe xa su tafi mid semester break Afeefah ce xaune da su Maryam da Rukayya inda suka saba xama bayan sun fito daga lecture tana masu explaining wani topic a course dinsu BiOC 312 da suka ce ba su gane ba, Maryam sae kallonta take don bata taba tunanin Afeefah na da maida hnkli hka ba ka rantse kace lecturer ce ynda ta xage take fahimtar da su da turanci, duk ajin anyi xaton kuka ne kadae abinda ta fi iyawa, Muryar lecturen Course din suka ji a bayansu da alamar ya gama lecture da yan 200lvl yace "Ashe bayan kuka ma kina da kkri wajen karatu Zainabu" Afeefah ta rufe fuskarta da sauri da littafin hannunta tana dariya da yake sun dan saba da lecturan tana yawan ganinsa office din Dr Sharif ko a department wani lkcn, su Maryam suka fara dariya suna kallonta, shima yyi dariyan ya wuce. Da yamma suna dawowa daga mosque Afeefah ta nufi cafeteria da Maryam suna tafe suna hira Maryam tace "kin ga yan matan nn basu sake xuwa gun mu ba" Afeefah tace "Allah ya taimake mu don ni tsoronsu ma nake, kila sun...." Maryam ta xabga mata harara tace "Da'alla, matsoraciya kawae to me suka isa su mana, ae Dr Sharif ya kirani a ranan ban san wnda ya gaya masa ba, muka je har department dinsu da shi na nuna su" Afeefah ta xaro ido tace "ba ki ji tsoro ba Maryam? To me ya ce masu" Maryam ta tabe baki tace "oho, kawae yace in tafi, nayi wucewa ta" drinks Maryam tayi masu orderin bayan sun xauna. Biyar saura suka fito daga cafeterian Afeefah tace "ni gida xan tafi Maryam, sae mun hadu next wkk, xan sha bacci wnn break din da muka samu" Maryam tace "wae meyasa kika daina jiransu Anty jidda, kuma fa Abdul na tutorial a class tun daxu kuma course din Dr sharif" Afeefah tace "sbda wani lkcin ina riga su gama lecture sae in ta jiransu har in gaji" Maryam tace "to mu shiga tutorial din" Afeefah tace "A'a ni baxan shiga ba xan yi karatuna a gida, byee" tana kai wa nn bata jira cewar Maryam ba ta kama hanyar main gate, Maryam ta tabe baki ta nufi Department don shiga tutorial, tafiya kawae Afeefah take ko rabin main gate din bata yi ba ta hango yan matan da suka samesu da Maryam a cafeteria ranan da kawayensu su kusan uku suna tafe suna hira da shewa. ta xaro ido a tsorace ganin tahowa suke ta inda take tafiya, rawa jikinta ya dau yi ta fara kalle kallen inda xata buya kan su iso inda take, wani cafe dake wajajen ta shige da gudu ta labe kmr munafuka xuciyarta na bugawa, bayan kusan minti Uku taji muryar matan a cafe din sun shigo da alamar xa suyi photocopy, saura kiris ta fashe da kukan tsoro ganin basu lura da ita ba yasa ta fice da gudu ta kama hanyar gate, mota taga ya ja burki gefenta, har xata falla a guje ta ga Dr Sharif ne, tsayawa tayi tana share hawayen fuskarta da sauri tana kalle kalle kmr munafuka don bata yi wani nisa da cafen ba, yana fitowa daga motar ya hade rae yana kallonta yace "Meyasa baki shiga tutorial ba?" Girgixa masa kai tayi muryarta na rawa tace "gida xan tafi" ya galla mata harara yace "kukan me kike?" Ganin xata fashe masa da kuka yasa ya daka mata tsawa ba shiri ta hadiye kukan har lkcn bata bar waige waigen da take ba ta ga ko yan matan sun fito, ya juya yana kallon inda take kallo, dae dae lkcn da yan matan suka fito daga cafen, bayansa ta nufa da sauri muryarta na rawa tace "Sirrr," kallon yan matan kawae yake su ma kallonsa suke lkci daya kuma duk suka dauke kai suka fara tafiya suna isa dai dai inda yake tsaye Afeefah na bayansa kmr munafuka suka gaishesa, bbu yabo bbu fallasa ya amsa suka ci gaba da tafiyarsu kmr sun hada baki suka juyo gaba daya suna kallon Afeefah sae kuma suka kwashe da dariya suka yi gaba da sauri, Afeefah ta fito daga bayansa tana share hawaye ya daka mata wani mugun tsawar da ya raxanata yace "kuka kike min?" ba shiri ta hadiye kukan tana girgixa masa Kai, ya bude mata front seat bata jira yace ta shiga ba ta shige da sauri, ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver snn ya tada motar ya nufi main gate, hanyar jan bulo taga ya nufa da ita, ita dae sae wasa da fingers dinta take, "kina jina?" Dago kai tayi tana kallonsa ta mayar da kanta kasa da sauri ganin ynda ya hade rae, "Seriously daga yau, i mean daga yau na kuma ganin kina kuka a sch xaki sha mamaki na, yhu re not a kid I c no reason xa ki dinga yi ma mutane kuka unnecessarily, kar in kuma ganin hawayen ki a sch" a dan tsawace ya kare maganan, ta gyada masa kai a hnkli, yace "kin ji ni da kyau kuwa?" Kai ta gyada masa nn ma, yace "to me nace?" a hnkli tace "kace kar in kuma kuka a sch" yace "good! Repeat after me" dago kai tayi tana kallonsa yace "ki ce, ke Zainab," murya can kasa tace "Ni Zainab," yace "kinyi alkawarin" nn ma a hnkli tace "nayi alkawarin," yace "baxa ki sake kuka a sch ba da ma ko ina!" Sunkuyar da kanta tayi ta maimaita abinda yace a hnkli, yace "yhu promised fa kika ce?" Kai ta gyada masa tace "yes sir" ya galla mata harara yace "da wani katon idonta a gurin" boye fuskarta tayi da tafin hannunta ta fara dariya a hnkli, dan murmushi yyi ya mayar da hnklinsa gaba daya kan tukin da yake, a hnkli dan kanta ta xame hannunta daga fuskarta. Nesa da gidansu ssae yyi parkin ya juya yana kallonta, ta dan wara ido tace "Sir dama kasan gidanmu?" Da sauri ta ba kanta answer tace "ohh Maryam ta taba xuwa da kai na manta" murmushi kawae yyi, tace "na gode sir" snn ta bude motar ta fice, "Zainab!" Taji ya kirata a nutse, ta juya da sauri tana kallonsa, a hnkli yace "Read ur books, dnt sleep too much during d break, ur exam is around the corner, nd I will b conducting my last test on Tuesday" Kai ta gyada masa tace "OK sir xan yi karatu," kai ya gyada mata ta kulle masa motarsa ta nufi gate dinsu shi kuma yyi reverse ya bar anguwar, tsaye ta ga Ya Aliyu a gate da alamar shigowarta yake jira, xuciyarta ya kusa shigewa cikinta, cikin rawar Murya tace "yayanmu"
Eeshatullah Goni😘😘🌸👩🏻 'Ya mace Kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
26.....
"Zainab wa ya ajiye ki a mota?" Afeefah da jikinta ke bari ganin yanayin yayan nata, cikin rawan murya tace "Wayyo yayanmu ni ban shiga mota....." Mari ya kai mata yana huci yace "Ni xa ki ma karya? I will so beat the hell out of yhu ynxun nn idan baki gaya min gskya ba, wa ya ajiye ki a mota nace?" A tsawace ya kare mgnr, Afeefah da har hawaye ya soma taruwa idonta ta tuno promise din da tayi ma Dr Sharif da sauri ta hadiye kukan, tana girgixa masa kai a hnkli tace "yayan Maryam ne ya xo daukar ta shine suka rage min hanya" bata san lkcn da karyar nn yyi formulatin kansa a bakinta ba, Aliyu da idonsa suka sauya launi ya fixgo hannunta ya nufi cikin gida da ita yana huci, dakin Mami ya nufa da ita, lkci daya duk ya xayyane ma Mami abinda ya gani da kuma abinda ta ce masa, Mami ta saki baki tana kallonta tace "wato ke kin xama me kunnan Kashi ko Zainab, bbu Wanda ya isa da ke knn a gidan nn, to wae ni hka kika ga yayyin ki na yi ne, wllh ka tafi da ita ka xaneta Aliyu, gobe idan ance ta shiga motar mutane gudu xata yi ta bar wajen" Afeefah dae kanta na kasa, Mami tayi mmki wae yau Afeefah aka sa gaba ana yi ma fada bbu ko digon hawaye abinda bata taba gani ba tunda ta haifeta, shi kansa Ya Aliyu ba karamin mmki yyi ba har ya mareta bata yi kuka ba, kofa ya nuna mata alamar ta fita, ta nufi kofan a sanyaye ta fita ta jira sa a corridor, dakinsa ya nufa da ita ya xaunar da ita gefen gadon yana kallonta fuskarsa a daure yace "me yasa baki jin magana Afeefah, baki da kudin mota ne xa ki shiga motar mutane?" Girgixa masa kai kawae tayi, ya ji tausayin ta ya dawo gefenta ya xauna yace "Haba yar Kanwata, ynxu kin daina jin maganata ko?" A hnkli tace "ina ji yayanmu" yace "to meyasa kike disobeying dina idan na hanaki abu" kanta a kasa tace "na daina" ya dan yi murmushinsa me kyau ya dago kanta yana kallon cikin idonta yace "yauwa princess dina" dan murmushi ita ma tayi tana kallonsa, ssae ya Aliyu yyi mmkin kukan da Afeefah bata yi ba yana mata fada, ya mike yace "go nd bath ki sauko ki ci abinci kinji" mikewa tayi ta gyada masa kai ta fita daga dakin ta tafi nasu. Da misalin karfe goma na dare Afeefah ta fito daga wanka knn tana shirin kwanciya, su Jiddah gaba daya suna falo suna kallo, wayarta dake ajiye gefen gado yyi haske alamar ana kiranta don alwayz a cylnt wayar yake, karasawa tayi ta dauki wayar ta kafa ma new numbern dake kira ido tana tunanin waye, har sae da ya kusa katsewa snn ta daga a hnkli ta kara kunnenta, shiru taji na kusan second sha biyar har tana shirin katsewa taji anyi sallama, mamaki ne dauke fuskarta jin muryar namiji, da kyar ta iya gather din courage tace "Waye?" Yace "Baki amsa sallama ne?" Ta dan yi jim snn tayi saurin cewa "Srry, wrong number malam" tana kai wa nn ta fara kkrin katse wayar, "Wait Zainab!" still tayi jin ya kira sunanta, da kyar ta ce "A ina kasan ni?" A hnkli taji yace "Allah ne ya hada ni da ke" kuma kallon nmbr tayi da sauri snn ta mayar kunnenta tace "don Allah kayi hkuri wrong number ne ka kira" murmushi taji yyi yace "Wrong number kuma? Ba da Zainab Mahmoud Umar nake magana ba?" Xaro ido tayi jin ya kira full name dinta tace "Dan Allah ka rufa min asiri a ina ka samu nmbr na?" Yace "Allah ne ya bani" a tsorace tace "toh ni ba ni bace" bata jira cewarsa ba ta katse wayar snn ta kashe wayar gaba daya, jikinta na rawa ta kwanta ta shige bargo don ita dae tasan bata taba ba namiji lambarta. Da Asuba ringing din wayarta ne ya tasheta daga bacci ta mike a firgice tana kallon wayar, wani kara ta saki da ya farkar da su Jiddah gaba daya snn ta fice daga dakin da gudu ta afka dakin ya Aliyu tana ihun sunansa, shi ma a firgice ya farka yana kallonta yace "me ya faru?" Bayansa ta labe tana kuka tace "yayanmu na kashe wayata kafin in kwanta wani aljani ya kunna min wlh" sake baki yyi yana kallonta aka bude kofar dakin ta fasa ihu, shi kansa sae da ya ji tsoron bude kofar, Mami ce ta shigo dakin a tsorace ita ma, sae ga Adnaan ma ya shigo da sauri, su Jiddah ma a rude suka shigo dakin, duk suka tsaya kallonta, Abba dake tsaye bakin kofar duk suka ba hanya ya shigo dakin yana Kallon Afeefah da mamaki yace "me ya faru Zainab?" Kuka ta fashe da ta fito daga bayan ya Aliyu da sauri ta nufi gun Abba tace "Abba ka ga na kashe wayata jiya da daddare kafin in kwanta kawae ina jin aljani ne ya kunna min ya fara ringing ina bacci, wllh Na kashe kafin in kwanta" cikin matsanancin kuka ta kare maganan, su Jiddah suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Abba ya daka masu tsawa, Sadiya tace "Abba ni ce fa na kunna xanyi browsing jiya da daddare bn da data" dariya ssae su Jiddah suke suna kallon Afeefah, Ya Aliyu ya daka masu tsawa yace "don me xa ku kunna mata waya, wawayen yara kawae" juyawa Abba yyi tsaki Adnaan yyi yana hararan Afeefah ya fice daga dakin ransa a bace, Mami ta yi kwafa ita ma ranta a bace tace "nasan maganin ki, ba dae ke yarinya bace xa ki tada mutanen gida da ihu, xa ki sha mamaki na" tana kai wa nn ta juya ta fice daga dakin ita ma, su Jiddah suka kuma kwashe wa da dariya, ya Aliyu ya dauki filo ya jefa masu a fusace snn ya Mike da sauri, da gudu suka fice daga dakin, ya juya yana kallon Afeefah ya galla mata harara yace "fita ki ban waje da'alla" mikewa tayi ta fice daga dakin a sanyaye.
Ees
hatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: Ya mace kyautar Allah
A true life love story
By Ashmaad
27__28
Afeefah ne xaune daki ita da Sadiya, ita tana karanta handouts dinta sadiya kuma na kwance tana danna wayarta, Mami ta shigo dakin tace "wae me ku ke yi ne? Ina Jiddah? Ku fito ku daura girkin rana don bbu yar da xan ma girki yau ta ci ku fito ku shiga kitchen" tana kai wa nn ta juya ta fita daga dakin, Afeefah ta ajiye handout din hannunta da sauri ta kwanta tare da lumshe ido kmr me bacci, Sadiya tace "ehh kya ma bude idon ne yarinya, sannun ki da wayo" tana kai wa nn ta fice, Afeefah ta kuma gyara kwanciya kmr me bacci, Jiddah ce ta shigo dakin bayan kusan minti biyar tace "ke Afeefah baxa ki fito mu shiga kitchen bne" Shiru Afeefah tayi kmr me baccin gske, Jiddah ta juya ta fice, Mami ce ta shigo dakin a tsawace tace "Zainab!" Mikewa xaune tayi da sauri tana murxa ido kmr xata yi kuka tace "Mami ni bacci..." Bayi ta shige da gudu ta kulle tun kan Mami ta karaso ganin ta yo kanta, Muryar Adnaan taji a dakin alamar Mami taje ta kirasa yana cewa "baxa ki fito ba sae na bude kofar nn, wa kika ajiye xae maki girki a gidan nn, ke baki da aiki sae dae a baki ki ci ki addabi mutane da kukan bnxa koh" murguda baki tayi kmr yana ganinta taki bude kofar, gate taji an bude downstairs ta washe hakora sanin ya Aliyu ne ya shigo, lkci daya ta saki kukan karya, Adnaan ya bude baki yana kallon kofar hka ma su Jiddah dake bakin kofar dakin a tsaye suna jiran fitowarta, muryar Aliyu su ka ji a corridor din rooms din yace "me ya faru?" Jiddah ta tabe baki tace "kaga yayanmu Mami ce fa tace mu je muyi girki shine ta shige bayi ta kulle" daga cikin bayin Afeefah tace "yayanmu ka ga fa karatu nake xa muyi test Monday" kmr xata yi kuka ta kare maganar, Aliyu ya watsa masu harara yace "mutane nawa xa suyi girkin? Ina su Sumayya?" Sadiya ta bata fuska tace "ba suna sch ba su" ya kuma watsa masu harara yace "ku biyu baxa ku iya girkin ba sae kace masu girkin gidan bikin, common get lost my frnd" Muryar Mami suka ji tana cewa "ka ga Aliyu ka fita idona bana son kana min hka a gidan nn ita wacece da baxata shiga kitchen ayi girki da ita ba, ta fi wani ne a gidan nn, ko idan ta tafi gidan mijinta ni xan bi ta ina mata girki?" Murmushi Aliyu yyi yace "sae mijin ya yafe mata girkin Mami," wani harara ta balla masa tace "Ka fita harkana fa, kuma ta fito idan ba hka ba in sa Adnaan ya daure min ita yyi mata shegen bugu" Juyawa Aliyu yyi yana hararan Adnaan, Adnaan ya fice daga dakin kmr xae tashi sama, Aliyu ya juya yana kallonsu Jiddah yace "ku bar dakin nn kar in taka ku" ficewa suka yi da sauri, Mami tayi kwafa ita ma ta fice tana cewa ta fito ta samesu kitchen idan ba hka ba sae dae ta ci bbu yau a gidan nn. Suna fita Afeefah ta bude kofar bayin, ta fito tana turo baki, ya Aliyu yyi murmushi ya kama hannunta ya nufi dakinsa da ita, har aka gama girkin rana Afeefah bata fita ba, Mami ta kwashe rabonta ta kara ma mai gadi Jiddah ta kai mashi, sadiya na kai ma ya Aliyu nasa a daki yace "Na Afeefah fa?" Tace "ina jin yana kitchen" yace "to dauko Mata," kai ta gyada masa ta fice duk da tasan bata da rabo, sae da ta isa falo ta fara dariya, ganin sadiya bata dawo ba yasa yace taje ta dauko abincin ta a kitchen da kyar ta yarda ta fita wae Mami xata doketa, tana shiga kitchen taga bbu komae an ma wanke tukunyar, ta koma sama kmr munafuka tace "sun cinye yayanmu" murmushi yyi yace "je dauko spoon ki xo mu ci nawa," kitchen ta koma ta dauko spoon suka ci a tare. Da yamma tana kwance dakin ya Aliyu tana kallo shi kuma yana dakin Mami wayarta ya soma ring mikewa tayi xaune ta dauki wayar gabanta na faduwa, wnn nmbr jiyan nn ne dae, sau uku yana kiranta yau bata dauka ba, mikewa tsaye tayi ta nufi dakinsu da gudu ta mika ma Jiddah wayar tace "Aunty Jiddah ki daga ki tambayi waye don Allah" karban wayar tayi tana kallon nmbr snn ta daga tayi shiru, jin anyi sallama yasa tace "wa ke magana wae," "ba da ke nake son magana ba, mika ma Zainab wayar" kmr munafuka ta mika ma Afeefah wayar. Afeefah tace "wae waye yace maki" Jiddah tace "oho" kara wayar a kunnenta tayi ta hade rae yace "Hello" tace "ina jin ka?" Murmushi yyi jin ynda ta amsa mashi yace "Me yasa kika ba yayarki wayar, kina tsorona ne?" Girgixa kai tayi tace "sbda me xan ji tsoron ka, ae Allah shine abun tsoro?" Yace "yea gskya ne," ta hade rae tace "kar ka kuma kiran layina ni ban san ka ba" yace "amma ni na sanki" a fusace tace "a ina ka san ni?" Cikin sanyin murya yace "nasan ki a bayero da kuma jan bulo" xaro ido tayi da mmki amma ta kasa cewa komae, yace "are yhu there?" Tsaki tayi tace "toh ni ban san ka ba kada ka kuma kiran layi na" katse wayar tayi ta jefar kan gado, Jiddah tace "wllh ki daina irin hka, baki san ko wani irin mutum bne kawae yaje ya cuce ki a bnxa, gwara ki bi sa a hnkli ku rabu lfya" Afeefah kmr xata yi kuka tace "to ni ya xan yi, bace kada ya kuma kirana ya ki ji" Jiddah tace "a hnkli xaki bi sa har ya rabu da ke, amma kar ki masa wlknci ko ki gaya masa bakar magana baki san wani irin mutum bne shi, baki kuma san meye a xuciyarsa ba, Afeefah ta bata fuska tace "wayyo na shiga uku to ina ya samu nmbrna Anty Jiddah?" Jiddah tace "oho ta ya xan sani nima" Afeefah tace "to in gaya ma yayanmu?" Da sauri Jiddah tace "ke! Gaya masa to tunda baki sa hnkli, so kike ya kirasa kawae ya xaxxagesa ki ja ma kanki" Afeefah tace "to to baxan gaya masa ba ba ruwana" fice wa Jiddah tayi daga dakin da sauri jin Mami na kiranta Afeefah ta xauna kan gado a sanyaye gabanta na faduwa, to waye wnn mutumin kuma, da daddare tana dan dube dubenta a wtspp Msge ya shigo da wani sabon nmbr, kura ma nmbr ido tayi lkci daya ta gane na me kiranta ne, gabanta na faduwa ta bude Msge din tana kallon sallamar da yyi mata, dakewa tayi ta amsa ko Allah xae taimaketa ya gaya mata inda ya Santa, bude Dp dinsa tayi da sauri tayi don ganin meye a kai, taga wata kyakkyawar yarinya rike da cake me kyau alamar birthday tayi, kallon yarinyar kawae take don gani take kmr ta taba ganinta amma ta rasa a ina, can ta fita taga bae mata reply ba still, kin sauka tayi tana jiran reply din, har bayan kusan minti takwas snn reply ya shigo, "ba ki yi bacci ba? Yhu re suppose to b readin ur book fa, who are yhu chattin with this late?" turo baki tayi ta mayar masa da cewa "Don Allah where did yhu get my contact frm, don Allah na ce" sae bayan kusan minti biyar reply ya shigo, "Go offline now!" Tsaki ta dan yi tana mmkin irin command din kmr ta san shi, reply ta mayar masa tace "ba ka ma Allah knn?" Lkci daya ya mata reply da cewa "to wa ke xan ma idan ban ma Allah ba, common go offline my frnd, idan baxa kiyi karatu ba ki kwanta kiyi bacci nd stop wasting ur tym here" ji tayi kmr ta saka kuka don takaici, gashi tana tsoron masa musu da ta tuno maganganun Jiddah, "OK" kadae ta mayar masa snn ta sauka ta kashe data ta jefar da wayar gefenta tayi kwanciyarta. Washegari kmr jiya vibration din wayar ta ne ya tasheta, ta jawo wayar da kyar tana kallon screen, din ta wara ido da sauri ganin lambar, samun kanta tayi da dagawa daga daya bangaren taji yace "almost tym for sallat baccin ya isa hka Madam" takaici ne ya isheta cikin bacin rae tace "to Ca nayi maka bbu masu tashi na ne a gidan mu" a nutse yace "ban ji ba, me kika ce" tsoro ne ya kamata tace "Ca nayi nagode, ynxu xan tashi" yace "OK" snn ya katse wayar. Da safe suna xaune dinnin suna breakfast, da ke ranan Saturday ne har da Adnaan da ya Aliyu Mami ce kadae bata dinnin din, Sumayya tace "ya Aliyu wnn hutun ka dde sosae" Afeefah ta galla mata harara tace "just two wk shine xa ki ce ya dde...." Wayarta da ke vibrate ne yasa tayi shiru tana kallon screen din wayar, ta dago kai tana kallon Jiddah da ta tabe baki ta ci gaba da shan tean ta, mikewa tayi ta nufi stairs da sauri, ya Aliyu ya bi ta da kallo, dakinsu ta shiga ta daga kiran kan ya katse ta kara a kunne, "Ae nayi xaton baxa ki daga ba" murguda baki tayi kmr yana ganinta ta ki cewa komae, "Zainab!" Ta amsa da "Na'am," yace "Gud mrnin" da kyar ta iya mayar masa da gaisuwar, yace "kinyi breakfast," girgixa masa kai tayi tace "shi nake yi" yace "okk srry, sae anjima" ji tayi an bude kofar dakin ta katse wayar da sauri ta juya tana kallon ya Aliyu, yace "wa ya kira ki?" Kame kame ta soma yi tace "yayanmu, kaga dama yayanmu Maryam kawata ce ta kirani," a nutse yace "karya kike, tell me the truth wa ya kira ki" muryarta na rawa tace "Ita ce yayanmu" ya fi minti biyar yana tsaye yana kallonta snn ya fice daga dakin, ta sulale kan gado ta xauna tare da sauke ajiyar xuciya, hka ta karashi mid break a gida a kullum xa a kirata sau hudu sau biyar kuma bata kin dagawa sbda abinda Jiddah ta gaya mata sae dae har lkcn ya ki gaya mata waye shi, kiri kiri ta daina hawa wtspp sbda shi don da ta hau xae ce ta sauka barin da nyt, gashi bata iya masa musu. Ran Monday da yamma ya Aliyu ya kare hutunsa ya kama hanyar lagos, Washegari Tuesday kusan a tare suka shigo sch da Dr Sharif, Afeefah ta sunkuyar da kai bayan su Jiddah sun nufi department dinsu, har sae da ya karaso inda take snn ta gaishesa, ya amsa va tare da ya kalleta ba ya nufi office dinsa. Har ya dan yi nisa ya juya yana kallonta yace "come, xo ki gyara min office" kmr munafuka ta bi bayansa ya bude office din suka shiga, yace "Just 10 mins ki gama gyara min office kafin in dawo" yana kai wa nn ya fita ta fara abinda ya sa, har ta gama bae dawo ba, ta gyara masa kan table dinsa ta jera masa duka buks dinsa gu daya, snn ta nemi guri ta xauna, har kusan takwas da rabi bata gan shi ba gashi suna sa lecture, taji kmr tayi kuka, sae kusan Karfe tara da rabi ya shigo yana kallonta yace "srry na je clinic ne, you've missed ur lecture koh?" Hade rae tayi bata ce komae ba ya karaso ya xauna yace "Wani lecture ku ke da shi" kanta a kasa ta gaya masa yace "to fiddo littafin kiyi karatu" mikewa tayi yace "ina xa ki?" Tace "xan fita in je inyi" yace "sit, kiyi a nn wajen" komawa tayi ta xauna kmr xata yi kuka snn ta fiddo littafin, shi dae sae kallonta yake ta farin glass din idonsa, can bayan minti kusan bakwae ta saci kallonsa taga idonsa na kan wani littafi, ta sunkuyar da kanta, bude kofar aka yi aka shigo da sallama Afeefah ta kafa ma yarinyar ido, yarinyar ta karasa kan table din tana cewa "yaya don Allah ka xo kayi ma baba sanusi magana, ka ji wae baxae kai ni ba yawo nake son xuwa" kallonta kawae yake ta ajiye basket din hannunta ta marairaice, Ya ajiye pen din hannunsa yace "Ummi ta sa ni ne" tace "ta sani mana, kawae shi sae ya dinga min abinda ya ga dama," mikewa Dr Shariff yyi yace "mu je" yarinyar tayi gaba yana biye da ita a baya, Afeefah ta bi su da kallo snn ta fiddo wayarta da sauri ta duba Dp din mutumi me kiranta taga hoton yarinyar ce a kai, duk sae tayi confuse tana tunanin to ko Dr Sharif ne ke kiranta, amma ae bae da nmbr ta, dubara ce ta xo mata tayi dailin nmbr dake kiranta, cikin second biyar wayar Dr Sharif da ke kan table ya soma ring, still tayi tana kallon table din, jiki ba kwari xata karasa table din ya shigo office din, juyowa tayi da sauri, yana kallonta yace "kina neman abu ne" girgixa masa kai tayi a daburce tayi saurin katse kiran da take masa, ya karasa table din yana kallon wayarsa murmusi dauke fuskarsa yace "lfya kike kirana" sunkuyar da kai tayi a hnkli tace "Sirr," Karasowa gabanta yyi yana kallon fuskarta yace "ya aka yi" kin bari su hada ido tayi murya can kasa tace "kayi hkuri ban san kai bne ba" murmushi yyi yace "to ynxu kin sani koh?" Juya masa baya tayi da sauri ta rufe fuskarta, ya nufi kujera ya xauna ya jawo basket din da Kanwarsa ta kawo masa ya shiga hada coffee, Ita dae har lkcn bata juyo ba, can ta nufi kofa tace "Na tafi Sir" a nutse yace "Zainab!" Juyowa tayi tana kallonsa snn ta karasa table din tace "gani sir" kujera ya nuna mata ta xauna snn ya mika mata mug din coffee. Girgixa masa kai tayi kanta a kasa tace "Ngd sir" jin bae ce komae ba yasa ta dago kanta a hnkli ta ga kallonta yake, sauke idonsa yyi daga kallon nata ya ajiye mata gabanta yace "je ki xubar a waje to" murmushi tayi ta dauki mug din a hnkli ta kai bakinta, rabi ta sha ta ajiye ba tare da ta kallesa ba tace "na koshi Sir" bae ce mata komae ba ta mike kanta a kasa tace "Sir I want to go nd read for test" yace "OK" snn ta fice daga office din. Ana gama sllhn Azahar Afeefah ta nufi lecture hall dinsu da Maryam, Maryam ta xauna kujerar gaba Afeefah tace "ke test fa xa muyi, mu koma baya" Maryam ta xaro ido tace "wani test?" Afeefah tace "na Dr Sharif mana" harara Maryam tayi Mata tace "ke wa ya gaya maki" Afeefah tayi shiru da dan mmki tana kallonta, sae a snn ta tuna ashe fa ita kadae ya gaya ma, "wllh nayi xaton kin sani, kuma bamu hadu yau bne da na gaya maki" Maryam tace "kin kyauta ae, da ni ce da na kira ki" bata jira cewar Afeefah ba ta nufi seat a baya, Afeefah ta bi bayanta sanin bata kyauta mata ba, gefenta ta xauna ta marairaice tana bata hkuri, Dr Sharif ya shigo hall din, tsit kke jin hall din bayan minti daya kowa yyi settle down, Dr Sharif yace "I will b conducting my last test today, hope yhu all are ready" kallonsa students suke da mamaki, bae damu da hka ba ya bukaci duk su fito da jakansu da any material da suka san is nt proper to b with dem while writtin his test, mikewa Afeefah tayi ta karbi jakar maryam da nata bayan sun dauki pen da takardar sa za suyi test din ta nufi front din hall din ta ajiye, hada ido suka yi ta dauke kai da sauri ta bar wajen ya bi ta da kallo, dictating questions din yyi masu snn ya basu time yace "this my last test, any one dat misbehaves I will cancel all the test he has done so far, I strictly warn yhu once more to respect ur selves" tsayuwarsa yyi bakin kofa yana danna wayarsa, bayan minti goma Afeefah ta juya tana kallon Maryam ta ga guda biyu kadae tayi ta ajiye pen, kallon Dr Sharif Afeefah tayi taga wayarsa yake danna wa, murya can kasa tace "kawo in rubuta maki 2 nd 4 a bayan paper da pencil sae ki goge da eraser" Ganin maryam bata tanka ta ba yasa ta mika mata papern nata gaba daya tace to gashi ki kwafa, nn ma bata ce komae ba, hkn yasa ta daga kai tana kallonsa ta ga kallonta yake, ajiye takardarta tayi da sauri, Dr Sharif yace "stand up" a hnkli kmr me shirin kuka tace "am srry sir" wani kallo ya watsa mata ba shiri ta mike ya nuna mata kofa alamar ta xo ta fita, kmr xata yi kuka ta nufi gaban class din tace "sir plss am srry i...." Tsawa ya daka mata yace "out!" Jakarta ta dauka ta fice daga class din ta nufi main gate, ta rasa dalilin da yasa bata yi kuka ba, cukuikuye takardar test din nata tayi ta jefar snn ta tsaida adai daita sahu ta hau ta tafi gida abunta.
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: Ya mace kyautar Allah
A true life love story
By Ashmaad
29.....
Mami na kitchen Afeefah ta shigo gida, Mami
tace "Har kun tashi?" Afeefah tace "ehh," snn ta
gaisheta ta nufi sama, kwanciyarta tayi bayan ta
jefa jakarta kan gado, nan da nan bacci ya
dauketa, vibration din wayarta da ke jakarta ne
ya farkar da ita ta mike xaune tana mitsika ido ta
jawo jakarta ta bude ta ciro wayar, tana kallon
me kiran nata, Nmbr Dr Sharif ne, ta yi tsaki ta
ajiye wayar ta koma ta kwanta. Da daddare tana
gugan Hijabbanta wayar ta ya fara vibrate ta
dauka tana kallon me kiran taga Nmbr Dr Sharif
ne still, sae da ya kusa katsewa snn ta daga, ta
kara a kunne tayi shiru, "kin ga dama knn" nn ma
shiru tayi masa, yace "Zainab!" Kin amsawa tayi
se da ya kuma kiranta tace "Na'am" hade da
murguda baki, "me yasa na kira ki daxu ba ki
daga ba" a takaice tace "bacci nake" yace "koh"
shiru tayi masa, ya dan yi murmushi yace "yhu
will explain dat tomorrow," katse kiran yyi, ta ja
dogon tsaki ta ajiye wayarta ta ci gaba da abinda
take. Tun daga ranan Afeefah ta soma wasan
yar buya da Dr Sharif da ta gansa xata gudu ta
canxa hanya idan ya kira ta ki dagawa, duk inda
tasan xae ganta daina xama tayi a gun, in suna
da lecture dinsa to ranan da wuri xata wuce gida,
masallaci ma Dena xuwa Wanda xa su hadu tayi,
sbda shi ta goge wtspp a wayarta, sae dae fa
ynxu kukan ta ya ragu ssae har aka dinga
Mamakin hka a gida, sau da yawa Maryam kan
tambayeta wae me ya hadata da Dr Sharif take
gudu idan ta gansa, sae dae tace bbu komae,
ana hka suka fara Shirye shiryen exams, ana
saura sati daya exams dinsu Afeefah na xaune
gaban department dinsu da su Maryam an gama
tsula ruwa knn, duk ta sakankance ranan dr
Sharif bae xo ba don bata ga motarsa a parkin
space ba kawae ta hangosa yana tahowa da
wani student da alamar lecture ya fito, mikewa
tayi da sauri ba tare da ta lura da wani katon
dutse dake gefenta ba xata falla a guje ta buge
kafa da dutsen sae ga ta kasa cikin ruwa, lkci
daya ta fasa ihu uwa wata jaririya tana cewa
wayyo kafarta, su maryam tuni suka mike a rude,
Maryam ta fara kkrin dagota amma ta kasa don
kin tashi tayi, Dr Sharif ya karaso gun da sauri
shi ya dagota ta fashe da wani matsanancin
kuka tana cewa wayyo kafarta, office dinsa ya
nufa da ita ya sa ta xauna kan kujera har lkcn
tana kuka, yana mata mugun kallo yace "ni
dodonki ne da xaki dinga gudu idan kin gan ni
Zainab? An ce maki ina da lkcn ki, listen daga
yau kika kuma gudu idan ki ka gan ni, I will make
yhu spell doom" kuka kawae take tana yarfe
hannunta, a dan tsawace yace "pull off dat hijab
my frnd" tana kuka ta fara kkrin cire hijab din
don duk ruwa ne da datti, yyi tsaki ya mike ya
nufi first aid box dinsa ya dauko ya dawo
gabanta ya durkusa yana kallon kafarta da ke jini
amma ya kasa taba kafan, yace "ina ke maki
ciwo?" Ankle dinta da toes ta nuna masa da
kneel, ya rasa ynda xae ce ta daga skirt din ma,
kawae ya Mike ya nufi table ya dauki wayarsa,
wata nurse ya kira tana dagawa yace "kina duty
ne pls farida" ta amsa masa da tana gida, yace
"OK plss ki xo Buk ynxu, over to my office wata
student dina ce taji ciwo xa kiyi mata dressing"
tace ga ta nn xuwa, yace "olryt tnxx" snn ya
katse wayar, kanwarsa teemah ya kira yace
"Fatima plss ki taho sch ynxu da spare hijab din
ki" bae amsa tambayoyin da take jefa masa va
yace "just come over" snn ya katse kiran ya
dawo kusa da Afeefah dake hawaye har lkcn, ya
daure fuska yace "srry" kae kawae ta gyada
masa a hnkli ba tare da ta kallesa ba, yana tsaye
kanta har Nurse Farida ta shigo office dinsa da
sallama yyi welcoming dinta, Nurse Farida ta
duka tana kallon kafar Afeefah yace "garin ya
hka" Dr Shariff yace "she's runnin ne" yar dariya
Farida tayi snn ta shiga fiddo kayan da xata
gyara mata kafar a first aid box, yace "ki duba
mata ankle dinta ma its hurting her" kuka
Afeefah ta fara ganin matar ta tsoma cotton
wool tace "na shiga uku sir kace ta min a hnkli
xae min xafi" harara ya balla mata yace "Naki"
da kyar ta bari nurse Farida ta wanke mata kafar
tana kuka, ya fita don bata waje ta duba mata
knee dinta, nurse Farida ta ga gurjewa kawae
tayi shima ta wanke mata snn tace "to sannu an
gama yan mata" Afeefah ta share hawayenta ta
mike xata sa hijab dinta ta ji ta kasa tsayuwa da
toes dinta ta koma ta xauna da sauri tace "xafi"
matar ta kuma duba kafar tace "kin yi targade
knn" kuka ssae Afeefah ta dinga yi tana yarfe
hannu, nurse din ta fita ta kira Dr Sharif tace
"Doctor tayi targade ne fa" kallon kafar kawae
yake snn ya karasa ya duka kusa da ita yace
"Sae an kai ki asibiti knn" Afeefah ta fashe da
kuka tace "Sir ni ba sosae fa yake min ciwo ba"
nurse Farida tace "Haba Dr ka gyara mata mana
ba sae anje asibiti ba" girgixa kai yyi yace "su
tafi asibiti dai" Dubu daya ya ba ma nurse din
tayi transport bayan yyi mata godiya ta wuce,
tana fita Fateema ta shigo, ledan hannunta ya
karba ya ciro hijab din ciki ya mika ma Afeefah,
ta karba kanta a kasa, Fatima tace "Yaya me ya
sameta" yace "gudu take ta fada cikin ruwa"
Fatima tace "eyya sannu" kasa dago kai Afeefah
tayi, Dr Sharif yace "yhu can go, ko ba tare da
driver kike ba," sallama tayi masa ta fita daga
office din, ya kalli Afeefah yace "tashi in yi
dropping din ki a gida, sae ki fadi kinyi targade a
kai ki clinic" mikewa tayi ta dauki hijab dinta ta
linke snn ya fita daga office din bayan ya dauki
car key dinsa ta bi bayansa tana dingishi, har
kofar gidansu ya ajiyeta, kanta a kasa tace "ngd
sir" snn ta bude motar ta fita ta nufi gate da kyar
sae kuma ta tsaya tana yarfe hannu, Dr Sharif ya
fito yana kallonta yace "ya aka yi?" Durkushewa
wajen tayi Cikin kuka tace "ni baxan iya tafiya ba
kuma ciwo kafata ke min" xae yi magana aka
bude gate dinsu, Mami ta fito da Rahamah,
Afeefah ta mike da sauri, Mami da bata ma kula
da Dr Sharif ba ta bude baki tace "meye hka
Zainab" kuka ta saka tace "Mami faduwa nayi a
cikin ruwa a makaranta ynxu gashi bn iya tafiya
sosae ba, shine ya dawo dani gida, ina jin kafar
ya karye ne" Rahmah ta juya ta fashe da dariya,
Mami ta hade rae tace "ke mahaukaciya ce da
xa ki fada cikin ruwa Zainab," ta girgixa ma
Mami kai tana hawaye, sae a snn Mami ta kalli
Dr Sharif, kansa a kasa ya gaisheta ta amsa tare
da cewa "mun gode bawan Allah" Afeefah ta
karbe da sauri tace "kuma makarantar mu daya
fa, shine ya kira aka sa min spirit da magani"
tana kai wa nn ta nufi cikin gida da kyar tana
dingishi, godiya Mami ta kara masa tace baxa ka
shiga daga ciki ba, dan murmushi yyi yace "A'a
mama, ngd" tace "To Allah saka da alkhairi"
sallama yyi mata ya shiga motarsa ita kuma suka
koma cikin gida da Rahmah don dama kasuwa
xata rakata ynxu kuma bbu maganar xuwa
kasuwan. Da daddare Afeefah na kwance daki
bayan Mami tasa Adnaan ya siyo mata
mugunguna a pharmacy ta sha kiran Dr Shariff
ya shigo wayarta, jawo wayar tayi ta daga a dan
kunyace tayi shiru, cikin sanyin murya yace "ya
kafar Zainab?" A hnkli tace "da sauki," yace "kun
je asibiti?" Tace "um um ni nace bna so," yace
"to ae sae an ja maki kafar xae daina," tace "ni
bana so ya dan daina" shiru ya dan yi snn yace
"in kawo maki fruits xa ki sha," shiru tayi bata ce
komae ba, yace "Zainab!" Tace "umm xan sha"
yace "mama xata bari ki fito?" Nn ma ta dan yi
shiru snn a hnkli tace "kila."
Eeshatullah Goni
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
30......
Bayan minti sha biyar Jiddah ta shigo dakin tana kallon Afeefah tace "ke ana neman ki downstairs," Afeefah ta mike xaune tace "ni?" Tsaki Jiddah tayi tace "A'a ni" snn ta fice daga dakin, Afeefah ta mike tana kallon kafarta da ke mata ciwo har lkcn, kasa taka kafar tayi don wani shegen ciwon da taji yana mata, da kyar tana dingisawa ta fita daga dakin ta sauka kasa, xaune ta ga yarinyar a falo Mami ma na xaune falon da Adnaan, Da kyar ta karaso cikin falon tana dingishi Mami tace "wae kafar har ynxu?" Kmr xata yi kuka tace "ciwo yake min sosae Mami" Mami tace "to sae a tafi asibiti gobe" Afeefah ta dan yi Mamakin ganin kanwar Dr Sharif, ta kirkiri murmushi tace "sannu da xuwa' yarinyar ta mayar mata da murmushin tace " ya jikin" Afeefah tace "da sauki" Ledan hannunta ta ajiye tace "Yayana yace in kawo maki" Afeefah ta kalli ledan a dan kunyace tace "ngdd" mikewa yarinyar tayi tace "ni xan koma Mumy ana jirana waje" Afeefah tace "tare ku ka xo?" Kai fateema ta gyada mata, Mami tace "ae da ya shigo," murmushi Fateema tayi ta kuma yi masu sae da safe, Mami ta kalli Afeefah da bata da niyar tashi tace "baxa ki rakata bane Afeefah" mikewa Afeefah tayi ta karbi hijab din jiddah tana dingishi ta bi bayan fateema da har ta kai kofa, har suka fita daga compound din bbu Wanda yace komae cikinsu, sauke glass din motar Dr Sharif yyi Afeefah ta karasa jikin motar kanta a kasa tace "ina yini sir" kallon kafarta kawae yake ta daga kai tana kallonsa jin bae amsa ba yace "har ynxu kafar bae daina ba" gyada masa kai tayi, yace "meyasa baki son a je asibiti a duba maki" tace "kila xa su ce xa su min allura kuma ni bna so" murmushi kawae yyi, a hnkli tace "sir ngdd" yyi noddin kansa yace "welcm, ki gaida mama" tace "xata ji," sae da safe ta kuma yi ma fateema snn ta nufi cikin gida ya bi ta da kallo, dariyar fateema ya sa ya dauke kai da sauri ya juya yana kallonta yace "meye hka" dariya take sosae ta kashe masa ido tace "waow at long last yaya!" Murmushi kawae yyi ya tada motar yyi reverse, tace "yaya amma student din ka kuma?" Harara ya galla mata ya maida hnklinsa kan tukin da yake. Afeefah na shiga gida Mami tace "har sun tafi" gyada mata kai kawae tayi ta kwanta kan kujera, Adnaan yace "kawar ki ce" mikewa xaune tayi da sauri tace "ehh ya aka yi?" ya daga kafada yace "na ga yarinyar na da hnkli da natsuwa ne" dariya Afeefah ta fashe da tace "ahaf ta dai fi karfin ka wllh gwara ma ka daina gnin hnklinta da natsuwa, class din yayanmu ce wnn" da gudu da yar kafarta me ciwo ta nufi sama tana kyalkyala dariya su Jiddah da Mami na taya ta.
Washegari da kyar Afeefah ta yarda aka tafi da ita asibiti a duba mata kafa, ba karamin wahala ta ba likitan da xae gyara mata targaden ba don sae da aka riketa ta dinga rusa masu ihu har sae da Adnaan ya mareta snn suka dan samu lfya, da yamma tana kwance ta fara bacci Dr Sharif ya kira wayarta, da kyar ta iya dagawa don har xaxxabi sae da targaden ya sa mata, murya can kasa ta gaishesa, yace "ya kafar kun je clinic" kuka ta sakar masa tace "bayan mun je an ja min, gashi wani sabon ciwo yake min" yace "wa ya ja maki?" Tace "wani likita ne mugu mana," yace "kiyi hkuri xae daina" da kyar tace "to" snn yyi mata sallama ta ajiye wayar, har kusan magrib Afeefah kasa tashi tayi daga kwancen da take tsabar ciwon da kafar ke mata, Mami ta shigo tace "wae har ynxu kafar ciwon yake maki?" Kmr xata yi kuka tace "Kinga Mami kumbura fa kila xae yi" Mami ta kalli kafar tace "gskya bae gyaru ba knn sae an koma" Afeefah ta fashe da kuka a tsorace tace "don Allah Mami kar mu koma wllh xae kuma mun tsami ne, kila sae xuwa gobe xae daina" Mami ta galla mata harara tace "a hkn kafa ya fara kumbura xa ki ce gobe xae warke? Bari dae Adnaan ya shigo" kuka ssae Afeefah take don bata mance axabar da ta sha daxu ba, Mami bata bi ta kanta ba ta fice, ana idar da magrib Adnaan ya shigo ya kalli kafar yace "ki tashi ki shirya mu koma" kuka ta kuma fashewa da bae bi ta kanta ba ya fice, tana cikin kukan wayarta ya soma ring ta dauka tana kallon Mae kiran, da kmr baxata daga ba da taga Dr Sharif sae kuma ta daga, ta sakar masa kuka tace "Sir kaga wae mai dani asibitin xa ayi a kuma jagwalgwala min kafar koh" shiru yyi bae ce komae ba ya barta ta ci gaba da kukanta, can yace "Zainab, where is d promise yhu made for me?" Hadiye kukan tayi lkci daya tace "ni?" Jin bae amsa ta ba yasa a hnkli tace "Kaga fa sir abun da xafi shi yasa nake kuka, wllh akwae xafi" yace "to ya isa, kina son ni in ja maki kafar?" A hnkli tace "ka iya ne?" Dan murmushi yyi yace "na iya" tace "to xan gaya ma Mami sae kae ka min," yace "OK," snn ya katse wayar, Afeefah ta shiga kwala ma Anty Jiddah kira, Jiddah ta shigo tana hararanta tace "lfya?" Afeefah tace "dan Allah kira min Mami baxan iya tashi ba" tsaki Jiddah tayi ta fice, ba a dau lkci ba sae ga Mami da Adnaan sun shigo dakin Adnaan na rike da makullin mota, Mami tace "ki tashi ki sa hijab" da sauri tace "Mami tsaya ki ji, wnn mutumin da ya kawo ni jiya yace xae gyara min kafar wllh, Dr ne shi ma, sunansa Dr Sharif Mami" Adnaan yace "to kawae Mami ya xo ya gyara mata don ni har tunanin tafiya asibiti nake da ita wllh" Afeefah ta marairaice tace "Ehh Mami, nima har tunanin binsa nake wllh" Mami tace "munafuka, ae sae ki kirasa ya xo ya gyara maki tun da hka kika fi so" dan murmushi tayi tace "to Mami" Mami ta fita Adnaan ya bi bayanta, suna fita wayarta ya soma ring ta jawo da sauri a tunaninta Dr Sharif ne sae ta ga ya Aliyu, a hnkli ta daga ta kara a kunne tare da cewa "yayanmu" "daxu na kira naji buzy, ke da wa kuke waya Afeefah?" Xaro ido tayi a dan tsorace tace "bbu kowa, ntwrk ne" "karya xa ki min knn" yarfe hannu tayi kmr xata yi kuka tace "yayanmu ni da kafata ke min ciwo ma tun safe bn san inda na jefa wayar ba" sauke ajiyar xuciya yyi yace "toh shknn princess, ya kafar ynxu" a hnkli tace "da sauki" yace "Adnaan xae kawo maki ice-cream na kira sa nace ya je ya siyo maki" washe hakora tayi tace "yauwa yayanmu nagode, nayi missin din ka ssae wllh" murmushi yyi yace "OK xan kira ki ltr ki min hira" tace "olryt yayana bye" ko ajiye wayar bata yi ba kiran Dr Sharif ya shigo wayar, kmr munafuka ta daga yace "ke da wa ku ke waya Zainab?" A hnkli tace "yayanmu ne Wanda ke lgs" yace "OK," tace "Sir na gaya ma Mamina tace to ka xo sae ka ja min kafar"
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
31__32
Adnaan ne yyi ma Dr Sharif iso har falon saukan baki, Afeefah dama tun da Dr Sharif ya kirata yace ya iso ta soma matsar kwalla tana kallon kafarta, Adnaan ya shigo dakin yace "ae sae ki tashi Hajiyata" mikewa tayi da kyar ta bi bayansa tana dingishi, kmr xata yi kuka tace ma Mami "don Allah Mami ki bar su anty Jiddah su rakani don kar in yi kuka" Mami tace "in xa su rakaki su rakaki mana" Jiddah ta mike Sadiya kam tace "bbu inda xani ni kam" Afeefah ta marairaice ta kalli kaninnta Sumayya da Rahama tace "ku baxa ku raka ni ba koh?" Mikewa Sumayya tayi tana dariya hka ma Rahamah snn suka nufi falon baki, Yana xaune yana danna wayarsa, Afeefah ta xauna edge din kujera a sanyaye tace "Sir ina yini" gyada mata kai kawae yyi, Xauna wa su Jiddah suka yi suma duk suka gaishesa, Jiddah sae kallonsa take da mugun mmki don tasan wnn ae lecturer ne, Dr Sharif ya amsa yana masu murmushi, Adnaan ya shigo falon yana kallonsu Jiddah da mmki yace "ku kuma me ku ke yi a nn" Afeefah ta marairaice tace "Allah sarki ya Adnaan ni fa nace su rakani kar in yi kuka" harara ya galla mata yace "sha sha sha kawae, har kina da bakin mgna" dariya su Sumayya suka yi, ya juya ya fice daga falon, Dr Sharif ya kalli Rahama yace "Get me cold water sis" mikewa Rahama tayi ta nufi fridge ta fiddo da ruwan sanyi ta mika masa ya karba snn ya mike ya nufi inda Afeefah take xaune, ya durkusa yana kallon kafarta, sae kuma ya mike ya fita daga falon yana rike da ruwan sanyin, ya wanke hannunsa snn ya dawo ya duka gabanta yace "Daurewa fa xa kiyi ki rufe ido" kai ta gyada masa hawaye na taruwa idonta, a hnkli ya daura hannun kan kafar, Afeefah ta sake kara ta dafa sa cikin muryar kuka tace "Sir wllh xafi yake min" hararanta yyi yace "take ur hands off me" ba shiri ta dauke hannunta daga kafadarsa, yace "Zainab!" Tace "Na'am" "ki rufe idon ki ki daure nace" Kai ta gyada masa hawaye na sakko mata, runtse ido tayi jin ya kuma kama kafar a hnkli, ba karamin daurewa ta dinga yi ba kar ta saki ihun bakinta, daga karshe dae dauriyarta ya kare ta kuma fasa ihu ta dafasa tana cewa "Wayyo Sirrr yana min xafi wllh" a dan tsawace yace "Zainab!" Muryarta na rawa tace "Sirr, ba kuka nake ba" yace "let go of me" cire hannunta tayi da sauri, yace "nace ki rufe idon ki" da sauri ta kuma runtse idonta, ba karamin axaba ta sha ba gashi Dr Sharif ya hanata kuka, hka tayi ta daurewa har sae da ta gaji ta saka masa kuka ssae, bae tanka ta ba ya gama abinda xae yi ya ji kafar yyi dae dae snn ya mike yana kallonta, juyawa tayi da sauri ta rufe fuskarta da kujera ta dinga kuka tana yarfe hannu, ya kalli Jiddah yace "Anty a dan taimaka min da man xafi" murmushi tayi ta Mike ta fita daga falon, ba a dau lkci ba dawo da man xafin ya karba ya duka gaban Afeefah juyowa tayi da sauri tace "Sirr" yace "srry shafa maki maganin xan yi kawae" mikewa yyi bayan ya gama shafa Mata, yace "Allah ya sauwake" Sadiya ce ta shigo falon autan Mami fadila na biye da ita rike da faranti me dauke da drink da ruwa, ta ajiye suka gaisa da Dr Sharif da take ma kallon mamaki ita ma, Afeefah tace "Sir kai fa aka kawo ma ruwa" murmushi yyi yace "am OK, tnx a lot" Sadiya tace "A'a da dae ka sha kadan sir" Murmushi kawae yyi ya xauna yana kallon fadila ganin ynda suka yi kama da Afeefah yace "hw are yhu" murmushi tayi tace "Fyn sir" "wani class kike?" Tace "am in ss1" ya ce "Nyc, art, science or a commercial student?" yar dariya tayi tace "Science student ce ni Sir" yace "Umm I c, wats ur favourite subject?" Ta wara ido tace "Biology Sir" ya xaro ido yace "Really?" Ta gyada masa kai yace "to in maki tambaya?" Mikewa xaune Afeefah tayi ta kyalkyale da dariya tace "Sir yi mata, bbu abinda ta sani sae kuka wa Mami" xaro ido duk occupant din falon suka yi jin abinda Afeefah tace, lkci daya suka saka dariya Dr Sharif dake murmushi yace "keep mute my frnd, ba ke taga kina yi ba" Fadila da har ta bata rae ta yi murmushi tana kallon Afeefah da tayi shiru bata ce komae ba, Dr shariff ya kalli Fadila yace "Dnt wrry, baxan maki question ba because yhu just started, amma ki maida hnkli ssae a karatu kin ji" Fadila tayi murmushi ta gyada masa kai tace "ngdd sir" Sumayya ya kalla yace wani class ke kike, tace "Ss2 sir" yace "dats Gud, a science student?" Gyada masa kai tayi tace "yes sir" yace "okk I will ask yhu questions some other tym" ya kalli Rahmah yace "ke fa" ta sunkuyar da kanta tace "am also in ss2 sir" yace "uhm great, I will also ask yhu questions some other tym" ta gyada masa kai tace "OK sir" Su Jiddah ya kalla yace "kuna 300lvl a buk studying Micro biology ryt?" Murmushi duk suka yi suka ce hka ne, yace "na taba shiga ajin ku?" Suka ce "ehh kana shiga, kuma muna haduwa a laboratory sosae," yyi murmushi yace "to ku maida hnkli a karatu kun ga ku ne manya, but if am nt mistaken kuna da yaya da ta taba Micro bio?" Jiddah tace "ehh Anty safeeya da Farida sun yi aure kuma" yace "Yea naga kuna kama ne da su" "Allah ya taimaka" duk suka ce Ameen, sosae yyi Mamakin duk yayyin Afeefah da kanninta mata ne, bae san cewa duk _'ya mace kyautar Allah_ ba ce, mike yyi yana kallon Afeefah ya ga ta wani hade rae, kmr xata yi kuka tace "Shine ni baka tambayeni komae ba koh sir" murmushi yyi yace "to izun ki nawa a islamiyya?" A hnkli tace "na sauke" dariya yyi yace "Ma'sha Allah ashe ke din Malama ce?" Murmushi tayi ta boye fuska yace "to Allah sa na tsoron Allah ne" tace "Ameen" to tashi ku je ki ce ma yayanku xan tafi, tace "Sir kafar fa?" Yace "a hka xa ki tafi" mikewa tayi tana durdurkusawa ta fita daga falon, ba a dau lkci ba sae ga shi sun dawo da Adnaan, Adnaan yyi masa sannu da aiki, Dr Sharif yyi murmushi yace "ae na gama wucewa xan yi," Adnaan yace "to mu shiga ku gaisa da Mamin mu," ba musa Dr Shariff ya bi bayan Adnaan suka nufi main falo, Mami na xaune falo Afeefah na xaune gefenta tana nuna mata kafarta suka shigo falon, sauke kafar tayi da sauri, Dr Sharif ya sunkuyar da kai ya karaso cikin falon da ladabi ya gaida Mami ta amsa da fara'a tana tambayarsa mutanen gida, yace "duk suna lfya" Mami tace "to ya sunan?" Murmushi yyi ya kuma sunkuyar da kai yace "sunana Aliyu" Mami tace "Au ashe ma 'da na ne, to mun fa gode Aliyu Allah maka albarka" yace "Ameen mama, ni xan koma" Mami tace "baxa ka ci abinci ba" yace "Alhmdllh mama na ci a gida" Mami tace "toh Allah tsare, mun gode ssae" sallama su Jiddah suka yi masa snn ya nufi kofar fita Adnaan na biye da shi a baya don ya rakasa, Mami ta buge Afeefah tace "baxa kiyi masa sae da safe ba" turo baki tayi tace "sae da safe," amma tuni ya fita, a bakin gate suka hadu da Abba cikin motarsa yana jiran Mai gadi ya bude masa gate, Adnaan ya karasa yyi masa sannu da xuwa da ladabi, snn yyi ma Dr Sharif alamar ya xo su gaisa, Dr Sharif ya karasa gun motar ya gaida Abba cike da ladabi, Abba na kallon Adnaan yace "bako kayi knn" Adnaan yyi murmushi Abba ya ja motarsa ya shiga gidan don mai gadi ya bude masa gate din, Adnaan ya raka Dr Sharif har inda motarsa yake snn ya kuma yi masa gdya yyi masa sae dae safe ya koma cikin gida, Karfe goma da rabi Afeefah ta mike daga falo don wucewa sama tayi bacci, ji tayi kafar ya rage mata ciwo ssae, ta nufi sama tana dingisawa ta shiga bedroom dinsu ta cire kayan jikinta ta shiga wanka, ko da ta fito turare kawae ta shafa ta sa kayan baccinta ta nufi kan gado ta kwanta ta ja bargon snn ta dauki wayarta, mis cals har shidda ta gani ta xaro ido ta bude da sauri don ganin ko na waye, ta ga na yayanmu har biyar sae na Dr Sharif guda daya, kmr xata yi kuka take kallon mis cals din ya Aliyu gashi ba ta da kati bare ta kirasa, kiran Dr Sharif ne ya shigo wayar, tayi shiru tana kallon wayar har ya kusan katsewa snn ta daga ta kara a kunne tayi shiru, A hnkli taji yace "Zainab!" Tace "uhm" "ba kiyi bacci ba" murya can kasa tace "ynxu xan yi" yace "OK ya kafar ynxu?" Tace "da sauki" yace "tell me d truth" a hnkli tace "Allah sir ya rage min ciwo ynxu" yace "OK Allah ya kara sauki" tace "Ameen" murya can kasa yace " yhu are starting exams next week, kina karatu kuwa Zainab" tace "Sir ina yi" yace "OK yhu knw kinyi missing test dina da yawa, hw are we goin to do now?" Kmr xata yi kuka tace "ni ma bn sani ba sir" yace "ina script din test din last wk da kika yi?" Tace "Na jefar sir" "Sbda nace ki fita?" A hnkli tace "ehh" murmushi yyi yace "don ma bn yage test din naki ba" Su jiddah ne suka shigo dakin da Sadiya, hkn yasa taki cewa komae, yace "Zainab!" Tace "Na'am" "kinyi shiru" juyawa tayi ta ga Su Jiddah sae kallonta suke, tayi murmushi tace "um um" Dr Sharif yace "Ko kin fara jin bacci ne?" Da sauri tace "ehh" yace "OK kiyi alwala kiyi addu'a kafin ki kwanta" tace "to xan yi" sallama yyi mata ya katse wayar ta ajiye tana kallon su Jiddah dake ta kallonta har lkcn, xata yi magana Jiddah tace "ke da waye" Afeefah na gyara kwanciyarta tace "Dr Sharif" xaro ido duk suka yi Sadiya tace "ko dae son ki yake Afeefah" mikewa Afeefah tayi da sauri ta xauna tana kallonsu, duk suka kwashe da dariya suka ce "tab soyayya ku ke ashe" Afeefah ta hade rae tace "wllh ba soyayya mu ke ba kawae dae...." Sae kuma tayi shiru ta rasa me xata ce masu, Suka kuma saka dariya suka ce "tab, Kinga 'yan matansa a Buk kuwa, duk da dae su suke ta haukansu, to a ina ma kuka hadu da shi" tsaki Afeefah tayi tace "ni dae ba soyayya muke ba" Jiddah tace "kya fada masu dae" Afeefah xata yi magana wayarta ya shiga ring ta duba ta ga ya Aliyu ke kiranta, xaro ido tayi tana kallonsu Jiddah tace "Don Allah Anty jiddah ki dauka ki ce masa ae nayi bacci tun daxu kafata na ciwo, idan yace ya kira ya ji buzy sae ki ce ke ce ke waya" Jiddah ta harareta tace "ehh Sannunki, ki ba Sadiya mana" da kyar ta lallabasu har da dan hawayenta ganin wayar ya kusa katsewa snn Jiddah tayi sallama kmr munafuka, a tsawace yace "who asked yhu to pick my cal ina wasa da ku ne, ina Zainab din" Jiddah tayi tsuru tsuru tana kallon Afeefah, Afeefah ta hade hannayenta a tsorace alamar ta rufa mata asiri, Jiddah tayi saurin cewa "yayanmu tayi bacci tun daxu, kasan likita ya xo ya kuma gyara mata kafarta" a tsawace yace "to wa ke waya daxu?" Jiddah da gabanta ke faduwa tace "ni ce yayanmu bata san na dauka ba ma, ta riga tayi bacci" yace "tasheta ki bata wayar" Jiddah ta juya tana kallon Afeefah ta shiga buga gado tana cewa "Zainab, ki tashi yayanmu ya bugo, Zainab, Zainab" tana shirin mika ma Afeefah wayar yace "kyaleta kawae, sae da safe" yana katse wayar Jiddah ta wurga wayar kan gado ta dinga kyalkyala dariya sadiya na taya ta, Afeefah tayi murmushi ta rungumeta tace "nagode sister" Sadiya tace "da kika ce masa waya kike bae tambayeki da Wanda kike wayar ba" Jiddah tace "ke dae bari ae abun ya bani mamaki" Afeefah a sanyaye tace "da ni ce da yayi min jaraba" Sadiya tace "wnn kuma ke kike shige masa ae" kwanciya Afeefah tayi bata kuma cewa komae ba, Dr Sharif ne ya fado mata, ta Mike da sauri ta nufi bayi tayi alwalan da yace tayi snn ta fito ta kwanta bayan ta gama addu'o'inta.
Washegari da asuba Afeefah tayi xaune bakin gado tana Mamakin mafarkin Dr Sharif har sau biyu da tayi daren ranan, mikewa tayi xata je yin alwala taji kafarta yyi mata sauki sosae, ba karamin farin ciki tayi ba tana kallon Jiddah da ta fito daga bayi tace 'kalli anty jiddah na fara iya taka kafar ynxu," Jiddah tace "ashe dae likitan gske ne lecturan" Afeefah ta harareta tace "ba sunansa lecturer ba, its either yhu cal him Dr Sharif, or Dr Aliyu tana kai wa nn ta shige bayi, su Jiddah suka kwashe da dariya, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh wayarta ya shiga vibrate ta dauka ganin Dr Sharif ne, bayi ta shige ganin su Jiddah sun xuba mata ido, gaishesa tayi ya amsa snn yace " ya kafar Zainab" tace "Sir ya daina min ciwo ssae gashi ina tafiya ynxu" yace "Alhmdllh, Allah kara sauki" tace "Ameen" yace "xa ki xo sch yau?" Ta girgixa masa kai tace "um um sae gobe" yace "ki daure ki xo xan maku revision yau" shiru ta dan yi snn tace "to xan xo" sallama yyi mata ya katse wayar ta bude kofar bayin xata fito ta ga su Jiddah labe bakin kofar bayin, ficewa suka yi daga dakin gaba daya suna dariya, ta tabe baki tayi kwanciyarta.
Yau ya kasance laraba kuma ranan da su Afeefah xa su kare exams dinsu, sanye take da atamfarta red colour da blue ta daura farin lab coat kan kayan nata tayi rollin kanta da black gyale karami ta sa flat shoe fari, ba karamin kyau tayi ba ranan duk da bata yi make up ko kadan ba don bata taba shiga skul ba hijab ba sae ranan, shima kuma don practical xa suyi na exams, Maryam ma sanye take da lab coat din da alamar laboratory xa su da safen, Maryam da ke ta kallonta tace "gskya Afeefah kin cije ni yau" Afeefah ta harareta bata tanka ta ba, wani faduwar gaba ne ya xo mata ganin Dr Sharif shima da alamar laboratory xa shi don sanye yake da white lab coat din shima, sak likita idan ka gansa, sunkuyar da kai tayi ta rasa dalilin da yasa duk lkcn da xata gansa sae ta ji faduwar gaba ba kadan ba, Maryam kam kasa daina kallonsa tayi, ba ita kadae ba har 'yan matan dake wajajen, wasu sae gaishesa suke yana sakar masu murmushi yana amsawa. Da kyar Maryam ta iya bude baki ta gaishesa ganin kusan a tare suke tafiyar ya amsa yana kallon wrist watch din hannunsa yace "so early hka xa ku lab?" "Um" kawae Maryam tace ba tare da ta kallesa ba, shi kam sae satan kallon Afeefah yake, dai dai lkcn da ta dago ita ma ta saci kallonsa suka hada ido, dauke kai tayi da sauri tana murmushi kmr munafuka murya can kasa tace "Gud morning sir" bae tanka ta ba yana kallon Maryam yace "hope yhu guyz are ready for the exam?" Maryam tace "in'sha Allah sir" yace "dats gud, Allah bada sa'a" ta amsa da Ameen, ya kuma kallon Afeefah ya dauke kai snn ya bar su nn suna jan kafa ya nufi lab, Maryam tace "ina son maki tambaya Afeefah" Afeefah ta dago tana kallonta tace "ina jin ki" Maryam ta dan yi shiru, har sae da Afeefah tace "kin yi shiru kuma" Maryam ta kirkiri murmushi tace "ki gaya min tsakanin ki da Allah meye tsakanin ki da Dr Aliyu Sharif" Afeefah ta dan hade rae tace "kmr ya" Yake maryam tayi tace "ko kuma ma dae mu je lab, am only joking" Afeefah bata tan ka ta ba har suka isa lab din. Karfe sha daya suka fito daga exam, Afeefah ta nufi cafeteria Maryam dake bin ta a baya tace "ya exams din?" Afeefah tace "Alhmdllh," Maryam tace "to Allah ba mu sa'a" a takaice Afeefah tace "Ameen" bayan ta xauna kujera ta fiddo wayarta, text din Dr Sharif ta gani, ta bude ta karanta content din, "Yhu look awful bbu hijab yau Zainab, Hijab rufin asirin 'ya mace, kar ki kuma irin shigar nn ki xo sch plss" dan tabe baki tayi, dai dai lkcn da wani text din nasa ya shigo wayar kuma, "ina maki magana daxu a lab shine kika yi ignoring dina koh?" Reply ta mayar masa kmr hka, "ae nayi xaton da 'yan matan nn naka kke shi yasa," bae mata reply ba ta yi tsaki ta mayar da wayarta jakarta, Maryam da a tunaninta tun tambayar da tayi ma Afeefah daxu ne yasa ta daure fuska tace "me xa ki ci?" Afeefah ta girgixa kai tace "A'a na koshi ni" ko rufe baki bata yi ba Dr Sharif ya karaso cafeterian yan matan da tace yana ma mgna a lab daxun na biye da shi a baya, kujera ya ja ya xauna gefen Maryam yace "Ya exams Maryam?" Maryam ta kirkiri murmushi tace "Alhmdllh," yace "Ma'sha Allah, wishing u ol success, no carry over in'sha Allah" murmushi kawae Maryam tayi tace "Ameen" yan matan guda biyu dama duk sun xauna, ya juya yana kallon su yace "wani drink xa a kawo maku?" Duk suka ce fanta, Afeefah dae sae Satan kallonsu take tana yin kmr tana danna wayarta don yan matan ba karamin haduwa suka yi ba, fanta hudu yasa aka kawo na roba da snacks ya mika ma matan biyu ko wanne daddaya snn ya ba Maryam ma, Afeefah kuma ya ajiye mata gabanta, dauka tayi da sauri ta mayar masa ba tare da ta kallesa ba tace "Thanks bna jin yunwa" murmushi yyi ya bude shi ya fara sha, fira kawae yake da 'yan matan dake ta basa lbri, Afeefah ta Mike ta saka wayarta a jaka ta xuge snn ta gyara blck veil din kanta don har lkcn lab coat na jikinta tana kallon Maryam tace "sae mun yi waya" tana kai wa nn ta fice daga cafeterian yan matan suka bi ta da kallo, ta nufi inda ta saba xama ta jira su jiddah, bayan minti biyu da fitan ta Dr Sharif ya mike yana kallon yan matan da Maryam yace "excuse me, xan dan yi makin phone call" ya fice daga cafeterian ya nufi inda yasan xai ganta, xaune ya sameta tana danna wayarta kamshin turarensa kadae yyi announcin mata presence dinsa a gun, "Zainab!" Juyawa tayi tana kallonsa, ya xauna dan nesa da ita yace "me na maki kike fushi?" Hawaye ne ya taru idonta ta ki cewa komae sae jujjuya wayar hannunta take, yyi shiru yana kallonta, mota ne yyi parkin dan nesa da inda suke xaune, Afeefah ta kafa ma motar ido ganin kmr motar ya Aliyu, to amma ae bae dawo ba, wayarta ne ya fara ring a take, taga Aliyun ne ke kiranta, ta daga yace "Am in ur sch Zainab," wara ido tayi tace "Da gske yayanmu ka dawo ne" inda yyi parkin kawae ya gaya mata, ta juya tana kallon Dr Sharif tace "kaga motar yayanmu na Lagos ne can, he came to pick me," Dr Sharif yace "OK in je mu gaisa?" Shiru ta dan yi sae kuma tace "to" mikewa tayi ta nufi motar gabanta na faduwa Dr Sharif ya bi bayanta.
0 comments:
Post a Comment