Karasowa cikin dakin Aliyu yyi yana kallonta, Afeefah tuni wayar hannunta ya sulale kan gado ta jawo pillow da sauri ta rufe ganin bae lura ba, tsaye yyi bakin gadon yana kallonta taki dago kanta, yace "Zainab!" Da kyar ta iya bude baki a hnkli ba tare da ta kallesa ba tace "Na'am" xaunawa yyi gefen gadon yace "Ki gaya min meyasa ke kadae ce baki jin mgna ta a gidan nn" Shiru tayi bata komae ba, a tsawace yace "Zainab!" Dago kanta tayi tana kallonsa da idonta da yyi ja, lkci daya hawaye ya cika idonta a hnkli tace "kayi hkuri yayanmu baxan kara ba" rungumeta yyi yace "Sau nawa kike making min wnn promise din kina break din sa Zainab?" Cikin muryar kuka tace "Na daina yayanmu" dago kanta yyi murya can kasa yace "promise?" Kai ta gyada masa tana hawaye, mikewa yyi ya kama hannunta suka fita daga dakin ya nufi nasa da ita. Kwata kwata Afeefah bata saki jiki da shi kmr ynda ta Saba ba ranan, duk sae ta ji ta a takure abinda bae taba faruwa da ita ba suna tare da Ya Aliyu, tsarabar da ya yo mata ma bata wani nuna farin ciki kmr ynda take yi da ba, kawae dae tana xaune dakin ne ta kafa ma plasman dake ta aiki ido, shi kuma yana danna laptop dinsa, gaba daya hnklinta na kan wayarta da ta baro a daki duk ta kagu ta fita, ta rasa dalilin da yasa ta damu da kiran Dr Sharif hka, Sumayya ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon ya Aliyu tace "yayanmu wae Mami tace in kira Afeefah" ba karamin farin ciki Afeefah tayi ba don sae da ta sauke ajiyar xuciya, Mikewa tayi tana kallon ya Aliyu tace "yayanmu na tafi Mami na kirana" kai kawae ya gyada mata ta dauki ledan tsarabar da ya bata ta fita ta nufi dakin Mami, kasan dakin ta xauna tana kallon Mamin tace "gani Mami" Mami tace "kin gama hada kayan naki?" Afeefah ta gyada Mata kai tace "na gama" Mami tace "je kiyi ma Abbanku sallama ynxu, gobe da sassafe Adnaan xae tafi kd sae ki bisa kawae" mikewa Afeefah tayi ta fita ta nufi dakin Abba, yana xaune falonsa yana kallon news, ta xauna kasa, yace "ya aka yi Zainab, yau ba ki yi bacci da wuri ba knn" tayi murmushi tace "eh bnyi ba Abba, dama Mami ce tace in xo in gaya maka gobe xan tafi kd" shiru Abba yyi yana kallonta can yace "toh shknn Allah kai mu, tafi ki kira min ita" mikewa Afeefah tayi ta fita daga falon ta koma dakin Mami tace "Mami Abba yace in kira ki" Mami tace "to jera min kayan nn kafin in dawo" Mami na Kai wa nn ta fita ta nufi dakin mai gidan nata, Kallonta kawae Abba yake har ta xauna snn yace "ynxu dae nuna min kike kin fini iko da Zainab a gidan nn koh Zuwaira?" Mami ta kallesa da mmki tace "kmr ya knn?" Abba yace "wato ke a ganin ki ke ya kamata ki dinga yanke wasu hukucin a kanta knn don Kinga ina maki shiru koh?" Mami tace "don nace xata kaduna shine nayi laifi Alhaji?" Abba yace "sae ana gobe xata tafi ya kamata a gaya min? kuma ma wae sae ki aiko min ita tsabar ki gwada min kin fi ni iko da ita ko me" Mami tace "Allah baka hkuri, kuma don naga Adnaan xae tafi kadunan ne gobe yasa nace kawae ya tafi da ita da su Jiddah, kuma kasan da sassafe yake tafiyarsa ba kmr Aliyu ba." Abba yace "to baxa su yi tafiyar sassafen da shi ba, ae Ali na nn da yamma sae ya Kai su" Mami bata ce komae ba, ya Mike ya shiga dakinsa ya dauko dubu 50 ya mika ma Mami yace "gashi kiyi Masu siyayyar da ya kamata" Mami ta sa hannu ta karba tace "Allah kara budi" snn ta mike ta fita daga dakin. Afeefah na gama gyara ma Mami kayan da ta sa ta ta tafi dakinsu, Jiddah kadae ce tayi bacci, Sadiya kuma na danna wayarta, kan gadonta ta nufa da sauri ta daga pillow ta dauki wayarta ta ga Dr sharif bae kuma kiranta ba, juyawa Afeefah tayi taga Sadiya ba kallonta take ba, kmr munafuka ta shige bayi da wayar, dailing number tayi, yana fara ringing ga katse ya kirata, "Baki yi bacci ba?" Kunya ne ya kamata don ko duba Karfe nawa bata yi ba, da sauri tace "ehh naga mis cal ne" Dr Sharif yace "na kira kin dauka kuma kika yi shiru" tace "uhm yayanmu ne ya kirani" Dr Sharif yace "OK, ya su mama?" A hnkli tace "suna lfya" yace "me kike yi har ynxu ba ki kwanta ba" tace "na hada kayana ne, gobe ya Adnaan xae tafi da ni Kaduna" yace "Really?" Kai ta gyada masa kmr yana ganinta, yace "Ashe xan yi missin crying student dina" murmushi Afeefah tayi murya can kasa tace "ae xan dawo kafin a kare hutu" a hnkli yace "Shknn, journey mercy Dear" shiru tayi jin abinda ya kirata da, "Are yhu there?" Ya tambayeta jin shirun, Da sauri tace "um na ngdd" yace "welcm, sleep sweet!" murmushi tayi ya katse wayar, ta fito daga bayin a sanyaye.
Washegari misalin Karfe goma Mami tasa Aliyu ya kai ta kasuwa don yi ma su Afeefah siyayyan tsaraban da xa su tafi da kaduna. Afeefah na xaune dinnin tana breakfast don tashinta knn tunda tasan tafiyar sae da yamma, Jiddah ta sakko ta mika mata wayarta tace "Ynxu dae tsakanin ki da Allah soyayya kuke da Dr Sharif din nn ko Afeefah" Afeefah ta hade rae ta karbi wayarta tace "Kinga Anty Jiddah bana so, kawae don ya kirani mu gaisa shine xa ki ce soyayya muke ni bna so" kmr xata yi kuka ta kare mgnr, dariya Jiddah take ta bar wajen da sauri kafin ta fara mata kuka, Afeefah ta daga kiran ta kara a kunne, muryarta na rawa ta gaishesa bayan tayi masa sallama, "Me aka maki?" Tambayar da yyi mata knn jin muryarta, a hnkli tace "Su anty jiddah ke neman tsokanata" yyi murmushi yace "to kiyi hkuri" shiru tayi bata ce komae ba, yace "kin fasa tafiyar yau ne" girgixa masa kai tayi tace "Abbanmu ne yace mu bari da yamma yayanmu ya Kai mu" yace "OK Allah kai mu" a hnkli tace "Ameen" yace "ltr" shiru tayi har ya katse wayar snn ta ajiye ta ci gaba da shan tean ta a hnkli. Da yamma misalin Karfe uku Afeefah ta gama shirinta da su Anty jiddah da Sadiya don tare xa su tafi amma su Washegari xa su dawo kano, Aliyu da kansa ya karbi jakar kayan Afeefah ya kai bayan mota, ita kuma ta haura sama da gudu ta shige dakinsu, Dr Sharif ta shiga kira tana kallon bakin kofar dakin a tsorace, yana fara ring ya katse ya kirata, kmr munafuka tace "sir dama em ina son in gaya maka ynxu xa mu tafi" murmushi yyi yace "ko in xo in raka ku?" Xaro ido tayi da sauri tace "A'a" yace "To Allah tsare hanya Zainab" a hnkli tace "Ameen ngd" Addu'o'in da xata karanta ya shiga tuna mata, ji tayi ya Aliyu na kiranta da sauri tace "toh toh ngdd sir, byee" da sauri ta katse wayar ta boye cikin hijab dinta jin har ya shigo dakin harara ya galla mata yace "ba ki ji ina kiran ki ne?" kmr xata yi kuka tace "yayanmu ina cikin bayi ne fa" ficewa yyi daga dakin ta bi bayansa, Mami taje tayi ma sallama snn ta fita don su Jiddah har sun shiga mota, gaba ta xauna as usual, Mami ta fito ta masu addu'ar Allah tsare hanya snn ya Aliyu ya ja motar suka bar gidan. Karfe Shidda da yan mintuna suka shigo kaduna, Afeefah ta juya ta kalli ya Aliyu jin wayarta na vibrate a hijab, ya lura da hkn yace "ya aka yi princess?" Murmushi ta kirkira tace "Um um ba komae" bakwae saura suka isa unguwar rimi tsabar traffic din kd, horn Aliyu yyi mai gadi ya bude gate, kusan a tare suka shiga makeken gidan da wata mota dake bayansu, ya Aliyu yyi parkin a parkin lot, Afeefah ce ta fara fitowa dae dae lkcn da mutumin cikin motar ya fito bayan shi ma ya gama parkin, wara ido tayi ta nufesa da gudu ta rungumesa tace "Ya Ma'aruf" rungumeta yyi shima yace "waow Zainab ku ne dama da magrib" Su Jiddah suka karaso suka gaishesa suna murmushi su ma, Aliyu kam kin fitowa daga motar yyi sae kallon Afeefah da har lkcn tana jikin Ma'aruf yake ta madubi fuskar nn tasa a daure. Ma'aruf yace "Driver ne ya kawo ku?" Afeefah tace "A'a yayanmu ne!" Sae a snn Aliyu ya fito yana kirkiran murmushi ya nufi inda suke ya basa hannu suka gaisa. Cikin gidan suka nufa gaba daya Afeefah na ta jero ma Ma'aruf tambayoyi, "to ya Ma'aruf ynxu xaka iya shiga da ni gurin da kuke xama idan kuna tuka jirgin in gani?" Dariya yyi ya lakaci hancinta yace "ke dae ba kya girma yarinyar nn koh?" Turo baki tayi xata yi mgna taga wani mummunan kallon da ya Aliyu ke mata, tuni ta hadiye abinda xata ce ta shiga wasa da yatsunta har suka shigo falon gidan. Hajiya Khadija mahaifiyar Ma'aruf ce ta sakko falon da mmki tana kallonsu tace "dama ku ne da magariban nn Aliyu" murmushi Aliyu yyi yace "wllh kuwa Ammi," mikewa Afeefah tayi da gudu ta rungumeta. Hajiya khadija tayi dariya tace "ke dae bakya girma ko Zainab, an xo hutu knn" murmushi Afeefah tayi ta rufe idonta, Hajiya khadija ta karaso cikin falon ta xauna da fara'arta ta amsa gaisuwar Su Jiddah, tana kallon Aliyu tace "barrister Ali knn, ina su Mami?" Yace "suna nn lfya Ammi," tace "kai baka xuwa sae ka kawo Zainab hutu koh?" Dariya yyi yana shafa kansa don ya ma rasa me xae ce ya kare kansa, mikewa Ma'aruf yyi yana kallon Afeefah yace "mu je ki ban lbrin Buk, ki kuma gaya min gskya samarin ki nawa?" Dariya tayi ta mike ta bi bayansa, Aliyu ya bi ta da kallo lkci daya murmushin da yake ma Ammi ya bace daga fuskarsa.
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
36__37
Afeefah na kwance daki tun fitowarta daga dakin Ma'aruf ita a dole tana fushi da Ya Aliyu sae kumbure kumbure take, tura kofar dakin aka yi Anty Jamila ta shigo tace "Zainab sakko ki ci abinci ana jiran ki" bata yi musu ba ta sauko daga kan gadon ta bi bayanta suka sauka kasa, ya Aliyu na xaune falo da Ammi da ya Saleem, Afeefah ta hade rae ta nufi dinnin, ta debi abincinta don su jiddah sun diba nasu, ilham tace "wnn dan abincin xae isheki Zainab?" Ba tare da Afeefah ta kalleta ba tace "ehh xae min" Anty jamila ta kalli Aneesah tace "ke kara mata me wnn dan abincin xae mata" da sauri Afeefah tace "wllh Anty ni ya isheni" kyaleta duk suka yi suka shiga cin abincinsu, da ke kadan ta xuba tuni ta cinye ta mike ta bar dinnin din, xata haura sama Ammi tace "har kin gama Zainab" tace "ehh na gama" dakin su Aneesah ta nufa ta shiga bayi don yin wanka, ko da ta fito kayan baccin ta ta fiddo a jaka tasa snn ta sa Hijab tayi kwanciyarta, balla sim dinta da ya Aliyu yyi ne ya fado mata nn da nn hawaye ya cika idonta taji wani mugun haushin sa kawae take ji ynxu, Ammi ce ta shigo dakin tace "ke baxa ki sauka falo kiyi kallo ba Afeefah," Afeefah ta ce "Ammi ni bna son kallon" Ammi tace "toh shknn, amma kar kiyi bacci sae kun gaisa da Baffan ki" Afeefah tace "toh" snn Ammi ta fita daga dakin, ko minti biyar Ammi bata yi da fita ba Ya Aliyu ya shigo dakin, rufe ido tayi da sauri kmr me bacci, ya karaso kan gadon ya xauna yana kallonta yace "Zainab!" Kin juyowa tayi bare ya sa ran idonta biyu, xagawa yyi ta daya side din yana kallon fuskarta ya kuma kiranta, nn ma taki amsawa, murmushi yyi don yasan idonta biyu sarae, ya mike ya fice daga dakin. Murguda baki tayi ta kuma tura kanta cikin pillow cike da jin haushin sa, Karfe tara da rabi Ilham da Jiddah suka shigo dakin suka ce Baffa na kiranta, mikewa tayi ta bi bayansu suka nufi falon baffa, murmushi yyi ganinta, ta xauna gefensa ita ma tana murmushin tace "Sannu da dawowa baffa" ya shafa kanta yace "yauwa mamata, ashe kun xo, ina su Abbanku da Mami," tace "duk suna lfya, sun ce in gaisheka" yace "Madalla, mun yi waya dasu daxu ma, ya makaranta ynxu kin xama 'yar jami'a koh" dariya tayi ta sunkuyar da kanta, baffa ya kalli Jiddah yace "ya baku xo min da Fadila ba Hauwa" jiddah tace "ba su yi hutu bne shi yasa" yace "Allah sarki, Adnaan na nn abunsa koh?" Jiddah tace "yana nn baffa" sun dde suna hira daga bisanni suka yi masa sae da safe dae dae lkcn da Ma'aruf ya shigo falon don yi ma Abban nasa sae da safe shi ma, Afeefah na shirin kwanciya Ma'aruf ya shigo ya xauna gefenta yace "gashi har xan tafi baki bni lbrin samarin ki ba koh?" Afeefah ta wara ido tace "ina xa ka Ya Ma'aruf?" Dariya su Ilham suka kyalkyale da suka ce "gidan sa mana" Afeefah tace "ohh na manta" dariya yyi yace "xa ki xo ki min sati koh?" Ta gyada masa kai tace "ehh xan xo yaya" yace "yawwa Kanwata" duk suka yi masa sae da safe snn ya fita daga dakin, Ammi ta shigo tace "Zainab taso ki kwanta bedroom dina" ba musu ta mike ta bi bayan Ammi.
Washegari da safe misalin Karfe goma su Jiddah suka fara shirin komawa kano, ya Aliyu ne ya shigo dakin da sallama, Afeefah da ke xaune gaban madubi tana shafe shafe ta hade rae tare da turo bakinta, gunta ya nufa yana kallonta yace "ina kwana Zainab?" Sunkuyar da kai tayi da sauri tace "yayanmu ni bn ganka ba, ina kwana," hancinta ya ja yace "dake ke makauniya ce ba" murmushin da bata yi niyya ba tayi, sae kuma a hnkli tace "ka yi hkuri" juyawa yyi yana kallonsu Jiddah yace "ina jiran ku a falo" har suka tashi tafiya Afeefah kin fita tayi har sae da Ammi tace "Zainab baxa ki je ku yi sallama da yayyin ki ba?" Mikewa tayi ba don ta so ba ta fita, kanta a kasa ta isa motar ya Aliyu ta daga ma su jiddah hannu snn ta nufi driver seat inda Aliyu yake ta dago kai a hnkli tace "Yayanmu Allah ya tsare hanya" ba tare da ya kalleta ba yace "Ameen" kmr xata yi kuka tace "yayanmu baka kalleni ba" fuskarsa a daure yace "in maki me?" Shiru tayi tana kallonsa lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya xata bar wajen ya kamo hannunta, bbu yabo bbu fallasa yace "to me kike son in maki Zainab?" Girgixa masa kai tayi hawayen idonta ya gangaro, murmushi yyi yace "toh ngd Zainab, will miss yhu a lot" murmushi ita ma tayi, ya ciro handkerchief ya share mata hawayen fuskarta a hnkli tace "yayanmu kayi hkuri, daga yau xan fara jin mgnr ka" murmushi kawae yyi yace "Allah ya sa" har suka bar compound din bata daina daga masu hannu ba sae taji ba ddi kmr ta bi su, Aneesah ce ta ja ta tana dariya ta nufi cikin gida da ita ganin hawayen idonta. Da rana Afeefah na xaune falo suna kallo da su Anty jamila, Afeefah ta kalli ilham dake gefenta tace "Anty ilham dan ara min phone din ki don Allah, ilham tace yana sama a daki, mikewa Afeefah tayi ta nufi sama da sauri ta dauki wayar, ta fiddo nmbr Dr Sharif da ta ajiye a jakarta tayi dailin, bugu uku ya dauka tare da yin sallama, rasa abun cewa tayi kmr mara gskya tace " Sir ina yini" shiru taji yyi hkn yasa tayi saurin kallan wayar ta ga ko ya katse ne amma taga bae katse ba, sunanta ta ji ya kira ta amsa a dan kunyace, yace "me ya sami wayar ki?" Kmr xata yi kuka tace "yayanmu ne ya kwace" da dan mmki yace "sbda me?" Muryarta na rawa tace "wae don ina waya" Dr Sharif yace "uhm OK, wnn wayar waye" a hnkli tace "na sister na Ilham" yace "ok" shiru tayi bata kuma cewa komae ba, yace "ya mutan gidan" tace "duk suna lfya?" Yace "kinyi missin dina kuwa?" Shiru tayi ta kasa basa amsa, a hnkli ta ji ya kira sunanta, murya can kasa tace "Na'am" murmushi yyi ya kuma yi mata tambayar, cike da jin kunya tace "nayi!" Yace "karya kike" xaro ido tayi tace "wllh sir nayi missing dinka" yar dariya yyi yace "really kina son gani na knn!" Kunya ne ya kamata ssae, taki cewa komae, a hnkli yace "Zainab!" Tace "uhm" yace "baki son ganina knn" murya can ciki tace "ina so" yace "Toh in xo ki gan ni" rufe fuskarta tayi da pillow da sauri wae ita kunya a hnkli tace "Uhm" yace "I promise xan xo kd in gan ki dear" sallama yyi mata jin bata da niyyar cewa komae kuma, Afeefah ta ajiye wayar tana murmushi. Tun daga lkcn kullum sae sun yi waya da Dr Sharif da wayar Ilham, Aliyu kuma sau dayawa ta wayar Saleem yake kira yace ya bata, sae dae ynxu ta daina dokin kiran Aliyu kmr ynda take da, wani lkcn har pretend take tayi bacci idan aka kawo Mata wayar. Ranan da ta cika kwana uku Ya Ma'aruf ya xo da yamma, taji ddin ganinsa ssae, dakin Ammi ya nufa tana biye da shi a baya, bayan sun gaisa da Ammin tasa yace "Ammi na xo tafiya da Zainab ne tayi ma Amina kwana biyu," Ammi tace "To ae Abban ku bae sani ba" Ma'aruf yace "xan kirasa in gaya masa Ammi" Ammi tace "A'a da dae ka bari goben ka xo da safe ka samesa ka gaya masa sae ku tafi da ita" bata rae Afeefah tayi ta xamo daga kan gadon Ammi, Ammi tace "Au to Allah baki hkuri, ku tafi Ma'aruf idan ya dawo na gaya masa, amma kai ma ka kirasa," murmushi Afeefah tayi ta mike da sauri ta fice daga dakin don xuwa ta hada kayanta, jikinta ne yyi sanyi tunawa da tayi Dr Sharif yace mata gobe xae xo, can dae a xuciyarta tace to ba sae ya sameni can gidan ba, ilham ta samu da sauri dakin Anty jamila tace "Anty ilham idan Wnn da yake kirana ya kira kice bana nn amma xan kirasa" ilham tace "toh"
Karfe shidda na yamma Ma'aruf ya isa gidansa da Afeefah, bell ya danna bayan minti biyu wata kyakkyawa da baxata wuce 23 ba ta bude kofar rike da wani handsome boy a hannunta, rungumesu yyi gaba daya Afeefah ta kwalalo ido tare da dauke kanta da sauri, matar cikin sanyin murya tace "Sae ynxu Hubbi" yace "Ba nace maki xan tafi gida daga can ba, ba mu hanya bby" sae a snn Matar ta lura da Afeefah, ta bata hanya tana kallonta, Afeefah ta dukar da kai da sauri, kama taga matar take mata da warce ta sani amma ta rasa a ina, kmr munafuka tace "Ina yini Anty" "lfya lau, sannu da xuwa" matar ta amsa Mata a takaice. Har bedroom din da xata ajiye kayanta Ma'aruf ya kai ta, yace "feel at home dear" gyada masa kai kawae tayi ya fita. Tana xaune kan darduma ta idar da sllhn magrib Amina ta shigo dakin, bbu yabo bbu fallasa tace "ki sakko ki ci abinci" tana fadin hka ta juya ta fice, Afeefah tayi jigum tana da ta sanin biyo ya Ma'aruf, har ta yi sllhn isha matar bata kuma kiranta ta xo ta ci abinci ba, a xuciyarta tace to ko tana tunanin budurwarsa ce ni, Ma'aruf ne ya shigo dakin da mmki yace "Zainab ba Amina ta xo kiran ki ba, meyasa baki sakko ba" murmushi ta kirkira tace "um na koshi" ya galla mata harara yace "c'mon taso mu je ki ci abinci, ko sae na shigo na dago ki" mikewa tayi da sauri yyi dariya ya juya ta bi bayansa a sanyaye hka kawae taji ita tsoron matar ma take, da kyar take tura abincin gabanta a dinnin din tsabar irin kallon da Amina ke mata ga Ma'aruf ya isheta da surutu. Mikewa tayi daga karshe kmr xata yi kuka tace "yaya ni na koshi" yace "ba ki isa ba, Maza cinye shi" mikewa Amina tayi tana rike da yaronta ta bar dinning din ta haura sama, ya bi ta da kallo, can ya maido da dubansa ga Afeefah yace "sae fa kin cinye shi Zainab" komawa tayi a sanyaye ta xauna ta shiga tura sauran abincin, tana gama ci ya ki barinta ta haura sama, tayi da ta sanin biyosa ba kadan ba hka ya dinga mata hira daga karshe dubara ya fado mata tace ya bata wayarsa xata kira Mami da ya Aliyu snn ya bata ta haura sama da sauri ta shige dakin da ya ajiyeta ta kulle. Hawaye ta shiga yi cike da tsoron matarsa ta ci kukanta daga karshe ta shiga dialing nmbr Dr Sharif, bugu biyu ya dauka tace "Sir" yace "Zainab!" A hnkli ta gaishesa ya amsa tare da cewa ina kika je, tace "gidan uncle dinmu" yace "ok, am comin down to kaduna gobe" wara ido tayi tace "da gske Sir" yace "yea ko kar in xo" da sauri tace "ka xo" yyi murmushi yace "shknn xan xo idan Allah ya yrda, layin waye wnn" tace "uncle dina," yace "OK sae da safe" tace "Allah ya kai mu," snn ya katse wayar ta ajiye a sanyaye ta kwanta. Washegari da kyar Afeefah ta fito yin breakfast kmr ynda Ma'aruf ya umarce ta, ranan ma bata samu fuska gun Amina ba don da kyar ta amsa gaisuwar ta, sama ta koma a sanyaye ta xauna dakin da take, goma saura Ma'aruf ya shigo dakin yace "Zainab sakko ki taya Antyn ki girki a kitchen yau yayanta xae xo daga kano"
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
38......
Afeefah ta dauki hijab dinta a sanyaye ta sa don bata iya masa musu, ta bi sa suka sauka downstairs, yana gaba tana biye da shi a baya har suka iso kitchen din, Amina da ke kkrin jona blender Fadil na bayanta ta juya tana kallonsu yace "Honey ga ta xata taya ki aiki" bbu yabo bbu fallasa Amina tace "A'a taje tayi xamanta ngd" Ma'aruf yace "Haba ki bari ta taya ki mana" bnxa Amina tayi masa hkn yasa ya nuna ma Afeefah sauran tomatoes din da take wankewa tace "je ki karasa wanke mata" kai Afeefah ta gyada masa a sanyaye ta shiga kitchen din ta ci gaba da wanke mata kayan miyan, juyawa yyi ya bar kofar kitchen din ya koma sama. Afeefah na gamawa ta juya tana kallonta a hnkli tace "Anty na gama" ba tare da Amina ta kalleta ba tace "sannu" shiru Afeefah tayi tana tunanin abun yi kuma, kayan salad da cabbage da su carrots da ta gani ta nufa ta daukosu ta nufi sink don wanke su, Amina dae bata ce mata komae ba har ta gama ta yanka salad din da cabbage carrot kuma tayi grating dinsa, hka ta dinga kame kame a kitchen din Amina bata tanka ta ba har dae ta ga ba sauran aiki tayi jigum, can tace "kawo sa in rike maki shi Anty," ba musu Amina ta sauke Fadil dake bayanta ta mika mata ta karbesa ta fita daga kitchen din. Misalin sha daya Amina ta gama duk girke girken da xata yi ta bar kitchen din. Afeefah na kwance tana rungume da Fadil dake ta wasa a jikinta Amina ta bude dakin da sallama ta tsaya daga bakin kofa tace "bani shi xae ci abinci" mikewa Afeefah tayi ta kai Mata yaron ta karbe sa ta juya ta fice. Amina na fita Afeefah ta jawo wayar Ma'aruf dake gunta har lkcn, taga alamar private sim dinsa ne shiyasa bata ga an kira ba, nmbr Dr Sharif tayi dialing, yana dagawa ta gaishesa a hnkli, ya amsa yace "Kin tashi lfya Zainab?" Tace "um" yace "ina hanya fa" ta wara ido tace "da gske sir" yace "yea ko in koma" da sauri tace "A'a," yyi murmushi yace "to sae na xo" ita ma tayi murmushin tace "Allah tsare hanya" tana ajiye wayar jikinta yyi sanyi, to ya ma xata gaya ma ya Ma'aruf xata yi bako, ga matarsan nn da bata da kirki.
Mikewa Afeefah tayi daga kwancen da take jin har an tada sllhn Azahar ta nufi bayi tayi alwala ta fito, ko da ta idar da sllhn kayanta ta ciro don ita tsoron kwalliya ma take a gidan tun kayan baccin jiya ne jikinta duk da tayi wanka, ta dan yi shafe shafenta snn tasa wani gown dinta na material ta maka dogon hijab a kai ta koma ta kwanta, Amina ce ta bude kofar dakin tace "ki je ki dauki abincin ki kitchen fa" to kawae Afeefah tace mata, Amina ta rufe kofar, bayan minti talatin Amina ta kuma bude kofar dakin tace "baki sauka kin dauki abincin ba kuma" mikewa Afeefah tayi da sauri ta nufi kitchen a sanyaye, Aminan na biye da ita a baya ta nuna mata abincin nata da ta ajiye Mata kan faranti da drink da ruwa snn ta juya ta fita kitchen din. Plate Afeefah ta dauka ta bude shinkafar don ba iya cinye duka xata yi ba, ta dibi kadan ta bude miyar ta diba, kaji ta gani a daya kulan dake kan farantin ta dauki daya, coslow din ma bata diba ba ta dauki ruwa maimakon drink snn ta fita daga kitchen din ta haura sama. Kasa cin abincin tayi ta dan cakalkala ta mayar kitchen tana neman bolan xubarwa, bell din gidan aka danna sae da ta dan tsorata ta fito daga kitchen din da sauri rike da abincin don kar Amina ta gani, kallo daya Amina tayi mata ta nufi kofa tana rike da Fadil murmushi dauke fuskarta, Afeefah ta koma kitchen din kmr xata yi kuka, ita dae ta kawo kanta, da ta sani da bata fara bin ya Ma'aruf ba, Amina na bude kofar ta rungume yayanta cike da farin cikin gninsa, rankwashi Dr Sharif ya kai mata yace "kina ma da hnkli kuwa, kada ni xa kiyi" dariya ta kyalkyale da tace "kai yaya, kaga ynda ka canxa kuwa yayana, welcm big bro nah," murmushi yyi ya karbi yaron hannunta ta basa hanya ya shigo falon, Afeefah kam kasa kwakkwaran motsi tayi a kitchen din jin kmr muryar Dr Sharif take ji a falon, ga kamshin turare irin nasa da ya gauraye gidan, Amina kuwa baki har kunne ta ga yayanta da take bala'in so, Dr Sharif ya xauna yana rike da Fadil yace "ina Captain din?" Tace "wllh ya fita tun daxu yaya, amma nasan yana hanya ynxu," kitchen ta nufa da sauri sae ta ga Afeefah a tsaye, dauke kanta tayi ta dauki faranti da glass cup ta bude fridge ta fiddo drinks da ruwa ta daura kai ta fice daga kitchen din tana cewa "yaya ina momyna da fateema, meyasa ba ka xo min da teema ba" yace "suna gida, idan kina son ganinsu ae sae ki je kanon" tace "Ayya yaya dama wllh kila next wk xan tafi kanon sae ga shi kace min xaka xo" hiran yaushe gamo suka dinga yi da yayan nata don sun kusa shekara ba su hadu ba, mikewa tayi tace "bari in hado maka coffee yayana, nasan kuna tare har ynxu" murmushi yyi ta nufi kitchen, wnn karan da mmki take kallon Afeefah dake tsaye har lkcn a kitchen, a dan fusace tace "wae ke me kike yi a kitchen a tsaye ne" bata jira cewarta ba ta shiga yin abinda ya shigo da ita kitchen din, hawaye ya cika idon Afeefah, Amina na fita daga kitchen din ita ma ta fita a sanyaye tana rike da plate din abinci har lkcn, assuring kanta ta shiga yi cewar ae da Dr Sharif ne ya xo Kaduna da ya kirata tasan Mae irin muryarsa ne kawae, tana fitowa daga kitchen din suka yi ido hudu da shi, sake plate din shinkafar hannunta tayi a kidime ta juya da sauri xata koma kitchen din sae kuma ta nufi stairs da gudu kmr munafuka, ya bi ta da kallon mamaki, Amina ta mike da mugun mmki ita ma ta bi ta da kallo snn ta maido da dubanta kan shinkafar kan tiles tace "anya yarinyar nn na da lfya ma kuwa, ba da ni ba wllh" wayarta ta shiga nema don kiran Ma'aruf, murmushi kawae Dr Sharif yyi yana shafa kansa yace "wa xa ki kira?" A fusace tace "Baban Fadil xan kira mana, do ni bnsan ko tana da iskokai ba yarinyar bbu ruwana, Dubi fa abinda tayi ynxun nn" Dr Sharif da har lkcn yana murmushi yace "Uncle dinta ne mijin naki" tace "ni bn san ynda suke ba, jiya ya kawota" Dr Sharif yace "kira min ita" bata fuska Amina tayi tace "tayi maka me yaya, ka rabu da ita ina jin ba ita kadae take ba" hararanta yyi yace "nace ki tafi ki kira min ita" sama ta nufa ba don ranta ya so ba ta shiga dakin da Afeefah take, ta sameta xaune tana rusa kuka bakin ranta, mamaki ne ya cika Amina, sae abun ma ya kusa bata dariya, ta dake tace "me aka maki kike kuka?" Afeefah ta girgixa mata kai da sauri muryarta na rawa tace "gida xan wuce Anty" Amina tace "to sakko a mayar da ke" mikewa Afeefah tayi da sauri ta dauki jakar kayanta, Amina tace "A'a bar jakar xa a biyo ki dashi daga baya sakko kawae" ba musu ta bi bayanta kmr munafuka ita dae har lkcn bata yarda Dr Sharif ta gani xaune falon ba, suna shigowa falon Afeefah ta shiga rufe fuskarta da Hijab dinta ta nufi kofa da sauri, har ta kusa ba Amina dariya, Dr Sharif yace "Zainab!" Juyowa Afeefah tayi da sauri tana kallonsa har lkcn fuskarta a rufe, kuka ta saki ganin shi din ne, Amina ta shiga kallon yayanta da mmki jin ya kira sunan Afeefah, mikewa yyi ya karasa inda Afeefah take yana murmushi yace "sauke hijab din" saukewa tayi ta sunkuyar da kanta da sauri, ya tsura mata ido snn a hnkli yace "baki son ganina ne kuma" muryarta na rawa tace "ina so" Amina ta kwalalo ido da mugun mmki tana kallonsu, yace "toh share hawayen ki" a hnkli ta shiga share fuskarta yace "follow me," ba musu ta bi bayansa suka koma falon ya xauna kan kujera ita kuma ta xauna kasa gefensa har lkcn taki dago kanta, da mmki Amina tace "yaya kasanta ne dama wae?" Yace "ehh nasanta, student dita ce" Amina ta xaro ido tana kallon Afeefah, murya can kasa Dr Sharif yace "kuma budurwata! koh Zainab?" Afeefah ta rufe fuskarta da hijab da sauri ta daura kanta bisa gwiwanta, Amina ta fashe da dariya tace "kai yayana, wae da gske kke don Allah" murmushi yyi yana kallon Afeefah da ke jin kmr ta nutse wajen, yace "karya nayi Zainab?" Kin cewa komae Afeefah tayi ya sakko nn kasa gefenta ya xauna yana kallonta a hnkli yace "Zainab" murya can kasa tace "um" yace "wae ke ba budurwata bace?" Kin dago kanta tayi, yace "shknn bari in tashi in tafi since yhu re denying me" dago kanta tayi da sauri a kunyace tace "Sirr"
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
39.....
Dariya kawae Amina take tana kallonsu, Dr Sharif yyi murmushi yana kallon Afeefah yace "to gaya min me ya sa ki kuka?" Shiru tayi bata ce komae ba, ya kuma yi mata tambayar, ta daga kai a hnkli tana kallon Amina, sae kuma tayi saurin sunkuyar da kanta, kallon Aminar Dr Sharif yyi yace "ke kika sa ta kuka knn?" Da sauri Afeefah tace "A'a sir bata min komae ba" Amina ta yo waje da ido ta dawo kusa da su ta xauna tana dariya tace "wllh yaya bn mata komae ba tun jiya da ta xo ta ki sake jiki fa," Dr Sharif ya galla mata harara yace "ke din? Kin sake mata fuska ne bare ta saki jiki?" Amina ta xaro ido ta kuma ta saka dariya tace "Ayya yayana ka tambayeta wllh bn mata komae ba jiyan ma da suka xo ban jin ddi ne" hararanta kawae Dr Sharif yake, Afeefah kam murmushi tayi ta sunkuyar da kai a hnkli tace "ni bata min komae ba kawae gida nake son wucewa" Amina ta yi dariya tace "to ka dae ji, in ma na maki wani abun kiyi hkuri Anty Zainab" sae a snn Dr Sharif yyi murmushi, Afeefah ma tayi murmushin cike da jin kunya, Amina ta mike tace "bari in kawo maka abinci big bro" kallon Afeefah kawae Dr sharif yake har lkcn taki dago kanta, Amina ta dawo falon ta dire kulan abincin ta koma ta dauko sauran, da kanta ta shiga xuba masa a plate, daga kai yyi ya kalleta yace "ita ta ci ne?" Amina tace "bata wani ci na kirki ba, breakfast ma ina kula da ita bata yi na kirki ba" spoon ya dauka ya sa a abincin da Amina ta xuba masa ya dauko ya ajiye gaban Afeefah yace "oya start eating ynxu" murmushi tayi hade da girgixa masa kai tace "Um na koshi sir" hararanta yyi yace "C'mon" bata kuma yi masa musu ba, ta dauki spoon din a hnkli, Amina ta xuba masa wani tana murmushi tace "bari in baku waje sir" daukar Fadil tayi tana dariya ta haura sama. Kasa cin abincin Afeefah tayi tsabar yanda yake kallonta ga wani mugun kunyarsa da taji tana ji, murya can kasa yace "Zainab!" Ba tare da ta dago ba tace "um" yace "kunya ta kike ji ne wae?" Gyada masa kai tayi, yyi murmushi ya soma cin abincin sa, ganin taki ci ne yasa yace "to tafi sama ki je ki ci" da sauri ta mike ta dauki abincin ta nufi stairs ya bi ta da kallo. Fitowa Amina tayi jin Afeefah ta bude dakin da take ta shiga dakin tace "har kin gama cin abincin" murmushi Afeefah tayi tace "a nn xan ci" dariya tayi tace "kunyar sir din naki kike" sunkuyar da kai Afeefah tayi da sauri, Amina ta ajiye Fadil kan gado tace "ga Fadil nn toh" juyawa tayi ta fita daga dakin ta koma gun yayanta, kallo ta samesa yana yi tace "yaya ae abincin xae huce" yace "eh jira nake ya huce dama" tace "wae da gske yayana budurwar ka ce Zainab" ba tare da ya kalleta ba yace "gashi na fada gaban ki" murmushi tayi tana kallonsa don har tayi aure bata taba jin yyi maganan mace ba don cewa yake ba su ne gabansa ba, lallai Zainab tayi sa'a, jin tayi shiru yasa Dr Sharif ya daga kai yana kallonta, tayi masa murmushi tace "na taya ka murna yayana, Allah baka Zainab! don yarinya ce me hnkli daga jiya na lura da hkn ga sanin ya kamata" murmushi yyi yace "Ameen ya Allah"
Har karfe uku suna hira da yayanta ya Ma'aruf ya shigo falon, yana dariya yace "Dama ana ganin ka bokan turai, baka da kirki Haiydar ko kira bbu fisabilillah" Dr Sharif yace "ae kai naga kana kiran, ba dae mun baka mata ba dole ka mance mu" dariya Ma'aruf yyi yace "ka ji gori koh, ke Amina kira min Zainab shi ma in basa Kanwata ko xan samu sakat" dariya Amina tayi tace "to ae budurwarsa ce Zainab din" Ma'aruf yace "kai Haba a ina ya san ta? Wae da gske Dr" Mikewa Dr Sharif yyi yana murmushi yace "wnn ba Matsalar ka bace" excusing kansa yyi ya fita don amsa wayarsa, Amina tayi dariya tace "a kano ya san ta" bayani tayi ma Ma'aruf ynda suka hadu da Afeefah, Ma'aruf yyi dariya yace "to in ji kin daina kishi da ita ynxu dae koh? Don kinsan ko ina son Zainab ynxu ya xama dole in bar ma wnda ko auren ma bae taba ba sbda halaccin da yyi min" dariya Amina tayi ta kai masa duka tace "kai dear! hka nace maka ina kishi da ita" yace "ahaf sae dae idan ba Aminar da na sani bace" tayi dariya tace "uhm ae ynxu Zainab ta xama Anty"
Ko da Dr Sharif ya dawo mikewa Amina tayi ta bar masu falon ta haura sama, Ma'aruf yana kallon Dr Sharif yace "ashe dae Kanwata kke so, ya xama dole in maka halacci in sa a baka" Murmushi Dr Sharif yyi yace "Allah sa ku banin dae" Ma'aruf yace "Serious in har da aure kke son ta an gama" Dr Sharif yace "Da aure nake sonta mana" Ma'aruf yace "ka shirya auren ne ynxu?" Dr Sharif ya shafa kansa yace "Ae karatu take ynxu, it won't b fair in katse mata karatun ta" Ma'aruf yyi murmushi yace "ka manta Amina na karatu ku ka bani ita" Dr Sharif yace "hka ne but bn san ko xa ayi mata aure ynxu ba, naga yayyinta mata ma basu yi auren ba" Ma'aruf yace "kai dae ynxu kke son auren ko ba ynxu ba?" Dr Sharif yyi shiru yana kallonsa snn yace "idan xa a bani" Ma'aruf yace "kar ka damu, aurensu ilham nn da 'yan watanni ne, xan yi convincing Abba ya hada gaba daya idan har yhu re jet serious coz nasan halin ka Haiydar" Sauke ajiyar xuciya Dr Sharif yyi yace "wllh da aure nake son Zainab, amma bari in maka tambaya daya, ya ku ke da Zainab? kuma ka gaya min gskyan wani irin dangantaka ne tsakaninta da Aliyu, tace min dad dinsu daya, hka ne?"
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
40.....
Shiru Ma'aruf yyi yana kallon Dr Shariff snn yace "Hka tace maka dad dinsu daya?" Dr Sharif ya gyada masa kai, Ma'aruf ya dan tabe baki yace "I wonder y they are still hiding things for the innocent girl, ba dad dinsu daya da Aliyu ba but don't tell her dat" kasa ce masa komae Dr Sharif yyi, can dae da kyar yace "to ya suke da shi? Nd y are they hiding it for her? Kana nufin shi ba dan gidan bne knn?" Ma'aruf yace "No! Ita ce ba 'yar gidan ba, ynxu dae mu bar xancen nn, ka bn go a head in yi ma dad maganan?" A sanyaye Dr Sharif yace "Baka gaya min ynda ku ke da ita ba" Ma'aruf yace " yar Kanin dad dina ne, her father is late" da mmki Dr Sharif yace "bn gne ba, make me understand plss, then wat is she doin in kano, mum dinta fa, kana nufin ba iyayenta bne a kano?" Ma'aruf ya sauke ajiyar xuciya yace "Ka ga da mu bar wnn xancen kawae Dr, she knw nothin about ol dis dat am sayin, infact duk gidansu bnda Aliyun da Adnaan sae yayyinta mata biyu da suka yi aure bbu wnda yasan ba yar gidan bace ita, kuma baxan so ta ji a bakina ba ko a gidana, in dae kana son Zainab da aure da gske ka kwantar da hnklin ka am there for yhu, ltr xa mu je mu samu dad am sure he will b vry happy don shi indae mace ta fito da miji aure yake mata bae jiran sae ta kare karatu kmr ynda dad dinsu Aliyu ke yi, tashi mu tafi masallaci, almost tym 4 sallat" har suka dawo daga masallaci Dr Sharif was nt him self, dama yasan ba biological brothern Afeefah bne Aliyu, ya ga alama da ddewa, Ma'aruf ya haura sama ya bar sa nn xaune yana ta sake sake, he is afraid of loosin Zainab, yasan tun daga randa ya fara sauke idonsa ya ji sonta, abinda bae taba faruwa da shi ba, da farko he was thinking tausayinta kawae yake don yaga alamar tana da rauni ga saurin hawaye, daga baya yaga ba hka bne don duk randa bae daura ido kanta a sch ba bai jin ddi, nd he is matured enuf ba sae wani ya gaya masa ya fada tarkon son Zainab ba, sauke ajiyar xuciya Dr Sharif yyi don yasan Ma'aruf will Neva let him down. Amina ce ta shigo dakin da Afeefah take ta ganta kwance tana bacci, tada ta tayi tace "lallai ma Antyn nn sae ki xo kiyi kwanciyar ki a nn kina bacci ki bar bakon ki a falo" mikewa xaune Afeefah tayi tana mitsika ido, Amina ta mata murmushi tace "to tashi ki kara shiryawa ki je ku yi hira, yace min sbda ke ma ya xo kano" Kai Afeefah ta gyada mata kawae ta juya ta fita, Afeefah ta mike ta shiga bayi, wanka ta kuma yi tayi alwala ta fito tayi la'asar, snn ta yi shafe shafenta, ta fiddo da wani riga da skirt dinta na atamfa ta sa, ba karamin kyau kayan yyi mata ba, tana kkrin sa Hijab Amina ta shigo dakin, xaro ido tayi tace "ko yar powder baxa ki shafa ba" murmushi kawae Afeefah tayi bata ce komae ba, Amina ta kama hannunta tace "xo mu je dakina ki shafa" bin bayanta Afeefah tayi suka shiga bedroom din Aminar ta xaunar da ita gaban madubinta, kwalliya ta shiga rangada mata tun Afeefah na nonnokewa sbda kunya har ta sake, light make up tayi mata, ta sa mata jan bakin da tasan xae amsheta, snn ta mata daurin dankwali ya xauna das a kanta, wae ina ma xa a iya kwatanta irin kyan da Afeefah tayi don Amina sake baki tayi tana kallonta, wane ba indiya ko balarabiya, ita kanta Afeefah sae da taji kunyar don bata taba kwalliya hka ba, hotuna Amina ta mata snn tace "to tafi kuyi hira da Sir din ki" rufe fuska Afeefah tayi da sauri cike da jin kunya, can ta dauki hijab dinta xa ta sa, Amina tace "meye hka xan gani?" Afeefah ta sunkuyar da kai tace "sa wa xan yi" Amina tace "Haba sae kace warce xata fita kofar gida, falo fa xaki xauna" karbe hijab din Amina tayi tace "yi tafiyar ki hka" Afeefah kmr xata yi kuka tace "baxan iya fita hka ba Anty" Amina ta sake baki tana kallonta can tace "to wllh baxa ki fita da hijab ba, gwara ki dauko mayafi toh" Afeefah ta marairaice tace "ban xo da mayafi ba anty" Amina tace "bari xan baki nawa," jan mayafinta mai kyau ta fiddo mata ganin atamfar na da ratsin ja ta mika mata tana murmushi tace "to ga shi ki yafa" a kunyace Afeefah ta karbi mayafin amma ta kasa yafawa don ba sabawa tayi ba, Amina ta karba tana dariya ta yafa mata shi a shoulder dinta gefe daya, snn ta dauki turare ta fesheta da shi ta fiddo mata red flat shoe dinta ta bata tace "sa kiyi tafiyar ki" a hnkli Afeefah tace "ngdd," snn ta sa ta fita daga dakin. Da kyar Afeefah ta sauko downstairs don ji take kmr ta nutse tsabar kunya, juyawa Dr Sharif yyi don ganin me sakkowa, ya kafa mata ido ko kiftawa bae yi, wani mugun sonta na fixgarsa, ta sunkuyar da kai da sauri, tana harhardewa ta karaso falon ta rakube gefen kujera kanta a kasa a hnkli tace "Sir ya hanya?" murmushi Dr Sharif yyi murya can kasa yace "Zainab!" Ba tare da ta dago kai ba tace "um" ya nuna mata gefensa yace "dawo nn" kin tashi tayi sae da ya kuma kiran sunanta snn ta mike da kyar kanta a kasa ta dawo kusa da shi ta xauna kasa, kallonta kawae yake, ta dago a hnkli tana kallonsa da dara daran idonta, ya lumshe ido yace "kinyi kyau" rufe fuskarta tayi da sauri murya can ciki tace "ngd Sir" Amina ce ta sakko ta shigo falon tace "baxa ku xaga kaduna ba yayana, da kun dan fita outing" kallon kanwartasa yyi yana murmushi yace "Yayanta xae bari in fita da ita?" Amina tace "ehh mana, bari in masa mgna" juyawa tayi ta koma sama, Dr Sharif na kallon Afeefah yace "wae mu je yawo?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba lkci daya ya Aliyu ya fado mata hka kawae ta ji gabanta ya fadi. Amina ce ta kuma sakkowa tana murmushi tace "yayanta yace xa ku iya fita amma kar ku dde" juyawa tayi tace "ina xuwa" snn ta kuma komawa sama, ba a dau lkci ba ta dawo falon tace "Anty ki tafi yayanki na kira a sama" Afeefah tayi murmushi ta gyada mata kai alamar ta ji, farantin Drinks din dake falon Amina ta dauka ta nufi kitchen, Afeefah ta Mike a hnkli don xuwa kiran ya Ma'aruf, rasa inda xata bi da Dr Sharif baxae bita da kallo ba tayi, don wani kunya take ji idan yana kallonta, tana fara tafiya mayafin jikinta ya xame kafin ta ankara har ya kai kasa, ta xaro ido da sauri ta durkushe wajen kmr xata yi kuka tana kallonsa, Dr Sharif ya kauda kansa yana murmushi, mikewa tayi da gudu ta nufi stairs rike da mayafin a hannu bin ta da kallo yyi yana murmushi, ba a dau lkci ba Ma'aruf ya sakko Afeefah na biye da shi a baya yana kallon Dr Sharif yace "amma fa baxa ka dde min da kanwa a waje ba Dr" Dr Sharif yyi murmushi yace "In'sha Allah" makullin mota Ma'aruf ya basa yace "ga aron mota" dariya Dr Sharif yyi ya karbi makullin yace "thanks frnd" Ma'aruf yyi masu Allah kiyaye hka ma Amina suka koma sama, yana gaba tana biye da shi a baya ya nufi parkin lot, juyawa Dr Sharif yyi yana kallonta a hnkli yace "koma ki dauko hijab din ki Zainab" Afeefah ta juya ta koma cikin gidan ta ajiye mayafin ta dauki hijab dinta, Amina tayi dariya tace "lallai ma yaya" murmushi Afeefah tayi kawae ta fita ta samesa cikin mota yana jiranta.
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
41.....
Sae da suka hau main road ba tare da Dr Sharif ya kalleta ba yace "Ina kike son in kai ki Zainab?" Shiru tayi bata ce komae ba, can kuma a hnkli tace "nima bn sani ba" yace "Ma'aruf bae taba fita dake bne duk xuwan ki hutu kd?" Ta girgixa masa kai tace "ae shi ba nn yake ba" Dr Sharif yace "yea hka ne na manta, bari mu je to ki ga state university din kaduna, da polytechnic dinsu, ko kin taba xuwa?" Girgixa masa kai tayi, ya nufi hanyar unguwar rimi, har cikin kasu ya shiga da ita, sae a snn Afeefah tace "Sir wae nn ne?" Dariya yyi yace "da fa, ga dayan a gaba shima xan shiga dake" tabe baki tayi tace "ko kyau, North west din mu ya fi kyau!" Dariya yyi ssae yace "kai bari yan Kaduna su ji ki bbu ruwana" dariya tayi tace "to ni ina ruwana da su daga na fadi gskya?" xagawa da ita cikin kasu yyi gaba daya, sae tabe baki take, ita a dole bae mata ba daga karshe tace "ni dae sir na gani, mu tafi kawae" yyi murmushi yace "to mu je tudun wada ki ga polytechnic dinsu na science?" Tabe baki tayi tace "ni bn san wajen ba" yace "ae nuna maki xan yi" tace "tohm mu je" polytechnic din art dake unguwan rimin ya fara nuna mata yace "akwae wani a barnawa ma, but ynxu na tudun wada xa mu" suna isa junction road yace "kalli can ki ga stadium dinsu" juyawa Afeefah tayi da sauri tana kallon inda yake nuna mata ta xaro ido tace "wnn dan wurin sir?" Dariya yyi ssae yace "don baki shiga bne" ta tabe baki tace "um ni dae dan karami ne" kwafa yyi yace "bbu ruwan sir dae, bari yan kd su ji ki su kama ki" dariya tayi tace "ni ina ruwana da su" ta sardauna crescent ya shiga sbda traffic, ta ce "Sir Dubi fa titin mu ma ya fi nasu girma da kyau ssae" yyi murmushi yace "eh mana" cikin mintunan da basu wuce goma ba suka isa poly road, Afeefah ta xaro ido tace "Sir nn ne polyn nasu?" Yace "yea" tace "kai shine yayanmu ke wani cewa makarantun kd sun fi namu ashe ba hka bne" dariya kawae Dr Sharif yyi ya nufi main gate din k.p.t, ya karbi gate pass ya shiga, dariya kawae Afeefah ta dinga yi ita a dole ta raina polyn, Dr Sharif ya girgixa kai yace "kin san shekaran polyn nn nawa?" Ta girgixa kai, yace "uhm ki bar raina sa, babban makaranta ce yarinya," tace "bn yadda ba, ka gaya min shekaran sa nawa!" Yace "this polytechnic was founded in 1956! Ki lissafa shekarunsa ki ga tun kan Independence, ya fi north west din nn naku da kike brag da iyakacinsa shekara biyar, kin manta slogan din kadunan ne wae? 'Center of education! Let me remind yhu" Afeefah ta saka dariya tace "kai Sir" murmushi yyi ya xaga da ita cikin polyn gaba daya snn suka fita ya shiga da ita ostrich bakery dake wajajen ya siya mata snacks kala kala, suka kama hanyar U.rimi, ya juya yana kallonta yace "its almost 6 pm da mun shiga gamji in ji cmmnt din ki, nd beside ma it's nt decent mu shiga da yamma" Shiru tayi bata ce komae ba, murya can kasa ba tare da ya kalleta ba yace "Mu je muyi hoto?" Shiru tayi kmr me naxarin abinda yace, sunanta taji ya kira, ta dago manyan idonta tana kallonsa a hnkli yace "Mu je studio muyi hoto nace?" Dauke kanta tayi, sae kuma tayi murmushi ta gyada masa. Hadadden studio ya nufa yana gama parkin ya juya yana kallonta yace "mu je" bude kofar tayi ta fito shima ya fito, yana gaba tana biye da shi suka shiga studio din, Afeefah taji baxata iya hoton ba bayan Sun shiga sbda kunya, ma'aikatan wajen duk a tunaninsu pre wedding pics suka xo yi, Dr Sharif yyi murmushi yace nml pic suka xo dauka, da kyar Afeefah ta iya tsayawa suka yi hoto da Dr Sharif tsabar kunya sae wani rurrufe fuska take, kala hudu kawae suka yi ya biya kudin suka ce su dawo gobe su karba bayan sun tura ma Dr Sharif a wayarsa, kasa kallon Dr Sharif Afeefah tayi har suka shiga mota, Eatry taga yyi parkin ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar ya mika mata ledan hannunsa, ta karba ba tare da ta kallesa ba, ya tada motar suka nufi gida, Dr Sharif na gama parkin bayan sun isa gida Afeefah ta bude motar ta riga sa fita da sauri tayi cikin gida, Amina dake kitchen ta fito tace "sannun ku da dawowa" Afeefah tayi murmushi kawae ta ajiye ledan hannunta tace "ina Fadil Anty?" Amina tace "tare mu ke girkin a kitchen ae, gashi can cikin kekensa" dariya Afeefah tayi ta mata sannu da aiki ta nufi sama da sauri kafin Dr Sharif ya shigo.
Bayan isha Ma'aruf yace da Dr Sharif "ya mgnr daxu Dr, mu tafi gun dad din ne ynxu? naji kace gobe xa ka koma!" Dr Sharif yace "to mu tafi frnd" takwas da kusan rabi suka isa can gidan, Dr Sharif yace "look captain kunyan dad nake wllh, just go in and explain to him" Ma'aruf ya hade rae yace "kaga matsala ta da kai koh" Dr Sharif ya marairaice masa yace "don Allah ka rufa min asiri kai ka shiga I just cnt go in" tsaki Ma'aruf yyi ya bar sa cikin motar ya nufi cikin gidan, ba karamin farin ciki dad yyi da xancen da Ma'aruf ya xo masa da ba, dad yace "ae wnn ba matsala bne in har uwar tawa tana so, kaga sae a hada da nasu jamila kawae, ka xo min da ita gobe mu ji ta bakinta" Ammi dake xaune falon tayi shiru dae tana kallonsu bata ce komae ba, dad ya juya yana kallonta yace "ko ya kika ga Uwar gida?" Sauke ajiyar xuciya tayi tace "Amma kuma Alhaji naga ae yana da kyau a fara jin ra'ayin iyayenta na kano ka ga ba wajen mu take ba bare kayi saurin yanke hukunci hka!" Dad ya hade rae yace "ji wani xance don Allah, da nan da can din ba daya ba mne, kuma nasan baxa su ce don me ba, don duk abinda na yanke tamkar su suka yanke ne" Ammi tace "To Allah rufa asiri, amma Dr Aliyu kam mutum ne, Allah dae ya xaba abinda ya fi alkhairi" Dad yace "yauwa xancen knn, Ameen ya Allah" Ma'aruf ya sallami iyayen nasa ganin ya bar Dr Sharif a waje snn ya bar gidan, Yana shiga motar ya sakar ma abokin nasa murmushi yace "In'sha Allah kmr ka samu Zainab frnd" murmushi Dr Sharif ya mayar masa yace "I trust yhu captain" goma saura suka isa gida, Amina tayi masu sannu da xuwa snn ta dauko masu abinci ta ajiye masu tsakiyar rug din falon ta nufi sama, Afeefah na shirin kwanciya Amina tace "kaddai har xa ki kwanta" Afeefah tayi murmushi tace "um bacci xan yi" Amina tace "to baki tafi kin ma Sir sae da safe ba yace baxae kwana nn ba" Afeefah ta kauda kanta a hnkli tace "toh" dariya Amina tayi ta fita daga dakin, Afeefah ta mike ta sa hijab dinta har kasa snn ta fita daga dakin ta sauka downstairs. Xaune ta samesa da Ma'aruf, ta karaso cikin falon kanta a kasa ta xauna daga kasa, cike da xolaya Ma'aruf yace "kin sakko fira knn" bata fuska tayi tace "A'a" yyi dariya ya mike yace "bari to in baku waje." Sae dae Ma'aruf ya haura sama snn Dr Sharif ya juya yana kallon Afeefah yace "har kin gama jin Kunyan" rufe fuskarta tayi da sauri yyi murmushi yace "to dawo nn" bata masa musu ba kanta a kasa ta dawo gefensa ta xauna daga kasa. Wayarsa ya mika mata yace "kin ga hoton da kika ki gani daxu" murmushi tayi ta karbi wayar tana kallon hoton nasu, ba karamin kyau suka yi ba barin Dr Sharif, tace "um bayan ka fini kyau!" Yace "kin dae fini" sunkuyar da kanta tayi tace "bn yarda ba" Ma'aruf ne ya sakko downstairs ya shigo falon da sallama yana mika ma Afeefah waya yace "ga yayanki" ba karamin faduwa gabanta yyi ba, ta karbi wayar da kyar, juyawa Ma'aruf yyi ya koma sama, sarae Dr Sharif ya lura da halin da Afeefah ta shiga, wayar na soma ringing ta daga a sanyaye tace "yayanmu!"
Eeshatullah Goni😘
🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
42___43
Shiru Afeefah tayi jin ya Aliyu bae ce komae ba, can ta kalli screen din wayar ta ga bai kashe ba kuma, a hnkli ta kuma cewa "yayanmu!" Yace "ina jin ki, ykk" jin yanayin muryar tasa yasa da damuwa tace "baka da lfya ne yayanmu?" Yace "lfyata qlau, I called daxu ma'aruf yace kin fita da matarsa" Afeefah ta gyada kai da sauri tace "uhn!" Yace "Shknn gud nyt, just called to say hi" murmushi tayi murya can kasa tace "am missin yhu yayana" shiru ya dan yi sae kuma a sanyaye yace "No yhu are nt Zainab! nasan haushi na kike ji ynxu kina ga kmr ina takura ki koh? Kiyi hkuri with tym xa ki gane meyasa nake maki hka kuma xan daina kin ji" shiru Afeefah tayi ita ma jikinta yyi sanyi, kmr xata yi kuka tace "yayanmu wllh ni bna fushi da kai, kaga ae bn da waya ne ynxu shi yasa bana kiran ka" ya Aliyu yyi shiru bae ce komae ba, a hnkli tace "Allah nayi missing dinka yayanmu, I missed yhu a lot" dan murmushi yyi bae dae ce komae ba, kmr xata yi kuka tace "ka ji!" Murya can kasa yace "naji! Kina son gani na to?" Xaro ido tayi da sauri tana kame kame tace "Lah ae to kila ma na kusa dawowa ko yayanmu, mun kusa komawa sch ka tambayi su Anty jiddah" yace "toh shknn, Allah dawo da ke lfya" a sanyaye tace "Ameen yayanmu" katse wayar yyi lkci daya, duk sae ta ji ba ddi abinda ta ce masa, da da ne kullum cikin kiransa take in ta xo kd wani lkcn ma har cewa take ya xo ta gansa, amma wnn karan har bata son ya kira, juyawa tayi a sanyaye tana kallon Dr Sharif taga kallonta yake, dauke kai yyi da sauri, ita kuma ta sunkuyar da kanta, ya mike ya karbi wayarsa a hannunta yace "je sama ki ce masu xan tafi" tace "har xa ka tafi sir" yace "yea" mikewa tayi a sanyaye ta nufi sama. Ma'aruf ne ya sakko tare da Amina yace "wato dae da gske baxa ka kwana nn ba ko Dr" Dr Sharif yace "abokina na jira na tun daxu, so I have to go," Amina tace "to amma yaya don Allah ka xo kayi breakfast a nn" yace "xan xo in'sha Allah" Makullin motar Ma'aruf ya dauka yace "da motar ka xan tafi, gudnyt" juyawa Ma'aruf yyi yana kallon Afeefah da ke tsaye yace "Baxa ki masa rakiya ba" Amina tayi dariya tace "to kai kaji ya mata sae da safe shi din?" Dariya Ma'aruf yyi yace "wae nn kunyar surikinsa yake" juyawa Afeefah tayi da sauri ta nufi sama, Amina tayi dariya tace "Ina kuma xa ki Anty yana fa jiran ki ne a waje" sae da Ma'aruf ya sa baki snn Afeefah ta sakko a kunyace ta nufi kofa ta fita. Har Dr Sharif ya tada motar ta karasa kanta a kasa tace "Sae da safe sir" yace "Allah ya kai mu" bae kuma jiran jin abinda xata ce ba ya ja motar ya bar wajen, jikinta yyi sanyi ta bi sa da kallo, juyawa tayi da sauri tun kan ta fara hawaye ta nufi cikin gida da gudu ta haura sama ta shige daki, sae a snn ta fada kan gado ta fashe da kuka, tayi mai isarta daga karshe bacci ya dauketa nn kwance. Washegari misalin Karfe sha daya Afeefah na kwance daki kmr mayya taki fitowa har Amina ta gaji da xuwa cewa ta sakko ta kyaleta, bude kofar dakin aka yi ta daga kai don ganin waye, Amina ce ta tsaya daga bakin kofa tace "to ae kya fito ynxu tun da sir ya xo koh?" Murmushi kawae Afeefah tayi, Amina ta juya ta bar dakin, mikewa Afeefah tayi da kyar ta sa hijab dinta ta fita daga dakin fuskarta a daure, yana xaune falo yana shan coffee, ta karasa kanta a kasa ta xauna kan rug din falon, kin cewa komae tayi shi ma hkn, can dae a sanyaye tace "ina kwana sir" yana kallonta yace "lfya Zainab," har yyi shiru sae kuma yace "wat made yhu cry?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, ya ci gaba da shan coffeen sa, mikewa tayi xata bar wajen yace "ina kuma xa ki?" Girgixa masa kai kawae tayi sae ga hawaye, dauke kai yyi ya dauki envelope karami dake kusa da shi ya mika mata yace "ga hotunan! ur copies" risinawa tayi ta karba murya can kasa tace "ngdd" "sit" yyi instructing dinta, ba musu ta xauna, yace "kar ki min kuka" gyada masa kae kawae tayi, ya dauko wani leda ya mika mata, kin karba tayi da farko, amma ganin ynda ya tsare ta da ido yasa ta sa hannu ta karba duk da bata san meye ba, ajiye mug din hannunsa yyi yace "xan koma kano" dago dara daran idanuwanta tayi tana kallonsa, a hnkli tace "to ngd sir Allah tsare hanya," yace "Ameen Zainab!" Kira min Amina, mikewa tayi ta nufi sama, tare suka sakko da Aminan ya mike yace "sae kin xo meenah, I will b on my way ynxu" Amina tace "kai yayana baxa ka jira Abban Fadil ba," yace "mun yi waya da shi, nace baxae same ni ba, beside mun ma hadu daxu da safe ae" Amina bata so hka ba a sanyaye tace "to shknn yaya ina xuwa" sama ta nufa, ya juya yana kallon Afeefah, murmushi yyi ganin ynda ta bata fuska, yace "me ya faru kuma?" Kmr xata yi kuka tace "ni ma wajen Mami na nake son komawa" dariya yyi yace "ae nn da few dayz xa ku koma sch," Amina ce ta sakko rike da leda ta mika masa tace "gashi yaya ka kai ma teemah" hararanta yyi yace "wa xa ki hada da kaya?" Marairaice masa tayi tace "ba jirgi xa ka bi ba yayana" karba yyi yace "shknn sae mun yi waya" Juyawa Zainab tayi ta haura sama da sauri, Dr Sharif yyi dariya yana kallon Amina yace "xa ki sha lallashi yau knn" dariya tayi tace "wae baxa ka tafi ba?" Yace "wae xata koma kano ita ma" dubu goma ya ciro ya daura kan fadil ya shafa kan yaron , yyi pecking dinsa yace "gudbye son" godiya Amina tayi masa ta raka yayan nata har gate, snn ta dawo cikin gida, dakin Afeefah ta shiga ta sameta xaune tana rusa kuka, dariya ssae abun ya bata, ta dake ta shiga lallashinta amma kmr dada tunxurata take hkn yasa ta bar dakin. Da yamma misalin Karfe biyar Afeefah ta bude ledan da Dr Sharif ya bata, waya iPhone 7 ta gani, tuni ta kwalalo ido a dan tsorace tana kallon kwalin wayar, mikewa tayi da sauri ta bude jakarta ta saka kwalin da ganinta kasan ba karamin tsoro ta ji ba.
After Magrib Ma'aruf ya tafi da Afeefah can gida, a hanya take gaya masa wayar da Dr Sharif ya bata, yace "iyye, lallai Aliyun nn na ji da ke, to kin gode, idan mun koma gida sae ki kirasa kiyi masa gdya, gobe sae in siyo maki sim" Afeefah tace "toh yaya"
ba karamin kunyar tambayar da dad ke mata Afeefah tayi ba, taki dago kanta don ji tayi da ma ta nutse wajen kawae, Ammi tayi dariya tace "ka bar ni da ita kawae Alhaji, xata gaya min gskya" dad yyi dariya yana kallon Afeefah yace "to tashi ki tafi" mikewa tayi kanta a kasa ta bar falon, dad yyi murmushi yace "Allah ya ji kan Umar ya gafarta masa," Ammi tace "Ameen ya Allah" snn ta mike ta bi bayan Afeefah, bedroom dinta ta kai ta ta xaunar da ita gefen gado tace "kar ki ji kunya ta dota, ki gaya min gskya kina son Aliyu wan matar yayan ki?" Afeefah ta sunkuyar da kai bata ce komae ba, sae da Ammi tayi da gske snn a hnkli ta gyada mata kai a kunyace, Ammi tayi murmushi tace "toh shknn tashi ki yi tafiyar ki" mikewa tayi da sauri ta bar dakin ta shige na su Ilham. A hanya xa su koma gida Afeefah ke ce ma Ma'aruf "yaya amma don Allah kar a gaya ma su Mami, kasan Abbanmu karatu yake son muyi, ni sae na gama karatuna" kmr xata yi kuka ta kare mgnr Ma'aruf ya dan tabe baki yace "na ji" duk da kawae amsa mata yyi don shi ya ma fi son a aurar da ita da karatun hofin. Hka Afeefah ta karashi hutun ta a Kaduna duk ta kagu ta koma kano ta rasa dalili, ana gobe xata koma Abba ya sa ya saleem ya yankar mata ticket, tsaraba ssae Ammi tayi mata, hka ma Anty Amina, ya Ma'aruf kuma laptop ya siya mata, Saleem kuwa da ya tambayeta me take so kawae Ca tayi yar karamar Nokia xae siya mata, da yamma Ya Ma'aruf da Anty Amina suka rakata airport, suna nn har jirgin yyi take off snn suka koma gida. Adnaan ne ya tare ta a airport din kd, Afeefah tayi mmkin da ya Aliyu bae xo tarar ta ba as usual. Bayan sun kama hanya tace "ya Adnaan yayanmu fa?" Adnaan yace "yana gida" shiru tayi bata kuma cewa komae ba har suka isa gida, bata damu da murnar dawowanta da yan uwanta ke tayi ba ta nufi sama da sauri ta shige dakin ya Aliyu, yana tsaye waya na kare kunnansa alamar waya yake, da gudu ta rungumesa tsam cike da farin ciki tace "yayanmu" da farko dakewa yyi, tana dago dara daran idonsa ta daura kan nasa kawae ya kasa, lkci daya ya sakar mata murmushinsa Mae kyau ya ja kumatunta yace "Welcm" bata fuska tayi tace "shine baka xo daukana a airport ba ko yayanmu" ajiye wayar hannunsa yyi yace "kin gaya min xa ki taso yau?" Ta wara ido tace "yaya ka manta bnda waya" yace "na tuna," tace "amma ya saleem ya siya min yar karama bn fara amfani da shi ba" gyada mata kai kawae yyi, ta juya ta nufi kofa tace "bari in je in gaida Mami" bin ta yyi da kallo har ta fita. Tana fita dakinsu ta nufa da sauri ta bude jakarta ta ciro wayar da Dr Sharif ya siya Mata ta shige bayi da sauri ta shiga kiran layinsa, yana dagawa tace "Sir na dawo" yace "haba, yaushe kika dawo" tace "ynxun nn" yace "welcm dear, result din ku ya fito" xaro ido tayi tace "da gske sir? Ka duba min nawa?" Yace "yep na duba, Allah ya taimake ki a course dina kadae kike da carry over" dafe kirji tayi sae kuma ta saka masa kuka, yyi dariya ya katse wayar. Ta ci kukanta ta koshi ta fito daga bayin. Cikin jaka ta boye wayar da sauri. Da daddare Afeefah na fiddo da tsarabar su jiddah wayarta dake cikin jaka ya soma ring, xaro ido su Jiddah suka yi jin Ringtone din, da gudu Afeefah ta nufi jakar don mancewa tayi bata sa a cylnt ba, kashe wa tayi gaba daya ta mayar jakar, Jiddah tace "iPhone Afeefah? Wa ya siya maki" bata fuska tayi tace " ya Ma'aruf" bata jira cewarsu ba taje ta ci gaba da abinda take, Sadiya ta sauke ajiyar xuciya har da su Sumayya. Hka Afeefah ta dinga kaffa kaffa da wayar kar yayanmu ya gani, laptop kuwa da ma ta kai ma Mami tace Ma'aruf ne ya bata, wayar kuwa bata nuna mata ba sae wnda saleem ya siya mata, ana gobe xa su koma sch da daddare Afeefah na xaune ita kadae daki ta shige cikin bargo ta gama waya da Dr Sharif knn tana danne dannenta, ya Aliyu ya turo kofar dakin ganin tun yamma bata sakko falo ba, tsayawa yyi yana kallon bargon, ko kadan Afeefah bata san an shigo dakin ba, ya karasa kan gadon ya yaye bargon a hnkli yana kallonta, a kidime ta mike xaune tana kallonsa, lkci daya ta shiga kkrin boye wayar hannunta, fixgewa yyi yana kallon wayar da mmki, kuka ta saki ta mike da gudu ta fice daga dakin ta shige dakin Mami, Mami da fitowarta daga bayi knn ta bi ta da kallon mamaki, kuka ta fashe mata da tace "wayyo Mami ki ce ma yayanmu dady ne fa ya siya min wayar" korarta Mami tayi daga dakinta a fusace, Afeefah tayi dakin Adnaan shi ma ta fashe masa da kuka tace "kaga ya Adnaan, dady ne ya siya min wayar fa" Adnaan yana kallonta da mmki yace "wani waya?" Cikin kuka tace "yana hannun yayanmu je ka gani kar yace ba shi ya siya min ba ya min duka" dariya Adnaan yyi ya mike ya fita ya samu Ya Aliyu dakin sa a kwance, kallon iPhone 7 din kan gadon Adnaan yyi ya karasa ya dauka yana dariya yace "Wae kaji dady ya siya mata tace" wani mugun kallo Aliyu yyi masa can yace "naji, ae ni bn ce mata komae ba kai mata wayarta" Adnaan ya fita da wayar ya kai Mata dakinsa, mikewa ya Aliyu yyi ya fice daga dakin ya nufi dakinsu jiddah, jakar kayan Afeefah ya nufa ya xuge ya shiga fiddo kayan ciki can kasan jakar ya ga kwalin wayar ya bude bae ga receipt ciki ba, kan farin envelope idonsa ya sauka ya dauki envelope din ya bude ya ga hotuna ne ciki, yana cikin fiddo hotunan aka bude kofar dakin ya daga kai suka yi ido hutu da ita ta shigo, mutuwar tsaye tayi bakin kofar cikin rawan murya tace "yayanmu" bae kuma kallonta ba ya ciro hotunan gaba daya yana kallo, mikewa Aliyu yyi da sauri ya dafa bango tsabar wani mugun jirin da ke neman kada sa daga durkushen da yake kansa na juya masa.
Eeshatullah Goni😘😘
?
?[5/23, 08:34] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
44.....
Afeefah ta fasa ihu a tsorace ta durkushe wajen tana kallonsa lkci daya ta fashe da wani matsanancin kuka ta daura hannu a ka tana kiran Mami, da kyar Aliyu ya iya jan kafarsa ganin tsayuwar ya gagaresa ya koma can gefen gado ya rike kansa da yyi masa nauyi ssae, Adnaan ne ya shigo dakin da sauri ya kalleta snn ya kalli Aliyun, su Jiddah ma suka shigo suka yi cirko cirko a bakin kofa su kalleta su kalli Yayanmu, Mami ce ta shigo dakin ita ma tace "me ya faru? Wa ke min ihu a gida?" rasa me bata amsa aka yi, Afeefah kam sae kuka take daga durkushen da take, kallon Aliyu dake xaune gefen gado har lkcn yana rike da kai Mami tayi ta ja tsaki ta juya ta fice daga dakin, Adnaan ya karaso cikin dakin ya karasa kusa da Aliyu yace "me ya faru bro? Me tayi maka" ganin Aliyu bae da niyar tanka sa yasa ya juya ya fice daga dakin shima, su Jiddah suka bi bayansa. Mikewa Afeefah tayi ta fice ita ma da sauri jikinta na rawa, dakin Adnaan ta shiga ta xube gabansa cikin kuka tace "ya Adnaan ka taimake ni yayanmu xae kashe ni yau" Yace "me kika yi ne wae?" Muryarta na rawa tace "Ni ma bn sani ba" hka tayi ta xama dakin Adnaan taki fita sae kuka take. Ganin gyangyadi take daga xaunen da take yasa Adnaan yace "ki kwanta Zainab" bude ido tayi, tayi shiru tana kallon bakin kofa can ta mike kmr warce kwai ya fashe ma ta fice daga dakin ta nufi dakinsu, su Jiddah na shirin kwanciya Afeefah ta shigo dakin ta nufi kan gado a sanyaye, duk suka bi ta da kallo, sae da ta kwanta snn Jidda ta karasa kusa da ita ta xauna tace "Afeefah me kika yi ma yayanmu" hawaye ne suka gangaro mata bata ce komae ba, daga karshe ta kauda kanta, mikewa jiddah tayi ta bar wajen. Har asuba Afeefah bata wani rintsa ba, ta rasa me ke mata ddi a duniyar, tasan a da ko da wasa bata tsallake duk umarnin da yayanmu ya bata amma tun da ta fara higher institution take disobeyin dinsa ta rasa dalili, sae da su Jiddah suka dawo daga gaida Abba snn ta mike jiki ba kwari ta fita don xuwa gaishesa, Abba na xaune falonsa ya Aliyu ma na xaune falon daga kasa gefensa, Afeefah ta karasa a sanyaye ta xauna daya gefen Abba murya can kasa tace "Ina kwana Abba" Abba yace "lfya lau mamata, kin tashi lfya" gyada masa kai kawae tayi kanta a kasa, Abba yace "an koma makaranta yau ko?" Kai ta gyada masa nn ma, yace "to Ma'sha Allah, sae a maida hnkli kin ji mamata" tace "toh Abba" juyawa yyi yana kallon Aliyu da ya sunkuyar da kansa yace "yauwa ina jin ka Ali" Afeefah ta tsura masa ido lkci daya hawaye ya taru idonta, dago kai yayanmu yyi suka hada ido da ita, ya dauke kai da sauri, da kyar ta iya bude baki tace "ina kwana yayanmu" Ba tare da ya kalleta ba cikin sanyin murya yace "lfya lau" kallon Abbansa yyi yace "dama Abba ina son xan koma can gida na ne, sbda Akwae wani case da muke dubawa ni da abokai na kafin in koma lagos, so we have to stay togeda don mu yi aikin tare" Abba yace "toh shknn Allah ya taimaka" yace "Ameen" snn ya mike ya fita daga falon, bin sa da kallo Afeefah tayi snn ita ma ta mike a sanyaye tace "Abba na tafi" Abba yace "bbu matsala dae koh" kai ta gyada masa tace "bbu Abba" ya sallameta ta fita. Hawaye ne suka shiga bin kuncinta ta nufi dakinsu ta fada kan gado ta dinga rusa kuka, kukanta ya tsananta jin fitar motar Aliyu, su jiddah dae na ta shirin sch abunsa bbu Wanda yace mata komae, gajiya tayi da kukan ta mike daga karshe ta shiga bayi ta wanke bakinta tayi wanka ta fito, duk sae ta ji kmr xaxxabi na neman rufeta, ta fiddo da kayanta da kyar ta sa bayan ta shafa mai ta koma kan gado ta kwanta, Mami ne ta shigo dakin tace "wato Zainab ni kike jira in shigo in gaida ki koh" mikewa tayi da kyar don kanta yyi mata nauyi a sanyaye tace "Mami kaina ne ke min ciwo" Mami tace "ki sakko kiyi breakfast sae ki sha magani" saukowa tayi daga kan gadon ta daura dankwalinta ta bi bayan Mami, tea kadae ta iya sha, Mami ta dauko Mata magani ta bata ta sha snn ta koma falo ta kwanta kan kujera, Driver ne yyi horn alamar yana jiransu, Jiddah da sadiya suka dauki jakarsu suka yi ma Mami sallama, Afeefah ta mike da kyar tace "Anty jiddah don Allah ki dauko min jakata da hijab a sama" Mami tace "kina da lecturen safe ne?" Afeefah ta gyada kai tace "Umm" Mami tace "ki bari kawae su tafi ko da rana sae ya kai ki tunda baki jin ddi" girgixa kae Afeefah tayi ta mike da sauri tace "A'a ni xan tafi ynxu Mami" sama ta nufa ta dauko hijab da jakarta ta sakko tayi ma Mami sallama suka bar gidan. Driver na ajiye su ko wannensu ya nufi department dinsa, Afeefah kam karkashin bishiya ta samu ta xauna duk da tasan tana da lecture din safe, gaba daya tunaninta na gun ya Aliyu, duk ta rasa sukuni, Muryar Maryam ta ji a bayanta tana cewa "uhm Afeefah me kirki ko kira" Afeefah tace "ae ke naga kin yi kiran" murmushi Maryam tayi tace "wayata ce ta lalace, amma ai na shigo duba mana result, nayi niyar karbar lambarki gun Dr sharif ranan amma na manta," Afeefah tace "hka yace maki yana da nmbr na" Maryam ta dan yi murmushi tace "tashi mu shiga lecture an kusa shiga" girgixa mata kai Afeefah tayi tace "akwae abinda nake jira, ki shiga kawae" Maryam tace "toh" snn ta nufi lecture hall, Afeefah na nn xaune har bayan kusan awa daya ta hango Dr Sharif yana tahowa da wani student, dauke kai tayi da sauri har suka karaso, ta dan sata kallonsa suka hada ido don shima kallon nata yake, sunkuyar da kanta tayi har suka wuce. Mikewa Afeefah tayi da sauri ta bar wajen don bata ma son ya dawo ya ganta, rasa inda xata tayi lkci daya hawaye ya cika idonta ta nufi gate kawae, tsaye tayi tana share hawayenta ta tsayar da adai daita, shiru tayi duk da taji tambayar da yake Mata na cewa ina xata, a hnkli ta samu kanta da cewa "Nasarawa G.r.a xa ni" bata jira cewarsa ba ta shiga adai daitan.
Suna isa nasarawan tayi masa kwatancen inda xata, dai dai bakin gate din gidan ya ajiye ta ta fito ta bude jakarta ta mika masa duba daya ya bata canjin dari biyar, bata damu ba ta nufi gate din ta gaida mai gadin dake xaune kan benci a sanyaye tace "yana ciki" yace "ehh yana nn" tura gate din tayi ta shiga gidan, sae da ta isa bakin kofar shiga gidan taji gabanta na faduwa, kmr tana tsoron handle din kofar ta murda a hnkli ta ji shi a rufe, tsoron danne bell ta ji, kawae ta nufi back yard, kofar kitchen ta murda ta ji a bude ta shiga snn ta rufe ta nufi falo, bbu kowa falon sae Ac da plasman dake aiki, a sanyaye ta nufi stairs ta haura sama, ta dde tsaye bakin kofar dakin daga bisanni ta tura a hnkli tare da yin sallama can ciki ta shiga.
Eeshatullah Goni
😘😘
[5/23, 08:34] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
45....
Mikewa xaune ya Aliyu yyi daga kwancen da yake ya cire bargon jikinsa yana kallonta, ta karaso cikin dakin a sanyaye tana kallonsa xata yi magana ya girgixa mata kai ya nuna mata kofa cikin sanyin murya yace "Leave! immediately" kuka ta sakar masa ta durkushe nn inda take tsaye ta hade hannayenta muryarta na rawa tace "don Allah don Annabi yayanmu kayi hkuri plss ina rokon ka" rike kae yyi a raunane yace "me ya kawo ki nn Zainab, meye na biyo ni, Let me be Zainab, just let me be plss leave..."kuka take a hnkli tana kallonsa, ya dago kansa a hnkli yana kallonta da idanuwansa da suka sauya launi, ya runtse ido ya mike cikin tsawa yace "leave Zainab" a tsorace ta mike hawaye na sakko mata, ganin ta nufosa yasa da sauri yace "kar ki karaso kusa dani, ki fita nace" bae ankara ba sae ganin ta rungumesa tsam yyi, ta kwantar da kanta kirjinsa muryarta na rawa tace "Don Allah yayanmu kayi hkuri ka yafe min, baxan sa..." Kasa karasa tayi don tasan karya xata kuma yi masa, runtse ido yyi wani mugun sonta na fixgarsa, lkci daya hawaye ya taru idonsa, a hnkli ya janyeta daga jikinsa ya koma gefen gado ya xauna ya rike kansa da yyi masa nauyi, ta sulale nn kasa ta xauna tana rera kuka, sautin kukanta ne ya ishesa ba shiri ya sakko kasa yana facing dinta ya kamo hannunta a hnkli yana kallon fuskarta murya can kasa yace "tel me the truth little sis, kina son lecturan nn Dr Aliyu Sharif koh?" Kasa dago kai tayi bare ta basa amsa, ya dago kanta yana kallon idonta da ya rine don kuka, yace "tell me little sis" a hnkli ta shiga gyada masa kai, kura mata ido yyi ita ma hka, lkci daya ya kirkiri murmushi ya sauke idonsa daga nata, murya can ciki yace "shi ya siya maki waya koh?" Nn ma gyada masa kai kawae tayi, ya rike hannayenta gam yana kallonta, hkn yasa ta sunkuyar da kai a tsorace, murya can kasa yace "its OK little sis, I understand kina son shi sosae, dama wani abokina ne ke son ki tun kina karama shiyasa kika ga nake hanaki kula samari, but tun da kina son Dr Aliyu baxan kuma hanaki mu'amala da shi ba, amma ki kula da mutuncin ki na _'ya mace_ kin ji my princess, yhu knw I do alwayz have trust...." Kasa ci gaba yyi sbda tokarewar da muryarsa yyi lkci daya hawaye ya taru idonsa gudun kar ta dago ta gani yasa ya mike da sauri ya nufi kofa ta bisa da kallo har ya fita daga dakin, ta kusa minti goma xaune a dakin duk jikinta yyi sanyi, tana tunanin to waye wnn da yayanmu ke son hada ta da, mikewa tayi daga karshe ta fita daga dakin ta sauka downstairs, kwance ta samesa kan kujera a falo, ta karasa a sanyaye ta xauna kasa gefensa tana kallonsa, amma ta kasa cewa komae, hannunsa ta kamo xata yi magana sae kuma tayi shiru, a hnkli tace "yayanmu baka da lfya ne?" Gyada mata kai kawae yyi ya dafe kansa yace "am having headache" da damuwa tace "ka sha magani?" Yace "na sha!" Lumshe ido yyi hkn yasa tayi shiru bata kuma cewa komae ba, tana nn xaune har bayan minti ashirin snn ta daga kai tana kallonsa ta ga bacci yake, mikewa tayi tana kallon agogo ta ga har goma ya gota, gyaran gidan ta shiga yi tun daga shara har goge goge ta gyara ko ina fes, snn ta nufi kitchen don ganin ko akwae foodstuffs, gnin bbu yasa ta tafi sama ta shiga dakinsa ta dauki wallet dinsa dake gaban mirror ta bude ta ciro dubu uku snn ta rufe ta mayar ta ajiye, pen da jotter ta dauka tayi rub da ciki kan gado ta shiga list din abubuwan da xata bukata na girki, da ke suna xuwa kasu da su Jiddah duk tasan price din cooking stuffs din, tana gama list din ta mike ta fice daga dakin, gun mai gadi ta nufa tayi masa sannu da xama snn tace "dama baba Wanda xae je min kasuwa nake nema" mai gadin yace "toh bari in kira maki kanina yana can saman layi" Afeefah tace "toh" snn ta xauna ya tafi kiran kaninsa, ba a dau lkci ba suka dawo a tare ta mika ma kaninnasa list din da kudi tace "sae ka yi kudin mota cikin kudin" godiya tayi ma mai gadin snn ta koma cikin gida ta haura sama don gyara bedroom, tana kwance dakin tana kallo bayan ta gama gyaran ta ji yayanmu ya kwala mata kira ta mike da sauri ta sauka kasa ta isa kusa da shi ta durkusa tace "yayanmu gani" idonsa lumshe yace "Check who's at d door" da sauri ta nufi kofa ta bude mai gadi ya mika mata kayan cefanen ta karba tayi masa gdya ya mika mata canjin, tace "A'a ka basa ya rike baba na gode" gdya shima yyi mata snn ta rufe kofar ta karaso cikin falo, ya Aliyu ya bude ido yana kallonta yace "wats dat?" Ta wara masa ido tace "cefane mana, girki xan maka yayanmu" ya dan yi murmushi ya kuma lumshe idonsa ta nufi kitchen, kiranta ta ji ya kuma yi bayan yan mintuna tana kkrin blendin tomatoes ta fito da sauri, yyi mata nuni da jakarta ta nufi jakar jin wayarta ne ke vibrate, da kyar ta iya ciro wayar tana kallon mai kiranta taga Dr sharif ne, kasa daga kiran tayi, hkn yasa a hnkli yace "pick ur call, Dr Aliyu koh?" Gyada masa kai kawae tayi kanta a kasa ta daga kiran ta kara a kunne tayi shiru, "Zainab!", Da kyar ta iya bude baki tace "Na'am, ina kwana sir" Dr Sharif yace "Me ya hanaki shiga lecture yau?" Shiru tayi har sae da ya kuma kiran sunanta snn a hnkli tace "Sir kaina ne ke min ciwo shi sa" yyi murmushi yace "shiyasa kika xauna karkashin bishiya knn kika hade rae kika ki shiga lecture kowa ya xo wucewa ki bi sa da harara daga karshe kika tafi gida koh?" Murmushi tayi ta girgixa masa kai tace "ni ba gida na tafi ba" yace "to ina kika tafi?" a hnkli tace "gidan yayanmu" "wani yayan naku?" Murya can kasa tace "Ya Aliyu" shiru Dr sharif yyi snn a hnkli yace "kina me?" Wara ido tayi tace "Am cookin for him he is sick" shiru Dr Sharif ya kuma yi na yan sakwanni snn yace "alryt, ayi girki lfya" lkci daya ya katse wayar, Afeefah ta dan yi stil kmr me naxari snn ta juya tana kallon yayanmu taga idonsa a lumshe, mikewa tayi a sanyaye ta koma kitchen, cikin minti arba'in ta gama hada lafiyayyen rice nd stew dinta da fried cow meat, ta yayyanke vegetables din ta ajiye gefe daya, snn ta shiga hada masa favourite drink dinsa na Ginger, jikinta ne ya bata ana kallonta ta juya da sauri ta gansa jingine jikin kofar kitchen ya rungume hannayensa yana kallonta, ta xaro ido ta isa gabansa da sauri tace " yayanmu ka tashi? Ya ciwon kan" jin yyi shiru yana kallonta yasa ta kamo hannunsa lkci daya ta sake da sauri tace "yayanmu jikin ka da xafi, har ynxu kan ne?" Kai ya gyada mata ya juya ya koma falo, bin bayansa tayi ta ga sama ya nufa, hkn yasa ta koma ta cigaba da abinda take, ta gama ta tsaftace kitchen din ta ajiye sauran kayan girkin da ya rage a deep freezer snn ta jera abincin a dinning, kwance ta samesa a daki yyi rub da ciki ta xaune gefensa tana kallonsa tace "yayanmu?" Juyawa yyi yana kallonta a hnkli yace "Zainab!" Tace "am through," yace "Weldon" tace "in kawo maka sama?" Yace "No sae anjima" tace "to ka siya maganin ciwon kan ne?" Gyada mata kai yyi, shiru tayi hkn yasa yace "ba lecturan ki ya kira ki ba daxu, may b kina da lecture ynxu, start goin to sch little sis" Tace "dama ynxu xan wuce yayanmu, amma xan dawo da yamma ka ji" Ya Aliyu yace "ki ci abinci to kafin ki tafi" shiru ta dan yi snn tace "sae dae in tafi da shi yayanmu" yace "OK bude wallet ki dauki transport," tace "nagode yayanmu" mikewa tayi ta bude wallet din ta dauki transport tace "byee yayanmu" binta yyi da kallo har ta fita snn ya maida kansa kan pillow ya runtse idonsa. Kitchen Afeefah ta nufa ta dauki kula ta xuba abinci ta debi ginger drink snn ta samu leda ta saka su ciki ta fito falo ta dauki handbag dinta ta fice daga gidan. Ana kiran Azahar ta shigo sch, masallaci ta nufa ta fara yin sllh ana idarwa ta yi ma yayanmu addu'ar Allah basa lfya snn ta mike ta fice, bin ta Maryam tayi tace "Wae na maki laifi ne Zainab, naga yhu are ignoring me" Afeefah tayi murmushi tace "ni baki yi min komae ba Maryam, daxu kaina ke ciwo shi sa bn shiga lecture ba" Maryam tace "To Allah sauwake, ynxu sae 4 kuma muke da lecture, mu tafi cafeteria sae in baki handouts ki duba abinda muka yi yau" Afeefah tace "to ki je can ki jira ni akwae inda xan tafi ynxu" Maryam tace "OK" snn ta nufi cafeteria, Sae da Afeefah ta daina ganinta snn ta nufi office din Dr Sharif da sauri, kwankwasa kofar tayi a hnkli, sae da ta kwankwasa har sau uku Snn yace "Come in!" A hnkli ta tura kofar ta shiga da sallama, yana xaune ya jinginar da Kai jikin kujera ya sauke kafarsa daga kan table dinsa ya gyara xaman sa, ta Karaso cikin office din, ido ya kafa mata ta cikin farin glass din idonsa, kanta a kasa ta karaso table dinsa tace "ina yini sir?" Yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "Har kin gama girkin knn Miss Chef?"
Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:57] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
46___48
Shiru Afeefah tayi tana kallonsa, sae kuma tayi murmushi tace "Um na gama" ledan hannunta ta ajiye ta fiddo kulan ciki da drink da plate da spoon tace "I brought this for yhu sir" bata jira cewarsa ba ta bude kulan abincin, dauke kai yyi ya shiga danna wayarsa yace "Abincin yayan naki xa ki kawo min?" Ta girgixa kai tace "ae da yawa na dafa sir" ganin xuba masa take son yi a plate ya dakatar da ita da sauri "No! ni am OK" tsayawa tayi tana kallonsa, yyi kmr bae san tana yi ba, can ta rufe kulan ta mayar da shi cikin nylon da plate din snn ta dauka ta nufi kofa, bin ta yyi da kallo har ta fice ta rufo masa kofar sa. Cafeteria ta nufa ta samu Maryam xaune da drink a gabanta, Maryam tace "har kin dawo?" "Um" kawae Afeefah ta ce mata, Maryam tace "ina ce office din sir kika tafi" hade rae Afeefah tayi tace "hka nace maki" bata jira cewarta ba ta bude leda ta fiddo abincin tana kallonta tace "Bismillah" Maryam ta dan yi murmushi tace "A'a ni na koshi" Afeefah tace "OK" diban abincin tayi cikin plate ta dauki spoon ta fara cin abun ta, jin wayarta na vibrate a jaka ta bude jakar ta fiddo wayar, jiddah ta ga ke kiranta, ta daga Jiddah tace "wae ina kika je yau Afeefah?" Afeefah tace "wajen yayanmu" Jiddah tace "shine kika ki shiga lecture?" Afeefah ta hade rae tace "to wae wa ya gaya maki bna sch? Ni ynxu ma ina nn kusa da dept dinmu," katse wayar Jiddah tayi Afeefah ta mayar jakarta, Ba tare da ta kalle Maryam ba tace "ke kika ce ma Anty Jiddah bn shiga lecture ba?" Maryam tace "No!" Afeefah na gama cin abincin gabanta ta mayar da plate din da spoon cikin leda ta kalli agogon cafeteria ta ga har biyu, mikewa tayi tace "Baxan iya jiran lecture har 4 ba, ni na tafi gida" Bin ta da kallo kawae Maryam tayi har ta fice abun ta, ta kama hanyar main gate. Afeefah na isa gida ta bi ta kofar kitchen ta lallaba ta wanke kulan abincin hannunta snn ta dauki ginger drink ta nufi sama, dakin Mami ta shiga Mami tace "har kin dawo, ina su Jiddah?" Afeefah tace "basu gama lecture ba su" gaisheta tayi Mami tace "ya ciwon kan?" Afeefah tace "Da sauki Mami" juyawa tayi ta fita daga dakin ta shiga nasu tayi kwanciyarta, biyar saura Mami ta kirata ta sakko kasa ta taya ta girka Supper, Afeefah na slicing Pumpkin leaves tace "Mami xa kiyi abinci da yayanmu koh?" Mami tace "a ina kika ga yayanku?" Afeefah tace "Ba yana gidan sa ba" Mami tace "to gidan nasa xan kai masa abincin" a hnkli tace "Kinga Mami bashi da lfya fa" Juyawa Mami tayi ta kalleta tace "shi ya gaya maki bae da lfya?" Afeefah ta gyada Mata kai, Mami tace "Adnaan baya nn ban san Wanda xae Kai masa ba sae dae ya xo ya karba da kansa," Afeefah kmr xata yi kuka tace "Mami ba sae ni in kai masa ba, bashi da lfya fa" harara Mami ta watsa Mata tace "idan naki ba ki fa?" Shiru tayi bata ce komae ba, Mami ta ci gaba da abinda take, Mami na kwashe tuwo Afeefah ta juya xata bar kitchen din ita a dole fushi take baxa a kai ma yayanmu abinci ba, Mami tace "ina xa ki? Ni xan wanke maki kwanukan can" kmr xata yi kuka ta nufi sink ta soma wanke kwanukan da suka bata, tana gamawa ta bar kitchen din ta haura sama. Wayarta dake jakarta ta ciro dae dae lkcn da ya fara vibrate, Dr Sharif ta ga ke kiranta, da kmr baxata dauka ba har ya kusa katsewa sae ta dauka tayi shiru, tana jin yyi murmushi snn yace "Dama mutum na cin abincin da ba da sunansa a girka ba Zainab?, ae kwadayi knn" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "Zainab" murya can ciki tace "Na'am" yace "yhu ran away frm my lecture yau koh? Nasan maganin ki" turo baki tayi bata ce komae ba yace "Gidan yayan naku kike koma knn!" Girgixa masa kai tayi tace "gida na dawo" a hnkli yace "Toh am srry dear in dan ban ci abincin ki bne, am just nt hungry a lkcn coz i finished drinking coffee kika shigo office," Shiru tayi bata ce komae ba yace "kin hkura?" Dan murmushi tayi yace "Gud almost tym 4 sallat will call yhu ltr" katse kiran yyi dae dae lkcn da su Jiddah suka shigo, Jiddah tace "ke dae ki daina abinda kike Afeefah, kwata kwata yau ba ki shiga aji ba wllh" Afeefah ta Mike fuuu ta fice daga dakin, a stairs suka hadu da Mami tace "ki shirya ke da Sumayya ku kai ma Aliyu abinci" ta wara ido tace "toh Mami" snn ta juya da sauri ta koma daki, Wanka ta shiga tana fitowa ta dauki kaya mara nauyi ta sa snn ta saka hijab ta dauki wayarta ta fice daga dakin, falo ta tadda Sumayya na jiranta, Mami tace "saura in yi biyan bashi da ku" Afeefah tace "ae baxa mu dde ba" a dai daita sahu suka samu a bakin titi, suna isa Afeefah ta basa kudinsa tace ma Sumayya ta karbo canji ta nufi cikin gidan, bbu kowa falo hkn yasa ta haura sama ta bude dakinsa da sallama ta shiga, Yana xaune gefen gado da wani abokinsa dake rike da mug din tea yana sha, fadawa kansa tayi tace "yayanmu ya jikin" wani tsawa abokin ya daka mata yace "ke dalla ja can, baki iya sallama bne xaki fado ma mutane daki hka" daga kai tayi tana kallonsa lkci daya ta hade rae, Aliyu ya juyo fuskarta ya sakar mata murmushi yace "Da sauki little sis daga ina da magrib hka?" Mikewa tayi tana hararan abokin ta gefen ido ta fice daga dakin da sauri, Aliyu ya juya yana kallonsa yace "kaga ba fa na son hka khabir," khabir yace "ae ni haushi take bn tunda har ta kasa gane sonta kke 4 ol dis while, toh wae ma ni 4 God sake meye amfanin boye ma wnn yarinyar the truth abou everything, she is matured enuf, a fada mata matsiyinta a gidanku ka fito fili kace sonta kke, hka kawae tun yarinya bata san kanta ba kke wahala da ita kawae daga karshe duk abun nn ya tashi a aikin bnxa, ni in ma baxa ka iya gaya mata ba sae ni in mata bayani wllh" girgixa Kai Aliyu yyi yace "akwae dalilin da yasa ake boye mata ba hka nn kawae ba, its a long story yhu knw" mikewa Aliyu yyi ya fita daga dakin dae dae bakin kofa ya hadu da Sumayya rike da basket din abinci ta gaishesa tace "yayanmu Mami tace mu kawo maka," yace "to ngd shiga da shi daki" dakin ta shiga shi kuma ya sauka kasa ya samu Afeefah xaune a falo kiris ya rage ta fashe, ya karaso kusa da ita yana murmushi ya xauna gefenta ya jawota jikinsa tun kan yace komae ta fashe masa da kuka har da shessheka tace "yayanmu ni bna son wnn abokin naka ka gaya masa bbu ruwansa dani ya daina min mgna idan ba hka ba xan gaya sa da Abba" murmushi Aliyu yyi yace "yi hkuri Zainab, amma me yasa ba kiyi sallama ba" cikin kuka tace "Allah nayi kunnensa dae ne bae ji ba" Aliyu yace "toh ya isa hka nn princess xan ja masa kunne" shiru tayi ya shiga share mata hawayen fuskarta tace "Nace ma Mami baka da lfya shine ta ba mu tuwo mu kawo maka ni da Sumayya," murya can kasa yace "to ngdd little sis" a hnkli tace "ya ciwon kan yayanmu?" Ya dago kanta yace "Alhmdllh ya daina" tayi murmushi tace "Allah ya sauke," yace "Ameen" saketa yyi ya Mike yace "tashi ki je kiyi alwala mu xamu tafi mosque" tace "to yayanmu" snn ta mike. Suna idar da sllh ya Aliyu yace su xo su tafi tunda dare yyi, ba dan Afeefah ta so ba ta sa hijab dinta ya basu kudin transport snn ya rakasu har bakin titi suka hau a dai daita ya koma gida. Hka rayuwa ta ci gaba da kasancewa kullum son Afeefah na kara wahalar da Aliyu amma bnda abokinsa khabir bbu Wanda yasan halin da yake ciki, ko kaninsa Adnaan bae sani ba, a hka ya karaci kwanakinsa a kano kullum cikin tunanin Zainab har ya koma Lagos bakin aikinsa, Afeefah kam shakuwarsu ya 'da da karfi da Dr Sharif, har Maryam da take boye ma sarae tasan soyayya suke da Dr Sharif kai hatta 'yan ajin gaba daya sun dago don duk ran da xae shigo masu lecture ya ga bata front seat xae bata umarnin ta dawo gaba, gashi duk tambayar da xae yi a aji ita xae ma Kashi 60 cikin dari, idan bata amsa dae dae ba kuma ya korata daga class din, a can Kaduna kuwa Dad na ta Shirye shiryen hada bikin su ilham da Afeefah ba tare da yyi shawara da kowa ba don a tunaninsa gwara yyi komae kafin ya sanar da iyayenta na kano, shi kansa Dr Sharif bae san shirin da dad ke yi ba. Yau ya kasance laraba ana saura yan kwanaki a fara exams, Zainab dake xaune gefensu Maryam da ke ta karatu da wasu kawayensu ta mike da kyar ta dauki jakarta tace "Kunga ni na tafi Cikina na min ciwo wllh" Maryam tace "to kin sha magani?" Afeefah tace "nasha da safe!" Allah sauwake sauran Kawayen nasu suka mata snn ta bar wajen, Office din Dr Sharif ta nufa don xuwa ta ce masa xata wuce gida, yana xaune yana duba assignment din yan 400l, ta karaso ta xauna kmr xata yi kuka tace "Sir xan tafi gida" ba tare da ya kalleta ba yace "Ba inda xa ki, xa ku yi tutorial yau" "wayyo sir ka ga fa bni da lfya ne" sae a snn ya daga kai yana kallonta ya cire siririn farin glass din idonsa yace "me ya same ki?" Kmr me shirin kuka tace "Allah ka tambayi su Maryam na ma kasa karatu, shi sa xan tafi gida" yace "to ina ke maki ciwo?" Kin gaya masa tayi hkn yasa yace "to bbu inda xa ki, ni bnga rashin lfya a idon ki ba" "Sir don Allah kayi hkuri kaina ke min ciwo" drawern sa ya ja ya fiddo paracetamol yace "gashi ki sha xa ki samu relief kafin tutorial" kuka ta sakar masa tace "ni baxan sha ba gida xan wuce" yyi murmushi yace "next semester ba lallai ki gan ni ba ma bare in dinga damunki ki shiga karatu kina cewa A'a" tace "Sir ina xa ka?" Yace "inda na fito mana, I came to lecture for sometimes a nn, nd my period is over xan koma clinic, I have passed d knowledge I was ordered to, don hka xan koma bakin aikina" Afeefah tayi shiru tana kallonsa ba tare da ta shirya ba murya can ciki tace "xan yi missin dinka sir!" Ya wara ido yace "Really!" Rufe ido tayi da sauri don bata san lkcn da ta fadi hka ba, ya mike ya xagayo ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta har lkcn fuskarta a rufe, a hnkli yace "Zainab!" Ba tare da ta bude fuskar ba tace "um" yace "da gske xa kiyi missin dina?" A hnkli ta gyada masa kai, yyi murmushi yace "to sauke hannun" ba musu ta xame hannunta daga fuskarta, abinda bae taba furta mata ba ya furta mata ranan murya can kasa yace "I love yhu Zainab" shiru tayi tana kallonsa lkci daya ta sauke idonta kasa, a hnkli yace "Am srry Zainab!" Yana fadin hka ya kamo fingers dinta bata ankaraba sae ji tayi ya saka mata wani ring din axurfa karami me kyau yana kallon fuskarta yana murmushi yace "Will yhu Marry me!" Shiru tayi tana kallonsa, can ta sunkuyar da kanta, cikin sanyin murya yace "Zainab" kmr me tsoron magana tace "uhm" ya kuma maimata tambayar da yyi mata, ta gyada masa kai a hnkli cike da jin kunya, ya wara manyan fararen idonsa yace "da gske Zainab" murmushi tayi ta dauke kanta, murya can ciki yace "Allah sa har xuci" ya kusa minti biyu durkushe gabanta yana kallonta daga karshe ya mike ya koma table dinsa ya dauki makullin mota yace "Mu je in siya maki magani, tunda kina kunyar gaya min Dysmenorrhea (Menstrual cramps) ne matsarki" ba karamin kunya Afeefah ta ji ba ta mike da kyar kanta a sunkuye ganin kallonta yake, ta nufi kofa, yyi murmushi ya bi bayanta. Wani pharmacy a wajen sch ya tsaya, ya siya mata mugunguna snn ya nufi gida da ita. Dai dai gate dinsu yyi parkin ya dauki ledan maganin ya mika mata ya gaya Mata ynda xata sha, kanta a kasa ta karba tayi masa gdya ta bude motar ta fita da sauri, bin ta da kallo yyi yana murmushi har ta shiga gida.
Ana gobe Afeefah xa su gama exams tana kwance daki da handout a hannunta tana karatu Sadiya ta shigo tace "wae kije in ji Abba" Afeefah ta mike ta ajiye handout din hannunta snn ta sa hijab ta fita ta nufi falon Abba, su Sumayya ta ji suna yi ma mutum sannu da xuwa a falo, ta karasa stairs ta leka downstairs ta ga yayanmu ne, da gudu ta sauka kasa ta karasa cikin falon ta rungumesa cike da murnar ganinsa don kusan 3 mnth knn bae xo ba, yyi murmushi yace "ya exams Zainab" ta wara ido tace "ae gobe xa mu gama, yayanmu ni wajen ka xan je hutu ba Kaduna ba" yana cire safar kafarsa yace "To Allah sa Mami ta yarda" mikewa yyi yace "naga motar Abba, yana sama?" Zainab tace "ehh" tare suka haura sama da ya Aliyu suka shiga falon Abba, Adnaan ne ya fito daga falon yyi ma ya Aliyu sannu da xuwa snn ya galla ma Afeefah harara yace "baki san ke ake jira ba" turo baki Afeefah tayi ta shiga falon tare da ya Aliyu tana wondering me tayi kuma ake kiranta, Abba na xaune da alamar ita yake jira, Mami ma na xaune a falon ta bi ta da kallo har ta karaso cikin falon ta xauna tana kallon Abba kmr mara gskya tace "Abba gani" xaunawa Aliyu yyi gefen Mami da tayi murmushin ganinsa tace "Ya hanya Ali?" Ya shafa kansa yace "Alhmdllh Mami, ya gidan" tace "Lfya lau, na ma yi xatan se da yamma xaka shigo da kace min kana Nasarawa" Aliyu yace "Nayi tunanin baxan samu Abba bne shi yasa na xo ynxu" se a snn Aliyu ya gaida Abbansa dake ta kallonsa gnin yanda ya rame, Abba yace "Lfya lau, kayi rashin lfya ne?" Girgixa kai Aliyu yyi yace "A'a lfya ta lau Abba" Abba yace "to yyi kyau" juyawa Abba yyi yana kallon Afeefah yace "Dama Zainab da kika je hutu wancan karan Kaduna ce masu kika yi aure kike so?" Juyawa Aliyu yyi yana kallonta, ita kuwa ba karamin faduwa gaban ta yyi ba, tayi shiru tana kallon Abba a tsorace, Mami tace "ba magana ake maki ba" hawaye ne ya cika idonta muryarta na rawa tace "ni bnce ma kowa hka ba" Abba yace "karya xa ki mana knn," fashewa da kuka tayi tace "Abba Allah ni ban ce ma kowa xan yi aure ba" Abba yace "to kin san kuwa Abbanku na Kaduna yana shirin bikin ki da nasu Jamila, jiya da daddare ya bugo min yana min bayani wae kin tsaida miji a Kaduna xuwan ki na kwanaki, ynxu ina son sanin waye mijin, kuma a ina kuka hadu, sannan ina son da bakin ki ynxu ki gaya min irin dokata na gidan nn kafin in sa a xane min ke"
Eeshatullah Goni
[5/22, 07:57] Umar Dalha: ?????? 'Ya mace kyautar Allah??????
A true life love story
By Ashmaad
49___50
Hawaye Afeefah ta shiga yi tana kallon iyayen nata a tsorace, da ganinta kasan ba karamin tsorata tayi ba, Mami tace "ki fa bude baki kiyi magana don duk kika bari na mike nn sae nayi maganin ki wllh" Da kyar muryarta na rawa tace "Abba ni gskya ta nake fada maku bn ce masu ina da Wanda xan aura ba fa" Aliyu ne ya mike da kyar yana kallon parent din nasa yace "Abba xan je in dan huta am having headache" Abba yace "A'a Ali ka xauna ayi maganar nn gaban ka, idan kuma tafiya xa ka yi da ita ta fada maka gskya to ka tafi da ita idan ba hka ba wllh Adnaan xan sa ya xane min ita" kuka Afeefah ta saki tana kallon ya Aliyu, a hnkli ya Aliyu yace "tashi mu je" da sauri ta mike ta bi bayansa, Mami ta bi ta da harara, suna shiga bedroom dinsa ya xauna gefen gadonsa ita kuma ta xauna kasa kusa da kafarsa yana kallonta yace "Aure kika ce ma su dad kike so Zainab?" Cikin kuka tace "Allah ni ban ce masu hka ba yayanmu" yace "to ya kika ce masu" share fuskarta tayi ta mike ta xauna gefensa tace "kaga yayanmu dama last hutun da na tafi ne can Kaduna, ashe sun san wnn lecture din namu, kanwarsa wata Anty Amina ce ke auren ya Ma'aruf shine sae ya xo ya gan ni, kila shi yace masu xae aureni amma ni bn sani ba" ta karashen mgnr tana kallon yayanmu, Shiru Aliyu yyi yana kallonta da mmki, a hnkli ya sauke idonsa kan axurfan yatsan ta dake ta kyalli ya kamo fingers din yana kallo yace "Zoben waye wnn Zainab?" Kallonsa Afeefah take, murya can ciki tace "Dr Sharif ne ya bani" da kyar ya iya nanata abinda tace yana kallonta, ta gyada masa Kai a hnkli, sake hannunta yyi bae kuma cewa komae ba, can ya mike ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom ta bi sa da kallo, wanka yyi ya fito, ya xura jallabiyarsa ya nufi kan gado ba tare da ya kalleta ba yace "Xan kwanta, idan kin fita ki rufe min kofa" shiru Afeefah tayi tana kallonsa, bayan minti kusan goma ta mike a sanyaye ta fice daga dakin. Misalin Karfe uku Aliyu ya fito daga dakinsa ya shiga dakin Mami, tana xaune tana kunce ma autar ta Fadila kitso, ya nemi gefen gado ya xauna Mami tace "Ya ku ka yi da Zainab din Ali?" Shiru ya Aliyu yyi kmr baxae ce kome ba sae kuma a hnkli yace "Ta ce bata san xancen ba, kuma hkan ne, bata sani ba don da ta sani baxata min karya ba" Mami tace "to don me Alhajin Kaduna xae mana hka, naga ae ba gun sa take ba, ko da ma can din take ba dattako bne wnn, Haba fisabilillah" Aliyu dae bae ce komae ba, waya Mami ta dauka ta shiga neman layin Hajiya Khadija mahaifiyarsu Ma'aruf, bugu biyu ta daga suka gaisa snn Mami tace "Hajiya daxu babansu Jiddah ke min wani bayani da bn gane kansa ba wae Zainab tace ta tsayar da miji a can Kaduna ko yane bn dae gne ba wllh" Mum dinsu Ma'aruf "Ayyo kinsan bikinsu Ilham ya kusanto shine yake nuna da ma Zainab na da tsayayye sae ya hadasu kawae, to ana hka ko sae ga yayan matar Ma'aruf ya xo da xancen yana sonta, ashe ma wae malaminta ne a makaranta, Alhaji ya sa na tambayeta ko tana sonsa tace min tana so, to shine fa Alhaji yace da a hada kawae xae fi armashi" Tun da Mum ta fara xancen ta yanayin Mami ya canxa, gnin ta kai karshe yasa tace "Kinsan Hajiya babansu na nan irin tsarin sa sae yara sun gama karatu ko suna dab da gamawa yake aurar da su, don hka gskya baxae ji ddi ba tunda Zainab dae..... ko kuma bari ma dae xan taho kadunan in'sha Allah ba maganar waya bace wnn" Sallama suka yi Mami ta ajiye wayar rae bace tace "ya xa su min hka, wajen su yarinya take ko salon su nuna...." Shiru Mami tayi gnin ynda Fadila ke kallonta, Aliyu kam mikewa yyi ya fita daga dakin, Mami ta kalli Fadila tace "tafi ki kira min Zainab" Afeefah na daki don throughout ranan bata fito ba fadila ta shigo tace "Anty Afeefah Mami na kiran ki" mikewa Zainab tayi gabanta na faduwa kmr me shirin kuka tace "tana ina?" Fadila tace "bedroom" a sanyaye Afeefah ta nufi dakin Mami gabanta na ci gaba da faduwa, a tare suka shiga da Fadila Mami ta kalli Fadila tace "ki tafi Su jiddah su tsefe maki fadila" juyawa tayi ta fita Mami ta kalli Afeefah da ta rakube gefen gado a kasa tace "Don uwar ki dama ke kika ce ga Wanda kike so a Kaduna" kuka ta fashe da tace "Mami wllh Mum ce ta tambayeni..." Rai bace Mami tace "Waye shi?" Gabanta na faduwa cikin in ina tace "Mami lecturer dinmu" da mmki Mami tace "Wani lecturan?" Kmr xata yi kuka tace "Wanda ya taba xuwa gidan nn, dama ashe kanwarsa ce matar ya Ma'aruf shine muka hadu da shi a can gidan ya Ma'aruf" shiru Mami tayi tana kallonta, da alama fada take son mata amma ta kasa, Can tace "Fita ki ban waje" a sanyaye Afeefah ta mike ta fita. Har dare bata fito daga daki ba sbda tsoron haduwa da Abba da take yi, gashi ta rasa dalilin da yasa ya Aliyu yaki shigowa dakinsu. Washegari sun fito daga exams ita da Maryam tace "Maryam ni na tafi gida" haduwa da Dr Sharif ne kawae bata son yi, tana isa gida gnin ba kowa a falo ta haura sama kmr munafuka, dakin Aliyu ta shiga ta gansa xaune yana rike da remote, Karasowa tayi ta xauna kusa da shi kmr xata yi kuka tace "Yayanmu mun yi hutu yau ni xan bi ka Lagos" girgixa mata kai yyi ba tare da ya kalleta ba yace "Abuja xan tafi gobe ba Lagos ba" kmr xata yi kuka tace "don Allah ka tafi dani Yayanmu ni tsoron Abba nake" bae tanka ta ba ya ci gaba da canxa tashar da yake, hkn yasa ta mike ta fita daga dakin a sanyaye ta nufi na su, wayarta dake vibrate a jaka ta ciro Dr Sharif ta ga ke kiranta da kmr baxata daga ba sae kuma ta kasa ta daga a hnkli, da damuwa yace "Shine kika tafi ko sallama bbu ko Zainab?" Shiru tayi, sae kuma a hnkli tace "Su anty Jiddah ne ke jirana shi sa, kayi hkuri" yace "Dama ina son mu yi wata magana ne dake sae naga kuma kin tafi, ba kuma na son na maki mgnr ta waya, hw are we goin to do it Zainab, I dnt want yhu to regret anything so we have to talk" shiru tayi tana tunanin to wace magana ce wnn yake son Mata, a hnkli tace "To gobe sae in xo sch" girgixa kai yyi a hnkli yace "am goin to Abuja gobe as early as possible Zainab, tafiyar is vry urgent" shiru ta kuma yi tana tsoron ce masa ya xo gidansu, tunawa tayi ae ya Aliyu yace xae tafi Abuja gobe kuma tace xata bi sa, da sauri tace "Sir ni ma gobe xan bi Yayanmu Abujan," shiru yyi snn yace "gun wa xa ku xo?" Girgixa masa kai tayi tace "Gidansa xa mu tafi, kila yana da wani aiki da xae yi" da mmki yace "just the two of yhu?" Gyada masa kai tayi tace "Ehh" rasa ma me xae ce mata yyi kawae yace "OK, ltr" ya katse wayar da sauri. Da daddare Abba na falonsa Mami ta shigo falon ta xauna tana kallonsa tace "Alhaji ina son xuwa kaduna gobe da safe don Allah" da mmki yace "ki je kiyi me?" Tace "Kan maganar jiya," Shiru Abba yyi snn ya nisa yace "Kinga idan abun nn na son xama tashin hnkli ne ki bar su suyi ynda suke so da yarinya don sun fi mu iko da ita, ni da su duk daya muke gun Zainab" cikin bacin rae Mami tace "ta ya suka fi mu iko da ita Alhaji, ka bari kawae ni ba tashin hnkli xan je yi da su ba magana ta fahimta kawae xan je mu yi" Abba yace "To shknn Allah Kai mu goben, sae Ali ya kai ki, tun da ma sun yi hutu ku tafi tare da Zainab din kawae" Mami tace "Ali kam bae fa jin ddi, tun da ya dawo na rasa me ke damunsa ko abinci ma na lura bae ci, driver ya kai ni kawae tunda Adnaan bae nn, Zainab kuma idan na dawo daga baya sae ta tafi bna son mu je tare" Abba yace "A'a da ita xa ku," Shiru Mami tayi bata ce komae ba, Abba yace "Ali kuma daxu ya shigo yace xae je Abuja gobe ba sae ya ajiye ku ba kawae, ni kaina na rasa meye damuwarsa xurfin cikin sa yyi yawa, kema da ku ka fi kusa bae gaya maki ba bare ni, da ma Adnaan ne" Mikewa Mami tayi tace "ina nn xae xo ya sameni ya gaya min" kofa ta nufa tace "bari in karasa abinda nake yi a daki Alhaji"
Washegari da Asuba Aliyu ya shigo dakin Mami, gaisheta yyi xae fita tace "Wae xaka Abuja yau ko Ali?" Yace "Ehh shiri ma xan tafi in yi ynxu" tace "To xa ka ajiye ni Kaduna" yace "To Mami" snn ya juya ya fita, Addu'a Mami ta shiga yi na Allah sa ta iya shawo kan dangin late tsohon mijinta, ta kuma ta fatan Allah sa baxa ta tarar da Yakumbo a gidan ba,(kanwar kakar Afeefah) tunda ta ji suna ta shirin biki ne,
Tunawa da tayi Abba yace ta tafi da Afeefah yasa hnklinta ya tashi don tasan in har Yakumbo na gidan abu ya kuma lalacewa knn, dubara ce ta fado mata, ta dae gama kimtsawa tasa Sumayya ta kira mata Zainab, Afeefah ta mike daga kwancen da take ta tafi kiran Mami, Mami tace "maxa ki shirya ki xo ynxu" komawa Afeefah tayi ta shiga wanka tana fitowa tasa wani atamfarta riga da skirt bayan ta shafa mai snn ta fito ta nufi dakin Mami, ido Mami ta kafa mata har ta karaso snn tace ta xauna, Afeefah ta xauna tana kallon Mahaifiyar tata, Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "Xa muyi tafiya ne ynxu, kina jina Zainab" kai Afeefah ta gyada mata Mami tace "Ki kama kan ki a duk inda xa ki kasance, ki kuma rike mutuncin ki na ya mace, kin ji dota" kai kawae Afeefah ta gyada ma Mami kanta a kasa Mami tace "Maxa ki je ki shirya kayan ki" Mikewa Afeefah tayi ta fita daga dakin tana tunanin to ina xa su bayan ta ce xata bi yayanmu Abuja, hawaye ne ya cika idonta ta shiga dakinsu ta shiga hada kayanta a jaka, bata yi wani breakfast din kirki ba, shi kansa Aliyun bae yi ba, Karfe bakwae da kusan rabi suka kama hanyar Kaduna, Sae da suka yi nisa ssae snn Mami na kallon Aliyu ta madubi tace "Aliyu tare xa ku wuce Abuja da Zainab bana son mu je Kaduna tare da ita, amma yaushe xa ka komo kano?" Shiru Aliyu ya dan yi snn yace "xan kusa sati biyu ina jin Mami" Mami tace "To ku tafi idan yaso nn da sati ko motar haya ce sae ka sa ta ta dawo" to kawae Aliyu yace ma Mami, Afeefah kam wani farin ciki ne ya lullubeta, har U-rimi Aliyu ya ajiye Mami bakin gate din gidansu Ma'aruf, rana ta farko knn tunda Mami ta haifi Afeefah ta ji faduwar gaban barinta da Aliyu abinda bae taba samun ta ba, don har lgs tana barin ya tafi da Afeefah, Aliyu yace "Mun tafi Mami" murmushi kawae ta iya yi masa, Afeefah kuma ta daga mata hannu, kallonta kawae Mami ke yi har ya ja motar, ta bi motar da kallo har ya bar layin snn ta ja kafa da kyar ta shiga gidan yayan late mijinta.
Surutu kawae Afeefah ta dinga yi ma Ya Aliyu a mota shi dae bae tanka ta ba lkci lkci kuma yyi murmushi har suka shigo Abuja wajajen Karfe sha biyu na rana.
Eeshatullah Goni
🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
A true life love story
By Ashmaad
51___52
Cikin kuka Afeefah tace "Ni ma ban san sunan anguwan ba" Dr Sharif ya dan yi shiru snn yace "To wae kukan me kike ma, ba ke kika ce xaki bi sa ba" gyada masa kai tayi bata ce komae ba, bayan kusan second goma yace "Shknn sae anjima" kuka ta saki tace "Sir don Allah kar ka tafi ka bar ni pls" murmushin da bae yi niya ba yyi cikin sanyin murya yace "to ya kike son in maki Zainab" ta girgixa kai tace "Ni dae kar ka kashe wayar don Allah" yace "To naji, sae ki ban lbri coz I don't have anything to say" a hnkli tace "To wani irin lbrin kke so" yace "me ddi" ta wara ido tace "Sir ni fa bn ma iya lbri ba, ka gaya min wani iri kke so dae" shiru ya dan yi snn a hnkli yace "Tell me meyasa kike so na" Xaro ido tayi da sauri tace "Sir lbri fa kace in baka" yace "um wnn ma ae lbri ne" rufe fuska tayi da kujera tayi yar dariya tace "Sirrr" yyi murmushi yace "Ma!" Jin tayi shiru yasa yace "ina jin ki fa" cike da jin kunya tace "Tunani nake yi sir" yace "To gama" bayan kusan second sha biyar a hnkli murya can kasa tace "Sbda kana da kyau ssae" murmushi yyi yace "Haba!" ta dago kanta da sauri tace "Allah sir, kana da kyau ba kadan ba don duk kafi kanninka kyau, shi sa 'yan mata ke son ka a sch, snn bbu ruwanka yhu are so kind nd understandin, kuma ka iya lecturing ba kadan ba, yhu are vry educated Sir, snn ga shi kae Medical Dr ne, kuma kana da taimako ba kadan ba" tun da ta fara xancenta Dr Sharif yyi shiru yana sauraronta, jin shirun yyi yawa yasa a hnkli tace "Sirr" murmushi yyi shima a hnkli yace "Ma!" Rufe fuskarta tayi da sauri, yace "Uhm shknn abinda ya sa kike so na?" Gyada masa kai tayi tace "um" yyi murmushi yace "to ngd" murmushin ita ma tayi snn tace "to ni baka gaya min ba" yace "meye bn gaya maki ba?" Cike da jin kunya tace "Abinda na gama gaya maka" yace "uhm wae dalilin da yasa nake son ki?" Gyada masa kai tayi a hnkli, yyi murmushi ssae, kmr Mae rada yace "Sbda kukan ki da shagwaban ki yasa nake son ki Zainab," bata fuska tayi tace "ni tun yaushe na daina kuka Sir" dariya yyi yace "ynxu fa kika gama min kukan Zainab, kuma ni baxan so ki koya ma yarana wnn kukan da shagwaba ba" shiru tayi bata ce komae ba, amma kiris ya rage ta fashe da kuka, dariya yyi don sarae yasan fushi tayi, a hnkli yace "fararen idanuwan ki masu rauni da saurin xubda hawaye suka ja hnkli na gare ki Zee nah, snn dimple din nn naki guda daya me kyau ma is nt left behind, ga wnn dogon hancin ki kmr na balarabiya, da dan karamin bakin nn naki da kike tabewa idan xa ki fara kuka" Afeefah ta fashe da kukan karya tace "Wayyo sirr ni xagi na kawae kke yi" dariya yyi sosae yace "Da gske fa nake bby, da wnn tsayin naki kmr daren sllh kina tafe kmr iska xae hankade ki one side" bata fuska tayi tace "Bye bye" da sauri yace "ohh tsaya bby, wasa nake maki wllh, but get this dear _Yhu are so pretty Zainab_ Allah ya maki baiwa da dama da baxan iya lissafo maki ba Zainab, I just love yhu Zee nahh, ina son ki da yawa, kullum addu'ata Allah ya mallaka min ke a matsayin matata uwar 'ya 'yana" rufe fuskarta tayi da sauri a hnkli tace "Thnk yhu sir" yace "ni baxa ki ce kina so na ba Zainab" a hnkli tace "I love yhu more" murmushi yyi yace "To yaushe xa mu hadu, ko yayanki baxae bari ba?" Ta dan yi shiru snn tace "idan na gaya masa xae bar ni, ae shi ba ruwansa" gate taji an bude ta wara ido tace "Sir kaga ya dawo ynxu" Dr Sharif yace "OK, shknn sae gobe knn" gyada masa kai tayi tace "Uhm Allah ya kai mu" a sanyaye yace "ki kula da kan ki Kinji Zainab" tace "To sir ngdd" kai kawae ya iya gyada mata ya katse wayar, ta kashe fitilar da ke kunne har lkcn da sauri kan ya Aliyu ya shigo, duhu ya gauraye falon, ta rakube jikin kujera inda baxae iya ganinta ba ta hade kai da gwiwa. Bude kofar falon ya Aliyu yyi gnin duhu falon ya ciro wayarsa ya kunna fitila ya shiga bin ko ina da kallo, kiranta ya shiga yi, ta ki dago kai bare ta amsa, ya karaso cikin falon yana kalle kallen inda xae gnta, ya ajiye ledan hannunsa da jakar kayanta da ya dauko a mota snn ya kunna Invertern falon nn da nn haske ya gauraye ko ina, ya ganta xaune jikin kujerar har lkcn kanta na hade da gwiwa, Karasowa yyi ya tsugunna gabanta ya dago kanta yana murmushi, kuka ta fashe masa da sae dae ba hawaye tana buge hannunsa, dariya yyi yana rike da fuskarta yace "Kiyi hkuri little sis, bn san xan dde hka ba wllh" juya masa baya tayi tace "Ni gobe xan wuce gida yayanmu na fasa hutun" murmushi yyi ya dago ta yace "Haba princess kiyi hkuri bn san xan dde bane" hawaye ne ya gangaro mata tace "ba sae da nace xan bi ka ba kaki kulani" yace "Gun abokan aiki na na tafi shi sa bn je da ke ba kiyi hkuri plss baxan kara ba" share mata hawayen ya shiga yi snn ya dago ta ya shigo tsakiyar falon da ita ya xaunar da ita shima ya xauna, ledan da ya ajiye ya jawo ya bude, ya fiddo drink din ciki da gasassun kaji, da kansa ya je kitchen ya dauko plates da cup, ya dibar mata nata ya ajiye mata gabanta, murmushi tayi tace "tnxx yayanmu" snn ta fara ci, shima ya diba nasa, ita ta fara tura sauran kajin gabanta tace "Yayanmu na koshi" yace "je ki sa a fridge," mikewa tayi ta nufi fridge ta ajiye ta dawo falon yace "baxa ki sha fura ba" ta girgixa masa kai tace "Na koshi" yace "to kinyi sllh?" Ta gyada masa kai, yace "Go nd brush ur teeth idan xa ki yi wanka kiyi sae ki kwanta ni ma bacci xan je in yi ynxu, kin gyara dakin da xa ki kwanta ko?" tace "Ehh na gyara" yace "Gud ki tafi da kayanki ciki" sae da safe tayi masa ta nufi dakin da xa ta kwanta rike da wayarta da jakar kayanta, Bakinta ta fara wankewa snn tayi wanka ta fito ta bude jakar ta fiddo rigar baccinta ta sa bayan ta dan yi shafe shafenta, ta kwanta knn wayarta ya fara vibrate ta duba ta ga Mami ce ke kiranta, dagawa tayi tare da yin sallama, Mami ta amsa tace "kin kwanta ne?" Afeefah tace "Ehh Mami" Mami tace "Ina Aliyun?" Afeefah tace "Yana falo" Mami tace "OK, kina jina?" Afeefah tace "Ehh ina ji" Mami tace "meyasa da aka tambayeki kina son malamin nn naku kika ce kina so?" Shiru Afeefah tayi bata ce komae ba, Mami tace "wato ke aure kike so ynxu ko Zainab?" A sanyaye Afeefah tace "wllh bnce ina son aure ba Mami Allah" Mami tace "Aa hka ne mana, da bakya so da baxa ki ce masu kina sonsa ba," Shiru Afeefah tayi lkci daya hawaye ya cika idonta, Mami tace "Shknn tunda hka kike so, sae a aurar da ke yayyinki ba su yi auren ba, don baxan kuma ja ma kai na bakin jinin da nayi ba a da, duk ynda suka yi da ke iyayen ki ne" kuka ta fashe da tace "Mami ni fa karatu nake," Mami tace "kinsan da karatun kika amsa masu kina sonsa sha sha sha kawae," Mami na kai wa nn ta katse wayar, Mami na katse wayar dama Aliyu ta kira don masa bayanin ynda suka yi da mutan Kaduna, Kuka Afeefah ta shiga yi a hnkli, jin wayarta na vibrate ta dauka don a tunaninta Mami ce, Dr Sharif ta gani da kmr baxata daga ba sae kuma ta daga a sanyaye don bata iya kin daga kiransa, cikin sanyin murya yace "ba kiyi bacci ba" "um" kawae tace masa, yace "kina ina ynxu?" A hnkli tace "bedroom" yace "kinyi kuka knn koh? Me aka maki?" Kukan ta sakar masa tace "Mami ce tace wae aure xa a min" shiru Dr Sharif yyi snn a hnkli yace "ke kuma ba kya so koh?" Ta gyada masa kai kawae, yace "Wa xa a aura maki?" Cikin muryar kuka tace "wae kai" shiru ya kuma yi snn cikin sanyin murya yace "kuma baki so na ko?" Girgixa masa kai tayi tace "A'a karatu nake son inyi ne Sir" yace "ki kwantar da hnklin ki Zainab, dama mgnr da nake son muyi knn jiya a sch kika wuce gida, Kinga ni ma is just of recent na ji abinda dad din Ma'aruf ke shiryawa don ba da ni yyi magana ba da Abba na yyi, but ki kwantar da hnklin ki, I will tel dem am nt ready ynxu don ko nace masu kina karatu a bari ki kare nasan ba lallai su yarda ba, sae in ce masu xan tafi course waje, hkn yyi ae koh?" Murmushi tayi a hnklk tace "Uhm ngd" yace "yauwa Zainab but make a promise to me plss" a hnkli tace "wani promise sirr?" A sanyaye yace "Dat no matter wat baxa ki taba ki na ba, promise me dat yhu will b my wife Zainab" shiru ta dan yi lkci daya tayi murmushi cikin sanyin murya tace 'I promise Sirr" yace "kar ki manta Zainab, alkawari kaya ne fa" a sanyaye tace "Na sani sir" murmushi yyi yace "To ngdd Zainab Allah baki ikon rike alkawari," a sanyaye tace "Ameen sir," yace "Gud nyt, kiyi addu'a kafin ki kwanta, ki kuma kula da kanki Zainab, ki kuma ji tsoron Allah a duk inda kika kasance" ta gyada masa kai cikin sanyin murya tace "Toh sir ngdd" katse wayar yyi, ta mike ta nufi socket xata yi plugging wayarta Aliyu ya shigo dakin.
Eeshatullah Goni 😘😘
0 comments:
Post a Comment