Lantana ranar jitayi kamar ansata a aljannah dan mugunta,daɗin dataji beda iyaka dan haka makwabta tashiga yiwa shela.
Ayko nanfa gidan yacika damƙam anzo ganin yayan zina
Suhaima ko rungume yayanta tayi ta hana kowa ya ɗauka gamida rufe fuskokinsu.
Se dare gidan ya watse.
Ga sanyi anayi,suhaima se ƙara rufe yaranta takeyi gudun kar sanyi yamusu illah,
Mahaifintane yakawo mata tabarmarshi da bargonshi da filo dayake kwana akai yabata yace ta dunga kwantar da yaran tana rufesu.
Shida kanshi yamusu huɗuba bayan ya tambayi wanne suna takeso asa musu.
Kanta tsaye,tace
"AbdulRahman da AmatulRahman"
ayko haka yasakamusu suna,dan yace koma taya suhaima ta samar da yaran shine sila,da beyi watsi da rayuwarta ba hakan bazata faruba,shiyasa memakon tsana shi tausayinta yakeji.
Washegari da asuba lantana tafito tafara balai akan azofa aɗrmebo mata ruwa,suhaima na shirin miƙewa se taji baffanta ya fito ya tafi da kurar.
Kukane ya kuɓcewa suhaima tana rungume da yaranta take faɗin.
"me yasa habibi kayimin haka?,meyasa kakase gane niba fasiƙa bace?,meyasa kakasa shaidata?,meyasa?" ta ƙarasa maganar cikin kuka.
Gari be gama wayeba sega hanne tazo gurin suhaimar bayan sungaisa tace mata.
"innace tace nazo na tayaki ɗaukar yaran kizo tamuku wanka tun ɗazu ta kwashe ruwan"
kukane ya kwacewa suhaima data tuno tata innar.
Haka suka tafi gidan su hanne.
suna zuwa toilet suhaima tashiga inna tamata wankan jego,sannan tasata ta zauna a ruwa.
Bayan sun fito inna ta wanke yaran,sannan ta ɗauko rigunan data siyo musu jiya da yamma tasaka musu.
duk da rigunan bamasu tsada bane amman,sunyi musu kyau.
Daga ƙarshede suhaima a gidan ta zauna inna na kulawa da ita har seda tayi arbain.
su twins ko irin masu girman,agir dinnanne,sunyi yan lukutaye dasu abunsu,gasu da wayo.
Bayan suhaima tayi arbainne takoma gidansu,taci gaba da bauta,dan bazata juri ganin mahaifinta nayiba.
ya hanata yace tabarshi shi yayi amman fafur taki amincewa.
Ruwa kawai take barinshi yana ɗebowa,amman tallah tuni ta koma bakin aykinta.
in zata tafi,seta goya twins,ɗaya agaba ɗaya abaya,innar hanne ce ta koyamata irin goyon.
Se tasaka hijab ɗinta ta rufesu ahaka zasuje sugama yawo arana su dawo.
Duk wani haske da suhaima tayi tuni ya dishe,sabida wahala.
Yau tun cikin dare Abdulrahman yake kwara amai,ga zazzafan zazzaɓi daya rufeshi,se kuka yakeyi,
Hankalin suhaima inyayi dubu yatashi tarasa inda zatasa kanta Allah Allah take gari ya waye.
Ayko bakwai abakin chemis din rabiu dan me gari yamata.
Duk saurinta seda ta samu layi,sabida chemis din shine kamar asibitinsu,dayake babbah ne.
Layin tashiga har yazo kanta.
Koda tashiga yagama dubashi,maganin dubu daya yarubuta mata.
kuka suhaima tasamishi akan yaymata bashi zata biyashi,buɗar bakinshi se cewa yayi.
"keko suhaima din Allah haka kikaje kika gama rabawa larabawan abun kyauta basu baki komaiba se tukuicin yayan zina?"
maganar ta doketa amnan tunda neman taimako takeyi dole ta bashi amsa a saukake.
"wlh kabiru yaran nan bana zina bane,zaku tabbatar da hakanne ranar da mahaifinsu yabiyo sahunsu"
"nufinki aure kikayi acan?"
Da sauri suhaima tace,
"Aure nayi,to mijina ne yasakeni shiyasa nadawo"
"tunda yasakekine to inga takardar sakin".
dayake da handbag dinta ta tafi ba musu,ta zuge ta ɗauko katin Atm se alokacin ta lura akwai wasu takardun kanana aciki ,duka ta ɗauko ta miƙawa Rabiu.
Amsa yayi yana dubawa,yana dariya,sannan yace.
"Suhaima ay wannan ba takaddun saki bane,takardun cire kuɗine akowacce ƙasa kake inkaje zaka cire kuɗin dake cikin asusun ajiyarka"
ido kawai suhaima take warewa,dan bata yarda da batun na rabiu ba.
ganin bata yarda bane yasa yace.
"kinga bari inbaki maganin kije kibashi,anjima inkina da lokaci inna tashi daga ayki,kizo muje kano a duba miki aga ko nawane aciki,da duk wani bayani zasuyi miki"
se yanzu hankalinta ya kwanta,dan ita lafiyar ɗanta yafi mata komai.
maganin yabata ta dawo gida,taba Abdurrahman,sannan taimusu wanka itama tayi,ta goyasu suka tafi tallah.
bayan ta dawone,taje gurin rabiu shima lokacin yatashi,dan haka a motarshi ya dauketa honda civic,suka nufi kano.
Tafiyar awa guda ce takaisu bakin wafer.
Da kyar suka samu suka samu wanda ze musu abinda yakawosu,baa sha wahala ba sabida a takardun harda pin number da accaunt no,dan haka,mutumin nagama dubawa ya ɗago yace musu.
"da akwai kuɗi aciki har kimanin naira miliyan dari dari"
"miliyan ɗari?"rabiu da suhaima suka haɗa baki gurin tambaya.
Tabbatar musu da hakan yayi.
suhaima sabuwar soyayyar mijintace takamata,wato yabatane dan beson tasha wahalar rayuws.
Dubu ɗari uku suhaima tasa aka ciro mata,sannan suka baro gurin.
Kasuwa tasa yakaita,nanfa ta dagargaji siyayya,tasu twins dinta,harda gidan sauro ta siya musu,da madara da cerelac,daduk wani nauin abinci na yara me gina jiki.
suturu kuwa tasiya musu su ba adadi,da pampers duk ta jidar musu,da takalma,da sabulan wanka dana gyara gashinsu,dayake gashi garesu sosai irin na larabawa.
seda takashe dubu ɗari biyu a siyayyarsu,sannan taba rabiu dubu talatin,se godiya yake mata,sabida yaji dadinsu.
haka suka kamo hanyar laminkwai,gab da magriba suka iso.
lantana na zaune se gani take ana shigo da kaya,har aka gama shigewa dasu ɗakin suhaiman.
wani baƙincikine yaziyarci zuciyarta,take tasha alwashin seta sace kayan.
Bata gama tunaninba,sega suhaima dame gyaran ƙofa,tasa yasakamata kuba a kofar,ta yadda duk balai bame shigar mata ɗaki.
shiga tayi ta ware komai,sannan ta kafa musu katifunsu da gidan sauronsu.
dubu ashirin ta ɗauka takaiwa maman hanne,sannan tamata bayanin komai,godiya taimata sosai gami da sa albarka.
a ƙofar gida tasamu mahaifinta,tamiƙs masa dubu arbain sannan tace masa.
"Baffa ka ɓoye kadunga cin abinci me kyau don Allah ko gobe suka kare kamin magana zan ƙara maka,kadena yiwa matarka biyayya sabida abun duniya kaji don Allah"
murnar da yayi bata da iyaka,dan azahirin gaskiya sabida kuɗi yake bin umarnin matarshi,dan yasamu nacin abinci.
Cikin kankanin lokaci,baffa ya sauya duk abinda yakeso yakeci,ba abinda yadameshi da girkin lantana.
su twins tuni sun fara iya zama,Abdurrahman dayake yafi ƙiriniya har yafara son yayi rarrafe.
Yanzu suhaima inzataje tallah se takaisu gurin maman hanne,dan bata dens tallan bane sabida masifar da lantana take zubawa mahaifinta.
sabida hankalin baffa ya kwantane yasa taci gaba da tallan.
ɗakinta kullum arufe yake ba damar lantana taimata sata.
kuɗinta insuka ƙare rabiu ne me zuwa ya ciromata wasu yakawo mata.
amanar rabiuce tasa suhaima ɗaukar miliyan guda tabashi,ya faɗaɗa chemis ɗinshi.
Watannin su twins bakwai suka fara rarrafe,abun gwanin shaawa.
*******
Saudiyya
Ba irin neman da baayiwa hajiya murja a riyad ba amman baa sameta ba hankalin shureim sosai yakara tashi,
hakanne yasa ya tuno da sabuwar dabarar dazatasa abarshi yatafi nigeria
Yau wani ɗan matashin yaƙi ya balle agidan sarki.
Shureim ne ɗauke da wuƙa a hannunshi,ze cakawa kanshi,idan baa barshi yatafi nigeria ba.
duk yadda sarki yaso ya ajiye wuƙar amman ina yaki,maimakon hakama har yafara yanka hannunshi jini na zuba,ya ɗaga ze caka acikinshi kenan,sarki yakwallah kara yana faɗin.
"na amince ka shirya katafi!!!!!"
da gudu ya wular da wukar yaje yarungume mahaifinshi yana kukan farinciki.
A Ranar ofishin jakadancin saudiyya dake nigeria suka bada sanarwar,zuwan ɗan sarkin saudiyya sarkin gobe da yardar Allah ze iso nigeria,.
Nan danan fadar shugaban kasa tafara shirin tarbarsa.
Shiko shureim da kyar ya amince se washe gari ze tafi,cikin dare gaba ɗaya angama haɗa komai na tafiyarshi kama daga escote dade sauransu.
washegari da misalin karfe goma na safe jirgin sama mallakin masarautar saudiyya,ya ɗaga da shureim da maƙarabansa,daga filin jirgin sama na garin zuwa kasar nigeria.
garin masoyi baya nisa.
muje [truncated by WhatsApp]
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Kungiyar matan aure na garin bauchi naga sakonku nagode sosai,Allah yasa ku ɗore da aywatar da abunda kuka fahimta a gidajenku,na Aure Ameen*
*dedicated to zahra bukar*
*49-50*
Gaba ɗaya titunan dake Abuja jamian tsarone ta ko ina,yayinda helicopters keta shawagi asama.
Ƙarfe biyar na yamma jirgin saudiyya ya sauka a airpot a Abuja.
Shureim ne yafara saukowa,sanye yake da farar jallabiya,ya ɗaura rawanin larabawa yayinda idonshi ke ɓoye cikin baƙin glass.
Tawagar shugaban ƙasace ta iso da sauri,shugaban ƙasa yatarbeshi,tare ds ambasadon saudiyya na nigeria.
Acikin tawagar shugaban ƙasa,Akwai minstan mata,hajiya salbiyya Adam itama taje tarbar shureim,Ministan kuɗi,Hassan Atk shima baa barshi abayaba,can daga gefe nahango tawagar ,Mufarka mata suma sunyo ƙungiya guda ƙarƙashin jagorancin admins ɗinsu,zinnira da Hameeda.
Kalli iya kallonka bazaka taɓa hango ƙarshen masoyan surbajo da suka cika airport din domin tarbo shureim ba.
Kai Abun rukuni rukuni ne,sanda shureim ya ɗags idonsa ya hangi yawan alumar Khaleesat hydar novels,kimanin mutum dubu sabain da uku,sunzo tarbarshi ay kawai se hawaye yafara zuba a idonshi,dan be taɓa tsammanin nigeria haka suke da karrama baƙiba,se yau.
Nanfa jamian tsaro suka kasa suka tsare suka hana kowa isa gareshi.
jerin gwanon motocine suka ɗaukesu zuwa vila,yayinda,Tafeesu novels,da m kaoje novels,da da da da da🤣suka mara musu baya da gudu.
Sabida cunkoson mutanene yasa motocin basa sauri,sun jima kamin suka samu suka isa vila.
Shureim da kyar yayi bacci washe gari ko,yace,anunamishi kano,danshi Azatonshi kusane daga inda yake.
Nande ya fayyacewa shugaban ƙasa abunda yakawoshi,sosai yatausaya masa,hakanne yasa shugaban ƙasa ya umurci minister yada labarai Hajiya Zahra Surbajo yace,tasa afara cigiyar suhaima ta kowacce kafa ta sadarwa,
Kwanaki uku aka kwashe ana sanarwa harda kyautar,kujerar makkah da maƙudan kuɗi gaduk wanda yasanar da ganin suhaima.
Shide shureim gani yake in aka kaishi kanon zefi ganinta da wuri,dan yariƙe sunan kanonne tun ranar da hajiya tabasu tarihinta.
har tsawon sati guda shuru kakeji.
Shureim duk yatashi hankalinsa.
Sabida yace a kano takene yasa aka fo tsaurara bincike abirni da kauyukan kanon.
********
Rabiune zaune A chemist ɗinshi yana duba marasa lafiya,yayinda gefe ɗaya kuma yake sauraron redio.
Wata murya yaji rangaɗeɗiya,tafara da cewa.
"Assalamu alaikum jamaa masu sauraro barkanmu da sake saduwa daku acikin shirinmu na filin cigiya da sanarwa,wanda ni Autar hajiya zan jagoranta,A shirin namu na yau zakuji kautukan da akasaka gaduk wand yanemo wata matashiyar budurwa me suna suhaima yar jahar kano,suhaimade ta baro saudiyyane a ranar........ Zuwa gida nigeria,suhaima farace me matsakaicin tsawo,sannan suhaima tana ɗauke da ciki a lokacin tahowar tata,ansaka kuɗi wuri na gugan wuri har naira miliyan goma,da kujerar makkah,ga duk wanda yabada sanarwar inda suhaima take,ga wanda Allah yasa yadace da ganinta,se ya tuntubi minister yada labarai akan nombobi kamar haka,08093235..🤣Allah yabada ikon ganinta akan lokaci Ameen".
jikin Rabiu har rawa yakeyi wajen zaro wayarshi a aljihu,gurin kwafe number,yana gamawa yayi dialing.
ba jimawa aka ɗauka,sabida dama layin sabo aka saka sabida hakan.
Nandanan Rabiu yashaida yasan inda take,batare da bata lokaciba yabada Address.
sallamar kowa yayi yanufi gidan su suhaima.
Ayko yaci saa tafito zata tafi tallah kenan.
cikin mutunci suka gaisa,sannan yace.
"Yau kinada babban baƙo,nikuma yau nayi byebye da talauci"yaƙarasa maganar yana dariya.
Itama dariyar tayi,sannan tace.
"wanne irin babban baƙo kuma rabiu?"
"nima wlh bansaniba ammande nasan tabbas yau zamuyi baƙi a garinnan"
"To Allah yasa baƙin na Alkhairine"
"Ameen,sannan yaude don Allah ki haƙura da zuwa tallan nan ni zan siye duka"
Dariya tayi ta ɗauka da wasa yake se gani tayi ya sauke abincin yafara bawa yara sadaka,yana gamawa,yaciro kuɗinta yabata.
Godiya tayimasa sosai,sannan ta koma cikin gida.
Lantana taji takaicin dawawor suhaima da wuri shiko baffs yaji daɗin hakan.
*********
Sanda labarin ganin suhaima ya isa fadar shugaban ƙasa shureim kafa ba takalmi yakwasa da gudu yafita waje dan ya ɗauka anzo da itane.
koda yaga babu ita ido kawai yake zarewa kowa se mamakin irin son da yake mata suke.
dakyar ya kimtsa,aka hsɗashi da jamian tsaro suka hau jirgi zuwa kano,daga kano gomnatin kano tashirya mishi motoci na alfarma,ana bugamasa jiniya,ƙarƙashin rakiyar minister yada labarai zahra surbajo,da shi kanshi gomnaɓ kanon,suka nufi garin lamin kwai.
muje zuwa.
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Wayyo masoyana kuyi haƙuri surbajo nasonku aduk inda kuke,nafeesa Abdullahi,baze yiwu surbajo tasa numberta a page ba sede ke ki rubuto taki kituro, da yardar Allah zata iso gareni,bama keba duk wani masoyina dayakeson hulɗa dani ya rubuto numbersa yaturo,zasu iso gareni kuma insha Allahu zan nemeku,banaki saka number na bane dan tsoroba kawai de dan jaddada tsarone nagode*
*dedicated to zahra bukar*
*51-52*
Duk inda suka wuce kallonsu akeyi,sabida motocine sunkai guda Ashirin jere akan titi.
Sannu a hankali suka iso garin na laminkwai,dan haka sauka sukayi akantiti,sukabi jar ƙasa zuwa cikin garin.
Wuyan shureim kamar ze tsinke sabida ƙara masa tsawo dayakeyi.
Yan garin sunga abun da basu taɓa ganiba,sabida suna hawa titin jar kasar lamin kwai ɗin,
Escote suka firfita daga motocinsu suna gudu aƙafa,motar da shureim yake ciki kuwa,escote ɗin larabawa kowa sanye da bakaken suit,fuska manne cikin bakin glass,kunne maƙale da bluethood,hannu ɗaya cikin riga riƙe da bindiga.
Wallahi koni tsarin yaminni.
Mutanan garin kiɗimewa sukayi,ganin fararen fata a ayarin tafiyarne,yasa alumar garin fara rawar murna.
Domin a tunaninsu man fetur ne a garin nasu,shine akazo a haƙo,yayinda wasu kuma tunaninsu yafi karkata akan service ne ya faɗo garin.
Hakanne yasa kowa ya shiga adduar Allah yasa agidansa ya faɗo.
acikin masu tunanin service ɗinne harda lantana,addua tayita ba adadi akan Allah yasa a gidansu ya faɗo.
Suna isa garin ƙofar gidan me gari suka tsaya,dama tuni rabiu yana binsu abaya.
me gari rawaninshi har yana faɗuwa sabida kiɗima,danshi azatonshi yan taadda aka gano a ƙauyen nasa.
Nan aka buɗew su Shureim ƙofa suka firfito,shureim kallon garin kawai yake yana mamakin ta yadda suhaima zata iya rayuwa acikinshi.
Number rabiu aka fara kira da sauri yafito tsakiyar filin,yana ɗaga hannunsa.
kofar fadar me gari kuwa tacika damƙam da mutane yan ganin kwakwaf su lantana ne agaba gaba,ta baro suhaima gadin gidan.
Shiko baffa bayanan yaje ɗaurin aure kwanar ɗangora,na yarinyar abokinshi.
Shureim ganin rabiu amatsayin wanda yasan inda suhaima take da sauri yakamosu ya riƙe yana tambayarshi tana ina.
Duk yadda akaso ya kwantar da hankalinshi abun yaci tura,dayake gurin akwai hayaniya shiyasa baa ji me suke faɗiba.
Ba musu Rabiu yamiƙe yayi gaba,su shureim suka mara masa baya,escote sojoji yan sanda,duk sun rufu akan shureim haka suka nufi gidan su suhaima aƙafa dayake ba nisa.
Suma zugar jamaar gari sesuka mara musu baya,dan gani karshen alewa.
Ay lantana tunda taga anyi hanyar gidansu ta runtuma da gudu har faɗuwa take tana tashi dan ita duk azatonta service ɗinne ya faɗo a gidan.
Har suka iso ƙofar gidan tun kan,ayi magana lantana ta ware murya tana faɗin.
"Allah mungodema service a gidanmu,to gaskiya mude ba siyar muku zamuyiba sede mubaku haya duk shekara"
ba wanda yabi ta kanta,Rabiu nashirin shiga gidan kiran suhaima se gata ta ɓullo daga wata kwana ta dawo daga gidan su hanne ɗebo shanyarta.
Shureim yatambaya to ina takw.
Rabiu cike da faraa yanuna masa suhaima dake tafiya kanta aƙasa burinta kawai ta shige gida,.
Ay ko acikin mayen giya inyaganta ze ganeta,da gudu yaje yasha gabanta escote nabinshi abaya,suhaima bata luraba sekawai jinta tayi aƙirjin mutum.
ƙamshin turarensane ya shaida mata ko waye ya rungumetan amman sabida ta tabbatar ne yasa ta ɗago idonta dan ganin shiɗinne ko kuwa.
Tana ɗago ido ta saukesu akan fuskar shureim dake zubar da kwallah,aruɗe take kallonshi,tana tunanin tayadda akayi yazo.
Kamin tayi wani yunƙuri se ganinshi tayi tsugune akan guiwarshi agabanta,ya haɗa tafin hannunshi guri guda yana kuka yana neman yafiyarta.
Jikintane yakama bari bakinta narawa sanda ta waiga taga dubban mutanen dake gurin,dansu yasmin tafeesu da sally da queen aeanah,da bilkisu u hamza,kan wata karamar katanga nahangosu suna kallon ikon Allah.
Suhaima tausayin shureim ne ya ziyarci zuciyarta,ganin yadda bedamu damasu kallonshiba,bedamu da matsayi da mukinsaba yazube akan jar ƙasa agabanta yana kuka.
itama tsugunawa tayi,ta haɗa goshinta da nashi suna kukan,a haka shureim yake neman gafarar ta kai kawai take ɗaga mishi alamun ta yafe mishi,sabida tsnanin murna jawota yayi jikinshi ya rungume yana kukan murna,a hankali yake shafo cikinta,jin hakan ne yasa ta fahimci cikin jikinta yake nema.
Hannunshi tajs suka shige cikin gidan.
wayyo lantana rasa abunyi tayi,har bigewa takeyi gurin bin bayansu zuwa cikin gidan.
Tawagar gomna fadar megari suka koma,suko sauran mutane so suke suji waye shureim agurin suhaima.
Ayko nafa rabiu yashiga masallaci yasa lasifika yana shaida musu mijin suhaima uban yayantane shureim,
lantana seda cikinta ya karta dan kiɗima.
Suhaima riƙe da shureim har zuwa ƙofar ɗakinta inda su twins ke zaune a tsakar ɗakin suna wasa da kayan wasansu.
suna zuwa taimasa nuni dasu.
Suko kamar sun sanshi atare dukansu suka rarrafo zuwa gareshi.
kallon suhaima yake yana kallonsu,jikinshi kamar mazari yazube aƙasa suka ƙaraso jikinshi.
rungumesu yayi ƙanƙam ajikinshi,sannan ya kife kanshi aƙasa yayiwa Allah sujjada,yana kuka yana fadin.
"Astagafiruka wa atubu ilaika ya ilahil alamin,"
kuka yake sosai a sujjadar,seda su twins suka fara kukan sungaji sannan ya ɗago.yana jijjigasu,suko se shafa bakinshi suke irin wasannan na yara.
Sumbatarsu kawai yake yana dariya.
lantanace tazo ta tsaya akan su ko kunya babu,ganin hakane yasa suhaima taja shureim suka shige cikin ɗakinta ta turo ƙofar,.
muje zuwa
In banga dogon comments ba anan zan tsaya
surbajo for life.
muje zuwa.
surbajo for life.
����������������
*KANO TO JIDDAH*
����������������
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*ATTENTION‼*
*DA WACCE TAYI DAME SHIRIN YI YANZU,SHARE NA HOTUNANA,WALLAHI DUKANKU BAN YAFEMUKU BA,INA ROKON ALLAH YA DORAMA DUK WANDA YAYI MASIFAR DATA FI KARFINSHI,SABIDA KUN CUTAR DANI CUTARWA MAFI MUNI,WALLAHI BANYAFE MUKU BA KUMA BAZAN TABA YAFEWA BA,ALLAH WADARAN MUNAFUKI ME FUSKA BIYU,KODA DAGA YANZU KUNDENA KARANTA LITTAFINA,ZAN MAIMAITA,ALLAH YA ISA BANYAFEBA,BURINKU BE CIKABA SABIDA SON DA MIJINA YAKEMIN BABU DIGON MUNAFUNCI ACIKI,NABARKU DA RABBUL ARSHIL AZIM,ALLAH KABIMIN HAKKINA��*
*dedicated to zahra bukar*
*53-54*
Wani bakin cikine ya tokari zuciyar lantana,
Memakon tabar gurin kujera tajawo ta zauna ta kasa kunne abakin kofar dan taji me zasuce.
Shiko shureim bin dakin kawai yake da kallo yana tunanin dkin kwanane koko dakin aje tarkace,kasa yin shuru yayi dubansa yakai gurin suhaima yace.
"Habibati me kukeyi anan bakya tsoron ginin ya fado akanku zaki barsu anan?"
Murmushi tayi sannan tace.
"wannan dakina kenan,tunda ka koreni acikinsa nake rayuwa,har zuwa sanda na haifi yayanka muka ci gaba da rayuwa tare aciki"
Ajiye su twins yayi ya jawota jikinshi ya rungume yana kuka,yana kar neman gafarar ta.
"hbibati ki yafeni,na cutar dake sosai wannan dakin da garin da jahar da kasar gaba daya basu dace dake ba,ko baki fadamin ba habibati jikinki ya nunamin kina cikin wahala da kunci na zamanki anan,ki gafarceni"
Itama kukan takeyi,suna rungume da juna,
Bakinciki karuwa yayi agurin lantana sabida abun da taso ji takasa jin sabida bada hausa suke .maganarba.
Su twins ganin iyayensu na kuka ne yas suma suka fashe da kukan.
Da sauri suka saki juna suka daukesu suna musu wasa.
Ranar gari ko ina yaɗauka suhaima mijinta yazo dan sarkin makkah.
koda tawagar gomna da minister suka buƙaci shureim yataho su tafi fafur yaki acewarshi,se ya ɗandana irin zaman da iyalinshi sukayi agarin.
Hakanne yasa aka baza jamian tsaro lungu da sako na garin,kofar gidan su suhaima ko cincirundon jamian tsarone.
Se da magriba baffa yashigo garin,ganin jamian tsaro ta koina har tsoratashi yayi,sanda ya iso kofar gidanshi ko ba karamin mamakine yakamashi ba,ganin an tsaidashi ana checking dinshi sekace barawo.
Seda suka gama bincikeshi tas sannan suka barshi yashiga cikin gidan.
A tsakar gida yasamu lantana,se safa da marwa takeyi.
Tana ganin shi tayi sauri ta nufeshi tana fadin.
"Gwanda da Allah yakawoka,to ga yarka nan da wani kato acikin daki suna iskanci,nayi nayi su bude kofar sunki"
Cike da mamaki yake kallonta,dan shi gaba daya kanshi ya kulle.
suhaima jin sallamar baffane yasa ta shaidawa shureim ga mahaifinta yadawo,dan haka buɗe kofar sukayi suka fito,gurinshi suka nufa.
Baffa ido kawai yake warewa na ganin balarabe a gidanshi,kallonshi yake kallo irin na kurullah,take ya hango kamannin Jikokinsa a fuskarsa,baki na rawa yace.
"suhaima ko baki faɗaminba wannan shine uban su yan biyu wanda yamiki cikinsu"
Cike da faraa tace.
"Baffa wannan shine babban dan sarkin saudiyya,kuma shine ake sa ran zamanshi sarkin kasar bayan mahaifinshi,aykatau naje gidansu,mahaifinsa ya haɗani aure da shi har muka smu cikin su twins,to wata yar rashin fahimtace ta shiga tsakanina dashi,shine dalilin dayasa nadawo gida,to gashi yazo nemana da kanshi yanzu"
"kan bura uba,wlh da sake,karya kike bakar munafuka,mu zaa munafunta,agidan ubanwa balarabe yake aurar bakar fata,ay dan sarki ko na lamin kwai ne yafi karfinki bare na kasar da babu irinta,kice kawai farkankine yayi kewarki yabiyo bayanki"cewar lantana tana wani jijjige jijjige
Akaro na farko da suhaima tayi shaawar ba lantana amsa,inda tace
"To ay dama lantana inkika dubi tsarina,shi kanshi dan sarkin laminkwai din yasan nafi karfinshi,ki dubeni da kyau ko amasarautar kano sede kaddara,dan srkin saudiyyan de shine daidai dani,kamar yadd kika gani,kuma koda ace farkanane shi,ay ina ga ya cancanci yabo tunda har yasan mutunci bariki ya iya biyoni har nan koda kuwa kowa be yaba masa ba kede yadace ki yabs,sabida ya nuna sanaarki tada tana da muhimmanci"
Lantana tsananin mamakin suhaimane ya hanata magana binta kawai take da ido.
Shureim gaida baffa yayi suhaimace ke fassara masa,cike da mutunta juna suka gaisa.
lantana dakinta tashige jiki a sanyaye dn bata taɓa tsammanin suhaima tasan ita tsihuwar karuwa bace,gaba daya ji tayi ta gama tozarta.
Se dare suka bar gurin baffa suka nufi ɗakin suhaima,shureim dama shi duk ya kosa subar gurin,sabida wasu kwari dasuke cizonsa dabesan kona meneneba(sauro)
suna shiga dakin pampers suhaima ta sauyawa su twins tasamusu over roll ta kwantar dasu akan katifunsu masu gidan sauro,dama tun suna gurin baffa suka fara jin bacci dan haka suna kwanciya baccinsu sukayi.
Shureim duk inda suhaima tayi binta yake da ido,wata zazzafar shaawartace ta kamashi,yakos yajita ajikinshi.
katifarta ta fara gyara musu tan ɗaura gidan sauro sabida sauro tagama daura gidan sauron kenan shureim yagaza hakura,ya jawota ta fado jikinshi.
kissing dinta yashiga yi kamar wani mayuwacin zaki,da kyar suhaima ta raba bakinsu tace tana haki.
"nanfa ba saudiyya bane,me kake shirin aykatawa,?"
idonshi a kankance yace.
"kusantarki nakeson yi,ko ku anan miji baya kusantar matarshi?"
murmushi tayi sannan tace.
"ba nufina kenanba nan toilet dinmu ba irin naku bane,ba lalle bane ka iya amfani dashi,kaga kuma inka kusanceni dole sekayi wanka"
ko tsaƴawa yagama saurarta beyiba ya sake manne bakinsu guri guda,sannu ahankali yake kissing dinta,har zuwa sanda ya rabasu da kayan jikinsu,abubuwan dayafi so sunanan yadda yabarsu dan haka su yadirarwa da matsa,
Rai da marmari anjima baa haduba,shiyada bidirin da ake acikin dakin,ya gagareni rubutawa.
sosai suka dirji junansu,cikin daren suhaima ta kunna risho ta dora musu ruwan wanka.
Daya tafasa ta sirka takaimusu toilet.
Shureim se a gurin wankanne yayi danasanin kusantarta,musamman idan ya daga idonsa yaga taurari da farin wata suna kallonshi yana kallonsu,ga wasu murguza murguzan beraye dake kai kawo cikin bayin,da badan tare suka shiga wankanba da wlh baze iyayiba.
A saudiyya shureim ne yakewa suhaima wanka kullum,to yaude shureim yakasa aykata hakan sabida tsoron berayen dake kai kawo,irace yau taimasa wankan dakyar yayi na tsarki suka fito.
Suna shiga ɗaki yadubeta yace.
"a irin wannan yanayin kike rayuwa,da naso na ramawa kura aniyarta nayi rayuwa tare daku anan,amman wlh yanzu bazan iyaba,rayuwar tayi muni da yawa,wlg idan nayi sati anan inaga zan iya mutuwa,kuma barinku kusake zama anan shima sabuwar cutarwace,don Allah kicewa su baffa su shirya cikin darennan gobe da safe,zamu wuce tare dasu gaba ɗaya,"
tsananin farinciki suhaima batasan sanda tayi wani ihu ta rungumeshi ba.
kayanta tasaka,sannan ta nufi dakin su bafɗa ta kwankwasa.
Baffane ya fito yana tambayarta lafiyade ko.
"baffa yace kushirya sabida da safe zamu wuce saudiyya gaba dayanmu"
Daga cikin naki murysr lantans najiyo tana fadin.
"mu shiryafa kikace,nufinki harda ni zaa tafi saudiyyar?"
"dukanmu zamu tafi"tabata amsa.
barin gurin tayi ta wuce dakinta,shiko baffa sabida murna ya gaza cewa komai.
Koda ta koma a zaune tasamu shureim yatasa su twins a gaba yana kallo.
Koda suhaima tace ya kwanta ki yayi,sabida aganinshi berayen nan zasu shigo dakin.
Daga shi har ita a zaune suka kwana rungume da juna.
0 comments:
Post a Comment