inaso inje ziyaran family na ne maybe nanda wata 4 kuma zanyi wata 1
Yazeed yace Allah ya kaimu nima next week zan tafi wani mission kuma zanyi Kamar 2-above month kamin na dawo
Mom tace toh Allah ya kaimu. Yazeed yace tare zaki tafi da Jamal kenan? mom tace eh,yace that's good daganan kowa ya kama harkansa
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮
Akwana atashi yaune yazeed zai tafi mission dinshi zakiyya tace baby inajin zan Komai aiki tunda kaga tafiya zakayi
Yazeed perfume ya fesa kamin ya tako Inda take ya zauna ya rike hannunta yace Ba Komai u can resume sannan ya danyi pecking lips dinta
Hararansa tayi tace kaga matsalarka kenan kai da an zauna ana magana sai ka fara canjawa jiya abu daya akayita yi amma baka gaji ba ni matsa Dan Allah ta fadi hakan tana dan turesa
Yace haba mine na bankwana fa zamuyi 2 months fa zanyi babu ke
Tace ni rabu dani bacci nakeji
Haka yazeed ya gama nacinsa amma zakiyya ta rufe idonta tace Sam
Dole ya hakura ya tafi tace Allah ya tura keya
Sannan ta kara lafewa acikin bargo ko wankan tsarki batayi ba sai bacci after 5 min ta zaburo a guje ta bude wani drawer ta dauko tabulet ta watsa kamin ta koma ta kwanta
馃崁yazeed kuwa direct dakin mom ya tafi ya sameta har lokacin tana kan sallayanta tana azkar Dan lokacin to 7 ne
Assalamu alaiki ya Ummi
Wa'alaika Assalam son,kaif asbahata ?
Asbahatu bikhairin,just came to to say bye to u
Take care of ur self u know that I will miss u ryt?
Yes mom I do
Matsowa kusa da ita yayi yayi hugging dinta tare da peck a goshi miyar masa tayi ya dago sai taga idonshi ya ciko da kwalla tace son when did u became a cry cry baby ne?
Murmushi yayi yace kawai zanyi missing dinki ne
Kumatunshi taja tace karka damu kaji ?just concentrate on ur mission
Okay kawai yace mata sannan ya fita
Jamal ne ya rakashi har airport akayi clearing dinsa jirginsu ya tashi by 8am on the dot.
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮
Akwana atashi yau yazeed zai dawo kuma saura 3 days adaura aurenshi da minal
Mom ta hadowa minal lefe na gani na fada tayi order from different countries; atamfofi,laces,material,jewellery,takalma,perfumes kayan kwalliya,inner wears etc
Abangaren su minal Komai ya kankama domin mom tace musu karsuyi kayan daki dakyar suka yarda amma dukda haka sukace zasuyi mata gara da show glass mom tace Ba matsala.
Minal ko gyara takesha sosai ta kara kyau sosai mom ma ta loda musu kudi tace idan Suna bukatan karu suyi magana
Dakyar tukun suka karba tare da yarjeniyan mom bazata kara kashe musu kudi Ba daga wannan.
馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁
Motoci ne Jere suka danno kai cikin jidmar mansion kamin suka tsaya yazeed ne ya fito ya kara kyau sosai yayi fari jikinnan sumulsumul
Ciki ya Shiga yayinda aka Parker motocin mom ne tayi masa sannu da zuwa tare da yaushe rabo kamin tace yaje yayi wanka sannan yaci abinci
Around 9 O'Clock Suna zaune a parlour mom tace yazeed yace yes mom ?
Tace akwai abinda nakesan fadama da fatan baz脿ka watsamin kasa a ido Ba
Yace mom kawai ki fadi magarnarki
Tace jibi za'a kawo Amarya gidannan
Amarya kuma?Jamal ne zaiyi aure?
Ah ah
To amaryan Waye?
Naka ne
Nawa?!mom kin manta I already married?
Nope,kasan Cewa zakiyya zabinka ne,kuma duk abinda kakeso nima inaso to shiyasa na yarda ka aureta Toh yanxu sai ka auri Wanda nakeso ko?
Amma mom kinsan banida burin kara aure?
Bata rai mom tayi tamike zata tafi yazeed yayi saurin rikota yace indai haka kikeso to na yarda
Murmushi mom tayi Allah ya maka albarka son
Ameen,amma mom wacece ita?
sunanta Amina Idan tazo zaka ganta
Karki damu sweetheart koma wacece ni zan aureta ai farin cikinki shine nawa kuma Ind.......
ME NAKEJI KAMAR MAGANAN AURE ACIKIN GIDANNAN?!
Kwass....kwass zakiyya ta shigo tana wani yatsine tana daga kofar hanci idonnan Kamar zai fado tsabar jaraba.
Zuwa tayi gaban yazeed tace to Baka isa Ba,Wlh yazeed baka isa ba kayi kadan kawai saboda ka kaskantar dani shine zaka wani ce zaka yi aure?ta fadi hakan Kamar zata makuro yazeed din
Mom kam batace kala ba kallonsu kawai take tana ganin ikon Allah na yadda zakiyya ke Abu Kamar Mara lafiya sannan kuma me yazeed zaiyi.
Yazeed bai nuna alamun ransa ya baci ba illa gyara tsayuwa da yayi hankali kwance yace kika ce ban isaba Toh ke a suwa? Ko ince why bazanyi aure ba馃槙?
Babu abinda zakiyya ta tsana Kamar tayi banbami taga be batawa mutum raiba
Sai tace tabdi jam eehh lallai why ma zaka ce?....to because I said so kanaji na ko yazeed? au Wai dama dagaske auren zakayi ? Wallahi za'a yi tashin hankali.
Kallonta yayi with an expression of I thought u don't care about me,all u care about is your boutique,boutique, boutique.
With a less concern yace eh aure zanyi jibi ma kuwa thank goodness kinzo a dai dai so no need to stress my self.
Tsalle ta daka tace wallahi ni zakkiya nafi karfin ayimin kishiya god forbid ai ba haka mukayi zaka kara aure ba....na haramta maka yin aure a gidannan yazeed da fatan kana jina?ta fadi haka tana zazzare ido tare da huhhura hanci Kamar maiya
Mom ne tayi carab tace
Hey...hey...hey kikace kin haramta masa?and who the hell do u think u are ?ke asuwa kunun bayan ludayi....just a zero behind a decimal point....ran mom yayi mugun baci
Iyee, its all my fault da bansani Anyi wajen dake Ba kamin a Shiga da ita, shiyasa kika sani bakin magana. Listen to me very attentively! Idan kika sake kikayi mana tashin hankali a gida ki tabbata zaman ki ya Kare. Banason in zama sanadin daba aure amma abin naki ya isa. Kin fara wuce gona da iri.
Yazeed ne ya riko mom yace calm down sweetheart bade aure bane Anyi angama karki damu kinsan I love u ko?muje dakikinki. Haka ya tisa mom a gaba har dakin ta. Tanaji Kamar ta yarfawa zakiyya tafi amma batason ta zubda girmanta.
Zaunar da ita yayi ya bata ruwa sannan yayi assuring dinta Cewa ba mai hanasa aure sai Allah daganan ya fita...
Zakiyya kuwa tasan ta tabo Dan yadda taga ran mom ya baci babu abinda zaihana tasa a saketa she must calm herself down. Taso tayi musu hauka amma bazata iyaba saboda tanason igiyan aurenta
Haka taje dakinta aguje tahau watsarda abubuwa tana fasawa hannunta na jini kamin ta fada kan gado ta fashe da wani matsanancin kuka.....
Yazeed ne ya turo kofan dakin ya shigo
Tasowa tayi attachment dinnan duk ya wargaje tana sending masa murderous glare ahankali yazo ya zauna akusa da ita being conscious with the glasses kar ya taka.
Hannunta ya riko ta warce ya kara rikowa zata warta ya rike gam yace haba my zakky uhm....yanxu shine kikaje kikayi fada da mum kinsan mahaifiyata ne tanada hakki akaina ya kikeson Nayi kinaso na haukace ne?
Rungumeta yayi kamin yaci gaba da fadin na dawo ko kiss ban damu sai kihau yima mahaifiyata fitsara kin kyauta kenan?a hankali ta girgiza kanta yace ai kinsan ko Nayi auren ke nakeso waccan zabin mom ne ko?ta gyada kai yace promise me zaki bawa mom hakuri tace on one condition idan kayi auren bazaka hada gado da matar ba yace ai wannan ko baki fadaba kinsan haka yake Insha Allah.
Tace to nima zan bada hakurin yace good daganan aka Shirya kuma akayi wani duniyar.
Jamal kam sune kirjin biki bai samu haduwa da yazeed ba sai Washe gari Inda za'akai lefe
Your one and only karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty馃挄
8 SEPTEMBER, 2019.
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 24*
Kamar yadda kuka sani yau za'a kawo lefen minal
gidansu ya cika taf da dangi,Yan uwa da abokan arziki kai har makiya ma sunzo domin asamu abin fadi acikin gari
Ana zazzaune akaji sallaman kawayen mom da aunties din yazeed sun iso firfitowa akayi ana musu maraba tare da shinfida musu dardumai
Gaggaisawa akayi da fara'a da mutunci Yan gulma da tsurku tundaga ganin masu kawo lefen sunsan minal ta cafka tayi sa'a zata Shiga gidan da akwai gida mai maiko
(Wannan yana daya daga cikin kuskuren da mutane keyi Suna ganin idan har ka auri me kudi ko me kyau Toh kayi sa'a saide abin Ba haka essential qualities da ake bukatan mutum ya lura dasu shine:
1.shin wannan mutumin ya kwantamin ?
2.shin yanada addini?
3.zai iya ciyaddani da halal?
4.shin 'ya'yana zasuyi alfari dashi amatsayin ubansu?
5.shin zasu gode min na zabanshi amatsayin baban su?
6.shin yanada akida mai karfi
7.is he loving and caring?
8.will always support me?
9.am I ready to live my whole life with him?
10.Does he respect my family
if those questions are satisfied then you are good to go,bawai idan ka auri mai kudi,handsome shine kayi sa'a Ba pls and pls Yan mata take note Ku core San duniya aranku Ku sank duk mijin da kika zaba Ba kanku kadai kika zabawa ba har da yaranku.Ku guji ranan da 'ya'yanku zasu kalleku suce muku kun cucesu kun zaba masu mafi munin uba.
Suma mazan idan kun aurensu zasusan Dan me kuka auresu Dan kudi ko Dan allah.
Shiyasa yanxu rate of zaurawa ke karuwa soboda tun kafin adaura aure an rusa ta an kasheta auren a mace tazo. AKIYAYE)
Abokan ya abubakar ne suka fara shigowa da akwatuna har aka Shiga da 6 akwai nasu Kate ba,7,8,9,10.........18 set uku kenan Wanda Duke da kalar fari,baki sai sky blue ga stones farare masu kyau ajikin ko wanne
Wasu set shida aka shigo dasu Wanda suke kalar brown guda 3 na inna,2 na baba sai 1 na kawayen Amarya
Kaya aka fara budewa hmm abin ba magana atamfofi 50,laces 30,material 25,an dinka goma goma atamfofi kuma ashirin ,English wears 25,Arabian gowns 30,sleeping dress 20,pants da bras dozen uku uku,takalma da jaka set 20,cosmetic traveling bag daya,gold jewellery 5 sets
Inna tace kayan sunyi yawa a rage Rabi sukace ah ah ai kaya sunzo in zasu koma to saide in ankawo amarya
Haka inna ma ta nasu tukuicin ban girma ;cin-cin,bakilawa,cake,doughnut, alkali,meat pie da samosa buckets buckets Wanda aunty fauzy ta bayar amatsayin gudun muwa sannan tahada musuda turaren wuta
Haka aka watse kowa yana farin ciki da annashuwa
THE WEDDING DAY
yazeed ne tsaye abakin mirrorn dakinshi zakiyya makale dashi tana wani shashshafa fuskanshi zuwa wuyanshi baby Wai da gaske auren zakayi,yace Toh zaky ba maganannan an gamata ba meye na dago da ita,zakiyya tace Toh naji amma kar ka manta kace bakasonta kuma bazaka hada gado da ita ba yace ina sane da wannan,happy now?tace yes
Fesa turare yayi kamin yayi mata peck a kumatu ya wuce
Zama tayi abakin gado tace koma wacece ke to kisani zaki kawo kanji cikin masifa ne Dan kishi dani sai an Shirya yanda ba'ayiwa uwata kishiyaba nima bazan zauna da ita ba馃槇
(Wannan banziyar akida ce mutum yace Wai Dan ba'ayiwa mahaifiyarsa kishiya ba shims ba'a masa ba karku manta Allah madaukakin sarki yace acikin suratun nisa'i
"Wa in kiftum all芒 tuksid没 fil yatam芒 fan kihu ma d'aba lakum minannisa'i masna wa sul芒sa war ba'a,fa'inkiftum all芒 ta'adil没 fa wahidatan au ma malakat aimanukum zalika adn芒 all芒 ta'ul没" 3:3
Allah madaukakin sarki ya umurci maza da su auri mata biyu,ko uku,ko hudu,idan bazasuyi adalci ba to su auri daya
Kinga da auren biyu ma aka fara kamin uku kamin 4 shikuma daya karshe
Kisani idan mijinki yace zaiyi aure kikayi adawa to kisani badashi kikeyi ba da Allah ne tunda Allah shi ya umarci ayi hakan
Dan Allah mata mu tashi munemi ilimi kuma muyi aiki dashi kodan gudun ranan da yayan mu zasu tambayemu Abu akan addini mutsaya muna zare ido mu Shiga kunya.
Ba'a tsufa ko girma daneman ilimi,idan bakusamu kunyi da yarinta ba lokaci bai kure ba tunda har yanxu kuna shan numfashi.
Kusaka yaran Ku amakaranta na boko da addini kodan suyi alfahari daku
Abin kunya ne ace Wai semi yar cikin Ku da Kanwarka bayanku ne zan Samar daku abinda ya dace.
Ku Duba abinda nake iya rubutawa?I am just 14 years, 11 months,20 days kuma ina university sannan na haddace takaddun addini turum. what do u expect idan nakai 18?what of 20? ba cika baki nake ba amma kuma kunsani akarancin shekarun da nake dashi inada tunanin manya.
Abin kunyane ace yar cikinki ko kanwar bayanki ta Fiki zurfin tunani.
Wani abin da ke bani haushi shine 'Yan mata masu shekaruna yanxu Kansu rawa yake,yanzu ne suke ganin Suma sun girma baza'a barsu a bayaba,Suna ganin sunyi boobs Kansu daya da uban kowa,basuda burin daya wuce ayi shigan tsiraici ana yawo a gari ana karya ka'ida da iyakar Allah,ana kara yada zina acikin alumma,tun daga fitanta har dawowanta mala'iku na tsine mata,manzon Allah ya tsine mata,bayin Allah salihai na tsine mata, ai tundaga nan ya kamata ta fahimci ta Shiga ukku,ta gama yawo ta lalace wallahi Mu kiyayi haduwar mu da Allah abin kunya ne kaje gaban Allah kana mai saba masa ka wulakanta a duniya ka wulakanta alahira.
Su mazan da suke ganinku suce u look breathtaking,u look sexy,u look hot ke tun daganan ansami matsala hot fa akace ba cool ba kinga ko anfada miki Inda mala'iku zasuyi dake ne in baki canja hali ba. Ancemiki zasu aureki ne ?babu mai aurenki lalataki zasuyi suyi gaba,wallahi ku ji kunyan randa zaku tsaya gaban Allah ana miki shari'ah keda iyayenki. Mu rufawa kanmu asiri mu nemi ilimi muyi aurenmu cikin rufin asiri har Allah ya karbi rayukan mu.)
Lovelies kuyi hakuri yau duk Mun kare a lecture wallahi rainane ya baci da abinda ke faruwa,duk mutane sun kwashe kayansu daga gaban annabi,amma karku damu I will make it up to you馃槈 Ku tayani da addu'a inada test guda biyu tomorrow masu zafi ne aradu; chemistry and Arabic thanks for your love
Your one and only favorite yobe girl,karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty馃挄
8 September,2019.
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 25*
An daura auren minal da yazeed akan sadaki naira dubu 50,Yan uwa da abokan arziki NATA taya murna makiya ma na hassada
Allah ka barmana makiyanmu kodan su zama dalilin da zamuyi nasara. Kai jama'a Imagine life without munafukai Allah barmana Ku Yan wuta馃槀
Mom ta aiko da kayan abinci da abubuwan da za'ayi walimah Dan babu wani event da za'ayi. Saboda abin yazo a kurarren lokaci ko mai wa'azi ba'a sami daman kira Ba.
Bayan la'asar akayi da mom Cewa za'a daukan minal around 5 pm inji ango(mom anya wannan magana kuwa zan yarda da ita?).
Hakan yasa aka fara shirya Amarya around 3:50 bayan Anyi sallar la'asar.
Liffaya mai kyau tasa wadda aka siyo mata awajen reemah's collection. Wani sarkan gold akasa mata Wanda yake na inna ne family necklace dinsu. Babbar ya ake bawa in za'a kaita dakin miji. Kuma ba'ayarda ka siyar Ba amma zaka iya upgrading.
Kyansa yananan Dan haka ba'amayi upgrading din Ba.
Dayawa daga cikin Yan makarantansu sunyi attending, ciki kuwa harda heedaya Muhammad da ma'ani yerima Wanda suke mutunci sosai.
Yan matan ne adakin minal yayinda aketa tsokananta itako sai cika take tana batsewa wai ita batason adinga zancen batsa a gefenta.
Hidaya ce tace Nide sake fuskannaki in gama kwalliyan yayinda ma'ani ke Cewa nikam yau sai na cika camera ta da hotuna, inajin ma inna sami dama zanje in karanta photography馃槈
Heedaya ne tace oh mude zamuzo muji ya aka Kare a Daren farko.
Harara minal ta ballo mata,aka fashe mata da dariya Ashe ta shaka,zaliha tace kai Ku rabu da ita bari ayi Daren farkon wannan Cuno bakin da take duk zata dena saide muga mutumiyar ka an zama miji dadi
Alamun zatayi kuka muryanta yayi tana Cewa wallahi zaliha karki bari na kamaki shegiya yar.....
Innace ta shigo tace inkika karasa sainaci ubanki.
Tunda ake hirar bansa baki Ba ina zaune a gefe ina typing a wattpad dina saboda kar ace na fiya rashin kunya sai alokacin na sako baki nace "assha!inna kin bata goma boyar bata gyaru ba in ita batayiba aike kinyi"
Dakuwa tayimin tace ingo naki yar jakan uban yarinya da baki cau cau Kamar babba kodan kinganki cikin Yan mata shiyasa kika falle ko?kinsa niqabi kamar da gaske ashe dai.......shegiya Da I damu Kamar na Yan chaina
Kafin ta karashe nayi Sauri nace wallahi Nide Ba yar China bace ina turo baki,aiko inna tayi kaina na fita a 360 har inacin karo da mutum Ashe ma sakina ce da habiba (from the nemesis of sakina)yi hakuri kawai nace kamin na 'buya a zaure ina haki sannan na sauke niqabi na,na saka gilashi na saboda naga alamun maza a waje.
Ciki su sakina suka Shiga aka gaggaisa kamin suka wuce domin mazajensu na jiransu.
Kanwar dad din yazeed aunty nafeesa da Umma habiba wadda take step paternal grandma ga聽 yazeed sai kuma aunty nina Kanwarka mom Wanda suka iso yau da safe sune sukazo daukan Amarya tare da motoci 3 kacal saboda basuso bidi'an tayi yawa
Aiko nan aka fara tashin hankali minal fa da taga da gaske tafiya za'ayi da ita kirjinta ya fara lugude duk dadin da takeji taji babu shi ya tafi kawai sai ta fara hawaye wiwi Ba magana nanfa聽 wattpad fans dinta sukayi CAA anata bata hakuri amma ina kukan karuwa yake tunba sanda sukayi sallama dasu inna Ba dasu baba da ya abubakar.
Inna da baba hawaye suke hankali kwance yayinda idanun yaya abubakar suka ciko da kwalla deeje Kam an jika gaban riga ma da hawaye da majina sai alokacin na lura da kwalliyar da tayi kominta yayi matching da kayanta hatta Jan baki da eye-shadow, da brows din duka blue ne. Abin dai sai kun gani. Nikam share kwallan da zai zubo min Nayi domin tausayi. Rabuwansu was heart touching haka aka kwashemu mu 10 aka kaimu gidan amarya.
Tundaga kofa akayi mana maraba,kai Mun sami tarba me kyau dakin zakiyya aka nuna mana muka kai minal Dan bada amana mu Yan mata 8 da tsofi 2.
Ba yabo ba fallasa ta karbemu. Amma ni dai hankalina bai kwanta ba kuma naga alamun hakan a fiskan wasu daga cikin mu amma dai sai Nayi shiru. Kar aji mutuwan sarki a bakina.
nuna mana dakin minal akayi Wanda yake part din baki ne na sama kuma acikin sashin zakiyya yake ada amma an daba kuma an gyarashi kai ya hadu. Allah dai ya kyauta ya Kare Daga sharrin makiya
Aikuwa hidaya ta cika alkawari Dan photo kam gida yashashi har minal dinma sanda akayi mata pic amma sanda ta sake ado tukunnan.
Haka dai har dare yayi munata shewa da tadi kamin aunty Nina ta shigo tace mana motocin tafiya najiran mu haka Muka tattari kafufun muka tafi minal Kam kukanta ta bude sabon shafi Dan ta manta da Cewa ita daya zamu bari(saima ankai mutum kabari zai San kadaici. Allah dai yasa muyi dariya a kaburburanmu.).
Hmm ai batamasan gidan wa aka kawota Ba saboda kanta na cikin gyale har muka kaita daki kuma ai batasan yazeed Nada mata Ba kuma bata tbna Shiga side din zakiyya Ba Dan haka bata gano ba.
Lokacin ko da akayi musu maraba kuka take ga hayaniya Dan haka bata gane muryan mom ba.
Aunty nafeesa da mom ne suka shigo,mom tayi Sauri taje wajen minal yayinda ta dago chin dinta tana mai Cewa " 'yata me ya sameki?"
Kuka minal ta kara fashewa dashi ta rungume mom Dan ta dauka mom tayi attending bikin ne
Tace "mom Ashe an gayyaceki?mom Dan Allah karki tafi ki barni kamar yadda su zaliha da untichlobanty da ma'ani da nasreen da hidaya da..."
Ya isa bazan tafi in barki ba mom ta fada hakan tana me daurewan kai ?kode batasan wa ta aura ba?kai maybe de tsoro takeji saboda first encounter dinta da yazeed wasn't good.
Shafa bayanta mom聽 tayi tana bata soothing words har tayi shiru tana shessheka (sobs).
Kinyi sallahn Isha'i ? mom ta tambayeta tace a ah. Mom tace to tashi kije Kiyi kinji
Shiga toilet din tayi taga irin na wannan dakin da aka kaita ne sansadowa tayi kamar barauniya Wai Dan kar fanfo din yaji motsinta ya bachi da gangan har zatakai hannu ta bude saide ta fasa
Fanfon dake jikin toilet irin na tsarkinnan tace ta matsa tayi alwalanta Dan akwai irinsa a gidan aunty fauxy so ta iya aiki dashi har wani smiling take irin itama ta Waye dinnan.
After tayi alwalan bata mayar da dankwalinta ba ta fito Dan ta manta da cewa ma su mom sunanan
Smiling suka mata ta miyar musu kafin mom tayi introducing mata aunty nafeesa sannan ta tada sallah
Aunty nafeesa Kam yaba Kyan聽 minal take tunba gashinba shi yafi dauke mata ido.
After ta idar mom ta zaunar da ita ta mata wa'azi ya tsumata sosai.
Abinda ta fada last ne yasa minal shock.
"Daughter Dan Allah ki rikemin Dana dakyau kuma iyayi miki wani Abu ki sanar dani"
"Kina nufin oga sir?"minal ta tambaya hankali tashe.
"Kwarai shi"mom ta bata amsa. Atake minal ta.........
Yey! Alhamdulillah馃拑馃帄馃帀馃巻 is my birthday your girl is finally 15years old 馃拑馃徏馃拑馃徏馃拑馃徏
love you all馃槝
Karamarsu babbarsu ce
Miss untichlobanty馃挄
*18TH SEPTEMBER,2019.*
[1/11, 1:53 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 26*
INTRODUCING NEW CHARACTERS SAFWAN AND SAHIR
Sahir and safwan 'ya'yan yayar zakiyya ce Wanda ta rasu two years ago ana kiransu sahboy and safboy tashin turaine su. An dawo dasu wajen zakiyya ne last two month acewar mamanta Wai idan yazeed bashida matsala to su zauna awajenta tunda babansu irin sugar daddy dinnanne dama dan kudi yayar ta auresa kuma sanda sukayi sharadi inta sake ta haihu tofa yaran nata ne shi babu ruwanshi Dan baya bukatan yara.
To ta haifi sahir (6 years old) and safwan (4 years old).
Yaran are very sweet kuma sun saba da zakiyya Kamar mamansu adan zamansu tare tunda dama Ba aiki take zuwa yanxu Ba kuma already sun saba kawai shakuwa suka karayi.
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
Atake minal ta sauke wani ajiyar zuciya aranta tace na Shiga ukku na lalace, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un sunana聽 death.
Da badan tana cikin matsala Ba da tayi smiling domin ta fadi kalmar death daidai
Bude baki tayi zatayi magana kawai sai taji ta kasa Cewa Komai sai hawaye mom kuwa bata kawo Komai a ranta Ba ta dauka minal tana kukan yadda dare daya Allah ya sauya rayuwanta ne(eh tabbas sauyin Shiga tashin hankali ba).
Mom tace bari inje intaho da angon naki Dan Nasan yanxu haka yana hanya idanma be karaso Ba kenan.
馃尮
Abangaren yazeed kuwa tun kayanshi na daurin aure ne ajikinshi dama shadda ne fari kal.
Yana shigowa gidan side din matarsa(I think yanxu matansa zance) ya nufa dama haka yakeyi tunda suka Shirya da zakiyya inya dawo sai yaje ya taho da ita dakinsa wataran idan a sama yazo ma to Anan za'a yada zango. Watarana kuma ya samota already a dakinsa.
Yana shigowa ya kalli right dinsa wani iri yaji aransa Wai yanxu matarsa ne a part dinnan left dinshi yayi ya tura kofan dakin zakiyya gaji abude.......
馃尮zakiyya tayi wa Kanta alkawari bazata biyewa yarinyar (Kamar yadda taji su mom sunce)da za'a kawo mata Ba tunda ma mijin nata bayaso ai yazo da sauki.
Sanda taji guda an shigo da Amarya wani ras ras ras ras gabanta yakeyi amma sai ta matse koda aka shigo da Amarya wajenta wani daci taji ya tsaya mata,tanaso tayi musu wulakanci amma su untichlobanty su hidaya su zasmeen su walia sun mata kwarjini.
Haka suka gaisa sama kamin suka fita itade idonta akan minal tanaso taga ma Wai wacece wannan yarinyar.
Koda suka fita wani Abu taji ya tsaya mata a wuya batasan sanda ta fashe da kuka ba kukanta take hankali tashe Wai yau ita zakiyya akayi wa kishiya da wani ido zata kalli mutane danma ita bamai kawaye bace saboda jiji dakanta.
Sahir da safwan kuwa na dakinsu.
Turo kofar dakinta taji Anyi tace Waye?yazeed ne ya shigo ta rungumeshi tare da fashewa da kuka. Sanda tayi shiru yace ina boys dina? Tace Suna dakinsu peck ya mata a kumatu yace taje ta kwanta sannan ya juya zai fita zuwa tayi ta tsaya a gabansa ta rike hannunsa "da fatan Ba dakin ta zaka kwana Ba?" Zame hannunsa yayi a hankali yace no dakina zanje na gaji sosai.
kansa ke masa ciwo Kamar zai fita kallansa tayi suspiciously tace are you sure ? Ya gyada mata kai tace ko inzo mu kwanane kasan ina tsoran rananda da zaka kwana da yarinyannan zan iya mutuwa saboda kishi
Ransa ne yabaci yace haba zakkya why are you acting like this kinsan fa aurennan mom ce ta.....
Fuck you yazeed! You are so fucking annoying i hate you just leave. Ta fada tare聽 fashewa da kuka Dan gani take yazeed a dakin minal zai kwana
Baice mata kala Ba Dan yanxu shi yana rasa meke damunsa Dan haka yabar mata dakin.
Sai alokacin taji wani irin saita daura aniyan zata bashi hakuri da safe.
Dakinsa ya Shiga zai fara rage kayan jikinsa saiga mom Tisa kyayarsa tayi har dakin minal dukda ko baiso hakan Ba amma shima he is curious yasan wa aka aura mass Dan yaga mom na rawan kafa akan amaryar.
Salamu alaikum suka fadi in unison yayinda mom da yazeed suka shigo dakin minal. Aunty nafeesa na zaune agefenta daga alamu nasiha take mata.
Tanajin sallamarsu ta sauke Kanta kasa kirjinta na lugude duk ta tsure cikinta ya kada.
Wa'azi sosai aunty nafeesa tayi musu harda kuka wajen bashi amana kamin ta kara yiwa minal nasiha sannan ta fita domin take ta kwanta Dan jirgin bakwai zatabi ta koma gida yayinda su mom zasubi na karfe ukun dare ita da Yan uwanta domi zuwa gida Kamar yadda tace(amma intention dinta shine ta basu Fili su wala tunda yayi sabuwar Amarya kuma bata bada ranan dawowa Ba.
Mom ne ta dafa minal tace yata ki dago da kanki kinga ni Kamar mahaifiya make awajen ki Dan haka babu wani batun kunya kinji?tsoro ne yadada balbale minal zuciyanta na dukan Tara tara yayinda captain yazeed Dada sa hankali ya zuba idanu Dan yaga face din new bride dinsa.
Shahada minal tayi ta dago fiskanta aiko stake captain yazeed ya sankare
Out of all Yan mata mom ta rasa Wanda zata aura masa sai barauniya?maybe Ba barauniya bace har leken asiri ce ko kuma ............. WAIT!so now he get it wato ta biyoshi ne last time dan taga yaya yake Dan tasamu yanda zata shigo life dinsa Gaskiya tayi making a huge mistake hmm he will deal with her
Kallon mom yayi ya mata godiya sannan yace Allah ya basu zaman lafiya tayi hakuri da abinda yayi mata. Kamar da gaske
Minal har hankalinta ya fara kwanciya tadauka an wuce shafin batasan ko bude littafin ba'ayiba.
Mom taji dadi sosai sannan ta sanar da minal Cewa yau ne tafiyanta sannan ta fita ta basu wajen domin komawa side din ta Dan agajiye take sosai.
Tana fita yazeed ma ya fito bayan yayi wa minal wani dangerous kallo yace Allah gaji kanki. Run daganan tasan ta Shiga ukku.
motansa yahau ya Shiga gari kawai ya samu wani ice cream palace ya zaun plan kawai yake nema yanda zaici ub*n minal Ba tare da mom ta gane ba. Lokacin rufewa ne yayi masu wurin suka masa magana kamin ya fita.
Daidai ya tsaida motansa a cikin gida idea ta fado masa murmushi yayi tareda danna kai cikin gidan.
Minal kam sanda ya fita aranta tace kai wannan oga sir din Anyi masifaffe ni inyazo ma wulakanci zan kafta mai. Wani zuciyan yace dubeki saikace zaki iya tuno kallon daya mata kamin ya fita tayi atake ta tsure ta kidime yanxu ya zatayi gashi mom zata tafi ta barta waiyo Allah.
Kwanciya tayi abinta sanye da kayan jikinta gyalenta kawai ta cire kamin tayi baje baje atsakiyar gado tana yaba laushin katifar. Allah sarki har tayi missing din tsohuwar gadonta da yar karama da katifarta.
Around 1 yazeed din ya dawo so direct ya shigo dakin minal domin aiwatar da aniyarsa kallonta ya tsayayi yana yaba kyanta.
Aranshi yace mutum ga kyau amma Ba hali money monger
Concentrate yazeed Karka bari kyanta ya rude ka idan Ba haka Ba bazaka iya cin ub*nta Ba聽
Alokacin minal ta Dade da Shiga duniyar mafarki Wai tana baccinnan yazeed yazo ya caka mata wuka sannan ya binne gawanta a bayan gidan.
Wani wawan juyi minal tayi acikin baccin dama ita A ne wajen style din bacci ta iyasu kala kala dankwalinta ne ya zame gashinta ya bude dama ta cire ribbon din sanda zatayi alwala
Tsaki yayi aransa yace mata halinsu daya ka Duba iyayenta basuda karfi sosai amma sanda tasa wig mai tsada. Ko ina ta sami kudin? Wata zuciyarsa ce tace masa ka manta barauniya ce ko yar 419?
Bubbuga gadon yayi fiskansa babu alamun wasa domin ya daura aniya kuma sai yayi.......
Toh fa ko menene aniyan yazeed? Fans me kuke gani yazeed zaiyi?don't forget to vote and comment your ra'ayoyi.
Miss untichlobanty馃挄
23rd September, 2019.
[1/11, 1:54 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮@mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 27*
Juyi minal tayi tace inna bacci,Wai har asuban yayi ne?
Haushi abin yabawa yazeed hakan yasa ya wantsalar da pillow din da take kai,aiki babu shiri ta mike ganin shine yasa taji wani faduwar gaba yazo mata
Tunda take arayuwarta bata tana jin faduwar gaba irin wannan Ba kuma bata taba jin tsoran wani Kamar yadda tsoron yazeed ya shigeta a yanxu Ba.
Wani irin kwarjini yayi Wanda tayi nadamar kallon idanunsa domin kuwa ko lokacin da suka fara haduwa bata kallesa da kyau Ba
Wani kirma jikinta ya fara ta fara karkarwa Kamar mejin sanyi.
A hankali muryatta Kamar zatayi kuka tace sannu da zuwa.
Wani kallo yazeed ya mata Wanda yasa hanjin cinkinta kadawa kamin yace uban Waye yabaki izinin kwanciya akan gadonnan? Wato anzo ansami banza ko shine kikayi yi relaxing kina bacci ?
Da izinin wa kikayi bacci? Tayi shiru...
Bakida kunnene ko yaya?muryanta na rawa idanunta ya cicciko da hawaye tace kayi hakuri yace will get down zaki sauko ko saina taka ruwan cikinki?
Babu bata lokaci ta diro saga kan gadon yayinda tayi kneel down run kafin a bata umarni yazeed ko Ba tare da ya kalli inda take聽 Ba ya taka ahankali cikin takunsa na kasaita da isa amma cikin kuzari Wanda zai nuna maka Cewa shidin wani jarumi ne kuma namijin duniya
Har izuwa bakin gadon ya isa sannan ya zauna ya cire hularsa me mugun kyau da tsada sannan ya ajiyeta a gefe
Dago kansa yayi yanaso ya karewa minal kallo amma hakan ya gagara sabida kirjinsa dake bugamasa da Sauri da Sauri amma dai baikai na minal Ba sai ya dauki hakan amatsayin baccin rai聽聽
Dan haka sai ya jingina Kansas da allon gadon yana mai lumshe idanu Kamar yadda yayi scan baya sanda ya fara haduwa da ita a gidansa.
Minal ko gabadaya jikinta yayi sanyi,ta sadakar Dan ita a ganinta Allah ne yake ramawa mutane irin tsiyar data musu sanda take gida.
Tayi tsuru tsuru da ido Kamar Mara Gaskiya,gabadaya jikinta ya jike da gumi ga wani fitsari ga zazzabi ya sauko mata tsabar rudewa.
Dukkanin shikashikan tashin hankali ta cikashi a halin domin ko hawaye sun Dade da fara safa da marwa a kumatunta bakinta ko yayi mata nawi ko hakurin ma takasa badawa sai tsilla ido take tana kallon kafafunsa Wanda Duke dake da Zara zaran yatsu da kuma gashi kwance luf luf akai.
Sanda suka dauki kusan minti goma a haka kamin yazeed yace sannuki da zuwa cikin masifa da bala'i hade da tashin hankali.
Minal Kam ta kasa dabbaka Komai Dan ita ko a film bata tana ganin irin yanayin聽 da tashiga Ba ganin take ko yaushe ma ziciyarta zai iya bugawa ta mutu zaboda yadda yake bugawa har cikin dodan kunnenta takeji
Abubuwa dayawa ke yawo azuciyar yazeed Wanda yana fahimtar wasu,Wasu kuma baya fahimtar su
Ba tare da buds idanunsa Ba yace kinsan ni soja ne jarumi kuma naga alamun kinason zama dani,kuma kinsan jarumi sai jaruma,Dan haka kamin infara considering dinki a matsayin matata sai kin cika wa dannan sharudan
Shiru ne ya biyo baya kamin yazeed yace ;
Na farko daga yau ke zakinayin dukkanin shara,moping,dusting, wanke-wanke,inkika saba wadannan to zan hada mini da wankin mota da safe sukuma masu aikin zasuyi girki da sauransu da yamma kuma zakiyi sharan bangarena sannan zaki dafa abinci kuma ni Vance ki kawomin jagwalgwalonki Ba.
Na biyu karki sake koda wasa ki na ganki a Inda nake domin ganin fuskarki kadai nakanji Kamar zanyi amai
Na uku abinda nace kiyi agidannan su kadai zakiyi idan kina neman izinin yin wani abu to ki rubuta a paper ki ajiyemin ka kibi duk umarnin da matata zata baki saboda marabarki da yar aiki shine darajar mom
Na hudu karki sake mahaifiyata tasan da wannan maganar idan Ba haka Ba to kin kusa ki bakunci barzahu
Hope kin gane ta gyada masa kai yace bakida bakine
Tace na gane
Yace good idan kinbi wannan dokokinn to zaki zauna lafiya amma idan kika saba to kema kinsan sauran.
Sannan ban yarda ki kwanta akan gadonnan Ba harsai naga how serious are
Itade taji bazata kwanta a gadon Ba sauran kuwa to kunde San sauran .
A hankali ta bude bakinta tace oga sir Dan Allah idan na cika sharudanka zaka sakeni yayi shiru kamin yace hakan ya ta allaka da yanayin biyayyarki may be in sakeki
Yana gama fadan haka ya tashi ya fice wani nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin numfashinta Wanda bata masan ta rikeshi Ba sannan ta goge hawayenta sannan tadau bargo ta Komai kan kujera ta kwanta tare da rufe kafafunta
Yazeed kuwa yana komawa dakinshi yayi wanka tare da brush sannan ya fito dressing room dinshi ya Shiga ya dauko pyjama dinshi blue tare da Rigan ya saka sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana mai lissafi yanda rayuwa ta kasance masa
Hakadai bashi yayi bacci Ba sai wuraren asuba koda ya tashin sallahn asuba Kansa yayi masa mugun nauyi hakadai ya daddafa yayi sallh yayi azkar yau ko karatun Qur'ani bai samu yayi Ba ya koma bacci. Dama Ba kullum yakeyi saboda yanayin life.
Minal ko tunda tayi asuba taje kitchen ta nemi kayan aiki aiko batasha wahala Ba ta samu ta kama aikintakarfe 8 cif saiga su atine da su larai sun shigo sukaga babu kayan aikinsu parlour suka leko jin motsin mutum aciki aiko聽 da gudu gudu Sauri Sauri suka karaso
Atine tace Allah sarki yar uwa yaushe Rabin da mu ganki ziyara kika kawo manane ko wajen hajiya kikazo kika bage da aiki saide kash hajiya ma jiya da daddare tabar kasan itada danginta kinsan fa mai gidan ya karo aure
Duka atinen ta fada a numfashi daya zuwa biyu Asabe ta kara da ya karo wulakanci Ba larai tace baza'aji mutuwar sarki abakina Ba
Minal ko murmushi take tana binsu da idanu Dan batada abin Cewa
Aikin sukayi kokarin karba minal tace ah ah sukace to shikenan suyi tare kamin ta yarda amma dukda haka tana tsoran kar yazeed ya ganosu聽
Su kuwa sai hira suke mata yarda tambayarta ko zata kwana musu Dan sunaso suyi kawance da ita tace musu ai Ba kwana Ba kwanaki ma zanyi ta fadi haka tana bawa kwanakin karfi, aiko sunji dadi Dan su nasu gane me take nufi ba
kafin karfe 10 sun gama Komai saura part din yazeed Wanda dama tunda basu ke gyarawa Ba lukman ne kuma yazeed yayi masa message Cewa Ba sai yazo Ba.
Su atine sai janta suke da hira tun tana nokewa har ta saki jikinta sumo abin ya musu dadi, binta tace ni wallahi na kosa naga amaryar Allah dai yasa Ba irin madam zakiyya bace
Atine tace yo imma batada mutunci ai ita ya shafa minal de tayi tsit tana jinsu
Minal tace to ita bari taje sama tayi wanka larai tace Wai ko kema bikin kikazo ne naji kina Cewa bari kije sama kiyi wanka ? Rasa amsar da zata nasu tayi sai atine tace kinada kayan sawa?
Binta tace ki wani tambaya dole da kayanta zata zo mana
Minal tacewa atine Dan Allah kinga rabu dasu zo Kiyi mini wani taimako
Sukace to sai kun dawo kamin su minal suka wuce dakinta ta cire hijabinta sannan ta kalli atine
Atine ko zare idanu takeyi domin in batayi kuskure Ba nanne dakin da aka kawo Amarya
Minal tace kinga kwantar da hankalinki nice amaryar ni zoki nuna mini Inda zan sami kayan sawa
Atine ta zaro ido tace Kece ME?
Minal tace kinga shiyasa ma ban dadi muku Ba saboda ban Shirya yin bayaniba zoni ki nuna Mani
Nuna mata dakin dressing atine tayi da yadda zata canja combination din saga 00000 sannan mata na toilet ma
Kamin ta fita tana mamaki da kuma al'ajabi minal kam wanka tayi sannan ta koma parlour jin shiru yazeed bai fita Ba yasa tace kika ma ya five run asuba idan Ba haka Ba ya za'ayi ace mutum yana bacci har 12.
Alokacin data koma kitchen domin dauko su tsintsiya su atine na kitchen din Suna cin abinci Suna ganinta sukayi caaa Wai meyasa bata fada musu akwai chemistry a tsakaninsu da oga sir Ba ?Wai kuma me yasa oga sir ya mata abinda ya mata kaman wata 3 zuwa 4 da suka wuce?
Murmushi tayi tare da tabe baki tace sirrin ne
Daukar tsintsiyarta da packer tayi ta wuce side din yazeed
Kirjinta ne ya fara tsinkewa karfa yaje yananan,hakan yasa ta fara sanda Kamar Mara Gaskiya sannan a hankali ta bude kofar da take ganin side dinshi ne tunda de tasan na mom
Leko kanta tayi taga..........
Me tagani?
Uhm kun ganni all of the sudden ko?ai bazan iya babu Ku bane kun zama wani bangare na life dina.
Ina sonku sosai fans dina馃槝
Don't forget to vote,share and comment
Miss untichlobanty馃挄
4th October, 2019
[1/11, 1:54 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
*CHAPTER 28*
Leko kanta tayi taga wani tsararren parlour wanda bata taba ganin irinsa Ba
Ko babban parlourn dake gidan taga baikai wannan kyauba dukda ko wannan din Ba wani girma bane dashi na hauka amma ya hadu
Kamshin daya bigi hancinta ne yasata dawowa saga tunanin data Shiga ga wani AC daya bugota har yanasa tsulan cikinta tashi
Shahada tayi ta Shiga da yar karamar sallamarta Wanda ko ita kanta bata jishi dakyau Ba
Sanyi ne sosai a parlourn Dan har tadan soma rawar dari a kasan ranta tace kaji daki sai kace cikin fridge Allah yaso da hijabi nazo....
Kalle kallenta tayi kamin ta soma abinda ya kawota
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
Yazeed kuwa tunda ya Komai bacci bashi ya tashi Ba sai around 12:00pm
A yangance ya tashi daga kan gadon nasa ya sauka Kamar bayason jikinsa ya rabu da lallausar katifar
Bandakinsa ya bude Wanda yaje tsaf Kamar Ba namiji ke amfani dashi ba, wanka yayi kamin yafito ya shafa mai yana tunanin yadda rayuwa ta juye masa
Wai yanxu shine yake da mata biyu,Wai jiya shi aka kawowa amarya kuma ma shi Ba wannan ke damunsa Ba
Ace mom ta rasa Wanda za'a aura masa kar fadin duniya sai wannan yarinya,wannan fitsararriyar,wannan gold digger din.
Hmmm nannauyan ajiyan zuciya ya ajiye sannan ya fara shafa wani mai me kamshi ajikinsa a hankali Kamar bayason ya shafa.
Daga mutum ya gansa yasan Cewa lallai wani Abu na damunsa dukda ko hakan bai yiwa kyawunsa wani lahani ko sauyi Ba
Ahankali ya tashi yana tafiya Kamar bayason yayi tafiyar,Ahankali ya Daga Zara zaran yatsunsa Wanda ke dake da fararen nails ya danna pin din dressing room dinshi ya Shiga sannan ya tsaya agaban wata kofa na glass a hankali ya bude sannan ya dauko wani gray hoodie tare da black three quarter.
Drawan under wears dinshi ya bude sannan ya dauko gajeran wando amma banda singlet jin Kamar motsi a part dinshi yasa ya leko
Amma baiga kowaba hakan yasa ya koma ya sanya kayansa cikin nutsuwa
A hankali yaji kamar an bude kofan dakinsa Dan haka ya kara lekowa domin ganin Waye Ba tare da dauko socks din dayayi niyya Ba.
Stake Dan guntun annuri dake tattare dashi ta dauke. Minal ya gani tana leken dakin domin tabbatar da Cewa bayanan ajiyan zuciya ta sauke tare da shigowa da Dan karfin guiwanta amma Ba a rashin nutsuwa Ba.
Baice mata kala Ba itama bata lura dashi ba domin kuwa idanunta ta ware bil hakki da gaskiya tana basu abinci
Jingina yayi a bakin kofar da yake sada dakinshi da dressing room din yana kallonta kawai yama rasa mai zaice ko yayi mata
Sanda ta karewa dakin kallon tas tanata murmushi Kamar wata shashasha
A hankali ta tube hijabin dake jikinta tayi wulli dashi kan stool din dake gaban mirror Wanda tayi nadamar yin hakan domin atake wani sanyi ne ya daketa Wanda har yafi na falon hakan yasa tadan shafa jikinta
Wannan hali nata tunba yauba inna ke fama da ita na cillar da hijabi ta ko'ina Ba tare data ninke Ba acewar inna wata rana Zara wulla kan Dan aljani
A hankali ta karaso izuwa bakin gadon sannan ahankali ta janyo bargon dake kan gadon kamshin yazeed ne ya daki kofar hancinta Wanda yasata lumshe idanu tare da kara bude kofofin hanci domin ta shaki kamshi
Wani Abu taji yana mata yawo ajiki amma ta share Dan a halin yanxu bata bukatan wani distraction
Abangaren yazeed kuwa kallonta ma kawai yake takaici ya cika masa zuciya Kamar ya mata suka ya rasa yadda zaiyi
Wani karago ne ya tsaya masa a makokoro flinching and unflinching fist dinsa kawai saiya Komai cikin dressing room din nasa
Minal ko ninke bargon tayi sannan ta ajiye badan ranta yaso Ba sai Dan kada hawan jini yazo ya tarar da ita a dakinsa (aikin gama ya gama)
Gadon ta fara gyarawa sanda ta gyara tsaf sannan ta kalli gadon gaji batada burin dayawuce ta kwanta akai
Kunji mutuniyar Ku fa na dakinta ma anhanata hawa balle na oga kwatakwata
Aiko kankace me,saiga minal ta tsuguna a gefen gadon sannan ta daura fuskanta akai tanashafa gadon da hannunta mai dauke da baby fingers masu tayi da laushi Wanda suka sha lallen amarci
A hankali ta mike sannan tayi abinda ya kawota dukda Cewa dakinnasa Ba wani datti bane dashi domin yazeed dinma Ba baya bane wajen tsafta.
Tas ta gara Komai sannan ta dibi kayan aikinta tayi gaba tare da manta hijabin nata adakinsa.
Shiko yazeed koda ya fito ya kalli Inda ta ajiye hijabin kwafa yayi dabadan dukan mace baya birgeshi Ba da babu abinda zai hanashi gyara mata zama,aiyana irin zaman dazaiyi da ita na halin ko in kula acikin gidan yake. Daga karshe ya tashi ya bude wani kofa na daban Wanda shi kuma balcony dinshi ne.聽
Mika yayi tare da furzar da iska yana mai shafa lallausan sajen dake habarsa Wanda suka a kwance luf luf.
Wayansa ya zaro a aljihunsa sannan ya latso number mahaifiyarsa domin taci ace sun isa yanxu amma yaji shiru bata kirashi ba.
Ringing uku yayi zuwa hudu ta dauka aiko atake yazeed ya shagwabe fuska Kamar tana ganinshi
Haba sweetheart dina ace kin isa tun yaushe amma shine聽 ko ki kira Babyn ki kiji yanake?
Dariya mom tayi sannan tace Allah sarki baby na ai Nasan yanxu akwai wacce zata kularmi. Dakai shiyasa kaga hankalina kwance Ashe har ka task Daga bacci.
Kwabe fiska ya dad'a yi yace haba mommy ni tun dazu na tashi yafadi hakan yana mai tura baki Kamar mom din na kallonshi.
Mom tace ai na dauka yau sai an hada da duka tukun zaka tashi saboda angwanci
Muryan kuka yazeed yayi yace "moooooom!"
Dariya mom ta karayi yace mom yaushe zaki dawo ? Tace aini son bazan dawoba har sai mun kusa sauka. Yace what!? Tace dagaske nake fa shiyasa na Baku space ma idan Ba kawomin labarin danakeson ji Ba tofa bazan dawoba yace haba mana mummy na! Tace uhm kai yazeed ni kaga tafiyana kit yaji ta kashe wayan.
Yasan Cewa she is very serious da abinda ta fada tunda har ta kirasa da sunansa na asali amma shi the last thing he wants to do on earth shine ko hannun yarinyar nan ya tana Allah ma ya kiyaye bara kawai yaje wurin zakiyya su samawa Kansu mafita.
Allah sarki fans Nayi missing dinku inaso inyi updating Mr. Romantic and I amma babu time
Karku manta dayin voting, sharing and commenting.
Love you all馃槝
Karamarsu babbarsu ce
Miss untichlobanty馃挄
7th October, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 29*
Bai tsaya yin wata wata Ba ya koma cikin dakinshi direct laptop dinshi ya dauko ya haye gadonsa sannan ya kunna CCTV dinsa domin rabonsa da ya Duba meke wakana acikin gidansa run shekaranjiya domin baya bukatar cin karo da kayan bakin cikin da baki ke aikatawa
Koda ya kunna forwarding yayi har izuwa na jiya tukunna ya tsaya
tundaga jiya da yamma ya fara kalla har izuwa Inda aka kawo minal zaliha ya hango tana rawar kai,tsaki yaja cikin ransa yace dubi wata me bakin fiska sai shegen rawan kai Kamar tsohon keke.
Kalla ya cigaba dayi har izuwa sanda mom ta kawoshi wani tsakin yaja tare da yatsine fiska sannan yadan kamo gefen lip dinsa na kasa yana tsotsa saboda takaici forwarding yayi har izuwa yau da safe
Bangaren masu aiki ya kalla yaga suna ta zirga zirgan su once In a while tunda asuba ne yawanci ma alwala Duke kamin sukayi wanka na minal ya Duba yaga ta tashi tana tafiya ahankali Kamar kazan da kwai ya fashewa take tafiya domin baccin bai isheta Ba .
Cikin nutsuwa yaga ta Shiga toilet sanda ta Dade bata fito Ba ran yazeed ne ya kara back a hanklai yace shegiya kome takeyi aciki haka oho...
Can saiga minal tafito tayi sallh ta fita
Duba parlour yayi yaga banan yaje Ba Dan haka ya Duba na kitchen aiko anan yaganta tana neme neme
Tsaki ya kara ja yana mai cizan lebensa na kasa,can yaga tayi murmushi ta dauki tsintsiya ta fita abinta. kwafa yayi wato ma aikin dadi yaje mata tasaba kenan Ba irin zakiyya bace.
Zuciyarsa ce tace masa yo kai what do you expect from a low class human being like her.
Girgiza kai kawai yayi irin zai San abinyi.
Ganin shiru bata dawoba yasa yasan Cewa ta fara aikin Dan haka bai bata lokaci Ba ya canja izuwa na dakin uwar gida sarautar mata.
Yawwnci Ba Komai bane sai yadda take kuka lokaci zuwa lokaci da yanda su sahir ke sha'aninsu hankali kwance illa in sunga tana kuka su tambayeta matsalarta in tace聽 babu sai su goge mata hawaye suna masu jin tausayinta hardai izuwa jiya da akakai minal wajenta da kuma sanda yazo dakin da yadda su kayi fada har yau da safe.
Da wuri yaga ta tashi Wanda hakan yabashi mamaki matuka Dan shidai yasan Ba sallah take akan lokaci Ba yayi magana,yayi fada,yayi fishi har ya hakura amma yau ta tashi da asuba Alhamdulillah shiryuwa ya samu matarsa ta fara gyarawa.
To his disappointment wanka tayi ta Shirya tsaf shirinta na zuwa office Kamar yadda ta saba wani ras yaji a kirjinsa,bakin ciki yayi masa kaluluwa a zuciya,wato ba'a yaban Dan kuturu saiya shekara da yatsu. Ganin ta dauki jakanta DIOR yasan Cewa ta tafi hakan yasa ya koma kitchen yayi playing Daga Inda ya tsaya sannan ya fara forwarding a hankali can yaga su atine sun Shiga Suna hayaniya ba'ajin me suke Cewa saboda yadda muryansu ya kacame Kamar gidan Suna
Parlour yaga sun nufa Dan haka yayi pausing yaje yayi playing na parlour ya fara forwarding aiko atake yayi playing yana mai kara hade fiskaganin abinda ya tsana ta fito tana tafiyar nan nata Wanda ke kara bata masa rai saboda yadda zuciyarsa ke bugawa aduk lokacin daya gani
Shara yaga ta fara tana aikinta cikin nutsuwa da kwarewa,shi kansa idan yace batada kyau yasan San zuciyane kawai amma ai she is not his type worse of all she is a gold digger. Mtswww wani wawan tsaki ya kara ja sannan taci gaba da kalla su binta yagani sun shigo nan yaga sun fara yiwa minal murmushi Suna magana tare kokarin karban aikin duk yadda yayi kokarin jin me suke Cewa ya kasa saboda yadda suke maganar kaman marasa Gaskiya can yaga sun kara hanyar kitchen hakan yasa yayi pausing tare da komawa na kitchen yayi playing aiko gaji yayi sun Shiga kafin suka fara aikin tare sunata hira minal nata musu murmushi
Aransa yace lallai yarinyannan wato ta rainani ko?wato har wani nasu aikin da nasata take kuma har tana murmushi lallai rayuwa batayi mata kunci Ba tukunna kwafa ya kuma yi yana kara gyara kwanciyarsa tare da janyo laptop dinnasa sosai sannan ya kashe Dan takaici ya masa yawa. Ruf da cikin yayi yana mai lumshe rikitattun idanunsa tare da sauke ajiyar zuciya.
Bayan yayi sallar la'asar ya dawo gida tundaga mai kofan parlour yajiyo kamshin abinci wani kurrr cikinsa ya bada sauti aiko yana dago Kansa karaf ya hango minal tana saukowa Daga stair case sanye take da black short bun da white t shirt sai dogon hijabi mai hannun Dan haka baya iya hango abinda ke jikinta.
He was expecting her takoma da gudu Dan ta buya amma to his surprise yaga tana pretending Kamar bata ganshi Ba
Itako minal kokari take ta Koma kitchen domin Duba abincinta,Dan haka da Dan sassarfa take saukowa,wani Abu yaji ya tokare masa numfashi saboda bakin ciki taga alamun yarinyarnan zata kawo masa rainin sense,Dan haka shima da sauri ya fara yawa aiko minal bata ankare Ba taji tayi karo da gini amma abinda ya bata mamanki shine irin kamshin da gadon yazeed keyi irinshi taji ya bigi hancinta
Taga taga tayi Kamar zata dadi yazeed yayi sauri rikota aiko tsayuwarta na daidai tuwa taji tassss! Ya dauketa da mari wutanta ne ya dauke na Dan wani lokaci.
Yazeed ko baice komaiba kawai sama yayi abinsa ya nufi side dinsa hankali kwance Kamar Ba shi ya kaftawa har mutane mari Ba.
Minal Kam sanda ta daskare awurin for almost five min kafin hawaye ya tsiranyo a idanunta
Ahankli take Daga kafafunta har ta isa zuwa kitchen ta samu har atine ta kashe mata Dan haka kawai tace wa atinen su dibi nasu domin dama yam porridge tayi
Aiko atine tace to aunty Amarya sannan ta diba musu Dana securities din da'ake bawa abinci guntun ta juye a flask takai dakin minal da sallama ta Shiga amma bataga kowa Ba Dan haka ta ajiye kawai ta fice abunta zuciyarta kal yawunta har tsinkewa yaje tana Allah Allah taci abincin minal Dan bazata manta sanda taci tuwo Ba.
Minal ko tana dawowa daki toilet ta fada tabaje akasa sai kuka
Jin alamun antaba kofar dakinta yasa ta sassauta murya
Tanajin anfita ta kara bude makokoro ta sha kukanta Kamar umarni Daga Allah.
Da daddare.......
Show some love by voting and commenting.
Sauri nake so bye, love you all馃槝
Miss untichlobanty馃挄
9th October,2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 30*
Duk Wanda kuke karantawa bakwayin commenting ko voting ina kallonku.
馃ズidan kuka karanta bakuyi voting Ba kuna nufin bai muku Ba kenan.
Asha karatu lafiya
Da daddare minal na zaune a dakinta idanunta da suka kumbura sanadiyyan kukan da tayi dazu sun Dan sace sai ajiyan zuciya takeyi.
Wani azababben yunwa ke nukurkusatta Kamar me Dan haka ta dauko flask din da atine ta kawo mata aiko tana ganin abinci mutuminta ta manta da Komai Kamar Ba ita ta gama sharar kuka Ba
Yam porridge dinta ta cinye tana mai side hannu kamin ta dauki flask din tayi kitchen domin ta wanke
Kitchen din ta Shiga ta wanke flask din kamin ta fito jikinta a sanyaye
Shigar jikinta na dazu ne saide yanzu ta daura zani domin Ba hijabin dazu bane
Zanin atamfa ne mai kyau Wanda ta dauko acikin kayan nata. Wani taku takejiyowa na isa da takama da nuna isa da kuma nuna kowa Ba kowa bane.
Tafiyarta ta cigaba dayi Ba tare da ta waiwaiya Ba domin wani bacci dake dibanta saboda gajiyar da tayi
Staircase ta kama za'a hau gaji an fincikota....Taga taga tayi kamin ta dai daita tsayuwarta da taimakon ginin dake gefenta wani nauyayyan ajiyan zuciya ta sauke kana ta hade ranta ta dago domin ganin wani uban ne yayi mata irin fincikar nan aiko tana dago idonta tage zakiyya ta hade rai tayi kananu da idanu
Ke Dan ubanki ankawoki aiki shine kikewa mutane yawo agida sannan bakisa uniform Ba kuma kinajin alamun mutane baki iya gaisuwaba? Tukunna ma urban Waye ya baki damar hawa sama?oh Ashe ankawo kaskancacciya yar uwarki Wanda batasan dokokin gidan mutane Ba tazo tana tsifo mana iyayi
Ganin minal ta kafeta da idanu Ba tare da tace komaiba yasa tace idan baki dena kallona da wannan shanyayyun idanun naki Ba sai naci ub*nki common get out of my sight useless human being. karbi kikai min wannan sama tunda abinda kikeso kenan.
Atine Wanda ta Shiga domin yiwa uwargijiyatta ta 2 Kumar amaryar oga yazeed tajiyo abinda zakiyya ke Cewa Shigowa tayi ta russuna tana mai Cewa sannu da zuwa aunty.
Zakiyya dake kallon minal ta kallo atine kamin ta kuma kallon minal tace haka ake gaidani agidannan.
Atine ne ta aro wani jarumta kana tace rankin shi Dade ai wannan itace amaryar.
What!?wannan abar me zubin aljanu?
Jikin atine na rawa ta gyada kai kana tace Allah bamu alkhairi ta fice tana mai zazzare idanu alamar kidimewa Dan bata bukatar rashin hankali ana zaune lafiya
Minal kam shiru tayi Kamar wata kulya ta dunkule a lungu daya takaici ya hanata yin komai
Zakiyya da mamaki da kuma kishi ya cikata yasa batayi wata wata Ba tace au Ashe Kece wannan dabbar wacce talauci ta dama akayi auren jari ai da kin sanar dani Cewa kuna bukatar kudi na baki Wanda za'a ciyarda danginki baki daya bawai Kiyi kokarin hada kanki dani Ba JAKAR BAIWA kawai,wuce ki hadomin tea kamin na saba miki.
Minal kam yau da badan sharadin da yazeed ya gindaya mata Ba da babu abinda zai hanata shukawa zakiyya rashin mutunci amma tana tsoro kada wancen azzalumin ya kasheta Dan tasan sojoji Ba mutunci bane dasu bare imani ko tausayi.
A hankali ta koma kitchen din sannan ta hadomata shayin domin atine ta nuna mata Komai da yadda zatayi amfani dasu.
A bakin kofar dakinta ta tsaya ta kasa Shiga zakiyya ko tana Shiga dakinta ta fada kan gado ranta na wani irin kuna
Can wajen 10min taji shiru Dan haka ta fito domin ta antayawa minal rashin mutunci aiko daidai lokacin minal ma ta aro jarumta minal na daura hannunta akan handle din zakiyya ta bude kofar a zafafe aiko take kofin shayi ya watsu musu dukkansu biyu Wanda yamafi zubowa minal din sannan ya fadi ya fashe
Wani wawan mari zakiyya ta kwasheta dashi kamin tace kan buhun bala'i ! ke wace iriyar dakikiya ce dabba kina Abu Kamar jaka!saboda tsabar bakida hankali bare lissafi shine zaki kama ki zuba mini tea ajiki?
To Dan matsiyacin ubanki ki gyara nan wurin sannan ki hado Mani wani kamin in fito Daga wanka.
Minal dago rinannun idanunta tayi ta nuna zakiyya da Dan yatsa kana tace ahir dinki duk haukarki ta kare a kaina tunda dani kike kishi amma kada ki kuskura ki kara sako da iyayena.
Kuma baza'a hado shayin Ba inga abinda zakiyi tana fadin haka tasa hannu ta fara kwashe glass din.
Zakiyya ko a harzuke ta nufi side din yazeed Kamar wata zakanya聽
Bude kofar tayi tagansa ya fito Daga wanka da alama kwanciya zaiyi.
Yazeed ko mayatar ce ke cinsa ya kasa jurewa,yayi azumin,yayi addu'an,yasha magani amma desire nanan Dan haka ya yanke shawarar gara yaje ya samu zakiyyan ko kadan ne ya samu da babu gara Ba dadi. Gwara yaje yayi yanda ya saba ya danyi maneji abinsa Dan shikam hakuri kawai yakeyi shekara da shekaru bawai dan yana gamsuwa Ba Dan tunda sukayi aure da zakiyya baifi sai 3 ya zama satisfied domin Daga tazama satisfied to shikenan fa zata fara raki Wai ta gaji.
Sai gashi Allah ya aiko masa ita tsuntsu gasashe Daga sama
Ganin yanayinta yasa yace Matas ya akayi ne yana mai kashe mata ido tare da fara takowa izuwa gareta tsaki taja domin ta gano me yake bukata kana fara huhhura hanci tana jijjiga tace "baby kaga irinta ko? kaga abinda mom tayi ko?gashinan ai yanxu ta aro maka wata kaskancacciya kuma ma abin haushin Wai Dan tsabar fitsara har ta dubi idona Wai nasata aiki Wai bazatayi ba kuma harda nuna mini Dan yatsa
Rungumota yazeed yayi danshi bayason irin yanda takeyiwa mahaifiyarsa shiyasa duk sanda ta fara zai yi kokarin kawqr da maganan inata dage to saide suyi fada
Turesa ta fara yi ni Dan Allah cikani kai ko wani lokaci sai ana serious Abu sai kazo kawani hau kakabe kakabe ni banson jaraba.
Kallonta kawai yake tare da murtuke fiska Kamar basho yagama mata kalar tausayi Ba sannan ya hankadeta kadan Daga jikinsa yace zakiyya yanxu akan hakkina zaki kirani jarababbe, Toh gashinan nabar maki ki jika kisha nima zan rike abina.
Rigan baccin daya ajiye kan gadonsa ya dauko ya zura sannan ya kwanta tare da Cewa inkin gama zaki iya rufemin kofar daki sannan ya juya
Baiji sanda tahau gadon Ba kawai ji yayi an rungumosa ta baya.................
馃幍i am waiting for your comments
Don't forget to vote
Miss untichlobanty馃挄
11 October, 2019.
4 - CAHAPTER 31-40
馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 31
Baice mata kala Ba yanaji ta fara tattabasa tare da masa wasu abubuwa ahankali wani mugun kuma jahilin feelings ke taso masa amma ko dar baiyi Ba a hankali yaji ta fara zurfafawa tsaki yaja kamin yadan matsa gaba kadan still hannunta na jikinshi
Matsowa itama tayi tanakai hannunta kan........ ai babu shiri ya mike tare da cire hannunta yayi wulli dashi
Kana ya fara magana a harzuke Wai me kika daukenine eh?ko kin dauka jarabata har takai nazama banida zuciya ne?ince P kuma nace banaso
Hannunta takai zata riko nashi yace karki kuskura ki tabani kinji na fadamiki.
Tace haba baby kayi hakuri mana kasan raina abace yake lokacin shiyasa na fadi hakan harara ya watsa mata kana ya kwanta Wanda yasa ta fahimci Cewa ya Dan hakura Dan haka ta fara aika masa sakwanni masu birki kwakwalwa aiko dama gogan naku ma a hanu yake Dan haka baiyi wasa da damarsa Ba ya bada kai bori yahau. saide kash zakiyya na zama satisfied ta fara nifa baby na gaji yazeed najinta kuma ransa na kuna danshi ko Rabi baije Ba ta cigaba da cewa ni ka barni na gaji please banason jaraba
Dan Allah ni ka matsa mutum sai shegiyar mayata Wai........
Hankadeta yayi hakan yasa bata karasa fadar abinda tayi niyan fada ba sannan ta dubesa aiko hatta jijiyoyin kansa sun tashi saboda Bacin rai聽.
Kofa kawai ya nuna mata Da hannu danshi kanshi tsoran motsi yake dan gani yake babu abinda zai hanashi yiwa zakiyya dukan kawo wuka a darennan.
Zakiyya na ganin haka tasan ta kwabsa domin ko ta bata masa rai Wanda hakan ke nufin bazai hukunta minal Ba tunda dama ta bada Kaine saboda taci uban minal gobe never the less she enjoyed it.
Aiko dole ta gyara kafin reshe ya juyewa mujiya, matsowa tayi kuwa dashi yace out,tace bab....
Kofa ya nuna mata tare da maimaita mata Cewa tabar masa daki rungumosa tayi yace ke banson iskanci meye hakan? tace ban koshi bane .
Wani harara ya watsa mata irin me kika mayar dani kamin ya yakiceta ya fada bathroom yana mai jin zafin hali irin na zakiyya Sam Daga bukatarta ta biya to shikenan shikam ko oho
Son kai yayi mata yawa........ Haka ya dinga sake sakensa yayi wanka tare da wankan tsarki sannan ya fito
Koda ya fito Bai sameta Ba Dan haka ya Shirya abinsa yayi kwanciyarsa zuciyarsa cunkushe ga kuma wutar d茅j脿 vu dake addabarsa yanajin Kamar zaiyi hauka.
Bashi yayi bacci Ba sai wajen 2:30 domin juye juye yaketayi dayaga babu sarki sai Allah kawai sai ya fara kuka hawaye nabin kuncinsa ga wani mugu Abu mai zafi daya tsaya masa a zuciya gameda abinda zakiyya keyi masa.
Abangaren minal kuwa kwashe ceramic din take tana kukan takaici da bakin ciki ita yanxu a haka zata karashe rayuwarta cikin bauta?Allah ka kawomin dauki shine abinda take fadi tana gama kwashewa ta zubar ta gyara wajen sannan ta tafi dakinta wanka ta Shiga ta Dade Kamar yadda ta saba(ko me takeyi oho muje zuwa daganan zamu gano)
Fitowa tayi sannan ta tsaya a gaban madubinta taci gaba da abinda take yi a bandaki kullum tun tana gida har ya zame mata jiki in batayiba batajin dadi.
Bayan ta gama Shirye shiryenta tayi alwala sannan ta kwanta tana mai nazarin rayuwarta
Zakiyya ko koda taje dakin ta Fadawa gadonta tayi tana mai tsaki kana tace kaika sani Idan jarabarka ta matso ka zama kazo ne sannan ta bingire da bacci Ba tare da tayi ko tsarki Ba balle wankan tsarki ko makamancinsa(uhm Allah kyauta)
MORNING
Yau kam minal sai 7 tukunna ta fito yin aikinta Wanda takeyinsa bisa kwarewa bayan ta kammala ta Koma daki tayi wanka ta Shirya cikin atampa blue mai mai circle yellow sannan ta zauna a kan kujera tunda batada right din zama a gado tana karanta wasikar jaki.
Banko kofar dakinta taji Anyi take jikinta ya dauki rawa domin tasan cikin biyu daya ne ko mijin ko matar sa
Aiko yazeed ne yana wani yatsine fiska Kamar yaga kashi sannan yace wato ke gaki hamshakiya ko in bada umarni ki take
Sai yayi murmushin gefen baki to ai shikenan kinga ko Ba Komai zaki ragewa washing machine dina aiki Wanda ke nufin bill din nepa da kuma kudin gas zai ragu domin Daga yanxu聽 ke zaki dinga wankemin singlets and boxers dina Mara mutunci gold digger kawai.(uhm yazeed kenan sai kace kuddin bill din wani Abu yaje rage masa)
Zaki tashi kije dakina ki dibo su yanzu ko sai na wanke miki wannan shegiyar fiskannaki da tafi
Jiki na rawa ta mike zata fita yace "hold on! dakata" ta jiyo wannan karan ranta adan bace
Yace ya zama dole kibi umarnin matata
Batasan lokacin da tayi kicin kicin da ido tace wallah nanne kuma kayi karya na rantse......
Aguje ta fice domin yunkurin da yazeed yayi zai kamota ya gwabe bakin da Kamar zai bita sai ya Fasa ya nufi dinning area yana mamaki Wai yarinyarnan ce ke masa irin wannan rainin wayon da fitsara?
Zuciyarsa ce tace masa what do you expect from a ghetto girl like her?inbatayi fitsara bama sai Allah ya tambayeta(fadi Gaskiya babana?
Dinning room ya Shiga abinshi ya hada tea yasha tare da cin plantain baifi 5 slice ba Sannan ya wuce gym room dinsa.
Minal ko data dauko kayan wankesu tayi tas聽 sannan ta shanya sannan ta koma ta nemi abinci taci
Zata koma dakinta taji ance ke!..ke!..ke! asararriyar baiwa zonan juyowa minal tayi a hasale kawai sai kalaman yazeed ya fado mata
Wani irin kallo takeyiwa zakiyya at any moment zata iya mata illa zakiyya ko dukda tana shakkun captain yayiwa minal din magana ko baiyiba amma bazata barta taci banza Ba
Zaki rama ne? Shiru minal tayi, zakiyya ta tabe baki kana tace zokiyi min tausa
Wani harara ta rafkawa zakiyyan aranta tace wallahi baki isa Ba saide mijinki ya kasheni
tasowa zakiyya tayi tana nufo minal domin dauketa da tafi minal ko rayawa take aranta irin rashin mutuncin da zata antayawa zakiyya Idan ta tabata Dan ita Ba jaka bace
Yazeed ne ya shigo cikin isa fiskannan Kamar bakin hadirin daya taso Daga yamma kamshin Cologne din da yakeyi ne ya Sanar da minal isowarsa
Atake kirjin minal din ya buga kana tsoro ya shigeta amma kunsanta da taurin kai bata nuna Ba saide tanaji jikinta har makarkata yakeyi
Wajen su ya iso ya watsawa zakiyya kallon me kikeyi Anan?tsaki taja ta wuce koda ya juyo ganin Inda minal ke tsaye聽 yaga empty,ta arce.
Zakiyya kam ficewa tayi Daga gidan tana Cewa malam sule idan ya dauko yaranta kar ya kaisu gida ya Kaisu su siyo cup cakes kamin ya kawosu boutique dinta Kamar yadda ya saba
Yace to hajiya Insha Allah ta wuce abinta ta shige cikin 4matic dinta ta wuce .
Don't forget to vote,share and comment pleeease because that is the only way zan gane yadda kukeson novel din.
Taku for life;karamarsu babbarsu wato
Miss untichlobanty馃挄
13th October, 2019.
馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮@mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 32*
Sama ya haura direct dakin minal ya Shiga ya sameta tana ajiyar zuciya yace follow me !
Ta dago idanunta ta kallesa domin neman karin bayani wani electric shock sukaji dukkansu biyu kamin ya waske ta hanyar Cewa ko bazaki iya zuwa bane kin kafeni da inu munafuka?
Shiru still tayi ya fice itama ta bisa subul subul tana mai gyara zaman yellow hijabinta
Koda ta shigo dakin akan coach ta samesa zaune ya daura daya akan daya yace bazaki iya karasowa bane?
Ahankali ta tako a tsure dukda bata bayyana hakan Ba ta tsaya a Dan gefensa
Yace closer tare da mata alamu da hannu ta Dan kara matsowa harara ya buga mata tare da Cewa cinyeki zanyi ta girgiza kai tana mai karasowa da Dan Sauri tsayuwa tayi a kansa
Ya kamo bakin hijabinta ya janyota kasa
Dan kara ta saki domin hijabin ya Dan kurji gefen wuyanta kana visa kuskure ta Dan taka kafarsa kamin ta zube,yace Dan kaniyarki haka zaki tsaya akan yayanki ta girgiza kai yace bakida baki ne tace a'a
Harara ya kwada mata yana mai hadawa da rakwashi kwas a tsakiyar kanta yace bakisan in antaka mutum hakuri ake basa Ba?girgiza kai tayi alamu tasani tana rarraba idanu Dan rankwashin ya shigeta
Janyota yayi ya matse cute pinky lips dinta聽 yana kalla yace wato gani sarkin mahaukata ko ina magana kin bawa banza ajiyata
A hankali hannunta na rawa ta daura akan nashi alamun ya sake bakin zatayi magana idanunta ko ya cicciko da hawaye saboda radadin da bakinta ke mata shikuwa wani yaaaam yaji Ba shiri ya saki bakin kana ya kauda kansa gefe domin jin bananarsa na kokarin kawo masa raini
Ahankali cike da in'ina tace kayi hakuri na taka ka,tsika jikinsa suka mike gabadaya yayinda hawayen da taketa boyewa ya samu nasarar saukowa
Ba tareda ya kalleta Ba yace nace miki kimin wanki shine Dan kin rainani ki kamin jika jika ko?
Muryarta na rawa tace wallahi me kyau Nayi kaga hannuna ma ta nuno masa gefen hannunta yadda yayi jaa Kamar ka taba jini聽 ya fita tsabar yadda ta dirji kayan
Tsaki yaja yace raguwar banza dan kin wanke singlets 3 da boxers 3 Wanda nasa jiya shine zakina wani nokewa Kamar marainiya
Batasan lokacin da tace aide nafi wasu juyowa yayi adan zabure Dan baiyi expecting ta mayar masa da magana Ba
Hannu yasa ya bige bakinta yace zaki tashi kibar gefena ko saina maujeki in canja miki halitta.
Da Sauri tabar dakin tana mai zubda kwalla,lallai tayi kuskuren amincewa da zancen auren Ba tareda ta saurari ko Waye su baba zasu aura mata ba sai a yanzu ne take kara ganin wautarta
Dakinta ta koma ta tsaya agaban madubi tana kallon yadda tayi kyau dukda kuwa ko petroleum jelly bata shafa Ba balle powder amma idanunta sundan fada ciki sannan ta zama kalar tausayi babu walwala a tattare da ita.
Haka rayuwa taci gaba wa minal yanxu har tayi wata 3 a gidan captain聽 tanayin aikinta Kamar kullum once in a while sukan hadu da zakiyya inta gama banbaminta minal kawai ce mata take Allah ya baki hakuri sannan ta wuce itako zakiyya babu abinda ta tsana Kamar tayima rashin mutunci ka nuna bai dameka Ba Dan haka sai tayita kumfan baki tana cika tana batsewa
Minal ko gani takeyi Kamar zakiyya taci noti kuma tana bukatan Sabo hakan yasa bata tanka mata har tayi ta gama
Aunty fauzy ta kawo mata ziyara har sai biyu Inda take kara jaddada mata girman aure da kuma yadda zata zauna da abokiyar zamanta lafiya. Ita dai minal kunne kawai ta kasa Cewa komi aranta ko tana Cewa cab ai bakisan halin abokiyar zaman tawa da mijinta ba da ko zancenta bazakiso muyi ba.
Yau saura 3 days auren zaliha Inda gobe ne za'ayi kamu
Minal nason tambayar captain izini tun last 2 weeks amma tsoro take yau kam shahada tayi ta turo kofar dakin da yar sallama a bakinta aiko abinda ta gani shi ya Daga mata hankali captain ne ya fito Daga wanka Daga shi sai gajeren wando fari kal da bathrobe Wanda ya barshi haka ba tare da ya daure igiyan ba wanda yayi sanadiyyar Nuna dukkan ilahirin faffadar kirjinsa mai dauke da gashi kwance luf luf Wanda keda laushi hamar gashin kan jariri.
Rikicewa tayi a maimakon ta fita saita fada bandaki aiko ta sule sai a kasa Inda ta bige makunin shower sannan ta gurde kafanta salati ta sake tare da sakin wata gigitacciyar kara hawaye kuwa tuni sun Dade da fara ture junansu wajen saukowa yiyinda ruwa ya mata sharkab.
Captain da bai San ta shigo dakinba yaji ihunta atake ya nufi bandakin ganinta shame shame a kasa ta jike da ruwa jakab ya sashi Jan tsaki tare da Cewa ke Dan ubanki me ya kawoki cikin bandaki na bayan yau ba ranan wankewa ba?
Kuka kawai take kamin tace Dan Allah ka taimaka mini wayyo kafata tsaki yaja da Kamar zai fita amma yadda take kuka yasa yaga bazai iya barinta ba yasa ya miko mata hannu aiko hannunta ta mika ta rike nasa take sukaji Kamar sun taba wayar wuta ba shiri ya saki hannun ji yayi jijiyarsa ta fara harbawa Wanda yasashi Cewa kaide kayi asara yazeed acikin zuciyarsa
Sake miko mata hannun yayi ya Dagata
Dingishi ta soma har zasu fita yace dakata !me kike nufi?
Kallonsa take alamun Neman Karin bayani yace au dake a haka kike nufin zaki Shiga dakina ki jika mini da ruwa saboda Yan garinku basuda lissafi?
Bata fiska tayi cikin rants tace badai garinmu ba wallahi
Yatsansa yasa ya dalle mata baki yace dani kike tayi saurin girgiza kai alamun a ah hannun yasa zai cire mata hijabin dake jikinta ta rike kyam kiciniya suka fara aiko yazeed ya riko hannunta duka biyu da hannu daya sannan ya zame hijabin da hannun daya yayi Ciro dashi
Kallonta ya farayi Inda idonsa ya tsaya kyam akan cikakkun breast dinta Wanda doguwar Riga jikinta da ta like mata har nipple dinta ana kallo wani yawun jaraba ya hadiya 'kutt kana ya kalli fiskanta aiko shi take kallo and she caught him staring at her boobs red handed
Waskewa yayi ta hanyar tabe baki sannan yace yanxu dama wadannan tsiyar ake boyewa?uhm aike yarinya bama kida abin boyewa danko tsirara zakiyi yawo bakikai akalleki ba uhm kwaila lamba daya kawai sannan ya fice ya barta a wurin minal ko tabe baki tayi tanacewa jeka dai Nasan borin kunyace kawai kumanima ai jikina tafi karfin mugu sannan ta murkuda baki
After Kamar 1min saiga yazeed ya shigo rike da wata T-shirt dinshi fari kal wulla mata tayi sannan ya fice yana yana mai Cewa yi Sauri kibar Mani daki
Domin alokacin har wani hajijiya yakeji tsabar sha'awa
Dan Rabon da yayi harka sati biyu kenan amma yanagudun abin kunya kuma ai yarinyar gold digger ce so he should be very careful kar mazakutassa takaishi ta baroshi.
Minal ko tsayawa kallon Rigan tayi wai me mutuminnan ke nufine Wai ko bazai bata wando bane?
Jin shiru bata fito ba yasa yace Wai Dan kaniyarki bazaki fita bane kullum kika Shiga bandaki Kamar mai haihuwa
Sauri tayi ta saka rigar tana mai Cewa ko yaushe ya taba ganin sanda nake Shiga bandakin oho mutum sai shegen fi'ili
Iya cinyarta rigar ta tsaya Dan haka ta fito tana jajjan rigar domin rufe jikinta
Aiko yazeed na ganinta sanda yaji numfashinsa yadanyi seizing
Kana ya dawo
Ganin yadda takeyi da fiska ya bashi dariya amma taci mur
Muryarsa Kamar yasha giya yace zonan
Zuwa tayi ta zauna a kasa domin bata manta da abinda ya mata ba sanda ta tsaya masa akai yace me yakawoki dakina ?
In ina ta fara tace dama Ami..niya..ta..ce zata..yi aure shine....nakeson naje
Tabe baki yayi yace naji zaki iya zuwa amma ko gidanku ban yarda kije ba
Kallonsa tayi alamun lafiya kake kuwa ?
Baibi takanta yace zaki iya bar mini daki kuma kitabbata kin kwashe tsummokaranki
Fita tayi tana nazari acewai mutum rabonshi da iyayensa kusan wata 5 amma Dan rashin imani ace bazashi ba ALLAH YA ISA
captain yazeed zaune a bakin聽 gadonsa yana buga game din chase a laptop dinsa Kiran mom ya Shigo dauka yayi
yace salamu alaiki ya habibaty
Mom tace Ameen wa alaikas salam son yakake?
Yace lafiya kalau mom i missed you amma ke naga baki damu da Babyn ki Ba
Dariya mom tayi tace Dan Allah dubeka wani kato dakai Wai baby na kai Wai bazaka barwa 'ya'yanka shagwabar bane?
Kwabe fuska yazeed yayi yadda yara keyi inka kwace musu alewa yace ai kowa da matsayinsa nidai Nasan ni Babyn ki ne ya kashe ido Kamar mom na kallonsa
Mom tace Allah ya kawo masu albarka sannan tasa serious tune tace yazeed naji shirufa bawani labari gashi har kunyi kusan wata 5 da yarinyannan kuma kasan dai daya Daga cikin abinda yasa naso maka aurenta kenan tunda naga kaida zakiyya bakuda tsarin haihuwa kusa ni sai mai shirin Haifa ta haifo mini
Hade rai yayi yana yatsine sannan ya tabe baki yace ai mom yarinyan ce tukunna ina Duba natsuwarta da hankalinta sannan inga ta dace ta zama uwar yayana koko?kuma kinga bata gama wani girma dazan daura mata nauyina Ba.
Sakin baki mom tayi jin abinda yazeed din yace
Yazeed kuwa jin tayi shiru yasa yace mom kina jina?
Kamar Wanda aka watsawa ruwan sanyi mom tace d'annan dama duk zaman da kukeyi da yar mutane Ba bata hakkinta kake ba? Kai a haka zaka rike mata biyun yazeed ?kana danne mata hakki?ja'iri shine harda wani Wai bazata iya daukan nauyinka ba sai kace wani abin arziki ka ajiye acikin wandon naka?to bara kaji yarinyar da kake renawan tsab zata daukeka harda guntu Dan jakar uba kawai........
Sai alokacin yazeed ya gane ya kwabsa Sosa 'keya ya fara kana yace mummyyy kiyi hakuri zan gyara Insha Allah
Mom tace karma ka gyara kai ka jiyota kuma zan dawo kasar inyi sati a gidan naku kamin na Koma gidana na Abuja saboda association Suna bukata na dama Hutu na dauka
Nan dai mom ta surfo masa kwadokwandon bala'i kamin tayi masa wa'azi ta kuma tunasar dashi hakkin matarsa dake kansa sannan ta kashe wayarta tana mai jinjina al'amari irin na tilon Dan nata shiko yazeed tabe baki yayi yace Allah ya kiyaye ni dayin abin kunya da jawakai raini
I will be waiting for聽 your comments
Miss untichlobanty馃挄
13th October, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 33*
Saukowa yakeyi Daga stair case domin zuwa masjid phone dinshi ya dau ringing
Dubawa yayi yaga mom yace yau nadebowa kaina
Picking yayi yana Cewa sweetheart har kinyi missing dinane ?
Ta dayan bangaren mom tace dan Allah ni matsa mini ka rufen baki ka sadani da dadiyata
Marairaice fuska yayi yace haba mummy abin fa baikai nan Ba mom tace yama wuce nan. Zaka hadani da ita inji muryarta koko? juyawa yayi ya fara komawa sama kana ya nufi hanyar dakin minal sallaya ya gani a hannunta alamun sallah zatayi harara ya banka mata sannan ya kika mata wayan yana mata kallon kashedi alamun inata kwafsa zaici ub**ta
Karba tayi jiki na rawa muryar Kamar zatayi kuka tace sallam alaiki, mom?
Ajiyan zuciya mom ta sauke tace wa alaikis salam diyata yar albarka yakike?
Dashi ke wayan a hands free yake聽 captain na jinsu tabe baki yayi yana mai lumshe idanu
Minal tace lafiya kalau mom tace ya hakuri da mijin naki?minal ta dago idanunta ta kafeshi dasu kana ta sauke tace Alhamdulillah
Mom tace sai hakuri kinsanshi baudadden mutum ne ga taurin kan masifa sai kina hakuri kinji tace Toh
Nanfa mom ta fara mata magana akan rashin hada gadonsu ita da yazeed itakam batasan Inda mom ta dosa ba Dan haka koda mom ta karashe kawai Cewa tayi Insha Allah za'a gyara Kiyi hakuri
Shiru ne ya Dan ratsa gurin jin shirun yayi yawa yasa mom tace da fatan babu wata matsala ko?minal tace babu mom tace Kin tabbata ? Minal cikin in'ina tace dama inaso inyi waya da gida ne salati mom ta rafka kamin tayi kicin kicin da ido tace to bari zanfadawa yazeed din ko?minal tace to na gode Allah ya saka da alkhairi mom tace Ameen. Sallama su kayi sannan ta jiyo domin mikawa yazeed wayarsa
Yazeed ko tun sanda mom ta fara yiwa minal wannan magana ya Lula duniyar tunani.
Tunani kala kala yakeyi kamin. A ransa Gaskiya ni sweetheart tana kwafsamin wannan ai sai tasa yarinyar ta rainani.
Haba fi sabilillah ni Gaskiya.....
Tunanin nasa ne ya datse saboda miko masa wayar da minal kallon hannunsa yayi ya zabga mata harara da tsaki sannan ya Karba ya fice yana mai banko kofar sannan ya kara wayar a kunne yace haba sweetheart ai saikisa yarinyar nan ta rainani ya zaki dinga.....
Ba karashe ba sanadiyyar mom data datseshi ta hanyar rafka uwar salati sannan ta kara da Cewa d'annan wallahi ka fita a idona na rufe kanajina ko?yazeed!yace na'am, yazeed!! Na'am,yazeed!!!sai nawa na kira sunanka yace uku tace to wallahi ka kiyaye ni ka fita daga idona in rife wato Dan wulakanci shine ka rife er mutane a gida baka bata hakinta kuma baka taba kaita taga iyayenta ba?kai ance ma haka ake auren?ko Dan kaga Nina aura ma ita shine zaka nuna min ban isa ba? Shikenan yazeed ni bazan yi fishi dakai ba amma ka sani hakkin yar mutane ma ya isheka kuma ka wuce yanxu basai anjima ba ka siyo mata waya tare da sim da kati da kuma data aciki sauran ya rage naka kuma batun raini saide kar a kuma tunda ka Riga da ka aurota....... Tiiiiitt mom ta kashe wayar
Kallo yazeed yabi wayar dashi kamin ya sauke wata nannauyar ajiyan zuciya. Shikam ya rasa yadda zaiyi da ransa wannan itace rana zafi inuwa kuna.
Koda ya fito da lukman taci Karo a hanya lukman yace boss!boss ya akayine na ganka haka na lura tun da safe Kamar wani Abu na damunka
Harara yazeed ya banka masa yace yau kuma wani fi'ili ka tsiro dashi babu kowan ma kake kirana da boss?
Dariya lukman yayi yace kai mutumi kaide baka canzawa Nide ba wannan ba meke damunka ?yazeed yace babu komai lukman yace haba yazeed na lura tun lokacin da akayi aurennan abotarmu taja baya yes nasani bamu nuna wa duniya Cewa mudin abokai ne especially ta fannin aiki amma hakan ba hujja bace dazaisa ka dinga boyemin damuwar ka kasan babu sirri a tsakaninmu, damuwar ka damuwata ce.
Kallonshi yazeed yayi irin 'look who is talking' dinnan sannan yace dama ba soja kayi ba da gidan radio ka nufa Kamar da gaske fisabillillahi luku tun Muna primary mukaci buri Cewa zama sojoji kuma masu mukami amma me sanda lokacin yayi ka kasa fadamin Cewa bazaka iya zuwa makarantar ba saboda cancer daya kama mahaifinka bakuda hali,ka boye mini sai a diploma ka kare saboda cika burinka kuma ka zama recruit shine yanxu zakana cemin Wai babu sirri tsakaninmu ai boye boye ka gama min ita mtsww.
Sauri yazeed ya fara domin ya wuce lukman amma lukman yayi Sauri rikosa yace haba aminina kar miyi haka dakai mana Nasan ko wannan mahaifinnawa ne ya Daga kar in fadi maka bada son raina bane kaima ka sani yazeed yace naji
In a bossy tone Lukman yace to shikenan idan min fito Daga masjid din sai ka fadamin matsalar ka
Kallon sa yazeed ya kuma yi kamin yace irin oga yayi magana kuma angama ko?
Lukman yace to ya ranka?table baki yazeed yayi kamin suka Shiga masallati yazeed na lissafi a zuciya lallai ba shakka lukman ya kasance amini a gareshi babu karya sudin masu kauna da rike amanar junansu ne kuma tare suke komansu kuma basu boyewa junansu matsalarsu to amma anya kuwa zai iya maganin matsalarsa? zai iya bashi wata shawara da zata anfaneshi kuwa? Toh zaide jaraba ya gani.
Koda suka fito yazeed yace muje ko?gyada kai lukman yayi alaman OK sannan suka Shiga gate din takowa suke a kaga saboda tazarar (Kamar dai yadda kuka sani kuma kuka gani a photo gidan akwai dadi da tsaki ga fili na hauka).
Hanyan garage yazeed ya nufa lukman yace zaka fita ne?gyada kai yazeed yayi kamin yace muje ka rakani
Lukman yace ina?yazeed yace zaka gani. Bugatti Byron yazeed ya nuna masa Dan haka yaje ya dauko key dinta ya dawo ya bude driver's seat ya shige ganin yazeed yayi kikam a dayan Abangaren yasa yace Shiga mana ko ka fasa ne ?
Koda yazeed ya nuna masa alamun abuse masa lukman yace aiko zaka kwana a tsaye yazeed yace an serious fa lukman yace nima haka..... Nan fa suka fara Daga karshe lukman yayi surrender yace kaide ka fita naci bata in bude ma Kafin ka cinyeni har kashi
Fitowa yayi ya bude masa kofar daidai zai Shiga lukman yakai masa kutfo a mazaunai
Shanyewa yayi ya nuna ko ajikinsa dukda ko ta ratsashi aiko lukman yana kewayowa ya Shiga zai rife kofa yazeed ya kafa masa rankwashi
Ouch! Ya dafe wajen sannan ya juyo ya kalli yazeed yace haba my guy irin wannan rankwashi yazeed Kam kauda kai yayi Kamar bashi yayi aika aikan nan ba yace inka gama zamu iya tafiya.
Hello wattys !yakuke ?
Toh kunji wata sabuwa sirrin boye kuma Ashe聽 yazeed and lukman are friends.
Kunyi tsammanin hakan?
Shin kuna ganin yazeed zai sami mafita a wajen amininsa?
Shin abinda mom tayi ya dace?
Ina jiran COMMENTS dinku.
Love you all馃槝
Miss untichlobanty馃挄
19th October, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 34*
Tafe suke babu mai magana can lukman yace ina zamu ne Wai?sanda yazeed ya dau Yan sakanni kamin yace muje makarfi plaza inason insiyo waya ne.
Gyada kai kawai lukman yayi alamun ok,Sannan ya kara speed din motar.
Chan yace inajinka. Yazeed sarai ya gane me lukman ke nufi da hakan amma saboda hali irin nasa yace kana jina name fa?
Side glance lukman yayi masa kamin yace zaka fadamin koko?yazeed yace me kenan?tsaki lukman yace sai ka rike matsalarka tunda bazaka iya fadamin Ba.
Shiru ne ya karade wajen kamin can yazeed yace ka tuna wannan yarinyar ?
Smiling lukman yayi domin plan dinsa yayi wato babu Wanda ya kaishi fahimtar abokin nasa idan聽 ka nuna masa baka damu da Abu Ba to Anan ne zai dauki abin serious.
Luku yace wace yarinya kenan?yazeed yace wannan yarinyar data Shiga booth?
Lukman yace wannan yarinyar daka gasawa aya a hannu kuma kaso ka gasa mata gyada a tsakiyar kai Allah ya taimaka brother Jamal ya kira mom?
Tsaki yazeed yaja yace matsalata dakai kenan ka fiya surutu yanxu waya tambaye ka duk wannan jawabin?
Lukman yace Nide Ba wannan Ba meye da yarinyar?
Yazeed yace ita...sai kuma yayi shiru lukman ya ehm ita me? Yazeed yace itace amaryar da mom ta aura min
Wani wawan birki lukman yana yana zare idanu ya kalli yazeed a tsora ce yace dude me kace ?
Harara yazeed ya aiko masa yace banson iskanci ai sarai ka jini.
'Kefta idanu yayi alamun mamaki sannan yace kana nufin yarinyar nan daka gama shekawa rashin mutunci mom ta aura maka kuma ka zauna da ita ?
Kawai sai ya fashe da dariya harda rike ciki kai mutumina Gaskiya life dinka na birgeni,Wai ina self respect din naka da ........ Ya tafi ?
Wani kallo yazeed ke aika masa if looks could kill da an Dade dakai lukman kabari.
Yazeed yace banson wulakanci ya ina maka serious magana kanamin dariya?karka batamin mood fa. Dan wulakan ci bakasan in ina magana ba'a datseni Ba?'kwafa yayi yace dallah mallam聽 zaka ja mota mutafi ko zaka tsaya kana batamin time?
Kunna Moran lukman yayi yana mai danne dariyarsa sannan yace haba nawan, Allah ya huci zuciyarka.
Tabe baki yazeed yayi yace in bata huce bafa?lukman yace zama ta huce Insha Allah .
Tsaki yaja sannan ya ci gaba ni yanzu Ba wannan Ba matsalarka shine Allah ya gani bana sha'awar聽 kusantar yarinyar nan , mom kuma ta dage ita kawai a haifo mata jikoki.
Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace zakiyya ko Kazan yadda muke ciki da ita
Gyada kai luku guy yayi alamun ya sani sanna yazeed ya kara da kuma inks lura amaryar tayi karama dayawa bana tunanin zata iya dani.
Wannan magana ta mugun bawa lukman dariya amma to avoid issues with his amini yasa ya shanye abarsa
Yace uhm sannunku manya manya su alharijunal auwaluna
Yazeed yace wallahi luk guy ka fita matsala na rantse da Allah zanma rashin mutunci inma harijancin ne aiba laifi na bane Allah ne yaso ya ganni haka wasu da kudi suke biya dan su zama harijan ?Toh Nina zamu a'bagas sai ince banaso?
Lukman yace chill man Daga wasa yazeed yaja tsaki kasa kasa yace aikin banza mutum matanshi biyu amma ya kare da azumi. Lukman yace karka damu wata rana sai labari.
Daidai lokacin suka iso plaza din, saukowa sukayi Daga Motan lukman ya latsa mukullin ya rufe sannan suka Shiga nan dai suka zabi latest Samsung Inda suka hau musu akan kalar wayan.
Yazeed yace lallai saide a siyi fari domin yafison farin kala ko shudi (blue or ruwan bula) yayinda lukman yace ai golden zaifi tunda itadin zata hau da kowa ni kaya kamar dai sarkar gold kuma ai mata nason kyale kyale ........
Haka suka cigaba da arguing Daga karshe mai Saida waya yace wannan abu mai sauke ne su siyi fari inyaso sai asa mata cover golden.
Nan suka yarda yayin da suke hada baki wajen Cewa that's it!
Bayan sun dawo Motan ne yazeed ya kalli luku yace guy bakace Komai ba.
Shima lukman domin ya rama abinda YAZEED ya masa sai yayi acting Kamar bai gane ba yace akan me fa ?yazeed yace abinda na fada maka mana
Lukman yace kawo kunnanka,yazeed yace ni in zakayi magana kayi lukman yace dadinta ni lamin lafiya nake kuma dadinta ba matsalata bace. Kanaso kaji koko? Yazeed yayi ajiyan zuciyar in defeat sannan ya matso na ya sanar masa da yadda zaiyi aiko yazeed ya zabura yace luku amma kasan if the plan backfired zai iya jawomin raini ko?lukman yace 'in order to succeed, you must take the risk' ko ba haka kake Fadawa mutane ba?gyada kai yayi alamar haka ne amma wannan din is it worth it?
Haka dai suka dawo gida lukman na kara karfafawa yazeed din guiwa sai wajen 10 tukunna suka rabu.
Koda ya shigo dakinshi wanka ya fada.
Ji yayi Kamar an Shiga dakinnasa amma ya basar Dan yasan bazai wuce zakiyya ba. Koda ya fito samunta yayi tana kwance tana chatting da sabuwar kawarta sumayya ,ko kallon inda yake batayiba,shima bai kulata Ba yayi hayewarsa ya kwanta.
Wajajen 3 yazeed gaji Kamar ana tabashi
Bude idanunsa yayi yaga zakiyya zaune tana kallonsa tace baby inason magana dakai dan daura fiska yayi yace magana bai iya jiran safiya bane ? Haba zakiyya fisabilillahi ace ki tashi mijinki tsakar dare Daga bacci lokacin da Allah yasa Dan bayi su huta Wai zakiyi magana dashi?to ina jinki
Tace baby wani urgent business trip ne ya taso min ana you know聽 that next week fa za'a fara bikin cousin sissy kaga we have to arrive early so I think聽 de I will not be around for 2 weeks.
YAZEED kam da mamaki ya cika shi danshi yanzu lamarin zakiyya ya daina bashi haushi ya fara bashi tsoro.
Tabe baki yayi alamun takaici yace OK jeki sannan ya Koma ya kwanta.
Tace baby Ba zancen tafiyan nawa bane ai.
Yace ok tunda dama Ba izini kikazo nema Ba to miye na fadamin?
Tace to katashi ka zauna magana is serious fa yace a haka ma inaji sannan ya rude idanunsa. Tace dama so nake na dauki white Prado dinka Ba.
Yace kinsan dai ko sweetheart bata tana hawa wannan Ba kuma kinsman ko tukani ba'ayi Dan kar ashiga min cikin Abuna.
Tace to jawabin na menene kuma aini Ba mom bace,kawai kaban motan.
Yace abinda jawabin ke nufi shine bazan bayar ba. Kuma zancen keba sweetheart bace kina nufin kin fita ne ? Ince mota 6 ne dake ko duk babu Wanda zaki iya tafiyar dashi ne?tace baby 4matic dina kullum shi make using its out of the picture,Prado na kuma paint dinshi ya tsufa kuma...........
Yazeed ne ya datseta ta hanyar Cewa ince paint ne kawai ya tsufa tace eh yace fine then use it mana.
Tace baby mutanefa zan Shiga yace anso gara ke,mutane nawa ne zasuzo da irin motan naki?the only help dazan baki shine ki dauki bakin not the golden one! Tace baby amma...... Hannu ya Daga mata hannu yayi sannan yace zaki iya barmin motata.
Tashi tayi tana gunguni bajar bajar tabar dakin shiko yazeed tabe baki yayi ya Koma tsakiyar gadonsa yayi d'ane D'ane.
Sarai yasan dalilin da yasa takeson tafiya da farin, saboda shidin customised ne. Hmm wato mai hali baya fasa halinsa,itadai burinta ko ina taje asan matar manya ta iso.
Baccinsa ya cigaba da narka kamar Ba gobe.
Miss untichlobanty馃挄
26 October, 2019
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 36*
Look yazeed ni bawai haihuwa bane banaso,matsalarta ne banso. Yanxu daga na aihu shikenan zan tsofe inyi loosing shape kuma I will be less attractive balle kai na sanka Nasan yadda abinnan yake ta fadi hakan tana nuna masa wandonsa ina nan dagwas ma ya aka Kare balle na fara loosing shape,gararin ka Koma wajen wanchan yarinyar.
Murmushi yazeed yayi aransa yace to me anfanin shape din daba Mora nake ba ? Ai inkinsan wata bakisan wata ba. Afili kuwa Cewa yayi idan Kiyi loosing shape din basai ayimiki plastic surgery ba?
(haramunne fa kawai wayo yazeed keson yi mata )tace idan kuma banmakai ga rayuwaba na mutu tun a garin haihuwan fa?yace bazama ki mutu ba tace to inna haifar ma ai akwai shayarwa,ga kukan masifa,ga kashi,fitsari eww!,ga su takuri mutum. Haka dai suka cigaba in yazeed ya bullo tanan sai zakiyya ta toshe inya Koma tachan ta toshe bai Ankare ba har lokacin sallar azahar yayi.
Ajiyan zuciya yazeed ya sauke sannan yace okay bari inje in dawo ko?ko kallon Inda yake batayiba balle ta ansa shi Dan wani mugun haushi yabata saboda kawai gani take so yake ya tsufar da ita da kuruciyarta ko 30years fa batakai Ba.
Koda ta dawo samunta yayi da wayarta a Hannu tana chatting da sabuwar kawarnan nata sumayta Wanda take kira da sumy. Yadda ya barta haka ya sameta illa ma kwanciya da tayi Wanda gaba daya alamu sun nuna batayi sallah ba. To ko tayi ma ai Anyi ba ayiba tunda duk ta cika kai da braided attached hair ga uban artificial nails da tasa yazeed yace zaky kinyi sallh gyada kai tayi alamar tayi sallan ba tareda ta dauke idanunta Daga kan wayanta ba.
Takowa yayi yadan zauna a gefenta kadan sannan ya karbe wayan yana murmushi ya ajiye a gefe tashi tayi ta zauna tana ciccin magani dan ta gano Inda aka dosa shiko yazeed janyota jikinsa yayi ya riko hannunsa yana shafawa kamin a hankali cikin kunnenta yace sweetheart zakiyi tafiya na sati biyu bazakiyi missing dina bane, ta dan tureshi tace is just two weeks fa? Dan zaro ido kadan yayi yace 2 weeks din just? Gyada kai tayi yace to shikenan I think I will take the second option ya fadi hakan yana mai danyin abin tausayi tare da turo bakinshi. Kallosa tayi dakyau tace and what's the second option? Kallon hanya stairs yayi aiko atake zakiyya tahau tureshi tana Cewa ai saikaje din dama nasan halin maza,bak.......
Maganar ta nema ta rasa sakamakon jin soft lips din yazeed akan nata babu wani jan aji ta fara maida masa martani dan itama a Hannu take kan kamin kace kwabo zakiyya ta fice Daga hayyacinta.
Yazeed,hannunshi yasa a cikin gashin dake kanta yana shafawa yayinda bakinsu ke hade Dana juna. Wasu irin salo zakiyya keyi masa Wanda yasa numfashinsa fara daukewa. Magana yakeson yi mata amma ina ya kasa.
Ana cikin haka yaji zakiyya tasa hannu ta fara zurfafa sha'ani, lokaci daya wani kasala ya sauko masa dan haka cikin kwarewa ya zura hannunshi cinkin riganta. Motsi ya fara ji dan haka ya tsaya cak da abin da yakeyi kokarin Daga zakiyya yake Daga jikinsa amma batamasan yanayi ba dan kara Shige masa takeyi.
Dan gatsa harcenta yayi Wanda hakan yasa ta saki bakinsa sannan ta lafe ajikinsa tana cigaba da kokarin cire masa Riga shiko numfashi kawai yake saki.
Riko hannunta yayi muryasa Kamar ta mashaya yace zaky....kinsan fa bamu kadai bane a gidan akwai possibility masu aiki su shigo anytime ki bari mu Shiga Daga ciki.
Tana jinsa amma taji gaba abinda takeyi ko ajikinta.
Babu abinda yake maimaita mata illa wani zai iya ganinsu tun muryasa yana fita har ya fara shaking harma ya daina fita tsabar desire.
Zakiyya kam da taga ya dameta da surutu kara kamo lips dinsa tayi Kamar wata mayun waciyar zakanya.
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮
Minal kam bayan komawarta daki dudduba wayarta tacigaba dayi har taji ankira sallah dan haka ta mike ta nufi kitchen domin ta hada kununta Wanda ta saba sha da daddare tunda yau zata je gidansu zally tasan zata gaji lubus,dan haka gara ta hada abinta tun yanxu.
Koda ta fito parlour zakiyya kawai tagani kwance tana chatting harara zakkiyan ta aika mata itako tasa ke mata smile sannan ta wuce kitchen.
Aiko hakan ba karamin haushi yabata ba dan haka tasha alwashin saukewa akan Wanda ya ajiye mata mara kunyarnan agida(yazeed Kenan).
Sharp sharp ta dama kununta sannan ta Koma daki batare da ta kallo zakiyya ba.
Sallah tayi abinta ta Ciro kayan da zata saka.
Alamun rufe kofa taji Wanda for sure ta tabbatar yazeed ne wanka ta fada da niyar inata fito zataje ta sameshi ya nuna mata abubuwan Daga nan ta wuce gidan biki.
Koda tayi wanka shafa mai tayi mai sanyaiyar聽 kamshi sannan tasa atamfarta ta shafa powder da pink lipstick sai kwalliyar nata yayi making sense.
To yanxu akeyinta daurin dan kwali,ta daura ta since ta daura ta kuma sincewa dakyar ta samu tadanyi wani yadanyi ma'ana sannan tabarshi.
Dafe kai tayi sannan tace kash Ashe ma fita zanyi kuma hijab zansa,dungure kanta tayi tace keda wallahi wani zubin sai ahankali,Idan ba fita zakiyiba mai zaisa Kiyi kwalliya.
Smiling tayi tace aiko kwalliyar bazai tashi a banza ba,wayarta ta janyo.
Click!click! Ta watsa selfie abinta sannan ta tuge dan kwalin ji. Hijaninta ta janyo ta sakala a wuyanta ta fice domin zuwa wajen yazeed not forgetting to take her phone of course.
馃尮 馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮
Takun saukowa Daga beni yazeed yakeji dan haka yayi kokarin fincike zakiyya Daga jikinsa Wanda聽 ta like masa ajiki kamar chewing gum kuma alokacin tayi nasarar balle masa button 2,Kare kaimi take shima ko daddagewa yake wajen bincineta Daga jikinsa,saide kash bai sami nasarar kwakuleta ba har mai wannan taku ta sauko,cikin mutuwar jiki ya dago da idanunsa dan ganin ko Waye aiko minal ce ta kame ta tsaya cak tana binsu da wani kallon tsana,jin haushi da kuma mamaki.
Take yaji zuciyarsa ta buga Wanda shi Kansa ko zaka yankashi bai San dalili ba.
Did you like this chapter, if YES! Then don't forget to share and comment.
NO negative comments 鉁�
More comments, more updates馃槈.
Karamarsu babbarsu ce
Miss untichlobanty馃挄
27 October, 2019
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KIRUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by@mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 35*
Koda asuba tayi yazeed da kyar ya tashi yayi alwala sannan ya tafi masjeed. Da ya dawo Shirye shiryen fita aiki ya farayi yanada meeting by 7-10 zai dawo gida dan yau sai ya kwashi gara zaibar zakiyya ta tafi (or akwai matsala)tunda business appointment din sai gobe,dan haka sai 4 na yamma tabi jirgi.
Koda ya fito Daga gidan tunawa yayi da wayan minal Wanda bai bata ba dan haka ya Koma yana mai Jan dogon tsaki da bakin cikin zai Sanya wannan aljanar a idanunsa well maybe ba bakin ciki yaje ba haushi yakeji saboda banzan plan din lukman Anyway Koma wannene shidai yasan bayaso yasata a idanunsa.
Dakinsa ya Koma ya dauko wayar daga charji ya kunna yayi downloading su WhatsApp da su Instagram da snap chat sannan ya tura聽 mata katin 10k yayi sub na monthly 10GB to amma taya zai bata ?聽
Tsaki yaja yace banida time I better hurry up. Dakin zaky ya fara Shiga yace karta tafi akwai wani serious magana da zasuyi inya dawo (馃榿yazeed fadi gaskiya) inyaso saiki ni jirgi tace mortar fa yace malam suke zai kama hanya anjima,Tace okay.
Yanda tayi magana Kamar bazatabi umarnin ba dan haka yazeed yace idan kika tafi batare da izinina ba karki dawo,aiko Kamar yasani dan batayi niyan tsayawa ba amma tanajin wannan magana ta sauke duk makaman yakinta dan bata Shirya zama bazawara ba.
Komawa tayi ta kwanta tana mai janyo wayanta sannan ta fara chatting da sabuwar kawar da tayi.
Direct dakin minal ya wuceya samota tana bacci ta d'are d'are akan gado pajama ne ajikinta da rigarsa me dogon Hannu
Ahankali yazeed ya tako yazo har Inda take abakin gadon ya zauna murmushin mugunta yayi koba Komai zaiyi enjoying game dinnab sannan ya ajiye wayar ahankali ya tattaro kafar minal ya hadota sannan ya dauketa direct kan coach yaje ya zauna rugume da ita kan cinyarsa sannan yakai bakinsa daidai kunnanta ahankali yace aljana !ke aljana! motsi tayi kadan tasa hannunta ta rungumosa domin tunaninta pillow ne tace kai inna! kai inna !yaushe ma aka kwanta?
Dan gira yazeed ya Daga yana smirking irin yarinya you don't know what is going on.
Hannu yasa ya shafa kumatunta yace aljana tashi. Tsaki taja duk acikin baccin tace wallahi deeje ko ki ficemin a daki ko in mugun saba miki.
Allah yayi minal da mugun gigin bacci saide idan t芒yi Baccin ya isheta wato ya sauka akanta amma inba haka ba wani zubin har magana zakuyi amma batasan Anyi ba.
Kallon agogon hannunshi yayi yaga har 6:23am yayi kawai sai ya kamo yatsan hannunta ya gantsara mata chizo zaburowa tayi tana yin kicin kicin da alamun bala'i yayinda take Cewa wallahi yau zanga uban dazai hanani chin uw**ki a gidannan,saina Keta miki聽 rashin mutunci,wallah.......
Maganarce ta makale saboda kankamota da yazeed yayi domin kokarin sauka takeyi.
Fiskanta ne ya chanja Daga fada zuwa dan tsoro da kuma mamaki,zazzare ido takeyi Kamar ankama malam da karuwa sannan tamike a tsorace tasowa yayi zai kamota ta turo baki sannan tace;wallahi nidai karka matso niba har iska bace! Zaro ido yazeed yayi sannan ya hade rai ya finciko hannunta ya matse sannan yace ubanwa yace ki kwanta akan gado sai alokacin ta tuna Ashe tana chanja bedsheet tayi bacci saboda yayi kura tunda ba hawa kai take ba.
Ba Kare kai straight forward tace kayi hakuri gyara gadon nake bacci ya daukeni, gyada kai yake da ma'ana biyu;
1.ya gane Cewa ba da gagan tayi bacci akan gadon ba.
2.yayi accepting apology din.
Yace kinsan wani Abu?ta gyada kai yace saboda kin bani hakuri ba tare da mishkila ba Daga yau na yarda kina kwana akan gadon.
Washe hakora tayi tana grinning like a fool tace l芒 dama kanada kirki ?ai na dauka .......sai kuma tayi saurin safe bakinta tana zare ido na abinsa ta fada dan batas么 y芒 fito Fili ba.
Matsowa ya karayi kusa da ita ya bata kwas yace da dance banida kirki ne?ina dai yin kirki nane ga Wanda yakeso. Hope kin gane ? Gyada kai tayi tace amma inada magana
Gira ya Daga alamun yanajinta,tace dan Allah idan kanayimin magana kadan dinga anfani da kalmomin turancin masu sauki.
Dan daure fiska yayi alamun nazarin yaushe yayi using complicated word ? Dan ware idanu yayi alamun ya gano yace hope dinne complicated word?tace to ai ka kara sani duhu menene complicated kuma ?yace oh. my. God! Kinyi makaranta kuwa?murmushi tayi sannan ta gyara tsayuwa tace ras! Har SS 3 ma kuwa. Jijjiga kai yazeed yayi.
Aransa yace I wonder how your teachers will be like kara kallon agogonsa yayi yaga har 6:39 yayi wayan yayi saurin daukowa yace ke ni ungo dallah banson shashanci wayace akwai Komai a ciki abinda baki ganeba ki nunamin sanda nake free Washe baki tayi tace Toh nagode Allah ya saka ya kuma mayar maka fiye dashi murmushi yadanyi domin yaji dadin addu'ar nata
Yace kin tana rike babbar waya kuwa ta gyada kai wani karfin guiwa ta samu na Cewa a dawo Allah ya kiyaye.
Alokacin har yakai bakin kofa kasakasa yace Ameen ransa wasai Daga damuwar jiya amma bai nuna ba.
Hade fiska tayi tana mai mamaki kamin ta tabe baki tace kaika jiyo mutum Kamar me aljanu yanzu yanzu sai ya chanja Kamar yama sunan abar?.... Emm...yauwa chameleon.
Washe baki ta karayi sannan ta dale gadon ta a guje tana mai bude kwalin wayar wow!masha Allah !wayyo Allah na wannan tawace?Allah na gode ma wayar mai kyau ni yanxu ko a mafarki akacemin zan sami wannan wayar a rayuwata ai bazan yarda ba kai Alhamdulillah kawai sai ta fara kuka su inna ta tuna tace bari anjima in rokeshi wata kila ya bari inje.
Wayar ta fara dubawa babu Komai a contact sai number din mom.
Camera ta Shiga ta dauki selfie kwalli daya tana turo kanta gaban cameran dan haka Rabin fiskantane ya dauku ga ranan hantsi ya dan hasko kumatunta abin sai yayi mugun kyau.
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
Yazeed ko a cikin mota a hanyarsu na meeting yayi shiru yana tunani Wai shin anya kuwa minal zata yarda da abinsa zaizo mata dashi ? Anya kuwa bazai bari yabi shawarar lukman ba batare da ya chanja ba?luku yace kawai su fahimci juna inyaso su hada gado da yardar yarinyar amma shi matsalarsa kenan kwanciya da Itan. Anya bazata masa ganin mahaukaci ba idan yace ta ara musu mahaifarta? As a surrogate mother? No !no! yazeed kar kayi haka.
Tsaki yaja yace bari kawai in zubawa sarautar Allah ido, amma na fasa kudirina.
Lukman ne yace boss yane yace ba Komai okay kawai luku yace dan ya fahimci abokin NASA is not in the mood.
10:15AM
Yazeed a mota Suna dawowa gira wayarsa ya zaro yayiwa zakiyya message cewa gashinan a hanya.
Yana dawowa ya samota parlour tana shan kanshi tana daddaga kai tana huhhura hanchi ita adole ga matar manya. Hannunta ya riko yana bata side hug yace Ashe zaki taroni dan smiling tayi kamin suka zauna a rants tana Cewa Koma wace magana ce Indai ba zancen zai bata white pradon bane to is useless.
Minal ce ta sauko domin ta fada masa batasan yadda zata buds au account din Instagram ba
Zakiyya cikin kallon wulakanci da kaskanci da nunawa dan Adam shidin ba kowa bane tace ke zonan.
Sumul sumul minal tazo ta tsaya adan gefe dan she is not in the mood to create a scene ga kuma yazeed ya kafeta da idanu.
Tace gani tana mai kafeshi da dogon kallo. Zuciyarsa ce ta buga na zakiyya ko girgiza yayi dan har wani tsorone ya shigeta saboda yadda minal din tayi maganar.
zakiyya tayi witnessing kallon da minal kewa yazeed amna bataga na yazeed ba dan haka zakiyyan tayi kwafa tana aiyana yanda zataci ub*n minal inta dawo sannan tace ni zanzo in sameki ne ko me kuke nufi ? Banson iskancinnan naku fa irin na talakawa.
Ran yazeed yayi mugun baci da yanda zakiyya ke gayawa minal magana dan haka yace baby ya isa mana me mayasa kika kiratane ?
Harara ta bankawa minal sannan tace ki kawowa MY LOVE coffee kuma saura ki tsaya kina tafiya Kamar tsutsa.
Minal aranta tace Nasan dan kinga idon mijinki ne kinsan bazan'kiyi ba da Kinyi kadan ki sani aiki wallahi tunda ke bakisan me ake kira da mutunci ba kema bai dace a mutuntaki ba, dadinta ma dai aikin mijina zanyi.
Kitchen din ta Shiga ta hado sannan ta kawo,bata 'kara kallansu ba ta hayewarta sama tana maijin haushin yazeed din. yana gani akaci fiskanta amma baiyi magana ba
kallon zakiyyan yazeed yayi yana dan smiling dukda ko izuwa yanxu tsoran answern dazai samu yake聽 yace baby I....uhm...hhhhh I need a baby!
Kallonsa tadanyi fiskanta a yatsine a lamun confusion tace you already have one, ko baby ka kirani ba ?....... Just wait a minute !do you mean kanason wanchan aba.....
Datseta yayi ta hangar Cewa no!d'a nakeso
Ajiyar zuciya ta sauke tace matsalar da dan sauki.
Hello team yaznal and yazya hope kuna lahiya? by the way did you like this chapter?
Don't forget to COMMENT.
See yah馃槝
Miss untichlobanty馃挄
26th October, 2019.
0 comments:
Post a Comment