Ido cikin ido minal da yazeed ke kallon juna, wani irin kallo ya banka mata aiko ga mamakinsa ta mayar masa da harara zakiyya ko bata masan Anayi ba dan kokarin zuge zip din wandon captain ma takeyi.
Tabe bakinta tayi,taja tsaki sannan kasa kasa cikin makoshinta tace Yan iska kawai duk dakunan gidannan bai isheku ba sai kunzo nan?
Karaf maganar ta fada kunnen yazeed minal ko juyawa tayi tafara Komawa sama cikin muryarsa dake fita dakyar yace ke.....
Juyowa tayi tana yatsine yazeed yace me like Cewa zaro ido tayi Adan firgice dan bata yi expecting dinshi yaji maganar ba聽 domin kuwa can Nasan makoshinta tayisa Wanda ko ita da tayi kunnanta basu jiyo da kyau ba.
Tsurewa tayi muryarta na rawa tace nifa bance Komai ba. Yace kizo nan yafada yana nuna mata kusa dashi da hannunsa yayinda yake kokarin mikewa da zakiyyan manne ajikinsa.
Wani abu ne yatasowa minal ya tsaya mata a makokoro ganin sunki rabuwa da junansu itako zakiyya sai faman romancing din yazeed take dukda ko alokacin ta fara gane abinda ke wakana amma ganin Cewa halittar da tafi tsana ce yasa tacigaba da aikinta dan wani feelings takeji Wanda bata tabajin irinsa ba.
Abinda bata sani ba shine acikin juice din da sabuwar kawarta sumayya ta bata jiya da yamma kamin ta dawo gida akwai maganin kara desire Wanda zai fara aiki after 15 hours domin ko sumayyar year lesbian ce kuma ta mutu a son zakiyya,toh plan dinta shine tunda tare zasuyi tafiyar sai tayi using din wannan to her advantage amma yazeed ya rusa mata plan.
Ko dazu ma sanda suke chatting zakiyyan fada mata takeyi Cewa ansami chanjin plan Wanda ranta yayi mugun back kuma bata so ba.
Bazaki zo ba? Ya fadi hakan Adan tsawace yana daure fuska.
Jikinta ne ya soma karkarwa bakinta na rawa idanunta ya ciki da kwalla tace zanzo amma wallahi ni tsoro nikeji.
Yace okay tunda ke bazakizo ba ni bari Nazo da kaina daidai lokacin zakiyya ta sami daman zuge masa zip din wando tare da yin kasa dashi Allah ya taimaka akwai boxers .
Aiko minal ta saki kara da gudu tayi sama shima ko ya tattaro duk karfinsa ya fincike zakiyya ya rufe zip dinsa sannan yabi bayan minal din koda ya iso bakin side dinta gani yayi ta kulle. Knocking yayi yace ki bude minal tayi mirsisi.
Murmushi yayi ya Koma side dinsa da Sauri ya Shiga parlourn sa. Inda gaba daya Anyi tiling yaje ya danna wani Abu Kamar makunnan wuta atake wajen ya bude wani Dan siririn corridor ne ko da ya kure corridor din kofofi 3 daya a hagu daya dama daya kuma a gabansa.
Na hagu shine back door na part din zakiyya, na tsakiya kuma na minal sannan na dama na mom kenan back door din mom yana kallon na zakiyya.
Bude na tsakiyan yayi ya Shiga kofar dakinta ya karasa yaji shima ta garkama masa key date kai yayi sannan ya zauna a kujera sai lokacin ya da part dinta Komai tas sai kamshi yakeyi.
Zafi yaji part din nata sai yaga AC a kashe tashi yayi ya kunna sannan ya dawo ya lume a kujera.
Minal ko jin ya dena knocking kusan 10 minutes yasa ta bude kofar dakinta a hankali tana leken kofan side din nata sannan a hankali tana sanda ta fito ta nufi kofar dan bata lura da yazeed Wanda ya lume cikin kujera ba.
Shiko yazeed tun fitowarta ya ganta binta yake da kallo wani Abu na tsarga masa a jikinsa Wanda ya ajiyeshi a matsayin sha'awa .
Bakinta kofan ta karasa ta takama key din ta murda a hankali handle din ta kama ta bude ta leko da kanta taga empty murmushi tayi tana shirin komawa taji an rungumota ta baya.
Ihu ta tsala Kamar yadda wasu mata keyi Idan 'kadangare yayo Kansu da gudu sannan ta daka tsalle zata antaya a guje馃榿. Da Sauri yazeed ya janyota baya sannan ya mayar da kofar ya rude yana mai lafta mai key.
Ihu ta kara tsalawa yazeed yayi sauri yasa hannunsa ya rufe mata baki sannan ya janyota tsakiyar parlourn.
Kokarin kwacewa ta somayi amma taji kyam saboda rikon oga yazeed ba wasa ba ko namiji karyarsa balle ita dukda ko ita ma ba wasa ba. Shima yazeed din yayi mamaki dayaga tana iya fiffincika domin inya Rikeka 'kwa'k'kwaran motsi ma gagarar ka yake.
Sakin jikinta tayi shiko yazeed ganin ta saki jikinta yasa ya sassauta rikon da yayi mata aiko ta gatsa masa cizo sakinta yayi yana yarfa hannu dan cizon ta ratsashi,guduwa minal ta soma kokarinyi aiko yazeed ya fincikota sai suka fada kan kujera. Zaro idanu minal ta somayi domin jinta da tayi a faffadar kirjinsa yayinda ta fara Shiga wani irin yanayi.
Shima dai haka takasance ta bangaren sa saide shi lumshe idanu yayi domin jin tsayaiyun breast dinta a kirjnsa.
Zakiyya ko dake general parlour koda taji minal na tsala ihu murmushi take tana jin dadi sannan tace thats my baby kaci ub*nta,yarinya zaki gane da yazeed kike tunda kika datse masa jin dadi tashi tayi dakyar聽 taje ta fara shirinta ranta wasai.
Koda ta gama shiryawa babu ko sallama tayi airport dan already yazeed yayi booking mata,sumayya ta kira sannan suka nema mata itama. Ta zamu first class din amma akwai mutane 4 a tsakaninsu.
Haka suka nemi wani Dan snacks a airport din sukwci kamin 4 tayi suka Daga izuwa birnin tarayya even though it is not a long journey.
馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮
Abangaren su minal kuwa yazeed yasa Hannu yana shafa fiskanta tsilli tsilli tayi da ido tana kokarin mikewa kara rikota yayi ta turo baki tace ni kabarni in tashi.
Yatsa ya daura a bakinta yace shiiii...
Me yasa kika fito?hararansa tayi Adan tsorace sannan ta kara zunburo baki tace to Ba Kaine kace duk abinda ban ganeba a wayan in fada maka zaka nunamin, to sabida zan tafi gidansu zaliha sai nace bari inje alokacin.
Yace ehmm cigaba tace to shine.....ina fitowa shine...
Sai kuma tayi shiru yace shine me?
Tace shine na...ganku...a parlourn....kunayi.
Yace Muna me ? tayi shiru murmushi yayi wanda ya kara fito da kyawunsa yace me mukeyi murmushi tayi tadan kamo hannunta tana wasa dashi tace ai banyi kama da yar iska Ba balle in fada. Yatsansa yadan sa ya dalle mata baki yace to su Waye Yan iska?Idonta ne ya ciko da hawaye ta turo baki sannan ta fara gunjin kuka tace dama kawai kace zali na kakeson ci. Ni kawai ka nuna min yanda zanyi infara su insaram din.
Daga gira daya yayi yana murmushi bata rai tayi ta hade gira tace ni kadaina mini irin haka nifa Ba yar iska....
Daure fiska yayi yace banson jin wannan Kalmar iskancin kinji ko?ta gyada kai yace ina wayan naki? Tace yana daki yace oya dauko to.
Yaga bata tashi Ba yace ko bakison in nuna miki ne?tace to hannun ka sai Alokacin ya lura da yadda ya riketa. Sakinta yayi ta tashi atare suka sauke ajiyan zuciya.
Jikinta a sanyaye ta Shiga dakin yayinda yazeed ya hadiye wani yawun jaraba 'kutt !
Hala WhatsApp people did you like this chapter?
Show some by COMMENTING
Your one and only
Miss untichlobanty馃挄
28 October, 2019.
WAIT OO INADA TAMBAYA WAI DAN ALLAH ME YASA KUKE TSORAN KADANGARE?
KOWA TA FADI AMSANTA.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by@mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 38*
Dauko wayar tayi ta fito nuna mata gefensa yayi tazo ta zauna karban way an yayi sannan ya bude mata gmail as Mrs yazeedjeedmar@gmail.com yana nuna mata. Instagram account ya bude mata shima as Mrs_yazeed_jeedmar. Tunani yake why ma yaje using mata identity dinsa? Ganin bashida answer yasa ya share. Bayan sun gama ya miko mata wayan yace Toh da fatan dai kinsan illolin social media ko?gyada kai tayi sannan tace ana wayar mana dakai a islamiya ai akan illolinsa yace good you should be careful karkina rubuta Komai kinji ?ta gyada kai yace kinga na bude mini Komai da sunana ne Dan haka ko me kikayi ni zai shafa tace Insha Allah zankiyaye bazan bata maka Suna Ba yace good girl.
Turo baki tayi tace ni Ba girl bace Dan zaro ido yayi da alamun tsokana yace kin zama big girl kenan ta gyada kai da alamun sakarci.
Murmushi kawai yayi ya girgiza kai shikam bil hakki da Gaskiya inyace minal na bashi haushi a halin yanzu karya yayi.
Saide yasani har yanxu baya Santa kawai dai yana kokarin ya fahimceta ne Kamar yadda luku ya bashi shawara.
Mikewa yayi zai fita minal ta riko hannunsa wani electric shock yaji itako minal da bata ma lura Ba giranta Adan hade tace Toni insaram dinnan kace hotuna ake posting ko ? Yace eh tace to naji ance insaram kuma Nide a sanina ram ragone toh Wai hotan rago ake sawa?
Dariya yazeed ya fashe dashi harda kama ciki sannan yace wayace miki insaram ne? Instagram akace, murmushi tayi tace au Ashe ma da sauki instaram ne Ashe,yazeed yace Instagram Ba instaram Ba minal ta turo baki tace Koma wannene.
Yazeed yace kawomin ruwa toh tashi tayi ta fita shi kuma ya shige dakinta bayan Kamar minti daya sai gashi ya fito. Wajen ya nema ya zauna koda ta kawo masa ruwan sip daya yayi ya ajiye.
Bubbuga ka minal tayi tace yanxu Dana akan murna daya shine kasani harna sauka kasa? Hararanta yayi yace ke banson raini fa karkiga ina sake miki fiska, bankai insaki bane ko me?
Tace Allah baka hakuri, ni yanxu dai bari inwuce. Yace okay batare da ya kalleta Ba. Dan turo baki tayi tace Dan Allah ka barni inje inga su innata yace bazaki bafa wallahi ko kofar gidan bikin kika fito bada kwakkwaran hujja Ba nida ke ne.
Hade fiska tayi tana huhhura hanci alamun ranta ya baci sannan ta saki hannunsa Wanda batasan ma tana rike dashi Ba.
Dakinta ta shige ta dauko su Jakarta da hijabinta ta Shirya sannan ta fice. Koda ta fito baya parlourn nata. Idonta ne ya cicciko da kwalla tace ni wallahi inason inga babana.
Gidansu zaliha ko ya cika makil da mutane,anata shiryen shiryen kamu.
Zaliha Kam duk tarin kawaye da Yan makarantansu da sukazo Ba agabanta suke Ba Dan tun safe take tsitstsilla ido ko zataga minal amma shiru har gashi yanxu 4 ya kusa har an fara tafiya venue din kamu.
Cika ta farayi tana batsewa domin ko lokacin bikin minal tun asuba take zuwa gidansu.amma ita yanxu har za'a fara biki batazo ba,saka da warwarar irin rashin mutuncin da zata kaftawa minal takeyi, aiko yar halak sai gata ta fado aguje tana Cewa Allah sarki aminiyas kema dai kin kusa Shiga Daga ciki.
Harara zaliha ta rafkawa minal tace me yakawoki gidan mu? Minal tace kai yar uwa Nasan Nayi laifi kimin uzuri mana amaryar Sulaiman.
Murmushi zaliha tayi dadi lokacin aka fara聽 Cewa Amarya da tawagarta su fito.
Kamu yayi kyau saide masha Allah domin ko Sulaiman yayi kokari sosai.
Minal ko hotuna taketa dauka amma baifi guda uku tayiwa kanta Ba kuma yayi kyau sosai.
Yazeed Kam minal tana fita ya wuce dakin zakiyya wayam ya gani babu ita babu alamarta, dunkule hannunsa yayi ya naushi gini atake gumi ya fara tsatstsago masa, duk target din daya gama wato wannan yarinyar ta rusamai ita? Kwanciya yayi a gadon zakiyyan ido lumshe yana nazarin yadda zaiyi da matsalarsa.
Bude ido yayi domin wata idea da tazo masa ya dau key ya fice, wani pharmacy yaje ya siyo sedative sannan ya dawo gida ziciyarsa fess.
Kitchen ya shiga da sedative dinsa ya zuba mata a kununta聽 sannan yace ai Kinyi kadan Yan mata,yau yadda na gama shiri na zan more kikayi ruining min,to akanki zan rage zafi. Tsaki yaja yana mai jin haushin irin kwabsin da minal din tamai kamin yace asha jagwalgwalo lafiya sannan ya fice.
Dakinsa yaje ya dauko CCTV dinsa ya fara kalla Kamar kullum zirga zirgan minal din yake kallo dukda ko badan wannan yake kunna TV dinba domin baya ma kallon nata part din ko ya kunna saboda acewarsa baiga abin kallo a rayuwarta Ba. saide ya kalli na sauran wurare especially gate area.
Yaukam tsintar kansa yayi dason kallon nata part din na kusan wata hudu kenan Wanda bai kalla Ba
Kallo yake yana forwarding domin kuwa yawanci shirmenta ne ko yadda take laftar abinci,murmushi kawai yake aransa yana Cewa wannan yarinyar Ba badai shiririta Ba wannan loma sai kace kato.
Dariya ya fashe dashi yace bata yau zan tsokaneta. Dariya ya kuma fashewa dashi yace kash saide gone zan tsokaneta Dan yaukam.......
Kallonsa ya cigaba dayi har lokacin da yayi gamo da abinda ya Daga masa hankali
Minal ce tsaye kaban madubin ta ta bude towel dinta tana kallon yadda kirjinta ya kuma ciccikowa,murmushi take saki domin itafa bilhakki da Gaskiya kyau takeyiwa kanta gyara towel din tayi ta gaba sannan ta juyi ta baya tana kallon yadda mazaunanta suka cika.
Babu shakka ko ba'afada mata itadin kyakkyawa ce.
Nunfashin yazeed ne ya fara daukewa Dan haka yayi saurin yin forwarding dinsa zuwa washegari shima data fito Daga wanka聽 same thing tayi haka yazeed yayita forwarding harna sati wasu abin su bashi dariya wasu kuma su Daga masa hankali su sashi yin zafafan muhawara da zuciyarsa.
Jinjina kai yayi yace wato abinda yarinyarnan keyi kenan in Anyi magana tace wa mutane Yan iska, hmm to yaude za'a Kare iskanci.
Koda ta dawo gida ta gaji lubus a parlour kasa ta zube tana lumshe idanu, tunowa tayi da kununta aiko da wuce direct kitchen ta cika cup tana yiwa Allah godiya dayasa ta dama kunun kamin ta tafi.
Dakinta ta haura tayi sallan isha'i domin tayi magrib acan,kayan bacci tasa ta kunna tv ta dane gado tana jin dadi yau zatayi bacci mai dadi. Kishingida tayi sannan ta dauko kununta tanasha aiko babu bata lokaci bacci yayi awon gaba da ita
Yazeed mafa yana yiwa Allah godiya da kika dama kamin ki tafi.
Fans what's your favorite part Anan chapter din?
Miss untichlobanty馃挄
2nd November, 2019
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 39*
Yazeed zaune dakinsa yana aiki a laptop dinsa.
Jin Kamar an rife babbar Koran parlour yasa ya kunno CCTV dinsa.
Na parlourn ya fara gani aiko minal ce zaune kan kujera da alamu ta dibo gajiya can yaga tayi hanyar kitchen Dan haka ya Koma na kitchen ganinta yayi tsaye tana diban kununta yace great! Insaram kina saukaka min aiki.
Gani yayi ta fice dan haka direct na side dinta ya wuce babu jimawa sai gata tashigo.
Kofar parlourn nata tasawa key sannan ta Shiga dakinta ta rufe Ba tareda tasa key ba.
Sallh tayi sannan ta kunna TV ta haye gado tana mika da murmushi alamun farin ciki.
Kishingida tayi sannan ta janyo kununta ta fara sha gani yazeed yayi ta fara zazzare ido tana dunkulewa can kuma sai tadan zabura haka takeyi once in a while har tasha Rabin kununta Inda ta bingire da bacci.
Muhawara me zafi yazeed keyi da kansa after Kamar 10 mins yasan lokacin maganin ya tsumata ko yankata zakayi bazata tashi Ba.
Tashi yayi yabi ta secret way dinsa har part din minal tare da spare key din room dinta just in case ta rufe.
Babu wata wata sai gashi a cikin side minal dakinta ya Shiga zuciyarsa na bugawa dukda ko Ba laifi yaje shirin yiba.
Ahankali yake dago kafarsa har ya iso Inda take jingine yana kare mata kallo ahankali yaki hannunsa zai tabata amma ya kasa,kawai sai ya zuba mata idanu yana cigaba da kallonta yayinda zuciyarsa ke tsananta bugawa
Tunani ya farayi karfa yaje ya fara son yarinyarnan,yar siririyar tsaki yaja yace yazeed why are you thinking about the impossible?
Tv din ya kalla yaga horror film take gani,wato shine dalilinta na tsurewan kennan.
Kashe TV din yayi yaje kitchen ya dauko coil paper ya rufe mata kunun.
Dalewa gadon yayi yama rasa mai zaiyi can ya tattaro jarumta ya kamo bakin riganta ya fara ja a hankali har ya ida dagashi. Idanunshi ne suka sauka akan fresh kirjinta Wanda suke farare fess kuma a tsaye kyam sai sheki suke.
Zuciyarsa ta buga dumm yayinda ya ja wata numfashi wadda taki fita Nadan wani lokaci wani gumi ke karyo masa,jiyake Kamar AC da fan din dake dakin basuda anfani.
Sosai ya birkice hannunsa na rawa yake romancing dinta, itakam minal da batasan ya ake ciki Ba sai kankameshi takeyi.
Ahankali yafara yawo da harshensa a wuraren wuyanta yana dan gaggatsawa leaving聽 Hickeys .
Kissing dinta ya farayi a lips aiko wasu abubuwa ke taso masa tun Daga tsakiyar kai har kafansa. Wani taushi ne da lips din na daban saide koda yayi kokarin zura harshensa cikin bakinta kin budewa tayi.
Sosai ya murza minal din sai wurin 2am ya hakura yayinda ya rage zafi.
Toilet dinta ya Shiga yayi wanka sannan ya fito koda yazo yana mayar mata da Riga rungumosa tayi tana Cewa waiyo codon zai cinyeni kokarin zareta yayi amma ta makale,saide batasan wata wutar take rura masa Ba dakyar ta sakeshi aiko ya wuce dakinsa saboda gudun kar a sani matsala.
Washe gari koda minal ta tashi taga ta bata jikinta bata kawo komaiba dan batama lura da sauyin discharge din Ba atunaninta normal discharge amma abinda yadan daure mata kai shine daya bushe yayi kanzo.
Basarwa kawai tayi abinta tayi wankan tsarki sannan tayi alwalarta tayi sallah saide wani mugun kasala takeji da dan ciwon jiki Wanda ta barshi a matsayin ta kwanta Ba daidai bane tunda dama tana kallo tayi bacci.
Sai alokacin ta tuna da da kununta sannan ta lura TV a kashe,Daga kafada tayi sannan tace watakila cikin gigin baccinnan nawa na kashe.
Kanta ne taji ya Sara mata kawai sai ta zauna a bakin gadon,janyo kofin kununta tayi zata sha sai taga an rude mata coil paper.
Dan gira ta hade Dan bata tuna sanda tayi hakan Ba amma to batada wani answer da zata bawa kanta.
Budewa tayi ta kurbi abunta sai taji bazata iya sha Ba saboda sanyin da yayi.
Jikinta taji ya fara yin weak sai ta barshi a matsayin gajiya ne. Mikewa tayi aiko luuu ta Koma ta fada gado sai bacci.
YAZEED ko yau yaje planning zasu sabon gidan daya ginawa iyayen minal Wanda dakyar da sudin goshi suka karba Suna godiya sannan ya bawa baban aiki a daya Daga cikin companies dinsa dake dealing da engines na mota.
Ya abubakar ma antanada masa aiki yana gama makaranta zai fara.
Gidan dai daya Gina mom ce tasashi amma aikin daya nasu yin kansa ne domin tun alokacin da mom ta tursasa masa yaje ya gaida surukansa ya fahimci Cewa sudin mutane masu dattako da wadatar zuci, kuma taji sun kwanta masa shiyasa ya fita Daga harkar minal din watannin da suka wuce Dan darajarsu ne.
Shiru shiru har 12 minal batazo Sharan dakinsa Ba. Mamaki ne ya kamashi to kodai maganin bai saketa bane?to amma ai 6 hours kadai zaiyi yana aiki. CCTV ya kunna yayi forwarding duk abinda ya faru Daren jiya playing yayi lokacin dayaga ta tashi sallah yaga tayi tazauna a bakin bed dinta da alamun confusion a fiskarta saboda yadda ta hade gira.
Kunun yaga ta kurba harde izuwa sanda ta dungura ko motsi bata yi yace no wonder.
Tashi yayi ya tafi dakin aiko ya samota tayi Dane Dane akan gadon.
Kafarta ya daura hannunsa zai tasheta yaji wani taushi,shikam mamaki yakeyi yadda minal Sam batayi kama da yar marasa karfi Ba.
Bubbuga kafarta yafarayi yana Cewa insaram,ke insaram tashi.......
See you soon, hope you enjoy?
Miss untichlobanty馃挄
3 November, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 40*
Janye kafarta tayi Ba tare da ta bude idonta Ba tace banaso....
Hannusa yasa ya janyo kafar yace tashi mana.
Kallonta ya tsaya yi fuskarsa Adan daure yayinda itako ko ta motsa sai ta lumshe ido ta bude ahankali tana kallonsa cikin wani irin kasala da yauki tuni ya soma kuncewa gaba daya, sai ya jishi on.
Wani siririn murya tasa mai gigitarwa tace ina kwana ?
Hararar ta yayi yace me ya hanaki zuwa aiki? Dan yatsine tayi domin wani mugun sarawa da kanta yayi tace kayi hakuri banajin dadi ne shiyasa.
Dariya ta bashi sannan ta Dan bashi tausayi ganin yadda take Abu don atunaninta jinya ne amma sai ya maske Dan karta kawo masa raini inya sake mata dayawa. Yace I don't care...kamin in rife idona in bude ki wuce daki ki sameni bai ko jira amsarta Ba ya ficewarsa.
Cike da mamakin irin halin mahauniya na YAZEED ta mike a daddafe ta nufi dakin NASA domin ta samesa. Kallon me kika tsaya yimin a bakin kofa ya wulla mata ta shigo tana Dan tangadi domin jirin dake dibarta.
Russunawa tayi a gabansa yace wato kina jira inje in tunasar miki aikinki ko?me ya hanaki share min side?
A hankali ta dago zaka rantse cutar ke damunta tace nace banajin dadi ne shiyasa inajin fever ke damuna.
Batayi aune Ba taji hannunsa akan goshinta kamin ya tana wuyanta.
Harara ya harba mata yace karyar banza lafiyarki kalau. Tace wallahi banajin dadi muryarta har rawa yake sanda take magana idanunta sun ciko da hawaye.
Dariya yazeed ke sonyi amma ya dake yace I don't care just get to work nemo tsintsiya.
Tashi tayi Adan fusace zata fice yace zonan ta dawo ta tsaya tare da kauda kai.
Yace for your punishment Daga yau ko wani Daren Allah sai kinmin tausa kinaji ta gyada kai yace good zaki iya fara sharan.
Hanyar kofa ta nufa yace ina kuma zaki tace tsintsiyar zan dauko yace dawo na manta ne jiya nasa lukman ya kawo min machine din da yake share dakina so you don't have to use broom.
Kallonsa ta tsaya yi batareda ta motsa Ba sai aloiacin ya tuna Cewa yayi using English ne Dan dafe goshi yayi aransa yace Imust find a way out ma wannan yarinyar dama yana daya Daga cikin hakkinta in ilmantar da ita.
Da Hannu ya mata alamun tazo matsowa tayi ya nuna mata wani lungu da yatsarsa yace zakiga wani Abu mai dogon baki Kamar na giwa dauko.
Dauko wa tayi ya nuna mata yadda zata kunna, ya ce gwada in gani gwadawa tayi tana Dan murmushi saboda har yanxu weak take jinta. Nuna mata yadda zata yi control din karfin yayi shima ta gwada.
Saboda karambani irin nata Kurewa tayi takai yatsanta wurin aiko taji Yana shirin zu'ke mata yatsa,janyewa tayi da Sauri tana Cewa waiyo Allah zai cinyemin yatsata.
Yazeed just chuckled and said da wa yace kikai hanunki wurin? oya kawo kiga yadda akeyi nuna mata yayi sannan yace Kiyi Sauri ki gama ki Shirya zamu fita. tace yaunefa auren zaliha yace ina sane da hakan. Dan turo baki tayi Dan gani take yazeed kawai so yaje ya kuntata mata. Tace to ina zamu? ya shhhh and work .
Kara turo bakin tayi kamin ta fara aikinta.
Bayan ta gama aikin zata fita yace karki batamin lokaci ki Shirya yanxu tace Toh
Tana fita shima ya Shirya cikin shaddarsa sky blue sabuwa fil da ita,ya feshe jikinsa da turare sannan ya kafa hularsa dinkin buhariyya amma mai tsadace saide bana almubazzaranci ba.
Chas ya fito dashi Kamar shine angon sannan ya fito domin har 1 tayi kuma 2:30 za'a daura auren.
Koda ya fito bai ganta ba Dan haka ya nufi part dinta dai dai ta rufe kofar kenan juyowarta keda wuya sukayi karo kallon kallon su kayi for what seems like eternity kamin yazeed yace muje ko? Tace yo Toni ka sakeni kullum sai kana wani rirrikeni sai kace na maka kama da yar iska.
Dalle bakin yayi yace ba kace banson jin wannan Kalmar ba? Tace toni Toni.....sai tayi shiru yace toke me? Tace babu kayi hakuri sakinta yayi sannan ya kamo hannunta suka fito.
馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮 馃尮
Lukman ne rike da takalminsa a Hannu yaji wani mummunar faduwar gaba.
Hazbiyallahu wa ni'imal wakil yace sannan ya goge black covered shoe dinshi ya fara sawa.
Sanye yaje cikin farar shadda kal harda babbar Riga wadda zubinsu kusan daya Dana yazeed ne. Kallon karshe ya karayiwa dakinsa daya banbanta Dana sauran kuratan sojojin yayi domin tabbatar da komai tsaf yake sannan ya fice domin shi da yazeed su halarci daurin auren Suleiman da zaliha. Sauri yayi ya rufe kofar dakinsa yana mai Cewa bari in hanzarta kafin uban complain dincan ya fara.
Koda ya Shiga motar da zasu tafi
Ya share kusan 30 mins amma shiru babu alamarsu Dan murmushi yayi yace sh*ge mutumi na yana can ya makalewa yar mutane in Anyi magana yace bayaso.
Nazarin irin kirkin abokin nashi ya fara tun Daga gidan daya canzawa parents din minal da gudun muwar kayan dakin daya yiwa zaliha da yadda ya hadawa sulaiman dinma lefe ya bashi dukda ko dakyar da sudin goshi Sulaiman din ya karba sannan ya Sanar da ahalinsa yazeed dinne yamai suko sai godiya suke Suna sa masa albarka.
Jin an bude motar yasa ya Dan firgita tare da Cewa sannu da fitowa amarya.
Yauwa sannu ina wuni ta fadi hakan Adan kunyace.
Yace lafiya ya gidan da maishi?
Bata amsa ba yazeed yayi knocking glass din window din lukman din. Lukman dinma ya fahimci matsala Dan haka ya fito ya bude masa kofar sannan ya Koma.
Koda suka Shiga yazeed yace shine Dan wulakanci zaka tsaya kana yiwa matata wannan surutun naka ko?lukman yace sorry sir! Yazeed yace kai ni karka wani cemin sir sai kace saniya.
Dariya minal keson yi amma ta cinyeshi.
Yazeed yace ke ta juyo yace kinsan wannan? ta gyada kai,yace wayeshi tace driver dinma ne yace Toh point of correction amini nane.
Zaro ido tayi zatayi magana yace rikewa kanki tambayoyinki Dan bazan iya a amsasu ba, kai luku muje dayan wajan.
Kunna motan yayi domin ya gane me yazeed ke nufi sannan ya figeta a guje minal bata shiryaba ta rungumo yazeed tana zazzare ido shiko wani sanyi gabobinsa sukayi Kamar ammasa wanka da ruwan sanyi.
Gaba daya abinda ya faru jiya ke tariyo masa tsab aiko yanayinsa kana daya ya sauya cikin kankanin lokaci. Lukman ko yana ganin duk abinda ke wakana Dan haka ya kara wuta yana mai kunshe dariyarsa.
Minal kam kunyace ta rufeta amma wallahi bilhakki da Gaskiya bata sakinsa dan gani take Suna raba jiki zata mutu saboda a 120 luku ke tafiya kuma dai kunsan motocin yanxu da shegen gudu.
What do you think of this chapter?
Inane yafi yi muku dadi?
Thank you and don't forget to vote.
Miss untichlobanty馃挄
8 November, 2019.
5 - CHAPTER 41-50
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮@mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 41*
A haka har suka iso sabon gidan iyayen minal, itakam ta rufe idonta kyam sai laftawa lukman da yazeed din kwandon Allah ya isa take a zuciyarta Dan gani take hada baki sukayi domin suyi mata mugunta.
Yatsa yazeed yasa ya dungure mata kai yace ai saiki sakemin Riga ko? Duk kin yamutsa Min Riga sai kace na fito Daga filin kokuwa, ko jikin nawa ne bai isheki Ba?
Bude ido tayi da sauri tare da hade fiska ta zabga masa harara kasa kasa tace sai kace wani abin arzikin ne ajikinnasa.
Yazeed yace me kikace zaro ido tayi tace babu aranta ko Cewa tayi Wai wannan mutumin aljanine ?taya akayi yaji me nace?
Wani smiling yazeed yayi yace matar aljani muje ko?
Wani numfashi me karfi taja ta zaro ido tana kallonshi tama kasa motsi.
Tabe baki kawai yayi ya fice sannan ya miko mata hannu ganin kawai kallonsa take Kamar taga fatalwa yasa ya fincikota suka fara nufar cikin gidan hannu cikin hannu.
Kallonsan kawai ta cigaba dayi shikam gabansa yake kallo yana murmushi Wanda ya rasa dalili, Ashe luku ya Ciro wayarsa yana watsa musu photo dan Ba karamin kyau sukayi Ba Kamar sune Amarya da angon.
Juyowa yazeed din yayi Dan ganin kallon yaki ya kare aiko tayi saurin kauda kai tana kyafta idanu cikin jin kunya. Aiko lukman ya kara hasko su Wanda su duk abinda ke faruwa basusan anayi Ba.
Koda suka Shiga gidan dauke da sallamar su suka zauna. A lokacin minal ta lura gidan mai mugun kyau ne. Yaba kyawun gidan take taji wata murya wadda yayi mugun tsoratar da ita dan batayi tsammanin wannan muryar anan ba. Saurin kallon wajen data jiyo murya tayi aiko Ba karya kunnanta sukayi mata Ba tabbas innarta ce sanye da super mai kyau ta kashe daurin dankwali tayi haske sai murmushi take kamin tace wanake gani haka? babban bako dan albarka zuwa Ba sanarwa ? Allah ya taimaka akwai abin naka ba bari inkawo ma.
Ah ah kace min tare kake da malam lukumanu. Murmushi yayi yace wallahi inna tare Mike ina wuni?...... Nan suka gaggaisa inna tace malan lukumanu irin wannan babban Riga haka sai kace ango Sosa kai yayi yace wallahi daurin auren classmate dinmu zamu.
Inna tace ayya Allah ya Sanya alkhairi.
Ganin Kamar inna bata lura da minal dake sankare scan kuryan parlourn Ba yasa yazeed Cewa inna bakiga bakuwar ki bane sai lokacin inna ta juya aiko minal ta gani tayi kuri tana kallon ta.
Inna tace ja'irar 'yarnan kina kallona bako gaisuwa?minal kam mikewa tayi ta fara takowa wajen innar ga mamakinsu sai ta rungumeta ta fashe da kuka haka aka lallasheta tace inna banganeba innan tace kwantar da hankalinki wato.................
Nan tayi mata bayani duk yadda akayi sannan ta kallo yazeed din tace baka fada mata bane? Murmushi yazeed din yayi yana kallon kasa yadan gyara hularsa sannan yace wallahi dama surprising dinta nakeson yi.
Inna tace dakyau aiko ta sufarasu dayawa harda kuka.
Turo baki minal tace bafa safarsu bane suprisu ne. Hararar ta inna tayi tace o ni 'yasu mai hali bata chanja halinsa, kice min bata chanza zani. To mike ki shige nan kofar ta bangaren hannun daman ki akwai聽 firji cikin akwai sobo ki dauko. Acikin drawer akwai tray saman canter kuma akwai cup ki dauko musu Toh tace sannan ta mike ta nufi kitchen din.
Koda ta kawo so'bon suna sha inna sai hira suke da yazeed da alama sun shaku, minal kam abubuwan da suka faru da ita ayau Nada wuyan shanyewa lokaci guda.
Mikewa su yazeed sukayi Suna Cewa zasu wuce lokaci na kurewa,minal din kuma sai su tafi gidan bikin tare da inna tunda itama innar zata Kamar yadda tace.
Wajen suka fita inna tace bazaki raka mijin naki bane? Tashi tayi akunyace tabi bayan su koda lukman yaga ta fito mota ya Shiga yana Cewa bari in bada guri kar adaga mini hankali da rana tsaka.
Yazeed ne ya kalleta yana mai Daga gira alamun yadai?tace uhm dama so nake nace nago....
Yazeed ya datseta ta hangar Cewa in godiya zakiyimun ki barshi dan Ba irinta nakeso Ba tace to irin wanne kakeso yace zan fada miki Ba yanxu Ba. Dan tabe baki tayi sannan tace to Allah ya kiyaye sai kun dawo. Murmushin gefen baki yayi sannan ya gyada kai ya shigewarsa mota sannan suka wuce lukman na fadin wallahi sobon nan yayi yana hajiya dashansa yazeed yace dam inajin haushinka dan wulakanci shine bayan ka shanye naka ka dauki nawa ko?lukman yace afuwan mutumina santi ke dawainiya da ni,tsaki yazeed yaja yana mai kauda Kansa izu.
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁
Abangaren ango Sulaiman Kam Sai murmushi take har yashiga dakin mahaifiyarsa cikin shirinsa na daurin aure nasiha tayi masa sannan tasa masa albarka domin kuwa Ba karamin so takeyiwa dan nata Ba cikin yara uku da Allah ya azurtata dashi wato;
Na farko Sulaiman mai shekaru 29, sai abdussalam mai shekaru 25,sai kuma fadeelah wacce take yar auta mai shekaru 17-18 kuma anfi saninta da deela ta zana jarabawarta this year.
Fita yayi ya nufi mota Inda abokansa ke jiransa domin tafiya wajen daurin aure.
Suna cikin tafiya sukayi realising ai birki bayaci nan hankali ya tashi salati suka somayi yayinda motar ke wujiga wujiga dasu akan titi kamin ta karasu da wani gini.
Allah sarki!cikin su Biyar da suka fito 2 ne suka rayu wato Muhammad da Ismail wadda akayi hospital dasu rai ahannun Allah amma ango da mutane biyu take suka cika. INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!
Allah taji kan musulmi.
Abangaren wurin daurin aure kam su ango shiru har 2:16pm.
Cikin gida kuwa mata sun cikashi dam Kamar lokacin bikin minal. Ana cikin shagali Amarya tasha kyau sai murmushi take black beauty akaji mai shela na magana Kamar haka: jama'a salamu alaikum, andaura auren malama zaliha usman da malam lukman shu'aibu akan sadaki naira dubu 80 bisa malam yazeed abdulmajeed umar amatsayin waliyin ango,kuma malam abubakar Yusuf amatsayin waliyin Amarya.
Cak kowa ya tsaya gidan yayi shiru bakajin Komai sai numfashi kamin kuma ya sake kacamewa da surutu masu tambayar Dama Ba Sulaiman zata aura bane ?nayi,Masu zagi da habaici Nayi,masu al'ajabi Nayi mai suma ma tayi nata wato Amarya.
Nan Yan daurin aure suka watse akayi gidansu Sulaiman domin jana'iza.
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁
Abinda ya faru kuwa shine ana cikin jiran ango sai..........
Kubiyoni acikin babi na gaba domin jin abinda ya wakana
Shin kuna ganin lukman da zaliha sun dace ? Yaya zaman nasu zai kasance?
Don't forget to comment and share with your friends.
Thank you.
Miss untichlobanty馃挄
12 November,2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 42*
Ana cikin jiran ango sai hayani ake ana gaggaisawa da Yan uwa da abokan arziki. Da kaga fuskokin jama'an kasan Cewa cikin farin ciki suke.
Wani matashin saurayi ne ya kutsa mutanen daurin auren sannan ya iso daidai da'iran wakilai da manyan mutane.
Sallama ya musu aka amsa sannan ya tsuguna ya Sanar dasu hatsarin su Sulaiman din.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un suka dinga maimaitawa yazeed ne ya kalli聽 lukman idonsa Adan zare yayinda shima lukman din yazeed din yake kalla.
Lallai Sulaiman ya kasance Dan clique dinsu lokacin da suke secondary wato su uku abokaine saide shi Baya burin zama soja sabanin lukman da yazeed.
Idanun su ne yayi ja musamman yazeed daya tuno yadda minal din keson aminiyarta zaliha. Yaya zasuyi in sukaji wannan labari matsala bibbiyu ga mutuwar Sulaiman ga rashin daurin auren.
Ganin Kamar wajen ya kara hautsinewa yasa suka daina kallon-kallon da suke.
Baban zaliha ne hawan jininsa ya tashi domin yasan yadda diyartasa ke mutuwan son Sulaiman din tabbas yasan akwai kaddara kuma ya zama dole yin tawakkali amma yaya diyartasa zata dauki wannan lamari? Abu daya ne mafita shine in ta samu Wanda zai kula da ita ya kwantar mata da hankali, to amma taya hakan zai kasance ? Da Kamar wuya tunda Ba bawa wani dama zata yi Ba.
Wannan tunanin yasa hawan jininsa tashi lokaci daya.
Bakinsa na rawa yace Dan Allah Idan akwai Wanda yasan in ya aureta zai iya mantar da ita Sulaiman dinta dukda ko bazata mantashiba amma dai hankalinta zai kwanta ya taimaka ya aureta.
Hawaye ne ya silalo a idanunsa yayinda samari suka dagashi suka sakashi acikin mota akayi asubiti dashi.
Yazeed ne ya kalli lukman kallon aboki ka taimaka ka aureta girgiza kansa ya alamun bazai iya Ba sannan yace yazeed kasan Cewa ayush nakeso kuma how sure are you Cewa yarinyar zata aminta dani?
YAZEED yace na sani lukman amma ka Duba halin da mahaifin yarinyarnan ya Shiga Ina ga ita yarinyar kuma?
Shin kana ganin kaf na wajen akwai Wanda ya cancanci ya aureta? Kana ganin akwai Wanda zai iya kwantar mata da hankali? sannan ya Daga mata kafa ta dawo cikin nutsuwarta kamin ya bukaci hakkinsa?
Girgiza kai lukman din yayi ya budi baki zaiyi magana yazeed yayi saurin Cewa Idan maryam( kanwar lukman din) ne acikin wannan yanayin fa?
Ajiyan zuciya ya sauke yace yazeed ni yanzu Idan ma na aureta ina zan ajiyeta ? Yazeed yace karka damu da wannan ka amince kawai lukman yace amma yazeed kana ganin nayiwa ayush adalci kuwa?
Yazeed yace India har tanasonka zata fahimta kuma ai ita dinma zaka aureta sannan Idan itace awannan yanayi ai bazataso aki auranta Ba.
Lukman yace amma..... Yazeed yace Dan Allah. Ajiyan zuciya lukman din ya kuma saukewa sannan yace shikenan na yarda.
Murmushi yazeed yadan masa sannan ya dafa kafadarsa alamun bada kwarin guiwa sannan.
Tashi lukman yayi ya tsaya sannan yace ni zan aureta.
Kallonsa jami'a sukayi, babu bata lokaci aka aminta dashi musamman da akaga Cewa shidin abokin yazeed, kuma shi yazeed din ya kasance suriki na gari.
Kuma ai masu iya magana na Cewa inkanason kasan halin mutum to ka tambayi su Waye abokansa.
Hakan yasa babu bata lokaci aka daura aure sannan akayi sanarwar jana'izan Sulaiman.
Nan hankali Yan cikin gidan ya kuma tashi aiko nan wasu sukasa kuka yayinda wasu sukayi shewa Suna fadin "ahaiye cass, yo dama anga mai Hannu da shuni an like masa anaso ashiga Dan aci bagas toh ta Allah Ba taku Ba zaliha dai anzama Amaryar lukmanu 馃榾馃榾馃榾馃榾 auren shige aka mata" wata mata tace yo danma mutanen suna da mutunci naji ance anbada sadaki naira tamanin kome? Kinsan gidan ya kacame banji dakyau Ba.
Wata tace naira tamanin ko sanda rake yafi haka shewa suka kuma sawa dai dai lokacin waliyin zalihan malam ado (Wanda akayiwa yarsa fyade #chapter 2)yayi sallama.
Iya dake sharar kwalla tama kasa magana saboda halin da diyarta ta Shiga domin tunda ta farfado ta kafe waje daya da ido Ba tayiwa kowa magana Ba sannan bata yi kuka ba, ta amsa sallamar sannan ta nufi hanyar kofa tana mai saka hijabinta.
Gaisawa sukayi sannan ya mata ta'aziyya,addu'a sukayi ma Sulaiman din sannan ya miko mata 80k cas Kamar yadda aka bashi sannan ya Samar mata yadda akayi lukman ya auri zalihan.
Godiya tayi masa sannan ta basa 10k nan fa ya rufe ido yace Sam bazai karbi kudin ba. Haka iya ta hakura ta tafi tana kara masa godiya.
Koda ta shigo ciki daki ta nufa ta boye kudin tunda kannenta guda 3 ne kawai a dakin sai innar minal. Matsowa kusa da zaliha data sandake da minal daketa aikin kuka iyan tayi sannan ta lallashi minal nan hankalin minal din yadan kwanta tunda lukman din da aka aurawa zaliha lukman abokin yazeed ne ba wani ba kuma yanada mutunci.
Nanfa suka fara kokarin saka zaliha tayi kuka amma shiru sanda innan minal ta matso kusa ta yi mata nasiha sannan tace ta rike mijin ta da amana ta danne zuciya tunda Sulaiman din ya tafi Anan tayi breaking ta hawaye suka fara zuba tahau shure shure Kamar mai tabin kwakwalwa. Ihu take tana Cewa wallahi ba mutu ba ni Sulaiman dina bai mutu ba,Nasan bazai barni ba ku sakeni,ni kusake ni.
Kanwar iya mai Suna iya murja ce ta fita sannan tace wa jama'a sun gode da halarta da sukayi.
Wannan matarnan ce tace yo ai bansan baban zaliha munafiki,Mara mutunci bane sai yanzu, Ashe batada hankali shine zai aurawa Dan mutane.
Tasss!taji an dauketa da tafi.
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁
Agidansu Sulaiman kuwa ana sanardasu wannan labari mahaifiyarsu ta yanki jiki ta fadi hospital akayi da ita Ashe coma ta Shiga.
Laila Kanwar Sulaiman rasa Inda zatasa ranta tayi. Kanin babansu Alhaji Ibrahim shi yasanar dasu wannan labari.
Lallashin laila da sauran family yake domin sunyi rashin da saiga goje(from chapter 10) ya shigo yana fito kallonsa kowa ya tsayayi
Shoki ya kwaso ya sauke sannan ya watsa zanku. Babansa ne ya daukesa da mari sannan yace kaide bansan me zanyi dakai ba da'ace a Asibiti aka haifeka da nace an canja Mani Kai, Allah ya Shirya amma ace mutum Dan uwansa ya rasu ko ajikinsa ?
Soka earpiece dinsa da yayi a kunne sannan ya kalli baban NASA yace kai tsohonnan ka kiyayen Idan ba haka ba kauna zaka raka wacan shegen Sulaiman din. Aikin banza duk kunbi kun cikawa mutane gida da kukan Munafurci.
Ke laila ki mana ko kallon Inda yake bata yi ba yace ba dake nake ba? Ta sharesa falla mata mari yayi yace ke Dan ub*nki Dan kinga anasonki shine zakiyi wa mutane hauka?
Kuka ta fashe dashi tace Allah ya isa wallahi Allah bazai barka ba. Wani mari ya dauketa dashi sannan ya take mata kafa yayi ball da ita yace kucaka kawai.
Fitonsa ya cigaba dayi har ya fice yana fadin Daga gadon asubiti uwar taku ma ta wuce.
Hey lovelies masu Neman update gashinan na muku.
See yah!
Miss untichlobanty馃挄
19 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 43*
Bayan daurin auren lukman ya kira ayush ya fada nata yadda akayi sannan ya fada mata yadda sukayi da yazeed tace Ba Komai ta fahimceshi.
Dadi yaji sosai kamin sukayi sallama irin ta masoya.
Sannan suka wuce wurin jana'izan da za'ayita bayan la'asar shida sauran jama'a.
Bayan andawo ananne sukayiwa iya sallama koda ta fito gaisheta sukayi tare da ta'aziyya ta amsa musu sannan sukace batun amaryan ne shine mukace bara muji yadda kuka yanke shawara saboda Asan yadda za'ayi.
Iya tace ai babu wani damuwa rana ita kuzo ku dauki amaryar ku sukace to ba matsala amma my again MJ tadanyi koda mako biyu ne tadan watstsake Daga radadin mutuwar iya tace hakan ma yayi bayan mako biyun sai kuzo. Insha Allah Nasan zaliha batada matsala.
Godiya sukayi kamin suka Koma gidansu Sulaiman domin yiwa Yan uwansa ta'aziyya.
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
Ya abubakar ne sanye da shaddarsa brown ya shigo gidansu Sulaiman domin yakanje once in a while Dan haka sun saba da Yan gidan bai taradda kowa ba sai laila dake zaune tama kasa kuka saboda duniyar tayi mata zafi Dana can ga rashin uba,yanzu ga mutuwar Dan uwa,ga mahaifiyarta rai a hannun Allah, ga takurar da isma'il聽 (goje) yake mata Dan kafin ya fita ma sanda yayi mata zagin uwa da uba sannan ya fice tareda Cewa ko tanaso ko bataso sai ta aureshi. Ga ciwon boyeyyen soyaiyar ya abubakar dake nukurkusatta tun tana karama domin tun kafin su zaliha da Sulaiman su fara soyaiya sunsan juna saboda kamin baban zalihan ya rasu yayi aiki akarkashin baban Sulaiman din,Dan haka ya abubakar kan takoshi Duba da Cewa shidin bashoda da namiji.
Anan dai ya abubakar ya zama abokin Sulaiman kuma ya saba da laila sosai tun tana shekaru 9 shi kuma 18 Inda yake ce nata baby laila har kwalliya yake mata sannan duk sanda tayi ado to shi zai fara gani. Shiyasa duk yadda goje ke mata naci ko kallonshi baikai tayi ba balle tasoshi gashi mugun Dan daba ne kuma tsaf zai iya kisa.
Sallama ya abubakar din yayi jin ba'a amsa Ba yasa ya shigo da alamu tayi zurfi a duniyar tunani Dan haka yazo gabanta ta yazauna Hannu yasa ya tallafo fiskanta dukda ko yasan Cewa bai dace Ba saboda yanxu ta girma ba kamar da ba yanzu shekarunta 17 amma yanayin daya ganta zuciyarsa ta raurawa bazai iya ganinta cikin yanayinnan Ba.
Da ido kawai ta kuresa yace baby laila Kiyi hakuri Nasan Cewa munyi dashi Kiyi hakuri kinji Allah ya jikan Sulaiman rungumeshi tayi tsam kamin ta fashe da kuka shima dai daskarewa yayi na wani lokaci domin rabon da susami kusanci irin wannan tun tana 12 barsu dai sukan rike Hannu once in aw while saboda Sabo dasukayi dayin hakan.
Kasa hanata yayi illa ma Daga baya ya zuro hannunsa ya rugumeta tsam.
Daidai lokacin su yazeed suka shigo ciki suma tunda bawani zaman makoki za'ayi Ba Dan basason bidi'a Dan haka babu mata a gidan sai waje ne ma mutane basu gama watsewa Ba.
Parking motarsu sukayi awaje kamin suka shigo suka ja suka tsaye baki a bude sallamar tasu ta makale domin abinda idanunsu sukayi artabo dashi ya Abubakar ne rungume da laila tan kuka yana shafa kansa da Hannu daya.
Kallon juna sukayi kamin suka sakewa juna murmushi.
Gira daya yazeed ya dagawa lukman yayinda lukman din ya masa thumbs up
Sidam sadam suka Shiga suka zauna a akujera yayinda ya Abubakar yace shh Dan Allah ki dena kuka sai lokacin laila ta bude baki cikin sarkewar murya tace ya abibi (yadda take kiransa) nikam na Shiga uku rayuwa tai min zafi.
Shafa bayanta ya farayi yace karki damu Komai zai wuce Allah ne gatan bawansa kuma ina tare dake ki daina kuka kinji tace to聽 Ummi. Yace yes Ummi tana inane muje kiraksni inyi mata ta'aziya.
Kuka ta kara fashewa dashi tace Ummi ta fadi ankaita asubiti.
Kallon juna su yazeed sukayi alamun what ? Gaskiya rayuwar yarinyar yana garari.
Ya Abubakar kuwa Cewa yayi Kiyi shiru kinji zata zamu lafiya Insha Allah Kiyi hakuri ki daina kuka. Ko kinaso nima in miki kukane ya fadi hakan a muryar wasa. Girgiza kai tayi tana turo baki yasa hannunsa yadan ja kumatunta yace good girl murmushi tayi kadan yayinda yake goge mata hawaye.
Yazeed ne yayi gyaran murya yana Dan shafe sajensa, Adan tsorace suka saki juna laila tayi saurin cewa bari in dauko hijabi na mu tafi asibiti sannan ta gudu yayinda Abubakar ke Sosa kai yana Dan dariya yace a'ah su angwayene dakansu? Ai banjo shigowanku ba.
Gyada kai yazeed yake yana smirking irin ai dole yayinda lukman kuma ya fadi abinda ke zuciyar yazeed din.
Yace mutumina ai dole bazakaji shigowarmu ba irin wannan dumi da kake sha.
Chanja zancen ya Abubakar yayi ta hangar Cewa kun Shirya my tafi asibitinne? Sukace mukam a Shirye muke shiri ai saikai. Mikewa yayi yace ai nima na Shirya sannan ya nufi kofa yazeed yayi saurin rikosa tareda Cewa聽 in-law dawo Duba rigarka dakyau. Lukman yace wani ai sai ya dauka dambe kayi.
Akunyace yadan Jade rigarsa squeezing din ya ragu. Lukman my man maganar nanfa bata Kare ba gara ma kaji.
Daidai lokacin laila ta fito. Gidan biki suka fara biyawa domin su dauki minal aje dubiyan da ita.
Fitowa sukayi a motan akabar Abubakar da laila daidai lokacin minal ta fito yazeed na kallonta ya saki murmushi.
Dan dunguransa lukman yayi yace my man kaima na....
ya Abubakar na kallon duk abinda ke faruwa Dan haka shima murmushi yake amma ba bakin tsokana.
Cikin gida ko zaliha ido ta rufe tace wallahi sai ta bisu. Aka buga aka raya tace Sam haka aka hakura akayi yarjejeniya da ita Cewa in aka barta toh Idan ta dawo zataci abinci.
Laila ko tana hango minal Yan hanjin cikinta suka kada domin ko bazata manta sanda suka tana haduwa sau daya ba sanda ta biyo ya Abubakar itada Sulaiman, minal ta dawo Daga islamiya ta mata duka Wai Dan tasha ruwa da kofinta. Shekaru 6 dasuka wuce.
Gaishesu tayi kamin su masa Shiga zaliha Kamar an jefota da takalmi a hannu.
Minal ne聽 ta zaro ido Adan tsorace tace zaliha me kikeyi awake?
Lukman ne yakalleta sannan ya kalli yazeed domin a tabbatar masa.
Kai yazeed ya gyada masa alamun itace matar tasa take yaji zuciyarsa yayi masa nauyi domin kuwa bayada interest a bakar Mace shiyasa ma yakeson ayush abinda bai sani ba shine ayush bleaching tayi.
Kara analysing dinta yake yazeed shima ya dunguresa Kamar yadda yamai dazu sannan kasa kasa yace inyi magana ko inyi shiru? Still idon lukman na kan zaliha yace yanzu fito kayi?
Ya Abubakar yace Inlaw barshi ba yanzu zamuyi magana ba sai nan gaba.
Zaliha ko binsu kawai take da ido,yazeed yace kai dallah kamo matarka kasata a mota mu wuce. Ya danyi hesitating kamin ya taka izuwa wajenta ya kamo hannunta. Wani yar yaji amma ya basar zaliha kam da hankalinta baya wajen batamasan an riketa ba ta janye hannunsa taje ta shige motar kamin tace Wai me kuke jirane? Yadda tayi magana Zaka rantse uwar su ce babu Wanda ya mata magana illa shigewar da sukayi.
Lukman ke tuka motar yayinda yazeed ke gefensa sai a abaya kuma minal tana owner's corner sai zaliha a gefenta sai laila a tsakiya sai ya Abubakar a karshe.
What do u think of laila? Kuna sonta?
Next chapter is a boom馃挜.
Takuce karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty馃挄
23 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty@nt馃尮
*CHAPTER 44*
Yazeed ne yasa Hannu ya gyara mirror yadda zai iya hango minal abinda bai sani Ba kuwa shine lukman ke Satan kallon zaliha ta mirror din Dan haka shima ya hararesa bayan Yan sakanni yasa Hannu shima ya
Juya dauke kai yazeed yayi kamin shima yasa Hannu ya kara juyawa.
Duk abinda ke faruwa ya Abubakar bai lura domin duk hankalinsa ya ta'allaka a yadda yaje zaune kusada laila Dan haka ya kafeta da ido yayinda take wasa da Yan yatsunta ganin yadda ya kafeta da ido bazata iya kallonsa ba.
Minal kuwa window kawai take kallo tana tunanin rayuwa yayinda zally tayi zugum da alamu ta tafi birnin China.
Yazeed da lukman a tare suka kai hannunsa zasu juya madubin kallon juna sukayi yazeed ya harareshi shikuma ya sakar masa murmushi.
Lukman ne ya kalli cikin mirror din Anan ya hango abinda ke wakana a duniyar su Abubakar.
Nuni yayiwa yazeed daidai lokacin suka iso leka mudubin yazeed yayi suka fashe da dariya.
Zabura yayi yace har Muna ido ne ? Lukman yace bamu ido Ba Muna hanya tukunnan suka kuma fashewa da dariya su minal Kam da basu gane meke faruwa ba suka tsaya kallonsu.
Fice wa sukayi suka Shiga asibitin. Wata nurse suka tambaya Inda aka ajiye Ummi din ta nuna musu tare da cewa su Shiga bibbiyu saboda ba'ason hayaniya nan dai suka fara Shiga.
A take laila ta fashe da kuka dakyar dai aka lallabata kamin min sukayi hanyar gida.
Mayar da zaliha gida sukayi,laila kuma aka kaita gidan Kanwar mamanta.
Ya Abubakar Kamar zai mayar da ita ciki. Sai bayan isha'i suka Koma gida, yazeed yayi sallama da lukman tare da Cewa akwai abinda zasu tattauna goben lukman yace ai baki daya kakeson yin magana Ba nima akwai maganar da zanyi dakai.
Shigowa ciki sukayi kamin yacewa minal tayi wanka ta Shirya ta sauko taci abinci Toh tace sannan ta sauko.
Gyada kai tayi sai ta tuna bayason gestures sai tace Toh sannan ta haura sama.
Wanka shima ya Shiga yayi sannan ya saka kayan baccinsa ya sauko yana Cewa yunwa nakeji amma hanji na ya daure maybe I should take some cappuccino.
Sofa ya samu ya zauna kamin ya janyo wayansa ya fara scrolling messages.
Minal ce ta sauko cikin wani farin rigan bacci na satin amma Ba shara shara bane saide yana like mata a jiki once in a while.
Kallonta yake tayi har ta ido gabanshi bai ankare ba tace gaji still kallonta yake.
Hannunta tasa ta tafa a gaban fuskansa tace nace maka gani.
Hannunta ya kamo ya janyota ta fado jikinsa kokarin tashi ta fara yi ya kankameta sannan ya Daga mata gira daya yace sannu da zuwa.
Kiciniya ta farayi tana Cewa ni Dan Allah ka sakeni Wai na maka kama da yar iska ne? Murmushi yayi yace Kayan jikinki ya amsa mini wannan,sannan tunda gaki kwance ajikina ai kinzama yar iskan ko turo baki tayi ta fashe da kuka ni wallahi ba yar iska bace yace time will tell. Itadai bata kulasa ba banda ci gaba da magana da tayi tace to ai kaika janyoni kuma ka wani rikeni sai kace zaka mayar ni ciki yace to wa ya sani ko cikin zan mayar dake.
Ganin babu sarki sai Allah yasa yasa ta kwanta luf ajikinsa babu abinda ke tashi a parlourn sai sautin numfashinsu kasa kasa minal taji yace "sai Anyi magana mutum yace shi ba Dan iska bane.
Tace me kace yace tunani nake. Harararsa tayi sannan ta kuma kwanciya can sai yace Wai meyasa bakison kirana da suna nane ? Saide kawai ki fadi magana,Ko kuma kicemin oga sir. Ko bakisan sunana bane ?
Girgiza kanta tayi a kirjinsa tace na sani mana ba kaima baka kirana da sunana ba saide ka dinga cemin insaram yace to mene sunan nawa?Dago da kanta tayi tana washe ha'kwara ita a dole kunya tace kawo kunnanka kaji.
Matso da kunnansa yayi a hankali kuma a kunyace tace oga ya..zeed.
Sanda tsikar jikinsa suka tashi domi. Tunda yake bai tabaji sunansa yayi masa dadi Kamar yadda yayi a bakinta ba.
Dan haka yace me ki kace ?ma'ke kafada tayi alamun bazata fada ba.
Puppy face yayi Yace please my insaram! Turo baki tayi tace ba gashinan ba kana sake cemin insaram yace to na daina Idan kika fadamin sunana to zan chanja miki suna.
Hannu tasa ta rufe fuskanta sannan tace oga yazeed
Yace to ki cire ogan tace yallabai zansa ?yace a ah tace to yaya kakeso Insa maka yace ah ah kawai ki kirani da suna na.
Tace a ah ba tarbiyya bace in kiraka da sunanka ko ba Komai ka girmeni.
Murmushi yayi yace beauty is secretly trying to be romantic da muryar tsokana. Turo baki tayi cikin shagwaba da wasa tace wallahi ya yazeed da gangan kake min turanci Dan kasan ban iya ba yace sorry Toh na daina karki damu kema zan koya mini turanci. kinaso ki Koma makaranta gyada kai tayi yace good zannayi miki lesson a gida inyaso sai Kiyi jamb da WAEC ko ? Tace eh yace beauty tace Waye beauty kuma yace Kece mana Sabon sunanki kenan. Ya miki? Ta gyada kai tare da Cewa eh yace kinsman ma'anarsa tace yana nufin kyau ba? Smiling yazeed yayi sannan shima ya gyada mata kai yadda take mai sannan yana kumatunta yace Ashe de beautyn tawa ba laifi.
Shiru wajen ya sake dauka kamin yazeed ya sake Cewa beauty ta dago ta kalleshi yace inason ki saki jikinki in Muna tare kinji? Ta gara kai yace kinaso ki zama kawata ? Ta sake gyada kai turo baki yayi yadda take mai inya mata abinda bataso yace bazakimin magana ba? Tace inaso in zama kawar taka. Tasar da ita yayi ta daina shima ya gyada zamansa Daga kishingida sannan ya miko mata Hannu yace friends? Shaking hannunsa tayi yace bakice friends dinba tace friends sai suka kyalkyale da dariya.
Daidai lokacin cikinsa yayi masa karar yunwa abinda bai tana faruwa dashiba ko a mission kuwa.
Pouting yayi yace beauty yunwa nakeji tace muje kaci abincinka to yace nope cappuccino zansha tace cup...po聽 mene? Yace cappuccino kin gaba sha ? Girgiza kai ya harareta tace a ah.
Yace okay muje kitchen in nuna miki yadda akeyi kai kawai ta gyada suka nufi kitchen dauko duka ingredients yayi sannan ya nuna mata yadda akeyi tace kai Ashe da sauke itama ta hada wani cup karba yayi ya murna yaji yayi dadi sosai zai iya rantsewa bai tabashan cappuccino me dadinshi ba.
Kurba itama tayi kamin ya riko Hannunta suka hau kan kitchen island suka zauna.
Yazeed nasha ahankali yayinda a kurba uku ta tada nata har tana kwarewa yazeed yace sannu bari in dauko miki ruwa tace barshi kawai bari in hada lamurje (lemonade) Insha saboda wannan cappuccino din maka na Daga min zuciya okay kawai yace
Lemon tsami ta dauko yace Kiyi ahankali kada ki yanke tace Toh. Lemonade ta hada tana kokarin saka sugar taji cikinta ya wani murda Dan dafe cikin tayi amma Ba tayi magana ba yazeed ya lura domin tunda ta fara hade hadenta yake binta da ido.
Ajiye cappuccino dinshi yayi yazo ya rikota yace lafiya tace babu kawai sai ta saki kara kadan yace ki fadamun menene?
Girgiza kai kawai tayi sannan ta dauko lemonade din tace sha kaji yayi dadi? Kurba yayi yace yayi sosai ma kuwa kin tabbata you are okay tace eh sha Rabi sai kaban in shanye inna na cemin duk sanda mutum taci abinci to Tasha ruwan lemon tsami saboda yana taimakawa wajen narkar da abincin.
Kara kurba yayi sai yaga minal tana hade fuskatana cije lebe.
Ajiye cup din yayi ya dafa kafadarta da hannu biyu amma kamin yayi magana minal ta saki kara Innalillahi ya yazeed cikina! kamin kace me kumfa ya fara fitowa Daga bakinta.
*Na Shiga uku ni yar mutum 2 jikar mutum 4 me kuma ya sami minal?*
Lemme kuku run for my life before you kill me!
Miss untichlobanty馃挄
24 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @miss_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 45*
Sulalewa tayi Take yazeed ya bita Ya tsuguna fuskanta cikin tafukan hannunsa yace ke rosy cheeks! Rosy cheeks ! Menene? Kunfan dake kara bulbulowa a bakinta ke kata Daga masa hankali.
Cikin shakewa da kafewar murya minal tace ma..d..dara. Ganin kamar bakinta yayi motsi yasa yazeed ya saurara da tamboyin da yake mata Dan ya rikice.
Ahankali ta sake Cewa mad...darrr..aaa kamin wani kunfa ya kuma fito wa Daga bakinta.
YAZEED yace madara? Ta rufe idonta ta bude a hankali alamun eh. Da Sauri ya kwatar da ita ya mike ya dauko madara ya bude ko kallon Inda kofi suke beyi Ba ya kafa mata.
Tana fara sha ya sauke ajiyan zuciya Wanda yayi dadai da murdawan da cikinsa shima yayi.
Basarwa yayi amma murdin da cikin ta kara yi yasa yayi sauri zau ajiye gorar madaran daya kawowa minal.
Minal kam ta lura da yanayin yadda yake yatsine fuska Dan haka a take tayi saurin sa hannunta ta hade gorar da hannunsa takai bakinsa daya fara zubda kumfa.
Sanda ta tabbata ya shanye kamin ta kwantar dashi a wajen jiki babu kwari ta nufi fridge ta dauko ruwa da wani madaran sai kitchen towel.
Bakinta ta goge sannan ta goge masa nasa bude ruwan tayi zata kafa abaki taji muryansa kasa kasa yace ki dau kofi. Ba musu ta dauka ta zuba tasha sannan ta zauna ta daura kanshi a cinyanta sannan ta bashi ruwa.
madaran ta kara bude musu ta zuba cup din zata sha yayi saurin mikewa Daga cinyarta Dan karfinsa ya fara dawo masa.
Pouting yayi Kamar yadda take masa kullum yace rosy cheeks ni zan fara sha. Dariya ta kyalkyale dashi saboda yadda yayi maganan Kamar wani Yaro.
Bashi tayi yasha sannan itama ta kafa kai tana sha, ji tayi ya fashe da dariya dan haka ta dago da idonta tana masa kallon dariyar me kake yi ?
Yace rosy cheeks literary we just kissed tace uhm? Yace munyi Sumba nida ke saboda daidai Inda na kafa bakina nan kika sa naki. Zaro ido tayi Take madaran ya kwareta sannu yayi mata ya shafa bayanta sannan ya bata ruwa.
Hararansa tayi idonta ya ciko da kwalla muryarta na rawa tace Nide wallahi bamuyi Sumba Ba danni ba..... Sai kuma tayi shiru.
Yazeed sarai yasan me zata ce dan haka yace uhmm? Tace babu sannan ta dauke cups din ta wanke ta nufi dakinta yayinda yazeed ya kira doctor tunda dare beyiba sosai 9:10pm nema.
Koda doctor yazo yazeed yayi masa bayani Dr din yace poison ne.
Yazeed yace ya sani. Dr din yace menene last Abu da sukaci kamin attack din yace cappuccino ne amma kuma abinda ya bani mamaki kullum ina sha ban taba samun attack dinba.
Doctorn yace lets check the expiring date then. Dubawa sukayi amma akwai har shekara 1 da wata 3 before yayi expire. Doctorn zan kaishi lab in bayar domin test dan something is fishy.
OK kawai yazeed yace聽 ya raka Doctorn har bakin main door sannan ya rufe.
Dakinshi ya nufa ya kunna CCTV sannan ya tafi kitchen direct.
Forwarding Inda su tala sukayi su girki yayi making sure indonshi akan Ronan cappuccino powdern.
Chan bayan sun fita yaga Jennifer ta shigo tana sanda da waige aiko bata tsaya ko ina Ba ta dauko cappuccino powdern tayi mixing da powdered poison sannan ta zaro wayanta tayi kira kafawa a kunnenta tayi kamin chan tace angama aikinindai yasha to zai mutu murus...... gyada kai tayi kamin tace yes ma amma ma problem din baza'a budemin gate Ba sai da izininsa.
Shiru ta kuma yi da alamu tana sauraron dayan bangaren kamin tace yes ma karki damu zan labe da motansu ya shigo ni sai infita...........thank you ma.
Take ya dauki wayansa ya ranbadawa lukman text Cewa a nemo masa Jennifer ko a ina take a muce ko a raye.
Aikinsa ya fara a apple laptop dinsa amma hankalinsa Sam baya kan aikin da yakeyi hankalinsa ya ta'allaka ne akan wakeson kasheshi tunda acikin cappuccino akasa guban kuma shi daya ke shan cappuccino a gidan.
Bayan Kamar 30 minute wayanshi ya fara ringing dauka yayi ta dayan bangaren lukman聽 yace sir mun samota a kawo motor park da alamu so take tabi motar asuba. Yazeed yace great! aikinka yayi kyau, Ina alfahari dakai.
Lukman yace thank you yanzu haka ma tana hannuna we tricked her to come with us.
Yazeed yace tayaya kuka yi ne?
Lukman yace my man Ba Kai daya bane charming fah kawai nuna mata Nayi ina bukatarta a gado Ba musu ta biyoni tana shigowa mota taga bani daya bane ta fara zagina tana kuka Wai na cuceta na yaudareta zanjawo a kasheta.
Dariya yazeed ya sheke dashi jin yadda lukman din ke kwatanta yadda tayi maganan yace shegiya ai kadan ta gani.
Minal ko bayan ta Koma dakinta wanka ta sakeyi ta canja rigarta sannan tasa hular baccinta ta nufi dakin yazeed domin yi masa tausa Kamar yadda ya umarta.
Koda tazo kofar dakinshi bude kofar tayi a hankali domin so take ta bashi tsoro Kamar dai yadda yara keyi.
Abinda kunnenta ya jiyo mata shiyasa ta tsaya cak tabbas Ba karya bane yazeed ne ke waya yana magana Kamar haka:
"Great aikinka yayi kyau ina alfahari dakai" wani aiki ne yayi kyau?
Wai tayaya kukayi ne?sukayi me?karde abinda nake tunani ne?kai noo yazeed bazai tana kokarin kasheni ba. Wata zuciya ne tace mata kin manta ya tsaneki? To amma in so yake ya kasheni me yasa ya CeCe ni? Kuma ai shima yasha.
"Shekewa yayi da dariya yace kadan ma tagani" tabbas damirin sunan mace yake aiki dashi towai me yake magana akai?
Ganin bazata sami answer dinta Ba yasa tazo gabansa tace ya yazeed dama so kake ka kasheni?
A zabure yazeed ya dago yana kallonta ido cikin ido..............
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁
Zakiyya zaune gefen wata farar budurwa fat sai sharar kwalla take,Ba laifi tafi zakiyya kyau amma da kaga farinta kasan Ba na Allah da annabi bane.
I am sorry sis! Shine abinda taketa maimaitawa tana shafa bayan yarinyar wacca bazata wuce shekara 21 Ba.
Budurwacce ta kuma share kwalla tace Wai yanzu haka lukman dina yana tareda wata ko?
Girgiza kai zakiyya tayi tace baya tareda ita tunda kince baya sonta nima yazeed dina yayi auren amma ko kallon arziki baya mata ranan da na taho har jibganta yayi. Kidena kuka kinji sister AYUSH?
Let me kuku run for my life before ayi min duka dan yau Nasan zanbar fans Suna tsimayi na
Expect me soon!
Anyway result dinmu ya fito kuma it was masha Allah no problem.
Thanks for your du'as love yah馃槝
@mzz_untichlobanty 馃挄
26 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 46*
Wasu hawayenne suka kuma zubowa Daga idanun ayush sannan ta girgiza kai tace sister zakiyya karki bani fake hopes Dan Allah kinsan namiji abin tsoro ne ta iya yuwuwa yanzu haka yana tare da amaryarsa ya manta dani.
Shafa kanta zakiyya tayi cikin murya mai laushi da nuna Cewa ta damu da yanayin da cousin dinta ta Shiga tace little sis have faith kinji ? I know that you are brave, ko sanda parent dinki suka rash you were so brave right ? Gyada kai ayush tayi zakiyya tace Toh kin bani you can go through it and kinyi trusting lukman dinki ko? Ayush ta kuma gyada kai tare da Cewa eh kamin wani hawayen ya silalo zakiyya tace good since have trusted him and you are sure that he loves you then there is nothing to worry about dago da manta tayi ta kalli zakiyyan tace are you sure?zakiyya tace 100% sure now give me a smile kinji?
Murmushin dole tayi zakiyya tace ko Ba ke bafa now tashi muje kick abinci.
Girgiza kai tayi tace banajin yunwa, hararanta zakiyya tayi tace zaki tashi ko yaya? Mikewa tayi tana Cewa sis wannan kallon ai sai ki cinyeni dariya suka fashe dashi kamin suka wuce dinning area domin cin da'am.
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
What!? Minal me kike nufi me zaisa in kasheki? Harara minal ta aika masa kamin tace abubuwa dayawa. Wato dama duk wannan abubuwan dakake min kanayine saboda in na mutu kar a zargeka?minal ta fadi hakan tana mai daga murya.
Tsawa yazeed ya daka mata ya daka mata yace banson hauka fah kodan kings ina Daga miki kafa shine zaki kawo mini rain in hankali ? In da inason na kasheki ne da tuni na kasheki.
Hararar sa tayi da rinannun idonta muryarta na rawa alamun zata iya fashewa da kuka at any moment tace amma wallahi bantaba nadamar aurenka Ba irin yau Nayi kuskure Dana yarda dakai Ashe Dama kai me kisan kaine? Ashe kasan abinda ka tanada shine harda cemin Wai mu zama abokai,Dama zaka iya min haka? zuciyata ta raurawa har yanzu na kasa yadda Cewa kanason ka kasheni, ya yazeed ka tasheni kacemin mafarki nake Ba dagaske bane,Ba kasheni kakeson yi Ba.
Tsintsiyar hannunta yazeed ya kama ya jata har izuwa bakin kofar dakinsa sannan ya wancalar da ita yace Anyi kokarin kashekin Kiyi abinda zaki yi sannan ya rufe kofarsa.
Wani irin zafi zuciyarsa ke masa Wai yau shi YAZEED ABDULMAJEED UMAR aka Cewa yana kisan kai? Da alamu sakarwa yarinyarnan fuskar da yakeyi ya janyo masa matsala.
Zaiyi kokari ya nisanceta ko tayaya ne domin ta fahimci kuskurenta sannan ta fada hakuri kamin ya yafe mata.
Wata zuciyar tace uhm tunda kuke da zakiyya ta taba baka hakuri ne inba tanada wani agenda ba.
Sai alokacin ya tuna da zakiyya yace ko ina ta Shiga oho bako waya? I will call her tomorrow.
Da sake sakennan ya fara bacci tare da aiyana irin azabar dazai ganawa Jennifer harsai ta fada masa Wanda yasata wannan aika aika.
.................
Minal ko yana rufe kofarsa ta fashe da kuka. Sanda tasha kukanta ya isheta sannan ta mike taja kafafunta jiki a sanyaye taje dakinta. Itakam ta Shiga uku da rayuwarnan da badan kartayiwa Allah butulci Ba da tace inama ta mutu Dan wallahi sanda wannan abun ya farune ta fahimci ta fada tekun son yazeed dukda ko bata tana yin soyaiya Ba amma dai ai tasha jin abubuwa akanshi gashi ita Ba takaddun Hausa take karantawa ba, wannan sai zaliha wani ajiyan zuciya ta sauke me nawi tunawa da zaliha da tayi ko yanzu a wani hali take oho, sai yanzu ta fahimci ciwon da zaliha keji.
Yanzu da ace ya yazeed ne ya zatayi? Dukda ko yayi kokarin kasheta wallahi itanasonshi a hakan ma. To kode tayi kuskurene? Kode bashi yakeson ya ya kasheta ba? Kode wani zancansa daban yakeyi ? Kai ya cancanta ta bashi hakuri sannan ta nemi Karin bayani tunda ko a musulunci babu kyau zato.
Kallon sama tayi tace astagfirullah Allah na tuba,nikam naga takaina karfa in mutu yau mijina na fishi dani.
Mijina? Kai Ahe ban taba kiransa da mijina ba ta fadi hakan tana Washe hakora Kamar ba ita ta gama drama yanzu ba.
Kai Gaskiya bani iya bacci in banbashi hakuri ba ta fada a magana zuci. Saukowa tayi Daga gadonta tare da Cewa gadona kar kayi kewata yanzu zan dawo kaji ? Kamar gadon yana jinta (typical me馃槀 yeah I have that kind of connection with my bed and phone.)
Sautin tafiyarta Kadai ke tashi saboda yadda gidan yayi shiru. Koda ta iso kofar dakinsa knocking tayi a hankali taji shiru ta sake knocking still shiru
Murda hannun kofar take shirin yi sai alokacin ta lura Cewa Ashe kofar batada Hannu sai wurin saka pin ta ciki ne akwai handle.
Nambobi ta fara daddannawa amma koda tayi sai uku duka wrong sai kofan yace bazata iya sa'a ba sai after 15 second itako da ba ganewa tayiba taci gaba da dadaddanawa.
.........................
Yazeed kwance a dakinsa har bacci ya fara daukarsa yajiyo taku na kara matsowa kusa da dakinshi kuma Idan ba kuskure yayi ba takun minal ne tayaya ta Shiga side dinsa ? Gush Ashe ya manta be rufe koda ba thank goodness kofar dakinsa in a rufe ba'a iya budewa ta sake sai ansaka pin da ace ba minal bace fa ?
Dawowa yayi daga tunanin da ya shiga jin minal ta fara knocking kamin kuma ta fara daddanna pin.
Yanaji machine din nata dit dit dit dit dit zu! Har sai uku alamun pin din ta is wrong amma yaji minal ta cigaba da daddanawa.
Tasowa yayi yazo bakin kofar yadda zaiyi magana ta jishi ba sai ya daga murya ba saboda girman dakin.
Yace ke dallah kibar nan wurin karki batawa mutane kofa aiko minal tanajin yayi magana tace ya yazeed Dan Allah ka bude Dan Allah baice Komai ba ya Koma yayi kwanciyarsa.
Minal ko jin shiru bai kara magana ba yasa ta jingina da kofar kamin tace Dan Allah kayi hakuri Nasan Nayi kusukure Dana zargeka ta fadi hakan tana shirin zubda kwalla.
Mamaki ne ya cika yazeed Wai hakuri ta bashi kuma ma da wur wuri haka ? Chabdi ai inda zakiyya ne wallahi saide ya mutu.
Baice Komai bayayi kwanciyarsa,can yaji Kamar shesshekan kuka wani zafi yaji zuciyarsa tamaisa amma ya daure wajen Cewa in kin gama kukan kibarmin side dina sannan karki sake ki kara zuwa inda nake.
Kuka ta fashe dashi tace Dan Allah karkayimin haka ya yazeed kayi hakuri bazan karaba.
Jin shiru yaji kulata yasa ta Koma dakinta zuciyarta cike da damuwa yanzu ita ta yaya zata bashi hakuri bayan yace bayason ya kara ganinta? Wani kukan ta kuma bingirewa dashi har bacci barawo ya saceta.
Good morning na cika alkawari,please make sure you spread a smile on my face comment and vote fah
Have a good day bye
Miss untichlobanty馃挄
28 November, 2019
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 47*
Da safe jiki babu kwari minal ta fito ta fara aikinta koda ta kammala,tayi wanka sannan lokaci zuwa lokaci takan sauko ta Duba dinning table ko yazeed ya sauko domin ta share dakimshi tunda yace bayason ya kara ganinta.
Komawa tayi dakinta ta zauna Jim kamin ta janyo wayarta sai alolacin ta tuna batada numbern zaliha kawai sai kawai taje gaban madubi ta shafa powder da lipstick saboda rage lokaci Kuma tayi kyau Ba laifi.
Fitowa tayi daga dakin aranta tana Cewa Nasan ya fita ma tunda safe kuma ko na hadu da shi ma nuna masa zanyi ina fushi dashi muga yadda zaiyi. Murmushi tayi kamar wata shashasha ko yadda yara keyi Idan sun kulla wani abin.
Laundry room ta Shiga ta dauko kayansa set 2 data goge dazu ta nufi part dinsa koda ta Shiga Ba kowa kuma parlourn nasa ma da duhu alamun babu kowa tace Ahe duk jirannan danayi na banza ce bayanan ma.
Ta bangaren yazeed kuwa Kamar jira yake ta Koma daki sai gashi ya sauko, kitchen ya nufa ya dauko hollandia yoghurt plain flavour saboda na fridge din parlourn sa ya kare sannan ya dauki cup ya fita.
Dakinsa ya Koma yasha yoghurt dinsa Dan baya mood din cin abinci. Kwantawa yayi abinsa ruf da ciki yana mai kashe wutan dakin sannan ya rufe idanunsa once in a while yana murmushi.
Da confidence dinta ta tura kofar dakin Dan ba'a rufe kirif take ba sai ta dauka ko ya bar mata ne Dan tayi shara Kamar yadda yasaba bari Dan haka bata kawo Komai cikin ranta Ba ta shigewarta.
Hijabin dake jikinta ta cire tayi cilli dashi akan gado sai kan fuskar yazeed Wanda dama tun dazu yaji takunta kuma yasan ta shigo dakin amma ita batasan da zamansa Ba. Baice uffan Ba balle ya motsa yayi luf cikin bargonsa sai kansa dake waje wanda yanzu yake lullube da hijabin minal. Tunani yake aransa yarinyarna badai sa hijabi Ba kam. Allah yasa da kyakkyawar niya ce.
Ajiye kayan tayi akan stool kamin ta dafe goshinta da hannunta tace ni yanzu ya zanyi ? Kullum yananan yana budemin wannan yar iskanci kofar dakin kayan nasa to yau kuma bayanan.
Kicin kicin tayi da ido tace Idan na kamo yaya yazeed dinnan sai na naushi bakinsa. Sai kuma ta kyalkyale da dariya tace Wai wayaganni na danne ya yazeed sai jibgarsa nake.
Wutan dakin ta kunna kamin ta dauko kayan aikinta. Ganin bargon NASA a wargaje yasa tace kai Ashe ya yazeed dinma kazami ne fadin jumlar tayi daidai da janye bargon aiko atake ta kwala ihu zata arta a guje yayi saurin wantsalota ta fado jikinsa kokarin tashi take tanata tuttureshi amma ya riketa gam hannunshi ta fara mintsini tana Cewa ya yazeed ni ka sakeni nifa Ba yar iska bace. Bai kulata Ba illa ma tashi da yayi zaune sannan ya ajiyeta akan gadon couch ya Koma ya zauna sannan yace rosy cheeks gyara gadon kizo in fada miki wani Abu. Dan hade fuska tayi tace me zaka fadamin? yace sirrine a kunne ma zan fada miki tace toh..........
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
Zakiyya zaune a parlourn gidansu Amarya tana oiling ma ayush din gashi Wanda Ba yabo Ba fallasa.
Wayanta ne ya fara ringing ta dauka kamin tayi magana akace madam the boutique has been on fire mun kira fire service sun kashe but we couldn't retrieve our goods.
Zakiyya da batasan sanda mike Ba tace what?how comes? Are crazy? incoming call taji hakan yasa ta Duba ganin sectary dinta ne yasa ta datse da gaggawa tana mai Cewa hello maryam wani irin nonsense nakeji Wai boutique ya kam..........
Bata karasaba Maryam tayi Sauri Cewa Ba nonsense bane ma munyi gobara, the came out of no where. Yanzu haka ina hospital saboda na none a gefen hannuna amma Ba wannan Ba new boutique dinma an Shiga an kwasge kayan tas sanna aka rusa ginin.
Take zakiyya ta yanki jiki ta fadi kasa sumammiya. Ace sukiyar da tayi shekara kusan 5 tana Tarawa cikin minti 5 babu su?ina impossible.
Inda Allah ya taimaka baki nasu wani hallara Ba tunda har yanzu saura 4 days a fara shagalin bikin ma Dan haka akayi asibiti da ita.
Sanda tasha drip 6 a rana daya dukda ko bata farfadoba saboda tsabar shock.
Yan gaisuwa kam sun kasa karewa an mayarda asivitin Kamar gidan Suna sai Shiga da fice ake.
Ayush zaune akan wani kujera a gefen gadon zakiyya taga Kamar hannunsa yana motsi. Rike hannun tayi ta fara jijjigawa tana kiran sis?sis sannu kinji ? A hankali zakiyya ta bude idanunta aiko babu bata lokaci hawaye sukayi sallama suka bemi mazauni a idanunta.
Mamanta ne tazo kusa da ita tana lalkashinta kamin tace Kiyi hakuri zakiyya akan namiji kike Neman kashe kanki? Sakinki yazeed din yayi ayush ne tayi saurin Cewa gaba mama saki kuma ? To mema zakiyyan tayi da za'a saketa?
Mama tace to inva saki Ba mezaisa ta sume har gadon asibiti caraf akaji zakiyya tace dukiya, dukiya itace abin da ta janyo.
馃槶mama dukkan dukiyan Dana Tara sun tafi,mama tace ban ganeba, zakiyya tace Nayi gobara babu abinda ya fita a boutique dina.
Dakin dake cike da mutane ne ya kaure da Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Nanfa Yan Jaje ma suka fara rububi anata kawo gudun muwa.
馃尮.....................
Abangaren malama zaliha kam Ba kanta Dan yanzu tadan dawo daidai Inda tace Allan katafur sai an nemo lukman ya saketa, ita bazata iya cin amanan Sulaiman Ba. Mahaifinta da aka sallamo washegarin faruwar abin ya nuna farinciki sosai dajin Wanda ya aureta.
Ganin dai kowa yanason auren yasa ta saduda amma da sharadi bazatayi zaman aure dashiba. Side ido suka zuba mata Suna kallon ikon Allah so saikace hauka? Allah dai shi kyauta ya kuma bata lafiya Dan gani suke ta tabu.
馃尮..........................
Laila na zaune a dakin da mahaifiyarta ke kwance rai a hannun Allah. Aunty kuma ta Koma gida bata dawo ba goje ya bankado kofar dakin. Harararsa tayi tace me ya kawoka? Murmushi yayi cikin muryarsa ta Yan shaye shaye yace rayuwar Abubakar na cikin hatsari.
Laila tace what? Wani Abubakar din ? Yace Abubakar Yusuf dai da kika sani Kiyi sauri.
Batasan Inda take wulla kafunta Ba hankalinta tashe tana rokan gone da ya hanzarta kar wani Abu ya sameshi
Koda suka fito farfajiyar asibitin babu kowa Duba da Cewa magriba tayi wasu masallatan ma har sun kira sallh matse bakita yayi kamin ya cusa mata tsimma ya daure sannan ya sakata a Booth.
Figar mortar yayi yabar farfajiyan asibitin wani gida ya kaita ko ince irin dakunannan da samarin yanzu Yan Abu yarima ashana kida,Yan zaman kashe wando keyi. Banda warin sigarin ,hamamin amai da zarnin fitsari babu abun da dakin keyi Ba Komai bane a ciki illa katifa sai karamar TV da wata akwati daya sai kwalaben giya a gefe da dusan sigari.
Cirota yayi Daga booth din ta hada gumi tayi jagab ya fara janta zuwa cikin dakin, turjewa ta farayi ya gaura mata mari take ta fashe da kuka. Hankadata ya dingayi har ya wullata kan katifan sannan yace zan since miki baki domin ya zama dole in dan dana su amma Idan kika sake kikayi ihu kinga wukannan daina Burma mini ita da fatan kinajina ? Hararsa tayi yace wallahi wannan kallon wani irin shauki yakesamin.
Since bakin yayi kamin ya kara da Cewa gara kiban hadin kai muyi mu gama lafiya asirinmu a rufe.
Tace wa'iyazu billah aini ina Neman gafarar ubangijina na shigowa wannan dakin da kuma zama a wannan katifar da bansan sau bawa akayi zina akanta ba. Ka since min hannuna! Bara kaji Wallahi tallahi karshenka bazatayi kyauba.
Kuma haihuwarka asarar nakuda da ragon Suna ce.
Wani mari ya kuma dauketa dashi wannan karan harbakinta sanda ya fashe. Ihu ta kwala tana kiran sunan mahalliccinta. Bata ankare ba taji goje ya danneta yana kokarin kai mata kiss kakkauda kanta ta fara yi babu abinda take tunowa sai yadda ya Abubakar zaiji inya riski wannan labari.
Cikin rashin sa'a goje ya cafki bakinta yana kokarin tura harshensa ciki. Ganin ta rufe bakin kam yasa ya matse mata bakin da hannunsa badan task ba ta bude ta mai ja masa Allah ya isa.
Aiko harshensa yana Shiga bakinta ta fara kwaranyo amai.
Cire bakinshi yayi Daga nata ya fara zabga mata Marika sanda ya ajiye mata takwas lafiyaiyu daidai lokacin Allah ya taimaka mata hannunta ya since
Kokarin Daga mata Riga goje ya fara aiko nan suka kama kokuwa Kamar ba gobe.
Yaga rigar yayi ya fara kokarin rabata da pant dinta amma taji yarda tun tana iya tureshi har ta kasa hakan yasa yayi nasarar zare wandon nata yayi wulli dashi.
Wani irin zafi taji a mararta ta kwalla ihu YA UBAN GIJI NA daganan bata kara ganin komaiba.
馃槶馃槶馃槶 oya join me along let's cry!kuzo muyi kuka tare this chapter is so heart touching.
Long chapter ne so I expect you to to share kuma Ku cika min comments section da COMMENTS.
me kuke tunani game da wannan chapter?
Sai anjima wallahi bacci nakeji yau ba update din dare.
Takuce karamarsu babbarsu wato ;
Miss untichlobanty馃挄
30th November, 2019
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: *馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳*
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 48*
Ruwan sanyin da taji yasa ta bude idanunta batare da ta shirya ba, dishi dishi take gani har Komai ya zamo mata tar.
A take ta zauna dukda ko irin azabar da maranta ke mata,babu bata lokaci duk abubuwan da suka faru da ita suka dawo mata.
Kallon jikinta tayi taga kusan gabadayan kirjinta a bude.
Bedshit din da yake dukun dukun taja ta rufe jikinta badan ranta yaso ba.
Kallon dakin ta farayi jiki a bari saboda sanyin da takeji taga goje da Rigarsa a kafadarsa zaune gefen kafarta da Goran ruwa yana cin shinkafa da wake sannan sai ya busa sigari ya kara wata lomar.
Janye kafarta tayi Daga kusa dashi tana mai jin daci a zuciyarta.
Sai alokacin yace Ashe kina Raye aina dauka kin mutu ne shiyasa na Zuba miki ruwan zanyi Dan tabbatarwa. Zo muci abin ci kinji. Sannan ya kara wata wata loma.
Kallon sa kawai take Dan batasan abin nasa yakai haka ba tace Allah ya kiyaye inci da Hannu na yace in baki cita ba ai kinyita,ina fata ma Nayi ajiya.
Kuka ta fashe dashi wannan karan mai sauti tace amma wallahi ni ban taba Sanin Cewa kai Dan iska tsinanne Mara mutunci bane sai yau,yanzu......
Tas ya wanketa da mari yace ke yarinya iya bakinki,baki isa ki fada mini maganar banza ba kuma Anan zaki zauna harsai sanda naga daman ki tafi zaki tafi.
Tace wallahi....... Wani Marin ya kuma dauketa dashi yace ba nace karki kuma yi min magana ba to bari kiji babu Inda zaki ko mutuwa zakiyi.
Wata kakkausar muryace a bayansa tace kaima baka isa ba kuma kayi kadan. Bai ankare ba yaji an damkosa ta baya aka jibgarsa Kamar Allah ne ya aikosa.
Gwara kansa yayi da gini sannan yace lailar?lailar kayiwa haka?toh wallahi ba me rabaka dani yau sai Allah. Naushi ya dinga kirba masa yayi kaca kaca cikin jini. Kafa ya dinga masa a tsakiyar kafafunsa. Goje ganin Idan bai ceci kansa ba, to fa zai iya kasheshi Dan haka ya tattaro duk karfin dayayi masa saura ya hankadeshi ya gudu.
Da Sauri ya mike zai bishi laila tace barshi ai aikin gama ya gama.
Da gudu ya nufi Inda take ya rungumeta. Tsawo lokaci suka dauka a haka kamin yace Laila me yasa kika biyoshi bayan kinsan halinsa?Ashe bakida hankali?yanzu ga idonta nan ai ko me yace miki bai dace ace kin bishi Ba! Ya fadi hakan cikin Daga murya, fada, da kuma nuna Bacin rai.
Laila da zuciyarta ke mata kuna ganin ya Abu ya rufeta da fada, Ba tare da ya bata Samar maganaba, cikin gunjin kuka tace haka fa yacemin Wai rayuwarka tana cikin hatsari shiyasa banmasan sanda na biyosa Ba idona ya rufe har nabar mahaifiyata ita kadai馃槶.
Shiru ne ya ratsa wurin na Dan wani lokaci kamin ya Abubakar cikin murya me taushi da ban hakuri yace me yasa idonki ya rufe da akace rayuwata tana cikin hatsari?
Zuciyarta ne ta buga dum! Jin tambayar daya Watso mata Ba tare da ta Shirya amsashi Ba.
Shiko jin tayi shiru yasa zuciyarta tayi sabyi domin bai sani amsar da yakeson Ba. Ga mamakinsa yaga ta dago ta kalli cikin idonsa kamin tace SABODA INA SONKA! Yaya na Dade da Fadawa cikin tekun soyaiyarka tun kamin Nasan ciwon kaina.
Na Riga da na nutse kuma bana burin a ceto ni, nafiso ace na mutu acikinta.
Ya Abubakar Kam daya daskare yama kasa magana Dan ko ya bude bakinsa sai ya rufe ta. Bai masa mata Ba dukda ko tsabar dadi jiyake Kamar zuciyarsa zai fado Daga kirjinsa.
Rigarta da ajayi cillo da ita ya dauko amma me duk a yage take Ba anfanin sata take farin cikin dake zuciyarsa ta sauyu zuwa bakin ciki.
Wani kububuwan kishi ne ya taso masa yana sararsa. Idanunsa ne suka cicciko da kwalla sai alokacin ya lura da Laila wadda taci gaba da kukanta.
Tazarce ne ajikinsa Dan haka ya cire ya bawa lailan yace tasa ta samosa a waje yana jiranta acikin taxi.
Hannu na rawa ta karba shi kuma ya fice.
Tana mikewa taga jini duk ya bata katifar da Sauri ta danne bakinta domin kar ihun data kwalla ya fita.
Durkushewa tayi a wajen ta kara bude Sabin babin kuka tana fadin ka cuceni ka lalatamin rayuwata bazan tana yafema Ba.
Sanda tasha kukanta sannan sako rigar ta dauko yageggen hijabinta tayi gyale dashi yayi da tayi kunzugu da rigarta tunda har lokacin jinin bai tsaya Ba, sannan ta fito.
Direct gidansu ya kaita har cikin daki yace tayi wanka ta gyara jikinta bata ya siyo mata magani sannan kar ta Fadawa kowa abinda ya faru tunda yanzu dare ne kar hankali ya tashi. Gone sai ya kaita wurin minal tunda inna ta tafi Maiduguri da zaliha acewarta Idan tabar kadunan zata Dan manta da mutuwar inyasi Daga nan ma sai a kara mata gyaran jiki.
Juyawa yayi zai fice cikin shesshekan kuka tace dama Nasan Cewa bazaka aminta dani Ba!me zakayi da second hand Wanda Dan shaye shaye ya karbe mata budurcinta? Kayi hakuri Nayi kuskure danace ina sonka.
Dawowa yayi ya riko hannunta cikin nashi yace Niko nakeda abinda zanyi dake,kuma batun budurcinki banida damuwa tunda bada kanki kika hada ba,karkisa damuwar Komai aranki domin irin soyaiyar danake miki koke bakimin irinta.
Tace Nasan kana fadan hakan ne Dan kana tausaya min馃槱 wallahi Idan haka sona gara ka fadamin ya fiyemin alkhairi. Yatsansa ya daura akan lebensa yace shhhh ! Karkice haka, kinsan kuma bans miki wasa in ana serious magana wallahi ina sonki koda wannan Abu bai sameki ba ni zan aureki balle da ya kasance akwai faruwar wannan lamarin ki Nayi an kara narka min dalman sonki a zuciyata kuma in kikaga ban aureki ba to Allah ne baisoba now give me that beautiful smile of yours kamin in tafi.
Small smile tayi masa hawaye ya tsiranyo, goge mata yayi yace Idan kika kara kuka Nayi fada dake tace na dena wallahi.
Shafa kanta yayi yace saina dawo.
馃尮.......................
Abangaren su yazeed kuwa minal Adan tsorace da kuma jin haushin tabata da yazeed keyi ta gama gyara dakin zuwa taji gefensa ta tsaya fuskannan a hade tace gani.
Binta yayi da kallo tun Daga saka har kasa da tabbas kayan sun karbeta ba karya.
Hannunta ya riko zai zaunar da ita a cinyarsa aiko ta mike zinbir Kamar ta zauna akan kaya.
Tace wallahi bazan zaunaba karfi da yaji nifa na ganoka ya yazeed dinnan so kake ka miyar dani yar iska ko? Juyawa tayi zatabar dakin yazeed ya janyota luuuu sai gata akan faffadar kirjinsa.....
Anan zan dasa aya, ina godiya sosai da irin soyaiyar da kuke nunawa littafinnan
Ku sanarda Yan uwa da abokan arziki Wanda kuke ganin ya dace su karanta littafinnan.
DAN ALLAH KU SANAR DANI KO KUNAJIN DADIN LITTAFINNAN? SANNAN KUMA ME KUKESO NA KARA KO NA RAGE ACIKI?
Miss untichlobanty馃挄
3th December, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 49*
Kokarin tashi ta fara yi amma yazeed ya riketa kyam kuka ta saka masa tace idan ma magana kakeson fadamin ba sai in zauna a gefenka ba.
Yanzu so kake in name layinmu Na da su talatu suce na gama cika baki yanzu nima na zama kalarsu. Wallahi Idan baba yaji ub*ana zaici da takalminsa.
Yazeed da yayi sakoko yana kallonta yace wayace miki za'a ce miki yar iska? aike kinyi aure kuma nine mijinki Dan haka babu Wanda zaice miki yar iskanci Dan na tabaki. Ki daina damun kanji kinji ? Turo baki tayi tace Gaskiya saina tambayi aunty fauziyya nasani ma ko wayo kakeson kamin? Idan na fada mata yadda mukayi sai inji me zata ce.
Cikin wayo da dabara yazeed ya kwatar da minal gaba daya a jikinshi ba tare da ta lura ba yace ke in banda abin ki kin tana ganin Inda ma'aurata suka fitarda sirrinsu? Ko bakisan Cewa manzon Allah SAW yace: Idan ma'aurata suka shiga daki sukayi wani Abu sannan suka fita waje Suna yadawa to Kamar akan titin sukayi"
Tace kwarai kuwa an fadi mana a islamiya Toh amma abinda ban ganeba shine Wai wani Abu ake nufi ?
Kallonta kawai yazeed yaje cike da mamaki yayinda itako duk hankalinta ya ta'allaka akan gemunsa da take wasa dashi. aransa yace Gaskiya ina da aiki babba a gabana wannan yarinyar fresh karatu take bukata.
Yace kinason in koya miki abin ne ta gyada kai tare da Cewa em.
Hannunsa yasa ya dago da ita ta zauna still tanakan cinyar tasa yayin da take Cewa "kai Gaskiya sajenka lauhi sai kace....." Ba ta karashe zancen ba sanadiyyar hade le'bensu da yazeed yayi guri daya kasa motsi minal tayi saboda gaba daya notinan jikinta sunyi sanyi, wani bakon al'amari aka bijiro mata dashi ba tare da ta Shirya ba.
Yazeed ko tsotsan lips dinta ya farayi kamin ya fara kokarin zura harshensa cikin bakinta amma ita dai tayi tsam tana jinsa yana abunsa janye bakinsa yayi Daga nata kamin yace lesson 1. Duk abinda na miki ki miyarmin kinji ta gyara kai a hankali yace good gwadamin yadda na miki yanzu.
Kwantar da kanta tayi a kirjinsa tace Gaskiya ni kunya nakeji!yace to aiko zanje na karo aure kuma irin zakiyya zan auto Wanda batajin kunya da Sauri ta dago da kanta tace Dan Allah kayi karka karo zanyi wallahi Idan ka karomin irinta na mutu da daya ma ya nakare? murmushi kawai yazzed yayi yace yi mugani to.
Gyara zamanta tayi sosai sannan ta rufe idonta a hankali ta daura lips dinta akan nashi Kamar yadda ya mata.
Wani irin yarrr sukaji dukansu biyu yayinda abin yazeed ya mike sosai. Tsotsa itama tayi sannan ta sake cikin mutuwan jiki yace kitabbatar kin rike Idan yaso zamu daura Daga step 2 in lesson 1,sannan ki dinga yin wanka ko wani lokaci kina saka kaya masu kyau shi zai kara bani kwarin guiwa wajen koyamiki karatun kinji tace um Dan ita jikinta yayi sanyi sosai.
Kwantawa ta kuma yi a jikinsa sannan ta dukunkune Kamar yar kulya babu abinda ke tashi sai numfashinsu.
Yazeed ne ya soma magana a hankali yace ji yadda kika lafe wa mutane a jiki ayi magana mice ke ba yar iska bace馃槣
Dukan kirjinsa tayi tace ai kaika miyar dani yar iska dama dance zama da madaukin kanwa shine kawo farin gashi. Yace to ya kikaji babin Yan iskan akwai dadi? Daga kai tayi akunyace tana murmushi Kamar gabuwa.
Dariya mai Dan Sauti kadan yazeed yayi yanajan kumatunta alamun tsokana yace rosy cheeks dina ta zama yar iska shagwabe fuska tayi tace banaso Dan Allah ya yazeed.
Yazeed yace Gaskiya ai nake fada gobe sai in kaiki amiki register ko ? Harararsa tayi ya mata gwaliyo. Yace amma ki daina cemin yaya ki samamin wani Suna fah.
Tace toh zanyi tunani ko ka cancanci hakan. Faking heart break yayi ya daura hannunsa a kirji,table baki minal tayi tace Wai me kakeson ka fadamin dazun? Yace kawo kunnanki kiji.
Matso da kunnan tayi sannan yace Abu uku ne kinaji ta gyada kai, yace so nake nace miki kinyi kyau sosai, sannan ki dena cilli da hijabinki ta ko ina ko kinason ki wulla akan Dan aljani ne?ta girgiza kai, kuma Idan kika kara cemin kazami to zan nuna miki kazantana Kingane ko? Tace eh yace good.
Tashi take kokarin yi zata fita yace ina zaki ? tace wutan abinci zan kashe in dibo nawa yunwa nakeji, yace me kika dafa?tace dambu ne.
Dan hade gira yayi yace dambu? me kuma wani dambu? Zaro ido waje tayi tace kana nufin bakasan dambu ba yace ban sanshi ba tace cabdi ! nikam bari inje inci abincina.
Yace ki zubo in gwada ci first time in history inji ya abincinnan naku na gargajiya yake ne?
Kallonasa take ido azazzare kamin abincin Dana Daga zakaci? Yq gyada mata kai kamin yace ko zakimin rowane? Girgiza kai tayi tace kaida abinka,Ai ban isa Ba. Shafa kanta yayi yace聽 duk abina naki ne kinji? Kai kawai ta Daga.
Mikewa tayi har ta iso bakin kofa yace inkinsan kinyi kazanta ki barshi.
Bubbuga kafa tayi tace Allah Idan nahadu da inna ko, wato yadani take a duniya ko?
Ince na dena kazantar? Ta karashe magana fuskarta Kamar zatayi kuka.
Yazeed yace au dama kinayin kazantar yanzu ne kika dena? Gaskiya Daga yau zan chaja miki Suna kin tashi Daga rosy cheeks kin Koma YAR KAZAME.
Kuka ta saka tace wallahi Allah ya yazeed karmka sakamin yar KAZAME banasoooo馃槦
Kashe mata ido daya yazeed yayi tareda gwaliyo yace yar KAZAME yi Sauri ki dauko mana abincina馃槣
Fita tayi tana kara volume din kukan shagwaban da takeyi. Koda ta isa kitchen zuzzuba abincin tayi sannan ta danna kararrawar kitchen Kamar yadda tala ta nuna mata.
Aiko baifi 2 mins ba saiga tala tace aunty Amarya sannu da aiki minal tace sannunku ga abinciku nan sai wannan na baba sule ya dawo ba tala tace eh ya dawo ina zai iya zama da madam zakiyya? Ai ko dawasa bazaiyi kuskurennan ba.
Murmushin yaje kawai tayi Dan ta tsani akawo mata zancen wani. Tace taka nace ba; Dan Allah Ku daina muzanta mutum abayan idonta babu kyau,wannan gulmace kuma kinacin namansa ne Idan yayi Abu ba daidai ba in zaki iya magana Kiyi in bazaki iyaba ki bishi da addu'a domin kema kina kuskure ya za kiji聽 Idan akayi miki hakan? Ki dena kinji.
Taka wacce jikinta yayi sanyi tace聽 na gode aunty kuma Insha Allah bazan kara aikata hakan ba Allah ya yafemana zunubanmu minal tace Ameen.
Abincinsu ta dauko da plate biyu na ita da yazeed tareda kunun aya mai sanyi wadda tayi tun da safeta daura akan katon flate sannan ta nufi bangarensa.
Ajiye tray din tayi a parlon sa sannan ta Shiga ciki domin ta kirashi yanda ta barshi haka ta sameshi tace na kawo abincin yana parlour.
Da Hannu ya mata alamun tazo karasawa kusa dashi tayi ya miko mata Hannu alamun ta dagashi.
Gira daya ta Daga irin yadda take mata alamun Idan naki fa? Yace 'yar kazame ai baki isaba sai kin dagni duk lomar dakikeyi karkicemin ta banza ce.
Yayi hakanne dan ya tsokaneta amma ga mamakinsa yaga tasa hannunta cikin nashi sai gashi ya mike.
Zaro ido yayi abinda bai taba yiba聽 hakan yasa wani sihirtaccen kyawunsa ya fito cike da mamaki ya kamo dantsen hannunsa ya na lagutsawa itako ji take Kamar ana mata cakulkuli Dan haka ta soma dariya tana kokarin ta kwace.
Cikin sa'a ta kwace hannunta yazeed ya biyota yana fadin ai baki isa ba, ina kika samosa karfinnan yar kazame?kode namiji na aura ?
Haka suka dinga kewaye dakin Suna dariya kamin Daga karshe yazeed ya samu ya cafkota. Ga mamakinsa kawai sai ta rungumesa sanda ya dauki Yan sakanni ya dawo Daga shock din daya Shiga kamin shima ya kewaya hannunsa a kwankwasonta.
Babu abinda ke tashi a dakin sai sautin nufashinsu kamin minal ta datse shirun ta hangar Cewa nagode.
Yazeed yace namefa tace na Komai ma.
Shima yace nima na gode ta.turo baki tace kwaikwayona kakeyi?ya girgiza kai tace to kaima name yace nima na Komai dukanshi tayi a kirji sannan ta falfala a guje tana fadin aradu kwaikwaya na kayi.
Murmushi yayi kamin ya fito parlourn ya sameta har ta zuba plate daya zata zuba wani yayi saurin riko hannunta yace me kike shirin yi?tace abinci nake zubawa mana yace a wuri zakisa mana ta zaro ido a karo na 5 tace kana nufin tare zamuchi ? Ya Daga kai tace a ah ka......
Bata karasa Ba sakamakon pecking lips dinta da yazeed yayi yace banasin korafi zuba mana.
Zubawa tayi ta cika plate din harda tozo yazeed yace Wai mu bawa zamuci abincin ne ?tace mu biyu mana yace shine kika zuba dayawa haka sai kace mu 5 ne?
Murmushi kawai tayi ta rufe flask din .
Dauko plate din yazeed yayi yakai kan carpet yayinda yaje riko da dayan hannunta.
Masu Neman update gashinan an muku
Miss untichlobanty馃挄
4th December, 2019
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by miss untichlobanty馃尮
*CHAPTER 50*
Janyota yayi har gaban abincin ya zaunar da ita sannan shima ya zauna itakam kallonsa kawai takeyi.
Idan tace ta taba tunanin yazeed zai zama haka to karya takeyi. Da bayan aurenta da sati daya wani ya fada mata Cewa yazeed zai zama haka da babu dalilin dazai hanata jibgarsa.
Shiko yazeed ganin ta tsareshi da ido yasa ya hura mata iska a fuska yace yar kazame ya akayi ne?ko duk Kyan nawa ne yasa ki yin muhawara da zuciyarki?
Bata rai tayi tace duk Wanda yacema kanada kyau to ya cuceka, yace zama ki fadi Gaskiya 'Yan mata.
Plate din data rufo abincin ya bude aiko atake yaji wani irin kamshi ta doki salansar hancinsa hakan yayi sanadiyar cikinsa ta bada wani kqra kuuuuu.
Minal ne ta kyalkyale da dariya yazeed kuma ya turo baki yadda take masa yace yar kazame banaso! Gwaliyo tamai tace nima banaso.
Spoon ya dauka ya dibi loma daya ya fara taunawa wth a straight face. Minal da ta nutsu tana jira taga reaction taga ya yatsine fuska. Take idonta ya cicciko da kwalla yazeed ko harararta yayi cikinbdaga murya yace me wannan kika Fadawa mutane.
Take hawayen dake makale a idonta ya gangaro tace kayi hakuri ni wal.........
Hannu ya Daga mata yace karki wani bani hakuri ya zaki Fadawa mutane abinci Kamar abincin Yan aljanna?so kuke na suma?
Tsayawa kallonsa minal tayi baki a bude yayinda ya sheke da dariya sanda yayi mai isarsa sannan.
Yasa Hannu ya rude mata bakin yana Cewa kar kuda ya Shiga bakinki,maganin mai cemin banida kyau.
Kicin kicin tayi da ido kamin takai masa naushi ya fara tarewa yana Cewa haba yar kazame na yi hakuri,haba yar kyakkyawa.
Hararansa tayi tace kaci sa'a.
Hannu tasa ta dumbuzo loma,yazeed Wanda ke shirin fauna lomarsa ta biyu ya kware a take saboda firgicin katan loman dayaga minal takai baki sannu tace masa sannan ta bashi ruwa yasha ta dawo ta gefensa tana shafa bayansa tunda dazu fuskantar juna suke.
Bayan numfashinsa ya dawo daidai yace yar kazame kicemin bana gani daidai tace da akayi me fa yace da gaske duk wannan lomar bakinki kika sa ? Ta Daga kai yace kafci ai wannan yakai inyi loma Biyar dashi. Tya kiga miko mata cokali yayi sannan shima ya dauka.
Spoon din yasa ya Dino daidai cinsa wani Dan Nasan a baking cokali yakai bakinsa yace lesson number 2, haka kakeson ki dinga cin abinci tace kafci wannan kawai kace na mutu da yunwa Gaskiya saide in gwada maka wani Wanda yafi wannan daina gani ko yayi.
Yace gwada mu gani. Cokalin ta cika sannan yakai baki yace atleast gwara wannan.
Tace to kauna lesson 1 dazan koyama shine ka dinga cin abinci da yawa bude bakinka ta fadi hakan tana ciko cokali, yace ke wannan yamin yawa ai so like in mutu?tace Allah sai kaci Idan Ba haka Ba kuma in daina kulaka. Masa bude bakinka kamin in zaneka ta fadi hakan Kamar da Dan shekara Bihar take magana.
Yazeed badan yaso Ba haka ya bude bakinka ta dinga dura masa itama tanaci sanda suka cinye tas.
Yazeed ji take Kamar an kika sa a wurin saboda irin cikar da cikinsa tayi.
Yace Inda in kara cin wani abinci sai bayan kwana 3 ya fadi hakan yana Dan nishi.
Minal ko dariya tayi alamun kana ruwa sannan tace ai bata in kara maka labari tuwo miyan taushe zamuci anjima kallonta yayi Adan tsorace yace menene kuma wannan tace zaka ganshi.
Yace to kije ki ajiye mana wannan abun anjima sai musha tace Ba sunansa abun Ba sunanshi kunun aya yace to kunun aya.
Yace yauwa har na kusa in manta duk dare zamu dinga yin karatu dake zan koya mini karatu da rubutu kamin ki koma makaranta,ko bakyaso? Washe baki tayi tace inaso mana Nasan baba zaiji dadi sosai in yaji wannan labari kuma Nayi alkawarin in maida hankali into karatu babu wasa yace good girl give me five ta miko masa Hannu sannan suka tafa Suna masu fashewa da dariya.
Mikewa tayi yace don't forget after each lesson sai kin min tausana fa karki dauka na manta ne and also Daga yau karki kara yin wani aiki kinji kawai ki dinga share part dina sai ki mana abinci. Murmushi tayi tace na gode sannan taje ta ajiye musu jug din kunun ayan fridge din falonsa,tunda tasha dazu da safe shiyasa bata wani damu dasha yanzuba.
Bayan ta dawo ta zauna yace toh ni zan Dan fita kinsan Jennifer ce tasa mana poison acikin cappuccino Dan haka dole in tuhumeta Inji Wanda ya sata.
Minal tace ikon Allah mutum mugun ice,Wanda ka yarda dashi shine zai sokeka a baya Allah ka rabamu ka kuma karemu Daga sharrin makiya. Yazeed yace Ameen sannan ya mike domin ya shirya koda ya shirya cikin khakinsa yayi mugun kyau ya fito a parlourn ya tadda ita tana kallon TV yace Toh yar kazame ni na wuce tace to sai ka dawo Allah ya bada sa'a.
Yace Ameen Ba rakiya ne?tace muje Toh in rakaka.
Har bakinka main kofa ta rakashi zata rude kofa yace baki jiba tace um? Yace Daga yau in zan fita zaki dinga min bye bye hug and peck kinji ?tace Nasan me hug din amma me kuma peck?
Pecking lips dinga yayi yace shine peck. Hannunsa ya ware ta rungumesa tanata Washe baki itakam yanzu babu abinda zatayi聽 sai godiya ga Allah Dan rayuwa ta ma ta dadi Alhamdulillah.
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
Da fatan ka yi aikinka daidai Dan banason kuskure irin na wannan banziyar arniyar Jennifer, nasa boka cuku cuku ya kaita gidanne dab tayi min aiki amma saboda rashin kwakwalwarta gashi an kamata.
Ta dayan Abangaren wayan ne akace ma babu wata matsala Nayi Komai daidai yanzu haka nabar gidan
Tace good I will transfer your balance yace thank you ma.
Datse kiran tayi sannan ta kara dialling wani number ringing biyu aka dauka tare da fadin shedaniya uwar shedanu,muguwa uwar mugu,dakalin majina a hauki a zame kihau uban mutum ki zauna daidai. Tawa ni kadai har abada Umarninki shine farin cikina.
Murmushi tayi tace daina Sakai kenan duk yadda raina ya baci to Dana kiraka nake wartsakewa.
Ya ake ciki da batun boka cuku cukun? Yace masoyiya yanzu nabar wurinsa kuma yace an gama Jennifer ko za'a kashe kowa dake numfashi bazata iya tuna Cewa ke kika sata aikin Ba balle ta fada tace good to me yaje bukata.
Saurayin yace yana bukatar jinin bakinka Kare da raguna uku ma aljanunsa naman kuma a soye ta tayi yaji sosai sai ayi dambu da naman Karen wannan nashine tace okay zan turo maka 500k sai kayi duk abunda ake bukata. Yace an gama my love tace to sweetheart sai anjima.
Wani number ta kuma dialling sannan tace da fatan kaga balance dinka yace eh na gani tace yauwa Gaskiya aikin yayi kyau boutiques din sun none kurmus shiyasa ma na kara maka akai. Sai kayi kokari duk kayan da kuka kwashen Ku kukai min warehouse din.
Yace ai nakai tun jiya tace excellent shiyasa nakeson aiki dakai baka disappointing dina. Yace na gode ma. Datse kirar tayi tana murmushin rashin imani tace just wait and see daina rushed rayuwarku gaba daya especially yazeed da zakiyya Dan kune salsalan matsalata.
馃尮............
Koda yazeed ya Shiga mota domin su wuce su hadu da tawagar convoy dinsu,lukman yace mutumina karka dauka ban gani ba. Yazeed yace ni kuma Allah ya sakamin tsanan Dan sa ido ba. Lukman yace to ai ba saka ido bane tunda ina wajen abin ya faru karara a vaiyane yazeed yace kaika jiyota ai shiyslasa tunda ban yarda a Shigo min compound ko securities Suna can nesa.
Amma Gaskiya mutumi na gode domin kuwa shawar da ka bani ita na dauka kuma yanzu haka in nace babu Wanda ya kaini jin dadi banyi karya ba lukman ya sheke da dariya yace anyi abin kenan?yazeed yace kaji matsalata Sakai to babu abinda ya faru. Lukman yace zama faru ai.
Gidan da aka ajiye Jennifer suka shiga. Gaba daya fuskanta ya kukkumbura ba'a ma iya gane kamarta.
Thank you for supporting me!
Don't forget to share and comment
GOOD NIGHT
Miss untichlobanty馃挄
4th December, 2019.
Plss babu cigabane
ReplyDelete