Yammatan gidan su hudu ne kannan farooq, sumayya ce kurum suke ciki daya dashi,sauran duk uban su daya amma kansu hade yake.Suna girmama mansura sun shiga dakin su suna labarin kyan Bilkisu.Da dare suna zaune dakin hajiyar farooq wadda take matukar jin nauyin mansura,da Bilkisu kadai take hira itama jefi jefi tace,yar nan na zata kin yi aure?Bilkisu tayi murmushi tace Allah bai kawo lokacin ba,ta dube ta cike da kulawa,to Allah ya kawo na alkairi kada ki yi ruwan ido ko ki ce sai wane kin ji ko?Bilkisu tace to hajiya,ni dai ma ban samu bane in na samu mai so yaushe ma zan tsaya cewa sai wane? Haka kawai ta ji hajiyan farooq ta kwanta mata a rai har ma tana sha'awar ta gaya mata matsalarta,hajiya ta gyara zama,me ke faruwa ne da ke 'yar nan? Bilkisu tace wlh ban sani ba hajiya,ni dai tunda na taso da sunan wasa ban taba 脿samun wanda yace ina sonki Bilkisu ba. Al'ajabi ne ya cika hajiya tare da tausayinta,tace ke ko da za ku jima ne ai da kun je bauchi in kai ki gurin mahaifinmu,shi malami ne waliyin Allah,
In'sha Allah matsalarki tazo karshe, mansura dake gefe tana jin su,da farko har ta ji haushin Bily menene na tona ma kanta asiri? Amma jin haka sai tace hajiya zamu je don batun aiki kiyi waya ki ce baki jin dadi, nima farooq yasha gaya min ko zamu je gurin kakansu a bauchi, in na gaya mata sai tace mu bar komai hannun Allah hajiya tace to sai ya kai ku in'sha Allah za'a warware matsalar kada ki damu,godiya suka yi sannan suka ci gaba da dan tattaunawa, ran jajibari suka zo gombe washe gari ranar idi suka dauki hanyar bauchi, gidan Modibbo Al'amin Dattijo mai ran karfe nan suka sauka, gida ne na alfarma ginin zamani da 'ya'yanshi suka tsara mishi,farkon gidan,shi ne a sasan farko mai dauke da tafkeken falo da dakunan bacci guda biyu,daga ciki dan autan shi ne jafar tare da iyalinshi tsohon yana da yara kusan guda 16, shidanne maza yayin da goman suke mata, ya'yanshi duk suna da rufin asiri matan kuma duk suna auran masu rufin asiri. Farooq ne yayi musu jagora zuwa falon Modibbo yana zaune kan wata lallausar darduma kan kafet, tsohon mai yawan shekaru ba yada rudu sam tuni matanshi sun jima da rasuwa,farooq ya zauna kusa dashi yana cewa,barka da war haka Akaramakallahu,ka ko shaida mu?Su mansura duk suka zauna gefe,ya dago ido ya kalle shi sannan ya kalle su?Yayi dan murmushi,Ummmarul faruku duk da baka zuwa gaishe ni ai ba zan manta ka ba,wadannan dai su ne ban san su ba, kila iyalinka ne,cikin yar dariya suka gaishe shi, farooq yakara shige mishi sannan yace ka min uzuri saboda nisan garin da nake aiki, amma ai ina yo maka aike ko?Aiken ka baya damuna nafi son kazo ka gaishe ni fiye da sakon ka,yace to zan kula,ni kaina ina son zuwa ka dinga sa min albarka,yanuna mansura ga mai dakin na nan,ya tashi yadauko dady,yana bacci ma yadora mishi akan cinya,ga kuma danka nan tsohon ya rungume shi masha Allah,yayi girma to ka kai su ciki gurin kawun naka,ya mike ko mu shiga ciki mace mai kirki da son mutane ta sauke su cikin farin ciki
da la'asar Farooq yana son ganawa da tsohon amma mutane sun mishi yawa,da yawa 'yan gaisuwar sallah ne, manyan attajirai ne tare da malamai,farooq ya shiga cikin gidan yace ku shirya muje mu gaida umman gidan mai martaba,hajiya fati tace gaskiya ne suma dai nasan gidan yau yan gaisuwar sallah sun yi yawa, amma gara yau akan gobe,tunda gobe hawa gaban bilkisu ya fadi tace a ranta dama farooq suna da dangantaka da gidan sarki?gidan su yarima kenan,sun shirya bilkisu cikin jallabiyya baka ta zagaya dan gyale tamkar yanda larabwa suke yi,takalmin ma baki ne.Hajiya fati ta yi ta yabon kyan bilkisu da tsarinta, mansura cikin shadda galila suka sha anko ita da farooq suka nufi kofar fada. Tsararran gida ne ginin zamani duk da girman gidan harabar cike da motoci na alfarma suka yi parking sannan suka fito me yasa gaban bilkisu yake faduwa? Sun shiga kofafi faluka kashi-kashi, kafin su ka shiga wani tafkeken falo, yana shimfide da carpet kirar china me shegen laushi,
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 24馃彽
Ga kujeru na alfarma kusan gefe uku kowacce da kalarta kuma ta dace da gefen da aka jera su, wata Dattijuwa ta nufo su da fara'a tana cewa Aa umar farooq kune a gidan ina gajiya?yace babu gajiya hajjo umma tana ciki kuwa?Tana nan bari ayi muku iso,ta fito tace gata nan zuwa, sai nan ta shiga gyara mata inda zata zauna,ma'ana ta shiga kakakabe kujerar duk da ba ko kura akanta,kyakkyawar mace ta fito sanye cikin wani leshi na alfarma, gwala-gwalai ne suke kyalli a yatsunta a hannun da na kafa, zuwa wuyanta. Tunda ta fito take kallon bilkisu a zuciyarta kuwa fadi take masha Allah, ta zauna kan kujerar ta dubi farooq da suka zube kan carpet tace idonka kenan ko farooq?Yayi murmushi yace ayimin afuwa umma, ta dubi su mansura tabe to wace ce matar taka cikinsu ko dukansu ne?Yana 'yar dariya ya nuna mansura sannan ya mika mata dady,kiyi hakuri umma ko gombe ma ina dadewa ban zo ba,saboda yanayin aiki wannan karon ma dan hutu ne muka samu,shi ne muka zo gaishe ku, tace to mungode Allah yayi albarka,
.ta nuna Bikisu wadda kanta ke sunkuye tace wannan fa?Bata san me yasa yarinyar ta tsaya mata a zuciya ba,farooq ne yayi magana,kawar mansura ce itama ta biyo mune tayi gaisuwa,umma tace mungode kwarai amma tana da aure ne?Yace tukunna dai tace to Allah yabaki miji na gari,shi da mansu suka ce amin, tace umman taka fa? Tana gaishe ki su sumayya ma ina ga yau za su zo,yaya gurin su anty salma su Aisha?Ta ce duk suna lfy sai gobe zasu zo gaida mai martaba,yace sai dai a gaishe su dan gobe zamu juya Modibbo ma mutane sun mishi yawa bai san ma munzo nan ba,tace yau kam Modibbo ai har dare amsar gaisuwa zai dinga yi.yanzun nan ma nake ma takwaranshi magana yazo yaje ya gaida shi tunda kwana uku zuwa hudu zai yi ya tafi farooq yace Al'amin yazo ne? Tace jiya me martaba yace mishi yazo gida yayi salla farooq yace ya fito ne?Yaushe rabon da mu hadu anfi shekara7,Umma tace kai dashi duk ba masu son zumunci bane bari in kira muku shi ku gaisa,
Dai dai nan wasu 'yanmata su biyu suka soma jere kayan ciye-ciye da shaye-shaye a gaban su mansura da farooq. Bilkisu gabanta ya tsananta faduwa kanta kuma yana kasa wasa take da zoben dake karamin yatsanta, umma ta kira layin Yarima tace babana ga yayanka ummar faruk kazo ku gaisa yace to su dan jira shi zai yi wanka, tace babana kayi sauri na sanka fa,yace to su ka ci gaba da hira tare da 'yan ciye-ciye, bilkisu kam kasa cin komai tayi kuma sai ta samu kanta da matsanancin jin nauyin umma,kula da hakan da umman tayi na kin ki cin komai da bilkisun tayi ne yasa tace ke kin ki cin komai saboda me?Ta dubi umman cikin jin kunya tare da dan murmushi,ta ce na koshi ne.Umma tace ka'idar gidan nan in ka shigo sai kaci abincin gidan,tasa hannu ta dauki yankakken apple ta saka abaki,tana taunawa a hankali idanun umma na kanta yarinyar sha'awa take bata,ta dubi mansura, yaya sunan kawar taki ne?Mansura tace sunanta bilkisu a ranta tace ta ci sunanta,Bilkisu maigadon zinari..
Kamshin data ji ne yasa gabanta ya tsananta faduwa menene take jine kodai mafarkin tane na yau da kullum?Muryar nan ta Yarima ta jiyo mai cike da kasaita da son girma, ya dubi farooq cike da sakin fuska yace,yayana sannu da zuwa,ashe da rabon zamu gaisa ne, farooq ya mike tare da mika mishi hannu,suka yi musabaha yana tambayar farooq iyali ya nuna mansura yace gata nan,ya dubi dady dake wasa kusa da umma, yaronka ne wannan? Yace eh Yarima ya tsugunna kusa da daddy yace Hello handsome, mansura tace ina yini, ya zuba manyan idanunshi kan fuskarta, yace lafiya yaya boy da yayana tace lfy,Bilkisu kam ta kasa dago ido ta kalli Yarima ganinta irin mafarkin da ta saba yi ne,mansu ta tabata tare da yi mata alama da ido wai su gaisa da Yarima, ta dago ta dube shi dai dai sanda ya zubo nashi idon kanta miyan bakinta ya kafe,ta kasa motsa lebanta ma bare ta iya furta wani abu,shi dai ya kauda kanshi amma zuciyarshi cike da mamaki,kyawunta tafi kama da larabawan gabas ta tsakiya,
Fiye da yan nigeria ta kuma kallonshi tana son ta tabbatar da cewa ba mafarki take yi ba,don haka tace Yarima! Ya kalle ta da sauri tayi dan murmushi har yanzun baka huce ba kenan?Cikin mamaki ya dube ta,a ina ki ka sanni ni?Ta dubi mansura sai kuma tayi shiru. Farooq yace cikin mamaki,kin san shi ne Bily?Tace tunda bai gane ni ba bar shi kawai,shiru Yariman yayi yana son tuna inda ya santa,umma cikin dan murmushi tace babana baka santa ba? Ya mike tare da fadin ban taba ganinta bafa, cike da rainin wayo ya fada,har ma su mansura da umma basu ji dadin yanda yayi ba,musamman mansura da tasan cewa Bilkisu ba ta da son magana da maza to ko shi ne Yariman mafarkinta?Shi ko ciki ya koma bilkisu ta bishi da kallo,Yariman mafarkinta ne tabbas, meyasa bai gane taba? Shin ko shi ba ya mafarkinta ne?Abokin wasanta tun suna yara? Suyi fada suyi wasa.
[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 25馃彽
Har suka koma gidan Modibbo mamakin Yarima tayi tana kwance a kan katifa a masaukinsu, Mansura ta dafata Bily a ina ki ka San Yarima? Cike da nadamar yi mishi magana ta ce shi ne Yariman mafarkina, tun muna yara amma dubi yanda yayi min, ba laifinshi ba ne ni ce da na mishi magana, Mansura ta dan yi murmushi kin manta ne cikin mafarki ne? Kin manta cewa mafarki ba gaskiya ba ne? Sam Bilkisu ta manta da wannan batun har ma ta ji haushin kanta game da maganar da ta mishi, tayi data sani sannan ta cika da al'ajabin ganin Yarima yanda ta San shi a mafarki haka yake.
Farooq ne zaune gaban tsohon suna tattaunawa cikin nisan dare, ya sanar mishi da Abu buwa masu yawa game da Bilkisu kuma tsohon ya yi mishi alkawarin ganawa da ita, da safe bayan yayi istihara kan lamarinta, hakan ce ta kasance da safe inda ya gana da Bilkisu ya yi mata yan tambayoyi domin yaga Lamari da yawa cikin al'amuranta, ya dube ta jikata ki kanyi mafarki ne haka ko na ruwa ko na gini ko na wani mutum? Tace eh to na kan yi mafarkin wani tun ina yarinya kuma har yanzu ina yi sai dai in ban kwanta ba, ya dube ta kamar ya ya kike yi? Tace ina mafarkin shi wani dan sarki ne, muna wasa kuma yana yawan ce min in je in nemi tarihinsa, tsohon ya kalle ta na tsawon lokaci tamkar me son ya karanci wani Abu a fuskarta, sannan yace Bilkisu In'sha Allah za ki yi aure, kuma a yanda na fahimci al'amaran mijin naki zai kasance wani ne ma'ana babban mutum ne, kuma lokacin ya kusa sai dai naga rigingimu da yawa kici gaba da addu'a nima zan taya ki, kanta a kasa tace In'sha Allah zan dinga yi zuciyar ta kam tab da tunanin wai ta kusa aure? Kuma mijin dan babban gida ne?
Yanzu zan ba ki wasu addu'a zaki dinga yin su a lokutan sallah da kuma bacci, duk da cewa na lura ke din mai tsayawa ce akan addininta, Allah ya yi miki albarka, tace na gode kwarai, In'sha Allah zan kiyaye, Mansura ko da ta ji labarinn da suka yi da tsohon daga bakin Bily murna ta hau yiwa aminiyarta ta kusa aure, tace da yace mijin da za ki aura dan babban gida ne sai na raya Yarima, Bilkisu ta kalle ta cikin sauri ki ka raya Yarima! Mansura ta ce sosai ma, Bilkisu taja dogon tsaki don Allah ki bar yi min mugun fata,ni fa Yarima nan ba wai ina sonshi ba be, ko cikin mafarkina aboki na dauke shi tunda shekarunmu daya, sannan ma sabonmu cikin mafarki ne tunda dibi wulakancin da yayi min gabanki Mansura ta ce Aa ba zamu shirya ba, ni fa bani da burin Auren yaro karami , Yariman nan fa na girme shi, Allah ya tsare ni da auran karamin yaro ko da Modibbo yace babba ne zan aura ina zaton yana nufin babba mai shekaru, shi ne kuma ya dace dani, Mansura ta ce ba wani ke dai kin cika ra'ayi kuma In'sha Allah shi ne mijin ki, fita Bilkisu tayi har ga Allah cikin ranta ta tsani zancan Yarima. suna cikin shiri sai gombe yau, kuma sai Kaduna, sun gama shiri tana cikin wani Jan yadi mai ratsin baki, tayi kyau sosai Mansura ta ce don Allah kiyi kwalliya ki dan yi shafe shafe zaki yi tamkar balarabiya, tace Aa bana so yar hodannan ta ishe ni tana magana tana fesa turare ta dauki karamin kum tana taje gashin ta zuwa baya farooq suka shigo shi da Yarima da kuma magajin Malam, da saure ta dauke dan kwalinta ta rufe kanta amma duk da haka Yarima ya gani, magajin Malam kam cewa yayi Masha Allah ya dubi Yarima ya mishi rada, kaga hurul inin duniya? Yi yayi tamkar bai ji ba kuma yaki kallon inda take tun da ya kalle ta sau daya, kan kujeru suka zauna Mansura ta gaishe su, suka amsa farooq yace Mansura babu rabon ku kalle hawa yau zamu tafi su kuma yau zasu fara, Mansura ta kalle Bilkisu, Bily ko mu tsaya ne? Ta yatsina fuska, A'a aikina Ku ku tsaya ni kam zani koma bakin aikina Yarima ya saci kallon ta wannan ya kula tana da gadara, shi zata ma gadara? Yaji bata iya ta gaishe shi ba don ma rainin wayo jiya har da nuna tasan shi ? Gashi yanzu ma ko ta gaida su magajin Malam yace ina kwana Malama? Ta dube shi lafiya, ya ya sallah ? Ya ce Alhamdulillah, jin muryarta ta saka magajin Malam rudewa yayin da Yarima yayi tsam da ranshi yana sauraronta, suna hira ne jefi jefi Yarima yace ma farooq mu zamu tafi dama mun zo gaida tsohon nan ne nima gobe ko jibi zan koma in ban zo yau ba maybe ba zan samu zuwa ba farooq yace to kun gaisa ne? Yarima yace kasan shi da mutane, mun zo yana da baki ya dubi magajin Malam duba mana tsohon nan ko bakin sun tafi,
A ran Bilkisu fadi take wannan dan rainin wayo ne,ban da haka mene nashi na Aiken wannan, shi kuma har da zuwa tashi tayi ta fita ta shiga gurin hajiya Fati, ta same ta tana shafa ma yarta mai,yar kyakkyawar yarta mai gashi, ta zauna tare da fadin baby zo nan in shafa miki man, dama gata da son yara. Hajiya tace kuna ta shiri ko? Tace wlh dan ma wannan Yarima ne ko wanene? Ya zo yana jiran Modibbo su gama da baki da yanzun mun dauki hanya, tace Aa Yarima yazo kenan? Tace ina jin shi din ne taci gaba da shafa ma Aisha mai tana sama yarinyar kaya sai ga Yarima ya shigo tare da sallama hajiya tace Aa mutanen wacan kasa yaushe a gari? Yace shekaran jiya nazo, gobe nake tunanin tafiya suka gaisa da yar hira Bilkisu tana jin su ta taje ma Aisha gashin ta sai nan ta dago kai ta dubi hajiya tace, hajiya ina ribbon din ta? Ta jeho mata sai ta dan kalle Yarima cikin sa'a suka hada ido ita ce ta soma kauda kai shi kuma ya mike bari naga dan takwarkwasasshen tsohon nan da ya ki mutuwa, hajiya Fati ta ce lallai haka ma zaka ce? Albarkarshi fa kake ci ya tafi.
Hajiya fati tace Yarima kenan,tsohon nan naka yana matukar ji da kai,kai ko tsiya ka ke mishi,Bilkisu kan ta duk adaure tun jiya tana son sanin wani abu da Yarima,tace shima yana da dangantaka da Dattijon nan ne?Ta dubi Bilkisu baki bude sannan tayi murimushi jikan shi ne kuma shine jika mafi soyuwa agurin shi, kenan suna da dangantaka da farooq? Cewar Bilkisu kanta bata amsa sai ga mansura ta shigo ki zo ga wayarki ta amsa ta fita tana amsa call din sa'adatu sani abokiyar aikinta ce, farooq ya cekuzo mu tafi fa,bilkisu tace to bayan ta gama amsa waya. Yarima zaune gaban kakanshi bayan sun gaisa ya dan mishi tsokana irin ta kaka da jika,sannan yace Aminu ana can ana ta shirmen ko?Ya shafa keyarshi tare da fadin a haba dai muna karatu ne ba shirme ba,yace to yaya batun aure kuma ina fata ka soma shirin yi?Ya dubi tsohon haba wane aure?Ai ba yanzu ba,sai yaushe?Sai na gama karatuna na fara aikina nahuta,yace nan da yaushe kenan? Yarima cikin jin dadi ya gyara zama domin yasan cewa in tsohon ya daure mishi
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽 MEKE FARUWA 26馃彽
In tsohon ya daure mishi gindi ba zai yi ba,to dole ne mai martaba ya hakura, ya soma lissafi, shekara 7 zan yi zuwa 8 yanzu nayi 4 ina cikin na5 , saura 3 da yan watanni, in fara aiki duk dai da komai mu barshi nan da shekara 7 ,lokacin shekaruna sun kai 31 kenan.
In soma neman Auren zuwa yin Auren kila ya kai shekara ko biyu haka in an hada tare kenan, tsohon yayi dan murmushi yace haka ne, to Allah ya taimaka, ya dauko wani Kofi ya juye ruwan zam-zam a ciki, sannan yayi wata addu'a ko nace ya tofa addu'a sannan ya mika mishi,
Yarima ya saka hannu biyu ya karba ya kafa kai ya shanye tare da addu'a nasan zaka zo kafin ka tafi ko? Yace eh to zan zo kila gobe ne fa tafiyar, yace to kayi kokari ka zo din dan zan baka wasu addu'o'i su farooq suka yi sallama suka shiga falon dan yiwa tsohon sallama, kusa da Yarima farooq ya zauna, su Mansura suna gefe Bilkisu a ranta du'a'i take yi Allah yasa kada tsohon yayi maganar matsalar ta a gaban wannan sarkin girman kan, farooq yace mu zamu tafi, tsohon ya ce to Ummarul Faruku, Allah yashi albarka, kawun ka ya yi min bayanin tsaraba, Allah ya kara budi mun gode da zumunci, to Ku tashi na sallame Ku har kai Aminu, ya nuna Bilkisu ke kuma jikata bari in dan ganki.
Ya dubi Dady dan zo nan, dady yaje gunsa ya shafa kansa Allah ya yi maka albarka, Mansura ta ce mun tafi sai wata rana, ya ce to ki kula da zumunci kada ki biye wa mijinki, suka yi dariya tare da mikewa, Yarima kam dama ranman gim kuma ya riga su fita, bayan duk sun fita ya dubi Bilkisu zaki samu dawo wa nan kusa? Tayi shiru sannan ta ce matsala ta yana yin aikina, amma da na samu dan Hutu zan zo, yace shi kenan amma ki rike addu'o'in nan da kyau, tace na gode, Ya ce zan ci gaba da addu'a nima a nan, tashi kije Allah ya yi miki albarka, ta tashi tana godiya suna sallama da Yarima Bilkisu ta fito, ya bita da kallo a ranshi yana tunanin shin KO dai yar uwarsu CE?
Menene hadin ta da. Kakanshi? Ya dan kalle ta yana jin mamakin kyan da cikar halittarta yake yi sai dai kuma kauyanci irin na matan arewa ya hanata ta nuna kyaunta, ya shiga motar bayan shima ya yi sallama da farooq.
Mansura duk murna ta cika ta son surukarta ya kara shigarta, haka nan Bilkisu ji take tamkar mahaifiyarta CE,ta zayyane mata yanda suka yi da tsohon, itama taji dadin jin hakan ta kuma yi fatan alkairi taso su biya gurin Umman Mamanmu amma suna sauri ne jiya da suka je Bauchi, zariya suka tsaya Mamanmu tasha murana jin batun da tazo dashi washe gari da sassafe suka nufi Kaduna ta koma bakin aikinta.
Yarima yana kwance a dakin shi can malesia, ya rasa dalilin da yasa zuciyar shi ta cika da son ya tuno inda ya san yarinyar wadda zuciyar tashi ta mata lakabi da beauty, amma ya kasa, ya sani bashi da saurin mantuwa da sun taba haduwa kyanta ba mai saurin gushewa a rai ba ne da zai tuna, wata zuciyar tace meyasa ka damu kanka da tunanin inda kasan wannan yar kauyen? Tsaki yaja sannan ya mike yana ayyanawa a zuciyar shi, cewa cikin lokutan da ya tsara bai cire na tunanin kowa ba,saboda bai ga macen da ta isa ya tsaya tunaninta ba, can haka ya tashi ya nufi kicin don kora wani abin mai dan sanyi.
Dattijon ya maida hankali ne kan rokon Ubangiji ya karkato hankalin jikanshi ga aure, duk addu'o'in da ya yi mishi cikin ruwa da wadanda zai dinga karanta wa duk saboda hakan ne.
kwana uku tsakani zuciyar Yarima ta tsumu da sha'awar yarinyar da zuciyar shi tasa mata suna beauty, in suna kwance da chelen sai ya dinga rayo beauty, in su Vicky ma yanzu ana dai harka ne kawai, a tsarin shi baya son ya nemi yar arewa don baya son raini, su din basu waye ba, bayan haka ma baya son ya samu zubar da darajar gidansu, to meyasa ya samu kanshi da jin sha'awar yarinyar, ya tuno cikar kirjinta da yanda mazaunanta suke juyawa, lokacin da zata fita daga cikin masaukinsu na gidan kakanshi, tunanin yanda yarinyar take yaji irinta ta yaya, zai kai ga samun haka? Duk da ya kula sai saka yake yana warwarewa, kafin daga karshe ya yanke shawarar neman farooq, bayan sun gaisa ne farooq yace, lallai yau za'ayi ruwa da kankara Yarima yayi murmushi yace dan dai da ba ka da number ta ne shi yasa bana gaisuwa.
yace, haka ne kam dama ina son in tambaye wannan yarinyar ne wani Abu shin kana da number din ta? Farooq yace wace kenan? Yarima yace, wadda Ku ka zo tare din nan,. Ya ce OK kana nufin Bilkisu ba? Yarima yace, kila ita din ce, kawar dai matarka. Farooq yace kana sonta ne?
Ko kusa, zan dai tambaye ta ne wani Abu.farooq dai ya tura mishi number. Yarima ya soma tunanin yanda za ta dauki abin da zai gaya mata, amma sai yace bari ma dai ya fara sanin ina ta san shi? Kuma yaya suke? Ma'ana shi da ita
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 27馃彽
Ta dan watsa ruwa don taji iska kamar yanda ta saba yi kullum in zata kwanta, ta shafa humra mai hade da wani turare mai dan karan kanshi, ta saka rigar baccinta haye gado. Mansu ta shigo tana cewa. Bily ga dan gidan ki wai yau ma nan zai kwana.
Ta jawo shi ta kwantar a bayan ta tace. Ai dama dadyna dan rigima nasan nan zaka kwana ko?
Yace, eh momy. Haka yake kiran su su duka. Momy Bilkisun ma yace momy mansu tace bari in je in kwanta kamshinki yana rinjayata. Bily tace kija mana kofa sai da safe.
Cikin bacci taji wayarta, cike da mamaki ta dauko ta daga saman kanta ba ko shakka kuskuren numba ne tunda ita ban da mansu da mijinta sai kannanta su Sakina sai ko abokan aikinta bata da mai kiranta amma duk da haka sai ta dauka cikin yana yin bacci tayi sallama daga can gefen ya amsa a kasaice, sannan yace.
A ina ne ki ka san Yarima?
Nan ta wartsake, haushin shi ne ya cikata tace rai a bace.
Wanene kuma Yarima? Ni ban san wani Yarima ba, kai Malam. Yayi shiru maganar ta matukar ba shi takaici,amma ya dake.
Kada ki damu please sanar dani.
Tace kai ni fa ban san shi ba.
Dole ne kin san shima don in da ba ki san shi ba ai baza ki nuna mishi sani ba,amma tunda kin ce haka menene dangantarki da Modibbo family?
Wadannan tambayoyin fa sun ishe ni haka, ta ce da shi.
Dole ne kuma ki amsa su. Shima yace a fusace.
Tsaki tayi sannan ta kashe wayar, ta kwanta zuciyar ta tam takaici.
A nashi gefen kam yafi ta bakin ciki sosai, bai taba zaton wata mace zata yi mishi wulakanci haka ba, wai macen ma yar Nigeria kuma yar arewa bakauyiya. Ya girgiza kai.
Alkawari ne sai na rama ko ta halin yaya ne. Ya yi niyyar share ta amma sai ya fasa. Kuma kiranta yayi
ta dauka, wai lafiya?
Amsa min tambaya ta, yace da ita sai ka zo ka shake ni na amsa maka din.
In kin fi son haka za ki samu.
Tace toh bismilla, ina jiran ka. Ta kuma kashewa.
Ya mike tsaye, ba a taba cin mutuncinshi haka ba,mace ce ma tayi mishi haka kai shi ko namiji ma bai taba mishi wannan cin kashin ba, bare Mace wadda bai dauke ta komai ba sai abin nishadi ya na bata daraja ta wannan fanni amma baya daukar raini, kwana yayi yana da na sanin kiranta kuma yanzun in ya barta haka taci nasara akan shi kai sai ya yagata.
Washe gari da safe yana kwance cikin bahon wanka tunani ne ya ci kanshi Sam ya kasa yin komai saboda takaici yana son ya samu mafita amma ya rasa sai dai zuciyar shi tafi tafiya kan Abu daya, ya yi soyayyan karya da ita ma'ana ya daure yace yana sonta sai ta shiga tarkon shi sannan ya yagata, ya gama wanka ya fito bai tsaya gurin shafe shafe ba, kai tsaye ya wuce bedroom din shi waya ya dauka sannan ya zauna kan wata kujera dake gaban dogon madubin nashi, ya soma kiran layinta dai dai suna karyawa ita da dady tana sauri ta fita ta dauki wayar tana dubawa shi din ne,dama ta zargi haka,ta dauka a dake yace.
Ki sanar dani in da ki ka sanni.
In an kifa?
Tace a fusace.
Zaki yarda ma,ba kamar ma in kin shirya yin aure? Dan nasan shi ne kawai zai yi maganin rashin kunyar ki.
A tsaye zancan yazo mata a ranta tace wannan kanshi daya kuwa? Amma a fili sai ta ce
Ba ka isa ka aure ni ba ka min kankanta ka min yaro, nasan kuruciyarka nasan yarintarka don haka ka min kadan kai kanin bayana ne don haka.....
Ya katse ta.
Ke!!! Kina hauka ne? Ni ki ke gaya ma haka ? Ki sani ban taba samun macen da taci min mutun ci irin haka ba,zan nuna miki ni yaro ne sai na aure ki kuma sai na ganar dake kurenki I promise za ki San wanene YARIMA
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 28馃彽
Duk yanda Bily taso kada tasa
abin aranta sai da hakan ya faskara,domin kwana
tayi tana tunanin dalilin Yarima na cewa lallai sai
yasan inda ta sansa,bayan tun farko shine ya
dauko hanyar da bazai yiwu ya sani ba,domin
daya saurareta lokacin data nuna tasansa hakika
daya ji cewa cikin mafarki ne.Sai yanzun yana
nuna shi fa dole ne ma ta sanar dashi saboda
wannan dalilin shine har yake ikirarin aurenta
saboda ya wulakanta ta.Da safe bayan sunyi
wanka da Dady tana shafa masa mai,Mansu ta
shigo Dady yace Good morning Momy,tace How
are you my boy,Bily ta saka dariya tare da cewa
Iye! Yaron yayi hankali.Mansu tace waya koya
maka gaisuwa ne?Ya nuna Bily tare da fadin
Momy din nan ce tace inna gaida Momy da
Abbana zan shiga gidan aljanna,wai haka tace ni
Musulmi ne?Dariya suka kama sakawa,Bily ta
soma saka masa uniform Mamansa tana cewa
yaron nan Bily ya baci da surutu.Bily tace,barshi
yayi zaifi daukan karatu,Mansu tace to ina kwana
ko gaisawa bamuyi ba,Bily ta amsa lafiya
lau,yaya twins?Mansu tace,daina min fatansu,ni
yanzun ma dayan na kosa yayo waje,ciki tuntuni
ya fita watan haihuwarsa?Bily cikin tausayawa
tace,gurin Allah ne lokacin da saura.Daya cika
zaki haihu mu samu yaro ko Dady?Dady yace eh
mana,Abba ma haka yace,Momy zata je asibiti ta
siyo mana yarinya,suka fito a tare suna
dariya.Faruk ya fito sanye cikin suit
bakake,Mansu tace har ka fito baban Dady?Yace
naso in makara ma,yakamata yanzu ina office,Bily
ta dubeshi antashi lafiya yayana?Yace lafiya lau
sister,hakan take ce masa tun kafin ayi bikinsu da
Mansu,ya tafi Mansu tana biye dashi,Bily ta bisu
da kallo.Gaskiya lamarin Mansu yana son
gyara,ace kullum mijinka baya karyawa yake fita?
Duk da an san yanzun da ciki,to tun kafin cikin
ma haka take yi,amma bari ta haihu lafiya zasu
zauna dole ta sake tsari.
PRINCE Modibbo kwance cikin kwamin wanka,zuciyarsa tam da takaici tare da tunanin yanda zai bullo ma matsalarshi,yana sha鈥榓war yarinyar,yana jin haushinta cikin ranshi yana raya zai iya komai dan ya muzguna mata ciki harda aurenta,wata zuciyar tace masa,kai da baka son aure yanzu amma ka yarda ka aureta?Yaba kansa amsa da cewa,zan aureta ne don in nuna mata cewa ni da ita ba tsararraki bane,kamar yanda ta zata,kuma ta sanar dani labarin kuruciyata kamar yanda take tutiya,sai nayi Teaching din ta lesson,I promise.Hannu ya kai kan wayarsa dake gefen bahon wanka ya dauka,layin Bily ya soma nema duk da bai tanadi abinda zai gaya mata ba,shi dai burinsa ya bata mata rai da safennan don yasan yanzu su safiya ne a Nigeria.Suna karyawa daidai wannan lokacin wayar Bily ta shiga ruri,haka kurum taji gabanta yayi wani mugun faduwa,ta jawo wayar ta tsura ma number din ido(+)din data gani shine ya tabbatar mata cewa Yarima ne,domin bata da wanda zai kirata daga kasar waje sai shi,tsaki taja sannan ta ajiye wayar,ki dauka mana Bily,inji Mansu ko baki san number din bane?Kamar ta share sai kuma ta dauka domin in taki dauka Mansu zata so jin dalili,kuma bata shirya bata labarin rigimarsu yanzu ba,domin Mansu tana bukatar hutu da akwantar mata da hankali,tare da guje yin wata magana da zata saka ranta ya baci. Tana daga wayar ta saka akunne ba tare da tace kala ba,fuskantar da yayi an daga wayar shine ya saka sa ya soma magana. Ina son sanin abinda kike takama dashi da har kike gaya min magana son ranki? Me kike takama dashi nace? Wanene ya tsaya miki? Ke 鈥榶ar wanene? In sarauta ce ke 鈥榶ar wane sarki ne? Ko mulki kike takama dashi wane Gwamna ne ya haife ki? Ko ke 鈥榶ar shugaban kasa ce? Ko 鈥榶ar wani mashahurin malami ce? Dan kasuwa sananne ya haife ki? Bani amsa dawa kike takama?
Duk maganganun da yakeyi tana jinsa afuskarta ko wani murmushi ne irin na bakin cikin nan takeyi bata son Mansu tasan halin da take ciki don haka sai ta mike ta nufi dakinta,Mansu ta bita da kallo aranta ko addu鈥榓 takeyi Allah yasa aminiyarta ta samu mai so ne.Bily ta zauna bakin gado daidai sanda yake cewa,ki sani ban taba samun mutumin daya bata min rai ba irinki,ko namiji dan uwana sai ke mace,macen ma bakauyiya.Ki sani sai na saki cikin damuwa fiye da yanda kika sakani,in har ki.....鈥渒ai! Ta katse sa da tsawa,saurara min.Taci gaba da magana da kakkausar murya,kai ba kowa bane,kuma kai ba komai bane,duk abinda kake takama dashi shirme ne,kuma ni na wuce da tunaninka,wanda ya tsaya min ya wuce da tunanin,wanda ya tsaya maka bama kai ba.Don sanin ko ni 鈥榶ar wanene sai ka saka cigiya,aure ne dai nace baka min ba,yaushe ma kashinka yayi kwari?Yaushe aka daina yi maka tsarki....?鈥淗ee!鈥淵a katseta you are very stupid,kin san me kike fada?Bari ma na gaya miki,kada kiyi zaton nima sonki ne yasa nace zan aureki,a鈥榓 zan aureki ne on my own baki san ta hanyar aure ne kurum zan gasaki yanda naso ba tare da mutane sun zargi wani abu ba,domin ni nan ina gudun abinda zai bata sunan Masarautarmu,zaki gane kin maida ma prince magana.Ya kashe wayarsa tare da dauraye jikinsa ya fita daga bahon.Bily ta tsura ma wayarta ido tamkar Yarima yana jiki ne,bakin cikin maganganun daya gaya mata takeyi,amma sai ta danne tare da kudurin inta fita zata sayi layin (zain)don ta samu ta huta,ta mayar da (mtn)din.Lokacin data fito,Mansu ta nemi jin wanda ya kira Bilyn,sai ta shara mata karya da cewa,abokiyar aikinta ce take shaida mata cewa ta fito karfe goma domin yau wani gidan buga jarida za a tura su.
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽 MEKEl FARUWA 29馃彽
Shi ko Yarima bai kara kulewa ba sai da ya gama shirinsa tsaf,don shiga school sai yaga karfe biyu har ma da rabi.Shi da zai shiga Lecture karfe daya,ya shiga wanka sha biyu da rabi ya tsara duk shirinsa zai gama komai zuwa daya don ya bata lokacin wankan sa ne afalo zaune yana tunanin mafita,har lokaci ya wuce.Ya shiga wanka da nufin yayi sauri ya fito,nan ma yarinyar ta masa sanadin rasa Lecture ya koma ya zauna.Ya rike kai bai taba tunanin akwai wata rana da zata zo ya shiga damuwar da zai shagala har haka ba a fili yana cewa dole ne ya dauki matakin gaggawa kan yarinyar nan koya samu nutsuwa karatunsa yana bukatar nutsuwa tare da kwantar da hankali.Cikin dare Mansu ta soma nakuda,Faruk ya buga ma Bily kofa duk sukayi asibiti har dady tunda gidan babu kowa,tasha wuya sannan Faruk ya saka hannu don ai mata aiki.Anyi nasarar ciro mata 鈥榶arta katuwa mai matukar kama da Faruk,satinsu daya suka dawo,鈥榶an Zaria da 鈥榶an Gombe kam gasu nan,sai da sati ya zagayo sannan akayi suna inda jaririya taci sunan Umman Bauchi,Mamansu Yarima kenan.Wannan kara ta jama 鈥榶ar farin jini gurin daukacin family din mai martaba,don duk yayyan Yarima sai da suka zo suna tare da sha tara ta arziki,ga kuma na Umman Bauchin sannan gana mai martaba,dankareriyar sarka da 鈥榶ankunne na gwal kirar Dubai.Kowa ina ka saka ina ka aje yake da yarinyar mai suna Sa鈥榓datu.Lallai tayi sa鈥榓,bayan an watse duk sun koma sai kannan Faruk,鈥榶ammatan su uku Sumayya,Fauziyya da Safina.Bily tana kula dasu tare da duk hirar da sukeyi,kusan duka su ukun basu da labari sai na Yarima.Kamar yanzun data shigo ta samesu,Sumayya ce kwance tana zuba masu Fauziyya labarin Yarima tana fadi,kunsan Allah Safina?Nasha alwashin wannan hutun indai yazo ko na kwana daya ne sai naje zan kuma masa magana ince ina sonsa ko in fada ma Ummansa.Safina tace da kin more,ni kaina sonsa nake,Fauziyya kuwa cewa tayi,ai ke Sumayya banza ce,da nice na samu dama irin taki mahaifiyata da tasa ciki daya,ai koda burauba ma sai na auresa.
Bily tace 鈥淎ssha! Ke ko Fauziyya menene na zunduma ashar haka?Babu kyau,don Allah ki daina鈥�.Duk suka hada baki gurin cewa,don baki ga gayen bane anty Bily,yana da kyau ga aji,dan kwalisa ne na karshe.Bily ta zauna bakin gado tana cewa,ni dai inda zan baku shawara ku dauka,dana ce karku yarda kuce da namiji kuna sonsa, don su maza ba a musu haka,Sumayya tace anty don baki gansa bane,kuma ina bala鈥榠n sonsa,duk hakurina ya kare,zan tunkaresa ne kawai.Safina ma tace Allah yasa ki iya,ya cika kwarjini ne da yawa.Bily ta kalleta aranta ko tausaya mata takeyi don Yarima da take magana bamai mutunci bane,ta sake cewa addini bai hana mace tace tana son namiji ba,amma Sumayya alkunya tana da kyau ko?Tamkar zatayi kuka tace,anty Bily nayi alkunyar bai ma san inayi ba,don haka ni zan gaya masa.Bily ta mike tana cewa,bari naje naga sahibata,na tsaya ina biye ma shirmenku.Safina tace,ba shirme bane anty,kema in kin gansa sai kin soshi,Bily tace Allah ya tsare ni.Fauziyya tace,kila kuma ita bazata soshi ba,tunda itama tana da kyau.Sumayya tace,mai kyaune kuma da mai kyau,anty Bily kuna kama da yaya Modibbo.Bily ta fita tana dariyan shirmensu.Ya sake kallon agogo,karfe takwas,yasan yanzu a Nigeria zai zama biyun dare kenan,tunda awa shidda ne tsakaninsu da Malesia.Bari dai ya bari sai yamma sannan,nan su rana tayi,wata zuciyar tace masa kafin yamma haka zakayi ta zama?Ka tuna fa yanda yarinyar nan taci maka mutunci,me zai hana kasan wanda take ikrarin ya tsaya mata din?Tuna hakan daya yi ya sakasa daukar waya ba shiri ya soma neman layin Magaji zuciyarsa tana kara tuno masa maganganu na batancin da yarinyar ta masa wanda yayi sanadin tsayawar al鈥榓muransa ciki harda karatunsa tare da holewarsa da mata ababen sonsa,bai taba zato akwai wata damuwa da zata shigar masa cikin huldarsa da mata tayi dumu-dumu ba hatta Chelen duk yanda taso taja shi bata iyawa saboda bacin rai.
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 30馃彽
Wayar ta katse ba鈥榓 dauka ba yaja tsaki sannan ya sake neman layin,ringing na uku Magaji ya daga wayar.Yarima yace,haba Magaji adinga rage bacci ana nafila mana,wannan bacci kamar ka mutu?Magaji yace,gara ma ni bacci nake,shima ibada ne wani ma ba鈥榓san ko shi da mata nawa yake ba,Yarima yace,na gode.Yanzu dai duk ba wannan ba,me kasani game da wannan yarinyar?Magaji yace,wacce kenan?Yarima yace,yarinyar da muka hadu gidansu Modibbo kawar matar Faruk din Umman Gombe?Magaji yayi 鈥榶ar dariya tare da cewa,nasan dama wata rana sai ka min zancan yarinyar,domin irin taku ce.Ya dan saurara kafin ya cigaba,gaskiya bansan komai kanta ba,ni da farko ma na zata kun hada iri can cikin dangi.Tsaki Yarima yaja,sannan yace kada ka bani haushi fa Magaji?Tunda kace baka san komai kanta ba,na baka awa sittin da shida daga yanzun,ina son sanin who is she?Ya kashe wayar ba tare da ya jira jin me Magaji zai ce masa ba.Tun misalin goma na safe Magaji ya soma neman sanin Bily,da farko gidan Modibbo ya nufa gurin Hajiya Fati don son sanin wacece Bily?Don nan ya soma ganinta gurin Modibbo ya soma shiga suka gaisa,baice ma Modibbo komai ba game da bukatar Yarima na son sanin Bilyn ba.Sun dan taba hira har ma Modibbo yake cewa,ina labarin abokinka ne?Magaji yace,yana lafiya sannan yace,bari ya shiga su gaisa da kawu.Modibbo yace,kawunku yana Yola,na aikesa sai dai mai dakin tana nan ciki,yace to bari mu gaisa dama nazo gaisheku ne.Sun gaisa da Hajiya,sannan yace dama Hajia ina so in tambayeki ne shin ko kin san Bily kawar matar Faruk din Gombe?Haj.Fati tace,ikon Allah nifa nayi mamakin ganinka da safe tunda kuka zo Yarima na nan ba wani zuwa kuke ba sai sa鈥榓.Tayi 鈥榶ar dariya sannna tace,wallahi ni ban santa ba,daga ita har matar Faruk din.Nima karo na farko kenan da fara ganinsu.Nan dai sukayi sallama ya fito,cikin mota ya soma tunanin wazai tunkara da wannan bukata?Yana ganin abinda sauki ashe duk ya wuce nan.Yayi tunanin to ko Faruk zai kira?Sai kuma yace,kai da Yarima yana son Faruk ya sani da shine mutum na farko da zai fara nema.
Nan Sumayya ta fado masa yarinyar da yake mutuwar so,yace bari ya kirata yau dai yaji muryarta tunda ya shiga ya fita da kyar ya samu number din ta gurin yaya Salma ya kasa kiranta,amma yanzu zai kira kila ma ya samu labarin daya fito nema.Dafda zata yanke Sumayya ta daga wayar duk da cewa wayar tana hannunta,haka nan bata gane ko number din wanene ba.Cike da yanga tace,hello! Ya lumshe ido don jin muryar da yake matukar so,sannan yace,Assalamu alaikum,Sumayya tace ,Wa鈥榓laikassalam,wanene please?Yace au baki gane ni ba?Tace,a鈥榓.Yace,to Magaji ne daga Bauchi,tayi 鈥榶ar dariya.Oh,Magaji ban gane kaba,koda yake bamu taba waya ba,yaya Bauchi? Yace,Bauchi lafiya duk suna gaisheki tace,ina amsawa,yaya Yaya Modibbo?Yace lafiya,dama wani taimako nake so ko zan samu?Tace in baifi karfi na ba,ai bazai gagara ba,yace kin san kawar matar Faruk dinku?Tace anty Bily kenan,nasanta jiyannan muka dawo daga gurinsu.Yace,yauwa don Allah menene labarinta?Kamar ya?Ta bukata,yace,ina nufin kinsan tarihinta?Ta girgiza kai tamkar tana gabansa bansan komai kanta ba,face nasan ita 鈥榶ar Zaria ce kuma ta gama karatu bansan me ta karanta ba,amma yanzu tana bautar kasa ne,yace to na gode,kina da number dinta ne?Tace,eh,amma sabuwar number dinta ne nace ta bani don ina sonta,kai ne zaka shiga?Yace ni wane ni,wani abokina ne.Da sauri tace,Yarima?Yace,a鈥榓.Tayi ajiyar zuciya har abin ya bashi mamaki,yace shikenan kiyi min text din number dinta,tace to.Da taso ta rokesa ya shigar da ita gurin Yarima,sai dai ta fasa,shiko zuciyarsa ta shiga rudu,kada dai Sumayya tana son yarima ne. Zuwa washegari,Magaji duk ya gama bige-bigensa shi dai bai gano komai ba game da Bilkisu,dole sai ya hada da zuwa Zariya.
Kwance agaban gidansa,cikin wani dan gado Yarima ne,daga gefensa Chelen ce tana sanye da Bra da pant,wasa takeyi da gashin kirjnshi,idanunsa lumshe zuciyarsa tana masa nacin me yasa yaba Magaji kwana uku?Ya matsu yasan ita wannan yarinyar 鈥榶ar uban wanene
Ita ko Bily daidai wannan lokacin hankalinta kwance,tunda ta cire(mtn)ta saka(zain)sai dai bata yarda ba kamar yanda tasoyi da,saboda numbers din dake kan(sim)din,tana son ta ba Mansu labari sai sun zauna tukunna.Magaji ya shigo Zaria kai tsaye unguwar T/wada ya nufa gurin wani abokinsa da sukayi karatu a (University)nan Bauchi.Ibrahim dan Zaria ne,a unguwar T/wada.Da kwatance ya iso T/ wadan,nan kuma ya shiga kiran number din Ibrahim amma is switch off.Tun safe yake neman wayar taki shiga,nan ya shiga nemansa ta hanyar tambaya duk ba sa鈥榓,yayi parking nan kusa da wani Masallaci da nufin yayi magriba,zaije ya nemi masauki.Amma cikin yardar Allah yana sahun gaba sai kawai yaga Ibrahim a sahun gabansa.Don haka suna idar da sallah sai yasa hannu ya dafa shi,nan suka fita wajen Masallacin,Ibrahim yana ta mamaki.A dakin matar Ibrahim suna cin abinci,Magaji yana fada masa dalilin zuwansa Zaria,yace na shigo garinku ne don neman labarin wata yarinya Bilkisu.Ibrahim yace,ikon Allah!鈥榶ar wace unguwa ce?Magaji ya kafa kofin ruwa yana sha,sai daya gama sannan yace,nan fa daya,wallahi bansan komai kan yarinyar ba,hasalima sau daya na taba ganinta.Ibrahim yace,to kai batayi maka kwatance bane?Magaji yace,nifa Bauchi muka ganta.Yarima ne ke sonta shine duk ya daga min hankali,yanzu haka gobe yake son jin ko ita wacece.Ibrahim yace,gaskiya ya baka aiki,Zaria tana da yawa,ta ina zaka soma nemanta?Magaji yace,shi yasa na biyo ta kanka tunda kaine dan gari.Babban misalin dazan iya badawa na yarinyar kawai shine,kyawunta nasan saboda tsabar kyanta bazata bata a unguwar da take ba.Ibrahim yace,to kafin a gano unguwar da take fa?Magaji yace to bari dai in mukayi Isha鈥榠 sai mu soma tun yau.Haka kuwa,suna idar da salla suka shiga gari.Da G.R.A suka soma don zaton Magaji na ko 鈥榶ar wani mai halince,gida-gida suka dinga bi cikin G.R.A sune har sha daya da rabi.Washegari ko suka soma da T/Wada,S/ Gari,haka sukayi ta yawon neman inda zasuji labarin Bily,amma shiru.Bayan sunyi sallar La鈥榓sar,suka shiga Ojo da har zasu wuce amma MGJ yace su shiga.
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 31馃彽
La'asar, suka shiga ojo da har za su wuce amma magajin yace su shiga anguwar.
Kai tsaye kusa da wasu samari suka yi dayan ko sai rantsuwa yake yi. Ibrahim yayi musu sallama suka amsa. In ban da dayan da yake ta zuba bai ma san ana sallama ba. Ibrahim yace, bayin Allah muna tambaya ne ko Allah yasa kun sani? Biyu suka hada baki gurin cewa,to magaji ya matso don Allah cikin ku ko akwai Wanda yasan wata Bilkisu? Yaci gaba. Yarinyar tana da kyau na ban mamaki. Samarin suka ringa kallon magaji kamar sunga wani sauna. Dariya ma ya basu, inda dayan yace Malam, Bilkisu suna da yawa a unguwar nan, kuma akasarin su kyawawa ne.Magaji ya yi shiru, can yace ita fa kyanta dabanne, kuma ta gama makaranta. Gaba dayan su suka sa mishi dariya har ma ya ji haushi zai tafi, sai daya daga cikin masu musun kwallon nan mai surutun tsiyan yace, Aa ko dai yana nufin Bilkisun gidan marina? Nan take samarin suka ce ita ce ma, don duk unguwar nan ita ce best a kyau. Magajin Malam da jin haka sai ya dawo yana cewa, don Allah yaro zo mu muje ka gwada min gidansu.Yace,to Magaji ya saka hannu cikin aljihu ya debo kudi 鈥榶an naira ishirin ya mika musu ba tare da ya kirga ba,yace na gode fa,suma suna ta godiya.Ibrahim yace,bari na zauna baya shi ya shiga gaba saboda zai dinga yi maka kwatancen inda zaka bi.Magaji yaji dadin haka,don yana son ya yiwa yaron tambayoyi musamman ma da yaga yaron zaiyi surutu.Ya dubi yaron,sannan yaci gaba da tuki,yace abokina kusa kuke dasu kenan? Yaron yace,E,gida biyu ne tsakaninmu dasu.Amma gurinta zaka?Magaji yace,eh,yaron mai suna Sule,yace ai ina ganin fa bata nan tana Kaduna,aikin gidan TV takeyi,ko bauta ma kasa naji 鈥榶an gidanmu suna cewa, suna zuwa yace da Sule ya shiga ya tambaya ko tana nan.Bayan fitar yaron ne Ibrahim yace da Magaji abokina zaka iya samun labarinta gurin yaron nan,don naga yana da surutu.Magaji yace nima na lura.Sule ya dawo da sakon cewa tana KD.Magaji yace,amma ka tabbata nan ne gidansu?Sule yace,nan ne,ko ba wata doguwa ba?Fara mai kyau?Magaji yace,itace,nan ne gidansu nan yaro ya labarta ma magaji labarin bilkisu
Bayan sun gama magaji ya kawo kudi ya bashi suka maida shi inda suka dauko shi suka tafi yana mamakin inda take zaune dan shi in ta tashi ne diyar wani hamshaki ce dan shi a zaton sa in ba'a samu gidan su a GRA ba toh cikin dai shahararrun unguwannin masu kudi take
Magajin Malam da ya gama ba Yarima labarin Bilkisu kamar yadda yaji sai Yarima yace,ka bincika sosai ko?Magaji yace duk wanda ka saka ba zai zo maka da sama da wannan labarin ba,sannan ga number dinta nan zan turo maka,wane saurayi ke nemanta?Bata dashi.Yarima yayi wani murmushi aransa kuma fadi yake,yarinyar nan ta cuce sa data ce ta sansa har kuma ta mammaida masa da maganganu.Layinta ya soma kira,amma sai aka ce ba zai je ba,nan take ya soma kiran sabon layin da Magaji ya tura masa,wayar ta soma ringing lokacin Bily tana tsaka da yin nafila,bata kalli wayar ba sai data idar ta sallame sannan ta dauko wayar cike da mamaki tace,to wanene wannan?Domin tasan ba kowa bane yasan layin,kuma wane mahaukaci ne da kiranta cikin dare haka?Tana dauko wayar ana sake kira,bata gane number din ba don shima bada wancan layin ya kira ta ba,sannan duk da(+)din data gani batayi tunanin cewa Yarima bane,duk da tasan cewa bata da wanda zai kirata daga wata kasa.Cikin mamaki ta saka wayar akunnenta,kafin tayi magana ya soma cewa,ke!鈥榶ar gidan masu rinin tsumma,鈥榶ar kauyen kayau,鈥榶ar talakawa tilis,鈥榶ar gidan ginin kasa.Kin cuceni da kika ce kin sanni,sai na saka brush na wanke bakina sosai saboda furtawa da nayi na cewa zan aureki.Wanene kike ikrarin kina dashi wadda mahaifinki Malam Mamman ke rini,uwarki ke aikatau?.....kai jahili! Ta katsesa da zafin rai,tana huci tace,kai jakin ina ne?Da baka san talaka da mai kudi da mai sarauta duk Allah ne ya halicce su ba?Kuma babu wanda Allah yafi so face wanda yafi bauta masa,kana zaton wayonka ne yasa Allah ya sakoka cikin gidan sarauta?Je ka shiga Islamiya,kana da bukatar sanin ilmin Tauhidi.Na biyu kuma duk da talaucinmu ba muzo roko gidanku ba,sannan Ubangijina shine wanda ya tsaya min,dashi nake takama,sannan baka san hakkin dan Adam ba da zaka min waya cikin dare.....ya katseta ni kika kira jahili?Tace ,eh.Zaki ga aikin jahilci,zan baki mamaki donni na wuce da tunaninki 鈥榶ar matsiyata kawai.Ya kashe wayarsa duk su biyun sun batawa juna rai,sun gaya ma juna maganganu masu zafi.
Yarima saboda shi namiji ne zufa ya shiga yi tare da yin jifa da wayarsa,yayinda ita kuma ta hau kan gado ta dora hannu akai ta saki kukan bakin ciki,bata iya fada ba,bata taba fada ba,don haka sai abin duk ya zamar mata sabo,don haka kwana tayi tana kuka,kafin gari ya waye fuskarta ta kumbura suntum,haka nan da ciwon kai ta farka,da kyar tayi sallah.Shirun da Mansu taji shiyasa ta fitowa,tasan babu lafiya don tasan Bily da yanzun tana kitchen.Ganinta cikin bargo yasa ta karasawa gaban gadon da sauri taga yanayin da bilyn take ciki hankali tashe tace Billy baki lfy ne ta daga kai kawai ta kamata zuwa jikinta tana mata sannu tace bari toh na kawo maki wani abu ki taba sai muje ko asibiti tace sam ita ba zata ci komai ba mansu Tai banza da ita ta tafi ta hado mata abincin amma sam billy sam taki ci sai kuka take tayi lallashin har ta rasa ya zata yi mata
Mansu ta kalli Faruk tace,baban dady na rasa yanda zanyi da Bily,dama so nake ka gama cin abinci in shaida maka yau ko fita batayi ba,bata ci komai ba sai kuka nayi tambayar duniyar nan taki ta gaya min damuwarta.Ya mike da sauri zo muje,tana zaune ta hada tagumi suka sameta,sannan duk da zafin da akeyi tasha rigar sanyi.Faruk ya jawo kujerar gaban madubi ya zauna agabanta,Mansu kuma ta zauna kusa da ita,ta dafa ta tare da cewa,Bily tunda ni kinki sanar dani damuwarki,ga yayanki nan sai ki gaya masa domin tun kafin in haihu nasan kina da matsala,boye min kawai kikeyi.Kada ki manta fa ni dake ko 鈥榶an biyun da suka fito ciki daya alokaci daya basu kaimu shakuwa ba,ga zatonki bansan kina da damuwa ba?Bily ta kalleta da idanunta da sukayi jajir suka kumbura,sannan ta kalli Faruk tayi wani dan guntun murmushi wanda yayi sanadiyar zubowar hawayen da take kokarin makalewa.Muryarta tana rawa tace kada ku damu,ba wani dogon abu bane ya faru.Ta saka hannu ta kama hancinta ta dan ja iska,sannan taci gaba kun san wani lokaci abu kalilan ne yake bata ma mutum rai,domin zagin da Yarima yayi min wallahi anyi min gomansa amma ban damu ba,sai nasa.Faruk suka kalli juna shida Mansu,sai suka ji zancan wani banbarakwai,Faruk ne ya soma magana,wane Yarima?Ta nuna sa Yarima naka,taci gaba saboda Yarima na canza layi,amma bansan inda ya kuma samun layina ba ya kirani jiya yayi min tatas,harda gorin talauci.Babu abinda yayi min ciwo irin yanda ya zagi uwata.Faruk har suna hada baki da Mansu gurin cewa zagi?Tace zagi dai,Faruk yace tun dama menene ya hada ku?Bata boye ba,nan ta warware masa komai game da mafarkinta da Yarima zuwa ganin data masa,ta masa magana har zuwa sa-in-sar da sukayi dare jiya.Abin yayi matukar bata ran Mansu,Faruk ko cewa yayi sai ya kirasa yaci masa mutunci,nan Bily ta jajirce kan cewa kada ya kirasa,ya kyalesa in halinsa ne zai hadu da daidai shi.Mansu ko kallon Faruk tayi sannan tace,wai shin shi Yarima wanene shi?.
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 32馃彽
YARIMA MODIBBO cikakken sunansa shine Al鈥榓min Isma鈥榠l Abdullah,shine da daya tilo namiji da iyayensa suka mallaka bayan sun haifi 鈥榶aya mata ishirin da biyu.Sarki Isma鈥榠l ya gaji sarauta ne gurin Babansa Abdullah tun yana da rai ya sauka yaba dan nasa Isma鈥榠l mulki.Modibbo shahararren Malami ne mai tarin ilmi,su aminan junane shida mai martaba sarki Abdullah,tare suka taso wannan dalili ne yasa daya baya aiwatar da komai sai da shawarar daya,don haka lokacin daya kawo masa shawarar sauka daga kan mulki,Modibbo ya amince tare kuma da bashi shawarar yayi wa dannasa aure hadi da nadin sarauta.Sarki Abdullah yace shima nufinsa kenan,kuma yana so ne ya hadasa da 鈥榶ar wajenka Sa鈥榓.Modibbo yace,wannan dama tasa donna gani cikin lamarin aurensa danayi istihara.Shekara daya jal da auren hadi da nadin sarautar ta sintilo 鈥榶arta mai kyau inda taci sunan matar Modibbo mahaifiyarsu Sa鈥榓,wato Salma.A takaice sai datayi mata shida sannan ya auri 鈥榶ar sarkin yankin Katsina,itama 鈥榶aya hudu duk mata.Lokacinne sarki Abdullah,Allah yayi masa rasuwa,Wazirinsa shima tsakaninsu sati daya,sai dan Wazirin mai suna Hafiz shima ya gaji mahaifinsa bayannan ya kara mata biyu jere banda sadaka ga kuma kwarkwarori bakin abinda Allah ya halatta masa,duk babu wadda tayi koda barin namiji.Al鈥榓marin daya daga masa hankali kenan,saboda yasan mace ba zatayi mulki ba yana son magaji,haka yake kullum cikin damuwa har girma ya fara shiga,domin da yawa 鈥榶ayan nasa ya aurar dasu.Umma mai babban daki haka suke kiran Haj.Sa鈥榓,tana tausayawa mijinta kullum tana addu鈥榓r Allah yabawa mijinta da namiji koda ba agurinta ba,ko gurin sauran kishiyoyinta ne.Lokaci yayi nisa,haihuwa ma harta tsaitsaya musu,ba wai sun tsufa bane,Allah ne kurum ya tsaida musu ita.Kwatsam!Sai ga ciki jikin Umma mai babban daki,batayi saurin sanarda mai martaba ba saboda tasan tana sanar dashi yanzun nan zai daga hankalisa,sannan ya hana idanunsa bacci yana rokon Allah yasa da namiji ne.Cikin hakane wani dare takai ziyara gurin mahaifinta Modibbo take sanar masa cikin dake gareta.Modibbo yace,na ganki cikin mafarki kina shayarda wani yaro namiji,sai dai ba yana nufin lallai namiji zaki haifa ba,domin mafarkin Annabawane kurum yake zama gaskiya.Murna ta cika ta tace,a taya mu da addu鈥榓,sannan bana son mai martaba yasan da cikin nan.Modibbo ya dubeta yace,saboda me?Tace zaya damu ne,yace wannan ba dalili bane,ki sanar dashi.Sai dai kada ki sanar dashi game da mafarkina,domin karya saka rai.Umma tace,to Modibbo na gode,Allah ya kara lafiya da nisan kwana,sukayi sallama ta dawo gida.Cikin satinne matar waziri Hafiz ta haifi danta namiji,mai martaba yayi murna tamkar shine aka haifamawa.Inda waziri yayi kara yasa ma yaro sunan mahaifin mai martaba,wato Abdullah.Da yake anfi kiran mai martaba Abdullah da Malam,saboda yana da ilmi na addini,don haka sai ake kiransa Magajin Malam,wato jaririn da aka haifa.Wannan yasa mai martaba kara son yaron,Umma mai babban daki ta sanar da mai martaba cewa tana da ciki,murna sosai ya shiga yi tare kuma da rokon Allah.Gefe daya kuma zuciyarsa tana cikin damuwa inya tuna shi bashi da kwan da zai samar da namiji kamar yanda wasu Likitocin suka shaida masa lokacin daya shiga neman taimakonsu.Amma ya dai mikama Allah lamuransa,ya kan tuna kalaman Modibbo da yake cewa,lallai kada ya zama daga cikin bayi masu cire rai daga rahamar Ubangiji.Haka dai ciki yayi ta girma har zuwa lokacin da aka haife sa.Ranar wata Juma鈥榓 an tafi masallaci,an haifesa ne awani asibitin kudi dake nan cikin garin Bauchi bayan Umma tasha wahala.Mai martaba yana Fada Jakadiya ta iso masa da albishir,zancen daya saka mai martaba farin cikin da Fadawa suka jima basu gani ba,nan take yace da Jakadiya ya bata kujerar Makka.Kafin mai jego ta dawo gida labari ya karade garin Bauchi da kewaye.Yanda asibitin ya cika shine dalilin sallamarsu zuwa gida.Tun ranar ake shagalin yanke-yanke har zuwa ranar suna,inda mai martaba ya saka sunan Modibbo yace tunda waziri yayi masa kara ya saka Magajin Malam Sai dai yana fatan inya sake samun wani namijin ya saka masa Abdullah,ko kuma in Modibbo ya girma yayi aure to yana fatan Allah ya barsa da rai yaga ya saka masa sunan Abdullah.Faruk ya dubi su Mansu yace,bazan iya sanar daku gatan da Yarima ya samu ba,duk abinda yakeso shi zaiyi shi zai ci,haka nan shi zai sa,banda yayi sa鈥榓r iyaye masu tarbiya da ilmi hadi da sanin yakamata,to ko daba karamar shagwaba zaiyi ba,ko ince daya lalace,tun yana karami yake zuwa Fada,mai martaba yasa ake kawosa.Wannan abin yasasa girman kai ganin yanda ake zubewa gabansu.Yarima wani yaro ne dan kwalisa mai tsananin tsafta tun yana karaminsa,ga manyance tare da son girma,yana da matukar wahala kaga y shiga harkar wani,haka nan baya son ashiga tasa,halayensa rabi na Turawa ne,ko ince na tsarin Musulunci ne,misali;yana da cika alkawari,in har yayi maka alkawarin abu tabbas ne babu go nd come,sannan ko kai waye karya ne ya zageka abayan idanunka shi dan karara ne ko kaji dadi ko kada kaji bashi da yawan hayaniya,shiyasa nayi mamakin sa- insarku.Ya dan dakata kafin yaci gaba,ya taso shi wani tauraro ne cikin kafatanin 鈥榶an gidansu,haka nan gurin Kakanmu Modibbo bai hadasa da kowa ba,to haka yake cikin dangi kowa yana sonsa.Yayi karatun Nursery da Primary a (C.N.I)wata makaranta ce mafi tsada a Bauchi.Secondary yayi tane akasar Spain,yanzu kuma yana Malesia yana karatun Likita ne fannin mata.Bansan yanda zan gaya muku halin Yarima ba,shi dai dabanne komai nasa dabanne,bansan yanda zanyi muku bayaninsa ba,yana da tsattsauran ra鈥榓yi,haka nan baya son duk wani abu da zaya zubarda mutuncin gidansu,yana da alheri.Kada kuce ina yabonsa hakane halinsa.Bily tace,niko baban dady banga haka ba,Faruk yace ni kaina nasha mamakin lamarinku,shi ba mai shiga cikin lamarin wani bane,baisan fa bacin rai ba.Bily tace,shidai ya sani.Mansu tace,kadai gaya masa ya kiyayeta,ai talaucin ba bawa yake dorama kansa ba,haka nan don kana da kudi ba yana nufin Allah yafi sonka bane ya baka,wani kudinma in mai su baiyi hankali ba sai su kaisa wuta.Yace zan kirasa.
[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 33馃彽
Bily tace,a鈥榓 don son Manzon Allah(S.A.W)kada ka masa magana,bana son kace masa kala!Nifa ya wuce agurina,kada ma yaga kamar ma na damu dashi ne koda abinda ya faru,please forget about him,na bar maganar.Faruk yace shikenan.
Mai martaba ya kalli Umma mai babban daki,sannan yace,Sa鈥榓datu menene na damun kanki don kawai nace mun yanke shawara za鈥榓 nemawa Yarima aure?Ranka ya dade,bawai na damu bane,ina duba karatunsa ne,sannan shekaru ashirin da hudu duka nawa yaron yake?Yayi dan murmushi.To ni banda Modibbo ya tsaidani da tuni ma anyi auren.Amma yanzun ma bazai dauki lokaci ba,Yarima yana bukatar aure.Shiru tayi domin tasan maigidan nata baya zartar da wani al鈥榓mari sai da shawarar mahaifinta masani mai tarin ilimi,haka nan tasan suna da dalilinsu.Ta dubesa sannan tace,ina fata Yarima bawani shirmen yakama ba?Mai martaba yace,a鈥榓 yana da kyau dai muga 鈥榶ayansa in Allah ya nufa zamu ga hakan,tace hakane,a ina ya samu matar?Mai martaba yace,wannan yana ga Modibbo,yace shine zai zabawa takwaran nasa mata.Umma tace,to Allah yasa mu dace,mai martaba yace amin. Duk da takaicin da Yarima yakeji na yarinyar,amma yana jin gara ya yarda kwallon mangwaron ya huta da kuda,don ba zai iya auren yarinyar ba,taje taci sa鈥榓 domin yaso ne ya aureta ya wahalsheta.Yanzu kuma baya jin auren nasu zai yiwu,tunda yaji ita wacece.Sannan ya jinjina ma karfin halinta kasancewarta mace kuma 鈥榶ar talakawa har kuma ta iya ja dashi,tunda ya gano cewa ita din abin tausayi ce to ya barta.Haka Yarima yaci gaba da harkokinsa,ahankali har ya warware ya ma manta da batun wata Bily.
Ga Bily itama tuni ta saka damuwarsa gefe ta shiga harkokinta.Takaicinta daya shine yanda har yau ta kasa yakar mafarkinta,don har yau tana mafarkin Yarima.Kara zage damtse tayi gurin addu鈥榓,Allah ya rabata da mafarkin Yarima,ta tattara komai nata ta barma Allah,ta kuma sha alwashin tabar kara zuwa gurin Modibbo tunda suna da alaka da Yarima,duk da yanda zuciyarta ke son tsohon
Kai ko Faruk sai taji tana jin haushinsa domin tasan dole ne yafi son Yarima da ita,tunda Mamansa da Maman Yarima uwa daya uba daya,wata kusan kuwa ai tafi wata.Wani sashe na zuciyarta ma har yana zargin koma shine ya gaya ma Yarima wacece ita?Amma ta kasa yarda don tasan Faruk bazai mata haka ba. Kawu yayi sallama ya shiga wurin Modibbo,cikin girmamawa ya zauna gaban mahaifin nasa,sannan ya sunkuyar da kai yace,ina yini Modibbo?Lafiya lau,ka dawo lafiya?Yaya kasuwa?Kawu ya amsa da Alhamdulillah.Modibbo yace,to madalla.Ka shiga ciki inka gama harkokinka sai ka fito zan aike ka gidan mai martaba kayo min iso,gobe in muna cikin masu rai zanzo gurinsa.Kawu yace,yanzu bana komai bari naje inna dawo sai na shiga gidan gaba daya.Modibbo yace,to shikenan,in baka gajiba.Amma da kadan huta,kawu yace,ban gaji ba,bari in tafi kawai.Ana shirin tashi daga Fada,kawu ya isa.Ya nemi iso aka shigar dashi Fada.Nan ya isar da sakon Modibbo ya dawo.Mai martaba sam baya son Modibbo yana zuwa da kansa,yafi son ya aiko masa cewa yana nemansa,shiya dauki Modibbo mahaifi ba suruki ba,don haka misalin karfe tara ya fice ta kofar baya inda Magaji ke jiransa cikin mota.Duk gidan babu wanda yasan ya fita,sai ko Magaji da suka fita tare,shima bai san inda zasu je ba,ya dai kirasa awaya yace masa ya amshi mota ya jirasa bakin kofar baya.Sun hau titi sosai,sannan yace Babana gidan Modibbo zamuje,Magaji yana mamakin mai martaba sosai,sam shi bashi da girman kai,sannan duk inda zaije aboye shiya zaba don ya rakashi.Magaji ne ya shiga yayo iso,babu kowa sai Modibbo yana ta jan carbi.Mai martaba ya zauna daura dashi,Modibbo ya mika masa hannu da suyi musabaha kamar koyaushe,mai martaba ya noke hannunsa suka gaisa.Modibbo yace,kai da nace zanzo?Mai martaba yace,Allah gafarta nine yakamata nazo donni danka ne.Modibbo yace,to amma kuma ai kai shugaba ne.Mai martaba yayi murmushi yace,amma Allah gafarta Malam,maganarmu bata shafi mulki ba,don haka in an bar batun mulki an dawo gida ni da ne,kuma duk da nagari dole ne yabi iyayensa Murmushi Modibbo yayi,yasan gaskiya ce mai martaba ya fada.Don haka kai tsaye yaje da fadin dalilin son haduwar tasu game da zancen takwarana ne yace Malam Shehu yazo min da sakamakon binciken dana sa shi.Yaci gaba,Malam Shehu Almajirina ne tunda dadewa,shi dan Zaria ne musamman nasa aka kira minshi awaya na sakasa yayo min bincike menene asalin Bilkisu?Kuma naji komai game da duk wani abu da shari鈥榓 ta nema asali ga mace,sai dai yarinyar ba masu hali bane yace sai muce Alhamdulillah ,don haka sai atashi 鈥榶an neman aure su tafi.Mai martaba yace,to Alhamdulillah, talauci kam sam ba abu bane da zai hana aure ina son zan tura Fadawa zuwa ga mai martaba sarkin Zaria,daga nan sai su nemi dagacin ko hakimin unguwarsu sannan kuma shi sai ya nemi mahaifinta.Modibbo yace,to,Allah ya shige mana gaba,zamu taya ku da addu鈥榓.Kwana uku da wannan magana,mai martaba ya tashi Fadawa da sako zuwa Zaria.Sun samu tarba ta karamci irin na Zage-zagin asali.Sannan suka sanar da sakon mai martaba nan mai martaba yaji dadin wannan batu,sannan yasa aka nemo masa dagacin yankin,ya umarcesa daya nemi mai unguwar Ojo suzo fada gobe.Washegari suka amsa kiran sarki,nan yayi musu bayani,sannan akace su nemo Malam Mamman mai rini,suna dawowa mai unguwa yasa akira masa Malam Mamman.Sakon ya samesa lokacin yana zugama Mamanmu rashin mutuncin nasa,yana cewa karuwancin ya isheshi haka,dole yana son Bily ta dawo gida ya gaji,kilama shi yana tafiya mutane suna nunasa bai sani ba.Shiru ta masa yayinda su Kariman da suka zugosa,suka hada dan dandali suna shewar dariya.Cikin haka ne aka kwada sallama,baiji ba yana sababi sai da aka sake sannan ya shuri takalminsa ya nufi hanyar waje,yana cewa ai wannan yarinyar da haihuwarta gara barinta.Yarinya ta balaga ta balage min agida ta zamar min kaya?Daidai nan ya isa kofar gida,ya mika ma dan sakon me unguwa hannu suka gaisa,dan sakon ya shaida masa cewa mai unguwa yana nemansa.Malam Mamman yace,lafiya dai ko?Lafiya lau,yace dai muzo tare.Suka rankaya gidan mai unguwa.Gefen tabarma suka zauna yayi gaisuwa,mai unguwa yace,Malam Mamman ka samu sakona ko? Mamman yace,kwarai,shine ma dalilin zuwana
0 comments:
Post a Comment