zinat dariya tashiga yi har sumayya tafara k'ulewa tace dallah malama idan kinsan dariya zakiyimin ai sai inkashe wayana daga na fad'a miki damuwata sai kitsareni da dariya.
zinat tsagaida dariyar tayi tace sorry my dear toh ai kece da laifi
sumayya tace ban fahimtaba me kike nufi?
zinat tace kefa ina fad'a miki kiyi baya-baya da mijinki domin su maza da sunga ana shige musu sai kiga sun 6ullo da sabon wulak'anci musamman ma wannan mijin naki, ammah da sunga anyi baya da su toh nan ne zakiga yadda zasu tattaleki.
hmm dear kenan kin mance har da hakan tajamin yarima yak'ara aure?
zinat tace ba dai hakan ba ko kin mance lokacin da kikayi baya da shi yadda yake zuwa yana tattalinki?
Dogon numfashi sumayya taja tace hakane yanzu nafahimta, shikenan dear koma dai mikenan sai munyi waya.
Ohk baby ammah please kikular min da kanki,
Dariya sumayya tayi tace ai kullum ina kular miki da kaina.
Aha dear fiye fa da yadda zaki kularma yarima.
Sumayya tace kema kinsan hakan, dariya sukayi sannan daga baya sukayi sallama.
Bayan sun gama wayar sumayya zagaye d'akin tashiga yi tana tunanin mafita dan ita sam shawarar da zinat tabata bata gansu da ita ba; sai chan daga baya tayi dariya tace yarinya da ni kike ja ayanzu zaki gane ainahin kalata.
Har wajen k'arfe goma Zarah shuru bataje part d'in yarima ba, kad'an kad'an ya duba lokaci duk ji yake ba dad'i rashin zuwanta har lokacin, tsintar kansa yayi da cewa kodai fushi take yi? ahankali yaja d'an guntun tsaki.
A chan 6angaren zarah ko da tagama shirinta kwanciyarta tayi part d'inta dan har a lokacin batada walwala duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi juyi kawai take a saman gadon tana jin wani irin k'unci a ranta, ahaka har bacci yad'auketa.
Yarima ma haka yai ta juyi yana mamakin yadda duk yakasa cire damuwa akan rashin zuwan zarah cikin ransa yace ko dai fushi take da ni? Dasauri yabud'e idanuwansa tare da mik'ewa zaune yadafe kansa ahankali yace me hakan yake nufi da ni? Meyasa nadamu da wannan yarinyar? Chan 6angaren zuciyansa yace masa toh ko sonta kake?
Dasauri yarima yace No! It can't be possible wlh! Mtsw wani irin haushin kansa ne yakamasa chan sai yaja dogon numfashi yace zan iya yarda dai nadamu da itane, to saboda me? Yatambayi kansa,
saboda tana nunamin kulawa,;,yaba kansa amsa,, chan kuma sai yayi murmushi tare da komawa yakwanta yamaida idanuwansa yalumshe yanajin wani iri a ransa, saida yakai kusan 1am sannan yasamu bacci yad'aukesa.
Dasafe ma haka yafita ammah zarah bata lek'osaba, ko da yaje hospital daurewa kawai yayi yaduba patients d'insa ammah duk motsi kad'an sai zarah ta fad'o masa a rai saidai kad'an-kad'an yayi ta jan tsaki.
Zarah ko breakfast bata samu tayiba dan jinta take wani iri sai wajen k'arfe ukku dataga yunwa tacita sosai ta fara gani bibiyu sannan tasa aka dafa mata indomie tad'anci kad'an,
Tun daga ranar bata k'ara shiga sabgar yarima ba haka take tursasa ma zuciyarta dan ganin ta danne sonsa da rashin ganinsa.
Ahaka kwana yadawo hannun sumayya sukasha kwanansu biyu ammah yarima har lokacin shi kansa ya rasa gane abinda yake damunsa, gashi yanason ko da sau d'ayane yasa Zarah a idonsa ammah girman kansa ya hana yaje inda take duk yadda tunaninta yafad'o masa a rai cikin sauri yake janyesa, dan ma yanzu sauk'in ba cika zama yayiba suna ta shirye-shiryen bikki.
Dangin ummi na masarautar agadaz sunzo da dama 6angare d'aya aka fitar musu daga cikin masarautar, ita kanta zarah da tagansu saida ta jinjina kai cikin ranta tace dole yarima da su rahma suyi kyau.
d'iyar yayar ummi ce safiya talik'e ma zarah saboda kusan kansu d'aya kullum tana 6angaren zarah ita take d'ebe ma zarah kewa kasancewar safiya akwai surutu, ahaka ranar girkin zarah yawuce ammah bata lek'a part d'in yarima ba.
Ita kanta sumayya tun lokacin da sukayi kaca-kaca da zarah rabon da zarah tasaka ta a idonta.
Ranar laraba aka gudanar da walimar bikkin rahma a cikin masarautar aka yanki fili akayi inda aka gayyato manyan malamai suka gabatar da wa'azi mai ratsa zuciya a chan tsakiyar fili naga an ajema amarya kujerar alfarma ta zauna alkyabba ce take sanye da ita tayi kyau sosai, daga 6angare guda kuma dangin amarya ne, sai d'ayan gefen dangin ango,
chan gefe nahango zarah da safiya zaune kusa da Aunty husna sunyi zugum suna sauraren wa'azi, nidai har nagama zagayena banga sumayya ba, bayan ank'are mutane sunci sunsha sannan aka watse.
ranar alhamis safiya part d'in zarah takwana tun da safe da suka tashi zarah tahad'a musu breakfast sukayi, nan suka zauna sukaita fira,
Bayan sallar la'asar suka shirya cikin anko d'insu na lace sunyi kyau sosai, musamman zarah d'inkin nata ya kar6eta, tana zaune gaban dressing mirror safiya tashigo, tsaye tayi tana kallon zarah, juyowa zarah tayi takalleta tasakar mata murmushi tace ya dai safiya?
Murmushi safiya tayi tace gaskiya kinyi kyau sosai Mrs prince (kasancewar sunan da take kiran zarah da shi kenan)
Kai safiya banason tsokana.
Wlh ba tsokana bane kema kinsan kina da kyau sosai,
Hmm safiya kenan ammah ai kinfini.
Safiya zaro ido tayi tace waceni? Wlh ban kamo ko k'afarkiba.
Harararta zarah tayi tace kedai kika sani da tsokanarki.
Hmm gimbiya kenan kema ai kinsan gaskiyane, yanzu dai kigama shirin gashi chan anfara d'aukar mutane ana tafiya da su wajen kamun, ko cikin motarki zamuje?
Zarah shuru tayi nad'an lokaci sannan tace anya zan yi driving d'innan? Kodai insa akaimu?
Haba kawai kijamu muje, ni nafiso muje a motarki.
Toh ai bansan wajen da za'ayiba.
Kar kidamu ni nasani sai muje.
Harararta zarah tayi tace keda ba garin kikeba ina kikasan wajen.
Dariya safiya tayi tace Allah dagaske, jiya munje mungano wajen, yanzu dai kiyi sauri kigama nasan anfara yanzu.
Zarah saka sark'a take tace ke banfa tambayi yarima ba.
Chab har ma sai kin tambayesa? Kizo kawai muje ai yasan hidima ake.
Mik'ewa zarah tayi tad'auki veil d'inta tayafa sannan tace bari inzo, bata jira Jin abinda safiya zatace ba tafita.
Ko da ta'isa part d'in yarima itama saida taji wani iri dan rabonta da d'akinsa kusan 5 day's kenan, ganin baya parlour yasa tawuce bedroom nan ma baya nan.
Fitowa tayi takoma part d'inta wayarta tad'auka takirasa har tatsinke bai d'agaba, mamakine yakama zarah nan tak'ara dialing d'in number d'insa sai da takusan tsinkewa sannan yarima yad'aga lokacin yana gidansu shaheed.
Zarah naji ya d'auka bata bari yayi maganaba tace ina wuni?
Daga chan 6angaren yarima saida yalumshe idonsa jin muryar zarah, sai da yayi kusan 3 minutes sannan yace ina jinki.
Zarah ma wani sanyi taji aranta saida tazauna saman gado sannan tace am dan Allah inaso zanje wajen kamu,
Sai kindawo, yarima yafad'a tare da kashe wayarsa.
Zarah murmushi tayi tare da mik'ewa tsaye, had'a ido sukayi da safiya da take tsaye itama tana murmushi, dariya zarah tayi tace kekuma fa?
Itama safiya dariya tayi tace ina kallon yadda ake waya da habiby, harararta zarah tayi tace nidai wuce muje sarkin 'yan sa ido,
Dariya safiya tayi tace gaskiya zanso inga soyayyarki da prince, na sansa da jin kai ku ma matansa yana yi muku? fad'amin sirrin.
Zarah d'aukar hand bag d'inta tayi da key d'in mota tawuce gaba, bayanta safiya tabi tana mata dariya har suka fita sukaje wajen motar zarah,
Zarah bud'e k'ofar tayi tashiga tazauna saida tayi addu'a sannan tatada motar abun yabata mamaki ganin yadda tatada motar batare da tsoron komai ba saboda wannan ne karo nafarko da tafita da mota dan tun lokacin da aka koya mata rabon da tashigeta, ahankali tajasu suna tafiya suna hira ammah duk hankalinta yana ga driving d'in da take ahaka har suka isa babban hall d'in da aka tanada.
Motocine duk inda kaduba gefe guda tasamu tayi parking sannan suka fito suka shiga daga chan gefe suka samu waje suka zauna daidai lokacin amarya da ango suka iso sunyi gwanin kyau, nan abokan amarya sukaje suka tarbosu aka kaisu har wajen da aka tanadar ma ango da amarya,
Daga gefen amarya sumayya ce zaune tayi kyau sosai itama sai yatsina take tana nuna isa, dan ma bawanda yadamu kowa hidimar gabansa yake,
Shaheed ne yaketa baza ido ammah baiga yarima ba ahankali yaduk'o yace ma rahma kinga yarima baizo ba ko? Bayan munyi da shi shiryawa zaije gida yayi.
Murmushi rahma tayi tace indai Bro ne zai aika wlh,
hmm barni da shi, wayarsa yad'auko yashiga kiran wayar yarima,
Yarima da yake shirin fitowa daga part d'insa ganin kiran Shaheed yasa yayi murmushi sannan yawuce yafita,
Lokacin da ya isa hall d'in abokan amaryane a fili suna ta kwasar rawansu shigowar yarima da abokinsa Dr khalil ne yasa gaba d'ayansu suka zuba masa ido, sanye yake cikin boyel milk colour wanda yasha d'inkin zamani ya yi masa kyau sosai kansa babu hula gashin kansa yasha gyara, nan MC yafara masa kirari
Daga chan gaba suka samu table d'in da ba mutane suka zauna, nan maza sukaita zuwa wajensa fuskar yarima a sake suke gaisawa.
Shaheed ne yayi ma MC magana nan mc yazo inda yarima yake cike da girmamawa yagaishesa sannan yace ranka yadad'e ga wajen da aka tanadar maka chan.
Yarima kallon saman high table yayi sannan yace no nan ma ya yi min, MC har yabud'e baki zaiyi magana nan yarima yad'aga masa hannu cikin sauri yawuce yabar wajen.
A chan nahango sumayya tunda yarima yashigo tafara washe baki dan duk a tunaninta wajenta yarima zaizo yazauna sai taga akasin haka ga 'yan mata sai wucewa suke tagaban su yarima ko Allah yasa sutaya, sumayya da take kallon matan murmushin mugunta tayi tace yau duk wacce tanemi tataya mijina za'ayi bura'uba wajen nan.
A chan 6angaren zarah ma safiya hira take yi mata ammah hankalinta gaba d'aya yana wajen yarima tun lokacin da yashigo, ganin matan da suke bi tagabansa yasa tacika fam ji take kamar taje tashak'esu.
Shidai yarima tunda yazauna bayan sun gama gaisawa da mutane dannar wayarsa yake baisan wainar da ake toyawaba.
nan aka fara kiran babban abokin ango yashiga fili ammah yarima ko motsawa baiyiba ganin haka yasa shaheed yace ma MC akira muhammad abokinsa dan yasan babu wanda ya isa yasa yarima yin abunda baisa kansaba, a k'arshe dai saidai muhammad yakoma madadin yarima.
Bayan yashiga yayi rawa sannan aka ce kowa yafita yanzu filin yakoma na amarya da ango.
Shaheed rik'o hannun rahma yayi suka tashi suka safko daga high table suka shiga tsakiyar fili yana rik'e da ita suke d'an takawa ahankali, sumayya ce tamik'e taje tafara watsa musu kud'i nan abokansu ma suka take mata baya aka dinga watsi da kud'i.
Dr khalil yana murmushi yace ranka yadad'e kataso muje muyi ma aboki da k'anwa lik'i.
Ta6e baki yarima yayi yace ba zan iya shiga wajen chan ba saidai kai idan zakayi.
Haba yarima ammah dai da baka kyautaba, yarima bandir biyu na 'yan 1000 yafiddo ya aje gaban dr khalil yace idan kai zakaje sai kawakilceni.
Zaro ido Dr khalil yayi yace ni kuma? A'a kai dai yafi dacewa kaje da kanta.
Banza yarima yayi masa yacigaba da dannar wayarsa,
Ganin haka yasa Dr khalil yamik'e yatafi dan yasan tunda dai har yarima yafurta a'a toh bawanda zaisashi yace eh, nan yashiga yi musu lik'i yace ma shaheed, yarima ne yawakiltashi yayi masu lik'e madadinsa.
Rahma da shaheed kallon juna sukayi sukai murmushi shaheed yace lallai yarima halinsa sai shi.
Safiya kallon zarah tayi tace Mrs prince muje muyi ma adda rahma lik'i,
A'a Safiya kije nidai ina nan,
Rik'o hannunta tayi tace haba Mrs prince dan Allah kitaso muje kinga ba dad'i.
Zarah ba dan tasoba tatashi suna rik'e da hannunsu suka nufi filin.
Kud'i suka ciro daga cikin jakunansu suka fara yi ma amarya da ango lik'e, zarah ji tayi ta bayanta ana zubo mata kud'i itama, dasauri tawaiwaya wani guy ne tagani fuskarsa d'auke da murmushi,
Harararsa zarah tayi tace dallah malam menene haka?
Fuskarsa d'auke da murmushi yace duk cikin sonkine baby kiban izini ingabatar miki da kaina,
Zarah Zaro ido tayi dasauri takai kallonta ga yarima da shima idanuwansa suna wajensu, ai yarima tunda yaga mutumin yana ma zarah lik'i wani irin abune yaji ya tokare masa zuciya wata irin harara yashiga wurga ma zarah,
Zarah saida 'yan cikinta suka kad'a ganin hararar da yarima yayi mata, cikin sauri tafito daga wajen, mutumin ma binta yayi yana ta mata magana ita kanta batama san me yake cemata ba har takoma mazauninta tazauna.
Shima zama yayi gefenta yace haba baby wai menene haka wulak'ancifa baida dad'i daga na ce ina sonki sai ki6ata rai?
Zarah cike da tashin hankali tace dan girman Allah kakyaleni ni fa matar aurece,
Murmushi saurayin yayi yace nima mijin aurene.
Zarah kallon yarima tayi da yake kallonsu idanuwansa sun kad'a sunyi jawur, shima mutumin kallon inda take kallo yayi dan yaga duk ta ida daburcemasa ganin yarima yasa yayi murmushi yace baby kinsan prince ne?
Zarah mik'ewa tayi cikin d'aga murya tace malam na ce kafita harkata ni matar aurece!
Tana fad'in haka tawuce tanufi inda yarima yake zaune ya cika fam.
Kujerar da take kusa da shi taja tazauna rau-rau tayi da ido kamar zatayi kuka tace wlh bani nace yabi niba kuma nafad'a masa ni matar aurece.
Yarima ta6e baki yayi sannan yace wani abu kikaji na ce?
Girgiza kai zarah tayi.
Cikin nuna rashin damuwa yarima yacigaba da dannar wayarsa yana d'an murmushi, nan ko zuciyansa cike take da bak'in ciki,
Daidai lokacin Dr khalil yadawo yaja kujera yazauna, fuskarsa d'auke da murmushi yace amaryarmu watau kinzo kin tsare mijinki dan kar wata tayi miki k'wace ko?
Murmushi zarah tayi sannan tace ina wuni?
Lafiya lou amarya ai da nahangoki nad'auka irin 'yan matan nan ne suka samu kar6uwa wajen yarima ashe amarya ce tazo takasa tatsare abinta, hakan da kikayi yayi kyau nabaki goyon baya dan na lura da 'yan matan amarya sai rawar kai suke akansa sunaso suyi masa magana ammah ya yi mu k'warjini.
Murmushi kawai zarah tayi.
Yarima kallon Dr khalil yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace Dr gaskiya ni nagaji kazo kawai muwuce.
Haba Dr tun yanzu zamu tafi?
Hmm bakaga time d'in sallah ya kusaba? Yarima na fad'in haka yamik'e tare da cewa idan ba zaka tafiba toh ni na tafi dan ko 1 minute ba zan k'araba anan, kallon zarah yayi yace kitashi mutafi.
Zarah ma kallonsa tayi tace da mota nazo, yarima mik'ama Dr khalil key d'in motarsa yayi yace gashi katafo da ita,
Kar6a Dr khalil yayi tare da mik'ewa yace nima ai bazan zaunaba.
Yarima kallon zarah yayi yace muje.
Zarah mik'ewa tayi tabi bayansa, wajen motarta suka nufa nan tamik'a masa key d'in.
Tunda suka fara tafiya kowa shuru yayi, yarima gudu kawai yake da motar, ahankali zarah tajuyo takallesa gani tayi ya wani had'e rai babu alamun fara'a a fuskarsa, janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tace kai dai kasani.
Suna isa gida yana yin parking key d'in motar ya aje mata sannan yabud'e yafita batare da yayi mata magana ba, itama zarah bud'ewa tayi tafita tabi bayansa tana shiga direct part d'inta tawuce.
Saman cushin tazauna tare da jan numfashi tace Allah ya taimakeni da mutumin chan ya ja min bala'i wajen yarima, chan kuma cikin zuciyanta tace bayan basonki yakeba bai damu da ke ba to akan me zaiyi kishinki? Jinjina kai tayi k'wallah duk ta cika mata ido tace hakane kuma, wayarta tad'auka takira safiya nan tashaida mata da ta tafi gida.
Yarima ma zama yayi saman cushin d'in parlournsa yadafe kai hango zarah da wannan mutumin abokin shaheed yayi sai murmushi yake ma zarah, da k'arfi zuciyansa tabuga jingine kansa yayi tare da lumshe idonsa dan shima ya san yayi namijin k'ok'ari da bai d'au matakiba akansa kuma bayason zarah tad'auka ko ya fara damuwa da ita ne, bugu da k'ari a gaban idonsa aka aiwatar da komai babu ta yarda za'ayi yazargeta.
Ahankali yaja tsaki cikin ransa yace toh wai ma akan me zan damu? Gefe guda na zuciyansa yace dole kadamu tunda akwai aurenka abisa kanta.
Kiran sallar magrib ne yasa yamik'e yanufi toilet dan yad'auro alwallah.
wajen k'arfe tara zarah na shirin kwanciya safiya tashigo, kallonta zarah tayi tace kar dai kicemin yanzu kika dawo?
No tun d'azun muka dawo ina cikin gida wajensu mamina, kinsan wani abu?
Girgiza kai zarah tayi.
Wani guy ne yatambayeni wai dagaske kina da aure, inkuma baki da aure toh please inbasa number d'inki, bansan lokacin da nazaro idoba nace karufa min asiri kar kaja prince yasa arufeni, ai matarsa ce.
Shima guy d'in bakiga yadda yarikiceba wai wlh bai d'auka matar aure bace kuma matar prince ya ce dan Allah inbaki hak'uri wlh da ya sani da bazai miki maganaba, kuma ya ce zai samu prince yabasa hak'uri nace ai da kuwa hakan ya fi.
Murmushi zarah tayi tare da kwanciya tamaida idanuwanta tarufe cike da kewar yarima ammah ko bakomai ta d'anji sanyi a ranta da tasakashi a idonta, nan itama rahma takwanta.
Gimbiya sumayya kallon yarima tayi da yake kwance ita kuma tana gefensa tace yarima Allah ya taimaki 'yan matan wajen nan da basuzo wajenkaba dan na lura da kallon da suka dinga yi maka wlh da sunzo da sai munyi bala'i.
Shine katafi ban saniba saidai nawaiga naga bakanan, kuma fa ko lik'i baka shigo kayi masuba.
Murmushi kawai yarima yayi tare da rungumota jikinsa, dasauri sumayya takallesa tace a gajiye fa nake yau, yarima kallonta yayi sannan yamaida idanuwansa yalumshe ganin haka yasa sumayya tagyara kwanciyarta ahaka bacci yayi awon gaba da su.
Ranar juma'a safiya jan zarah tayi sukaje part d'in ummi ammah zarah kasa sakin jiki tayi cikin dangin yarima daga uhm sai uhm-uhm daga k'arshema tattarawa tayi tadawo turakarsu.
Da dare duk inda zaka nufa a cikin masarautar shirin tafiya dinner akeyi, mutane duk sun saka material sunyi kyau.
sumayya tare da rahma sukaje shago akayi musu shiri suka fito gwanin kyau musamman ma amarya rahma.
Wajen 8:30pm zarah tagama shirinta cikin anko d'inta tufke gashin kanta tayi sannan tasaka head d'inta tayi gwanin kyau kallabin tayafa a kafad'arta sannan tazura takalminta tad'auki hand bag d'inta tana fitowa sukayi kici6is da safiya da wata 'yar uwarta tsaye sukayi suna kallonta itama kallonsu tayi fuskarta d'auke da murmushi tace masha Allah 'yan mata kunyi kyau sosai.
Haba Mrs yarima wlh bakiga yadda Kikayi kyau ba kamar kece amaryar.
Uhm zaki dai fara tsokanata ne da kika saba.
Safiya kallon 'yar uwartata tayi tace dan Allah iman ya kika ga matar prince?
Murmushi iman tayi tace wlh tayi kyau sosai ji nake daman ma nice ita.
Ku dai kukasani da tsokanarku, tana fad'in haka tawuce tanufi part d'in yarima tabarsu nan suna ta binta da kallo.
Zarah tana shiga lokacin yarima yana zaune saman 3 seater yana kallo, ahankali tayi sallama, juyowa yarima yayi yakalleta saida gabansa yafad'i ganin wani irin kyau da tayi, Zarah ma tsura masa ido tayi sanye yake cikin dakakkiyar shaddarsa coffee colour ya yi mata wani irin kyau, sun dad'e suna kallon juna sannan yarima yajanye idonsa yamaida ga TV, zarah ajiyar zuciya tasafke sannan tace barka da hutawa.
yauwa yarima yace batare da ya kalletaba.
Ahankali tace dan Allah zan tafi wajen dinner d'in.
Juyowa yarima yayi yakalleta sannan yace bazaki jeba.
Marairaicewa zarah tayi tace dan Allah kabarni
Wani irin kallo yarima yayi mata sannan yace kije kihad'o min coffee.
Zarah aje jakkarta tayi tafita tana turo baki ko da takoma part d'inta kallon su safiya tayi da suke jiranta tace bari tayi sauri tahad'a ma yarima coffee.
Sukace toh, nan tayi sauri tashiga kitchen tad'aura.
Bayan tagama d'auka tayi tanufi part d'insa tana shiga mik'a masa tayi, sannan tace dan Allah toh intafi?
Yarima kallonta yayi tana ta turo baki sannan yace na fad'a miki bazakijeba, juyawa zarah tayi zatabar d'akin cike da jin haushi.
batare da ya kalletaba yace kisamu waje kizauna.
Kujerar da take opposite d'insa tazauna ta cika fam,
A hankali yakai cup d'in bakinsa yana sha.
Wayartace tafara ringing saida takalli yarima da yake kallonta sannan tayi picking tace safiya kutafi kawai bazan samu damar zuwaba, tana fad'in haka takashe wayarta,
Sun dad'e a zaune zarah duk ta k'ule ji take daman yabarta tatafi part d'inta ko baccine tayi.
Har wajen goma saura suna Zaune a haka, Kiran wayan shaheed ne yashigo a wayarsa murmushi yayi sannan yayi picking yace ya dai ango?
A chan 6angaren shaheed cike da k'ulewa yace dallah malam katafo kawani bar mutane suna ta jiranka.
Ta6e baki yarima yayi yace ai bance ajiraniba.
Kar dai kacemin bazaka zo ba? Cewar shaheed
Yarima yace ni ban fad'aba malam.
Toh mujiraka kenan?.
Uhm zan gani, yana fad'in haka yakashe wayarsa gaba d'aya gudun kar ak'ara kiransa.
Zarah da tunda yafara wayar kafesa tayi da ido har yagama ahankali tace toh saidai muzauna gidan tare.
Kallonta yarima yayi yace me kikace?
Dasauri tagirgiza kai tace ba magana nayiba.
Murmushi yarima yayi sannan yacigaba da shan coffee d'insa.
Zarah duba time tayi ganin har 11 ta kusa sannan tamaida kallonta ga yarima tace bacci nake ji inje inkwanta?
Yarima batare da ya kalletaba yace zaki iya shiga kikwanta.
Zarah turo baki tayi tace a nan?
Yarima komawa yayi yakwanta a saman kujerar tare da d'aukar remote yacanza channel.
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Wannan page d'in mallakinkine *Ummu Rahma* marubuciyar *'DAN GARGAJIYA* nagode sosai da kulawarki agareni Allah yabarmu tare_
*PAGE* 3⃣9⃣
Zarah zamanta tayi nan tafara gyangyad'i saida taji baccin yana cinta sosai sannan tamik'e tana turo baki tashiga bedroom d'in yarima,
Har ta kwanta saman gadonsa sai kuma taji bata iya yin bacci haka dan haka tatashi saida tacire kayan sannan tashiga toilet d'insa cikin sauri tayi wanka tafito d'aure da towel, saida tatsane jikinta sannan tafara tunanin abinda zata sanya, raba ido tafarayi daga k'arshe da taga ba yadda zatayi yasa taja tsaki tace nasan halinsa ina iya zuwa zan fita yayi min wulak'anci
saman gadon tahau takwanta tare da k'udindine jikinta da blanket bata kawo komai a rantaba takashe gloves ahaka bacci yad'auketa.
Wajen 12 yarima yakashe kallon yatashi yashiga bedroom kunna gloves d'in yayi tare da kai kallonsa a bed d'insa zarah k'udindine take tana baccinta hankali kwance murmushi yayi sannan yacire kayansa yawuce yashiga bathroom
Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yakashe gloves d'in yakunna marar haske sosai yaje yakwanta gefen zarah,
Zuba mata ido yayi yanayin yadda take bacci tana burgesa, ya dad'e yana kallonta sannan daga baya yajanyo blanket d'in zai rufa shima, zaro ido yayi ganin yadda jikinta yabayyana dan gaba d'aya towel d'in ya rabu da jikinta, k'irjinta yazuba ma ido yana kallo sannan daga baya yaruntse idonsa yana jin wani iri a jikinsa, duk yadda yaso yadaure kasawa yayi ahankali yabud'e idonsa tare da yaye dukkan blanket d'in.
Rungumota yayi jikinsa zarah baccinta kawai take hankalinta kwance ahankali yafara zagaye hannuwansa a jikinta daga k'arshe yamaida yakwantar da ita sannan yacigaba da wasa da kowane sashe na jikinta,
Zarah cikin bacci taji kamar wani abu yana bin jikinta dan ji tayi kamar ana mata tafiyar tsutsa, dak'yar tabud'e idonta tare da safkesu akan yarima da yake a k'irjinta,
Zaro ido tayi tare da d'aura hannunta a kansa tana nema taturesa muryarta tana rawa tace pppplease yarima kadaina,
Yarima duk yafita hayyacinsa ahankali yad'ago kai yakalleta da narkakkun idanuwansa batare da yayi mata magana ba yahad'a bakinsu yafara kissing d'inta, inda hannuwansa suke yawo a kowane sassa na jikinta nan da nan Zarah tamik'a wuya dan dama ita kanta tasan tayi missing d'insa.
Sun dad'e suna abu d'aya har Zarah tagaji ammah yarima bai k'yaletaba saida yagaji dan kansa sannan yabarta.
Zarah tana turo baki takalli yarima da yake kwance idanuwansa a lumshe yana maida numfashi tace shine katasheni daga baccina? Chan k'arshen gado takoma takwanta tare da janyo blanket tarufe jikinta ita kanta wani irin sanyi takeji a ranta fuskarta d'auke da murmushi a haka bacci yayi awon gaba da ita.
Yarima ma yadad'e a haka shi kansa yasan yana cikin farin ciki dan ji yake kamar yau yafara sanin Zarah, ahankali yabud'e idonsa yakalleta chan k'arshen gado ta k'udundune jikinta, jawo wayarsa yayi yaduba time lokacin 1:50am.
Dak'yar yasamu yamik'e jikinsa ba k'wari yashiga bathroom dan yatsarkake jikinta.
Bayan ya fito komawa yayi yakwanta tare da juya mata baya fuskarsa d'auke da murmushi ahaka bacci yayi awon gaba da shi.
Zarah ko da yarima yatayar da ita tayi sallah tana ganin ya tafi masallaci tasaka kayanta tafito takoma part d'inta, tama yi tunani safiya nan takwana ammah sai taga bakowa, saida tatsarkake jikinta sannan tad'auro alwallah tazo tayi sallah.
Bayan tagama saman gadonta tahau tayi kwanciyarta ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Wajen 10 safiya tatashe dak'yar Zarah tatashi dan ji take baccin bai ishetaba, kallon safiya tayi tace kekuma yaushe kika shigo?
Dariya safiya tayi tace tun d'azun nashigo ina parlour jin shuru baki fitoba yasa nashigo, Zarah maida idanuwanta tayi talumshe tace please safiya kibarni inyi baccina.
Janye blanket d'in da Zarah take rufe da shi safiya tayi tace ank'i d'in tunda kinje kunsha love da prince shine har yanzu baki tashiba,
Zarah tunowa tayi da darensu na jiya nan tabud'e idonta tana murmushi tace toh ina wuranki?
Hararta safiya tayi cikin wasa tace aikam dai daruwana tunda kika hana babban abokin ango zuwa dinner, mutane suna ta nemansa.
Da munsa rai tare zakuzo sai mukaji shuru ashe kina nan kin rikitamana prince dan tunda naga gayun da kikayi nasan dak'yar idan prince zai iya barinki kitafi batare da wani abuba
Ta6e baki Zarah tayi tare da tashi zaune tace kinsan dai halin yarima indai yasa kansa toh babu wanda zai iya hanasa dan haka nidai bani nahanasa zuwaba daman chan baiyi niyaba.
Safkowa tayi taje tashiga toilet tayi wanka bayan ta fito zama tayi tatsantsara kwalliyarta sannan tad'auko super English blue colour tasaka nan tamurza d'aurin kallabinta, sark'arta ta gold tasaka nan kyaunta yak'ara fitowa.
da k'arfe biyu daidai aka d'aura auren rahma da shaheed, auren da mutane dayawa suka hallara.
Saida su zarah sukayi sallar azuhur sannan suka shiga cikin gida da yake cike da jama'a.
Safiya jan Zarah tayi suka shiga part d'in sultana sadiya dayake a chan rahma tazauna,
A parlour suka tarar da sultana da sumayya sai wasu abokan sultana sadiya a zaune suna hira.
Cike da girmamawa su zarah suka gaishesu, nan abokan sultana sadiya suka amsa ammah banda ummah da sumayya da suka had'e rai.
Safiya ce takalli sumayya tace Aunty sumayya ina adda rahma?
Ta6e baki sumayya tayi tare da cewa kin bani ajiyartane?
Safiya murmushi tayi tace yi hak'uri dan naga tare kukene saisa natambayeki.
'Daya daga cikin k'awayen ummah ne tace kai sumayya miye nabak'ar magana? Kikasani ko k'awayen amaryane?
yamutsa fuska sumayya tayi tace nasan baku gane wacchan ba? tanuna zarah
Eh gaskiya bamu santaba wacece ita?
Ummah ce tace toh wacece banda munafukar kishiyarta.
'Daya daga cikin matan ne tace tace wlh sumayya banga laifinkiba toh waima ubanmi tazo yi mana a nan?
Sumayya tsaki taja tace gulmar da tasaba ko?
Safiya da zarah tsaye suke suna kallon ikon Allah , k'arama zarah da bata wani damuba dan tasaba da wulak'ancinsu Ummah.
Safiya ce tace haba bayin Allah daga tambaya sai cin mutunci? Sumayya cikin 6acin rai tace ke safiya kikiyayeni ko ranki ya6aci.
Ta6te baki safiya tayi tace Allah yabaku hak'uri sannan takama hannun zarah suka wuce wani room da taga wata abokiyar rahma ta shiga.
A chan saman gado suka hango amarya zaune taci k'walliya tasha kyau har ta k'oshi, gefenta k'awayentane suka zagayeta sunata hira.
Safiya jan zarah tayi sukaje suka zauna bakin gadon.
Zarah fuskarta d'auke da murmushi tace sannunku? ina wuninku?
Gabad'ayansu suka amsa sannan tacema rahma amarya kinsha kyau Allah yabada zaman lafiya.
Murmushi rahma tayi sannan tace Ameen nagode sosai,
'Daya daga cikin 'yan matan amaryace tace gimbiya wannan ma friend d'inki ce?
Girgiza kai rahma tayi tace matar Bro ce.
Kallonta sukayi sukace ba dai yarima ba?
Shi man amaryarsace 2 months kenan yanzu da aurensu, cewar rahma.
Gabad'ayansu suka juyo suka kalli zarah d'aya daga cikinsu tace ashe matansa biyu, masha Allah gaskiya tana da kyau sosai kamar prince.
Wata tace saisa baya kallon mata ashe yasan ya aje mata kyawawa a gidansa.
Sai tayita haifo mana kyawawan yara, cewar safiya.
Zarah da kanta yake sunkuye d'ago kai tayi tagallah ma safiya harara.
Dariya safiya tayi tace daga fad'in gaskiya sai harara?
shuru zarah tayi tak'yaleta, tanajib wasu daga cikin 'yan matan suna ta maganar yarima har taso taji haushi, sai daga baya suka canza hira.
Saida sukayi sallar la'asar sannan suka fito sukaje part d'in dada basu wani dad'eba suka koma na ummin yarima nan suka zauna suna hirarsu.
Saida akayi sallar magrib sannan aka d'auki amarya aka kaita gidanta da yake kusa da masarautar, zarah cikin motarta sukaje gidan amarya, kowa saida yayaba tsari da kyaun gidan anzuba mata gaya na'azo agani dan room nd bedroom 3 akayi mata, nan akaita santi daga k'arshe kowa yayi Allah yabada zaman lafiya sannan aka watse aka bar amarya da wasu abokanta.
Shaheed kallon yarima yayi da yake shirin barin gidansu yace haba yarima yanzu kana nufin bazaka rakani wajen amaryataba?
Harararsa yarima yayi yace akace maka dole sai naje? Idan su muhammad sukaje ai ya wadatas,
Cike da jin haushi Shaheed yace shikenan duk yadda kayi daidaine daman jiya k'in zuwa dinner kayi.
Wai kai baka ganin rahma k'anwace agareni akanme zan dinga shige muku.
Ta6e baki Shaheed yayi yace nikuma abokine wanda bakada kamarsa, toh laifine dan kaje?
Rik'o hannun yarima yayi yace please yarima kataimaka karakani d'akin amaryata.
Murmushi yarima yayi yace toh shikenan naji jeka ka ida shiryawa kazo muje dan ni yau dawuri nakeson komawa gida saboda agajiye nake.
Shaheed yace angama ranka yadad'e.
Wajen k'arfe tara suka raka Shaheed gidansa, Tunda suka shiga d'akin da amarya take yarima bai d'aga kai yakalli kowaba dannar wayarsa kawai yake, nan abokansu da na amarya sukaita tsokanar ango da amarya, duk yadda wasu sukaso yarima yayi magana ko sunsamu shiga ammah baiyiba dan nunawa yayi kamar baisan da zamansu, nan aka k'ara yi musu nasiha sannan suka tashi sukabar gidan,
yarima yana shirin shiga motarsa saiga wasu mata biyu sun iso cikin kwantar da murya sukaimasa sallama.
Rik'e yake da murfin motar ya amsa musu ciki-ciki.
Ahankali d'aya tace dan Allah in bazaka damuba munaso kayi dropping d'inmu.
Ta6e baki yarima yayi sannan yace ba hanyarmu d'ayaba kudaije wajen wad'anchan su k'ila hanyarku sukayi.
Matan kallon juna sukayi sannan d'aya tace toh please zamu iya samun phone number d'inka?
Wani irin kallo yarima yayi musu sannan yashiga motarsa yaja yabarsu nan tsaye.
A k'arshe saidai suka koma wajen sauran abokan ango suka shiga motocinsu Cike da takaicin abinda yarima yayi musu.
Yarima ko da yakoma gida wanka yayi sannan yabi lafiyar gado yakwanta.
Zarah ko daman koda tadawo dak'yar tasamu tayi wanka takwanta batayi tunanin daman zuwa part d'in yarima ba dan agajiye take.
_Toh mudai saidai muce amarya rahma da ango shaheed Allah yabada zaman lafiya_
*BAYAN SATI 'DAYA* 'yan bikki duk suka watse zarah tayi missing d'in safiya dan 'yan kwanakin nan da sukayi sun saba sosai, yanzu saidai zaman kad'aici kuyangintane suke d'ebe mata kewa tahanyar bata labarai masu dad'i.
Yau kasancewar girkin zarah ne kwance take saman bed d'inta kanta yana kallon ceiling da alamu tunani take, ringing d'in wayantane yakatseta ganin mai kiranne yasa tasaki murmushi dan rabonta da yarima tun lokacin bikki, saida takusan tsinkewa sannan tayi picking, yarima baijira tayi maganaba yace kihad'o min coffee yana fad'in haka yakashe wayarsa, fuskar zarah d'auke da murmushi tamik'e tanufi kitchen dan ko bakomai tasan yau zata sakasa a idanunta.
Bayan tagama had'a masa hijab d'inta tasaka kasancewar daman har tayi shirin kwanciya,
Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga yarima dasauri yad'ago kai yakalleta sannan yamaida kansa yacigaba da dannar laptop d'insa, zarah k'arasawa tayi kusa tashi tare da zama gefensa sannan tace ga coffeen.
Yarima batare da ya kalletaba yace ina zuwa,
Haka yabar zarah rik'e da cup har kusan 5 minutes sannan yakar6a,
Mik'ewa zarah tayi zata tafi, batare da ya kalletaba yace ina zakije?
Murmushi zarah tayi tace zanje inkwanta ne.
Ban baki iziniba, cewar yarima da yake dannar laptop.
Marairaicewa tayi tace wlh bacci nakeji.
Ko inda take yarima bai kallaba.
Zarah turo baki tayi sannan takoma tazauna,
Yarima tagefen ido yana kallon yadda take ta fushi.
Zarah ita kanta har tagaji da zaman cikin ranta tace lallai mutumin nan ya raina min wayau miyake nufi da ni ne? Chan kuma sai tayi murmushi tare da cire hijab d'inta nan gashinta yabazu kallon yarima tayi da ya aje cup d'in yana cigaba da dannar laptop, amsar laptop d'in tayi ta aje gefe, yarima binta yayi da kallo cike da mamaki Ahankali tafad'a jikinsa tare da rungumesa cikin shagwa6a tace please kazo muyi bacci kaga har 11 fa tayi.
Wani iri yaji a ransa ammah yadake yace kikwanta mana ni sai nagama abinda nake.
Zarah d'ago kai tayi tana kallon cikin idonsa ahankali takai bakinta cikin nasa yarima daman kamar jira yake nan yacafke nan suka fara rikita junansu sun dad'e a haka sannan zarah tazare jikinta takwanta tare da jawo yarima jikinta dak'yar yasamu yakashe gloves.
yau makara sukayi sallar asuba har saida gari yafara haske sannan zarah tafarka duba time tayi taga 6:15am zaro ido tayi sannan takalli yarima da yake kwance yana bacci har takai hannu zata tadasa sai kuma tafasa, rigarta tajanyo tasaka sannan tafara k'ok'arin janye blanket d'in da yake rufe ciki,
Jin ana jan blanket yasa yafarka, zarah saida tasafka daga saman gadon sannan tace katashi yau munyi late.
Tana fad'in haka tazura hijab inta tafita tabar d'akin.
Yarima janye blanket d'in yayi cikin sauri yamik'e yashiga toilet yana mamakin yadda yamakara yau baisamu jam'i ba, chan kuma yaja tsaki da yatuno basuyi bacci da wuriba.
Zarah ma ko da takoma part d'inta saida tatsarkake jikinta sannan tayi sallah, bayan tagama kitchen taje tashiga nan tafara tunanin me zata had'ama yarima na breakfast, chan kuma sai tayi tunanin tahad'a mai kunun gyad'a dan tasan yana sonsa sosai.
Nan tad'aura ruwan kunun sannan tafere doya tadafa, bayan ta dafu tadaka tayi yamball.
Bayan ta gama wanka tashiga tayi da tafito tashirya cikin swiss less d'inta, veil tayafa sannan taje tad'auki basket d'in taba wata kuyangarta tarik'e suka nufi part d'in yarima
A gaban dressing mirror tagansa tsaye yana fesa turare, d'an rissinawa tayi tagaishesa, tacikin mirror yarima yake kallonta saida yagama fesa turaren sannan ya amsa.
Fuskarta d'auke da murmushi tace breakfast d'inka na dining,
Shuru yarima yayi har ta juya zata fita ahankali yarima yace kije kishirya in ajeki gida.
Dasauri zarah tajuyo cike da jin dad'i tace yanzu?
Eh, ammah idan baki shirya zuwaba shikenan.
Zarah cikin sauri tace na shirya kagani?
Yarima kallonta yayi sannan yazo yawuce yafito yanufi dining,
Zarah bayansa tabi har yaje yazauna nan tayi serving d'insa sannan itama tazauna tayi serving d'inkanta,
nan sukacigaba da breakfast d'insu ba wanda yai magana, zarah saboda zumud'i bataci abun kirkiba tatashi, yarima kallonta yayi yace shi kuma sauran wa zai ida cinye miki?
Itama kallonsa tayi tace nak'oshi ne,
Wani kallo da yayi matane yasa takoma tazauna tacigaba da turawa ba dan tana jin dad'insaba yarima yarigata tashi yabar wajen, nan zarah tabisa da kallo har yashige bedroom d'insa, sannan takalli plate d'insa ahankali tace shi bai cinyeba ammah ni shine zai ce incinye,
Mik'ewa tayi tatattara kayan tasaka cikin basket tad'auka tafita tabar d'akin.
Ko da takoma part d'inta cike da farinciki tashiga bedroom d'inta tad'auko handbag d'inta sannan tacanza veil saida tak'ara gyara fuskarta sannan tafito.
Daidai zata shiga part d'in yarima sai gashi ya fito, kallonta yayi sannan yace muje, a tare suka jero suka fito, guards d'insa har sun taso nan yarima yad'aga musu hannu, d'aya daga cikin motocinsa suka shiga dakansa yayi driving d'insu tunda suka fara tafiya ba wanda yayi magana zarah ko k'agare take su isa gida taga iyayenta wani irin nushad'i takeji dan fuskarta takasa 6oye farin cikinta,
Yarima ta mirror yakalleta yaga tana ta murmushi ta6e baki yayi sannan yamaida kallonsa ga titi, gudu yake sosai cikin k'ank'anin lokaci suka isa gidansu zarah,
zarah cikin sauri tabud'e k'ofar tafita sannan takalli yarima da shima yake kallonta tace zaka shigo kugaisa?
Yarima duban agogon hannunsa yayi sannan yace saidai in nadawo,
Toh sai kadawo Allah yakiyaye,
Ameen yace sannan tarufe motar har saida taga ya tafi sannan tashiga gida da gudu ba ko sallama tana k'walama mama kira,
Mama dasauri tafito d'aki tana cewa muryarwa nakeji kamar ta d'iyata, zarah rungume mama tayi tace oyoyoo mamanmu,
mama dariya tayi tace kai zarah har yanzu dai dasauran k'uriciya atare da ke, dariya zarah tayi tace mamanmu nayi missing d'inki fa, daidai lokacin yaya rauda da rahma suka fito daga d'akinsu sukace wa mukeji kamar zarah?
Zarah kallonsu tayi tana dariya tace nice dai, Aysha ce tazo tarungumeta tana murna mama tace sakarmin ita kar kikayar da ita.
Aysha sakinta tayi tana turo baki tace kai mamanmu ya za'ayi inkayar da ita.
mama jan hannun zarah tayi sukaje suka zauna saman tabarma.
Aysha da yaya rauda kallon juna sukayi sukai murmushi sannan suma sukaje suka zauna.
Cike da girmama zarah tagaishe da mama, nan mama ta amsa mata tare da tambayarta ya mutanen gida?.
Duk suna lafiya lou suna gaisheku.
Mama tace muna amsawa,
Sannan zarah takalli yaya rauda tagaisheta.
fuskar yaya rauda d'auke da murmushi ta amsa, zarah tace ya k'arfin jikinki?
Yaya rauda tace ai jiki ya warke,
Nan Aysha tagaisheta, zarah tace 'yar k'anwata ya gidan?
Dariya tayi tace Alhmdllh, ya yayana?
Zarah murmushi tayi tace yana gaisheku,
Aysha tace nad'auka ma tare zakuzo.
Eh shi yasafkeni yana saurine zaije hospital saisa bai shigoba ammah da anjima zai shigo.
Toh Allah yakawosa lafiya, sukace Ameen.
Daidai lokacin Abbah yashigo d'auke da leda yace a'ah yau mune da manyan bak'i?
Zarah cike da jin dad'i tace abbah sannu da dawowa, ina wuni?
Lafiya lou ya gidan da mijin naki?
Lafiya lou abbah kowa yana lafiya,
toh masha Allah.
kallon mama yayi da takar6i ledar hannunsa yace bari inje insamo abinda za'a dafa ma d'iyata mai d'an dad'i-dad'i.
Zarah murmushi tayi tace a'a abbah kabarsa agirka abinda ke akwai.
harararta rauda tayi tace toh baki isa kiyi mana buk'uluba sannan tace abbah ahad'o da kaji,
Dariya abbah yayi yace toh d'iyata yanzu kau dan yau dole aci dad'i.
gaba d'ayansu dariya sukayi sannan abbah yace sai nadawo, sukace adawo lafiya.
Nan suka zauna suna hira.
Mama shinkafa tabada aka 6arzo mata tad'aura burabusco, bayan abbah yadawo su rauda suka gyara kayan miya nan suka d'aura miyar dage-dage wadda tasha naman kaji, hadad'en kunun zak'i suka had'a.
Bayan sunyi sallar azuhur gabad'ayansu suka had'u saman babbar tabarma suka had'u suna ci cike da nishad'i.
Bayan sun gama atare sukayi wanke-wanke sannan suka zauna hira,
Abbah ne yace zarah rauda tafad'a mana yadda kukayi da wannan saurayin nata saidai banji dad'iba da kika amsar masa kud'insa, murmushi zarah tayi tace abbah kadaina cewa haka hak'intane fa na amsar mata kaduba kaga irin wahalar da tasha ai dan taci kud'in bawani abu bane,
jinjina kai abbah yayi yace hakane to yanzu ya kuke gani ya dace ayi da kud'in?
Mama ce tace nidai atawa shawarar ina ganin yafi dacewa shine kasiyar da wannan gidan kasamu gida wanda yad'anfi wannan girma ko mai d'akuna ukkune kasiya mana tunda akwai sauran kud'i a wajenka,
Gabad'ansu sukace hakan ko za'ayi,
Abbah yace bank'i ta takuba toh yanzu idan maganar auren Aysha tatashi ya za'ayi?
Zarah ce tayi karaf tace aure kuma abbah?
Murmushi sukayi gabad'ayansu sannan abbah yace kiyi hak'uri bamu fad'a mikiba malam bello ne yazo yasameni yace yanaso abashi aurenta,
Zarah a firgice tace malam bello?
Mama ce tace Malam bello dai naki,
Zarah kallon Aysha tayi tace daman soyayya kukeyi?
Aysha dasauri tagirgiza kai tace wlh bahaka bane Aunty zarah shine yace yana sona da nak'i amince masa sai yasamu abbah yafad'a masa kuma nanashi labarin rayuwata yace ba matsala daman yasan komai tunda yanzu nadaina toh yana sona yanaso inmaye gurbinki, yanzu haka har danginsa sunzo sati guda da yawuce sun nemi aurena,
Zarah farincikine fal yabayyana a fuskarta cike da jin dad'i tace gaskiya nayi murna sosai kar kidamu 'yar uwata ni tuni nacire malam bello daga cikin zuciyata gaskiya nayi murna Allah yakaimu musha bikki.
Sukace Ameen,
bud'e jakkarta tayi tad'auko cheque d'in 500,000 tamik'a ma abbah tace abbana nima ga tawa gudunmawar ataimaka acanza mana gida insha Allahu ko da bikkin Aysha ya zo Allah zai rufa mana asiri.
Abbah yace a'a zarah baza'ayi hakaba ki aje kud'inki rannan ma fa kin aiko mana da kud'i kema kisamu abu mai amfani kisiya.
Zarah tace abbah bana tunani zan iya tara kud'i alhalin ku kuna nan kune yafi cancanta kutara baniba, ban ta6a tunanin samun naira d'ayaba batare da kun fad'omin arai ba, k'wallah ce tacika mata ido tace abbah dan Allah kataimaka kakar6a kusanya min albarka.
Dukansu tabasu tausayi yanayin yadda tayi maganar nan abbah yakar6a shi da mama sukaita sa mata albarka suna jinjina halin 'yar tasu tabbas sunsan sunyi sa'ar d'iya kamar zarah.
Abbah yace toh shikenan kuban lokaci zanyi tunani akan maganar canza gidan ammah fa kuyi hak'uri dan bawani babba za'a siyaba.
Sukace eh bakomai mun amince.
Abbah yace toh masha Allah, Allah yayimuku albarka gabad'ayanku.
Cikin jin dad'i sukace Ameen y rabb.
Nan abbah yamik'e yace bari inje wajen Yaya muda mugaisa.
Sukace Adawo lafiya.
Bayan ya fita nan suka cigaba da hirarsu.
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Sak'on gaisuwa da jinjina agareki yayata takaina *SADNAF* kinfi k'arfin page a wajena kema kin sani ina ji dake irin sosai d'innan, nagode sosai da soyayyarki agareni saidai ince Allah yabarmu tare, I hrt u dear😘_
*PAGE* 4⃣0⃣
Zarah sawa tayi Aysha taje gidansu khairy takira mata ita nan suka zauna suna ta hirarsu cike da jin dad'i da nishad'i.
Bayan sallar isha'i yarima ne ya iso k'ofar gidansu Zarah wayarsa yad'auka yakirata, zarah ganin maikiranta yasa tayi murmushi sannan tayi picking tare da yin sallama,
Daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi sannan yace gani a waje,.zarah ahankali tace toh zaka shigo kugaisa da su abbah ko?
Jim yarima yayi sai chan yace kizo kishigo da ni, yana fad'in haka yakashe wayarsa.
Zarah mik'ewa tayi tayafa gyalenta sannan tace ma su abbah ga yarima nan zai shigo sugaisa, abbah yace toh badamuwa.
Fitowa tayi waje tagansa zaune cikin motarsa ya jingine kansa a sit d'in da yake zaune sai yafiddo k'afa d'aya a waje inda d'ayar take cikin motar.
Takawa tayi ta isa inda yake tarik'e k'ofar motar tare da yin sallama.
Yarima bud'e idanuwansa yayi da suke lumshe yakalleta, ahankali ya amsa mata.
Murmushi zarah tayi tace sannu da hanya ya aiki?
Yarima saida yajanye idonsa daga kallonta sannan yace Alhmdllh.
Bismillah kashigo kugaisa, cewar zarah.
Ahankali yarima yafito daga motar yamaida yarufe chan kuma sai yabud'e yad'auko hularsa yasaka, kallon zarah yayi da tatsaresa da ido yace kallon fa?
Fuskar zarah d'auke da murmushi tace kayi kyau
'Dan guntun murmushi yarima yayi sannan yace kema haka.
Dariya zarah tayi tace ni kyaun mi zanyi ai kafini.
Yarima ma kallonta yake yace shikenan mushiga dare yakeyi,
Zarah tsayawa tayi tace wuce gaba sai inbiyoka.
Harararta yarima yayi yace gidankune ko namu?
Murmushi zarah tayi sannan tawuce nan yabi bayanta har cikin gida, da sallamarsa yashiga, nan suka amsa masa.
Saman tabarmar da aka shimfid'a masa yazauna, cike da girmamawa yagaishe da abbah da mama suka amsa tare da tambayarsa mutanen gida.
Kansa sunne k'asa yace duk suna lafiya suna gaisheku.
Abbah yace masha Allah muna amsawa.
Sannan rauda da Aysha suka gaishesa, cikin sakin fuska ya amsa masu tare da tambayar rauda ya k'arfin jiki tace Alhmdllh yanzu ta warke.
Mama kallon zarah tayi tace kikawo masa abinci man,.zarah mik'ewa tayi tace toh mama.
Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh abarsa kawai a k'oshe nake.
Kusan a tare su abbah suka mik'e sannan yace a'a yarima nan ma ai gidane bari mubaka waje kaci, nan suka wuce suka shiga d'aki, daidai lokacin zarah tadawo d'auke da kulolin abinci ta aje gabansa sannan tazauna gefensa, tana bud'ewa wani irin k'amshi yadaki hancin yarima nan tafara serving d'insa, bayan tagama kallonsa tayi fuskarta d'auke da murmushi tace bismillah,
Yarima d'aukar spoon d'in yayi yafara cin burabuscon sannan yakalli zarah da take wasa da gefen gyalenta yace ke bazaki ciba?
Kallonsa tayi tana murmushi tace ni naci d'azun,
Daganan Yarima yacigaba da ci, bai wani ci dayawaba yature plate d'in saidai kunun zak'in da yasha sosai,
Zarah kallon plate d'in tayi tace ba dai ka k'oshiba? Bakafa ci dayawaba.
Yarima kur6ar kunun zak'in yayi sannan yace kinsan banason cin abu mai nauyi da dare.
Zarah shuru tayi sannan takwashe kwanukan, bayan ta dawo Yarima kallonta yayi yace kije kiyi ma su abbah magana muyi sallama dare yakeyi.
Zarah 6ata fuska tayi tace tun yanzu?
Banza Yarima yayi mata,
Ganin haka yasa tamik'e taje tasanar da su abbah, kusan a tare suka fito, sama-sama suka d'anyi hira sannan sukayi musu sallama, har wajen mota yaya rauda da Aysha suka rakasu, Yarima bandir d'in 'yan 1000 yad'auko yamik'a ma Aysha yace tasiya kayan kwalliya, godia Aysha tayi masa sannan suka tafi.
Tunda suka kama hanya ba wanda yayi magana har suka isa gida, yana yin parking d'in motar daidai lokacin sumayya tafito daga 6angaren iyayenta, tsaye tayi fuskarta d'auke da murmushi tana jiran Yarima yafito, zarah ce tafara fitowa sannan Yarima, ganin zarah yasa fara'ar da yake fuskar sumayya tagushe ahankali tace ina Yarima yaje da wannan matsiyaciyar? Watau dakansa ma yake kaita anguwa? tsanar zarah ce taji tak'aru a cikin zuciyarta, batasan lokacin da suka iso inda takeba saidai ji tayi yarima ya ce kekuma daga ina kike?
Sumayya ta6e baki tayi tace daga wajen ummah na amso wani sak'one, zarah d'an rissinawa tayi tace Aunty sumayya ina wuni?
Wata uwar harara sumayya tawurga mata tare da jan tsaki sannan tawuce tabi bayan yarima da yayi gaba,
Zarah ko kad'an batayi mamakin hakan ba nan tabi bayansu tawuce part d'inta.
Cire kayan jikinta tayi tashiga wanka, bayan tafito tayi shirin bacci nan tabi lafiyar gado takwanta.
Sumayya har part d'in yarima tabisa lokacin yana shirin cire kaya yashiga wanka tsaye tayi tana kallonsa, kallonta yayi yace ya dai?
Sumayya ta6e baki tayi tace gaskiya yarima baka kyauta min.
Da mamaki yarima yakalleta kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace da akayi miki mi?
Matsowa tayi kusa da shi tace akan me zaka d'auketa kakaita anguwa alhali tana da motarta kuma zaka iya sawa akaita.
Murmushi yarima yayi yace ko da ace iyayenki ba a tare muke da suba zan iya d'aukarki in kaiki sumayya ammah banda gidan abokai dan baya cikin tsarina, yana fad'in haka yawuce yaje yashigewarsa bathroom,
Sumayya fitowa tayi cikin fushi tawuce part d'inta.
Yarima bayan ya fito shima shirin bacci yayi yakwanta.
Sumayya ma koda takwanta sak'e-sak'e kawai take a ranta ta yadda zata kawar da zarah, dan gani take itace kawai matsalarta a rayuwa.
*BAYAN KWANA BIYU*
Sumayya ce zaune a bedroom d'inta nan ta aika aka kira mata zabba'u bayan tazo tsugunnawa tayi tagaisheta cike da girmamawa, fuskar sumayya ba yabo ta amsa sannan tace kinsan dai ba akan komai zan kirakiba sai akan waccen matsiyaciyar yarinyar, kud'i sumayya tamik'a mata jikin zabba'u yana rawa takar6a tace ranki yadad'e me kikeso wlh zan iya komai kifad'i yadda kikeso ayi yanzu.
Murmushin mugunta sumayya tayi sannan tace matso kiji abinda nakeso kiyi min dan yau banso taje wajen yarima,
Dasauri zabba'u tamatso sumayya bata damu da tsamin da jikin zabba'u yakeba nan tayi mata rad'a a kunne, washe baki zabba'u tayi tace angama indai dan wannan d'an aikin ne ranki yadad'e kikwantar da hankalinki
Murmushin Jin dad'i sumayya tayi sannan tace haka nakeso zaki iya tafiya, bayan zabba'u ta fita sumayya zagaye d'akin tashiga yi cike da jin dad'i cikin d'aga murya tace yes yau burina zai cika.
Wajen k'arfe tara yarima kiran zarah yayi yace tahad'a mai coffee.
Bayan tagama saida tak'ara gyara jikinta sannan tazumbula hijab tafito, kuyanginta tasallama sannan tad'auki cup d'in coffeen tanufi part d'in yarima, tafiya take wani tsantsi taji ya ja ta wata irin k'ara tasaki kafin takai k'asa nan duka coffeen yazube a jikinta, duk yadda taso tamik'e kasawa tayi nan tafara hawaye saboda wani irin zafi da zugi dak'afar takeyi mata, waige tashiga yi ko Allah ya sa taga wani saida tayi kusan min biyar ahaka sai ga wata baiwarta tazo wuce, ganin zarah yasa tarud'e cikin sauri ta iso inda take tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke?
Zarah tana cije baki cike da dauriya tace taimakamin intashi nan baiwar tataimaka mata tatayar da ita duk yadda zarah taso tataka k'afar kasawa tayi daga k'arshe saidai baiwar tarik'eta tana k'engasawa suka koma part d'in zarah, nan saman gado tazaunar da ita tare da taimaka mata tacire hijab d'inta,
Zarah jingine kanta tayi da jikin gadon tare da runtse ido, baiwar cike da rikicewa tace ranki yadad'e bari inje infad'a ma yarima, har ta mik'e cikin sauri zarah tarik'ota dak'yar tabud'e baki tace kar kifad'a masa please je kikira min sahura (kuyanga) dasauri baiwar tafita daga d'akin,
bayan minti biyu sai gasu sundawo, a firgice Sahura tanufi wajen gadon tace ranki yadad'e me yake faruwa da ke?
Murmushin k'arfin hali tayi tace kar kidamu bawani abu 'yar fad'uwace nayi, yanzu so nake kitaimaka kihad'omin coffee kikai ma yarima.
Sahuru matsar k'wallah tafarayi tace ranki yadad'e ya akayi hakan takasance?
Murmushi zarah tayi tace kidaina kuka inaji miyar ku6ewa ce aka d'an zubar da ita ammah nidai yanzu kitaimaka kije kihad'a min coffeen, mik'ewa sahura tayi tace toh ranki yadad'e Allah yabaki lafiya,
Gyad'a kai kawai zarah tayi, bayan sun fita ta6a k'afar tad'anyi kad'an dasauri taruntse ido tare da furta wash saboda wani irin zafi da taji, ahankali takwanta tare da runtse idonta tanajin wani irin zogi.
A chan 6angaren yarima zaune yake a parlour yana kallo ammah gabad'aya hankalinsa baya ga kallon kad'an-kad'an ya duba time ammah shuru zarah batashigo ba, nan yak'ule tsaki kawai yake ja.
'Daya daga cikin guards d'insane yashigo yace ranka yadad'e wata kuyangace tazo ta ce gimbiya ta aikota
Yarima izini yabada yace abarta tashigo.
Sahura ce tashigo d'auke da cup tsugunnawa tayi cike da girmamawa tace ranka yadad'e gimbiya ce ta umurceni inkawo maka coffee,
Yarima da tunda tafara maganar bai kalletaba sai alokacin yajuyo yawatsa mata wani mugun kallo yace ke nasa kihad'o min ko ita? Kikoma kimaida mata abunta kice ita tafi k'arfin tazo takawo min?
Duk'ar da kanta kuyangar tayi tace ranka yadad'e kagafarceni wlh gimbiya bata jin dad'ine,
Yarima a firgice yace bata jin dad'i? Me yasameta?
Kuyangar k'ara duk'ar da kanta tayi tace ranka yadad'e lokacin da tafito zata kawo maka sai tazame yanzu tana chan k'afarta ke ciwo.
Yarima a firgice yace what! Garin ya hakan yafaru.
K'ara duk'ar dakanta tayi tace kagafarceni miyar ku6ewace aka zubar a waje itace ta zameta.
Yarima lumshe idonsa yayi tare da jin gine kansa jikin kujerar da yake zaune, d'aga ma kuyangar hannu yayi alamun tatafi, saida tak'ara duk'ar da kanta tagaishesa sannan tatashi tafita tabar d'akin.
Yarima wani iri yakeji a ransa ya dad'e zaune sannan yamik'e yafito yanufi part d'in zarah, bai samu kowaba a parlournta yana shiga bedroom yatarar da ita zaune saman gado kuyanginta biyu tsugunne k'asa suna yi mata sannu,
Yarima bai kula da gaisuwar da kuyangin sukeyi masaba yanufi wajen zarah, cikin sauri kuyangin sukabar d'akin.
Yana zuwa rikicewa yayi ganin yadda take cize le6e, k'afar yarik'o a rud'e yace sannu ko muje asibiti? Nan kawai yake miki ciwo?
Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cike da mamakin ganin yadda yarikice mata,
Ganin haka yasa yarima yasaki k'afar tare da zama yadafe kansa dogon numfashi yaja sannan yad'ago kansa yakalleta yace garin ya hakan tafaru?
Zarah murmushi tayi tace inaji wani yazubar da miyar ku6ewace bai luraba nima bansan da itaba nataka shine nafad'i ammah dasauk'i.
Yarima rik'o k'afartata yayi yana dubawa ahankali yafara murza mata, wata irin k'ara zarah tasaki tare da ruk'unk'umesa nan k'wallah tafara fita daga idonta cikin muryar kuka tace please kadaina akwai zafi,
Yarima shi kansa saida yalumshe idonsa ahankali yajanyeta daga rik'on da tayi masa tare da tallabo mata kai yana kallon cikin idonta yace kidaure ind'an murza miki kar tayi tsami inyaso gobe sai muje hospital bazanyi miki da zafiba,
Zarah share k'wallar idonta tayi tace please kayi min ahankali wlh da zafi.
Yarima murmushi yayi yace kar kidamu ahankali zanyi miki.
Sakinsa Zarah tayi sannan takoma takwanta nan Yarima yajanyo k'afartata yad'aura saman jikinsa, ahankali yashiga murzawa yana kallon Zarah da take cize le6e, haka yayi ta murza mata ahankali chan daga baya sai yakoma murzawa da k'arfi nan Zarah tasaki k'ara tare da rik'o hannunsa, Yarima cigaba yayi da murzawa inda yakejin kukan nata har cikin ransa haka yadaure yacigaba da murza har saida yaga kumburin ya d'an sa6e sannan yabarta, Zarah jikinsa tafad'a tacigaba da rusa kuka, rungumeta yayi tare da lumshe idonsa ahankali kamar mai rad'a yace kukan ya isa haka please,
Zarah cigaba tayi da kukan nan yarima yashiga d'an bubbuga mata bayanta ahaka tad'an rage sautin kukan nata, sun dad'e a haka daga k'arshe bacci yad'auketa
ahankali yarima yakwantar da ita tare da gyara mata kwanciyar sai alokacin yakula da hannunta da tak'one ya yi ja abunka da farar mace dan ma Allah ya taimaketa k'unar bata tashiba, shafa hannun yayi cike da tausayi nan zarah tamotsa, tausayintane yak'ara kamasa, har ya mik'e zai tafi sai kuma yaji baya iya tafiya yabarta dan haka yadawo yakwanta gefenta tare da zuba mata ido cike da tausayinta ahaka shima bacci yad'aukesa.
kiran sallar asubane yatashesa kallon zarah yayi da take baccinta sannan yaduba k'afar yaga kumburin ya safka ahankali yasafko daga saman gadon yashiga toilet d'inta yad'auro alwallah bayan ya fito a d'akin yashimfid'a darduma yayi sallah,
yana zaune saman dardumar yana addu'a zarah tafarka, ido tazuba masa cike da mamaki, cikin ranta tace kar dai ace nan d'akin yakwana?
Kallon agogo tayi ganin 6am yasa tatashi zaune dak'yar tare da safko k'afarta k'asa tamik'e tana fara taku d'aya tasaki wata irin k'ara tare da komawa tazauna.
Yarima cikin sauri yashafa addu'an yataso yazo inda take yace kin farka? Ya k'afar taki?
Zarah cize le6e tayi sannan tace dasauk'i, rik'ota yarima yayi yace muje kiyi alwallah,
Zarah k'engesawa take ahankali yarima yana rik'e da ita har suka shiga toilet, tsaye yayi yana kallonta ganin haka yasa Zarah tamarairaice fuska kamar zatayi kuka tace please kafita.
ta6e baki yarima yayi sannan yafita tare da janyo mata k'ofar.
Bayan ta gama knocking d'in k'ofar tayi nan yarima yabud'e yana rik'e da ita yazo da ita wajen darduma, saida yazaunar da ita saman darduma sannan yaje yad'auko mata hijab tasaka sannan yakoma saman gadon yazauna yana kallonta, daga zaune tayi sallar,
Bayan ta gama ganin tanaso tatashi yasa yarima yaje yad'auketa cak yamaidata saman gado yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta, Zarah shigewa tayi jikinsa nan yarima yarungumeta ahaka suka koma baccinsu.
Wajen k'arfe goma yafarka ahankali yazareta daga jikinsa sannan yamik'e yafita yabar d'akin yakoma part d'insa.
Nan yarubuta drugs yaba guard d'insa yace yasiyo masa sannan yashiga bathroom yayi wanka.
Bayan ya fito shiryawa yayi bai ko tsaya breakfast ba yafito saida yakar6i drugs d'in sannan yawuce part d'in zarah.
ko da yashiga bedroom d'in zaune take saman gadonta tana ta fama zata zage zip d'in rigarta amman ta kasa, shigowar yarima yasa tabisa da kallo, suna had'a ido nan tajanye idonta garesa tare da gaishesa,
Yarima saida yazauna gefenta sannan ya amsa mata tare da tambayarta ya jiki, zarah tace Alhmdllh sannan tacigaba da kai hannu zata zage zip d'in rigar,
Ganin takasa yasa yarima yakai hannunsa zai zage mata, zarah kallonsa take shima yazuba mata ido suna kallon juna bata san lokacin da yazage zip d'inba saidai ji tayi ya salu6e mata hannuwan rigar ta safka k'asa, zaro ido tayi cikin sauri tafad'a jikinsa tarungumesa tareda kare k'irjinta,
sun dad'e a haka sannan yarima yajanyeta daga jikinsa tare da d'auko towel d'in da yaga an aje gefe yamik'a mata, cikin sauri zarah takar6a tad'aura tare da duk'ar da kanta k'asa cike da jin kunya,
Cike da rashin damuwa yarima yamik'e sannan yace muje inrakaki toilet d'in, zarah bata musaba tamik'a mai hannunta yatasheta tsaye yana rik'e da ita har suka shiga toilet sannan yafito tare da jawo mata k'ofar yakoma saman gado yazauna yana jira tafito.
Bayan kamar minti goma sai gata tabud'e k'ofar, cikin sauri yarima yaje yarik'ota yazo yazaunar da ita bakin gado sannan yad'auko mata lotion tashafa, Bayan ta shafa magani yad'auka yashafa mata a k'afar yana d'an murzawa zarah saboda zafi har da 'yar k'wallarta, dakansa yaje yabud'e wardrobe yad'auko mata kaya yamik'a mata sannan yaduba agogon hannunsa yace bari insa akawo miki breakfast kiyi sannan ga tabs nan kisha guda biyu ni nawuce hospital,
Zarah binsa tayi da kallo har ya juya ya fara tafiya tace am bakajiba,
tsayawa yayi cak batare da ya juyoba, ahankali tace nagode sosai da taimakon da kayi min.
Yarima murmushi yayi sannan yabud'e k'ofar yafita.
Zarah ma murmushin tayi nan tafara saka kayanta.
Bayan tagama nan aka kawo mata breakfast tayi sannan tasha magani takoma takwanta, tunda takwanta tunanin yarima kawai take musamman ma idan tatuna hidimar da yayi mata daga jiya zuwa yau dan batayi tunanin samun hakan daga garesaba ta dalilin haka har yakwana part d'inta, murmushine yasu6uce mata, wani irin sonsane taji yana fizgarta.
A chan 6angaren gimbiya sumayya koda kuyangarta tazo mata da labarin abinda yafaru da zarah tayi murna sosai har d'aga hannuwanta tayi tai ddu'a Allah yasa ta sanadiyar haka zarah tagurgunce a ranar baccinta tayi cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
Wajen k'arfe 12pm zarah ce a parlour zaune saman cushion ta mik'e k'afafuwanta, gefenta plate ne mai d'auke da tufa tana ci, sumayya ce tashigo da sallamarta fuskarta d'auke da murmushi.
Ba zarah ba hatta kuyanginta sunyi mamakin ganinta cikin wannan yanayin, gaba d'ayan kuyangin zarah suka duk'a suka gaisheta
Sumayya nuni tayi musu alamun subar d'akin.
Cikin sauri suka tashi suka fita,
saman d'aya daga cikin cushin d'in tazauna har a lokacin fuskarta d'auke da murmushi takalli zarah da tazuba mata ido tace gimbiya zarah ashe tsautsayi yafad'a miki, gaskiya banji miki dad'iba toh waima garin ya hakan takasance da ke? Ke bama hakaba Ina fatan dai baki gurgunceba.
Zarah tunda sumayya tafara maganar tazuba mata ido cike da mamaki, chan sai tayi murmushi tace kar kidamu tsautsayi ne da k'addara, kuma da kike maganar gurgwancewa ko da ace na gurgunce ai ba abun damuwa bane tunda Allah ne daman yabani k'afar dan ya kar6a alokacin da yakeso shine zan damu bayan naci moriyarta? Inaso kisani ni nayarda da k'addara nasan duk abinda zai sameni daga ubangijine.
Ta6e baki sumayya tayi tace hakan ya yi kyau saidai fa natayaki murna da baki nakasaba dan kinsan babu yadda za'ayi yarima yazauna da gurguwa.
'Daga mata hannu zarah tayi tace please ya isa haka idan kin gama abinda yakawoki zaki iya fita dan a yanzu banda lokacinki.
Dariyar mugunta sumayya tayi sannan tamik'e tsaye tace dakyau zarah am naga kamar kina jin jikin buguwar da kikayi bari dai inbarki kid'an samu kihuta saidai ince sai mun had'e a karo nagaba.
Murmushi zarah tayi tace kar kidamu nagode sosai, saduwar alkhairi.
nan sumayya tawuce tafita daga d'akin zarah binta tayi da kallo sannan daga baya tajinge kanta a jikin cushin d'in da take tare da maida numfashi
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Sak'on gaisuwa mai tarin yawa agareka Dr S Fulani😍👍*_
_Yau page d'in nakine *Sadiya Sidi Sa'id*, ko da ace sau goma zan mallaka miki page toh bazan ta6a gajiya ba saboda cancatarkice tasa haka, nagode sosai da soyayyar da kike nunamin_
*PAGE* 4⃣1⃣
Wajen k'arfe biyu da taimakon wata kuyangarta zarah tasamu tayi wanka tai sallah ko da tayi lunch maganin tak'ara shafa ma k'afar sannan takwanta saman 3 seater nan bacci yayi awon gaba da ita.
Wajen k'arfe ukku yarima yadawo daga wajen aikinsa, bayan yayi wanka ya shirya yai lunch sannan yafito yanufi part d'in zarah dan yak'ara dubata, ko da yashiga ganinta yayi tana bacci ahankali yataka yaje wajen kujerar da take kwance a kanta, daga gefen k'afarta yatsaya nan yakai hannu yad'an tatta6a k'afar gani yayi kumburin ya sa6e kad'an yarage nan yad'auki maganin yak'ara shafa mata sannan yafita yabar d'akin.
Zarah ko da tafarka k'amshin turaren yarima ne da taji yashaida mata yazo d'akin murmushi tayi sannan tatashi tana bin bango tasamu har taje toilet tad'auro alwallar sallar la'asar, bayan ta fito shimfid'a darduma tayi daga zaune tayi sallah bayan ta gama ahankali tamik'e tana d'an k'engesawa har taje parlour tazauna.
Wajen 8 yarima yashiga part d'inta lokacin tana zaune saman gadonta cikin shirin baccinta tana tufke gashin kanta, ido tazuba mai har yazo gefenta yazauna, kallonta yayi sannan yad'auke kai ahankali yace ya k'afar ina fata dai tayi sauk'i?
Zarah marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace da dai sauk'i, yarima ido yazuba mata sai chan yad'auko k'afar yad'aura jikinsa yana dubawa batare da ya kalletaba yace ammah ai kumburin ya sa6e kuma zaki iya d'an takawa, jin shuru batayi maganaba yasa yad'ago kai yaga ta tsaresa da manyan idanuwanta, janye k'afar yayi daga jikinsa sannan yace kinsha magani?
Gyad'a mai kai tayi alamun eh,
Yarima mik'ewa yayi yace akwai abinda kike buk'ata ne?
Zarah k'wallah ce tacika mata ido tayi shuru,
Yarima har zai shareta yatafi sai kuma yaji baya iyawa, komawa yayi yazauna tare da rik'o hannunta yace ya akayi ne?
Zarah jikinsa tafad'a tare da rungumesa tana jin wani irin sonsa a cikin zuciyanta.
Lumshe idonsa yayi tare da kai hannu yana shafa gashin kanta, nan ta ida lafewa a jikinsa,
ahankali yajanyeta idanuwanta suna a rufe yakwantar da ita ya d'an jima yana kallon fuskarta chan kuma ko me yatuno cikin sauri yamik'e har ya juya zai tafi kawai sai ji yayi ta ruk'o masa hannu.
Cikin sauri yajuyo yakalleta wani irin tattausan murmushi zarah tasakar mai wanda yakusan zautasa sannan tasaki hannunsa tace sai dasafe.
Yarima kasa magana yayi dak'yar yaja k'afafunsa yafita yabar d'akin cike da kasala,
ahaka yakoma part d'insa yakwanta cike da kewarta dan duk jikinsa ya mutu jiyake kamar yakoma d'akinta yakwanta ko bakomai zai rungumeta yad'anji sauk'in abinda yakeji tare da ita ammah yasan jin kansa bazai barsa yayi hakanba, chan kuma sai yatashi zaune tare da dafe kansa yace me yake faruwa da nine? kar dai ace... dasauri yamik'e tsaye yafara zagaye d'akin yace hakan bazai ta6a kasancewa ba, ni dai nasan tausayinta nakeji, inba hakaba ya za'ayi inso yarinyar chan, me takeda shi da kamata *yarima suhail* zaiso? Nasan dai abu d'aya yasa nake zaune da ita saboda za6in iyayena ce ammah babu soyayyarta a tare da ni.
Nan sarautar tamotsa masa cikin rashin damuwa yakoma yakwantar tare da kashe gloves d'in d'akin, zarah ce kawai yake gani a duk juyin da zai yi saidai yaja tsaki ahaka yasamu bacci yad'aukesa.
A chan 6angaren zarah ma bayan yarima ya fita daga d'akin jawo pillow tayi tarungume a jikinta tare da lumshe idonta tana jinta cikin wani irin yanayi, chan kuma sai ga k'wallah tana fita daga idonta ahankali tafurta Allah kasa ma wannan bawan sona koda da k'wayar zarrane tausayin kantane yakamata dan ita kanta tasan yadda takeson yarima suhail batayi ma malam bello rabin sonba, tana acikin yanayin baccin yad'auketa.
Da asuba taji sauk'in k'afan sosai dan dakanta taje tayo alwallah batare da antaimaka mataba dan jitayi ta daina yi matazafi,
Bayan tayi sallah komawa tayi takwanta dan jiya ta dad'e bacci bai d'auketaba.
Wajen k'arfe goma yarima yagama shirinsa saida yayi breakfast sannan yafito yanufi part d'in zarah, yana shiga lokacin zarah ta fito daga wanka tana zaune tana shafa kallo d'aya yayi mata yajanye kai,
Zarah saida gabanta yafad'i dan ya yi mata wani irin kyau, ahankali tagaishesa,
Amsa mata yayi batare da ya kalletaba sannan yace ya k'afar dafatan yanzu tayi sauk'i?
Zarah shuru tayi,
Ahankali yarima yatako yazo saman gadon yazauna,
Zarah kamar jira take nan tad'auko k'afar tad'aura a jikinsa,
Kallonta yayi nan tad'aga mai gira tare da yin fari da ido tace duba kagani,
Yarima zuba mata ido yayi yana kallonta dan gaba d'aya ta rikitasa,
Zarah turo baki tayi tace kaduba min, yarima baisan ma tana yiba dan gaba d'aya hankalinsa ya tafi wani wajen daban, ganin haka yasa zarah tata6osa,
Firgit yayi,
murmushi tayi tace ya dai tunanin me kake?
Yarima janye idonsa yayi, cikin borin kunya tare da duba agogon hannunsa yace ina tunanin wani theater ne da zanyi a hospital yanzu, janye k'afar zarah yayi daga jikinsa tare da mik'ewa,
Zarah binsa tayi da kallo sannan tace am baka dubamin k'afarba,
Juyowa yayi yakalleta yace naga ai alamun tayi sauk'i, yana fad'in haka yajuya yayi tafiyarsa.
Zarah murmushi tayi sannan tatashi tad'auko kayanta tasaka sannan takoma parlour tayi breakfast.
Bayan tagama kallo takunna tana yi cike da jin dad'in da ita kanta tarasa namenene.
Yarima baibaro hospital ba sai dare saboda ranar suna clinic ga kuma meeting sunyi,
Bayan ya dawo yayi shirin bacci yakwanta sai kuma yaji yanaso yaje yaga zarah dan rabonsa da ita tun safe,
Shigowar sumayya ne yasa yad'ago kai cikin sauri yakalleta ganin itace yasa yajanye idonsa daga kallonta,
Gefensa tazo takwanta tare da shafa sajen da yake a fuskarsa tace yarimana ya kake?
Batare da ya bud'e idonsaba yace klau, kefa?
Rungumesa tayi sannan tace nima haka dear,
Murmushi kawai yayi.
Sumayya d'ago kai tayi takallesa cike da so tace ina sonka sosai masoyina,
Murmushi Yarima yayi tare da bud'e ido yakalleta har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.
Sumayya zuba masa ido tayi ahankali tace toh kaima kace kana sona dan tunda mukayi aure baka ta6a furtamin hakaba a k'arshema sai kayi min rashin adalci.
Fuskar Yarima cike da mamaki yace sumayya rashin adalcin me nayi miki?
Maida kanta tayi takwantar a k'irjinsa sannan tace na auren da kak'ara man.
Murmushi yayi yace k'arin aure shine rashin adalci sumayya?
Ta6e baki tayi sannan tace ammah ai baidace kayi min kishiyaba kuma karasa wadda zaka aura sai 'yar talakkawa,
Cikin d'aga murya Yarima yace ya isa haka sumayya!!
Sumayya cike da mamaki tad'ago kai takallesa har ta bud'e baki zatayi magana wata uwar harara da yawurga mata yasa takoma takwanta cike da tsanar zarah dan tasan duk saboda itane yacanza mata har yake yi mata tsawa, cikin zuciyanta tace dasannu zan kawo k'arshen wannan matsalar, ahaka tayita sak'e-sak'e cikin ranta har Yarima yayi bacci yabarta sai daga baya itama baccin yad'auketa.
A 6angaren zarah tun tanasa ran Yarima zaizo dubata ammah har dare baizoba nan takaici yacikata tace daman nasan bai damu daniba nan k'wallah tashuga zuba a idonta cike da tausayin kanta.
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_~Masha Allah my dear *Sadiya Sidi Sa'id* ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna *MAHAIFIYA* hak'ik'a kin baje mana basirarki a cikinsa mun ilmantu, mun nishad'antu sannan kuma mun wa'azantu, gaskiya na jinjina miki sosai da namijin k'ok'arin da kikayi, Abinda kika fad'a daidai Allah yabaki ladan kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, nagode sosai da soyayyarki agareni inaso kisani ina ji da ke har cikin zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare~_
_*I dedicated this page to you Admin of Admins*_
_On your birthday, today I wish u a year with loads of fun, excitement nd beautiful memories. Happy Birthday Admin of Admins *Hayatu Baba Zubairu (Yaya Hayat)*_
*PAGE* 4⃣3⃣
Da asuba saida yayi sallah sannan yatada zarah saida yataimaka mata tayo alwalla sannan tazo tayi sallah.
tana gamawa k'wallah ce cike da idonta takalli yarima da yake zaune ahankali tagaishesa.
Gyad'amata kai kawai yayi alamar ya amsa, janye idonta tayi daga kallonsa sannan tace nasan bazaka ta6a yadda cewa bani nazuba poison d'inba ko? Wlh ko da sau d'aya ban ta6a kawo ma raina incutar da kai ba, juyowa tayi takallesa da shima ita yake kallo sannan tace nasan bazaka ta6a yadda daniba a yanzu ka tsaneni ko?
Har a lokacin kallonta yake baice komai ba, zarah mik'ewa tayi dak'yar taje inda yake zaune tatsugunna tace koda ace zaka yanke min hukunci inaso kataimaka kayi min wanda iyayena bazasuji labariba, ammah dan Allah kataimaka kayi bincike kafin kazartas min da hukuncin,
Sai a lokacin yarima yajanye idonsa agareta sannan yace zarah kinji na ce miki wani abu?
Girgiza kanta tayi cikin sauri har a lokacin k'wallah tana fita daga idonta.
Toh indai banceba kikyaleni kije kikwanta kihuta.
Zarah girgiza kai tayi cikin kuka tace taya kake tunani zan iya kwanciya alhali ina cikin wannan matsalar?
Tausayi tabashi yanayin yadda tayi maganar, d'aura hannunsa yayi a kumatunta sannan yace kar kidamu, yana fad'in haka yatashi yafita daga d'akin,
Zarah kife kanta tayi da gadon tana mai ci gaba da kukan.
Koda yaje magana sukayi da doctor sannan yashigo yace ma zarah tataso sutafi har a lokacin kuka take jikinta ba k'wari dakyar take takawa, har bakin mota doctor yarakasu sannan sukayi sallama.
lokacin da sumayya tatafi d'akinta takaicine yacikata ganin burinta bai cikaba domin taso ace poison d'in yafara aiki agabansu dada saboda tasan da anga haka k'arshen rabuwar yarima da zarah tazo.
tsaki taitayi daga k'arshe dabara tafad'o mata nan takira kuyangarta zabba'u tace taje tasa mata ido akan duk wani motion d'in zarah
nan zabba'u takwashi gaisuwa sannan tafito tasamu inda ba za'a gantaba tala6e, tun daga fitowar zarah har tafiyar da sukayi da yarima asibiti duk akan idontane,
nan tazo taba sumayya labari dariyar mugunta sumayya tayi tare jinjina kai ahankali tace lallai zarah kinyi jarumta.
tunda asuba tazuba ido domin taga dawowarsu,
lokacin da yarima yayi horn suka shigo gate da mamaki yake kallon dada da umman sumayya da ita kanta sumayya da suke tsaye cikin ransa yace tabbas wannan aikin sumayya ne.
zarah kau rikicewa tayi takalli yarima tace shikenan yarima sun gano ni nashiga ukku.
yarima batare da ya kalletaba yace kar kisaki kinuna akwai wani abu indai kika nuna suka gane babu ruwana sai kisan yadda zaki Kare kanki,
daidai lokacin yagama parking d'in motar yabud'a yafita batare da ya kalletaba.
zarah tana ganin haka itama tabud'e tafito cikin zuciyanta tana ta addu'a
bayan yarima tabi a tsorace shidai tafiyarsa yake hankali kwance gab da zai isa wajen da su dada suke nan wayarsa tafara ruri tsayawa yayi yad'auko wayar yana dubawa murmushin nasara yayi sannan yayi picking d'in wayan batare da yayi magana ba,
daga chan 6angaren akace ranka yadad'e Dr, Ahmad ne yake magana daman wannan patient d'inne da kayi ma theater toh ya farka.
yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace idan kun tabbatar da babu abinda yake damunsa toh sai kuyi masa wannan injection d'in da na aje inyaso da anjima idan nashigo sai in rubuta masa drugs.
daga chan 6angaren akace toh ranka yadad'e sai ka shigo, yarima baice komai ba yakashe wayarsa, sannan yamaida kallonsa ga dada da tatsaresa da ido ammah ko inda su umman sumayya suke bai kallaba.
murmushi yasakar ma dada yace ranki yadad'e ya akayi naganki nan a tsaye a wannan lokacin?
fuskar dada a d'aure tace daga ina kuke?
shuru yarima yayi yana murmushi,
dada tace ashe yarinyar nan dagaske guba tazuba maka tunda da taci abincin saida kukaje asibiti, kai wlh bansan samna bane sai yanzu matar da tayi shirin kasheka itace kataimaka mawa toh wlh dole memartaba yaji maganar nan.
har a lokacin yarima murmushi yake sai chan yace dada bai dace kice hakaba tunda baki gani da idonki ba, kirana fa akayi daga hospital akan wani emergency case cikin dare shine zarah tace zata bini mukaje tare kuma ma yanzu ai gabanki aka kirani waya.
sumayya tayi karaf tace wlh bahaka bane poison d'in da tacine a cikin abinci kiduba kiga yadda duk tazure,
ummanta tace ai wannan dama daga ganinta poison taci.
yarima murmushi yayi sannan yace sumayya gabanki tazuba min poison d'in? gabanki tayi girkin? Lokaci guda yajero mata wad'annan tambayoyin.
sumayya tace toh ai lokacin da takeyi naga ta zuba wani abu.
yarima wani mugun kallo yawurga mata yace toh kina dai nufin la6e kikayi mata.
sumayya hararar zarah tayi da take raku6e bayan yarima tace wannan gajar zan yi ma la6e? tak'aryata mana idan batayiba, kuma naga lokacin da katafi kakaita asibiti.
murmushin mugunta yarima yayi yace toh in ko ta zuba min poison toh tare da ke aka zuba kokuma ke d'in kika Zuba.
zaro ido sumayya tayi tace ni ya za'ayi inzuba maka poison?
yarima kallon dada yayi yace ranki yadad'e kiduba kiga inda ace yarinyar nan ta zuba poison kina tunanin zata amince taci abincin alhali tasan zata iya mutuwa?
dada jinjina kai tayi batare da tace komai ba.
yarima suhail rik'o hannun zarah yayi yace bari mushiga daga ciki.
kallon ummah yayi da tacika tayi fam yayi murmushi yace ummah gaskiya ya kamata kija ma d'iyarki kunne tadaina la6e, na barku lafiya.
jan zarah yayi suka shige sukabar su dada a tsaye, sultana sadiya da harara tabi yarima ji take kamar tashak'esa yamutu kowa yahuta,
dada kallon sumayya tayi tace sumayya yakamata ki iya bakinki yanzu gashinan kinja naji kunya, tana gama fad'in haka tawuce tanufi turakarta.
sultana sadiya kallon sumayya tayi da duk tasusuce tace ai ga irinta nan gashinan kinja yaro k'arami yana nema yarainani,
sumayya turo baki tayi tace ammah ai ummah bak'arya nayiba.
ummah tace ko da ace ba gaskiya bane ai bakida k'wak'warar hujja, wlh matsalata da ke bakida isashen wayau, duk yadda zakiyi abu bakisan yadda zaki fitar da kankiba.
sumayya cikin fushi tace haba ummah dame zan ji? da rashin cin nasara ko da surutun da kikeyi min?
sultana sadiya ganin d'iyartata tayi fushi yasa tafara lallashinta har saida taga ta hak'ura sannan tace tafi kiyi baccinki kicire komai a ranki ina tare da ke kinji ko d'iyata.
Toh ummana kema kije kihuta, murmushi sultana sadiya tayi sannan tatafi cike da tausayin 'yartata.
Yarima ko da suka shiga cikin gidan yana rik'e da zarah har part d'insa umurni yaba guards d'insa yace kar subar kowa yashigo koda ace sumayya ce, gaba d'ayansu sukace to ranka yadad'e angama.
Suna shiga zarah cikin sauri taduk'e k'asa saboda wani irin juwa (jiri) da yake kwasarta.
Tsaye yarima yayi yana kallonta sai chan yace kitashi mushiga ciki sai kikwanta.
Zarah kasa magana tayi dak'yar tamik'a mai hannun.
Ganin haka yasa yarima yatayar da it's tsaye ganin bata iya tafiya yasa yad'auketa yanufi bedroom da ita.
Maida idanuwanta tayi tarufe ahaka yakwantar da ita Saman gadon daga gefenta yazauna tare da shafa fuskarta cike da tausayinta yace bari insa ahad'a miki breakfast kiyi.
Girgiza kai zarah tayi alamun a'a tare d's rik'o hannunsa.
Yarima ido yazuba mata ahaka har tayi bacci,
Ahankali yazare hannunsa daga cikin nata sannan yakoma gefenta yakwanta dan rama baccin da ake binsa.
Wajen 11am yafarka har lokacin zarah bacci take, wanka yashiga yayi lokacin da yafito ganin zarah yayi ta farka,
Ganinsa d'aure da towel yasa tamaida idanunsa tarufe, yarima kallonta yayi yace kin tashi?
Batare da ta bud'e idontaba tace uhm.
Cigaba yayi da shirinsa saida yagama sannan yashiga bathroom yahad'a mata ruwan wanka, bayan ya had'a dawowa yayi kusa da ita yazauna sannan yace taso muje kiyi wanka ko kin samu k'arfin jikinki,
Zarah bud'e idonta tayi ahankali sannan tace toh,
Yunk'urin mik'ewa tashiga yi amma takasa, ganin haka yasa yarima yataimaka mata tatashi zaune sannan yamik'a mata towel, juyawa tayi alamun yazage mata zip d'in rigar,
Hannu yakai yazage mata, ganin tana ta kare-karen jikinta yasa yarima yata6e baki sannan yajuya mata baya.
Ganin haka yasa zarah tacire rigar sannan tafara yunk'urin mik'ewa, juyowa yarima yayi yarik'ota tasafko daga saman gadon tana fara takawa nan tayi baya zata fad'i cikin sauri yarima yatarota, cak yad'auketa yanufi toilet da ita, zare towel d'in yayi daga jikinta sannan yasakata cikin ruwan,
Zarah dasauri takai hannu takare k'irjinta ahankali tace kafita zanyi.
Kallonta yarima yayi yace kina ganin zaki iya? Gyad'amasa kai zarah tayi, baice komai ba yajuya yafita yabar toilet d'in.
Zarah kwance tayi cikin ruwan tana jin dad'in ruwan, kasa yin wankan tayi nan tamaida idanuwanta talumshe.
Yarima tura guard d'insa yayi part d'in zarah wajen kiyanginta aka kar6o mata kayan da zatasa,
Ya dad'e Zaune ammah zarah bata fitoba, ganin haka yasa yarima yamik'e yanufi toilet d'in.
Tsaye yayi bakin k'ofar toilet d'in yana kallonta, zarah idanuwanta a lumshe batamasan da shigowarsaba, wucewa yarima yayi ya ida isa wajen k'irjinta yazuba ma ido sai daga baya yad'ibi ruwan ya watsa mata a jiki, firgit tayi tabud'e idonta, sponge yad'auka yafara wanke mata jikinta zarah kasa hanasa tayi dan tasan indai tace zata hanasa toh ita bazata iya yiba, ganin yadda yazuba ma k'irjinta narkakkun idanuwansa yasa ta maida idanuwanta tarufe cike da jin kunya ahaka yarima yawanketa tas, bayan ya gama nad'ota yayi a towel yana rik'e da ita suka fito.
Bakin bed d'insa yazaunar da ita sannan yad'auko mai yashafa mata, shi yataimaka mata tasaka kaya sannan rik'ota suka koma parlour yazaunar da ita, dining yaje yakwaso musu breakfast, a saman lallausar carpet d'in da yake shimfid'e a tsakiyar parlourn, kallon zarah yayi yace kisafko muyi breakfast d'in.
Zarah kallonsa tayi tace na k'oshi, kallon da yayi matane yasa tasafko tazauna, dakansa yahad'a musu breakfast yatura mata nata gabanta, da k'in shan tea tayi sai juya spoon d'in take ganin yarima ya kalleta yasa tad'aga cup d'in tafara sha kad'an-kad'an batasha wani na kirkiba ta aje sannan tad'an ci chips d'in.
Yarima ma bawani nakirki yaciba yamik'e, nan yabada umurni akazo aka kwashe komai, bedroom yashiga yad'auko mata drugs yazo yabata dak'yar takar6a tasha kasancewarta batason shan drug's,
Nan yahad'a injection yayi mata.
Zarah har da 'yar k'wallarta takoma saman 3 seater takwanta.
Yarima bedroom d'insa yashiga, bayan 'yan mintuna yafito da key d'in mota, kallonta yayi da itama tazuba mai ido, saida yajanye idonsa daga gareta sannan yace akwai abinda kike buk'ata?
Ahankali tace a'a.
Ohk, ni na wuce hospital, cewar yarima.
Ahankali Zarah tace adawo lafiya.
Chan k'asan mak'oshinsa ya amsa yace Allah yasa.
Ko da yafita k'ara gargad'in guards d'insa yayi kar subar sumayya tashigar mai part, sannan yawuce yatafi.
Zarah taso tatashi takoma part d'inta ammah takasa, a dudduk'e tatashi tagyara mai bedroom d'insa tasa aka gyara parlour sannan takunna kallo tana yi.
Wajen k'arfe biyu wanka tayi tashirya sannan tayi sallar azuhur, Ko da aka kawo lunch k'inyi tayi dan ji take gabad'aya abinci ya fita ranta yanzu dan haka tayi zamanta.
Around 3 o'clock yarima yadawo, har lokacin Zarah tana zaune tana kallo, kallonsa tayi tace sannu da zuwa.
Yauwa, cewar yarima da yazuba mata ido, sai Chan yace ya k'arfin jikin?
Saida tad'an ciji le6enta sannan tace Alhmdllh yai sauk'i.
Wucewa yayi yashiga bedroom d'insa dan yakimtsa.
Bayan ya gama yafito kallon zarah yayi yace kinyi lunch?
Uhm kawai zarah tace.
Kallonta yarima yayi alamun rashin yadda sannan yace muje kik'ara.
Zarah turo baki tayi tamik'e tana tafiya dak'yar har suka isa dining, ko da suka zauna yarima ne yayi serving d'inta sannan shima yazuba nasa, ahankali yakeci idonsa yana kan zarah da take turo baki har lokacin batayi ko loma d'ayaba.
'Dago kai tayi takalli yarima ganin yana kallonta yasa tad'ibi abincin takai bakinta, dak'yar take taunawa saida tayi kusan minti biyar tana tauna sannan tahad'e, ganin haka yasa yarima yajanyo plate d'in gabansa yad'ebo batare da ya yi magana ba yakai wajen bakinta, kallonsa zarah tayi cike da mamaki, ganin fuskarsa ba alamun wasa yasa tabud'e bakin yasaka mata, zarah tana yatsine fuska take taunawa, yanayin yadda take taunar ya burge yarima dan haka yaita bin bakinta da kallo, ahankali yacigaba da feeding d'inta idanuwanta sukayi rau-rau kamar zatayi kuka, d'ura mata yacigaba da yi har saida yaga alamun ta k'oshi sannan yabata drugs yamik'e yabar wajen.
Zarah goge k'wallar da tazubo mata tayi sannan takalli plate d'insa da ko rabin abincin bai ciba, ahankali tace to shi kuma wa yabarma nashi yacinye?.
Mik'ewa tayi tadawo parlour nan tatarar da yarima kwance saman 3 seater yana kallon wrestling, chan saman 2 seater taje tazauna ganin wrestling yake kallo yasa haushi yakamata ahankali tace mutum yana kallonsa an canza mai channel, batasan maganar ta fitoba saidai jin yarima tayi ya ce d'akinki ko d'akina?
Kallonsa zarah tayi taga hankalinsa yana ga T.V kamar ba shi yayi maganan ba, mamaki yakamata shuru tayi batace komai ba.
Kiran wayan yarima da akayine yasa yamik'e yafita batare da ya ce mata komai ba.
Mik'ewa tayi taje tad'auko remote tacanza channel tacigaba da kallonta.
Har akayi sallar isha'i yarima bai dawoba wanka tashiga tayi tashirya, dinner kad'an tayi tasha drugs d'inta sannan tabi lafiyar gadon yarima tayi kwanciyarta.
Wajen 9pm yarima yadawo ganin tana bacci yasa shima yayi shirin kwanciya yakwanta, zuba ma fuskarta ido yayi yana kallo cike da tausayinta daga k'arshe yarungumota jikinsa tare da jan dogon numfashi, yanayin yadda yamatseta har saida tamotsa sannan yad'an safsafta mata rik'on, zage mata zip d'in rigarta yayi sannan yatura hannuwansa cikin rigar tare da lumshe ido yana jin wani sanyi a ransa, ahaka bacci yad'aukesa.
Cikin dare juyin da zarah zatayi jinta matse yasa tafarka, mamakine yakamata ganinta jikin yarima, jin hannunsa tayi a k'irjinta murmushi tayi tare da zuba ma fuskarsa ido tana kallo cike da sonsa k'wallah ce tacika mata ido cike da tausayin kanta tace ina ma ace kana sona muka kasance haka, jin k'irjinta ya fara bugawa yasa takoma takwanta tare da gyara kwanciyarta.
Da asuba ko da yafarka ahankali yajanyeta daga jikinsa sannan yatashi yashiga toilet saida yayi wanka sannan yad'auro alwallah, yana fitowa zarah tafarka zage zip d'in rigarta tayi sannan tamik'e tashiga toilet.
Lokacin da tafito har ya fita masallaci dan haka tayi sallarta ko da tagama saman gadon takoma takwanta, ba ita tafarka ba sai wajen 11 lokacin yarima har ya fita.
Gyara masa part d'insa tayi sannan takwashi kayanta takoma part d'inta, bayan sun gaisa da kuyanginta bedroom d'inta tashige wanka tayi tashirya sannan tafito tayi breakfast.
Bayan ta gama saman 3 seater takwanta wayarta tad'auko tahau chart daga k'arshe da tagaji tabud'o novel *(K'ADDARA CE)* cikin wayar tana karantawa gaba d'aya tamaida hankalinta ga karatun, sallah ce kawai takesawa tana ajewa ahaka har tagama.
Da dare kwanciyarta tayi part d'inta duk sai taji babu dad'i, tana kwance wayarta tafara ringing janyowa tayi tana ganin yarima ne batasan lokacin da murmushi yakubce mataba, zuba ma wayar ido tayi har saida taga ta kusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama cikin 'yar siririyar muryarta, daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi daganan shuru yabiyo baya sai chan yarima yace ya jikin naki?
Zarah kwantar da murya tayi sannan tace Alhmdllh ya yi sauk'i.
Ohk, kinsha drugs d'in?
Cikin shagwa6a tace uhm,
Daga chan 6angaren yarima saida yalumshe idonsa sannan yace kin tabbata.
Zarah kamar zatayi kuka tace dagaske fa na sha.
Daga nan duk sukayi shuru saida sukayi kusan minti ukku sannan yarima yace sai dasafe.
ahankali tace Allah yakaimu ko inzo intayaka bacci?
Yarima baisan lokacin da murmushi yaku6uce masaba sannan yace no kiyi kwanciyarki, yana fad'in haka yakashe wayarsa.
Zarah ma murmushi tayi sannan ta aje wayar saman bedside tare da kashe gloves.
Sumayya tsaye take bakin k'ofar yarima ta cika tai fam dan duk wayar da yayi da zarah a gaban idontane, cikin fushi tatako ta iso bakin gadon tace haba yarima wannan wane irin zaluncine?
Yarima kallonta yayi cike da mamaki yace zalunci kuma?
Cikin d'aga murya tace eh zalunci, akan me zaka kira waccan jakkar yarin....
'Daga mata hannu yayi fuskarsa ba alamun wasa yace kar kikuskura kik'ara min shouting koda ran girkin kine sai akace banda ikon yin waya da matata? Toh bari kiji wlh kikiyayeni ko in sassa6a miki.
Sumayya ta6e baki tayi tace eh d'in adai dunga jin tsoron Allah.
Wani irin kallo da yayi matane yasa tasha jinin jikinta, cikin 6acin rai yace indai kinsan abinda yakawoki kenan toh kifita kiban waje kar kimin hauka yana fad'in haka yajuya mata baya.
Sumayya ta ji haushin abinda yayi mata cikin ranta tace babu inda zanje, infita waccan gajar tashigo, ahankali tahau gadon takwanta tare da rungumo yarima ta baya tace toh kayi hak'uri na daina.
Yarima lumshe idonsa yayi sannan ahankali yace shikenan sumayya.
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Wannan page d'in tukuicine agareki mummyna chubad'o muhammad, hak'ik'a kin wuce duk yadda kike tunani a zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare mummy😘*_
*PAGE* 4⃣5⃣
Ahankali yake warwarewa har yagama sannan yabud'e yafara karantawa gabansane yafad'i ganin sunansa aka rubuta da larabci, sai wasu rubutu da shi kansa baisan menene aka rubutaba saboda mitsi-mitsine daga chan k'asa kuma sunan zarah yaga anrubuta sannan daga gefe akasa d'aya ansa _ni zarah zan mallaki yarima_ gabansane yacigaba da fad'uwa cike da mamaki yace zarah ce tasamin laya dan tamallakeni? Me take nufi da hakan? cikin sauri yaje yad'auko na toilet d'in yawarware sunansa da na zarah kawai ne jikin takardar, tsaye yayi cike da mamaki yana k'ara bin takardun da kallo,
Zarah kwance take d'akinta duk kasala ta rufeta tanaso taje part d'in yarima ammah ta kasa saboda batajin dad'in jikinta, daga k'arshe dai daurewa tayi tamik'e tad'auko alkyabbarta tasaka sannan tafito tanufi part d'insa.
Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga tsaye tagansa rik'e da layar, juyowa yayi yaimata wani irin kallo, cak zarah taja tatsaya cikin ranta tace shikuma wannan mutumin me yake nufi da hakan?
Muryarsa taji ya ce abinda kikayi shirin yi toh bai yuwuba dan haka sai kicanza sabon shiri ammah ni nafi k'arfin duk wani sihiri.
Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai, ahankali tace ban fahimci akan abinda kake nufiba.
Yarima wurga mata harara yayi yace kar kimaidani wanda baisan abinda yakeba ko kin d'auka banga layun da kika ajeminba cikin toilet da k'arshin pillow na ba, zarah zaro ido tayi tace ni kuma?
Mik'amata yarima yayi yace toh ai sai kiduba kigani idan k'arya akayi miki, cikin sauri takar6a tashiga dubawa, tsoro da fargaba duk suka cikata, cikin sauri tad'ago kai takalli yarima da shima yake kallonta, muryarta tana rawa tace wlh ban aikataba bansan wanene yake neman jamin sharri ba, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, dasauri taje wajen yarima tarik'o hannunsa k'wallah duk ta cika mata ido tace kayarda dani wlh bani bace nakawo maka laya,
Fizge hannunsa yayi cikin d'aga murya yace idan bake bace toh wanene? Kuma sunan wanene a jiki?
Zarah kallonsa take cike da mamaki tace yanzu ka yarda zan iya yi maka asiri? Cike da rashin damuwa yace toh idan ban yardaba me kikeso inyi?
Murmushi Zarah tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace da ace ni mushrikace da ba akanka zan faraba kuma ba zan ta6a amincewa in aurekaba da tun farko zan san yadda zanyi inga ban aurekaba saboda nima inada wanda nake so, kuma da ace ina asiri da tun farko zanyi maka ba sai munkai wannan lokacinba, wlh nagaji da wannan sharrin da ake ja min komawane yaje dan kansa, tak'arashe maganar cikin kuka,
Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d'ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad'in haka tawuce tafita tabar d'akin.
Tafiya take zata koma part d'inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k'afartaba, hawaye d'aya na bin d'aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al'amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka?
Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad'i, cikin sauri taji an rik'ota tafad'a jikin mutum, d'ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad'e meyake faruwa dake ne haka?
Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik'e Zarah suka ida isa part d'in Zarah.
Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d'akin.
Zaunar da Zarah tayi saman d'aya daga cikin cushin sannan tazauna k'asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d'in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke ne?
Zarah ahankali tabud'e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.
Jakadiya gyara zamanta tayi tace gimbiya kifad'a min matsalarki ni nayi alk'awali zan taimaka miki kid'aukeni a matsayin uwa,
Zarah d'ago kai tayi takalli jakadiya har a lokacin hawaye suna zuba daga idonta cikin muryar kuka tace ya akeso inyi da rayuwata? Narasa wanene yake k'ullamin sharri da angama wanchan sai afad'a ma wannan shin ya akeso inyi? Ni zan iya hak'ura da auran inkoma gidanmu,
Cikin sauri jakadiya tagirgiza kai tace a'a ranki yadad'e kar kice haka dan Allah kifad'amin abinda yake faruwa nayi alk'awali zan taimaka miki.
Zarah kallonta tayi cike da gamsuwa da maganar jakadiya sannan takwashe duk makircin da akeyi mata tafad'a ma jakadiya,
Jakadiya jinjina kai tayi tace wannan ba aikin kowa bane sai na gimbiya sumayya,
Zarah cike da mamaki tace yanzu kina ganin itace zata yi min haka?
Jinjina kai jakadiya tayi tace tabbas itace dan nasan wacece gimbiya sumayya da mahaifiyarta fiye ma da haka zasu iya yi.
Zarah share hawayen fuskarta tayi tace toh wlh zan iya hak'ura da auren inkoma gidanmu.
A'a gimbiya kar kice haka bai dace kikaraya ba, mu munsan halinsu, kuma sumayya da kikaga yarima ya aura toh auren had'ine ba auren soyayya bane sukayi.
hatta shi kansa yarima da kike gani akwai abinda mahaifiyar sumayya take k'ullawa akansa wanda ita kanta sumayya bata saniba.
Zarah ido tazuba mata cike da mamaki.
Jakadiya tacigaba da cewa akwai wani lokaci da dada ta aikeni wajen sultana sadiya, lokacin da nashiga parlour bakowa har na juyo zan baro d'akin najuyo magana k'asa-k'asa a bedroom d'in sultana sadiya tsaye nayi lokacin da najuyo tana cewa so take gimbiya sumayya tahaihu idan yaron yafara wayau tanaso tabi kowace hanya dan ganin ta kawar da yarima inyaso mijinta abashi rik'on k'warya kafin jikan nata yagirma daga baya yazama shine sarkin gari, ta san idan yahau toh sai yadda taso mulkin gidan zai tafi, dan ta tsani mahaifiyar yarima taso ace itace tahaifi d'a namiji Wanda zai gaji garin ba mahaifiyar yarima ba, ina jin haka cikin sauri nafito nabaro part d'in gudun kar taganni dan nasan idan taganni toh bazata ta6a barinaba.
Zarah cike da rud'ewa tace daman haka matarnan take? Toh shi yarima baisan halintaba ya amince ya auri d'iyarta.
Murmushi Jakadiya tayi tace tabbas yarima yasan kad'an daga cikin halayyarta dan tun yana k'arami idan yaje part d'inta wahalar dashi take dan akwai lokacin da tata6a watsa mai ruwan zafi, tagargad'e ni da idan nafad'a ma wani sai tayi sanadiyar barina aiki, kasancewar nikad'aice lokacin da abun yafaru.
Toh ba'a gane taba? Cewar zarah.
Eh toh, yarima yana da wani irin hali wanda ba komai bane yake iya bud'e cikinsa yafad'aba wannan halinsane tun yana k'arami, kuma na tabbata shi kansa yana sane da abubuwan da tayi masa kawai dai ya sharene,
indai wajen makircine toh kala-kala matarnan ta iya dan ina tunanin dasa hannunta sumayya takeyi miki wad'annan abubuwan.
Zarah jingine kanta tayi cike da jin tausayin mijin nata, Jakadiya tace ranki yadad'e kigode ma Allah da basubi ta wata hanyarba dan ganin sun kawar da ke, koda basubin boka ammah sun san makirci kala-kala.
Jinjina kai zarah tayi cike da mamakin halin su sumayya, ahankali tace duk makircinsu basu isa suyi abinda Allah bai nufa ba, kuma ina neman kariya daga ubangijina, saidai bansan yadda zanyi inshawo kan yarima yafahimceniba.
Jakadiya tace kar kice haka ranki yadad'e kuma baidace kiga laifin yarima ba tunda duk baya makircinsu da suke miki baiyi tasiriba a garesa ammah a yanzu kiduba kiga har da sunansa da naki aka had'a kinga ai bakowa bane zai iya k'in yarda, yanzu dai abu d'aya zakiyi shine nake tunani kamar zai taimaka wajen ganin kin ku6utar da kanki, zarah kallon Jakadiya tayi tace wane abune please kifad'a min.
nan Jakadiya tace kice yatambayi guards d'insa sufad'i Wanda yashiga da baya nan tunda ke kince baki shigaba,
Zarah tace anya kina tunanin zai amince?
Eh insha Allahu ai ya aminta da su yasan bazasu ta6a yi masa k'aryaba,
Zarah jinjina kai tayi tace nagode sosai jakadiya, hak'ik'a kin taimakeni a lokacin da nake buk'atar taimako nakekai kukana ga ubangijina,
Jakadiya tace kar kidamu gimbiya har cikin raina nake jinki dan kece kikafi dacewa da yarima ba sumayya ba kuma ina fatan yakasance kece zaki fara aje mana magajin yarima.
Zarah saida gabanta yafad'i dasauri tagirgiza kai tace kar kice haka, sumayya ita tafi dacewa tahaihuwa da yarima.
'Yar dariya jakadiya tayi tace tuni tayi watsi da damanta koda haka mahaifiyarta taci buri itama ammah a yanzu k'addara ta riga fata,
Zarah cike da mamaki take kallonta tace ban fahimci abinda kike nufiba?
Murmushi jakadiya tayi tace kar kidamu dasannu zaki fahimta nan ba da dad'ewaba, jakadiya tana fad'in haka tamik'e tare da d'an rissinawa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.
Zarah d'aga kai tayi tace nagode sosai jakadiya saidai ince Allah yabaki ladar abinda kikayi min.
Jakadiya murmushi tayi tace kar kidamu ai yi ma kaine, nidai fatana kirik'e sirrin maganar da nafad'a miki.
Zarah murmushi itama tayi tace insha Allahu babu wanda zai san maganar nan bayan mahaliccinmu sai ni da ke.
Jakadiya tace nagode, nan sukayi sallama tafita, zarah tsaye tayi tana tunani cike da jinjina ma sumayya da mahaifiyarta sannan daga baya tawuce tashige bedroom d'inta takwanta, nan hawaye suka cigaba da fita daga idonta tana tunanin hukuncin da yarima zai yanke mata akan laifin da ba ita ta aikata shiba, fashewa tayi da kuka tace ya ubangiji kakawo min d'auki, kuka tayi sosai saida taji kanta ya fara ciwo sannan tadaina haka taita juyi saman gadon daga k'arshe bacci yayi awon gaba da ita.
Yarima bayan zarah ta fita zama yayi saman gadonsa tare da dafe kansa cike da takaici, mamakin zarah ne yakamasa dan baita6a tunanin haka daga garetaba tun daga yanayin tarbiyarta, ya dad'e zaune yana jinjina lamarin dan abun ya d'aure masa kai sosai dan idan ya ce ba ita bace toh wanene zaiyi hakan?, tsaki yaja cike da takaici sannan yakwanta abu guda yatsaya masa a rai kalmar da tafurta ta nima ina da wanda nakeso, haka kalmar yaita jinta a kunnensa tana masa yawo har daga k'arshe bacci yad'aukesa..
A chan 6angaren sumayya kiran sultana sadiya tayi tana yin picking bata bari tayi ko sallama ba cikin jin dad'i tace ummah na aiwatar da komai kuma ina tunanin nasara a cikin aikin namu, daga chan 6angaren sultana sadiya dariya tayi tace gaskiya naji dad'i daughter ai ina fad'a miki ta ruwan sanyi zatabar gidannan dan makirci kala-kala babu Wanda ban iyaba idan akayi wani baiyiba sai acanza wata hanyar, cikin jin dad'i sumayya tace saisa nake k'ara sonki ummana dan duk abinda nakeso kema kinasonsa na rabbata yanzu yarima zai zama nawa ni kad'ai.
Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kar kidamu d'iyata farin cikinki shine nawa, saisa nake burin kihaifo min jika wanda zai gaji masarautar nan ammah kinkasa fahimtar inda nadosa, Indai kinsan kina yin planning toh kitaimaki kanki kidaina tun kan waccan munafukar tafara haihuwa,
Gaban sumayya saida yafad'i dan bata ta6a yin tunanin hakaba, ahankali tace hakane kuma ummah insha Allahu bama zata haihuba zata bar gidan.
Sultana sadiya tace na dai fad'a miki kirufa ma kanki asiri kidaina.
Cikin shagwa6a sumayya tace toh ummah na ji.
Uhm Allah yasa dagaske, cewar sultana sadiya.
Ameen ummana.
Yauwa toh yanzu kikwanta kiyi bacci dare keyi.
Toh ummah ko mi kenan sai kinjini, nan sukayi sallama suka kashe wayoyin.
Sumayya fad'awa tayi saman gadonta cikin murna tace yes nasan zuwa gobe waccan munafukar zata koma kongon gidansu, ahaka tayi bacci cike da farin ciki.
Cikin dare zazza6i da ciwon kai suka tashi zarah daga baccin da take nan taita juyi saman gadon daga k'arshe k'asa tasafka takwanta, ciwon cinta yake babu wanda zata iya kira dan ko hannunta kasa d'agawa tayi daga k'arshe, tana nan tana juyi ahaka aka kira sallar asuba.
Har aka gama sallah akan kunnenta ammah takasa tashi dakyar tasamu tamik'e tana dafa bango har tashiga toilet, saida tahad'a ruwan d'umi tayi wanka sannan tad'auro alwallah daga zaune tasamu tayi sallah sannan talalubo paracetamol tasha, nan saman darduman tayi kwanciyarta har saida gari yafara yin haske sannan tamik'e tajanyo alkyabbarta tasaka, cikin rashin k'warin jiki tafito duk wanda yaganta ya san batada lafiya, ko da kuyanginta suka gaisheta hannu kawai tad'aga musu taku take dak'yar tana dafa bango tana tsayawa tahuta ahaka ta isa part d'in yarima.
Tana murd'a k'ofar bedroom d'in yarima tsaye tayi tare da jingine kanta jikin k'ofar tana maida numfashi,
Yarima da daidai lokacin yasafka daga saman gadonsa tsaye yayi yana k'are mata kallo ko da cikin fushi yake da ita ammah hakan bai hana yaji wani iriba da yaganta cikin yanayin.
Zarah ahankali tatako tamatso kusa da shi, yarima d'aure fuska yayi yace meyakawoki wajena? Ko wani abun kikazo kik'ara shirya min?
murmushin k'arfin hali tayi sannan ahankali tace nasan kana jin haushina akan abinda yafaru, shuru tayi nad'an lokaci sannan tace ammah dan Allah ina neman alfarma guda,
saida takalli cikin idonsa sannan tacize le6e cike da dauriya tace kataimaka kayi bincike kafin kazartas da hukunci, katambayi guards d'inka sufad'a maka wanda yashigo part d'inka da bakanan dan ni wlh duk jiya ban shigoba sai dare, k'wallah ce tacika mata ido tace bawai na ce kar kad'auka ba ni bace sannan kuma ban hanaka d'aukar matakiba idan kagane niceba kawai ina tunatar da kai ne kar kayanke hukunci batare da kayi bincikeba, a kullum addu'a ta Allah yabayyanar da gaskiya bazan ta6ayin bak'in cikiba idan hakan yazama k'arshen tarayyarka da ni, saboda ni nasan gaskiya bata k'arewa saidai k'arya tak'are,
Yarima cike da mamaki yake kallonta koda ya san har cikin ransa ya san maganganun da tafad'a gaskiya ne ammah hakan baisa yanuna a fili ya aminceba, zarah dafe kanta tayi ahankali tace na barka lafiya juyawa tayi tana fara tafiya nan jiri yakwasheta tayi baya zata fad'i.
cikin sauri yarima yatarota tafad'o jikinsa, ahankali yafurta ya salam, saboda wani irin zafi da yaji jikinta saikace zafin garwashi, rikicewa yayi yama mance da abinda yafaru cike da damuwa yace zarah daman bakida lafiya? Me yake damunki? Lokaci guda yajero mata tambayoyin duk ya rud'e.
Zarah dak'yar tabud'e idonta tare da dafe kanta da yake sara mata, cikin muryar kuka tace kabarni inma mutuwa nayi babu abinda yadameka, wlh abinda akeyi min ya fi wannan ciwo kabarni kawai inmutu kowa yahuta, k'ila idan namutu zaka yarda da magana ta,
Yarima cike da rud'ewa yace kidaina cewa haka zarah, kifad'amin abinda yake damunki,
Zarah turesa tashiga yi cikin kuka tace ni kabarni wajen mamana zanje nasan su zasu fahimceni tunda sunsan abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iyaba.
Yarima rungumeta yayi a jikinsa yace kidaina cewa haka zarah, baisan lokacin da yayi su6ul da baka yace nima na yarda da ke.
Zarah idanuwanta suna lumshe batare da ta bud'eba tace dagaske ka yarda da ni?
Shuru yarima yayi yana mai nazarin maganar sai kuma chan yace eh.
'Dan guntun murmushi tayi sannan ahankali tace nagode.
Chak yarima yad'auketa yad'aurata saman gadon yakwantar da ita, wayarsa yad'auko yakira Dr feedoh (babbar likitace ta 6angare mata da take aiki a hospital d'insa) bayan sun gaisa yace kizo gida kisameni, cikin sauri tace toh ranka yadad'e, kashe wayar yayi tare da kallon zarah da taketa cize le6e tana girgiza kai daga ganin yanayinta kasan tana jin jiki, sannan yace ina zuwa, yana fad'in haka yafita
wajen guards d'insa yaje suna ganinsa duk suka duk'a suka kwashi gaisuwa,
yarima hannu kawai yad'aga musu sannan yakallesu d'aya bayan d'aya..........
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Wannan page d'in tukuicine agareki mummyna chubad'o muhammad, hak'ik'a kin wuce duk yadda kike tunani a zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare mummy😘*_
*PAGE* 4⃣5⃣
Ahankali yake warwarewa har yagama sannan yabud'e yafara karantawa gabansane yafad'i ganin sunansa aka rubuta da larabci, sai wasu rubutu da shi kansa baisan menene aka rubutaba saboda mitsi-mitsine daga chan k'asa kuma sunan zarah yaga anrubuta sannan daga gefe akasa d'aya ansa _ni zarah zan mallaki yarima_ gabansane yacigaba da fad'uwa cike da mamaki yace zarah ce tasamin laya dan tamallakeni? Me take nufi da hakan? cikin sauri yaje yad'auko na toilet d'in yawarware sunansa da na zarah kawai ne jikin takardar, tsaye yayi cike da mamaki yana k'ara bin takardun da kallo,
Zarah kwance take d'akinta duk kasala ta rufeta tanaso taje part d'in yarima ammah ta kasa saboda batajin dad'in jikinta, daga k'arshe dai daurewa tayi tamik'e tad'auko alkyabbarta tasaka sannan tafito tanufi part d'insa.
Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga tsaye tagansa rik'e da layar, juyowa yayi yaimata wani irin kallo, cak zarah taja tatsaya cikin ranta tace shikuma wannan mutumin me yake nufi da hakan?
Muryarsa taji ya ce abinda kikayi shirin yi toh bai yuwuba dan haka sai kicanza sabon shiri ammah ni nafi k'arfin duk wani sihiri.
Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai, ahankali tace ban fahimci akan abinda kake nufiba.
Yarima wurga mata harara yayi yace kar kimaidani wanda baisan abinda yakeba ko kin d'auka banga layun da kika ajeminba cikin toilet da k'arshin pillow na ba, zarah zaro ido tayi tace ni kuma?
Mik'amata yarima yayi yace toh ai sai kiduba kigani idan k'arya akayi miki, cikin sauri takar6a tashiga dubawa, tsoro da fargaba duk suka cikata, cikin sauri tad'ago kai takalli yarima da shima yake kallonta, muryarta tana rawa tace wlh ban aikataba bansan wanene yake neman jamin sharri ba, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, dasauri taje wajen yarima tarik'o hannunsa k'wallah duk ta cika mata ido tace kayarda dani wlh bani bace nakawo maka laya,
Fizge hannunsa yayi cikin d'aga murya yace idan bake bace toh wanene? Kuma sunan wanene a jiki?
Zarah kallonsa take cike da mamaki tace yanzu ka yarda zan iya yi maka asiri? Cike da rashin damuwa yace toh idan ban yardaba me kikeso inyi?
Murmushi Zarah tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace da ace ni mushrikace da ba akanka zan faraba kuma ba zan ta6a amincewa in aurekaba da tun farko zan san yadda zanyi inga ban aurekaba saboda nima inada wanda nake so, kuma da ace ina asiri da tun farko zanyi maka ba sai munkai wannan lokacinba, wlh nagaji da wannan sharrin da ake ja min komawane yaje dan kansa, tak'arashe maganar cikin kuka,
Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d'ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad'in haka tawuce tafita tabar d'akin.
Tafiya take zata koma part d'inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k'afartaba, hawaye d'aya na bin d'aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al'amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka?
Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad'i, cikin sauri taji an rik'ota tafad'a jikin mutum, d'ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad'e meyake faruwa dake ne haka?
Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik'e Zarah suka ida isa part d'in Zarah.
Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d'akin.
Zaunar da Zarah tayi saman d'aya daga cikin cushin sannan tazauna k'asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d'in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke ne?
Zarah ahankali tabud'e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.
Jakadiya gyara zamanta tayi tace gimbiya kifad'a min matsalarki ni nayi alk'awali zan taimaka miki kid'aukeni a matsayin uwa,
Zarah d'ago kai tayi takalli jakadiya har a lokacin hawaye suna zuba daga idonta cikin muryar kuka tace ya akeso inyi da rayuwata? Narasa wanene yake k'ullamin sharri da angama wanchan sai afad'a ma wannan shin ya akeso inyi? Ni zan iya hak'ura da auran inkoma gidanmu,
Cikin sauri jakadiya tagirgiza kai tace a'a ranki yadad'e kar kice haka dan Allah kifad'amin abinda yake faruwa nayi alk'awali zan taimaka miki.
Zarah kallonta tayi cike da gamsuwa da maganar jakadiya sannan takwashe duk makircin da akeyi mata tafad'a ma jakadiya,
Jakadiya jinjina kai tayi tace wannan ba aikin kowa bane sai na gimbiya sumayya,
Zarah cike da mamaki tace yanzu kina ganin itace zata yi min haka?
Jinjina kai jakadiya tayi tace tabbas itace dan nasan wacece gimbiya sumayya da mahaifiyarta fiye ma da haka zasu iya yi.
Zarah share hawayen fuskarta tayi tace toh wlh zan iya hak'ura da auren inkoma gidanmu.
A'a gimbiya kar kice haka bai dace kikaraya ba, mu munsan halinsu, kuma sumayya da kikaga yarima ya aura toh auren had'ine ba auren soyayya bane sukayi.
hatta shi kansa yarima da kike gani akwai abinda mahaifiyar sumayya take k'ullawa akansa wanda ita kanta sumayya bata saniba.
Zarah ido tazuba mata cike da mamaki.
Jakadiya tacigaba da cewa akwai wani lokaci da dada ta aikeni wajen sultana sadiya, lokacin da nashiga parlour bakowa har na juyo zan baro d'akin najuyo magana k'asa-k'asa a bedroom d'in sultana sadiya tsaye nayi lokacin da najuyo tana cewa so take gimbiya sumayya tahaihu idan yaron yafara wayau tanaso tabi kowace hanya dan ganin ta kawar da yarima inyaso mijinta abashi rik'on k'warya kafin jikan nata yagirma daga baya yazama shine sarkin gari, ta san idan yahau toh sai yadda taso mulkin gidan zai tafi, dan ta tsani mahaifiyar yarima taso ace itace tahaifi d'a namiji Wanda zai gaji garin ba mahaifiyar yarima ba, ina jin haka cikin sauri nafito nabaro part d'in gudun kar taganni dan nasan idan taganni toh bazata ta6a barinaba.
Zarah cike da rud'ewa tace daman haka matarnan take? Toh shi yarima baisan halintaba ya amince ya auri d'iyarta.
Murmushi Jakadiya tayi tace tabbas yarima yasan kad'an daga cikin halayyarta dan tun yana k'arami idan yaje part d'inta wahalar dashi take dan akwai lokacin da tata6a watsa mai ruwan zafi, tagargad'e ni da idan nafad'a ma wani sai tayi sanadiyar barina aiki, kasancewar nikad'aice lokacin da abun yafaru.
Toh ba'a gane taba? Cewar zarah.
Eh toh, yarima yana da wani irin hali wanda ba komai bane yake iya bud'e cikinsa yafad'aba wannan halinsane tun yana k'arami, kuma na tabbata shi kansa yana sane da abubuwan da tayi masa kawai dai ya sharene,
indai wajen makircine toh kala-kala matarnan ta iya dan ina tunanin dasa hannunta sumayya takeyi miki wad'annan abubuwan.
Zarah jingine kanta tayi cike da jin tausayin mijin nata, Jakadiya tace ranki yadad'e kigode ma Allah da basubi ta wata hanyarba dan ganin sun kawar da ke, koda basubin boka ammah sun san makirci kala-kala.
Jinjina kai zarah tayi cike da mamakin halin su sumayya, ahankali tace duk makircinsu basu isa suyi abinda Allah bai nufa ba, kuma ina neman kariya daga ubangijina, saidai bansan yadda zanyi inshawo kan yarima yafahimceniba.
Jakadiya tace kar kice haka ranki yadad'e kuma baidace kiga laifin yarima ba tunda duk baya makircinsu da suke miki baiyi tasiriba a garesa ammah a yanzu kiduba kiga har da sunansa da naki aka had'a kinga ai bakowa bane zai iya k'in yarda, yanzu dai abu d'aya zakiyi shine nake tunani kamar zai taimaka wajen ganin kin ku6utar da kanki, zarah kallon Jakadiya tayi tace wane abune please kifad'a min.
nan Jakadiya tace kice yatambayi guards d'insa sufad'i Wanda yashiga da baya nan tunda ke kince baki shigaba,
Zarah tace anya kina tunanin zai amince?
Eh insha Allahu ai ya aminta da su yasan bazasu ta6a yi masa k'aryaba,
Zarah jinjina kai tayi tace nagode sosai jakadiya, hak'ik'a kin taimakeni a lokacin da nake buk'atar taimako nakekai kukana ga ubangijina,
Jakadiya tace kar kidamu gimbiya har cikin raina nake jinki dan kece kikafi dacewa da yarima ba sumayya ba kuma ina fatan yakasance kece zaki fara aje mana magajin yarima.
Zarah saida gabanta yafad'i dasauri tagirgiza kai tace kar kice haka, sumayya ita tafi dacewa tahaihuwa da yarima.
'Yar dariya jakadiya tayi tace tuni tayi watsi da damanta koda haka mahaifiyarta taci buri itama ammah a yanzu k'addara ta riga fata,
Zarah cike da mamaki take kallonta tace ban fahimci abinda kike nufiba?
Murmushi jakadiya tayi tace kar kidamu dasannu zaki fahimta nan ba da dad'ewaba, jakadiya tana fad'in haka tamik'e tare da d'an rissinawa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.
Zarah d'aga kai tayi tace nagode sosai jakadiya saidai ince Allah yabaki ladar abinda kikayi min.
Jakadiya murmushi tayi tace kar kidamu ai yi ma kaine, nidai fatana kirik'e sirrin maganar da nafad'a miki.
Zarah murmushi itama tayi tace insha Allahu babu wanda zai san maganar nan bayan mahaliccinmu sai ni da ke.
Jakadiya tace nagode, nan sukayi sallama tafita, zarah tsaye tayi tana tunani cike da jinjina ma sumayya da mahaifiyarta sannan daga baya tawuce tashige bedroom d'inta takwanta, nan hawaye suka cigaba da fita daga idonta tana tunanin hukuncin da yarima zai yanke mata akan laifin da ba ita ta aikata shiba, fashewa tayi da kuka tace ya ubangiji kakawo min d'auki, kuka tayi sosai saida taji kanta ya fara ciwo sannan tadaina haka taita juyi saman gadon daga k'arshe bacci yayi awon gaba da ita.
Yarima bayan zarah ta fita zama yayi saman gadonsa tare da dafe kansa cike da takaici, mamakin zarah ne yakamasa dan baita6a tunanin haka daga garetaba tun daga yanayin tarbiyarta, ya dad'e zaune yana jinjina lamarin dan abun ya d'aure masa kai sosai dan idan ya ce ba ita bace toh wanene zaiyi hakan?, tsaki yaja cike da takaici sannan yakwanta abu guda yatsaya masa a rai kalmar da tafurta ta nima ina da wanda nakeso, haka kalmar yaita jinta a kunnensa tana masa yawo har daga k'arshe bacci yad'aukesa..
A chan 6angaren sumayya kiran sultana sadiya tayi tana yin picking bata bari tayi ko sallama ba cikin jin dad'i tace ummah na aiwatar da komai kuma ina tunanin nasara a cikin aikin namu, daga chan 6angaren sultana sadiya dariya tayi tace gaskiya naji dad'i daughter ai ina fad'a miki ta ruwan sanyi zatabar gidannan dan makirci kala-kala babu Wanda ban iyaba idan akayi wani baiyiba sai acanza wata hanyar, cikin jin dad'i sumayya tace saisa nake k'ara sonki ummana dan duk abinda nakeso kema kinasonsa na rabbata yanzu yarima zai zama nawa ni kad'ai.
Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kar kidamu d'iyata farin cikinki shine nawa, saisa nake burin kihaifo min jika wanda zai gaji masarautar nan ammah kinkasa fahimtar inda nadosa, Indai kinsan kina yin planning toh kitaimaki kanki kidaina tun kan waccan munafukar tafara haihuwa,
Gaban sumayya saida yafad'i dan bata ta6a yin tunanin hakaba, ahankali tace hakane kuma ummah insha Allahu bama zata haihuba zata bar gidan.
Sultana sadiya tace na dai fad'a miki kirufa ma kanki asiri kidaina.
Cikin shagwa6a sumayya tace toh ummah na ji.
Uhm Allah yasa dagaske, cewar sultana sadiya.
Ameen ummana.
Yauwa toh yanzu kikwanta kiyi bacci dare keyi.
Toh ummah ko mi kenan sai kinjini, nan sukayi sallama suka kashe wayoyin.
Sumayya fad'awa tayi saman gadonta cikin murna tace yes nasan zuwa gobe waccan munafukar zata koma kongon gidansu, ahaka tayi bacci cike da farin ciki.
Cikin dare zazza6i da ciwon kai suka tashi zarah daga baccin da take nan taita juyi saman gadon daga k'arshe k'asa tasafka takwanta, ciwon cinta yake babu wanda zata iya kira dan ko hannunta kasa d'agawa tayi daga k'arshe, tana nan tana juyi ahaka aka kira sallar asuba.
Har aka gama sallah akan kunnenta ammah takasa tashi dakyar tasamu tamik'e tana dafa bango har tashiga toilet, saida tahad'a ruwan d'umi tayi wanka sannan tad'auro alwallah daga zaune tasamu tayi sallah sannan talalubo paracetamol tasha, nan saman darduman tayi kwanciyarta har saida gari yafara yin haske sannan tamik'e tajanyo alkyabbarta tasaka, cikin rashin k'warin jiki tafito duk wanda yaganta ya san batada lafiya, ko da kuyanginta suka gaisheta hannu kawai tad'aga musu taku take dak'yar tana dafa bango tana tsayawa tahuta ahaka ta isa part d'in yarima.
Tana murd'a k'ofar bedroom d'in yarima tsaye tayi tare da jingine kanta jikin k'ofar tana maida numfashi,
Yarima da daidai lokacin yasafka daga saman gadonsa tsaye yayi yana k'are mata kallo ko da cikin fushi yake da ita ammah hakan bai hana yaji wani iriba da yaganta cikin yanayin.
Zarah ahankali tatako tamatso kusa da shi, yarima d'aure fuska yayi yace meyakawoki wajena? Ko wani abun kikazo kik'ara shirya min?
murmushin k'arfin hali tayi sannan ahankali tace nasan kana jin haushina akan abinda yafaru, shuru tayi nad'an lokaci sannan tace ammah dan Allah ina neman alfarma guda,
saida takalli cikin idonsa sannan tacize le6e cike da dauriya tace kataimaka kayi bincike kafin kazartas da hukunci, katambayi guards d'inka sufad'a maka wanda yashigo part d'inka da bakanan dan ni wlh duk jiya ban shigoba sai dare, k'wallah ce tacika mata ido tace bawai na ce kar kad'auka ba ni bace sannan kuma ban hanaka d'aukar matakiba idan kagane niceba kawai ina tunatar da kai ne kar kayanke hukunci batare da kayi bincikeba, a kullum addu'a ta Allah yabayyanar da gaskiya bazan ta6ayin bak'in cikiba idan hakan yazama k'arshen tarayyarka da ni, saboda ni nasan gaskiya bata k'arewa saidai k'arya tak'are,
Yarima cike da mamaki yake kallonta koda ya san har cikin ransa ya san maganganun da tafad'a gaskiya ne ammah hakan baisa yanuna a fili ya aminceba, zarah dafe kanta tayi ahankali tace na barka lafiya juyawa tayi tana fara tafiya nan jiri yakwasheta tayi baya zata fad'i.
cikin sauri yarima yatarota tafad'o jikinsa, ahankali yafurta ya salam, saboda wani irin zafi da yaji jikinta saikace zafin garwashi, rikicewa yayi yama mance da abinda yafaru cike da damuwa yace zarah daman bakida lafiya? Me yake damunki? Lokaci guda yajero mata tambayoyin duk ya rud'e.
Zarah dak'yar tabud'e idonta tare da dafe kanta da yake sara mata, cikin muryar kuka tace kabarni inma mutuwa nayi babu abinda yadameka, wlh abinda akeyi min ya fi wannan ciwo kabarni kawai inmutu kowa yahuta, k'ila idan namutu zaka yarda da magana ta,
Yarima cike da rud'ewa yace kidaina cewa haka zarah, kifad'amin abinda yake damunki,
Zarah turesa tashiga yi cikin kuka tace ni kabarni wajen mamana zanje nasan su zasu fahimceni tunda sunsan abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iyaba.
Yarima rungumeta yayi a jikinsa yace kidaina cewa haka zarah, baisan lokacin da yayi su6ul da baka yace nima na yarda da ke.
Zarah idanuwanta suna lumshe batare da ta bud'eba tace dagaske ka yarda da ni?
Shuru yarima yayi yana mai nazarin maganar sai kuma chan yace eh.
'Dan guntun murmushi tayi sannan ahankali tace nagode.
Chak yarima yad'auketa yad'aurata saman gadon yakwantar da ita, wayarsa yad'auko yakira Dr feedoh (babbar likitace ta 6angare mata da take aiki a hospital d'insa) bayan sun gaisa yace kizo gida kisameni, cikin sauri tace toh ranka yadad'e, kashe wayar yayi tare da kallon zarah da taketa cize le6e tana girgiza kai daga ganin yanayinta kasan tana jin jiki, sannan yace ina zuwa, yana fad'in haka yafita
wajen guards d'insa yaje suna ganinsa duk suka duk'a suka kwashi gaisuwa,
yarima hannu kawai yad'aga musu sannan yakallesu d'aya bayan d'aya..........
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Wannan page d'in mallakin kine maman fodio hakik'a ke masoyiyace ta gaskiya saidai ince Allah yabar k'auna_
*PAGE* 4⃣6⃣
Kallonsu yayi d'aya bayan d'aya sannan yace jiya bayan na fita zarah ta shigo part d'ina?
Gaba d'aya shuru sukayi suna tunani sai chan d'aya daga cikinsu yace gaskiya bata shigoba,
Yarima ido yazuba mai sannan chan yace toh ko akwai wanda yashigo?
Nan ma shuru sukayi, Yarima yace kuyi tunani dai.
Chan sai suka kalli juna sai suka eh toh ranka yadad'e gimbiya sumayya ta shigo bayan magrib, gaskiya inba itaba babu wanda yashigo.
Yarima jinjina kai yayi yace kun tabbata? Gabad'ayansu sukace eh ranka yadad'e.
Yarima baice komai ba yawuce yashige,
Koda yashiga parlour saman kujera yazauna tare da dafe kansa mamakin sumayya duk yacikasa ahankali yace idan na fahimta toh duk wani abu da yake faruwa toh dasa hannun sumayya a ciki, toh meyasa sumayya take yin haka? Meyasa takeso taga ta yi silar mutuwar auren zarah? Anya ba da sa hannunta aka zuba poison a abincinba? Wani huci yafitar mai zafi sannan yace koma me kenan da sannu gaskiya zatayi halinta ba zan zargetaba, yana nan zaune a wajen wayarsa tafara ringing ganin mai kiransa yasa yai picking tare da cewa Doctor kin iso?
Daga chan 6angaren tace eh ranka yadad'e gani a waje dogarawa sun hanani shigowa.
Yarima yace ohk, ba d'aya daga cikinsu wayar.
Toh ranka yadad'e, cewar doctor feedoh, nan tamik'a ma dogari d'aya waya, yana d'auka Yarima yace kubarta tashigo.
Jin muryar Yarima yasa yarissina kamar yana gabansa sannan cikin girmamawa yace toh ranka yadad'e angama.
Yarima kashe wayarsa yayi tare da mik'ewa yashiga bedroom d'in tsaye yayi bakin gadon yana k'are ma zarah kallo da gabad'aya ta galabaita, ahankali yazauna gefenta tare da dafa kanta yace ya jikin?
Gyad'amai kai kawai tayi,
Mik'ewa yayi yafito waje yasa d'aya daga cikin guards d'insa yaje yazo mai da doctor feedoh, cikin sauri yatafi.
Nan Yarima yadawo parlour yazauna yana jiransu, bayan minti biyar sai ga guard d'in tare da doctor feedoh sun shigo, duk'awa guards d'in yayi yace gata ranka yadad'e,
'Daga masa hannu yarima yayi,
Fuskarsa d'auke da murmushi yace u ar wlcm Dr.
Dr feedoh saida tazauna sannan tace thanks Dr, ya mai jikin.
Alhmdllh yace tare da mik'ewa yace bismillah mushiga daga ciki kidubata,
Ohk sir, cewar dr feedoh nan yarima yawuce gaba tana biye da shi har cikin bedroom d'insa, daga gefen da zarah take kwance yazauna, kallonta yayi da tazuba ma Dr feedoh ido, ahankali yace ga doctor nan zata dubaki.
Fuskar Dr feedoh d'auke da murmushi tace sannu gimbiya, ya k'arfin jikin naki?
Zarah ma d'an guntun murmushi tayi cikin k'arfin hali tace Alhmdllh.
Dr matsowa tayi tana fiddo kayan aikinta daga cikin jakka tace ranki yadad'e ko zaki iya fad'amin abinda yake damunki?
Zarah kallon yarima tayi da shima yatsareta da ido, shafa kanta yayi sannan yace kidaure kiyi mata bayani kinji? d'aga mai kai tayi alamun toh, yana fad'in haka yamik'e yace doctor bari inbaku waje.
Doctor feedoh murmushi tayi cikin girmamawa tace a'a ranka yadad'e kayi zamanka ka ga inda na6ace sai kataimaka min.
Murmushi yayi yace kar kidamu ai nasan aikinki, bakida matsala, yana fad'in haka yafita yakoma parlour
Yana fita doctor feedoh gefen gadon tazauna, fuskarta d'auke da murmushi tace ranki yadad'e kamar da me dame kike ji?
Ahankali zarah tabud'e baki tace zazza6i da ciwon kai.
Dr rubutawa tayi tace bayansu babu abinda kuma kikeji?
Zarah shuru tayi kamar tana tunani sai chan tace sai kuma yawan kasala da bacci, jinjina kai Dr tayi tace bayansu bakya tashin zuciya?
Girgiza kai zarah tayi.
Nan Dr tarubuta sannan tace toh kina cin abinci?
Ba sosai ba, cewar zarah.
Dr idon zarah d'aya taduba sannan tad'auko wata roba tamik'a mata tace ko zaki taimaka kiyo fitsari nan ciki, saboda akwai awon da nakeso inje yanzu inyo.
Zarah kar6a tayi tamik'e dak'yar, ahankali take tafiya har taje toilet d'in yarima, nan tayo fitsarin tafito tamik'a ma doctor, kar6a Dr tayi ta aje sannan tace ranki yadad'e kiyi hak'uri munason mud'an d'ibi jininki kad'an.
Zarah bata musaba tamik'a hannunta tare da runtse idonta nan Dr feedoh tad'ibi jinin sannan tamik'e tace bari inje inhad'o miki result d'in.
Gyad'a kai kawai zarah tayi.
Dr ko da tafito a parlour tasamu yarima kallonsa tayi fuskarta d'auke da murmushi tace ranka yadad'e munyi duk abinda yadace yanzu zanje inyi mata test zuwa anjima kad'an insha Allahu zan dawo da result,
Jinjina kai yarima yayi sannan yace toh bakomai Dr Allah yamaidoki lafiya.
Ameen tace sannan tawuce tafita.
Bayan ta fita yarima mik'ewa yayi yashiga bedroom d'in, kallon zarah yayi da take lumshe ido alamun bacci zatayi hannunta yaduba sannan yace baby bari ind'an sa miki drip,
Zarah batace komai ba, kalman babyn da yakirata da shi takemata yawo a cikin kunnenta dan wannan ne karo nafarko da yakirata da hakan,
Shima kansa yarima saida yaji wani iri ammah yashare nan yahad'a drip d'in yasa mata, sannan yawuce yashiga bathroom dan yayi wanka.
Lokacin da yafito zarah har tayi bacci dan haka yashirya sannan yakomo gefenta yazauna yana ganin yanayin yadda ruwan yake shiga jikinta.
Bayan awa d'aya sai ga Dr feedoh tadawo, nan yarima yabada izini abarta tashigo bayan ta shigo fuskarta d'auke da murmushi tace ranka yadad'e albishir nazo maka da shi kuma ina fatan samun goro daga wajenka.
Kallonta yarima yayi cikin rashin fahimta sannan yace albishir kuma?
Har a Lokacin fuskarta d'auke da fara'a tace eh ranka yadad'e.
Yarima yace ohk, ina jinki.
Dr feedoh kallon zarah tayi da tad'an bud'e idonta alamun ta farka tasakar mata murmushi sannan tace madam tana d'auke da juna biyu.
Yarima kalmarce yaji tana yawo acikin kunnensakamar a mafarki, Kallonta yake yace me kikace?
Murmushi Dr tayi sannan tace tana d'auke da ciki na tsawon wata ukku da rabi (14wks) kenan, nan tamik'a masa result d'in tare da takardar magani.
Yarima kar6a yayi ya duba sannan ya jingine kansa a jikin gadon tare da lumshe idonsa yana jin wani irin nishad'i a cikin ransa ahankali yace Alhmdllh, Allah nagode ma, nan yabud'e idonsa yasafkesu akan zarah da take kallonsa ammah bata gane abinda ake nufiba.
Kallon Dr yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace nagode doctor tabbas kinmin babban albishir kuma dole inbada tuk'uici, ammah abun mamaki ya akayi har yakai tsawon wannan lokacin ammah ban ganeba?
Murmushi Dr tayi sannan tace kuma doctor kana saurin fahimtar na wasu matan ammah kai naka sai gashi cikin ikon Allah, Allah ya 6oye abunsa har tsawon sati goma sha hud'u (14 wks) sannan yabayyana kuma har da k'arin ba wani laulayi takeyi ba.
Jinjina kai yarima yayi tare da kallon zarah da idanuwanta suke rufe yace hakane, Allah shi yake ajiyarsa kuma sai ya so yake bayyanata, yana fad'in haka yamik'e yaje yabud'e wardrobe d'insa yad'auko cheque yacike sannan yazo yaba Dr feedoh yace ga goron albishir d'inki.
Dr feedoh d'an rissinawa tayi takar6a cikin jin dad'i tace nagode sosai Dr, Allah yasafketa lafiya, nan tacigaba da yin addu'a.
Fuskar yarima d'auke da murmushi yace Ameen mungode.
Dr feedoh jakkarta tad'auka sannan takalli zarah tace toh ranki yadad'e Allah yasafke mana ke lafiya, sai anjima.
Yarima ne kawai yace Ameen tare da mik'ewa yarakata har bakin k'ofa nan tak'ara yi masa godia sannan tatafi.
Yarima dawowa yayi bedroom d'in inda yatarar da zarah har a lokacin idanuwanta a lumshe suke, tunda taji an ambaci ciki gabanta yashiga dukan ukku-ukku dan ita ta ma rasa shin murna take ko bak'in ciki, a chan 6angare guda kuma murna take, bata ankaraba sai jin Yarima tayi ya d'age mata riga yana shafar cikinta, sharesa tayi tak'i bud'e idon nata, ya dad'e ahaka sannan yamik'e yace kitashi kiyi breakfast,
Zarah shuru tayi ta k'yalesa da mamakinsa sai ganin hawaye yayi sun gangaro daga idonta, da mamaki yake kallonta cikin ransa yace kar dai ace cikin ne bata so? Haushi ne yakamashi dan haka yashareta yawuce yafita daga d'akin.
Zarah tana jin fitarsa tabud'e idonta tare da bin k'ofar da kallo cike da tausayin kanta tace taya zan haihu da mutumin da baya sona, chan kuma gefe d'aya na zuciyanta tace ammah kuma yanason abinda yake cikin cikinki, hannu takai tashafi cikin cike da mamaki tace taya ciki yazauna min tsawon wannan watannin ban saniba? Toh wai ma duka yaushe akayi aurenmu?
Tunani tashiga yi sai kuma chan tace idan ban mantaba wata ukku da sati ukku kenan ya kama sati (15) kenan, gabantane yafad'i tace na shiga ukku yanzu cikin satina na biyu ciki yashigeni? K'wallah ce tacigaba da fita daga idonta, batasan lokacin da Yarima yashigoba sai ji tayi ya ce kitashi kiyi breakfast.
Zarah kallon yadda yahad'e rai tayi sannan tamik'e dak'yar, Yarima yataimaka mata yasa mata pillow a bayanta ta jingine sannan yahad'a mata tea mai kauri yamik'a mata, kar6a zarah tayi tafara kur6a jikinta yana rawa saboda wata irin yunwa da takeji.
saida tasha kusan rabin cup d'in sannan tamik'a ma Yarima ya amsa ya aje sannan yazubo mata chips, cikin sauri zarah tajanye kanta ahankali tace na k'oshi.
Yarima ido yazuba mata sannan yace ammah yanzu ba ke kad'ai bace kuma bakiga yadda duk kika rameba ya kamata kidinga daurewa kina d'an cin abinci.
Zarah rik'o hannunsa tayi tare da marairaicewa tace dan Allah kar kafad'a ma kowa ina da ciki.
kallonta yayi cike da mamaki yace saboda mi?
Rau-rau tayi da ido sannan tace kawai hakanan.
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa nan yakwashi kayan breakfast d'in yafita da su parlour, zarah da kallo tarakasa har yaficce sannan takoma takwanta tare da maida idonta talumshe tana tunanin wai itace da ciki, hannunta tad'aura saman cikin, tana nan kwance haka sai ga Yarima ya shigo hannunsa d'auke da ledar drugs da injection da yabayar asiyo.
Ajewa yayi saman bedside tare da d'auko ruwa sannan yace kitashi kisha maganin,
Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace idan nasha amai zanyi.
Yarima zama yayi gefenta tare rik'o hannunta yace kar kidamu bazakiyi amai ba,
Toh kawai tace, nan yataimaka mata tatashi zaune sannan yabata maganin saida ta runtse idonta sannan takar6a takai baki cikin sauri takora da ruwa, sannan tabud'e ido,
Nan yafara k'ok'arin had'a injection, kallonsa take a tsorace ahankali tace kuma harda ita za'ayi min?
Shuru Yarima yayi saida yagama had'awa sannan yakalleta har da d'an guntun k'wallarta taso tabashi dariya ammah yadake yace kigyara sai inyi miki.
Zarah komawa tayi takwanta tana kuka ciki-ciki, kallonta yayi yace kar kimotsa fa.
Batace komai ba jin zai shigar da allurar yasa tarik'esa gam, tare da runtse idonta.
Murmushi Yarima yayi sannan yatsira mata ahankali, bata ma san lokacin da yazare inj d'inba dan kwata-kwata bataji zafintaba, sai ji tayi yana cewa toh shikenan angama, zarah k'in sakinsa tayi saidai ji yayi tana fitar da sautin kuka k'asa-k'asa.
Ahankali yajanye daga rik'on da tayi mai tare da zuba mata ido sai chan yace kukan fa?
Turo baki tayi cikin shagwa6a tace ba kaine ba kayimin injection ba.
Murmushi yayi tare da jan d'an k'aramin bakinta sannan yace toh ai banyi miki da zafiba ko ak'ara wata?
Cikin sauri tagirgiza kai tare da cewa a'a.
Ido yazuba mata itama shi take kallo, ahankali tace kaida ma kake fushi da ni,
Murmushi yayi yace ni ba fushi nake da keba, kidaina maganar ta wuce kinji ko?
Murmushi zarah tayi tare da d'aga mai kai, hannunsa tarik'o tad'aura saman cikinta tace kana son babynmu?
Yarima ido yazuba mata sai chan yace ke kina sonsa?
Cikin sauri tace eh,
Mik'ewa yayi yace bari inje inhad'a miki ruwa kid'an gasa jikinki.
Murmushi kawai zarah tayi tare da komawa takwanta.
Toilet d'insa yashiga yahad'a mata ruwan wanka, bayan ya had'a fitowa yayi d'auke da towel yamik'a mata, kar6a tayi tare da mik'ewa dak'yar tacire rigar jikinta sannan tad'aura, yarima kamata yayi yarakata har toilet sannan yajanyo mata k'ofar.
Kwance tayi cikin ruwan tana jin wani irin nishad'i a cikin ranta, tunowa tayi da sumayya saida gabanta yafad'i, tsintar kanta tayi cikin zuciyanta tana addu'an neman kariya daga sharrinta.
Nan tafara wanka duk jikinta ya yi sanyi ahaka tagama sannan tafito, lokacin yarima baya d'akin, gaban dressing mirror tazauna tashafa mai sannan tamik'e taje tagyara gadon, bayan ta gama parlour tafito tasami yarima da yake zaune yana jin wani irin dad'i a cikin ransa, kallonsa tayi da shima yakalleta, turo baki tayi sannan tace ni banda kayan da zansa.
Janye idonsa yarima yayi sannan yamik'e yafita yaje ya aiki d'aya daga cikin guards d'insa part d'in zarah dan yakar6o mata kaya.
Lokacin da yadawo zarah tana bedroom nan yarima yakar6a yaje yakaimata sannan yadawo parlour yayi Kwanciyarsa saman 3 seater.
Bayan ta gama kwanciyarta tayi saman gadonsa nan bacci yayi awon gaba da ita,
Saida aka kira azuhur sannan yarima yamik'e yashiga bedroom, kallon zarah yayi da take baccinta hankali kwance, takowa yayi yazo yazauna gefenta tare da yaye blanket d'in da tayi rufa da shi gani yayi tana zufa alamun zazza6in ya safka, hannu yakai yad'age mata riga tare da shafa cikin nata, ido yatsura ma fuskarta duk tayi fayau da ita, murmushi yayi sannan yamik'e yaje yacire kayansa yashiga bathroom,
Bayan ya fito wanka shiryawa yayi sannan yaficce yatafi masallaci, rufe k'ofan da yayine yasa zarah tafarka, ji tayi zazza6in ya safka, ahankali tasafka daga saman gadon saida tagyara mai sannan tafito takoma part d'inta.
Koda tashiga saida tak'ara wanka sannan tad'auro alwallah.
Bayan ta yi sallah sawa tayi akayi mata faten tsaki taci saboda shi taji tana buk'ata.
tana cikin ci saiga yarima ya shigo, ido yazuba mata tare da yamitsa fuska,
Ganin haka yasa zarah tayi murmushi tace bismillah.
menene wannan? Cewar yarima.
Faten tsakine kazo kad'and'ana kaji akwai dad'i.
no, aci lafiya, ya jikin naki?
Dasauki, cewar zarah.
Ohk, Allah yak'ara sauk'i, idan kin gama kisha drugs d'inki.
Ahankali tace toh,
Juyawa yayi yafita yabar d'akin nan zarah tacigaba da cin faten.
A chan 6angaren gimbiya sumayya tun tana sa ido dan taga yarima ya kori zarah ammah shuru a k'arshema a gaban idonta yaje d'akin zarah sannan agaban idonta yafito.
Ahankali tafurta da alama aiki ya 6aci, takaici ne yacikata batasan lokacin da tace anya waccan munafukar bata asirce yarima ba? Tsaki taja cikin jin haushi tace akwai alamar tambaya a cikin lamarin nan, dan babu yadda za'ayi ace kullum itace da nasara, wlh duk sihirinta sai nayi silar barinta gidan nan
A haka zarah tacigaba da kula da cikinta, yanzu ta samu sauk'in zazza6in da takeyi saidai yawan amai idan taji k'amshin abinda bata so, abinci ko sai ta za6i irin wanda takejin zata iya ci, ta d'an rame ammah ta k'ara haske da kyau fatar jikinta ta k'ara laushi.
A 6angaren yarima yana zuwa yaduba lafiyarta, sannan yana kiranta a waya koda ace bai jeba, itama tana k'ok'arin ganin ta je part d'insa koda sau d'ayane a cikin kwana biyun, har lokacin ba wanda tabari yagane tana da ciki.
*BAYAN SATI BIYU*
A ranar da cikinta yacika wata hud'u, bayan sallar la'asar ji tayi kwanciyar ta isheta, mik'ewa tayi tanufi part d'in yarima lokacin da tashiga a parlour tasamesa yana sa agogo a hannunsa da alama fita zaiyi. kallonta yayi ganin ta zuba mai ido yace ya dai?
Murmushi zarah tayi tare da marairaicewa tace dan Allah inaso inje ingaishe da su dada.
Keda bakida lafiya kuma zaki fita? Cewar yarima.
Zarah shuru tayi sai chan tace na fa samu sauk'i kuma ni zaman ne ya isheni saisa nakeson ind'an mik'e k'afar.
'Daukan hularsa yayi yasaka sannan yace ohk, muje nima yanzu fada zanje.
Cikin jin dad'i zarah tafad'a jikinsa tare da cewa nagode,
yarima janyeta yayi daga jikinta tare da kallon cikinta yace kar kiji ma baby ciwo.
Murmushi zarah tayi tare da jawo hannunsa tad'aura saman cikinta tace kar kadamu babynka yana lafiya,
Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace muje memartaba yana jirana, zarah wucewa tayi gaba yarima yabi bayanta suna fitowa a jere suke tafiya, saida suka zo wajen turakar dada sannan zarah tashiga yarima yawuce fada.
koda tashiga a parlour ta tarar da dada da kuyanginta ana mata tausa a k'afarta, nan kuyangin dada suka dinga duk'awa suna gaisheta, zarah tadinga amsa musu cikin sakin fuska sannan tasamu waje a k'asa saman carpet tazauna gefen dada da take saman cushin, fuskar dada d'auke da murmushi tace a'ah yau amarya ce dakanta?
Murmushi zarah tayi tare da duk'ar da kai cikin girmamawa tagaishe da dada.
dada amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayarta ya suke.
Alhmdllh duk muna lafiya, cewar zarah cike day kunya.
Ina wannan miskilin mijin naki? Kwana biyu ban gansaba, ko kuma kun min k'wace yanzu ku kad'ai yasani, dada tafad'i maganar cikin tsokana.
Murmushi zarah tayi sannan tace taya zai mance da ke uwar gida? Ai mu bamu isa mushiga tsakaninku ba, aikine kawai ya6oyesa.
Gidanku ja'irar yarinya kawai, ammah shi aikin bai 6oye muku shi ba sai ni dan rashin adalci.
Dariya zarah tayi sannan tace ranki yadad'e taya zai mance da mu sabon jini?.
Knocking d'in k'ofan da akayine yasa dada tabada izini a shigo, d'aya daga cikin kuyangartace d'auke da wani tray, nan tazube takwashi gaisuwa wajensu sannan tacema dada ranki yadad'e gashi angama.
Murmushi dada tayi tace toh mik'omin shi nan itama kishiyata taci, cikin sauri kuyangar takai gaban dada ta aje.
dada kallon zarah tayi da take wasa da yatsun hannunta tace ga fa dambun kifi kici dada tafad'i haka tare da bud'e murfin da aka rufe shi da shi.
zarah k'amshin yadaki hancinta daurewa taso tayi nan zuciyanta yafara tashi, wani irin tuk'a taji yana taso mata cikin sauri tamik'e dagudu tanufi k'ofa, dada cike da mamaki tace lafiya me yake faruwa?
Batama san dada tanayi ba kafin tafita daga k'ofan sai aman yakubce mata nan tafara kwararashi..
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Jinjinar bangirma agareki mummyna chubad'o muhammad, nagode sosai da dedicated d'in book da nasamu saidai ince Allah yabarmu tare 4ever😘_
*PAGE* 4⃣7⃣
Dada da take zaune ido tazuba mata tana kallon ikon Allah ganin tana ta aman kamar zata amayen 'yancikinta yasa tafara yi mata sannu nan tasa kuyangarta d'aya tad'auke dambun kifin daga wajen.
Bayan zarah ta gama aman a galabaice alkyabbarta kawai tacire saboda ita kad'ai ta6aci.
dada kuyangi tasa sugyara wajen nan tacigaba da jera ma zarah sannu sannan tace tashiga ciki tagyara jikinta,
A kunyace tace toh sannan tawuce toilet da yake cikin bedroom d'in dada batare da ta kalli dada ba,
Dada ido tazuba mata tana kallonta har tashige sannan tayi murmushin jin dad'i tace Alhmdllh da alama mun samu rabo.
Zarah jiki ba k'wari tahad'a ruwan d'umi tayi wanka bayan ta fito kayan jikinta tamaida tunda su basu 6aciba, zaune tayi takasa fitowa saboda wata irin kunyar dada da takeji na amai da tayi mata a parlour.
Ta dad'e a zaune sannan daga baya tamik'e lokacin da tafito parlour da mamakinta taga angyara wajen tes d'akin sai k'amshin turaren wuta yake, kallonta dada tayi har tazauna sannan tace sannu 'yar nan ai da kin fad'i bakison k'arnin kifin da ban bud'eba, kuma bakida lafiya baku fad'amin ba ai da nazo na dubaki, kokuma wannan miskilin mijin naki taya zai fad'a, abinda ma yashafesa bai fad'aba barema ayi tunanin fad'an na wani.
K'ara duk'ar da kanta tayi k'asa cike da jin kunya.
Ganin haka yasa dada tace yanzu me kikeson ci? Naga kin amaye duk abinda kikaci.
Cikin jin kunya tace na k'oshi.
A'a wane irin kin k'oshi keda ba komai cikin cikinki, k'walah ma kuyangarta kira dada tayi tace aje akawo ma zarah tuwo, cikin sauri kunyarta tace angama ranki yadad'e sannan tafita tabar d'akin.
Dada tace ai nasan shi tuwo zaki so shi, murmushi kawai zarah tayi.
Bayan 'yan mintuna sai ga kuyangar nan ta shigo d'auke da kular tuwo, wata kuma tana rik'e da na miya da plate nan suka aje gaban zarah.
Dada tace suzuba mata taci, nan suka zuba sannan suka bud'e miya kala biyu ce sukace ranki yadad'e wace za'a zuba miki?
Zarah kallon miyan tayi ganin miyan ku6ewa d'anya da ta ganye ce yasa tace azuba mata ta ku6ewa nan suka zuba mata sukace ranki yadad'e man shanu fa?
Cikin sauri tagirgiza kai tace kar kuzuba min.
Cikin sauri sukace angama ranki yadad'e sannan suka tashi suka fita daga d'akin.
Dada kallon zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace kici man.
Murmushi zarah tayi sannan tafara d'iba taci, ta ji dad'in miyan sosai ga tuwon mai laushi irin mai wucewa silif wanda take so nan tacigaba da ci ahankali cike da jin nauyin Dada.
Ganin haka yasa Dada ta tattara hankalinta ga news d'in datake kallo dan zarah tasamu taci sosai.
Haka zarah tad'anci sannan tature plate d'in, kallonta dada tayi tace ba dai har kin k'oshiba?
Zarah ahankali tace eh dada na k'oshi.
Kidaure kid'an k'ara ko kad'anne, cewar dada.
Zarah cikin jin kunya tace na k'oshi.
Dada tace toh shikenan, nan tamaida hankalinta ga TV.
Zarah samu tayi tamik'e dan tawanko hannu.
Da kallo dada tabita cike da farin ciki dan ko ba'a fad'a mataba yanayin zarah da tagani yasa ta gane cikine gareta, ahankali tace Allah sarki sumayya naso inga jininki ammah da rabon na zarah zan fara gani....tana chan tana tunani batasan lokacin da zarah tadawo ba sai da tafara tattara kwanukan sannan hankalin dada yakai wajen, zaro ido dada tayi da cewa miye haka zakiyi?
Zarah batare da ta kalli dadaba tace ranki yadad'e zan d'an rage kayanne.
Dada tace a'a aje bari ma'aikatan suzo sukwashe keda bakya jin dad'in jikinki, kawai kizauna kihuta.
Dada ai zan iya, cewar zarah.
A'a kibari suzo sukwashe.
Zarah ajewa tayi sannan takoma tazauna,
Dada tace da kin shiga ciki kin d'an kwanta kihuta.
Murmushi Zarah tayi sannan tace dada ai yanzu ma nakeso inwuce gida.
Jinjina kai dada tayi tace kar kikwanta nan musaceki ko?
Yanayin yadda dada tayi maganar saida yaba Zarah dariya tace a'a dada kawai dai akwai abinda zanje inyine.
Cikin gamsuwa da maganar dada tace toh ai shikenan hakan ma mungode Allah yabada ladan zumunci, Allah yayi muku Albarka.
Ameen ranki yadad'e, nan Zarah tayi ma dada sallama tafita.
Dada binta tayi da kallo cike da sha'awa tace Allah sarki sumayya kema Allah yasa ina da rabon ganin naki d'an,
Ita kanta dada tana mamakin yadda cikin jikokinta ta fi son sumayya, hakan ya samo asaline ta dalilin duk cikinsu ita sumayya tun tana k'arama daman itace ta wajen dada inbata wajen ummanta to tana wajen dada, dan a k'arshema dada ce tayi yayenta.
Zarah tana cikin tafiya har zata shiga 6angarensu sai ga sumayya ta fito, saida gaban Zarah yafad'i dan rabon da taga sumayya Ita kanta ta mance dan zata iya cewa tayi kusan 2 weeks.
Tsaya sumayya tayi tana kallon zarah cike da mamaki ganin yadda tacanza tak'ara fresh da kyau, chan sai taja tsaki sannan cikin fad'a tace ke dabbar ina ce kina ganin mutane zasu wuce ammah kikasa basu hanya suwuce.
Zarah murmushi tayi cikin rashin damuwa tare da dakewa tace kar kidamu ke ai naga ko cikin dangin namu na dabbobi kamar makauniyace tunda duk fad'in hanyarnan kirasa ta inda zakibi sai ta wajena.
Cike da mamaki sumayya takalli Zarah dan bata d'auka zata iya yada mata magana irin hakaba, ran sumayya in yayi dubu toh ya 6aci cikin d'aga murya tace eh dole kice haka dan a yanzu kinsha jan miya kin waye kina gani kamar daidai kike da ni, toh wlh bari kiji ni nan da kike gani bani ta6uwa kuma duk ubanda yace zai ta6ani toh aikam zai ta6o ma kansa masifa da bala'i ke sai kinyi kuskuren abinda kika aikata agareni.
Zarah dafe kanta tayi cikin kwantar da murya tace please malama kiban waje inwuce idan ke kinsaba hargagi toh ni ban sababa dan har kin fara haddasa min ciwon kai.
Sumayya a harzuk'e tace ke ko ubanki bai isa yafad'amin maganaba bare ke jakkah,
Zarah murmushin takaici tayi sannan tace Allah sarki kar kidamu nasan jahilcine yayi miki yawa ammah dan Allah ya kamata kikoma islamiyya gimbiya, tana fad'in haka tacanza hanya tawuce tabar sumayya tsaye tana ta balbalin bala'i.
Sumayya cikin 6acin rai tawuce tanufi turakar iyayenta, a parlour ta tarar da sultan Abbas da mahaifiyarta, ganin Abbanta yasa tad'an saki fuska gefensa tazauna cikin sakin fuska tagaishesa.
Murmushi sultan Abbas yayi sannan ya amsa mata tare da tambayarta mijinta.
Sumayya cikin shagwa6a tace Abbah yana lafiya.
Toh ya 'yar uwartaki dafatan kuna zaman lafiya?
Sumayya ji tayi kamar ya da6a mata wuk'a a mak'ogwaro jin ya kira wadda tafi tsana a rayuwarta a matsayin 'yar uwarta, murmushin yak'e tayi sannan tace abbah tana nan lafiya.
Toh masha Allah adaicigaba da hak'uri sumayya kizauna da ita lafiya banason fad'a ko tashin hankali.
Toh Abbah daman muna zaman lafiya.
Cikin jin dad'i sultan abbas yace yauwa 'yar abbah Allah yaimiki abarka.
Ameen abbana, cewar sumayya sannan takalli sultana sadiya da tazuba musu ido tana murmushi, itama sumayya murmushin tayi sannan tace ummana ina wuni?
Lafiya lou daughter ya gidan?
Alhmdllh ummah,
Toh masha Allah ina fatan mijinki da 'yar uwartaki suna lafiya.
Sumayya cike da mamaki take kallon ummah ganin yadda ummanta take Magana a gaban abbah.
sumayya murmushi tayi mai fassara sannan tace duk lafiya lou ummah.
Sultan Abbas mik'ewa yayi yace bari inje fada nasan yayana yana chan yana jirana dan akwai wata jana'iza da zamuje ta abokinsa.
Sultana da sumayya nan sukayi mai adawo lafiya dan sultana sadiya har bakin k'ofa tarakasa sannan tadawo.
Da mamaki take kallon sumayya da lokaci guda tacanza fuska, sultana sadiya cike da damuwa tace sumayya lafiyarki?
Sumayya k'wallah ce tafara fita daga idonta cikin muryar kuka tace ummah na tsani yarinyar chan natsani inbud'e idona inganta cikin gidannan.
Sultana sadiya cike da damuwa tazauna gefen sumayya tare da rungumota jikinta cikin rarrashi tace sumayya kema kin sani nima hankalina ba zai ta6a kwanciyaba in ina ganinki cikin damuwa, kicigaba da hak'uri insha Allahu zarah ta kusan fita tabar miki gidanki.
Sumayya cikin sauri tad'ago kai takalleta tace ummana taya hakan zata kasance, wlh yarinyar chan yadda kikasan ta asirce yarima, kiduba kiga duk makircin da ake k'ullah mata ammah bai ta6a d'aga kai yakalletaba, ni wlh har na fara gajiya ina tunani akwai abinda tak'ullah.
Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kidaina damuwa daughter kibarni da ita in ta san wata toh batasan wataba ni nasan yadda zanyi da ita dan suhail na sumayya ne ita kad'ai.
Cike da jin dad'i sumayya tak'ara ruk'unk'ume ummanta tace nagode sosai ummana Allah yabar min ke.
Sultana sumayya cike da son d'iyartata tace Ameen daughterna.
A chan 6angaren zarah lokacin da tashiga part d'inta a parlour ta yada zango saman 3 seater tare da jingine kanta da kujerar tana maida numfashi ahankali, chan taji wani irin tuk'a ta taso mata, cikin sauri tamik'e tanufi toilet,
Saida ta amaye dukkan tuwon da taci duk ta galabaita, dak'yar tasamu tawanke fuskarta tafito tahau saman gadonta tayi kwanciyarta,
Tana mamakin yadda yau daga safe zuwa yanzu ta yi amai ya kai biyar.
Juyi kawai take saman gadon har aka kira sallar magrib tayi sallah tana zaune saman darduma tana lazumi aka kira isha'i.
Bayan ta gama sallah wanka tashiga tayi sannan tayi shirin bacci, yunwa taji tana ji ammah gudun kar tayi amai yasa tayi kwanciyarta haka.
Wajen 8:30pm kwance take saman gadonta ga yunwa duk ta addabeta, kawai ji tayi tanason shan ice cream,
Sharewa tayi tai kwanciyarta tana ta juyi daga k'arshe ji tayi bata iya daurewa indai batasha ice cream d'inba toh akwai matsala, dan haka tamik'e cikin sauri tad'auko hijab tazumbula tafito tanufi part d'in yarima har tana tuntu6e.
Tana shiga tasamesa zaune a parlournsa yana kallon ball gabad'aya ya tattara hankalinsa a TV d'in kasancewar yana son wasan, bai ankaraba sai jinta yayi ta fad'o jikinsa,
Kallonta yayi cike da mamaki yace ke lafiya? Zarah k'irjinsa tashige tare da fashewa da kuka.
Yarima gigicewa yayi yace lafiya zarah? Meyake faruwa?
Cikin sheshek'an kuka tace ni ice cream nakeson sha, bana iya cin abinci da naci amai nake, d'azun ma saida nayi wajen dada.
Yarima ajiyar zuciya yasafke sannan yace yanzu saboda ice cream kike kuka?
Turo baki tayi cikin shagwa6a tace uhm.
Wayarsa kawai yajanyo batare da yayi magana ba yakira wani guard d'insa yace yaje yasamo masa ice cream yanzu, daga chan 6angaren guard d'in cike da girmamawa yace toh ranka yadad'e angama.
Kashe wayar yarima yayi tare da kallon zarah da tatsaresa da ido har a lokacin k'wallah tana fita daga idonta, sannan yace bari akawo miki.
Gyad'a kai kwai tayi sannan tacire hijab d'inta takoma ta lafe a k'irjinsa wani irin numfashi taja dan har cikin ranta taji dad'in hakan,
Yarima maida idanuwansa yayi yalumshe yanajin yanayin d'umin jikinta.
Haka suka kasance babu wanda yak'ara magana sai chan wayarsa tafara ringing, d'aukota yayi ganin mai kiransa yasa yayi picking batare da yayi magana ba,
Daga chan 6angaren akace ranka yadad'e ansamo,
Kallon zarah yayi da tazuba mai ido sannan yace ohk ina zuwa.
Jin haka yasa zarah tasafka daga jikinsa nan yamik'e yanufi k'ofa yakar6o yadawo saida yazauna sannan yamik'a ma zarah k'atuwar ledar.
Cikin sauri tak'ar6a fuskarta d'auke da murmushi tace nagode sannan tabud'e robabin ice cream ne manya kusan guda biyar nan tafito da guda, kallon yarima tayi da yake kallonta tace zakasha?
Girgiza mata kai kawai yayi.
Mik'a mai d'ayan tayi cikin shagwa6a tace karik'e min insaka sauran cikin freezer kar yanarke.
Yarima zuba mata ido yayi batare da ya yi magana ba kamar ba zai kar6aba sai kuma chan yakar6a.
Mik'ewa tayi tanufi freezer d'insa tasaka sannan tadawo tazauna saman cinyarsa tare da kar6a tabud'e robar, jikinta har rawa yake nan tafara sha.
yarima ido yazuba mata yana kallon yadda take sha saikace wadda akace za'a k'wacemawa, hannu baka hannu k'warya takeyi.
Har saida takusan shanyewa sannan ta aje takalli yarima tayi murmushi ahankali tace nagode nan takwanta k'irjinsa tayi lamo,
Ahankali taji yarima yana neman tura hannuwansa cikin rigarta, maida idanuwanta tayi talumshe fuskarta d'auke da murmushi.
Cikinta yashiga shafawa, yanayin yadda yake shafarsa wani irin shock takeji a jikinsa, nan tak'ara lafewa,
Ahankali yamaida hannuwansa a k'irjinta yana shafa cikin wani irin salo, zarah nema tayi tarikice mashi nan taruk'unk'umesa.
Cigaba yayi da abinda yake saida yayi kusan 5 minutes sannan yafitar da hannunsa daga cikin rigarta, ahankali yabud'e idanuwansa da suke lumshe tare da lek'a fuskar zarah da tatura cikin k'irjinsa kamar zata shige ciki sai maida numfashi take kad'an kad'an, murmushi yad'anyi kad'an sannan yad'auketa cak yanufi bedroom d'insa bai zameta a ko'inaba sai saman bed d'insa.
Zarah na ji ya safketa cikin sauri tajuya mai baya, murmushi yayi sannan yawuce yakoma parlour yakashe kayan kallon sannan yadawo bedroom d'in, kashe gloves yayi nan yahau gadon yakwanta daga bayan zarah.
Hannunsa taji yad'auro saman cikinta, murmushi tayi sannan ahankali itama tad'aura hannunta saman nashi tana shafawa juyowa tayi takallesa cikin d'an hasken da yake d'akin har a lokacin hannunta yana cikin nasa ganin shima idanuwansa suna a kanta yasa tamaida kanta a k'irjinsa takwanta.
Lumshe idonsa yayi yana shak'ar k'amshin gashin kanta, sai chan yace meyasa bakison cin abinci?
Zarah d'ago kai tayi takallesa ganin idanuwansa a rufe yasa kamar zatayi kuka tace amai yake sanyani.
Bud'e idonsa yayi yakalleta, sannan yace kidinga ci kokad'anne.
Umhum kawai zarah tace.
Hannu yakai yajanye mata gashinta da yabazu har gefen idonta, ido suka zuba ma juna suna ma junansu wani irin kallon da su kansu basusan ma'anarsaba, yarima ne cikin sauri yafara janye idonsa daga cikin nata.
Zarah ma cikin jin kunya tamaida kanta takwantar a k'irjinsa,
Ahankali taji ya kai hannunsa yana neman rabata da 'yar rigarta.
Yana cirewa tazame jikinta daga nasa.
Da mamakinta sai ganin yarima tayi ya dawo bisa ita, zaro ido tayi kafin tayi magana sai jin bakinsa tayi cikin nata, sun dad'e a haka sannan yagangaro wuyanta zuwa k'irjinta.
Zarah bada kai tayi dan ita kanta tasan abuk'ace take da mijin nata.
Bayan komai ya lafa Zarah kukan shagwa6a tasaka mai, yarima rungumota yayi jikinsa yana d'an bubbuga bayanta ahankali alamun lallashi.
Zarah cigaba tayi da kukan, ahankali yabud'e idanuwansa da suke lumshe cikin muryarsa da tadashe yace kukan fa?
Turo baki Zarah tayi cikin kuka tace toh bakaibane kaban wahala, kuma wanka nakeso kayi min.
Ido yazuba mata sai chan yace na ji.
Janyeta yayi daga jikinsa yamik'e yanufi toilet, saida yatsarkake jikinsa sannan yahad'a mata ruwan d'umi.
Bayan ya fito kallonta yayi yace muje.
Hannu Zarah tamik'a mai alamun yad'auketa.
Yarima babu yadda ya iya haka yaduk'a yad'auketa yanufi toilet da ita, cikin komin yasakata.
Har ya juya zaya tafi Zarah cikin sauri tarik'o hannunsa tare da fashewa da kuka tace kayi min wankan.
Yarima haka yatsaya yana mata wanka ita kuma tana zuba mai shagwa6a, har yagama sannan yahad'a mata wasu ruwan yace tayi wankan tsarki.
Ganin ya juya zai tafi yasa zarah tace bana fa iyayi please kataimaka kayi min.
tsaye yarima yayi cikin ransa yace yarinyar nan ta raina min wayau, kamar yace bazaiyiba sai kuma chan yafara yi mata.
Zarah kallonsa tayi ganin yadda yahad'e rai yaso yabata dariya, nan tafara yin dariya ciki-ciki, tanak'unshe dariyar karaf suka had'a ido da yarima.
Wata uwar harara yawurga mata sannan yasaketa yafita yabar toilet d'in.
Zarah dariyarta tacigaba dayi ahankali sai daga baya da tatuna a inda take yasa tatsagaita yin dariyar sannan tayi wankanta.
Bayan ta gama fitowa tayi tatarar yarima lokacin har ya kwanta, dan haka itama rigarta tamaida sannan taje bayansa takwanta.
_*BAYAN KWANA UKKU*_
Sultana bilkisu ce zaune parlourn dada bayan sun gaisa nan suka shiga yin hira suna cikin hirar ne dada tace ummin suhail ashe da rabon zanga jinin yarima.
Ummi cikin rashin fahimta tace dada ban ganeba.
dada har ta bud'e baki zatayi magana sai ga sultana sadiya ta shigo da sallamarta.
Gabad'ayansu suka amsa mata nan tazauna saman d'aya daga cikin cushin d'in, cike da girmamawa tagaishe da dada.
nan dada ta amsa mata tare da tambayarta gida.
Alhmdllh cewar sultana sadiya fuskarta d'auke da murmushi tace ina fatan kina cikin k'oshin lafiya?
Dada tace Alhmdllh saidai abinda ba'a rasaba kinsan yanayin tsufa.
Gabad'ayansu sukace Allah yak'ara lafiya.
dada tace Ameen.
Sultana bilkisu fuskarta d'auke da murmushi tace sultana anwuni lafiya?
Kallonta sultana sadiya tayi tare da yin d'an guntun murmushi sannan tace lafiya lou sultana dafatan kina lfy?
Alhmdllh, cewar ummi.
Sultana sadiya tace wai ni ina yarima ne naga kwana biyu bansashi idonaba ko baya garin?
Mamakine yakama sultana bilkisu ganin yadda tayi tambayar, bayan jiya-jiyannan yarima da yaje gaisheta yace mata daga turakar umman sumayya yake ya je sun gaisa.
Sultana bilkisu d'an murmushi tayi sannan tace yana nan man, ashe baya zuwa yagaisheki, gaskiya yarima halinsa sai shi ya kamata kuyi mashi fad'a yagyara.
Rik'e baki sultana sadiya tayi tace taya zanyi mai fad'a? Rufamin asiri wa zai iya da halin wannan miskilin yaron.
Dada murmushi tayi tace ina ruwan yarima, ni har mamakin halinsa nake wani lokacin ma cewa nake anya shi kad'ai ne?
Ta6e baki sultana sadiya tayi tace ranki yadad'e shi kad'aine kawai dai iskancine yayi masa yawa dan ko mahaifiyartasa kamar bata isa da shi ba.
Sultana bilkisu murmushi tayi tace haba sultana kema shedace tsaye nake kan suhail, kuma ina masa fad'a akan wannan hali nasa ammah ya k'i canzawa.
Ta6e baki sultana sadiya tayi tace duk dai lokacin da yafara aje 'ya'ya ai dole ya aje wannan iskancin nasa.
Dada murmushi tayi sannan cikin jin dad'i tace ai insha Allahu nan ba da dad'ewaba zamu sha suna.
Gabad'ayansu kallon Dada sukayi cike da mamaki sukace suna kuma?
Murmushi dada tayi tace ashe ku ma baku saniba, ai matarsa cikine da ita.
Murmushi sultana sadiya itama tayi sannan tace ranki yadad'e batada komai ai sumayya har yanzu Allah bai kawoba.
Dada kallonta tayi tace kekuma kinji ki da wata magana ai amaryarsa ce keda ciki.
Sultana sadiya jin maganar tayi kamar an jefota cikin kunnenta, nan gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa, cikin k'ani'anin lokaci fara'ar fuskarta tagushe,
akasin sultana bilkisu da taji abun kamar a mafarki farin ciki nan yadabaibaye zuciyanta cikin ranta Alhmdllh kawai take cewa, dan batada buri a duniya da yawuce taga jinin yarimanta.........
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Yau page d'in nakune my fan's mutanen saudiya, sak'onku yana zuwa a gareni nagode sosai da soyayyar da kuke nunamin saidai ince Allah yabarmu tare, jinjinar bangirma agareku Sis Aisha*_
*PAGE* 4⃣8⃣
Sultana sadiya dak'yar tasamu tad'an tsaida nutsuwarta sannan tad'an yi d'an murmushi mai kama da yak'e tace ranki yadad'e ya akayi kikasan cikine da ita kuma an tabbata shi d'inne?
Murmushi dada tayi sannan tace tabbas cikine da ita dan rannan k'arnin kifi kawai taji ammah saida tayi amai ke ko yanayinta zaki kallah sai kin gane hakan kuma ko jiya da yarima yazo gaisheni saida namatsa mai da tambaya sannan yafad'amin ashe cikin har ya kai tsawon wata hud'u, kinsan halin yarima ba komai yake fad'aba.
Sultana sadiya saida gabanta yayi wani irin fad'uwa, cikin zuciyanta tace wata hud'u??? batasan lokacin da tace hmm ai yarima ya iya munafunci.
Ganin yadda sultana bilkisu da dada suka zuba mata ido yasa tayi murmushi tace ya za'ayi ni a matsayina na mahaifiyarsa yak'i fad'amin, ai ya kamata tasamu kulawa sosai a wajenmu tunda mune matsayin dangi yanzu a wajenta saboda da mu take zaune.
Dada murmushi tayi tace tabbas maganarki gaskiya ce koda munso ace sumayya ce tafara haihuwa ammah bakomai tunda haka Allah yak'addara kuma dukkansu d'ayane tunda duk matansane,
Sultana sadiya cikin rashin nuna damuwa tace ai d'a nakowane da zarah da sumayya duk d'ayane a wajena.
Murmushi sultana bilkisu tayi tace nima haka ina sa rai nan ba da dad'ewaba my dota nima tahaifo mana baby.
Dariya sultana sadiya tayi sannan tace saidai daga baya dan mu nan ba da dad'ewaba zamu amshi jika.
Eh munji babu komai muma namu insha Allahu yana nan zuwa.
Dada ido tazuba musu cikin jin dad'i sannan tace Allah yakawo masu albarka.
Gabad'ayansu suka amsa da Ameen.
Mik'ewa sultana sadiya tayi tana murmushi tace ranki yadad'e zan wuce akwai bak'uwa da zanyi yanzu hakama ina sa ran ta iso, insha Allahu zan je induba jikin my daughter.
Cikin jin dad'i dada tace toh bakomai.
Sultana bilkisu tace sai anjima sultana.
'Dan rissinawa sultana sadiya tayi sannan tace na barku lafiya, tana fad'in haka tajuya tafita.
Nan sultana bilkisu da dada suka cigaba da hirarsu, saida maraice yayi sannan sultana bilkisu tayi ma dada sallama takoma part d'insu cike da farin ciki akan cikin zarah.
A 6angaren sultana sadiya ko da tafita bak'in cikine yatokare mata mak'ogwaro, takaici duk yacikata ita kanta ta yi mamakin yadda akayi ta iya danne bak'in cikinta a gaban su dada.
Ko da ta isa part d'inta a parlour tayada zango nan tashiga kaiwa da kawowa ahankali take furta na shiga ukku ya akayi wata daga zuwanta tariga d'iyata samun ciki, kai da sake dole ne inbi ta kowace hanya wajen ganin na zubar da shi, taya wata d'iyar talakka zata fara aje jika a masarautar nan? Ba dai hakan yana nufin plan d'in da nashirya ya rugujeba? Inaaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba wlh, Tsanar zarah sa yarima ne taji ya k'aru a cikin zuciyanta.
Cike da 6acin rai tajanyo wayarta takira sumayya, sumayya na yin picking sultana sadiya cikin d'aga murya tace ke kina ina?
Daga chan 6angaren gimbiya sumayya tace ummah lafiya naji ki haka? Ina gida.
dan ubanki kizo yanzu kisameni ina jiranki.
Sumayya cike da mamakin mahaifiyartata tace toh ummah,
Sultana sadiya bata k'ara magana ba ta kashe wayar tare da wulli da ita saman cushin.
Daga chan 6angaren sumayya da mamaki tabi wayar da kallo ahankali ta furta lafiya? Kiran me ummah take min haka cikin gaugawa? Ba abinda yafi d'aure mata kai sai jin yadda ummah tayi mata magana cikin tsawa.
Ahankali tafurta Allah dai yasa lafiya, tana fad'in haka tamik'e tasaka alkyabbarta sannan tafito tanufi part d'in mahaifiyartata.
Ko da ta isa a tsaye tatarar da sultana sadiya tana zagaye d'akin tana cize le6e, cike da rud'ewa sumayya ta isa wajenta tace ummana lafiya me yake faruwa?
Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace sumayya komai ma ya faru.
Cike da mamaki sumayya tace ummana ban fahimcekiba.
Taya zaki fahimceni sumayya bayan kinyi wasa da damarki? Toh gashinan abinda nake guje miki ya faru..."sultana sadiya tafad'i hakan cikin d'aga murya"
Sumayya tsaye tayi tana kallon ummanta cikin rashin fahimtar inda tadosa.
Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kishiyarki tana d'auke da cikin yarima na tsawon wata hud'u.
Wani irin fad'uwan gaba yaziyarci sumayya tsaye tayi cak tana jin abun kamar a mafarki, chan sai ta k'yalk'yale da dariya tace ummah ciki kuma tsawon wata hud'u? Kina nufin zata haihu da yarimana? Chan kuma sai ta fasa k'ara tare da furta wlh k'aryane hakan ba zai ta6a faruwaba.
Kallon ummah tayi tafashe da kuka tace ummana wlh ban yardaba babu yadda za'ayi inbar wacchan matsiyaciyar tahaihu da yarimana ummah wlh sai na kasheta saidai nima a kasheni.
Sultana sadiya jin d'iyartata tana surutai cikin d'aga murya gudun kar ajisu yasa tajanyo sumayya suka shige bedroom d'inta.
Suna shiga sumayya tafad'a jikinta tare da fashewa da kuka tace na shiga ukku ummana ya zanyi da rayuwata ummah na tsani yarinyar chan, ba zan ta6a yadda cin mutuncin da yarima yayi minba ace 'yar talakkawa yayi ma ciki wlh ya munafunceni Allah ummah Sai na kasheta saidai shima yakasheni.
Sultana sadiya rungume d'iyartata tayi cike da tausayinta tace kidaina cewa haka sumayya kinga abinda daman nake guje miki yanzu gashinan kinyi wasa da damarki.
Sumayya cikin kuka tace ummana wlh ba zan ta6a yarda a zalunceniba inma haihuwarce ai ni yafi dacewa inyita.
Sultana sadiya rik'ota tayi sukaje bakin gado suka zauna cike da tausayi tace sumayya kiyi shuru hakanan muyi magana.
Sumayya share hawayen fuskarta tayi nan tazuba ma umman ido.
Sultana sadiya tace yauwa ko kefa, yanzu dai da farko inaso kikwantar da hankalinki kinutsu kar kice zaki kawo tashin hankali a gidan aurenki dan kinsan wannan mijinnaki ba zai d'auki hakan ba, sannan indai kinsan kina planning toh kidaina kisamu kema cikin nan kiyi sa, inyaso ita zarah kibarni da ita nasan yadda zan 6ollo ma lamarin.
Sumayya tace ummah toh cikin nata fa?
Tsiyata da ke Sumayya wani lokacin baki ganewa, tunda dai nace kibarni da ita ai nasan abinda zanyi, na dai fad'a miki kar kikuskura kice zakiyi mata wani abu da kanki.
Sumayya tace toh ummah.
Yauwa kokefa.
Murmushi kawai Sumayya tayi batare da tace komai ba.
A 6angaren sultana bilkisu kuwa koda takoma 6angaren su a bedroom d'in sultan Ahmad tayada zango lokacin yana zaune yana duba wata newspaper,
Bud'e k'ofan da tayi tashigo yasa yad'aga kai yakalleta ganin yadda taketa fara'a yasa ya aje newspaper d'in tare da yin murmushi yace da alamu yau matartawa tana cikin farin ciki.
Sultana bilkisu Ida k'arasowa tayi wajensa tazauna fuskarta d'auke da fara'a tace tabbas ranka yadad'e ka yi gaskiya domin yau ina cikin wani irin farin ciki.
Rik'o hannunta yayi yace toh nima afad'amin farin cikin da ake nima intaya.
Sultana bilkisu murmushi tasakar masa sannan tace ranka yadad'e mun kusan samun jika.
Jika fa kikace?
Eh ranka yadad'e, tabbas auren zarah da yarima akwai alkhairi a cikinsa, my son ya kusan zama daddy.
Sultan Abbas kasa 6oye farin cikinsa yayi yace Alhmdllh Allah abun godia, gaskiya naji dad'i kuma nayi farin ciki dan arayuwata inason ganin jinin yarima,
Dariyar jin dad'i sultana bilkisu tayi tace was yaga yarima da d'a.
Shima sultan Dariyar yayi yace Allah dai yasafke lfy, Allah yakawo masu albarka.
Ummi cikin jin dad'i tace Ameen farin cikina.
Gabad'ayansu suka sakarma juna murmushi, jin kiran sallar magrib ne da aka fara yasa suka mik'e, sultan Ahmad yayi alwallah yawuce masallaci.
Sumayya ko da takoma 6angarensu bedroom d'inta tashige tafad'a saman gado nan wani sabon kukan yakubce mata yi take babu k'ak'autawa tausayin kanta yakamata, saida tayi mai isarta sannan tajanyo waya takira zinat.
Zinat nayin picking babu ko sallama sumayya tace baby na shiga ukku.
Daga chan 6angaren zinat tace haba baby akan wane dalili zakice kin shiga ukku, me yake faruwa ne?
Sumayya fashewa tayi da kuka tace zinat dole ince haka domin ina cikin matsala bansan ya zanyi da rayuwataba.
Baby kinutsu kimin bayanin abinda yake faruwa kidaina kuka.
Sumayya tsagaitawa tayi da kukan da take tace zinat wannan bagidajiyar yarinyar daga zuwanta wai har ta samu ciki, wlh ba zan ta6a yarda ba.
Zinat cikin d'aga murya tace kina nufin wannan kishiyar taki?
Toh in ba itaba wa kike tunani ni wlh kasheta zanyi kowa yahuta inyaso nima daga baya akasheni.
Zinat ajiyar zuciya tayi tace kar kice haka baby kiyi hak'uri kijira zan shigo,
Har sai yaushe zaki shigo kina nufin inbari har sai ta haihu? Cewar sumayya
A'a baby ai very soon zan shigo, kijirani zuwa next month zan shigo wlh sai munyi silar zubar da cikin.
Sumayya tace toh zan gwada inga idan zan iya hak'uri har sai kin shigo.
Zaki ma iya baby, yanzu dai nidai burina kikwantar da hankalinki kar kije ki aikata abinda zai je yadawo.
Hmm baby kenan kidaina maganar kwanciyar hankali dan ayanzu hankali ya gama kwanciya kawai dai sai anjima yanzu zan d'an huta.
tana fad'in haka bata jira jin komai daga wajen zinat ba takashe wayarta.
Mik'ewa tayi taje tawatsa ruwa tayi shirin bacci tahaye gadonta dan yau cewa tayi babu abinda zai kaita wajen yarima saidai yayi baccinsa shi kad'ai dan shi kansa haushinsa takeji,
duk yadda taso tayi baccin kasawa tayi kalmar cikin zarah yatsaya mata a rai duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi daga k'arshe saida tasha maganin bacci sannan tasamu bacci yayi awon gaba da ita.
_*Washe gari*_
Wajen 12 zarah zaune take saman cushin hannunta rik'e da waya tana chart sallamar da taji anyine yasa ta amsa tare da d'ago kai takalli mai sallamar, da mamaki take kallon sultana sadiya da take sakar mata murmushi, cikin sauri zarah tamik'e tsaye fuskarta itama d'auke da murmushi tace sannu da zuwa ummah.
Yauwa d'iyata, a'ah kice jiki ya warware, cewar sultana sadiya.
Zarah cikin Jin kunya tace bismillah ummah kizauna.
Zama sultana sadiya tayi har a lokacin fuskarta tana kan zarah, cike da jin kunya zarah tazauna k'asa tace ummah ina wuni?
Lafiya lou dafatan kina Lafiya, ya k'arfin jikin naki.
Cikin jin kunya zarah tace ummah ai na warke,
toh masha Allah, Allah yak'ara sauk'i, ai ba a fad'amin bakida lafiya ba sai jiya naji wajen dada.
Zarah shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta tana murmushi, ahankali tamik'e tace ummah bari inkawo miki ruwa.
Murmushi sultana sadiya tayi tace kibarsa kawai saikace wata bak'uwa.
Wucewa zarah tayi tace ummah bari dai inkawo miki, sultana sadiya binta tayi da wani irin kallo har tashige kitchen, ahankali tafurta tabbas yarinyar nan cikine da ita.
Zarah ko da tashiga kitchen dafe k'irjinta tayi tare da safke ajiyar zuciya dan ta tsorata sosai da fari da taga ta shigo sai daga baya da taga ba da wata manufar tazoba sannan taji dad'i, ahankali tafurta Allah yasa umman sumayya ta shiryu.
Nan tacigaba da had'a mata kayan marmari da drinks kala-kala a saman tray ta d'aura tad'auko tafito.
A gaban sultana sadiya ta aje tace ummah kifara da wannan kafin ingirka miki abinci.
Murmushi sultana sadiya tayi tace a'a zarah keda bakida lafiya kibarsa kawai dan ni nan a k'oshe nake,
Zarah ruwan inibi tatsiyaya a cup tamik'a mata tace ummah toh ko yayane kisa albarka.
Kar6a sultana sadiya tayi tana murmushi tace nagode zarah, kur6a d'aya tayi ta aje sannan tace zarah kiyi hak'uri akan abinda nayi miki wlh sai daga baya nagane hakan ba daidai bane,
Murmushi zarah tayi tare da d'ago kai takalleta tace ummah bakimin komai ba wlh dan ke matsayin uwa kike a wajena.
Nagode sosai zarah, Allah yaimiki Albarka, Allah yasafkeki lafiya.
Zarah kasa amsa mata tayi saboda wata irin kunya da tarufeta.
Mik'ewa sultana sadiya tayi tace toh ni zan wuce.
Ummah tun yanzu?
Haba zarah me zan zauna inyi ni da nake matsayin suruka, yanzu dai indai kinsan kina buk'atar wani abu kidinga aikawa ana fad'amin insha Allahu ni kuma zan samo miki koma menene, yanzu haka ga zogale chan nasa ana dafawa na baro sun kusan gamawa, Indai angama zan aiko miki da ita nasan zakiso cinta..
Murmushi zarah tayi cikin jin dad'i tace toh ummah nagode.
Haba minene abun godia ai keda sumayya duk d'aya nad'aukeku, zansa a ma k'wad'a miki da k'uli-kul'i dan akwai wata baiwata data iya irin wad'annan k'wad'on masu dad'i ita zansa tayi miki.
Zarah duk'ar dakanta tayi tace nagode sosai ummah, Allah yak'ara girma da d'aukaka.
Sultana sadiya tace Ameen sai na aikon, tana fad'in haka tawuce nan zarah tarakata har wajen part d'inta tare da k'ara yi mata godia.
Sultana sadiya tace bakomai, nan tawuce cike da farin ciki dan ta san tarkonta ya kama kurciya...
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Masha Allah my dota *hafnan* Ina tayaki murnar kammala novel d'inki maisuna *FATALWAR MIJINA* hak'ik'a kin zuba basira sannan kin koyar da darasi a cikinsa gaskiya salon novel d'in ya burgeni, Allah yabaki ladar abinda kika fad'a daidai kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, ur mommo love you more😘_
_~Masoya sak'onku yana isowa agareni ina godia sosai Allah yabar k'auna, mutanen katsina ku ma sak'onku ya iso agareni nagode sosai nima ina gaisheku~_
*PAGE* 4⃣9⃣
Haka sultana sadiya ta isa 6angarensu farin ciki fal a zuciyanta, cikin sa'a ko da ta isa tatarar angama dafa zogalen, nan tasa wata baiwarta tak'wad'a mata, sannan tawuce cikin bedroom d'inta inda tad'auko k'ullin maganin da tasa aka samo mata.
Bayan an gama kwad'on a parlour aka kawo mata cike da jin dad'i tabud'e taduba saida tad'ibi nata sannan tazuba ma sauran maganin tamotse yadda ba za'a ganeba sannan tajuye a cikin wata kula mai kyau, murmushin mugunta tayi tace zarah kinyi babban kuskure da kikayi saurin yarda da ni dan bakisan wacece ni ba,
Sallamar da akayine daga wajen d'akin yasa ta amsa saida tagama abinda take sannan tabada izinin ashigo, jakadiya ce tashigo cikin sauri taduk'a tagaishe da sultana sadiya cike da girmamawa.
Sultana sadiya kallonta tayi a wulak'ance saida tayamutsa fuska sannan ta amsa.
Jakadiya k'ara duk'ar da kanta tayi k'asa tace ranki yadad'e daman dada ce ta aikoni wajenki.
Shuru sultana sadiya tayi na d'an lokaci sannan tace ina saurarenki.
Jakadiya ledar da take hannunta ta mik'a mata tace gashi tace akawo miki.
Kar6a sultana tayi tabud'e batasan lokacin da Murmushi yakubce mataba ganin wata had'ad'ar sark'a da dada ta aiko mata da shi, cikin sakin fuska sultana sadiya tace kice mata nagode.
K'ara duk'awa jakadiya tayi tace Allah yaja da ranki nabarki lafiya,
Gyad'a mata kai kawai sultana sadiya tayi,
Har jakadiya ta wuce zata fita sultana sadiya takirata.
Cikin sauri jakadiya tadawo taduk'a tace ranki yadad'e na amsa kiranki.
Sultana mik'a mata kular tayi tace gashi kikai ma gimbiya zarah.
Cikin sauri jakadiya takar6a cike da mamaki tace ranki yadad'e gimbiya zarah ko gimbiya sumayya?
Harara sultana tawurga mata cikin fad'a tace zarah nace miki ko sumayya?
Jikin jakadiya yana rawa tace kigafarce ranki yadad'e gimbiya zarah zan kaimawa Allah yahuci zuciyanki.
K'ofa sultana sadiya tanuna mata, cikin sauri jakadiya tad'auki kulan tafito.
A chan 6angaren zarah bayan sultana sadiya ta tafi komawa tayi saman cushin tazauna tare da dafe kanta mamakin sultana sadiya duk ya kamata dan yau ne karo nafarko da tafara ganin fara'arta, tunowa tayi da duk wulak'ancin da take yi mata a baya, murmushi zarah tayi wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa.
Jakadiya tafiya take ammah mamakine yacikata ahankali take furta miye had'in sultana sadiya da gimbiya zarah? Miyasa batace inkai ma gimbiya sumayya ba sai zarah? Anya ba wata k'ullalliya da matarnan take shiryawa?
Bari dai inje sai inji daga bakin gimbiya.
Lokacin da ta isa a parlour tasamu zarah zaune tana shan fruit salad, cike da girmamawa taduk'a tagaishe da zarah, cikin sakin fuska zarah ma tagaisheta tare da tambayarta su dada.
Murmushi Jakadiya tayi tace suna lafiya sannan tamik'a mata kular tace ranki yadad'e gashi daga sultana sadiya tace inkawo miki.
Murmushi zarah tayi batare da ta kar6a ba tace bud'e mugani.
Cikin sauri Jakadiya tabud'e, zarah lek'awa tayi tace ba laifi kwad'on ya min kyau saidai ba zan iya ciba.
Murmushi Jakadiya tayi tace ranki yadad'e wai miye tsakaninku dan nayi mamakin ganin ta bada kwad'o akawo miki.
Itama zarah murmushi tayi sannan takwashe komai tafad'a ma Jakadiya.
Jinjina kai Jakadiya tayi tace duk tak'are cikinki ne da taji ance kina da shi takeso taga bayansa.
Ta6e baki zarah tayi tace koma mekenen ta Allah ba tataba dan ni nafi k'arfinsu, ban yarda da kwad'on ba aje kawai azubar da shi a 6oye inda wani ba zai ganiba bare yaci.
Jakadiya tace angama ranki yadad'e, Allah yatsare mana ke.
Zarah jingine kanta tayi da kujera nan jakadiya tamik'e tafita tabar d'akin.
Bayan fitarta Zarah mik'ewa tayi tashiga bedroom d'inta, saman gadonta takwanta tana mamakin halin sumayya da mahaifiyarta, ji take da ace sumayya zata amince suyi zaman lafiya da zatayi farin ciki da hakan dan ita da zuciya d'aya take zaune da ita.
Tunowa tayi da gogon nata nan tayi murmushi dan ita kanta ta san tayi missing d'insa rabonta da shi kusan 3 day's kenan, wayanta tad'auko talalubo number d'insa, lokacin yarima yana cikin duba patients d'insa ganin me kiransa yasa yamaida wayan silent yacigaba da aikinsa dan lokacin gab yake da yatashi yakoma gida.
Zarah ganin ta tsinke baiyi picking ba yasa ta aje wayar tare da maida idanuwanta tarufe dan tasamu tad'anyi bacci, ammah gefe guda ji take tana buk'atar son cin zogale da balango dan tunda taga wadda sultana sadiya ta aiko mata taji tana kwad'anta.
Mik'ewa tayi tafito parlour dan tasa asamo mata, daidai lokacin sumayya tashigo d'akin babu ko sallama.
Zarah tsaye tayi tana kallonta cike da mamaki dan sumayya had'e rai tayi sosai ba alamun fara'a a tare da ita daga gani kasan ba mutunci yakawotaba.
Ta6e baki zarah tayi tace haba baiwar Allah ya za'ayi kishigo min d'aki babu ko sallama saikace kin shigo d'akin arna.
Wata uwar harara sumayya tawurga mata cike da 6acin rai tace tunda gidan ubankine ai dole inyi sallama, ke ni nan bai min kama da d'akiba sai dai kongo dan haka ank'i ayi sallamar banza matsiyaciya, kuma cikin da kike tak'ama da shi indai ina numfashi bazaki ta6a haifesaba ke gidannan ma dole kibarsa dan yarima ba ajin aurenki bane, ni banga abinda yagani a jikinkiba har ya amince ya aureki, banza 'yar matsiyata.
Murmushi zarah tayi cikin rashin damuwa tace sumayya ni yanzu banada lokacinki abinda yake kaina ya isheni, kuma ciki da kike magana Allah ne yabani baki isa kiyi min abinda Allah baiyi min ba.
Cikin k'araji sumayya tace kar kikuskura kiyi min gori dan wlh zansa kiyi nadamar da bakita6a yiba a rayuwarki, kinci sa'a ina rangwanta miki ammah wlh da tuni kinbar gidannan kuma cikine kirufa ki aje sai nayi silar zubar da shi.
Zarah shafa cikinta tayi tace malama kinfa dameni da haukanki, kifita kiban waje ko yanzu insa afitar min da ke.
Ta6e baki sumayya tayi tace duk yadda kikayi daidaine ammah inaso kisani ni sumayya na tsaneki, tsanarki bazata ta6a fita daga zuciyana har sai ranar da naga na cika burina, tana fad'in haka tajuya tafita daga d'akin a harzuk'e.
Zarah tsaye tayi tabita da kallo har ta fita, ahankali tafurta Allah yashiryeki sumayya.
Ringing d'in wayanta da tajiyo yasa cikin sauri takoma bedroom d'in tad'auko, ganin mai kiranta yasa tasaki murmushi tare da zama gefen gado saida tasaita nutsuwarta sannan tayi picking.
Gabad'ayansu shuru sukayi sai chan Zarah tayi sallama,
Daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi.
Zarah murmushi tayi tace barka da hutawa, ya aiki?
Yarima saida yalumshe idonsa sannan ahankali yace Alhmdllh, y kk?
Cikin shagwa6a tace ina lafiya, saidai babynka da yake wahalar da ni.
Uhm sry, kawai yarima yace,
Zarah kamar zatayi kuka tace ni balango nakeson ci please katafo min da shi.
Yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace yanzu duk nan gidan ace kin rasa naman da zakici, kuma baki iya sawa ayi miki?
Zarah kukan shagwa6a tasanya sai tace ni wlh nasiye nakeson ci na nan banason k'amshinsa.
Yarima jin kukan nata yake har cikin ransa dan duk ta kashe masa jiki, ahankali kamar mai jin bacci yace toh shikenan zan tafo miki da shi, kukan ya isa.
Zarah tsagaitawa tayi daga kukan da take tace toh nagode please kahad'o min da shawarma, sai kadawo.
Yarima tsinke wayar yayi tare da dafe kansa yana tunanin ta yadda zai fara tsayawa wajen me nama siyan nama, tsaki yaja nan yajanyo wayarsa yakira d'aya daga cikin yaransa yace yaje yasiyo mai balango mai dad'i da shawarma.
Yana gama wayan yamik'e yad'auki key d'in motansa yafito yanufi gida.
Zarah bayan sungama wayar dariya tayi sannan tatashi tashiga wanka.
Bayan ta fito simple makeup tayi nan tashirya cikin gown d'inta maikyau. Saida tayi sallah sannan tajanyo wayarta takira su mama dan sugaisa, hira sukayi sosai nan mama take shaida mata jibi za'ayi baikon Aysha da malam bello, Zarah murna tayi sosai dan har cikin ranta taji dad'in hakan dan tasan malam bello zai kular mata da k'anwarta, nan tace insha Allahu zata shigo ranar, bayan sun gama waya da mama takira Aysha sukasha waya tana tsokanarta daga nan kuma tasa taba yaya rauda wayar nan ma sukaita hirarsu sun dad'e suna hira sannan sukayi sallama.
Mik'ewa Zarah tayi tad'auko veil d'in gown d'in, a gaban dreesing mirrow tatsaya tatufke kanta tayi kamar gambo sannan tayi rolling d'in k'aramin veil d'in nata nan tayi gwanin kyau, tafito tanufi part d'in yarima dan tasan indai ba ita tajeba toh mawuyacine yakawo mata dakansa.
A parlour tasamesa zaune yana waya, gefensa sumayya ce sai wannan cika take tana batsewa, ganin zarah yasa tawurga mata harara tace malama lafiya zaki shigo ma mutane?
Murmushi zarah tayi tace malama ba fa wajenki nazoba.
Yarima da yake waya juyowa yayi yazuba mata ido, itama Zarah kallonsa tayi tasakar mai murmushi, muryar sumayya taji ta ce kedai wlh ban san wace irin natatta bace ke kullum kina manne da mutum, ta6e baki zarah tayi tace kanki akeji.
Yarima kashe wayar yayi batare da ya kallesuba yace kudai bakuda aiki sai fad'a.
Sumayya kwantar da kanta tayi a kafad'ansa tace dear itace tawani shigo ma mutane dan neman fad'a...tak'arashe maganar tare da wurga ma zarah harara.
Zarah murmushin mugunta tayi mata sannan ta ida isa gefen Yarima tazauna 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace baby nifa zuwa kawai nayi inkar6i abinda nace kasiyo min wlh yunwa nakeji babynku yana wahalar da ni yau, janyo hannunsa tayi tad'aura saman cikinta tace baby kaji motsi yakemin....tak'arashe maganar tare da kashe mai ido d'aya.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta tare da safke ajiyar zuciya ahankali yace bari inkirasa.
Sumayya cikin 6acin rai tace babbar bura'uba ke wa zakiyi nuna ma duniyanci? Wlh baki isaba kanki farau cikine?
Zarah murmushi tayi tace sorry Auntyna wlh ba kaina farauba kawai dai ina buk'atar ci ne,
Yarima mik'ewa yayi tare da yin dialing d'in number d'in yaron nasa yana shirin kira, knocking d'in k'ofa da akayine yasa yabada izini ashigo.
'Daya daga cikin guards d'insane yashigo d'auke da leda d'an rissinawa yayi yace ranka yadad'e sak'one aka kawo maka.
Kar6a Yarima yayi batare da yayi magana ba, nan guard d'in yajuya yafita.
Yarima juyowa yayi ya kallesu duk sunci face, yanayin yadda sukayi ya so yabashi dariya, tsaye yayi da ledar sai chan yabud'e yaduba ganin kashi biyu ne yasa yad'auki kashi d'aya yamik'a ma sumayya yace ga naki.
Yamitsa fuska sumayya tayi tace duk naman da yake gidannan sai ansiyo na waje, ni gaskiya bazan iya ciba.
Ta d'auka yarima zai lallasheta kawai sai gani tayi ya mik'a ma zarah duka ledar yace gashinan.
Kar6a zarah tayi tare da yin murmushi tace nagode sosai baby, nan tamik'e tare da kallon sumayya da tacika tayi fam tace Aunty sumy kiyi hak'uri idan na 6ata miki sai anjima, tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.
Yarima komawa yayi yazauna tare da d'auko remote yana canza channel, sumayya kallonsa tayi tace yarima kana ganin abinda yarinyarnan take min ammah baka iya yi mata magana.
Wani irin kallo yawurga mata kamar ba zaiyi maganaba sai kuma chan yace sumayya akan me zanyi magana bayan a da tana baki girmanki kece dai kikak'i kirik'e girman naki kinga kenan laifin nakine dan haka in zaki gyara toh kigyara.
Sumayya haushine yakamata gani take kamar ya goyi bayan zarah, yamutsa fuska tayi tace ya dai kamata kadinga adalci a tsakaninmu dan mu dukanmu matankane kuma ita d'in da kake ma rawan kai ai.......wata irin harara da yawurga matane yasa tayi shuru batare da ta k'arashe maganartaba,
Cigaba yayi da kallonsa inda Sumayya tamik'e cike da jin haushi taficce tabar d'akin.
Cikin rashin damuwa yarima yayi kwanciyarsa saman kujerar, dan shi yanzu halayyar Sumayya har ta daina bashi mamaki.
A chan 6angaren sultana sadiya koda jakadiya tadawo mata da kular tambayarta tayi zarah ta ci kwad'on? Jakadiya saida taduk'ar da kanta k'asa cike da girmamawa sannan tace eh ranki yadad'e dan dukansa tacinye ta ce tana godia sosai.
Murmushin jin dad'i sultana tayi sannan tace kai haba toh menene abun godia a ciki? Ai taimakon kai ne, yanzu zaki iya tafiya.
K'ara duk'awa jakadiya tayi tace toh ranki yadad'e atashi lafiya, tana fad'in haka ta tashi cikin sauri tabar d'akin.
Bayan ta fita sultana k'yalk'yalewa tayi da wata irin dariya tace yarinya bakisan wacece ni ba wayace miki koda da second d'aya zan iya sonki? Kallon agogon da take manne ga bangon d'akin tayi sannan tace nan da minti talatin cikinki zai tashi aiki, tana fad'in haka tayi murmushin mugunta sannan tajanyo wayarta takira sumayya nan tafad'a mata komai.
Sumayya murna tayi sosai har da 'yar taka rawarta nan tanemi 6acin ranta tarasa.
Yau ko da taje d'akin yarima da dare shi kansa saida yayi mamakin ganinta cikin farin ciki bai dai tambayetaba yashareta yai kwanciyarsa haka tazo bayansa takwanta yanajinta tarungumesa nan yamaida idanuwansa yalumshe ahaka bacci yai awon gaba da su.
Da safe sumayya sa wata kuyangarta tayi takular mata da duk wani motsin zarah dan ta yi tunanin za'a fito da ita aje asibiti ammah da mamakinta har wajen 10am ammah shuru dan haka tashirya da kanta tanufi part d'in zarah dan tagane ma idonta abinda yake faruwa, cikin ranta tace ina ma insameta kwance tana fama da ciwo, murmushine yakubce mata tace Allah yasa haka, daidai lokacin tad'aga labulen d'akin zarah tashiga, curus taja bakin k'ofa tatsaya ganin zarah da tayi zaune saman lallausan carpet d'in da yake shimfid'e a tsakiyan parlourn hannunta rik'e da waya tana dannawa da ka ganta kasan tana cikin k'oshin lafiya.
'Dago kai zarah tayi takalleta tare da sakar mata murmushi sannan tace sannu da zuwa Aunty sumy, kishigo man.
Ta6e baki sumayya tayi cike da mamaki tace bashi yakawoni ba.
Zarah ma kallonta takeyi tace toh me yakawoki?
Cikin nuna isa sumayya tace wannan ba matsalarki bace malama saidai inaso ink'ara tunatar miki akan mijina babu abinda ban iyayi, dan haka a kowane lokaci kisaurareni, tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.
Zarah binta tayi da kallo har tafita sannan tayi murmushi tace Allah yashiryaki sumayya, A kullum ba zan ta6a yin k'asa da gwiwaba wajen addu'a Allah yakareni daga dukkan sharrinku.
Sumayya tana fita bata zarce ko'inaba sai part d'inta a parlour tayada zango tashiga zagaye d'akin cike da tashin hankali nan takira wayan ummanta.
Ummah tana d'aga wayan sumayya tace ummah na shiga ukku wlh waccan matsiyaciyar tana nan lafiya lau babu abinda yasameta anya kuwa ummah kin zuba mata?
A firgice sultana sadiya tace sumayya me kikace? Tana nan lafiya lau fa kikace kai ba zan ta6a yaddaba.
Gimbiya sumayya kamar tafashe da kuka tace wlh ummah tana nan babu abinda yasameta ummah gaskiya cutarki akayi ba maganin zubar da ciki bane aka baki.
Cike da jin haushi ummah tace ke gidanku sumayya da me zanji da rashin zubewar cikin ko da banzar maganarki marar amfani, ni babu wanda yacuceni wannan maganin na sanshi kuma nasan nazubar da cikine dan da anyi amfani da shi ba'ayin rabin awa sai ciki ya fita , toh inhakane ya akayi cikin nata bai zubeba?
Shuru ummah tayi tana nazari sai chan tace kenan hakan yana nufin zarah bataci k'wad'onba? Tabbas bataciba.
Sumayya cike da mamaki tace ummah kina nufin bata ciba? Toh ko tasan k'ullalliyar da kikayi matane?
Ummah girgiza kai tayi kamar tana a gaban sumayya, tace batasan komai ba akan haka saidai idan wani dalili yahanata ci.
Toh fa ummah yanzu ya za'ayi wlh banason cikinnan nata kokad'an...sumayya tak'arashe maganarta cikin kuka.
Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace kidaina kuka sumayya kikwantar da hankalinki yau zansa ashirya mata wani kwad'on ni zanje da kaina inkai mata taci.
Sumayya fashewa tayi da dariya kamar ba ita bace take kuka cike da jin dad'i tace ummah hakan kawai za'ayi gaskiya da kin gama min komai dan ni yanzu wlh cikinta ya fi aurenta da yarima d'agamin hankali.
Hmm duka dai da matsala sumayya ammah dasannu zamu magance komai.
Sumayya cikin jin dad'i tace Allah yabar min ke ummana.
Dariya sultana sadiya tayi tace Ameen shalelena yanzu dai bari inje inyi abinda yadace.
Toh ummana sai najiki, nan sukayi sallama kowa yakashe wayarsa.
Sultana sadiya k'wala ma d'aya daga cikin kuyanginta kira tayi, cikin sauri tashigo jikinta yana rawa taduk'a cikin girmamawa tace ranki yadad'e na amsa kiranki.
Yamitsa fuska sultana sadiya tayi sannan tace kije kisami baiwata sabura kice nace yanzu tahad'amin kwad'on zogale yaji kayan had'i sai takawo min nan ina jiranta.
Kuyangar tace toh ranki yadad'e angama, cikin sauri tamik'e tafita tabar d'akin.
Sultana sadiya maida kanta tayi ta jingine ga kujerar da take tana murmushin mugunta.
0 comments:
Post a Comment