Sultana sadiya tana nan zaune tana sak'e-sak'e a ranta a k'allah ta ci kusan minti goma sha biyar a haka, zuwan da baiwarta tayine yasa tabata izini tashigo.
Baiwar shigowa tayi d'auke da wata kula a hannunta cikin sauri tazube k'asa tana kwasar gaisuwa wajen sultana sadiya.
Sultana yatsine fuska tayi sannan ta amsa ciki-ciki, baiwar k'ara duk'ar da kanta tayi sannan tace ranki yadad'e na cika umurninki.
Sultana kallon kular tayi sannan tace bud'e mugani,
Cikin sauri tabud'e mata, tana addu'a cikin ranta Allah yasa kar sultana tace baiyiba dan tana tsoron wulak'ancinta.
Ta6e baki sultana tayi tace tashi kitafi.
Cike da jin dad'i baiwar tace toh ranki yadad'e nabarki lafiya, tana fad'in haka tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.
Mik'ewa sultana sadiya tayi taje tad'auko maganin tazuba tamotse sannan tayi murmushi tace yau dai dole kicisa zarah, k'ulle maganin tayi tamaida ma'ajinsa sannan tadawo tasaka alkyabbarta tasa wata kuyangarta tad'aukar mata kular suka fito suka nufi 6angaren su zarah.
Zarah lokacin kwance take saman 3 seater tana ta juyi saboda wata irin yunwa da takeji gashi ta kasa cin komai, wayarta tad'auko takira yarima har tatsinke baiyi picking ba.
Haushine yakamata ta aje awar tana ta jan tsaki kad'an kad'an, bayan minti biyu sai ga kiransa ya shigo.
Zuba ma wayar ido tayi har tatsinke batare da tayi picking ba.
Daga chan 6angaren yarima da yafito wanka mamakine yakamasa ganin batayi picking ba kuma tsakanin kiran da tayi mai zuwa lokacin baifi 2 minutes ba, har zai k'ara kiranta a karo nabiyu sai chan 6angare d'aya na zuciyansa yace ba ajinka bane kak'ara kiranta, tsaki yaja ya aje wayan yacigaba da shirinsa ammah kuma duk da haka a cikin ransa yana jin ba dad'i dannewa kawai yakeyi dan shi abun har mamaki yake bashi ganin yadda yake ma zarah ko sumayya bata samun haka.
Lokacin da sultana sadiya ta iso part d'in zarah har a lokacin zarah tana kwance, ganin sultana sadiya yasa gabatanta yayi wani irin mummunan fad'uwa cikin ranta tsarin ubangiji take nema, koda sultana sadiya yau ma kamar jiya fuskarta a sake take.
Zarah cikin sauri tamik'e tsaye, murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace ummah sannu da zuwa.
Sultana sadiya ma maida mata martanin murmushin tayi saida tazauna sannan tace yauwa zarah.
A k'asa zarah tazauna cikin girmamawa tagaisheta.
Amsa mata sultana sadiya tayi tace ya k'arfin jikin naki?
Zarah duk'ar da kanta tayi tace Alhmdllh ummah.
Kuyangar da sukazo tare da sultana sadiya duk'awa tayi tagaishe da zarah.
Cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan sultana ta amshi kular tace tafita tajirata a waje, ahankali tace anganma ranki yadad'e sannan tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.
Sultana sadiya kallonta tamaida ga zarah da take wasa da yatsun hannunta tace yau ma dai ga kwad'on na kawo miki dan nasan masu ciki akwaisu da kwad'ayi bare ma irin wad'annan kwad'on ganyukan...tak'arashe maganar tana 'yar dariya.
Murmushi zarah tayi tace toh ummah nagode sosai.
Sultana sadiya tace haba zarah ai bakomai ke da sumayya duk d'aya nad'aukeku.
Zarah ahankali tace hakane ummah Allah yasaka da alkhairi.
Ameen, kibud'e kigani man,,,cewar sultana sadiya.
Zarah bata musaba tajanyo kular tabud'e saida tahad'iyi yawu saboda kwad'on ya burgeta kamar taitaci dan ganinsa yasa yunwar da takeji ta tashi, maidawa tayi tarufe takalli sultana sadiya da tatsareta da ido tace ummah ya yi min sosai kuma nagode Allah yasaka da alkhairi.
Murmushi sultana sadiya tayi tace kar kidamu zarah, kici kawai naga kamar yunwa kikeji.
Gaban zarah saida yafad'i jin sultana ta ce taci cikin ranta tace Allah yaimin tsari da abinda kuke shiryawa akaina, itama murmushin tayi tace ummah zanci sai zuwa anjima yanzu bana jin cin komai.
Fara'ar da take fuskar sultana sadiya raguwa tayi tace haba zarah yau fa dakaina nayi kwad'on kuma nayo tattaki nakawo miki ai bai dace kik'i ciba.
Zarah marairaicewa tayi tace ummah zan ci ai inason kwad'on kawai dai nafiso sai zuwa anjima.
Sultana sadiya cikin ranta tace wannan d'iyan akwai d'an banzan wayau anya batagane abinda nayimataba? murmushi sultana sadiya tayi tace hakane ammah ko kad'anne kid'anci kiji.
Zarah kallon sultana sadiya tayi, gyad'a mata kai sultana tayi alamun taci.
Zarah ido tazuba ma kwad'on tarasa yadda zatayi tana tsoron taci asamu matsala, d'ago kai tayi takalli sultana.
Sultana sadiya tasakar mata murmushi tace kici man.
Zarah har ta kai hannu zata d'iba sai ga yarima ya shigo da sallamarsa da mamaki yake kallon sultana sadiya itama ido tazuba masa tana kallonsu dan kwata-kwata bataji dad'in zuwansaba.
Zarah hamdala tayi tare da janye hannunta daga cikin kular.
Sultana sadiya murmushi tasakar mai tace ranka yadad'e ashe kana nan ai ban saniba da na aiko ankiraka mun gaisa.
Yarima batare da ya ce mata komai ba yasamu waje yazauna, kallon Zarah yayi da take zaune gaban kula sannan yamaida kallonsa ga sultana sadiya, ahankali kamar wanda baya son magana yace ummah barka da rana?
Sultana sadiya washe baki tayi tace yauwa yarima dafatan na sameku lafiya? Ai na ji labarine wajen dada ashe amaryarmu batada lafiya shine nazo ind'an dubata.
Jinjina kai kawai yarima yayi batare da yayi maganaba,
Haushine yakama sultana sadiya cikin ranta tace ka ji dai da abunka munafuki, chan sai tace ya jikin nata?
Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh
Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa janye idonsa yayi yamaida ga kallon dramar da ake a TV d'inta.
Wajen shuru yayi ba wanda yak'ara magana, ammah gabad'aya yarima hankalinsa yana ga zarah dan ransa ya bashi dakyar inba wani abu sultana sadiya take son shiryawaba.
Sultana sadiya ko ta cika ta yi fam takaicinta shigowar da yarima yayi batare da tasamu zarah ta ci kokad'an bane, ji take kamar tarufe yarima da duka, ganin baida niyar basu waje yasa takalli zarah tasakar mata murmushi tace dota bari intashi intafi Allah yak'ara lafiya.
Itama zarah murmushin tayi sannan tace nagode ummah, sultana sadiya kallon yarima tayi tawurga ma k'eyarsa harara sannan tace ni na wuce.
Yarima batare da ya juyo ya kalletaba yace toh ummah mungode.
Wucewa sultana sadiya tayi zata fita cikin sauri zarah tamik'e tabi bayanta koda suka fito sultana sadiya kallon zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace zarah kikoma kar kibar mijinki shi kad'ai.
Zarah duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya tace toh ummah mungode sosai Allah yabada lada,
Sultana sadiya tace Ameen.
har zarah ta juya zata tafi sai jin sultana sadiya tayi ta kira sunanta, tsayawa zarah tayi tare da juyowa.
Murmushi sultana tasakar mata sannan tace dan Allah kitabbata kinci kwad'on nan ko kin d'an samu k'arfin jikinki dan daga ganin yanayinki yunwa kikeji, na san zai taimaka miki sosai idan kikaci kinga badad'i ace kina zama da yunwa.
Zarah murmushi itama tayi sannan tace toh ummah insha Allahu zan ci.
Cike da nuna kulawa sultana tace kin tabbata?
Zarah d'agamata kai tayi alamun eh.
Murmushin jin dad'i sultana sadiya tayi tace yauwa Allah yaimuku albarka.
Zarah tace Ameen ummah, nan suka k'ara bankwana sannan zarah tajuyo tadawo part d'inta, yarima har a lokacin yana zaune inda tabarsa, ahankali tace sannu da zuwa?
Yarima batare da ya kalletaba ya amsa
Wucewa tayi tad'auki kwad'on sai a lokacin yarima yajuyo yakalleta yace ina kika sami wannan abun?
Zarah kallon kular kwad'on tayi sannan tace ummah ce takawomin.
Ta6e baki yarima yayi sannan yace kinci?
Girgiza mai kai kawai tayi alamun a'a.
Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace ban amince kiciba.
Zarah fuskarta d'auke da mamaki tace saboda mi?
Yarima juyowa yayi yawurga mata harara sannan yace saboda hakan nayi ra'ayi.
Shuru zarah tayi batace komai ba, cikin zuciyanta tace daman ai ba ci zanyiba, chan kuma tace anya yarima baisan wani abuba game da matarnan?
Muryar yarima taji ya ce meyasa da nakira wayanki bakiyi picking ba?
Zarah cikin zucinta tace kujini da mutum saikace ba ni nakirasa bai d'aukaba, kallonsa tayi taga idonsa yana a kan tv, ahankali tace bana kusa da wayanne.
mik'ewa yarima yayi yana kallonta yace akwai abinda kike buk'atane?
Zarah kallonsa tayi tace inason cin faten tsaki.
Toh ai zaki iya sa ma'aikatanki suyi miki ko?
Zarah gyad'amai kai tayi alamun eh.
Wucewa yarima yayi zaifita cak yaja yatsaya batare da ya juyoba yace wannan abun kije kizubar a shara sannan ko nan gaba ban amince a aiko miki wani abu kiciba, duk abinda kike buk'ata kisa ma'aikatanki suyi miki indai bakya iya yi dakanki.
Zarah cike da mamakin maganarsa tace Toh.
Wucewa yarima yayi yai tafiyarsa yabar zarah nan tsaye rik'e da kula.
Bayan ya fita Wucewa tayi tashek'a ma zogalen ruwa saida tawankesa tass sannan tak'ulle a leda takira wata kuyangarta tace taje tazubar a bola ammah kar tabari kowa yaganta.
Kuyangar duk'awa tayi tace Toh ranki yadad'e sannan tamik'e tafita.
Zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tana mamakin yarima tace anya baisan wani abuba game da halin su sultana? Chan kuma tatuna da maganar jakadiya da tafad'a mata cewa yarima ko iyayensa bai cika bari suna sanin ta cikinsaba saboda yana da zurfin ciki sosai, jinjina kai tayi sannan tamik'e taje tahad'o coffee dan ji tayi fatenma duk ya fita ranta.
Ahankali tasamu tasha coffeeen ba laifi sannan tajanyo remote tacanza channel tacigaba da kallonta, ahaka har aka kira magri tamik'e taje tad'auro alwallah.
Bayan sallar isha'i saida tayi karatun alk'ur'ani sannan tamik'e taje tashiga wanka,
bayan ta fito shafe jikinta tayi da lotions masu k'amshi, powder da lipstick kawai tashafa sannan tad'auko night gown d'inta iya cinya tasaka, gyara gashin kanta tayi tafeshe jikinta da perfumes alkyabbarta tad'auko tad'aura saman kayan jikinta saida takashe gloves d'd'in d'akin sannan tafita tasallami kuyanginta tawuce tanufi part d'in yarima.
Ko da tashiga parlournsa bakowa dan haka tawuce tanufi bedroom d'insa ahankali tabud'e k'ofar kwance tahangosa tsakan makeken gadonsa ya yi pillow da hannuwansa kansa yana kallon ceiling kamar mai tunani.
Maida k'ofan tayi tarufe saida tacire alkyabbarta sannan tataka tanufi wajen bed d'insa, tsaye tayi tana kallonsa har a lokacin bai juyo yakalletaba da alama ya yi nisa cikin tunanin da yake, ahankali tahau gadon takwantasaman jikinsa tare da d'aura kanta saman faffad'an k'irjinsa, yarima sai a lokacin yakallota.
Zarah murmushi tasakar mai tare da shafa d'an siririn sajen da yake a fuskarsa, da mamakinta sai gani tayi shima ya sakar mata tsadadden murmushinsa ahankali ya d'aura hannunsa a bayanta ya rungumeta zarah ido tazuba mai inda yarima shikuma yazuba ma k'irjinta ido, sai daga baya yamaido kallonsa a fuskarta yana kallon cikin idonta sai kuma chan yamaida idanuwansa yalumshe,
Zarah murmushi tayi sannan tazame jikinta daga nashi tamik'e dan takashe masu gloves, da mamakinta sai ji tayi yarima ya rik'o mata hannu, cikin sauri tajuyo takallesa shima d'in ita yake kallo daga sama har k'asa, sun dad'e a haka sai daga baya yajanyota tafad'o jikinsa yarungume ahankali kamar mai rad'a yace kinci abinci yau?
Zarah turo baki tayi kamar zatayi kuka tace na sha dai coffee,
hannunsa yakai yajenye mata riga yana shafar cikinta yace coffee ai ba abinci bane,
Zarah d'ago kai tayi takallesa cikin shagwa6a tace toh ai kaima shi kakesha da dare.
Yarima ido yazuba mata har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.
Zarah maida kanta tayi takwantar a kafad'ansa sannan cikin wata irin siga tace please dear inason zuwa gida gobe?
Yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace me akeyi gidan?
Zarah murmushi tayi sannan tace gobe za'ayi baikon Aysha.
Da mamakinta sai gani tayi ya yi murmushi sannan yace toh Allah yakaimu kishirya sai insa akaiki,
Cike da jin dad'i zarah tad'ago takai mai wani hot kiss a baki cikin wani irin salo wanda yakusan rikita yarima, sannan cikin wata narkakkiyar muryarta tace nagode dear, yarima wani iri yaji danma ya dake bai nuna mataba, kashe mai ido d'aya tayi tace ka gama min komai dear,
Yarima hannu yakai yashafi wuyanta ahankali yace bakomai, daga nan yagangaro da hannunsa yazame mata d'an siririn hannun rigarta wanda yasa fiye da rabin k'irjinta yafito waje, zarah ido tazuba mai ganin yadda yakafeta da manyan idanunsa, hura mai ido tayi ahankali, lumshe idonsa yayi sannan yakai bakinsa a wuyanta yafara kissing d'inta cikin wani irin salo da yarikita zarah daga nan yagangaro zuwa k'irjinta gaba d'aya yasalu6e mata rigar da take jikinta, inda hannuwansa suka kasa tsayawa waje d'aya a jikinta, zarah ma ba'a barta a bayaba biye mashi tayi suka cigaba da faranta ma juna.
Bayan sun samu nutsu zarah a k'irjin yarima tashige tana mai kukan shagwa6a, yarima jin kukan nata yake har ransa duk yadda yaso yashare kasawa yayi ahankali yace zarah wai me kike ma kuka haka?
Zarah k'ara tura kanta tayi cikin k'irjinsa sannan tace ni bacci nakeji
Yarima batare da yayi maganaba yashiga d'an bubbuga mata baya kad'an-kad'an, cikin sanyayyar muryarsa yace sorry my princess.
Zarah d'ago kai tayi kallesa tace princess?
Yarima shuru yayi dan shi kansa baisan kalmar ta fito daga bakinsaba, ganin ta tsaresa da ido yasa yace Zarah kikwanta kiyi bacci,
Komawa Zarah tayi takwanta tana murmushi dan har cikin ranta ta ji dad'in sunan da yakirata da shi, ahankali tace ina ma yasoni, maida idanuwanta tayi talumshe tana ji yana shafa mata baya ahaka bacci yad'auketa
Da asuba saida yai wanka yad'auro alwallah sannan yatasheta yawuce masallaci,
kayanta tamaida sannan tafito takoma part d'inta a chan tayi wanka tai sallah sannan tabi lafiyar gado takwanta.
wajen 9am zarah tafarka tayi wanka tashirya cikin tsadadden lace d'inta black colour mai ratsin red, ya yi mata kyau sosai, bayan tagama shirinta cikin jin dad'i tafito tanufi part d'in yarima, a dining tasamesa zaune cikin shirinsa yana breakfast, wajensa tanufa tajawo kujerar da take opposite d'in tasa tazauna, kallonsa tayi taga ya tsareta da idanunsa, murmushi tasakar mai tare da kashe mai ido d'aya sannan tace ina kwana?
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace lafiya, ya jikinki?
Langwa6e kai zarah tayi tare da 6ata fuska kamar zatayi kuka tace da d'an sauk'i ammah jiya ka ban wahala sosai.
Harara Yarima yawurga mata yacigaba da breakfast d'insa,
Zarah k'unshe dariyarta tayi tare da d'an duk'ewa tace wash cikina,
Bata ankaraba sai ganin Yarima tayi ya mik'e cikin sauri ya nufo inda take, rik'ota yayi yace lafiya? Meyasami cikin?
'Dago kai zarah tayi takallesa tasakar mai murmushi tace kar kadamu dear kawai d'an motsamin yayi.
Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yajuya zai bar wajen, zarah ruk'o hannunsa tayi, yarima tsaye yayi batare da ya juyoba.
marairaicewa tayi tace kanason babynmu ammah bakason Zarah ko?
Yarima runtse idonsa yayi yana jin tambayartata taimai nauyi sosai a kai shi kansa baisan amsar tambayartataba, ahankali yazare hannunsa daga cikin nata sannan yace idan kin gama shirin kije zan sa akaiki gidan.
Zarah shuru tayi batace komai ba saima binsa tayi da kallo har yafita yabar d'akin,,,Zarah safke ajiyar zuciya tayi cike da tausayin kanta sannan tamik'e tashiga tagyara mai bedroom bayan ta gama tagyara mai parlour sannan tafita takoma part d'inta.
Veil d'inta red tad'auko tayafa tarik'o handbag d'inta kuyanginta biyu suka take mata baya sannan tafito, a gaban gidan taga motocin Yarima ukku jere da guards d'insa hud'u suna jiranta,
ganinta yasa sukayi sauri suka bud'e mata dank'areriyar motar da take tsakiya, Zarah tana shiga aka maida aka rufe, motar baya kuyanginta suka shiga inda guards d'in Yarima suka shiga suma nan akaja motocin ajere suka fita daga masarautar.
Koda suka isa unguwarsu Zarah wani irin nishad'i Zarah takeji dan rabonta da gida ta kwana biyu, a k'ofan gidansu akayi parking d'in motocin cikin sauri guards sukazo suka bud'e mata k'ofan tafito.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Sak'on gaisuwa da jinjina agareki mrs oga, *Hauwa A Usman* nagode sosai da kulawan da nake samu daga gareki mummyn zarah, inaso kisani ko da page ko babu ke tadabance a wajena saidai ince Allah yabarmu tare Allah yasa zumuncinmu yad'aure har jikokinmu I hrt u more dear❤_
*PAGE* 5⃣1⃣
Zarah tana fitowa nan kuyanginta suka take mata baya har cikin gidansu, Zarah dagudu ta isa wajensu mama da suke zaune suna 'yan soye-soye, jikinmama tafad'a tace cikin murna tace oyoyoo mamana.
Mama ma rungumeta tayi cikin jin dad'i tace oyoyoo Zarah na.
Yaya rauda kallon Zarah tayi tace ikon Allah kedai har yanzu baki girmaba.
Zarah turo baki tayi cikin shagwa6a tace yaya rauda na fa kwana biyu banga mamanaba, mama janye Zarah tayi daga jikinta tace rabu da ita zarahna,
Daidai lokacin kuyangin zarah suka iso suka duk'a cikin girmamawa suka gaishe da su mama
Cikin sakin fuska su mama suka amsa musu tare da tambayarsu gida sukace Alhmdllh, kallonsu zarah tayi tace zaku iya tafiya amaidaku gida, duk'awa sukayi sukace to ranki yadad'e angama, mama leda tasamu tak'ulla musu su donut tabasu, nan sukayi sallama da su mama sannan suka mike suka tafi.
Zarah kallon mama tayi da tazuba mata ido, murmushi Zarah tayi tare da duk'awa tagaishe da ita.
Mama amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayarta mijinta da mutanen gida
Zarah cikin jin kunya tace duk suna lafiya mama.
Juyowa tayi tana dariya tace yaya rauda ina kwana? Harararta yaya rauda tayi tace yanzu k'arfe sha biyu zaki kira mana kwana.
Afuwan yaya rauda ina wuni?
Murmushi yaya rauda tayi tace lfy lou ya gidan?
Zarah tace Alhmdllh komai daidai.
Sai a lokacin zarah taji k'amshin soyen ya daki hancinta, yamitsa fuska tayi jin zuciyanta yana shirin tashi tace wai banga amaryaba,
Mama tace tana nan d'aki tana k'ullah kunun aya, cikin jin dad'i zarah tace wow bari inje insha har na ji ina son sha, cikin sauri tawuce tanufi d'akin.
Mama da yaya rauda binta sukayi da kallo cike da sha'awa dan ko ba'a fad'a musuba sunsan zarah cikine da ita.
Tana shiga d'akin taja tatsaya, Aysha da take zaune tana k'ullin kunun aya ganinta yasa tataso dagudu tarungumeta tana oyoyoo Aunty zarah, zarah ma dariya tayi tace ke zaki karyani ni sakanni,
Aysha janye jikinta tayi tana dariya tare da zuba ma zarah ido tace Auntyna kinga yadda kika koma kamar ba keba
Murmushi zarah tayi tace ke banson tsokana, amaryarmu ya shirye-shiryen bikki? Allah yasa kar asa mana bikkin nesa.
Dariya Aysha tayi tace wlh Aunty zarah nima addu'an da nake kenan.
Da mamaki zarah takalleta tace lallai Aysha ashe bakida kunya toh Allah yakyauta,,,,tana fad'in haka tawuce tanufi wajen kunun ayan tabar Aysha tana ta dariya.
Zarah zubawa tayi sosai tasha har saida taji ta k'oshi sannan tabarshi.
Duk yadda taso tataya su mama girki kasawa tayi saboda k'amshin tayarmata da zuciya yake, dole tahak'ura tayi zamanta.
Abbah ma koda yadawo ya yi murna sosai da ganin 'yar tasa.
Wajen k'arfe ukku 'yan neman aure sukazo anmusu tarbar mutunci, inda aka tsaida maganar akan nan da watanni hud'u masu zuwa.
Sun kawo su biscuits su alewa bakin gwalgwado sun bada sai kud'in nagani inaso da na neman aure.
ko da abbah yazo musu da labarin su mama sunyi murna sosai nan sukaita fatan alkhairi.
Nan aka zauna aka k'ullah kayan aka d'ibi na dangi sannan aka aika mak'ota nasu.
Mama duk yadda taso zarah taci abinci k'iyawa tayi daga k'arshe saidai tabada aka siyo mata awara nan tazauna taci.
Bayan sallar isha'i suna zaune suna hira zarah handbag d'inta tabud'e tad'auko dubu d'ari biyu tamik'a ma abbah tace gashinan Abbah ko kayan kitchen anfara siya mata.
Abbah girgiza kai yayi yace a'a zarah akwai kud'i hannuna dan na ware wanda zan cika incanza mana gida, kud'in da suka rage ne nasamu nabud'e shago ina kasuwanci dasu nakeso inmata siyayyarta.
Zarah cikin jin dad'i tace hakane Abbah ammah dan Allah kataimaka ka amsa kuk'ara sai asamin albarka.
Kar6a yayi nan sukaita sa mata albarka.
Aysha da take cikin d'aki tana waya fitowa tayi takalli zarah tana murmushi tace Aunty zarah kizo kugaisa da malam bello yana nan k'ofan gida.
Zarah girgiza kai tayi tace a'a Aysha kinga ban tambayaba, marairaicewa Aysha tayi tace iyakarki fa zaure nan zaku gaisa,,,tafad'i haka tare da mik'ama zarah gyalenta.
Zarah kar6a tayi tayafa ba dan tasoba tamik'e tabi bayan Aysha.
Daga waje suka hangosa tsaye zarah wajen k'ofar gidansu tatsaya, malam bello kallo d'aya yaimata yad'auke kai fuskarsa d'auke da murmushi yak'araso wajen da suke yana mai cewa a'ah ashe yayarmuce.
Murmushi zarah tayi tace malam ina wuni?
Lfy lou zarah ya gida da mai gidan.
Cikin jin kunya tace kowa yana lafiya, kallon Aysha tayi da taketa murmushi tace malam ga dai amanar k'anwatanan akularmin da ita.
Dariya malam bello yayi yace kar kidamu yayarmu insha Allahu zanyi iya bakin k'ok'arina.
Zarah cikin jin dad'i tace Allah yasa malam mungode sosai, Allah yakaimu lokacin.
Gabad'ayansu sukace Ameen.
Daidai lokacin motar yarima ta iso wajen da suke, yana yin parking saida gabansa yafad'i ganin zarah tsaye da wani, baima lura da Aysha ba datake gefe, suna had'a ido da zarah wata irin harara yawurga mata, zarah saida gabanta yafad'i cikin ranta tace nashiga ukku, dakewa tayi tataka ta isa inda yake fuskarta d'auke da murmushi tabud'e mai k'ofan tace sannu da zuwa.
yarima wani irin kallo yaimata yace wanene wancan kuke tare da shi?
Koda ta tsorata da hararar da yai mata ammah tadake tayi murmushi sannan tace mijin da Aysha zata aurane...shine dan bakida hankali kike tsaye da shi ke kad'ai kina ta yimai dariya?
Zarah da mamaki takallesa tace bafa ni kad'ai bace baga Aysha chan ba.
Sai a lokacin idonsa yakai ga su Aysha dasuke tafowa inda suke, ajiyar zuciya yasafke sannan yafito daga motar daidai lokacin su Aysha suka iso wajen da suke,
malam bello cikin girmamawa yarussina zai gaishe da yarima.
Cikin sauri yarima yarik'o hannunsa sukayi nusabaha fuskarsa a sake yace Allah yasa alkhairi ango,
Malam bello duk'ar da kansa yayi cikin girmamawa yace Ameen ranka yadad'e nagode,
Aysha ce tace yayana ina wuni?
Kallonta yayi fuskarsa a sake yace k'anwata kin wuni lafiya? Sai mukaji labari, Allah yasa alkhairi,
Aysha cikin jin kunya tarufe fuskarta, malam bello ne kawai ya amsa da Ameen.
Dariya zarah tayi tace magulmaciya kawai.
Yarima kallon zarah yayi yace menene kuma abun gulma? Daga tana jin kunyan yayanta.
zarah fari taimashi da ido.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta yace k'anwata bari mushiga ciki ingaishe da su abbah.
Aysha murmushi tayi tace toh yayana afito lafiya.
Zarah jerawa sukayi da Yarima suka shiga gida inda sukabar malam bello da Aysha suna ta hirarsu.
Koda sukazo shiga yarima ja yayi yatsaya, zarah kallonsa tayi tana shirin yin magana yace muje mana.
Zarah murmushi tayi sannan tawuce gaba yarima yabi bayanta har suka shiga cikin gida, har a lokacin su mama suna zaune tsakar gida, zarah tabarma tad'auko tashimfid'a mashi yazauna cike da girmamawa yagaishe da su abbah,
Fara'a bayyane a fuskarsu suka amsa mashi tare da tambayarsa mutanen gida, yarima saddar da kansa yayi k'asa yace Alhmdllh, Ya hidima?
Alhmdllh,,cewar su abbah.
Masha Allah, Allah yasa alkhairi, Allah yakaimu lokacin.
Cikin jin dad'i suka amsa da Ameen y rabb.
Yaya rauda kallonsa tayi tace ranka yadad'e barka da dare.
Murmushi yarima yayi yace yayarmu anwuni lfy?
Yaya rauda tace lafiya lou Alhmdllh, y hak'uri da mu?
Murmushi kawai yarima yayi.
Zarah mik'ewa tayi taje tad'auko abinci takawo mai, ganin haka yasa su abbah suka tashi suka bashi wuri dan yasamu yaci.
Bayan su Abbah sun tashi zama tayi gefensa dan tazuba mai, kallonta yarima yayi yace kindai san bana cin abinci da dare.
Zarah ma 6ata fuska tayi takallesa kamar zatayi kuka tace abincin gidan namu ma bazakaciba?
Yarima kallon kunun ayan da takawo mai yayi yace zuba min wannan dai.
Toh tace sannan tatsiya mai a cup tamik'a mai, kar6a yayi yafara sha kad'an kad'an, wayarsa da ya aje gefe zarah tad'auka tana wasa da ita, yarima baice mata komai ba ahaka har yashanye, kallonsa tayi tace ko ak'ara ma?
Girgiza kai yarima yayi sannan yace kije kiyi ma su mama sallama kizo mutafi dare yakeyi.
Mik'ewa Zarah tayi, yarima kallonta yayi yace wai ke yau kin ma ci abinci?
Zarah yamitsa fuska tayi tace na dai ci awara.
Shuru yarima yayi baice komai ba,
wucewa tayi taje tasanar da su mama zasu tafi nan tafito tare da su mama,
Nan suka yi sallama suka fito daidai lokacin Aysha zata shigo gida, kallonsu tayi tace ba dai tafiya zakuyiba.
Yarima murmushi yayi yace ko mukwana?
Dariya Aysha tayi tace eh ranka yadad'e.
Zarah kallonta tayi tace ina angon har ya tafi?
Susa kai Aysha tayi cikin jin kunya tace uhm.
Dariya Zarah tayi nan Aysha tarakasu har wajen mota sukayi bankwana takoma gida.
Tunda suka fara tafiya tsit motar tayi, ahankali yarima yajuyo yakalli zarah da tajingine kanta a sit d'in da take zaune ta zuba ma waje d'aya ido kamar mai tunani, janye idonsa yayi daga killonta yacigaba da tuk'insa duk sai yaji babu dad'i yanayin da yaganta.
Ahankali yace akwai abinda kike buk'atane?
Zarah juyowa tayi takallesa taga ba ita yake kalloba idonsa yana a titi, shuru tayi tana kallonsa jin tayi shuru yasa yarima yad'an juyo yakalleta karaf suka had'a ido, zarah duk'ar da kanta tayi sannan tace ice cream nakeson sha.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace meyasa kikeson shan kayan sanyi, ya kamata kidaina tunda yanzu ba ke kad'ai bace.
Zarah 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace toh.
Yarima saida yabiya yasiyo mata sannan suka wuce gida, yana yin parking Zarah tabud'e tafita, kallonta yarima yayi yace wannan fa wa zai kawo miki?
Murmushi Zarah tayi tace sorry mancewa nayi nan tad'auka sannan tawuce cikin gida.
Yarima ma fitowa yayi yawuce fada dan sugaisa da memartaba.
___________
A 6angaren sultana sadiya ranta a 6ace takoma part d'inta a parlour tatarar da sumayya zaune tana jiranta dan sumayya tunda taga shigar sultana part d'in zarah yasa tafito tazo turakar iyayenta dan tasamu labari wajen ummanta idan tadawo,, ganinta yasa sumayya tamik'e cikin murna tace ummana angama komai ko?
Kallonta sultana sadiya tayi tare da jan tsoki tace sumayya wanchan banzan mijin naki ya 6ata min duk wani plan nawa.
Sumayya a tsorace tadafe k'irji tace ummah kar dai kicemin asirinmu ya tonu?
Sultana sadiya zama tayi saman kujera cikin 6acin rai takwashe komai tafad'a ma sumayya duk abinda yafaru.
Sumayya ajiyar zuciya tayi sannan tace ummah wlh banji dad'in faruwar hakanba, yanzu saboda Allah ido zansa mata har tahaihu? Yanzu ita zata aje ma yarima magaji?,,,sumayya tafad'i haka tare da fashewa da kuka, cikin kuka takalli sultana sadiya da abun duniya yadameta tace ummah ko kid'au mataki ko kar kid'auka wlh ba zan ta6a barin zarah ba sai naga bayanta.
Sultana sadiya jawota tayi tazaunar da ita gefenta tace sumayya banaso kije kiyi abinda zai jawo abinda za'ayi da ansani,
Sumayya shigewa tayi jikin ummanta tana kuka tace ummah a kullum ina fad'a miki bandamu da abinda zai faruba indai burina ya cika.
Sultana sadiya d'ago kan sumayya tayi tana share mata hawaye tace kidaina cewa haka sumayya kibari abi komai a sannu, sumayya mik'ewa tayi tana ja da baya tace a yaushe duk za'ayi hakan bayan ta haihu? Girgiza kai tayi tace ummah kibarni kawai, tana fad'in haka tajuya tafita daga d'akin.
Sultana sadiya k'walah mata kira tashiga yi ammah ina sumayya tafiyarta tayi.
Dafe kanta sultana tayi tace wannan wace irin rayuwa ce?
Sumayya koda takoma part d'inta batabi ta kuyanginta da suke gaishetaba dagudu tashige bedroom d'inta tamaida tarufe, jingine kanta tayi da k'ofar tashiga rusa kuka, tana jin wayanta tana ringing tashare tacigaba da kukanta, daga k'arshe takoma saman gadonta takwanta nan tak'ara sautin kukanta saida taji kanta ya fara ciwo sannan tatsagaita kukan nata.
Wasa-Wasa ciwon kai da zazza6i suka rufeta haka tajanyo blanket tarufa ahaka tayi ta juyi har cikin dare sai daga baya bacci yayi awon gaba da ita.
Da safe ko da kuyangarta zabba'u tazo tayita knocking jin shuru yasa tatura k'ofan tashiga cikin sauri ta isa inda Sumayya take k'udundune da bargo tana rawan sanyi,
Kallonta zabba'u tayi a firgice tace ranki yadad'e mi yasameki?
Sumayya dakyar tabud'e baki muryarta na fita ahankali tace je kikira min yarima.
Cikin sauri zabba'u tamik'e tace toh ranki yadad'e.
Yarima zaune yake yana breakfast inda zarah take gefensa tana shan ruwan lipton wanda yasha kayan yaji, knocking d'in k'ofa akayi zarah kallon Yarima tayi da yature cup d'in tea d'insa gefe yamik'e saida yabaro dining area sannan yace yes,
Guards d'insane yabud'e yashigo saida yad'an russuna sannan yace ranka yadad'e gimbiya sumayya ce tayo aike,
Yarima saida yazauna saman cushin sannan yabashi izini yabarta tashigo.
Kuyanga zabba'u koda tashigo zubewa tayi k'asa takwashi gaisuwa wajen yarima, hannu kawai yarima yad'aga mata, zabba'u k'ara duk'an da kanta tayi tace ranka yadad'e daman gimbiya sumayya ce batada lafiya tana chan kwance yanzu haka ita ta aikoni inzo insanar da kai.
Zarah jin an ambaci sumayya batada lafiya yasa tamik'e tabaro dining area,
yarima nuni yayi mata alamun tatafi, zabba'u k'ara duk'awa tayi takwashi gaisuwa sannan tamik'e cikin sauri tabar d'akin.
Zarah kallon yarima tayi da yamik'e cike da jin tausayi tace meyake samunta?
Shima yarima kallonta yayi yace bari inje indubata, Zarah bayansa tabi tace muje tare.
Yarima baice komai ba nan suka fito suka nufi part d'in sumayya duk inda suka ratsa bayi da Kuyangi duk'awa suke suna kwasar gaisuwa,
ko da suka shiga parlournta nan ma kuyanginta suka zube suka gaishesu, hannu yarima yad'aga musu cikin sauri suka fita sukabar d'akin.
Bedroom d'inta suka nufa, nan Zarah tayi knocking d'in k'ofan, zabba'u da take tsugunne k'asa tana jera ma sumayya sannu, mik'ewa tayi taje tabud'e k'ofan ganin su yarima ne yasa cikin sauri taja gefe tare da d'an rissinawa tace ranka yadad'e sannunku da zuwa,
Yarima baibi takantaba yawuce yanufi wajen bed d'in sumayya, cikin sauri zabba'u tafita tabar d'akin.
Zarah ma bayansa tabi suka isa, sumayya d'ago kai tayi takalli yarima sai hawaye, daga gefen gadon yarima yazauna yace sumayya bakida lafiya? Meyake samunki.
Sumayya d'agowa tayi tarungume yarima tare da fashewa da kuka,
jikinta yaji da zafi ahankali yace zazza6i kike? Gyad'a mai kai tayi, sorry yace nan yashiga shafa bayanta.
Zarah da take tsaye kamar zatayi kuka saboda tausayi, cikin muryar tausai tace sannu Aunty sumayya ya jikin naki?
Sumayya cikin sauri tad'ago takalli Zarah dan kwata-kwata bata lura da itaba, duk ciwon da takeji ammah hakan baihata wurga ma Zarah hararaba sannan takoma jikin yarima talafe.
Tsaye Zarah tayi duk jikinta ya yi sanyi,
Yarima janyeta yayi daga jikinsa tare da maidata yakwantar yace bari inje ind'auko drugs kinji?.
Gyad'a mai kai sumayya tayi, mik'ewa yayi yakalli Zarah yace kisa ahad'a mata breakfast bari indawo.
Toh Zarah tace sannan takalli sumayya da taketa rawar zazza6i tace Aunty sumayya Allah yasauke.
Banza sumayya tayi takyaleta, Zarah bata damuba tawuce nan tasa kuyangin sumayya suka had'o mata breakfast takar6a tadawo bedroom d'in, a saman bedside ta aje sannan takalli sumayya tace intaimaka miki kitashi kiyi breakfast d'in?
Kallonta sumayya tayi cikin tsana tace ba ruwanki da ni malama.
Daidai lokacin yarima yadawo kallon Zarah yayi yace batayi breakfast d'inba?
d'aga kai kawai Zarah tayi batare da ta yi magana ba.
Yarima wucewa yayi yazauna gefen gadon yace sumayya kitashi kiyi breakfast sai kisha drugs.
Yamutsa fuska sumayya tayi tace na k'oshi, taimaka mata yarima yayi tatashi zaune yace kidaure kici ko kad'an ne.
Sumayya jikinsa tafad'a tace ni bana iya ci,
Kallon Zarah yayi da take tsaye yace zuba mata breakfast d'in.
Zarah toh tace sannan tazo tazuba chips cikin plate sannan tahad'a tea mai kauri tamik'a mai cup d'in.
kar6a yarima yayi sannan yace ma sumayya kidaure kisha ko kad'anne, sumayya ganin yadda yarima yake lalla6ata yasa ta amince zatasha dan tasan halinsa idan yaga tana haka zai iya shareta yayi tafiyarsa, haka tabud'e baki yashiga bata tanasha ahankali tana k'ara langwa6ewa saida yaga ta d'an sha nakirki sannan yabarta,
Kallon zarah yayi da take rik'e da plate d'in chips tana yamitsa fuska dan k'amshin ya fara isarta, ganin haka yasa yarima yakar6i plate d'in yad'aura saman bedside nan yad'auki fork yad'ibo yafara bata, kad'an taci nan yabata drugs d'in tasha.
Zarah cike da tausayi tace sannu Aunty sumayya, banza sumayya tayi tak'yaleta.
ganin haka yasa yarima yace sumayya tana miki magana fa.
Wani irin kallo tayi ma zarah sannan ciki-ciki tace yauwa.
Yarima ganin tana shirin komawa takwanta yace sumayya kitashi kid'an watsa ruwa ko kinji dad'in jikinki.
sumayya langwa6e kai tayi tace toh kataimaka min ban iya yi.
yarima kallon zarah yayi da take kallonsu, murmushi tasakar mai tace bari inje inhad'a mata ruwan wankan, bata jira jin abinda yarima zaiceba tamik'e tanufi toilet d'in sumayya.
yarima binta yayi da kallo har tashige sannan yamaida kallonsa ga sumayya da tatsaresa da ido ganin yadda yake bin zarah da kallo Wani irin takaici yacikata.
Ahankali yace akwai abinda kike buk'ata?
Girgiza kai kawai sumayya tayi, daidai lokacin zarah tafito daga toilet d'in kallon yarima tayi tace ga ruwan chan na had'a,
Yarima kallon sumayya yayi yace muje kiyi wankan.
Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka tace bana iya tashi jiri nakeji please kad'aukeni,,,tafad'i hakan tare da kallon zarah.
zarah d'auke kanta tayi kamar bataji abinda taceba.
Yarima shuru yayi kamar ba zaiyiba, zarah juyowa tayi takallesa nan suka had'a ido, cikin rashin damuwa tasakar mai murmushi , janye idonsa yayi daga kallonta babu yadda ya iya haka yad'auki sumayya yanufi toilet da ita.
zarah tana ganin sun shige bata kawo komai a rantaba nan tagyara mata bedroom d'inta tas sannan tafita takoma part d'inta.
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
*PAGE* 5⃣2⃣
Koda suka fito daga toilet d'in da mamaki yarima yaga zarah bata d'akin ammah ko'ina angyarsa fes room d'in sai k'amshi yake, murmushi yayi dan ya san ko ba'a fad'aba toh aikin zarah ne.
Ita kanta sumayya saida tayi mamaki dan bata ta6a tunanin haka daga zarah ba.
Ta6e baki tayi cikin ranta tace gulmammiyar kawai duk dai abinda zakiyi bazanta6a fasa k'udirinaba akanki, muryar yarima taji ya ce muje kizauna.
Haka yarik'ota sukaje bakin gado yazaunar da ita, marairaicewa tayi tace please kashiryani.
Wani irin kallo yayi mata yace shiryawarma bazakiyi da kankiba?
K'wallah ce tacika mata ido tace kaga fa banda lafiya, Banza yarima yaimata nan yamik'e yaje yabud'e wardrobe d'inta yad'auko mata kaya, saida yashafa mata lotion sannan yataimaka mata tasaka kayan.
Komawa tayi takwanta yarima kallonta yayi yace bari intafi hospital
Sumayya cikin muryar tausayi tace yau bazaka hak'uraba?, kaga fa banda lafiya.
Wani irin kallo yarima yaimata sannan yace zan turo miki kuyanginki in akwai abinda kikeso sai sutaimaka miki,, yana fad'in haka yajuya yafita yabar d'akin.
Sumayya ba haka tasoba cikin ranta tace ammah da wacchan gajarce ai da ka zauna,,nan tak'ara jin wata irin tsanar zarah, knocking d'in k'ofa da akayine yasa tabada izinin ashigo.
Kuyanginta ne suka shigo nan suka zube suna kwasan gaisuwa wajen shugabartasu tare da yi mata ya jiki.
Sumayya fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa musu sannan tace sufita subata waje tana son hutawa, cikin sauri har suna rige-rige suka fita sukabar d'akin.
Nan Sumayya tagyara kwanciyarta dan Wani irin bacci takeji, ahaka bacci yai awon gaba da ita.
Bayan sallar la'asar zarah fitowa tayi tanufi part d'in Sumayya dan tadubata da jiki.
Lokacin Sumayya tana Kwance suna waya da zinat dan tunda tafarka baccin taji zazza6in ya safka dan har wanka tasamu tayi taci abinci sannan tasha drugs d'in da yarima ya aje mata.
knocking zarah tayi ahankali, Sumayya jin ana knocking yasa tabada izinin shigowa dan tayi tunanin ko kuyangintane.
Ahankali zarah taturo k'ofar tashigo tare da yin sallama,,, ganinta yasa fara'ar da take fuskar Sumayya tagushe ahankali tace baby ina zuwa bata jira jin abinda zinat zataceba takashe wayan tana kallon zarah a wulak'ance, cikin d'aga murya tace me yakawoki part d'ina?.
Zarah murmushi tayi tace Aunty Sumayya ya jikin naki?
Harara tawurga mata tace wannan ba damuwarki bane kar kik'ara shiga sabgata ke ni ko ganinki banason yi saboda bana sonki na tsaneki,
Zarah da mamaki take kallonta ahankali tace Sumayya har ga Allah ni da zuciya d'aya nake zaune da ke kuma inaso kisani ni ban iya irin wannan zamanba dan ita rayuwa duka nawa take.
Tsawa Sumayya tayi mata tace ke kifita idona duk wani dad'in bakinki bazaiyi tasiriba akaina kuma wannan cikin da kike tak'ama da shi ke kina jin dad'i zaki haifarma yarima magaji toh indai ina numfashi bazaki ta6a haihuwarsaba.
zarah bataji haushin kalaman da Sumayya tafad'aba dan idan da sabo toh tasaba jin irinsu, Ta6e baki tayi tace Sumayya kenan ciki Allah ne yabani kuma shikad'ai zai iya ikonsa akan abunsa ni na yarda da k'addara duk abinda yasameni nasan *DAGA ALLAH NE* bazan ta6a jayayya da ikon Allah ba dan shi musulmi anaso yadinga yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau, dan haka *K'ADDARA CE* kawai zatasa cikin nan yabar jikina.
Sumayya har ta bud'e baki zatayi magana sai ga yarima ya bud'e k'ofa, cikin sauri tafashe da kukan k'arya tace yanzu saboda Allah zarah ni zakiyi ma gorin haihuwa?
Zarah mamakine yacikata cikin sauri takalli yarima da yake gefe wata irin harara yawurga mata.
Sumayya dasauri tataso tazo tafad'a jikinsa tana kuka, cikin sheshek'ar kuka tace yarima kana jinta tana min gorin ciki ni dan Allah bai baniba.
Yarima tausayinta yaji nan yarungumeta jikinsa,, zarah mutuwar tsaye tayi dan bata ta6a tunanin makircin Sumayya ya kai hakaba,,, k'wallah ce tacika mata ido muryarta tana rawa tace please yarima kafahimceni wlh ba haka bane.
Wani kallo da yarima yaimata zarah saida takusan sakin futsari cikin 6acin rai yace kin kyauta gorin ciki kikayi mata, shin ke wayonki ko dubararki suka baki?,
Zarah matsowa tayi tace yarima kar kayarda da maganarta wlh duk abinda tafad'a ba haka bane.
Hanya yarima yanuna mata yace kifita tun kan ranki ya6aci.
Zarah kallon Sumayya tayi da take manne a k'irjin yarima tana mata gwalo, juyawa tayi tafita tabar d'akin cikin 6acin rai tare da nadamar zuwanta.
Sumayya tana ganin zarah ta fita nan tasake fashewa da wani sabon kukan, cikin kuka tace yarima kana jin abinda tacemin ko, daman mutum yana ba kansa haihuwa?
'Dagota yayi daga jikinsa cike da tausayinta yace Sumayya kidaina cewa haka kiyi hak'uri ita haihuwa ubangiji shi yake bayar da ita ga wanda yaso sannan kuma shi yake hana wanda yaso, a tsawon dad'ewarmu kin ta6a gani na nuna damuwata dan baki haihuba?
Girgiza kai Sumayya tayi,
yace gud, dan haka kar kik'ara damuwa kema Allah bai mance da keba in da rabo zaki haihu.
Sumayya rungumesa tayi cikin jin dad'in maganarsa tace na gode sosai ranka yadad'e....A chan k'asan zuciyanta kuma cewa tayi koma me zakace bazan ta6a amincewa waccan jakkar tarigani haihuba dole ind'au mataki akan cikinnan nata.
Yarima janyeta yayi daga jikinsa tare da tallabo fuskarta suka k'ura ma juna ido, murmushi sumayya tasakar mai.
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayansa tafara ruri, ganin daddynsane yasa yasaki sumayya tare da d'an matsawa kad'an sannan yayi picking d'in wayan tare da yin sallama.
Daga chan 6angaren sultan Ahmad amsa masa yayi.
Yarima cikin girmamawa yagaishe da mahaifin nasa, nan sultan Ahmad ya amsa masa sannan yace yarima kana ina yanzu?
Ina gida daddy,,,cewar yarima.
Kazo yanzu kasameni.
Toh daddy.
Juyowa yayi yakalli sumayya da tatsaresa da ido yace ni na wuce.
Sumayya cikin rashin jin dad'i tace Toh.
Nan yarima yafita yabarta.
Sumayya tana ganin fitarsa nan tabushe da dariya cikin jin dad'i tace lallai yarima da ni kakeja ai wlh ba abinda zai hanani d'aukar k'wak'waran mataki akan wannan bagidajiyar matar taka, yanzu ko tana ina? Nasan dai ana chan ana ta kuka,,,nan ma Sumayya tayi dariyar jin dad'i sannan tawuce taje tabud'e bedside d'inta tad'auko wani pills tasha sannan tahau saman gadonta tajanyo wayarta takira zinat nan sukacigaba da wayansu.
Zarah bayan ta bar part d'in gimbiya Sumayya nata takoma tana shiga bedroom d'inta tamaida tarufe, saman gadonta taje tazauna tadafe kanta mamakin makircin da Sumayya tayi matane yadameta, maganganun da yarima yafad'a matane suka cigaba da yawo cikin kunnuwanta.
Ita ba komai tafi ji ba sai yadda yarima yayarda da maganar da yaji Sumayya ta fad'a , ba abinda yafi 6ata mata rai irin taga yarima yana fushi da ita.
Duk yadda taso tadanne kukan da yake cinta kasawa tayi nan tarushe da kuka,,,,haka tasha kukanta tak'oshi sannan tamik'e taje tawanke fuskarta tare da d'auro alwallah nan tazo tashimfid'a darduma tad'auko alk'ur'aninta tacigaba da karantawa dan samun sauk'in k'uncin da takeji a zuciyanta.
Tana nan zaune har aka kira sallar magrib tayi sallah.
Bayan sallar isha'i wanka taje tayi tai shirin baccinta tahaye saman gadonta takwanta.
Yarima kasancewar fita sukayi da su daddy basu dawo gida ba sai around 9pm, koda suka dawo part d'in sumayya yawuce dan yadubata, lokacin da yashiga kwance yatarar da ita tana waya, ganinsa yasa tayi saurin janye wayar a kunnenta tare da sakar mai murmushin rashin gaskiya.
Kallonta Yarima yayi yace dawa kike waya?
Gabantane yafad'i chan dabara tafad'o mata tace am daman ummah ce muke waya da ita ta kirani ne tayi min ya jiki.
Ta6e baki yarima yayi sannan yace ohk, ya jikin naki ina fatan dai yanzu yai sauk'i dan naga tun d'azun zazza6in yasafka?
Sumayya langwa6e kai tayi Sannan tace dasauk'i.
Yarima duba agogon da take manne a hannunsa yayi sannan yace ohk, Allah yak'ara sauk'i, kikwanta kiyi bacci.
Murmushi sumayya tasakar mashi sannan tace toh dear Allah yakaimu.
Ciki-ciki yarima yace Ameen sannan yafita yabar d'akin.
Sumayya na ganin ya fita tajanyo wayarta takanga a kunne tare da cewa baby kina jinmu da mutumin?
Zinat da ta saurari duk hirarsu dariya tayi tace ina jinki baby da wannan munafukin mijin naki ai bari inzo garin wannan cikin da yake tak'ama za'a haifa mai sai munga bayansa.
Dariya sumayya tayi tace baby ina fa jin haushi idan kina ce ma mijina munafuki.
Daga chan 6angaren ta6e baki Zinat tayi tace yoh wanene inba munafukinba ai tunda har ya amince yayi miki kishi toh na gama ganinsa da mutunci.
Murmushi sumayya tayi tace kina sa ina jin haushi in kina tunomin da waccan bagidajiyar.
Dariya zinat tayi tace ai wlh bari inshigo garin zata gane kurenta, dear yanzu dai kikwanta kiyi bacci dare keyi.
Sumayya kallon agogon da take manne a bangon d'akin tayi tace nasan dai yanzu akwai abinda zakiyi saisa kike korata.
Dariya zinat tayi tace yoh mefa zanyi.
Hmm kedai kika sani wlh nasan bakida gaskiya, yanzu dai kije kar intsaidake....sumayya na fad'in haka tayi switching off d'in wayanta tana dariya ta aje saman bedside sannan tagyara kwanciyarta tare da kashe gloves.
A 6angaren yarima koda yakoma part d'insa bayan ya yi shirin bacci kwanciyarsa yayi, zarah ce tafad'o masa a rai, wani irin haushi yaji lokacin da yatuna gorin haihuwan da tayi ma sumayya, tsaki yaja sannan yajuya yayi kwanciyarsa.
Tun daga ranar zarah take 6oye kanta a room d'inta dan bata yadda kwatakwata suhad'u da yarima koda abun yana damunta kawai dai daurewa take.
yarima ma shi kansa daurewa kawai yakeyi duk yadda zaiji yanason ganinta danne zuciyansa kawai yake koda daman shi a tunaninsa ba ita yakeson ganiba saboda babynsa da yake manne a cikintane kawai yasa yake jin kewarta.
Sumayya ko gaba takaita dan tunda tafahimci yarima da zarah basu jituwa nan wani irin farin ciki yadabaibayeta dan hakane ma tatsiri k'ara shige ma yarima dan ma baya bata had'in kai sosai.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Yarima ne zaune d'akinsa yana cike wasu files, wayansa yad'auko yakira abban sumayya bayan sun gaisa yake tambayarsa sauran files d'in, daga chan 6angaren abbah cewa yayi ai d'azun da sumayya tashigo nabata tabaka halan bata bakaga?
Murmushi yarima yayi cikin girmamawa yace abbah ina tunanin mantawa tayi bari inmata magana.
Sultan Abbas yace toh lafiya lau kome kenan sai kakirani.
Yarima yace toh abbah nagode sosai.
Bayan sun gama wayan yarima lalubo number d'in sumayya yayi yakirata ammah har tak'arashi ringing batayi picking ba, tsaki yayi yace ko ina taje ta aje wayar....mik'ewa yayi yafito yanufi part d'in sumayya a parlournta kuyanginta ne kawai cikin girmamawa suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baibi ta gaisuwar da sukeyi masaba yace sumayya fa?
'Daya daga cikinsu ce tace ranka yadad'e tana cikin d'akinta, wucewa yarima yayi yashiga bedroom d'inta da mamakinsa yaga babu kowa motsin ruwan da yaji a toilet ne yasa yagane wanka take, waje yasamu a gefen gadonta yazauna, abinda yahangone saman bedside d'inta yasa yamik'e yanufi wajen da mamakinsa, tsaye yayi kamar wanda ruwa yaci sai chan yakai hannu yad'auko saida yarazana da yaga drugs jibgi guda, d'aya bayan d'aya yad'auka yana dubawa inda zuciyansa tashiga bugawa da k'arfi, daidai lokacin sumayya tafito daga wanka dan saurin da take kenan tazo takwashe gudun kar yarima yashigo yagani, tsaye tayi kamar wadda ruwa yaci tsoro da fargaba duk suka cikata.
Yarima juyowa yayi yalalleta da idanuwansa da suka rine suka koma launin ja saboda 6acin rai..
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
*PAGE* 5⃣3⃣
Sumayya hawaye ne suka fara zuba daga idonta cikin muryar kuka tace please yarima kafahimceni wlh ba abinda kake tunani bane, sharrin shaid'anne kawai.
Wata uwar harara yabanka mata yace na tambayeki?......wlh Sumayya kin ban mamaki daman pills kikesha dan kar kisamu ciki? Inaso kisani duk abinda kika aikata kanki kikayi mawa kuma kanki kika zalunta, na gode ma Allah da bake kad'ai gareniba, kuma idan ke bakyason had'a zuri'a da ni toh wata tanaso, cikin ikon Allah sai gashi Allah yaba zarah ciki har kina ik'irarin cewa tana miki gorin ciki, ashe nan kekad'ai kikasan abinda kike shukawa tsawon dad'ewar da mukayi.
Ammah fa zarah ta burgeni.
Sumayya cikin sauri tad'ago kai takallesa hawaye sha6e-sha6e a fuskarta.
murmushin tskaici yayi sannan yace eh Sumayya,,,sannan inaso kisani kanki kika cuta ba ni ba kuma bazakiga illan hakanba sai nan gaba, a duk lokacin da kika 6ata mahaifarki kar kiyi kuka da kowa sai kanki.
Sumayya rusgar kukanta take kamar wanda aka aiko ma da sak'on mutuwa,girgiza kai tashiga yi dak'yar ta iya bud'e baki tace dan Allah yarima kayi hak'uri wlh sharrin shaid'anne.
Murmushi yarima yayi cikin rashin damuwa yace Sumayya kidaina cewa Sharrin shaid'anne, duk abinda kikayi daidai dake ne bazan yi komai akaiba dan da hankalinki saidai ina gargad'inki da kiguji lokacin da zaki kaini k'arshe dan wlh had'uwarmu bazatayi miki kyau ba....fuskarsa a d'aure kamar wanda bai ta6a dariyaba yace ina kika ajemin files d'ina?
Hannunta yana rawa tayi mai nuni da chan saman wani d'an k'aramim table.
Yarima zuwa yayi yad'auka batare da ya k'ara kallon inda takeba yawuce zai fita daga d'akin, cikin sauri Sumayya tabiyosa tace please yarima kasau.....hannu yad'aga mata sannan yaficce yabar d'akin.
Sumayya na ganin fitarsa nan taduk'e k'asa tashiga rusa sabon kuka cike da bak'in ciki da danasi, ita ba pills d'in da yarima yakamata da su bane yafi tayar mata da hankali, kawai tana tsoron labarin yaje ma su dada dan idan labari yakai musu ta san kashinta ya bushe, cikin sauri tamik'e tajanyo wayanta talalubo number d'in mahaifiyarta takira, sultana sadiya tana yin picking taji kukan sumayya ya cika wayan, a rud'e tace lafiya sumayya? Me yake faruwa?
Sumayya duk yadda taso tayi magana kasawa tayi kuka kawai take,,,sultana sadiya ta yi tambayar ammah ba amsa sai kuka, k'ulewa tayi tadakama sumayya tsawa tace ke ni kinutsu kiyi min bayani!
Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace ummah yau nashiga ukku asirina ya tonu wajen yarima kuma nasan sai su memartaba sunji.
a chan 6angaren sultana sadiya da take tsaye zama tayi tace sumayya me kika aikata?
Sumayya k'ara fashewa tayi da kuka tace ummah ya shigo ya kamani da pills.
Zaro ido sultana tayi cikin fad'a tace sumayya anya kina da hankali? Ban gargad'ekiba akan yin family planning? Ke wace irin kidahumace, wlh kije na gama shiga subgarki tunda ke bakida wayau, toh yanzu ga kishiyarki chan da ciki k'ila idan tahaihu zaki dawo cikin hayacinki.
Sumayya k'ara rushewa tayi da kuka tace ummah dan Allah kitaimaka min wlh na daina daga yau,
Sultana tsaki taja cikin 6acin rai tace kar ma Allah yasa kidaina inma wani yake zugaki kina wannan iskancin toh ba abu bane mai kyau, kin barni ina ta fama wajen ganin na taimakeki anzubar da cikin wata ashe ke kina nan kina d'irkan maganin hana haihuwa, kije kawai kiyi yadda kikeso ni na zare hannuna ga lamurranki....sultana sadiya tana fad'in haka takashe wayanta.
Sumayya tana jin sultana sadiya ta kashe wayan, dafe kanta tayi tacigaba da rusa wani irin kuka, tunowa tayi da zinat cikin sauri tanemo number d'inta tayi dialing.
Har tatsinke zinat batayi picking ba, tana shirin k'ara kira saiga kiran zinat ya shigo, cikin sauri sumayya tayi picking.
Zinat cikin muryar bacci tace ya dai baby,
Sumayya fashewa tayi da kuka tace zinat na shiga ukku.
Zinat cikin tashin hankali tace sumayya me yake faruwa? Wanine yarasu?
Sumayya cikin kuka tace zinat asirina ya tonu wajen yarima ya gano ina amfani da pills.
Tsaki zinat tayi tace toh sai me dan ya gane?
Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace sumayya kinsan abinda kike cewane? Ko bakiji abinda nace mikiba.
Zinat murmushi tayi tace haba sumayya ni wlh kunya kike bani yanzu saboda Allah saboda d'an wannan abun kike 6arnan hawayenki?
Sumayya shuru tayi tana saurarenta fuskarta d'auke da mamaki.
Zinat jin batayi maganaba yasa tace baby kikwantar da hankalinki kimori rayuwa kar ki saki kiyarda kifara haihuwa yanzu dan wlh zakiyi saurin tsufa kuma daga inda kika fara haihuwa yara duk sai sun rikitaki bakida lokacin kanki, kuma mijinki zaiyi baya da ke.
Sai a lokacin sumayya tayi magana tace zinat kifahimceni wlh yarima yana son haihuwa.
Tsaki zinat tayi tace kefa matsalata dake kenan baki ganewa, kinsan daga inda kika fara aje 'ya'ya komai zaibi ya jagule miki mijinkima zai fara tunanin k'ara aure dan gaba d'aya zaki gunduresa, kibari kawai sai shekara mai zuwa lokacin kin tara abinda kika tara na dukiya a lokacin mijinki yana muradin 'ya'yan sosai toh zakiga rawan kai wajensa dan bazai k'ara yarda yayi nisa da ke da babynkiba, indai kuma kina tunanin cikin wannan bagidajiyar yarinyar ne toh kidaina tunani kikwantar da hankalinki dan da nazo zai tashi aiki.
Sumayya cike da gamsuwa da maganar zinat tace hakane saidai yanzu ummah ta yi fushi da ni bansan ya zanyiba.
Dariya zinat tayi tace kar kidamu zan fad'a miki yadda zaki shawo kan yarima da ummah.
Sumayya murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai zinat saisa nake k'ara sonki.
Dariya zinat tayi tace bakomai baby nima kinsan ina sonki sosai insha Allahu nan da upper week zan shigo garin, Sumayya wani irin farin ciki taji ta dabaibayeta tace kai baby ammah wlh naji dad'i kuma nayi murna, ji nake kamar injawo lokacin yayi.
Dariya zinat tayi tace kai baby gaskiya naga alama kinyi missing d'ina sosai, yanzu dai bari inje bank zan yi miki depositing d'in wasu kud'i idan nagama komai zan kiraki muyi magana.
Sumayya ciki jin dad'i tace ohk dear sai najiki.
Yarima koda yakoma part d'insa tisa files d'in yayi gaba yana kallo ya kasa cigaba da aiwatar da komai, tausayin zarah ne da nadamar abinda yayi mata suka kamasa, dan tabbas ya san zarah ta cika mace ta gari tunda tana d'auke masa buk'atunsa kuma har ta amince tayi renon cikinsa abinda 'yar uwarsa ta jini takasa, tunowa yayi da wulak'ancin da yakeyi mata tsaki yaja tare da dafe kansa yace ya akayi hakan ya kasance? Tabbas nasan zarah fushi take da ni, ji yayi duk ba dad'i dan haka yamik'e yafito yanufi part d'inta.
Yarima ahankali yatura k'ofa yashiga ganin babu kowa parlour yasa direct yanufi bedroom d'inta.
Zaune yahangota saman gadonta ta buga tagumi, zarah juyowa tayi takallesa wani irin dad'i taji a ranta sannan tajanye idonta daga kallonsa,
Yarima tsaye yayi yana k'are mata kallo ta d'an rame, duk sai yaji ba dad'i,,,ahankali yataka yanufi inda take daga gefen gadon yazauna,
Kallon zarah yayi da tad'auke kanta tak'i kallonsa tabbas ba k'aramin fushi take da shiba, hannu yakai yarik'o nata gabad'ayansu wani irin shock sukaji a jikinsu yarima runtse idonsa yayi ahankali yafurta zarah....shuru yayi maganar ta lak'afe a mak'ogoronsa dan baisan ta inda zai faraba.
Har a lokacin fuskar zarah a d'aure take kuma bata juyo takallesaba tana dai saurare taji abinda zai ce mata,
Chan k'asan mak'oshinsa kamar wanda akayi ma dole yace please kiyi hak'uri.
Ba zarah ba hatta shi kansa yarima da yayi maganar saida yaji wani iri dan a karo na biyu da zarah taciri tuta yaimata abinda bai ta6a yi ma waniba bayan iyayensa shine kalman hak'uri,
Zarah fizge hannunta tayi tamik'e cikin sauri tanufi toilet, yarima kiran sunanta yashigayi ammah ina tuni ta shige nan tamaida tarufe,
Cike da takaici yarima yadafe kansa da hannuwansa biyu shi kansa ya san tabbas ba k'aramin 6atama zarah rai yayiba a karo na farko da yaji haushin kansa ya kamasa dan gaba d'aya zuciyansa zafi take masa.
Ya dad'e zaune saida yayi kusan 30minutes ganin batada niyan fitowa yasa yamik'e jiki babu k'wari yafita yabar d'akin.
Zarah tunda tashiga toilet d'in kuka tashiga rerawa ita kanta batasan tak'amaiman dalilin da yasa take kukanba, saida taji fitar yarima sannan tawanke fuskarta tabud'e k'ofan tafito tahaye saman gadonta takwanta tana sheshek'ar kuka.
Shi kansa yarima duk ji yayi ba dad'i dan gaba d'aya ji yake komai ya kwancemasa duk wanda yakallesa sai yasan yana cikin damuwa, koda yakoma part d'insa key d'in motansa yad'auka yafita yabar gidan yaje gidan gona.
A saman 3 seater d'in da take parlourn yakwanta gabad'aya shi kansa ya rasa gane tak'amaiman abinda yasa duk yacanza dan wani iri yakejinsa daga k'arshe kallo yakunna nan yazauna yana kallon wrestling.
A nan yayi sallar isha'i sannan yakama hanyan gida.
Koda yakoma gida, part d'in zarah yakallah har zai wuce nasa sai kuma yaji baya iya wucewa dan haka yafasa yanufi part d'inta, a parlour yasamu kuyanginta zaune baibi ta gaisuwar da sukeyi masaba yawuce yanufi bedroom d'inta.
Lokacin zarah tana kwance saman darduma tana tasbihi, k'amshin turarensane da taji yasa tagane ya shigo d'akin, cikin sauri tamaida idanunta tarufe kamar mai bacci,
Yarima tsaye yayi yana kallonta dan duk atunaninsa baccin takeyi, ahankali yatako ya iso inda take duk'awa yayi yad'auketa yanufi gado da ita.
Koda yakwantar da ita zama yayi gefenta ahankali yazare mata hijab d'in da take jikinta sannan yazuba ma fuskarta ido ganin yadda tayi fayau da ita.
Zarah ahankali take safke numfashi kamar irin na masu bacci, tana jinsa yakai hannu yad'age mata rigar da take jikinta nan yashiga shafa cikinta, duk'ar da kansa yayi yai kissing d'in cikin sannan yagyara mata rigarta yajanyo blanket yalullu6eta.
Mik'ewa yayi yanufi k'ofa koda yabud'e saida yajuyo yakalleta sannan yafita tare da rufe mata k'ofan.
Zarah tana jin fitansa tabud'e idonta, yaye blanket d'in tayi tamik'e taje tamurza ma k'ofanta key sannan taje tayi wanka tayi shirin baccinta takwanta.
Yarima ma koda yakoma part d'insa wanka yayi yashirya sannan yahau saman gadonsa yakwanta, ina nan bacci yace baisan batunba, haka yaita juyi, nan zarah tacigaba da fad'o mai a rai ko ya runtse idonsa ita kad'ai yake gani duk yadda yaso yajanye tunaninta a ransa kasawa yayi, yarima ya ja tsoki ya fi sau goma a lokacin, sai daga baya yasamu bacci yad'aukesa.
____________
Dasafe bayan yarima ya gama shirinsa yana shirin fita sai ga sumayya ta shigo d'akin, kallo d'aya yayi mata yad'auke idonsa nan gabad'aya fara'ar da take a fuskansa tagushe.
Sumayya bata damu da yanayin da tagansaba zuwa tayi tazauna gefensa cikin kwantar da murya tace please yarima kayi hak'uri kayafemin abinda na aikata insha Allahu bazan k'araba na daina.
Ko inda take bai kallaba yashareta,
Sumayya marairaicewa tayi tace dan Allah kayafemin na yi maka alk'awali wlh bazan k'araba.
Wani irin kallo yarima yawurgamata sannan yace sumayya duk abinda kika za6a ma kanki daidai da ke ne, bana bak'in cikin hakan,
Shuru yad'anyi na lokaci kad'an sannan yace a tunaninki mata nawa suke bibiyata, mata nawa duk'awa suna rok'ona sukeso in auresu? Ke kin samu dama saisa kike yadda kikeso, hanya yanuna mata yace tun kan mutuncinki ya ida zubewa a idona tashi kifita kiban waje.
Sumayya kallonsa tayi taga babu alamun wasa a fuskansa dan haka tayi sauri tamik'e, tsayawa tayi gabansa tace please yarima ka.....wani irin kallo yawatsa mata cikin sauri tajuya tafita tabar d'akin.
Binta yayi da kallo cike sa takaici dan gani yake duk ita taja zarah take fushi da shi, tsaki yaja sannan yamik'e yad'auki wayansa da key d'in mota yafito.
Part d'in zarah yawuce dan yadubata saboda baya jin dad'in fushin da take da shi.
yana shiga zaune yatarar da ita a parlour saman cushin ta ci kwalliyanta tana sanye cikin english wears riga da skirt ta tufke gashin kanta, gabanta cup d'in coffee ne aka d'aura saman table.
Yarima tsaye yayi yana kallonta dan gabad'aya taso tarikitasa da yaganta, zarah d'ago kai tayi suka had'a ido saida gabanta yafad'i cikin sauri tajanye idonta daga kallonsa dan ita kanta saida tasamu tasaita nutsuwanta.
Takowa yayi yazo inda take zaune daga gefenta yazauna gab da ita nan yazuba mata ido, sharesa zarah tayi tad'auke kanta gefe kamar batasan da zamansaba.
Yarima ma janye idonsa yayi daga kallonta nan sukayi shuru gabad'ayansu, ganin batada niyar yin magana yasa yarima yace ke baki iya gaisuwaba?
Zarah d'aure fuska tayi kamar ba zatayi maganaba sai kuma chan tace ina kwana?
Shuru yarima yayi kamar bai jitaba saida yayi kusan minti d'aya sannan yace ya kike?
Ta6e baki zarah tayi sannan tace lafiya,,,,,tana fad'in haka tamik'e zatabar wajen.
Cikin sauri yarima yajanyota tafad'o jikinsa, ido suka zuba ma junansu zarah cikin sauri taruntse idanunta, yarima cigaba yayi da kallonta sai chan yakai hannunsa yashafi k'ashin wuyanta, ahankali kamar mai rad'a yace baby bakison cin abinci duk kin rame.
Zarah shuru tayi tak'yalesa tana ji yatura hannunsa cikin rigarta yana shafa cikinta tare da kwantar da kansa saman k'irjinta, su dukansu cikin wani irin yanayi suka shiga
Zarah ce tafara dawowa cikin hayyacinta dan haka tabud'e idanunta tanemi taturesa ganin ta kasa yasa tafashe mashi da kuka,
Cikin sauri yarima yad'ago yakalleta yace lafiya?..
Cikin kuka tace ni kakyaleni.
Yarima batare da ya yi maganaba yasaketa nan cikin sauri tamik'e tashige bedroom d'inta.
Yarima binta yayi da kallo har tashige nan yamaida kansa yajingine da kujera haushi da takaicin kansane yakamasa, daga k'arshe mik'ewa yayi jiki ba k'wari yawuce yabar part d'inta.
_Comments_
*nd*
_Share_
0 comments:
Post a Comment