Ahaka yarima yaje wajen aiki ammah kwata-kwata baida kuzari, Dr khalil shi kansa saida yalura da yanayin yarima,,,,,ko da yatambayesa abinda yake damunsa yarima banza yayi dashi yak'yale, kan dole Dr khalil yaja bakinsa yayi shuru dan ya san kome zaiyi toh bazai samu amsar tambayarsaba.
Zarah koda tashige bedbroom d'inta saman bed d'inta tafad'a tashiga tacigaba da kukanta wani irin son yarima ne yake fizgarta daga gefe guda kuma haushinsa takeji,,, ahaka tasha kukanta saida taji yunwa tana niyar yi mata illah sannan tamik'e taje wanko fuskarta tafita tad'auki coffeenta tasha.
Sumayya koda yarima yakoreta daga part d'insa bata wani damuba sosai cikin ranta cewa tayi na zan hanyar da zan 6ullo maka,,,,daga nan wucewa tayi tatafi turakar iyayenta.
Tana shiga a parlour ta tarar da sultana sadiya kishingid'e tsakiyan kuyanginta suna ta yi mata hidima, ganin sumayya yasa suka zube gabad'ayansu suna kwasar gaisu sumayya ko kallon inda suke batayiba ganin haka yasa cikin sauri suka ficce daga parlourn gudun kar suyi laifi.
Sultana sadiya tana ganin sumayya ta shigo nan tahad'e fuska babu alamun fara'a ko kad'an a tare da ita.
Sumayya jiki ba k'wari tazo tazauna gefenta ahankali tace ummana.
Sultana sadiya batare da ta kalletaba tace me yakawoki wajena.
Sumayya fashewa tayi da kuka tare da fad'awa jikin sultana sadiya, shuru sultana tayi tak'yaleta.
Cikin kuka sumayya tace ummah dan Allah kiyi hak'uri wlh na daina.
Sultana sadiya sai a lokacin ta kalleta tace sumayya kikyaleni kawai tunda bakyajjn magana kije kawai na sallamaki wajen wad'anda kike jin maganarsu.
Sumayya Cikin kuka tashiga girgiza kai ahankali tace ummah wlh ina jin maganarki akasine kawai aka samu kuma insha Allahu na daina bazan k'araba, dan Allah kiyafe min wlh duk na zubar da pills d'in.
Sultana sadiya cike da tausayin d'iyartata tashiga d'an bubbuga mata bayanta kad'an cikin sigar lallashi tace toh shikenan sumayya na hak'ura ammah dan Allah kidaina irin haka kinsan idan labari yajema su dada bazakiji da kyauba ke kinsan ko mahaifinki yaji sai kashinki ya bushe.
Sumayya share hawayen fuskarta tayi cikin jin dad'i tace insha Allahu ummah ba zan sakeba.
Murmushi sultana sadiya tayi tace yauwa d'iyata, yanzu sai kije kisamu kilallashi wanchan miskilin mijin naki ko shima ya safko, Allah yaimiki albarka.
Ameen ummana, insha Allahu zan k'ara bashi hak'uri....nan tazauna sukasha hira da ummah cike da jin dad'i sannan daga baya tayi mata sallama tafito tanufi turakarsu dada dan tagaisheta.
koda tashiga fuskarta d'auke da murmushi taduk'a tagaishe da dada,
Cikin jin dad'i dada ta amsa mata nan sumayya tazauna gefen dada tana murmushi tace 'yar tsohuwa me kika ajemin?
Ido dada tazuba mata tace me fa zan aje miki bayan gakinan kinyi 6ul-6ul da ke kin koma d'imemiya wai mi wanchan miskilin yake d'irka miki?
Dariya sumayya tayi tace wlh dada hutune kawai,,,dada cikin rashin yarda tace kodai mun samu k'aruwane?
Girgiza kai sumayya tayi tace wlh dada banda komai.
Rik'e ha6a dada tayi tace sumayya kodai zakije asibiti aduba lafiyanki, tunda shi wanchan miskilin bai damu da hakanba.
Dada na je ance lafiya ta lau fa kawai dai lokacine baiyiba.
Ajiyar zuciya dada tasafke sannan tace toh Allah yanuna mana lokacin, Allah yasa ina da rabon ganin d'an cikinki.
Dariya sumayya tayi tace Ameen dada.
Ho 'yar nema ko kunyata bakyaji....cewar dada.
Dariya sumayya tashiga yi tace kunya ai ya wa-ne yanzu.
Dak'uwa dada tayi mata tace gidanku sumayya, ja ira kawai.
Sumayya tsagaitawa tayi da Dariya da take tace afuwan ranki yadad'e na daina.
Murmushi dada tayi tace toh ya wajen 'yar uwartaki ina fata tana lafiya.
Ta6e baki sumayya tayi tace inaji lafiya lou take.
Sakin baki dada tayi tana kallonta tace sumayya ban fahimcekiba? Kar dai kicemin baku zaman lafiya.
Sumayya k'wallah ce tacika mata ido tace toh dada ya zanyi yarinyar da bata k'aunata kullum batada aiki sai had'ani da mijina, ni me natsare mata da zata dinga min haka.
Dada da mamaki take kallon sumayya tace sumayya yanzu yarinyar nan da nake gani kamar babu ruwanta itace takeyi miki haka?
Hmm dada kenan kawai dai abar maganar dan in kikaji wasu abubuwanma da takeyi sai kinyi mamaki, ni yanzu babbar matsalata fushin da yarima yakeyi da ni kusan kullum sai ta had'amu.
Dada salallami tashiga yi tace na shiga ukku ni Asma'u, yanzu saboda Allah yarinya tazo tararar da ke gidan mijinki sannan tace zatayi miki irin haka?
Toh kibarni da yariman yadawo zan gansa idan shi bazai iya d'aukan matakiba a kai toh ni zan d'auka ko inhad'asa da memartaba tunda shi yana jin maganarsa.
Cikin jin dad'i sumayya tace yauwa Dadata ammah dan Allah kar kifad'ama yarima ni nafad'a miki dan wlh zai iya kakkaryani.
Cike da tausayin jikartata dada tace kar kidamu sumayya insha Allahu bazan ceba, kuma ko na ce ai bai isa yata6akiba dan ko dole inrama miki.
Cikin jin dad'i sumayya tace kibarsa kawai Dada ni zaman biyayya da hak'uri kawai nake da shi, duk abinda yayi min dan kansa, dan na ma fi ganin laifin wacchan munafukar matar tasa mai mugun hali.
Tsaki Dada taja tace kibarni da su kawai,
haka sumayya tazauna tayi ta 6ata zarah a wajen dada nan Dada tahau tazauna tana ta jimamin halin zarah.
Yarima koda yadawo wanka yayi yashirya sannan yad'anci lunch kad'an, yana gamawa fita yayi yanufi part d'in zarah dan kwata-kwata yanzu wani iri yakeji game da ita rashin zuwanta part d'insa ba k'aramin d'aga mai hankali yakeba.
Yana shiga bedroom d'inta daidai lokacin tafito wanka d'aure take da towel tana tsaye gaban dreesing mirror tana yin shafa.
'Dago kai tayi takallesa nan suna had'a ido tajanye fuskarta daga kallonsa, yarima tsaye yayi yana kallonta batare da yayi maganaba.
Tana gamawa tawuce tanufi wajen wardrobe d'inta tabud'e tad'auko kayanta, juyowar da zatayi sai ganin mutum tayi bayanta tsaye, k'ara d'aure fuska tayi ta ra6a ta gefensa zata wuce yarima jawota yayi tafad'o jikinsa yarungumeta,
K'ok'arin turesa tashiga yi nan yak'ara matseta a jikinsa ahankali yace wai ke meyasa kike min haka?
Harararsa zarah tayi tace wani abu kaga na yi maka?
Zuba mata ido yayi yana kallonta da mamaki sannan yace dan kinga ina lalla6aki saisa kike min yadda kikaga dama
Ta6e baki zarah tayi tace kar ma kalalla6ani indai nice na gama shiga sabgarku tunda daman sai kunga na shiga sannan zaku sami daman wulak'antani,,,,fashewa tayi da kuka tace ni duk abinda sumayya takemin me nata6a cewa shine ni kamar jira ake ko banyi mata wani abuba sai ace na yi toh ya kukeso inyi!!! tak'arashe maganar cikin d'aga murya.
Yarima shuru yayi yakasa magana sai chan yarungumeta a k'irjinsa tare da runtse idonsa yana jin wani iri a ransa,,,ahankali kamar me rad'a yace ix owk zarah, insha Allahu hakan ba zai k'ara faruwaba,
Zarah janye jikinta tayi daga nasa tawuce zatabar wajen, kallonta yarima yayi yace wai ke dan kin samu ina lalla6aki shine kike min haka?
Zarah juyowa tayi takallesa sannan tace toh ni me kaji na ce maka?
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayarsa tafara ringing,,,d'aukowa yayi yaduba ganin me kiransa yasa yayi picking tare da yin sallama.
Daga chan 6angaren dada amsa mashi tayi sannan tace toh dodo kazo yanzu ina son ganinka.
Yarima kallon agogon hannunsa yayi sannan yace yanzu kuma?
Cikin fad'a dada tace eh, inkuma bazakazoba saboda ka rainani toh sai infad'ama ubanka shi sai yasa kazo.
Yarima shuru yayi baice komaiba.
Jin ya yi shuru yasa dada tace ko bakaji abinda naceba?
Cikin k'osawa da maganar yace ganinan,,,,yana fad'in haka yakashe wayar ko inda zarah take bai kallaba yawuce yafita yabar d'akin
Zarah da ido tabisa har yatafi sannan tad'auki kayanta tasaka, cikin ranta ji take daman batayi ma yarima hakaba.
Yarima koda ya isa turakar su dada a parlour yasameta zaune tana jiransa, ko da yayi sallama ciki-ciki ta amsa masa, saman d'aya daga cikin kujerun yazauna cikin girmamawa yagaisheta.
Amsa masa dada tayi daganan d'akin yad'au shuru ba wanda yak'ara magana, ganin baida niyar yin magana yasa dada tace toh d'an nema watau shine kayi zaune baka ma jin zaka iya tambayata dalilin kiran da nakeyi maka.
Murmushi kawai yarima yayi batare da ya yi maganaba.
Dada gyara zamanta tayi ta fuskanci yarima sosai sannan tace suhail na ji abinda kakeyi ma 'yar uwarka kuma na gode ba ita kayimawa ba ni kayimawa.
Da mamaki yarima yake kallonta har saida takai aya sannan yace ranki yadad'e wani abu tace na yi mata?
Harararsa dada tayi tace kai kar kamaidani k'aramar yarinya ko ka d'auka duk abinda kukeyi mata kai da matarka bai dawowa a kunnena?
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa nan yacigaba da dannar wayarsa da take hannunsa.
Nan dada tacigaba da cewa Toh bari kaji ko kaso ko kak'i sumayya 'yar uwarkace kuma za6inmu ce sannan wannan aure naku mutuwa kawai zai raba, ita wacchan matar dan kaga za6inka ce saisa kake ma 'yar uwarka wulak'anci son ranka kuma inaso kasani ciki Allah yake bayarwa kuma itama sumayya in da rabo zata haihu.
Yarima banza yayi mata kamar ba da shi take maganaba,,,dada k'ulewa tayi ganin baida niyar yin magana tace watau ga sakarya tana magana bakaji ma zaka iya tankamin.
Saida yarima yayi Kusan minti biyu sannan yad'ago yakalli dada da tatsaresa da ita, murmushi yayi sannan yace toh ranki yadad'e na ji.
ta6a hannu dada tashigayi tace na shiga ukku yanzu saboda Allah suhail ni kake ma haka? Ko mahaifinka bai isa yayimin hakaba sai kai?
Shuru yarima yayi yakyaleta nan dada tayita masifarta daga k'arshe jingine kansa yayi da kujerar da yake zaune yamaida idanunsa yalumshe.
Dada tsura masa ido tayi takasa cigaba da fad'an dan gabad'aya yarima ya gama kashe mata baki, cike da takaici tanuna k'ofa tace tashi kafita kabani waje.
Yarima bud'e idonsa yayi tare da d'aukan wayansa yace na barki lafiya.
Dada binsa tayi da kallo har yaficce takaici yacikata saisa batason wani abu yahad'ata da yarima dan takaici kawai take kwasa, cikin ranta kuma tana jinijna ma halinsa, ahankali tace wannan mutumin halinsa sai shi, ina amfanin miskilanci irin haka, lallai matansa da suke zaune da shi suna k'ok'ari.
Yarima koda yafita daga nan 6angaren iyayensa yawuce, ko da yashiga parlour ummi batanan, bakowa ciki, dan haka yasamu waje yazauna tare da dafe kansa dan shi gabad'aya anhad'a masa zafi dayawa tsaki yaja yace ta ko'ina ba sauk'i.
Sultana bilkisu da tafito daga bedroom tsaye tayi tana kallon d'an nata da gabad'aya hankalinsa baya a jikinsa, cike da tausayinsa tataka ta isa inda yake daga gefensa tazauna, Sai a lokacin yarima yad'ago yakalleta nan yasakarmata murmushi.
Sultana bilkisu ma maida masa martani tayi sannan tace my son lafiya naganka nan zaune?
Yarima duk'ar da kansa yayi yace ummina barka da rana.
Ido tazuba mai tace dafatan kuna lafiya?
Lafiya lou ummi.
Toh ya wajensu sumayya da zarah.
saida yajingine kansa da kujera sannan yace duk suna lafiya.
Toh ya d'iyartawa da jiki?
Yarima d'an sosa kai yayi alamun jin kunya sannan yace ummi dasauki.
Toh masha Allah, Allah yaraba lafiya.
Shuru Yarima yayi baice komai ba.
Sultana bilkisu rik'o hannunsa tayi tace my son me yake damunka?
Yarima kallonta yayi yana murmushi yace bakomai ranki yadad'e.
Sultana bilkisu batayi mamakin jin hakan daga garesaba dan ta san halin d'an nata, murmushi tayi tace shikenan ammah dan Allah kadinga hak'uri ka san ganinka cikin irin wannan yanayi ba k'aramin d'agamin hankali yakeba.
Yarima kwantar da kansa yayi saman cinyar ummi yace kar kidamu ummina babu abinda yake damuna kawai dai ji nayi inaso inzo inganki.
Cikin jin dad'i sultana bilkisu tashiga shafa gashin kansa tace Allah yaimaka albarka my son.
Ameen ummina....nan Yarima yamaida idanunsa yalumshe, sultana bilkisu tazuba mai ido tana kallon d'an nata cike da so da k'auna.
Tun daga lokacin Yarima yadaina shiga harkar kowa dan yanzu tun safe idan yafita baya dawowa sai wajen 9pm saboda meeting da suke zama, kuma idan yadawo sai ya gargad'i guards d'insa akan kar subar kowa yashigo masa hutawa yakeson yi.
ba zarah ba hatta ita kanta sumayya saida tad'an shiga damuwa.
_*After one week later*_
Yau yarima kasancewar bai fitaba zaune yake d'akinsa a parlour yana kallo zarah ce tashigo da sallamarta.
Yarima batare da ya juyo ya kalletaba ya amsa, zarah wani irin sanyi taji a ranta da tagansa, takawa tayi ta isa inda yake zaune da mamakinsa sai gani yayi ta zauna saman cinyarsa,
Sai a lokacin yarima yakalleta shi kansa wani irin sanyi yaji a ransa, zarah k'irjinsa tashige tare da fashewa da kuka.
Runtse idonsa yarima yayi yana jin kukan nata har cikin ransa, rungumeta yayi muryarsa tana rawa yace zarah me yake samunki?
Zarah tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace akwai abinda yake samuna bayan wanda kayi min?
Ido yarima yazuba mata batare da ya ce komai ba,
cikin sheshek'ar kuka tace shine kagujemin kadaina shiga sabgata gabad'ayama kadaina zaman gidan.
Yarima tallabo fuskarta yayi yace toh ya kukeso inyi muku naga kamar kinfison hakan, kefa kikace kin daina shiga sabgata saisa nabarki kihuta.
Zarah rungumesa tayi tace hakan da kayi ba k'aramin d'agamin hankali yayiba dan Allah kayi hak'uri na daina.
Yarima kallon cikin idonta yayi sannan yace meyasa bakison cin abinci?
Zarah turo baki tayi tace taya zanci abinci bayan babynka yana matsamin ina tunanin missing d'in daddynsa yayi......tak'arashe maganar tare da kashe mashi ido d'aya,
Yarima hannunsa yakai cikin rigarta yana shafar cikinta, zarah maida idanuwanta tayi talumshe tana jin dad'in hakan da yakeyi mata.
Gabad'ayansu shuru sukayi ba wanda yak'ara magana, ahankali taji hannunsa suna yawo cikin rigarta,
Chan kuma sai ya janye hannunsa daga cikin rigarta yace tashi muje kici abinci,
Zarah d'ago kai tayi takallesa tare da turo baki tace nifa na k'oshi.
Yarima zuba mata ido yayi sannan yace ammah ai ga shedanan yau bakici abinciba.
Zarah kamar zatayi kuka tace ni ice cream nakeson sha,
Jan hancin yarima yayi sannan yace toh kije kici abinci zan bayar asiyo miki,
Zarah mik'ewa tayi tana gyara rigarta sannan tace toh ammah fa kad'an zan ci.
'Daga kai kawai yarima yayi batare da ya yi maganaba.
Juyawa Zarah tayi tafita tabar d'akin, nan yarima yakoma saman 3 seater yakwanta yana ci gaba da kallonsa yana jin wani irin nishad'i a ransa.
Daga k'arshe yamik'e yazari key d'in motarsa yaficce yabar gidan.
Zarah koda takoma part d'inta kad'an taci abincin nan tazauna zaman jiran yarima yakawo mata ice cream d'in ammah shuru, zuwanta biyu part d'insa ammah baya nan.
Ahaka har akayi sallar isha'i taje tayi wanka tai shirin baccinta,,,,tana cikin saka night gown d'inta sai ga kiran yarima ya shigo wayanta cikin jin dad'i tayi picking kamar zatayi kuka tace shine kabarni ina ta jiranka.
Daga Chan 6angaren yarima cemata yayi tazo ta amsa gashinan.
Cikin jin dad'i Zarah tace toh.
Cikin sauri ta ida shirinta tafito tanufi part d'in yarima.
Tana shiga ganin baya parlour yasa tawuce bedroom d'insa ahankali tatura k'ofan tashiga, saman gadonsa tahangosa zaune yana ta waya hannunsa rik'e da paper da biro yana rubutu.
Takowa tayi ta iso bakin gadon, d'ago kai yarima yayi yakalleta sannan yai mata nuni da ledar da take aje k'asa.
Cikin jin dad'i zarah taje tad'auki ledar, a nan k'asa tazauna tabud'e tad'auko d'aya sannan tatashi tasaka sauran cikin freezer d'insa.
Dawowa tayi tad'auki wanda ta aje taje gefensa tazauna tabud'e tana sha.
Har a lokacin yarima yana ta 'yan rubuce-rubucensa, zarah ahaka tashanye sannan taje toilet d'insa tawanke bakinta.
k'arshen gadon taje takwanta tana kallonsa yana ta wayansa, daga k'arshe da taga wayar batada niyar k'arewa dan haka tamik'e takoma gefensa tazauna, marairaicewa tayi ahankali tace wai wayar ba a gamata hakanan dare fa ya yi.
Kallonta yarima yayi nan zarah tad'aga mai gira,
idanuwansa yamaida ga agogon da take manne ga bangon d'akin ganin har 11pm ta yi yasa yayi sallama yakashe wayar.
Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido sannan yace bazaki kwantaba?
Zarah batare da tayi magana ba tamik'e taje takwanta, yarima kashe gloves d'in d'akin yayi sannan shima yahau gadon daga gefen zarah yakwanta.
Zarah tana ganin ya kwanta nan tamaida kanta saman k'irjinsa, yarima kamar daman jira yake nan yarungumota jikinsa tare da k'ok'arin rabata da rigar jikinta, yana cirewa Zarah tazame jikinta takoma gefe,
numfashi yarima yaja, cikin kasalalliyar muryarsa yace ya dai?
Zarah cikin tsokana tace ni bacci nakeji.
Yarima matsawa yayi gab da ita sannan yace tun d'azu me yahanaki baccin?.
Zarah turo baki tayi har ta bud'e baki zatayi magana sai ji tayi yarima ya had'e bakinsu waje guda yafara kissing d'inta cikin k'warewa,
Zarah gabad'aya tafita hayyacinta inda kowane 6angare na jikinta yake kar6an sak'onsa, k'ara rungumesa tayi jikinta ita kanta ta san ta yi missing d'insa.
nan yashiga sarrafata son ransa, har tagaji ammah yak'i barinta daga k'arshe kuka tasa mashi ammah Yarima baima san tana yiba dan gabad'aya hankalinsa baya tare da shi.
Saida yagaji dan kansa sannan yabarta zarah chan gefe takoma takwanta tana sheshek'an kuka.
Yarima duk sai yaji ba dad'i dan haka yajanyota jikinsa batare da ya yi maganaba yashiga d'an bubbugamata baya alamun lallashi.
nan zarah tarage sautin kukan nata daga k'arshe bacci yayi awon gaba da ita.
Yarima na jin ta yi bacci yajanyeta daga jikinsa yalullu6eta da blanket sannan yatashi yanufi toilet dan yayi wanka.
Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yahau gadon yakwanta tare da jawo zarah jikinsa yarungume yana shafar cikinta d'an wata biyar, a haka bacci yad'aukesa
Da asuba saida yayo alwallah sannan yatayar da zarah yawuce masallaci.
jikinta duk ciwo yake haka tajanyo kayanta tasaka tafita takoma part d'inta, a chan tayi wanka tad'auro alwallah tai sallah bayan ta gama tahaye saman gadonta takoma bacci.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
*PAGE* 5⃣5⃣
Bayan sallar la'asar yarima zaune yake saman cushin daga gabansa table ne ya d'aura laptop d'insa yana dannawa yanayin yadda yamaida hankalinsa gabad'aya akan laptop d'in zai tabbatar maka da abu mai muhimmancine yakeyi.
Sumayya kamar anjefota tashigo d'akin ba ko sallama.
Yarima d'ago kai yayi yakalleta sannan yacigaba da abinda yakeyi,
Takowa tayi ta iso inda yake, tsaye tayi gefensa fuskarta a d'aure tace haba yarima gaskiya bakayimin min adalci.
Yarima d'ago kai yayi yakalleta fuskarsa ba alamun wasa yace ke baki iya sallama ba?
Ta6e baki Sumayya tayi sannan tace a inda yadace ake sallama, nidai na fad'a maka kaji tsoron Allah, kuma inma laifi nayi maka ai na baka hak'uri.
Ture laptop d'in yayi gefe tare da d'ago kai yakalleta cikin 6acin rai yace ke matsalata da ke bakida isassar tarbiya yanzu haka ake magana da miji?
Sumayya kallonsa tayi cikin 6acin rai tace nice banda tarbiya? lallai yarima nagode, ammah inaso kasani ba babbar marar tarbiya sai wacchan d'iyar matsiyatar da ka auro wadda talauci yai mata..... yarima a fusace yamik'e tsaye, marin da ya wanka matane yasa takasa k'arasa maganar.
Da mamaki Sumayya take kallonsa tace yarima ni kamara?
Nunata yayi da yatsa yace anmareki ko zaki ramane? Wlh Sumayya kikiyayeni na fara gajiya da wannan haukan naki, kuma wadda kike kira matsiyaciya Wlh ta fiki daraja a idona dan kwatakwata yanayin tarbiyanku ba d'aya bane,
Sumayya fashewa tayi da kuka tace wlh ba zan yardaba sai na rama abinda kayimin kuma sai na fad'ama dada saboda wacchan matsiyaciyar ka.... yarima k'ara wanketa yayi da mari yace indai kika k'ara kiranta da matsiyaciya wlh sai na takaki cikin d'akin nan kuma inda sabo toh kin saba had'ani da su dada saidai inaso kisani babu wanda ya isa yasani inyi abinda banyi niyaba, harara yawurga mata sannan yace fita kiban waje ko yanzu in6ata miki rai, shashashar banza.
Sumayya tana dafe da kuncinta tajuya saida takai bakin k'ofa sannan tajuyo tace kasaurareni zaka san ka ta6a Sumayya,,,,tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.
Yarima komawa yayi yazauna tare da dafe kansa zuciyansa tana masa wani irin zafi, takaicin Sumayya ne yacikasa cikin ransa yace ina amfanin auren irin wad'annan mata,,, daga k'arshe mik'ewa yayi yaje yashige bedroom d'insa.
Sumayya koda takoma part d'inta kuka take sosai takaicinta duk akan zarah yarima yayi mata mari biyu,,,nan tsanar zarah tak'ara kamata ji take kamar taje takashe zarah kowa yahuta,
Haka tawuni tana kuka, kiran zinat ne da yashigo wayanta yasa tatsagaita da kukan da take har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking.
Daga chan 6angaren zinat cewa tayi baby tun d'azun nake kiranki ammah bakiyi picking ba why?
Sumayya shuru tayi, zinat tace hello baby kina jina?
Sai a lokacin Sumayya cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace sorry bana kusa.
Daga chan 6angaren zinat dafe kanta tayi tace oh my god baby ke kullum bakida aiki sai kuka? Yanzu kuma wa yata6aki.
Sumayya cigaba tayi da kukan, cikin kuka tace dole kice haka zinat bakisan cikin halin da nakeba yau akan wacchan jakkar yarima yai min mari biyu.
Cikin d'aga murya zinat tace mari?
Sumayya cikin sheshek'ar kuka tace eh, wlh ba zan k'yaletaba sai na rama abinda yayimin akanta, inma saboda cikinta yaimin haka toh wlh sai na zubar da shi.
Ajiyar zuciya zinat tayi sannan tace baby kiyi hak'uri gobe zan shigo garin sai musan yadda zamu 6ullo ma lamarin dan wlh bazamu hak'uraba.
Koda Sumayya kuka take ammah kuma bai hanata murnaba, cikin jin dad'i tace dagaske kike baby gobe zakizo?
Dariya zinat tayi tace ai daman kiran da nake miki kenan kishirya gobe kina da babbar bak'uwa.
Hmm kinjiki da tsokana wai bak'uwa, ammah fa naji dad'i sosai baby ai dole inyi babban shiri, Allah yakaimu goben da rai da lafiya, wlh har kinja bak'in cikin da nake fama da shi ya ragu.
Dariya zinat tayi tace kai baby, yanzu dai bari inje inyi visa dan ta flight nakeson zuwa, me kikeso intafo miki da shi.
Shuru sumayya tayi kamar mai tunani sai kuma chan tace kiza6o min abu mai dad'i wanda zaisani farin ciki.
Ohk baby angama koma mekenan zan kiraki.
Sumayya kashe murya tayi tace baby kiyo shiri sosai dan gobe ba d'agi, kema kinsan nayi missing d'inki ga wanchan banzan kwana biyu rigima kawai muke bare ma ind'an samu sauk'i.
Dariya zinat tayi tace shikenan baby ai dole gobe mukasance da juna dan nima ba k'aramin missing d'inki nayiba, zan kiraki da anjima muyi magana.
Ohk baby sai najiki, nan sukayi sallama suka kashe wayan.
Sumayya hawayen fuskarta tagoge tace lallai gobe koma me za'ayi saidai ayi ammah sai nayi silar zubewar cikin chan nata, shi kansa sai ya gane kuskurensa na marina da yayi,,,murmushin mugunta Sumayya tayi sannan tamik'e tanufi toilet dan tawatsa ruwa saboda gabad'aya jikinta ciwo yakeyi mata.
A chan 6angaren zarah tana chan d'akinta kwance dan wata irin kasala takeji daga wanka sai sallah kawai suke tashinta, daga k'arshe da kwanciyar ta isheta tashi tayi tad'auko littafatanta na islamiyya takoma parlour tazauna tana nazari.
Bayan ta gama kiran ummi tayi a waya suka gaisa nan ummi take tambayarta idan akwai abinda take buk'ata.
Zarah tace bakomai ummi.
Toh indai kinji kina buk'atar wani abu kiyo waya kisanar da ni Zarah banason nok'e-nok'e ni uwace kinji?
Cikin Jin dad'i Zarah tace toh ummi insha Allahu, nagode sosai Allah yak'ara girma da d'aukaka.
Ummi ta ji dad'in addu'an sosai tace Ameen daughter adai cigaba da hak'uri,,,,nan sukayi sallama suka kashe wayan.
Murmushi Zarah tayi cikin jin dad'i dan har cikin ranta tanason matar.
Daganan takira su mama a waya suka gaisa.
Bayan sallar isha'i koda tagama shirinta kwanciyarta tayi part d'inta dan cewa tayi ba zata koma wajen yarima ba yak'ara wahalar da ita irin na jiya dan ita kad'ai tasan wuyar da tasha.
Yarima ma koda yagama shirinsa kwanciyarsa yayi dan shi kansa ya san inba sa'a ba dawuya yau Zarah tadawo, murmushi yayi wanda baisan ya su6uce masaba, shi kansa ya yi mamakin yadda yacanza haka cikin k'ank'anin lokaci, cikin ransa yace toh me hakan yake nufi?,, 6ari guda na zuciyansa yace kodai ka fara sonta?
Zumbur yayi yatashi zaune cikin d'aga murya yace hakan ba zai ta6a yuwuwaba, toh me hakan yake nufi?
Ahankali yace kawai dai na damu da itane saboda babyna da yake tare da ita ammah ban yarda cewa akwai macen da nakesoba dan har yanzu ban samu *ZA'BINA* ba, ajiyar zuciya yayi cikin gamsuwa da tunanin da yayi sannan yakoma yakwanta.
______________
sumayya tunda tatashi shirye-shiryen tarban zinat take daga tasa a girka wanchan sai a sauke a girka wanchan, part d'inta wani irin gyara yasha a ranar duk ma'aikatanta saida sukasan tana cikin farin ciki,
Kad'an kad'an ta kira zinat taji idan sun tafo, zinat dariya kawai takeyi mata tace har yanzu muna airport.
Yarima ne zaune part d'insa rik'e da laptop yana duba wasu drugs da yakeso ayo masa order d'insu, nan wayarsa tafara ringing, baibi ta kan wayarba saida yagama abinda yake sannan yad'auko yaduba ganin Aunty husna ce yasa yayi murmushi tare da yin dialing, tana yin picking yace ranki yadad'e big sis.
Daga chan 6angaren Aunty husna dariya tayi tace da girman kujerarka Yarima mai jiran gado, daman cewa nayi bari inkiraka inji inkananan kazo mugaisa gani a part d'in ummi tunda mu ka fi k'arfinmu baka iya zuwa inda muke yanzu.
Yarima k'ayataccen murmushinsa yayi mai k'ara bayyanar da kyaun fuskarsa sannan yace sorry sweet sis wlh ina ta so inshigo hidima ce tahana ammah yanzu bari inshigo sai muyi magana.
Murmushi husna tayi cike da k'aunar d'an uwan nata sannan tace ohk ina jiranka sai ka shigo.
Murmushi yarima yayi sannan yakashe wayan tare da mik'ewa yashiga bedroom d'insa saida yawatsa ruwa sannan yashirya cikin wata maroon d'in gizna nan kyaunsa yak'ara bayyan feshe jikinsa yayi da perfumes batare da ya sa hulaba yafito yad'auki wayoyinsa a parlour yawuce yafita.
A chan harabar gidan yatarar da shaheed tsaye rik'e da waya da alama neman number d'insa yake, murmushi yayi sannan yawuce yanufi wajensa, sai a lokacin shaheed yad'aga kai yakallesa yana murmushi cikin sauri ya isa inda Yarima yake yace ranka yadad'e yanzu daman nake neman number d'inka sai ma gaka.
Hannu Yarima yamik'a mai sukayi musabaha sannan yace toh gani me aka kawomin?
Dariya shaheed yayi sannan yace nazo ingaishekane kawai, rahma ce taji zuwan Aunty husna shine nakawota sugaisa.
Murmushi Yarima yayi yace kace ka had'a zumunci, toh ya kake ya kwana biyu?
Ajiyar zuciya shaheed yayi sannan yace Alhmdllh ai mun kwana biyu bamu had'uba dan ko a fada ban ganinka.
Wlh kau busy nakene aikine yatisoni gaba banda lokacin zama.
Cikin tsokana shaheed yace aikin iyaliba,
Wata uwar harara yarima yawurga masa sannan yace kana tunanin mace zata hanani fita?
Dariya shaheed yayi sannan yace idan so yai so ai ba abinda bai iya faruwa, na lura da kai yarima kamar har yanzu bakasan menene so ba.
Yarima sharesa yayi tare da duba agogon hannunsa yace mushiga mugaisa da big sis.
Girgiza kai shaheed yayi yace a'a ni ai na shiga mun gaisa kawai kaje in ka fito kasameni a fada, murmushi yarima yayi yace mutum sai gulma kai a dole sirikine kunyar ummi kakeji.
Uhm dole inji kunyarta tunda ta ban auren d'iya.
Ta6e baki yarima yayi yace kaji da gulmanka, ni bari inshiga.
Toh shikenan sai mun had'e, nan sukayi sallama suka rabu.
around 3 o'clock, flight d'in su zinat yasafka, tun kan ta iso takira sumayya nan sumayya tatura driver yaje yad'aukota.
Lokacin da suka iso tun a parlour tafara k'wala ma sumayya kira.
Da gudu sumayya tafito daga bedroom d'inta tazo tarungumeta, tana murna dariya zinat tayi tace toh sakarni haka kar kikayar da ni dan agajiye nake.
Sumayya janye jikinta tayi daga na zinat fuskarta d'auke da murmushi tace sannu da zuwa babyna.
Dariya zinat tayi tace yauwa baby kinga yadda kika koma kuwa? Ni da naganki a video chart na d'auka camera ce tamaidake haka ashe kinma fi haka a fili, baby kodai kin k'unsa?
Ta6e baki sumayya tayi tare da shafa cikinta tace wlh baby bakomai nan.
Murmushi zinat tayi tace inma akwai ai zan gane...tak'arashe maganar tare da kashe mata ido d'aya.
Dariya sumayya tayi tace bare ma bakomai yanzu dai muje kici abinci kihuta.
Ohk dear, suna rik'e da hannun juna suka wuce suka nufi bedroom d'in sumayya, saman gado zinat tafad'a tare da furta wash.
Daga gefenta sumayya tazauna tace sannu baby kinsha hanya, bari in had'a miki ruwa kiyi wanka.
Kallonta zinat tayi tace saidai in ke zakiyi min.
Murmushi sumayya tayi tace bakida matsala koma me kikeso zaki samu dan ni yau ina cikin farin ciki,,,,,tak'arashe maganar tare da mik'ewa tanufi toilet.
Bayan ta had'a mata ruwan wankan fitowa tayi taga har a lokacin kwance take, dariya sumayya tayi tace kedai baby ragguwace wlh.
Harararta zinat tayi cikin wasa sannan tace eh d'in na ji, yanzu dai zo kitaimaka min incire kayan.
Kusan a tare suka shiga wankan, bayan sun fito shiryawa sukayi sannan suka fito parlour cikin plate d'aya suka zuba abinci suka ci,
Bayan sun gama a saman 3 seater kusa yada zango inda sumayya tayi matashin kai da cinyar zinat suna hirarsu suna dariya.
Zinat kallon sumayya tayi tace baby mushiga ciki kiban hak'ina kinsan d'azun da muna wanka daurewa kawai nakeyi.
Dariya sumayya tayi tace kai baby bama zaki bari mugama hirarba, yauwa yanzu taso mufara zuwa wajen wacchan 'yar matsiyatan dan inbanga mun aiwatar da k'udirinmu ba akanta toh hankali bazai ta6a kwanciyaba dan a yanzu nasan yarima baya gidan maybe ma sai dare zai dawo saisa nakeso muyi komai mugama.
Zinat dariya tayi tace hakan fa za'a baby tashi muje,,,kusan a tare suka mik'e suka fito suka nufi part d'in zarah.
Lokacin zarah tana zaune ita kad'ai tana kallo, dan gabad'aya kuyanginta basa nan, turo k'ofan da akayine aka shigo yasa tad'ago kai takalli su sumayya, tsaye sukayi su dukansu fuskarsu babu alamun fara'a.
Saida gabanta yafad'i ammah tadake tace sannunku da zuwa, bismillah mana kuzauna.
Harararta sumayya tayi tace ba zamane yakawomuba dan haka kar kidamemu.
Zinat ce tayi karaf tace sannu amarya ya ciki? Gaskiya cikin nan ba k'aramin kyau yak'ara mikiba saidai kiyi hak'uri dan sai mun cika k'udirinmu akansa.
Da mamaki zarah take kallonsu tace ban fahimci abinda kuke nufiba.
Zinat da sumayya kallon juna sukayi sukai dariya sannan sumayya tace kar kidamu yanzu zaki gane.
Zarah ganin suna nufo inda take Zaune yasa tayi sauri tamik'e tsaye tace wai me zakuyi min?
Suna isowa sumayya tad'aga hannu takwasheta da mari, cikin sauri zarah tadafe kuncinta tace sumayya me nayi miki da zaki mareni?
Bata rufe bakiba nan zinat itama tamareta,
Zarah hawaye suka fara fita daga idonta cikin zafin nama tad'aga hannu itama ta sharara ma sumayya mari,
Sumayya dafe kuncinta tayi tace kam bura'uba lallai yarinyarnan kin isa tunda har zaki iya marina,
Zarah cikin 6acin rai tace kamar yadda kika isa toh nima haka na isa, yadda bana shiga harkarki toh nima kidaina shiga tawa, juyowa tayi tanuna zinat tace kekuma inke babbar marar kunyace toh kik'ara ta6ani.
wlh duk wadda tak'ara ta6ani sai tagane batada wayau, ni kubani hanya inwuce.
Turata sumayya tayi tafad'a saman kujera sannan tace wlh yau nice silar zubewar cikinki,,,tana fad'in haka nan suka rufe zarah da duka, ta ko'ina bugunta suke.
Zarah duk'ewa tayi gudun kar subugar mata ciki, kuka kawai take, daga k'arshe sumayya tajawota daga saman kujerar tafad'o k'asa, nan suka cigaba da bugunta suna takata zarah kuka take tana neman agaji,
Wata baiwartace tajiyo ihunta cikin sauri tanufo d'akin tana zuwa taga su sumayya akan zarah janta suke suna nema subugi cikinta ammah ta duk'e, k'ara baiwar tasaki cikin sauri tanufo wajen tare da rungume zarah jikinta tana kuka tace dan Allah kuk'yaleta,
Sumayya cikin 6acin rai takaima baiwar mari tace ke har kin isa ina waje kitako kizo har ma kinemi kishiga harkar da ba takiba tashi kiban waje ko yanzu in kasheki.
Baiwar ture sumayya tayi tace wlh saidai kukasheni ammah bazan bari kucigaba da dukantaba.
Kan baiwar suka koma suka fara dukanta dak'yar ta k'waci kanta tatashi taruga dagudu tabar d'akin.
Zarah amai tafarayi tana maida numfashi sama-sama, ganin haka yasa suka kwashe da dariya sannan sumayya tace a haka kawai idan muka barki mungama da ke matsiyaciyar banza.
Zinat kallonta tayi tace anya sumayya cikin nan ya zube?
Sumayya k'afa takai zata harbi cikin zarah cikin rashin sa'a sai k'afar tatsaya a k'irjinta
sannan sumayya tace ai dolema yazube muje kawai baby, nan tajawo Zinat suka fita daga d'akin suna dariya.
Zarah kwance tayi wajen tana maida numfashi sama-sama dan ko hannunta bata iya d'agawa.
Ko da baiwar tafita dagudu tayi part d'in yarima cikin rashin sa'a guards d'insa sukace bayanan dan haka tanufi hanyar waje.
Yarima koda yashiga part d'in ummi bayan sun gaisa zama yayi suka d'an ta6a hira da su Aunty husna saida aka kira sallar la'asar sannan yatashi yatafi masallaci.
Bayan ya gama sallah a hanyarsa ta dawowa tsayawa yayi suka gaisa da jama'a sai wajen biyar sannan yasamu yanufo gida, part d'in su ummi yai shirin komawa sai ga wannan baiwar da gudu tana zuwa gabansa tazube k'asa tana haki.
da mamaki yarima yake kallonta yace ke lafiya?
Cikin rawar murya tace kagafarceni ranka yadad'e ga su gimbiya sumayya chan d'akin gimbiya zarah suna dukanta wai zasu zubar mata da ciki.
A firgice yarima yace duka kuma!, kuna aikin mi kukuma?
Girgiza kai tashiga yi tace kagafarceni wlh na shiga intaimaka mata shine suka had'a da ni har suka fashemin baki dak'yar nasamu nagudo.
Yarima bai ida saurarentaba yayi gaba cikin sauri yanufi 6angarensu, bai damu da gaisuwar da akeyi masaba dan baima san anayiba cike da tashin hankali yawuce part d'in Zarah, yana shiga yaganta kwance k'asa tana maida numfashi, cikin sauri yanufi inda take tare da janyota jikinsa a rud'e yace Zarah sannu garin ya haka yafaru, hannu yakai saman cikinta yana shafa.
Zarah fashewa tayi da sabon kuka muryarta tana fita ahankali cikin wahala tace me natsare ma sumayya takeson ganin bayana? Me yasa tatsaneni haka? Wannan wane irin tsanace tayimin har take ik'irarin kasheni.
Yarima runtse idanunsa yayi dak'arfi yana jin wani irin tsanar sumayya a ransa,,,ahankali yabud'e idanunsa yasafke akan fuskar zarah sahun hannuwansu sumayya ne kwance a fuskarta, bakinta kuma jini ne yake fita, handchief d'insa yajanyo yagoge mata jinin, ahankali yakai bakinsa cikin nata yayi kissing d'inta, sannan yad'auketa chak yanufi toilet da ita,
Ruwan d'umi yahad'a yasakata ciki dakansa yaimata wanka sannan yad'aukota yafito da ita, zaunar da ita yayi bakin gado, cikin sauri zarah taruk'osa, kallonta yayi cike da tausayinta yace bari ind'auko miki kaya.
Zarah sakinsa tayi nan yawuce yanufi wardrobe d'inta yabud'e yad'auko kaya yataimaka mata tasaka sannan yad'auko magani yabata tasha saboda jikinta da yaji alamun zazza6i, zama yayi gefenta nan zarah tafad'a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka.
Yarima shafa kanta yayi yace please kukan ya isa haka, zarah rage sautin kukan tayi sannan tace please kamaida ni gidanmu inba hakaba sumayya sai ta ida nufinta a kaina,
Yarima k'ara rungumeta yayi jikinsa sannan yace kar kidamu babu abinda zata iya yi miki wannan ma a bisa kuskure ta aikatasa ammah....sai kuma yayi shuru batare da ya ida fad'in maganar da take bakinsaba.
Janye zarah yayi daga jikinsa yamik'e, cikin sauri zarah taruk'o hannunsa, kallon fuskarsa tayi da gaba d'aya ta canza saboda 6acin rai,,,muryarta tana rawa tace ina zakaje? Please kar kayi mata komai.
wani irin kallo da yayi matane yasa cikin sauri tasakesa dan gaba d'aya ya gama tsoratata.
Batare da yayi maganaba yajuya yafita.
a 6angaren su sumayya koda suka koma part d'inta dariya suka cigaba da yi, sumayya cikin jin dad'i tace yanzu nasan burina ya cika, zinat tsagaitawa tayi da dariyarta tace baby toh yanzu idan mijinki ya dawofa ya zakiyi.
Ta6e baki sumayya tayi tace bazan damu da abinda zai min ba tunda nasan duk abinsa bai isa yasakeniba, dariya zinat tayi tace angaisheki gimbiyar yarima aikinki yana yin kyau, yanzu dai muje kiji da ni tunda hankali ya kwanta.
Kallonta sumayya tayi tace ina zuwa, nan sumayya tafito tasamu kuyanginta da suke tsaye waje tana yamutsa fuska tace kar kubari kowa yashigo min nan duk wanda kuka saki kukabari yashigo toh a bakin aikiku.
gabad'ayansu suka duk'a sukace angama ranki yadad'e.
juyawa sumayya tayi takoma ciki.
Suna rik'e da junansu suka wuce suka shiga bedroom tun a hanya suka fara cire ma junansu kaya, jikin sumayya har rawa yake tajanyo zinat suka fad'a saman gado.
Cike da 6acin rai yarima yake tafiya yanufi part d'in sumayya, duk bawan da yatunkaresa zai masa magana da yaga yanayinsa zaiyi sauri yaja baya.
Kuyangin sumayya da suke gadin k'ofa ganin yarima yasa sukayi saurin ja baya tare da duk'awa suna kwasar gaisuwa, yarima baibi ta kansuba yawuce,
koda yashiga a parlour yatarar babu kowa dan haka cikin sauri yawuce yanufi bedroom d'inta.
_Toh fa koya za'a k'are idan yarima yashiga yaga sumayya tare da zeenat?_
_ko wane irin mataki zai d'auka akanta?_
_*duk amsar tana cikin next page dan haka Muje zuwa*_

_Masha Allah, sak'on gaisuwa agareku masoya a duk inda kuka kasance, gaskiya ina jin dad'in yadda kuke comments a groups akan novel d'in *YARIMA SUHAIL* da yadda nake samun sak'on gaisuwa daga gareku nagode sosai saidai ince Allah yabar k'auna, Sis Nerja'art tana yinku over_
*PAGE* 5⃣6⃣
Cikin zafin nama yarima yatura k'ofan, abinda yaganine yafirgitasa a kid'ime yafara furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un.
Sumayya da zinat da suke manne da juna basu ma san shigowarsaba dan gabad'aya basu cikin hayyacinsu saida sukaji yana salati sannan sukayi saurin rabuwa da Juna, cikin sauri zinat tajanyo bedsheet tarufe jikinta.
Sumayya wata irin razanannar k'ara tasaki tare da furta na shiga ukku na bani na lalace dan Allah yarima kayi hak'uri ba laifina bane sharrin shaid'anne.
Yarima da yake tsaye jikin k'ofa ya runtse idonsa innalillahi kawai yake nanatawa dan samun sauk'in abinda yakeji a ransa inba hakaba ya san zai iya abinda za'azo ana da na sani.
Cikin sauri zinat tajanyo zanenta tad'aura tana zare ido saboda a tsorace take, Sumayya ko bedsheet d'in tayaye tarufe jikinta da shi har a lokacin kuka take tana jin abun kamar a mafarki.
Ahankali yarima yabud'e idanuwansa da suka koma launin ja saboda tsananin 6acin rai, murmushin takaici yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace Sumayya ban ta6a sanin ke dabba bace sai a yau, ke ko dabba ma ta fiki k'wak'walwa mai kyau, ace a matsayinki na mace kina aiwatar da wannan mummunan halayyar, wlh a yau na tsaneki Sumayya bana fatan k'ara sakaki a idona, na yi da nasanin amincewa da nayi na aureki.
kallon zinat yayi yace kekuma har da tako min gida kika daki matata sannan kuka aikata masha'a a cikin gidana!
Sumayya cikin kuka tace dan Allah yarima kayi hak'uri wlh nabi ka nai maka alk'awali bazan k'araba dan Allah kar katona min asiri.
Zinay had'e hannuwanta tayi waje guda tana kuka tace dan Allah ranka yadad'e kayi hak'uri wlh tsautsayine yakawoni.
Yarima maida d'akin yayi yarufe sannan yace da fari zan fara rama ma matata dukan da kukayi mata,,,wucewa yayi yajanyo adaptor irin mai kaurin nan yatsige kan yad'auki wire d'in, wajen da suke yanufa daga bakin gadon yatsaya yafara shaud'a musu, ihu suke suna kuka nan tacigaba da had'awa da mari daga k'arshe k'asa yajanyosu yacigaba da duka da harbi da k'afa, ihu suke suna kuka ammah yarima bai k'yalesuba saida yaga ya had'a musu jini da majina basu iya kotsin kirki sannan yabarsu,
Jikinsu duk sahun bulala ya kwanta duk saida sukayi da sun sani akan ta6a zarah da sukayi.
Yarima kallon Sumayya yayi da take kuka yace wannan ramama matata nayi, sannan kuma ada nazo da niyar inyi miki saki d'aya ammah ganin abinda kike aikatawa ya sa zan miki....cikin sauri Sumayya tace dan Allah yarima kar kasakeni please kacigaba da dukana kar kafurta kalmar.
Wani irin kallo yarima yai mata mai tattare da tsana sannan yace kije na sakeki saki ukku dan bana buk'atarki a cikin rayuwata.
Wata razanannar k'ara Sumayya tasaki tare da rarrafowa ta iso inda yarima yake cikin kuka tace dan Allah kabarmin saki d'ayan wlh shi kad'ai ma ya isheni please ka janye biyun tafad'i haka tare da ruk'o rigarsa.
Yarima fizge rigarsa yayi yace kar kik'ara ta6ani da wannan hannun naki mai najasa, wucewa yayi yabud'e bedside d'inta yad'auko paper da biro nan yarubuta mata saki ukku ya cilla mata sannan yace na baki nan da awa d'aya kitattara komatsenki kifita kibarmin gida inko ba hakaba zan sa6a miki.
Sumayya dafe kanta tayi tare da k'ara sautin kukanta tace na bani na lalace yau ni ya zanyi da rayuwata,,,,kallon zinat tayi da take raku6e waje guda fuskarta duk ta kumbura tace shikenan zinat kinja min yau nima aurena ya mutu yau ni nashiga ukku ina zansa rayuwata.
Yarima a fusace yace na dai fad'a miki kar kibari indawo in tarar da ke,,, yana fad'in haka yajuya yabud'e d'akin yafita.
Sumayya tana ta k'wala mai kira yai mata banza, nan tacigaba da kukanta.
Zinat na ganin ya fita ta rarrafa tajanyo rigarta da veil d'inta tasaka, dakyar tamik'e tsaye, sumayya ganin zata fita yasa cikin kuka tace zinat ina kuma zaki tafi kibarni kina ganin matsalar da kika jefani.
Zinat jakkarta tad'auka batare da ta kalli sumayya ba tace tafiya zanyi tun kan yarima yadawo ya6allani koma me kenan nidai sai munyi waya dan haka kinga ma tafiyata kisan yadda zakiyi kikare kanki,,,zinat na gama fad'in haka tabud'e k'ofan taficce cikin sauri, gudu-gudu haka tasamu tafita daga masarautar bata tsaya jiran abun hawaba tacigaba da sauri sai da tayi nisa sannan tasamu tahau abuabun hawa.
Sumayya na ganin zinat ta fita nan ma k'ara fashewa da sabon kuka tayi tace na bani ni yanzu ya zanyi da kaina wai nice yarima yasaka wlh ba zan yardaba sai anmaida aurenmu,,,,rarrafawa tayi tajanyo wayarta tana kuka tai dialing d'in number d'in ummanta.
Ummah tana yin picking taji kukan sumayya yana tashi, ahankali tace ya salam sumayya me kuma kike ma kuka kedai inba kukaba ba abinda kika iya.
Cikin kuka sumayya tace ummah ya sakeni.
Ummah da take kishingid'e zumbur tamik'e tsaye tace me kikace sumayya saki?
Eh ummah.
Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un garin ya haka yakasance sumayya? Nashiga ukku ni halima, dan ubanki kifad'amin me kikayi yasakeki.
Sumayya cikin sheshek'ar kuka tace ummah daga na daki matarsa shine yasakeni.
Dan Allah asashi yamaida ni
Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kin tabbata abinda kika fad'amin gaskiya ne?
Eh ummah.
Toh shikenan yanzu yi maza kije wajen su dada kisanar da su, nima ganinan zuwa ai dole kikoma d'akinki.
Sumayya cikin kuka tace Toh ummah,,,nan takashe wayar tare da mik'ewa tajanyo kayanta tasaka.
A firgice tafito cikin sauri tanufi turakar su memartaba, tana shiga parlour dada ce kawai nan sumayya taduk'e k'asa tare da fashewa da sabon kuka.
Dada rud'ewa tayi tace lafiya sumayya me yake faruwane? Bakida lafiya ne?
Sumayya girgiza mata kai tayi tace kod'aya dada, yarima ne yasakeki.
Dada dafe k'irji tayi tace Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, saki fa kikace?
Memartaba da yake ciki yana shirin fita jin hayaniya yasa yafito yana cewa hayaniyar me nakeji haka?
Sumayya duk'awa tayi tagaishesa cikin girmamawa,
Saida memartaba yazauna sannan ya amsa mata tare da cewa lafiya sumayya kike kuka?
Dada girgiza kai tashiga yi tace ranka yadad'e wlh yarima baya da mutunci yanzu saboda Allah ace ya saki 'yar uwarsa?
Memartaba cikin d'aga murya yace saki kuma? Anya kuwa sakinta yayi dan bana tunanin yarima zai zartas da wannan hukuncin batare da na saniba.
Dada tallabe ha6a tayi tace wlh indai yarima ne zai aika.
Memartaba kallon sumayya yayi yace ke kallanni nan fad'amin me kikayi masa yasakeki?
Sumayya rage sautin kukanta tayi sannan tace banyi masa komai ba daga matarsa ta ja ni fad'a har da cemin juya marar haihuwa, shine nikuma nabiye mata nan mukayi fad'a shine yakamani yai min duka,tafad'i hakan tare da d'age hijab d'inta su memartaba salati suka shiga yi da suka ga kwanciyar bulala a jikinta.
Cikin sheshek'ar kuka tace bayan ya gama dukana shine yasakeni.
haushine yacika memartaba yace banyi tunanin hakan daga wajen yarima ba banta6a tunanin zai iya min cin mutunci irin hakaba ammah bari inkira iyayenku suzo asan yadda za'a 6ullo ma lamarin.
Memartaba wayarsa yad'auka yakira mahaifin yarima da na sumayya yace duk suzo da iyalansu susamesa.
Bayan kamar minti goma sai gasu su duka sunzo harda Aunty husna da rahma da suke gidan basu koma gidajensuba,
Lokacin su memartaba suna zaune suna tattauna al'amarin gabad'ayansu suka duk'a suka gaishesu, kowa da mamaki yake kallon sumayya.
Bayan su memartaba sun amsa gaisuwa, gyaran murya yayi yace wani ya aika akira min yarima dan na kira wayansa a kashe.
Abban sumayya ne yace toh ranka yadad'e nan yamik'e yaje ya aiki wani dogari yace yaje yakirasa.
Yarima bayan ya baro part d'in sumayya nan yakoma 6angaren zarah yanayinsa kawai zaka kallah kasan ba k'aramin tashin hankali yake cikinsaba, kallon zarah yayi da take kwance ta zuba ma waje d'aya ido tana kallo, daga gefen gadon yazauna tare da dafe kansa yana tunanin lamarin sumayya dan gabad'aya ta gama ficce masa a rai, wayoyinsa yakashe gabad'aya dan ya san dole sai memartaba ya nemesa dan dama gudun kar amaido masa aurenta yasa yaimata saki ukkun.
Zarah ruk'o hannunsa tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace tunanin me kakeyi?
Kallonta yarima yayi cike da tausayi yace in kaiki asibiti adubaki ko?
Girgiza kai zarah tayi tace babynka lafiyarsa lau dan basu samu sun ta6asa ba nikuma ciwon jikine kuma nasan zan warke insha Allahu.
Yarima d'aura hannunsa yayi saman fuskarta sannan yace ammah kina buk'atar asa miki drip kuma jikinki akwai zazza6i.
Zarah maida idonta tayi talumshe, yarima zuba mata ido yayi yana kallonta.
Knocking d'in k'ofan da akayine yasa yamik'e yaje yabud'e kuyangar zarah ce cikin sauri taduk'a tagaishesa, yarima batare da ya amsa mataba yace ya dai.
Jikinta yana rawa tace ranka yadad'e daman dogari ne aka aiko daga turakar sarki yace yana son ganinka.
Yarima baiyi mamakin hakaba, dawowa yayi yakalli zarah da take kwance ta ji duk maganarsu, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace bari indawo sai muje hospital.
'Daga mai kai kawai zarah tayi, nan yarima yajuya yafita yanufi turakar memartaba.
Lokacin da ya isa baiyi mamakin ganin family d'insa da suka hallaraba, bayan ya yi sallama, waje yasamu k'asa chan gefen Aunty husna yazauna, cikin rashin damuwa yagaishe da su memartaba.
Ciki-ciki memartaba ya amsa masa nan d'akin yad'au shuru kowa saurare yake yaji memartaba ya fara magana.
Gyaran murya memartaba yayi sannan yakalli yarima da kansa yake sunkuye k'asa yace wannan taron ba dan kowa nayisaba sai dan kai yarima.
suhail ka bani kunya ban ta6a tunanin hakan daga garekaba koma menene ai ana son sasacin a cikin aure, wace irin zuciyace ta d'ibeka har kasaki matarka.
Gabad'aya 'yan d'akin sukace saki!! Nan aka fara kallon kallo.
Memartaba nuna sumayya yayi da take kuka har Lokacin Sannan yace toh gatanan dai ya saketa, ke kifad'a musu dalilin sakin suma suji.
Sumayya saida takalli yarima da kansa yake sunkuye sannan tamaimaita abinda tafad'a ma su memartaba.
Da mamaki yarima yad'ago yakalleta jin k'aryar da tadage tana shararawa, wata uwar harara yawurga mata nan Sumayya tafara dabarbarcewa.
Yana hararanta karaf a idon dada cikin fushi tace kikwantar da hankalinki kiyi bayaninki dan babu abinda ya isa yayi miki tunda kina a gabanku,
Nan Sumayya tacigaba da bayani.
Bayan ta gama d'akin yad'au shuru kowa yana jimami a cikin ransa, dadyn yarima ko kunyace takamasa ganin abinda d'ansa ya aikata ma d'iyar d'an uwansa, ummi ma jin abun take wani iri dan bata ta6a tunanin hakan daga garesaba.
Gyaran murya memartaba yayi yace kunji jawabinta, kunga abin kunyar da yarima ya aikata kan bare yarabu da 'yar uwarsa, toh yanzu ba sai anja maganar da nisaba na umurceka kamayar da ita d'akinta.
Sai a Lokacin yarima yad'ago yakalli memartaba cike da girmamawa yace ranka yadad'e kagafarceni, bata fad'a muku saki nawa nayi mataba? Ko daman idan anyi saki ukku ana komawa.
Nan d'akin yarikice da salati memartaba yace da hankalinka zakayi ma matarka saki ukku yarima? Sakin da ubangiji bayaso ana yi, ina iliminka da tuninka suke.
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.
Memartaba yace inji a lokaci guda kayi sakin?
Sumayya tayi karaf tace eh ranka yadad'e gabad'aya yayimin.
Toh Alhmdllh tunda gabad'ayane kuma cikin fushine zamu iya d'aukansa a matsayin saki d'aya kaga sai kamaidata d'akinta yanzu....cewar memartaba
Yarima k'ara duk'ar da kansa yayi sannan yace kagafarceni ranka yadad'e na riga da na haramta ma kaina k'ara auren Sumayya,
A firgice kowa na d'akin yakalli yarima, nan Sumayya tafashe da kuka tace na shiga ukku dan Allah kutaimaka min yamaidani d'akina.
Memartaba kallon yarima yayi yana jinjina kai dan ya ma rasa abinda zai ce masa,
Dada ce tashare kwallar da tazubo mata saboda tausayin Sumayya sannan tace ranka yadad'e ka gani ko? Lokacin da nake fad'a maka wulak'ancin da yarima yake ma Sumayya ba ka yarda, duk wulak'anci da cin mutuncin da matarsa takeyi mata bai ta6a tankawaba sai ita da suka d'an samu sa6ani shine yadank'ara mata har saki ukku.
Ummi kallon yarima tayi kallon mamaki, yarima cike da jin kunyar ummi yaduk'ar da kansa k'asa.
abban Sumayya ne yai k'arfin halin cewa kuyi hak'uri yanzu haka wani haukan ne Sumayya tayi masa kuma ba a ji daga garesaba.
Memartaba murmushin takaici yayi sannan yace bana buk'atar jin komai daga garesa, nagode sosai suhail ni kawulak'anta tunda ni na aura maka Sumayya yanzu ka maido min abuna ka ce ban isa inyi maka abinda bakasoba,
Saboda ganin kamar ban kyauta makaba yasa nabarka kaje ka auro za6inka bayan shekara d'aya da aurenku da Sumayya, duk labarin da ake bani akan abinda kake ma Sumayya ban ta6a yardaba sai gashi yau na gane ma idona abinda zai d'aga min hankali abinda d'ana nacikina bai aikataba sai gashi jikana namiji tilo d'aya ya aikata ma 'yar uwarsa.
Yarima d'ago kai yayi yakalli memartaba yace kagafarceni ranka yadad'e nima ba a son raina na aikata hakanba, wlh Sumayya ba gaskiya tafad'a mukuba.
Memartaba d'aga masa hannu yayi yace dakata bana buk'atar jin komai daga wajenka abinda idona yagane min ya isheni.
Daddyn yarima kallon yarima yayi cike da takaici yace suhail ka ban kunya kana gani yadda nake zaune da d'an uwana lafiya ammah karintse ido kakarta min rashin mutunci har haka, yanzu da wane ido kakeso ink'ara kallonsa.
Girgiza kai yarima yashiga yayi yace kayi hak'uri daddy wlh nima ba a son raina hakan takasanceba.
Memartaba a hankali yafurta innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, kallon kowa yayi d'aya bayan d'aya sannan yamaida kallonsa ga dada yace kin gani ko? Ni yanzu banma san wane hukunci zan yanke masaba ko zan samu d'an sauk'i a raina.
Dada kallon yarima tayi sannan tace ma memartaba ranka yadad'e kaga ita tagaban goshin tasa tana chan tana hutawa babu abinda yadameta bata ma san wainar da ake toyawaba ita ga 'yar gaban goshi me ciki.
Jinjina kai memartaba yayi sannan yace nasan abinda zanyi, kallon Rahma yayi da take kuka yace ke jeki kisamo min takarda da biro, mik'ewa Rahma tayi tafita.
Nan kowa yayi jugum yana jira yaji hukuncin da memartaba zai yanke.
Bayan kamar minti biyar sai ga Rahma ta dawo rik'e da takarda da biro, tsugunnawa tayi gaban memartaba tamik'a mai,
Kar6a memartaba yayi yace yauwa, sannan yakalli yarima da yake zaune har Lokacin bai d'ago kansa mik'a masa memartaba yayi yace kar6a.
'Dago kai yarima yayi yakalli takardar sannan yamaida kallonsa ga me martaba, a karo na biyu memartaba yace kar6a mana.
Hannu yarima yamik'a yakar6a tare da tsare memartaba da ido yana jira yaji abinda zai ce.
Shima memartaba kallonsa yake sannan yace inaso karubuta ma wacchan matar taka itama saki ukku.
Gabad'aya d'akin d'agowa akayi aka kalli memartaba cike da mamakin kalmar sakin da ya ambata.
yarima ko gabansane yayi wani irin fad'uwa saida biron takubce daga hannunsa, tashin hankaline k'arara yabayya a fuskarsa.
har a lokacin memartaba kallonsa yake fuskarsa ba alamun wasa yace indai kana son cigaba da zama a gidannan toh dole kasaketa saboda hakan shi zaifi dacewa karabu da kowace d'aya daga cikinsu.
Dada gyad'a kai tayi tace tabbas ranka yadad'e ka kawo shawara mai kyau inma cikin da yake jikintane yake ma rawar kai toh taje gidansu da abinda tacigaba da raino zamu dinga aika mata da duk abinda take buk'ata har sai ta haihu, intaso tashayar da abunta inkuma batasoba tabamu abunmu a haka zamu sami wacce zata kular mana da shi.
Ummi ita kanta saida gabanta yafad'i dan ita jin abun take kamar a mafarki tabbas ta san d'anta akwai dalilin da yasa ya saki sumayya saidai miskilanci da zurfin jikinsa bazasu ta6a barinsa yafad'aba.
Abban sumauya ne yaduk'ar da kansa yace ranka yadad'e ataimaka a sassauta ma yarima wannan hukuncin yai masa tsauri.
Sultana sadiya da take gefe takaici duk ya cikata tana ji kamar tashak'e yarima yamace kowa yahuta, jin maganar da mijinta yayi yasa tawurga masa harara, sai a lokacin tace ranka yadad'e tabbas wannan hukuncin da kayanke shine daidai dan yarima ya tozarta min d'iya,,,, d'aga mata hannu sultan abbas yayi yace ke banason hauka na san duk abinda yaima sumayya toh tana da laifi a ciki dan na san sumayya bata ji.
Sultan Ahmad ne yai k'arfin hali yace ma sultan Abbas kadaina cewa haka domin yarima bai kyautaba.
Memartaba gyaran murya yayi nan kowa yanutsu, sannan yace duk naji k'orafinku saidai inaso kusani babu wanda ya isa yasa incanza maganata dan ku kanku kunsani ni kaifi d'ayane bana magana biyu.
Duk'ar da kansu sukayi sukace Allah yaja da ran sarki me adalci.
Memartaba kallon yarima yayi da duk sanyin A-C d'in da take d'akin ammah bai hana yayi zufaba, murmushi Memartaba yayi sannan yace suhail ina saurarenka dan kaji abinda nafad'a.
Aunty husna ce tad'auki biro d'in da tafad'i tamik'a mashi.
Cikin sanyin jiki yarima yak'arfi biro d'in yad'aura saman paper, nan kowa yazuba mai ido ana jira yarubuta.
Ido yazuba ma paper tare da d'aura biro d'in kamar zaiyi rubutu nan gabansa yashiga dukan ukku-ukku jinsa yake wani iri gabad'aya komai ya kwance masa, yarasa cikin biyu wane zaiyi shin sakin zarah zaiyi ko kuma ya amince yarabu da family d'insa, runtse idanunsa yayi yana jin wani irin k'unci a ransa........
_Shin yarima zai amince yasaki zarah?_
_Ko zai amince yarabu da family d'insa kamar yarda memartaba yafurta?_
_*Muje Zuwa dan jin yadda zai kasance*_
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

_*Nagode Sosai da kulawarku agareni masoya, gaskiya naji dad'i dan naga k'auna zallah daga gareku, banda abinda zanyi inbiyaku saidai ince Allah yabar k'auna da dank'on zumunci😘*_
*PAGE* 5⃣7⃣
Ahankali yabud'e idanunsa da gaba d'aya suka canza launi, ji yake kamar yarubuta ma zarah saki sai kuma yaji bazai iya aikata hakanba dan shi kansa ya san idan yasaketa bai mata adalciba.
'Dago kai yayi yakallesu d'aya bayan d'aya har a lokacin idanunsu suna a kansa,,,Yarima kallonsa yasafke ga memartaba cikin sanyin jiki muryarsa tana rawa yace kagafarceni ranka yadad'e bazan iya rabuwa da matataba.
Gabad'ayansu a firgice suke kallonsa hatta shi kansa memartaba yayi mamakin furucin da yafito daga bakin yarima.
Murmushi memartaba yayi sannan yace suhail idan na fahimceka toh kana nufin ka za6i matarka akanmu ko?
Cike da damuwa yarima yagirgiza kai yace ranka yadad'e ba haka nake nufiba kawai dai... katseshi memartaba yayi yace kawai dai me!!! Toh bara kaji indai har bazaka iya rabuwa da itaba toh mu yazamar mana dole murabu da kai, dan haka kaje kawai na cireka daga cikin masarautata yanzu ka fita daga cikin iyalaina dan haka na baka awa d'aya kaje duk wani abu da kasan mallakinane kaje kakawo min sannan kafita kabarmin masarauta, inkuma ba hakaba zansa a fitar da kai a wulak'ance.
Gabad'aya d'akin shuru sukayi kamar ruwa ya cisu dan sunsan tunda har memartaba yafurta toh tabbas ba wanda ya isa yacanza.
Yarima runtse idonsa yayi yana jin yadda maganar memartaba take dukan dodon kunnansa wani irin d'acine yakeji a ransa
Ummi ko rufe fuskarta tayi da alkyabbarta tana goge hawayen da suka taru a idonta, gabad'aya lamarin ya rikitata.
Daddy ma shikad'ai yasan abinda yakeji a ransa game da maganar da mahaifinsa yafurta, kawai dai ya dakene bai nuna ba.
Dada ce takalli memartaba tace ammah ranka yadad'e ba... d'aga mata hannu memartaba yayi yace banason jin maganar kowa daga cikinku dan ni nariga da nagama magana yanzu lokacin da nabaka zai fara aiki.
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, ahankali yamik'e jiki ba k'wari kamar wanda kwai yafashe mawa a ciki haka yake tafiya har yafita daga d'akin.
Rahma da Aunty husna ko kuka sukeyi ahankali, inda sumayya take kuka akan mutuwar aurenta.
Yarima ahaka ya isa part d'insu, bakin gadonsa yazauna yadafe kansa shi kad'ai yasan abinda yakeji gashi an hanasa yai magana, tunani yashiga yi shin in ya bar gidansu ina zaije? Tunowa yayi da maganar memartaba da yace ya fara cin lokacin da yabasa, dan haka yajanyo wayarsa yakira wata number bata dad'e tana ringing ba akayi picking,
Yarima k'ok'arin saita nutsuwarsa yayi suka d'an gaisa sama-sama sannan yace Dr Mu'az kana gari?
Daga chan 6angaren wanda aka kira da Dr mu'az yace eh ranka yadad'e.
Ohk, please kaje kasamar min hotel maikyau yanzu zan shigo Abuja.
Cikin jin dad'i Dr mu'az yace angama ranka yadad'e Allah yakawoka lafiya.
Ameen yarima yace sannan yakashe wayar,
Sannan yakira yasa ayankar masa ticket na mutum biyu yace yanzu yakesonta, kasancewar sanannene nan suka amsa masa, bayan sungama wayar yai musu transfer d'in kud'insu, bayan ya gama Dr khalil yalalubo bai wani 6ata lokaciba yai picking
Yarima ko gaisawa bai bari sunyi ba yace Dr khalil kana ina yanzu?
Daga chan 6angaren Dr khalil yace ranka yadad'e ganinan wajejan anguwarku gidan Auntyna.
Ohk, please kazo yanzu akwai inda nakeso kakaini.
To ranka yadad'e ammah ya naji muryarka haka? Lafiya dai ko?
Yarima kashe wayarsa yayi batare da ya bashi amsaba,,,,mik'ewa yayi yaje yafara had'a duk wani abu da yasan ba mallakinsa bane yaware ma daddy da memartaba nasu sannan yad'auki nashi, wajen wardrobe d'insa yaje yabud'e nan yafara fitar da kayansa yana sawa a trolly, cikin trolly guda yazuba duk wani abu da yake buk'ata sannan yajawo,
Tsaye yayi yana k'are ma room d'insa kallo yana jin k'unci a ransa, janyo trollyn yayi yafito cikin sauri guards d'insa suka zo suka kar6a nan yace suwuce masa da shi waje.
Cike da ladabi suka amsa masa.
Daga nan part d'in zarah yawuce kallonta yayi har lokacin tana kwance, ita kanta zarah yanayinsa kawai tagani tasan yana cikin tashin hankali,
Yarima batare da ya janye idonsa akantaba yace tashi kihad'a kayanki,
Zarah saida gabanta yafad'i tace na'am.
Shareta Yarima yayi yawuce wajen wardrobe d'inta yabud'e nan yafara zuba mata a trolly duk abinda yasan zata buk'ata saida yazuba mata a ciki, bayan ya gama juyowa yayi yakalli zarah da tatsaresa da ido yace tashi muje.
Zarah k'wallah ce tacika mata ido tace ina zamuje?
Tsawar da Yarima yadaka matane yasa tamik'e ba shiri tajanyo veil d'inta tayafa nan Yarima yawuce gaba tana biye da shi, wata kuyangarta ce cikin sauri takar6i trollyn da yake hannun Yarima
Zarah tana biye da yarima gabad'aya kanta ya d'aure gashi yarima bai bata fuskar da ma zata iya tambayarsaba ahaka har suka fito harabar gidan, da mamakinta sai gani tayi sun nufi turakar su memartaba.
mamaki bai ida kamataba saida suka shiga d'akin taga gabad'aya family d'in yarima suna a ciki, bata lura da yanayin da suke cikiba, dasauri tatsugunna tagaishesu, gabad'ayansu babu wanda ya amsa mata,
Ta d'auka basujiba nan tak'ara gaishesu, dady da abbah ne kawai sukayi k'arfin halin amsa mata,
'Dagowa tayi takalli ummi da talullu6e kanta da alkyabba, sai kuma takalli su Aunty husna da rahma da suketa kuka, nan jikinta yak'ara yin sanyi, daganan tamaida kallonta ga sumayya da take gefen dada tana ta rusa kuka, inda dada tabuga uban tagumi, sultana sadiya ko ta cika tayi fam.
gani tayi yarima ya wuce wajen memartaba nan yarussuna yamik'a masa wasu files, a wulak'ance memartaba yakar6a sannan yace ina fata komai ne nan kakawo min.
Ahankali yarima yace eh ranka yadad'e,
Jinjina kai memartaba yayi sannan yace yarima ka bani mamaki yanzu saboda mace ka amince karabu da kowa naka, inaso kasani dangi basu canzuwa ammah ita mata a kowane lokaci zaka iya canzata, tunda ka za6i mace akan danginka toh sai katashi kutafi.
Zarah cikin sauri tad'ago kai takalli memartaba da yake maganar dan kwata-kwata bata fahimci inda maganarsa tadosaba,
Dada ce cikin damuwa tace ammah har a yanzu suhail idan ka amince zaka rabu da ita toh bismillah dan kasan memartaba yana nan akan bakansa,,,tak'arashe maganar tare da mik'a masa takardar.
girgiza kai yarima yayi yace kugafarceni har yanzu ina akan bakana nima yana fad'in haka yamik'e
Sumayya ce tasake fashewa da kuka tace yanzu saboda waccan jakkar kasakeni saki ukku yarima, wlh bazan yardaba sai ka maidani d'akina, duk inda kaje zaka dawo kataddani.
Zarah sai a lokacin ta fahimci abinda ake tattaunawa gabantane yashiga dukan ukku-ukku a firgice takebin kowa na cikin d'akin da kallo,
Rahma ce tayi saurin mik'ewa dagudu taje tafad'a jikin yarima, cikin kuka tace dan Allah bro kar katafi kabarmu dan Allah ka amince karabu da matarka kazauna cikin danginka.
Yarima idanuwansa ne suka kad'a sukayi jawur kallon daddy yayi da ya janye fuskarsa gefe, a 6angaren abbah ma gefe d'aya yake kallo,
Yarima har ya bud'e baki zaiyi musu magana sai kuma yafasa, janye rahama yayi daga jikinsa, kallon umminsa yayi da taketa k'unshe kukanta, wani iri yaji a ransa gudun kar yaimata magana yaja tayi kuka saisa baice mata komai ba yawuce yanufi inda zarah take tsugunne tana hawaye.
Kallonta yarima yayi yace tashi muje.
Girgiza kai zarah tashiga yi dak'yar tabud'e baki muryarta tana rawa tace please yarima kar karabu da danginka ni yafi dacewa karabu da ni dan danginka sune komai naka, mik'ewa tayi tare da fashewa da kuka had'e hannuwanta tayi waje guda tace dan Allah yarima na rok'eka kacika umurnin memartaba kasakeni kawai, cikin sauri taje takar6o takardar hannun dada tadawo inda yake tsaye tamik'a mashi tace please karubuta min sakina, kar katafi kabar su ummi, neman tura mashi tankarda tayi a hannunsa ganin ya k'i kar6a yasa tawuce inda ummi take zaune tatsugunna cikin kuka tace please ummi kisa baki yarima yarubuta min sakina bana son yasamu matsala da kowa dan ku kune farin cikinsa.
Ummi kasa 6oye kukanta tayi nan tafara sheshek'ar kuka, zarah ganin ummi batada niyar cewa komai yasa tamik'e takoma wajen yarima tace kaduba kaga ummi da 'yan uwanka kuka suke yanzu ka amince katafi kabarsu cikin....wani gigitacce mari yarima yakwad'a mata wanda gabad'aya 'yan cikin parlourn saida suka kallosu, yarima cikin 6acin rai yace zarah kidawo hayyacinki.
Nan zarah tashiga hankalinta tare da kife kanta a k'irjin yarima tarushe da wani sabon kukan, yarima jin kukan nata yake har cikin ransa, janyeta yayi daga jikinsa nan yarik'e mata hannu suka fara tafiya, memartaba janye idonsa yayi daga kallonsa inda su daddy daman basu d'ago ba dama.
Aunty husna ce cikin sheshek'ar kuka tace yarima na rok'eka kar ka aikata hakan dan Allah kadawo,
Jan hannun zarah yayi suka ficce daga parlourn Aunty husna har ta mik'e zata bi bayansa nan taji muryar memartaba ya ce kar wanda yasaki yabi bayansa.
kan dole takoma tazauna.
Yarima yana fita nan yatarar da Dr khalil tsaye yana jiransa, wajen motar dr khalil yanufa.
Cikin sauri Dr khalil ya iso inda yake yace yarima ya naganku haka?
Yarima kallon guards d'in yayi yace susaka masa kayansa a boot, cikin sauri suka cika umurninsa.
Nan suka bud'e masa motar yashiga, zarah da take tsaye fuskarta rufe da mayafi itama aka bud'e mata baya tashiga.
Dr khalil da yake tsaye zuwa yayi yashiga motar tare da kallon yarima yace ranka yadad'e ina muka nufa?
Yarima batare da ya kallesaba yace airport.
Cikin sauri Dr khalil yatayar da motar, lokacin da zai fita daga masarautar yarima runtse idanunsa yayi yana jin wani iri a cikin ransa,
Tafiya suke ammah gabad'aya babu wanda yayi magana,
Dr khalil juyowa yayi yakalli yarima da yazuba ma titi ido cike da damuwa yace ranka yadad'e wace irin tafiya ce ta gaugawa takamaka haka? Ina zakaje?
Yarima batare da ya juyo ya kallesaba yace Doctor ga amanar hospital d'ina nan na damk'a a hannunka domin nasan zaka kularmin da shi kamar yadda zan kula da shi ammah ban saniba ko nan gaba za'a kawo wanda zai maye gurbina, koma mekenan nidai na aminta da kai.
Kiiittt yaja burki yatsaya tare da juyowa yakalli yarima, cike da damuwa yace please yarima kaimin bayani yadda zan fahimta dan gabad'aya ka d'aure min kai, wace irin tafiya ce zakayi haka? Ina zakaje please kafad'a min.
Yarima duba agogon hannunsa yayi sannan yace please kayi sauri flight d'in da zamu bi ya kusan safka.
Tada motar Dr khalil yayi dagudu yafigi motar.
Yarima ta mirror yakalli zarah da tabuga uban tagumi, jingine kansa yayi a kujeyar da yake zaune tare da k'ura mata ido ta mirror d'in, zarah ko bata ma san yanayiba dan gabad'aya ta yi zurfi cikin tunani.
Suna isa flight d'in yana safka, Dr khalil cikin sanyin jiki yakalli yarima yace Dr toh yanzu sai yaushe zaka dawo?
Murmushin k'arfin hali yarima yayi sannan yace kar kadamu ba wani dad'ewa zanyiba.
Jinjina kai Dr khalil yayi sannan yace ammah zanyi kewarka dayawa,
Yarima kallon abokin nasa yayi yace nidai fatana karik'e min amanata kacigaba da tafiyar da komai daidai kamar ina nan.
Murmushi Dr khalil yayi yace karkadamu insha Allahu zanyi kamar yarda kace,
Nagode sosai abokina,,, yarima yafad'i hakan cikin jin dad'i, sannan yabud'e k'ofar yafita,
Nan shima Dr khalil yafita, yarima dakansa yabud'e ma zarah k'ofan, dak'yar tasafko k'afanta tafito, nan yarima yana rik'e da ita yai waya akazo aka kawo masa komai nasa, kayansu aka fitar aka saka a cikin flight d'in.
Dr khalil har wajen jirgin yarakasu nan suka k'ara sallama da yarima cikin rashin jin dad'in nisan da zasuyi da juna.
Zarah ko saboda tashin hankalin da take ciki baisa tayi murnaba koda wannan shine karo na farko da tafara shiga jirgi.
Daga gefen yarima take zaune har jirgin yatashi, wani irin kunci da bak'in ciki yaziyarci zuciyan yarima a lokacin da suka fara tafiya, bak'in space d'insa yajanyo yadad'e idonsa, zarah cikin rashin k'arfin jiki takwantar da kanta a saman k'irjin yarima.
Rungumeta yayi cike da tausayinta, ahaka zarah tayi bacci.
Cikin k'ank'anin lokaci suka isa garin abuja.
Jirginsu na dira yarima yakira Dr mu'az yace gamu mun safka.
Dr mu'az cewa yayi ranka yadad'e ai gani nan tun d'azu nake jiran safkarku.
Tada zarah yayi da take bacci nan suka fito.
Wani mutum ne wanda bazai wuce tsaran yarima ba koda ma zai girmi yarima toh dakad'an ne, nan ya iso inda suke fuskarsa d'auke da fara'a.
Yarima koda yana cikin damuwa ammah hakan baihana sa nuna jin dad'in ganin abokin nasaba,
Dr mu'az cike da jin dad'i yace sannu da zuwa prince suhail.
jinjina kai kawai yarima yayi sannan yamik'a masa hannu sukayi musabaha.
kallon zarah yayi yace sannu madam.
Zarah batare da ta kallesaba tagaishesa, daga nan yace prince zamu iya tafiya.
Murmushi kawai yarima yayi nan yaruk'o hannun zarah, inda Dr mu'az yasa aka d'aukar musu kayan aka saka bayan boot.
Koda suka kama hanya Dr mu'az kallon yarima yayi yana murmushi yace prince ka kwana biyu bakazo garin nan ba yau ma ji nake kamar a mafarki naganka.
Murmushi yarima yayi yace kaima kasan yanayin aikinmu ne yake 6oyemu tunda kaima kakwana biyu baka lek'aniba.
Dariya Dr mu'az yayi yace wlh abokina nima naso inzo abubuwan ne sukaimin yawa kowane lokaci busy nake ammah da badan hakaba ai da ba abinda zai hanani zuwa dan kaima ka san banda aboki sama da kai dan kaimin *HALARCI* a rayuwata wanda bazan ta6a mantawaba.
Murmushi yarima yayi yace kadaina magana akan abinda yariga da yawuce.
Hmm ai duk zuciya mai adalci bazata ta6a mance alkhairin da akayi mataba,,,daidai lokacin Dr mu'az yashawo kwanar gidansa.
Kallonsa yarima yayi cike da mamaki yace ni da zaka kai hotel ya naga ka kawomu gidanka?
Murmushi Dr mu'az yayi yace taya kake tunani zan iya barinka kazauna a hotel alhali ina cikin garin nan, ai kaima kasan hakan bai daceba.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonsa sannan yace kar kadamu ni nasan fiye da hakan ma zaka iya yimin ammah ni nafi buk'atan son zama a hotel d'in.
Doctor Mu'az tsayar da motar yayi yajuyo yakalli yarima cike da damuwa yace ranka yadad'e kayi hak'uri da inbarka kazauna a hotel na k'wammace ni inbar maka gidana kazauna inje inkama haya,
Yarima shuru yayi baice komai ba.
cike da damuwa Dr mu'az yace dan Allah ka amince muje gidana.
Zarah da take zaune baya tana saurarensu ita kanta cikin ranta bata son suje hotel.
Murmushi yarima yayi yace shikenan na amince Dr.
Cike da jin dad'i Dr mu'az yace nagode sosai doctor.
Nan yatada motar, a bakin gate d'in gidansa yayi horn, cikin sauri megadi yazo yabud'e masa gate nan yacinna motarsa cikin makeken gidan.

_Ummu Zainab tsakanina da ke saidai addu'a dan banda abinda zan biyaki da shi, Allah yak'ara lafiya, Allah yasa ciwon zakkar jikine, Allah yatashi kafad'unki, Nagode, Nagode, Nagode sosai Allah yabiyaki abinda kikayi min_
*PAGE* 5⃣8⃣
Koda yayi parking kallon yarima yayi yace ranka yadad'e mun fa iso.
'Daga kai kawai yarima yayi, nan Dr khalil yakalli zarah ta mirror yace gimbiya bismillah mun iso, murmushi zarah tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace toh.
Gabad'ayansu suka bud'e motar suka fito, yarima kallon zarah yayi da take taku dak'yar yace ko intaimaka miki?
Zarah batare da ta kallesaba tagirgiza kai, nan Dr mu'az da yarima sukayi gaba tana bayansu har suka shiga a main parlour suka tarar da matar gidan zaune ganinsu yasa tamik'e fuskarta d'auke da fara'a tace oyoyo ga manyan bak'i,
Dr mu'az ne yayi murmushi yace dear yau fa ga prince a gidan namu,
Murnushin jin dad'i tayi tace yau muntaki sa'a gaskiya,
Saman kujerun da suke d'akin suka zauna nan matar dr mu'az tad'an russuna cikin girmamawa tagaishe da yarima.
Murmushi yarima yayi sannan ya amsa mata,
Wajen zarah tanufa tana murmushi tace gimbiya sannu da zuwa ina wuni?
Murmushi itama zarah tayi sannan tace ina wuni.
Bayan sun gama gaisawa, Dr mu'az yace ranka yadad'e ga d'an akurkin gidan namu ina fata zaku iya rayuwa a cikinsa.
Harararsa yarima yayi yace kai fa tsiyata da kai ka iya tsokana.
Dariya Dr mu'az yayi yace ai gaskiya ce nafad'a,
Kallon matarsa yayi yace jamila gashinan prince yau wani irin farin ciki nakeji da naganni tare da shi, abokina ne tun daga primary har secondary tun lokacin banda komai muke tare da shi, shine silar yin karatuna dan a lokacin iyayena basuda komai mu talakkawane sosai da taimakonsa nayi karatu har nakai wannan matsayin da nake da shi kinga ko taya zan iya mance prince?
Jinjina kai matarsa tayi tace tabbas hakane bazaka ta6a mancewa da halacci da yayi makaba, saisa a kullum yana cikin addu'anmu.
Kallonta yarima yayi yace madam kema kin biye ma wannan mijin naki sarkin tsokana.
Murmushi Dr mu'az yayi yace prince kenan kaima kasan gaskiya nafad'a saidai idan kanason 6oyetane.
Shuru yarima yayi baice komai ba.
Zarah dai tana zaune tana saurarensu ita dai burinta takwanta tahuta.
Matar mu'az mik'ewa tayi tace bari akawo muku ruwa kusha kafin agama abinci.
Bayan ta fita Dr mu'az kallon yarima yayi yace ranka yadad'e muje kuza6i part d'in da yayi muku a cikin gidan nan.
Girgiza kai yarima yayi yace no ba sai mun za6aba duk wanda aka bamu munaso yanzu magrib ta gabato muna buk'atar kimtsawa ga madam babu lafiya ina so asamo min drip zansa mata,,,yak'arashe maganar tare da kallon zarah.
Dr mu'az yace ayya Allah yasauk'e bari inje insa asamo daga nan ashigo muku da kayanku, yana fad'in haka yamik'e yafita yabar d'akin.
Yarima kallon zarah yayi da ta jingine kanta a kujerar da take yana shirin yin magana sai ga Matar mu'az ta shigo dan haka yafasa.
A gabansu ta aje k'aton tray d'in da yake d'auke da kayan marmari nan tatsiyaya musu drinks a cups ta aje ma kowa gabansa sannan tace kuyi hak'uri abincin ya kusan zama ready.
Murmushin k'arfin hali zarah tayi tace bakomai Aunty hakan ma mun gode, nan tad'auki cup d'in tafara shan drink d'in.
Nan Dr mu'az yashigo bayansa megadine janye da trollies d'in su yarima d'aya daga cikin rooms d'inne Dr mu'az yasa aka shigar da kayan sannan yakalli yarima yace ranka yadad'e kuduba kuga idan part d'in baiyi mukuba sai a canza.
Murmushi yarima yayi yace kar kadamu yayi mana, kallon zarah yayi yace muje kisamu kihuta.
Jamila cike da tausayi takalli zarah tace sannu gimbiya, Allah yabaki lfy.
Cikin Jin kunya zarah tace Ameen Aunty nagode, nan tamik'e tabi bayan yarima.
Wani makeken d'akine mai d'auke da room nd bedroom ya tsaru sosai komai na cikinsa mai kyau da tsada ne, angyara ko'ina fes, suna shiga bedroom zarah saman gadon tafad'a takwanta agajiye, kallonta yarima yayi sannan yawuce yashige bathroom dan yawatsa ruwa.
Bayan ya fito kallon zarah yayi da take kwance yace kitashi kije kiwatsa ruwan ko kinji k'arfin jikinki.
Zarah kallonsa tayi ganinsa d'aure da towel yasa tad'auke kanta, batare da ta k'ara kallonsaba tamik'e tanufi wajen kayansu wardrobe d'in tabud'e saida tagogeta sannan tabud'e trollies d'insu duk tajere musu kayansu, Bayan ta gama ta gefen yarima taratsa taje tashige bathroom, cikin sauri yarima yad'auko kayansa yasaka sannan yatayar da sallar magrib a gida, dan a lokacin ana gab da sallame sallah a masallaci.
Yana saman darduma zarah tafito d'aure da towel tawuce wajen wardrobe d'in tad'auko gown tasaka sannan tayi sallah.
Koda yarima yagama saman gado yakoma yazauna nan yajanyo wayoyinsa yacire dukkan sim d'insa yakashe wayar ya aje.
Dafe kansa yayi yana jin wani iri a ransa dan baisan halin da umminsa zata shigaba dan gabad'aya itace damuwarsa, abubuwan da suka faru nan suka fara dawo masa a rai.
Zarah da take tsaye tana kallonsa wani irin tausayin mijin nata takeji, ita kanta zuciyanta zafi take musamman ma da tasan ta dalilinta yarima yafad'a wannan matsalar, hawayene suka fara fita daga idanunta, ahankali tataka ta isa inda yake daga gefensa tazauna,
'Dago kai yarima yayi yakalleta ganin tana hawaye yasa yace zarah meyake samunki ko jikin ne?
Girgiza kai tayi tace banso karabu da kowa nakaba saboda ni, da ace ni karabu da ni inyaso koda bayan na haihu ne sai ka amshi babynka.
wani irin abu yaji ya tokare masa zuciya akan maganar da tayi, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace zarah ba zan miki doleba indai kinsan bazaki iya zama da ni ba toh kifad'amin insha Allahu zan baki takardarki dan zan iya rayuwa ni kad'ai koda ace banda kowa,
Jikinsa tafad'a tare da fashewa da kuka tace kayi hak'uri ni ba haka nake nufiba wlh zan iya zama da kai a kowane hali.
Wani irin sanyi yaji a ransa,
Knocking d'in da akayine yasa yajanyeta daga jikinsa tare da mik'ewa yawuce yaje yabud'e.
Dr mu'az ne yana murmushi yace ranka yadad'e ga fa dinner chan a dining yana jiranku inkuma nan za'a kawo muku toh.
Yarima murmushi yayi yace ohk, gamunan zuwa nan yamik'a mai ledar hannunsa yace ga sak'on ansamo.
Kar6a yarima yayi yace nagode.
Koda yajuyo kallon zarah yayi da take kuka, itama d'ago kai tayi takalleshi, ahankali yace kukan fa?
Zarah turo baki tayi tace bakai bane kake fushi da ni.
Yarima wucewa yayi ya aje ledar saman bedside batare da ya kalletaba yace tashi muje kiyi dinner inyaso sai insanya miki drip d'in daga baya.
girgiza kai zarah tayi tace ni na k'oshi.
Kallonta Yarima yayi yace me kikaci da kika k'oshi?
Shuru tayi batace komai ba dan haka yarima yace oya tashi muje.
Mik'ewa zarah tayi taje tad'auko hijab d'inta tasaka sannan tabi bayan yarima suka fito.
A main parlour suka tarar da su zaune suna jiransu ganinsu yasa suka mik'e suka nufi dining.
Jamila ita tayi serving d'in kowa, zarah tunda tarik'e spoon d'in kallon plate d'in kawai take.
Yarima ahankali yad'ebo yaci idanunsa suna kan zarah, d'ago kan da zatayi ne suka had'a ido cikin sauri tad'ebo taci,
bawani dayawa yaciba nan yatsare zarah da ido har saida yaga ta d'an ci na kirki sannan yamik'e yakalli Dr mu'az da shima yake kallonsa yace Dr ba dai har ka k'oshiba.
Murmushi yarima yayi yace am ohk.
Jamila ce tace ranka yadad'e ko dai girkin ne baiyi makaba acanza maka wani?
No madam girkin ya yi min dad'i sosai kawai k'oshine nayi.
Zarah ma ganin zai bar wajen yasa tamik'e, kallonta jamila tayi tace gimbiya kodai kema abincin baiyi mikiba.
Girgiza kai tayi tace wlh Aunty jamila yai min dad'i sosai sai ma nazo kin koyamin.
Dariya jamila tayi tare da kallon mijinta tace sweet kana jin gimbiya tana tsokanata.
Dr mu'az murmushi yayi yace kibarsu na lura kamar abincin baiyi musu ba.
No kawai dai a gajiye muke muna buk'atar hutune....cewar yarima.
Ohk doctor ahuta lafiya, nan sukayi musu sallama suka koma masaukinsu, zarah wajen wardrobe tanufa dan tacire kayan jikinta dubawa tayi ammah ba sleeping dress ko kala d'aya, juyowa tayi takalli yarima kamar zatayi kuka tace baka sakomin kayan bacciba.
Kallonta yarima yayi batare da yayi magana ba, ganin haka yasa zarah tace ni kuma ban iya bacci da na jikina.
Toh ya kikeso inyi ina zan je yanzu insamo miki sleeping dress a yanzu, kibari zuwa gobe insha Allahu zan samo miki, yanzu kizo insa miki drip d'in.
Zarah turo baki tayi taje tahau gadon takwanta nan yarima yahad'a drip d'in yasa mata, bayan ya gama daga gefenta yayi zaune yazuba ma waje d'aya ido,
Zarah kallonsa take cike da tausayinsa dan ko ba a fad'aba yanayin yarima kawai zaka kallah kasan yana cikin damuwa kawai dai daurewa yakeyi baya nunawa.
maida idanuwanta tayi talumshe tana ji kamar tarungumo mijinta talallashesa ko ya rage damuwar da take tare da shi.
Wajen k'arfe tara yarima yatashi yaje yashiga wanka, lokacin da yafito daidai lokacin ruwan yak'are nan yacire mata sannan yawuce wajen wardrobe yafiddo kaya.
Zarah mik'ewa tayi itama tashiga toilet dan tawatsa ruwa.
Lokacin da tafito tsaye take d'aure da towel tana kallon yarima da yake zaune bakin gado ya dafe kansa, ahankali tataka ta isa inda yake, janye hannuwansa tayi da yadafe kan, nan yarima yad'ago yakalleta damuwa k'arara a fuskarsa.
Cike da rashin damuwa zarah tazauna saman cinyarsa nan idanunta suka cika da k'wallah ahankali tace meyasa kake shiga damuwa? Bakasan ganinka cikin irin wannan yanayin yana d'agamin hankali ba? Taya ni hankalina zai kwanta alhali kai gabad'aya naka hankalin a tashe yake, dan Allah kadaina shiga damuwa wlh ni ina tare da kai a kowane lokaci,,,,tak'arashe maganar tare da fashewa da kuka.
Yarima runtse idanunsa yayi yana jin wani iri akan kukan da takeyi rungumeta yayi a k'irjinsa nan zarah ta narke mashi tacigaba da wani irin kuka
Cikin wata irin murya yace please zarah kukan ya isa haka.
Cigaba tayi da kukanta, nan yarima yacigaba da lallashinta ammah tak'i daina kukan, tallabo fuskarta yayi yana kallonta yace wai zarah ya kikeso inyi ne? Nima kinaso inyi kukan ne?
Cikin sauri zarah tagirgiza kai tare da rage sautin kukanta.
Da mamakinta sai gani tayi yarima ya sa harshenta yana lashe hawayen fuskarta, ai nan sai kukan yatsaya tacigaba da binsa da kallo, daga karshe yatura bakinsa cikin nata yana mata tsotsar lolli pop, kamar daman zarah jira take nan tabiye masa suka cigaba da kissing d'in juna, tana ji lokacin da yazare mata towel d'in da yake a jikinta nan yacigaba da yawo da hannuwansa a jikinta, zarah ma hannuwanta tad'aura tana shafar lallausan gashin da yake kwance a k'irjinsa cikin wani irin siga.
Sun dad'e a haka sannan daga k'arshe yarima yad'auketa suka haye gado nan zarah ta dage sosai wajen ganin mijinta ya samu nutsuwa duk yadda takejin batada lafiya ammah haka tadaure taba yarima kanta, shi kansa ahankali yadinga bi da ita saboda ya san batada lafiya kawai dan ba yarda zaiyi da sai yahak'ura yabarta.
Bayan komai ya lafa yarima rungumeta yayi a k'irjinsa yana shafar gashin kanta, zarah ko cikin jikinsa talafe idanuwanta a lumshe tana numfashi ahankali.
kallon agogo yayi ganin lokaci ya ja yasa nan yajanyeta daga jikinsa yamik'e.
Zarah batare da ta bud'e idanunta ba tayi saurin rik'o hannunsa, yarima juyowa yayi yakalleta yace ya dai?
Cikin shagwa6a zarah tace nima ina son wankan.
Batare da ya yi magana ba nan yaduk'a yad'auketa yanufi toilet da ita saida yatara ruwa sannan yasafketa ciki, zarah sai a lokacin tabud'e idanunta ganin baida niyar shigowa yasa tace please kashigo muyi wankan.
Shuru yarima yayi.
Ganin baida niyar yin magana yasa tajingine kanta tare da runtse idanunta, da mamakinta sai ji tayi ya shigo cikin ruwan bud'e idanunta tayi tare da komawa jikinsa.
Ganin batada niyar yin wankan yasa yarima yayi mata sannan shima yayi nasa, wankan tsarkine kawai tayi da kanta bayan sun gama shagwa6a tasa mashi kan dole yad'auketa suka baro toilet d'in.
A saman gadon yadireta nan shima yakwanta tare da jawo blanket yalullu6esu, zarah jikinsa takoma takwanta nan yarungumeta ahaka har tayi bacci ammah yarima bai samu yarintsaba sai wajen k'arfe ukkun dare.
Da asuba sun so sumakara sallah, dan saida gari yad'an fara haske sannan suka tashi.
Bayan sunyi sallah baccinsu suka koma, basu suka farka ba sai wajen 11am.
Yarima yafara shiga yai wanka lokacin da yafito zarah ta gyara ko'ina k'amshi kawai yake tashi.
Bayan ya fito itama taje tashiga lokacin da tafito yarima har ya gama shirinsa cikin dakakkiyar shaddarsa ya yi gwanin kyau, gaban dreesing mirror zarah tatsaya nan tafara shafa lotion, tana ganin yarima ta cikin mirror d'in yadda yatsareta da ido, karaf suka had'a ido.
'Daga masa gira zarah tayi alamun ya dai?
Janye idanunsa yayi daga kallonta.
zarah tana cikin shafa takallesa kamar zatayi kuka tace wayana fa tana chan na baro ban zo da itaba.
Shuru yarima yai mata, ganin haka yasa tacigaba da shirinta nan tawuce tabud'e wardrobe tad'auko atamfa d'inkin riga da skirt nan tasaka sannan taje gaban mirror tamurza d'aurin kallabinta tare da feshe jikinta da turaruka, juyowar da zatayi nan suka had'a ido da yarima murmushi tasakar mashi tace nayi kyau?
Janye idanunsa yayi daga kallonta sannan yace ba laifi.
Matsowa zarah tayi kusa da shi kamar zatayi kuka tace kana nufin dai banyi kyau ba toh bari inje incanza kayan,,,juyawa tayi kamar da gaske.
Ruk'o hannunta yarima yayi baisan lokacin da yace kinyi kyau ba.
Juyowa zarah tayi tana murmushi tace kaima kayi kyau sosai k'albina.
Kallonta yarima yayi yanaso yagaskaka kalmar da tafito daga bakinta.
Kashe masa ido tayi tare da janyo hannunsa tad'aura saman cikinta tace babynka fa yunwa yakeji.
Janye hannunsa yayi daga cikinta yace muje kiyi breakfast.
Zarah tana rik'e da hannunsa suka tafo har zasu fita nan yarima yatsaya, kallonsa zarah tayi tace ya dai naga ka tsaya?
Shima kallonta yayi sannan yace haka zaki fita ba mayafi.
Oh sorry dear wlh mancewa nayi, nan tawuce taje tabud'e wardrobe tad'auko veil d'inta tayafa sannan tazo suka fita a jere.
Zaune suka tarar da mu'az da matarsa a main parlour suna hira, ganin su yarima yasa suka fad'ad'a fara'arsu mu'az ne yace sannunku da fitowa, hannu yarima yamik'a mashi sukayi masabaha sannan suka samu waje suka zauna
Jamila ce cikin girmamawa tagaishe da yarima nan ya amsa mata.
Zarah ma saida ta gaishe da mu'az sannan tagaishe da jamila.
yarimane yace ashe baka fita aikiba?
Taya zan fita bayan ina da manyan bak'i, ai yau ina tare da kai kwana zamuyi muna hira jiya ma dan naga agajiye kuke saisa nabarku,
Murmushi kawai yarima yayi batare da ya yi magana ba.
Jamila ce tamik'e tace muje kuyi breakfast gashichan tun d'azun yake jiranku.
Gabad'ayansu suka mik'e suka nufi dining nan jamila tayi serving d'in mijinta.
inda zarah itama tayi serving d'in yarima, ruwan lipton kawai zarah tazuba ma kanta tafara sha.
Kallonta jamila tayi tace gimbiya menene wannan zakisha?
Zarah kallon yarima tayi da shima yatsareta da ido sannan tamaida kallonta ga jamila saida tasakar mata murmushi sannan tace Aunty jamila banaso da madara nafi jin dad'insa a haka.
Ayyah Allah sarki ammah ai hakan baya maganin yunwa.
Murmushi Zarah tayi tace kar kidamu lafiya lou nake jina idan nasha.
Haka suka cigaba da breakfast d'in duk d'agowar da zatayi sai sun had'a ido da yarima,
Ganin batada niyar cin chips d'in yasa yarima yace ya za'ayi ruwan lipton kad'ai yarik'eki kici chips d'in mana.
Zarah yamutsa fuska tayi tace na k'oshi.
Mu'az ne yace toh in batasonsa dear ko kije kigirka mata wani abun taci.
murmushi Zarah tayi tace a'a abarsa kawai nafi jin dad'in hakan kawai.
Nan kowa yacigaba da breakfast d'insa, bayan sun gama Zarah taimaka ma jamila tayi suka kwashe kwanukan suka kai kitchen sannan suka dawo nan suka tarar da su yarima a parlour suna ta hira koda rabin hiran duk mu'az ne yakeyinta dan yarima daga uhm sai uhm-uhm sai in tabada amsace shine zaiyi magana, ganin haka yasa jamila taja Zarah sukaje parlournta suka zauna suna hira.
Zarah kallon wani pic d'in wata yarinya tayi da yake manne a bangon d'akin tace Aunty jamila wannan fa babynki ce?
Jamila kallon pic d'in da Zarah take kallo tayi sannan tace eh itace d'iyan da nahaifa tana da 2yrs tarasu tun daga kanta har yau ban k'ara ko 6atan wataba.
Cike da tausayi Zarah take kallonta tace Allah sarki, Allah yakawo masu albarka.
Cikin jin dad'i jamila tace Ameen gimbiya nagode sosai.
nan sukayi shuru nad'an lokaci sannan jamila takalli Zarah cike da sha'awa tace Allah yasafke mana ke lafiya musha suna.
Cikin jin kunya zarah tace lah Aunty jamila banda fa komai
Dariya jamila tayi tace gimbiya kenan ai saidai kifad'a ma wani ba dai ni ba dan daga ganin yanayinki ya nuna cikine da ke gaskiya kinyi sa'a da kika samu yarima a matsayin mijinki dan ina jin labarinsa sosai wajen mijina yarima mutumin kirkine.
Murmushi Zarah tayi sannan tace Aunty jamila kema ai kuna da kirki sosai.
jamila tana shirin yin magana sai ga Dr mu'az ya shigo kallonsu yayi yace a'ah kuna nan kuna ta hira.
Kallon juna sukayi sukai murmushi sai jamila tace eh mun baku wajene kud'an labarta, muma sai mukazo nan muyi namu dan kar mu matsa muku.
Dariya mu'az yayi yace eh kun kyauta gaskiya, yanzu ma fita zamuyi saisa nalek'o, kallon zarah yayi yace gimbiya kije prince yana son ganinko.
Ahankali tace toh sannan tamik'e tafita takoma masaukinsu, a bedroom tasami yarima zaune yana jiranta.
Daga gefensa taje tazauna, kallonta yarima yayi yace bakyajin magana ko? Na yi miki magana akan zama da yunwa ammah kink'i dainawa.
Zarah saman kafad'ansa tad'aura kanta cikin siririyar muryarta tace kayi hak'uri wlh idan naci amai zanyi.
Cike da tausayinta yace ammah ai sai kija su mama sud'auka bana kula da ke.
d'ago kanta tayi takalleshi sannan tace babu wanda zai ce baka kula da ni saidai wanda baisan wanene yarima ba,,,tak'arashe maganar tare da kashe mai ido d'aya.
Yarima jan hancinta yayi yace bakijin magana ko?
K'irjinshi takwantar da kanta cikin shagwa6a tace ina ji man, inshirya muje tare?
Rungumeta yayi sannan yace ina zamuje tare?
Turo baki tayi tace inda zakaje man.
No kar kidamu kiyi zamanki ba wani dad'ewa zanyi ba, kifad'i abinda kikeso insiyo miki.
Murmushi zarah tayi tace duk abinda kasiyo min inaso.
kallonta yarima yayi yace kidai fad'a kar insiyo abinda baiyi mikiba.
Wani irin fari tayi mashi da ido sannan tace za6in mijina shine nawa indai ya yi maka toh nima zaiyi min kar kadamu my prince.
Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yace shikenan, mik'ewa yayi nan zarah itama tamik'e tabi bayansa har suka fito main parlour lokacin mu'az yana zaune yana jiransa ganin yarima yasa yamik'e.
Jamila da zarah har wajen k'ofa suka rakasu sukai musu Allah yakiyaye hanya sannan suka dawo suka zauna suna hira.
_Comment_
*Nd*

_Wishing an amazing day and many great things to come to a wonder person. *Happy Birthday my dear umm abideen🎈*_
*PAGE* 5⃣9⃣
Wajen k'arfe biyu su yarima suka dawo lokacin zarah tana a room d'insu tsaye gaban dreesing mirror tana kwalliya yarima yaturo k'ofan yashigo,
Dagudu zarah taje tafad'a jikinsa cikin wata irin siririyar murya tace sannu da zuwa my prince.
Rungumeta yayi sannan cikin kasalalliyar murya yace yauwa ya gidan?
'Dago kai zarah tayi suka had'a ido tace gida ba dad'i saboda baka nan ammah yanzu da kadawo yayi dad'i.
Yarima baisan lokacin da murmushi yasu6uce masaba yace tsokana ko?
Marairaicewa tayi tace dagaske fa.
Rik'o hannunta yayi yace muje parlour kiga abinda nasiyo miki,
Zarah bata musaba tabisa suka fito parlour.
Babban trolly ne tagani aje koda yarima yabud'e cike yake taf da kaya, saman kujera yazauna yace duba kiga.
Zarah bin kayan tayi da kallo sannan tafara d'agawa d'aya bayan d'aya daga gowns ne sai English wears jibgi d'aya da sleeping dress, rigunan tafara d'agawa daga mai budad'en k'irji sai 'yar firit wadda bama zata rufe cibi ba, wasu ma sharashara ne, sai mini skirt da wando atak'aice dai dukkan kayan ba wanda zaka iya zama da su cikin gida bane, saidai in daga kai sai mijinkane.
'Dago kai tayi takalli yarima murmushi yasakar mata yace ya sunyi?
Itama zarah murmushi tayi tace sunmin kyau sosai.
Cikin jin dad'i yarima yace toh kije kigwada, zarah kallonsa tayi tace toh ammah ai kayan bazasu sanyuba cikin gidannan tunda bamu kad'ai bane.
Yarima jingine kansa yayi da kujera sannan yace zasu sanyu man in zaki fita ba sai kidinga d'aura zaneba.
Shuru zarah tayi nan taja trollyn tashiga bedroom da shi, d'auko kayan tayi tafara dubawa tana gwadawa a jikinta daga 'yar riga iya cinya, sai wacce bata rufe cibiba sai marar hannu, gunguni tafara tace inbanda abin Yarima ya za'ayi yasiyo min wad'annan kayan sai kace wata arniya,,,daidai ta d'auko wata zata saka sai gashi ya shigo.
Juyowa tayi takallesa yana tsaye bakin k'ofa ya hard'e hannuwa, murmushi suka sakar ma juna sannan tajuya tasaka rigar,
Kallon kanta tayi ta mirror rigar shara-shara komai na jikinta a waje yake ga iyakar tsawonta iya cinya.
Tana shirin cirewa sai jin yarima tayi ya rungumeta ta baya, lumshe idanuwanta tayi tana murmushi, yarima ta cikin mirror d'in yake k'are mata kallo, ahankali cikin kunnenta yace kinyi kyau baby.
Zarah bud'e idanunta tayi ta mirror suka had'a ido nan tasakar mai murmushi sannan tace nagode,
Gyad'amata kai kawai yayi sannan yajanye jikinsa daga nata, Zarah tana shirin cire rigar yace please kibarta.
Juyowa tayi takallesa sannan tace lunch fa zamuje kayi,
Duba agogon hannunsa yayi sannan yace no zan fara wanka before inyi lunch.
Ohk, bara inje inhad'a maka ruwan,
Yarima baice komai ba yawuce yad'auko towel,
zarah toilet tawuce tahad'a mai ruwan wanka lokacin da tafito ganin yana cire kaya yasa tafito takoma parlour.
Zarah tana zaune yafito sanye cikin k'ananun kaya sunyi mai gwanin kyau.
Tsaresa tayi da ido tana kallonsa.
Ganin batada niyar daina kallonsa yasa yarima yace ya dai?
Janye idonta tayi cike da jin kunya tare da mik'ewa tace bari incanza kaya muje kayi lunch, ta gefensa tatafo zata ratsa tawuce, jawota yarima yayi tafad'o jikinsa, wani irin kallo yake aika mata da manyan idanunsa kallon da yake kashe mata jiki sannan yace ba sai kin canza kayaba kisaka hijab da zane kawai sai muje.
Cikin kasalalliyar murya tace toh, ba yadda ta iya haka tawuce bedroom tad'auko zane, cikin ranta tana cewa ina ma ace guy d'innan sona yake da naji dad'i.
Hijab d'inta har k'asa tad'auko tazura sannan tafito tasamesa a parlour yana jiranta, tsaye tayi tana kallonsa ganin yadda ya jingine kansa da kujerar da yake zaune samanta, cike da tausayi tabisa da kallo dan ko ba'a fad'aba tasan tunani yakeyi.
Gyaran murya zarah tayi nan yarima yad'ago kai yakalleta yace kin fito?
d'aga masa kai zarah tayi batare da tayi magana ba, nan yamik'e yana gaba tana biye da shi suka fito main parlour basu tarar da kowaba cikinsa nan suka wuce dining, zarah kujera tajawo masa yazauna sannan tazauna gefensa nan tayi serving d'insa, ganin bata da niyar zuba nata yasa yarima yace ke ina naki?
Yamitsa fuska zarah tayi sannan tace ni na k'oshi.
Kallonta yarima yayi yace me kikaci da zaki k'oshi? Turo baki zarah tayi tace ban iya ci.
Yarima batare da yayi magana ba yad'ebo yace bud'e bakin.
Zarah ganin fuskarsa ba alamun wasa yasa tabud'e bakinta yasaka mata, tana yatsine fuska tana tauna ahaka yakeci yana feeding d'inta itama, har saida yatabbatar da ta k'oshi sannan yabarta nan suka tashi suka koma part d'insu.
Suna shiga zarah tacire hijab d'in tashiga bedroom takai cikin wardrobe ta aje sannan tafito tasami yarima a parlour zaune ya tsura ma waje guda ido, wajen da yake tanufa bai ankaraba sai jinta yayi a jikinsa, kallonta yayi nan tasakar mashi k'yataccen murmushinta, shima maida mata yayi tare da d'aura hannunsa saman cikinta yana shafa yace kinga babyna shima ya samu wadataccen abinci ammah da sai kizauna da yunwa kina k'wararman shi.
Zarah kamar zatayi kuka tace toh ai shine yake wahalar da ni, kuma baka ganin laifinsa sai nawa shi dayake ana sonsa ammah ni ba a sona.
Yarima kallonta yayi yace zarah wanene baya sonki?
K'wallah ce tacika mata ido tace kai man, kawai dai kana zaune da ni ne ba dan kana sonaba,,,tak'arashe maganar tare da fashewa da kuka.
Cike da mamaki yarima yake kallonta ganin batada niyar daina kukan yasa yace, kukan ya isa haka zarah toh ke tsakaninki ga Allah kina sona?
Tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace akwai macen da zata ganka tace bata sonka?
Tsareta yayi da ido yace tambayarki nayi kiban amsa
Kwantar da murya tayi tace ina sonka sosai,,,cikin sauri tafad'a k'irjinsa tare da rufe idonta alamun kunya.
Murmushi me sauti yarima yayi sannan yace yau kika fara sona ko?
Girgiza kai zarah tayi cikin sauri sannan tace ni tun tuni nake sonka.
Shafa bayanta yarima yayi yace toh nagode.
'Dago kai tayi takallesa tayi kalar tausayi sannan tace toh kai baka sona ni ba ajin aurenka bace ko?
Yanayin yadda tayi maganar yaso yaba yarima dariya, murmushi yayi sannan yace ni ban ce ba.
Langwa6e kai tayi tai kalar tausayi tace toh kana sona?
Jan hancinta yayi yace ko ban furtaba jikina ai ya isa yanuna miki amsar tambayarki.
Girgiza kai tayi tace babu abinda zan iya ganewa ta haka nafiso kafurta min da bakinka, in ma bakasona toh ya zanyi dole in hak'ura k'ila wani lokacin zaka soni nidai fatana kar inhaihu babyna yataso yaga daddynsa baya son mahaifiyarsa.
Tausayinta yakama yarima goge mata hawayen fuskarta yayi sannan yace kikwantar da hankalinki zarah domin duk kin mallaki abinda kowane namiji zaiso mace dan shi, kuma da ace bana sonki kina tunani zan amince inrabu da kowa nawa inza6eki?
Girgiza kai zarah tayi tare da maida kanta takwantar a k'irjinsa tana jin wani irin dad'i a ranta son mijinta yana fizgarta ga tausayinsa da yadabaibaye mata zuciya, hawaye yana zuba daga idonta tace nagode sosai my soulmate insha Allahu bazan ta6a yin abinda zai 6ata maka raiba, nayi ma alk'awali zan kasance da kai a kowane hali, fashewa tayi da kuka tace ina sonka sosai zan iya rasa komai saboda kai, ina fata kaima zaka kasance da ni duk rintsi duk wuya.
Wani irin sonta yaji yana zagaye duk illahirin jikinsa shI kansa mamakine yakamasa ganin a lokaci guda ya ji kamar an dasa masa sonta a k'irjinsa, matseta yayi jikinsa tare da runtse idanunsa yace baby nima ina sonki insha Allahu nima babu abinda zaisa inrabu da ke indai zaki cigaba da sona toh nima zan cigaba da nuna miki *K'AUNA* har k'arshen rayuwata.
Zarah dasauri tad'ago kai takallesa dan jin maganar tayi kamar a mafarki yarima ya furta mata kalmar so.
'Daga mata kai yayi, alamun eh.
cikin jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai insha Allahu nikuma zan cigaba da nuna maka k'auna zallah.
Ringing d'in da wayar yarima tafara yasa yajanye Zarah daga jikinsa yamik'e yaje yad'auko dan yasan mu'az ne kawai yake da new number d'in da yacanza.
Picking yayi tare da yin sallama
Daga chan 6angaren mu'az amsa masa yayi tare da cewa sorry prince kun fito lokacin mun shiga ciki da madam.
Murmushi yarima yayi yace kar kadamu ai nayi muku uzuri.
Dr mu'az dariya yayi Sannan yace godia muke ranka yadad'e, ina fata princess zata aramin kai mud'an fita.
Yarima kallon Zarah yayi da tatsaresa da ido sannan yace toh zan dai tambayeta inji idan zata amince.
toh kodai inzo da kaina intambaya?,,cewar mu'az.
Murmushi yarima yayi yace kar kadamu ganinan zuwa.
Bayan sun gama wayar kallon Zarah yayi yace princess bari inje indawo.
6ata fuska Zarah tayi tace yanzu saboda Allah ba zaya barka kazauna da matarkaba duka yaushe kuka dawo?
Matsowa yarima yayi yazauna gefenta tare da shafar fuskarta yace kar kidamu baby bazamu dad'eba.
Zarah turo baki tayi tace nidai uhm-umh.
Tallabo fuskarta yayi yakai bakinsa cikin nata yafara aika mata da wani mayen kiss, gabad'aya yarikita zarah jikinta yamutu, ahankali yazare bakinsa daga nata yace baby sai nadawo.
Kasa magana zarah tayi saidai kai kawai tad'aga mashi dan gabad'aya jikinta yai sanyi.
murmushi yayi sannan yamik'e yafita.
Da kallo tabisa har yaficce sannan tajingine kanta da kujerar da take zaune sama, nan tashiga maida numfashi, ita kanta tana jinjina ma yarima dan duk hanyar da zaibi yarikita mace ya santa, hannu takai tashafa le6enta tana murmushi.
Tana zaune taji ana knocking d'in k'ofa cikin sauri tamik'e tashiga bedroom tad'auko hijab tasaka sannan tadawo tabada izinin ashigo.
Jamila ce taturo k'ofan tashigo had'e da yin sallama.
Zarah kallonta tayi tana murmushi tace oyoyoo Aunty jamila.
Zama jamila tayi kusa da Zarah sannan tace najiki shuru tun d'azun baki fitoba,
Murmushi zarah tayi tace wlh kau Aunty jamila nima inata so infito sai gashi kin rigani.
Hmm kedai ko prince ne yarik'e ki dan da alama prince d'an love ne.
Dariya zarah tayi tace kai Aunty kin bani dariya wlh, ku ma fa damukaje yin lunch kuna chan.
Dariya tayi tace au kin rama kenan.
Nan suka cigaba da hira sai gab da magrib sannan jamila takoma part d'inta.
Bayan sallar isha'i zarah wanka tayi tashirya cikin d'aya daga cikin sleeping dress d'in da yarima yasiyo mata, riga da wando iya cinya, tufke gashin kanta tayi tadawo parlour tazauna tana jiran yarima, kad'an kad'an ta kalli agogon bango dan a k'agare take yadawo.
Sai wajen k'arfe tara sannan yaturo k'ofan yashigo, juyowa tayi dasauri takallesa,
tsaye yayi yahard'e hannuwansa shima yana kallonta , mik'ewa tayi dagudu tanufi inda yake tafad'a jikinsa,
Rungumeta yarima yayi, zarah cikin shagwa6a tace shine kaje kayi zamanka kabarni ko?
Yarima shafa kanta yayi yace sorry baby yanzu gani ai nadawo inkuma ba'a murna da dawowar tawa sai inkoma.
'Dago kai tayi takallesa idanuwanta sukayi rau-rau da hawaye tace kuma zaka iya komawa?
Murmushi yarima yayi tare da janyeta daga jikinsa yace toh sarkin kuka yanzu dai muje kitaimaka min inyi wanka dan agajiye nake.
Rik'o hannunsa zarah tayi suka shiga bedroom towel tad'auko tamik'a mashi sannan tawuce bathroom tahad'a mashi ruwan wanka,
koda tafito yana tsaye inda tabarsa, kallonsa tayi tace na ma d'auka ka cire kayan?
Wani irin kalloh yayi mata wanda yake sakar mata da kasala sannan yace baby ke fa nake jira kizo kitayani cirewa.
Zaro ido zarah tayi tace karufan asiri wlh ba zan iyaba.
Murmushi yarima yayi tare da tunkaro inda take yace zaki iya man, ai lada zaki samu.
kallonsa tayi nan yad'aga mata gira.
cikin sauri tajuya zata bar wajen, janyota yarima yayi yace dole fa sai kinyi min abinda nakeso kinsan ban ta6a neman komai narasaba a rayuwata kuma umurni nabaki indai kinaso mushirya dole kiyi abinda nakeso.
Zarah kallonsa tayi ganin dagaske yake yasa tafara cire masa button d'in rigarsa, ahankali tacire rigar nan tasafke idanunta akan lallausan gashin da yake kwance saman k'irjinsa, d'ago kai tayi takallesa nan yad'aga mata gira.
Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace please kataimaka kacire wandon da kanka,,,tafad'i hakan tare da mik'a mashi towel.
Ganin yadda tamarairaice yasa yarima yayi Murmushi sannan yakar6i towel d'in.
Dasauri tajuya masa baya dan yacire.
Yarima koda yacire, saidai ji zarah tayi ya sungumeta ya nufi toilet d'in da ita bai zarce ko'ina ba sai cikin ruwan da tahad'a mashi nan shima yashiga,
Zarah kunyace takamata cikin sauri tarufe fuskarta da hannunta tare da sa kukan shagwa6a.
Yarima bai damuba nan yazage zip d'in rigarta yacire rigar sannan yarabata da wandonta,
Daga gefe yakoma yana wankansa ammah idanuwansa suna a kan zarah.
Jin ya kyaleta yasa tajanye hannuwanta daga fuskarta, karaf suka had'a ido da yarima da yake wankansa, cikin sauri tamaida idanunta tarufe tana jinsa yagama wankan yafita yabarta cikin ruwan.
Saida taji fitarsa sannan tabud'e idanunta nan tayi wankan sannan tad'auro towel d'inta tafito.
Tsakiyan gado tahangosa kwance ya yi matashin kai da hannuwansa, ganinsa a wannan yanayin yasa taji ba dad'i a ranta takowa tayi tazo tahau gadon tare da kwanciya saman k'irjinsa, cikin 'yar siririyar muryata tace meyake damunka?
Batare da ya kalletaba yace ba matsalarki bace kikyaleni.
Zarah kamar zatayi kuka tace wlh matsalarka tawace indai kana cikin yanayinnan toh nima damuwa nake shiga.
Wani irin kallo yarima yayi mata sannan yace wai har zan nemi abu wajenki kik'i yimin, hakan ya nuna min son da kike ik'irarin kina min toh ba gaskiya bane.
Zarah jikintane yayi sanyi tace kayi hak'uri wlh kunyarka ne nakeji ammah bazan k'ara sa6ama umurninkaba.
Shuru yarima yayi yakyaleta.
Tallabo fuskarsa tayi tace please my soulmate *KAYARDA DA NI*
sai a lokacin yarima yakalleta yace shikenan na yarda da ke baby, atare suka sakar ma juna murmushi nan yarima yakai hannu yacire towel d'in da take d'aure da shi.
kafin tayi magana har ya birkiceta takoma saman katifar nan yadawo kanta.
Zarah ga jikinta bata jin dad'insa ammah haka tadaure taba yarima kanta yayi yadda yakeso,
Saida yagaji dan kansa sannan yabarta.
Shi kansa yana jinjina ma dauriyarta dan ya san ya bata wahala sosai.
daga k'arshe d'aukanta yayi yanufi toilet da ita dakansa yayi mata wankan tsarki, shima yatsarkake jikinsa sannan yad'aukota suka fito.
Saman bed d'in yahau da ita nan suka kwanta tana manne a jikinsa yana shafa gashin kanta, cikin kunnenta yake rad'a mata cewa nagode sosai zarah, hak'ik'a kina sani cikin farin ciki Allah yaimiki albarka yadda kike faranta min kema Allah yabaki masu faranta miki.
Zarah k'ara shigewa tayi jikinsa cike da jin kunya,,ahaka bacci medad'i yayi awon gaba da su.
________________
A chan masarautarsu yarima ko bayan yarima yabar gidan, memartaba kallon family d'in nasa yayi da gabad'aya kowa yake cikin yanayi, saida yak'are musu kallo d'aya bayan d'aya sannan yace toh kunga dai abinda yafaru, yarima ya ci amanata ya nuna min ban isa da shi ba dan haka tunda ya za6i matarsa a kanmu shikenan yaje na sallama mata shi yaje yaga idan za'a iya rayuwa ba dangi ko dashi ko babu shi gidana ba zai k'i cigaba da tafiya daidai ba,
sannan yakalli sumayya da take ta kuka yace kekuma sai kiyi hak'uri da k'addararki dan dama chan Allah ya k'addara yarima ba mijinki bane na da'iman, dan haka daga yanzu zakije kifara iddah kafin muga yarda Allah zai tafiyar da al'amarinsa, saidai muce Allah yamusanya miki wani mijin da zaifi zama alkhairi agareki.
Yanzu kai Ahmad kaine yakamata kakasance magajin garina a yanzu.
Sultan Ahmad k'ara duk'ar da kansa yayi cike da biyayya yace ranka yadad'e ka gafarceni ba nak'iba ammah da d'an uwana aka nad'a magajin garin.
Girgiza kai memartaba yayi yace na riga na gama magana, dan haka idan da mai magana zai iyayi.
Kowa shuru yayi, ganin ba mai niyar yin magana yasa memartaba yasallamesu nan duk suka duk'a suka kwashi gaisuwa sannan suka tashi kowa yawatse cike da damuwa a ransu.
Ummi koda takoma part d'inta a parlour saman kujera tazauna tarushe da kuka, rahma da husna da suke bayanta tsaye sukayi suna kallon mahaifiyar tasu cike da tausayinta suma hawayen yana fita daga idanunsu.
Wajen da take suka nufa cikin sauri suka fad'a jikinta suna kuka, rahma ce tayi k'arfin halin cewa ummi kikira bro a waya please kice yarabu da matarsa yadawo gida wlh muna sonsa bamu iya zama babu shi, meyasa yaza6eta akan mu, dan Allah kice yadawo
Ummi cigaba tayi da kukanta cike da tausayin d'an nata, ahankali tace rahama na yarda da yarima nasan abinda zai iyayi da wanda bai iyawa kuma na tabbata akwai abinda sumayya tayi masa wanda yaja har yasaketa dan ban yarda da maganar da tayiba a gaban memartaba.
Rahama tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace ummi bakya tunanin ko wacchan matar tasace tashiga tsakaninsu har hakan yakasance?
Girgiza kai sultana bilkisu tayi tace bana tunanin haka daga wajen zarah dan zarah mutuniyar kirkice.
Kidaina cewa haka ummi kinsan fa ita za6insa ce sumayya kuma za6in iyayenmu ne kinga daman bason sumayya yakeba,,,,cewar Aunty husna.
Murmushi ummi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace zarah ba za6in suhail bace kamar yarda yake zaune da sumayya toh itama biyayyace kawai tasa ya aureta.

0 comments:
Post a Comment