Ummi cigaba tayi da cewa Zarah za6ina ce ni da mahaifinku mu mukasa yarima ya aureta saboda tunda sukayi aure da sumayya baida kwanciyar hankali, bai ta6a zuwa yakawo min k'orafiba koda sau d'aya, gudun kar d'anmu yashiga cikin wani yanayi yasa ni da mahaifinku muka had'asa aure da zarah batare da kowa ya san mune silar aurenba sai yanzu da ku kukasani.
Su rahma ido suka zuba ma mahaifiyar tasu suna kallonta cike da mamaki,
Nan ummi tacigaba da cewa kuma zarah tana zaune da yarima tsakani ga Allah na yarda da tarbiyarta kuma da kuke maganar ko magani tayi masa, ko d'aya ba haka bane.
mace zata iya mallakar namiji ta hanyar kulawa da yi masa duk abinda kikasan yana so dan haka nima nafi tunani ta haka zarah tasamu fada sosai a wajen suhail.
Hawayene yacigaba da fita daga idanun ummi girgiza kai ummi tayi tace burina duk inda d'ana yake sukasance suna cikin k'oshin lafiya shi da matarsa.
Su Husna jikin ummi suka fad'a suna kuka cike da tausayin d'an uwan nasu.
Sultan Ahmad koda suka fito daga fada kallon d'an uwan nasa yayi cike da jin kunyan abinda yarima ya aikata ma d'iyarsa, cike da damuwa yabud'e baki zaiyi magana nan sultan abbas yatari numfashinsa yace kar kace komai yaya indai akan mutuwar auren sumayya ne nasan wani abu tayi ma d'ana saisa ya yanke mata wannan hukuncin kuma dan memartaba yana cikin 6acin rai bai tsaya yasaurari ta bakinsaba saisa abun yakasance haka yanzu dai addu'a zamu cigaba da yi masa duk inda yakasance Allah yatsare mana shi, kar kasa komai a ranka yayana zumuncin mu mai d'aurewane har k'arshen rayuwarmu tun bamu mallaki 'ya'ya da mataba muke tare taya zasuzo a yanzu kayi tunanin zasu shiga tsakaninmu?
Sultan Ahmad jinjina kai yayi cike da jin dad'in kalaman d'an uwan nasa yace nagode sosai abbas samun d'an uwa irinka sai antona a fad'in duniyarnan
Murmushi sultan Abbas yayi yace kar kadamu ai duk a wajenka nakoyi wannan halayyar.
Haka suka rabu kowa yanufi part d'insa cike da k'aunar d'an uwansa.
Sultan Ahmad koda yashiga yatarar da su sultana bilkisu zaune suna kuka, tsayawa yayi daga bakin k'ofa yana kallonsu yana jin wani irin k'unci a ransa, ganinsa yasa ummi tataso cikin kuka tafad'a jikinsa tace dadyn suhail yanzu shikenan na rasa d'ana bana k'ara ganinsa?
Sultan Ahmad janyeta yayi daga jikinsa yaje yazaunar da ita sannan shima yazauna a gefenta, cike da k'warin gwiwa yace bilkisu ke kanki kinsan abinda suhail ya aikata bai kyautaba kiduba kiga d'iyar d'an uwana jininsa yayi ma saki d'aid'aya har ukku, har yana ik'irarin cewa ta haramta ma kansa sumayya, na d'auka yarima yana da tunani koma me sumayya ta aikata masa ai baidace yaimata saki ukku ba, toh taya kike tunanin abinda ya aikata bazai 6ata mana rai ba?
Sultana bilkisu tsagaitawa tayi daga kukan da take tace nasan haka ranka yadad'e ammah hukuncin da aka yanke ma suhail ya yi masa tsauri dayawa yanzu bamusan yanayin da zai shigaba ga matarsa da ciki ina zasuje wa suka sani?
Rik'o hannunta sultan Ahmad yayi yace bilkisu kikwantar da hankalinki suhail fa ba yaro bane insha Allahu duk inda zasu kasance suna cikin k'oshin lafiya addu'a kawai zamucigaba da yi har Allah yataimakemu memartaba yasafko daga fushin da yake insha Allahu suhail zai dawo yayi rayuwa cikin danginsa.
Murmushin jin dad'i ummi tayi tace hakane ranka yadad'e Allah yakawo mana ranar da hakan zai kasance da nafi kowa farin ciki,
Su rahma da suke gefe suna sauraren iyayen nasu cike da jin dad'in maganar da mahaifinsu yayi sukace Allah dai yatsare mana su.
Ameen sultan Ahmad yace tare da mik'ewa yawuce part d'insa.
A 6angaren su sumayya koda suka isa 6angaren iyayenta tusa sultana sadiya tayi a gaba tana kuka har da mirgina lallashinta sultana sadiya take ammah kamar k'ara tunzurata take, sumayya kuka take sosai tana cewa dole sai ta koma d'akinta wlh bazata ta6a yadda ba zarah asiri tayi tarabasu da yarima.
Daga k'arshe jugum sultana sadiya tayi tana sauraren d'iyartata, suna cikin haka sai ga sultan abbas ya shigo ganin sumayya kwance k'asa tana mirgina yasa yadaka mata tsawa yace ke menene haka kikeyi?
Sumayya tashi tayi a zaune tana cigaba da kukanta.
Sultana sadiya ce tayi k'arfin halin cewa yauwa gama kanan dan Allah kazo kataimaka asan yadda za'ayi sumayya takoma d'akinta wlh tana son mijinta sosai.
Murmushi sultan abbas yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace sadiya kenan ai ban d'auka zaki mance da saki nawa bane suhail yayi mata,
Ke kuma,,yanuna sumayya da yatsa yace garin haukanki kinje kin kashe aurenki na tabbata suhail ba zai ta6a yimiki saki ukku ba batare da wani k'wak'waran daliliba, toh yanzu wa gari yawaya? Sai kizo kujera da mahaifiyartaki kiyi ta zaman gida, babban bak'in cikina ma da kikayi silar raba yarima da family d'insa.
Cikin 6acin rai sultana sadiya tace haba Alhaji wannan wane irin cin mutuncine tun a gaban memartaba kake ta kware ma d'iyarka baya toh inaso kasani hannunka baya ru6ewa kacire kayar kuma ni nasan sumayya ba abinda zatayi ma yarima wanda zaisa yaimata wannan saki haka saidai idan wacchan munafukar matsiyaciyar yarinyarce tashiga tsakaninsu.
Dakata ke banson shashanci nalura kamar ke kike goya ma yarinyar nan baya tana yadda takeso dan haka kukiyayeni ko gabad'ayanku insa6a muku, wlh kikiyayi lokacin da zakiji kunya dan naga kina d'orema k'arya gindi, ni a wajena da yarima da sumayya duk d'ayane dan dukansu 'ya'yanane bana goyon bayan kowa sai gaskiya dan haka gatanan tayi ta zaman gidan zata gane ai idan iyaye da miji d'ayane, duk dai inda mace takasance komai gatanta toh gidan miji shine kwanciyar hankalinta,
Sannan ke sumayya ina k'ara tunatar da ke saki ukku ne yarima yaimiki bakida ko sauran igiya d'aya dan haka dole yanzu kicire tunanin komawa gidansa dan yariga da yayi miki nisa,,,,sultan abbas yana kaiwa nan a zancensa yawuce yashige part d'insa cike da 6acin rai.
Sultana sadiya da kallo tabisa dan gabad'aya ya kashe mata baki ga takaici da yacikata, cikin kuka sumayya tace ummah yanzu shikenan na rasa yarima ya zanyi da rayuwata.
Cikin 6acin rai sultana sadiya tace ai ga irintanan ke kibar ganin ina goyon bayanki kema ai kina da naki laifin a ciki yanzu gashinan kinja mijina nima yad'au fushi da ni yadda kika kaso aurenki toh nima bazakiyi silar mutuwar nawaba dan haka dole kihak'ura kicire suhail a ranki tunda bashikad'ai bane namiji a duniyar mutumin ma da baya k'aunarki baisan darajarkiba toh miye amfanin zama da shi hak'urin dai zakiyi Allah yamusanya miki da mafi alkhairi.
Sumayya ganin mahaifiyarta kamar itama tana nema takware mata baya dan haka tamik'e tawuce tashige room d'inta tana kuka.
________________
Yarima koda yafarka baccin da suka koma bayan sallar asuba kallon agogo yayi ganin har 11 ta yi yasa yajanye zarah daga jikinsa, zaune yayi yana k'arema fuskarta kallo cike da sonta dan yanzu ya tabbatar ma kansa yana son zarah, janye gashin da yasafko wajen idonta yayi nan yaduk'a yakai mata peck a goshi, ahankali zarah take bud'e idanunta nan tasafkesu akan fuskar yarima, murmushi tasakar masa tare da rik'o hannunsa d'aya.
Shima murmushin yamaida mata yace baby kin tashi?
Mik'a zarah tayi tace jikina ciwo yakemin, jan d'an k'aramin bakinta yarima yayi yace toh muje inmiki wanka.
Turo baki zarah tayi tace saidai kad'aukeni dan ban iya tashi.
Hmm shikenan yadda kikeso haka za'ayi ai nasan nine nagajiyar da ke d'in,,yafad'i hakan tare da d'aura hannunsa saman cikinta yana shafa.
Ido zarah tazuba ma kyakkyawar fuskarsa bata ko kyaftawa, hura mata ido yarima yayi nan talumshe idanunta cike da jin kunya.
Murmushi yayi tare da d'aura kansa saman k'irjinta yace baby kallon fa?
Zarah batare da ta bud'e idanuntaba tace ni ba kai nake kallo ba,
Bakinsa yakai yad'an ciji le6enta har saida tad'anyi k'ara sannan yace toh wa kike kallo.
Rik'e le6enta tayi kamar zatayi kuka Sannan tace ni mijina na kallah ko laifine dan na kallesa?
Batare da ya bata amsaba yad'auketa yanufi toilet da ita atare sukayi wanka sannan suka fito suna rungume da juna, tana tsaye gaban dreesing mirror tana kwalliya nan yarima yai mata tsaye yana kallon kwalliyarta kashe mashi ido tayi tace nayi kyau?
Ta6e baki yarima yayi yace ko d'aya bakiyi kyauba,
Haushine yakama zarah nan ta6ata fuska tace Allah a'a
K'unshe dariyarsa yayi yace ammah ai kinsan nafiki kyau ko?
Harararsa tayi cikin wasa sannan tace saidai muzo d'aya ammah bakafiniba.
Murmushi yarima yayi tare da rungumota jikinsa yace ban yardaba nan yajanyo wayarsa yai musu selfie.
Zarah zame jikinta tayi tanufi wajen wardrobe nan tad'auko wata gown cikin kayan da yarima yasiyo mata tasaka nan tanad'e gashinta kamar gammo sannan tayi rolling d'in d'an k'aramin veil d'in kayan nan tayi gwanin kyau, juyowa tayi takalli yarima da yatsareta da ido tace toh yanzu ya kaganni?
Murmushi yayi yace har yanzu dai ina akan bakana, dariya tayi nan tamatso yacigaba da yi musu pic's saida sukayi kusan kala ashirin ganin baida niyar dainawa yasa tajasa suka fito main parlour nan suka tarar da mu'az da matarsa nan suka zauna suka gaisa daganan suka wuce dining gabad'ayansu suna breakfast.
Zarah da yarima saidai kallon love suke aika ma junansu mu'az da jamila suna lura da su saidai suyi murmushi ahaka har suka gama breakfast d'in nan suka hau yin hira, yarima kallon mu'az yayi yace abokina inaso insamu gida insiya dan gaskiya ba zan iya cigaba da zama a nan ba saboda da takura muzauna muku nan zamu d'aura muku nauyi nikuma banason hakan indai kana ganin ba matsala toh kasanya min cigiyar gida.
Cike da damuwa Dr mu'az yace ranka yadad'e banta6a tunanin jin haka daga garekaba da kai da kaya ai duk mallakar wuyane, idan har kai ka mance abinda kayimin toh ni ban manceba kuma bana iya mancewa, wlh yarima zan iya sadaukar da duk abinda namallaka a gareka dan ka fiye min komai dan Allah kataimaka kucigaba da zama da mu Indai akwai abinda mukeyi muku wanda bakuso kusanar da mu insha Allahu zamu daina, gyad'a kai jamila tayi tace eh wlh zamu daina dan muna jin dad'in zamanku a tare da mu.
Yarima murmushi yayi yace kar kudamu ba wai saboda wani abu nakeson barin gidanba kawai dai dan kar mushiga hak'inku ne.
Girgiza kai mu'az yayi yace kar Allah yakawo ranar da zanji wani abu game da zamanmu tare nidai ka amince mucigaba da zama wlh munajin dad'in zama tare da ku.
Yarima kallon zarah yayi nan tasakar mashi murmushi, kallonsa yamaida ga mu'az yace shikenan na amince ammah ban d'aukar maka alk'awaliba.
Murmushin jin dad'i mu'az da matarsa sukayi nan sukaima yarima godia daganan suka cigaba da hira koda rabin hirar mu'az da matarsa sai zarah ne sukeyi dan shi yarima da ido yake binsu saidai yayi murmushinsa mai tsada.
Sun dad'e suna hirar sannan Dr mu'az da yarima suka tashi suka fita inda zarah da jamila suka shiga kitchen dan suhad'a musu lunch, a tare sukayi komai duk yadda jamila taso zarah tabarta tayi ita kad'ai ammah zarah k'iyawa tayi saida aka gama komai tare da ita sannan suka kai saman dining suka jera daga nan kowa yawuce part d'insa dan yashirya jikinsa.
Koda yarima yadawo Zarah taimaka masa tayi yai wanka yashirya bayan sungama cin abinci part d'insu suka dawo nan tayi d'aid'aya saman cinyarsa tana zuba masa shagwa6a yana biye mata a ranar haka suka kasance takasa tatsare indai ba masallaci yarima zaijeba toh suna manne har dare yayi, taje tahad'o musu coffee a one cup a tare sukasha sannan sukaje sukayi wanka suka kwanta saida sukayi 'yan wasanni batare da sunyi making sex ba sannan sukayi bacci kowa yana jin d'an uwansa sosai a cikin ransa.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Dr mu'az ne da yarima zaune a parlour suna hira, kallon yarima yayi yace yauwa prince ina zuwa,
d'aga masa kai kawai yarima yayi batare da yayi magana ba nan Dr mu'az yamik'e yanufi part d'insu,
Bayan minti biyu yafito rik'e da wasu files, kujerar da yarima yake zaune yaje yazauna, kallon yarima yayi suka fuskanci juna sannan yace prince dan Allah wani taimako ne nakeso kayi min.
Kallonsa yarima yayi yace ina jinka Indai baifi k'arfinaba toh insha Allahu zanyi maka.
Murmushi Dr mu'az yayi yace tabbas baifi k'arfinkaba, nan yafiddo files d'in yamik'a ma yarima yace gashi ammah kayi hak'uri da karambanin da nayi maka muna buk'atarkane a hospital d'inmu.
Yarima dubawa yayi yaga upper ce ta aiki aka basa har da babban matsayi an nad'asa head of department d'in surgeon.
Girgiza kai yarima yayi yace gaskiya kayi hak'uri ba zan iyaba kaima sanin kankane ina da hospital d'ina.
Marairaicewa Dr mu'az yayi yace nasan da haka ammah dan Allah kataimaka ka amince ko yayane kasa albarka a cikin aikin nan kar kak'i amincewa dan muna buk'atar babban surgeon kamarka.
yarima shuru yayi kamar yana nazari sannan yace shikenan zanyi tunani akai.
Cikin jin dad'i Dr mu'az yace Allah yasa inji alkhairi.
Bayan yarima yadawo part d'insu kwance yake saman 3 seater ya yi matashin kai da hannuwansa kansa yana kallon ceiling,
Fitowar zarah kenan daga bedroom rik'e da apple tana ci, tsaye tayi tana kallon yarima da kwata-kwata batama san lokacin da yashigoba dan duk atunaninta bai dawoba.
Takowa tayi ta iso inda yake janye kansa tayi tazauna sannan tamaida kan nasa saman cinyarta, yarima lumshe idanunsa yayi.
shafa sumar kansa tayi tace ashe ka dawo ban saniba.
Murmushi yarima yayi yace uhm ban dad'e da dawowaba,
duk'o da kanta tayi takaimashi peck a saman idonsa da yake lumshe, ahankali yabud'e idanunsa nan suka sakar ma juna murmushi, d'age rigarta yayi yayi kissing d'in cikinta sannan yace ina fatana kuna lafiya keda babyna.
Cike da tsokana zarah tace lafiya lou muke prince saidai missing d'inka da mukeyi.
Shafa cikinta yashiga yi yace nima nayi missing d'inku sosai yanzu muje ciki inga in dagaske kunyi missing d'ina.
Dariya zarah tayi tace nak'i wayon naka babu inda zanje.
Mik'ewa yarima yayi yad'auketa yanufi bedroom da ita tana wuntsila k'afa bai direta a ko'inaba sai saman gado, zarah shirin safka take nan yarima yarik'ota yace toh sarkin tsoro ni ba abinda zanyi miki magana ce nakeso muyi.
gyara zamanta tayi tafuskacesa tana jira taji abinda zaice mata.
Yarima janye idanunsa yayi daga kallonta yayi shuru har na kusan minti ukku sannan yakwashe yadda sukayi da Dr mu'az yafad'a mata.
Zarah kasa 6oye farin cikinta tayi nan tashiga washe baki, kallonta yarima yayi yace toh ya kike gani?
Cikin jin dad'i tace wlh nima na goyi bayan hakan kaga kaima zaka ji dad'i kuma taimakone Allah zai baka lada dan irin wannan aikin naku duk abinda za'a ba mutum baza'a ta6a biyansaba ladarku tana wajen Allah.
Murmushi yarima yayi yace hakane shikenan tunda kin amince toh nima na amince.
cikin jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai my soulmate Allah yabarmin kai ni kad'ai.
Dariya yarima yayi yace toh Allah yasa,
'Dago kai zarah tayi takallesa tace ashe ka iya dariya haka gaskiya tana yi maka kyau saidai kai bakacika yin dariyaba murmushinma kafin kayi sai ansha wuya.
Jan hancinta yarima yayi yace yau kuma tsokanata akeji?
Murmushi zarah tayi tace ba tsokana bace gaskiya ce nafad'a dan ranar da nafara ganinka lokacin da kukazo islamiyarmu ranar da muke walima saida nakusan rikicewa dan ka burgeni sosai saidai a lokacin fuskarka a d'aure take.
Murmushi yarima yayi yace kedai kin cika tsokana nidai yanzu tashi muje muyi wanka mukwanta dan ni yau agajiye nake ga bacci da nakeji.
Mik'ewa zarah tayi tace angama ranka yadad'e, nan suka cire kayansu sukaje sukayi wanka bayan sun fito shiryawa sukayi cikin kayan baccinsu sannan sukabi lafiyar gado suka kwanta.
Wanshe kare koda yarima yaje ma mu'az da batun amincewarsa sosai mu'az yai murna,
bayan kwana biyu yarima motarsa yasiya maikyau da tsada sannan yafara zuwa wajen aikin.
Sosai ma'aikatan asibitin suke girmamasa musamman ma da sukasan matsayinsa da kuma matakin karatunsa, kamar dai yadda yake baya shiga harkar kowa toh nan ma haka hidimar gabansa kawai yakeyi.
Sosai sukejin dad'in aiki da shi musamman ma da sukaga k'wararrene sosai a 6angaren theatre.
Bayan kwana biyu
Zarah kwance take saman gadonsu tunanin 'yan gidansu kawai take dan tasan dole sai sun nemi wayarta, tana cikin tunanin batasan lokacin da yarima yashigoba saidai jin mutum tayi gefenta, murmushi tasakar masa tare da cewa sannu da zuwa ashe ka dawo.
Shima murmushin yayi sannan yace ai daman bazakiji dawowataba tunda kin tsunduma kogon tunani wai ma tunanin me kikeyi haka?
Ajiyar zuciya Zarah tasafke sannan tace tunanin su mama nake nasan zasuyita neman layina bazasu samuba,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka,
Yarima kallonta yayi yace kar kidamu ai sunsan dai kina cikin k'oshin lafiya zan kira miki su wani lokacin kugaisa.
'Daga kai Zarah tayi cike da gamsuwa da maganar yarima, jikinta yarima yakwanta tare da tura hannuwansa cikin rigarta yana cakud'ata
Ganin yana shirin nemanta yasa tazame jikinta takoma parlour dan yanzu gabad'aya ji take batason yarima yana kusantarta saboda sai takwana jikinta yana ciwo ga yawan amai da tashin zuciya musamman yanzu da cikinta yafara yi mata nauyi, ammah indai wassani zaiyi da ita bata damuwa saidai tasan halin gogan nata dawuya ya iya tsayawa iya romancing.
Ganin ta gudu yasa yarima yashareta yai kwanciyarsa dan ya lura kwana biyu haka take masa Indai zai nemeta toh sai tasan hanyar da tabi takubce masa.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_[5/3, 9:51 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Aunty Aliyah Sharif bazan iya mancewa da ke ba akodayaushe kina raina dan haka kimatso kusa yau page nakine big Aunty, sai wanda kikaso zai karanta, jinjinar bangirma agareki 😍_
6⃣1⃣
Sumayya tunda takwana biyu ganin dagaske aurenta ya mutu gashi bata ganin yarima yasa tahak'ura tasaki ranta, ahaka akaje aka kwashe kayanta a part d'inta sannan aka rufe gabad'aya 6angaren yarima aka kaima memartaba key d'in.
Sumayya kwance take saman gadonta sai a ranar tajanyo wayarta takunna dan rabonta da ita tun ranar da aurenta yamutu, number d'in yarima tayi dialing da mamakinta taji bata shiga, dan haka talalubo ta zinat nan tafara ringing har ta tsinke ammah batayi picking ba, nan ma sumayya tak'ara kira saida tayi mata 3 missed call ammah bata d'aukaba dan haka tatura mata message dan daman tasan mawuyacine zinat tayi picking d'in wayar.
Bayan kamar minti biyar sai sumayya tak'ara kira da mamakinta saiga zinat tayi picking, cike da jin dad'i sumayya tagyara kwanciyarta tare da cewa Hi baby.
Daga chan 6angaren zinat a tsorace tace sumayya ya dai?
Murmushi sumayya tayi tace ke fa tsiyata da ke kin cika tsoro toh kisaki jikinki komai ya wuce.
Uhm sumayya kenan taya zan saki jikina bayan d'an banzan dukan da wannan mugun yayimin ke yanzu dai ya maganar aurenki?
Murmushi sumayya tayi tace hmm kibarsa kawai ai yanzu aurena da yarima ya k'are wlh ban ta6a tunanin zaimin wannan cin mutuncinba haka koda nasan inason yarima ammah babu yadda zanyi dole inciresa a raina tunda ko giyar wake nasha aurenmu bazai ta6a komawaba.
Zinat cikin ranta murna fal ji take kamar tazuba ruwa k'asa tasha saboda murnar auren sumayya ya mutu, a fili 6oye murnarta tayi tace Allah sarki baby ba haka nasoba toh yanzu ya su memartaba sukayi da sukaji labarin rabuwarku Allah dai yasa basuji abinda mukayi ba.
Dariya sumayya tayi tace kefa tsiyata da ke kin iya tsoro, daman fa nasan miskilancin yarima bazai ta6a barinsa yafad'aba kuma koma ba hakaba nasan yarima bazai iya tonamin asiriba saboda bayason tashin hankali, nikuma gudun kar ma yatona min yasa nayi sauri narigashi kai k'ara......nan takwashe duk abinda yawakana talabarta ma zinat.
Ajiyar zuciya zinat tayi tace gaskiya kinyi namijin k'ok'ari toh yanzu yarima shikenan ya bar gida bazai dawoba?
Hmm ba zai ta6a dawowaba, ni wlh kin ban mamaki da kika iya tafiya kikabarni ban ta6a tunanin hakaba daga gareki zinat.
Kwantar da murya zinat tayi tace kiyi hak'uri baby wlh gabad'aya rikicewa nayi ammah insha Allahu wani lokacin zan shigo.
Cikin jin dad'i sumayya tace gaskiya da naji dad'i dan gabad'aya kad'aici ya isheni Allah yakawo min ke lafiya.
Ameen baby zankiraki anjima.
Ohk, sai kin kira,,nan sukayi sallama.
Tun daga ranar sumayya da zinat suka koma suka d'inke kullum suna manne da juna ta waya inba wayaba toh ta chart da video call, yanzu sumayya kusan kullum tana d'akinta suna waya da zinat.
Sultana sadiya ganin yanzu hankalin d'iyarta ya kwanta yasa itama tad'an kwantar da hankalinta ammah magana bata had'asu da ummin yarima dan da taga ummi zata fara d'aure fuska koda ummi tayi mata magana indai sukad'aine shareta takeyi inkuma gaban su dadane toh shine take amsa mata ciki-ciki.
Ummi tun abin yana bata mamaki ganin ba ita tayimataba ammah da ita take gaba, daga k'arshe abun yadaina damunta.
Dada da memartaba ma danne damuwarsu kawai suke akan tafiyar yarima ammah su ma suna jin abun yana damunsu cikin rai, daga inda suka tuna da abinda yayi ma 'yar jikarsu sai kuma suji ba dad'i, dan haka ne suke nuna ma sumayya kulawa sosai ga tausayinta da sukeji saboda akanta akafara sakin aure a masarautarsu.
_________________
Zarah ganin yarima kwana biyu bai nemetaba dan yanzu har romance ya dainayi mata saidai kawai yarungumeta suyi bacci, nan abun yad'an fara damunta.
Yau ma tana fitowa daga wanka ganinsa tayi a kwance yana duba wata newspaper dan haka taje tafad'a jikinsa, kallonta yarima yayi yace Zarah sai kin ji ma babyna ciwo?
Turo baki tayi cikin shagwa6a tace au ba ma ni zanji ciwon ba babynka zanji mawa ko? babyn da yanzu andaina kulamu.
Aje newspaper d'in da take hannunsa yayi yace wajen me nadaina kulaki?
Kwantar da kanta tayi a k'irjinsa tace toh ba kai bane kadaina min komai?
Yarima ya fahimci inda tadosa ammah yanuna bai fahimtaba yace magana nadaina yi miki ko kulawa?
Girgiza kai Zarah tayi cikin jin kunya tace ka daina making sex da ni.
Murmushi yarima yayi yace toh ai naga kamar bakiso saisa nabarki kihuta.
Zaro ido Zarah tayi tace karufa min asiri taya zan k'i son lada, kawai dai babynka ne yake wahalar da ni, dan dadyn nasa jarumi ne,,,tak'arashe maganar tare da kashe masa ido d'aya.
Murmushi yarima yayi yace kar kidamu nima banason babyna yana wahalar min da ke kihuta warki kawai nayi miki uzuri.
Da mamakinsa sai yaga Zarah ta fashe masa da kuka.
Cike da mamaki yace lafiya zarah? Me kikeyi ma kuka?
Cikin kuka tace toh bakai bane.
Murmushi yayi yace toh kinaso inyi?
Cikin sauri tad'aga kai.
Toh shikenan kidaina kuka, nan yakwantar da ita yashiga lashe mata hawayen fuskarta daga nan yalalubo bakinta yacigaba da tsotsa kamar wanda yasamu lolli pop, gabad'ayansu jikinsu rawa yake dan sunyi missing d'in juna sosai, daga nan yarima yazare towel d'in da yake jikinta yagangaro da kansa a k'irjinta, ahankali yacigaba da lalla6ata har saida yaga sun samu nutsuwa sannan yabarta.
Duk da lalla6ata da yayi ammah saida jikin zarah yai ciwo dan daurewa kawai take, ko shi kansa yana lura da yadda take cize le6e.
Cike da tausayinta yashiga yi mata sannu daga k'arshe yad'auketa sukaje yaimata wanka shima yayi nasa sannan suka fito hatta kaya shi yasaka mata, jin jikinta ya d'au zafi yasa yad'auko drugs yabata sannan yad'auketa suka dawo parlour nan yakwantar da ita saman cinyarsa yana wasa da gashin kanta ahaka bacci yai awon gaba da ita.
Ganin tayi bacci yasa yarima yajingine kansa a jikin kujerar da yake zaune cike da tausayin zarah, nan family d'insa suka fad'o masa a rai, tunani barkatai yashiga yi daga k'arshe janye zarah yayi yagyara mata kwanciyarta nan yasafko k'asa yadafe kansa da hannuwa biyu, tunowa yayi da yadda yarabu da danginsa kowa yana d'aura masa laifin da bashida laifi a cikinsa, kukan da ummi takeyi ne ahankali yashiga dawo masa a kunne da lokacin da tad'ago idanuwanta da sukayi ja tasafkesu akansa,
Girgiza kai yashiga yi yace taya zan samu kwanciyar hankali ummina kin zubar da hawayenki saboda ni, ya zanyi da rayuwata.
Zarah da tafarka tun lokacin da yajanye mata kai, ido tazuba mashi tana sauraren duk abinda yake cewa tausayinsa ne yakamata dan sau tari daman yarima yana k'ok'arin ganin ya 6oye damuwarsane saboda ita saidai inaaa tuni ta gama karantar hakan, safkowa tayi daga saman kujerar tadawo k'asa kusa dashi tazauna tare da dafasa,
'Dago kai yarima yayi yakalleta murmushi yasakar mata tare da 6oye damuwarsa sannan yace kin farka?
Zarah k'wallah ce tacika mata ido tace taya kake tunani ni zan samu kwanciyar hankali alhali kai bakada shi?
Ido yazuba mata cike da mamaki sannan yace wa yace miki bana cikin kwanciyar hankali?
Hawayen da take dannewane suka zubo tace suhail me kamayar da ni, ko duk farkawar da kake cikin dare katashi kayita tunani ka d'auka ban san komai ba?
Mamaki k'arara yabayyana a fuskar yarima yace Zarah wa yafad'a miki haka?
Fad'awa tayi jikinsa tana kuka tace yarima babu abinda ban saniba sau tari kana k'ok'arin 6oye damuwarka idan kana a gabana saidai in bamu tare shine kake zama kayita tunane tunanenka, meyasa kake haka, kai doctor ne kasan illar yin haka tunda kuna fad'a ma wasu sudaina yawan damuwa ammah sai gashi kai kanayi.
Yarima rintse idanunsa yayi da k'arfi yana jin wani iri a ransa dan tunda yabaro iyayensa bai ta6a samun kwanciyar hankali ko na second d'ayaba saidai yana k'ok"arin 6oyewane saboda Zarah ga kuma ciki da take d'auke da shi bayaso ta silarsa wani abu yasamesu,
janyeta yayi daga jikinsa tare da bud'e idanunsa da suka kad'a sukayi ja, cikin sanyin jiki yace Zarah kukan ya isa haka, kidaina sa damuwa a ranki idan kin ganni haka, kinga bake kad'ai bace kar wani abu yasameku ke da babynmu.
Girgiza kai Zarah tayi tace taya hankalinmu zai kwanta bayan wanda muke a k'ark'ashinsa yana cikin damuwa? Taya zan yafe ma kaina bayan ta dalilina karabu da kowa naka?
K'ara fashewa tayi da sabon kuka sannan tace banso karabu da sumayya ba dan 'yar uwarka ce ko bakomai itace matarka ka tafarko, indai har saboda ni kasaki sumayya toh wlh na yafe mata abinda tayi min duniya da lahira, please ka amince mukoma gida kamaida matarka kazauna cikin danginka, ko da ace hakan zaiyi silar mutuwar nawa auren.
Wani irin abu yarima yaji ya soki mak'ogwaronsa jin ta ambaci rabuwa da shi, tureta yayi daga jikinsa cikin 6acin rai yace Zarah na sha fad'a miki ko babu ke zan iya rayuwata, ammah kar kik'ara min zancen sumayya dan na riga nayi mata saki ukku kuma kidaina tunanin ta dalilinki nasaketa wlh ko d'aya, na saketane saboda wani dalili nawa kuma idan kin gaji da zama da ni zaki iya fad'amin,,,yana fad'in haka yamik'e yad'auki key d'in motarsa yaficce yabarta nan zaune dan gabad'aya ya kashe mata baki ta ma rasa abinda zatace masa.
Cigaba tayi da kukanta kamar wadda aka aiko ma da sak'on mutuwa, ita takaicinta rabuwar yarima da danginsa gashi kwata-kwata ya kasa fahimtar inda tadosa, dan ita tasan tanason yarima sosai, k'ara sautin kukanta tayi cike da tausayin kanta da mijinta saida tayi mai isarta sannan takwanta nan k'asa.
Har akayi sallar isha'i yarima bai dawoba dan haka Zarah tana nan zaune inda take, sallah kawai take tayar da ita, koda yadawo taddata yayi inda yabarta tahad'e kanta da gwiwa cikin ransa duk sai yaji ba dad'i haka yawuce yashige bedroom nan yai wanka yashirya har ya hau gado ya kwanta sai kuma yaji bai iya barinta a wannan halin dan haka yamik'e yafito parlour.
Zarah da tana jin shigowarsa ammah tashare jin bai kulataba ya wuce bedroom yasa siraran hawayen bak'in ciki suka zubo daga idonta, tunani tashiga yi anya yarima da yace yanasonta da gaske yake? Anya ba kawai ya fad'a bane dan yakwantar mata da hankali?, tana cikin haka sai jinsa tayi ya dafata, ahankali tad'ago kanta takallesa,
Cike da damuwa yarima yace Zarah meyasa kikeson d'aga min hankali? Menene abin kuka, ke kuka baimiki wahala na lura, yanzu dai taso muje kiyi wanka ga ice cream chan nasiyo miki kisha kinji?
Zarah shuru tayi nan yarima yataimaka mata tamik'e suka shiga bedroom saida yad'auko mata towel sannan yaje yahad'a mata ruwan wanka, lokacin da yafito har tacire kayanta ta ma d'auka zai taimaka mata tayi wankan ammah sai taga ya je yai zamansa dan haka tawuce taje tayi tana mamakin yarima yadda kwata-kwata shi bai iya lallashin maceba saidai shi a lallashesa.
Bayan ta fito wankan lotion kawai tashafa sai humra sannan tawuce taje tabud'e wardrobe tad'auko sleeping dress d'inta tasaka, zuwa tayi tahau gadon takwanta, yarima kallonta yayi yace bazakisha ice cream d'inba yau?
Kamar tace masa eh ammah ganin tanason sha yasa tamik'e batare da tayi magana ba taje tad'auko tazauna tasha, saida tashanye roba d'aya sannan tamik'e taje tasaka sauran cikin freezer taje tawanko bakinta tadawo takwanta, lokacin yarima har ya kwanta, daga gefensa itama takwanta dan yau haka sukayi kwanciyarsu batare da sunji d'umin junaba, tana jin yarima yana ta juyi batasan ya yak'areba har bacci yai awon gaba da ita.
Da asuba bayan sunyi sallah baccinta takoma inda tabar yarima zaune yana dannar system d'insa.
Wajen k'arfe goma da tafarka da mamakinta baya nan, kallon agogo tayi taga har k'arfe goma ta yi, mik'ewa tayi tafito parlour nan ma bainan dan haka tasan ya je wajen aiki, gyara d'akin tayi sannan tashiga tayi wanka tashirya.
Bayan ta gama fitowa tayi main parlour nan tatarar da jamila zaune tana kallo,
Cikin sakin fuska zarah tagaisheta.
Murmushi jamila tayi tace maman baby kin farka, ya gidan.
Lpy lou Aunty jamila, halan har sun ficce.
Dariya jamila tayi tace lokacin kina bacci suka fita dan prince cewa yayi akwai theater d'in da zai shiga k'arfe tara saisa tun 8:30am suka fita.
Numfashi zarah taja tace gaskiya Aunty jamila kina k'ok'ari tun da safe kike tashi kina had'a breakfast.
Toh zarah ya muka iya, indai kace bazaka girka da wuriba ai sai miji yafita batare da yayi breakfast ba daganan kuma sai afara cin abincin masu siyarwa nikuma natsani inga mijina yana cin abincin waje ke ni ko na 'yar aiki banaso inga yana ci.
Jinjina kai zarah tayi tace wlh nima Aunty jamila banaso inga mijina yana cin girkin 'yar aiki ammah ba yarda na iya.
Murmushi jamila tayi tace toh ya kuka iya ai gidan sarauta ya gaji haka, kedai shawarar da zan baki kikula da mijinki sosai dan kinsan 'yan matan yanzu bare ma irinsu yarima na tabbata bakowace mace bace zata gansa batare da taji ya burgetaba, dan rannan mijina ya fad'amin a hospital har 'yan mata sun fara shige masa dan ma baibasu fuska saisa suke yin baya da shi.
Ajiyar zuciya zarah tasafke tace toh ya zanyi Aunty jamila jin dad'inama da baya kulasu ammah ni kaina indai zai fita hankali baya kwanciya sai yadawo kuma dai gashi badaman ayi masa kulle.
Dariya jamila tayi tace kinjiki da wata magana wai kulle, kedai kicigaba da addu'a Allah yakare miki mijinki.
Ameen y rabb,,nan zarah taje tahad'o breakfast tadawo tazauna tana yi suna hira.
Bayan sun gama a tare suka shiga kitchen suka had'a lunch sannan zarah tawuce part d'insu tayi wanka tashirya.
Wajen k'arfe ukku gabad'ayansu parlour suka dawo suka zauna suna kallo suna hira jefi-jefi har akayi sallar la'asar ammah su yarima basu dawoba, jamila kallon zarah tayi tace mutanen shuru basu dawoba.
Uhm wlh kau Aunty jamila nima tunanin da nake kenan Allah dai yasa lafiya.
Ameen y rabb,,,cewar jamila, suna cikin haka sai ga su yarima sun shigo da sallamarsu.
Juyowa sukayi suka kallesu tare da amsa musu sallamar sannan sukace sannunku da zuwa.
Amsawa sukayi,
jamila ce tace tun d'azun muna ta jiranku ammah shuru.
Dr mu'az kallon yarima yayi sukayi murmushi sannan yace munje neman auren prince ne dan cewa yayi yanaso ya auri 'yar garin nan,,,yak'arashe maganar tare da kallon zarah da tacika tayi fam.
Jamila ma kallonta tayi tace laahhh my har da kai ake had'a baki dan ak'aro ma gimbiya abokiyar zama? Gaskiya ni ban goyi bayankuba.
Zarah saboda bak'in ciki kamar tad'aura hannu saman ka tafasa ihu,
Yarima murmushi yayi yace toh ya aka iya tunda ina so, yanzu dai bari inshiga ciki ind'an watsa ruwa, batare da ya kalli zarah ba yawuce yashige yana dariya ciki-ciki.
Murmushi mu'az yayi yace sorry gimbiya kar kiga laifina prince ne yaimin dole saisa nabisa mukaje,
Jamila k'unshe dariyarta tayi tace ku dai kukasani nidai ina bayan gimbiya.
Zarah shuru tayi kamar ruwa ya cita ta ma rasa abinda zatace,
Nan dr mu'az yashige yana dariya ciki-ciki.
kallonta jamila tayi tace ranki yadad'e kitashi prince fa na chan yana jiranki.
cike da k'ulewa tace Aunty jamila toh me zanyi masa.
Rik'e baki jamila tayi tace haba Zarah banyi tunanin jin haka daga garekiba ai na d'auka ko da ma kishiyarce bazata firgitakiba tunda kinsan kinriga kin zarce mata, kinga tashi kije kitaimaka ma mijinki nima kinga tafiyata.
Zarah ba dan tasoba tamik'e tanufi part d'insu lokacin da tashiga bedroom tsaye taga yarima gaban dressing mirror yana shafa da alama daga wanka yafito.
Tsaye Zarah tayi tana kallonsa, shareta yayi yai kamar baimasan tana wajenba, bayan ya gama ta gefenta yazo zai gifta yawuce sai a lokacin ya kalleta ta cika tayi fam, danne dariyarsa yayi Sannan yace kekuma fa?
Ai zarah kamar daman jira take yayi magana nan tafashe da kuka,,,,da mamaki yake kallonta yace Allah yabaki hak'uri daga tambaya sai kuka? Toh indai tambayarce toh nadaina nan yawuce yai tafiyarsa yabud'e wardrobe.
Dagudu zarah taje tarungumesa tabaya tacigaba da kukanta.
shuru yarima yayi yana jin kukan nata yana ta6a har cikin ransa,
ganin baida niyar yin magana yasa zarah cikin kuka tace menakeyi maka da kakeso kayi aure? Dan Allah indai wani abu nakeyi maka kafad'amin wlh zan daina,
juyowa yarima yayi yakalleta yaga haik'an take ta kukanta, murmushi yayi yace zarah ni na ce kinmin wani abu?
Girgiza kai tayi tana mai cigaba da kukanta.
tallabo fuskarta yayi yace kuma ni kikaji nace aure zanyi?
Nan ma Girgiza kai tayi.
murmushi yayi sannan yace tsokanarki fa daman mu'az yake dan yaga yadda zakiyi sai kuma gashi ya gani.
Zarah fad'awa tayi jikinsa tana cigaba da kukanta, dariya yarima yayi yace lallai ashe matar tawa tana tsoron kishiya ai na d'auka da jaruma nake zaune.
Duka zarah takaimasa a k'irji cikin kuka tace kai ko? Wlh ban yarda sai na rama,
dariya yarima yayi yace toh nidai bani nayi maganar ba.
'Dago kai zarah tayi takallesa tare da tsagaitawa da kukan da take tace ina sonka sosai akanka ba abinda bazan iyaba idan mace tara6eka ji nake wani iri sumayya ma dan ba yadda na iya nasan idan nace zanyi kishinta toh banyi ma kaina adalciba.
Murmushi yarima yayi yace aiko sai kinyi hak'uri dan yarima mijin mace hud'une.
Turo baki zarah tayi tace insha Allahu a haka zaka tsaya ba k'ari.
Dariya yayi yace lallai yarinya sai kinji ana gud'a ankawo min amaryata sabuwa gal.
Harararsa tayi cike da k'ulewa tace ai nima d'in gal aka kawo maka ni,
K'unshe dariyarsa yayi sannan yace toh ni mekikaji na ce?
Marairaicewa zarah tayi tace dan Allah kayi hak'uri akan abinda nayi maka jiya insha Allahu ba zan k'araba, wlh bana jin dad'i inga kana fushi da ni duk sai inji wani iri.
Goge mata hawayen fuskarta yayi yace kar kidamu ni ban rik'ekiba daman ai ke bakya laifi.
Murmushi zarah tayi tace ka dai fad'a dai kawai nidai yanzu kashirya muje kayi lunch dan nasan ka kwaso yunwa.
Toh ranki yadad'e yadda kikeso haka za'ayi.
dariya zarah tayi tace au abun harda tsokana?
uhm ni na isa intsokaneki,
nan zarah tataimaka mashi yashirya sannan suka fito inda suka tadda su mu'az suna zaune suna jiransu.
Ganinsu yasa mu'az yakyalkyale da dariya yace prince har ka gama lallashin?
Harararsa yarima yayi yace tunda ka had'aba.
Zarah duk'ar da kanta tayi cikin jin kunya.
jamila tace ammah dai nasan saida akasha da-ga kafin kashawo kanta.
Murmushi yarima yayi yace baby toh gaki gasu kisan zaman da kike dasu dan so suke suga ank'ara miki kishiya.
Turo baki Zarah tayi tace kabarni da su ai insha Allahu dagani ba k'ari ni kad'ai na isheka ko?
Dariya sukasa mata dan yanayin yadda tayi maganar ya basu dariya, yarima murmushi yayi yace kekad'ai fa kin isheni baby.
nan suka wuce dining suna dariya, zarah ganin tsokananta suke yasa tasharesu nan sukayi lunch, bayan sun gama nan taja yarima suka koma part d'insu sukaita shan love d'insu
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:52 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
*PAGE* 6⃣2⃣
*BAYAN WATA DAYA*
Zarah cikinta ya girma sosai dan a lokacin watansa takwas da ta zauna k'afafuwanta har kumbura suke, lalla6ata kawai yarima yake dan indai yana gida baya bari tana komai saidai shi yayi mata.
Yau ma kwance take saman cinyarsa suna kallon wani series film, d'ago kai tayi takallesa tace my dan Allah kataimaka kakira min su mama mugaisa kaga har yanzu bamuyi waya da su ba.
Kallonta yarima yayi batare da yayi magana ba, ganin haka yasa zarah tace ammah Indai kaga da matsala toh kabarsa kawai.
janyo wayarsa yayi yace ai dolema inkirasu dan nasan hali yanzu kin fara min kuka.
Murmushi zarah tayi tace karufa min asiri kai ai d'an alalla6ane ranka yadad'e inba hakaba yanzu mutum ya amsa query.
Hmm haka dai kikace, yanzu dai bari inkirata mugaisa, nan yarima yakira mama cikin girmamawa yagaisheta, bayan sun gaisa nan yamik'a ma zarah.
Cike da jin dad'i zarah tace hello mamana,
Daga chan 6angaren mama tace zarahta.
Murmushi zarah tayi tace ina wuni mama?
Lfy lou zarah, ya gidan,,cewar mama.
Lafiya lou mama nayi missing d'inku kwana biyu.
Daga chan 6angaren mama tace aikam dai zarah kun 6oye, ai muna neman wayanki bata shiga.
Zarah d'ago kai tayi takalli yarima da hankalinsa yana wajen T.V sannan tace eh wayarce tasamu matsala saisa, ina fata duk kuna lafiya ina abbanmu da su yaya rauda?
Mama tace babanku baya nan saidai su rauda, ai muna ta kiranki mufad'a miki munkoma sabon gida.
Wata irin k'ara zarah tayi cike da murna tace Alhmdllh gaskiya naji dad'i Allah yasa alkhairi, Allah yatsare sai munzo ganin gida.
Dariya mama tayi tace Ameen y rabb, toh Allah yakawoku lafiya.
Ameen mama, aba su yaya rauda mugaisa.
Nan mama tabasu sukasha hira har suna cewa zasuzo dan sun fitar da anko d'in bikkin Aysha, nan zarah tace a'a kar suzo dan sun d'anyi tafiya ammah idan sun dawo zata nemesu, sun dad'e suna hira sannan sukayi bankwana suka kashe wayar cikin jin dad'i.
Mik'ama yarima wayarsa tayi tace ka gama min komai nagode sosai my soulmate,
Murmushi yarima yayi yace toh yanzu hankali ya kwanta ko?
Girgiza kai zarah tayi tace har yanzu da saura, hankalina bai ida kwanciyaba.
Kallonta yarima yayi yace toh menene yayi saura?
Marairaicewa tayi tace dan Allah kakira ummi mugaisa da ita ko tasamu sauk'i a ranta dan nasan duk inda ummi take yanzu bata cikin kwanciyar hankali.
Nan da nan fara'ar da take fuskar yarima tagushe gabad'aya damuwa tabayyana, shuru yayi baice ma zarah komai ba.
Ganin haka yasa zarah tace dan Allah kataimaka koda minti biyune mugaisa da ummi.
Da mamakinta sai gani tayi ya janye mata kai daga saman jikinsa nan yamik'e yashige bedroom.
Da kallo zarah tabisa cike da tausayinsa, nan tamik'e tabi bayansa, saman gado ta tarar da shi kwance yayi pillow da hannuwansa, takawa zarah tayi taje tahau gadon takwanta daga gefensa tare da rungumesa cikin kwantar da murya tace kayi hak'uri mijina idan na 6ata maka rai, nima ba ason raina hakan yakasanceba kawai dai gani nayi yakamata ace koda sau d'ayane ka kira ummi dan nasan a yanzu duk inda ummi takasance toh hankalinta a tashe yake, ammah da taji kana cikin k'oshin lafiya na tabbata hankalinta zai kwanta,
Yarima maida idanunsa yayi yalumshe yana jin wani iri a ransa.
Zarah cigaba tayi da cewa kafini sanin yadda ummi takeji a game da kai, kana tunani ko da sau d'aya hankalinta zai kwanta alhali batajin ko muryarka?
shuru yarima yai yakyaleta kamar yaba banza ajiyarta.
Ganin haka yasa zarah tafashe da kuka tace shikenan kayi yadda kakeso tunda haka kaza6a idan namutu ba shikenan ba.
Yarima jin maganartata yayi har cikin ransa, rungumeta yayi tare da bud'e idanunsa yace zarah kidaina cewa haka insha Allahu bazaki mutu kibarni ba, indai ummi ce bari inkirata yanzu.
Zarah cikin jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai mijina Allah yasaka da alkhairi.
Murmushin k'arfin hali yarima yayi yace Ameen dear, wayarsa yajanyo yalalubo number d'in ummi.
Ummi tun bayan tafiyar yarima bata samun kwanciyar hankali dan ko abincin kirki bataci, sultan Ahmad shi yake tsareta yake samu tana ci, kullum aikin d'ayane daga lallashi sai wa'azi ahaka tad'an safko tafara sakewa.
Yauma zaune take saman darduma tana lazimi, wayartace datake kusa da ita tafara ringing, ido tazuba ma wayar ganin sabuwar number ce kamar ba zata d'aukaba har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama.
Yarima jin muryar umminsa yasa yalumshe ido yana jin wani irin nishad'i a ransa, nan Ummi taita magana ammah shuru.
Zarah ce tata6osa ahankali tace kayi magana.
sai a lokacin yabud'e idanunsa sannan yace hello Ummina.
Jin muryar yarima yasa sultana bilkisu tarikice tarasa mezatayi murna ko kuka, ai sai ji yayi ta fashe da kuka tace my son kaine? Shine katafi kabarni baka ko nemana? Ni miye nawa laifin da kagujeni, baka tunanin halin da zan shiga?
Yarima runtse idanunsa yayi yanajin wani irin d'aci a ransa, cike da tashin hankali yace ummina kiyafemin wlh ba ason raina hakan yakasanceba, kema kinsani ba zan iya zaman second d'ayaba batare da kina a rainaba.
Cikin kuka Ummi tace nasan haka my son dan Allah kadawo gareni ko nasamu sauk'in abinda nakeji a raina, kataimaka kazo inganka ko hankalina ya kwanta.
Yarima hawayene yaji suna zuba daga idanunsa, ahankali cikin muryar lallashi yace Ummi kikwantar da hankalinki muna cikin k'oshin lafiya, indai har kina kuka toh nima zaki sani inyi.
Jin haka yasa ummi tayi saurin tsaida kukanta tace nadaina my son, yaushe zakazo?
Karkidamu ummina very soon zanzo gareki kicigaba da yi min addu'an da kikasaba.
Murmushin jin dad'i sultana bilkisu tayi tace Allah yaimaka albarka kaida zuri'arka my son, a yanzu hankalina ya kwanta da naji kuna cikin k'oshin lafiya, kuma insha Allahu akowane lokaci zakucigaba da kasancewa cikin addu'ana, yanzu kuna ina?
Shuru yarima yayi nad'an lokaci sannan yace ummi muna nan cikin k'oshin lafiya.
Ajiyar zuciya tayi tace masha Allah gaskiya naji dad'i toh ina d'iyar tawa?
Yarima waigawa yayi yakalli Zarah da tahad'e kai da gwiwa tana kuka k'asa k'asa, dafata yayi nan tad'ago kai yamik'a mata wayar kallonsa tayi, nan yai mata nuni alamun takar6a.
Bayan ta amsa muryarta tana rawa tayi ma ummi sallama, amsa mata ummi tayi nan Zarah ta gaisheta cike da girmamawa.
Ummi bayan sun gaisa, cikin sanyin jiki tace Zarah kiyi hak'uri da abinda yafaru mune muka ja miki.
Girgiza kai Zarah tashiga yi cikin sheshek'ar kuka tace ummi kidaina cewa haka *K'ADDARA CE* kawai taja hakan kuma har ga Allah ban ta6a tunanin kun cutar da ni ba koda sau d'aya, saidai abu d'aya nake tunanin kunyi min shine kun sama ma rayuwata farin ciki, baku k'yamaceniba a matsayina na talakka kun had'ani aure da d'anku, taya zan yi wani tunani nadaban akanku? Wlh ummi ku masoyanane nagaskiya ku iyayene agareni dan dani da 'ya'yanku duk d'aya kukad'aukeni,
K'ara fashewa da kuka Zarah tayi tace ummi wlh kun gama min komai a rayuwata tsakanina da ku saidai addu'a dan banda abinda zan biyaku.
Ummi Murmushin jin dad'i tayi tare da goge hawayen fuskarta sannan tace Allah yaimuku albarka Zarah, Allah yasafkeki lafiya mucigaba da addu'a insha Allahu memartaba zai safko daga fushin da yake kudawo gida.
Murmushi zarah tayi tace Allah yasa ummi,
Yarima zare wayar yayi daga kunnenta tare da switching off d'inta gabad'aya.
Zarah da mamaki take kallonsa da ya aje wayar tare da komawa yakwanta yamaida idanunsa yalumshe, saman k'irjinsa takwanta ahankali cikin muryar lallashi tace kayi hak'uri insha Allahu komai zaizo k'arshe.
'Dan guntun murmushi yarima yayi sannan yace niko zama na nan ya fi min dad'i koda sau d'aya bana tunanin komawa gidanmu, nidai burina iyayena susami kwanciyar hankali.
Da ido take binsa har yakai aya sannan tace kadaina cewa haka yarima koma me akayi maka yakamata ace ka hak'ura domin 'yan uwa dabansuke ba a iya canzasu, cikin dangine zakashiga kai rayuwarka kaji dad'i.
Murmushi yarima yayi yace naji yanzu dai aji da ni sarkin surutu.
Zaro ido zarah tayi tace anya zan iya? Kaga fa yanzu nayi nauyi.
Kar kidamu baby zaki iya nima ai ahankali zan miki dan banason wannan rakin naki.
shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace au nice ma sarkin raki?
Dariya yayi sannan yace toh ai haka kike,
Uhm naji ai kaine baka tausayina.
Yarima yace au haka kikace? Toh shikenan bari kigani.
Zaro ido zarah tayi tace dan Allah kayi hak'uri da wasa fa nake.
Shareta yarima yayi nan yakwantar da ita, ganin tayi rau-rau da ido yasa yai murmushi tare da komawa gefenta yakwanta, kansa yana kallon ceiling.
Kallonsa zarah tayi ganin baida niyar yi mata komai yasa tace toh ka fasa?
Juyowa yayi yakalleta yana murmushi yace sarkin tsoro ni ba abinda zan miki daman.
Dukan wasa zarah takaimasa tace kai ko?
Dariya yayi yace ya na iya tunda Allah ya had'ani da matsoraciyar mata.
Uhm kaima kasan ni jaruma ce.
Nidai bansan komai ba ammah bari inyi just na 5 hours tanan zan d'an gane jarumtarki.
Zaro ido zarah tayi tace karufamin asiri ai sai inmutu.
Kumatunta yaja yace ba zaki mutuba dear, maida kanta tayi saman k'irjinsa tace Allah yasa ina da rabon rayuwar,
Yanzu in namutu shikenan aurenka zaka sake kamance da ni,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka.
Rungumeta yayi yana ji kamar ta soka masa mashi a mak'oshi da ta ambaci mutuwar, ahankali yace zarah kidaina cewa haka dan ni bana tunanin zan iya son wata bayan ki, ban ta6a son wataba sai ke.
'Dago kai tayi takallesa tace har sumayya?
Yarima ji yayi wani irin takaici da tsanar sumayya sun dabaibayesa musamman ma da yatuna halin da yasameta ita da k'awarta,,,cike da takaici yagirgiza kai yace sumayya auren had'ine akayi mana,
Zuba mai ido zarah tayi tace toh kai bakada za6in kanka mu dukanmu baka akayi?
Cike da k'osawa da tambayoyinta yajanyeta daga jikinsa yamik'e yace baby kin cika tambaya har kinsa kaina ya fara ciwo yanzu dai bari inje ind'anyi wani research a system,,yana fad'in haka yaje yad'auki system d'insa yakoma parlour.
Zarah da kallo tabisa cike da so da k'auna har yaficce, sannan tayi murmushi tare da janyo pillow tarungume a k'irjinta.
______________
Ummi bayan yarima ya kashe wayar ajiyar zuciya tayi dan har cikin ranta taji dad'i da taji d'anta yana cikin k'oshin lafiya kuma ta ji hankalinta ya kwanta, a ranar saida kowa yasan tana cikin farin ciki dan rabon da aganta a yanayin tun ran da yarima yabar gidan.
A 6angaren sumayya ko hidimarta kawai take koda tanajin ba dad'i akan mutuwar aurenta ammah zinat tuni ta fara mantar da ita damuwarta dan basuyin ko 2 hours batare da sunyi wayaba nan wata shak'uwa tak'ara shiga tsakaninsu, da ace za"a duba wayarta a lokacin blue films da pic's ne kawai cikinta da ta zauna part d'inta batada aiki sai kallo sai waya, wulak'anci ko k'aruwa yayi dan ma'aikatansu har ji suke daman bata dawoba dan gabad'aya indai zata fito toh sai ta hanasu kwanciyar hankali.
Sultana sadiya ganin hankalin sumayya ya kwanta yasa itama taji dad'i a ranta, hatta shi kansa sultan abbas koda ya nuna fushi yake da ita saida taje tasamu tabasa hak'uri sannan tasamu sauk'in mahaifin nata.
Yau ma kamar kullum kwance take tayi d'aid'ai a saman gadonta tana waya da zinat, inkaganta sai karantse da namiji take waya dan shagwa6a kawai take zuba mata akan tazo taimata ko sati guda ne.
Zinat tace anya baby kina ganin ba matsala ni fa ina tsoron abinda yafaru da farko yak'ara faruwa dan kinga wanchan mijin naki har tabbai yabarmin a jiki.
Ta6e baki sumayya tayi tace ke kema tunawa da shi ai wlh tunda yasakeni toh sai nayi silar rabasa da wannan tsinannar matar tasa.
Dariya zinat tayi tace baby har yanzu dai kina akan bakanki, yanzu dai kisaurareni end of this week zaki ganni.
Wani irin k'ara sumayya tayi tace dagaske kike ko wasa?
Dariya zinat tacigaba da yi, sai chan tad'an tsagaita dariyar tace kai baby zaki ciremin kunne, zan shigo man ammah anya ba a hotel zan safkaba, saboda ni a yanzu gidanku yafi k'arfina.
Cike da Jin dad'i sumayya tace bawani fin k'arfi, dan Allah kizo kawai wlh babu matsala kinsan ba za'a barni indinga fitaba a yanzu.
Ajiyar zuciya tasafke tace toh shikenan baby sai na shigon.
Jibi kenan ko? Cewar sumayya.
Kai kedai kin cika hanzari zan dai gani idan jibin.
Chab wlh baki isaba tunda dai kika furta toh dole kizo ranar dan ba kad'an nayi missing d'inkiba.
Toh shikenan dear yadda kikeso haka za'ayi.
Nan sukacigaba da hirarsu sunfi 1 hour sannan daga baya sukayi sallama kowa yakashe wayarsa,
Memartaba tun bayan tafiyar yarima shi kansa ji yake duk ba dad'i, indai yana zaune fada kad'an kad'an ya kalli kujerar da yarima yake zama saidai yaga sultan Ahmad ne madadinsa, daurewa kawai yake yana danne zuciyansa dan shi kansa yasan yana kewar yarima ammah daga sa'ilin da yatuno abinda yarima ya aikata masa sai yaji wani irin haushinsa ya cikashi.
Dada ita kanta tana jin ba dad'i akan tafiyar yarima dan abu biyu yahad'e mata ga mutuwar auren sumayya ga tafiyar jikanta,
Tausayin sumayya yasa kusan kodayaushe sai ta aika ankira mata ita taji abinda takeso, nan sumayya take ida komawa kalar tausayi tafad'i abinda takeso ko menene nan da nan Dada take sanyawa ayi mata, ciki kuwa harda canza mata mota tasa akayi mata, tana jin tausayinta sosai saboda akanta aka fara jawarci a masarautar tasu.
Shaheed ma ba k'aramin girgiza yayiba da yaji labarin tafiyar yarima, duk inda yake tunani yarima ya sani toh ya je babushi babu alamunsa.
_*Bayan Kwana Biyu*_
Sumayya ce zaune a parlour suna hira da ummanta cike da jin dad'i sunyi nisa da hirarsu sultana sadiya takalli d'iyartata cike da k'auna tace sumayya idan kika gama iddah kinga sai kisamu wanda kike gani yana da dama-dama ki aura.
6ata fuska sumayya tayi tace haba ummah wane irin aure yanzu ai ni nayi sallama da aure.
Zaro ido sultana sadiya tayi tace kirufa min asiri kinsan dai su memartaba da abbanki bazasu ta6a amincewaba, indai manemanki sukazo kawai kisamu kishige kicire wanchan matsiyacin a ranki.
Yamutsa fuska sumayya tayi tace ummah har kina tunanin zan iya zama da wani bayan yarima? Ni koda ma an matsamin sai nayi aure toh wlh saidai inyi auren kisan wuta inyaso daga baya infito inkoma wajen mijina dan ni Indai ba yarima ba babu wanda zan iya aure.
Jinjina kai sultana sadiya tayi cike da mamakin furucin d'iyartata tace sumayya anya yarima bai asirce min ke ba? Taya ana ga gabas kekuma kina ga yamma, ubanme suhail yakeda shi da zaki nace masa?
Dariya sumayya tayi tace kai ummah ni wlh kina ban dariya,,,,yauwa na ma mance infad'a miki gobe k'awata zinat zatazo.
Washe baki sultana sadiya tayi tace ayya na gane, wai ya business d'in naku yana dai tafiya daidai ko?
Yatsina fuska sumayya tayi tace eh toh dan tana turo min kud'i sosai, gobe ma zatazo min da wata sark'an gold da nasa tasiyo min cikin kud'in.
Cikin jin dad'i sultana sadiya tace angaisheki d'iyar albarka, kina jan kud'i, kai gaskiya naji dad'i Allah yakaimu goben, Allah yakawota lafiya.
Ameen ummana, nan sumayya tacigaba da bata labari akan business d'insu.
Wanshe kare sumayya shirye-shirye tayi sosai na tarbar zinat, girki ko anyi yakai kala goma, ummah dai binta take da kallo dan ko ba'a fad'a mataba tasan zinat tana da muhimmanci sosai a wajen sumayya, tun daga kan yanayin hirararta da take yawan yi mata sannan kuma batada k'awar da takema rawar kai kamar zinat dan haka take kallon shak'uwace sukayi sosai tunda tun a school suke tare.
Sumayya taso abarta taje da kanta tatarbo zinat ammah ummah tace ba ruwanta taje tasami abbanta tatambayesa, kan dole tahak'ura dan tasan bazai ta6a barintaba dan haka tatura driver d'insu yaje yad'aukota.
Koda ta iso sumayya tayi mamaki sosai ganin shigar da zinat tayi dan shigace ta mutunci ba kamar wadda takeyiba in zatazo, haka takaita wajen sultana sadiya cikin mutunci suka gaisa idan kaga yadda zinat tagaishe da sultana sadiya sai karantse ga Allah cewa d'iyar mutunci ce.
Bayan sungama gaisawa sumayya janta tayi zuwa part d'inta, suna shiga dariya sumayya tashiga yi tace kai baby wannan shiga da kikayi sai mutum yarantse cewa musulmace kamila, yau kece da babban veil.
Hmm kedai bari baby nima jina nake wata iri ke dakyar na iya tako gidannan dan gani nake kamar zamu had'u da wannan mugun.
Ta6e baki sumayya tayi tace wannan ai tuni yai nisan kiwo dan soyayya tarufe masa ido ya za6i matarsa yabar iyayensa, inma asiri waccan makirar tayi masa to sudai sukasani.
Ke ni naji dad'in tafiyarsa dan yanzu zamu wala zamuci karenmu babu babbaka.
Haka dai kikace baby ammah nifa banso aurena yamutuba dan inason mijina.
Ta6e baki zinat tayi tace ni da bakyaso ko?
Kirufan asiri kema ai shedace kinsan ina sonki sosai baby da ace ban sonki da bazan kulakiba,,,cewar sumayya.
Ammah ai kinfi sonsa,,,
Dariya sumayya tayi tace zinat kenan ba bayaba wajen kishi, ni banfi sonsaba kowa da matsayinsa a wajena yanzu dai muje kiyi wanka kici abinci.
Ohk ma.
nan suka sakarma juna murmushi sannan sukawuce sumayya tataimaka mata tayi wanka sannan suka je tayi lunch bayan tagama suka zauna hira daga nan suka haye saman network.
Haka zinat tacigaba da zama gidansu sumayya kullum suna manne da juna, sultana sadiya har mamaki take yadda yanzu sumayya ko firar da take fitowa suyi ta daina kullum suna k'unshe cikin bedroom,,,nan tai mata uzuri ta d'auka duk saboda jin dad'in zuwan k'awarne dan ankwana biyu ba a had'uba kuma ko bakomai yanzu taga d'iyarta tana cikin farin ciki dan rabonta da taganta cikin yanayin tun tana tare da mijinta.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:52 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
*PAGE* 6⃣3⃣
Yarima tsaye yake gaban dressing mirror yana shiryawa inda zarah take zaune chan saman gado rungume da pillow ta zuba masa ido tana kallonsa.
Yana gama shirinsa juyowa yayi yakalleta tare da sakar mata murmushi yace ya dai baby?
Murmushin itama tayi tace ina kallon yadda handsome man yayi kyau nidai fatana kar aimin kwacensa.
Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.
Ganin haka yasa itama taja bakinta tayi shuru, nan yazo yad'auki key d'in motarsa da waya.
Rik'o hannunsa zarah tayi tare da marairaicewa tace please kakulanmin da kanka.
Zuba mata ido yarima yayi chan sai yajanye kallonsa daga fuskarta zuwa kan cikinta d'an kuntun murmushi yayi sannan yace nima kikular min da babyna.
Zarah sakin hannunsa tayi tare da d'aga masa kai, kallon fuskarta yayi yace sai nadawo.
Ahankali tace adawo lafiya.
Nan yajuya yafita yabarta nan zaune, shafa cikinta tayi sannan takoma takwanta tana mamakin halin yarima yadda cikin lokaci guda idan miskilancinsa yamotsa ko ita kanta bai saurara mata.
koda yaje hospital bayan ya gama round ya duba patients d'insa da suke ward, office d'insa yakoma nan yajanyo system d'insa yacigaba da research kasancewar kusan abinda yake kenan indai yazauna shikad'ai dan yasamu sauk'in yawan tunane-tunanen da yake.
Knocking d'in da akayine yasa yabada izini ashigo, ahankali taturo k'ofan tashigo tare da yin sallama.
Jin muryar mace yasa yarima yad'ago kai yasafkesu akan wata kyakkyawar yarinya wadda bazata gaza 25yrs ba sanye take cikin lace ta d'aura labcut daga sama sannan tayi rolling da veil kalan kayan, janye idanunsa yayi daga kallonta yamaida kan system d'in tare da d'aure fuska.
Bata damu da yadda yad'aureba tatako ahankali tazauna kujerar da take opposite d'insa, cikin kwantar da murya tace sannu da hutawa doctor.
Yarima batare da ya kalletaba yace meyakawoki office d'ina?
Batayi mamakin yadda yayi mataba dan daman tasan halinsane saidai ba yadda ta iya dole tafurta masa sirrin da yake cikin zuciyanta.
Murmushi tayi tace sorry doctor yanzu zan fad'amaka dalilin zuwana dafarko dai am Dr leemah ni staff ce a hospital d'innan dan nasan baka sanniba.
A gaskiya kana burgeni sosai yanayin yadda kake tafiyar da rayuwarka kuma naga kamar baka shiga harkar kowa komai naka da kakeyi me ajine saisa kake burgeni dan Allah idan ka amince inaso muk'ulla friendship.
'Dago kai yarima yayi yawurga mata wata irin harara har saida Dr leemah tatsorata ammah tadake dan a yadda takejinsa a ranta bata damu da duk abinda zaiyi mataba.
Ganin baida niyar yin magana yasa Dr leemah tacigaba da cewa kar kadamu indai zaka amincemin duk abinda kakeso zanyi maka koma menene,,,
Janye system d'in gabansa yayi tare da kallonta kamar ba zaiyi maganaba sai da yayi kusan 3 minutes sannan yace kin gama?.
Fari tayi masa da ido sannan tace eh my dear.
K'ara d'aure fuskarsa yayi tamau sannan yace ni anfad'a miki irin wad'annan banzayen mazan ne?
Ammah ai taimaka ma juna zamuyi ni kawai burina inga ka amince muna friendship koda ace bakasoniba nasan wata rana zaka soni.
Hanya yarima yagwada mata cikin tsawa yace get out of my office! kokuma yanzu in 6ata miki rai.
Ganin ba alamun wasa a tare da shi ga wani irin k'warjini da yayi mata, cikin sauri tamik'e tafita tabar office d'in tana mamakin halin yarima.
Bayan ta fita dafe kansa yayi saboda 'yar hayaniyar da yayi har yaji kansa ya fara ciwo, mamaki yake yadda daga fara aikinsa zuwa yanzu matan da sukazo daga different departments suka kawo masa kansu sunkai goma, tsaki yaja cike da jin haushi daga k'arshe tashi yayi yatattare komai yad'auki key d'insa yaficce, saida yafara zuwa masallaci yayi sallar azuhur sannan yawuce gida.
Lokacin da ya isa zarah tana zaune a parlournsu tana kallon wani indian series film, gabad'aya tamaida hankalinta a kallon dan tunda tayi wanka tayi sallah tazauna kallon hannunta apple ne take ci.
Sallamar da yarima yayine yasa tajuyo takallesa cike da mamakin ganin ya dawo ukku batayiba murmushi tasakar masa tare da cewa sannu da zuwa.
Yauwa kawai yace batare da ya bi ta kantaba yawuce yashige bedroom.
Mamakine ya ida kamata ganin yadda daga jiya zuwa yau duk ya canza mata, mik'ewa tayi dakyar tanufi bedroom d'in tana shiga lokacin yarima yana cire kayansa.
Takawa tayi ta isa inda yake, murmushi yarima yasakar mata yace ya dai?
Ajiyar zuciya zarah tasafke tace na d'auka laifi nayi maka.
Kallonta yarima yayi yace mekika gani?
Langwa6e kai zarah tayi tace toh ai naga duk ka canzamin.
Murmushi yayi tare da shafa fuskarta yace kar kidamu baby babu abinda kikayi min ai ke bakya laifi, yanzu dai bari inje inyi wanka kije kijirani kinji?
'Daga kai zarah tayi tare da sakar masa murmushi.
Yauwa baby, yarima yace sannan yawuce yashiga toilet.
Zarah zuwa tayi tafiddo masa kayan da zaisa sannan tazauna tana jiransa yafito.
Koda yafito ita tataimaka masa yashirya sannan suka fito, ita taje tad'ebo musu abinci takawo musu nan yarima yana ci yana lalla6ata itama tana ci,
Bayan sun gama zarah tagumi tazuba tana kallon yarima cike da son mijin nata.
Janye mata tagumin yayi yace kallon fa?
Duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya.
janyota yayi jikinsa yakwantar da ita saman cinyarsa tare da zame mata kallabinta yana shafar gashin kanta.
'Dago kai tayi takallesa tana murmushi tace my heartbeat akodayaushe naganmu a tare wani irin farin ciki nakeji a raina, ina k'ara godema Allah da ya mallakamin kai a matsayin miji abun sona.
Murmushi yayi sannan yace zarah banta6a tunanin zan iya son wataba a yanzu dan ko kusa bansa ma raina yin soyayya ba ammah a lokaci guda kinchanza min ra'ayina sai gashi Allah ya dasamin sonki a raina, a yanzu na gama yadda da cewa kece macen da nafara so a rayuwata ina fata Allah yabarmu tare dan kincika macen kirki tabbas su ummi gata sukayi min da suka za6amin ke a matsayin mata.
Tashi zarah tayi zaune tafuskancesa tana murmushi tace nafi kowa farin ciki dan gani nake kamar nafi kowace mace sa'ar miji dan komai na mijina daban yake.
jan hancinta yayi yace kedai kin iya tsokana na lura da ke.
shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace ni fa gaskiya nafad'a dan mijin nawa komai nasa maitsada ne sauk'inma da yanzu nad'an samu sauk'in miskilancinsa,,,tak'arashe maganar tare da kashe masa ido d'aya.
Matsota yayi a jikinsa tare da tura hannuwansa cikin rigarta yace zarah nagama amincewa da ke a rayuwata sannan kuma d'an zaman da mukayi da ke a yanzu nima ina mamakin yadda gabad'aya nafara canzawa, girgiza kai yayi sannan yace bansaniba ko dan na baro gidanmu, murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace nima kaina ina mamakin hakan.
Zarah fad'awa tayi jikinsa cike da tausayinsa da k'aunarsa tace my heartbeat kakwantar da hankalinka insha Allahu zaka koma cikin family d'inka dan nima ina buk'atar inganka cikinsu.
Yarima batare da ya bata amsaba yalalubo bakinta yakaimata zazzafan kiss sannan yakwantar da kansa saman cinyarta tare da maida idanunsa yalumshe.
Zarah ajiyar zuciya tasafke nan tacigaba da wasa da gashin kansa batare da ta k'ara maganaba dan hakan kawai da yarima yayi ya sa tagane bayason maganar.
______________
Yau ma kamar kullum sumayya da zinat manne suke da juna suna hirarsu dan a 'yan kwanakin da zinat tayi saida tasan yadda tayi tasa sumayya tafara cire yarima a ranta, suna cikin hirar zinat kallon sumayya tayi tace baby inaso kirakani kasuwa daga chan muje gidan wannan friend d'in tawa khausar saboda jibi nakeso inwuce yola.
Shuru sumayya tayi kamar ba zatayi maganaba sai kuma chan tace baby kina ganin za'a barni infita? Kinsan halin abbana ba zai aminceba.
Ta6e baki zinat tayi tace ni fa tsiyata da ke kin cika tsoro fitar da zamu d'anyi kawai mudawo, kuma ai ko a 6oyene sai kifita batare da ya saniba kifad'ama ummah kawai dan gaskiya dole muyi tafiyarnan a tare inkuma ba hakaba ban k'ara zuwa gidannan idan natafi.
Zaro ido sumayya tayi tace baby meyayi zafi haka, indai hakane toh na amince muje ammah gaskiya sai zuwa gobe saboda su abbah yanzu suna nan fada, zansan yadda zanyi inlalla6i ummah ta amince, ammah kikace zaki daina zuwa wajena ai bansan yadda zanyi da rayuwataba da mi zanji da mutuwar aurena ko da rabuwarki da ni?
Rungumota zinat tayi tace kiyi hak'uri baby kema kinsan bana iya rabuwa da ke,
Murmushin jin dad'i sumayya tayi tace nagode sosai baby Allah yabarmin ke.
Ameen babyna, cewar zinat.
Wanshe kare shiryawa sukayi cikin atamfarsu sukayi anko d'inkin riga da skirt kayan sun kamasu sosai, nan sukayi gwanin kyau, sumayya ce tafito tanufi part d'in mahaifiyarta
Zaune tasamu sultana sadiya tana waya dan haka tasamu gefenta tazauna tana jiranta.
Bayan ta gama wayar juyowa tayi takalli d'iyartata cike da so tace sumayya wannan gayu haka sai kuma ina?
Murmushi tayi sannan tace ummana dan Allah taimako guda nakeso kiyimin.
Zubamata ido sultana tayi tace ina jinki.
Gyara zamanta tayi tamarairaice tace ummah kinga zinat gobe takeson tawuce gida shine takeso dan Allah inrakata kasuwa tanaso tayo siyayya.
Ajiyar zuciya tasafke tace sumayya bank'i ta takiba saidai mahaifinki nake ji ma tsoro kinsan halinsa idan har nabari kika fita toh ba keba hatta ni kaina sai raina ya 6aci.
Rik'o hannunta sumayya tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah ummah kibarni inje, wlh indai banjeba bazataji dad'iba Indai abbah ne bazan bari muhad'uba kuma yanzu ai sun fita da daddy.
Shuru tayi kamar menazari sannan tace toh shikenan kije ammah dan Allah kar kidad'e sannan kutafi da guards da kuyangi.
Cikin jin dad'i sumayya tarungume ummanta tace nagode sosai ummana insha Allahu bazan dad'eba.
Dariya sultana sadiya tayi tace nidai na fad'a miki.
Mik'ewa tayi itama tana dariya tace karkidamu ummah bazan dad'eba.
Koda tadawo room d'inta zaune tatarar da zinat tana jiranta, ganinta yasa tamik'e tana Murmushi tace baby da alama naga munyi nasara.
Itama Murmushin tayi tace sosai ma, d'auko key d'in motarta tayi tare da d'an k'aramin veil d'inta tace yanzu dai zo mutafi tun kan abbah yadawo.
Cikin sauri suka fito sumayya bata tafi da kowaba kamar yadda sultana sadiya taso,
Motarta suka shiga tayi mata key, dagudu tafita daga masarautar.
Kasuwa suka fara zuwa sukayi shopping sosai duk inda suka ratsa kallonsu ake, sun dad'e a kasuwan sannan bayan sun gama suka wuce gidan k'awar zinat.
Kasancewa khausar tasan da zuwansu sosai ta tarbesu nan suka baje sukaita hirarrakinsu, sumayya jin irin labaran da suke fitowa daga bakin khausar saida ta jinjina kai ganin da aurenta ammah har zina take, abinda ita batayiba kenan saidai shan minti.
Sun dad'e suna hirar nan tamatsa ma zinat tatashi sutafi ammah zinat tak'i, tana kallo yadda khausar take shige ma zinat nan haushi yakamata,
Zinat ita kanta saboda sumayya ne yasa bata biye ma khausar ba dan duk yadda take huld'a da mata toh batayi gaban sumayya dan ta tsani ganin 6acin ranta sannan bataso taga kowa ya ra6eta.
Ganin yadda sumayya tacika tayi fam yasa zinat tace tatashi sutafi, haka khausar tacikasu da sha tara na arzik'i ammah kwata-kwata bata birge sumayya ba dan Indai mace zata ra6i zinat toh tsanarta takeyi.
Koda suka kama hanya gabad'ayansu shuru sukayi, murmushi zinat tayi tare da kallonta tace baby ya dai naga duk kin canza lokaci guda.
uhm dole kiga na canza baby wlh waccan friend d'in taki inbatayi wasaba sai na nakasata dan naga take-takenta nema take tashige miki.
Zaro ido zinat tayi tace kai sumayya yanzu khausar d'in?
Ta6e baki tayi tace koma wacece, nasan kina harkokinki abayan idona wannan bazan damuba tunda ba gabana kikayiba.
ajiyar zuciya zinat tasafke tace sumayya kema kinsan yadda nake jinki a raina bana tunanin akwai wadda nakeso sama da ke.
Kedai ayi sha'ani kawai baby nidai nasan ba kowace jakka zan iya ba kainaba,
Dariya zinat tayi dan tasan kishintane sumayya takeyi.
Daidai lokacin sumayya tayi horn, ganin motarsa yasa masu gadi cikin sauri suka bud'e mata gate dan sunsan halin gimbiyartasu yanzu zatace anyi mata laifi komai girmansu bazai hana tawulak'antasuba.
Koda tayi parking d'in motar nan ma'aikata sukayita zuwa gaiahesu a wulak'ance suke amsawa sannan tasa aka shigar musu da kayansu ciki.
Koda tashiga a parlour tasamu ummah tana ta saffa da marwa hannunta rik'e da waya, ganinsu yasa tayi ajiyar zuciyata tace ku sai yanzu kukaga damar dawowa?
Kallon juna sukayi sukai Murmushi sannan sumayya tace ummah siyayyarce dayawa mukayi.
Uhm kudai kawai kuce kun biya yawonku, ni kun barni nan cikin tashin hankali yanzu inda ace abbanki ya tambayeni mezance masa? Yanzu kuduba kuga yanayin shigarku dukkanku veil k'arami kuka fita da shi, ke sumayya kinsan dai yanayin gidan nan ammah kike komai yadda ranki yakeso
Marairaicewa sumayya tayi tace kiyi hak'uri ummana insha Allahu bazan k'araba.
Toh shikenan kushiga ciki kuhuta bari insa akawo muku abinci.
Toh ummah,,sukace tare da mik'ewa suka shiga bedroom d'in sumayya.
Koda suka shiga zinat kallon sumayya tayi da take shirin cire kaya tace baby yakamata kihuce hakanan daga fushin kinga ni gobe zan bar garin.
Shareta sumayya tayi tad'aura towel tana shirin wucewa toilet nan zinat tasha gabanta tace yau kuma baza'ayi wankan da ni ba?
Cike da jin haushi sumayya tace kije wajen wad'anda sukafini sai kuyi.
Rik'o hannunta zinat tayi tace baby *KIYARDA DA NI* babu wadda tafiki a wajena kekanki shedace dan kinsan hakan.
Murmushi sumayya tayi tace toh shikenan baby yanzu kicire kayan muje muyi wanka.
Cikin jin dad'i zinat tace toh nan suka wuce suka shiga wanka.
Bayan sun fito zinat wucewa tayi tasama d'akin key tazare tanufo inda sumayya take tsaye ta tsareta da ido, murmushi tasakarmata tace baby gobe zamu rabu dan haka kizo kisallameni dan nasan kafin ink'ara zuwa garinnan sai ankwana biyu tunda ke bazuwa kikeyiba.
Murmushi sumayya tayi tace shine harda sa key?
Uhm ina tsoron abinda yafaru yak'ara faruwa dan gabad'aya yarima ya gama tsoratani.
Dariya sumayya tayi tace lokacin fa kinban dariya dan kinma fini rikicewa, gaskiya yarima ba bayaba.
itama dariyar tayi tace wlh yana min k'warjini saisa banaso inzo gidanki idan yana nan.
Ta6e baki sumayya tayi tace baby kidaina tunomin har kinja raina ya fara 6aci.
Janyota zinat tayi tace sorry baby muje infaranta miki ran naki.
Haka suka wuce saman bed suna dariya nan suka shiga faranta ma junansu rai.
Abban sumayya da sultan Ahmad da suke tsaye daga chan waje guda suna hira a gaban idanunsu su sumayya suka dawo.
Cike da jin takaici sultan Abbas yace ma d'an uwansa yaya kaduba kaga wai d'iyar cikinace take sanye da wad'anchan suturar har ma tafita batare da saninaba.
Shi kansa sultan ahmad baiji dad'in yanayin da yaga sumayya ba ammah dan yakwantar ma da d'an uwannasa hankali yace kayi hak'uri kasan fa sumayya yarinyace kuma ko ba ma hakaba yaran yanzu addu'a kawai yakamata mucigaba da yi musu Allah yatsare mana su, insha Allahu da ta samu miji aurar da ita zamuyi tunda shi wanchan shashashan ya yi ma kansa.
Murmushi kawai sultan abbas yayi ba dan ya amince da maganar d'an uwannasaba haka yadaure suka gama hira sannan sukayi sallama kowa yawuce turakarsa.
Sultana sadiya da take zaune a parlour ganin mijin nata tayi kamar anjefosa yanayinsa da tagani saida tagirgiza, cikin 6acin rai yace da izinin wa wacchan yarinyar tafita?
Gaban sultana sadiya saida yafad'i rasa abinda zatace masa tayi.
Tsawa yadaka mata yace ba tambayarki nakeba!!!
rikicewa tayi tace am daman.....katseta yayi yace wlh kikiyayeni inba hakaba zan sassa6a miki, ashe har kwashe-kwashe tayi min cikin gida batare da saninaba daga ganin wacchan yarinyar da suke tare babu alamun tarbiya a tare da ita dan haka bazan d'auki wannan dak'ik'ancinba.
Ahankali cikin rarrashi tace Allah yahuci zuciyanka dan Allah kayi hak'uri.
cikin 6acin rai yace yanzu ina sumayyar take?
Nuni tayi masa da room d'inta tace tana ciki.
Wucewa yayi yanufi part d'in sumayya tura k'ofar yayi ammah yajita a rufe gam da alama key akasanya mata, har zai yi knocking sai kuma yafasa dan haka yawuce yatafi part d'insa.
Sultana sadiya da take zaune taga wucewarsa ajiyar zuciya tasafke tace Allah ya taimakeni, suma k'ila sunganshi saisa suka rufe d'akin.
Tana cikin tunanin kawai sai ganinsa tayi ya fito rik'e da spire key a hannunsa,,,zaro ido tayi tace ranka yadad'e me zakayi haka?
Wata uwar harara da yawatsa mata yasa ba shiri taja da baya.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Masoya nagode sosai da addu'o'inku agareni, gaskiya nayi farin ciki da irin kulawar da nasamu da kiran da kuka dinga yimin, ban ta6a tunanin ina da masoya irin hakaba saidai ince Allah yabar k'auna, sis nerja'art tana sonku over*_
❤❤❤
_~Masu tambayata yarima suhail daga farko ta pc, please kuyi hak'uri insha Allahu mun kusa gamawa za'a baku document idan muka gama~_
*PAGE* 6⃣4⃣
K'ok'arin bud'e d'akin yashiga yi, yana bud'ewa mutuwar tsaye yayi lokacin da ya hangosu tsakiyar gado lullu6e cikin blanket, gabansa ne yayi wani irin mummunan fad'uwa ganin abun yake kamar a mafarki murza idanunsa yayi yabud'e yagadai a zahirine nan yafara rafka salati.
Sumayya jin muryar abbanta yasa tadawo hayyacinta nan tarikice tafito daga cikin bargon, cikin sauri yajanye idanunsa daga kallonsu hawaye suna malala daga idanunsa.
Ganin abbanta yasa tasaki wata irin razanannar k'ara tare da rufe duka jikinta da bargon tana kuka cike da tashin hankali.
Zinat ma lek'o kanta tayi daga cikin bargon cike da tsoro da firgita.
Sultan abbas girgiza kansa yacigaba da yi cike da takaici yana salati muryarsa tana rawa yace sumayya kin cuceni kin zalunceni ni a matsayina na mahaifinki ba irin wannan tarbiyar nabakiba Allah yasani, wlh baki isa kisani jin kunya a gaban ubangijinaba.
Cikin sauri sultana sadiya tanufo d'akin dan ta d'auka dukansu yakeyi da tajiyo k'arar sumayya cewa take haba Alhaji dan Allah kayi ha....maganarce talak'afe a bakinta lokacin da ta hango su sumayya a wannan yanayin wata irin k'ara tasaki tare da zama dirshan a k'asa tana wani irin kuka, nuna sumayya tayi da yatsa tace sumayya abinda kikeyi kenan? abinda kika za6ar ma rayuwarki kenan? nashiga ukku ni sa'adiya mekikeso duniya tad'aukeni? K'ara sautin kukanta tayi tace wlh daman tunda naga wannan munafukar k'awartaki hankalina bai kwanta da itaba, kaicona ni sadiya wannan wace irin *K'ADDARA CE* tafad'amin.
Sumayya ko inba kukaba ba abinda take tsanar zinat ce da mummunar rayuwar da tayi takamata a karo nafarko da taji ta yi nadama akan abinda take aikatawa, girgiza kai tashiga yi tace wlh ba laifina bane kuyafe min abba, ummah kiyafemin wlh bazansakeba nadaina daga yau.
Kallon zinat tayi da take k'udundune tana zare ido gabad'aya jikinta rawa yake, cike da tsanarta sumayya tace Allah ya isa zinat kin 6ata min rayuwata wlh na tsaneki na tsaneki.
Sultana sadiya dak'yar tasamu tamik'e cikin kuka tanufi inda sumayya take tace wlh kasheki zanyi sumayya inhuta da wannan bak'in cikin naki.
Sultan Abbas ne yajanyota cikin d'aga murya tace ni kasakeni ina amfanin haihuwar d'iya irin sumayya? Kaduba kaga mugun abinda take aikatawa.
Sultan Abbas share hawayen fuskarsa yayi tare da kallon sumayya yace kinyi farin ciki kin saka iyayenki kuka kin kyauta ni bazan miki komai ba tunda ke babbace ba yarinyaba kinsan daidai ammah ni ban haifi d'iya irinkiba dan haka kije na sallama ma duniya ke, sannan dole memartaba yasan da maganar nan,,,,yana fad'in haka yaja sultana sadiya suka fita daga d'akin.
Sumayya cigaba tayi da kukan tana k'wala ma iyayenta kira ammah ahaka suka fita suka barta, juyowa tayi takalli zinat tace kin cuceni kin 6atamin rayuwa kin kashemin aure munafukar banza 'yar iska wlh dole yau asirinki yatonu dan ba nawa bane kawai yatonu.
Zinat cikin kuka tace sumayya dame kikeso inji da abinda yasameni ko da wulak'ancinki? Ni yanzu bari intashi intafi
'Daga hannu sumayya tayi tasharara mata mari tace babu gidan ubanda zakije dole ne kema kizauna duk abinda za'ayimin kema ayi miki.
Cikin kuka zinat tace wlh baki isaba wannan tsakaninkine da iyayenki ni babu ruwana.
'Daga hannu sumayya tayi tak'ara d'auketa da mari cike da jin haushi zinat tace kam ni kika mara? Nan tad'aga hannu itama tarama sai dambe yakaure a tsakaninsu dukan juna suka shigayi.
Daga k'arshe safkowa akayi daga saman gadon aka cigaba da dambe, duk suka fashe ma juna baki, sumayya samu tayi tayada zinat k'asa tabi tadanne tacigaba da bugunta ta ko'ina, kuka kawai zinat take tanaso takwaci kanta.
Sumayya cikin kuka take cewa wlh baki isaba dole kizauna munafuka, yadda asirina yatonu toh dole kema naki yatonu..tana fad'in haka tatadata taje tajanyo doguwar rigarta tasaka.
Sultan Abbas koda yafito zama yayi saman kujera tare da dafe kansa takaici da bak'in ciki duk sun cikasa, sultana sadiya na a gefensa k'asa zaune tana ta rusa kuka itama cike da takaici da bak'in ciki, gabad'aya akarasa me lallashin wani
Wayarsa ce datafara ruri yajanyo ganin mahaifinsane yasa yayi picking muryarsa tana rawa yai sallama.
Jin yanayin muryarsa saida hankalin memartaba yatashi yace abbas ya najika haka ko bakada lafiya ne?
Ahankali yace a'a ranka yadad'e,
memartaba cewa yayi toh kazo yanzu akwai sak'on da nakeso inbaka zaka kaima governor,
Shuru Sultan Abbas yayi dan baima san abinda memartaba yake cewaba.
Daga chan 6angaren memartaba cewa yayi abbas ko bakada lafiya ne?
Girgiza kai yashigayi kamar yana a gaban memartaba sannan yace ranka yadad'e kagafarceni bansan ya zanyi da rayuwataba wannan wace irin masiface.
memartaba kwata-kwata bai fahimci inda yadosaba yace wai abbas me yake faruwa? sai a lokacin yajiyo sautin kukan sultana sadiya,,,cike da tashin hankali memartaba yace meyake samunku haka? Mutuwa akayi ko me?
Cikin karyayyar zuciya yace ranka yadad'e ko d'aya, kataimaka kazo kaga halin da muke ciki da idanunka.
Toh yanzu dai gamunan zuwa kasaurareni.
Toh kawai yace sannan yakashe wayar.
Sumayya fitowa tayi daga d'akin tana sand'a wuri tasamu daga chan nesa da iyayenta tazauna k'asa cikin kuka tace dan Allah kuyafemin abbah wlh na tuba bazan k'araba.
Wata uwar harara sultan abbas yawurga mata.
Sultana sadiya ko rarrafawa tayi ta isa inda sumayya take tarufeta da duka tace kin cuceni sumayya ban ta6a sanin wannan rayuwar kike aikatawaba wlh sai na kasheki kowa yahuta.
memartaba saida yakira sultan ahmad yace suhad'u gidan abbas sannan yamik'e yakalli dada da tuni ta shirya hankalinta a tashe tana jiransa sutafi, yace muje.
Koda suka fito kusan a tare suka shiga gidan da su sultan ahmad da ummi, suna shiga parlourn ganin sultan abbas sukayi ya dafe kai inda sultana sadiya take dukan sumayya tana kuka.
Dada da ummine sukayi saurin isa wajen suka rik'e sultana sadiya.
Dada tace sadiya menene haka kikeyi sai kin kasheta?
Cikin kuka sultana sadiya tace ranki yadad'e kubarni inkasheta kowa yahuta wlh sumayya batayiba ina ma ace ba jininabace.
Sultana bilkisu ce tayi saurin toshe mata baki tace haba sadiya menene haka kike cewa? Yakamata kidawo hayyacinki.
Gyad'a kai sultana sadiya tayi tace kune zakuga kamar banda hankali ammah ni nasan abinda nake kubarni kawai.
Memartaba da gabad'aya an d'aure masa kai waje yasamu yazauna sannan yace kowa yasamu waje yazauna ayi magana Cikin kwanciyar hankali.
Gabad'ayansu k'asa suka zauna, memartaba da dada ne kawai saman kujera, sumayya ko tana daga chan nesa da su tana kuka.
Kallonsu Memartaba yayi d'aya bayan d'aya sannan yace kun d'aure mana kai dan gabad'ayanku kuka kukeyi ya kamata kufitar da mu bak'in duhunnan da kuka sakamu a ciki
Sultan abbas share hawayen fuskarsa yayi sannan yanuna sumayya yace ranka yadad'e kaduba kaga wai wannan d'iyar cikinace ammah kwata-kwata bata d'auko halinaba ina amfanin haihuwar d'iya irinta me bak'in hali.
Dada zuba masa ido tayi sannan tace kuyi mana bayani yadda zamu fahimceku mana.
Cike da takaici yashiga girgiza kai tare da runtse idanunsa sai chan yabud'e.
memartaba ne yace muna saurarenka.
Muryarsa tana rawa yace ranka yadad'e gatanan wai jininkace take neman mace 'yar uwarta.
Gabad'ayansu cikin rashin fahimta suke kallonsa
Sumayya da take raku6e gefe k'ara sautin kukanta tayi
Dada ce tace kayi mana bayani yadda zamu fahimta.
Nan yakwashe yadda yashiga yaganta da k'awarta yafad'a musu.
Gabad'aya labarin ya girgizasu nan aka fara salallami.
Dada batasan lokacin da tazamo k'asaba daga saman kujerar da take zaune, kallon sumayya tayi tace Allah wadai wlh bakiji dad'in rayuwarkiba ashe hakanan nake ganinki kamar mutuniyar kirki nan ko 'yar banzace,,,tak'arashe maganar tare da fashewa da kuka.
Memartaba idan ransa yayi dubu toh ya 6aci duk sanyin A-C d'in da take d'akin ammah zufa yake, yana kallon sumayya cike da mamaki, sannan yace sumayya abinda kika za6arma kanki kenan abinda ubangiji yaharamta, laifin da Allah ya kife mutunen annabi lud'u saboda shi, kina zuwa islamiyya kin karanta kuma kinsani saidai bakiyi amfani da saninkiba shin mancewa kikayi da fad'ar ubangiji da yace ya halitta mana mata dan musamu nutsuwa daga garesu, haka kuma yahalitta maza dan kuma mata kusamu nutsuwa daga garesu, shin hakan da kikeyi ke kina ganin shine daidai agareki? Rayuwar da ko dabbobi basu irinta, wlh baki gani dabba tana neman jinsinta, Ko kinsan makomarki idan kika koma ma mahaliccinci?
Girgiza kai sumayya tashiga yi cikin kuka har muryarta ta fara dishewa tace kuyafemin wlh na daina zinat itace ta6ata min rayuwa da ace ban amince ma zinat ba a matsayin k'awata da hakan bata kasance da ni ba.
Murmushi memartaba yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace tashi kizo min da k'awartaki
Mik'ewa tayi jiki ba k'wari tanufi bedroom d'inta, tana shiga tatarar da zinat ta had'a komai nata, cike da tsanarta sumayya tace munafuka alguguma babu inda zakije kizo memartaba yana nemanki.
Cike da tsoro zinat tadafe k'irji tace eyeh na'am.
Harara sumayya tawurga mata tace dallah kizo mutafi ko yanzu asa afiddoki.
Ai zinat cikin sauri tawuce tabi bayan sumayya, suna fitowa parlour nan ta ida tsurewa tsaye tayi tana binsu da kallo cike da tsorata.
Sultan ahmad ne yadaka mata tsawa yace bazaki zaunaba?
Cikin sauri tazube k'asa jikinta yana kakkarwa.
Memartaba kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yajinjina kai yace toh wanene mijin wacece matar?
Kuka kawai suke aka rasa me amsawa a cikinsu.
Dada ce cikin 6acin rai tace dan ubanku ba tambayarku akeba ko sai ansa dogarawa sun tambayeku?
Sumayya rage sautin kukanta tayi cike da nadama tace wlh duk abinda na aikata zinat ce silah, ita ce silar mutuwar aurena, ita tahanani inyi ma mijina biyayya.
Gabad'ayansu salati suka saka, dada tace kar dai kice min yarima baida laifi acikin sakin da yayi miki.
'Daga kai tayi tace eh baida laifi wlh duk abinda nafad'a muku k'aryane, yarima yana k'ok'arin kyautatamin wannan ce take hure min kunne.
Gabad'ayansu saida maganar Sumayya tarikitasu sultana sadiya cikin kuka tace wlh sumayya banda abinda zance miki saidai ince kije da halinki duniya zata koya miki darasi.
Dada ko mik'ewa tayi tanufi wajen sumayya tahauta da duka tana fad'in sumayya kin cuceni kin rabani da jikana kin had'ani da shi kinsa nad'aura masa karan tsana, bazan barkiba dole kema yau kibar gidannan.
Sultana bilkisuce tazo tajanye sumayya da takasa tashi, cikin muryar kuka tace narok'eki dada kiyi hak'uri kibarta, dada girgiza kai tashiga yi tace ya akeso inyi ina zanga jikana?
Rik'o hannunta sultana bilkisu tayi taje tazaunar da ita tace kiyi hak'uri dada duk inda yarima yakasance yana cikin k'oshin lafiya.
Memartaba da yake binsu da kallo sai a lokacin yayi magana yace kaicona ina ma ace naba yaronnan dama yafad'i ta bakinsa, tabbas 6acin rai baiyiba kamar yadda zartas da hukunci cikin fushi baiyiba.
Sumayya kin zubarmin da k'ima da daraja a cikin masarautata kin rugazamin duk wani farin cikina na rayuwa, kin rabani da jikana da nafi so a rayuwata.
Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace kuyafemin wlh *nayi nadama*
Jinjina kai Memartaba yayi yace sumayya kenan dole ku amsa hukuncin abinda kuka aikata kamar yadda nake zartas ma da sauran al'ummah dan haka zansa ayi muku bulala tamanin tamanin
Murmushi sumayya tayi tace indai har haka zaisa insamu sauk'in abinda na aikata toh na amince.
Sultan Ahmad ne yace ranka yadad'e yakamata a sassauta musu.
Girgiza kai Memartaba yayi yace wannan shine adalci nan yajanyo wayarsa yakira wani amintaccen dogarinsa sahalu,
ko da yazo nan memartaba yace ashiga da su sumayya ciki ai masu bulala tamanin tamanin, kasa tashi dogarin yayi dan jin maganar yayi kamar ba daidai yajiyoba, saida memartaba yace umurni nabaka kuma amana dan haka banda ragi,
cike da girmamawa yace toh ranka yadad'e.
Nan aka shiga da su sumayya cikin d'akinta dan gudun kar wasu sugani, sumayya tafara kwanciya dan ita bata tsorata da bulalar da akace za'ayi mataba ita dai burinta ubangijinta da iyayenta suyafe mata, bulalar farko wata irin k'ara tasaki koda akan adalci yayi musu ba kamar wadda za'ayi ma namijiba su ya d'an safsafta musu saboda matane, bai kyaletaba saida yayi mata tamanin tun tana iya motsi har takasa daga k'arshe sumewa tayi ahaka aka gama tana a sume, sannan yadawo kan zinat itama tana ihu da hargagi ahaka aka gama aka barta kwance bata iya motsin kirki.
Memartaba gudun kar suji k'ara yasa aka kunna tv tare da cika volume ammah duk da haka sunaji sama-sama, ummi, dada, sultana sadiya kuka kawai suke ahankali cike da takaicin abinda sumayya ta aikata
Bayan dogarin ya fito nan yatabbatar ma da memartaba ya yi kamar yadda ya umurcesa nan memartaba yasallamesa yatafi.
Sawa yayi aka rage volume sannan yakallesu cike da damuwa yace yanzu ya duniya zata d'aukeni? Da wane suna za'a kirani? Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un wannan wace irin *k'addara ce* yanzu duk mutuncina da darajata sun zube a idanun mutane
Sultan abbas cike da damuwa yace ranka yadad'e ni kaina narasa ya akayi ina zaune da sumayya ammah bansan abinda take aikatawa ba, kokuma ni k'arani kan waccan uwar banzar da akodayaushe take tare da ita ammah batason laifinta sannan ace batasan duk wani motion d'in d'iyartaba toh wannan wace irin soyayyace takeyimata, wannan ba so bane haukane tunda baki iya tarbiyar da d'iyar cikinki dan haka daga ke har ita kutafi kuban waje bana buk'atarku a cikin rayuwata.
Sultana sadiya k'ara fashewa tayi da sabon kuka tace nashiga ukku idan karabu da ni ina kakeso inje inji dad'i bayan banida kowa bayanku dan Allah kayi hak'uri kayafe min wlh bansan sumayya tana wannan mummunar halayyarba.
Cikin d'aga murya sultan ahmad yace kai miye haka kakeyi idan rai ya 6aci ai baidace zuciya ta6aciba yakamata kadawo hayyacinka ita kuma sadiya miye nata laifin aciki? Itada ba ita tayimakaba shine zaka had'a da ita?
Girgiza kai sultan abbas yashigayi yace kubarni nikad'ai nasan abinda nakeji su dukansu banason ganinsu.
Memartaba jinjina kai yayi yace babu inda zasuje, sannan yakalli sultana bilkisu yace jeki kigano min su sumayya.
Mik'ewa sultana bilkisu tayi cikin sauri tanufi part d'in sumayya tana shiga yanayin yadda taga sumayya saida tatsorata dan batada banbanci da matatta, zinat ko numfashi take fitarwa sama-sama tana jan jiki daga kwancen.
Cikin sauri ta isa inda sumayya take tashiga jijjigata ganin bata motsi yasa tamik'e taje tad'ebo ruwa tamakaka mata, wani dogon numfashi sumayya taja ahankali tashiga motsa hannunta nan hawaye suka shiga malala daga idanunta, ahankali tabud'esu tasafke akan ummi da itama take hawayen, muryar sumayya ciki-ciki tace ummi kice min mafarki nake ba gaske bane, wlh ummi nayi nadama nadaina kuyafemin.
Ummi rungumo sumayya tayi a jikinta tace shikenan sumayya yanzu dai bari ingasa miki jikinki kinga duk ciwone.
Murmushin k'arfin hali sumayya tayi tace ummi ciwon da nakeji a zuciyata yafi radad'in bulalarnan dan Allah kitayani ba su abbah hak'uri.
Ummi sharemata hawayen fuskarta tayi tace kar kidamu yanzu dai muje kifara gasa jikinki,,,,haka ummi taje tahad'a mata ruwan d'umi ita tataimaka mata tagasa jikinta tayi wanka sannan tashiryata takwantar da ita saman gadonta saboda jikinta yad'au zafi sosai.
Juyowar da ummi zatayi nan taga zinat tana d'aukar kayanta tana bin bango dakyar take tafiya har tafita daga d'akin.
Ai tana fitowa parlour tacikaro da su memartaba rikicewa tayi tasaki jakkarta tare da duk'awa tace dan Allah kuyafemin wlh natuba bazan k'araba.
Murmushin k'arfin hali memartaba yayi yace dole ki amsa hukunci tunda kece silar lalacewar sumayya, kuma kece silar rugujewar duk wani farin ciki na masarautar nan dan haka yanzu zansa akaiki gidan yari kid'an kwana biyu.
Zinat sake fashewa tayi da sabon kuka tace dan Allah kuyi hak'uri wlh ba zan sake dawowaba.
Memartaba wayarsa yad'auko yai kira, cikin mintuna kad'an saiga wani k'aton barde yashigo nan memartaba yace atafi da zinat gidan yari duk wani aiki me wahala asata kar a sassauta mata .
Cike da girmamawa yace angama ranka yadad'e, nan yatusa zinat gaba tana kuka tana rok'onsu ammah ahaka aka fita da ita babu wanda yasaurareta.
Sultana bilkisu fitowa tayi tashaida musu halin da sumayya take ciki ammah kowa shareta yayi yace baruwansa, dada ma cewa tayi tamutu mana ina ruwan wani, sultan ahmad ne kawai yatausaya mata nan yakira family doctor d'insu.
Memartaba da takaici ya isheshi mik'ewa yayi batare da yayi ma kowa maganaba yawuce yaficce nan dada tabi bayansa.
Ganin haka yasa sultan abbas ma cike da 6acin rai yatashi yawuce part d'insa, sultana sadiya ma tashi tayi tabi bayansa dan gabad'aya hankalinta atashe yake addu'a take cikin ranta akan Allah yasa kar aurenta yamutu.
Sultan ahmad da sultana bilkisu ne suka cigaba da zama har doctor yazo yaduba sumayya yabata drugs tasha, nan sultan ahmad yatafi yabar sultana bilkisu wajen sumayya tana cigaba da kula da ita tare da kwantar mata da hankali har dare sannan tafara shirin komawa turakarsu, sumayya ba dan tasoba haka tahak'ura tabar ummi tatafi.
bayan ummi ta tafi nan tadasa wani sabon kukan cike da nadamar abinda ta aikata, ji take ina ma tabud'e ido taga duk a cikin mafarkine komai yafaru saidai inaa *k'addara ta riga fata* haka tayita juyi tana kuka har wajen k'arfe d'ayan dare nan tatashi dakyar jiki ba k'wari taje tad'auro alwallah akaro na farko a rayuwarta da tafara tunanin yin nafila, nan taita sallah tana neman yafiyar ubangiji har wajen k'arfe ukkun dare, tana zaune a saman darduma tana lazumi ahaka bacci yai awon gaba da ita.
Sultana sadiya koda tabi sultan abbas part d'insa tana ganin ya zauna bakin gado nan tazo tatsugunna gabansa cike da nadama, cikin kukan tace Dan Allah kayafemin wlh zan canza rayuwata, duk abinda na aikata wlh akan kuskure da *SON ZUCIYA* na aikatasa, tabbas a yanzu nasan ba gata bane nanuna ma sumayya, dan Allah kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko nasamu d'an sauk'i acikin raina.
Murmushi sultan abbas yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace sadiya kin aikata babban kuskure wanda tabonsa ba zai ta6a gogewaba a raina, na aureki ina gani kamar zaki taimaka min wajen ganin mungina rayuwarmu da ta 'ya'yanmu cikin tsafta, ashe bahaka bane ni kad'ai nake haukana ke kin riga kin tsara taki rayuwar, toh me yayi saura a yanzu? Me zakice min?
Cikin kuka tashiga girgiza kai tace kayi hak'uri wlh tsautsayine insha Allah yanzu zan gyara.
A wulak'ance yakalleta yace kar ma kigyara dan ba matsalata bane dan haka kitashi kifita kiban waje tun kan ranki ya6aci.
Cikin sauri sultana sadiya tamik'e tare da cewa Allah yahuci zuciyanka sannan taficce tabar d'akin tana waiwayensa.
Memartaba koda yakoma turakarsu cike da tashin hankali tare da nadamar abinda yayi ma yarima suhail maganganun da yayine akansa yadinga dawo masa a k'wak'walwa, jiyake ina ma ace ya tsaya yai bincike kafin yakori jikansa dayafi k'auna a rayuwarsa Memartaba harda 'yar k'wallarsa, dada ita kanta koda tana cikin tashin hankali ammah haka tadanne tashiga lallashin mijin nata dan soyayi yaje yafara neman yarima a lokacin, dakyar tasamu taja ra'ayinsa yafasa zuwa dan darene,
A 6angaren ummi ma koda takoma part d'insu kuka taci sosai har sultan ahmad yashigo yatarar da ita, cike da tausayinta yazauna gefenta d'ago kai tayi takallesa cikin kuka tace kagani ko suhail d'ina baida laifi dan Allah kasa baki memartaba ya amince sudawo gida.
Rungumota yayi jikinsa cikin lallashi yace sultana kikwantar da hankalinki suhail zai dawo agaremu tunda baida laifi a ciki, na tabbata memartaba zai sa anemo masa shi dan shi kansa yana cikin damuwar rashin suhail.
Kicigaba da addu'a kinji ko?
'Daga masa kai tayi alamun eh, nan yacigaba da kwantar mata da hankali daga k'arshe suka kwanta.
Gabad'aya family d'in babu wanda yasamu yayi baccin kirki dan kowa hankalinsa atashe yake.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
*PAGE* 6⃣5⃣
Asubar fari sumayya tafarka koda daman ba wani baccin kirki bane tayi, alwallah taje tad'auro tazo tagabatar da raka'atanil fijir sannan tazauna tayi ta tasbihi da istigfari kafin atayar da sallah.
Bayan ta gama sallah alqur'ani tad'auko tashiga karanta abinda ta iya acikinsa har saida gari yai haske sannan tayi addu'a takoma takwanta ammah bacci yace d'aukarni inda kika barni, haka tayita juyi ga baccin tanaji ammah ba dama, saidai hawaye kawai da suke fita daga idanunta.
A ranar haka tawuni cikin d'akinta bata fitaba saboda kunyar iyayenta da takeji, ko breakfast batasamu tayiba koda tana jin yunwa dan rabonta da abinci tun jiya da rana.
A 6angaren memartaba ko tun dasafe yatura aje abinciko masa yarima duk inda ake tunani za'a gansa anje babushi har gidansa da yagina saida akaje ammah babu labarinsa har marece yayi ana nemansa sannan daga baya akazo aka shaida ma memartaba.
Memartaba baiji dad'iba cikin daren har so yayi yafita dakansa yak'ara bincikawa ammah su sultan ahmad suka bashi baki dak'yar sukasamu yahak'ura.
Sumayya ko sallah ce kawai take tashinta daga saman gadonta cikin d'an k'ank'anin lokaci duk tatsure tarame kamar ba itaba, chan wajen marece ummi tashigo ganin sumayya a wannan yanayin saida tatausaya mata nan tasa aka kawo mata abinci dak'yar tasamu tad'anci kad'an sannan tak'ara yi mata nasiha da wa'azi, sumayya kuka tayi sosai sannan tace ummi dan Allah kuyafemin wlh bazan k'araba, sharrin shed'anne nadaina, k'ara sautin kukanta tayi tace ummi ina jin tsoron had'uwana da ubangijina.
Ummi cike da jin tausayinta tashare mata hawayen fuskarta tace yauwa sumayya indai har kinyi tuba wadda bazaki koma abisa abinda kike aikatawa toh ubangiji zai yafe miki zai kar6i tubanki domin ubangijinmu mai tausayin bayinsane idan yaso yana yafe abinda yake tsakaninsa da bawansa komai yawan zunuban mutum Indai katuba toh zai yafe maka inyaso, hak'ine kawai baya yafewa dan wannan tsakanin mutum da wanda aka zaluntane, dan haka kicigaba da istigfari da yawan tasbihi tare da addu'a, sannan yanzu kitashi kije kinemi gafarar iyayenki dan suma suna da hak'i a gunki.
Rik'o hannun ummi tayi cikin dashashar muryarta da tasha kuka tace ummi kitaimaka min kirakani k'ila idan dakene zasu iya yafemin ammah idan naje nikad'ai korata zasuyi.
Shafa kanta ummi tayi tace kar kidamu sumayya bazasu korekiba insha Allahu, tashi muje ammah bazan shigaba kekad'ai zaki shiga.
Mik'ewa sumayya tayi dakyar take tafiya jiki babu k'wari sultana sadiya tana rik'e da ita sukanufi part d'in iyayenta.
Daga bakin k'ofa sultana taja tatsaya, nan sumayya tatura d'akin ahankali tashiga, sultan abbas zaune yake a parlournsa yana kallo ammah idan mutum yalura zai gane ba kallon yakeba dan gabad'aya hankalinsa yayi wani wajen daban, daga nesa da shi kad'an sultana sadiya ce ta buga uban tagumi ta tsura ma waje guda ido.
Shugowar sumayya yasa gabad'ayansu suka juyo suka kalleta daga nesa dasu kad'an tatsugunna bata damu da mugun kallon da sultana sadiya take watsa mataba, duk'ar da kanta tayi nan hawaye suka cigaba da zuba.
Ummah ce cikin fushi tace ubanmi kikazo yi mana nan? Ko sai kinga kin kashemu sannan hankalinki zai kwanta?
Girgiza kai tashiga yi, muryarta tana rawa tace ummah Abbah dan Allah kuyafemin wlh nadaina.
Munafukar banza wlh ko kitashi kifita kiba mutane waje ko yanzu insa6a miki.
Shuru sumayya tayi kamar ba da ita takeba saida sultana sadiya ta kwatsa mata tsawa sannan tamik'e jiki babu k'wari kallon iyayen nata tayi d'aya bayan d'aya sannan tafita tana kuka.
Ummi da take tsaye ganin ta fito tana kuka yasa tace sumayya basu hak'uraba?
'Daga mata kai sumayya tayi tace ummi kitaimaka muje tare k'ila insuka ganki zasu hak'ura.
Rik'o hannunta sultana bilkisu tayi tace kar kidamu yanzu dan suna cikin fushine kibari ak'ara koda kwana biyune sai kik'ara komawa yanzu muje kikwanta kihuta.
Girgiza kai sumayya tayi cikin muryar tausayi tace ummi dan Allah zanbiki part d'inki inzauna tunda wajenkune kawai nake samun sauk'i.
Murmushi ummi tayi tace shikenan sumayya muje ai da nan da chan duk d'ayane, cikin jin dad'i sumayya tayi ma ummi godia sannan sukaje part d'inta tahad'a kayanta suka tafi.
Room d'in da rahama tazauna nab taza6a aka shigar mata da kayanta, bayan ta yi sallah gado tahau takwanta nan tashiga rama baccin da ake binta.
Ummi bata barinta tana zama ita kad'ai janyota take sufito parlour suzauna takunna musu kallo, daga k'arshe malami tasamo mata yake zuwa yana koyar da ita littafan addini duk bayan sallar magrib.
Nan da nan sumayya tacanza takoma so silent dan magana ma bata dametaba bare fita babu inda take zuwa indai bata room d'inta toh tana tare da ummi, idanuwanta sun wani k'ank'ance saboda yawan kuka dan kuka kawai takeyi tasamu sauk'in zuciyanta ganin da take itace silar rugujewar duk wani farin cikin family d'insu, ga su yarima da take ganin ta zalunta, kullum addu'arta d'ayace Allah yabayyanasu ko tasamu tarok'i gafararsu.
su kansu ma'aikatan gidan saida suka dinga mamakin sauyin da sumayya tayi.
Memartaba ko badan komai yakyale sumayya ba sai dan ya fiso sai yarima ya dawo yayanke mata hukunci da kansa dan aganinsa hakan shine daidai.
a yanzu tare dashi da 'ya'yansa ake fita neman yarima idan suka fita tun safe basu dawowa sai dare, wasa-wasa duk inda ake tunani za'a gansa anje ammah babushi babu dalilinsa saida akayi sati guda sannan yasa anayi masa safka tare da addu'a akan Allah yabayyanasa.
Gabad'aya memartaba ya fita hayyacinsa dan ko abincin kirki baida lokacin zama yaci, dada ita kanta batada buri sai nason ganin yarima.
Su ko iyayen gayya ba a magana dan danne zuciyarsu kawai suke ammah basuda buri da yawuce suga d'ansu, dan ita kanta ummi kusan kullum sai ta kira number d'in da yarima yakirata da ita but switch off take, tasha ta6oye a part d'inta taci kukanta, tana danne damuwartane saboda 'ya'yanta da sumayya.
Dan rahama saida ummi tataka mata burki sannan tadaina zuwa gidan, shaheed kullum baida aiki sai lallashinta dan gabad'aya tarikice masa koda shima yana cikin damuwar rashin abokinsa.
ita ko husna daman ba gwanar zuwa bace koda ma tayo ma ummi waya tace zatazo toh hanata zuwa ummi take kan dole suke hak'ura.
Memartaba yau tunda yatashi da wani irin zazza6i yatashi hankalin kowa saida yatashi anso akira masa family doctor ammah yahana, chan zuwa anjima tun yana daurewa saigashi yakasa daga k'arshe saida zazza6in yakwantar da shi, wasa-wasa sai ciwon ciki, gabad'aya saida hankalin kowa yatashi dan ko abinci baya yadda yaci, dakyar aka samu ya amince akakira family doctor d'insu yadubasa.
Da family dr yazo yadubasa maganin zazza6i yabada sannan yace dole sai anje anyi masa scanning anga menene yake causing d'in ciwon cikin dan cikin har d'an kumburi yafara.
Koda akaso memartaba ya amince aje k'iyawa yayi yace shi ba inda zaije ai Allah yana sane da halin da yake ciki sucigaba da yi masa addu'a kawai in da rabon yatashi toh zai tashi, shidai burinsa suje sucigaba da bincika masa yarima.
Nan fa hankalin kowa ya ida tashi aka shiga lallashinsa akan ya amince aje, ita kanta sumayya hankalinta ya tashi sosai dan wajen ummi takejin komai taso taje taganosa ammah ummi tace a'a kar tatafi saboda gudun kar wata matsalar takunno kai, su rahama ma kusan kullum yanzu sai sunzo dubasa ummi da taga suna niyar zama sudad'e sai tahad'e fuska kan dole suke tashi sukoma gidajen mazajensu.
Ita kanta sultana sadiya gabad'aya tayi sanyi sosai dan kowa saida yai mamakin sanyin da tayi, dakyar tasamu mijinta yasafko daga fushin da yake da ita shima saida taje tana ma dada kuka tana rok'onta sannan dada ta amince takirasa tarok'esa akan yai hak'uri sannan yahak'ura ammah ya ce kar wanda yasa baki akan sumayya,
_______________
Yarima firgit yayi yafarka daga baccin da yake nan yatashi zaune tare da dafe kansa yana furta innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, mafarkin da yasabayi ne kusan kullum dan a yanzu mafarkin ya zame masa jiki, saidai na yau yafi firgitasa.
memartaba ne yake gani cikin wani irin yanayi yana kiransa yana cewa yadawo garesa, yau kuma har da umminsa da sauran danginsa yagani a ciki,,,,dafasa da akayine yasa yajuyo yakalli zarah, cike da tashin hankali tace meyake faruwane ko mafarki kayi?
Murmushi yasamu yak'ak'aro yayi mata, ganin idanuwanta sun cika da k'wallah yasa yajanyota jikinsa yarungume sun dad'e a haka sannan yace zarah kidaina damuwa mafarkine kawai nayi ba wani abuba.
Ajiyar zuciya tasafke tace toh ai ina lura da kai kusan kullum sai ka tashi a razane.
Kidaina damuwa dear kinsan sharrin mafarki nima daga yanzu ban k'ara damuwa addu'a kawai zan cigaba da yi incanza hannu.
'Dago kai tayi takallesa cikin ido tace promise?
'Daga mata kai yayi yana murmushi sannan yakwantar da ita tare da rufeta da blanket, rik'o hannunsa tayi, ganin haka yasa yakwanta a gefenta nan suka sakar ma juna murmushi, hannu yakai yana shafar cikinta ahankali yace oya sleep now.
Maida idanuwanta tayi tarufe, nan yazuba ma zara-zaran eye lashes d'inta ido, yanaji har bacci yad'auketa sannan yazare hannunsa yamik'e jiki babu k'wari yanufi toilet.
Mafarkin da yayi yashiga dawo masa nan yad'ibi ruwa yawatsa ma kansa tare da safke ajiyar zuciya, alwallah yad'auro sannan yafito yacigaba da yin nafila bashi yadainaba har saida aka kira sallar asuba yayi raka'atanin fijr sannan yaje yatashi zarah.
Saida yaga ta mik'e sannan yawuce masallaci.
Lokacin da yadawo gari ya d'anyi haske dan a chan Dr mu'az yabarosa shi yadawo gida.
Daga bayan zarah yaje yakwanta tare da rungumota ta baya ahaka yasamu bacci yai awon gaba da shi.
Chan cikin bacci juyin da zaiyi yaji ba zarah yalaluba bai jitaba dan haka yabud'e idanunsa, bin d'akin yayi da kallo ko'ina fes sai k'amshi ke tashi ammah babu zarah a ciki, murmushi yayi sannan yakai kallonsa ga agogon da take manne a jikin bango.
Zumbur yayi yamik'e ganin har 12pm tayi, mamakine yakamasa ganin irin baccin da yasha kuma zarah bata tashesaba cikin sauri yawuce yashiga bathroom.
Bayan ya fito tsaye yake gaban dressing mirror yana shiryawa baisan lokacin da zarah tashigoba saidai ji yayi anrungumesa ta baya, murmushi yayi tare da kallonta ta cikin mirror, itama murmushin tasakar masa sannan tace ashe ka tashi dear? Dafatan antashi lafiya my heartbeat, jawota yarima yayi tadawo gabansa saida yaja kumatunta sannan yace shine kika tashi baki tasheniba?
Ash dazafi fa,,,tafad'a tare da turo d'an k'aramin bakinta da yasha jambaki, sannan tace toh ai gani nayi jiya bakayi baccin kirkiba tunda katashi baka komaba.
Cije le6enta yayi sannan yace injiwa yace ban koma bacciba?
Fari tayi masa da ido tace ina fa kallonta lokacin da kake sallah duk farkawar da zanyi sai naganka kana sallah.
Hancinta yaja yace toh naji sarkin sa ido yanzu dai jeki kid'auko min kaya insa intafi kinga nayi late.
Kwantar da kanta tayi a k'irjinsa tare da marairaicewa tace please kahak'ura da zuwa yau tunda baku clinic kaga sai kazauna gida kahuta.
K'ara rungumeta yayi a jikinsa tare da tura fuskarsa cikin gashin kanta da yazame mata d'ankwali, jin baiyi maganaba yasa zarah tace please kar kaje.
Janyeta yayi daga jikinsa yace toh in nazauna me zakiyi min, Inma ba ciwon kai ba da zaki sanyani.
Zarah turo baki tayi tace au nimace nakesanya ka ciwon kai? Toh shikenan kayi tafiyarka inda ba a sanyaka ciwon kai,,,tana fad'in haka tajuya taficce daga d'akin.
Murmushi yarima yayi yace ina ruwan zarah sarkin rigima, nan yawuce yabud'e wardrobe yad'auko kayansa yasaka sannan yafito parlour yatarar da zarah zaune ta had'a rai.
Murmushi yayi yazo gefenta yazauna tare da rik'o hannunta yace baby fushi kuma?
Fizge hannunta tayi tace ni kakyaleni kaje kawai chan inda ba'a sanyaka ciwon kai, daman nasani ni ba ajin aurenka bace kawai dai nayi babban kuskure da na amince ma zuciyata tafara sonka.
Yarima ido yazuba mata cike da mamaki har saida takai aya sannan yace nifa zarah dawasa nakeyi miki babu inda zanje yau ina nan gida tare da mummyn baby.
Mik'ewa zarah tayi tana turo baki tawuce zata bar wajen nan yajanyota saman cinyarsa yace please fushin ya isa haka tunda na fad'amiki babu inda zanje.
Uhm ni da nake sanya maka ciwon kai.
Oh zarah ni fa wasa nake miki yakamata kiyarda dani.
Murmushi zarah tasakar masa tare da tallabo fuskarsa da hannu biyu sannan tace idan ban yarda da kai ba habibinah toh dawa zan yarda?
Shima maida mata martanin murmushin yayi yace nima tunanin da nake kenan baby, yanzu dai jeki ki kawo min breakfast inyi dan yunwa nakeji inyaso daga baya naji da rigimar taki.
Kissing d'in bakinsa tayi tace angama ranka yadad'e yadda kakeso haka za'ayi sannan tamik'e tana tafiya dakyar tafita taje parlour tad'ebo musu breakfast sannan tadawo nan suka zauna sukayi breakfast.
Bayan sun gama bajewa sukayi saman carpet yarima yad'aura kansa saman cinyarta, turo baki zarah tayi tace ni kad'agani inba so kuke kai da babynka kukaryaniba.
'Dago kai yayi yakalleta yace shikenan tunda haka kikace bari ma kawai intashi intafiyata.
Cikin sauri zarah tagirgiza kai tace a'a kayi kwanciyarka ni da wasa nakeyi.
Dariya yarima yayi yace dad'ina da matarnan tawa matsoraciya ce toh me kikeji ma tsoro a ciki?
Zarah d'aure fuska tayi tace ai dole inji tsoro saboda 'yan matan garin nan kamar mayu nasan kullum idanunsu suna a kan mijina saisa duk fitar da zakayi hankalina a tashe yake har sai ka dawo,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka.
Da mamaki yazuba mata ido yana kallonta, ganin hawaye sun fara zuba daga idanunta yasa yatashi zaune tare da janyota jikinsa yace zarah yakamata kisan abinda mijinki zai iya da wanda ba zai iyaba, ni a yanzu 'yan mata basu a gabana dan babu ma wacce ta isheni kallo.
Uhm ammah ai su kana gabansu idan su basa gabanka.
Janyeta yarima yayi daga jikinsa tare da jingine kansa a jikin kujera yamaida idanunsa yalumshe.
Ido zarah tazuba masa sannan tarik'o hannunsa ahankali tace kayi hak'uri.
Bud'e idanunsa yayi yakalleta yace zarah mekikayi min da kike ban hak'uri?
Cikin shagwa6a tace toh ai naga kamar fushi kake da ni.
Ta6e baki yayi yace no ko d'aya ni ba fushi nake da keba kawai rigimarkice naga tanaso tafi k'arfina.
Rik'o hannunsa tayi tare da marairaicewa tace toh nadaina kayi hak'uri.
Murmushi yarima yayi tare da duba agogon da take mak'ale a hannunsa sannan yace bakomai baby yanzu dai tashi muje kirakani wata 'yar unguwa, cike da jin dad'i zarah tace dagaske dear.
Murmushi yayi tare da d'aga kai.
Fad'awa tayi jikinsa tarungumesa tace nagode sosai dear wlh daman ina ta so infita inga gari dan tunda mukazo babu inda naje.
Dariya yarima yayi tare da janyeta daga jikinsa yace baby kibi ahankali kar kiji ma babyna ciwo.
Itama dariyar tayi tace ni na isa inji masa ciwo ai da sai na amsa query wajen dadynsa tak'arashe maganar tare da mik'ewa taje bedroom tacanza kaya, Cikin atamfa tafito d'inki riga da skirt sannan tayafa veil tayi gwanin kyau.
Koda tafito ido yarima yazuba mata, matsowa tayi tahura masa ido kad'an, ajiyar zuciya yasafke sannan yace koma kisanyo hijab.
Turo baki tayi tace kaduba fa babban gyalene a jikina,
Mik'ewa yayi tare da d'aukan key d'in motarsa yace tunda baki shirya fitaba ni na wuce.
Cikin sauri tarik'o hannunsa ahankali tace dan Allah kayi hak'uri toh bari insanyo.
Kumatunta yaja yace muje hakan kar inja saboda turo bakin nan yata6o k'asa, duka zarah takai masa cikin wasa nan yagoce yana dariya yace kisameni a waje, yana fad'in haka yawuce yafita.
Zarah saida tabiya tashaida ma jamila zasu fita nan tayi mata adawo lafiya sannan tazo tatarar da yarima cikin motarsa zaune yana jiranta, tunda tafito yatsareta da ido har tabud'e motar tashigo sannan yajasu batare da yayi maganaba.
Gugu yakeyi sosai da motar zarah ko titi tazuba ma ido tana kallon tsarin garin cike da burgewa, gaban wani babban Boutique yayi parking daga sama zarah taga ansa symbol d'in baby's paradise, muryar yarima taji yace bismillah madam.
Murmushin jin dad'i zarah tayi sannan tabud'e tafito, tare suka jera suka shiga ciki yanayin tsarin wajen ya burgeta sosai bin ko'ina da kallo take duk kayane masu kyau da tsada ahaka har suka haura saman step nan kuma taga kayan jarirai da na k'ananun yara, kallon yarima tayi tana shirin tambayarsa nan yasakarmata murmushi yace kiza6ar ma babynmu kaya.
Zaro ido zarah tayi tace babyn da baizo duniyaba bamusan ko namiji bane ko mace.
Murmushi yayi a karo nabiyu sannan yace kar kidamu baby duk wanda Allah yabamu munaso kuma in munsiya zamu iya ajewa ko saboda gaba.
Murmushi tayi cike da gamsuwa da maganarsa tace hakane dear, nan tafara d'iban over roll saida tad'ibi kusan kala goma sannan tad'auki kayan baby gurl kala biyar na baby boy kala biyar.
kallon yarima tayi da yazuba mata ido tace nagama, janye idanunsa yayi batare da yayi maganaba nan yacigaba da d'iban kaya duk wanda yayi masa d'auka yake saida yahad'a kusan kala talatin, trolly guda yacika da kayan baby's, zarah ko baki tasaki tana kallonsa har yagama sannan suka dawo k'asa itama yasata tad'ibi nata kayan sannan sukaje wajen payment yabiya su kud'insu nan aka kaimasa har cikin motarsa sannan suka shiga yatada suka tafi.
Yawo yayi da ita sosai yanuna mata wajaje dadama sunje pack da malls iri-iri, sayayya yayi mata sosai tun daga kayan tand'e-tand'e zuwa na amfani dan ko turaruka masu tsada yasiya mata, sai gab da magrib sannan suka dawo gida agajiye.
Bayan sallar isha'i kwance suke saman gadonsu zarah tana rungume a jikinsa shikuma yana dannar wayarsa, ahankali zarah tad'ago takallesa, yanayin yadda take kallonsa yasa yagane magana takesonyi dan haka ya aje wayar gefe sannan yace ina saurarenki dan wannan bakin naki nasan akwai magana a cikinsa.
Murmushi tayi tare da gyara kwanciyarta sannan tace tabbas hakane my heartbeat taimako da alfarma nakeso kayimin.
zubamata ido yayi batare da yayi maganaba, zarah janye idanunta tayi daga kallonsa sannan tace dan Allah kataimaka kakira min su mama mugaisa kuma kaga k'ashen watannan za'ayi bikkin Aysha.
Murmushi yarima yayi yace ai muna waya da su suna ma cewa ingaisheki bana fad'amikine saboda gudun rigimarki sannan maganar bikki kuma saidai kiyi hak'uri bazan iya barinki kijeba kuma na fad'ama su mama mun d'anyi tafiya, suma sunsan yanzu kinyi nauyi, dan haka kibari idan Allah ya safkeki lafiya sai muje kigansu.
Mamakine da bak'in ciki suka cika zarah tamarasa abinda zatace masa daga k'arshe zame jikinta tayi takwanta saman gadon tare da juya masa baya.
Shareta yarima yayi dan yasan inyace zai lallasheta a wannan lokacin rigima zatayi masa sosai, daga k'arshe mik'ewa yayi yakoma parlour yai kwanciyarsa saman kujera a nan yagama abinda zaiyi yai baccinsa.
Zarah ma saida tasha kukanta sannan bacci yai awon gaba da ita, cikin dare ko da tafarka talaluba taji babu yarima nan tatashi taduba bata gansaba dan haka tadawo parlour, ganinsa tayi kwance saman kujera yana ta baccinsa.
Zuwa tayi tazauna k'asa gefen kujerar nan tad'aura kanta saman kujerar ahaka tacigaba da baccinta.
Juyin da yarima zaiyi nan yaji abu ya takuresa, yana bud'e idanunsa da mamaki yake kallon zarah da take bacci a takure, dafe kansa yayi tare da furta oh zarah, sannan yamik'e yad'auketa yanufi bedroom da ita, yana kwantar da ita saman gado tana bud'e ido, daga gefenta yarima yakwanta yace kedai kinason wahalar da kanki menene nakwanciya a chan.
Kanta tad'aura saman k'irjinsa tace toh ai kaine kak'i kwanciya kusa da ni bayan ka sabamin ban iya bacci sai tare da kai, kuma fushi kake da ni,
Shafa kanta yayi yace ni ba fushi nake da keba zarah kawai na d'an baki wajene kihuta.
marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace toh kadaina guje min dan Allah kayi hak'uri na daina.
murmushi yarima yayi yace shikenan zarah nadaina yanzu dai kiyi bacci sai dasafe.
k'ara shigewa tayi jikinsa tare da cewa Allah yakaimu my heartbeat.
Tura kansa yayi cikin gashin kanta yana shak'ar k'amshinsa inda hannunsa yake shafar bayanta da shi ahaka bacci mai dad'i yai awon gaba da su.
_Comment_
*nd*
_Share_
0 comments:
Post a Comment