Da sauri ta dau wayar ganin sunan Adam, kafin ta dauka ta katse, hakan yasa tasan flashing ne.
kiransa tai tace 鈥渒a nemo inda yake?鈥�
Afreey banda katin da zan kirashi.
Haushi ya kamata ta kashe wayar katin 1k ta tura mai Adam murna harda tsale, nan ya kira Khalid kai tsaye.
Khalid na kokarin shiga shagon wayar Adam ta shigo, dagawa yai dan dama yana nemanshi shima.
Adam yace 鈥淜halid? Ina ka shiga ne? Inata nemanka?鈥�
鈥淵aushe kake da lokaci akwai inda ya kamata kaje.鈥�
Khalid ya fada ki tsaye, Adam yai dariya yace 鈥淜waro kai matsala ta dakai kenan komai naka serious, kana ina ne yanzu? Danbatta?鈥�
鈥淣o ina kano nayi aure kwana biyu baya.鈥�
Aure?
Adam yai tambayar cikin tsananin tashin hankali, shikenan Afreey ba shi ba samu daga gareta, hankali a tashe yace 鈥渒ai uban me ya kaika aure bayan kasan da wacce ke jiranka.鈥�
Baiyi mamaki ba dan ya saba da shirman Adam yace 鈥淪orry Abba.鈥�
Adam ya gane magana ya makamai yace 鈥淜halid Afreey kila sai ta kasheni intaji.鈥�
鈥淵aushe kake da time?鈥�
Ina zamu? Gun Amarya?
A鈥檃 ka je Naibawa ka nemi yafiyarsu.
Yanayinsa ne ya canza yace 鈥渋na ka tare? Ina san zuwa ziyara.鈥�
Ka tabbatar?
鈥淢enene? Bakasan nunata?鈥�
鈥淎kan me zanyi hakan? Indai kai ka shirya ganinta to.鈥�
Adam yace 鈥淎i dole na nemi ganin matar kwaro.鈥�
Khalid yace 鈥渒a samu kaje in har kanasan kwanciyar hankalinka da cigaban rayuwarka.鈥�
鈥淣aji zan duba.鈥�
鈥淏ye inada abinyi.鈥�
Ya fada tare da kashe wayar.
Shiru Adam yai yana tunanin yanda zasu kare in Afreey taji lalai akwai tashin hankali, in kuma bai fada mataba ba shi ba neman d鈥檃n abu daga gareta.
*****
Sai magrib ya dawo, yana dawowa ya ga ba kowa a falan, kitchen ya wuce ya ajiye ledar kayan miya da nama da kuma lemon fata daya siyod鈥檃ki ya tura, tana zaune tana rubutu a takarda, tana ganin an bude kofar ta kalleshi, ganin yanda ya hade fuska yasa ta mike tace 鈥淪annu da zuwa.鈥� Yanda tai maganar kamar an sa mata goruba a baki ne ya dan bashi dariya sai dai baiyi ta ba yace 鈥測auwa鈥�
Kinyi abincin dare?
鈥淣a tsaya abune in mun dawo nayi.鈥�
Kin tsaya abu?
Eh, kaga, ta matso tana nunamai, dazu wata idea tazomin, me kake tunanin idan na ajiye wacce.鈥�
Ta fada tana nunamai yanda ta tsatsada abin, kallan takardar yai sannan ya jinjina kai yace 鈥渒infini sanin abin indai har kikaga hakan yafi to kiyi amfani dashi.鈥�
Muje?
Ina?
Kace inka dawo zamu.
Alokacin dana dauka zakiyi abincin dare kenan.
Kallan mamaki tamai tace 鈥測anzun ma in mun dawo zanyi ai.鈥�
Wannan ra鈥檃yinki ne, in kin gama tuwon kafin 8 maje.
Ido ta zaro tace 鈥渢uwo a daren nan?鈥�
Kallanta yai ya tsare gida, kallansa tai tace 鈥渟ai kai magana ka hade rai, taya zanyi tuwo a daren nan?鈥�
鈥淲annan matsalarki ce ba tawa ba.鈥�
Ya fada yana neman wuceta ya shiga ciki, da sauri tasha gabanshi tace 鈥渕uje in mun dawo musai abu a hanya.鈥�
鈥淏anida ra鈥檃yin yin hakan.鈥�
Ido ta kafeshi dashi ranta a matukar bace, kalanta yai yace 鈥渕atsa.鈥�
Kin matsawa tai ta kara tare kofar da hannunta, kallanta yai yace 鈥渒inasan in nuna miki karfi?鈥�
Taya zakace nai tuwo a daren nan? Bayan kai kace zamu gidana in ka dawo?
Kalanta yai bai ce komai ba, tace 鈥渕eyasa kake min haka? Menama?鈥� Tai maganar idanunta na cikowa.
Kallanta yai yace 鈥渒insan yanda mace take a gidan mijinta? Kinsan abubuwan da wata macen take a gidan mijinta?鈥�
Su kenan? Ni kasan me yasani...........
Bakinsa yasa kan lebanta ya ciza, itakam gaba daya numfashin ta ya dauke dif?
Kallanta yai yace 鈥渒ada ki kuskura ki kara fadamin wannan kalmar, in kika sake kuma bansan me zai biyo baya ba鈥�
Yana kaiwa ya matsar da ita ya wuce, har yayi gaba yace 鈥渒i wuce kiyi abinci, na ajiye nama da kayan miya a kitchen.鈥�
Toilet ya shiga yana shiga ya furzar da wata iska.
Zainab kam da kyar ta daidaita kanta, shekarata hudu da Adam, ya akai ban taba samun kaina cikin wannan yanayin ba? Shi da yake saurayi? Nida nasan komai?
Samun kanta tai da wucewa kitchen ta daura ruwan tuwo.
Wayyo ni Zee na tuwo馃ズ
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/7, 11:27 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
"The emotion that can break your heart is sometimes"
#OneLove鉂�
*Gaisuwa yan AYUSHER FANS CLUB馃グ*
{55}
Ruwa ya kuna, jin ruwan heater din ba zafi sosai yasa yasan yau ba'a kawo wuta ba.
Wanka yai a toilet din ya fito yasa jallabiya,yasa turare spray na turarensa Lynx sannan ya fito ya nufi waje yana jin mostinta a kitchen, kokarin zuba man daya taho da shi yai ya fara duba wayar gen din.
Karar dayaji ya fito daga ciki ne ya sashi shiga ciki da gudu, kitchen ya shiga, tuwon da take tukawa ne ya zubo mata a hannu ta kone, dagowa tai ta kalleshi idanunta sun ciciko, da sauri ya karaso ya rike hannun fitilar wayarsa ya kara haskawa bayan hasken fitilar kitchen din, ganin yanda gun yai ja yasa ya jata jikin sink ya fara zuba ruwa, kwace hannunta tai sannan ta juya zata koma gun tukin tuwon.
Hannu yasa ya kara riko saman hannunta, ya dawo da ita jikin fanfo hannun ta ta shiga kwacewa, tace "sakeni" tai maganar cikin rawar murya.
Bai kulata ba ya cigaba da zuban ruwan, yana gamawa ya fara mata addu'a a gun ganin ba zuma a gidan dan yaga haka umma keyi, sai yaga inta kone sai ta shafa zuma.
Kara fizge hannunta tai ta fara kokarin komawa gun tuwon.
Kafadarta ya kamo da karfi yace "ki bari mana, so kike ta tashi?"
Wani kallo tamai hawaye suka zubo mata tace "ta tashi din, ba dai tuwo kake so ba?"
Hannu yasa ya rage gas din sosai sannan yasa hannu ya jaa ta zuwa falo, suna zuwa ta kwace hannunta tana neman komawa, kara kamota yai, kallansa tai ta ce "sakeni" tai maganar cikin wani irin rauni.
Naki
Sakeni please ta fada hawaye na gangaro mata, naki nace
Karfi ta fara sawa tana kokarin kwace kanta hakan yasa ya ja ta jikinsa ya rungume, hannu tasa tana kokarin toreshi sai kuma kawai ta fashe da kuka.
Har cikin ransa yake jin kukanta, kuka take sosai hakan yasa gidan ba abinda kake ji sai kukanta da alama ta dade tana tarashi.
Sai datai mai isarta sannan ta dago ta kalleshi idanunsa sunyi jaaa sosai, tace 鈥淏azan iya zaman nan ba Allah.鈥�
Kallanta yai yace "ke yarinyace haryanzu? Shekararki nawa? Har sai yaushe zakisan aure ba wasan yara bane? Haka kikaga iyayenmu na yi?鈥�
Hawaye ne ya gangaro mata tace "haka ake auren? Tunda nazo gidan nan banda aiki me kake sani? Tun asuba in ka fita sai rana sannan kana dawowa abinci kawai kake ci ka fita sai dare, ni kadai a gida kamar mayya? Kwana biyu zuwa uku jinsa nake kamar na shekara, bazan iya ba wlh, gashi kai kullum fada bafa fadan ke ban haushi ba ni da nake yin duk abinda ka sani haushin kaina nakeji, maidani gida dan Allah, na hakura da komai ma.鈥�
Ta karasa maganar tare da kara zubo da hawaye, na tsawalla ne? Nasan bazata gyaru lokaci daya ba, na zafafa mata ne? Daga zuwa? Tambayar da zuciyrsa tamai kenan, amma ita ba yarinya bace sai yaushe zata daidaita kanta?
Dago fuskarta yai yasa hannu yana share mata kwallar.
Hannu tasa ta ture hannunsa tace "nasan ba damuwa kai dani ba ban kuma nemi hakan ba amma a kalla ka dinga........"
Bakinshi da taji cikin nata ne yasata yin shiru, lab'an bakinta ya tsotsa sannan ya kalleta, idanunta ne suka rarage girma tana kallansa cikin wani yanayi, a hankali ta bude baki zata sake magana ya kara sa bakinshi cikin nata, yanzu kam harshenta ya kamo, samun kanta tai da maida mai murtani, jin yanda yake mata salo ne yasa taji kafafunta na neman kasa daukanta, ganin yanda tad'an murguda kafa kad'an ne yasa ya dan turata jikin kujera, har a lokacin bakinsa na cikin nata suna sumbatar juna cikin wani yanayi yoo abinka da me aikin karfi balle an kai lokacin ba a d鈥檃na ba馃檴
A hankali ya dago ta ya bude idanunsa da sukai jaaa, itama idanunta ta bude a hankali tana kallansa, a hankali cikin magana mai kamar ta rad'a muryarsa a dan daushashe yace "bakyasan na dinga barinki ke kadai?" Yai tambayar yana kokarin ce mata zan yi kokarin ganin na baki lokaci na.
kallansa tai kawai sai jiyai tace "Ka dauko mana gen din........"
Duk da yasan abinda ke ranta kenan amma a wannan yanayi da yake kokarin fitarda hakkinsa bai kawo zaiji haka ba.
Kallanta yai yace "shine matsalarki kadai?"Yai tambayar cikin wani yanayi da duk wanda yaji zai san yayitane ta rashin jin dadi kalamanta.
Eh ta fad'a kai tsaye.
Wani murmushin takaici yai sannan ya daga ta yace "kiyi aiki har illa masha Allah."
Ya juya ya fita ya koma waje? da kallo ta bishi dan ya tado mata da sha'awar data manta da ita, me ya sameshi? Ko dayake shi me zai saneshi kullum ransa dama a bace yake.
Khalid kam a waje zuciyarshi takai matuka gun baci, hada gen din yai ya sa socket din ya tada, tana jin karar gen ta fito waje cikin jin dadi, ganin wuta ta bayyana yasata kallansa cikin jin dadi matuka.
Ko kallanta baiba ya wuce ciki, biyoshi tai tare da rufe kofa, tace "ashe ka siyo?"
Bai tanka taba ya wuce dakin.
Ganin yanda ya shiga yasa ta juya kitchen, da kyar ta kwashe tuwon saboda hannunta daga ta sashi gun zafi sai taji gun na zafi.
Haka taita duba kitchen din ganin kubewa bushashiya yasa ta kada ta kawo falo.
Daki ta shiga yayi sallar isha'i ya hau kan gado rigingine, ya riga ya taso da abinda bazai iya maidashi ba, na kai ma abincin, ta fada tana saurin matsawa gun laptop tana kokarin zama, ganin yaki motsawa yasa ta matso tace "na kai"
Ta fada tana dan tabashi dan ta dauka ko bacci yake.
Ganin bai motsa ba yasa a ranta tace 鈥測a gaji ne?鈥�
Juyawa tai har zata xauna sai kuma ta kalleshi ganin alamar bacci yake yasa ta cire kaya ta wuce toilet, dan taji duk kanshi abin girki takeyi.
Wanka tai ta daura zani tare da rufa mayafi a saman kanta, bude kofar tai ganin haryanzu yana nan a yanda yake yasa ta fito.
Taku biyu ya dago ganin yana bukatar fita waje, kallanta yai, itama ta kalleshi, sam ta manta yanayin da take tace 鈥渒a tashi?鈥�
Wani abu ya hadiya, yana kallanta, ganin yanda idanunsa sukai ne yasa tace 鈥渂akajin dadi ne? Ko gajiyaya?鈥�
Baisan tanka ta dan kalamanta na d鈥檃zu ba karamin bata mai rai sukai ba, neman dauke idanunsa yai daga kanta.
Mikewa yai rai a bace yana kokarin barin daki, hannu tasa ta riko hannunsa ba tare da tayi shawara da zuciyar ta ba, tace 鈥渂akajin dadi ne?鈥�
Kallanta yai kawai ya kwace hannunsa ta dauka fita zai kawai taga an kashe wutar dakin.
Hannu yasa bayan ya dawo ya jawo nata hannun, a hankali ya karasa da ita kan gado yana jin wani abu na kara taso mai.
Mikewa tai kafin tai wani yunkuri ya maidata, Kh.......
Jin bakinsa cikin nata ne yasata yin shiru, wani irin salo yake da shi kansa baisan ya sani ba, a hankali ya kai bakinsa kan wuyanta, wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki wanda tunda tazo duniya bata taba ji ba, hannu yasa a kan zaninta, cikin wani yanayi na rashin karfi ta sa hannu saman hannunsa, idanunta a lumshe.
Hannu yasa ya ture hanun nata ya zare mahafin xanin, sam Khalid ya gama fita hayyacinsa, balle su Zainab wacce aka tsinci kai a wata duniyar da ba鈥檃 taba zata ba, bakinsa yakai...........nai fito a guji, ai takalmi nama sai daga baya na dawo na dauka.
********
Sai da ya kammala sannan nutsuwa ta zo mai, a hankali ya mirgina tare da lumshe idanunsa, Zainab kam bata taba kawo wannan yanayi ba sai dai gaba daya kwakwalwarta ta tafi dan ta manta meya faru a dan lokacin nan, bata san a wani yanayin ta tsinci kanta ba, shekararta 4 da Adam ya akai take jin kamar yau ta fara?
Dagowa yai ya kalleta, ganin idanunta a kansa yasa suka hada ido, da sauri ta dauke nata idon, Khalid duk da hankalinsa ya kwanta amma haushin rashin hakurinsa yake, yaso ya barta da aikinta data aura.
Mikewa yai ya shiga toilet, ya kara yin wani wankan, yana fitowa ya zubama inda take ido, juyowa tai jin motsin ya fito kuma taji shiru, ganin yana kallanta, yasa itama ta zuba mai nata idan, tana san sanin tunani me yake?
Dan hasken dake fitowa daga toilet ne yake dan haske dakin kadan, ganin yaki dauke idanunsa yasa tace 鈥渁kwai ruwan zafin?鈥�
鈥淜adan鈥� ya fada tare da wucewa jikin wardrobe, mikewa tai bayan ta gyara zaninta sannan ta fara kokarin saukowa daga kan gado, ta sako kafa daya zata sako dayan tai baya da sauri ya rikota, mikar da ita yai, kallansa ta sakeyi a hankali sannan ta juya.
Hartaje bakin toilet ta juyo ta kalleshi, meya sameshi? Ta tabbatar da dane sai yayi magana, kunya yakeji? Abinka da saurayi tai maganar a ranta gana wanka.
Shiru tai tana tunanin abinda ya faru a d鈥檃n lokacin nan.
Murmushi tai ita kadai sannan ta karasa ta fito.
Ganin baya dakin yasa ta fito falo, a kwance ta ganshi baiko ci abincin ba, kuma da alama yayi bacci.
Kallansa tai cikin mamaki, kusa dashi ta matso tace 鈥淎bincin fa?鈥� Ta tabashi tana tambayarsa.
鈥淣aci dumame, banaji zan iya cin wani abu ynzu.鈥�
Ido ta zubamai, danta a bace wato ya sata tai abinci sannan yace 鈥渂azaici ba?鈥�
A kufule tai ciki, yanajin rufe kofarta, ido ya rufe.
Tana aiki tana masifa haushi ma ya isheta ta rufe laptop din, fitowa tai waje ta shiga duba yanda ake kashe gen din tana kashewa ta wuce ciki kallansa tai a falo a kwance cikin jin haushi tace 鈥渋nyasan a falo zai kwanta ai ya dauko bargo da pillow.鈥�
Ta wuce ciki harta kwanta taji ta kasa bacci ta dauko ta fito dashi, kusa dashi taje ta samai bargon ta ajiye pillow din ta juya.
Hartai bacci ranta a bace yake.
*******
Ina kudin da Rahinatu tace ta aikon dashi jiya? Naira hamsin?
Goggo ta kalleta tace 鈥淗anne wai dan Allah ni ba yyar mijinki bace zaki sani a gaba da fad鈥檃? Akan ma naira Hamsin?鈥�
Yo ko shi mai gidan ne yacimin hamsin ai naji dalili bare ke kece kika min sirfen? Billahi lazi sai kin biyani hamsin dita.
Goggo tace 鈥渮an baki hamsin sau hudu ma amma ki bari Adam yazo.鈥�
Kan bala鈥檌 to wlh yau ko za鈥檃 mutu sai kin biyan.
Akan tsinanita hamsin kike min masifa?
Tsinaniya? Inyi sirfen in sameta kice tsinaniya?
Yo me akai akai hamsin banda talauci?
Ran Hanne ya kara baci tace 鈥渢o wlh sai kin biyani in ba haka ba kuma wlh daga yau har kwana biyu bake bacin abinci a gidan nan.鈥�
Sadiya zo ki ban Hamsin naba matarnan.
Sadiya dake sirfe waken alalen siyarwa tace 鈥渂adai nawa ba kam wlh, kina gani abin aurena nake hadawa.鈥�
Ta juya tana aikinta.
Hanne tace 鈥渢o wlh ki shirya dakon yunwa.鈥�
Yo a wani abincin? Dumamen tuwo ko saban tuwo?
Koma menene.....
Ta fada tai ciki.
********
Sau uku kenan tana kiran Adam bai dauka ba, kwafa tai tace 鈥渮aka san nika wulakanta wlh.鈥�
Adam kam daga yaga kiran Afreey sai yaji hanjin cikinsa na kadawa, gaba daya ya rasa yanda zaiyi, dan ma y saida katin dari takwas a wanda ta turomai aka bashi dari bakwau yaci indomi, da yau kam tsoro da yunwa sai sun halakashi.
Ya zaiyi ya sanar da Afreey wannan labarin?
**********
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
**********
[1/7, 11:27 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
鈥淭he best and most beautiful things in the world cannot be seen or even touched. They must be felt with the heart鈥�
Helen Keller
{56}
Wajen karfe biyu ya bude idanunsa, jin ba karar gen ga kuma haske kwan wuta ta waje yasa yasan nepa ne, kafafunsa ya sauko dasu daga kan kujerar, gaba daya jikinsa ciwo yake yi.
Daki ya nufa a hankli ya bude dakin, tare da dan haska wayarsa, tana kwance tana bacci, murmushi ne na wani yanayi da yake tausayin kanshi da ita ya bayyana a fuskarsa kafin ya nufi cikin dakin, a hankali ya isa kusa da ita, ya zauna a ta gefenta tare da zubawa fuskarta ido, bacci take kadai ko tana mafarki? Murmushi yai tare da cewa mafarki tana aiki? Yanayin fuskarsa ne ya canza yadan sukunyo yana kallanta cikin wani yanayi da shi kadai yasan me zuciyarsa ke ciki, a hankali ya kai bakinsa kan goshinta ya sumbata tare da dan lumshe idanunsa, sannan ya kalleta ya yace 鈥渨hat should i do with you?鈥� Yai maganar cikin wani irin sanyi murya mai kamar ta rad鈥檃 mai ratsa zuciya.
Mikewa yai ya gyara mata bargon sannan yai alwala ya kunna heater ya fito daga dakin, nafiloli yai yasa pillow yai bacci a nan kasan.
Yau kam ya d鈥檃n makara dan sai biyar da rabi ma ya farka daga bacci, da sauri ya mike ya shiga toilet din dake falo yai wanka sannan ya nufi daki, tana kwance tana bacci har ya sa kaya, d鈥檃n motsi tai bai kalleta ba ya cigaba da shiryawarsa, idanunta ta bude ganin hasken fitila.
Yana gaban madubi yana sa turare, wayarta ta jawo ta duba agoggo sannan tace 鈥測auma da wuri zaka fita?鈥�
鈥淕aisuwar ki kenan?鈥� Yai tambayar tare da kallanta yana sa agoggo, tace 鈥渨ai wani irin aiki ne tun safe bai karewa? Kuma irin wannan aikin karfin Allah ni nasan ba wani abu ake baku ba.鈥�
Juyawa yai bai tanka mata ba ya sa mabalen rigarsa sannan ya dau wayarsa, kallanta yai yace 鈥渂a saikinyi abinci saboda ni ba, kiyi yanda kikeso.鈥�
Ya juya ya fita, shiru tai, a ranta tace 鈥渢ausayi na yake?鈥�
Ba tare da wani dogon nazari ba tai sallah sannan ta kwanta, dan baccin awa biyu tai sannan ta mike cikin jin dadin bazatai abinci ba ta gyara dakin tai wanka ta had鈥檕 tea ta dauko dubulan tana ci tana aikinta, charge na karewa ta kuna gen ta cigaba da hidimarta, yau ta shirya yin website na gidan Tv dinta da logi, shiyasa ta dukufa sosai a falo tana ta hidima, sai karfe hudu taji gen ya mutu, fitowa waje tai tana dubawa, ganin ba mai yasa ta juye ragowar na jarkar wanda bashi da yawa ta kara kunnawa ta koma ciki.
Tana zama harta dau mouse sai taji yunwa ta kamata, ta mike tai kitchen, ganin tuwon jiya yasa tai shiru ita kadai a kitchen tana tuno abubuwan da suka faru a daren jiya, samun kanta tai da rufe fuskarta tana murmushi, dan ta tabbatar kila kunyarta yake shi yasa ya kasa dawowa cin abinci.
Shiru tai kafin tace 鈥渢o me zaici?鈥� Ginin kitchen ta kalla haka kawai taji zuciyarta duk ba dadi, jitai bata ma jin cin abincin hakan yasa ta fito daga kitchen din, zama tai a falo, duk yanda taso yanzu tai aikin ta kasa, daga ta tuno yana ta gini sai taji ranta ya baci.
Rufewa tai sannan ta kunna tv bayan tai sallah, abinda ta ganine yasata mikewa ta zauna sosai, ganin masu aikin gini tai ana lafta musu kasa suna dauka, wasu na shafa sumunti, wasu na kankare kasa suna ta faman gyara, jitai gaba daya hankalinta ya tashi abinda Khalid yakeyi kenan?
Waya ta dauko da sauri ta dubo sunansa tana neman kiranshi kawai wayar Aunty ta shigo mata, idanu ta rufe sannan ta dauka.
Aunty daga can tace 鈥淶ainab sam baki da kirki, wlh badan ke 鈥榶ar yaya bace ko kallan inda kike bazan karayi ba a rayuwata.鈥�
Zainab tace 鈥渕e kuma nai?鈥�
Tace 鈥渁i ko kudin mahaifinki ne ya turo na miki kayan daki da jere da kuma kayan gara a kalla kya kirani kice sunyi kyau ko basuyi kyau ba, in har bazaki kirani akan gajiyarmu ba.鈥�
Shiru tai Aunty tace 鈥渟hikenan, Allah ya bada zaman lfy.鈥�
鈥淏a haka bane banyi tunanin kiran bane, amma komai yayi kyau.鈥�
Kai ta daga kawai tace 鈥渟hikenan sai anjima鈥� kafin Zainab tai wani abu ta kashe wayar, shiru tai, tana mamakin wannan abu kawai dan bata kira ba sai taji haushi?
******
Karfe biyar da rabi ya dawo, dan ya ajiye aikin zaman shagon, yanzu daga gun gini garaje yake wucewa, yayi sa鈥檃 dama store ne ba shi kadai bane ke aiki agun.
Tsayawa yai ya siyo kayan miya, bread da kwai sannan ya taho gida.
Tana zaune a falo yunwa ta isheta yasa ta dumama tuwon tana ci, kallanshi tai bayan ta amsa sallama, tace 鈥測au da wuri haka?鈥�
Harzai mata magana kawai ya fasa ya wuce ciki, kitchen yakai kayan ya ajiye sannan ya wuce daki, da kallo ta bishi tana tunanin gajiyar aiki ce hala? Karar rashin mai gen din ya fara, kafin ya mutu, dan ajiyar zuciya tai bayan ta gama cin abincin ta wuce kitchen ta wanke hannu ta ajiye kwanan ta duba abinda ya siyo sannan tai daki ta sanar mai ba mai.
Jin karar ruwa yasa ta fahimci wanka yake, zama tai a bakin gado, fitowarsa ne yasa ta kalleshi, tana ganin sa daure da towel ga gaba daya saman jikinsa a waje, Khalid irin mazan nan ne masu fadi sannan jikinshi a dan murde yake, wankan dayai yasa gashin kirjinsa sun kwanta, da sauri ta mike ta juya bayanta gabanta na faduwa.
Baiko bi ta kanta ba ya goge jikinsa da karamin towel din da ke hannunsa sannan ya sa jallabiya ya sa turare.
Kokarin fita daga dakin yake tace 鈥渘aga ka dawo da wuri.鈥�
鈥淓h da wani abin ne?鈥�
Dan takowa inda yake tai tace 鈥渮akaci tuwon?鈥�
Kallanta yai yace 鈥淎鈥檃 indai kinci shikenan.鈥�
Ya fada tare da fitowa daga dakin, wannan wannan ta fada tana nuna kofa kafin ta daure fuska ta fito.
Yana zaune a falo taje gefe ta zauna ganin wayarsa yake dadanawa yasa ta zauna a kasa inda laptop dinta yake, a kan centre table ta fara duba aikinta, ganin shirun yayi yawa yasa tace 鈥渒o zaka kaini gidan?鈥�
鈥淚nkin shirya muje na kaiki.鈥� Ya amsa hankalinsa na kan waya, shiru tai tana tunanin me yake a wayar da ko kallanta baiyi ba?
Mikewa tai ta shiga daki, ta gyara fuskarta ta dauko mayafi da key ta fito.
Haushi ne ya kara kamata ganin har ta isa kusa dashi baiko kalleta ba, sai datace 鈥渕uje?鈥�
Kallanta yai sannan ya mike yai waje.
Da harara ta bishi sannan tabi bayanshi suka isa gaban mota.
Key ta mikamai ya amsa ya shiga itama ta zagaya ta shiga, shiru tai tana kallanshi samun kanta tai da tuno abubuwan da suka faru a baya a cikin motar, wani murmushi ne ya bayyana a fuskarta, ta kalleshi tana tuno sanda zai tambayeta kwatancen gidanta sai wani left da right yake ce mata, ya wani ce mata excuse me? In zai mata magana, Murmushi tai ita kadai, har suka isa gidan bai tanka ba.
Bala na ganin motarta ya bude cikin hanzari, suna shiga ya taho da gudu yana kwasar gaisuwa.
Bayan sun gaisa ne tai hanyar ciki, ganin Khalid tai a ciki mota bashi ko da alamar fitowa, dawowa tai tace 鈥淢uje mana.鈥�
鈥淣o jeki fito.鈥�
Ido ta kuramai cikin kuluwa yau tunda ya tashi ko maganar arziki bai mata ba, abinda ya faru daren jiya fa? A banza yake? Kenan duk yanda ya nunamin karya ne? Abinda kawai take rayawa a ranta kenan, yawon bakinta ta had鈥檌ya tace 鈥渁binda zan dauko nada nauyin bazan iya dauka ba.鈥�
Kallanta yai sannan ya mike, suna shiga tai ciki.
Kallan gidan yai jiyai jikinsa duk yai sanyi, ganin tafkeken falo, da gun dinning a gefe, wanda yake hade da kitchen.
Zama yai akan kujera ta wuce daki ta bar kofar dakin a bude, ganin ta kasa jawo akwatin dake saman wardrobe din ne yasa ta tura kujerar jikin madubi ta hau, ganin ta jawo amma ta kasa dagoshi ta sauko dashi yasa ta sauko ta fito falo.
Kallan Khalid tai tace 鈥渄an taimakamin.鈥�
Kallanta yai bai amsa ba kuma bashi da alamar mikewa, kallansa tace 鈥渕agana nake ma.鈥�
Tambaya ma bata iya ba, abinda zuciyarsa ta fadamai kenan yai ajiyar zuciya.
Kallanta ya sake sannan ya kara dauke kai, wani abu ne ya tokare a mokoshinta a kufule ta juya, karfi tasa ta jawo akwatin, da kyar ta shiga kokarin neman saukewa kawai taji an dageshi daga hannunta, kallan juna sukai kafin ya ajiye a kasa, kallansa take har ya ajiye ya dago tace 鈥渒asan zaka tayani meye bazaka amsamin ba?鈥�
Bai kula ta ba ya fara neman juyawa, ranta ne ya kara baci tace 鈥淜ayi nadamar aure nane?鈥�
Tsayawa yai ya juyo ya kalleta, idanunta ne suka fara cicikowa tace 鈥渁kan me yau kwata kwata kaki min maganar kirki? Abu na maka? In haka ne ka fad鈥檃min mana, ai kai ba mai ajiye magana a ransa bane.鈥�
Kallanta yai yadan yi wani mosti da bakinsa, wanda baikai murmushi ba yace 鈥渕e kikeso in ce miki? Bakya ganin na baki dama ki zauna da aikin da kika aura ne?鈥�
Me yasa taji zafin kalamansa? Bayan hakan take so? Tambayar data wa zuciyarta kenan.
Kallanta yai yace 鈥渄amar ce bakya san na baki?鈥�
Da gaske kake?
Eh, Na dauka abinda kikeso kenan?
Yai tambayar yana kallanta, murmushi tai tace 鈥渂an dauka zaka bani dama haka bane shiyasa, nagode sosai.鈥�
Kai ya daga alamar to sannan yace 鈥渒arki damu鈥� ya juya ya fita.
Shiru tai a gun meyasa bata farin ciki? Bayan abinda takeso kenan?
Fitowa tai ta nufi kitchen, zare cylinder din jiki tai sannan ta shiga fito da abubuwan abinci wanda ke ciki, yana zaune a falo harta gama.
Kallanshi tai tace 鈥渄an tayani.鈥�
Baice komai ba ya dau akwatin ya fita dashi, kallan cylinder din yai yace 鈥渄o you really need that?鈥�
Tace 鈥渆h bansan ya akai Aunty bata sa a ciki ba.鈥�
Bai ce komai ba ya dauka, kallan kayan abincin yai yace 鈥渨annan fa?鈥�
Kamar tace Mu tafi dasu sai kuma kawai jikin ta ya bata zaiji haushi, tace 鈥渢unanin ba Bala nake.鈥�
Murmushi yai ya dauka ya fito, kallan dayar motar da Dady ya sai mata tai ta kalleshi tace 鈥渕otar can.鈥�
Kallan motar yai sannan ya kalleta, kamar zata sake magana sai tace 鈥渂akomai.鈥�
Wucewa yai ya shiga motar, ta sallami Bala sannan suka fito yana ta godiya.
********
Sai da sukai dan tafiya tace 鈥渒o zaka kaini Jifatu? Akwai abinda nake san siya.鈥�
Batama san ya ake tambayar abu ba?
Baice komai ba ya wuce da ita, shiga sukai tare ta dauko mai da take shafawa da abin wanka na shower gel, suna zuwa gun biyan kudi aka buga akace 3000, tana kokarin bada katinta Khalid ya mika nashi, nan aka zara wayarsa ce tai kara akan alert da akai, yana dubawa yaga 1000 ne kadai ya rage a ciki, ajiye wayar yai sannan suka fito.
Haka kawai ta ke jin abin banbarakwai, tunda take bata taba siyan abu an biya mata ba, sai dai ta biya duk abinda ta siya ta kuma biya na wanda sukaje tare, ita ko da Dady ba yawo suke tare ba bale har suje siyayya.鈥�
Suna kokarin shiga mota yaji ance 鈥淜waro?鈥�
Juyowa yai ya kalleta, Zainab wacce taji muryr mace itama ta juya.
Kallan kallo sukai, yanayin fuskar Zainab ne ya canza tana ma budurwar wani irin kallo.
Ta kusa da ita ta wuce taje kusa da Khalid tace 鈥淎she zan ganeka?鈥�
Khalid ne ya saki murmushi mai sanyi yace 鈥淪afeenah? I never expect to see you here.鈥�
Dariya tai cikin jin dadi tai ajiyar zuciya tace 鈥渋nalilahi shekaru nawa?鈥�
Shima dariya yai yace 鈥渢un a skul.鈥�
Tace 鈥渨a?鈥� Tai tambayar tana nuna Zainab da kanta.
My wife, ya fada yana murmushi.
Idanunta zaro tace 鈥渕e?鈥�
Fuska ya hade yace 鈥渂an isa yi bane?鈥�
Dariya tasa tace 鈥渂awai baka isa bane, Afreey ta sani?鈥�
Fuska ya hade yace 鈥淶aki fara ko?鈥�
Tace 鈥渟hekaranjiya muka hadu da ita kuma tana ta zancenka kaga ina zan kawo wannan yanayin?鈥�
Zainab dake tsaye ta ciga ta gama batsewa ta bude mota ta shiga ta zauna tana harararsu, ganin Khalid ma dariya yasa ta karajin wani irin mugun bacin rai.
Safeena ce tace 鈥渒uma kun dace amma kamar na santa.鈥�
Murmushi yai yace 鈥渘a san wannan basai kin fada ba.鈥�
鈥淥h ni Kwaro ban taba tunanin zakaso wata har kai aure ba, na dauka karatu zaka aura.鈥�
Murmushi yai yace 鈥渒efa?鈥�
Horn din motar ne yasa ta kasa magana, kallanta yai yace 鈥淢adam ta gaji da jira.鈥�
Oh ni, yau Afreey tazo taga abu, wato Madam ta gaji? Oh ni wannan abu sai kara ban mamaki yake, oh ni Kwaro.
Dariya Khalid yai yace 鈥渂ye.鈥�
Ya karasa tare da shiga motar, Zainab ya kalla wacce ta cika ta batse, ta murtuke fuska tamau.
Yace 鈥渕u tafi?鈥�
Wani banzan kallo tamai ta juya kai, shima ya ja suka tafi, tsayawa yai a gun 鈥榶an cuwa cuwa yaduba wallet dinsa ganin 300 yasa yasai musu mai suka wuce gida.
Suna isa ta fito daga motar rai a bace tai ciki, tsayawa yai ya zuba mai sannan ya wuce ciki, yana jin cikinsa na karar yunwa, sai dai yasa a ransa dole koma menene ya jure.
Kitchen ya wuce ya gutsiri bread din daya siyo ya dau ruwa ya fito falo yaci ya sha ruwa.
*******
Safeena kam suna rabuwa ta shiga kiran kawayensu na skul tana fada musu Khalid yayi aure, kowa Afreey ya shiga hangowa suna tunanin yanda zasu fada mata.
*******
Nusaiba bazaki tashi kici abinci ba? Wai meke damunki ne?
Kallan Basma tai tace 鈥渘i wlh Mumy Uncle nakeso鈥�
Basma tace 鈥渂anace karki kara maganar nan ba? So kike ran Dadynki ya baci?鈥�
Hawayenta ta share tace 鈥渢o ni Allah bazan iya hakura ba.鈥�
Idanun Basma ne suka ciko, ta tuno abinda tama Mahaifiyar Zainab da ita kanta Zainab daga koyarwa, share kwallarta tai tace 鈥渢o sai dai kuwa ki mutu wlh na sake jin maganar nan dukan tsiya zan miki a dakin nan.鈥�
Nusaiba ce ta kalleta tace 鈥淒ady zan fadawa tun.......鈥�
Marin da Basma ta wanka mata ne yasata yin shiru, in sake jin maganar banzan nan.
Ta juya ta fita, ba shakka alhakin Ummy dashi zan mutu, tunda ban nemi yafiyarta ba, banama jin tasan nice na kwace mata mijin harta rasu.
Hawayenta ta share cikin wani yanayi......
*********
Yau kam tana tashi taga baya gida, samun kanta tai da jin haushi, kwanciya tai ko dakin ta ki fitowa.
Lalai ma Khalid din nan? Ta fada cikin jin haushi.
Bargo taja ta rufe kanta dashi ta dauko wayarta, gun sako ta bude, me zata ce mai?
Haushi ne ya kamata ta ajiye wayar, ta kara jan bargo tare da yin kwafa.
********
Afreey me kike gani? Ai nasan Babanki dan Albarka ne ba shakka zai dubemu.
Kallan Director Kabir tai tace 鈥渂adai da gaske kake bako?鈥�
鈥淗aba Afreey kema kinsan ba wasa nake ba, in babanki ya taimakemu wannan karan ba abinda bazan miki ba.鈥�
Wata dariya tai tace 鈥渘a taba neman abu a gunka? Duk duniya ina da komai danake so abu daya ne ya gagaren wanda shima dole ko da menene sai na mallakeshi, banaji ya shafeka bare ka taimaken.
Ran Director Kabir ne ya baci amma ya ya iya? Daurewa yai yace 鈥渒i taimaka ko baki to ya sa a taimakemu dan Allah.鈥�
Zan duba, abinda tace kenan ta fito, tare da hararan kofarsa, wayarta ta dako ta kara kiran Adam, amma sai Kamalu ne ya daga yace mata wai bashi da lafiya.
Kwafa tai ta kashe wayar dole ta je inda yake taji uban me yake boye mata.
Nace Um um dai da dai kin hakura馃お
******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/7, 11:27 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
{57}
Yau kam sam takaici ma ya hanata yin aiki dan in ta tuna wai ya bata dama tai aikinta sai taji ranta ya kara baci, yanzu ma a karo na ba adadi ta mike tsaye a kufule tace "da cewa nai bansan aikina? Kasan haka meyasa ka....." sai kuma ta kasa karasawa ta zauna akan gado cikin takaici, tun dazu take jin yunwa amma bakin ciki ya hanata ma cin abincin sannan dama ita mace ce mai wahalar da cikinta, tana jin yunwa amma in abu na gabanta to ajiyeshi take.
Mikewa tai ganin azahar har tayi tai wanka ta sa turarukanta masu kamshi ta shafa hoda kanta ba dankwali ta nufi kitchen, bread din da aka gutsira ta kalla ta duba taga ba alamar anyi amfani da cup, kenan bread kawai yaci ko me?
Dankali ta fere ta fara soyawa shiru tai tana tunani, are you okay? Abinda kunuwanta suka jiyo mata kenan, tai shiru tana tunani ai Khalid tun kafin ma su fara wata doguwar magana in har tana cikin wani yanayi yake tambayarta hakan, wanda har take mamakin yanda Adam baya gane halin da take ciki amma shi yake ganewa, kenan ya san abin nan da yake mata yana bata mata rai amma ya cigaba? Tana tunani har dankalin ya kone, haushi ne ya kamata kawai ta hada tea tasha a kitchen din, ji tai idanunta sun ciciko, maida kwallarta tai tana tunanin tunda ta taba auran Adam ta taba zama tunani da har xataji tana shirin kuka?
Fitowa tai daga kitchen din kawai ta dau wayarta ta kira Nabila, waya suka shiga yi Nabila na tsokanarta ina Yaya Ango.
Zainab cikin kuluwa tace "ina na sanmasa."
Nabila tai dariya tace "Wai yaushe a gari Aunty ake bari a gida ba ita take bari ba."
Fuska ta daure tace "karki batan rai, dan na gaji da zaman nan wlh, ga rashin wuta, ga mutum sai zafin rai."
Wata irin dariya Nabila tasa wanda tasa Zainab jin haushi tace "dariya kike?"
Nabila ta tsagaita tace "Aunty mamaki nake ban taba ji kina complain akan wani ba shiyasa"
Zainab tai tsaki tace "wannan in na fara zubo miki complain a kansa ai yasin sai muyi awa biyu a waya."
Nabila ta sake dariya tace "da alama Aunty na san Ya Khalid sosai."
Fuska Zainab ta daure tamau kamar tana ganinta tace "abinda yafi so, ce miki akai banda aikinyi?"
"Kinada aikin yi kike samun dama da lokaci na jin haushinsa?"
Zainab tace "ke kika san wannan, Nusaiba fa?"
"Hmm ni ina na san mata, sai wani hade min rai take kamar ni na kar zomon."
Shiru Zainab tai kafin tace "ke kuma uwar rashin hakuri, kiyi hakuri ki dan lalabata harta saki ranta."
Ajiyar zuciya tai kafin tace "zan gwada amma Allah ta kawon wargi zanyi gaba kin sani."
Na sani kiyi hakuri dai, haka suka danyi hira kafin ta kashe, shiru tai tana tunanin abinyi ganin tanata tunani kawai ta mike ta dauko laptop聽 dinta ta fara aiki, sai la'asar tai sallah sannan ta dafa indomie ta zauna tana ci.
Tana gamawa ko kwanan bata dauke ba ta cigaba da abinda take, sallamar Khalid ce yasa ta dago ta kalleshi tare da amsawa.
Ido ta zubamai ji take kamar ta dade bata ganshi ba, shima kallanta yake yanda tabar kanta a bude da yanda tai zaman nata har jikinsa yaji abin, murmushi tamai shima samun kansa yai da mata sannan ya shiga ciki, daki ya wuce ta bishi da kallo yau ma bashi da niyyar kulatan?
Daki ya wuce ya watsa ruwa saboda gajiyar dayai sannan ya dan zauna akan gadan yana shafa aboniki a bayansa, dan sosai bayansa ke mai zafi, ganin bai fito ba ga charge dinta ya kare yasa ta mike tai dakin.
Ganin sa sanye da wando da farar vest wanda ya daga ta sama yasa ta jawo kofar, shiru tai tana tunani kamar abu taga yanayi, me yake? A hankali tadan tura kofar tadan sa idanta.
Jitai yace "leken me kike?"
Bude kofar tai tace "a ina nai leken?"
Kallanta yai ya rufe man, jin kanshin man zafi yasa tace "me kake?"
Bakomai.
Yai maganar yana maidashi kan madubi.
Haushi ne ya kara kamata dataga yana neman barin dakin, haka ya wuce ta gabanta ranta a matukar baci ta bishi da harara.
Yana kokarin fita daga kofar ta rike rigar sa tace "nice bakasan zama guri daya dani?"
Juyowa yai ya kalleta, tace "ka bar falo ka dawo daki yanzu na shigo dakin ka fita, me kake nufi?"
Kallanta yai ya kalli hannunta data rikeshi, yace "haka kike gani?"
Tace "ba hakan bane?"
Abinda zuciyarki ta raya miki shine daidai a gareki?
Fad'amin ba hakan bane?
"Ba haka bane."
Yai maganar yana kallanta, to menene? Dama ka bani nai aiki?
Hmmm bakyaso?
Ba wai banaso ba amma at least ka dawo yanda na sanka, wannan halin daka faramin yasa ina tunanin abubuwa dayawa.
Zaiyi magana yaji ana buga kofa, kallanta yai yace "bari na duba."
Sakeshi tai zuciyarta na kara hasala, harta juya taji karar text a wayarsa, dauka tai da niyar fitomai da ita, abinda ta gani akan screen din wayar ne yasa yanayinta canzawa.
Idanunta ne suka ciciko, hankali a tashe ta bude wayr ta duba sakon dakyau, bata taba tunanin daukar wayar wani ba bare tunanin bude ta, alert ne na katin dari da aka saka suka turo balance na 900, sam ta kasa dauke idanunta daga kan screen din wayar, jikinta ne ya shiga rawa, tana maimaita 900 a ranta, idanunta ne suka ciciko hawaye suka zubo daga cikinsu ba tare da ta sani ba, jin motsinsa yasa ta ajiye wayar hankalinta a matukar tashe.
Shigowa yai yace "makocinmu ne, bamu kyauta bamu shiga ba yazo mun gaisa yace matarshi za........"
Ganin yanayinta yasa yace "menene?"
Kallansa tai, matsowa kusa da ita yai ya dago fuskarta yace "menene?"
Kwacewa tai da sauri ta shiga cikin toilet, tana shiga ta rufe, shiru yai yana kallan kofar, yana san suyi magana dan kalamanta sun sa jikinsa yin sanyi, da alama abinda yake mata ya mata tsauri ganin lokaci daya komai ya canza mata, samun kansa yai da jin haushin kansa, sai dai baisan meyasa yake hakan ba.
Ganin taki fitowa yasa ya fito falo, Zainab kam tana shiga ta tsaya a jikin kofar ta jingina bayanta gaba daya ta kasa tabbatar da abinda idanunta suka gani, tabbas zero biyu ta gani, kanta ta shiga bugawa a jikin kofar.
Har yai alwala a falo yana jiran ta fito suyi sallah baiga ta fito ba, massalaci ya fita har ya dawo bata fito ba dakin ya shiga sannan ya mike ya kalli toilet din ba alamar fitila ga duhu, buga kofar yai yace 鈥淶ainab?鈥�
Jin shiru ya sake cewa 鈥淶ainab?鈥�
Nan ma yaji shiru hannu yasa yana kokarin budewa jinshi a kulle ta ciki yasa ya shiga murdawa yana cewa 鈥淶ainab! Zainab?鈥�
Bude kofar tai da sauri ya kalleta yace 鈥渓afiya?鈥�
Yai tambayar yana duba jikinta, hannunsa tadan ture ta wuce ciki, hijab ta dauka, ta tada sallah ba tare da tace komai ba, shiru yai yana kallanta kafin ya juya ya fita, waje yaje ya kuna gen ya zauna a falo, sai dai gaba daya hankalinsa baya falan yana dakin balle dayaga har a lokacin bata kunna wutar dakin ba.
Ganin ya kasa daurewa ya mike ya nufi cikin daki, kallanta yai wanda hasken waje ya dan haska dakin, tana zaune a inda tai sallah ta sa kanta cikin kafafunta, hawaye kawai ke zubo mata ta rasa dalilinsu, gaba daya haushin kanta takeji ta ko wani bangare.
A hankali ya taka zuwa inda take ya zauna tare da sa hannu ya dago kanta, kallansa tai idanunsa na kanta yace 鈥渂akida lafiya ne?鈥� Yai maganar cikin sanyin murya.
Ummy me nakeyi? Ummy na, Ummy! Abinda zuciyarta ke fada kenan, Kuka kawai ta fashe dashi hankalin Khalid ne ya tashi, kallanta yai yace 鈥渕enene?鈥�
Baki da lafiya ne? Yai maganar cikin tsananin damuwa.
Kuka kawai take tana tuno a yanzu haka tana da kudi saman da miliyan biyu a account dinta wanda Dady ke sa mata, ga dubu dari tana da shi a cikin dakin nan na kudin gaisuwa daya kawo, tana da gida babba, tana da motoci, tana da fili me take a rayuwarta da har.........
Dagatan da yai ne yasa ta kalleshi, zaunar da ita yai a kan gado, hannayensa yasa akan fuskarta yace 鈥� menene?鈥�
A hankali ta girgiza kanta alamar ba komai
ni ne?
Kallansa tai jikinsa ne yai sanyi yace 鈥� am sorry, am really sorry鈥�
Kai ta shiga girgizawa tana hawaye, goshinsu ya hada hannayensa na kan fuskarta a hankali yace 鈥渘a sani laifi nane鈥�
tace 鈥渓aifinka name?鈥� Tai maganar hawaye na zubo mata.
鈥淣a komai鈥�
Tunowa tai da abinda tai jiya gen yini yai a kunne, taje jifatu ta kashe mai 3000, ya siyo abubuwan gida na bukata, hawaye ne ya sake zubo mata.
Hannu yasa ya share mata sannan ya jawota jikinsa ya rungume, yace 鈥測a isa haka nan, yaushe kika zama mai raki?鈥�
Dagowa tai ta kalleshu tace 鈥渂an sani ba, bansan ya akai na zama mai raki ba.鈥�
Murmushi ya mata mai sanyi a dan jawota cikin sanyi yace 鈥渒in zama mai raki but i like it.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渟hiyasa kake shareni?鈥�
Haka kika gani?
Ba hakan bane?
Dam........
Hannu tasa ta rufe bakinsa tace 鈥測a isheni ba sai ka tisa min ba.鈥�
Murmushi yai, itama tai murmushin karfin hali, cikinshi ne yai kara, kallansa tai tace 鈥渂akaci abinci ba?鈥�
In ba鈥檃 ban a gidana ba a ina za鈥檃 bani?
Shiru tai tana maimaita kalaman a ranta, indomie naci in dafa ma? Karkace nama tuwo plz.
Kin manta nace kiyi duk abinda kikaga shine daidai.
Mikewa tai ta fito dan so take ta kadaice, tana shiga kitchen tai shiru, hawayen da ta rasa dalilin zubarsu ne suke gangaro mata.
Idanunta ta rufe haka ta dafa indomie din, ta fitomai dashi falo, kallansa tai tace 鈥渒ai na ke ciwo zanyi sallah na kwanta.鈥�
Kallan mamaki ya mata, gani yai kafin yai magana harta wuce ciki.
Laptop da takardunta ya kalla, meke damunta??
Tana sallah ta kwanta, shima harya kwanta a falo ya samu kanshi da mikewa yai ciki, haryai bacci idanta biyu, tayi shiru tana tunanin rayuwa, sai wajen asuba ta samu bacci ya dauketa.
*********
Suna zaune a cikin office din taro, shugaban gidan tv din ne ya kallesu ranshi a matukar bace yace 鈥渒una san cemin haka zan cigaba da sa kudina yanzu ba riba?鈥�
Kabir yace 鈥淩anka ya dade kadan kara ha......鈥�
Desk din daya daka ne ya sashi yin shiru, kallanshi yai yace 鈥渒ana tunani kai ba dan kanina bane zan barka ka cigaba da aiki anan? Wlh kaji na fadama bazan dauki wannan asarar ba, da ka san bazaka iya ba uban waye yace ka kori Zainab?鈥�
Fuska ya hade baice komai ba, to Allah kaji na fadama ficikata bazan sa ba, ace gidan tv yanzu banda asara ba abinda nake samu? Kudin biyan ma鈥檃ikata ma neman gagarata yake, duk wadanda suka dau nauyin talluka sun ajiye, ka je ka saka mutanen dakaga dama suna shiri yanzu sam ba wanda ma yake kallan tashar to Allah bazan dauka ba kaji na fada ma, inhar naga bazan iya ba saida gidan tv din zan, yana kaiwa nan ya mike yai waje.
Da kallo suka bishi sannan suka kalli Kabir wanda ya cika fam
*******
Adam ne ya kira Goggo, tana zaune tasa dumamen tuwo a gaba ta kasa ci saboda bakin ciki wulakancin da aka mata kafin a bata dan Hanne sai data kare mata cin mutunci.
Ganin kiran Adam yasa ta dauka da sauri tace 鈥淎dam ya ya? An dace?鈥�
Yace 鈥渋na fa aka dace Goggo bayan muna cikin tashin hankali, Khalid da takeso yai aure.鈥�
Goggo hankali a tashe tace 鈥渦ban wa yace yai aure? Wannan d鈥檃 anyi an banza, garin ya ya ka bari yai aure?鈥�
Ni kya tambayen garin ya ya? Nine babansa? Ni wlh yanzu bansan me zan ce mata bane.
Ka nuna mata baka sani ba, kai maza kasa ta nemarma aiki kafin ta sani.
Cikin jin dadi yace 鈥渉aka ne Goggona, nagode鈥�
Nan ta kashe wayar tana fatan dacewa.
******
Wajen karfe 10 ta farka, mamaki ne ya kamata dataga tayi bacci dayawa haka, wayarta ta ajiye tana kokarin saukowa taji tayi ringing, d鈥檃uka tai da sauri tace 鈥淯mma鈥�
Bayan sun gaisa cikin farin ciki Umma tace 鈥渘a kira Khalid bai dauka ba dama cewa zanyi gobe zamuzo da Asiya.鈥�
Cikin tsananin murna Zainab tace 鈥淎llah ya kaimu Umma, karki manta da...鈥�
Umma ce ta katseta tana dariya tace 鈥渋na zan manta da wainar geron ki? Kina san wani abin bayan shi?鈥�
A鈥檃 Umma.
Umma tace 鈥渟ai munzo goben.鈥�
Cikin jin dadi sukai sallama.
Murmushi tai na dadi.
*******
Khalid kam a rana yana duba wayarsa yafi sau ashirin yana fatan ganin sako daga Zenith bank, duk da yasan abin na jan dan lokaci amma zuciyarshi ta kasa hakura
Haka ya hau mota ya taho gida.
********
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/9, 12:20 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
{58}
Wayarsa ya dauko a cikin mota, yasa hannu zai danna kira akan sunanta kawai yaga kiranta ya shigo, shiru yai yana kallan number murmushi bayyane akan fuskarsa, dagawa yai.
Daga can tace 鈥淯mma ta sameka?鈥�
Kai ya girgiza tare da cewa 鈥渟allamu Alaikum.鈥�
Kunyar kanta taji dan zumudi yasa ta manta, a hankali ta amsa, yace 鈥測anzu zan kirata.鈥�
Tace 鈥渙kay dama cema zatai gobe zasuzo.鈥�
Shiyasa zumudi ya sa kika kira?
Har ka gano?
Murmusbi yai yace 鈥渁kwai abinda kikeso?鈥�
Shiru tai tana tuno kudin da ke account dinsa, yanayinta ne ya canza cikin sanyi tace 鈥渁鈥檃鈥�
Ba abinda kike so?
Hmmm ta fada tare da daga kai kamar yana ganinta.
Shikenan sai na dawo.
To tace ta kashe wayar, shiru tai tana tunanin kenan in nashi da kudi ta ina zai ci abinci? Mikewa tai ta wuce kitchen, ganin ba nama yasa tai shiru, sai dai bata zafafa tunani ba ta hau yin jellof din macaroni, dan in ta tuna 00 biyu kacal sai taji idanunta na neman kawo ruwa.
Tana kitchen tana kwashe talliyar, sam bataji alamun shigowarsa ba, shikuma ganin bata falan yasa ya taho kitchen da ajiye nama da kayan miyan daya karo dan yasan dole zata bukata saboda zuwan su Umma.
Ganinta a kitchen tana kwashe abinci yasa shi yin murmushi, ajiye wa yan a hankali sannan ya karasa inda take, hannunsa yasa a ta ratsin cikinta, a tsorace ta juyo dan sam bataji motsi ba, gabanta yayi wani irin faduwa.
Tana juyowa kansu na gwaruwa da juna, wata yar kara ta saki, ya saketa kawai baisan sanda yasa dariya ba.
Zubamai ido tai yana dariya yauce rana ta farko data taba gani yana dariya haka a kusa da ita, fuska ya canza ganin yanda take kallansa.
Yace 鈥渕enene?鈥�
Harararsa tai tace 鈥渂ansan ka iya dariya haka bane.鈥�
Murmushi yai sannan ya matso ya kara kai hannunsa matsen cikinta ya zagayo dasu, wani irin yanayi ne ya ratsata, kansa ya sako ta kan kafadarta yace 鈥渕e kike?鈥�
Dan juyowa tai tana san bashi amsa sai dai ganinshi daf da ita yasa ta kasa, sumbatar bakinta yai yace 鈥渒in gama aikinki ne?鈥�
Juyawa tai ta karasa tana neman daidaita numfashinta sannan tace 鈥渋na zanyi raina yana bace?鈥�
Yar ajiyar zuciya yai yace 鈥渇adamin nikam menene baya bata miki rai?鈥�
Kallansa tai kadan tace 鈥渘i zan fadi hakan.鈥�
Murmushi yai yasa hannu ya juyo da ita sannan ya kara matsewa yace 鈥渉aka nake?鈥�
Sai na fada?
Ta tambaya tana kallansa, saketa yai sannan yace 鈥渂ari na watsa ruwa.鈥�
Juyawa yai da sauri tace 鈥渋nka fito kazo ka ci abinci.鈥�
Da sauri ya juyo ya kalleta, yace 鈥渘i kikawa?鈥�
鈥淲a ya fadama? Abinci ne nima ban ci ba.鈥�
Duk da haka samun kansa yai da kallanta sannan ya juya ya fita.
Yana fita tai ajiyar zuciya ta hau fifita da hannunta, sannan ta dan yi murmushin da bata san dalilinsa ba.
******
Wanka yai ya zauna a kan gado yana dan mike bayansa tare da daukan maganin zafi.
Zainab kam ganin baifito ba yasa ta leka daki, ganinshi yauma kamar jiya yasa ta juya, jitai yace 鈥渂akya gajiya da leke?鈥�
Kofar ta bude ta shiga tana dan kallan dakin tace 鈥渨ai ni nacema leke nake?鈥�
Kanki fa? Ya daina ciwon?
Kallansa tai sannan ta daga kai, kallanta yai shima ya mika mata man zafin dake hannunsa yace 鈥渃an you help?鈥�
Me kake?
Ta fada tana takowa inda yake, mika mata yai yace 鈥渟hafan a tsakiyar nan.鈥�
Kallan jikinsa tai da sauri tace 鈥渉annunka fa?鈥�
Baya kaiwa.
Hannu yasa ya jawota ta zauna a kusa dashi, juyawa yai ya kwanta akan gadan yana nuna mata.
Kallan bayansa tai sannan ta lakuto a hankali ta fara shafamai, yanda yake dan motsa bayan inta taba gun ne yasa ta fahimci zafi gun yake mai, idanunta ne suka canza, tsananin tausayinsa ne ya shiga ratsa sassan jikinta, cikin yanayi na tsananin tausayi tace 鈥渃iwo yake ma?鈥�
Dan juyowa yai yana daga kwance yace 鈥渒adan.鈥�
Shiru tai ta kasa ci gaba da shafawa sai idanunta data rufe, hangoshi take yana aiki tukuro a idanunta, jin bata shafawa yasa ya kara dan jiyo da kansa.
Ganin idanunta lumshe tana tunani yasa ya mike zaune, kusa da kunnenta ya matso yace 鈥淒o you need me that much?鈥�
Ido ta bude ta ganshi daf da ita, hannu tasa ta hankadashi kan gado tace 鈥渨annan fassarar fa?鈥�
Yace 鈥渒in tabbatar?鈥�
Da sauri ta mike tace 鈥渋n ka so ka fito.鈥�
Ta juya falo da sauri, shiru yai sannan ya kalli laptop dinta wanda da alama tadan tabata amma ba sosai ba, charge ne ya kare? Ba mai ne?
Kitchen ta shiga ta bude ledar da ya siyo nama da kayan miya, shiru tai a ranta tana tambayar wannan nawa suke? Kenan 900 din ta ragu kenan? Hankalinta ne ya kara tashi, haka ta kawo abincinsa falo ta koma kitchen dauko nata.
Kaya yasa sannan ya fito, ta ajiye mai abincin a falo, yana kokarin zama ya ga tana neman wucewa da plate dinta wanda ta zuba abinci itama.
Ina zaki?
Ya tambaya yana kallanta, kallansa tai ta kalli abincin, matsowa tai ta dau serving spoon tana neman zubamai, hannunta ya rike, kallansa tai abincinta ya ajiye a kusa dashi sannan yace 鈥渮auna.鈥�
Ba musu ta zauna tana kallanshi, yace 鈥渕e ya sameki jiya?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渘amanta?鈥�
Kin manta?
Hmmm ta fada tare da kallan gefe.
Fork dinta ya sa a plate din sannan ya kalleta.
Kallansa tai tace 鈥渂adai baka kake san kace nai ba ko?鈥�
In na fadi haka laifi ne?鈥�
Murshi tai zatai magana taga yasa fork dinsa a ciki bai ce mata komai ba.
Kallansa tai yana ci bai ce mata komai ba.
Tsayawa tai kawai tana kallanshi, ganin taki ci yasa ya kalleta yace 鈥渟un kawo wuta?鈥�
A鈥檃
鈥淢e kikai yau to?鈥�
鈥淜a damu ka sani ne?鈥�
鈥淏anaji鈥�
Haushi ya kamata ta harareshi sannan ta janye plate dinta tace 鈥渁i wannan abinci nane, kaci naka.鈥�
Kallanta yai kawai baice komai ba, harta mike kuma ta koma ta zauna tace 鈥渁i ma ka cinyen nawa sai kaban naka.鈥�
Murmushi yai yace 鈥渘awa da naki ba daya bane?鈥�
Kallansa tai cikin wani yanayi, sai kuma tai shiru, mikewa tai ta shiga daki, kudin nan ta dauko dubu 100 ta zuba musu ido tana kallo, mikewa tai ta fito falo.
Ya gama cin nata yana shan ruwa yaga ta dawo, kallanta yai har ta zauna kusa dashi kadan.
Ajiye kudin tai a kusa dashi.
Kallan bakar ledar yai sannan ya kalleta, tace 鈥渒udin ka ne daka kawo.鈥�
Kudina?
Ya fada yana kallanta, tace 鈥渉mm nina ce muyi aure dan haka bai kamata na amshi kudinka ba.鈥�
Yanayin fuskarsa ne ya canza, bacin rai ne karara ya bayyana a fuskarsa, Zainab tace 鈥渒a amsa nagode da ka kawomin a kalla nasan........鈥�
Yanda taga idanunsa sunyi jaaa sosai ne yasa ta kasa cigaba da maganar, mikewa yai kawai taga ya fita waje, shiru tai tasan bazai amsa haka kawai ba amma itakam zuciyarta bazata iya nustuwa ba in ta tuno kudin nan.
Khalid kam ransa yakai kololuwa gun baci, shikadai yasa yanda zuciyarsa ke tafasa, wayarsa dake kara ya daga.
Salmanu
Bayan sun gaisa yace 鈥渄an Allah ka dan kaima Umma dubu daya da dari biyar, zan bata gobe in tazo ta baka, nasan kudin hannunta dasu zatai mota.
To shikenan.
Salmanu zai sake magana Khalid ya kashe dan baisan yai magana mai tsayi kar a gane bacin ransa.
Jin ana kiran sallah yasa ya duba gen din ganin akwai dan mai kadan yasa ya tada.
Shigowa yai tana zaune tana cin abincinta gefe kuma ga kudin nan, baiko ce komai ba ya wuce yai alwala.
Fitowa yai ya kalleta yace 鈥渋n kin gama kiyi alwala muyi sallah.鈥�
Kallansa tai fuskarsa a daure, ruwa tasha ta dauke kwanukan sannan tai alwala, sallah sukai, bayan sunyi addu鈥檕i tace 鈥淜h......鈥�
Kallan daya mata ne yasata yin shiru, mikewa yai ya shiga daki, ya zauna akan gado tare da daga kansa yana neman kwantar da ransa.
Zainab kam tasan bazai amsa da wuri ba amma dalilin fishin ne bata sani ba, har sukai bacci ba wanda ya sake maganac daga zata mai intaga yanayinsa sai tai shiru, haka tai aikinta sunyi sa鈥檃 8 aka kawo wuta, nan ta cigaba , shikam 9 ya kwanta.
Yauma a daki ya kwanta dan kukan datai jiya ya tabashi.
Karfe 4 ya farka, kallanta yai ta matso kusa dashi tana ta baccinta, bargo ya gyara mata sannan ya mike yai wanka yai alwala yasa kaya.
Zama yai kusa da ita, ya sa hannu yadan tabata kadan.
鈥淭ashi kiyi sallah zan wuce.鈥�
Idanunta ta bude, ta kalleshi.
Haryanzu ranka a bace yake?
Kallansa tai tace 鈥渙kay鈥�
Yai dan shiru kafin yace 鈥渒i gyara gidan kafin suzo, sannan ki yi musu abinci.鈥�
Bata amsa ba sai dai ta kalleshi, yace 鈥渨ajen azahar zan dawo nima鈥�
Kai ta daga kawai batace komai ba.
Kallanta ya sakeyi yace 鈥渋nsunzo ki tabbatar kin musu sannu da zuwa kin kuma gaisheta kafin ku fara magana.鈥�
Idanunta ne kawai a kanshi, yace 鈥渟annan kisa mayafi.鈥�
Ajiyar zuciya tai tace 鈥渄uk ni kadai?鈥�
Hmm sirikarki ce.
Kai ta daga sannan tace 鈥渢o.鈥�
Mikewa zaiyi ta riko rigarshj, kallanta yai tace 鈥渂azaka.......鈥�
Katseta yai yace 鈥渘a wuce.鈥�
Shiru tai tana kallansa har ya fita.
*******
Haka ta mike tai gyaran gida, dan tunda tazo yaune ta gyara ko ina ta share, bayanta ne taji ya amsa, tab yaushe raban datai shara? Dan dama ita ba gwanar aiki bace.
Haka ta shiga kitchen tasa shinkafa da miya.
Kallan kudin tai a falo, ajiyar zuciya tai sannan ta dauke ta maidashi kan madubi a daki.
Wajen karfe sha biyu da rabi ta gama abinci tai wanka tana shafa mai taji buga kofa.
Da sauri tasa kaya ta dan shafa hoda tasa turare ta fito, hartazo kofa ta koma da gudu ta yafa mayafi.
Sannan ta fito.
Umma ce ta kalli Asiya tace 鈥渘an ne kin tabbatar?鈥�
Asiya tai dariya tace 鈥渘an ne wlh Umma zuwana biyu fa da Yaya.鈥�
Umma tai murmushi zatai magana sukaji an bude.
Zainab cikin tsananin jin dadi ta tarbi su Umma.
Haka suka shiga ciki tana mata sannu da zuwa.
Umma kam baki yaki rufuwa, sai jin dadi take.
Ciki suka shiga ta tuna kalaman Khalid hakan yasa ta tsuguna ta gaisheta, Umma ta kalleta cikin jin dadi tace 鈥淶ainab鈥�
Zainab cikin jin dadi itama tace 鈥淯mma sannunku da hanya.鈥�
Hira ce ta barke Umma nata tambayarta zaman kadaici da sauransu, sunyi sallah Asiya ta taimaka mata suka kawo abinci.
Umma ta kalli Zainab tace 鈥渒in fadamai munzo?鈥�
Yace 鈥渨ajen azahar zai taho.鈥�
Umma tai murmushi tace 鈥渟ai ki kirashi kiji ko ya taho.鈥�
Cikin kunya ta dau waya tadan matsa.
Khalid na ta gyaran wata mota wacce yake sauri ya gama ya taho yaji kiranta ya daga.
Tace 鈥淪u Umma sun iso.鈥�
鈥淥kay ganinan zuwa.鈥�
Nan suka kashe wayar, hankalin Umma nakanta, Zainab ta dawo ta zauna tace 鈥淵a jikin Abba?鈥�
Umma tace 鈥渄a sauki.鈥�
Suna dan hira wanda duk kalamanta Umma na kula dasu, tundaga yanda take kawo abinci, mantawa datai da spoons sai da Asiya ta dauko, ta kawo ruwa ta manta da cup da sauransu.
Khalid sai biyu da kwata ya samu ya iso, Umma tana kallan ba sannu da zuwa ba komai, har ya gaida Umma basu yi magana ba, Umma ta kalleta tace 鈥淜i kawo wa mijinki nashi abincin.鈥�
Kallan Umma tai dan gaba daya ta juye, tace 鈥渁i duka na juye Asiya dan dauko plate ya diba.鈥�
Khalid ne yai saurin cewa 鈥渘i nace ta hada gaba daya naga haka muka saba a gida.鈥�
Umma ta fahimci kareta yai sai dai batace komai ba, Zainab ya kalla yace 鈥渂ani plate.鈥�
Mikewa tai ta daukomai, ta ajiye tana neman tashi ya dan maida ita a wayance, baisan Umma duk ta gani ba.
Kodaga yanayin yanda suke magana Umma tasan da matsala, kallan Asiya tai tace 鈥淎siya kwashe kwanukan ki wanke.鈥�
Asiya ta mike ta kwashe tai kitchen dasu.
Umma ta kalli Zainab sannan ta kalli Khalid ta gyara zamanta, harxatai magana tace 鈥淜halid bamu guri.鈥�
Yace 鈥淯mma.....鈥�
Sai kuma ya mike yana kallan Zainab yana fatan kar tai baran barama a gaban Umma, dan duk yanda Umma ke santa in taji yanda ta dauki aure da d鈥檃nta lalai da matsala.
Jiki a sanyaye yai hanyr daki Umma tace 鈥渒a jira zanyi magana dakai, dan dama babbar maganar a kanka ne.鈥�
Baice komaj ba yai ciki.
Kallanta Umma tai tace 鈥渂a auren soyayya kukai ba?鈥�
Kallan Umma tai sai dai batace komai ba, Umma tai jinjina kai tace 鈥淜oma auren me kukai bashida tasori a wannan lokacin tunda an riga anyi, ke matarsa ce shi kuma mijinki ne, sai dai wani irin zama ne haka Zainab? Ba girmama juna? Ba ganin mutuncin miji? Sannan da alama ma fada kukai daga aure.鈥�
Kallanta Zainab tai idanunta suka dan ciko tace 鈥淯mma!鈥�
Umma tace 鈥渘a sani nasan duk laifin na Khalid ne sai dai a matsayinki na mace ya kamata ki ja mijinki, Khalid dama tun kafin yai aure ni nasan matarsa sai tayi hakuri da halayensa, sam namiji ne mai wani irin ra鈥檃yi da akida da kuma zafin rai.
Sai dai mu da muke iyayensa mu munsan dalilinsa na yin hakan, duk da hali ne nashi amma ya fara wannan halin ne daga sanda ya shiga jami鈥檃.
Khalid ganin yanda mahaifinsa ke fita tun asuba aikin tuki baya dawowa sai can dare wani sa鈥檌n ma baya dawowa sai bayan kwana biyu yasa ya slakanta wahalar mahaifinsa da shi, gani yake mahaifinsa na wannan wahalar ne saboda yai karatu hankali a kwance, wanda kuma a zahiri hakan ne, mun daura burin mu akan Khalid.
Tun daga nan baisan komai ba sai karatu gani yake karatu kawai zaiyiya faranta mana, karatu kawai ya sani, baya ko shiga cikin gida gun mu a lokacin ko a makaranta bai taba cemana gashi da wani abokinsa suna hira ko sunje yawo ba, hankalinmu ya fara tashi ganin dan mu na neman tattare duk rayuwarsa akan karatu, lokacin ne muka sa dokar cin abinci tare, sannan dole in yana gida ya fito a yi hira dashi.
Alhamdulila wannan doka da muka sa itace ta maido da zumunci da kaunar junanmu.
Hatsatin mahaifinsa ya sa daga karatu ya koma aiki, dan a lokacin da abin ya faru ya gama karatu, sai kuma gaba daya rayuwarsa ta koma aiki, bashi can bashi can yana ta faman had鈥檃 mana kudin da zamuyi rayuwa, komai na rayuwarmu na kansa, shine cinmu shine suturarmu, shine maganin mahaifinsa, karatun kannensa da sauransu.
Umma ta kalli Zainab wacce tai shiru sai kwalla dake zubo mata.....
***
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/9, 12:21 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
{59}
Zainab ta kalla ta kamo hannunta wanda hakan yasa ta dago ta kalleta.
Kinsan meyasa nake fada miki hakan?
Shiru Zainab tai sai maida kai kasa datai.
鈥淜e da shi kun taso rayuwa daban daban, akwai abubuwa dayawa da zakiga basu miki ba a zaman takewarku dashi, Khalid ko bashida lafiya baya taba fadamana, duk kuwa yanda yake jin wahalar ciwo baya taba fadamana, saboda bayasan mu damu, in dai har zai zauna da mutum to baya san ya zama ila ko takura ga wanda yake tare dashi.鈥�
Dan dakatawa tai saboda idanunta dasuka dan ciko, tace 鈥� shi da kanshi bazai taba iya fada ba, wanda hakan zaisa a koda yaushe cikin ko wani hali yake zai cigaba da boyewa.鈥�
Murmushi tai tace 鈥淶ainab kuyi hakuri da junanku, shi aure tunda ibada ne dole sai an jure, akwai lokacin sabawa akwai lokacin shiryawa, sai dai kada ya zama in ya hade rai kema zaki hade, ko in yana fishi kema zaki dau fishi, Khalid d鈥檃na ne, sai dai bazan fifita shi saboda ke ba tawa bace, ina fatan zaku kula da junanku ku dau junanku a matsayin abu guda d鈥檃ya.鈥�
Kai Zainab ta daga cikin wani yanayin, Umma ta kalleta ta kalli agoggo tace 鈥測ima Khalid magana yazo zamu wuce, nabar Abbansu a gida ba babba.鈥�
Zainab na mikewa tace 鈥淎siya.鈥�
Asiya dake tsaye a hanyar kitchen tana jira su gama ne ta shigo.
Umma ta kalleta tace 鈥渒ingama?鈥�
Eh Umma.
Zainab ce ta tura kofar, yana zaune akan gado hankalinsa na waje, haka kawai hankalinsa yaki kwanciya, mikewa yai ya zo bakin kofa ya tsaya yana tunani.
Tana bude kofa ya sa hannu ya jawota ya maida kofar ya rufe, kallansa tai fuskarta dauke da mamaki.
Shima kallanta yai, hannunta da ya rike da karfi ta kalla sannan tadan murza hannun alamar zafi.
Sassauta rikon yai yace 鈥渙h sry, me Umma tace miki?鈥�
Idanunsa ta kalla tace 鈥渕e kake sanji?鈥�
鈥淜e nake tsoro kar ki fadi ba daidai ba.鈥�
Harararsa tai tace 鈥淯mma na jiranka.鈥�
kai ya dan kauda yace 鈥渂adai kiyi baran barama ba ko?鈥�
Tace 鈥淯mma tace ka fito zasu wuce.鈥�
Kallanta yai sannan ya saketa ya juya zai fita, da sauri tace 鈥渒a kaisu a mota.鈥�
Juyowa yai ya kalleta a hankali tace 鈥減lease.鈥�
Kallanta yai fuskarsa a sake jiyai tace 鈥淜aji?鈥�
Murmushi yai sannan ya kalleta yace 鈥渕uje tare?鈥�
Kai ta girgiza alamar a鈥檃 tace 鈥渒aje ka dawo鈥�
Okay yace sannam ya dau key yasa a aljihunsa ya fito.
Da kallo ta bishi wani irin tausayinsa ne ke ratsata gaba daya jikinta, daurewa tai ta fito hannunta dauke da leda data sa ma Asiya atamfa a kayan data dauko a gidanta, da dubu biyu a ciki.
Haka sukai sallama harta cema Umma dan Allah wani hutun Asiya tazo.
Umma tace 鈥渟hikenan, tunda naga akwai wani dakin ta zo insha Allah.鈥�
Har jikin mota ta rakasu, ta ba Asiya ledar da wayau ta juya bayan taga fitarsu.
Suna fita Umma ta kalli Khalid tace 鈥淜halid!鈥�
Yace 鈥淣aam Umma.鈥�
Kallansa tai tace 鈥測aushe mahaifiyarta ta rasu?鈥�
Shiru yai Umma tace 鈥渄a alama ta dade ba tare da ita ba, dan Allah ka kula da ita, ina tausayinta, duk inda kaga aure yayi kargo to lalai miji ne, in har kaga aure ya tabarbare to miji ne, na san halinka sarai sai dainina fatan zaka canza saboda ita, ka ba rayuwarta mahimmanci, ka bata kulawa wanda ta dace dashi, na tabbatar kana santa, to ka jata a jiki ka fahimtar da ita hakan.鈥�
To Umma abinda yace kenan yana tuno kukan datai ranan.
Umma ta kalleshi tace 鈥渒o abinda mijinta ya mata ya isa ta samu farinciki, ina tausayin ta matuka, ina fatan ku ba juna kulawar da kuke bukata, tana bukatar lokacinka, ko yaya ne ka kokarta ka bata.鈥�
Shiru yai haka Umma tai ta dan sanar dashi lamura da hakuri har ya kaisu tasha, dan yaso kaisu ma ta hanashi dubu biyu ya ciro a wallet dinsa ya mika mata yace 鈥渒iba Salmanu 1500 daya baki jiya, ya sa hannu a aljuhu, dari biyar ya ciro yace ki kara wannan dubu daya kenan sai kudan lalaba kafin karshen satin nan zan turo kudi.鈥�
Murmushin karfin hali tai tace 鈥淎llah ya kawo sanda zaka huta Khalid鈥�
Tai maganar tare da share kwallarta. Murmushi yai yace 鈥渂akomai Umma muyi fatan Allah ya sa musu albarka dai.鈥�
Umma tai murmushi tace 鈥渉aka ne Allah ya musu albarka.鈥�
Kallan Asiya yai yace 鈥測ar Umma ba鈥檃 baki na yin iloka ba.鈥�
Kallansa tai ta dago leda tace 鈥淎unty!鈥� Tai maganar cikin kama kai na mai laifi.
Umma ta kalleta sannan ta kalleshi.
Asiya tai tsuru tana jiran fada sai jitai yace 鈥渒inyi godiya?鈥�
Da sauri ta kalleshi tace 鈥渂ansan ta ajiye ba sai da ka tada mota.
Inkinje gida ki kira a wayar Umma kiyi godiya.
鈥淣adauka zaka min fada鈥�
鈥淎untynki ce yanzu da barece zan miki.鈥�
Murmushi sukai dukansu, nan suka sauka yana ce mata zaizo dan zuwa asibiti karshen wata saboda lokacin Abba ne da zai ga likita.
Nan suka tafi ya juyo, har ya isa gida zuciyarshi sam ba dadi, inya tuna ko sanda mahaifiyarta ta rasu bai sani ba wani haushin kansa ne yake damunsa.
Yana shiga duhun magrib na kawo kai, hannu yasa a aljihu ya tuna ashe bashi da kudi, ga mai jiya ya kare, shiru yai a waje idanunsa sunyi jaa yana tausayin ta, inya tuno gidan mahaifinta da gidanta sai yaji duk ya raina kansa.
Jin ana kiran sallar magrib yasa kawai ya fita ya gangara masallaci.
Zainab kam tunda suka tafi ta shiga daki ta zauna a kasa a lungun gado, kanta ta kwantar a kan gwiwowinta, bazata taba yafema su Kabir ba taji zata yafe musu na abinda suka mata amma Allah bazata yafe musu na korar Khalid ba, jin yanda ya taso cikin karatu da aiki ace aikin daya samu an koreshi saboda ita bazata taba yafe musu ba, dan itakam gani take duk saboda ita ne.
Sam bata damu da daren daya kawo kai ba, waya ta dauka ta duba site din gidan tv din su, ganin yanda abubuwansu ke tafiya ba wani ci gaba sai ma ci baya yasa ta cigaba da karantawa tana duduba shirye shiryensu.
Jin bude kofar dakin ne yasa tadan juyo.
A hankali ya karasa inda take, ya zauna a kasa kusa da ita yai zama irin wanda tai yana kallanta.
Murmushi tai tace 鈥渒a dawo?鈥�
Sannu da zuwa!
Au sannu da zuwa, ka kaikus?
Ummm sun wuce, kinyi sallah?
Kallansa tai sannan tadan sa hannu a kafadarta, yace 鈥渒inyi?鈥�
Nayi la鈥檃sar.
Magrib nake tambaya.
Kai ta dan girgiza tace 鈥渋na fashi ko shima sai na fito dala dalla?鈥�
Murmushi ya sa ya matso kusa da kunnenta yace 鈥渕e yasa baki fadan yau bane?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渙h ni yaushe ka koma haka wai?鈥�
Dariya yai yace 鈥渄azu? Yanzu? Jiya?鈥�
Hannu tasa tadan turashi tace 鈥渄a alama haka kake tun da鈥�
Hannun data turashi dashi ya rike, yanayin kallan da take mai yake mata ne ya canxa, yanzu kam tausayin junansu suke.
Murmushi mai sanyi ya mata yace 鈥渒ina shekara nawa Ummy ta rasu?鈥�
Idanunta ne suka ciciko da kwalla tace 鈥渄a alama bamu san komai game da junan mu ba.鈥� Tai maganar hawaye na gangaro mata tana kokarin yin murmushi.
Hannunsa ya sakalo cikin nata ya sako kansa kan nata kan yace 鈥渋 am a bad person.鈥�
Idanu ta rufe tace 鈥渁鈥檃 i am the bad person here.鈥�
Wani abu ya had鈥檌ya yace 鈥渇adamin yaushe ta rasu?鈥�
Kanta ta zame ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace 鈥渋na 9 years, sanda ta haifi Nabila.鈥� Tai maganar cikin rauni.
Hannunsa dayan ya zagayo dashi ya shafi fuskarta yace 鈥渂ansan tun kina yarinya bane.鈥� Yai maganar cikin rawar murya.
Hannun dake kan fuskarta ta daura nata hannun akai tace 鈥渕atar Dady teacher dina ce a skul鈥�
Teacher?
Ya tambaya cikin yanayi na mamaki, dagowa tai ta kalleshi cikin duhun dakin tace 鈥渉mm nice na kawowa Ummy abinda zai lalata rayuwarta, na kawowa Dady wacce zata shiga rayuwarsa data iyalinsa, na ba Adam damar tarwatsa rayuwarsa, kaima gashi na shiga taka rayuwar ina neman hanaka..........鈥�
Bakinsa dataji cikin nata ne ya sa ta kasa ci gaba da magana sai hawaye dake gudu akan kuncinta, hawaye me yaji ya zubo a fuskarsa, raban dayai hawaye harya manta, saboda sam duk abinda yazo gabansa mutum ne mai jajircewa.
A hankali ya dago bayan sun gama sumbatar juna, hannayensa yasa akan fuskarta ya dago da fuskarta yace 鈥渂ake bace dalilin dayasa hakan ya faru da Ummy, sannan Adam zuciyarsa ce ta lalatashi ba ke ba, ni kuma nine na shiga rayuwarki ba ke kika shiga tawa ba.鈥�
Hawaye ne ya zubo mata tace 鈥渒oba ni nai komai ba akanka kam nasan nice鈥� tai maganar hawaye na sake zubo mata.
Jawota jikinsa yai ya rungume tsam cikin wani yanayi, sai data huce sosai sannan ta dago, wayarsa ya kunna, yace 鈥渁m sorry gobe zan siyo mai.鈥�
Kai ta daga tace 鈥渂akomai鈥�
Yace 鈥渟annan kudin dana baki na gaisuwa nine nai ra鈥檃yin baki sannan abune daga cikin al鈥檃darmu ta hausa, na kuma yine dan karan kaina, karki kara neman bani abinda na bada a auranki, ki barni naji da.鈥� A ransa ya karasa da rashin lefen da ban miki ba.
Murmushi tai tace 鈥渙kay鈥�
Fadamin ya Ummy take? Kamarku daya? Yai tambayar yana kwantar da ita akan cinyarsa.
Kallansa tai tace 鈥渒amarmu daya, ai kaga bana kama da Dady.鈥�
Inji wa?
Injini.
Ta fada tana dariya, ido ya zuba mata baice komai ba.
Shiru tadanyi harya dauka bazatai magana ba sai kuma tace 鈥淟okacin Ummy da Dady ni kadai ce a gunsu, yanzu abubuwa dayawa bazan iya tunawa ba a abinda ya faru a lokacin, sai dai a kwakwalwata nasan suna tsananin so na, ina kuma jin dadin yanda rayuwata take a wannan lokacin, kafin a kawo Basma sabuwar Aunty skul din mu..............鈥�
Abinda ya faru a baya ta sanar dashi, hawayen dataji na diga akan fuskarta ne yasa ta runtse idanunta zuciyarta na wani irin bugawa da karfi? Hannu tasa akan fuskarsa.
Jin hawayen daga idanunsa yake yasa zuciyarta ta kara rauni, mikewa tai ya jawota jikinsa, ya matseta sosaj, haushin kansa ne ya kamashi, taya zai kira kansa miji bayan baisan komai game da ita ba? Yana mata kallan dan ta taso cikin kudi, tana komai da kanta yasa take ganin komai dole ya tafi yanda take so?
Jin yanda take kuka tana cewa 鈥淜ayi hakuri.鈥�
Ya karasa zuciyarshi yin rauni, meyasa take bashi hakuri? Bayan shine zai bata?
Khalid me kake yi????
Wata ajiyar zuciya hai wacce kana jinta kasan wanda yake cikin yanayi na karayar zuciya ne yake yinta.
Zainab ce tace 鈥渟hiyasa bansan komai ba sai aikina, gani nake shine zai kwatomin darajata, kayi hakuri nayi amfani dakai bansan halin da kake ciki ba kenan.鈥�
Dago da ita yai ya kalleta sosai yace 鈥渨hy me?鈥�
Idanunsa ta kalla, yace 鈥渟anda kike neman wanda zaki aura, why me?鈥�
鈥淚 don鈥檛 know i just feel like in har dakai ne i can do much better鈥�
Gani tai yayi murmushi, sannan ya kalleta yana shafa gefen fuskarta yace 鈥渟hiyasa bakya san yanda da mutane?鈥�
Ummm gani nake kowa na amince dashi haka zaimun yanda Adam da Dady sukai akan mace.
Nifa?
Dan kanta tadan kwantar kan hannunsa tadan lumshe ido ta bude tace 鈥渂ansani ba.鈥�
Murmushi yai yace 鈥淯mma gulmata ta miki ko?鈥�
Ummm tasan bazaka min da kanka ba.
Murmushi yai yana kallanta, itama murmushi tai tare da kai kanta kasa, hannu yasa ya jata kan cinyarsa yace 鈥渒in yadda dani?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渂ansani ba鈥�
Hannayensa yasa ya zagayota yace 鈥渋n sanar dake?鈥�
Murmushi tai tace 鈥渂ana sal......鈥�
Iskar daya farzar ne yasata yin dariya, dagata yai ya mike tace 鈥渋na zaka?鈥�
Wanka zanyi na tafi masallaci.
Murmushi tai har ya dau towel sai ji tai yace 鈥渒o zaki taimaka da......鈥�
Ai bai karasa ba ta mike cikin hanzari ta fita daga dakin garin sauri har kafarta ta buge amma bata nuna ba, murmushi yai sannan ya zauna a bakin gado.
Shiru yai yana tunani, kenan ba dan Umma ta nunamai ba haka zaita daukanta ayanda yaso? Itama haka?
Taya tai rayuwa da abubuwa biyu? Gana uba ga rashin uwa? Sannan miji yazo daga baya? Sannan aikinta?
*********
Duk yanda taso tai bacci ta kasa, screen din wayarta ta bude, hoton Khalid wanda ya dauka ranar graduation dinsu ne akan alan wayar, ajiyr zuciya tai sannan ta kira number Adam.
Adam dake zaune ransa a bace yana kallan su Kamal nacin shinkafa yaje ci yace mai wai gaskiya a鈥檃 bazai bashi gun kwana abinci ma ya dinga bashi ba, haushi duk yabi ya isheshi.
Ganin kiran Afreey yasa ya daga ba tare da ya sani ba.
Tace 鈥淎dam ka nemo?鈥�
Jin muryarta yasa ya mike tsaye da sauri, yace 鈥渘aam?鈥�
Tace 鈥渄ama dubu goma zan baka tunda baka nemo inda Khalid yake ba shi.......鈥�
Wallahi na nemo.
Wani wulakantacen murmushi tai tace 鈥渋na ne?鈥�
Ban san ina bane amma tunda munyi waya dashi in na tambayeshi zai fadamin.
In ka nemo ka fadamin sai na tabbatar zan turoma kudin.
Da sauri yace 鈥渮uwa zakiyi?鈥�
Wannan ba damuwarka bane.
Me kike gani in na kirashi kikazo inda zamu hadu?
Yai tambayar yana neman sa鈥檃r amincewarta.
Me yake a kano?
Bansani ba nima in mun hadu ma tambayeshi ko?
Shiru tai dan bata yarda da Adam ba amma tace 鈥渢o ka mai magana sai na jika.鈥�
Ta kashe wayar tare da zubawa hotonsa ido cikin shagwaba tace 鈥淜halid!鈥�
Nace hmmmmm馃あ馃あ
*******
Bayan yayi sallah ne sukai sa鈥檃 nepa suka kawo wuta, cikin jin dadi ta kalleshi sai kuma tasa yar dariya.
Yace 鈥渁ikin ya tashi ne?鈥�
Tace 鈥淢e kake gani zaifi batawa su Kabir rai?鈥�
Akan me?
Kawai da in bude gun aikina daban da kuma in bude in kwashe masu kwazan aikinsu wannan kake gani?
Murmushi yai yace 鈥済ashi kin fada.鈥�
Cikin jin dadi ta kalleshi, yau ne ya fara amsa mata akan tambayar aiki da take mai.
Harta dauko laptop suka dauke wuta, kallan Khalid tai kamar zatai kuka.
Yce 鈥渟orry zasu dawo dashi.鈥�
Haka ta maida laptop din, tara nayi ya fara hamma.
Kallansa tai ba dole ba yanata uban aiki kullum ba hutu.
******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/9, 12:22 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
{61}
Gaba daya ji tai numfashinta na sarkewa, mai lemo ne ya matso yace 鈥渂aiwar Allah lafiya?鈥�
Khalid wanda ya shiga mota yaja ya fara tafiya a hankali yana kallan glass din madubinsa ta baya, Zainab a kufule tace 鈥渋n kasan bakasan barinta meyasa ka taho?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渁m sorry amma sai na dan duba halin da take ciki, kar wani abu ya faru.鈥�
Baki Zainab ta bude cikin mamaki tace 鈥渂adai fadamin kake zaka koma inda take ba?鈥�
Eh, ya fada tare da dan yin baya da motar, Zainab kam wani mugun kishi ne ya turnuketa, Khalid ne yai parking ya juya yana kallan bayan motar inda Afree take a tsaye mai lemo na mata magana.
Zainab ce ta juya tana kallanta, sanye take da riga english wears rigar takai mata gwiwa, sai wando jeans pencil, ta yane kanta da mayafi.
Wani irin kishi ne ya kara rufeta, Khalid ta kalla wanda ke kallanta sanda ta wuce ta shiga mota ji take kamar zatai hauka.
Juyowa yai sannan yace 鈥渒ina ganin ba matsala?鈥�
Wata uwar harara ta watsamai tace 鈥渋n da matsala ka je ka kaita gida mana.鈥�
Okay to ko zaki fara zuwa sai na biyoki?
Tace 鈥渕ene?鈥�
Gani tai yana neman fita cikin hanzari ta rikoshi tace 鈥渄a gaske zuwa zakai?鈥�
Eh na dauka mun gama maganar? Ya fada yana kallanta.
Idanunsa ta kalla tace 鈥渒a ajiyeni ni matarka ka tafi gun wata?鈥�
Bakya ganin halin da yake ciki? Sannan waye yace min duk sanda naso nai aure?
鈥淗alin da take ciki?ni halin da nake ciki fa?鈥�
Ido ya kura mata hana kallanta, ta kauda kai tace 鈥渕aganar aure ai ba auranta kai ba.鈥�
鈥淏ari na je gidansu daga can na gabatar da kaina.鈥�
Ya fada tare da juyawa yana neman fita, da sauri ta kara rikeshi tace 鈥渨ai da gaske kake?鈥�
Kinga alamar wasa a nan?
Tace 鈥渕aidani gida.鈥� Ta fada cikin raunin murya.
Yace 鈥渒e dai kikace naje gidansu yanzu.鈥�
Yaushe na fada?
To meye na hanani?
鈥淏ansani ba amma nidai.......鈥�
Sai kuma tai shiru, murmushi yai ya matso saitin kunenta wanda hakan yasata dan dagowa, yace 鈥渇adamin sunana.鈥�
Sunanka?
鈥淓h, in ba haka ba yanzu na fita na maidata gida.鈥�
Kai ta dauke tace 鈥渕eyasa ka taho guna kasan hankalinka yana gunta?鈥�
Fadi kona koma gunta ki fada.
Dan baki ta motsa yace 鈥渂anji ba.鈥�
Ta kara motsa baki, shikenan tunda bazaki fada ba, ya koma ya zauna.
Kai ta juya tana kallan waje ta glass tace 鈥淪weet.鈥�
Murmushi ya saki, ya juya yaga ba motar Afreey agun, ajiyar zuciya yai yana fatan Allah yasa ta cireshi a ranta.
Zainab ya kalla yace 鈥淯r sweet is here.鈥�
Samun kanta tai da jin kunya, murmushi yai sannan yaja suka tafi.
Hade rai tai, hannu yasa ya kamo hannunta, kallansa tai tace 鈥渕eyasa baka bitan ba?鈥�
Ina zan bita bayan naga bakya so?
Shiru tai tana tunanin shigar da Afreey tai da yanda tai kwalliya, maza irin haka suke so? Meye damuwata da abinda suke so?
Sake sake tai tayi har suka isa.
********
Cikin gidan aka bude musu gate sukai parking ba wai katan gida bane sai dai kana ganinshi kaga gidan dake da rufin asirinsu, a gun talaka kuwa gida ne na masu kudi.
Ledar hannunsa daya dauko ta kalla kallanta yai sannan ya kalli ledar da take kallo, mika mata ledar yai yace 鈥渒i rike.鈥�
Amsa tai ta rike.
Bangarenta suka wuce Zainab tai knocking din kofar, daga ciki wata yarinya wacce batakai Asiya ba tazo ta bude.
Cikin tsananin murna tace 鈥渙yoyo Aunty.鈥�
Zainab ta kalleta tace 鈥淎mira kece kika girma haka?鈥�
Amira ta basu guri suka shiga,
Falo suka shiga, Zainab tace 鈥渋na yaran gidan?
Suna islamiyya
Kefa?
鈥淏ana jin dadi ne, Umma na sallah ne鈥�
Zama Khalid yai a kasa, Zainab ta kalleshi tace 鈥渒a hau kujera mana.鈥�
Kai Yadan girgiza mata zatai magana Aunty ta fito sanye da hijab tace 鈥渋kon Allah, wallahi ban dauka ds gaske kike ba.鈥�
Zainab ta kalleta tace 鈥渒ai Aunty.鈥�
Zama tai akan kujera tana kallan Khalid tace 鈥渓ale lale, Ango godiya nake dan nasan Allah Zainab haka kawai bazatacs zatazo ba.鈥�
Gaisheta yai, ta amsa cikin girmamawa yanda taji ya gaisheta cikin girmamawa.
Cikin jin dadi take kallansa sannan ta kalli Zainab wacce ta rasa ina zata zauna, ganin Khalid a kasa.
Tace 鈥淎marya.鈥�
Zainab ta dake ta zauna a saman kujera tana amsa gaisuwar Amira.
Amira dake tsugune ce ta gaida Khalid ya amsa yana tambayar ta makaranta.
Zainab ta mika mata ledar sannan tace 鈥淎jinta nawa yanzu?鈥�
Aunty ta kalleta tace 鈥渒o kunya ma tambaya kike?鈥�
Dan dariya tai tace 鈥淩abona da ita na dade.鈥�
Aunty ce ta mike tai kitchen, sai data shiga sannan ta sa Amira ta kira Zainab.
Nan suka hada kayan da aka shirya dominsu, wanda tayi ne tana san ganin ko da gaske take.
Khalid kam zubo yasha yaci samosa guda daya, wayarsa ya dauka ya mata text, ko na barki na dawo da daddare?
Da sauri ta mai reply tace 鈥渁鈥檃鈥�
Murmushi yai sannan ya mike, Amira data fito ya kalla yace 鈥淎untynki zata tsaya anan wai sai dare, ko zakima Umma magana zan wuce sai na dawo?鈥�
Juyawa tai ta sanar da Mamanta, Zainab dake zaune mamaki ya kamata yaushe tacemai zata zauna?
Mikewa tai ta fito falo, kallan Aunty yai yace 鈥淎unty na dawo daddare tace tana nan ita.鈥�
Cikin farinciki ta kalli Zainab tace 鈥渕asha Allah nagode sosai Zainab.鈥�
Zainab tai yake kawai, haka ya fito tabi bayanshi, suna fita waje tace 鈥測aushe nace zan zauna?鈥�
Dazu ko kin manta?
Cikin mamaki tace 鈥淎鈥檃 fa nace.鈥�
Au haba? Nikam eh na gani.
Tace 鈥渘i Allah bansan doguwar hira, ki daure kanwar Ummy ce ita kanta tanasan kadaicewa dake.
Dan baki ta turo yai murmushi yace 鈥渟ai na dawo.鈥�
Haka tana gani ya shiga mota, ya kalleta yace 鈥渒o na kawo miki laptop dinki? Naga suna da wuta.鈥�
Kallansa tai tace 鈥淟alai ma.鈥�
Murmushi ya yace 鈥渒i fadi sunan.鈥�
Tace 鈥渘aki.鈥� Ta juya tai hanyar ciki, jitai yace 鈥渂azaki fada ba?鈥�
Da sauri ta wuce ciki tana murmushi.
********
Marin data xuba maine yasashi gigicewa, hankali a tashi ya kalleta yace 鈥淎freey yadaga zuwana zaki wankeni da mari?鈥� Ya fada tare da rike gun.
Cikin hucci take kallansa tace 鈥渘i zaka maida yar iska?鈥�
Kamar ya? Haryanzu hannunsa na kan fuskarsa dan yaji abin.
Hannu ta daga tana neman kara mai wani yai baya da sauri yace 鈥淎freey lafiya?鈥�
Cikin tsananin masifa da tashin hankali tace 鈥渢a ina? Taya Khalid zai aureta?鈥�
Adam ya kalleta wato taji yayi aure kenan?
Kallan Adam tai tace 鈥渦ban me kake har hakan ta kasance?鈥�
鈥淣i kuma? Wai ya kikeso nai da Khalid ne?鈥�
鈥淔adamin inane gidansa?鈥�
鈥淚na na sani?鈥�
Haushi ya tuketa tace 鈥渁i kasan inda gidan matarka yake, ina ne?鈥�
Adam cikin rashin fahimta yace 鈥済idan matata suke?鈥�
Jakar hannunta ta cillo inda yake ta sameshi kuwa, kallanta yai yace 鈥淎freey lafiya?鈥�
Cikin masifa tace 鈥渒ana haukar ina Zainab ta auri Khalid?鈥�
Kallanta yai kawai kuma ya bushe da dariya yace 鈥淎freey yunwa kike ji? Wace Zainab din?鈥�
Wani kallo tamai hawaye na zubo mata tace 鈥渂akada hankali amma ko? Tun yaushe nace ma akwai abu a tsakaninsu?鈥�
Jin abin yai sama taka kamar irin an mai duka din nan.
Kusa da ita ya matso yace 鈥渒ina san cemin Honey ce matar Khalid ko me?鈥�
Sai yaushe zaka fahimta? Sau kuma nawa kake san na fada? Da idona fa na gansu.
Baya baya ya fara yi yana girgiza kai alamar a鈥檃, wayarsa ya dauko da sauri ya kira number Goggo.
Goggo kam acan tun jiya take kwance ba lafiya, ita kadai a dan tsukukun dakin da take, yunwa ta gama cinta harta gaji, gayan tuwon dake gefe ta dauka ta hauci, wallahi yau zata bar kauyen nan ko menene sai dai ya faru amma bazata zauna ta mutu ba, dole ya samu ko hamsin ne tasa a waya ta kira Hajiya Bilki ko aikatau ne ta samar mata amma bazata zauna awannam gidan ba.
****
Adam kam duk yanda ya kirata rashin service yasa taki shiga.
Haka ya hakura yana dagowa yaga Afreey bata gun, hankalinshi a tashe ya dannawa Khalid kira.
Khalid na ganin kiran bai daga ba dan yasan dalili shikuma bai san suyi magana ta waya, dan yanasan sashi yaje gidansu Razy abubuwane suka hadarmai yasa ya manta.
******
Acan gidan Aunty kuwa, Zainab batasan sanda ta sake ake ta hira ba, yayin Amira ne suka dawo su Samira.
Kaya suka cire, Samira tasa riga da wando ta fito.
Zainab ce ta kalleta sannan ta shiga daki ta kirata.
Samira ta shigo tana cewa 鈥淎unty gani鈥�
Zainab ta kalli Kayan tana tuno Afreey, sannan tace 鈥渒ayan jikinki ina ake saida irinsu? Nabila ce take so.鈥�
Samira tace 鈥済asu nan a ko ina, akwai a stores akwai a kasuwani irinsu saban gari.鈥�
Shiru tai dan batasa saban gari ba, amma ta dake tace 鈥渮an fadamata鈥�
Haka suka dawo ana hira itadai sai duba waya take.
Khalid kam sai 8 na dare ya taho, wayarsa daya kashe saboda kiran da Afreey keta mai ya kunna.
Texts ne suka fara shigowa.
Kansa yadan dafa sannan yaa Zainab text akan yana hanya.
*****
Ayusher 馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/9, 12:22 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
{60}
Yau harya shirya tana bacci, kusa da ita ya nufa ya sunkuyo ya sumbaci goshinta, sannan ya fita, yana tafe yana addu鈥檃r dacewa da aiki dan bai taba jin haushin fita da sassafe da yake ba irjn yau.
Haka ya wuce gun aikin ginin da suka ci karfi dan an kusa kammalashima.
Zainab kam tana ta bacci, wani irin bacci take wanda take jin dadinsa matuka, kamar a mafarki takejin buga gate, idanunta ta bude sannan ta kalli agoggo, a zabure ta mike zaune ta kara kallan wayarta da gaske 11? Wani irin bacci ne hakan?
Jin bugun kofa yasa ta mike toilet take san shiga amma ganin kar wanda ke bugawa yaji haushi yasa ta zura hijab ta fito.
Tana budewa taga matar na kokarin juyawa, jin karar budewa ne yasa ta juyo ta kalleta tace 鈥渙h ashe kina nan.鈥�
Zainab ta kalleta cikin rashin fahimta, dariya matar tai tace 鈥淢aman Al鈥檃min ce daga nan gidan.鈥� Ta nuna mata makotanta.
Zainab tace 鈥渙h Allah sarki.鈥�
Ta fada tana kallanta, Maman Al鈥檃min tace 鈥渂ari na shigo mu gaisa dan inata sa rana bansamu na zo ba.鈥�
Jin haka yasa Zainab ta fahimci ciki take san shiga hakan yasa tai gaba da sauri, shigowa tai tana cewa 鈥渂a dai bacci kike na tasheki ba?鈥�
Zainab ta kalleta tace 鈥渢aimako kikai ai.鈥�
Dan dariya tai suka shiga falo, ta zauna sannan suka gaisa cikin mutunci.
鈥淚na tacewa zanzo gun Amarya mu gaisa amma inata famar hidimar aiki.鈥�
鈥淢asha Allah, a kalla yafi zaman haka.鈥�
Dariya tai tace 鈥渄uk da agida nakeyi amma sosai nake samu.鈥�
Zainab tadan jinjina kai.
Murmushi tai ta kalli Zainab tace 鈥渁 kano kike?鈥�
鈥淓h rabi.鈥� Ta fada tana murmushi.
Maman Al鈥檃min tai dan dariya tace 鈥淎llah sarki, ni anan kano nake.鈥�
Bata jira Zainab tace wani abu ba tace 鈥済a wannan, nasan ku amare ba a rabaku da 鈥榶an abubuwan ku, zan shigo na rasa mai zan kawo miki shine na dauko abinda nake saidawa.鈥�
Ta fada tare da mika mata ledar.
Bude ledar Zainab tai cikin rashin fahimtar menene a ciki ta kara daga robar ruwa wanda aka cika ta da wani abu dark brown, sannan sai kulin garin abu kamar kuka a leda fara, dayan kuma abu ne a dunkule a cikin ledar.
Kallanta tai tace 鈥渕enene?鈥�
Dariya Maman Al鈥檃min tai tace 鈥渉aba haba, Amarya kodaga shekarunki ai nasan lokacin auren ne dai baizo da wuri ba, kar kisani dariya taya zaki nuna baki san menene ba?鈥�
Cikin mamaki Zainab tace 鈥渘a menene? Allah ban sani ba.鈥�
Baki ta bude tace 鈥渟hekararki nawa?鈥�
Nan da wata biyu zanyi 29, baki ta sake budewa tace 鈥渁mma baki san wannan ba?鈥�
Eh, abin mahimmanci ne?
Gaba daya kallan mamaki take mata tace 鈥渋kon Allah, yanzu yara yan 16 ma sun san kayan mata balle ke?鈥�
Kallanta tai sannan ta kalli cikin ledar, ko irinshi maman Basma ta bata? Amma ita kazace sai su ruwan kankana, wannan kuma daban.
Maman Al鈥檃min ganin da gaske Zainab bata sani ba tace 鈥渒iyi kokari ki shanye na ruwan, wannan kuma ki dinga diba kina sawa a nono ko yoghurt kina sha, in kika sha kikaji amfaninsu na miki bayani.
Zainab ta jinjina kai cikin gamsuwa tace 鈥渋nsha Allah, nagode sosai.鈥�
Mikewa tai ta kawo mata ruwa da dubulan dasu alkaki, kadan taci sannan tace zata wuce saboda tana da gyaran Amarya da zatayi.
Zainab ta zuba mata su a leda ta rakota har kofa sannan sukai sallama, komawa ciki tai ta wuce tai wanka ta sa kaya sannan ta shiga kitchen ta daura indomie, wayarta ta dauko sakon Khalid ta gani da alama dazu ya mata.
Kin tashi?
Murmushi tai kamar yana ganinta tace 鈥渂ayan makara nai, sai fa 11 na tashi.鈥�
11? Dama agoggo ta iya bacci haka?
Nice agoggo?
Murmushi yai sannan ya maida wayar ba tare da ya maida mata ba, Hello?
Nice agoggon?
Haushi ne ya kamata ta ajiye wayar, indomie dinta ga juye ta fito falo tana kallan wayar, har ta cinye baiyi reply ba.
Haushi ya kamata ta juya wayar ta rufeta, kitchen ta shiga ta wanke kwanukan sannan ta kalli ledar, a hankali ta bude robar ruwan ta dan lashi kadan.
Meye wannan?
Ta tambaya tana dan kara kai bakinta kadan ta dan kurba.
Ajiye wa tai ta rufe robar tana cewa 鈥渁ikam ban iya sha.鈥�
Fitowa tai falo ta dau wayarta, ganin missed call din Khalid yasa ta kirashi da sauri.
Harta katse bai daga ba, ajiyar zuciya tai tace 鈥渕e kuma nai?鈥�
Jin karar wayar ne yasa ta kalleta, hannu takai zata daga sai kuma ta hau dan kwantar da zuciyarta sai da ta bari tai ringing uku sannan ta daga.
Kina san wani abu ne?
A鈥檃
Okay sai na.......
Kashewa zakai?
Eh da wani abin ne?
A kufule tace 鈥渂akomai鈥� kafin ma ya kashe ta kashe.
Fuska ta bata sannan ta tambayi kanta, me nake san ji?
Koma menene a kalla ba kawai ya tambayen ya kashe ba.
Kwan wuta ta kalla suma wadan nan nepan banda rashin mutunci sai yaushe zasu kawo wuta?
Waya ta daga ta kira Nabila suka fara hira, wacce rabin hirar mita take mata akan Khalid ya kira wai kawai ya tambayeta abu yace zai kashe.
Dariya kam Nabila tayishi harsai da cikinta ya kulle, tace 鈥淎unty ni wlh girki nake karkisa na kone.鈥�
Girki? Ta maimaita sannan tace 鈥渘abila sai anjima.鈥�
Da sauri ta kashe ta kalli agoggo, karfe 3?
Mikewa tai ta wuce kitchen kamar wacce aka mintsina kawai ta hau yin abinci.
Khalid kam dadi yaji dan yauma da wuri yabar garage gida ya nufo hannunsa dauke da bread, da mai na gen.
Harya shiga falan baiji mostinta ba, hakan yasa ya nufi daki, bata daki sai dai jin karar ruwan flushing daya ji ne yasa yasan tana toilet, murmushi yai sannan ya zauna a bakin gado ya zubawa kofar toilet ido yana jiran ta fita.
Bude kofa tai, sam batasan zata ganshi ba hakan yasa gabanta faduwa, ganin yanda ta tsorata ne yasa ya taso da sauri, tsoro kikaji?
Kallansa tai sannan ta harareshi tace 鈥渂a tsoron kaso bani ba?鈥�
Kallanta ya sake yin ya rike hannunta yana kallan fuskarta.
Samun kanta tai da yin kasa da idanunta, murmushi yai yace 鈥渄azu kinji haushi ne?鈥�
Dagowa tai ta kalleshi ta bata fuska tace 鈥渂a haushin kaso bani ba?鈥�
Murmushi yai yace 鈥渉aka ne?鈥�
Ba hakan bane?
Sun kawo miki wuta? Ya tambaya yana zama akan gado.
Kh......
Sai kuma tai shiru, yace 鈥淜halid zaki ce?鈥�
Shiru tai tare da kauda kai, yace 鈥渇ada gani.鈥�
Kallansa tai tace 鈥淜halid wai me yasa kake san cemin agoggo?鈥�
Ta fada cikin dakewa.
Khalid?
Kallansa tai sai kuma tai shiru, Khalid? Khalid? Ya maimaita sannan ya mike ya shiga toilet.
Shiru tai tare da binshi da kallo, ko banza na rama, ta maimaita tare da yar dariya.
Kitchen ta wuce ta juye abincin sannan ta dawo falo.
Fitowa yai sanye da yar karamar riga da wando.
Kallan ta yai, ta kalleshi taga ya daure fuska, dariyarta ga guntse har yazo inda take, gani tai ya zauna a kasa inda take ya mika mata man zafin hannunsa.
Kallansa tai ya dago kansa yana kallanta, amsa tai jikinta a sanyaye.
Rigarsa ya daga yace na shafa anan, ya nuna mata kafadarsa.
A hankali ta lakuto tana shafamai gaba daya jikinta yai sanyi, jin yanda take shafawa a hankali yasashi lumshe idanunsa.
A hankali yace 鈥渕e kike cewa wancan Mutumin?鈥�
Wani mutumin?
Wancan mutumin dai, sunanshi kike kira?
Yanzu kam ta fahimta hakan yasata cewa 鈥渕eyasa kake sanji?鈥�
Kansa ya sake dagowa yana kallanta yace 鈥渋n fadamiki?鈥�
Eh!
Hannunta ya riko ya ya juyo tare da dan mikowa yana kallanta, yanayinta ne ya canza, tana kallansa, in fada miki?
Da sauri ta dago man zafin saitin fuskarta tace 鈥渒a manta?鈥�
Wani abu ya had鈥檌ya yace 鈥渋na dai tausayinki amma ai ba dole.....鈥� sai kuma yai shiru tare da yin murmushi.
Zama yai kusa da ita yace 鈥淎llah karki kara cemin Khalid.鈥�
To me kake so na cema?
Shima sai na fada miki?
Ahh to zan ce ma K? Tai fadi yanda ake kiran K
Ke? Kin manta keke, ko dayake ki fada nima sai na ce miki Z, ya fadi Zet yana kallanta.
Z? Eh ba K kika ce ba?
Allah bazan yadda kacemin Z ba.
Dariya yai sannan yace 鈥淎untyn ki dake garin nan a wace unguwa take?鈥�
Sharada menene?
Ko zaki kirata ki fada mata zamu je?
Ido ta zaro tace 鈥渕uje ina?鈥�
Kallanta yai yace 鈥済aisheta, ki kirata kiji in gobe tana nan.鈥�
Baki ta bude tana kallanshi, sai dai samun kanta tai da jin dadi a kasan ranta, tunda take da Adam bai taba ce mata ko Auntynta ta gaida ba, ita dama zumuncin bai dameta ba balle taje, in har taje gidan to lalai haihuwa ce ko biki, bata taba kawo yau ya kamata taje su gaisa ba.
Kallan Khalid tai fuskarta dauke da murmushi ta sauko ta ja plate ta fara zubamai abinci, hannunta dake komarin suba miya ya rike, a hankali ta dago ta kalleshi yace 鈥渒inci abinci ne?鈥�
Zanci anjima.
Hannunta ya sake ta suba miyar, zata mike ya sa hannu ya kara riketa, kallansa tai, spoon ya juya mata saitinta ya kalleta ya nuna mata bakinshi.
Tace 鈥渄an Allah kaci abincinka.鈥�
Fuska ya daure yace 鈥渁she yau zan kwana da yunwa.鈥�
Cikinka ne fa?
Eh cikin nawa ne zan gani ko an damu shi.
Khalid hooo abinda ta fada a ranta kenan, spoon din ta dauko ta debo ta nufi bakinshi jin abin take wani banbarakwai.
Baki ya bude ta samai, amsa yai yana ci yana kallanta, sai dayaci sosai, ruwa ta dauka ta zuba takai bakinta ta kurba zata sha, amsar cup din yai ya sa hannu a kugunta ya matso da ita dad dashi, ruwan ya sa a bakinsa sannan ya jawota jikinsa ya sa bakinshi cikin nata ya zuba mata ruwan, tana hadiyewa ya shiga yin salo da bakinta.
Gaba daya jitai jikinta ya mutu, yau kam ta dage sai kokarin biyema bakinsa takeyi, jitai wani abu na tsirga mata, kallansa tai da idanunta da suka shanye?
A hankali ya kai bakinsa kusa da kunnenta yace 鈥渮an iya jira?鈥�
Hannu tasa ta turashi baya ya dan yi baya jikin kujera.
Mikewa tai da sauri tai kitchen.
Kallan maganin nan tai kawai ta samu kanta da dauka ta dauke numfashi tana sha, sai datasha kusan rabi sannan ta ajiye tana maida numfashi.
Waya ta dauka ta kira Aunty ta sanar da ita sakon Khalid.
Ba karamin mamaki Aunty tai ba dan kasa bata amsa tai sai da Zainab tace 鈥淎unty kina ji?鈥�
Da sauri tace 鈥渋na nan sai kunzo.鈥�
********
Washegari.
Karfe hudu ya dawo ta shirya tsaf cikin lace peach anyi ratsin marron da light brown a jiki, dinkin ya amshi jikinta sosai, tayi kyau matuka, tana zaune tana waya da Nazifi akan list da take so ya turo mata, Khalid ne ya gama shiryawa a daki ya fito falo.
Sanye yake cikin shadda sky blue yasa hula dark blue yayi kyau sosai shima, kallansa ta shiga yi tana murmushi.
Muje?
Ya fada yana kallanta, wayarta ta kashe bayan sunyi sallama sannan ta kalleshi tare da mikewa ta yafa mayafinta a kasan kafadarta, kusa da ita ya tako a hankali, yaja mayafin ya maida shi saman kanta.
Idanunsa tadan dago ta kalleshi sannan tai murmushi.
Hannu ya mika maga kallansa tai sannan tasa nata hannun cikin nashi suka fito.
Mota suka shiga ya kalleta yace 鈥渕e zamu kai?鈥�
Shiru tai kafin tace 鈥渂asai munkai wani abu ba, ai ta gida ce.鈥�
Bai ce komai ba ya ja motar, sai daya fita sannan ya fito ya rufe gate, shiru tai tana kallanshi harya dawo.
Kallanta yai yace 鈥渕usai fruit?鈥�
Kamar tace 鈥渁kwai halin hakan? Sai kuma tai shiru.
Sai da sukai tafiya sosai suna tafe tana bashi labarin yanda ta zauna a gidan, kan titi ya gangara yai parking ganin mai fruit.
Yace 鈥渂ari na siyo.鈥�
Shiru tai tare da daga kai.
Harta wuce ta dawo baya tana san kara tabbatar da idanunta.
Parking tai kusa da motar dake gun, sannan ta nufeshi.
Mika dari biyar yai ana zubamai fruit din yana tunanin ya isa?
Jiyai ance Khalid?
Kallanta yai sannan ya dauke kai ya maidashi gun lemo da ayaba.
Kusa dashi taje cikin wani irin shauki take kallanshi kallan shigar dayai da yanda yai kyau yasa takeji kamar ya rungume shi.
Kusa dashi taje tace 鈥渒asan ina zani?鈥�
Kallanta yai, tace 鈥済unfa Adam zani yanzu ina san jin inda kake.鈥�
Kai ya girgiza cikin kufula sannan yace 鈥渉ala baki da abinyi ne shiyasa.鈥�
Murmushi tai cikin farin ciki tace 鈥淜a dawo gidan Tv din nan zan musu magana....鈥�
Baiko bi ta kanta ba ya amshi ledar ya juya, kallan Zainab yai ta glass wacce ta cika tai fam, ko daga cikin glass yana ganin tsantsan kishi dake bayyane a fuskarta.
Kallan Afreey yai yace 鈥渨uce kije inda zaki please鈥�
Yai maganar sannan ya juya, rigarsa ta kamo wanda hakan yasa Zainab zaro ido, bude kofa tai da sauri tace 鈥淪weet muje in ka gama.鈥�
Ta fada cikin faduwar gaba dan ita kanta batasan me take fada ba.
Afreey ce ta kalleta, cikin rashin fahimta take kallan Khalid, kallanta yai sannan ya nufi inda Zainab take cikin sanyanyan murmushi.
Juyowa yai ya kalli Afreey yace 鈥渮o ku agaisa, she is my wifey鈥�
Jakar hannunta ce ta fadi jitai kanta na wani irin juyawa, Khalid ya kalli Zainab sannan ya kalli Afreey yace 鈥淪afiya zo ku gaisa.鈥�
Kallansa tai idanunta ne suka fara canzawa, yasan ba zuwa zatai ba hakan yasa ya kalli Zainab yace 鈥渕uje?鈥�
Kai ta daga da kanshi ya taimaka mata ta shiga motar sannan ya rufe mata motar ya juya ya nufi inda Afreey take, jakar data yar ya dauka ya mika mata yace 鈥渄a alama tsayuwar ta miki dadi, mu mun wuce鈥�
Ya juya yashiga yaja suka tafi.
Gaba daya kanta ke juyawa, wayarta daje ta zabga kara wanda Adam ke kiranta ya mata karya akan bayannan.
Wani irin ihu ta saki jin da gaske ba mafarki take ba.
Nikam jin ihun nan bansan sanda na arta a guje ba馃弮馃徎鈥嶁檧
0 comments:
Post a Comment