Kallansa tai sannan ta dauke idanta tace " akwai inda zani acan"
Bai tada motar ba sai dai yana nazari, kallansa tai tace "muje!"
Motar ya tada suka fara tafiya, hannunta rike da wayarta tana kallan sunan Dady, can ta danna kira.
Ringing uku aka dauka, sai dai me? Jitai muryar mace, Basma daga can take "Zainab?"
Da sauri Zainab ta kalli wayar wani abu ya tokareta, Basma tace "yahkuri na daga wayar, yanzu ya dawo break daga gun aiki ya shiga toilet ne."
Kashe watarta Zainab tai sannan ta rufe idanunta kamar mai bacci.
Har suka shiga danbatta bata bude idanta ba da alama daga tunane tunane bacci yayi gaba da ita, suna kan titin shiga danbatta ne yace "ina ne unguwar?"
Shiru yaji hakan yasa ya duba mirror din gabar motar, ganin tana bacci yasa yace "Hello!"
Zai sake magana yaga ta farka a zabure, tana Inalilahi wa Inalilahi Raji'un.
Idanunta ta bude a tsorace, tana maida numfashi, Khalid ya gangara gefen titi.
Kallansa tai ta tana jin haushin yanda yake gaminta yanayin da bata san kowa ya sameta a ciki.
Daurewa tai tace "muje."
Yace "inane?"
Kallan garin tai sannan tace "I don't know."
Juyowa yai ya kalleta yace "You don't know?"
"Hmm yafi shekara biyar dana zo i can't remember."
Baisan sanda wata dariyr rainin hankali ba, haushi ya kamashi yace "then ki kira kaninta muji."
Wayarta ta dauka ta kirashi, daga can yace "Zee kece?"
Tace " Sabir Aunty na nan kuwa?"
Aunty Amina?
Eh
Yace "mijinta ya koma Abuja da aiki ya akai?"
Okay shikenan, kafin ya sake magana ta kashe wayarta.
Khalid ta kalla tace "batanan."
Baki yadan bude yana kallanta kafin ya danyi wani abu daga cikin kirjinsa zuwa bakinsa, yace "yanzu ya za'ayi?"
Oho!
Fuskarsa ya hade yace "Then zan iya ajiyeki anan na tafi."
Kallansa tai da sauri sannan ta kalli waje tace "anan?"
Kai ya daga mata alamar eh sannan yace "kina tantama?"
Tace "shikenan, ka barni anan din."
Daurewa yai ya juyo ya kalleta duk fuskarta ta kumbura, idanunta sunyi jaa samansu sun kumbura yace "Am sorry na san ba hurumina bane sai dai yau ma zan sake ciga hurumin da ba nawa ba, wannan zabin kina gani shine ya dace?"
Dagowa tai daga jinginar datai tace "me kake nufi? Ba dai kana so kacemin na cigaba da zama da mijin da na kamashi da mace a cikin gidana ba?"
Gabansa ne ya fadi, abinda ya faru kenan? Yanayin fuskarsa ne ya canza dan ya tausaya mata, kauda kanta tai ganin kallan tausayin da yake mata tace "meye laifina? Kula dashi danai ko kuwa kula da mahaifiyarsa? Meye laifina dan na kula da mijina? A tunanina inayin daidai gwargwadon abinda zan iya bansan menene laifina ba........"
Hawayen da taji suna neman zubo mata ne yasa ta kasa cigaba da maganar, Khalid ne ya kalleta duk da tausayinsa daya kamashi bai hana cemata "kina tunanin duk abinda ya faru baki da laifi kenan?"
Kallansa tai bayan ta dake tace "fadamin menene laifina?"
"Wani irin rashin kula da rayuwar da bataki ba da kikeyi da har za'ace bakisan kanwar mijinki ba? Wannan wace irin rashin kula da gidanki ne?"
Shiru tai tana tunani, tabbas duk matsalar daga nan ta fara, datasanta da duk.....
Dakewa tai tace "Naji wannan ne laifina bayan shi kuma fa?"
Shiru yai yana kallanta kafin yace "komai daya faru rabi naki ne, sannan bakya tunanin gidanku ya kamata kije?"
Fuska ta hade sosai tana kallansa kafin tace " tafi ka barni anan.
Bai kulata ba yaja motar suka cigaba da tafiya itama haushi baisa tace komai ba.
Wayarta ta daga ta kira Bala.
Bala na tsaye a na canza key din gidan wayarta ta shigo, ya gaisheta.
Tace "sun tafi?"
Yace "a'a."
Takardar fa?
Bai nan komai ba.
Shikenan tace ta kashe wayar.
A bakin kofar gidansu yai parking, sannan ya kalleta yace " ki kwana anan gobe na maidake gidanki."
Kin kulashi tai bata kalleshi ba, fita yai daga motar shima ba tare da yace komai ba ya dau jakar ta a booth ya shiga ciki.
Da wani kallo ta bishi tana mamakin hali irin nasa, ko kadan baya burgeta namiji sai tsinanen zafin rai? Ita sam ta tsani namiji mai gadara da neman isa.
Khalid ne ya shiga ciki.
Yana shiga tsakargida yaga Asiya a tsaye tana kiran su Amie su fito su wuce islamiya, kallanta yai tana ganinsa ta matso tana yaya an dawo?
Eh Asiya in zaki wace kiyima bakuwa magana a cikin mota kice ta shigo.
Bakuwa? Mota? Kallanta yai bai amsa ba ya wuce ciki.
Su Amir na ganinsa suka gaisheshi suka fito da gudu suna sa takalmi.
Umma data idar da sallah ne a daki ta fito tace "Khalid? Kaine da ranan nan?"
Zama yai kusa da Abba yana cewa eh wlh.
Kallan Abba yai sannan ya kalli Umma dake kikarin zama, Abba yace "ya akai?"
Dan hannunsa yasa ya shafi keyarsa yace "matar danake ma aiki ne muka taho tare."
A tare sukace "ina?"
Khalid yace "ta samu matsala da mijinta ne shine na kawota nan kafin komai ya warware."
Fuskar Abba dauke da mamaki yace "iyayenta fa?"
Khalid yai dan shiru kafin yace "ba'a kusa suke ba, da alama kuma batada kowa a kusa."
Umma tai shiru kafin tace "kace ta shigo ne?"
Na fadawa Asiya, shiru sukai suna tunannin wannan abu.
Asiya data fito ne ganin mota a kofar gidansu yasa ta nufeta, Amir yace "Ya Asiya motar yaya ce?"
Bata kula su ba ta nufi motar.
Zainab dake ciki ta bude kofar tana kallanta, Asiya ta gaisheta cikin nutsuwa sannan su Amir ma suka gaisheta.
Kanwar sa?
Asiya ta daga kai tace "eh, ya Khalid yace ki shigo."
To, islamiya zaku?
Tace "eh Aunty."
Zainab tana tsaye tana kallansu gar suka wuce tai murmushi tace da alama age mate din su Nabila ce sai dai ta fisu nutsuwa, tunowa tai da fadan da sukeci haka kawai ta samu kanta da murmushi.
Kallan gidan tai bayan tazo jikin kofa ta tsaya, itadai ta kasa shiga ciki.
Abba ne ya kalli Khalid yace "ka shigo da ita bakowa ne zai iya shigowa gidan mutane kai tsaye ba."
Nan Khalid ya mike ya fito.
A waje ya ganta tana ganinshi ta hade rai, shima fuskarsa a hade take yace "ki shiga."
Wucewa gaba tai kai kace gidansu ne, tun daga tsakar gidan take mamakin gidan, gidane dan karami, soro inda dakin Khalid yake sai kofa ta ciki, kana shiga dan madaidaicin tsakargida ne wanda aka sumumteshi tsaf, daga gefe akwai rijiya, sannan bandaki a ta gaban rijiyar.
Daga can kusa da asalin cikin gidan kuma kitchen me a gun, gefen kitchen din kuma inda suke sa murhu ko gawayi.
Sai dai kidan a share yake tsaf, hatta gun wanke wanke an wanke gun tas, duk da ta raina gidan amma ta aminta da tsaftar gidan a haka suka shiga, Umma na tsaye a kan barandar tana ganinta ta fara lale lale da babbar bakuwa.
Zainab ta shigo cikin kunya.
Umma ta nemi data shiga cikin falan, Zainab ta shiga, Abba ne a zaune ta gani kafarsa daya babu yana jingine da bango duk da haka yana ganinta yace "barka da isowa."
Zainab ta zauna ta gaisheshi sannan ta gaida Umma, Khalid dake tsaye ya juya ya bar falan.
Tana ganin yabar falan kunya ta kara kamata, Abba ya kalleta bayan ya amsa gaisuwar yace "ashe abu kuma baiyi dadi ba?"
Kasa tai dakai batace komai ba, yace "bakomai ki zauna anan sai ki kira mahaifinki asan abin yi."
Gudum yin musu yasa kawai tace to.
Umma ce ta nuna mata dakin Asiya nan ta mike ta shiga, gaba daya itakam kunya ma takeyi, ya akai bata tafi hotel ba?
Umma ta shiga ajiye kawo mata abinci, kunya ta kara kama Zainab dole ta mike ta tayata ajiyewa.
Umma ta zauna kusa da ita tace "karki sa komai a ranki kiyi sallah kici abinci ki huta, Allah zai kawo mafita kinji."
Kallan Umma tai haka kawai tunanin Ummy ce a kusa da ita yazo mata, idanuntane suka ciciko a hankali hawaye ya zubo mata.
Umma ta kalli yanda duk idanunta ya kumbura, tausayinta ya kamata tace "yahkuri kinji."
Zainab ta share hawayenta sai dai ta kasa cewa komai, kawai jitai ta nasan Umma ta rungumeta ta rasa me yasa take ganin kamar Ummy ce a gun.
Umma ganin yanda take kallanta yasa ta fahimceta, rungumeta tai tana cewa "bakomai kinji, insha Allahu Allah zai kawo miki mafita duk da bansan me ya faru ba amma nasan ke mace ce ta gari."
Kamar ta tabo Zainab kawai Zainab tasa kuka, wannan kukan jitake kamar a jikin Ummy take yinshi.
Khalid wanda ya fita siyo juice a shagon kusa dasu me ya dawo rike da leda, yana shigowa yani yanda Zainab ke kuka, kusa da Abba kawai ya ajiye ya fita zuciyarsa na tausaya mata.
Wayar Abba ya dauka ya fita Yana fita ya daga waya ya kara kiran Razy.
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[11/25, 3:59 PM] Maman Zara Whatsapp: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{32}
**********
Goggo na zaune tana ta cusa abinci kana ganin kasan cin dole da cin yunwa take ma abinci, Adam na zaune a gefe cikin takaici yace "yanzu Goggo har kinsamu damar dafa indomie kina ci? Muda rayuwarmu take neman shiga garari?"
"Kana sane ko jiya tsinaniyar yarinyar nan bata banni naci abinci ba so kake na muti kafin ma samu ba Zainab hakuri."
Kallanta yai gaba daya duk ya canza, kana ganinsa kasan a birkice yake, yace "Goggo koza'a mutu Zainab bazata taba komawa dani ba, kema kinsani, yanzu akam takardarta wlh sai ta kaimu kotu."
Goggo ta tsame hannunta daga plate din ta kalleshi tace "duk ba kai kaja mana wannan masifar ba."
Da sauri yace "wai kin dane zancen ni naja mana ki nemo mana mafita ko kuwa? Abinda ya faru ya faru amma Sai kara tusawa kikeyi, dana sani ke kanki kinsan nayi, haryanzu bansan uban me ya shiga kaina ba."
Goggo ta kalleshi bayan tasha ruwa tace "nidai mafita daya ce yasin bazan koma kauyeba, kasani tunda kai aure matarka ta dakoni ko da wasa ban sake zuwa can ba, kanina inya ishen da zancen Sadiya nasan abin makaranta kana kallo Zainab ke taimakawa mu tura, mo hanyar ban komaba kuma wlh yanzu bazan koma ba."
Cikin masifa yace "nima cewa nai mu koma? Tambayarki nake yanda zamuyi."
Itama cikin masifa tace "kaina zaka huce? Uban wa yasa ka ja mana?"
Haushi ne ya kamasu duka kowa yai shiru.
Adam ta kalla sannan tace "wai kai da uban me kake da kudin da take baka duk wata?"
Haushi ne ya kamashi bai tanka mata ba.
Goggo ta sake cewa "ko kuma me kale gani idan ka bata takadar sai dai kace mata bazaka bata takardar saki ba harsai ta barma gidan nan."
Kallanta yai da sauri yace "mene?"
Goggo tace "kana gani dai korarmu za'ai nan da awa anjima kaga dai key ake canzawa, kuma wlh tunda ta furta ko za'a mutu sai ka bata takardarta, gwara muma mu cafki gidan, ai harga Allah kaima cutarka kuliyarcan tai."
Shiru yai yana kallanta kafin yace "kina tunanin Zainab zata yadda?"
Tace "karma ta yadda, in bata yadda ba kace mata kuje kuton ai ita idan gari ce aikin gidan tv take mutane dayawa sun santa bazata taba bari sirrinta ya fito duniya ba, kasan yanda take san aikin nan nata."
Kai ya jinjina cikin gamsuwa sannan yace "Goggo Allah banasan rabuwa da Honey."
Yai maganar kamar mai shirin kuka.
Tace "inka kara cemin Honey sai na wankeka da mari shasha shan banza, kai dai wlh banga amfanin ka ba, sam ni na rasa banzan hali da sokon tunaninka."
Adam yai shiru gaba daya hankalinsa ya kasa nutsuwa, wani bangare na zuciyarsa na kwadaitamai abinda Goggo tace.
Goggo ta kalleshi tace "tu ra mata sako a waya, ka fada mata in tanasan takardarta sai ta baka gidan nan."
Da sauri yace "yanzu?"
Tace "da sai yaushe?"
Nan ya dako waya yana kallanta.
鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�
Rasy dake kwance Bash na gefenta yana neman kai hannu cikin rigarta ne ta buge hannun sannan ta kalli wayarta dake kara, dagawa tai tace hello.
Khalid yace "Raziyya kinga dama kin daga?"
Nan ta fahimci waye tace "Drivern mota kiran wayar na menene? Na tabbatar banci bashinka ba."
Murmushi yai yace "kin bayyana kanki ko sai naje gidanku na fadawa iyayenki abinda kikeyi?"
Da sauri ta mike tsaye tace "gidan mu?"
Yace "eh kokin dauka bawanda zai san inda gidanku yake?"
Kumbura fuska tai cikin bacin rai, Khalid yace "mu hadu dake gobe a kano, zan kiraki inji inda kike, kada ki kuskura kik'i daga wayarki inba haka ba zan wuce Naibawa yar lemo na fadawa iyayenki abinda kikeyi, Ahhhhhh bansan ya zasuji ba insuka ji, bayan yayarki ta rasu, ina tsoron halin da zasu shiga."
Yana kaiwa nan ya kashe wayar.
Cikin takaici da bacin rai tabi wayar da kallo, a Zuciye ta cillar da wayar kan gado sannan tai wata kara mai karfi tace "Kyankyasan nan......."
Bash ne yasa hannu zai riketa kafa ta sa ta haureshi a matse matsin kafarsa, wani irin kara yasa shima tare da durkushewa a gun.
*********
Umma zama tai a gabanta Zainab Taci abinci sannan ta fito daga dakin bayan taga ta zauna tana hutawa, Zainab tabi bayanta da kallo cikin wani yanayi.
Abba dake falo ne ya kalleta yace "Uwar 'ya an fito?"
Zama tai kusa dashi cikin tausayi tace "da alama batada wanda zata dogara dashi taji dadi."
Kallanta yai yace "kamar ya?"
Kai ta girgiza alamar rashin sani tace "haka kawai nakeji kamar ta dade cikin kewa tana neman wanda zai dubeta."
Shiru Abba yai cikin tausayinta shima.
Zainab ta kalli hoton Ummy a wayarta tai murmushi tare da kwantar da kanta akan dan karamin gadan Asiya, Ummy na!
Ta fada tana shafar hoton, sako ne ya shigo wayarta, kallan sakon tai cikin mamaki ta kara karantashi.
Gaba daya mamaki ne ya kamata, duk da tasan karshen zamanta da Adam yazo amma bata taba tunanin zai nemi bata takardarta bugu daya ba, sannan abinda ya kara bata mamaki wai ta bar mai gidanta?
Wata dariyar bakinciki ta saki tace "Ummy wace rayuwa nai duk tsawon shekaru na???? Me yasa nake gani kamar duk wahalar danasha bata biya min komai ba??"
Umma ce ta turo kofar dakin, Zainab ta kalleta tare da gyara zama, Umma ta ajiye mata ledar juice din tace " badai tunanin kike ba?"
Kallanta tai tana san fada mata abinda ke ranta amma gani take daga ganinta sainta zake???
Kai ta girgiza tace "a'a."
Umma tace "ko nazo mu zauna tare? Dama na fita ne na dauka kina san hutawa."
Zainab tai murmushi tace "zan kwanta ki huta kema."
Nan Umma ta juya tana murmushi.
****
Tana fita Dady ya kirata a waya, kallan wayar tai kafin ta daga.
Daga can yace "Zainab ashe kin kira?"
Murmushi tai tace "eh na kira dazu."
Yahkuri bangani ba sai yanzu dana dau waya zanyi waya ma ga kiranki.
Shiru tai kenan Basma batace mai komai ba ko me?
Tace "dama kira nai mu gaisa ta daga tace kana toilet."
Oh Basma ta daga? Ai bansani ba saboda ina fitowa na taho kila shiyasa bata samu damar fadamin ba."
Zainab tace "bakomai."
Ina aiki ne in na tashi ma kira, kafin ta kara magana
ya kashe wayar da alama aiki yake sosai, sai dai ba karamin sanyi jikin ta yak ba ta kwanta kawai ta rufe idanunta.
馃槳
***********
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[11/27, 7:28 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{33}
Wajen sallar magrib su Asiya suka dawo, har lokacin Zainab na zaune tana nazarin wannan rainin hankalin, yanzu ne ta tabbatar ma kanta baxata sake kuka akan Adam ba domin kuwa ya nuna mata dama can ba santa yake ba abin hannunta yakeso, duk da tasan hakan kafin auransu amma ita a nata tunanin zaman da sukai yanzu yaci ace tafi abin hannunta daraja agunsa, daga wannan lokaci tayi alkawari hawayenta bazai kara diga akansa ba.
Sallama taji tare da dan turo kofa, amsawa tai tana kallan kofar.
Asiya ce ta shigo har kasa ta tsuguna ta gaisheta, Zainab ta amsa cikin jin dadi sannan tace "kun dawo?"
Eh Aunty
Ta fada tana mikewa, Zainab ta danyi shiru kafin tace "kiyi hakuri bakuwa ta tare miki daki."
Murmushi tai tace "bakomai Aunty."
Kayanta ta dauka ta fita daga dakin, da kallo ta bita tanaji inama su Nabila na nan ta nuna musu mutsuwar yarinyar, haka kawai ta samu kanta dayin murmushi.
Fitowa tai zatai alwala ganin magrib tayi, kunya takeji sosai gani basuda hadi da juna gashi sun amsheta kamar yar su.
Tana bude kofa taga Umma a bakin kofar, dariya sukai a tare, Umma tace "yanzu dama zance ki fito kiyi alwala, ashe kin taso."
Dariya tai batace komai ba, a tare suka fito ta kara gaida Abba sannan suka fito tsakar gida.
Umma ta wuce ta duba miyar dake kan gawayi, shiru Zainab tai tana kallan yanda take gyara wutar, kafin ta wuce dan toilet din, alwala tai sannan ta fito.
Asiya dake shimfida babbar tabarma a kan baranda ne taji tace "Umma yaya ya fita ne?"
"Bansani ba wlh sai dai ki duba dakinsa."
Umma ta kalli Zainab tace "Kin fito?"
Zainab tace eh tare da wucewa ciki, bayan ta ajiye botar.
Bayan Sallar Isha'i tana zaune rike da wayarta tana kara maimaita sakon Adam, Asiya ce ta shigo dauke da tiren abinci ta ajiye mata, sannan ta juya.
"Kazo Danbatta gobe gidansu kwaro, naji yanda zan bar ma gidan."
Haka kawai ta turamai ta ajiye wayar tare da kurawa kwanan gabanta ido tana tunanu, kauda tunanin komai tai a ranta sannan ta bude kwanan.
Tuwo ne na semovita miyar kubewa danya, murmushi tai tana tuno rabanta da tuwo, dan sam Goggo da Adam basa san tuwo shiyasa ma ba'ayi sai jefi jefi.
Tana cin abincin tana jiyo hirarsu a tsakar gida, jin gaba dayansu ne a wajen yasa idanunta suka dan ciciko tunda take a tsawon rayuwarta bata taba zama da iyayenta da kanenta ba ana hira haka.
Haka ta ci tuwon sosai, jin kunyar sai dai a kawo mata a dauke mata ne yasa ta kwashe kanukan ta fito.
Hira sosai suke ana tsokanar Asiya tana ta rantsuwa, tana ganinta ta mike ta anshi tiren.
Umma ta kalleta tace "Zainab zo ki zauna anan."
Kallan Khalid tai wanda kansa ke kan bare gujiya, wacce sai yanzu ta kula da abinda ake, Umma tace "kin iya ci?"
Kallan gujiyar tai dan bata taba ci ba sai murmushi kawai datai, Abba ne yai dariya yace "da alama bata taba ci ba."
Amir ya sa dariya yace "Abba yanzu a duniya dama akwai wanda bai taba ci ba?" Ya fada yana cin wani.
Asim ya dan ture shi yace "wlh a santi yake wannan da rake ake sha ba'a san tsoyar dazai ba."
Dukansu ne suka sa dariya har ita zainab din wanda ta kaudakai tana dariya.
Takowa tai a hankali ta zauna daga kusa da Asiya, Umma tace "ko a dauko miki pillow?"
Da sauri tace "a'a."
Khalid ne ya kalleta kadan sannan ya dan tura kwanan dan gefensu kadan.
Amir ne ya ja kusa dasu yana cewa Yaya to ita Aunty da kakema Tuki data dawo nan gidan kenan ka daina aikin?"
Abba ne yadan talle mai keya yana cewa "to Barrister uban san jin magana."
Nan suka cigaba da hira ana dariya, Zainab kam gaba daya abin sha'awa yake bata, har sai wajen 9 Khalid ya mike ya koma daki, nan suma suka sake hira kadan kafin suka shiga ciki.
Asiya ta kalla tace "ina zaki?" Ganin ta dau bargo tana neman fita.
Asiya tace "Umma tace na kwana a dakinsu Amir su zasu kwana a falo."
A'a kwanta anan, ta fada tana nuna mata dakin.
Asiya tai murmushi tace "to Aunty."
Bargonta ta shimfida a kasa, ta sa pillow sannan ta fito ta fadawa Umma yanda sukai, ba karamin dadi Umma taji ba.
Can wajen 11 Asiya nata baccinta Zainab tai shiru tana kallan yanda maganin sauro ke ta fitar da hayaki, mikewa tai ta sa hijab dinta ta fito falo a hankali ta fita waje.
Ido ta kurawa sararin samaniya wanda farin wata ya haskashi sosai.
Gefen baranda ta zauna ta zubawa sama ido tana tuno yanda tai rayuwarta da yanda ta wahalar da kanta da mahaifinta akan abinda batada hakki akai, yanzu gashi ita abinda take da hakki akai ma an nuna mata rashin matsayinta.
Tunda ta fito yake kallanta ta jikin window din dakinsa, yana zaune a daki yana karatun littafan daya siyo na aikin gidan tv da zasuje jarabawa, tunda harkar mass yai yana bukatar sani a wannan bangaren.
Haka kawai idanunta suka samu kansu da kallan window din dakin, ganinsa tai ta window, dan dakinsa haske hake tal da kwan wuta.
Mikewa yai ya fito daga dakin sannan ya nufo ta "akwai abinda kikeso ne?"
Kallansa tai bata san sanda tai wani murmushi ba tace "yau ya da magana ba kamar yanda ka saba ba?"
Dan kansa ya juyar gefe baice komai ba, kallansa tai sannan ta nuna mai guri tace "inasan tambayarka abu."
Kallanta yai sannan ya zauna daga gefe tare da kallan gabansa inda rijiya take.
Itama gabanta take kallo tace "wacece yarinyar nan?"
Raziya sunanta.
Raziyya! budurwarsa ce?
No.
Then?
Yayarsa ce budurwarsa.
Kallansa tai da sauri tace "kamar ya?"
Bai kalleta ba haryanzu yace "I don't know the details."
Shiru tai kafin tace "it doesn't matter to me anymore"
Yanzu kam kallanta yai yana mata kallan tambaya, murmushi tai na takaici sannan tace "kana tunanin zan cigaba da asarar rayuwata saboda mutum irinshi?"
yace "kin tambayi kanki waya maidashi haka?"
Wani kallo tamai tace "Me kake nufi?
Ta tambaya tare da canza fuska, yace "I can't tell, ki duba ki gani da kanki."
Kallansa tai sannan tace "aiki yi ne bai samu ba, ko ni na hanashi samu?"
Samun kansa yai da wata dariya sannan ya mike tsaye yace "Yana nema kenan?"
Shiru tai tana kallanshi, tunda take ta taba jin inda Adam yai applying?
Kallanta ya sake yi sannan yace "Sai da safe."
Da ido ta bishi har ya wuce soro, hannu tasa ta dafa kanta, a hankali ta saki wani murmushin takaici, dan tabbas bata ma taba jin inda yai applying ba, sai dai in ta tambaya yace "yayi bai samu bane."
Haushin kanta ne ya kamata kenan tun ba yanzu bama suka maidata sokowa?
************
Bala ne a tsaye a bakin kofa yace "Goggo ku nake jira zan kule na kwanta."
Adam ta kalla dake gefe a kwance a kasa kamar mara lafiya haushi ya kamata, kafa tasa ta shureshi ya dago yace "wai Goggo meye haka?"
Kwanciya ma kai? Taga sakon?
Wayarsa ya dauka sannan ya kalla, da sauri ya kalli Goggo yace ta gani.
Me tace?
Ta fada tana saukowa.
Nan ya fada mata abinda tace, wata irin dariya tai tace "Alhamdulila dama nasan yarinyar nan yar albarka ce."
Adam ya kalleta yace "Goggo kina ganin hakan ne ya dace?"
Wani banzan kallo tamai tace "da ubanwa yasa ka soma yi?"
Haushi ne ya kamashi ya kalleta zaiyi magana muryar Bala ta kara katseshi "Dan Allah ku fito na rufe."
A zuciye ya mike yaje waje, kallan Bala yai yace "idan baka matsamin daga nan ba sai na koreka daga wannan lokaci."
Bala yace "Hajiya tace......."
Muryar Goggo yaji tace "ita Hajiyar ce tace ka tafi sannan daga gobe gida ya zama namu naga inda zaka cigaba da aiki."
Jikin Bala ne yai sanyi ya koma daki.
******
Washegari da sassafe Goggo ta tashi Adam ya taho danbatta.
Khalid nagun Salmanu suna wani aiki, yana so ya gama ya je kano gun yarinyar nan, yaji meke faruwa ya fadawa Adam a samu su fahimci juna su daidaita.
Duk da yasan ba huruminsa bane amma yana ganin hakan ne ya dace.
Adam sai da tambaya ya isa gidansu Khalid dam ya kira wayarshi a kashe.
Zainab na zaune a daki ko abinci ta kasa ci tana jiran zuwansa dan tasan tabbas da wuri zaizo.
Kamar daga sama taji Amir na fadawa Umma wai wani yazo yana waje, gun Aunty yazo.
Hijab dinta ta zura kawai Umma sai ganinta tai ta fito.
Dariya tai tace "ashe kinaji?"
Tace "eh Umma, ina kwana?"
Umma ta amsa ta gaida Abba.
Umma ce tace "mai gidan ne?"
Zainab tace eh, murmushi Umma tai tace "sai hakuri, nasan kema dole kiso ki koma, zuciyar mace rauni gareta."
Batace komai ba ta taso ta fito.
Adam na tsaye a jikin motarta yana karewa unguwar kallo ta fito.
Kallanta yai sannan yace "Honey!"
Bata ko tankashi ba ta bude mota ta shiga, shima shiga yai ya zauna mamaki ne ya kamashi dayaga ta tada motar taja sun fara tafiya.
Baice komai ba har suka fita dan wajen gari kadan, gefe ta gangara da motar sannan ta juyo ta kalleshi, idanunta ta dan rufe saboda abinda take tunowa, jitai ya kamo hannunta.
Da sauri ta bude ido ta kalleshi, Honey ki yafemin dan Allah, wlh kuskure ne.
Hannunta ta fizge sannan tace "kuskure? Hakane kuskure ne wanda ko wani dan Adam zai iya aikatawa, yanzu bani takardata na baka takardun gidan."
Da sauri ya kalleta yace "wai da gaske kike?"
Tace "kai kana tunanin zan iya zama a gidan daka kwanta da wata? Watan ma ba matarka ba?"
Shiru yai tare da sa kansa kasa, safe ta bude ta dauko papper da biro ta mikamai, tace bani ga takardun gidan a ciki."
Kallanta yai gaba daya jikinsa yai sanyi, yana hawaye ya rubuta saki daya, tace "daya? A haka zan baka gidan?"
Haka ya rubuta saki uku yana hawaye, amsa tai sannan tace "nagode da kyautatawa da amanata daka rike, yanzu na fahimci kula da kai da mahaifiyarka danai ba abinda ya dadeni dashi, ko da yake ance laifinane."
Kai ta jinjina tace "in aka duba dakyau hakan ne, kallansa tai tace "fitarmun daga mota."
Kallanta yai yace "takardun gidan?"
Wata dariya tasa tace "ohh"
Sannan ta sake kallansa ta hade rai tace "Kasan me ake kira da duk yanda akai da jaki sai yaci kara?"
Kallanta yai tare da firfito da idanunsa, tace me? So kake na fadama waye jakin?
Hucin fushi ya fara yi yace "ni kenan?"
Tace "kila."
Haushi ne ya tukeshi yace "Yanzu kina nufin dama ba gidan zaki bamu ba takardarki kike so?"
Dan kai ta kawai sannan tace "kai a naka haukar sai kawai na baka gidana saboda ina tsoronka? In dan saki ne ba ka san zan ita kaika kotu kaban dole ba? Da kai da wanda ya baka shawarar ka koma ka fada mata ta dinga yin tunani kafin ta bada shawara.....Ahhh bansan ko zaku iya tunanin ba dan na fahimci abin kamasal."
Kallansa ta sakeyi tace "fita!"
Adam yatuno basu da inda zasu, kallanta yai yace "Honey ki taimaka wlh bamu da inda zamu, dan Allah ki taimaki rayuwar mu."
Fita!
Honey ki taimaka mana dan All.......
Get Out nace.....
Yanda tai maganar cikin tsawa sai daya sani razana nima, ba Adam kadai daya fita ba nikaina sai da naji ina neman hanyar tafiya馃檴馃毝馃徎鈥嶁檧
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[11/29, 2:03 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
_Faty Muktar Allah ubangiji ya jikan Baba ya kai haske kabarinsa, yasa mutuwa ta zama hutu a gareshi Ameen suma Ameen_
{34}
Knocking din motar ya fara cikin tashin hankali, Zainab tana zaune ta zubawa takardar ido, bata taba tunanin wannan lamarin ba, lalai Adam, kallansa tai yanata jijiga kofar motar, zuge glass din tai ta kalleshi, da sauri yace "Honey ki taimaka ki ban takardar dan Allah ki yafemin na tuba wlh, Honey ki taimaki rayuwata dan Allah."
Kallansa kawai takeyi, Honey dan Allah ki yafemin, wlh wlh bansan meya shiga kaina ba.
Daurewa tai tace "ka biyoni inda ka ajiye motarka ka dauka"
Da sauri yace "Honey ki bari mu tafi tare, dan Allah ki tsaya ki........."
Jan motar datai ne tai gaba ya sashi zubewa a kasa wani zazzafan hawaye ne ya zubomai.
Zainab tana zuwa kofar gidan ta ajiye motar a inda ya ajiye, tunanin wanda zataba key dinshi tai sannan tai hanyar ciki, tai sa'a sai ga Amir nan.
Yana ganinta ya karaso da gudu yana cewa "Aunty Umma nata nemanki."
Kallansa tai sannan ta mikamai key tace "Amir ka tsaya a jikin motarnan zakaga wani yazo yana neman key ka bashi wannan."
Amsa yai sannan tai ciki, tana shiga taga Umma a tsaye tana zagaye, Umma!
A hankali ta kirata tana kallanta, da sauri Umma ta taho, itama Zainab ta nufo ta, sai da suka matso kusa da juna sannan Umma tace "Alhamdulila dan na tsorata da akace bakya nan a waje ina tsoron kar wani abu ne ya faru kikai wani gun."
Tsayawa tai tana kallan Umma, ashe haka uwa ke da dadi?
Murmushi ta mata sannan ta nuna mata takardar tace "ya sakeni Umma."
Da sauri Umma ta amsa, da yake ba boko tai ba sai dan wanda Khalid ya nuna mata a gida ta dai dan fahimta gane cikin kokonto da sauri ta kalleta tace "Har Uku?"
Murmushi Zainab ta sakeyi tace "Eh Umma."
Shiru Umma tai tana kallanta, kafin tace "ki shiga ciki ki sanar da mahaifinki."
Kai ta daga sannan tai ciki, Umma ta bita da kallan tausayi sosai dan har sai dataji idanunta sun dan ciko.
Gun Abba ta nufa ta sanar dashi yanda akai, hankalinsa shima ya tashi yace "wannan wani sakaram miji ta samu dahar zaiyi saki uku lokaci daya?"
********
Adam kam yaci uban tafiya yana tafe kamar mara lafiya, dakyar ya iso ga uban yunwa dake damunshi, yana zuwa Amir ya bashi key ya tafi ball dinsa, shiru Adam yai yana kallan gidan data fito dazu, gaba daya ya rasa abinda xaiyi sai dai yasan duk abinda zaice yanzu a banza yake gwara yaje gun Goggo su samo shawara.
Jan motar yai ya fito, a hanya ya tsaya yasai biscuit da juice ya cucusa sannan ya karasa gida.
Bala na tsaye yana kallan Adam dake ta danna mai horn, Bala na kallansa bai ko binta kansa ba yana jin radio dinsa, haushi ne ya kama Adam ya fito a zuciye ya nufi Bala yace "kai Bala ka bude min gate ko sai na ci mutuncin ka?"
Bala cikin maganarsa ta hausar yan niger yace " Hajiya ta kira yanzu tace ku bar mata gida dan haka bazan bude ba."
Adam cikin kofula ya nufoshi, Bala ya kalleshi yace "ka tabbatar zaka iya dukana?"
Kallansa yai kamar zai karasa gunsa sai naga ya bude gate ya shiga, Bala yace "awa biyu na baku ku fito daga gidan nan, dan Hajiya tace inbaku fito ba na dau hukunci da kaina, sannan kunsan mu buzaye ba hakuri, nan da awa biyu yan sanda zasuzo inkunga dama karku fito."
Adam ya wuce ciki, haryaje zai shiga ya dawo da gudu ya zare key din motarsa dan dama ya saba wannan shirman balle in a gidane sau dayawa ma baya rufe motar.
Bala ya bishi da kallan takaici yana tuno abinda suka mai jiya, har fara yake su wuce awa biyun nan dan wlh sai ya rama wulakancinsa.
Adam ne ya shiga falo, Goggo na zaune ta soya dankali da kwai tana ci tana kallan tv, daga bakin kofa ya tsaya ya zuba mata ido, gefe ta hada tea dinta mai kauri.
Kallansa tai tace "Adam ka dawo?"
Kasa mata magana yai sai kallanta kawai da yake, kallansa tai tace "matsalarka kenan sai kai abu kazo kana nadama, kai dai dakai sa'a matarka nasan aikinta in ba haka ba uban wa zai bar ma gida?"
Haryanzu kallanta kawai yake tana cin abincinta tana magana, ganin yaki shigowa ne yasa tace "karka damu duk wanda yai saki da wanda aka saka sai yaji haka nadan wani lokaci amma komai zai warware a hankali, kazo kaci abinci naka na kitchen."
Ganin takaici yaki karewa ne yasa ya matso ya kashe tv din sannan ya kalleta rai a bace.
Kallansa tai tana kurbar tea tana harararsa kafin tace "uban wa yasa ka aikata? Da zaka nemi hucewa akaina?"
Huci ya fara yi yana kallanta, bata tankashi ba dan gani take duk saboda ya saki matarsa ne, abincinta ta cigaba daci, kawai jitai yasa kuka.
Kallansa tai tace "tashi kaje daki kayi abinka ni karka sani a gaba kamar ni na kashe ma aure."
Cikin masifa yace "bake kika kashemin ba amma kinada babban hannu a ciki."
Kallansa tai tace "a ina kenan?"
A zuciye yace "ta kwaci sakinta bata kuma bamu gidan ba, yanzu Bala yace mu fita nan da awa biyu."
Cup din tea din dake hannunta ta yar bata sani ba, tea din ya zube dan har kan cinyarta, ko zafin bataji ba dan ma ba tafashashe bane, Adam ne ya matso yana kuka yace "Goggo ya zamuyi?"
Kallansa kawai take kafin tace "Sakin ka bata kafin ta baka takardun gidan?"
Yace "cewa tai in na bata zata bani."
Baki kawai ta bude tana kallansa, yacigaba to na bata kuma ta koren dan da kafa ma na nufi gidan.
Nawa ka mata?
A hankali yace uku........
Wani wankenken mari yaji ta zabgamai, da sauri ya kalleta, rufeshi tai da duka ta ko ina da hannu biyu, tana dukanshi tana wannan wannan nikam bakin cikinka ne zai kasheni ban taba ganin mutum wanda gaba daya baida lissafi da tunani ba irinka, ka kwashe komai na gadon mu ka cinye a tsinanen karatun da ba abinda ya tsinana mana, kayi aure mun taho nan tunda aka bikinka ko kauye bamu kara zuwa ba sannan yanzu kazo kana cemin ka bada saki uku ba tare da ko daki biyu mun samu inda zamu zauna ba?
Adam kuka kawai yake yana cewa "na dauka zata bani wlh."
Daina dukanshi tai kawai ta fashe da kuka wiwi, Shikenan rayuwarmu ta kare munga ta kanmu."
Adam yana kuka yace "Goggo nanda awa biyu yan sanda zasuzo su koremu."
Kallansa tai kamar ta kara jibgarsa sai dai a wannan lokacin mafita take nema, wayarta ta dauko ta hau kiran Zainab, ta roketa ko dakin waje ne ta taimaka ta barsu su zauna, duk yanda ta kira Zainab bata dauka ba, daga baya ma ce mata akai wayar a kashe take.
Hankalin Goggo ya sake tashi matuka.
Kallan Adam tai da sauri tace "tashi mu hada kaya, duk wani abu mu tattare mu debi rabanmu."
In muka kwashi kayan ina zamu?
Tace "kai ka tafi wani gidan ka kwana ni zani gidan Hajiya bilki na dan kwana biyu sai musan abin yi."
Kallanta yai yace "ni banida inda zani, Ziyad bayanan sannan ko yana nan ma a gidan iyayensa yake kwana anan, Goggo ki taimaka ki tafi dani"'
Wayarta ta dauka ta kira Hajiya bilki sai dai tai rashin sa'a domin bata kasar sunje sari dubai.
Hankali a tashe ta kalli Adam, nan ta sake kiran wata kawarta, ita kuma jin zatazo kwana yasa tace tanada baki, Goggo hankalinta ya tashi nan fa ta shiga kiran duk nambobin kawayenta dana kusa da wadanda ba wani ma shiri suke ba, sai dai duk wanda yaji kwana zatazo sai ya fara kame kame da alama dukansu bamai san tazo kwana.
Hankalinta a tashe tace kafin yan sanda su wulakantamu a unguwar nan ka tashi mu kwashe kaya tunda kunada yar motar nan masan yanda zamuyi.
Haka suka kwashe kaya, Goggo sai data kwashe duk wani fruit da juice na gidan, taso kwasan su dankali Adam yace a ina zaki dafa inkin dauka? Haka ta ajiye amma sai data kinkimi indomie da taliya.
Haka su fito sukai ta lafta kaya a boat din mota a waye, Bala na ganinsu ya fara waya wai da yan sanda yana cewa kuna hanya? To sai kun iso.
Goggo naji suka sake rudewa, haka suka fito Adam najan Goggo tana makalewa dan itakam wannan gida bata san barinsa, suna zuwa gate ta koma ciki da gudu tana kuka.
Falo ta koma ta zauna akan kujera, Bala da Adam ne suka biyota, Bala yace "Goggo kin fito ko sai na radeki?"
Kallansa tai tace "ka radeni amma bazan bar gidan nan ba."
Dariya yai yace "to ki zauna bari su karaso."
Adam ya kalleta yace "Goggo?"
Wani mugun kallo tamai tace "nikam ka ciceni wlh, kai dayin tsiya ni da shiga tashin hankali?"
Adam zaiyi magana sukaji ana bubuga kofa, kallanta yai da sauri yace "gasunan ki fito kafin a toxartamu."
Mikewa tak ya jawota tana tafe tana tirjewa kai kace karamar yarinya ce, a haka suka isa gate, Lokacin Bala ya bude musu.
Kallansu sukai sannan suka kali Bala ogan yace "wad'an nan Hajiyar take nufi?"
Bala yace eh
Kallansu yai yace "kum wuce ko kuwa?"
Haka Adam yaja Goggo ya cusata a mota suka tafi."
Bala ya bisu da harara badan Hajiya tace duk abinda suka dauka karya hana ba ai da sai ya kwashe kayan da suka kwaso.
Suna tafe a hanya goggo na hawaye, daga ta tuno sai ta make Adam.
*******
Khalid kam wanda baisan abinda ake ba daga gun aikinsu da Salmanu ya wuce tasha ya hau kota zuwa kano, yana isa ya kira Razy wacce gaba daya tun jiya take cikin tashin hankali, haka ta daga cikin takaici, Khalid yace kina ina? Ko kina gidanku?
Da sauri tace "ina Tarauni, nan ta sanar dashi inda take."
Haka ya hau adaidaita ya karasa gidan data kwatantamai sannan ya kirata.
Fitowa tai dan tun jiya ta kori Bash ita kadai ce a gidan, a kofa ta ganshi a tsaye, baki tadan tabe ganin ko聽 mota bashi da ita.
Kallansa tai tace "anan zamuyi maganar?"
Yace "eh"
Kallansa tai tace "ko ka shigo ciki?"
Kallanta yai yace "bana shiga gidan karuwai."
Labanta ta ciza cikin takaici tace "to anan zamuyi maganar?"
eh.
Haushi ne ya kara kamata ta kalleshi rai a bace, jingina yai da bango, tace "ka shigo jikin gate din to banasan sirrina ya fita ne."
Yanzu kam ya dan kalleta sannan ya dan shiga ya tsaya daga jikin gate din.
Kusa dashi taje ta tsaya, kallanta yai yace "Me nene tsakaninki da Adam da har kika lalatamai rayuwa?"
Hannunta ya kalla wanda ke kokarin taba kirjinsa, kallanta yai sannan yai wani murmushi yace "me? Nima seducing dina zakiyi?"
Cikin kallan jan hankali tace "kai ba namiji bane."
Biro ya ciro ya ture hannunta dashi sannan ya kalleta yace "you can't seduce me ko kayanki kika cire a gabana."
Kallansa tai tace "do you have that confidence?"
Kai yadan karkace ya daga mata kadan sannan yace "you are not that attractive bansan ya akai kika jan ra'ayin maza ba, ahhh na tuna suma tunaninsu ba daya yake ba."
Fuskarta ce ta canza, ranta yakai matuka gun baci tace "am not that attractive?"
Yace "badai sun miki karya akan you are ba?"
Yanda take kumbura take hura hanci ne yasa yasan taji haushi sosai kallanta yai yace "fadamin menene tsakaninku?"
"Kai meye tsakaninka da Zainab? Meye naka na shiga abinda bai dameka ba?"
Kallanta yai yace "inje Naibawa?da alama can zan fi jin komai."
Da sauri tace "zan fadama."
Kallanta yai yace "meye tsakaninku?"
Bakimta ta ciza idanunta suka ciko tace "kasan bakar rayuwar da muka fuskanta akansa?"
Kallanta yai baice komai ba, hawayen da suka zubo mata ta goge sannan ta kalleshi idanunta na kara cikowa tace "Abinda ya mana ko rabinshi ban mai ba, mu gaba daya rayuwarmu ya salwantar shifa? Rabashi kawai nai da matarsa."
Kawai? Ya fada yana kallanta, kome ya muku meyasa baki fadamai ya nemi yafiya ba in har bada saninsa bane?"
Yafiya? Ta maimaita sannan tasa wata dariya tace "gun wa? Gun wacce ta rasu? Ko guna? Ko gun iyayen mu?"
Kallanta yai yace "Raziya!"
Yanda ya kirata ne yasa ta zubamai ido, wannan karan shine lokaci na farko data mai kallan mutunci, murmushi tai na takaici sannan tace "Zan fadama yanzu."
Kallanta yai sannan ta sake murmushi ta bude baki zata fara magana..........
*********
Hankali a tashe Dady yace "saki?"
Zainab tace "eh dady yanzu na amshi takardar."
Cikin fada yace "wani irin hauka ne wannan? Taya mutumin da kece wahalarsa zai sakeki ba tare da dogon nazari ba? Me kikai haka?"
Tace "ba abinda namai."
To fadamin meya faru haka? Yanzu zanyi booking flight zan taho gidan nazo na daukeki.
Da sauri tace "inje ina?"
Ki taho nan mana, ina zaki zauna ke kadai kiyi idda?
Tab ai dataje su zauna gida daya da Basma gwara ta zauna ita kadai, da wace fuska zasu kalli juna a gidan? Gasu Nabila basa nan bare su rage musu matslar zaman?
Dady ne ya katseta meya hadaku?"
Shiru tai tana tunani, ta ina zata iya cemai ta kamashi da mace a daki?
Daurewa tai tace ya samu canjin ra'ayi na zuciya ne, sannan nima na gaji da zaman,
Canjin ra'ayi? Gajiya da zama?
Kina gidanki? Zanzo anjima.
Da sauri tace "bana gida Dady."
Cikin mamaki yace "kina ina?"
Ina gidan ina gidan.... can tace "gidansu wannan driver din."
Mamaki ne ya kamashi yace "turon da Address zanzo."
Yana kaiwa nan ya kashe, idanunta ta runtse, Umma ce ta kwankwasa kafin ta shigo.
Zainab ta kalla wacce ke rike da waya, abinci ta ajiye mata sannan ta xauna kusa da ita ta kamo hannunta.
Zainab ce ta kalleta cikin jin dadi tace "Umma!"
Murmushi Umma ta mata tace "bakomai, Allah na tare dake."
Kai ta daga da sauri tace "Umma menene laifina? Dan na kula dasu? Danki yace komai laifinane."
Ta karasa tana hadiye kukanta.
Umma tai murmushi tace "kyale wannan shi dama haka yake fadar magana dan ran mutum ya baci."
"Eh mana haka yake duk sanda yazo sai ya konan rai"
Umma tace "kingani ko? Kyaleshi haka wannan halin nasa yake."
Zainab tace "ga fadar bakar magana ba ruwanshi da yanda mutum zai ji."
Umma Tace "d'a nane amma akwai wannan" ta fada tana dariya, itama dariya Zainab tai kafin tai shiru tana kallan Umma....
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[11/30, 10:26 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{35}
Umma ta zuba mata ido tasan ita kadai tasan me takeji da har komaima fada takeyi, ganin yanda Umma ke kallanta ne yasa tai kasa da ido, a hankali Umma ta sa hannun kan goshinta, zafin dataji ne yasa ta kalleta da sauri, Zainab ta kalleta cikin mamaki sannan tasa hannu a wuyanta, itakam bataji komai ba.
Umma fitowa tai ta wuce gun Abba da sauri, Abba ne ya kalleta yace 鈥淚na yar......鈥�
鈥淎bban Khalid yarinyar nan fa batada lafiya, tsabar zafin abinda ta gani da alama yasa batasan ma meke faruwa da ita ba.鈥�
Cikin mamaki yace 鈥渕eta gani?鈥�
Shiru tai batace komai ba, murmushi yai yace 鈥渘ayi shiru tunda sirrinku ne yanzu ya za鈥檃i? Asibiti za鈥檃 kaita?鈥�
Khalid ne bansan inda yake ba, nakira wayarshi bata shiga ba, gaba daya hankalin Umma a tashe yake, Abba ne ya miko matw paracetamol a cikin magungunansa yace 鈥渒i bata wannan tasha ta kwanta in akai sa鈥檃 kiga komai yazo da sauki.鈥�
Amsa tai ta fito da sauri dakin ta shiga Zainab na zaune ta kurawa kasa kallo, jin motsin Umma ne yasa ta kalleta da sauri, Umma ta mika mata magani, amsa tai tasha batare da ta tambayi dalili ba, Umma ta zauna kusa da ita tace 鈥渒in fadawa baban naki?鈥�
Kai ta daga ahankali, Umma tai shiru tana kallanta cikin tausayawa.
Juyowa Zainab tai sannan tai murmushin yake tace 鈥淯mma abinda na fada miki.......鈥�
Bazan fadawa kowa ba, kai ta girgiza da sauri tace 鈥渂ashi ba, ko an sani ma magana ta wuce ai, kawai bansan Dady yasan meya faru ne, sannan kiyi hakuri dan yace zaizo.鈥�
Kai Umma ta jinjina tace 鈥渄ole yazo ai saboda halin da kike ciki, amma meyasa bazaki fadamai ba?鈥�
Idanunta ne suka fara canzawa tace 鈥渢aya zan fadamai abinda nasan zaizamarmai tabo?鈥�
Umma tai shiru tana kallanta, bata tambayeta dalili ba ita kuma Zainab batace komai ba sai dai a ranta tace tasan tabbas Dady ya sani bazai yafewa kansa ba zaiyi tunanin duk abinda ya faru ne yajawo haka.
********
Taku biyu tai zuwa gaban Khalid, batare da ta juyo ba tace 鈥淎dam da Ya Fiddausi ni kaina bansan ya akai suka hadu ba, sai dai tun sanda na dawo daga makarantar kwana take bani labarin saurayin datai, wani irin so suke ma junansu, wanda gaba daya iyayenmu suka maidashi dan gida, a lokacin ina makaranta.
A gidan mu yawanci yake cin abinci saboda karatun da yake a BUK, Yaya na tsananin sansa, dadin dadawa daya ce mata shi AA ne yasa ta kwallafa rai dashi, tanada yawan ciwoka wannan kam kowa yasan saboda ciwonta ne, ga wahalalen ciwon baya da take dashi, akoda yaushe Adam ne ke kula da magungunanta, dan ko yana makaranta in lokacim shan maganinta yai yana kiranta, wani irin soyayya sukema juna wanda ni har mamaki nake in na dawo ta dinga min zancen, sau biyu ina ganinsa sai dai yanda yake nunawa Yaya tsantsar so da kauna yasa ma gaba daya nima na aminta da shi, iyayenmu sun sadaukar da duk wani kauna akanshi, dan akwai sanda yazo gunta cikin tashin hankali saboda bashida kudin biyan kudin makaranta, haka ta sanarwa Baba ba tare da wani kokonto ba suka saida keken dinki Mamanmu aka bashi ya biya.
Sam yanda suka daukeshi kai kace sirikinsu ne, dan shi im ta tashine da an daura musu aure kafin ya gama karatun, Baba ne ya hana a cewarsa hankalinsa zai rabu biyu, gashi yace bayasan tai karatu saboda yanayin lafiyarta, gwara ta xauna shi ya musu, Baba baiso ba sai dai ita Yaya ta nuna hakan takeso dan duk abinda ya fada shi take so.
Haka ya cigaba da karatunsa, duk sanda Baba ya samu kudi burinsa yamai dinki ko ya bashi ya kashe, ni da nake boarding sai nai zuwa nawa amma dakyar Baba ke bani dubu daya da dari biyar a gabana kuma zai ba Yaya dubu hudu-biyar yace taba Adam.
Haka suka share shekara 3 suna cin soyayya mai tsafta dan yasha faduwa jarabawa in bai samu damar biya ba haka Baba zaici bashi a biya mai, hartakai an samu ya kammala karatunsa.
Wata biyar da kammala karatunsa komai ya fara canzawa, dan ko Yaya ta kirashi baya dauka, hankalinta ya tashi, har garinsu ta nike gari taje sai dai randa taje mahaifiyarsa ke fada mata an tafi sa ranar Adam sannan tace ta rufa mata asiri kafin ma wani yaji ta kwashi kafarta ta tafi dan da wacce xai aura.
Dakyar Yaya ta kawo kanta gida, tundaga ranar ciwo ya rufketa, banda kiran wayarsa da kuka ba abinda takeyi, abinci wannan sai ana dura mata takeci.
Baba dakanshi yaje garin sai dai wulakancin da mahaifiyarsa ta masa akan yana musu bakin ciki dan zai auri mai kudi da kuma wanda Adam ya masa akan shi aba Fiddausi hakuri shiyanzu saura wata uku bikinsa gini ma sukeyi na inda zasu zauna.
Haka Baba ya dawo cikin tashin hankali da bakin ciki, Yaya ta shiga tashin hankali ta rame duk ta kanjame ga azababbem ciwom baya da takeyi, a haka ne na kammala karatu na dawo gida.
Ranar daurin auransa........
Hawayenta ta share sannan ta cigaba, ranar da komai na rayuwarmu ya ruguje, Yaya ciwonta ya tashi ga ciwon yunwa da damuwa, munje asibiti akace jininta ya hau sosai sannan zuciyarta ta fara kumbura, haka aka bamu gado aka yanke mana uban kudi zumzurutu da zamu biya, saboda munje asibitin gomnati abu yaki yiwuwa dole muka dawo na kudi.
A ranar auransa ciwonta ya tashi a asibiti gashi sunce bazasu mana komai ba harsai mun bada rabin kudi tunda haryanzu basuga komai ba.
Haka Baba ya fito ya saida mashin dinshi wanda ba wani kudi ya hada ba, ya daga gidan mu sai dai ba mai siya, Mama tai kuka da kanta ta nufi kauyensu akan yazo saboda sunansa kawai take kira, Mama ta nemi yazo ko na awa daya ne in ta ganshi sai ya koma, sai dai mutumin nan da aka tambayeshi wacece ma sai cewa yai bai taba ganinta ba da alama neman taimako tazo.
Haka Mama ta dawo tana kuka, ga Yaya numfashinta ma ya daina fita daidai, hankalina a tashe na shiga gun likitan na sa gwiwowina a kasa ina neman ya taimaka wa Yaya.
Juyowa tai tana kallansa tace 鈥渒asan meyace?鈥�
Bata jira amsarsa ba tace 鈥渃ewa yai sai na bashi kaina zai taimaketa.鈥�
Haka na fito ina kuka sai dai ganin yanda yaya take ga Mama na kuka a gefenta, ga Baba ya dawo jiki a sanyaye yasa na koma dakin nan.
Hawayenta ta share ta cigaba haka na ba likitan dako sunanshi bansani ba kaina, sai daya biya bukatarsa sannan yazo aka bata gado, sai dai duk sanda zai dubata sai ya kusanceni, haka duk dare banda kuka ba abinda nakeyi, a rana ta uku da kaita asibiti, ciwonta ya tashi sosai, gun likita na nufa yana biya bukatar sa Allah yai ajalin Yaya.
Tana kaiwa nan ta hadiye wani abu daya tsaya mata, Mama tana ganin yaya ta tasu ta fadi a kasa ciwom barin jiki ya kamata, har yau tana nan komai yi mata akeyi.
Takowa tai zuwa inda Khalid yai mutuwar tsaye tai, tace 鈥渒anada magana akan abinda na aikata?鈥�
Kallan idanunta dake nuna mikin da aka bude take sannan ta share hawayenta tace 鈥渢undaga nan nike ciyar da gidan mu, saboda Baba na gida yana kula da Mama, tun kuma daga sanda na taso da kudirin halaka rayuwarsa dan da wannan kadarin kadai na taso zuwa yanzu鈥�
Tadan ja numfashi sannan tace 鈥渋n ka gama jin abinda kake san ji ni zan shiga ciki.鈥�
Da sauri ta wuce kafin tajira mai zaice, tana shiga tasa kuka.
Gaba daya Khalid ya kasa ko motsi, saboda abinda yaji bai taba tunanin abin yakai haka ba.
ne ya kamata, sannan ya juya dakyar ya fita daga gidan.
*******
Kanasan cemin tsinaniya dubu ashirin kadai gareka a banki?
Kallanta yai yace 鈥渢o me nakeyi dazan samu kudi?鈥�
Ranta a bace tace 鈥渄uk ina uban kudin da matarka take baka? Duk wata dubu saba鈥檌n take baka ko ka dauka bansani ba? Kudin da take baka ko ita bata cin rabinsu.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渋na suke kuwa? Duk na cinye.鈥�
Haushi ya kamata tace 鈥渁mma wannan wannan ni dai banji dadin haihuwa ba, to yanzu gidan ubanwa kake so mu kwana?鈥�
Inafa na sani mu koma kawai can gidansu kawo shehu.
Kaci gidanku mu koma mu musu uban me bayan kasan yanda muka rabu?
Haushi ya kamashi yace 鈥渢o sai dai kuwa mu kwana a mota.鈥�
Kallan motar tai sannan tace 鈥渋n muna bukatar bayan gida fa? Dan ni yanzu ma ji nake.鈥�
Sai kije na kan hanya.
Kwade kansa tai tace 鈥渃emaka akai banda mafadi, nidai wlh Adam ka cuceni wannan abu dakai wlh ni ka cuta.鈥� Ta karasa tana murza ido.
Ya kalleta a kufule yace 鈥渟ai dukana kike kina cewa nina ja miki, amma kinsan hadda ke ko? Dakin tubure sanda zan kawota ai da duk ba haka ba.鈥�
Baki ta saki tana kallanshi tace 鈥渒enan laifi nane?鈥�
Bawai naki kadai ba namu ne duka.
Haushi taji tundaga nan bata sake mai magana ba, haka suka sai naman tsire da lemo sukai parking suna ci kowa rai a bace, suna gamawa ta kalli gari tace 鈥測anzu haka zamu kare a titi?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渒o mu roki babanta? Ko dan daki daya ya sai mana.鈥�
Wani banzan kallo tamai kafin tace kai Addu鈥檃 ma karyasa a daureka.
Da sauri ya shafi hannunsa sannan yai shiru, haka suka zauna a mota suna kallan juna kafin Goggo baccinya dauketa yo bata saba zama gum ba badan kallo ko taune taune.
******
Yana tafe gaba daya zuciyarsa ba dadi.
Yana shiga kan layinsu yaga motar datai parking mutumin dake jikinta yana tambaya, Khalid yaje wucewa yaji ance Khalid!
Yana juyowa yaga Dady, mutumin yace 鈥測auwa ga Khalid din ma.鈥�
Da sauri Khalid ya karasa ya gaisheshi.
Dady ya sallami mai motar sannan ya kalleshi ya amsa gaisuwar yana cewa 鈥淎llah yayi a hanya zamu dinga haduwa.鈥�
Murmushi Khalid yai, tafiya suka fara Dady yace 鈥淎she abokinka sakinta yai.鈥�
Da sauri Khalid ya kalleshi, Dady yace 鈥渂aka sani ba? Saki uku ya mata.鈥�
Idanunsa ya dan runtse cikin takaici wannan haukar na Adam, Dady ya murmusa yace 鈥渕ungode sosai da taimakom da ka mana, dama tunda na ganka hankalina ya kwanta dakai, ashe raban zaka cecemu ne.鈥�
Da sauri Khalid yce 鈥渂a wani abu danai鈥�
Dady ya kalli gidan da Khalid ya tsaya sannan yace 鈥渘an ne?鈥�
Khalid yace 鈥渆h鈥�
Nan ya shiga yabar dady a waje yana kara kallan gidan.
Umma na tatar koko ya shigo, tana ganinshi ta hade fuska, murmushi yai yace 鈥渢uba nake Ummana duk dabansan laifina ba.鈥�
Tace 鈥渋nata kiranka wayarka a kashe.鈥�
Yace 鈥淵ahkuri Ummana, munyi bako.鈥�
Bako? Ya iso kenan?鈥�
Yace 鈥渆h ashe kunsan da zuwan.鈥�
Ajiye abin tatar tai ta matsar dashi ta shiga ciki tace 鈥渟higo dashi.鈥�
Haka Dady ya shigo ya shiga falo.
Abba dake zaune yana jin radio ya kalla bayan ya zauna, gaisawa sukai cikin girmama juna, Khalid ya ajiye musu ruwa sannan ya dan matsa gefe.
Zainab kam tundataji Umma ta fada mata zuwansa gabanta ke faduwa haka ta dake ta zura hijab ta fito.
Tana fitowa Khalid ya mike ya fito.
Dady ne ya kalleta, Abba yace 鈥淜halid ka bude musu dakinka su shiga ko kuma taimaka min na koma daki na basu guri.鈥�
Dady yace 鈥渂akomai wlh ka zauna magana ce wacce kun sani gwara ayi a gabanka.鈥�
Abba ya kalli Khalid yace 鈥淜halid karaso.鈥�
Haka Khalid ya taimaka mai ya shiga daki, Sannan yazo ya fita.
Dady ne ya kalleta yace 鈥淶ainab!鈥�
Kallansa tai tare dayin murmushi bayan sun gaisa ne ta mikamai takarda.
Ransa yayi mugun baci dan bacin ransa ya fito karara ya kalleta yace 鈥渨annan wani irin butulci ne?鈥�
Kallansa tai batace komai ba, yacigaba 鈥渘asani sarai kin aureshi ne saboda ni, kin samu wanda baya sana鈥檃 wanda kuma bashi da burin tabuka komai saboda kina tsoron abinda ya faru da mahaifiyarki, yanzu kin fahimci wayanka baya sai ma komai?鈥�
Idanunta ne sukai jaaa sai dai haryanzu batace komai ba, Dady tausayinta ya kamashi yace 鈥渇adamin menene ya jawo sakin nan?鈥�
Kallansa tai tace 鈥測anda manfadama ra鈥檃yinmu ne ya banbanta da juna.鈥� Yanda tai maganar cikin dakewa tayita sai dai Dady ya fahimci tana cikin tashin hankali, hakan yasa yace 鈥渢ashi mu tafi gida, duk zaman da aka ga kinayi ke kadai ne ma yasa abin yakai haka.鈥�
Gida?
Ta fada da sauri tana kallansa, yace 鈥渕e? Badai kina tunanin na barki anan bane?鈥�
Kallansa tai tace 鈥淒ady kafi kowa sanin yanda nake da matarka wani irin zama zamuyi a gida daya?鈥�
Matata? Matata ba mamanki bace?鈥�
Shiru Zainab tai kafin tace 鈥渒ayi hakuri Dady amma bazamu iya zama gida daya ba.鈥�
Kallanta yai sannan a hankali yace 鈥渢aya zaki zo gidan mutanen da baki da hadi dasu kice zaki zauna kiyi iddah a gunsh? In ke kin yarda su ce miki akai sun yarda ko ni ce mike nai na yadda?鈥�
Kallansa tai ta matso kusa dashi sannan ta tsuguna a kasa tace 鈥淒ady ka taimaka ka barni anan, inasan zama anan, inaji a jikina hankalina zaifi kwanciya anan.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渁nan gidan?鈥�
Ta fahimci meyake nufi tace 鈥渆h, dan Allah dady kamin alfarmar kabarni, nasan Umma bazata hanani ba.鈥�
Shiru yai yana kallanta kafin ya ja nunfashi yace 鈥渟ai na tambayesh.鈥�
Da sauri tace 鈥渘a gode Dady ta fada tana share kwallarta.
Dady ya zuba mata ido wai itama tata kaddarar kenen, lalai alhakin Ummy ne ya kamashi, gashinan yarsa na kunsar abinda ya kunsawa yar wani, ita nata ma sakin wulakanci har uku.
Zainab ce takatse tunaninsa tace 鈥淒ady ka taimaka ka sanar a gun aikina akan zan dau hutun wata uku, ko kuma kace nayi tafiya gudun kananan maganganu, nima zan tura musu email.鈥�
Kai ya daga alamar fahimta tausayinta na kara kamashi.
Haka ya tambayi Abba da Umma wanda a take suka amince tare da mai alkawarin kula da ita harta gama idarta.
Haka ya fita gaba daya jikinda yai sanyi, Khalid ya nemi ya maidashi Kano a motar Zainab, nan ya amince sai dai suna fita yace Khalid ya kaishi shago zaisai abu, nan fa Dady yahau siyo su Buhun shinkafa, taliya, Marconi, shinkafar turo, indomie, juices ruwa da sauransu, Khalid da sauri yace Dady?
Dady yace 鈥渒a taimaka Khalid nima hankalina zaifi kwanciya akalla na taimaka da wani abun, nayi ne dan hankalina ya kwanta, nasan xaka fahimci halin da wannan mahaifin ke ciki.鈥�
Haka suka kai kaya yasa dubu ashirin a cikin katan din juice, Khalid kansa bai sani ba, haka suka ajiye suka nufi kano.
A hanya sai godiya Dady yakeyi yana jimamin wannan abun.......
******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[12/1, 9:40 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
There are wounds that never show on the body that are deeper and more hurtful than anything that bleeds.
Laurell K. Hamilton, Mistral's Kiss (Merry Gentry, #5)
{36}
Shiru sukai suna tafiya a hanya gaba daya Khalid na lura da yanayin dady, hankalinsa ba a karamin tashe yake ba kuma da alama bai san barinta acan, dan dai ba yanda zaiyi ne.
Kallansa Khalid yai yace "in bakasan barinta acan mu kuma a dakota."
Kallansa Dady yai sosai yaji dadin maganar dan abinda ke kunshe a ransa kenan sai dai tayaya?
Kallan Khalid yai tare da yin murmushi yace "yauce rana ta farko tunda nake da Zainab dana taba ganin tana san zama a guri kamar gidanku, gidana a zaune kawai take amma sam ba ta sakewa a ciki, gidan kanwar mamanta data zauna kuwa dama kowa yasan ba so take ba tana zaune ne saboda batasan zama a guna, ta ya zan tilasta mata ta taho inda bazata ji dadi ba?"
Mamaki ne ya kama Khalid dan sosai yana mamakin wannan halin na Dady taya zai zauna komai sai ra'ayin yarsa?
Cewa yai " Amma ni ina ganin nesanta kanta daky da takeyi shiyasa bazata taba sakin jikinta ba, amma in ta zauna cikin yan uwanta dole ta saki jikinta."
Kallan Khalid yai cikin jin dadin kalamansa kafin yace "tsoro na akoda yaushe yanda halin rayuwa yake, ina tsoron ajali na yazo muna wannan zaman."
Labarin Razy ne ya fadomai, da tashin hankalin da suka shiga, ga ita kanta rayuwar da Zainab din ta fuskanta a gidan mijinta, rage gudun motar yai sannan ya kalli inda suke harsunzo kano dan suna daf da shiga kurna.
"Ina ganin ba shawara bace a barta acan, hankalinka bazai taba kwanciya ba, sannan iddah zatai ni ba muharaminta bane, Kuma gidan mu ne dole zan shiga ciki, sannan inada abokai dake zuwa, Abba ma abokansa na zuwa dubashi baza'ace duk sanda wani yazo tana killace a daki ba."
Dady ne ya kalleshi yace "me kake tunani? Zainab bazata taho ba."
Zan ajiyeka a inda kai masauki zan kawota anjima ku wuce tare.
Mamaki sosai ne ya kama Dady yace "kana tunanin zataji maganar ka?"
Khalid baice komai ba ya wuce da Dady, sosai Dady yaji dadin abin nan sai dai sam baisa rai akan zata biyoshi ba, ya daiji dadi sosai a kalla Khalid ya nuna mai shi d'a nagari ne.
Khalid na ajiyeshi ya juya danbatta.
Zainab na zaune a daki Umma na gefenta, ajiye kudin hannunta tai tace "Zainab ki ajiye mai annn duk randa yazo kya bashi, dan bazamu amshi waccen ku amshi wannan ba, waccen din ma a dole muka amsa dan karyaji ba dadi ne."
Zainab ta kalli Umma tace "Allah Umma bakomai dan Allah ki ajiye? Nima bazanji dadi ba in kika ki amsa."
Ajiye mata tai kusa da ita tace "saboda Allah nake zaune dake bawai dan wani abu ba, banasan harkar kudi ta ratsa daga nan in ba'ai wasa ba san zuciya ne zai shiga."
Kallan Umma tai sannan ta daga kai kawai batace komai ba dan rayuwar nan taso ba karamin birgeta take ba.
Zama kusa da ita Umma tai tasa hannu a goshinta tace "masha Allah Zazzabin ya tafi." Ta fada tana kallan Zainab wacce itama ke kallanta.
A tare sukai murmushi Zainab jiki a sanyaye tace "Umma nagode sosai sosai."
Kafadarta ta dafa tace "ki rage sa komai a ranki, Allah baya dorawa bawansa abinda bazai iya ba, duk abinda ya sameki kisa a ranki kaddarace ta Allah sai kiyi fatan sa'ar cin jarabawar."
Kai ta daga ahankali idanunta sun ciciko da hawaye.
Murmushi Umma tai.
A falo ta zauna suna dan taba hira da Abba kasancewar su Asiya dasu Amir duk suna makarantar islamiya.
Jin sallamar Khalid ne yasa Umma ta kalli waje, dayake labulen a dage yake ta amsa tana cewa "har an dawo?"
Karasowa yai yana cewa "eh Umma"
Abba yace "badai gudu kai ba ko?"
Kallan kafar Abba da aka cire yai sannan yace "a hankali muka tafi."
Kallan Abba yai yace "Abba inaganin zamanta anan bazai yiwu ba."
A tare suka kalleshi, ya kalli Abba yace "iddah zatai bai kamata ta zauna inda ba muharammanta ba, sannan hankalin mahaifinta bazai taba kwanciya ba inya barta anan, kuma jikina naban kamar baya jin dadi."
Da sauri Umma tace "meke damunshi?"
Kai Khalid ya daga alamar rashin sani sannan yace "ban sani ba wlh haka dai nakeji."
Umma ta kalleshi zuciyarta duk ba dadi, dan maganar gaskiya tana san zama da yarinyar ta fahimci tana da tabo na rashin uwa ga kuma takaicin namiji.
Abba ne ya kalleta ya sani sarai zuciyarta ba dadi sai dai ya zasuyi? Kallan Khalid yai yace "bari a kirata na mata magana."
Da sauri yace "bari na mata magana."
Kallansa sukai cikin mamaki, shikuwa yasan halinta dan zaman nan da sukai ya tabbata aka mata lagwalagwa ba abinda zai faru.
Knocking din dakin yai, daga ciki tana zaure rike da takardar Adam tace "waye."
Khalid yace "nine."
Mamaki ne ya kamata tace "ya akai?"
Magana zamuyi.
Umma ce ta mike tace "ko na mata magana?"
Khalid ya girgiza kai alamar a'a daga ciki tasa hijab sannan tace "shigo."
Tura kofar yai ya shiga a bakin kofar ya tsaya yace "kizo na kaiki kano, ku wuce da babanki."
Kallansa tai cikin mamaki tace "in wuce ina?"
Gidanku!
Fuska ta hade sosai tace "a matsayinka nawa kenan?"
"Na d'an gidan nan"
Baki ta bude cikin kuluwa da takaici tace "da nace ba d'an gidan nan bane kai?"
Yace "tambayarki haka ta nuna min."
Wata dariyar takaici tai sannan tace "korata kake kenan kome?"
Yace "ba korarki nai ba ina nufin ki bi babanki."
"Nafi karfin ka wulakantani wlh."
Wani mugun kallo tamai ta mike a tsananin zuciya ko kayanta bata dauka ba kawai wayarta da laptop da tab dinta ta dauka ta fito rai a bace.
Kofa ya bude mata alamar hanya, tsayawa tai tana kallansa cikin takaici kafin tai kwafa.
Umma ta gani a tsaye a falo, Umma na ganinta ta matso tace "Zainab."
Zainab tai kasa dakai idanunta suka fara neman rauni, dakewa tai tace "Umma zan wuce."
Tana fada tai hanyar neman fita, da sauri Umma ta rikota sannan ta dago da ita tace "ba korarki mukai ba Zainab, nikaina inasan zamanki anan sai dai ba yanda zanyi."
Kallan Khalid tai kenan shiya kawo wannan maganar?
Abba ta tsuguna tawa sallama sannan ta kalli Umma tace "nagode muku Allah ya saka da alkairi."
Umma ta dauko yar wayarta tace "samin numberki."
Nan Zainab tasawa Umma ta kira wayarta dashi sannan ta kalli Abba tace "Allah ya kara lafiya."
Khalid ta kalla wanda ke tsaye jikin kofar dakin Asiya, wani takaici ne ya kamata ta sake sallama da Abba ta fito.
Umma har tsakar gida ta rakora tana neman fita waje Zainab tace takoma.
Kayan abincin da aka kawo Khalid ya fito dasu, kalan Umma tai tace "Umma ki taimaka ki bar wadan nan dan Allah badan ni ba."
Jikin Umma ne yai sanyi, ta jawo Zainab ta rungume idanunta harda hawaye, Zainab ta share nata da sauri tace "Umma ki taimaka."
Kallan Khalid tai tace ya barsu.
Khalid ne ya fito waje, yana neman bude mota, kallansa tai tace "bani makulina."
Kallanta yai sannan ya kalli motar yace "wazai kaiki?"
"Banaji wannan ya dameka tunda motatace."
Kallanta yai yace "ki bari na kaiki tukun."
"Motarnan tawace sannan jikina ne banaji akwai damuwarka akai, bani."
Ta karasa tare da mikamai hannu,
Bai tanka taba ya shiga motar ya zauna, haushi ya kamata ta bude motar inda yake tace "fito."
Yace "shigo."
Tace "Malam fito ko?"
Yace "Malama shigo ko?"
Jitake kamar ta shakeshi, hankalinta harya kwanta zamanta anan ya koreta kuma yanzu yazo yana wani abu?
Kallanta yai yace "dare nayi."
Ranta a tsananin bace ta bude ta shiga baya yaja suka tafi, har suka isa ba wanda yawa wani magana, kaini gidana.
Kallanta yai yace "kamar......."
Kaini nace, kome zan da rayuwata ba damuwarka bane."
Dauke kai yai yana kaita gidanta ta amshi key sannan ta kalleshi ta wuce ciki.
Bala da gudu ya bude mata tana shiga tama Khalid text "You are Fired."
Yana fita ya gani, kallan gidan yai jiki a sanyaye sannan ya kira Dady ya fadamai.
Dady cikin jin dadi yahau godiya, alokacin ya taho gidan.
Zainab na zaune a falanta ta hade kafafunta tana kallan gida, komai na gidan bataso gani take komai anyi lalata dashi, kankame jikinta tai kawai tasa kuka.
Dady wanda ya shigo ne ya kalleta cikin tausayi, tana ganinshi tasa kuka sosai, tausayinta ne ya kara kamashi yace "tashi mu wuce saboda ba'asan fita."
Kallansa tai tce "Dady anan zan zauna."
Kallanta yai da sauri yace "bazai yiwu ba."
Tace "to kaini gidan Aunty."
Yace "wai akan me bazaki zo mu tafi ba?"
Kallansa tai ta rasa me zatace, tuno da kalaman Khalid tai wai gidan iyayensa ne, Dady yace "mu tafi kinji?"
Idanu ta runtse kafin ta daga kai.
Haka Suka hada kaya suka wuce Abuja, tunda taje gidan magana ba hadasu take da Basma ba, kullum tana daki kamar yanda ta saba, Basma kuma ta rasa yanda zatai ta shawo kanta, Dady ne inyana nan yake kiranta falo shima da Basma su zauna duk da batama Basman magana ko ta mata a kalla tana amsamai in ya sako maganar Basman
Sai dai hakan ba karamin birgeshi yake ba duk da ba san zaman take ba akalla yanzu tana zama a falan in yana nan.
*******
A can bangarensu Goggo kuwa haka suk nufi kauye ganin ba yanda zasuyi dan dakyar goggo tai bacci ranar a cikin mota, gidan kawu shehu sukaje Goggo ta kalli Adam tace "karka fito da kayan tun kafin a tozartamu mu fara shiga tukun"
Haka suka shiga gidan Kawu shehu, matansa biyu da yaransa su goma sha daya, sai Sadiya dasuka barmai.
Yana zaune a kan tabarmar kaba yana ta kankare kaho yaji ana ihun kawu Adam yazo.
Shiga sukai cikin mamaki kowa ke kallansu, makota sai lekowa ake ta kanga, Goggo nasa kafa ta taka kashin kaza, da sauri ta matsa gefe tafara cewa "matsalata da kauye kenan, kaji ko ina......."
Kallan da Kawu Shehu da matansa suka mata ne yasata tai shiru, haka suka zauna, kowa na musu kallan mamaki, Kawu shehu yace "dama kuna raye? Ai mu tuni muka cire tarihinku."
Goggo tace "wato mutuwa kake so muyi ko me?"
Matarsa Delu tace "tunda danki yai aure kika bishi shekara hudu ko kafarki mun gani? Ko falen atamfa kin aiko mana? A matsayinmu na masu rike miki 'ya."
Dariya Goggo tai tace "Adam ina taliyar da muka siyo dako ka shigo da ita."
Kawu shehu ne yace "basai an shigo da ita ba, meya kawoku?"
Adam yace "dama Goggo ce zata dawo nan da zama."
Delu tace "nan ina?
A wani dakin? Bayan mu kanmu gurin kwana wahala yake mana? Ruwa duk ya cinye mana gini?"
Kawu shehu ne yace "ki koma inda kika fito ki zauna nima yara rasa inda zasu kwanta mukeyi, lokacin da zaki tafi danace ki barmana gidanki me kikace? Hanani kikai a gabana kika saidashi ma abokina."
Goggo tasa dariya tace "wasa yakeyi kamar bakusan Adam ba, Sadiya nazo gani, tunda batanan bari mu wuce."
Har sun shiga mota Delu tace "taliyar, nan Adam ya bude mota dole ya cirota aka shiga da ita ciki."
Suka ja suka tafi, haka Goggo suka je kano wajen gidan Zainab Goggo tana kallan gidan tana hawaye, Dakyar suka samu gidan haya daki daya a cikin katan gida mai dakuna kusan goma ban daki daya daga can kasan unguwar gidan Zainab suka zauna, Haka suka saida motarnan Goggo tasai yar mitsilar tv canjin suka sai kayan abinci suka zauna a gida.
Adam kam takaicin rashin mota sam yasa ko fita bayasanyi, wannan lamari na kona mai rai matukar gaske.
Banda fada shida Goggo kullum ba abinda suke a gidan, haka ya nemi majalisa yake zama, kudin mota kam an sashi a gaba sai ciye ciye akeyi kai kace bazai kareba.
Duk gidan nan Goggo batawa kowa mutumci, dan garkame dakinta takeyi saboda batasan yara suzo mata kallo.
*********
Bayan wata uku..........
Wannan lokaci abubuwa da dama sun canza, su Nabila da Nusaiba an dawo, murna agun Zainab baya musaltuwa, Nabila kam taji bakin ciki dan jitai kamar ta je ta kashe Adam duk da batasan me ya mata ba amma haushin wulakanta hallacin Zainab yasata jin takaici matuka.
Su Khalid anyi Jarabawa, Zainab aka turowa takardun tai marking dan sai data turawa director din email akan ita zata dau ma'aikara dakanta, ganin yanda komai nasu yai kasa daga tafiyarta yasa yake lalabata, ta sanar kar wanda yasa suna sai dai ai amfani da numbers hakan yasa sanda tai marking batasan ko wanene na Khalid ba, sai dai akwai takarda daya wanda ita kanta sai datai bincike a google kafin tai marking dinshi saboda tsabar fasahar da aka rubuta ya wuce tunaninta.
Kusan duk kwana biyu sai tayi waya da Umma sosai wannan wayar ke debe mata kewa, har Allah yai ta kammala iddar ta, sannan ta tura ranar interview ga wadanda suka ci sannan tahau shirin dawowa.
Khalid dake zaune cikin shagon dayake aiki ne sako ya shigo mai, baki ya sake sosai dan bai taba yin jarabawa ance yaje interview ba sai wannan, wayar ya kurawa ido yana kallan sakon dan ya kasa gasgata abinda yake gani.......
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[12/3, 3:52 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{37}
聽 Goggo na zaune adan kucilin falanta da tana kallo, Adam dake kwance a dan mitsilin dakinsu ne yace "Goggo dan Allah rage magana haba, tsakani da Allah kallo da sassafen nan?"
Ranta a bace tace "ka fito ka bar gidan nan ko sai jikinka ya gayama? Ai tun jiya nace ka samo aran yar mota ka kaini gidan Hajiya Bilki."
Komawa yai ya ja bargo baice mata komai ba, haushi ya kamata ta taso ta shigo dakin da karfi ta yaye bargon tace "ko tsinaniya kujera banda ita sai dai na zauna a kasa amma kai ka shige cikin bargo banda uban bacci da yawon banza baka da abinyi."
Cikin kufula yace "koma me nake meya dameki? Ni ki barni da rashin matata dake damuna."
Wani kallan banza tamai tace "har wani rashin matarka? Nawane ragowar kudin mu?"
Kallanta yai yace "wani kudin bayan kin kwacesu?"
Yaushe?
Kallanta yai ya saki baki kafin yace "banasan wasa, wancan satin kikace nawane ragowar kudinmu nace miki dubu dari da ashirin kika ce na kawo miki darin baki yadda dani ba kinji kudin sunyi saurin karewa.
Kanta tadan sosa tace "ina nasa?"
Da sauri ya mike yace "bangane ba."
Hankali a tashe suka fara neman kudi a cikin dakin, hankalin Goggo yayi dubu ya tashi ji take kamar rayuwarta aka gutseri.
Gaba daya kayan dan kayan nasu suka fito dashi waje suna dubawa, sai dai bashi ba labarinsa.
Goggo ta kalli Adam tace 鈥測aushe ka bani?鈥�
Shiru yai yana tunani kafin yace 鈥渒amar da safe ne?鈥�
Karya kake wlh, ni baka ban ko ficika ba, bayanda za鈥檃i ka ban makudan kudi nai wazgarere dasu har sati daya bansan inda suke ba.
Gabansa ne ya fadi dan maganar gaskiya ranar ya ciro kudin daga masallaci sai majalisa yaje yana dawowa gida zai bata yaga wayam, kallanta yai yace 鈥渒i dai duba Goggo.鈥�
Daga can makotanta ta kalla wadanda kowa ya fito yana kallansu, haushi ya kamata tace 鈥渒u kuma me kuke kallo?鈥�
Asabe da dakinta ke kusa da nasu tace 鈥渒udai kusan barawon daya dauke a cikin ku dan mu gidan nan ba鈥檃 sata.鈥�
Ran Goggo ya baci ta kwashi kaya ta shiga ciki, kallan Adam tai tace 鈥渇adamin, uban wa kaba kudin?鈥�
Yace 鈥渨ai Goggo wa nake dashi da zan ba inba ke ba?鈥�
Zama tai dabas a kasa tace 鈥測anzu ya kake so muyi?鈥�
Yace 鈥渘izance haka Goggo yanzu ya zamuyi?鈥�
Takaici ne ya kamata tace 鈥渨ai uban me ma kake harynzu baka samu aiki ba?鈥�
Ransa ne ya baci ya fita daga gidan, kanta ta rike wanda ke sarawa.
********
Gaba daya sun sa kaya a cikin mota, Nusaiba da Nabila sai murna ake za鈥檃bi Zainab.
Zainab dake daki ta kalli dakin, bata taba kawowa zata dawo tai dogon zama a gidan nan ba, duk da wata uku tai amma agunta dogo ne.
Jawo dakin tai ta fito, a falo taga Basma, fuskarta a hade tace 鈥渮amu wuce.鈥�
Basma ta matso tace 鈥淒ady yace ki kirashi kafin ku wuce.鈥�
To tace batace komai ba daga nan.
Basma tai shiru tanaji suna waya da Dady yana ce mata su tafi da mammab ya dinga kwana a dakin waje kafin asan yanda za鈥檃i dan sam hankalinsa bai kwanta da barinta ita kadai ba, in su Nabila suka taho.
Suna sallama ta kalli Basma tace 鈥渕un wuce.鈥�
Da sauri Basma tace 鈥淶ainab!鈥�
Tsayawa tai batare da ta kalleta ba, Basma ta dan tako tace 鈥淶ainab ki yafemin, sharrin zuciya da sharrin kawaye ne ya sani yin abinda nai, akullum ina danasanin wannan abu, gashi dalilinshi bazan sake haihuwa ba.鈥�
Kallanta tai da sauri, hawayenta ta share tai murmushi tace 鈥渉ukuncin da Dady yamin kenan鈥�
Gaba daya jikin Zainab ne yai sanyi, tama kasa ko cewa wani abu saboda mamakin wannan zancen.
Basma ta nufi kofa tace 鈥淣usaiba banda fada dake da Nabila.鈥�
Nusaiba ta dan turo baki sannan tace 鈥淢umy mun wuce.鈥�
Haka suka shiga mota Zainab ta shiga Mammab yaja suka tafi, gaba daya jikinta a sanyaye.
*********
Sam Khalid ya kasa gasgata abinda ke faruwa, yana fitowa daga shago ya nufi garage inda suke dan aiki, yana yi yana mamaki, sam zuciyarsa taki amincewa.
Haka ya dawo gida, sai dai sam ya kasa fadawa Umma da Abba, gani yake karsu sa rai azo ba鈥檃 dace ba, dan harya gaji da sanar dasu zaije jarabawa sai sun gama sa rai yazo bai samu ba, duk sai yaji ba dadi.
Shiyasa wannan karan ya barma kansa, in haryaje yaga da gaskene aka dace sai ya fada musu, dan ma yanzu hankalinsa ya kwanta ba bashin da ake binsu, duk sun biya, sannan Abba ba laifi in ya rike sanda biyu yana iya dan matsawa daga can zuwa can.
***********
Zufa ce ke karyo mata ta ko鈥檌na, daga yanda take runtse ido zakasan mafarki take mara dadi, jin sautin numfashin Adam da Raziyya ne yasa ta sa hannunta toshe kunenta kafin a hankali ta bude idanunta.
Kwance take a kan gujera a falo, wani abu tadan hadiya tare da kunna fitilar wayarta, duk da Dady da kansa yazo aka kwashe komai aka sa mata sabo na gidan amma ganin komai take kamar yanzu ake yinsa.
Mikewa tai ta kunna watar falan kawai ta dako laptop dinta ta hau aiki, ta shirya abubuwa da dama wanda inta koma za鈥檃i.
Haka tai ta aikinta har asuba tai, sallah tai sannan ta shirya, gadanta ta kalla, duk sanda zata fita yawanci Adam na bacci in bayayi kuwa to yana kitchen yana hada mata tea, wani abu ne mai daci ya zo bakinta hadiye shi tai sannan ta dau jakarta ta fita su Nabila na bacci.
A waje ta tadda Mamman, nan ta gaisheshi suka tafi, a hanya tacemai idan su Nabila sun shirya ka kaisu sumana siyayyar abin gida, yace 鈥渢o Hajiya.鈥�
Nan suka karasa ta fita tai ciki.
Mutanen dataga sun fara hallara ne tai murmushi tace 鈥渋s good to be serious.鈥�
Tana shiga station din taga duk staff dinsu a bakin kofa, hadda rike takardar da aka rubuta Welcome back.
Wani irin dadi taji dan dama wata ukun nan kamar mara lafiya tayisu saboda rashin aiki.
Murmushi ne yabayyana a fuskarta nan ta fara amsa gaisuwarsu cikin jin dadi, Head Director ne ya matso yana tafi, yace 鈥渂arka Zainab yau kamar sallah nake jinta.鈥�
Kallansa tai bayan sun gaisa tace 鈥淵allabai inaji sai mun shiga meeting kafin a fara interview.鈥�
Da sauri yace 鈥渁n gama Hajiya.鈥�
Nan suka wuce, Ramlatu ta gani ta taho da sauri, kallanta tai da sauri ta gaisheta, Zainab ta amsa sannan sukai ciki.
Sun yi discussing akan abinda zasuyi sannan ta bashi takardun da zaiyi reviewing na abubuwan da za鈥檃suyi nan gaba.
Wani irin dadi yakeji na ganin Zainab balle data kawo abubuwan cigaba yasashi jin wani kwarin gwiwa.
Karfe goma tara daidai ta nufi dakin da za鈥檃i interview kujerar ta ce a tsakiya, tana shiga ta zauna, kallan su tai tace 鈥渕u fara?鈥�
Sukace eh,
Kowa ya shigo tana rike da takardar dayai jarabawa da ita, tana mai tambayoyi tana duba takardar, su takwas ne.
Number 5 aka kira, ba tare da ta dago ba ta shiga duba takardarshi, ganin wannan takardar da ta wahalar da ita ne yasa ta kara dudubawa tana kara bin komai, har ya iso ya zauna.
Rufe takardun tai sannan ta dago dan taganshi.
Kallansa tai idanunta suka dan fito, tasan ita tace yai Applying amma bata kawo ya ci ba.
Wulakancin da ya mata ta tuno, fuska ta daure sosai, sannan ta kalleshi, shima kallanta yai fuskarsa daidai ba alamar fara鈥檃 ba alamar daurewa.
Takardarsa aka miko mata, ta amsa tana duba sunanshi, skul din dayai result dinsa da sauransu.
Kallansa ta sakeyi, H.Director ne yasa dariya yana kallan takardunsa yace 鈥渕asha Allah, irin wannan cik exams haka.鈥�
Cikin jin dadi ya kalli Zainab yace 鈥淒a alama kema abin ya birgeki.鈥�
Fuska ta hade tamau sannan ta kalleshi tare da ajiye biro din hannunta, nan ta fara watso mai tambaya, amsa yake bata yana kallanta, itama idanshi a kansa take mai tambayar.
Dan kai ta dauke bayan duk ya gama bata amsar tambayoyinta sannan tace 鈥渒a tabbatar ba satar amsa kai ba?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渟atar amsa?鈥�
Tace 鈥渆h from this naga Math ka karanta, then taya ka bada wannan amsar? Ta fada tana circling din takardarsa shafi na biyu.鈥�
Wani dan murmushi yai tare da dan kauda kai kadan, dan ya fahimci da saninta take watsomai tambaya dan yanda ta dinga jero mai tambayoyi yanda yaga suna kallanta ya tabbatar ba haka tawa kowa ba.
Fuska ta hade tace 鈥淢urmushin me kake?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渄a wanda yai satar amsa da masu kula da exams hall din har suka bari akai wanene mai laifi?鈥�
Fuska ta kare daurewa tace 鈥渒ana nufin satar amsar kai?鈥�
Kallan na kusa da ita yai yace 鈥淪ir kasan yanda mukai Exams din nan it seems like she is not there.鈥�
Nan ya mata bayani ba yanda za鈥檃i wani yai satar amsa.
Kallan Khalid tai sannan tace 鈥淚dan aka baka aiki a news room ya zakai?鈥�
Nan ya cigaba da bata amsoshinta, sai kara mai tambaya take sai da H.Director yace 鈥淶ainab ya isa haka wannan tambaya haka.鈥�
Shiru tai tana mai wani kallo, kallansu yai ganin basa kallansa yadan daga mata kafada alamar ko a jikinshi.
Haushi ya kara tukota ta harareshi tare da cewa 鈥渘ext.鈥�
Fita Khalid yai, har ta bude takarda ta kalli kofar inda ya fita sannan ta cigaba, sai da suka gama sannan ta fito.
A inda suke zaune ta ganshi, dauke kai tai ta wuce.
Shima yi yai kamar bai ganta ba yai gaba.
Tana shiga office dinta ta zauna, Malama shigo? D鈥檃n Gidan nan?
Haushi ya kara kamata data tuno maganganun daya watsa mata.
Tana zaune Ramlatu ta shigo dasu saboda ana nunu namusu ko ina.
Zainab tana dagowa suka hada ido, daure fuska tai ta maida kanta kan computer din dake gabanta, nan Ramlatu tace musu 鈥渨annan itace Director Zainab nasan kunganta agun Interview.鈥�
Nan kowa ya gaisheta, dagowa tai ta kallesu, har Khalid sannan ta amsa tace 鈥淪ai kunji daga garemu.鈥�
Nan suka fita, haka suka gama aka sallamesu akan su koma su jira sai an nemesu.
Khalid na fitowa ya runtse ido yana addu鈥檃 cikin zuciyarsa, wani irin yanayi yake ciki wanda shi kadai yasan ya yake ji.
Fitowa yai da sauri dan yaje gida ya kai musu labari.
Yana fitowa yaga wata mota tazo ta wuce, yarinyar dake janta kamar Raziyya.
Da sauri ya kara kallan motae sai dai ta riga ta wuce, shiru yai kafin ya juya ya nufi tasha.
Zainab kam kafadar da Khalid ya daga mata ta tuno wani mugun murmushi ta saki tace 鈥渒o a jikinka ko? Let me see in zaka juri wahalar da zan baka.鈥�
Ta saki wani murmushin jin dadi, samun kanta tai cikin nishadi in ta tuno wahalar da zata bashi.
********
Ran Nusaiba a bace ta kalli Nabila tace 鈥渨ai da gaske Aunty ta koreshi? Nifa Allah saboda shi na dage sai na zo.鈥�
Nabila ta kauda kai tana latsa wayarta tace 鈥渁ikinyi ne bakidashi wlh, haka a skul kika bi kika ishemu da zancen Ya Khalid kamar kanin Dady.鈥�
Nabila tace 鈥渕ijina ai yafi kanin Dady a guna.鈥�
Miji? Nabila ta tambaya sannan tace 鈥淎llah kanki ba daya ba, da alama kina bukatar ganin likita.鈥�
Ran Nusaiba ya baci tace 鈥渟ai ki kaini ai.鈥�
Mamman ne yce 鈥渁yi hakuri kar ai fada dan Allah.鈥�
Nan kowa ya kauda kai har suka isa Jifatu.
*****
Khalid cikin sauri ya isa gidan, hannunsa rike da ledar ayaba da lemo.
Umma na ta shanyar kayan data wanke ya shigo, cikin jin dadin da ya kasa boyowa yace 鈥淯mmana.鈥�
Kallansa tai tare da dan goge hannunta a zaninta tace 鈥淜halid an dawo?鈥�
Cikin jin dadi yace 鈥淯mma insha Allahu mun samu aiki.鈥�
Idanun Umma ne suka fifito tace 鈥渁iki?鈥� Yanda tai maganar kadai zakasan wani irin yanayi ta shiga mai wuyar fassarawa.
Abba da ya dosanu sandar sa guda biyu yana kokarin fitowa waje ne yce 鈥淎iki Khalid.鈥�
Cikin jin dadi yace 鈥渄aga Interview nake yanzu.鈥�
Wani irin dadi ne ya kama Umma harda hawayenta.
Fadar irin dadin da suka shiga a wannan lokaci ma wahala ne dan ni kaina nasan Allah ne kadai yasan yanayin da suka shiga duba da irin lokacin daya deba yana gwagwarmayar neman aiki.
(Yan uwa dake neman Aiki irinsu Khalid suma Allah ya dubesu ya basu)
**********
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[12/4, 9:39 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
For you my dear Yan Sauyi members馃グLove you soo much馃
{38}
Tana zaune tana kade sauran dake ta mata yawo akai, haushi duk ya bi ya isheta na rashin wuta da tun shekaran jiya wutar su ta samu matsala, wani uban tsaki taja data kalli taliya da manjan dake gabanta a roba wanda har yayi sanyi ta kasa ci saboda takaicin sauro.
Kofa ta bude ta hau korar sauran, tanaji makotanta nata hira da shewa a waje, wani uban tsaki ta sake jaa tace 鈥渒a rasa uban me suke banda zaman gulma.鈥�
Buta ta dauka zata shiga bandaki, da sauri Asabe ta mike ta warce butarta tace 鈥淭sohuwa wannan butar tawa ce鈥�
Kallanta tai tace 鈥渨ace tsohuwar?鈥�
Asabe tace 鈥渢o yarinya wannan butar tawa ce.鈥�
Haushi ya kara tike Goggo ta waiga taga bataga butarta ba tace 鈥渢o uban waye ya daumin tawa butar?鈥�
Asabe tace 鈥渟ai ki tambayi na gidan amma ba ni ba.鈥�
Ta ja kafarta ta bar gun, Goggo ta hau neman butarta sai dai bata ganta ba, nan ta matso inda suke hira tace 鈥渦ban waye ya dau min buta?鈥�
Kande ta mata wani kallo tace 鈥渟ai ki tambayi yaran da kika kira da danki tunda kinfi kowa sanin ba mai dau miki buta anan.鈥�
Takaici ya kama Goggo ta juya rai a bace, waje ta leka, Adam ta gani suna zaune a kujera suna hira, rai a bace tace 鈥淎damu!鈥�
Kalamta yai yace 鈥淕oggo.鈥�
Ka mikon butar nan ko kuwa?
Butar dake gefensu ya kalla sannan ya mike ya dauko ya kawo mata, yana shigowa tace 鈥渨uce ciki yanzu zan fito.鈥�
Yace 鈥渉ira muke.鈥�
Ka wuce ko sai na makeka?
Fuska ya hade ya shiga ciki, taliyar data bari ya jawo ya juya ya hau ci, bayan gida ta tsaya yi hakan yasa ya cinye taliyar kafin ta fito, yana lokar karshe ta bude labulen ta shigo.
Kallansa tai tace 鈥渦ban wa yace kacimin abinci?鈥�
Yace 鈥渁u zakici? Gani nai tun dazu kika ajiye shi gashi haryai sanyi.鈥�
Ranta a matukar bace ta karaso tace 鈥渘i wai dan Allah yaran nan sai yaushe zakai hankali? Gaba daya ni bantaba ganin mutum wanda bashi da tunani ba irinka, kanyar mana da kudi ka kala min karyar ka bani, yanzu yar dubu ashirin din da muka siyo kayan abinci muke cancanawa kaci naka dazu amma yanzu ka tasa nawa ka handame.鈥�
鈥淵ahkuri Goggo na dauka baci zakiyi ba鈥�
鈥淜o ba ci zanyi ba ai ka bari nace bazanci ba ko?鈥�
Nadai baki hakuri ya isa haka nan.
Ganin zasu sake fadam da kullum suke ciki yasa ta zauna ta kalleshi tace 鈥測anzu Adam haka zamuyi ta zama? Ga kudi mun cinyesu ga nan da wata biyu za鈥檃 amshi kudin haya? Banda wahar rashin abinci da muke neman shiga?
Shiru yai yana kallanta yace 鈥� Goggo na rasa yanda zamuyi duk inda nakai takarduna ko nemana yin jarabawa basayi.鈥�
Goggo ta baza tagumi tace 鈥渘ikam da alama rayuwarmu tai kusan zuwa karshe.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渒arki damu Goggo ina tunanin zuwa gun Zainab ta taimaka min.鈥�
Wani wulakantacen kallo tamai tace 鈥淶ainab? Lalai bakada hankali, inda raban an kulleka daga nan kaga shikenan ni na huta ai.鈥�
Fuska ya hade tace 鈥渘i fita ka siyo mana maganin sauro.鈥�
Mikewa yai ya fita rai a bace.
*********
Yau ake aka kira sababbin ma鈥檃ikata, tun safe take tunanin yanda zasu kare ita da Khalid dan tana tunanin abinda zatamai ta rama.
Fitowa tai ta nufi inda aka kirata akan isowarsu.
Tana shigowa suka fara gaisheta, kallansu ta hau yi daya bayan daya sai dai me? Gani tai sun cika su takwas ba tare da taga Khalid ba.
Juyowa tai ta kalli Ramatu wacce itace ta taho dasu, tace 鈥渟u kenan?鈥�
Ramatu tace 鈥渆h.鈥�
Kallansu Zainab ta sakeyi, a hankli ta fara takowa daidai inda suke, hartazo kan ta takwas din, mace ce yar gayu taci kwalliya sosai, makeup yaji a fuskarta, tana da kyau sosai ga diri, Zainab ta kalleta daga sama har kasa sannan tace 鈥測a sunan ki?鈥�
Cikin gayu tace 鈥淎freey.鈥�
Afreey? Zainab ta maimaita sannan tace 鈥渁re you telling me Afreey ne sunanki?鈥�
Da sauri tace 鈥渟unana 鈥淪afeena Sani amma Afreey ake ce.......鈥�
Kafin ta karasa taga tayi gaba, ranta a matukar bace tai hanyar kofa.
Ramatu ce ta matso da sauri tace 鈥淒irector ance ke za......鈥�
Kallan data mata ne yasa tai gum, kofar Director ta nufa tasa hannu zatai knocking taji yana waya 鈥渁i Ranka ya dade karka damu, zan sata a labaran da takeso, ahhh bakomai mune da godi........鈥漴an Zainab a matukar bace bude kofar Director da karfi.鈥�
Yana ganinta yace 鈥渢o bari na kira.鈥�
Kashe wayar yai ya kalli Zainab yace 鈥淗ajiya kin raba musu aikin?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渕e kake shirin yi?鈥�
Name kenan?
Wacce yarinyar me take anan?
Ohhh Afreey? Am sorry dama yanzu nake shirin fada miki yar kanwar Senate Musa ne, ai kinsan shi ko?鈥�
Wani banzan dariya tai tace 鈥渟ai a kai ya?鈥�
鈥淥hh to shine take san aiki a gidan tv shine akin magana, nasan kema zakiji dadi tunda yanzu duk abinda muka je nema zamu iya amfani da ita.鈥�
鈥淵aran dayai interview a maimakonta fa?鈥�
Wa kenan?
Wani kallo tamai yace 鈥渙hhhh yaran da kuka danyi fada? Naga kamar bakya sansa shiyasa nai replacing dinsa da ita, sannan shi na duba maga bashi da wata hanya balle ya dawo yace mun cuceshi.鈥�
Kamar zatai magana kawai ta fasa, gaban desk dinsa ta nufa tasa hannu ta dau biro ta jawo paper.
Kallanta yai yce 鈥渒arki damu yarinyar akwai hazaka.鈥�
Bata kulashi ba sai data gama rubutunta sannan ta tura mai gabanshi ta ajiye mai biro da karfi.
Kallanta yai da sauri bayan ya kalli takardar yace 鈥渨ani irin resignation letter? Zainab menene hakan?鈥�
Hannunta ta daura daya akan desk din sannan ta kalleshi tace 鈥渒ai processing dan na ajiye aikina daga wannam lokacin.鈥�
Hankalinshi a matukar tashe ya dawo ta gabanta yce 鈥淶ainab meke faruwa haka? Kinfi kowa sanin duk inda muka kai takarda sai suce dake zasuyi aiki, me kike nufi damu?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渄ama ina da matsayi?鈥�
Wani irin zance ne wannan bayan kina ganin komai sai da amincewarki nake?
Wani irin dariya tai na takaici tace 鈥渄a amincewa ta? Sanda kake kawo wadanda suka maka ina sani?鈥�
Yace 鈥渨ai akan Afreey ne? Naga yaran can ba sanshi.......鈥�
Ranta a bace tace 鈥渒o na soshi ko karna soshi meye nawa a ciki? Aiki yazo nema ya samu saboda iliminsa? Meya kawo zancen zabi anan? Sannan in maganar zabi ne zan iya sanar dakai, kaf cikin wadanda sukai interview shi ne mutum na farko da na fara tabbatar da gwaxanda da cancantarsa, sannan me? Ka koreshi saboda ka kawo yar uwar wani senate?鈥�
Wannan yrinyar da badan badan ba da......
Kallanta yai yace 鈥渢o yanzu kiyi hakuri za鈥檃mai text yazo kinga sai mu dau mutum 9 kenan.鈥�
Meye dalilin da zaisa mudau 9 bayan 8 mukai?
Da sauri yace 鈥淗aba Zainab bazaki daga min kafa ba? Nayi laifi nayadda na dauka sai dai nima ki barta aman.鈥�
Shiru tai kafin tace 鈥渘aji kasa amai text.鈥�
Tana kaiwa nan taja takardar datai rubutu a jiki ta fita.
Da hararar ya bita yace 鈥測arinya karama ta nemi maidani kaninta.鈥� Kwafa yai sannan ya danna ma secretary dinsa kira.
Yana shigowa ya sanar dashi a kira Khalid.
Komawa office dinta tai ta zauna tare da shan ruwa ta rufe idanunta.
*********
Khalid na garaje wayarsa tai kara dauka yai sai dai yanajin kiran na waye ya fito daga kasan mota da sauri, nan yace gashi nan zuwa.
Da sauri ya nufi gida cikin tsananin farin ciki dan da har jikinsa yai sanyi ganin ba鈥檃 kirasu ba.
Wanka yai ya shirya sannan ya shiga ya sanar dasu Umma.
Dadi agunsu Umma kamar me, nan suka hau zabgamai addu鈥檃 ya fito ya nufi tasha.
Tayi sallah kenan tana duba wasu takardu taji knocking.
Ramatu ce ta shigo tace 鈥淒irector suna jira.鈥�
Okay ganinan.
Takardunta ta mika mata tace 鈥測i photocopy din wadannan.
Da sauri ta amsa sannan ta juya, wayarta ta dauka ta kira Nabila.
Nabila ta dauka tace 鈥淎unty dan Allah anjima muzo?鈥�
Ina?
Gun aikinki, sai mu dawo tare.
Shiru tai kafin tace 鈥渟hikenan.鈥�
Tana ji suna ihu a tare ita dai ta kashe wayarta ta mike.
Tana bude kofar ta ciki yana bude kofar ta waje.
Kallansa tai sannan ta dauke kai ta kalli ragowar dake gun.
Da sauri Khalid ya karaso, suma suka mimike.
Suka matso inda take, Ramatu ce ta mika musu takardun datai photocopy kowa yadau daya sannan ta kallesu tace 鈥渕uje鈥�
Nan tai gaba suka bi bayanta zuwa broadcast room.
A lokacin ama gabatar da shiri, haka suka tsaya sukaga yanda ake, nan suka nufi control room, nan ma sukaga yanda akeyi, da yanda ake editing da sauransu.
Sai dasuka gama sannan ta sake yima kowa gwaji dan sai sun gama yimusu training an gwada sosai sannan zata san inda zata sa kowa.
Juyawa tai ta nufi office dinta.
Wani producer ne ya fito daga bakin kofa ya mika ma Khalid flask yace 鈥減lz kaima Director Zainab.鈥�
Amsa Khalid yai ya juya ya wuce, Afreey ce ta bishi da wani kallo mai wuyar fassarawa.
Sai da Ramatu ta nuna mai inda zaibi yaje office dinta.
Knocking yai sannan ta bashi izini ya shiga, tana zaune a kan computer desk, ta sa glass tana aiki, bata dago ta kalli wanda ya shigo ba har ya karaso inda take.
A hankali ta dago tare da kallansa, ganin Khalid ne yasa ta maida danta kan abinda take tace 鈥� ya akai?鈥�
Ajiye mata flash din yai a kusa da ita sannan yace 鈥渁ikoni akai.鈥�
Kallan flash din tai sannan ta kalleshi, shima kallanta yai.
Juyawa yai zai fita, har yayi taku biyu dai kuma ya tsaya ba tare da ya juyo ba.
Kallansa tai tace 鈥渕e? Akwai wani abu ne?鈥�
Juyowa yai yce 鈥渄a akwai amma yanzu babu.鈥�
Zare glass din tai tace 鈥渂aka da abinda zaka cemin?鈥�
Kallanta ya sakeyi yace 鈥渘o, I don鈥檛 think i have.鈥�
Tace 鈥渙kay shikenan.鈥�
Glass dinta zata maida yace 鈥渄a zan tambayeki how have you been? To amma energy din ki da na gani ranar interview yasa nasan bana bukatar tambayar.鈥�
Kallansa tai tace 鈥淢asu gida ya gida?鈥�
Yace 鈥淕idan mu normal, ya naku gidan?鈥�
Bata tanka mai ba ta cigaba da aikinta.
Shima bai nemi karin magana ba ya juya ya fita.
Yana fita ya nufi inda ya barsu.
Afreey dake tsaye daga tsakiyar corridor ya kalla, dauke kai yai kamar bai ganta ba, har ya wuceta tace 鈥淜halid!鈥�
Bai juyo ba sai dai yadan tsaya, tace 鈥淜halid!鈥�
Juyowa yai ya kalleta yace 鈥淥h Safeeya!鈥�
Kallansa tai tace 鈥減retending kake baka ganeni ba ko kuma dagaske kake?鈥�
Kallanta yai baice komai ba kawai ya juya yabar gun.
Da kallo ta bishi cikin wani yanayi, waya taba tunani zata tsinci Khalid anan?
Khalid ne ya koma suka cigaba da abinda suke, ransa yayi matukar baci duk juyowar dazaiyi zai ga idan Afreey akansa.
*********
Cikin tsananin murna Nusaiba da Nabila suka shiga mota, kaya iri daya suka saka, sai murna suke yau zasu fita dan sun gaji da zaman gida.
Har suka isa suna hira kai bakace sune masu fada ba.
Mamman ne yace 鈥測au lalai take sallah, haryanzu ba鈥檃i fadan gadan ba?鈥�
Dariya Nabila tai tace 鈥渄ama can wannan ce uwar neman fada.鈥�
Nusaiba tace 鈥渘i ko ke?鈥�
Dariya sukai dukansu Mammab yi parking.
Nabila ce ta kira Zainab, sai data kusa katsewa ta daga, tace 鈥淎unty munzo.鈥�
Ku shigo zan turo a karaso daku.鈥�
Cikin jin dadi suka fito.
Suna isa sukaga wani daga kofa nan suka sanar da inda zasu je, security din yace su jira ya tambayo.
Bai dade ba sai ga wanda zainab ta turo nan, murna kamar me suka taho suna murmushi.
Haka suka shiga ciki.
Kamar da wasa Nusaiba ta hango wani kamar Khalid.
Da sauri ta juyo ta kalli Nabila tce 鈥淣abila duba mun can kamar Uncle dina.鈥�
Uncle dinki? Kanin Mumy?
Haushi ya kamata tace 鈥測aya na to.鈥�
Yaya? Ina kika ga yaya?鈥�
Ran Nusaiba a bace tace 鈥渂ashi ma.鈥�
Ta dago taga bata ganshi ba, da sauri tabau waige waige.
Nabila ta sa hannu ta jata tce 鈥渋nka yaya ne in ma Uncle kya ganshi daga baya.鈥�
Har suka isa Nusaiba bata bar waige ba.
******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[12/6, 8:36 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
The worst part of holding the memories is not the pain. It's the loneliness of it. Memories need to be shared.
鈥擫ois Lowry
{39}
Khalid na kammala abinda aka sashi ya mike, ganin masu aikin rana duk sun tattafi yasa yadau jakarsa ya fito.
Office din Zainab ya kalla, a ransa yce 鈥渨annan agoggon ko ta tafi?鈥�
Fitowa yai ya sauko kasa, yana fita daga gate yaji ance 鈥淜halid!鈥�
Zabgegiyar mota dake gefensa ya kalla, Afreey ce a cikinta, kansa ya kauda ya cigaba da tafiyarsa, binshi take a hankali tace 鈥淜halid!鈥�
Tsayawa yai ya kalleta yace 鈥淪afiyya meke damunki wai?鈥�
Magana nakeso muyi.
Kallanta yai yace 鈥渋n inada ra鈥檃yi kenan ko?鈥�
Nasan in bakada ra鈥檃yin abu bamai saka canzawa, sai dai dan Allah ka tsaya muyi magana.
Kallanta yai, ya kalli wayar hannunsa yace 鈥渕inti uku na baki, menene?鈥�
Tana san cewa ya shigo amma tasan bazai taba shiga ba tunda maganar ma daya ta kare.
Kallansa tai tace 鈥渞anar........鈥�
Kallan daya mata ne yasa ta yin shiru, kafin tai murmushi tace 鈥渘asan duk abinda zan fada bazaka yadda ba, sai dai Allah ranar.......鈥�
Kallanta yai yace 鈥� can you stop talking about that?鈥�
Tace 鈥渒a san fatan da nake a koda yaushe akan Allah ya hadani dakai nama bayani?鈥�
It doesn鈥檛 matter to me, koma me ya faru a wannan lokacin bashida amfani a gareni kinsan me nake nufi in na fadi haka
Yana kaiwa nan yai gaba, da kallo ta bishi har sai da ya kulle.
********
Nusaiba na shiga ta kalli Zainab tace 鈥淎unty naga wani kamar Uncle a can.鈥�
Ta fada tana nuna mata inda ta ganshi, Uncle? A gidan wa kike da uncle anan?
Nabila ce tasa dariya tace 鈥淜anin Muny ya fara aiki anan ai.鈥�
Kanin ta?
Zainab cikin mamaki ta tambaya.
Nusaiba cikin masifa tacewa 鈥淣abila bansan wulakanci.鈥�
Gwalo Nabila ta mata tai gaba dasauri tana dariya.
Nusaiba ta kalla tace 鈥� waye Uncle?鈥�
Nusaiba tace 鈥淯ncle daya miki driver.鈥�
Uncle?
Nusaiba tai kasa dakai wai ita a dole kunya.
Gaba Zainab tai ganin batada lokacin wannan shirmen, mota suka shiga sunara fada Nabila tace 鈥渋n ba neman suna ba na tabbatar ko a hanya ya ganki bazai ganeki ba.鈥�
Nusaiba tace 鈥渋n bai ganeni ni ba ni sai na tuna mai ai.鈥�
Wata dariya Nabila ta saki wanda ya kara tunzuro Nusaiba.
Zainab ce ta kallesu tace 鈥測a isheni haka nan, Allah yasa insaki jin bakin wata.鈥�
Nan suka shiru, suna hararar junansu.
**********
Washegari....
Goggo ce ta zazzage lalitarta, naira dari ne a ciki kacal, wani irin ajiyar zuciya ta saki mai ban tausayi, ga wuta amma ko tv bata da niyyar kunnawa, saboda damuwar dake cikin ranta yafi karfin kallo.
Cikin ta ne yai wani irin kara, fitowa tai tsakar gida ta nufi waje.
Sai dai yau Adam baya ma kofar gida, haushi da takaici ya kara kamata, haka taje gun mai shayi ta sai bread na naira hamsin sannan ta koma ta hada tea, ta dau gwangwanin madara ta bude taga ba komai, yaushe suka siyo madarar? Milo ta bude shima taga ba komai, lalai Adam ne ya juye, ranta a tsananin bace ta sa sugar ta shaku ruwan buno da bread.
Zama tai tana tunanin abinyi.
Wayarta ta dauko da sauri tana san kiran Hajiya bilki, sai dai jitai ana ce mata batada kudi, haushi ne ya kara tiketa ta ajiye wayar ta kwanta kamar mara lafiya.
Adam na zaune suna musu a babbar majalisa, soron wani abokinsu suke zuwa susa kallo suyi ta musu ana hira da shewa, kallansu yai yace 鈥渨lh Allah da gaske nake.鈥�
Kai malam karka raina mana hankali, wannan ce matar taka.鈥�
Adam ya kalli Zainab dake jikin Tv yace 鈥渨lh da gaske nake.鈥�
Dariya suka sheke mai da ita, daya daga cikinsu yace 鈥渋n har kai mijinta ne to ni dan gidan Dangote ne.鈥�
Adam a hasale ya tashi yace 鈥渨ai ya zan tayi muku rantsuwa kuki yadda, da na dauko wayata wlh dana nuna muku.鈥�
Kallan jikinsa suka fara yi, wani yace 鈥淢alam kai ka maidamu kananan yara in bacci kakeji kai maza kaje ka kwanta.鈥�
Dariya suka sheke mai dashi, ran Allah yai matukar baci ya fito rai a bace, ya shige adaidaita.
Sam baima damu da kayan dake jikinshi ba balle silifas din dake kafarsa.
Kofar tv station din su Zainab yai parking, kallan dan adaidaitar yai yace 鈥渂ari na shiga na amso ma kudi.鈥�
Ransa a bace yace 鈥淢alam bansan wulakanci, bani kudina.鈥�
Adam yace 鈥測anzu zani gun Matata na amso maka.鈥�
Ciki yai da sauri, Security ne ya tareshi yana tambayarsa ina zashi.
Adam yai dariya yace 鈥渂aka ganeni ba? Mijin Zainab ne Adam.鈥�
Kallansa Security din yai sai yanzu yaga kamar sa amma meye hakan? Ya fada a ransa.
Adam ne yai ciki, duk inda yai kallansa ake ana mamakin waye wannan.
Haka ya shigo duk inda yai kallansa ake suna gulmar shigarsa dan duk sun sanshi.
Kan kace me zance ya yad鈥檜 akan mijin Zainab yazo, kamar an koroshi daga daji.
Khalid na zaune yana aikin da aka bashi, zancen yazo mai, cikin mamaki yace 鈥渕ijinta? Adam?鈥� Wata yar iska ya furzar yana tunanin meya zo yi? Da sauri ya mike ya nufi office dinta.
Zainab na zaune tana tattare takardun da zasu presentation a wani plastic company suna san suyi aiki dasu.
Knocking taji, kallan kofar tai tana tunanin ya kamata ta samu secretary dan dama an bata a farko itace bataso saboda gani take westing din kudin su sukeyi gwara tai abinta da kanta.
Izini ta bada ya tura kofar ya shiga, yana shiga Khalid na shiga corridor din.
Mutane ya gani ana leke ana gulma, juyawa yai ya koma ya zauna.
Tsananin mamaki ne ya kamata har ya shigo bata ce mai komai ba.
Adam yana ganinta yai murmushi yace 鈥淗oney!鈥�
Karasowa yai inda take yana cewa 鈥淵aushe raban dana ganki.鈥�
Kallansa tai tsaf sannan tace 鈥淢e kake anan?鈥�
Honey wallahi ganinki.......
Fuskarta ce ta canza sosai bacin rai ne ya bayyana a cikinta karara, yatsa ta nuna mai rai a bace tace 鈥渄on鈥檛 you dare call me with that name.鈥�
Tsoro ne ya kamashi, dan yanda yaga yanayinta ya canza gaba daya sai yaji ya kasa magana.
Kallansa tai bayan ta mike tace 鈥淯ban me kake min agun aikina?鈥�
Ho....Zainab......
Cikin tsawa da fada tace 鈥渕e ka daukeni? Wulkantani kazo yi ko mutuncina kazo ci.鈥�
Kai ya shiga girgizawa da sauri yace 鈥� ba haka bane wlh, bansan ya akai ba na ganni a bakin nan.鈥�
Wani murmushi tai tare da daga gira daya ta bacin rai tace 鈥渒a dauka bansan me kazo yi bane? Kazo ne ka ci mutuncina ka nunawa mutane bama tare yadda zan zama abin kwatance da wulakanci a cikin mutane.鈥�
Shiru yai jikinsa duk yai sanyi, tace 鈥渂a laifinka bane, kome kai laifina ne da ban sa an kulleka ba bayan abinda ya faru.鈥�
Komawa tai ta zauna tace 鈥渇ita!鈥�
Juyawa yai jiki a sanyaye kamar an mai duka, haryakai kofa ya juyo yace 鈥淜i taimaka min dana mota.鈥�
Kallansa tai yace 鈥渁daidaitar dana shiga ban biya ba.鈥�
Tace 鈥渂anaji wannan ya dameni, ka fita ko sai na sa an fitar dakai?鈥�
A hankali ya bude kofar ya fita, suna jin an bude kofa yan gulma kowa ya juya, ana kallan yanayinsa kowa da gulma dake cinsa.
Adam na fita suka shigo, daga gefen Khalid suka tsaya suna dariya, wani yace 鈥渨annan anya tana bashi abinci ma?鈥�
Dariya wani yai yace 鈥渄ama duk wanda ya auri wannan ai ya auri rashin kwanciyar hankali鈥�
Afreey dake kefensu tace 鈥渕ijinta ne?鈥�
Ramatu tace 鈥渆h.鈥�
Cikin mamaki Afreey tace 鈥渁mma yazo a haka?鈥�
Dariya sukai wani yace 鈥渋na kwanciyar hankali da alama daren jiya duka tamai.鈥�
Khalid wanda ransa yakai matuka gun baci yana dannewa ji yai wani yace 鈥渒ai harna tausayamai, wannan da alama ko abinci sai ya tambayeta yake ci.鈥�
Desk dinsa ya daka da karfi wanda yasa kowa kallansa, murmushi ya musu yace 鈥渁m trying to see how strong i am.鈥�
Kallan mamaki suka mai zasu cigaba da gulmar sukaji yace 鈥淎hhh ni yaushe ma akace za鈥檃i meeting din?鈥�
Ramatu ta kalli agoggo tace 鈥渂ata fada mana ba, wazai tambayo ta.鈥�
Da sauri kowa ya watse kai kace korarsu akai.
Ramatu ta kalli Khalid tace 鈥渒o zaka tambayota?鈥�
Mikewa yai ba musu.
Afreey tai shiru tana tunanin yanayin daya faru a wannan lokacin, tabbas dan a tsaya da maganar ya daki desk, meye nashi a ciki?
Knocking yai, ta bashi izini.
Bata dago ba sai daya maida kofarya rufe.
Dagowa tai ta kalleshi, tace 鈥測a akai?鈥�
Karasowa yai kawai taga yaja kujerar dake gabanta ya zauna.
Sake kallansa tai tace 鈥測a akai?鈥�
Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru, murmushi tai tace 鈥渒aganshi?鈥�
Hmmm
Murmushi tai tace 鈥渋t seems like kowa ya zama busy saboda hakan.鈥�
鈥淎re you okay?鈥�
Kallansa ta sakeyi tadan karkatar dakai kadan tace 鈥� kai da ka saba ganewa sai ka duba ka gani, am i okay?鈥�
Dan matsowa yai yana kallanta, juya kai tai gefe saboda batasan kallan, komawa yai ya zauna yace 鈥測ou are not.鈥�
Da sauri ta kalleshi tace 鈥渕ene?鈥�
Yace 鈥渢hen ke kina tunanin u are?鈥�
Tace 鈥渟osai, meka daukeni? Kana tunanin karamin abu kamar wannan zai sani damuwa?鈥�
Dan hannunsa yasa ya shafi wuyansa, harararsa tai tace 鈥渒ana nufin zai sani kenan?鈥�
Yanzu ma baice mata komai ba sai dai ya mata kallan eh.
Haushi ne ya kara kamata ta hade fuska tace 鈥渘aji ya sani, jeka kacemusu bayan lunch xamuyi meeting din.
Okay yce sannan ya mike, haushi ne ya kara dan kamata ganin ya mike hankali a kwance tace 鈥渕ikomin ruwa a fridge.鈥�
Juyowa yai ya kalleta, alama tamai daya miko mata, kallanta yai sannan ya bude fridge ya dauko ya zo gabanta ya ajiye, har ya juya tace 鈥渟aura cup.鈥�
Kallanta ya sakeyi sannan ya dauko yazo ya ajiye mata, harya sake juyawa tace 鈥渙hhh ga wani file can a saman shelf daukomin.鈥�
File? Ya fada yana kallanta, tace 鈥渆h.
Dauko mata yai yazo gabanta ya ajiye yana kallanta.
Juyawa yai tace 鈥淥hhhh bana san shan ruwan nan zo ka siyomin fanta a shagon kasan layi.鈥�
Takowa yai yazo inda take, tana guntse dariyarta ta dauko 1000 ta mika mai, amsa yai sannan ya kalleta yana juya kudin sannan ya mika mata.
Kallansa tai tace 鈥渘a meye?鈥�
Yace 鈥淥hhh bakya san ruwa ya kamata kije ki siyo fanta.鈥�
Fuska ta tsuke tace 鈥渒ana nufin na fita na siyo?鈥�
Kudinta yakara mika mata yace 鈥渂a wannan a cikin aikina.鈥�
Tace 鈥渋n babu senior dinka a gun aiki tasa ka by right kuma dole kayi.鈥�
Dan ajiyar zuciya yai yace 鈥渂y right zanyi amma in har bani da abinyi kenan.鈥�
Ya ajiye mata kudin sannan yace 鈥測anzu na fahimci you are okay.鈥�
Kallansa tai tace 鈥淪am baka biyo halin Umma da Abba ba.鈥�
Shima kallanta yai yace 鈥渒ema baki biyo halin Dady ba.鈥�
Wani kallo tamai tace 鈥渂akinka baya rasa abin fad鈥檃 ne?鈥�
Yace 鈥渋n har naki bai rasa ba.鈥�
Hade rai tai tace 鈥� mene?鈥�
Bai bata amsa ba ya juya ya ya fita.
Yana fita ta kalli kofa, sannan ta kalli kudin.
Khalid na fita ya samu kansa da dan murmushin da baisan daga ina ya fito ba.
Afreey dake nesa a tsaye ce ta kalleshi sannan ta tako inda yake.
Kallanta yai bayan ya hade fuska yana neman wucewa.
Tace 鈥渕enene tsakaninku?鈥�
Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kawai yai gaba.
Shiru tai tana kallan office din Zainab.
0 comments:
Post a Comment