Aunty ce ta shigo daki inda Zainab ta idar da sallar isha鈥檌.
A bakin gado ta zauna ta kalli Zainab cikin jin dadi wanda fuskarta ta kasa boye hakan tace 鈥渘agode sosai Zainab, yau bakisan irin farincikin da kika sani ba.鈥�
Zainab dake kallanta tace 鈥渒iyi hakuri Aunty yau ma badan Khalid ya sani zuwa ba da haka zan ta cigaba da zama kamar banda kowa.鈥�
Dan ajiyar zuciya tai tace 鈥淒a alama kinyi dacen miji na gari, Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa.鈥�
Samun kanta tai da cewa Ameen, wanda hakan yasa Aunty murmushi tace 鈥渄a alama ana san wannan mijin.鈥�
Kallanta tai tana murmushi tace 鈥渂ansani ba Aunty, bansan ya akw gane ana san mutum ba, na dai san kawai yanzu rayuwata ba daya take dana da ba, inaji kamar bazan iya yini ba tare da shi ba.鈥�
Ta karasa maganar tana sauke kanta kasa, Aunty ta dafa kafadarta tace 鈥淜iyi kokarin faran tamai rai da janshi a jiki, mazajen yanzu ka ja su a jiki ma ya aka kare bare, na tabbatar shi zai nuna miki me nene a ranki.鈥�
Zainab tadan kalleta, Aunty ta dan dafa kafadarta tace 鈥淎llah ya kareku dwga sharrin masu sharri, amma anan gidan zaku cigaba da zama?鈥�
Zainab tace 鈥淓h nan yake so.鈥�
鈥淗aka ne, kin kyauta Allah ya kara muku fahimtar Juna.鈥�
Ameen tace sannan ta kalleta tace 鈥淎unty har yanzu baban Amira?鈥�
Murmushi tai na yake tace 鈥測ana leko nan sanda ya ga dama kawai dai baya zama ne.鈥�
Shiru Zainab tai tana mata kallan tausayi, Aunty tadan harareta tace 鈥渉ar mun saba ki daina min kallan tausayi.鈥�
Wayar Zainab ce tai kara Aunty ta miko mata ita, ganin Khalid ne yasa tadan juya baya ta dauka 鈥淯r sweet ya iso.鈥�
Kana waje?
Eh
Okay ganinan zuwa.
Kashe wayar tai ta kalleta tace 鈥渮amu wuce.鈥�
Kinasan wani abu?
A鈥檃 ta fada tana gyara dankwalinta.
鈥淒ama ke kam ta yaushe zakice ma kina san abu? In dai akwai abinda kikeso ki fadamin ko Samira sai na aiko ta kawo miki.鈥�
Zainab ta daga kai sannan ta dau mayafinta ta yafa.
鈥淒an Abin matan nan na bar ajiyarsu saboda kinga yanda muke zaune da shi, amma in kinaso zansa a kawo miki.鈥�
Tana jinta amma sai tai kamar bataji ba tana kiran Amira, haka suka fito yaran suka rakata har mota.
Suna fita daga gidan ta tsuke fuska, baiko kalleta ba shima ya dauke kai haushi ne ya kamata ganin suna ta tafiya baice komai ba tace 鈥渋na kaje da ka gudu?鈥�
Ina kike san naje?
Kallansa tai tace 鈥渢ambaya da tambaya?鈥�
Amsa da amsa?
Juyowa gaba dayanta tai tace 鈥渂a dai....鈥�
Jin ya kamo hannunta ne yasata yin shiru, hannunta ya rike yace 鈥渂a dai me?鈥�
Murmushi tadanyi tace 鈥渟akeni dare yayi kana tuki da hannu daya.鈥�
Sai kin kira sunana tukun.
Kallansa tai tace 鈥渘ifa Allah bansan ya akai na samo sunan nan ba.鈥�
Koma ya akai kika samo ni sunan yamin.
Murmushi sukai dukansu, har suka isa gida.
*********
Washegari
A hankali ya bude idanunsa ganinta kwance kusa dashi ne yasashi sakin wani sanyanyan murmushi, hannunsa yasa a gefen fuskarta yana dan shafawa, mostin dayaga tayi ne yasa shi zare hannunsa.
Wayarsa ya dauko yana duba time, yana kokarin sauka yaji ta rikeshi.
Juyowa yai ya kwanta yana kallanta, idanunta ta bude tace 鈥渟hiri?鈥�
Eh.
Inka tafi sai dare?
Bakya san na fita na dade?
Shiru tadanyi, hannunta ya kamo ya daura akan fuskarsa.
A hankali yace 鈥渮an dawo da wuri鈥�
Murmushi tai tace 鈥渒adan taimaka min da printing din wasu takardu.鈥�
Okay.
Ya fada kallan juna sukai a hankalu ya matso ya sumbaci bakinta, sannan ya zame gefen kunnenta yace 鈥渟ai yaushe?鈥�
Murmushi tai tace 鈥渒wana 9 nake.鈥�
A zabure ya dago yace 鈥渢a me?鈥�
Ta hade rai tace 鈥渢ara鈥�
Kallanta yai yace 鈥渢ara? Da gaske kike?鈥�
Eh ya zanyi?
Wani abu ya hadiya kawai ya mike ya nufi toilet, dariya tadanyi sannan taja bargo ta rufe fuskarta, wai Khalid baida kunya dama?
Sako ne ya shigo wayarsa, bata kalli wayarba bare tasa ran dauka tana kwance tana murmushi ita kadai, jiya kwata kwata bata bude laptop dinta ba, anya lafiyar ta kalau kuwa? Kwanan nan aikin ma ba sosai take ba batasan meyasa in tana tare da Khalid mantawa ma take da maganar aiki.鈥�
Kunyar kanta da kanta ne ya kamata ta kara shigewa bargo.
Khalid ne ya fito bayan yai wanka yai alwala.
Kallanta yai yace 鈥渒in koma?鈥�
Dan idanun ta ta leko ta kalleshi, zama yai a bakin gado yana shafa mai yace 鈥渋nata san tambayarki izinki nawa a karatu?鈥�
Karkamin dariya.
Yadan kalleta yace 鈥渂a鈥檃i abin arziki ba kenan?鈥�
Tace 鈥渢unda na gama primary na daina zuwa.鈥�
( Magana ta gaskiya wannan matsalar tana addabarmu, iya kacin karatunmu na islamiya daga primary ne, da zaran an fara secondary an girma shikenan an daina zuwa islamiya, ana ganin an girmi zuwa islamiya amma bamu girmi karatun boko ba, dan Allah ko ba a je islamiya ba mu dinga kokarin yin tilawa a gida, dan Allah dayawan mu sai mifi wata ko qur鈥檃ni bamu bude ba.
Ke da ni da shi da ita dan Allah mu dinga tunawa da Al-Qura鈥檃ni muna karantashi ko ya ya ne, in karatu kullum bazai yiwo ba a kalla duk bayan kwana biyu ka karanta.
Allah yasa mu dace Ameen)
Vest dinsa yasa sannan ya fara sa kaya yace 鈥渂iyar?鈥�
Tace 鈥渁鈥檃鈥�
Kallanta yai yace 鈥渂adai biyu ba?鈥�
Dan dariya tai tace 鈥済oma, biyar kass biyar sama.鈥�
Agoggo yasa ya dau wayarsa ya matso kusa da ita ya nuna mata kuncinsa, dan shiru tai tana kallansa.
Kallanta yai ganin yanda ya kalleta yasa ta fahimci yaji haushi, neman dagawa yai da sauri ta riko wuyan rigarsa ta sumbaceshi a kan labansa.
Tana neman sakeshi ya sa hannu ya kara riketa ya kai bakinshi cikin nata, dagowa yai a hankali yace 鈥淎llah kwana tara yamin yawa.鈥�
Jan bargo tai ta rufe fuskarta juyawa yai ya fita.
Sam bai ciro wayarsa ba saboda ganin yadanyi late yana fitowa daga masallaci ya wuce gun aiki.
Yana ta aikin wayarsa tai kara, zarota yai ya duba ganin Abba ne yai saurin dauka suka fara hira.
Sai da sukai sallama sannan yaga sako, budewa yai idanunsa ya zaro yana kara kallan sakon, cikin tsananin farin ciki ya tura sakon wayar Zainab.
Zainab kam bacci kadan tai ta tashi tai wanka sannan ta fara aiki, turamai takardun da zai mata printing tai ta email.
Mikewa tai ta hada tea tana sha tana aiki, shiru tai tana kallan screen samun kanta tai da murmushi.
Ya xaiyi in nace nai wanka?
Fuska ta rufe ita kadai kamar wanda yake gabanta sai murmushi take kai kace albishir aka mata.
Jin sako ya shigo wayarta ne yasa ta dau wayar tana fatan Khalid ne.
Ganin shidin ne yasa ta bude sakon da sauri.
Cikin hanzari ta kira wayarsa, Khalid wanda yai murmushi ganin kiranta ne ya mike yai gefe ya daga wayar.
Zainab cikin farin ciki tace 鈥淵anzu naga text.鈥�
Bari na zo gida.
Yanzu?
Eh
Ya fada batace wani abunba ya kashe wayar ya kalli shugabansu yace 鈥渮aije gida sannan daga yau bazai sake zuwa ba dan ya samu aiki.鈥�
Sosai ya tayashi murna dan ya san kwazon Khalid.
Jin Khalid zaizo yasa Zainab ta mike da sauri tai kitchen kawai ta hau shan robar hadin nan da aka bata.
Kunyar kanta ne ya kamata tasa dariya ita kadai tana mamakin me take yi,
Mai zaici?
Indomie ta fara kokarin sawa.
Khalid kam gida ya wuce direct yana bude kofar falo tana fitowa daga kitchen.
Wani murmushi ya mata sannan ya bude hannayensa.
Murmushi tai itama hakoranta suka fito tace 鈥渂adai nufinka in ruga in rungumeta ba?鈥�
Hade fuska yai yace 鈥渋dan bakiyi ba kuwa komawa zan.鈥�
Kaifa kace zaka dawo bani nace ka dawo ba.
Ina cikin farin cikin ma bazaki min ba?
Kallansa tai shima idanunsa na kanta, takowa ta fara yi a hankali har tazo inda yake.
Hannu yasa ya jawo ta jikinta ya rungume kawai sai jitai ya dan dagata.
Dariya tasa tana dan dukan bayansa tace 鈥渁jiyeni dan Allah.鈥�
Ajiyeta yai ya kalleta kallansa tai tace 鈥淐ongratulation.鈥�
Thanks dear.
Ya fada yana kallanta, idanu ta dan zubamai, sannan ta kamo hannunsa ta bude tafin hannunsa.
Murmushi yai yace 鈥渕enene?鈥�
Wad鈥檃nnan hannaye sunsha wahala
Kallanta yai yana murmushi.
Idanunta ne suka ciciko ta dago tana kallanta cikin magana mai shirin kuka tace 鈥測anzu ka daina aikin ginin.鈥�
Kai ya daga mata fuskarsa a sake, ta kara cewa 鈥渒a daina aikin mota?鈥�
Murmushi yai ya daga mata kai.
Sakeshi tai jin zuciyarta na rauni tai kitchen da sauri.
Kallanta yai kafin ya bi bayanta, shiga tai tana sa indomie.
Kusa da ita yazo ya sa hannu ya rungumeta ta baya yace 鈥渕enene?鈥�
Bata juyo ba tace 鈥渂akomai, ya Umma tai?鈥�
Kansa yadan tukufo ya kwantar a bayanta yace 鈥渒uka kikai?鈥�
Bata juyo ba tace 鈥渂ansan meke damuna ba wlh, nifa ina dadewa kafin nai kuka amma yanzu komai sai naji inaaa...鈥�
Sai kuma tai shiru, murmushi yai sannan ya kalli kusa da ita ganin bottle a bude yasa ya kalleta yace 鈥渘a meye?鈥� Yai maganar yana dauka.
Kwacewa tai da sauri tace 鈥淢akociyar mu ce ta bani.鈥�
鈥淢enene? Kikasha kuma?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渂a sai kaji ba鈥�
Tai maganar tana boyewa a batanta.
Dariya yadanyi yace 鈥渒awai daga zuwa ta baki abu sai ki hau sha? Sannan harda kin fadamin?鈥�
Jeka jeka falo ka zauna.
Ta fada tana turashi.
Murmushi yai ya fita.
Falo ya zauna ya dau waya ajiyar zuciya yai ganin uban kiran da Afreey da Adam suke mai.
Number Adam ya kira, ringing daya Adam ya dauka, yace 鈥渄an gidanku kana ina? Kana ina nace?鈥�
Yai tambayar cikin zafi da fada kamar wanda ke shirin dukansa.
Khalid yace 鈥渒aje Naibawan?鈥�
Uban Naibawa zani ba Naibawa ba, ka yaudareni ka cuceni sannan kace wani nace Naibawa, kana ina?
Khalid yace 鈥渕u hadu an jima, a Naibawar daka tsana.鈥�
Bai jira yace wani abu ba ya cigaba 鈥渮an turoma da Address din dan nasan ka manta gidan, in mun hadu acan naji me kake san cewa.鈥�
Wayarsa ya kashe sannan ya kalli sakon Afreey kala kala data mai, kansa yadan dafa yana cikin tsananin farnciki amma ana neman sashi tunani.
Kiran Abba ne ya sake shigowa, nan Abba ya kara tayashi murna yace 鈥測aushe zaka fara?鈥�
鈥淏ansani basai gobe suka ce naje.鈥�
Khalid dadi ya hanani rufe baki.
Kace Umma taci abinci kar dadi ya hanata.
Shigowar Zainab falan ne yasa ya kalleta, tare da yin sallama da Abba.
Batai auni ba taji ya jawota kan cinyarsa.
Plate din hannunta ta rike sosai tace 鈥渮aka sani bari.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渢unda Allah yayi yanzu na bar wancan aiki, haka zan zauna na saki a gaba ina kalli har sai kin cika 9 days?鈥�
Tace 鈥渢o ya kake so nayi? Ka dai san ba鈥檃yi.鈥�
Na sani amma kwana 9 tsakani da Allah?anya Sweet din nan naki zai iya jira?鈥�
Dariyarta ta guntse tace 鈥渨ai sai wani kiran kanka Sweet kake.鈥�
鈥淚n baza鈥檃 kirani da hakan ba ni ba sai na kira kaina dashi ba?鈥�
Murmushi tai ta ajiye plate din sannan ta mike yace 鈥淒ady na gaidake.鈥�
Kunyi waya ne?
Eh na fadamai an samu aiki.
Murmushi tai, plates din indomie din ya dauka ya kalleta yace 鈥渢hanks.鈥�
Murmushi tai tana kallansa yana ci, meyasa kwanan nan take jinta kamar wata yar mitsilar yarinya?
Bai kalleta ba sai jitai yace 鈥渘i adaina kallo na, abarni da takaici kwana 9.鈥�
Mikewa tai tsam ta dau wayarta tai daki, tana shirin shiga tace 鈥渘a gama鈥�
Ta shige daki, na gama? Ya maimaita cikin rashin fahimta, da sauri ya kalli kofar dan ya gane.
Jiyai ya koshi da abinci ya mike tsam yai hanyar daki.
*********
Zazzabin daya rufeta ne yasa Mumy saukowa gun mahaifinta tana sanar dashi halin da Afreey ke ciki, kallanta yai sannan yace 鈥済arin ya ya?鈥�
Wlh bansani ba yanzu na shiga naga bata je aiki ba na ganta a kwance.
Mikewa yai ya hau sama inda tafkeken dakinta yake, tana kwance cikin bargo sai kallan wayarta takeyi.
Abbi ne ya zauna tare da yaye mata bargo, kallansa tai tana hawaye.
Yace 鈥淏aby na menene?鈥�
Mikewa tai ta rungumeshi tasa kuka.
Hankalinsa ne ya tashi ya na tambayar menene.
Tace 鈥淎bbi bazan iya hakura dashi ba dan Allah ka kwatomin shi.鈥�
Wanene?
Kallanss tai tace 鈥淜halid.鈥�
Ajiyar zuciya yai yace 鈥渟au nawa ina miki magana akan wannan talakan yaran? Na dauka tun a makaranta na hanaki?鈥�
Kallansa tai tace 鈥淎bbi please.鈥�
Mikewa yai rai a bace ya bar dakin.
Haushi ne ya kamata kawai ta zubo da duk kayan dake kan madubinta.
Abbi na jinta, Mumy na kokarin shiga yace 鈥渂atta.鈥�
*******
Takardun da aka watsomai ne yasa ya kalleshi yace 鈥淜ayi hakuri yaya.鈥�
Ni zaka maida dan iska? Ce maka skai banda abinyi ko me? Ko kuwa ce ma akai kudin da na sa na bude gidan Tv dinan a waje na samosu? Yau zan kira Zainab ta taimaka ta dawo, in kuma har bata yadda ba to zan sai da gidan tv din nan da a gurina yanzu bashida wani amfani.
Kafin Kabir hai magana ya juya ya fita.
Cikin takaici ya ke sakin huci na jin haushi.
Ya zaiyi?
Ya zaiyi?
Nace wa kake tambaya馃檮
*******
Da kyar Sadiya ta bata hamsin aka siyo mata kati ta nufi gun network tana komarin kiran Hajiya bilki.
Wayar Adam ce ta shigo dauka tai da sauri tace 鈥淎dam an dace?Afir ta samo mana aikin?鈥� Tai tambayar cikin zumudi.
Adam yace 鈥渨ake zancen aiki rayuwata tana neman karewa an kwacemin mata?鈥�
Mata? A gidan ubanwa kaga mata?
Zaina.....
Kaifa bakada hankali wasa wasa, wato ba neman aiki kake kazo ka daukeni ba can ka cigaba da haukarka.
Goggo Khalid ne fa ya aureta?
Waye Khalid? Inama maganar aiki kana min maganar Zainab.
Khalid fa Goggo abokina driver din nan.
Idanu ta zaro hankali a tashe tace 鈥渕e?鈥�
Nace mele馃檮
******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/11, 11:28 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
{63}
Kofar dakin ya bude, a tsaye ya ganta jikin wardrobe tana duba abu.
Kofar ya maida ya rufe sannan ya ya tako zuwa inda take.
Kallansa tai tace "har ka gama cin abincin?"
Hannu yasa a kugunta ya dan jawota a hankalu yace "ta ina zan iya ci?"
Idanu tadan raba tace "dalili?"
Dan fuska yadan gimtse kadan yana kara jawota jikinsa.
Kikace kin gama.
Ido tadan zaro tace "na gama me?"
Kallan mamaki ya mata yace "me kike nufi?"
Tace "cewa mai ka gama, cin abincinka nake nufi."
Saketa yai fuskarsa a daure yace "ka gama? Haka kika ce kenan?"
Eh da kai mai kake tunani?
Haushi ne ya kuleshi ya kalleta yace "ba sai kinji ba."
Dariyarta ta guntse tace "ina zaka?" Ganin ya juya.
Baiko kalleta ba ya shiga toilet, yana fitowa ya ganta akan gado tana bude wasu takardu, ransa ne ya kara baci ya nufota zai wuce ya koma falo.
Har yadan wuceta yaji an riko rigarsa, bai kalleta ba ya kwace rigarsa zai wuce.
Ji yai ta riko hannunsa, juyowa yai ya kalleta, tace "ina zaka?"
Kin amsa mata yai sai dai kallanta da yai, tace "azahar tayi? Dan wani sa'in banjin kiran sallah da rana, kar na makara banyi sallah ba."
Wani murmushi ya saki yace "are you playing with me?"
Murmushi tai itama ta daga kai tace "eh, sai dai da alama nayi winning."
Baisan sanda ya sake yin wani murmushin ba yace "ramawa kikai kenan?"
Sakeshi tai tana cewa "at least ka sani, me? Zaka ajiyeni kaje gunta? Nima a kalla na rama rabi."
Hannu yasa ya riketa yai baya da ita ta kwanta sannan ya kwanto yace "ba laifi at least for me ina san mace tai kishi na."
Fuska ta hade tana kallansa tace "yaushe nace kishi nake?"
Hannunyasa yana shafa gefen fuskarta yace "inje gunta? Ko in nuna miki kira nawa tamin?"
Wata harara tamai tace "sai ka dawo." Ta dan sa hannu tana neman tureshi, hannunsa ya rike yai baya dashi kan gado sannan yace "fadamin me kika ce dazu?"
Fuska ta daure tace "kaji meye na tambaya?"
Murmushi yai a hankali ya karaso yakai bakinsa cikin nata..............to dai an lula馃お
聽 Yanda take fitar da numfashi a hankali idanunta a lumshe tana jin wani irin shauki na ratsata, bata taba tunanin abinda ake ji yakai haka ba, ita da Adam iya kaci ayi abu wani sa'in ko minti goma baiyi ake gamawa, dan ita abin ma sam baya kanta daga anyi an wuce gun take shiga wata sabgar.
Jin hannun Khalid ya jawota ya kwantar a kan bayansa yasa ta kwantar da kanta idanunta har yanzu a lumshe suke, tana fitar da numfashi a hankali ta dan ja bargo ta rufesu.
A hankali taji muryarsa yace "ashe shi yasa naji bazan iya cin indomie din ba."
Hannu tasa tadan mintsineshi kadan tace "wai ni haka kake ko yanzu ne ka zama haka?"
Murmushi yai baiyi magana ba, wani irin dadi ne ke ratsa shi.
Zainab kam tuno yanda al'amarin ya kasance dazu tai, dole gobe ta shiga makota gun Maman Al'amin.
Khalid ne taji yace "Ina so zamu hadu da Adam zamuje Naibawa ne."
"Adam? Me zakuyi?"
Tai tambayar cikin mamaki, yace "Gidan su Raziyya ina tsoron kar mahaifiyarta ko mahaifinta wani ya rasu Adam be nemi yafiyarsu ba?"
Me ya musu?
Juyowa yai ta kwanta a kafadarsa, yasa hannu a tata kafadar yana dan shafawa ya fara bata labarin abinda ya faru.
Hawaye ne ya shiga zubo mata yana diga akan kirjinsa, tadan dago ta kalleshi tace "Da alama ni......."
Dan dagowa yai ya sumbaceta hakan yasata yin shiru sai hawaye daya gangaro.
Ya kalleta yace "ba laifinki bane, san zuciya ce ta Adam tasa hakan ya faru, kuma alhakinta ne ke binsa."
Idanu tadan runtse, kallanta yai yace "ki daina dorawa kanki laifin wani, bake kika sanshi yai ba, sannan baki san da ita ba."
Kallansa tai sannan ta daga kai a hankali alamar gamsuwa.
Murmushi yai itama ta saki murmushi........
*************
Masha Allah Khalid anje Zenith an kuma turashi bank na Zenith dake ka titi zoo road wajen Sahad store, duk da daga kasa zai fara amma Alhamdulila shikam dadi yakeji kwarai da gaske.
Zainab kam yau da aiki ta tashi sai data gyara ko ina na gidan ta shige gidan Maman Al'amin, sunyi hira nan taga suna ta hade hade, ana ta hidima, itama ta sai nata ta zauna tana mata bayanin yanda ake amfani dashi.
Zainab kam kunya take in taji Maman Al'amin na mata sharhi, nan ta tambayeta kananan kaya tace "ai gobe ma zata kasuwa."l
Zainab ta ce itama zata kawo kudi a siyo mata, tayi mamaki ganin awanta daya da rabi a gidan ita da sam bata zuwa makota gidan yan uwa ma ya aka kare.
*******^^
Karfe 2 Khalid ya fito, dan sai gobe zai fara aikin full, ga shigar da zasu dinga yi ma a kayyada take.
Ajiyar zuciya yai sannan ya dau wayarsa聽 ya kira Adam wanda yana kaance cikin bargo takaici ya gama isarsa.
Yana ganin kiransa ya daga jin muryar Khalid yai yace "ka fito mu hadu."
Adam zai yi magana yaji karar katse layi, wani kululun takaici ne ya kamashi, a kufule ya mike yana neman abinda zaisa, ransa bai gama baci ba sai daya ga ba kayan dazaisa a dakin, sai wata riga da wando na jeans haka yasa ya fito.
Aljihunsa ya duba naira hamsin ce dashi, haka ya hau bus yana tafe rai a bace dan bus din an cika ga sai kwaraf kwaraf take.
A titi aka saukeshi ya fara tafiya.
Kusa da gidan ya tsaya rai a bace yana duba Khalid, kenan nama rigashi zuwa ko me?
Daga nesa ya hango Khalid, ji yake kamar ya ruga ya bishi ya danneshi yai ta naushinsa har sai ya ji dalilin daya sashi auran matarsa.
Har Khalid ya iso gun idanun Adam na kansa kamar zai cinyeshi.
Khalid ne ya kalleshi yace "Sorry ban iso da wuri ba."
Adam ne ya karaso kusa dashi ya dunkule hannu yana kallansa rai a tsananin bace yana huci.
Khalid ya kalleshi yace "menene?"
Tambaya kake?
"A'a amsa nake."
Ya fada yana kallan gidansu Razy.
Haushi ya kara tuke Adam ya dan bugi kafadar Khalid yace "banda cin amana ka rasa wanda zaka yaudara sai matata? Hannu ya dunkule ya naushi Khalid wanda sai daya fadi gefen bakinsa ya fashe, wani murmushin jin dadi yai.
Muryar Khalid yaji yace "tunanin me kake?"
Kallansa yai da sauri kenan ba naushin yai ba?
Khalid ne yace "muje?"
Adam a kufule yace "da gaske Honey ka aura?"
Honey? Wa kenan?
Adam ya hade rai sosai yace "Da gaske Zainab ka aura?"
Kallansa yai sannan yasa hadu yadan daki kafadarsa yace "meye naka na tambayar matar wani bayan ba saka akai ba?"
Baijira yace wani abu ba yace "muje."
Adam ji yai kamar yai ihu dan bakin ciki, kofar gidan Khalid yadan buga daga cikin dattijon ya fito ya bude yana tace "waya rufe kofar."
Khalid ya kalla cikin jin dadi yace "oh saurayin nan kaine?"
Khalid yadanyi kasa dakai yana cewa "nine baba."
Cikin farin ciki yace "bismillah."
Nan ya koma ciki Khalid ya kalli Adam sannan yai ciki, shikuma ya bishi rai a bace.
Baba na shiga ya fara kiran Raziyya wacce ke kwance tana daddana waya, bakin cikin gidan duk ya isheta.
Baki ta saki ganin Khalid, kallan Adam tai, shima ya kalleta.
Fuska ta hade tace "me kake anan?" Tai tambayar tana kallan Adam.
Baba ne yace "Ah kinsan shi ne?" Yai tambayar yana cewa "Bismillah kuzo ku zauna."
Khalid ne ya fara zama sannan Adam ya zauna a darare.
Khalid ya ajiye ledar lemo da ayaba daya siyo yace "Ina wuni?"
Baba ya amsa, Adam be ya gaisheshi ya amsa sannan ya kuramai ido yace "kamar na san......."
Muryar Razy ce ta tabbatar da tunaninsa datace "Baba baka ganeshi ba? Kalleshi da kyau."
Shiru Baba yai yace "ya isa haka nan."
Kallan Adam yai yace "me kake anan gidan?"
Adam yai shiru jiki a sanyaye.
Baba yace "me ya kawo ka?"
Adam ne ya kalli Khalid gani yai Khalid din bai ko kallan sa, hakan yasa yace "kuyi hakuri abinda ya faru."
Muyi hakuri? Me dame ka mana?
Adam yai shiru, muryar Baba yaji yace "ka san rayuwar daka jefamu? Kasan halin da muka shiga a tsawon shekarun nan?"
Adam ya kalli Baba jikinsa ne ya fara sanyi.
Baba yai dan gyaran murya yace "mun dauke ka kamar d'a amma ka saka mana da butulci, sai dai kaddara ta riga fata Allah yayi ta wannan hanyar ajalinta zaizo, sai dai mahaifiyarta dake kwance tun faruwar abin, da kanwarta data sadaukar da rayuwarta saboda mu........"
Shiru yadanyi yana kallan kofar dakin da maman take.
Adam kam jiyai idanunsa ya ciciko da kwalla, Baba ya kalleshi yace "idan aka fara cewa da ace bata sanka ba, da ace ka taimaka kazo, da ace da ace da ace...... to magana ta baci dan in abu ya faru ya riga ya faru."
Razy ce ta juya ciki da gudu tasa wani wahalalen kuka wanda su kansu suna jiyo kukanta.
Jin yanda take kuka ne yasa Adam zubar da hawaye, tabbas yanzu ne ya fahimci ya tafka babban laifi, ya dau alhakin su.
Gwiwowinsa yasa a kasa, yace "Baba ka yafemin, dan Allah......." yai maganar murya a raunane.
Baba ya kalli Khalid yace "mun gode sosai, ko dan darajar ka zan yafe masa, sai dai bansan mahaifiyarta da kanwarta ba.
Ni dai ma yafe mai, Allah ya yfe mana gaba daya."
Adam ne ya kara share hawaye yace "nagode sosai."
Khalid ne ya kalli Baba yace "zamu iya ganin ta?"
Eh tana dakincan.
Nan ya rakasu, ganinta yasa Khalid duk dauriyarsa sai da idanunsa suka ciki.
Gaba daya ta rame ta yamushe duk da baisanta ba amma kana ganinta zaka gane.
Tana dan jingine dan tana jin maganarsu a waje, bakinta a dan karkace yake maganar bata yinta yanda ya kamata sai dai tanayi wanda ke zaune da ita zai gane.
Khalid ya gaisheta ta amsa, Adam yasa gwiwowinsa a kasa yana gaisheta.
Tana ganinshi ta fara zubar da kwalla tai saurin kauda kainta.
Adam ya nemi yafiyarta, Baba yace "ki yafe masa tunda ya fahimci laifinsa."
Tadanyi shiru kafin cikin maganar ta tace "Allah ya yafe mana gaba daya, na yafemai."
Kuka Adam yasa yana kara basu hakuri, wanda hakan ya raunana zuciyarsu duka.
Haka suka fito daga dakin, Dakin Razy Baba ya kalla yace "Raziyya fito."
Ya dan murda kofar, jin kofar yai a garkame.
Raziyya? Fito ko?
Kuka kawai takeyi.
Khalid ne ya matso yace "Baba a barta daga baya ya dawo, da alama abin ya dawo mata, in ta dan huce ya dawo."
Baba ya jinjina kai sannan yai ma Khalid godiya.
Adam kam sai kara neman yafiya yake yana godiya har suka fito.
******
Allah ya yafe mana laifukanmu馃槳
Ameen
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/13, 9:20 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
The believers are those who spend in charity during ease and hardship and who restrain their anger and pardon the people, for Allah loves the doers of good.
Surat Ali Imran 3:134
{64}
Ajiyar zuciyar data sakeyi a karo na ba adadi ta sakeyi, wayar ta data rabe gida biyu ta kalla, dan tana jin Zainab tai auri kuma wai drivernta ta saki wayar kasa ta fadi, tagumi ta sake bazawa ta sake yin ajiyar zuciya.
Haka zata cigaba da zama anan damuwa ta mata illa, yanzu taya Zainab zata musu haka?
Tuno abinda Adam yai tai ta baza tagumi dan ba shakka tun daga nan komai ya tarwatse, ajiyar zuciya ta sakeyi, tana tuno yanda tai rayuwa cikin jin dadi da walwala, yanzu gata a wani dan dakin da ake ajiye abincin tumakai, sai shi ta gyara take lalabawa.
Mikewa tai ta fito, tana kallansu suna surfe suna hira, Sadiya na gefe tana ta fama yin abincin saidawa.
Kusa da ita taje tace "Sadiya zuban shinkafar a kwana yunwa nakeji."
Kallanta Sadiya tai tace "Goggo taya zan baki ribar? Kina gani yanda nake ta faman hada kudin nan saboda bikina."
Shikenan karki bani ki bari yunwa ta kasheni.
Ta juya a kufule, da kallo Sadiya ta bita sannan ta dau plate ta dan zuba kadan ta kai mata.
Goggo ta amshi kwanan tace "Sadiya ko zaki taimakan da dari biyar? So nake na koma kano."
Dari biyar? Bandashi gaskiya, haba Goggo yanzu dan Allah bakiji kunyar ma tambayata kudi ba? Ki tafi ki barni a gidan nan banda gori ba abinda naie sha har na dage na fara neman na kaina shine yanzu zakizo ki dauran wahala.
Cikin mamaki Goggo tace "sau nawa ina bada kudi daga can a baki? Sau nawa ina sa Zainab ta ba Adam kudi ya turo miki?"
Shiru tai kafin tace "amma daga baya ai daina turowa kukai."
To ko mun daina dai a kalla ai kinci rabanki kema, dari biyar shine kike fadan magana haka?
Jikin Sadiya ne yai sanyi tace "zan kawo miki anjima."
Ta juya ta fita.
Goggo ta sa hannu tana cin abincin........
*********
Khalid na fitowa ya nufi titi, Adam na binshi a baya, gaba daya jikin Adam yai sanyi har suka isa titi ba wanda yama wa wani magana a cikinsu.
A bakin titi suka tsaya, Adam ya dan matso kusa da Khalid a hankali yace "nagode."
Shiru Khalid yai bai kalleshi ba, Adam ya juya kai cikin kuluwar yanda ya manna mai, jiyai yace "ka san rayuwar da Raziyy tai a asibiti?"
Kallan Khalid yai, wanda idanunsa ke kan titi bai jiyo ba, yace "likitan saboda rashin kudi duk sanda zai duba Firdausi sai yayi amfani da ita, can you imagine how much she suffered?"
Hankalin Adam ne yai matukar tashi yace "wani irin bala'i ne wannan?"
Khalid ya kalleshi yace "a lokacin da kake can kana jin dadin rayuwa a kasan mace, su suna can suna cikin tashin hankali, a lokacin da kake can kana baccin asara su suna can suna zaman makoki, ko da wasa ka taba tunanin kaje ka ga ya suke rayuwar su?"
Adam ne ya hadiyi wani abu yana kallan Khalid, sai yanzu Khalid ya kalleshi yace "ka dawo gobe ka nemi yafiyar ta, dan duk wannan abin dake samunka alhakin su ne ke yawo dakai, nasan dama can kana da naka issue din amma abin bai kai haka ba.
Yana kai nan yaga adaidaita ya tsayar, ganin Adam yai ya nufo adaidaitar, ya kalleshi yace "ina zaka?"
Adam ya kalleshi yace "gidanka."
Kai me?
Kallansa yai yace "Kai kace in na shirya ganinta zaka kaini."
Khalid yai wani murmushi yace "yanzun ka shirya?"
Adam yai shiru.
Khalid ya matsamai ya fara shiga sannan ya shiga suka nufi gidanshi.
A bakin gate din dan karamin gidan suka sauka Khalid ya bashi kudi sannan yai gaba Adam nabinsa a baya.
Kallan gidan yai anan Zainab ke zaune?
Khalid yace "muyi sallah tukun." Ya fada tare da dan gangarawa hanyar masallacin da ake ta kiran sallah."
Sai da sukai sallah sannan suka fito Khalid ya kalleshi yace "yanzu me kakeyi?"
Aiki nake nema.
Aiki? Ina da ina ka ciki?
Adam adan kufule yace "Khalid wai ni kai abokina ne ko babana?"
Khalid ya kalleshi yace "kai ai ba a maganar abokantaka dakai, sai dai ai magana kai tsaye."
Me ka dauken?
Ya tambayeshi yana kallansa, Khalid ya shareshi suka nufi gidan.
Gidan Adam ya kara kallo da gaske nan Zainab take?
Danne tunaninsa yai yabi bayan Khalid.
*******
Zainab kam tana dawowa daga gun Maman Al'amin ta bubude abubuwan da aka bata, tunawa tai tace yawan shan fruit shine zata dinga yi musamman ma kankana da ayaba in ta hadasu ta barkada da madara, murmushi tai ta boyesu a drawer a kitchen sannan ta sa abinci tanayi ita kadai tana murmushi, fitowa tai ta hada turaren wuta ta turara kanta, tana yi tana kunyar kanta, batasan meke damunta ba, ta dade da sanin ana turara jiki dan Aunty tasha yi a gabanta ma amma sam rashin lokaci bai taba sa tayi tunanin yi ba sai yau.
Sai data gama ta fito ta zauna a falo tana duba aikinta, jefi jefi ita kadai sai ta saki murmushi, agoggo ta kalla a karo na uku, haryanzu?
Ta fada a ranta tana kallan wayarta, jin ana kiran sallar magrib yasa ta mike tai alwala, tai sallah, tana nade sallaya taji alamar sallama ana neman shigowa.
Wani irin farin ciki ne ya kamata sallayar ta ajiye ta fito da sauri, daga bakin kofa ta tsaya tana kallanshi.
Shima a bakin kofar ya tsaya yana kallanta, a tare suka sakarwa juna murmushi sannan cikin dan salo da ita kanta bata san tana da shi ba tace "sai yanzu?"
Dan taku biyu yai, ya bar Adam daga gefen kofa ta waje hannu ya bude mata, kafad'a ta noke tace "bayan kayi late dayawa."
Hannu ya kafa nuna mata da kansa, ta kara noke kafada, dan fuska ya hade yace "shikenan."
Ya fada yana neman zama, takowa tai a hankali ta rungumeshi.
Juyowa yai ya kara rungumeta cikin rada a kunne yace "I miss u baby."
Murmushi tai ta kara dan kankameshi.
Kamshin turaren wuta mai sanyi take yi, idanu ya lumshe a hankali yace "do u wanna kill me?"
Tace "in ka mutu wa zai kula dani?"
Tai maganar ne a ranta sam batasan a fili tai ba sai jitai yace "I........"
Dagata yai da sauri yace "bani kadai nake ba, na manta sam."
Kallan mamaki tamai tace "kai da waye?"
Kallanta yai da yake hijab din datai sallah yana jikinta, yace "Adam ne"
Adam? Wani Ad....Adam dai?
Yace "eh"
Me zaiyi anan?
Murmushi yai yace "matar abokinsa zai gani."
Fuska ta daure, yace "Adam."
Juyawa tai yasa hannu ya riko kugunta, matso da ita yai yana kallanta.
Kallansa tai, yace "bakon mijinki ne, tafiya zakiyi baku gaisa ba?"
Daidai nan Adam ya shigo, zuru yai yana kallansu, basu ma san ya shigo ba.
Zainab ce tace "am sorry, bansan me zai cemin ko nace mai bane."
Kome zai ce ko me zakici wannan abu ne daga baya? But at least ku gaisa."
Okay ta fada, sannan ta mai murmushi.
Juyowa tai kawai sukaga Adam a tsaye zuri, kallansa tai duk ya rame yai baki, Khalid ne ya ja hannunta ya zauna sannan ya zaunar da ita kusa dashi, ya kalli Adam yace "Adam zauna mana."
Adam ya zauna a takure, baki na dan rawa yace "Ho......"
Mugun kallon da Khalid yamai ne yasa yace "Zainab!"
Kallansa tai tace "kana lafiya?"
Idanunsa ne suka ciciko yadan takure yace "lafiya kalau ya gida?"
Lafiya ta fada tana kallan Khalid.
Adam ya kara kallansu, ya hadiye wani abu, duk sai yaji ya raina kansa, Khalid ne yace "dan kawo mai ruwa"
Cikin dan rada tace "nayi Abinci."
Murmushi yai yace "thanks dear."
Kallansa tai yace "kawo mana please."
Mikewa tai Adam na zaune na kallan ikon Allah yana ganin Zainab ta tashi ta kawo musu abinci abinda har suka gama zama a shekara 4 da sukai bata taba kawo mai abinci ba, ajiye wa tai sannan ta kalli Adam tace "Goggo fa?"
Yadan daure yace "tana kauye."
Kauye?
Cikin dakewa yace "eh ta koma can kafin na samu aiki."
Kai ga daga Khalid ne ya kalleta, ta koma ta zauna kusa dashi, yace "Baby ko zaki shiga ciki muci abinci tukun?"
Baby? Wa? Ni? Ganin tana ta aune aune ya kanta yasa ya ciro waya yace "kidan samin a charge."
Amsa tai tace "okay ku gama."
Ta wuce daki.
Tana shiga daki ta zauna a bakin gado tare da sa hannu a saitin zuciyarta dake bugawa da sauri, kwanciya tai tasa pillow ta rufe fuskarta, nice baby?
Ahhh wannan Khalid din ko? Ta fada sai kuma tai murmushi,.....
Nace ke kadai dai馃お
A falo kam Khalid ne ya zuba abinci ya kalli Adam yace "Adam Bismillah."
Adam ya kalleshi dan dai yana jin yunwa ne amma yanayin daya samu kanshi a ciki bayaji zaiso cin wani abu.
Haka suka zuba abinci, suna ci Khalid yace "yanzu meye plan dinka?"
Plan? Bandashi ina dai fatan samun aiki.
Ka tabbatar ma ni kana neman aikin?
Kunya ce ta kama Adam ya kalleshi, cikin jin haushin kansa yace "Afreey na tambaya."
Wani kallo yamai yace "meyasa kake so a rayuwarka ka dogara da wani? Bazaka gwada abu da kanka ba sai dai kai tabi kana neman a taimaka ma? Tundaga fara karatunka haryau baka kula komai wani bane yake maka? Haka kake so rayuwarka ta kare?"
Shiru yai jikinsa ya kara mutuwa yace "Khalid kai dani ba daya bane."
Ba wani ni dakai ba daya bane, duk dan Adam daya ake haifarsu, kai dai kasawa kanka ka biye zuciyarka banda san jikinka baka san komai ba."
Shiru yadanyi yanajin rashin Zainab a ransa, ga yazo yaga yanda suke rayuwarsu gaba daya ba kalar tashi ba, jiyai hawaye ya zubo mai.
Khalid ya kalleshi yace "ka zama mai kokarin neman naka wannan zaisa ka rage biye shirmen da zuciyarka ke raya maka a koda yaushe."
Dan shiru sukai Adam ya daure ya kalli Khalid聽 yace "Khalid da gaske Zainab dina kake aure? Gata dai na ganta naga kamarta amma gaba daya ba ita bace."
Khalid ya kalleshi yace "Wace Zainab dinka?"
Da sauri yace "oh"
Khalid ya dan sha ruwa yace "ka duba ka nemi abinyi, karka dogara da Afreey kasan halinta sarai, in har zata taimaka ma to ko kuwa komenene dole kabi abinda take so, sannan maganar matata bana san menene dalilinka na tambayar matar da ba muharramarka ba."
Adam yai shiru yana cin abincin, har saida suka gama ba wanda ya sake magana, Adam yasha ruwa Khalid ya kalleshi yace "kafin ka samu aiki zaka gwada wanda nai da?"
"Wanene? Zan iya ko wani aiki ne indai ba aikin karfi bane."
Khalid ya kalleshi, kamar zaiyi magana ma sai ya fasa.
Adam yace "kayi shiru."
"Kafi kowa sanin aikin karfi nake to cewa ba aikin karfi ba kana nufin baka so kenan."
Adam yadanyi shiru dan shikam bashi da karfin yin aiki gaskiya.
Mikewa yai ya shiga daki, Zainab na kwance akan gado tana searching a google.
Khalid ne ya kalli wayarta ganin harya shigo bataji ba, hannu yasa ya fizge wayar.
Mikewa gai da sauri tana neman kwacewa.
Dariya yai ya daga wayar sama, hannunsa ta shiga jawowa tana san kamo wayar.
Kafada ya daga mata sannan ya dan karkace kai kadan yana kallanta.
Tace "bani please."
Kai ya daga wayar na sama ya fara karantawa.
Love name to call your husband?
Fuska ta rufe da sauri cikin jin kunya, dariya yai ya kalleta yace "abinda kike nema kenan?"
Fuska ta dauri ta kalleshi tace "Wata ke so shine zan tura mata."
Wata? Wannan? Ya nunata ta cikin madubi.
Tace "ce maka akai nice?"
Mika mata wayar yai yana cewa "in ni ake nemarwa ma na yafe, dan Sweet din nan nakeso, a taimaka a kirani da hakan."
Wayar ta amsa tace "na dauka baka so, tsokana ta kake."
"Ah a taimaka a kirani da sunan nan nidai"
Dan baya ta juya dan haka kawai taji dan kunya, tana mamakin yanda akai wai ita ke kunyar abu in yace, bayan shi sauray.......
Kansa ya sako takan kafadarta dan juyowa tai ta saitin daya sa kansa, kuncinta ya sumbata yace "muje mun gama."
Kai ta daga, sannan ya kalleta, kallansa tai, ya kara kallanta, itama kallansa ta sake cikin rashin fahimta, kallanta yai yana nuna mata gefenta da kansa.
Kallan kan gadan tai, hikab din data cire ta kalla, kallan kanta tai yane yake da mayafi.
Yace "sa"
Dauka tai ta zura suka fito.
Adam tunda suka fito yake kallansu, har suka zauna sannan ya daure ya dauke kai.
Khalid ne ya matsa gefe yana daddana waya alamar ya barsu suyi magana.
Zainab tai murmushi in barinsu za'ai suyi magana ai sai ya tashi.
Kallan Adam tai tace "yanzu a ina kake?"
Ina gidan wani abokina ne ina neman aiki kafin a dace.
A gun wa kake nema?
Dan kallan inda Khalid yake yai sannan yai shiru, kallanshi tai tace "in kansan aikin nepa ka turo takardunka na turawa Dady, amma sai dai ka fara daga can kasa kamar yanda na fadama."
Adam yai shiru,wato dai ko wani aiki sai aikin karfi, harga Allah shikam baisan aikin karfin nan.
Nepa din ma in daga can kasa ne ai yasan wahala suke sha, daurewa yai yace "nagode Zainab zan turo, sannan...."
Ya dan yi shiru yana kallanta, yace "dan Allah Zainab ki yafemin, abinda nazo roka kenan."
Kallansa tai tace "nice zan nemi yafiyarka ka yafemin Adam."
Kai ya gitgiza yana dan share kwala yace "ba abinda kika min nine na miki laifi"
Tace "na yafe maka, kaima ka yafemin."
Cikin dan rawar murya yace "na yafe miki."
Mikewa yai ya kalli Khalid yace "Khalid zan wuce."
Khalid ne ya mike yace "muje na rakaka."
Zainab ta shiga daki a kudin nan ta ciro 10k sai kuma ta rage ta dauko 5k dan tasan halin Adam a kwana daya ma sai ya cinye kudin.
Fitowa tai ta mika mai tace "ka rage wani abin ba yawa."
Harzai amsa sai kuma yace "ta ina zan amshi kudinki?"
Tace "karka damu ba wani abin."
Shiru yadanyi kafin ya amsa, Khalid ne yace "muje?"
Nan suka fito, Adam kam gaba daya jikinsa yayi sanyi, harya hau adaidaita bai ce kala ba, a ciki ma zugum yai.
Khalid kam na komawa gida yaga Zainab na kwashe kwanuka, murmushi yai tana dawowa daga kitchen ya kalleta yace "Baby dan dubamin daki kiban wayata."
Kallansa tadanyi, Khalid fa akwai sa aike, haka ta wuce daki tana shiga ta ganshi shima ya shigo.
Kallansa tai cikin mamaki, matsowa ya farayi yanda taga yanayi da idanunsa ne yasa ta gane nufinsa, kallansa tai tace "sai kace ba wayarka zan dako ma ba."
Ba kirana kikai ba?
Kallansa tai sannan tai yar dariya tace "yaushe akai hakan kenan?"
Yanzu, na tabbatar naji ance Sweet zo kaga.
Baki ta bude tace "har haka nace?"
Kai ya daga yace "sosai dan haka kunnena yaji."
Haka dai kunnenka ke san ji.
Karasowa yai inda take yace "fadamin yanda kunne na ke san ji to."
Tace "Sweet ga wayarka."
Murmushi yai yace "okay, ai kece wayar tawa na gane irin juya maganan nan ne."
Dariya tai tace "oh ni wai dama haka kake? Anya su Umma sun san.........."
Jin ya jawota ne yasata yin shiru, kallansa tai cikin wani yanayi, hannunsa yasa ya riko fuskarta a hankali ya kai bakinsa ya sumbaci saman goshinta, ya sako ya sumbashi karan hancinta, ya sumbaci idanunta dake lumshe, sannan ya sumbaci kucinta.
Idanunsa ya lumshe sannan yakai kan labanta ya sumbata, dagowa yai a hankalu ta bude idanunta, kara kallan bakinta yai sannan ya nufeshi................
********
Afreey tashi kici abinci nace ko?
Bargo ta sake ja tace "banaci."
Afreey wai wani irin abu ne haka? So kike hankalinmu ya tashi?
Cikin kuluwa tace "ki kyaleni banaci, in har kuna so naci abinci ku kawon Khalid."
Tace "mene?"
Bargo ta kara ja ta rufe kanta gaba daya.
Mumy haka ta mike ranta a bace ta fito.
Nace cikin wa?馃お
*************
Yau da safe tana tashi sakon shugaban gun aikinsu Abubakar ta gani, mamaki ne ya kamata dan tambayarta yake sanda take available yana san ya kira akwai maganar da yakeso suyi.
Shiru Zainab tai tana kallan text din, tare da tunanin me yake san yace mata........
^******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
********
[1/14, 10:54 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{65}
Ganin kira ya shigo cikin wayarta ne yasa ta daga 鈥淎ssalamu Alaikum Sir鈥�
Daga can Abubakar ya amsa yace 鈥淶ainab inata cigiyarki shiru bake ba labari.鈥�
Shiru tai batace komai ba, yace 鈥淶ainab me zai haka ki taimaka ki dawo aiki? Wlh akwai matsala rashinki a nan yasa komai na neman tarwatsewa.鈥�
Murmushi tai tace 鈥淵allabai am sorry amma bazan koma ba.鈥�
Yace 鈥渘a sani an bata miki rai amma kiyi hakuri Zainab ki taimaki gun da kika bunkasa da hannunki karya ruguje.鈥�
Shiru tadanyi kafin tace 鈥淎n sorry yallabai amma i can鈥檛 do that.鈥�
Yana kokarin magana tace 鈥渘agode.鈥�
Ta kashe wayar, shiru tai tara da dafa kanta, sannan a hankali tadan sauke ajiyar zuciya.
Rubutun da take a takarda ta cigaba, har sai da azahar tai sannan ta mike tasha tea tai sallah sannan ta sa abinci.
Daki ta shiga dubawa tana neman flash dinta data ba Khalid sanda zai mata printing.
Wandan dayasa jiya ta jawo tana dubawa, takardar data ji a ciki ne yasa ta cirota tana dubawa, list din kayan da zai dinga sawa ne daga sun gama training kenan wani satin zai fara sasu?
Shiru tai tana tunanin kila bashi da ko dubu daya ma ina yaga kudin siyo wadan nan kayayyakin?
Zama tai a bakin gado tana tunani, ya zatai da Khalid?
Ganin tunani na mata yawa yasa kawai ta cigaba da abinda take tana duba abinci.
^**********
Sakon daya shigo wayarsa ne yasa ya kara kallan sakon baya ya gama karantawa.
鈥淜halid wannan shine magana fa karshe da zan ma in har bakazo ba to lalai zakaji sallahun mutuwa ta gobe.鈥�
Ajiye wayar yai ya rufata ta baya ya cigaba da abinda sukeyi, har sai 5 da suka tashi sannan ya dagota.
Kallan text din ya sake kawai ya danna kira.
Afreey na kwance cikin bargo taga kiran Khalid, cikin sauri ta yays bargo ta daga tace 鈥淜halid!鈥� Tai maganar da sauri cikin zumudi.
Yace 鈥淪afiyya sai yaushe zaki daina abu na marasa tunani?鈥�
Cikin mamaki tace 鈥淜halid?鈥�
Yace 鈥淏ansan me kika dau kanki kika dau rayuwa ba sai dai daga wannan lokaci zan canza numberta sannan zan sanar dake abu daya, kiyi kokarin daraja rayuwarki da wad鈥檃nda ke tare dake, ki nemi wanda ke sanki ki aura wannan shirmen da kike kira da sunan so ba shine so ba, ina miki fatan alkairi.鈥�
Kha....... karar kashe wayar dataji ne yasa tace 鈥渒halid! Khalid.....鈥�
Ganin da gaske ya kashe ta shiga sake kiransa sai dai ana tace mata wayar a kashe take, haushi ya isheta ta cilar da wayar.
*******
Khalid kam yana kashe wayar ya fito ya nufi gida.
Zainab na zaune ganin an kawo wuta ta dawo falo, harta fara aiki taji hankalinta nakan kofar waje, tana yi tana kallan time, tv ta kunna ta zauna tana kallan shirin da akeyi, gaba daya shirin dake gudana a gidan tv din ga rainashi, daga masu shirin har yanda shirin ke tafiya, tsaki tai wai a hakan plan dinta ake bi, tasha ga canza ganin ana wani indian film ta tsaya tana kallo, shigowar gate taji a hankali ta mike ta leka kofa, murmushi tai sannan ta koma da sauri ta zauna sai kuma ta girgiza kai tai saurin kwanciya akan kujerar, nan ma taga baiyi ba tai saurin daukan littafin datagama rubutu dazu ta rike wai a dole karatu take.
Khalid ne yadan kwankwasa tare da murda kofar falan, yi tai kamar bataji ba, sallama yai sannan ya kalleta, kallansa tai tadan basar ta amsa sallamar sannan tace 鈥渟annu da zuwa.鈥�
Ta cigaba da kallan littafin, kallanta yai sannan ya shigo har ya zauna kusa da ita bata kalleshi ba, sa fuskarsa yai cikin littafin yace 鈥測a naga kamar a juye?鈥�
Kallan littafin tai sam batama san ta yanda ta rike ba saboda hankalinta bai wajen, kallansa tai tace 鈥減racticing din karatu a juye nakeyi.鈥�
Practicing? Kai ta daga tace 鈥渆h.鈥�
Ohhhh ba laifi amma..... ya jawota jikinsa, kallansa tai ya daure fuska tace 鈥渒aratu fa nake鈥�
Nima wani karatun zan zuba miki, tadan kauda kai tace 鈥渒aratu?鈥�
Yace 鈥渆h na tabbatar karatuna yafi wannan saurin shiga.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渟hine tunda ka tafi ba ko yar text, balle waya.鈥�
Kallanta yai cikin mamaki wanda hakan yasa tai saurin runtse idanta tare da jin haushin kanta, murmushi Khalid yai mai fadi wanda hakoransa suka fito yace 鈥渁u fishin kenan?鈥�
Kanta tasa a cinyarsa da sauri cikin jin haushin kanta, murmushi ya sakeyi ya kwanta akan bayanta yace 鈥渂ut i like it, i wish za鈥檃 cigaba da yin fushi dani indai akan haka ne.鈥�
Ya dan dago yana cewa 鈥淏aby in miki text yanzu?鈥�
Dagowa tai tace 鈥渒ana gida me.....鈥�
Sai kuma tai shiru tana murmushi ganin tunda ta fara murmushi yakeyi, tace 鈥渕enene?鈥�
Yace 鈥渋 just feel like i need it now.鈥�
Tace 鈥渕e kenan?鈥�
Hannu yasa akan cinyarta yana tahowa dashi, ture hannunshi tai, dariya yai yace 鈥渞aguwa.鈥�
Wace?
Nidai banfadi suna ba.
Ah to nidai mutum bazaicemin raguwa ba.
A gwada?
Tureshi tai tace 鈥渄ama nasan juya maganar zakai.鈥�
Yace 鈥渢unda kin sani ya akai kika biyemun?鈥�
Dan laban bakinta ta hade sannan ta wadd tace 鈥渇anshewa kake yi ne?鈥�
Me?
Ta matso kusa da kunnensa tace 鈥済aurantakar da akai da?鈥�
Ta mike da sauri tana neman guduwa, hannu yasa ya jawota, fadowa kan cinyarsa tai yace 鈥渇anshewa kike?鈥�
Kallan sa tace 鈥渘i kuma name?鈥�
Bakinsa yakai saitin kunnenta sai yace 鈥渘a fasa fada.鈥�
Yasa dariya, sauketa yai ya mike yana dariya, tace 鈥渇adamin name?鈥�
Ciki ya wuce ya fada toilet, tana biyoshi taga baya dakin.
Shiru tai tana tunani name?
Falo ta dawo ta kashe tv ta kawo kai abinci falan.
Khalid na fitowa faga wanka yasa yar riga da wando ya fito.
Kallan abincin yai sannan yace 鈥淯r sweet na godiya.鈥�
Tace 鈥渋n Sweet na godiya ya fadamun me yake nufi.鈥�
鈥淎yya am sorry baby amma da alama Sweet dinki bai shirya sanar dake yanzu ba.鈥�
Fuska ta daure tace 鈥渟hikenan.鈥�
Zama yai ya kalleta yace 鈥渂ani abinci.鈥�
Kallansa tai wannan sakalci? Haka ta zuba kai ta sa spoon ya sau spoon din yana cin jellof din shinkafa da wake datai.
Wayarta ta mikomai? Ya amsa yana kallan email din da Adam ya turo na result dinsa, result ne da kana gani kasan wanda yasha dakyar ya wuce, duk da sake jarabawar dayai dayawa.
Kallansa tai tace 鈥淏ari na turawa Dady.鈥� Tai maganar tana neman amsar wayar, hannunta ya hade da wayar ya juyo yana kallanta, yace 鈥渂a yanzu ba.鈥�
Cikin mamaki tace 鈥渏iya nace mai zan tura inya turo.鈥�
Yace 鈥渉aka kika ce, sai dai daga alamun maganar Adam haryanzu baisan kanshi ba, in har aka nemomai a tsukukun nan mutuncin Dady zai zubar ba komai ba.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渕e kake tunanin yi kenan?鈥�
Ya dan murmusa yace 鈥渂arshi yai aikin gini danai na wata biyu am sure zai dawo hankalinsa.鈥�
Okay shikenan ta fada cikin gamsuwa.
Abinci ya gama ci yasha ruwa, sai data maida kwanukan sannan ta zauna a dan gefensa, hannu ya nuna mata alamar ta matso, dawowa tai kusa dashi.
Kwanciya yai akan kunjerar ya kwantar da kansa a kan cinyarta, sannan ya sa hannunta acikin sumarsa.
A hankali ta shiga shafawa yana dan lumshe ido, kallansa tai cikin tsantsan san da batasan sanda yai mata kamu haka ba tace 鈥渄azu Shugaban gun aikina nada ya kirani.鈥�
Idanunsa yadan bude ya kalleta, nan ta fadamai yanda sukai, kallan idanunta yai yace 鈥渒in tabbatar hakan kikeso?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渢a ina zan manta abinda suka ma?鈥�
Murmushi yai yace 鈥渄an bugamin nan.鈥� Ya nuna mata kafarsa.
Matsawa ta shiga yi, tsabar yanda ya aikatu kwanakin nan yasa har yanzu jikinsa ciwo yake.
Can tace 鈥測a zamuyi da kayan da zaka siya?鈥�
Bai kalleta ba yace 鈥渮an yi aiki da weekends din nan zan san yanda za鈥檃i insha Allah.鈥�
Shiru tai tana kallansa idanunsmta sukai rau rau tace 鈥淪weet idan naga tanasa ba mijin kyautar abu ya zatayi?鈥�
Yanzun ma bai kalleta ba idanunsa na lumshe yace 鈥渋ndai kyautar batai yawa ba ai bakomai, amma menene?鈥�
Shiru tai wanda hakan yasa ya bude idansa yace 鈥渕enene?鈥�
Kallansa tai tace 鈥減lease!鈥� Tai maganar cikin rauni idanunga na digo da hawaye.
Mikewa yai yace 鈥渕enene?鈥�
Ta kalleshi tace 鈥減lease ka barni na saima kayan.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渘ace za......鈥�
Rungumeshi tai kam wanda hakan yasa jikinsa yin sanyi, tace 鈥渂akasan yanda nakeji ba in ka je gun aikin gini din nan, dan Allah kayi hakuri ka bari nasaima kyautar abu nake san ma amma nasan bazaka taba amsa ba, shiyasa na fadama kar ranka ya baci.鈥�
Ta kara kankameshi, kanta ya shiga shafawa, duk da ba mace bace kai gashi sosai a kallantana da nata daidai gwargwado dan in ta gyara shi yana kwanciya luf.
Dagota yai ya sa hannu yana share mata kwallarta, yace 鈥渁na kiran sallah muyi sallah ko?鈥�
Kai ta daga tana kallanshi.
Alwala tai sukai sallah tare, yace ta dauko qur鈥檃ni nan tamai karatu yaji, ya mata gyara sannan ya dan daura mata kadan.
***********
Adam kam sai duba waya yake yana jiran sakon Zainab na cewar ta tura komai ya kammala sai dai har dare yai bai ga komai ba, wajen karfe 9 sako ya shigo wayarsa da sauri ya dauka ganin numberce yasa ya bude a dan zuciye.
Number aka turo mai a kasa akasa ka kirashi, namai bayani zakazo gobe, sunanshi Gaddafi.
Sannan kaje gidan su Raziyyan?
Daga Khalid!
Zanzo gobe? Har aikin ya samu?
Shiru yai sannan ya tuna yau yaso zuwa gidansu Raziyyan amma baisamu ya fita ba saboda jiya kasa bacci yai in ya tuno abinda ya faru a gidan Zainab sai yaji sam baccin yaki zuwa.
Jiya itace rana ta farko da ya taba kasa bacci arayuwarsa,
********
Salmanu ne ya shigo bayan an mai izini, hannunsa dauke da bakar leda.
Umma tace 鈥淪almanu sannu da zuwa鈥�
Shigowa yai yana dariya yace 鈥淯mma kinjini shiru ko?鈥�
Tace 鈥渁i da bakazo yau ba sawa zanyi Asiya ta kiramin kai a waya naji ko lafiya.鈥�
Dariya yai yana karasowa, Abba yace 鈥渘ikaina nace wannan d鈥檃 lafiya?鈥�
Kusa da Abba ya zauna yace 鈥渨lh munje dutse ne neman aiki Abba.鈥�
Umma tace 鈥渕asha Allah, Allah yasa a dace.鈥�
Ameen yace ya ajie ledar gaban Umma yace 鈥淯mma ga tsarabar zuwa dutse.鈥�
Budewa taj tana cewa 鈥渕ungode, Abban Khalid gashi an kawo mana dankalin hausa.鈥�
Mungode sosai.
Asiya ce ta fito gaisheshi tai sannan tai hanyar komawa ciki.
Umma tace 鈥淎siya zo ajiye wannan, yanzu yayanki Salmanu ya kawo.鈥�
Kusa da Umma tazo ta dauka, tana dagowa suka hada ido da Salmanu, murmushi ya mata ta dauka ta ajiye.
Zata koma ciki Umma tace 鈥渮o ki kawo mai abinci, Salmanu alale ne nasan kana so.鈥�
Kallan Asiya yai yace 鈥淎siya zubomin alale.鈥�
Ya kalli Umma yace 鈥渁she raban zanci alale ne yasa na rike yunwata.鈥�
Umma tai dariya, kallan Asiya yai harta zubo ta kawo mai sannan ta juya ciki.
*********
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
***********
[1/16, 9:58 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
聽 聽聽 .........................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link馃憠馃徎 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{66}
Kwance take akan kirjinsa kamar me bacci, yana dan shafa kafadarta zuwa bayanta.
Shima yana kwance ne sun luluba da bargo, a hankali tace 鈥淒ady dazu yamin text yana san jin sanda kake dawowa gida, yana san kiranka.鈥�
Kin fadamai?
Hmm tace kafin tafan yi ajiyar zuciya kadan tace 鈥渘a san maganar aiki ne, in na fara aiki ya kake gani zamuyi?鈥�
Ba tare da dogon nazari ba yace 鈥渒afin ki tafi sai kin gama komai na gida kinyi abinci kin ajiye sannan ki fita鈥�
Da sauri ta dago tace 鈥渄a safen?鈥�
Yace 鈥渆h haka duk mata masu aiki sukeyi.鈥�
Amma ni da nake fita da wuri fa?
鈥淪ai ki tashi tsakar dare.鈥�
Baki ta bude tana kallansa, kallanta yai yace 鈥渕enene?鈥�
Tace 鈥渨ani sa鈥檌n sai na kasa gane wanene kai鈥�
Kara jawota jikinsa yai yace 鈥渟o kike nace ki fita aiki sanda kikeso ba tare da kinyi komai ba?鈥�
Tace 鈥渂a haka ba amma ta ina zai iya aikin gida nai abinci kafin na fita?鈥�
Kafada yadan daga sannan ya dan sumbaci goshinta yace 鈥渮aki iya tunda kina san aikinki kina kuma san Sweet dinki.鈥�
Bata san sanda tasa dariya ba sannan ta kalleshi tace 鈥渕ekace?鈥�
Yace 鈥渒ina san aikinki kina kuma san mijinki, ba haka bane?鈥�
Dan ido ta dan kikifta tace 鈥渒o haka ne sai ka fada kai tsaye? Sai a bari na fada da kaina.鈥�
Ko baki fada ba jikinki ya fadamin me zai sa na jira sai kin fada?
Dariya ta sake ta sa hannu ta dan tureshi ya dan murgina kadan tace 鈥淎llah nikam na rasa irinka.鈥�
Ta juya mai baya tana kunshe dariyarta, juyowa yai ya rungumeta ta baya, hannunsa ya sako saman kirjinta yasa kansa a bayanta yace 鈥淎llah in na tuno shekararki hudu da shi sai naji kamar......鈥�
Dan yawon bakinta ta hadiya sannan ta dan lashi kasan lebanta kadan, batace komai ba, shiru yadanyi jiyai tace 鈥渒asan meyasa banji haushin yimai magana ba balle harnai tunanin taimakon shi?鈥�
Meyasa? Ya tambaya yana dan kara gyara kansa dake wajen wuyanta.
Juyowa tai suna fuskartar juna, daf suke da juna, tasa hannu akan fuskarsa tana dan shafawa kadan tace 鈥渢a hanyarsa na hadu dakai, sannan ta hanyarsa muka kai inda muke yanzu, da ban aureshi ba kila bazan sanka ba, da bai ci amana ta kila bazamu kai wannan stage din ba.鈥�
Tadan yi wani lalausan murmushi tace 鈥渟hiyasa ko haushinshi banaji.鈥�
A hankali wani murmushi ya bayyana a fuskar Khalid, matso da fuskarsa yai ya sumbaci lebanta yace 鈥淭hat鈥檚 why nima nake yafemai duk sanda na tuno hakan.鈥�
A tare sukai murmushi sai kuma ta canza fuska, tace 鈥済wara ni dama haka ka ganni dashi kaifa?鈥�
Nifa?
鈥淓h yarinyar da har gun aiki a manne kuke kai da ita.鈥�
Wa? Ya tambaya yana kallanta, tayi kicin kicin da fuska yace 鈥渨ai Safiya?鈥�
Oho koma wa sunanta ni bai damenba.
Murmushi yai yace 鈥淜arki tsaneta please yanda ta taso ne yasa take ganin duk abinda take so kamar kayan shago ne da zataje ta siya haka take ji, sannan ni ba komai tsakaninmu da ita, ita tana tunanin so na take ni kuma nasan ba sona take ba, duk sanda hankali ya shigeta am sure zata fahimci hakan.鈥�
Dan baki ta tabe tace 鈥渘aji da alama kamafi saninta akaina.鈥� Ta karasa maganar tana dan harararsa.
Murmushi yai ya kara kankameta tare da lumshe idanunsa.
A hankali tace 鈥渕aganar dazu? In fita gobe?鈥�
Murmushi yadanyi idanunsa na rufe yace 鈥渁bu daya sannan please banda mai tsada.鈥�
Shiru tadanyi tana tunani, itakam ya zatai da Khalid?
A hankali bacci ya daukesu.......
************
Kabir ne ya kara kiran number a karo na goma sha biyar, yanzun ma harta katse bata dauka ba, Mumy ce ta shigo dakun kawai ta ja akwati ta fara zuba kayan Afreey a ciki.
Afreey dake kwance ce tadan leko kallan Mumy tai cikin mamaki ta mike zaune da sauri tace 鈥淢umy me kikeyi hakan?鈥�
Tace 鈥淕un yayarki zaki tafi yau鈥�
Da sauri tace 鈥測anzun Paris xan tafi? Ban shirya ba?鈥�
Gashinan ina shirya miki ai, sannan in kinje shekara biyu zakiyi acan.
Ido ta zaro ta mike zaune da sauri tace 鈥渕e kike nufi Mumy?鈥�
Tace 鈥渂adai taurin kai kike mana akan wani fakiri ba? Mahaifinki ne ya yanke hukuncin nan sannan nima na amince dashi, nan da awa biyu jirgin ku zai tashi.鈥�
Awa biyu? Ta fada tare da mikewa tsaye da sauri ina zata san ma inda yake? Ga ya canza number.
Ranta ne ya baci ta kalli Mumy tace 鈥渕umy ki barni plz bansan zuwa wlh.鈥�
Mumy bata kula taba ta cigaba da hada kaya.
Afreey haka ta shirya dan dole Abbi da kanshi yai shirin yi mata rakiya suka tafi kasar Paris suna tafe tana hawaye har jirgi ya tashi bata daina kiran Khalid ba.
*********
Kayanta ta jawo bayan motarsu ta sauka ta nufi gidansu Kamalu, cikinta sai uban karar yunwa yakeyi.
Haka ta isa gidan sai dai Kamalu yace mata Adam ya fita tun safe.
Ganin yanda iyayen Kamalu ke mata wani kallo yasa ta nemi bashin dari biyu agun Kamalu ta nufi gidan Hajiya bilki.
Kallanta sosai mai gadin ya shiga yin dan ya kasa gasgata idanunsa kan Goggo ce.
Sai datace 鈥淣uhu bude min mana.鈥�
Yace 鈥渉ajiyar bata nan.鈥�
Tace 鈥渋na taje?鈥�
Yace 鈥渨lh ban sani ba dazu ta fita.鈥�
Bari na shiga na jirata.
Sai dai ki jirata a harabar gidan dan ba kowa a ciki.
Cikin takaici ta wuce harabar gidan ta zauna, sanyi sai busawa yake sai rakubewa takeyi.
Adam kam cikin farinciki ya isa inda mutumin yace su hadu.
Tunda ya iso yaga sunata aikin gini, cikin mamaki yace 鈥渙h aikin fad鈥檃d鈥檃 gun aikin nepa din sukeyi?鈥�
Haka ya isa can ciki inda mutumin yake yana zaune suna cin abinci shinkafa da wake da suka siya yanzu.
Kallan Adam yai yace 鈥渙h harka iso?鈥�
Ya kalleshi cikin mamaki yace 鈥渆h amma me kuke anan?鈥�
Ya tambaya yana kallan yanda suke cin shinkafar tundaga yanayin jikinsu.
Gaddafi ya kalleshi yace 鈥渒aci abinci ne?鈥�
A鈥檃 Adam yace yana kallanshi.
Alama yamai daya zauna, Adam ya zauna ya kalli plate din da aka turo mai, loma daya yaci yace 鈥渁 ina zan yi aikin? Naga nan kamar ba aikin kuke ba.鈥�
Dariya Gaddafi yai yace 鈥渓okacin cin abinci ne daga mun gama zakaga kowa ya d鈥檃u harama.鈥�
Cikin rashin fahimta yake cin abincin, kafin ya gama yaga ragowar sun gama kowa ya mike, gani yai suna ta aiki kowa da abinda yakeyi.
Adam ya kalla yace 鈥渒ai tunda farkon zuwa ne sannan yace baka taba yi ba ka fara da kwaso kasa.鈥�
Shinkafar daya firzo ne yasa ya kalleshe, kallansa yai yace 鈥渒asa?鈥�
Gaddafi ya kalli inda ya farzo shinkafar yace 鈥渆h ko kafinsan farawa da hada siminti?鈥�
Baki Adam ya bude yana kallansa yace 鈥渁ikin gini nazo yi?鈥�
Eh da me ka dauka?
Kallansa Adam yai ya mike da sauri zai tafi, sai dai tunawa dayai kudin da Zainab ma ta bashi a biyan bashi ya kare dakyar ya samu na mota yau, yazaiyi ya koma?
Haka ya nufi gun yashi yana gamawa akasashi hadin siminti, awa biyu jinta ya dingayi kamar wanda ya wuni, jikinsa duk yadau ciwo.
Gun Gaddafi yaje yace kansa na ciwo.
Gaddafi ya duba awa hudu kawai yai yace ga kudinka nayau ya mika mai dubu daya Adam ya kalleshi yace 鈥渒ullum nai dubu daya zan samu?鈥�
Yace eh, amma kaga Khalid dake aikin mutum biyu dubu biyu yake samu kullum, wani sa鈥檌n ma na mutum uku yake.
Baki Adam ya bude shiva Khalid bane bazai kashe kanshi da aiki ba amma dubu daya kullum? Kwana goma dubu goma?
Murmushin jin dadi yai tunda bazai samu waccan ba gwara ya lalaba dama yanata mamaki ace abinda yama Zainab bai dameta ba harta bashi aiki?
Amsa yai ya fito cikin jin dadi.
Har zai hau motar unguwarsu ya canza ya hau ta Naibawa.
Tsayawa yasai lemo da ayaba na dari da hamsin yana tuno Khalid hk yai.
A kofar gidan ya tsaya yana tunani, zata kulashi yau? Yai tambayar jiki a sanyaye sannan yai sallama.
Baba na rubutu da alkalami a alo a waje ya amsa tare da bada izini.
Adam ne ya shigo ya karasa kusa dashi ya tsugunna yana gaisuwa.
Baba wanda tun shigowarshi yake kallansa harya karaso.
Amsawa yai yace 鈥渟annu da zuwa.鈥�
Adam yace 鈥測auwa Baba yamai jiki?鈥�
Kallansa yai haryanzu yana jin zafinsa kadan yace 鈥� gun Raziyya kazo?鈥�
Kasa yai dakai yace 鈥淏abs ku kara yafemin bansan haukar danai haka ta ruguza rayuwarku ba.鈥�
Kallansa yai yace 鈥淢un yafema dan abinda ya faru yasa na rufe ido na toshe kunena har sai da abokinka ya farkar dani na fahimci lalai nima na tafka babban kuskure, nikaina dana sanin abinda na aikata nakeyi wanda yanzu idan duniya suka gama sani bansan yanda rayuwarta zata kare ba.鈥�
Jikin Adam ne ya sake mutuwa tausayinsu dajin haushin kanshi ya sake kamashi, kwalla ta zubomai yace 鈥渒uyi hakuri Baba.鈥�
Murmushi Baba yai ya girgiza kai yana kokarin wanke rubutun yace 鈥渄uk abinda ya faru laifi nane ina neman Allah ya yfemin, ya bata miji na gari itama.鈥�
Fitowar Raziyya daga bandaki ne yasa ya kalleta, buta ta ajiye ta bugamai wani banzan kallo tana neman wucewa ciki.
Baba ne yace 鈥淩aziya dawo nan.鈥�
Dawowa tai inda ya nuna mata fuskarta a daure tamau.
Baba ya mike ya dau rubutun ya nufi dakin mama ya barsu.
Adam ne ya kalleta, cikin dauriya yace 鈥淪a....Au Raziya.鈥�
Bata ko kalleshi ba balle yasa ran zata bashi amsa.
Yacigaba 鈥淩aziya ki yafemun dan Allah, nayi kuskure na sani nine silar jifawar rayuwarki haka, amma ki yafemun ba dan halina ba.鈥�
Idanunta ne suka ciko tana kallanshi, a hankali hawaye suka gangaro kan fuskarta.
Daurewa yai yace 鈥渒iyi hakuri dan Allah.鈥� Yai maganar cikin rawar murya.
Kallansa tai sannan ta mike, da sauri yace 鈥淩aziyya!鈥�
Tsayawa tai batare da ta kalleshi ba, yace 鈥渄an Allah kiyi hakuri.鈥�
Daki ta shiga ta rufo kofar yana daga waje yana jin kukanta, sai dai itakam wannan karan kukan tausayin kanta take dan ko yanzu a dole take zaune a gidan nan amma ta riga ta saba da namiji batasan yanda zata kare rayuwarta ba.
Haka ya musu sallama ya fito jiki a sanyaye.
********
Sakonsa data gani ne ya sata sakin murmushi mai sanyi, kallan kayan data amso daga gun Maman Al鈥檃min tai, sannan ta sake karanta sakon.
Baby i miss u.....
Fuska tadan rufe sannan ta kara kallan kayan dake kan kujera wanda ta fita ta siyo yanzu, dan tana dawowa ta tsaya a gidan Maman Al鈥檃min ta amso kayanta.
Murmushi tai sannan ta mike ta shiga dasu daki, budesu ta dingayi tana gwadawa, kunya duk ta rufeta ganin kayan duk kamar kayan 鈥榶an iskan titi.
Wata riga tasa wacce gaba daya rabin kirjinta a waje yake ga rigar iyakarta gwiwa, da sauri ta hau cirewa tana cewa 鈥渋na na isa sa wannan?鈥�
Wayarta ce tai kara ta dauka tare da cewa 鈥淗ello Yallabai鈥�
Abubakar yace 鈥淶ainab da gaske bazaki dawo ba?鈥�
鈥渆h!鈥� Ta fada kai tsaye, ajiyar zuciya yai yace 鈥渘a fahimceki shikenan ni kuma zan saida broadcasting station din nan dan dama solution dina kece in har bazaki dawo ba zan sashi a kasuwa.
Cikin sauri tace 鈥渕a鈥檃ikatan ciki fa?鈥�
Wannan sai su nemi wani aikin dan dama na ba Kabir kwana daya tunda bai samo solution ba yu din nan na koreshi.
Shiru tai kafin tace 鈥渨a zaka saidawa?鈥�
Ban sani ba sai wanda yake so naga kuma zai siya yanda nake so.
Shiru tadanyi kafin tace 鈥渒a saidamin.鈥�
Fuskarsa dauke da mamaki yace 鈥渋n saida miki?鈥�
Tace 鈥渆h, in har saidawa zakai ka saidamun.鈥�
Shiru yadanyi yace 鈥渒izo mu tattauna, kiji ko zaki iya siya.
Okay kasa time ka turon, nan sukai sallama.
Shiru tadanyi, kafin ta kalli kayan, murmushi ta sake, jin fitsari ne yasa ta shiga toilet, tana fitowa ta shiga kitchen tana tafe tana wa kanta dariya tare da cewa 鈥渁i baya nan kafin ya dawo na cire.鈥�
Jellof din taliya datai ta zuba ta fito falo tana ci tana duduba abu a laptop dinta, tana gamawa ta cigaba da abinda take ko plate din bata maida ba, jin ta buga mata ba charge yasa tai ajiyar zuciya sannan ta dau plate din zata wuce kitchen.
Karar gate taji, wani murmushi ta saki sam ta manta shigar dake jikinta, dan window ta leka ta sake sakin murmushi tana kallansa har ya kusa bude kofar, kallan kanta tai ido ta zaro sannan tai hanyar daki da sauri, sai dai ko kusa da kofar bata je ba ya bude kofar.
Baki ya saki yana kallanta, idanunsa kuwa ya bude su sosai tun daga kanta yake kallanta, ta tufke gashinta a tsakiyar kai? Sakowa yai rigar kalar ash ce wato kalar ruwan toka, ta zauna dam a jikinta, a hankali ya sauko kasan cinyoyinta dake waje, da alama ma bata jin sanyi.
Wani irin abu ne ya taso mai, a hankali ya fara takowa, jin alamar yana tahowa yasa ta taka kafafunta tai daku da sauri, tana shiga yana turo kofar, kallansa tai ya kalli yanda rigar ta mata ta gaba.
鈥淲ow da alama Baby so kike ki kasheni鈥� ya fada yana dan jingina kansa da jikin kofa.
Kallansa tai sannan ta juya da sauri zata shige toilet, cikin hanzari ya karaso ya kamo kugunta ya jata suka fada kan gado.
Kallansa tai tace 鈥渄an Allah barni na cire kayan kunya nake.鈥�
Kunya? Ya tambaya yana kara kallan jikinta yace 鈥渋na kunya ana neman zautar dani? An samu hanya?鈥�
Dan idanunta ta juya tace 鈥渘i dai karka fassarani, nasan ai basumin kyau ba kamar wata.....鈥� sai kuma tai shiru tana kunyar yanda yake kallanta.
Murmushi yai a hankali yace 鈥渋 like it, i like it soo much.鈥�
Kunyace ta rufeta ta ja pillow ta rufe fuskarta dashi.
Hannu yasa yana kokarin jan pillow din itama tana kara rikeshi, yana ja ya fizge kallansa tai tace 鈥渄agani.鈥�
Um um
Allah nauyi gareka
Dan murginawa kusa da ita yai yace 鈥渋n nauyi gareni kiyi maza ki koyi yi a sama.鈥�
Baki ta bude da sauri ta dau wani pillow din ta makamai tace 鈥淟aaaaa, Allah da alama ba karatu kawai kai a daki ba.鈥�
Dariya yai yace 鈥渕e nai?鈥�
Tace 鈥淜afi karfina wlh鈥� ta fara kokarin mikewa, riko hannunta yai yace 鈥淏aby i miss u.鈥�
Juyowa tai a hankali tana kallanshi, murmushi ya mata, samun kanta tai da kwanciya kusa dashi, hakan yasa suka kwanta a rigingine hannunsu na rike da juna.
Yace 鈥渋na kika samo kayan rudani?鈥�
Tace 鈥渕akota鈥�
鈥淎hhh lalai na amince da zuwa gunta.鈥�
Murmushi tai tace 鈥淚 like it.鈥�
Yace 鈥渕e?鈥�
Tace 鈥渋nkace you miss me.鈥�
Murmushi yai yadan juyo da fuskarsa yace 鈥渋n nace I luv you fa?鈥�
Kallansa tai zuciyarta na bugawa da sauri cikin wata murya da ita kanta batasan tana da ita ba tace 鈥渋 really want to ask you, yaushe ka fara sona?鈥�
Yana kallanta yace 鈥淚 can鈥檛 say, na dai san before ki bar aiki.鈥�
Murmushi tai tace 鈥渒enan sanda kaje Abuja ka....鈥� sai kuma tai shiru jin nauyin maganar.
Kai yadan daga mata yace 鈥淯mm shiyasa it hurt danaji kina min wani zancen aiki鈥�
Murmushi tai tace 鈥渕eyasa bakai tunanin me yasa ban nemi kowa ba sai kai?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渂ansan wannan tunanin at that time I feel like zakicemin saboda ni talaka ne.鈥�
Kallansa tai, a hankali ya kai ido kan saman rigarta.
Bakinsa ya sa cikin nata..........
*************
Uwar hamma ta saki sannan tai mika tana kokarin mikewa, kallan Hajiya Bilki dake kanta tai, tace 鈥淏ilki kin dawo?鈥�
Hajiya Bilki ta kalleta tace 鈥渋nalilahi wai da gaske kece? Adama?鈥�
Goggo tai dan yake tace 鈥淏ilki nice鈥�
Kallan mamaki ta shiga mata har suka shiga ciki.....
Goggo ta daure tace 鈥淏ilki duniya ce ta juya dani nazo dan Allah ko aikatau ki nema min.鈥�
Shiru tai tana kallanta tace 鈥渕e ya juya haka lokaci daya? Ina sirikarki?鈥�
Shiru tai kafin tace 鈥渟un rabu.鈥�
Kuka ta sa mata, Hajiya Bilki tausayinta ya kamata tace 鈥渒i kwana anan gobe mayi magana.鈥�
Dadi kamar ya kashe Goggo balle an bata abinci tashi ga falansu ana ta kallo ta rakube a kasa tana yi, har yaran suka kaji suka kwanta tana ta uban kallo, sai da Hajiya Bilki tace su kwanciya ake in dare yayi haka.
Dole ta tafi dan dakin da aka ce ta kwanta, kallan dakin tai tace da Hajiya bilki katan daki take ban amma yau???
Haka ta kwanta.
******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧[1/20, 11:47 AM] +234 816 537 8773: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
*Sweet din Baby na gaisuwa 馃槈馃槈*
{67}
Kwanciya sukai bayan sunyi sallar asuba alarm dinsa ne ya buga ya bude idanunsa tare da kashewa, a hankali ya janyeta daga jikinsa, har ya cire kaya zai shiga toilet ya kalleta, hannu yasa ya dan tab'ata cikin bacci ta gyara kwanciyarta.
Kara tabata yai yace "Baby tashi."
Idanunta ta bude a hankali ta budesu da kyar cikin bacci tace "ya akai?"
Yace "breakfast."
Idanunta ta maida ta rufe tace "anjima zanci in na tashi."
Yace "bake ba ni."
Idanunta tasake budewa dakyar tace "baga haka kake tafiya."
Yace "hmm haka nake tafiya amma daga jiya na daina, tashi ki samun wani abun kafin na fito daga wanka."
Bata san sanda ta ware idanunta ba tace "yanzu wai zan sama?"
Kai ya daga alamar eh yace "kidan yi sauri kinsan bama late."
Tana kokarin magana ya shiga toilet, tsananin mamaki ne ya rufeta, wayarta ta jawo ta duba time 6:20am? Haka ta mike kamar zatai kuka tai kitchen, tama rasa me ake ci da sassafen Allah, sannan me zatamai kafin ya fito daga wanka? Kwai ta soya ta dafa ruwan tea ta dauko bread ta fito dashi falo, murmushi tai tana tuno yanda Aunty ke tsananin san tea da bread da kwai ashe yau zai mata rana.
Tana ajiye cup yana fitowa, kallansa tai hamma ce ta聽 zo mata dan bacci takeji sosai, zama yai ta kalleshi, tea din ya hada ya fara sha, kallanta yai yace "kije ki kwanta."
Mikewa tai zata wuce, hannu yasa ya riko hannunta ta koma ta zauna.
Kallanta yai sannan ya nuna mata kuncinsa, murmushi tai sannan tace "bayan an hanani bacci?"
Yace "yanzu aka fara hanaki, dan kullum a gida zan dinga break."
Kallansa tai cikin mamaki tace "a gida?"
Kuncinsa ya kara nuna mata yace "Sweet na jira."
Sumbatarsa tai ya saketa ya cigaba dacin abincinsa, mikewa tai ta wuce ciki ta kwanta, sai dai duk yanda taso tai bacci ta kasa sai juye take, jiya har sha biyu basuyi bacci ba dan bayan sun kwanta hira sukai cikin nishadi da kauna sukai bacci, yau me ya faru haka?
Daki ya shigo ya dau agoggonsa tana kwance tana kallansa, kallanta yai ya sakar mata murmushi sannan ya matso kusa da ita ya sumbaceta a hankali yace "See u baby"
Samun kanta tai da mai murmushi itama, fitowa yai shiru tai a daki a hankali ta sauko ta bude waje ta tsaya a baranda tana jin yanda sanyi ke busawa, hanzu a haka ya fita da kafa?
Shiru tai tana kallan motarta, juyawa tai ciki.
*********
Goggo cikin jin dadi take cin soyayyen dankali da kwai, loma takeyi kai kace bata taba ci ba.
Hajiya Bilki ce ta turo kofar dakin, Goggo tai saurin zuba na hannunta cikin plate din ganin yanda ta cika hannu, kallanta tai tace "Bilki!"
Hajiya Bilki ta na tsaye a jikin kofa ta kalleta tace "inkin gama cin abincin kizo ki tafi."
Kallan ta tai da sauri tace "in tafi ina?"
Murmushi Hajiya Bilki tai tace "ina na sani? Ina fada miki ne bana bukatar mai aiki balle kuma ke dana san hallinki"
Hankalin Goggo ya tashi tace "Bilki na canza yanzu sam ba haka nake ba, ba ruwana wlh ba zan kushe komai ba zan kuma kular miki......"
Katseta tai da cewa "Ko kin canza ko baki canzs ba maganar dai guda daya ce kiyi hakuri ki nemi wani gun."
Goggo ta kalleta tace "yanzu Bilki ina neman alfarma gunki duk yanda muke amma ki kasa min?"
Kallanta tai a kule tace "yanda muke? A yaya muke? Ke da kika sa dana ya fada soyayyar Nabila kikace zaki hadasu aure, yaran nan ya kamu da santa amma dame kika sakamin? Ko cewa nai zaije sai ki fara kame kame, ko duk daga baya kina tunanin ban fahimceki bane?"
Goggo ta kalleta tace "kindai san banda iko akanta ko kin manta kanwar Zainab ce?"
Haushi ya kama Bilki tace "kinsan haka kika kawo mai hotonta?"
Sum sum tai dakai Bilki tace "ni wannan ma abarshi ya wuce ga wannan, ta ajiye mata dubu biyu tace "kiyi na mota, sannan in har baki kara dawowa gidan nan ba zanfi kowa farin ciki xan kuma fahimci kin san darajar kanki."
Ta juya ta fita.
Baki Goggo ta bude tana kallan ikon Allah, wannan dankalin kasa karasa ci tai, ta dau kayanta dake leda ta dau dubu biyun ta fito, tana tambayar 'yarta ma inda Bilkin take suyi sallama amma sam taki ko kulata.
Haka ta fita gaba daya ranta ba dadi, ta koma gidansu Kamalu tana fatan samun Adam.
********
Adam ne ya shirya ai dole ya koma gun aikin nan, dan yama Khalid text ma bai ko mai reply ba, kenan bashida wani zabi.
Ya fito tana tace yana hamma sai jerota yakeyi dan ya saba baccin safe yau kuwa gashi karfe tara wai zai fita.
Yana shawo kwana Goggo na saukowa daga cikin adaidaita, kamar da wasa ya kara kallanta.
Kallansa tai cikin jin dadi tace "Adam!"
Kallanta yai ya karaso yace "Goggo? Me kike anan?"
Kallansa tai tace "da Kamalu baicema nazo ba?"
Kinzo me?
Ya tambaya yana kallan kayanta a leda.
Tace 鈥淎dam na gaji da zama a kauye wlh, ga bani da waya gaba daya komai ya tsaya min cak.鈥�
A kufule yace 鈥渒ina gani nima a dosane nake ina kike so na saki?鈥�
Tace 鈥渂azamu rasa na Allah ba.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渨lh komawa zakiyi yanzu.鈥�
Ina zan koma?
Kauyen kije can ki lalaba kafin Allah ya sa nadan tara, kinsan yanzu aikin da nakeyi ne? Gini fa nakeyi? Duk yanda nake tunda kikaga na dage kema ai sai kiyi hakuri da yanda Allah yai dake.鈥�
Kallansa tai ranta a matukar bace, yace 鈥淎llah Goggo komawa zakiyi yanzu.鈥�
Fuskarta ta hade tace 鈥渘a maka rana dole kamin dare, duk inda nake kai kadai nake tunanin halin da kake amma abinda zaka cemin kenan?鈥�
Yace 鈥淕oggo dan Allah ki barni da abinda ke damuwa, idan na tuno abinda nama mutanen can ji nake gaba daya na tsani kaina, ki barni da wannan bazan kuma kara da rokon karaki a gidan mutane ba.鈥�
Lalai Adam ni kake fadawa haka? Akainane bazakai roko ba? Sanda na haifeka tsabar san da na dorama tun kana ciki yasa mahaifinka ya tsokaneni ya sama Adam wai ni Adama kai Adamu, mutane akanka kasan irin zagin dana sha? Na saida duk abubuwa na saboda kai amma haka zaka cemin?
Ransa a matukar bace yace 鈥渕e na miki? Dan nace kawai Goggo ki koma ki kira ma zauna da kafata? Ke ba abin alfahari bane kiga ina aiki?鈥�
Ido ta zubamai ranta a matukar bace adaidaita ya tara suka shiga, ranta duk a bace, shiru sukai har suka je tasha kallanta yai yace 鈥渒iyi hakuri Goggo zanzo da zaran na samu dan kudi.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渒a aikon da waya.鈥�
Yace 鈥渮an aiko da zaran na hada kudi.鈥�
Haka ya shiga mota ranta duk ba dadi, me zata ce ma yan gidan?
Sai da suka tafi sannan ya juya ya tafi gun ginin, kallan gun yai shikam wlh baisan aikin nan amma ya zaiyi? Yanzu Kamalu ma ba magana yake mai sosai ba ya kuma tabbatar ya gaji da zamanshi ne, dole ya shiga ciki.
*******
Har ya iso gate din gidan yana waya da Dady kafin suyi sallama ya kashe wayar.
Zainab wacce ke kwance akan gado rike da wayarta gefe kuna takarda da biro ne tana duba abu a wayarta tana rubutawa a takardar, sam bataji alamar shigowarsa ba, lokaci ta kalla a wayarta taga har shida saura.
Mikewa tai ta fito falo dan shan ruwa, zaune ta ganshi ya jingina kansa da kujera idanunsa a rufe.
Kallansa tai cikin mamaki, sannan ta tako har inda yake, kallansa samun kanta tai da kasa dauke ido daga kansa, idanunsa a rufe yace 鈥淏aby in kin gama kallan nawa zan bude ido.鈥�
Kanta ta dauke ds sauri tana cewa 鈥測aushe ka shigo?鈥�
Idanunsa yadan bude sannsn yasa hannu ya jawota ta dan zaune a karkace akan cinyarsa.
Kansa ya kwantar akan kafadarta yace 鈥渏ira nake ki fito.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渋n ban fito bafa?鈥�
鈥淣asan zaki fito ma tunda Sweet dinki bai dawo ba, ina kika ga nutsuwa?鈥�
Wani murmushi tai tace 鈥渢aya akai kasan banda ita?鈥�
Dagowa yai ya kalleta yace 鈥淚 know it, you don鈥檛 have to tell me.鈥�
Wai why are you so confidence?
Kansa ya maida yace 鈥渕e zai sa na jira sai kin fadi abinda na sani?鈥�
Murmushi tai, kin samu cinya kin ki tashi, gashi ni kuma ina san mikewa.
Kallan mamaki tamai tace 鈥渨aye ya sani akan cinyar?鈥�
Nine sannan yanzu kuma nace a dagani.
Mikewa tai rai a bace, ta daure fuska tamau, kallanta yai bayan ya mike yace 鈥渂ari nadan watsa ruwa muyi sallah sai muci abinci鈥�
Kai ta daga kawai fuskarta haryanzu a tsuke, baiko bi takanta ba ya wuce yana murmushi shi kadai.
Haushi ya isheta, kallan atamfar data sa tai tace ko in sa kananan kaya? In kuma nasa ai sai yafi fadam abinda yaso tunda ba dashi ya ganni ba.
Zama tai a bakin kujera, meya sameshi?
Kofar daki aka bude, ya leko kai yace 鈥淏aby ina towel dina?鈥�
Dan kallansa tai tace 鈥測ana inda ka ajiye.鈥�
Zo ki daukomin.
Banfa dauka.......
Maida kofar yai ya rufe, a kufule ta mike, tana shiga taga towel daure a jikinsa.
Kallansa tai tace 鈥淪weet kace baka ganshi ba?鈥�
Murmushi ya sakar mata yace 鈥渟o nake kawai naga kinzo.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渇adamin gaskiya so kake kaga raina ya baci ko?鈥�
Bingo ya akai kika sani?
Baki ta bude tace 鈥渄alili?鈥漷ai tambayar cikin mamaki.
Sirri nane ni kadai but i like it.
U like it?
Bai bata amsa ba ya shiga toilet yana kokarin rufewa yace 鈥渒o za鈥檃 tayani wankan?鈥�
Juyawa tai ta fita daga dakin tana ajiyar zuciya, wai meke kan Khalid? Sam baya kunyar fadar abu? Ta dauka shine zai dinga ma jin kunyarta amma yanzu taga alama ita ma ke jin kunyarsa.
*******
Abincin data ajiye mai ya kalla sannan ya zauna ya kalleta, saukowa tai ta zubamai, ta samai spoon kallanta yai ta kalleshi mamaki ne ya kamata dataga fuskarsa a daure gam.
Mikewa tai ta zauna tana kallan ikon Allah, harya gama cin abincin be ce mata komai ba, ruwa yasha yace 鈥渒washe kwanukan.鈥�
Kwashewa tai gaba daya mamaki ya rufeta, tana dawowa taga ya bar falan.
Daki ta nufa, ganin baya nan ta tsaya a jikin dakin, jin karan gen ne yasa tasan yana waje.
Yana shigowa ya xauna akan kujera baiko kalli inda take ba, gaba daya hankalinta ya tashi, kallansa tai a hankali ta dan zauna daga gefensa tace 鈥渕enene?鈥�
Kallanta yai yanayin sa gaba daya ta kasa fahimta, tace 鈥渕enene?鈥�
Next time in abu ya shafeki ya kuma shafeni ina san jinshi daga bakinki.
Kallan mamaki tamai tace 鈥渨ani abin nai?鈥�
Murmushi yai.
Kallansa tai ta riko hannunsa tace 鈥淜anasan hankalin Baby ya tashi?鈥�
Kallanta yai sannan ya kalli hannunsa data rike murmushi yai yace 鈥淢eyasa baki fadan kina tunanin siyan gidan Tv dincan ba?鈥�
Kallansa tai kana ganin yanayin da fuskarta ta bayyanar zakasan dana sani ne tace 鈥淎llah I thought na fadama, sannan abin bai tabbata ba.鈥�
Duk abinda ya shafeki ya kuma shafeni ina san ko ban xama na farko ba ya zama na sani daga bakinki, ni bai zama dole sai na fada miki komai ba but i want you to tell me, zaki iya kiranshi selfishness........
Rungume shi tai wanda hakan yasashi yin shiru, am sorry nayi laifi, amma dan sankai sai kace na fadama kai kuma ba komai ba.
Murmushi yai yace 鈥渆h am a man akwai abinda dole ni kadai zan iya rikeshi.鈥�
Dagowa tai tana kallansa tace 鈥渟elfishness鈥�
Yace 鈥渆h dana bakiji nace ki kirashi da hakan ba?鈥�
Dan harararsa tai tace 鈥渉aushi kaji maganar kajita daga gun Dady?鈥�
Yace 鈥渁鈥檃 matsayina da yardar da kikamin nake san na duba.鈥�
Murmhshi tai tace 鈥淎llah bansan yanda zanyi dakai ba.鈥�
Ta fada tana dan matsawa, kara jawota yai yace 鈥渁kwai matsala kenan鈥�
Tame? Ta tambaya tana dan yin baya a kan kujera ganin yanda yake kwantowa.
Sai da suka karasa jikin kujera sannan ya nufi fuskarta kamar mai shirin sumbata dan harta rufe idanunta sai jitai yace 鈥渟aboda ke kadaice a yanzu kike da yanda zakiyi dani.鈥�
Ido ta bude ta kalleshi, murmushi yai yace 鈥測au ke nakeso kiyi.鈥�
Ya fada yana dan motsa bakinsa, kallansa tai tace ka danne ni.
Baki gane yaran ba kenan?
Dan sumbatar lebansa tai tace 鈥済ashinan nayi.鈥�
Kallanta yai dan yanda ya kankance ido yana kallanta har ya bata kunya tace 鈥渕enene kuma?鈥�
Yace 鈥渋na tunanin yanda zanyi dake ne.鈥�
Dariya tai tace 鈥測anda zakai dani?鈥�
Yace 鈥渆h鈥�
Mikewa yai ya zauna yace 鈥淒ady yace cikin weekend din nan zaizo, zakuje gun Abubakar din.鈥�
Zamuje dai bazaka rakani ba?
Eh ya fada kai tsaye.
Tace 鈥渂a ko yar kara?鈥�
Yace 鈥渟o kike nace eh?鈥�
Dan fuska ta kauda, murmushi yai yace 鈥渁m sorry amma no.鈥� Ya karasa maganar da murmushi.
Shiru tai jin kansa tai akan kafadarta ya kwanta sannan ya jasu suka jingina da kujerar, ya sa hannunsa ya zagayo da ita ta cikinta.
Idanu ta lumshe a hankali.
*******
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
********
[1/20, 11:47 AM] +234 816 537 8773: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{68}
Alhamdulila Dady ya zo an sai broadcasting station, sunje danbatta Khalid ya kai Abba asibiti dan kwana ma sukai a can sai washegari suka dawo, ba karamin dadi Khalid yaji ba dayaji Salmanu yacemai yar gida yake san ayi, sai dai Khalid yace mai tunda tana shirin fara exams na waec da neco ya bari sai ta gama.
Sun dawo kano cikin kewa da jiran lokacin hutu dan Asiya tazo dan itama tasan su Nabila zasuzo.
*******
Yau wata biyu da sati biyu da aure, sati uku kenan da fara aikinta.
Khalid ne ya fito daga wanka harya gama shiryawa bata shigo dakin ba, sanye yake cikin suit wanda a koda yaushe inya saka kyansa da kyan zatinsa ke kara fitowa agoggonsa ya daura a ahannunsa sannan ya dau jakarsa ta aiki da wayarsa ya fito daga dakin.
Abincinsa ya gani a falo hakan yasa kawai ya zauna ya bude, soyayyiyar indomie ce, kadan yaci dan tun daren jiya yake jin cikinsa a cunkushe.
Daga waje yaji tada mota hakan yasa yasan tana waje, tea ya hada yadan kurba, yana sha yana kallan gidan mikewa yai ya dau plates da cup din ya wuce kitchen, kallan kitchen din yai ga kwanukan datai amfani dasu nan a sink, ajiyewa yai kawai ya fito.
Tana gani ya fito ta fito daga cikin motarta tace 鈥淪weet kai nake ta jira sauri nake yi.鈥�
Ko kallanta baiyi ba yacigaba da sa takalminsa, da sauri ta tuno hakan yasa tace 鈥淥h ina kwana?鈥�
Ta fada tana tahowa inda yake.
Bai kalleta ba sai dai ya amsa gaisuwarta.
Hannunsa tadan riko tace 鈥渕uje?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渋na?鈥�
鈥淕un aiki na akiyeka na wuce鈥�
Dan kallanta yai yace 鈥渘o ki wuce.鈥�
Tace 鈥渄an Allah Sweet ka daina min haka kazo mu wuce tare plz鈥�
Hannunsa ya dan zare yace 鈥渟ai na dawo.鈥�
Ya fito daga gidan bayan ya bude mata gate, bin bayansa da kallo tai sannan tai ajiyar zuciya agoggo ta kalla sannan ta juya cikin sauri ta shiga mota, tana kallansa yana tafiyarsa, haka ta wuceshi ta tafi gun aikinta.
Gaba daya komai ya cabe mata dan tana aikatuwa saboda komai na gun ya durkushe sai faman saita komai takeyi, meeting ta wuce direct ranta a matukar bace take magana, tana gamawa ta fito ta wuce office dinta, tea dinta tasha sannan ta fito tana duduba abinda akeyi.
Sai data tabbatar komai na tafiya yanda takeso sannan ta koma office dinta ta cigaba da aikinta.
Secretary dinta ce ta shigo tace 鈥淗ajiya ta gama yin aikin.鈥�
Kallanta tai tace 鈥渢abi duk wanda zai dauko rahoto yanzu ta taimaka musu da aikin rike kaya.鈥�
Kallanta tai cikin mamaki ganin yanda kullum Ramlatu a wahala take karewa, Zainab tace 鈥渕enene? Kice in bazata iya ba tabar aikin.鈥�
Haka ta juya ta sanar mata, Ramlatu tace 鈥渢o鈥� sannan ta juya.
Kanta tadan dafa dake mata ciwo sannan ta kalli wayarta, kan sunan Sweet ta bude ta zubawa sunan ido ajiyar zuciya tai sannan ta kifa wayar ga cigaba da aikinta.
Sai yamma lis sannan ya dawo, yauma ya rigata dawowa, yanda ya tafi dama haka ya dawo yaga gidan, yana tunanin raban da gidan nan yaga shara yakai sati biyu, kitchen ya shiga shiru yai, tunanin gyarawa dakansa yai sai kuma yai tunanin daga sanda ya fara ya tabbatar bazata sake yi da kanta ba.
Juyawa yai ya shiga toilet yai wanka, akan gado ya dan mike yana waya da Salmanu.
Suna sallama yaji shigowar motarta, kayanta ta kwaso ta shigo ciki, ajiyewa tai a falo sannan ta shiga daki, yana zaune yana dane dane a waya kallansa tai tace 鈥淪weet ka dawo?鈥�
Eh kawai yace ba tare da ya kalleta ba, kallansa tai sannan ta matso ta zauna dan kusa dashi tace 鈥渟ai yaushe zaka dinga kallona in ina ma magana?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渄an matsa zan wuce masallaci.鈥�
Jiki a sanyaye ta mike ya sauko ya fito ya wuce masallaci.
Kanta tadan shafa sannan ta shiga toilet, wanka tai sannan ta sa kayan bacci sai datai sallah sannan ta fito falo, gen aka tada dayake ya canzo musu gen karshen watan daya wuce.
Zama tai ta jawo takardun ta tana dudubawa, Khalid ne ya shigo baiko kalli inda take ba yai hanyar daki.
鈥淪weet abinci fa?鈥�
Sai nayi isha鈥檌 yace kawai ya wuce ciki.
Shiru tai ganin ta kasa maida hankalinta kan abinda takeyi hannunta tasa a gefen kanta tana dan murzawa tana cigaba da abinda takeyi.
Har ya fito zai fita masallaci sallar isha鈥檌 tana nan yanda ya barta tana ta hidima.
Kallo daya yama inda take ya wuce, sai dayaje kofa ta lura ya fito da kallo ta bishi ganin ya wuce bai ko bita kanta ba.
Idanu ta rufe sati daya kenan da canzawar Khalid sam yanzu ko magana baya bari suke mai tsawo, ita kuma ga abubuwa sun cude mata bata san ya zatai ba.
Tana nan tana tunani harya dawo, mikewa tai tana kallansa, zama yai akan kujera a falan ta wuce kitchen ta kawo mai abinci sannan ta zubamai, zama tai kusa da inda ta ajiye abincin tace 鈥渒o na baka?鈥�
Kallanta yai yace 鈥渒ina da time din?鈥�
Kallan takardunta tai tace 鈥渙h am sry.鈥�
Mikamai tai ya kalleta jiyai wani abu ya tsayamai a wuya, ruwa ya kurba sannan ya dan ci abincin kadan dan haryanzu cikinsa bai ware ba, mikewa yai ya maidashi kitchen ya kara kallan kitchen din kawai ya wuce daki.
Tana nan a zaune dai sai 11 ma tai sallah, ta danci abinci sannan ta kara komawa ta zauna sai karfe 1 ta kashe komai ta shiga daki.
Khalid ta kalla dake kwance yana bacci, kusa dashi taje ta sa hannu ta ratsin cikinsa ta keantar da kanta kusa da kanshi, tabashin datai ne yasa ya dan farka.
Sha鈥檃wa ke cinta kwanan nan dan harmamakin kanta takeyi duk sanda zata kwanta sai taji Khalid take bukata, shiru tai tana tunanin yanda da ya nuna mata kulawa, a haka har bacci ya dauketa.
juyowa yai tare da dan haskata, bacci take hankalinta a kwance.
Ido ya zuba maga kafin ya juya ya koma baccinsa.
Karfe biyar da rabi ta farka, ganin baya dakin ba kuma ya toilet yasa ta fito falo da sauri, zaune ta ganshi akan sallaya yana karatun alqur鈥檃ni.
Ruwan shinkafa ta saka sannan ta dawo falo inda yake, kusa dashi ta zauna ta dan sa kanta akan kafadarsa.
Ganin ya rufe qur鈥檃nin yasa tace 鈥淪weet me kake tunani yau in muka dawo mu taho tare muyi siyayyar abinda babu a gida?鈥�
No kimin list zan taho dashi in na dawo.
Kallansa tai tace 鈥渨ai haka zamu cigaba da zama?l
Yanayin muryarta ne ya canza cikin rauni ta cigaba da ba haka kake ba meyasa lokaci daya kake neman canzamin? Bayan kasaba min da kai?in nama wani abin ka fadamin please amma ka daina nisanta kanka dani.
Kallanta yai kallan dayasa tasha jinin jikinta, yace 鈥渘i haryanzu Zainab yarinyace yar shekara 10?鈥�
Kallansa tai tace 鈥淪weet鈥�
Idanunsa yadan runtse yace 鈥渋 just don鈥檛 know what to do next, na gaji da miki uzuri na kuma gaji da nuna kamar raina bai baci ba.鈥�
Cikin shakka tace 鈥渕e nai?鈥�
Yace 鈥渉aryanzu tambaya kike?鈥�
Tace 鈥渋n ban tambaya ba ta ina zan sani? Gaba daya kasa na rasa yanda xanyi bansan menama ba amma duk ka canzamin.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渋ndai wacce ke gabana yar shekara 10 ce zan dane komai na sanar da ita.鈥�
Kallansa tai bakinta na rawa tace 鈥淜a san bansan......鈥�
Katseta yai cikin zafi yace 鈥渃an you please stop saying that? Komai kice baki sani ba? A koda yaushe ina miki uzurin rashin sanin abu sai yaushe ne zakisan abinda ya dace dake? Naji laifinane danai tunanin san da kikemin zai canzaki, sai dai da alama san da kikemin bai kai rabin wanda kike ma aikinki ba, nabaki dama kiyi yanda kikeso harzuwa sanda limit dina na hakuri dake zai kare daga lokacin kuma....鈥�
Hannu tasa ta rufe mai baki, tana kallan kwayar idanunsa hawaye na zubowa kuncinta.
Idanu ya runtse, ganin yanda hawaye ke zubo mata, ganin ya kasa jurewa ne yasa hannu ya jawota jikinsa.
Cikin kuka tace 鈥淎m sorry, na sani tunda na koma aiki na kasa baka mahimmanci kamar da amma Allah komai nakeyi kana raina abubuwan ne sun.......鈥�
Muryarta ce ta sarke saboda kukan dake neman kwace mata, bayanta kawai yake shafawa dan ba shikadai ne matsalar da suke fuskanta ba.
Dagota yai yana share mata hawayenta, hannunsa dake kan fuskarta ta rike tace 鈥渁m sorry.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渂an hanaki aikinki ba but at least respect your marriage, na sani naso kaina in nace ina san ki bani full attention dinki sai dai in kina cikin gida i need your attention, bakisan meke going dani ba, bakisan a ya na dawo ba, bakisan wani hali nake ciki ba, kawai aikin da kikeyi shine abinda ke gabanki, wani irin so ne da zama da muke?鈥�
Wasu hawayen ne suka digo saman hannunsa tace 鈥渒ayi hakuri na daina, nima please ka daina janye jikinka daga gareni.鈥�
Shiru yai yana kallanta, ba ruwa kika sa ba?
Da sauri ta mike ta shiga kitchen, kusa dashi ta dawo tana murmushi tace 鈥渒asan yaushe raban dana taho naga idanka akaina?鈥�
Ko ban kalleki ta ido ba ina ganinki.
Kusa dashi ta zauna ta kamo hannunsa tace 鈥淧lease ka dawo Sweet din dana sani.鈥�
Yaushe raban da a share gidan nan?
Kallansa tai tare da dan sauke ido kasa tana kallan falan, duk da ba datti yai sosai ba amma kana gani kasan an dade bai ga kulawa ba.
kitchen fa?
Kallansa tai cikin jin kunya tace 鈥淣a na....鈥� sai kuma tai shiru, yace 鈥渢oilet fa?鈥�
Sweet abubuwa sun min yawa wlh.
Kallanta yai yace 鈥渒ina tunanin akanki mata suka fara aiki? In har bazaki iya ba zan taimaka na samo mai min.鈥�
Mai aiki zaka samo mana?
Tai maganar kai tsaye, yace 鈥渁鈥檃 wace zata kula dani nake nema.鈥�
Wani mugun kallo tamai tace 鈥渕ata kake nufi?鈥�
Yace 鈥渆h tunda kin auri aikinki ni zan auri mai kula.........鈥�
Katseshi tai tace 鈥渘aji ai ba cewa nai banda hannun yi ba.鈥�
Oh I thought hannunki na aiki ne kawai.
Kallansa tai tace 鈥渄a can da nakeyi fa?鈥�
Da can yaushe?
Tadan kauda kai tace 鈥渒afin na fara aiki.鈥�
Mikewa yai yana neman shiga daki, mikewa tai ta bishi ta rungumeshi ta baya.
Tsayawa yai yana jin abu na tsirgamai, tace 鈥淜o sunana baka kira ba.鈥漜ikin sanyi tai maganar
Dan murmushi yai sannan ya juyo da ita murmushi yai yana kallanta, dan ido ta juya kadan sannan ta dago dakanta ta sumbaci bakinsa.
Kallansa tai tace 鈥淚 miss you.鈥�
Murmushi ya sake tana neman sakeshi ya sa hannu ya rikota, yace 鈥渉aka ake missing?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渆h mana.鈥�
Jeki rage gas kizo na fada miki wani abu.
Sakeshi tai ta shiga cikin kitchen, kallan kitchen din tai me takeyi tabar kitchen din ta haka? Ita da batasan kazanta?
Dole Khalid ransa ya baci, zuma ta dauko tadan diga kadan a auduga sannan ta riga almiskh ta dan yi matsi dashi na dan minti biyu sannan ta cire ta fito.
Yana zaune a kujera ta dawo, hannu ya mika mata ta karaso ya jawota jikinsa, kallansa tai tana murmushi, yace 鈥渒afin mu fita aiki mu dinga gyara ko ina? Zan tayaki da gyara gado.鈥�
Zama tai akan cinyarsa tace 鈥渁m sorry bansan me nakeyi har abin yakai haka ba, sannan gyaran gado ai ba aiki bane.鈥�
To ko bakyaso?
Cikin dan shagwaba tace 鈥渋na so, amma Allah karka sakemin zancen wata mai taimako.鈥�
In har kema kin ajiye aiki a office kin ba mijinki kulawa a gida.
Dan kwanciya tai akan jikinsa dagota yai yakai bakinshi cikin nata, yau kam anji jiki dan an dade ba鈥檃 gamu ba abin ba鈥檃 cewa komai.
Saboda lokacin aiki ya kusa tare sukai wanka tana fitowa ta wuce kitchen ta fara gyarawa, tana fitowa taga ya gyara daki, kallansa tai harya shirya, tace 鈥渢hanks.鈥�
Murmushi yai sannan yace 鈥淭hank god mun shirya abin bai zo ba.鈥�
Kallansa tai sannan a ranta tace oh ya haka? Ya kamata yazo tun last week.
Kallanta yai tana sa kaya yace 鈥渕enene?鈥�
Kai ta girgiza tace 鈥渂akomai.鈥�
Fitowa sukai tare suka sha tea da bread da butter, suka fito.
Sai dadi takeji kana ganin fuskarsu zakasan suna cikin farin ciki tun balle Zainab fuskarta wasai sai murmushi take.
Kallansa tai tace 鈥減lease!鈥�
Yace 鈥渘o kije plz karki late.鈥�
Ka manta nice shugaba inada damar yin late please mu tafi tare.
Murmushi yai ya matso kusa da kunnenta yace 鈥渂akyasan rabuwa dani?鈥�
Murmushi tai tace 鈥測anzun ma baza鈥檃 barni na fada ba?鈥�
Haryanzu kansa na kusa da kunnenta yace 鈥渄azu an nunamin anyi missing dina sosai.鈥�
Dadinta nima nasan anyi.
Kallanta yai yace 鈥渋nyeee鈥�
Tace 鈥渕e? Kana mamaki? Ai naga alama nima daina shiru ya kamata nai鈥�
A tare sukai murmushi ta ja hannunshi jikin mota ta sake cewa 鈥減lease.鈥� Tai maganar cikin jan ra鈥檃yi.
Haka suka shiga a tare dadi ya kamata suka fito.
**********
Sai yaushe zaka daina zuwa?
Kallanta yai yace 鈥渦ngo.鈥�
Ya mika mata leda, kallan ledar tai tace 鈥渕enene?鈥�
Kara mika mata yai, amsa tai ta bude, magungunan da Mama ke sha ne a ciki.
Kallansa tai tace 鈥渘a meye?鈥�
Yace 鈥渟hekaranjiya naji Baba na cewa zai siyo, ki bashi wannan.鈥�
Dan harararsa tai tace 鈥渨aya saka?鈥�
Murmushi yadanyi yace 鈥渟hima laifi ne?鈥�
Juyawa tai zata wuce.
Yace 鈥淩aziyya!鈥�
Tsayawa tai a inda take sannan tadan juyo kadan, yace 鈥渄an Allah ki yafemin, yau zuwana na 12 kenan.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渘a dauka a zuwanka na 5 na cema na yafema.鈥�
Yace 鈥渘aji wannan amma nasan baikai zuciya ba.鈥�
Kallansa tai batace komai ba, murmushi yake yai yace 鈥渟hikenan.鈥�
Dan maganin dake leda ta daga tace 鈥渁ngode.鈥�
Ta wuce, murmushi ya saki yabita da kallo harta shiga cikin gida.
Yana tafe a hanya mazan dake gabanshi yana ji suna gulmar Su Raziya, jikinshi ne ya sake yin sanyi dayaji dayan yace 鈥渁h dama ta ina namiji zai gama amfani da mace yace zai aureta?鈥�
Dariya dayan yai yace 鈥済atanan a jibge a gidan duk wadanda suka dana ba wanda ya kawo tayi.鈥�
Ransa ne ya kara baci haka ya wucesu ya wuce gun aikinsa.
Babban shagon da yake zaman jira ya shiga, yana aiki yana tunani, murmushi yai ganin sakon Khalid dayace 鈥淚n ka gama dawowa hankalinka ka min magana na fada mata.鈥�
Reply yamai yace 鈥淗ankalin nawa bace wa yai?鈥�
鈥淥h na dauka haka kacemin.鈥�
鈥淗aka kace?鈥� Ya tura yana dariya yai sannan ya cigaba da aikinsa.
Sai shida ya taso a hanya ya tsaya yasai bread da kayan tea dan sachet sannan ya wuce gida.
Dan karamin dakin daya kama.
**********
Tana zaune a cikin dan kitchen din tana ta murza gyada, sai uban gumi takeyi tana yin mai.
Kafadarta ce ta shiga amsawa, ta saki wata uwar hamma sannan ta dan gutsiri gwaibar dake gefenta.
Hanne ce ta kalleta ta dan tabe baki dan tana kishin yanda Adam ya turo mata kudi ta fara sana鈥檃r man gyadar nan.
Goggo ce ta gama ta fito tana mika, jaraba ta fada tare da daukan wayar.
Kin gama?
Na gama, wai Adam haka zaka sani a gaba kullum sai kaji abinda nai?
Kudina na baki kike aiki dashi ko kinsan wahalar danasha kafin na samesu?
Daukan hotunan na yau na gani.
Wata uban kwafa tai sannan ta dau hoton tace 鈥渋n Umaru yazo ya turama.鈥�
Yace 鈥渆h zan fadamai.鈥�
Cikin takaici ta kashe wayarta, kwafa ta sakeyi gaba daya ta kasa gane kan Adam dan har tunani take Adam dinta ne wai?
0 comments:
Post a Comment