*GIDAN MAI UNGUWA*
Suna zaune suna hira da yaran su da makota da suka zo biki. Lado ya shigo yana sharce zufa ranshi a hade yace "Mama zo kiji wai diyar gidan haya baba ya aura."
Salati Hannatu ta sanya tana dafe kirji" Diyar gidan haya fa kace Lado?"
"Wallahi ita ce ya aura wannan yarinya karama da ita, wacce wallahi ko ni ta yimin kankanta da aure wai ita baba ya aura."
Zugum suka yi suna jimamin wannan masifa da mai unguwa ya kwaso musu. Sai gashi ya shigo yana saba babbar riga, yasha fararen kaya yana ta bude hakora. Makota sukai mishi fatan alheri suka fita. Ya kalle su yanda duk sukai shiru kamar masu zaman makoki yace "Lafiya kuwa kuke zaune da tagumi kamar ance iyayen ku sun mutu?"
Cikin takaici Hannatu tace " cewa akayi mai unguwa Tanko ya mutu shine muke jimami."
"Ubankine ya mutu billahillazi bani ba, munafukai kawai duk kishi ne na sani."
Jummai ta kalli yanda yaran ke zaune rai a hade tace" Ko wacce ta wuce gidanta, kuma ku tafi wurin sana'ar ku an gama taro."
"Allah sarki Jummala ayi hakuri dai aure ne nariga nayi ko da taro ko babu taro sai amarya tazo." ya fice daga gidan.
Haka kuwa yaran jiki a sabule suka yi musu sallama duk suka fita. Suka bar iyayen cikin jimamin wacce mai unguwa ya debo musu matsayin kishiya.
Yana fita ya hadu da da baban Ladi yana haki kamar dan tsere.
"Kai Lawal meye haka kake ta haki, lafiya dai ko?"
"Ina lafiya Ranka-ya-dade Maman Ladi ta gane kai ne mijin, tace wallahi ba zata bada amarya ba."
Shekeke mai unguwa ya bishi da kallo "Yo ita shegiyar matar taka an gaya mata tana da ikon kan matar dana biya sadaki ne?, to billahillazi ka koma ka fada mata anjima a bani amaryata ko wallahi taga kalar nawa haukan, banzaye bayan na biya kudi na sai ace za'ayi min iko."
"Ranka-ya-dade wallahi shakeni ta yi bazan iya komawa ba."
"Aikuwa zata san waye Tanko billahillazi a garin nan." ya shige gida a fusace.
*CIKIN GIDAN HAYA*
Maman Ladi da 'yan korenta zaune kofar dak'inta, suna kara zugata kan kada t yarda akai diyarta gidan mai unguwa.
"Nifa da hankali na wallahi bazan ba Tanko Ladi ba, kuma yazo ya gani."
"Wallahi Maman Ladi gidan shi babu abinci, babu suturar arziki."cewar Ladidi.
"Nifa nasan waye Tanko, domin munyi artabu da shi watarana ana fad'a gidan mu yazo rabo y dinga tsine mana" cewar wata kawar Maman Ladi mai suna Atuwa.
"Ayererre a dade anayi, aure dai the auro dole a ba Tanko matarsa."
"Ke Talatu wallahi ko Ubankine bazan bayar ba, kuma ki daina shiga sabgata Maman Ladi nake."
"Aifa yau ko uwata zaki zaga bazan damu ba ai dama duk wanda y shiga motar kwadayi yasan inda zata kaishi."
Cikin fusata Maman Ladi ta nufo Inna Talatu ta hauta da duka, sai dambe. Kaya-kaya ana kokarin rabawa sunki rabuwa domin a zuciye Maman Ladi take sai jibgar Inna Talatu take yi, ganin haka yasa Inno shigarwa Inna Talatu dama tare suke adawa da wannan aure. Aikuwa hadasu Maman Ladi ta yi t dinga jibga tana gwara kawunansu.
Ladidi dake tsaye gefe ta kalli Mairon Ado tace"Ke Mairo zo ki tayani dibar abinci idan kina so."
Abule dake zaune tana kallon fad'a ta dubi su Mairo "Walle Mairo ta karkije wanga cin amana ta zata yi."
"Wani shegen yace miki cin amana zanyi?"
"Ke na shegiya." cewar Abule.
Mari Ladidi ta kawo ma Abule, Mairon Ado ta tare tana hararar Ladidi"Kika tabata sai na sabautaki wallahi matsiyaciya kawai mai..." bugun bakinta da Ladidi ta yi yasa ta yi shiru ba tare data shirya ba.
Abule na ganin haka ta hau Ladidi da duka baji ba gani. Suma suka hau fad'an su uku, gefe kuma gasu Maman Ladi. Gudar masu daukar amarya ne y dakatar da wannan rikice, aka shiga kallon-kallo.
"Munzo daukar amaryar mai unguwa."Cewar Maimounath makociyar mai unguwa da ya roka suzo dauko amarya tunda yan'uwan shi sunki zuwa. Ita kuma Maimounath dama da biyu tazo saboda basa ga maciji da 'yan gidan haya.
Shewa Inno data gama dokuwa gurin Maman Ladi tasa tana fadin"Gaya musu su fito muku da amarya ku cika umarnin mai unguwa."
"Aikuwa dai yar'uwa abamu amarya a mutunce mu kaita dak'in ango a mutum.." wani duka taji ya sauka a kanta wanda yasa ganinta ya dauke na 'yan sakanni.
"Bari naji' yar iskar data kara cewa na bada diyata akai gidan mai unguwa." cewar Maman Ladi dake tsaye rike da muciya.
Nan fa 'yan koren Maman Ladi ko wacce t dauko abun duka.'Yan daukar amarya na ganin haka ga Maimounath durkushe a kasa, ai sai suka sanya gudu suka barta. Ladidi ta kalle ta ta tuntsire da dariya tana fadin "Su yan daukar amarya ansha wahala, ina bakin fadin amarya yake?"
Cikin karfin hali Maimounath ta mike ta shake wuyan Ladidi ta fara jibga, ganin haka Maman Ladi da sauran suka rufeta da duka, sukai mata lilis suka barta kwance.
*WURIN MAI UNGUWA*
Sauran da suka koma suka fadi ma mai unguwa abun dake faruwa, aikuwa ya mike ya saba riga shida abokin shi Kallah da baban Ladi suka nufi gidan.
Yana fadin " Wallahi yau Lawal matar ka zata san Tanko take raina wa."
" Ayi hakuri don Allah Ranka-ya-dade."
Matan naji Hannatu t dinga dariya "Maman Sani yau zaki ga angon da daukar amarya, Allah yasa Maman Ladi ta mai dukan tsiya."
" Uhm Uhm Hannatu mijin kine fa."
"Maman Sani ayi sha'ani kawai wallahi."
Nan suka dinga tattaunawa suna kara jajantawa kansu aikin da ya dauko musu.
*CIKIN GIDAN 'YAN HAYA KUWA*
_MEZAI FARU DA ZUWAN MAI UNGUWA_
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*WANNAN SHAFIN NA MUSAMMAN NE GAREKU DOMIN KU DIN NA MUSAMMAN NE, KODAYAUSHE INA YI MUKU FATAN ALHERI*
_BRO HUSSAIN ATK_
-BRO HASSAN ATK_
_AUNTY HASSANA ATK_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*70~75*
Maimounath kwance ko motsi bata yi saboda ta daku, su mai unguwa suka doka sallama suka shigo. Ganin ta kwance yasa sauran matan suka nufeta da sauri suna tambayar lafiya. Inna Talatu dake tsaye kofar dak'inta ta bude baki da karfi tace"Su Maman Ladi ne suka jibgeta wallahi."
Mai unguwa ya kalle su fuskannan a daure yace " ku dauketa ko kaita kemis ina zuwa."
Suka dauketa su uku suka fice.
Ya kalli Maman Ladi dake tsaye bakin kofarta, inda ta rufe Ladi dake aikin kuka ita batasan mai unguwa. Yace" Nazo daukar matata da kai na."
"Sai dai idan uwar matar ka zaka dauka."ta bashi amsa.
Ya kalli Baban Ladi, ai kuwa da sauri ya matso jiki na kakkarwa yace"Haba Maman Ladi don Allah ki bari a tafi da ita wallahi yanzu bamu da iko da ita."
"Algungumi ba inda zata indai nina haifeta, kuma wallahi naga uban da zai dauketa."
"Nine kuwa uban da zai dauketa billahillazi."cewar mai unguwa.
"To kana iya zuwa ka dauketa ai matsiyaci."
"Kece dai matsiyaciya shegiya me bakin hali."
Da sauri Kallah yace" Ranka-ya-dade surukar kace fa yanzu a tauna kalamai."
Wani kallo ya buga ma Kallah wanda yasa Kallah tsugunnawa yana fadin "Tuba nake Yallabai."
"Wallahi yau zaa bani matata ko kuma na yi bala'i billahillazi,kuma wannan mai kama da buhun fulawar ta yi kadan na kira ta da suruka."
"Kana iya zuwa ka dauketa ai idan kai ka haifa min yarinyar, mai kama da sauro."
Karasawa kofar dak'in ya yi yana kokarin shiga, aikuwa Maman Ladi da mutanen ta suka rufe shi da duka ga makota nata shigowa kallo. Dukan shi suke suna karawa shikuma kokarin ceton kansa ya ke don kuwa baisan tsiyar da suka shirya mai ba kenan.
Kallah da Baban Ladi nata rokon su dai na amma sunki don haka Kallah ya ranta ana kare yana fadin"Naji bayanin yanda aka kare idan mun hadu, domin wa'innan matan babu alamun tausayi tare dasu."
Makota na leke suna bada hakuri wasu kuma suna kara zuga wa.
Jiniyar motan 'yan sanda suka jiyo, aikuwa suka sake mai unguwa da sauri suka shige dakunan su.'Yan sanda suka shigo su biyar uku mata biyu maza cikin gidan. Mai unguwa na ganin su ya sanya ya mike da kyar yana goge jinin bakin shi yace"Kuci uban su sosai ku tafi dasu setation don Allah, billahillazi bazan yafe musu ba kuma a fito min da matata."
"Kayi hakuri mai unguwa zamu dauki mataki insha Allah."
Nan aka sanya 'yan sanda matan suka shiga dakunan duk aka tarkato su waje.
Maman Usman ce kadai bata nan, domin ta yi tafiya bata gari duk wannan bidirin da ake yi. Gaba daya matan gidan aka tasa su gaba zuwa ofishi, mai unguwa yace a taho masa da mata, aka kuwa fito da ita sai kuka take.
Aka tasa keyarsu hada 'yan biki sai setation.
*Ofishin' yan sanda*
Suna zaune Dpo ya shigo, ganin mai unguwa manne da bandeji a Hannunsa da gefen kunne yasa ya karaso da sauri.
"Mai unguwa maiya same ka haka ne, ba dai hatsari kayi ba?"
"Bari Ddo waccan tsinanniyar matar ce ta jimin ciwo wallahi."
Sai lokacin Dpo Muhammad Abubakar ya lura da matan dake tsaye gefe guda. Da mamaki ya kira sajan yana tambayar meyafaru, nan suka fada mishi tun daga kiran da akayi musu da kuma yanda suka tadda mai unguwa ga Maimounath ma sun daketa.
"Dankari! Kenan menene matsalar?"
"Ranka-ya-dade sai dai a kira mai unguwa ya yi bayani."
"Kirashi su."
"Yes sir." ya fita ya kira mai unguwa suka shigo tare.
Nan ya zaiyane komai da ya sani dangane da fad'an da kuma dukan da suka yi mishi da Maimounath. Nan Dpo ya fito ya tara su wuri daya ya fara tambayar ba'asi. Wasu su fadi gaskiya wasu akasin haka, dukka ya tattara ya hada ya yi tagumi yana kallon su. Duk sukai shiru suna kallon shi yace "Aba mai unguwa matarsa su tafi."
Kuka Maman Ladi ta sa tana fadin" Wallahi bazan yarda diyata taje gidan shi ba, domin da farko ai basu fadamin gaskiya duk munafukai ne."
Tsawa ya daka mata ta yi shiru tana kallon shi. Ya yi musu dogon sharhi kan boye mata da suka yi sannan ya yi umarnin Maman Ladi da sauran duk zasu bada dari biyar-biyar na dukan mai unguwa da Maimounath kudin magani. Haka suka bayar suna Allah ya isa a zuci. Haka ya dinga musu nasiha yana ankarar dasu illar abun da suke yi, daga bisani ya sallame su suka fito. Maman Ladi na kuka Ladi nayi suka rabo ta hau mashin din mai unguwa suka tafi. Su kuma matan gidan da 'yan biki ko wacce ta yi hanyar gidan ta.
Maman Ladi na koma wa ta dinga rabawa 'yan gidan duk kayan bikin data hada tana cewa "Wallahi dana kai gidan mai unguwa gara na zubar dashi." Ta kira almajirai ta dinga rabo.
*GIDAN MAI UNGUWA*
Yana tsayar da mashin ta sauka ta tirje taki shiga, juyin duniya Ladi taki shiga gidan. Mai unguwa ya fusata ya dinga zaginta. Hayaniyarshi ta sanya matan lekowa jin yana surfa zagi, aikuwa ganin Ladi tsaye kikam kamar gunki yasa Jummai dauko mayafi ta fito,tana zuwa ta riko hannun Ladi, aikuwa bata yi gardama ba ta bita suka shiga gidan.
Takaicin hakan yasa mai unguwa gunduma musu ashar yana cewa"Ban aurota don ku zauna da ita ba, billahillazi kar wacce ta koya mata bakin hali." basu kula shi ba suka shige dak'in Jummai dukkansu.
Zaunar da Ladi ta yi tana rarrashi Hannatu ta debo mata abinci suka saka ta gaba suna ta bata hakuri. Da kyar ta yi shiru yana ajiyar zuciya taci abincin tasha ruwa ta haye gadon Jummai ta kwanta. Kallon juna suka yi Hannatu tace "To yanzu ya zaki yi taje dak'inta?, kuma fa dak'in ba komai basu kawo kaya ba."
"Barni dashi Hannatu zai gane kuranshi ya sake ya shigo da sunan tafiya da yarinyar nan dak'inta."
Duk suka zauna suna dakon zuwan mai unguwa, kamar ya sani kuwa yaki zuwa ya shige dak'i ya kwanta yana jinyar jikin shi.
*WASHEGARI GIDAN HAYA*
Maman Ladi ta tashi zuciya tunkushe da bakin ciki, ta kira Inno tace "Inno ki kwashe kayan gadon nan ki siyar dasu ki ban kudina ko nawane gara nayi asara dana kai ma mai unguwa."
"Haba Maman Ladi kiyi domin diyar ki mana, kinsan dai mai unguwa bazai kula da ita yanda ya dace ba, kiyi hakuri ki kai mata."
Shiru Maman Ladi ta yi tana tunani, can tace "Shikenan ku shirya kukai kayan to." ta shige dak'i. Gyada kai Inno ta yi domin ta tausaya wa Ladi da auren mai unguwa dama dan basu san waye angon ba yasa suke bakin ciki.
Haka kuwa rana na yi aka kwashe kaya sai gidan mai unguwa.
*LADI GIDAN MAI UNGUWA*
Da safe suka tashi suka fara ayyukansu, Ladi nata baccin gajiya har suka gama hadin karin safe. Hannatu t taso ta, aikuwa t sanya kuka ita gida zata je, da kyar suka samu ta yi shiru t zauna suka kar ya. Mai unguwa na jinsu yana kwance dak'i duk jikin shi ciwo yake domin yaci duka ba kadan ba.
Suka zauna suna da janta da hira har ta sake dasu. Mai kura ya yi sallama suka shigo tare dasu Inno da Ladidi, Abule, Maman Dare, Maman Akintola, Inna Talatu, matar Malam da sauran matan gidan d makota.
Nan su Jummai suka yi musu tarba ta mutunci, mai kura ya jide musu kayan suka hau shiryawa. Ladi t dinga yi musu kuka tana cewa su tafi da ita. Hakuri suka dinga bata Maman Akintola tace " Ladi kana da iyaye fa a gida na me anguwa kayi hakuri kawai ka zona kaji ko." ta gyada mata kai tana kuka har suka gama jere suka tafi. Mai unguwa na dak'i yaki fitowa yana kunyar ya yi ido biyu dasu saboda dukan da ya sha jiya, sai da suka tafi sannan y fito yana hura hanci.
Yace"Jummala ruwan wanka"
"Babu." ta fadi a takaice.
"Allah ya hana ki muguwa kawai." ya fice yana hararar Ladi.
Nan Jummai ta dinga rarrashe tana nuna mata ta yi biyayya zata ji dadin zama tare dasu, ta gyada mata kai tana kuka suka shigar da ita dak'inta.
*'YAN GIDAN HAYA*
Suka koma suna bata labarin matan mai unguwa sun rike Ladi kamar yarsu, wannan yasa Maman Ladi ta saki ranta domin tasan matan nada mutunci ba kamar shi ba. Hankalinta ya dan kwanta ta rage fargabar diyarta zata cutu gidan mai unguwa. Mijin kuwa tun ranar bai dawo ba sai yau, ko kallon shi bata yi ba.
*Ya ya zaman Ladi zai kasance da mai unguwa kenan??*
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
_ALHAMDULILLAH SADAUKARWA GA DAUKACIN AHALIN ALHAJI ABUBAKAR SA'EED ARDO BORO, UBANGIJI YA TSARE MU YA KARE MU GA SHARRIN MAKIYA, ALLAH YA SHIRYA MANA ZURI'A DAYYIBA AMEEN._
🌹 *BAMU DACE DA JUNA BA*🌹
_UMMU BASHER_
*Allah sarki wasu iyayen basu san cewa kwanciyar hankali yafi kudi ba, shiyasa suke ganin 'ya'yansu sunfi karfin talaka. Amma ga Ummu basher ta fada mana cewa zaman lafiya, kwanciyar hankali, soyayya da sauransu duk ana samu koda babu kudi, zaa dace da juna. ina taya ki murna na kammala wannan littafi k'awas, Allah ya kara basira da zakin hannu hade da kwarin idanu. Ina yinki sosai dinnan. Muna biye a DANA SANI*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_Ma cherie ta mai unguwa Tanko ina kika kai mana SAADAT angon BUSHRA, kina kamshi muna miki feshin humra tawan more grease._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*80~End*
Sosai gidan 'yan haya fad'a ya yi sauki, ko wacce na kokarin kare martabar sana'arta tun bayan dawowar Maman Usman taji duk abun da ya faru, nan ta nuna musu cewa muddin suna da sana'ar yi to ba zasu kasance suna ganin bakin juna ba. Hakan yasa suka dage kowa ya kama sana'a suna kuma kokarin ganin an zauna lafiya. Bata taba kai ma diyarta ziyara ba, sai dai tana samun labarinta wurin kawayenta.
*GIDAN MAI UNGUWA*
Sosai suka rike amanar Ladi, kasancewar yarinyar tana yi musu biyayya ta shammace su basu yi tsammanin zata yi hakuri ba duba da halayya ta gidan data fito. Suna kare ta sosai don ganin mai unguwa baici zarafinta ba, sun yarda duk abun da zai ma ta ya yi musu gudun magana cikin gari.
Sun hada kai suna ganinta kamar yaran su mata dake gidan aure.mai unguwa ya yi jarabar ya yi masifar hadin kansu yaga basu da niyar canzawa, gashi duk abun da suka ce shi Ladi keyi don haka yasa musu ido kawai yana kallon su.
Lokaci yaja kwanaki sun shude haka satittika haka watanni yau Ladi watan ta biyar gidan mai unguwa ba tare da taje gida ba. don haka yau take ta zumudin zuwa gidan su. Ta gama shiryawa ta fito da mayafinta a hannu tace"Maman Sani zan tafi."
"Lallai Ladi da safiyar nan zaki tafi?"
Rau-rau ta yi da ido kamar zata yi kuka tace"Maman Sani ina son ganin Mamana fa."
Dariya suka yi suna tsokanar ta ganin zata yi kuka. Da sauri mai unguwa ya fito yana gyara mashin dinshi yace " ke zo mu tafi ki bar wa'innan matan."
"To a dawo lafiya Ladi a gaida gida."
"Insha Allah za suji." ta fita suka tafi.
*GIDAN 'YAN HAYA*
Maman Usman na zaune cikin su suna hira, sai nishadi suke kamar basu ba. Maman Akintola tace " wallahi gida namu ya yi dadi fa kowa ya yi shiru ya yi hakuri kome ya wuce."
Suka sa dariya dukkan su, sai jin sallamar Ladi suka yi. Da gudu ta shigo ta rungume uwar sai kuma tasa kuka. Maman Ladi murna Sosai ta yi na ganin Ladi tace" To rigimatu kukan na menene?"
"Mama baki taba zuwa gidana ba."
Duk matan gidan sukai dariya, Maman Usman tace " Ladi sai kuma aga Maman ki gidan ki ba kunya ko?, kamar ba diyar fari ba."
"Kai mama kema sau daya kika je ai."
"To zan dinga zuwa kullum." ta fadi tana dariya.
Ladi ta rufe ido da hannayenta tace "Yana waje fa tare muke dashi."
Rankwashi matar Malam ta sakar mata akai" Ja'ira shine tun dazu baki fadi ba kika zauna shagwaba?"
Da sauri Maman Usman ta dauko tabarma ta shimfida tace "Maza jeki shigo dashi."
Tare suka dawo sai sunkuyar da kai yake yi alamun kunya, domin ya tuna abubuwa da yawa da ya faru cikin wannan gida, gashi kuma yau ya shigo matsayin sirikin su. Ya nemi wuri ya zauna, Ladidi ta kawo mai ruwa, matar Malam ta kawo mai fura. Suka zauna suna gaisawa a kunya ce.
Bayan sun gama gaisawa suka zauna.
Maman Usman tace "Alhamdulillah nayi farin ciki ganin wannan rana, domin ada can ba muyi tsammanin abu makamancin wannan ba, mai unguwa matsayin suriki cikin gidan haya. Lallai abun mamaki ne sosai da hakan ya faru amma sai gashi sanadin haka zaman lafiya da fahimtar juna ya dore tsakanin mu, ina fatan zamu kasance masu hakuri mu jure neman na kanmu mu guje ma rigima da tashin-tashina."
"Kwarai hakane Maman Usman domin kin dade kina nusar damu illar fad'a cikin gidan nan, amma bamu dai na ba sai gashi tun bayan auren Ladi da mai unguwa zaman lafiya yazo ya daure sosai, Allah yasa mu kasance koyaushe haka." cewar Inna Talatu.
Maman Ladi ta yi ajiyar zuciya tace "Gaskiya munyi zaman rashin hakuri da junan mu, mun kasance masu biye ma zuciya da rashin sanin meke mana ciwo muna fad'a da junan mu alhali Allah ya ri ga ya kaddara zaman mu tare, musamman ni na kasance mai daukar duk abun da diyata ta fadamin game da mutanen gidan nan koda bana nan, sai dai abun farin ciki shine bata dauki wannan hali taje gidan miji dashi ba, ina kira ga iyaye dasu dinga kwabar ya'yansu kan maganganu, su daina yarda da maganar yara koda suna tunanin gaskiya ce. ina fatan zamu yi hakuri mu kasance masu yafiya mu zauna lafiya."
"Gaskiya ne Maman Ladi mun kasance masu kyashi da hassada, mun dauki mugun hali na fad'a da juna mun yafa, mun tsane junan mu kan bambamcin ra'ayi, ina fatan zamu cire kyashi a ranmu mu rungume zaman lafiya." cewar Ladidi.
Maman Dare ta yi dariya tace "To a madadin yan'uwana da basa jin hausa sosai, muna mika namu hakurin gare ku da fatan zamu cigaba da kasance wa cikin farin ciki da zama lafiya gaba dayan mu duk kuwa da bambanci yare da addini da muke dashi."
" Tabbas auratayya na daya daga cikin abun da ke haddasa zaman lafiya, domin sanadin auratayya ne zaman lafiya da farin ciki suka wanzu cikin gidan nan, ina fatan kowa zai maida hankali wurin bada aure tsakanin al'umma domin hakan na bada gudunmawar zaman lafiya." cewar Inna Talatu.
Mai unguwa ya kalle su yace " Lallai haka ne maganar ku gaskiya ce, domin dukkan mu masu laifi ne, mun kasance mutane marasa hakuri a rayuwa, komai muna sanya ido kanshi, mun kasance mutane masu addini da ban da kuma harshe wanda mu kammu muka kasa hade kai mu zauna lafiya, amma ina fatan yanzu zamu yi hakuri mu duba akasin da muka fuskanta a baya mu hadu mu gyara da kanmu. Mu gudu tare mu tsira tare domin zaman lafiya yafi zama dan sarki."
Kowa ya yi na'am da zancen su aka hadu aka nemi yafiyar juna aka yi addua aka tashi. Mai unguwa ya yi musu sallama ya dau matarsa suka wuce gida cikin farin ciki da annashuwa.
*GIDAN MAI UNGUWA*
Bayan sun dawo aka zauna hira bayan magriba. Mai unguwa yace " Ina fatan zaku yi hakuri da halina muci gaba da zaman lafiya daku, kuyi hakuri ku yafe min duk abun da nayi muku."
Cikin farin ciki suka dinga murna suna jin dadin canjin da aka samu daga mai gidan nasu.
Rayuwa kenan yau mai unguwa ne ya bada ijiyar mabudin rumbu a hannun matanshi saboda tsananin zaman lafiya.
Yau gashi duk sun fahimci juna sun yanke duk wani abu da zai haddasa masu rashin fahimta, sai fatan daurewar zaman lafiya.
Ina fatan madaukakin sarki Allah ya cigaba da zaunar damu lafiya, da kasar mu lafiya. Allah ya bamu ikon fahimtar amfanin zaman lafiya, mu rungume zaman lafiya fiye da tashin hankali mu hade kanmu cikin aminci da salama ameen.
Alhamdulillah tammat bihamdi, nan na kawo karshen wannan littafi na 'YAN GIDAN HAYA, ina fatan Kuskuren dake ciki ubangiji ya yafe mun, wanda nayi dai-dai Allah ya karbi niyyata na fadakar d al'umma muhimmancin zaman lafiya ya sanya muyi tarayya cikin ladan da dukkan masoya.
*Ina yi muku fatan alheri masoya duk inda kuke, Allah ya sada mu da alheri, na gode ma kowa da kowa duk masu jumurin bibiyar littafi na tunda ga kan BADDEEYERH, GIDAN MARAYU, SANADIN K'AWATA, SAI KUMA 'YAN GIDAN HAYA.*
*Ku kasance dani cikin TUSHE MAFARI domin yanzu wasan ya fara, tare da daukacin members dake rubutu kan _TUSHE MAFARI_ . Ga Fauziyya Lawal Ammany muna tafe muku da wani sabon littafi mai suna _BAHAGON TUNANI_ nan ba da dadewa ba insha Allah fans fatan alheri.*
_Allah ya daukaka zamani writers ya kara mana zumunci tsakanin mu ameen_
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك 🙏🏼🙏🏼👏🏻👏🏻
0 comments:
Post a Comment