ďin mu ne,kuma rashin insa gareni babbar matsala ce".
Sai data kai ƙarshen zance Mama ta ɗago kaita dubeta kana tace, "kina nufin yanzu nabarki kije?".
kai ta ɗagama Mama alamar "eh".
Sai Mama tace tare da Safiyya zaku je?".
Sai Hafsat tace, "a'a Mama kinsan ba department ɗin mu ɗaya da itaba.
Sai Mama tace, "to gaskiya Hafsat abar wannan tafiya har dasafe " har zata koma wata magana saiga Abban Hafsat yadawo daga masallaci.
Bayan ya shigo ya zauna sungama gaisheshi kana Mama tayi masa bayanin da Hafsat tamata,kuma tafa ɗamasa yadda tace da Hafsat.
Bayan ta gama yace, "aa bazamu hanamata zuwa ba, kuma kin san yanayi karatun da takeyi yana bukatar kula sosai dan haka tashi ga kuɗi kije kinji ƴar Abba".yana faɗa yana dubanta.
Sai Mama tace "kafison ta tafi"?.
Yace, "eh haka yafi abunda nakeso shine muyi mata fatar alhairi".
Bayan Abba yabata kuɗi ta ɗau kayan ta tayi musu sallama tafice.
Bayan fitarta Mama ta dube Abba kamar tayi kuka tace' "masa ita yanzu karatun Hafsat bata sonshi dan gabanta na yawan faɗuwa akan karatun Hafsat shiyasa yanzu bata da wata natsuwa akanta.
Sosai Abba yayi mata magana kan ta aje wannan maganar gyafe kwai suy mata fatar alhairi.
Tana fita takirashi tace ina yake gata tafito.
faɗa mata wurin yayi,taje tasa meshi.
Tana shiga motar shiko yaja suka tafi.
Ti-ti taga ya miƙe yana ta tafiya dan ba hanyar gidan sace yabi ba,dan haka ta juyo ta dube shi tace,
"Hayat naga sai miƙi ti-ti kakeyi hala ina zamuje?".
Batare daya dubetaba yace "Zamfara".
Tace, "Hayat yanzu da daren nan".
Yace, "eh yanzu nake da ra'ayi zuwa,inbazaki je ba na saukeki".
Tace, "aa kayi haƙuri in na ɓatama".
Bai sake ceda ita komai ba har suka isa Zamfara.
Hotel suka sauka ɗaki ɗaya ya kama musu,bayan sunyi wanka sunci abinci wasu kayan bacci ne ya bata ya umarce ta data sa,jikin ta narawa ta saka su,dasu da babu duk ɗaya suke ajikin ta.
Jikinsa ya jawota ya rungume ta haɗi da shaƙar ƙamshin jikin ta, lokaci ɗaya ya fara romance ɗinta.
Hannunsa yasa cikin rigar ta ya fara shafar duk wani ilahirin sassan jikin ta.
Sosai take jin daɗin abunda yake mata dan haka ta ba da kai sai yadda yayi da ita,sosai yabata wuya adaren, dan ba su suka kwanta ba sai biyu saura.
Kuma asuba nayi tafarka tayi sallah kana tazo ta kwanta.
Shima yana gama sallah ya kwanta haɗi da jawo ta jikin sa,romance ɗinta ya fara,duk da yanzu bata so saboda jiya ba ƙaramar wahala ya bata ba amma bazata iya ce masa bata soba,dan kar ransa ya ɓaci.
Sai bakwai da wani abu ya barta kushi ba dan ya gaji ba sai dan meeting ɗin da yake dashi 7:30.
Wanka yayi kana ya shirya yayi beak yayi mata sallama ya tafi yace sai ya dawo.
A dawo lafiya ta masa haɗi da addu'a,sai kace mijin ta😉.
Yana fita tayi wanka ta shirya tabi lafiyar gado dan bacci ne a idon ta sosai.
Haka suka cigaba da zama garin Zamfara har kwana biyar.
Zaune suke saman kujera ita dashi sai wayar ta tafara kaɗawa,har taso taƙi ɗauka kuma sai ta ɗauka,tana karawa kan kunnin ta ba abunda aka fara ce da ita sai, "kina ina?".
Sai Hafsat tace, "ina ruwanki da inda nake".
Sai Safiyya tace, "to wallahi bari kiji yau zuwa gobe na baki, duk inda kike ki dawo,kuma inba haka ba zanje gida na faɗamusu abunda akeci dan nagaji da ganin ki cikin wannan muguwar rayuwa." tana faɗar haka ta datse kiran saboda wani kukan baƙin ci dayazo mata.
Tana kuka tana faɗin "me Hafsat tanema tarasa da zata rinƙa bibiyarsa kamar mijinta".
Kuka tashiga rerawa sosai kamar ta cire zuciyar ta tajefar saboda baƙin ciki,kuma ba abunda yafi ƙuna mata rai gashi yanzu saura sati ɗaya afara exmas amma ita Hafsat ba itace gaban taba.
Tunda suka gama wayar da Safiyya jikin tane yayi sanyi sosai,kan ta taɗago ta dubeshi dan shima ita yake kallon kana ta buɗe baki tace, "Safiyya ce takirani,har tana yimin barazanar zata faɗima su Mama bana schoocl,kuma nasan tunda tace zata faɗa to sai ta tafaɗa,dan Allah kayi hakuri mukoma dan nasan halin Abba ko kasheni zai iyayi".
Tafaɗa haka hawaye na fita a idonta.
Haɗi fuska yayi haɗi dagoge mata hawayen dake fita a idonta kana yace,
Dan takiraki ta gaya miki haka shine harda wani tada hankali, aikinsa duk bazata faɗa ba saboda tana faɗa za'a dakatar da karatun ku, kuma ai zata fiki jin haushi tunda tafiki son karatun".haka yaci gaba da yi mata faɗa da daɗin baki ƙarshema ya umarce ta data kashe wayarta dan ko ankuma kira baza'a samuba.
Dan yace bazaiyi komaiba sai yagama aikin da ya kawoshi.
Tun daga lokacin Safiyya ko takira wayar Hafsat kashe take,sosai hankalin ta ya ƙara tashi dan har gidan sa taje amma mai gida yace yayi tafiya,gaba ɗaya ta rasa natsuwar ta har dai lokacin da Mamar Hafsat takirata tace takira wayar Hafsat kashe ko lafiya take?.
Tace eh karutu ne yayi mata yawa dan har sako tabani na faɗa muku to nima ban dawo ba saboda hostel nake kwana.
Aikuwa Mamar Hafsat najin tare da Safiyya suke ta samu natsuwa kana tayi musu fatan alhari.....
*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*©SUMY NA'IGE*✍🏼
[4/17, 22:07] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 6📑*
*__________📖* Bayan ya kammala abunda zai kaishi suka dawo gida da sati ɗaya taneme ya barta dan taje school dan Monday za su fara exams.
Yace ta shirya ya kai ta amma kafin ya dawo gida ta tabbatar da tadawo dan baya son yadawo babu abunda zaici.
School ɗin ya aje ta kana ya ƙarasa wurin aikin sa.
Class ɗin su taje bata jima da zuwa ba aka fara lectura.
2 dai-dai suka gama lectures ďinsu,kuma suna fitowa bata tsaya komai ba ta kama hanyar fita.
Har zata fita daga cikin makarantar sai Safiyya ta ganta tana ta sauri,da saura Safiyya tayi ƙarasa gare ta.
Mayafin ta ta riƙo,lokacin da take daf da fita school ɗin.
Safiyya tace, "ina zakije dakike ta wannan sauri haka?".
Kallon sama da ƙasa tayi mata kana tace, "wurin da kika aikeni zan je" tana faɗa tana hararar ta.
Sai Safiyya tace, "koma dai me yau ba inda zaki dan Mama na can hankalin ta tashe tana sun ganin ki dan haka yau gida zamuje ta gannki ko tasamu natsuwa".
Hafsat tace, "Safiyya har sau uku taki ra sunan ta, bana son kina shiga rayuwa ta Safiyya kirabu dani nayi rayuwata,ki barni rayuwar ki ko tawa? kuma bazan je gidan ba inki haihu da uwarki kije kifaɗa ɗin ina gidan saurayi na".
Tana faɗar haka ta kama hanyar fita ta bar Safiyya sake da baki tana kallon ikon Allah.
Har zata fice sai ta dawo,gaban Safiyya ta ƙarasu kana tace, "daga yau kada ki kara shiga rayuwa ta dan ni tunda jimawa nafitar dake rayuwa ta dan haka kema ki barni bana son sa idon".
Mai adai-daita ta tara kana ta faɗa masa unguwar da zai kaita.
ita ko Safiyya gaba ki ɗaya mamaki da tsoro sun da baibaye zuciyar ta,dan gani take kamar ba kai sake Hafsat ke gaya mata wannan maganar ba,amma a ko da yaushe tana wa Hafsat fatar shiriya itada kullihin musulmi.
Bayan ta dawo daga school wanka tayi kana ta gabatar da sallah sannan tazo ta fara gyaran gida,tana kammalawa ta ɗura sanwa.
Saura ƙiris ta kammala sai gashi yadawo,aikuwa tunda taji horn ɗin motar sa gaban ta ya bada dummmm,saboda bata kammala girgin taba kuma tasan halin sa sarai baya sun jira.
Tana cikin wannan tunani tafara jin knocking ɗinsa.
Da sauri taje ta buɗe masa ƙofa dan kar ta ƙara ma kanta wani laifi.
Ƙarɓar jakar dake hannun sa tayi haɗi dayi masa sannu da zuwa.
Karɓawa yayi haɗi da ƙarasuwa daga ciki.
Ruwan wanka ta haɗa masa,bayan yayi wanka ya fito, ta tayashi shiri,bayan ya kammala shirinsa parlour ya fito dan yaci abinci dan ya kwasu yunwa yau.
Komai bai gani ba a dinning, dan haka ya ƙwala mata kira,ita ko tana can tana sauri taga komai ya kammala amma ina dan tana cikin haka taji yana kiran ta.
Da hanzari tazo gareshi,aikuwa tunda ta ƙarasu ya jefeta da wani kallo wanda yasa cikin ta juyawa lokaci ɗaya.
Tambayar ta ya farayi yace, "ina abinci na?".
Jikin tane ya fara karkarwa tace, "kayi haƙuri nakusa kammalawa".
Sai da yajefe ta dawani kallo kana yace, "sai yanzu kika dawo kenan?".
Kai ta fara girgiza masa tace, "a'a muna gama lectures na dawo wallahi ko ina banje ba".
Tsawa ya da kamata haɗe da cewa karya kikeyi kin dai tsaya iskancin kine shiya sa baki dawo ba" nan ya dinga cin zarafin ta har da kukan ta tana bashi haƙuri amma yaƙi ko saurarin ta,daga ƙarshe ma key ɗin motar sa ya ɗauka yafi ce a gidan.
Har ya fita ya dawo ya ƙwala mata kira, da sauri tafito daga kiching haɗi da durƙusawa gaban sa.
Tun bata kai da durƙusawa ba yace ta haɗa kayan ta tabar masa gidan sa.
Aikuwa yana faɗar haka da sauri ta faɗa jikinsa tana bashi haƙura,amma ina baya ko saurarin ta dan da ƙarfi yajaye ta jikin sa ya kifeta da wani azaftaccin mari har guda biyu kana yace, "kuma wallahi kafin na dawo kinbar gidan nan tunda ba na ubanki neba" yana faɗar haka ya ficewar sa yana huci".
Kuka takeyi kamar ranta zaifita dan ita ba komai yafi ƙona mata raiba irin yadda yace tabar masa gida, to ina zata je?.
Wani tunani ya faɗu mata arai aikuwa da sauri ta miƙe daga durkushin da take ta koma kiching taci gaba da aikin ta.
Bayan ta kammala girki, sosai ta fara gyaran gida,bayan ta kammala tasaka turare mai ƙamshin gaske wanda lokaci ɗaya yasa gida yabada wani ƙamshi mai sanyaya zuciya.
Toilet taje tayi wanka,bayan ta fito ta shafe jikin ta da ma yukka masu ƙamshi haɗi da hummara ta musamman,dressing ɗin english wears tayi masa wanda tasan yafi so sosai.
Tana gamawa ta ɗauko wasu turarukka ta feshe jikin ta dasu.
Tarigi ya ta ɗauru alwala,sallah magarb da isha'i ta gabatar kana ta fito parlour ta zauna zaman dawowar sa.
Batayi minti biyar da zama ba sai ga horn ɗin motar sa.
Aikuwa da sauri ta ƙara feshi jikin ta da turare haɗi da dauko lollipop tasaka a baki, ta fara tsutsu sai kace wata ƴar yarinya.
Bai ma tsaya wani knocking ba yasa key ya buɗe ƙofar.
Tsaye ya ganta tana masa murmushi haɗi dayi masa wani kallo mai ciki da so da ƙauna.
Jikin sa tafaɗa haɗi da faɗin "My Hubby nah, sannu da zuwa".
Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi sauri ta haɗa bakin sa da nata tana shayar da shi lolopop ɗin da ke bakin sa.
Aikuwa tuni jikinsa ya karɓi saƙon da take bashi haɗi da shaƙar ƙamshin da ke fita a jikin ta.
Bare abu ga ma abuci son ƙamshi,sosai ta mantar dashi fushin da yakeyi da ita,tsayowar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta zowa bedroom ɗinshi.
Sai da komai ya lafa kana ya jawuta jikin sa sosai kana yafara magana ahankali yace, "My love jibi ne ta fiyar dan haka ki kasan ce cikin shiri dan tafiyar safe zamuyi".
Gabanta ne ya faɗi dan ita har ta manta da wata tafi ashe tafiyar na nan kuma gashi Monday za su fara exmas.
Jikin ta asanyaye tace, "Allah ya kaimu jibi lafiya".
"Ameen" yace da ita haɗi da kai bakin shi da nata ya fara kissing ɗin ta.
Duk abunda yake mata bata wani jin daɗin sa saboda tunda yayi maganar tafiyar jikin ta yayi sanyi dan tunani take anya zata bishi tabar exmas ɗinta?kum gashi aski yazo gaban goshi dan daf take da ta kammala degree ta afannin gaenacology kuma da bata ci wannan exmas ba zasu iya withdraw ďinta kuma gashi tana da carryover har guda biyu.
Suna cikin haka tace, "a'a gaskiya bazan jeba".
Ahankali yace, "mikika ce?".
Tace, "aa ba da kai naki ba".
*************
Yau takama Monday kuma yau zasuyi tafi kuma yau zasuyi exmas.....
Wani zatayi tafiya ko exmas......
*GASKIYA ZAN DAKATAR DA RUBUTA WANNAN BOOK, SABODA RASHIN COMMENT DA BAKUYI DAN HAKA NAKEYI MUKU FATAR ALHAIRI,AMMA IDAN KUN GYARA NIMA ZAN CIGABA DA RUBUTU AMMA IDAN BANGA GYARA BA TU KOWANIN MU YA HUTA😁*
[4/17, 22:07] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*TUKWICI*
*All gaskiya writers Fans*🥰
*Musamman gareki Maman Zee ƙaunarki gareni ba mai ƙarewa bace.*🥰💕💞
*SHAFI NA 8📑*
*__________📖* Cikin ikon Allah ya aje mata Question paper ya wucewarsa batare da yayi mata magana ba.
Aikuwa yana wuce ta ta fara yiwa Allah kirari a zuciyar ta haɗi da godiya a gare shi.
Tunda ga lokacin taci gaba da rubuta mata exams har suka kammala ba tare da ta samu wata matsala ba, sai dai gaba ki ɗaya ta dawo hostel da zama dan bata da lokacin komai sai na karatu, kuma tunda ta fara rubuta ma Hafsat jarabawa ba wanda ya gane ba Hafsat bace in ba ƙawar karatun Hafsat ba Naja'atu.
Sosai taba Safiyya gudunmuwa wajan ganin tayi ma Hafsat jarabawa, duk da ba department ɗaya suke da Safiyya ba amma tayi ƙoƙari sosai dan gabaki ɗaya ta hana ma kan ta barci ko da yaushe tana library wajan karatu, tayi nata tayi na Hafsat, har Allah ya nuna mata ta gama lafiya sosai tayi rama saboda rashin natsuwa da rashin isashen bacci.
Tunani ta farayi lokacin da suka gama exams yadda zata koma gida ba tare da Hafsat ba, dan haka ta yanke shawarar taje gidan sauranyin nata ta gani ko zata ganta,har zata je kuma ta fasa saboda ba ƙaramin baƙin cikin ganin sa takeyi ba dan haka ta yanke shawarar takira ta a waya.
Miss call kusan biyar tayi mata amma bata ɗauka ba sai ga na shidda kana ta ɗauka batare da tace komai ba.
Safiyya ba tadamu da rashin maganar taba dan haka tace, "kidawo dan ni zan koma gida kuma kin san da naje zasu tambaye ki dan haka gobe zan koma ko ki dawo ko kada ki dawo na dai faɗa miki".
Bata ma bari taji me zataceba ta tsinke wayar.
Ita ko Hafsat tunda suka sauka ya kama musu hotal bata sake koda leƙo ƙofa ba dan baya barin ta.
Kuma yanzu ko lafiya bata isheta ba dan yanzu bata da wani kuzari, ga wata rama da takeyi duk tabi ta bushe kuma tana cin abinci amma kamar bata ci, sosai abun ke bata tsoro dan ita gabaki ɗaya tunda sukayi tafiyar nan bata cikin kwanciyar hankali, abu kaɗan ya isheta kuka.
Yau ma kamar kullum suna kwance yana romance ɗin ta son ran shi, sosai yake jin daɗin abunda yake mata, ƙoƙarin shigar ta ya fara amma tana ɗan kaucewa, saboda yanzu ko kaɗan bata son abun da yake mata dan yanzu da ya gama abunda yakeyi da ita sai wani azaftaccin ciwon mara ya taso mata wanda kesa jikin ta kar-karwa lokaci ďaya.
Sosai take wahala kuma duk wannan uban ciwon marar dake taso mata ta gagara faɗa masa ya dena amfani da ita ko suje hospital a'a ita baza ta iya faɗa masa ba dan kar ransa ya ɓaci.
Duk da tana ƙoƙarin hanashi amma shi bai masan tanayi ba.
Ba ɓata lokaci ya afka cikin ta ya fara abunda yake so da ita son ranshi.
Aikuwa yana gamawa ya ɗan kwanta dan ya huta yaci gaba da abunda yake yi.
Ita ko yana sauka daga kanta, lokaci ɗaya wani abu ya taso mata ƙasan marar ta, tun tana dauriya kar ya gane har abu yazo yafi ƙarfin ta, lokaci ɗaya ta fara fita hayyacin ta, duban sa ya kai gare ta aikuwa lokaci ɗaya ya zabura ya mike zaune haɗi da tambayar ta, "lafiya mike damun ki"?.
Ita ko batama san yana yi ba saboda a lokacin bata masan inda kanta yake ba.
Abun yaga yafi ƙarfin sa dan haka da sauri ya saka jallabiya ya ɗauke ta domin suje hospital.
Cak ya ɗauke ta ya kai mota, rasa asibitin da zai kai ta yayi, dan dare yayi gashi kuma bawani sanin garin yayi ba.
Masu gadin hotel ɗin ya tambaya yace su nuna masa hospital mafi kusa? dan matar shi ce ba lafiya haɗi da nuna musu ita a cikin motar.
Wani private hospital dake kusa da hotel ɗin suka nuna mai godiya yayi musu kana yaja motar da gudu bai tsaya ko ina ba sai cikin hospital ɗin.
Cikin gaggawa Likitoci suka karɓe ta, lokaci ďaya suka fara bata taimako .
Sun jima kanta kafin su shawo kan lamarin.
Bayan komai ya ɗan lafa kuma ta samu barci dan haka suka fito daga ɗakin da take.
Yana ganin sun fito ya fara tambayar su ya jikin nata?.
Komai basu ce dashi ba sai babban doctor daga cikin su yace dashi "ka biyo mu office".
Komai bai ce dasu ba ya bi bayan su.
Bayan sun isa office dukan su suka zauna, kana suka nuna masa kujera domin ya zauna.
Bayan ya zauna sai babba daga cikin Likitocin yayi gyaran murya kana yace, "da farko dai munyi nasarar ceto matar ka dan yanzu haka ta samu bacci kuma insha Allahu ina har takiyaye ƙa'idojin da zamu ɗaura ta akai to babu shakka zata samu lafiya sosai da sosai.
Sai abu na biyu muna tayaka murnar matar ka na ɗauke da juna biyu har na tsawon wata huɗu....." aikuwa tun Doctor bai kai da ƙarasa maganar ba yace, "what haɗi da faɗin ciki!.
Gabaki ɗaya Likitocin kallon shi suka farayi cike da mamaki.
Dubin doctor yayi kana yace, "Doctor kun duba da kyau kuwa? dan ni matata bata da ciki gaskiya".
Results ďin scanning ďinta dake gaban sa ya bashi yace, "duba kagani".
Karɓa yayi ya fara dubawa, abunda yagani ne yayi matuƙar bashi mamaki da tsoro.
Yana gama dubawa sai ya ɗago da kansa yana kallan Doctor kana yace, "Doctor na gani kuma na yarda tana da ciki amma ina son a zubar da shi dan ba yanzu zamu haihu ba, ko nawane zan biya kawai a zubar da shi".
Tunda ya fara magana gaba ki ɗaya Likitocin suka zuba mishi ido suna kallon shi har ya kai ƙarshen zancen shi.
Sai da ya gama kana babba daga cikin Ƙikitocin yace, "kafin na gaya maka komai ina son kasan wani abu ɗaya, lokacin da kake ba matar ka ƙwayoyin hana ɗaukar ciki to kasani sosai sukayi mata illah a mahaifar ta, dan ikon Allah ne yasa wannan cikin ya shiga cikin mahaifar ta har ya zauna ya kai wannan lokacin ba tare da ya zube ba,sosai mukayi mamaki lokacin da muka ga yadda mahaifar ta take dan sanadiyar wannan magani da kake bata mahaifar ta tafara lalacewa sosai, dan ko da wannan cikin ya kai matakin haihuwa to na tabbata bazata iya haihuwa da kanta ba sai ammata aiki, dan haka yanzu idan kace a zubar da cikin to za'ayi ɗayan biyu, dan sanadiyar haka mahaifar ta zata iya lalacewa bazata ƙara ɗaukar ciki ba ko kuma wajan cireshi ta rasa ran ta, kaga ko baza kayi fatar ko ɗaya a cikin waɗan nan su samu matar kaba".
Sai da Anwar ya nisa kana ya dube Doctor yace, "Doctor kada kaji komai nasan haka bazata faru ba, kawai a cire shi dan bana son cikin".
Gabaki ɗaya Likitoci da ke office ɗin kallon sa sukeyi dan abunda ya faɗane ya basu mamaki.
Sai Doctor yace, "banƙi ta taka ba amma sai nayi magana da matar taka idan ta aminta acire to ba komai zamu cire amma idan bata aminta ba to gaskiya ba zamu cire ba saboda aikine mai wuyar gaske?".
Sai Anwar yace, "kada ka damu da matata dan nasan zata aminta dan haka kuyi aikin kawai".
Sai doctor yace, "a'a sai naji ta bakin ta".
Sai Anwar yace, "ba damuwa idan ta farka zaka iyayi mata bayani".
Doctor yace, "ba damuwa".
Bayan gari ya waye kusan ƙarfe goma Hafsat ta farka, kuma Alhamdlillah dan ta samu sauƙi sosai.
Bayan tayi wanka tayi break tasha magani Doctor yazo ya duba ta kuma yaga jikin da sauki dan ba wata matsala yanzu dan haka yace bari yakira sauran Likitocin.
Aikuwa yana fita Anwar ya ƙarasu gareta wani kallo ya jefa mata haɗi da yimata ya jiki.
Bayan ta ƙarɓa yace, "ni zaki munafur ta, ashe kin san kina da ciki amma kika ƙi sanar dani, to bani kika cuta ba kanki dan ni bazan aureki da ciki ba dan haka tun wuri kisan abunyi".
Da sauri ta ɗago da kanta ta kalleshi bakin ta na kar-karwa tace, "wani ciki, wallahi ni banda ciki kuma da'ace inada ciki da kai kanka zaka sani".
Wani kallo ya watsa mata haɗi da jefa mata wasu takardu yace, "duba kigani".
Jikinta na kar-karwa ta ɗauka ta fara dubawa aikuwa tana gama dubawa ta zabura haɗi da sanya hannu akai tace,"ciki gareni fah!.
Wasu hawaye suka fara bin kuncin ta haɗi da durkusawa ƙasa ta fara kuka mai tsoma zuciya.
Tsawa ya daka mata haɗi da faɗin tayi shuru zaiyi magana da ita.
Hannun ta ta ɗaura kan bakin ta kana tace, "na daina".
Yace, "abunda nake so dake idan Likitoci suka tambaye ki kin yarda azubar da cikin kice eh kin yarda, dan idan baki yarda ba to wallahi bazan aureki ba kuma sai dai kije kisamar masa uba amma ba niba".
Jikin ta na kar-karwa tace' "na yarda ko ma basu tambayeni ba na yarda kuma kayi hak'uri kada ka fasa aurena please".
Har zai sake magana sai ga Likitoci sun shigo ɗakin.
Ƙarasawa sukayi gaban gadon da take kwance, bayan sun gaisa sukayi mata ya jiki kana sukayi mata bayanin da sukayi ma Anwar har wanda yayi musu na azubar da ciki.
Bayan sun gama yimata bayani sai ɗaya daga cikin su ya dube ta yace, "kin amince azubar da cikin?".
Duƙar da kanta ƙasa tayi wasu hawaye masu zafi nabin kunci ta, tunani ta fara idan aka cire shikenan baza ta sake haihuwa ba kenan?ko ta rasa ranta, kuma yace bazai aureni da ciki ba to ya zanyi?.
Shurun da sukaji tayi ne yasa suka yi mata magana kallon su tayi da idon ta dasu ka sauya zuwa ja, sosai ta basu tausai dan haka suka ce da ita kin amince?".
Sai da ta rufe idon ta kana tace, "a'a ban amince ba".
Tun bata kai da rufe bakinta ba Anwar ya daka mata tsawar da tasa ƴan cikin ta kaɗawa.
Bai ma damu da Likitocin dake wajan ba yace, "me kika ce? baki amince ba?".
Jikinta na kar-karwa tace, "Hayat kayi haƙuri dan Allah ka taimaki rayuwata".
Har zaiyi magana sai ɗaya daga cikin Likitocin yace, "Malam bari kaji koda a ce ta aminta azubar da cikin tomu ba zamu zubar ba, dan mu ba aikin mu bane, idan kaga zaku iya zama har ta samu sauƙi to bazamu hanaka ba amma idan kaga baza ku iyaba to zaku iya ƙarawa gaba amma mudai bazamu zubar mata da ciki ba bare ciki har na wata huɗu".
.
Yace, "ko minti biyar baza muyi anan ba bare har na sa kuɗina taci gaba da kwanciya anan".
Kallon ta yayi yace, "ki tashi muje sai kije can ki haifar musu shi dan wallahi kar ma ki soma cewa nawa ne" yana faɗar haka ya kama hanyar fita batare da yaji mi zasu ce dashi ba.
Suma Likitocin fita sukayi har sun fita sai ɗaya daga cikin su ya dawo ya sameta sai kuka takeyi kamar ranta zai fita yace,
"Shawara zan baki duk yadda yaso kada ki yarda a zubar miki da ciki dan ke zai cutar, shi a kowane lokaci yake son haihuwa zai iya wani aure ya haihu amma ke shikenan baza ki saki haihuwa ba har abada, dan haka ki tashi kije yana jiranki " yana faɗar haka shima yafice daga ɗakin.
Sai da tayi kusan minti biyar kana ta tashi ta fara bin bango ta fita a ɗakin har ta kai wurin da motar sa take.
Tun bata ƙarasu wajan saba ya fara afka mata wata muguwar harara.
Motar ta buɗe ta shiga aikuwa tana shiga yaja motar da ƙarfi kamar zai tashi sama ya fice.
Suna isa hotel ɗin ko kallo bata ishe saba ya buɗe motar ya barta ba tare daya kalleta ba.
Haka tafito tana tafiya a hakali har ta isa ɗakin da suke.
Koda ta shigo yana toilet yana wanka wuri tasamu ta zauna, bata jima da zama ba ya fito yayi kamar bai san da zaman mutum a wurin ba.
Har ya gama shirin sa zai fita kana ya dube ta yace, "ki tattara naki da naki dan gobe zamu koma gida kuma wallahi ba zaki sauka gidana ba sai dai kije gidan ubanki" yana faɗin haka yafice warsa batari da ya tsaya yaji mi zata ceba.
Yana fita ta fara kuka mai ban tausai, tana cikin kukan ne Safiyya takira ta kuma abunda yasa tak'i magana dan kar taji tana kuka.
Haka ya barta har dare batare da ya sake wai-wayar taba.
Kuma babbar matsala duk baifi rashin ƙarfin jikin da bata dashi ba kuma ga yunwa ta dame ta dan tun safe rabun ta da abinci gashi yanzu dare yayi kuma har yanzu bai dawo ba.
Har barci ya fara ɗaukar ta sai gashi ya dawo, da sauri ta tashi dan a tunanin ta ko zata samu wani abun da zataci koda tea ne tasha.
Koda ya shigo sarai ya gan ta amma sai yayi kamar bai ganta ba har yaje toitel yayi wanka yazo ya kwanta, sai ta ƙaraso da sauri gareshi tace, "Hayat dan Allah ka taimakamin da ko ruwan tea ne wallahi yunwa nakeji?" tana faɗa kamar tayi kuka.
Kallo ma bata isheshi ba bare tasa ran zai ƙarɓa mata magana.
Data ga alamun bazata samuba dan haka ta zo ta kwanta.
Bata jima da kwanciya ba ya fara jawota jikin sa yana wasa da ita son rashi, ita ko tunda taga abunda yake son yi da ita ta fara masa kuka tana faɗin, "dan Allah kayi haƙuri ka barni wallahi banda lafiya kuma yunwa nakeji".
Yi yayi kamar bai jita ba haka yayi yadda yake so da ita kafin ya barta.
Sosai tayi kuka a wannan daren dan iya wahala ta wahala dan har ƙaramin suma sai da tayi, kuma tundaga lokacin bata koma barci ba har gari ya waye.......
0 comments:
Post a Comment