Nuni yayi mata da ta zauna saman cinyar sa,ba musu ko ta tashi ta zauna,tana zama ya sanya wata sassanyar ajiyar zuciya,sabida jin fatar shi da ta ta sun haɗu waje ɗaya,shi kansa ya san yana son Hafsat so ba nawasa ba amma a zahirin gaskiya ba za'aya auren ta ba duk son daya kemata,kuma ba dan komai ba sabida yariga da yasanta ƴa mace,kuma da ta yarda zata zubar da cikin wata ƙila ya yarda ya aure ta.
Jikinsa ya ƙara sanya ta, kana ya fara shaƙar ƙamshin dake fita jikinta, hannun sa ya kai saman sassan jikin ta ya fara shafar ta, lokaci ɗaya yaji wani sanye ya mamaye zuciyar sa,sosai yake son taraiya da Hafsat ba dan komai ba sai dan yadda yake samun natsuwa da ita sose.
Ita kowa tunda taji ta saman jikin sa wasu hawaye masu zafi suka fara fita a idon ta,uwa uba lokacin da ya ɗora hannusa saman jikin ta,jikin ta ne ya fara karkarwa sabida baƙin cikin ɗaura hannusa da yayi kuma ga ciyo da ke ɗawai niya da ita.
Bukinsa ya fara ƙoƙarin ɗaurawa saman nata, lokaci ɗaya ta fara ka-karin amai haɗi da sauka saman jikinsa, Wani baƙin ciki ne ya rufe shi bai san lokacin da ya kifeta da mari ba kana yace,
"Wallahi Hafsat muddin kina buƙatar kanki da lafiya kibi abinda nake so, dan wallahi ko aman jini ki kai sai nayi yarda nake so dake ko nayi miki abinda har ki mutu bazaki mantani ba,dan haka maza kije ki gyara jikin ki ki sameni bedroom yanzu nan".
Yana faɗa yana kama hanyar da zata sada shi bedroom.
Sanin halinsa da tayi dan haka ta tashi taje ta gyara jikin ta kana ta sameshi a bedroom ɗin sa.
Koda ta shiga ɗakin yana waya yana faɗin, "My love kin san na kusa dawowa kuwa?,dan haka ki fara shirin, dan kin san dana dawo ba jimawa za'ayi aure na dake".
Daya ke hands-free yasa dan haka tana jin dun abinda suke fada.
tace, "hmm My dear har kasa naji ƙunya".
Murmushi yayi kana yace, "kada ki damu ba jimawa zan cire wannan kunyar take dan ni tana cutar dani".
Mumushi tayi mai ɗan sauti kana tace, "yaushe zaka dawo inason na kasance cikin shiri?".
Yace,"a'a bazan faɗa ba akoda yaushe dai ki kasance cikin shiri kinji tawa".
Tace "to tace dashi".
Haka dai suka cigaba da waya cikin so da ƙaunar junan su.
Bayan sun kammala wayar ne ya kai duban sa ga Hafsat dake tsaye kamar wadda aka dasa kana yace, "kinyi min tsaye akai, ki ƙaraso mana".
Jikin ta a sanyaye ta ƙaraso gareshi,
Tana ƙarasowa ya jawuta jikinsa haɗi da sanya bakin sa cikin nata,to fah daga nan labari ya sauya.
Washe gari tunda safe Baban Safiyya yace suje ta gwada masa gidan Anwar,hijab ɗinta tasaka batare da tayi ko beark ba suka kama hanyar gidan Anwar.
Sunsha wuya kafin tagano gidan dan har za su juyo su dawo gida sai tagane gida,amma kuma ganin gidan da sukayi baiyi affani ba dan gidan kulle yake kuma koda suka tambaya akace mai gidan ya jima da barin garin.
Sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi na rashin ganin Hafsat,dan koda suka dawo gida ba inda ba suneme ta ba amma basu ganta ba,dan haka Baban Safiyya ya yanke shawarar yaje ya sanar da Baban Hafsat abinda ake ciki duk da yasan bai rasa jin ɓatan Hafsat a unguwa amma gwanda yaje ya ƙara sanar dashi koda ya sani.
Da yamma bayan ya dawo daga kasuwa ya shirya yaje wajan Baban Hafsat.
Koda yaje wajan Baban Hafsat,bayan sun gaisa kana Baban Safiyya ya faɗa masa abinda ke faruwa gami da ɓatan Hafsat.
Sai da Baban Hafsat ya numfasa kana yace, "Alhaji Aliyu to miyasa zaka tare ni da wannan magana bayan tun wancan lokaci na shaida maka na fitar da Hafsat daga cikin ƴaƴana,amma kuma yanzu kazomin da wannan zanci,dan haka bana son wannan zanci dan Allah daga yau kada ka ƙara haɗani da ita".
Har Baban Safiyya zaiyi magana sai Baban Hafsat yace, "a'a kada kasoma, kai kaji zaka iya riƙunta kuma yanzu tace bata so duniya take so tabi dan haka ka kyale ta ga duniyar nan ta ishe ta riga da wando".
Yana faɗar haka ya shigewar sa gida ransa a ɓace.
Haka baban Safiyya ya dawo gida jikinsa a sanyaye kamar ba lakka ajikinsa.
Haka dai suka canye kwana biyu suna neman ta amma basu ganta ba,daga baya sukayi haƙuri suka cigaba da addu'a Allah ya bayya nata.
Tunda sallah asuba da ta farka tayi wanka haɗi da ɗuru alwala tayi raka atanin fajar kana tayi sallah asuba,tajima zaune tana istigifari da hailala da addu'a nema tsari daga sharin mutum da aljan.
Bakwai saura ya farka haɗi da wata irin miki,gyafin da take ya kalla kana ya buɗa baki yace, "waya baki umarnin ki tashi daga nan ehh?".
Ko kanta bata ɗago daga ƙasa ba tace, "lokaci sallah ne ya bani umarnin tashi".
Aikuwa cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya ƙaraso gaban ta yana nunin ta da ɗan yatsa kana yace,"saki faɗin abinda kika ce?".
Irin yadda yake mata maganar ko ita ta tsora ta sosai dan haka bata ce komai ba taci gaba da lazumin ta amma gaban ta sai dukan uku-uku yake.
Magana yayi mata cikin tsawa yace taje ta haɗa masa beark,aikuwa ba musu ta tashi taje kitchen ta fara haɗa masa abinda yake so.
Tana tashi yabita da kallo haɗi dayi mata kwafa kana yace,"zanyi maganin ki,nan ba da jimawa ba".
Yana faɗin haka ya kama hanyar da zata sadashi da toilet.
Ita ko badan komai ta tashi tashiga kitchen ba sai dan kar ya hanata zowa makaranta.
Agurguje yayi wanka ya fito dan so yake yaje gun Hajara ta rakashi wajan malamin da yayi masa aiki akan Hafsat a wancan lokaci dan ko yanzu so yake ayi masa aki a kanta,dan yaga yanzu sai wata gardama take mishi idan yace tayi masa abu saɓanin da.
Koda ya zo parlour tana kitchen bata ƙarasa aiki ba dan haka ya sameta kitchen ɗin yace, "ya fita yadawo yanzu".
Bai jira cewar taba yafita yana ta sauri kamar wanda akayi ma kyata zata tsere masa.
Key yayi ma motar sa, kana ya kama hanyar da zata sada shi da layin buge,dai-dai kan kwanar gidan yayi packing ɗin motar sa.
Yana fitowa a mota ba abinda ya fara cin karo dashi ina ba condoms ba, tsaki yayi kana yace, "shiya bana sun zuwa wannan unguwar sabida haka".
Kwanar ya shiga,aikuwa yana shiga sai ga ƴan mata da samari sai fitowa suke cikin ɗakunan da suka kwana,wasu da alamu ma matan aure ne dan ga sunan har da goyon su,abin dai sai wanda yagani,yana ƙara tafiya sai yaga wata yarinya ita da wani saurayi za su shiga wani ɗaki, kuma daka ganta ita ƴar makaran tace dan ga kayan makaranta nan ajikin ta na secondary school, ɗaki suka buɗe suka shiga kana suka rufe ƙofa.
Gab da zai shiga ɗakin Hajara yaga wasu samari su biyu sai tunkuɗar wata yarinya suke suna faɗin, "wallahi yau sai kin bari muna ɗaki tunda ba ubanki ne ya bamu kuɗin da zamu biya ba".
Ita ko sai turjiya take wai ba inda zata je.
Da suka ga zata ɓata musu lokaci suka tisa ƙyayar ta gaba suna faɗin,"shigiya jarababba wallahi mungaji dake dan haka yau sai kin bar muna ɗakin mu".
Yarinya ta sosai dan idan ka ganta bazaka ce tasan wani abu ɗa namiji ba,tsaki yayi haɗi da ƙarasawa ɗakin Hajara.
Yana zuwa ba Knocking ba komai yatura ƙofar ɗakin ya shiga.
Cikin sa'a koda ya shiga ba kowa aciki dan ko ita tana toilet tana wanka,koshi dan yaji motsin ruwa ne ya tabbatar da haka.
Zama yayi sama katifar dake ya she a ɗakin yana jiran ta.
Bai jima da zaman ba sai gata tafito daga ita sai wani ƙaramin towel da bai rufe cinyar taba.
Bata ma lura dashi ba sai da yayi gyaran murya kana ta san da zaman sa.
Aikuwa suna haɗa ido dashi wani sanyi daɗi ne ya ziyarci zuciyar ta lokaci ɗaya,dan haka bata san lokacin da ta faɗa jikin sa ba.
Ƙoƙarin raba ta da jikinsa ya fara amma sai ya tuna da akin da zatayi masa dan haka ya kyale ta,jikin sa ta fara shafa duk da baya so amma abinda ya keson tayi masa ya hana ya dakatar da ita.
Ita ko da taga bai da katar da itaba yasa ta kai bakin ta zuwa nasa ta fara kissing ɗinsa,ba yadda ya iya haka yabiye mata har suka samu biyan buƙata kana ya jawo ta jikin sa haɗi da kai mata kiss a baki kana yace,
"My dear na,ina so ki kaini wajan malamin da ya taɓa yimin akin akan Hafsat".....ai tun bai rufe baki ba ta ɗago kanta da sauri ta dube isa kana tace,
" nifa bana sun kana min maganar ta dan a rayuwa ba ƴar da na tsana kamar ta".
Da ƙyar dai yasha kanta ta yarda zata kai shi amma sai laraba da ƙarfe uku na dare yazo su tafi dan lokaci ne ake zowa wajan malamin.
Yace, "to sai yazo".
Yana faɗa yatashi ya shiga toilet yayi wanka,jikin sa ta goge masa haɗi da tayashi sanya kayan sa.
Har mota tarakashi gab da zai shiga mota ya juyo ya kalle ta kana yace, "Hajara yanzu shikenan kin bar hostel kin dawo nan dazama ko".
murmushi tayi haɗi da faɗin,"sai mun haɗu ko".
tana faɗar haka ta wuce ta barsa batare da taji mi zai ce ba.
Key yayiwa motar sa kana ya dawo gida, koda ya shigo zaune ya same ta tashirya tana zaman jiran dawowar sa.
Kallon ta yayi yace, "ina beark yunwa nakeji". "yana dining". Tafaɗa haka ataƙaice.
Sai da tabari yagama beark tazo tace mishi makarnta take sun zuwa sabida lecture ne da ita ƙarfe goma.
Wani kallo yabita dashi kana yace, "bawani makaranta so dai kike ki tsere,amma kisani bana gudun ki gudu dan na san da kanki zaki dawo gareni, kana yace zaki iya tafiya".
Yana faɗin haka takama hanyar fati,har zata ɓuɗe ƙofa ya dakatar da ita yace ta bari yazo ya kaita da kansa kuma zai jiri da tagama abinda take ta dawo in kuma ba haka tasan sauran.
Ba musu ta tsaya har ya kammala abinda yake yazo ya kaita makaranta.
Da shigar ta school bata tsaya ko ina ba sai office ɗin shugaban makaran ta.
shugaban makartar ya bata wata takarda wadda akayi ma signing yace taje ta kaima iyayen ta su sa hannu,idan sun sa sai ta kawo dan wani sati za suwu ce abuja daga can kuma kowace a bata ƙasar da zata je karatu.
Bayan ta fito ɗakin shugaban makaran ta tashi ga class ɗinsu,bayan sun gama lecture tana sauri ta fito ne sai ta haɗu da ƙawar ta Maryam.
Hafsat bata ma ganta ba sai Maryam tace, "Hafsat ran jumu'a yaushe kika koma gida dan naga Safiyya sai nemanki take?".
Murmushi Hafsat ta ƙaƙalo kana tace,"tana fita niko na koma".
Sai Maryam tace, "gaskiya Hafsat Safiyya na son ki da yawa kinga yarda tabi tarikice kuwa".
Mumushi Hafsat tayi haɗi da cewa, "bari na wuce sai gobe idan na shigo".
Tana faɗar haka tafice batare da ta tsaya jin me zata ce ba.
Da sauri take tafi har tafita daga makarantar, bakin gate ta ganshi yana jiran ta dan haka bata tsaya komai ba tashiga motar sa suka wuce.
Tana wucewa Safiyya na fitowa daga class ɗinsu,Maryam tagani zata wuce hostel dan haka da sauri taje gare ta tayi mata magana.
Juyuwa Maryam tayi haɗi da yimata murmushi kana tace, "Safiyya Hafsat kike nema ne hala".
Sai tace,"eh wallahi har yanzu bamu ganta ba".
Tace, "yanzu fah naga Hafsat kuma tare muke har aka gama lecture".
Safiyya tace, "yanzu!".
Ta faɗa haɗi da zari ido.
Suna cikin wannan maganar sai ga ƙawar su Saratu tazo tace, "nima naga Hafsat yanzu bakin gate tashiga wata mota".
Wani baƙin ciki ne ya turnuƙata,tace kena Hafsat su ta rainama hankali tana gidan saurayin ta. Tayi wannan maganar a zuciyar ta.
Kallon su tayi tace, "oky nagode sai anjima".
Tana faɗar haka takama hanyar fita makaranta,sosai ran ta ya ɓace wato Hafsat suta mayar ƴan isaka wanɗanda basu da aikin yi, to daga yau ba mai koma shiga harkar ta inta iya ta tabbata tare dashi.
Gida ta koma dan ko lecture da zatayi bata tsayayi ba sabida ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba.
Cikin sa'a koda ta isa gida Baban ta bai fita ba,bayan ta zauna sai Mamar ta ce, "har kin dawo ne?".
Sai tace, "eh Mama". Sai ta kalle Baban ta da idon ta da sukayi ja-jir tace, "Baba Hafsat fa bata ɓata ba"......nan dai ta faɗa musu abinda tasani.
Ko Baban Safiyya ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba amma bai ce komai ba sai Allah kashirya.
Mama ko inda take fita ba nan take sauka ba kuma tace wallahi ko Hafsat tadawo baza ta zauna gidan ba.
Ko Yayan Safiyya shima yayi faɗa kamar ya shaƙo Safiyya tunda itace mafarin zuwan ta gidan.
Tunda Hafsat tashiga makaranta duk abinda take akan idon sa har maganar da sukayi da Maryam,abin da kwai bai sani ba shine shigar ta office ɗin shugaban makaranta.
haka ya dawo da ita gidan sa ba abinda take masa sai aikin bauta amma yana kai ta makaran ta tayi abin da zatayi ya mai data har akazo darin da za su je wajan malamin su shi da Hajara.
Tun shabiyun dare ya fara jin cikin sa na murɗawa har akazo lokacin da sukayi yazo sutafi,kuma lokacin ne ma cikin nasa ya fara yimasa wata murɗa wada yasa yafita haiya cinsa lokaci ɗaya.
Ita ko bata masan abinda ake ciki ba sai gab da asuba tana tashi ta ganshi cikin wannan halin sosai hankalin ta ya tashi dan haka cikin hanzari ta ɗauko wayar sa,kuma sai tara waza ta kira tunda bata san kowa nasa ba.
Har aka gama sallah asuba tarasa ya zatayi sai can ta tuna da akwai mai gadi gida,dan haka da gudu taje ta sanar da mai gadi abin da ke faru,aikuwa mai gadi na shiga cikin gidan ita ko ta lallaɓa ta ɗau kayan ta na makaran ta ta gudu.
Cikin sa'a tana fita tasamu dan acaɓa ta faɗa masa suna unguwar su suka kama hanya.....
*#Vote*
*Comment*
*Share*
*©SUMY NA'IGE.*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼.*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION*
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.
*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.
*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~
*SHAFI NA 17📑*
*__________*📃 Bakin ƙofar gidan tace ya sauke ta,kuɗi tabashi haɗi dayi masa godiya,dan ƙuɗin da ta bashi sunfi hakanan amma ya amsa baice da ita komai ba,gidan ta kaman hanyar shiga har takaɗa ƙafar ta ɗaya sai Yayan Safiyya Abbas yazo da sauri ya tare ƙofa haɗi da antayamata wani kallo kana yace,"wallahi ba inda zaki shiga dan ba gidan ubanki bane, sai da kika gama lalacinki zaki ɗauko wasu shegun ƙafafunki kice kizo gidan ubanki ko?, To barikiji tun wuri ki kama gabanki tun ban illatakiba".
Haƙuri ta fara bashi tace, "wallahi Yaya ba inda naje sune suka saceni"....tun bata rufe baki ba ya wanke ta da wani mari wanda yasa ƙiris kaɗan ta kai ƙasa.
Suna cikin haka sai ga Mama ta fito taga wake musu hayaniya bakin ƙofar gida.
Hafsat tagani tana ƙoƙarin tashigo shiko Abbas ya hanata shigowa,aikuwa da sauri Mama ta ƙarasa wurin tana kunfar baki tace, "wallahi baki isa kishigo gidannan ba,tunda ba ubanki ne ya gina munashi ba".
Roƙun Mama Hafsat tafariyi amma Mama taƙi koda saurarin ta,daga ƙarshe ma Mama komawa tayi gida ta ɗauko mata kayan ta ta jefomata su waja.
Mazan dake zaune bakin ƙofar gidane suka taso suna ba Mama haƙuri amma ko kallo basu ishetaba,kuma gashi Baban Safiyya bayanan yayi tafiya tun jiya,kuma Safiyya ma batanan jiya gidan gwaggon ta ta kwana.
Mutanin dake wajan da suka ga Mama taki haƙura ita da yaranta sai ɗaya daga cikinsu ya dube Hafsat kana yace,"kinga tunda sunce baziki shigar musu gidaba to kije ki koma gidan iyayenki zaifimiki".....tun bai rufe bakiba sai ga Ammar ƙanin ta yazo wajan,da sauri ya ƙarasa gareta yana faɗin,"Aunty daina kuka zo muje gida kinji,ai kema kinada gidan uba dan ba shegiya ceke ba".
Kai ta fara girgiza masa kana tace, "a'a Ammar kaji ne bazanje ba"....jikar kayanta ya ɗauka haɗi da jan hannunta yace dole sai sun tafi,ba yadda ta iya haka suka tafi gidansu.
Suna isa gidan har zasu shiga sai ga Baban ta ya fito domin ya tafi wajan aiki sai yayi arba da su,wani kallo yayiwa Ammar shida yake riƙi da hannuta da jikar ta kana yace, "wazan gani a gidana?, wallahi muddin kana son kankai da lafiya kabata kayan ta ta ɓacemin da gani".....tun bai rufe bakinsa ba ta durƙusa gabansa tana kuka tace,
"Baba dan Allah kayimin haƙuri wallahi ba lafina bane dan Allah Abba ka koma bani wata dama".....wata uwar tsawa ya daka mata wadda yasa ta haɗe sauran maganar da zata faɗa bata shirya ba.
Tswar da yayi ne yasa Ummar Hafsat fitowa bata shirya ba.
Hafsat tagani durƙushe da ƙasa ita da Ammar suna ba Baba haƙuri,da sauri ta ƙaraso garesu kana tace, "Hafsat lafiya waya taɓamin ke"....tsawa Abban Hafsat yayi mata haɗi da yimata nuni da ta koma cikin gida.
Gabansa tafaɗi tana kuka tana faɗi, "dan Allah Abban Hafsat ki barmin ƴata "......kallon da yayi mata ne haɗi da wata tswa wadda tasa ta komawa cikin gida bata shirya ba.
Yana ganin Ummar Hafsat ta koma gida yayi ma Ammar nuni da yashiga gida,ba musu ko yashiga ita ko Hafsat ya nuna mata hanya kana yace, "tunda duniya kike so to gaki gata".. ...yana faɗar haka ya maida ƙofar gida ya rufe yabar Hafsat durkushe da ƙasa tana kuka.
Tana ganin ya maida ƙofa ya rufe ta tashi ta haɗa kayan ta zata fara tafiya kenan sai taji zuciyar ta tafara ciyo,lokaci ɗaya mararta ta fara murɗawa amma duk da haka sauri take ta bar unguwar tasu.
tayi nisa kaɗan da unguwar ciyon mara yataso mata wannada bata taɓa jin irinsa ba kuma lokaci ɗaya ta gagara tafiya,wani waje ta samu domin ta zauna amma kafin ta ƙarasa ta faɗi,lokaci ɗaya jini ya fara bin ƙafafun ta kuma gashi hanyar mutane basu cika bintaba sai ɗai-ɗai ku.
Tanacikin wannan uwar wuyar sai ga wani mai napep ya fito cikin unguwar,tun bai ƙaraso wajan ba yaga mutum yashe aƙasa sai birgima yakeyi,har yasu yayi tafiyar sa sai kuma ya tsaya,jinin da yaga yana fita jikinta ne yasa ya ɗauke ta da sauri yasa cikin napep yashiga ya wuce hospital da ita.
Emergency room aka kaita,taimakon gaugawa suka bata kuma cikin ikon Allah sai gashi ta dawo cikin hayyacinta,kana sukayi mata allurar bacci.
Doctor ne yafito riƙi da ta kardar magani yaba wannan mai napep yace yaje ya sayo yanzu nan,ba musu ko yaje yasayo magani da ƴan kuɗin da yasamu yanzu da safe har ma da ragoyar najiya,aikuwa yana kai ma Doctor magani bai tsaya komai ba ya kama ga bansa.
Bayan doctor yasa mata ruwa da magani yafito dumin suyi magana da wannan mai napep amma bai ganshi ba,haka yayi tajira har yamma kuma bai dawo ba,kuma gashi anasun akaru wasu maganukkan da babu.
Har akayi magarb bai dawo ba,kuma lokacin ta farka da ƙarfin jiki sose,Nurses ɗin dake kula da sune taje tasanar da doctor farkawar ta,dan haka da sauri sai gashi yazo,kallon ta yayi kana yace,
Mike miki ciyo yanzu?".
Tace, "ba komai".
Yace, kin tabba ta". "Tace eh".
Wanda ya kawoki bai dawo ba har yanzu dan naso nayi masa bayani amma tunda bai dawo ba bari nayi miki bayani dan naga jikin naki da alamun sauki".
Mamaki ta farayi to waya kawo ta, gani kamar zata ɓata masa lokaci ne tace, "to inaji".
Yace, "da farko dai kiyi haƙuri dan cikin dake jikinki ya zobe.....ai tun bai rufe baki ba wasu hawaye suka fara bin kuncinta haɗi da jero ma Allah godiya cikin ranta.
Haƙuri ya ƙara bata ganin hawayen dake zuba a idonta sannan yace,"kuma kina yawan sa damuwa aranki,dan haka ki daina dan kina gab da kamuwa da ciyon zuciya".
A hankali ta ɓuɗe bakin ta kana tace, "insha Allahu zan daina".
Tambayar ta yayi tana jin unwa tace eh,Nurses yayiwa magana yace taje ta kawo mata tea da magani.
Bayan Doctor yafita ta kai dubanta ga kayanta dake kusa da ita,tashi tayi taje gun kayan ta duba kana taga komai akwai dan haka hamdala tayi kana taje toilet tayi wanka,tana fitowa sai ga Nurses tazo da tea da magani aikuwa tanasha ta ƙara jin ƙarfin jikinta sosai ba jimawa sai bacci yayi awun gaba da ita.
Ba ta farkaba sai da gari yawaye kuma koda Doctor ya dubata ba wata matsa dan haka ya rubata mata magani haɗi da bata kardar sallama.
Yana sallamar ta tashi tayi ta haɗa kayan ta tafice,mai napep ta tare ya kaita makaranta,bayan ta sallameshi ta ɗau kaya tawuce hostel,ɗakin ƙawar ta Naja'atu tashiga kuma koda taje bata sameta ba dan suna cikin makaranta,kayanta ta aje kana taje ta kwanta,bata jimaba da kwanciya ba bacci yayi aun gaba da ita.
Koda su Naja'atu suka dawo daga lecture bata farka ba sai kwasar bacci ta take.
Dubanta Naja'atu tayi sosai taga Hafsat ce kwance a gado,dan haka da sauri tashiga tashe ta,a hankali ta fara ɓuɗe idon ta ta sauke su kan Naja'atu da sauri Naja'atu tace,
"Hafsat dama kinshigo makaranta amma bakije office ɗin shugaban makaranta ba har anyi summiting ɗin takardun da akace iyaye suyi signing dan gobe ne za suje abuja,dan haka kitashi kiyi sauri ki kai kafin yafice daga makarantar".
A hankali Hafsat tace, "Naja'atu wallahi bazan iya zowa ba dan ban da lafiya,amma kiɓuɗa jikata ki ɗauka ki kaimasa".
Naja tace,"a'a bazaiyi nakai ba dan kinsan sai kinyi signing dan haka tashi narakaki muje".
Ba yadda ta iya haka ta tashi suka tafi office ɗin shugaban makaranta,cikin ikon Allah suka sameshi akayi duk abinda ake kana suka dawo hostel.
Bayan kwana biyu da faruwar haka jikinta ya warware sosai dan yanzu ba abinda bazata iyayi da kanta ba,kuma ba abinda ake sai shirye-shiryen tafiyar su.
Yadda Baba maigida ya same Anwar sosai hankalinsa yatashi dan haka yafito da gudunsa yaje wani gida maƙotansu ya kira wani maigadi ya kamamasa suka kaishi hospital....
*#Vote*
*Comment*
*Share*
*©SUMY NA'IGE.*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼.*
*SAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION*
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.
*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.
*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad@GaskiyaWritersAss.~
*SHAFI NA 18📑*
*__________*📃 Yasha wuya kafin a samu ciyon cikin ya lafa,sai da a kace musu ya samu bacci sannan Baba mai gida hankalinsa ya ɗan kwanta lokacin kuma ya tuna da yarinyar da tazo ta sanar dashi amma yanzu ba gantaba to ina take?.
Tunda Baba Safiyya ya shigo garin, kan hanyar sa ta zuwa gida wani maƙofcin sa ya taresa ya faɗa masa abinda matar sa da ɗiyansa suka wa Hafsat,sose ya nuna bacin ransa a kan haka dan haka bai tsaya wata-wata ba ya ƙarasa gida da sauri ransa a matuƙar ɓace.
Tun a suron gida yafara ƙwalama Mamar Safiyya kira yana faɗin, "Suwaiba! Suwaiba! Suwaiba!.
Gabanta ne yayi mutuƙar faɗuwa dan abu mai wuyane kesa Baban Safiyya yakira sunan ta,amsawa tayi jikinta a sanyaye.
Kallon da yayi matane yasa ta ƙarashiga tashin hankali kana ya buɗe baki yace, "an cemin Hafsat ta dawo amma kin koreta keda ɗiyanki, to bari kiji wallahi duk inda Hafsat take sai kin nemumin ita,muddin kina son kici gaba da zama gidan nan".....yana faɗin haka ya ficewar sa gidan ko takan maganar da take masa bai tsaya bi ba.
Sosai Hankalin Maman Safiyya ya tashi kuma lokaci ɗaya ta fara dana sanin abinda tayiwa Hafsat.
Ɗakin Safiyya tashiga ta faɗamata abinda a ke ciki kana tace, "Safiyya wai ina kika san Hafsat na zuwa?".
A hankali Safiyya ta buɗe baki tace, "wallahi Mama ban saniba , aikune kuka koreta da kunbari Baba yazo duk hukunci da yayanke ba shikenan ba amma kuce sai kun koreta,kuma ni ko makaranta na daina ganinta bare nasa ran zan ganta".
Sai da Mamar Safiyya ta shafe hawayen da suka zobu mata kana tace, "idan Allah ya kaimu gobe kiƙara dubumin makarantar ku, ko Allah nasa tana can".
Safiyya tace, "tau Mama Allah yasa a dace".
Tace "Ameen Safiyya".
Haka suka kwana Baban Safiyya na zuba musu masifa.
Ita ko Ummar Hafsat tunda Abban Hafsat ya umarceta da ta koma gida aikuwa tana shiga gida ta fara kuka mai cin rai,lokaci ɗaya ta fara tunanin ƴan uwanta da iyayenta, dan da tana tare da iyayen ta da bazaiyi mata haka ba, gashi yanzu ya rabata da iyayenta kuma yanzu ya rabata da ƴarta kwaya ɗaya tak, lokaci ɗaya ciyon zuciyar ta yatashi, cikin ƙanƙanin lokaci tafara fita hayyacin ta,aikuwa Abban Hafsat naganin haka ya hankalinsa yayi ƙololowar tashi,da sauri ya ɗauke ta yakai mota suka wuce hospital dan a lokacin sheɗarta tayi sama kamar zata fita.
Bayan kwana biyu da dawowar shugabanin makarantar su abuja aka aika kiran ɗaliban da za suyi wannan tafiyar,bayan kowa yazo aka bashi duk wani abinda zaya buƙata acan kana aka faɗama kowa ƙasar da zaije karatu,haɗi dayi musu nasiha mai ratsa zuciya, Hafsat ita da wasu maza huɗu su za suje India karatu haka dai akaraba kowane department namiji huɗu mace ɗaya, kowane da ƙasar da aka turashi.
Bayan angama rabamusu kayansu da wani abin affanin su kana akace kowa yaje yayi bankwana da iyayensa da ƴan uwansa da kwana uku ne suka ragemusu da su tafi, kuma ga rana ta uku za suwuce abuja dan daga canne za suyi tafiyar.
Bayan angama yi musu bayani kowa ya kama gabansa, wasu ma suna fitowa suka wuce gidan iyayensu, murna fil a zuciyar su.
Saɓanin Hafsat , dan inkowa na murna ita kuka take haɗi da fargaba, dan itakam ba wanda tasan zata je tayiwa ban kwana dan ba mai sonta dan ko iyayenta sun koreta bare ma wasu, haka ta koma hostel ciki da baƙin ciki da danasanin bin *UMARNIN SAURAYI* da kuma biyema Hajara.
Tana isa hostel ta faɗi kan gado tafara kuka kamar ranta zai fita, Naja'atu ba irin magiyar da batayi ba ta faɗa mata damuwar ta amma taƙi, daga baya data ga bata son faɗamata ta dawo rarrashin ta tana faɗin, "haba Hafsat keda yaka mata ki kasance cikin farin ciki amma gashi sai kuka kikeyi, ai Allah ya kamata kiyima godiya bakiyi ta kuka ba, ai duk gamu muna so amma Allah ke ya zaɓa dakije dan haka dan Allah kitashi ki daina kuka please".....haka dai tayi ta bata magana har tasamu ta daina kuka kuma daga baya sai ga zazzaɓi yarufe.
Bayan sun isa hospital likitoci suka dubata kana suka bata gado, sai da ta kwana sannan Ummar Hafsat ta farfaɗu, bayan likitoci sun ƙara dubata suka tabbatar da ciyon ya lafa kana suka ba Abban Hafsat izinin shiga ya ganta.
Koda ya shiga tana kwance kanta na kallon cilin alamu kamar tunani take, a hankali ya ƙaraso gab da gadon da take wance, ƙujerar dake wajan ya jawu ya zauna kana ya ɗura hannansa saman nata, sai a lokacin tasan da yashigo, dubansa tayi haɗi da fitar da kwalla kana tace, "Abban Hafsat, inason nayi maka wata magana wadda ban taɓa yimaka irin taba, dan haka bari kaji, da farko dai inason naje ga iyayena, na biyu kuma ina har kanaso nacigaba da zama da kai amatsayi mata to ba shakka sai ka nemumin ƴata wallahi ban zan iya jure rashin taba a halin da nake ciki, muddin kana so nacigaba da rayuwa sai kanemun ƴata......kukane ya kufuce mata lokaci ɗaya ta furta ashe haka iyaye keji idan ƴa-ƴansu sukayi nesa da su?".....tarine yaci ƙarfinta kuma gashi tana tari sai jini ya biyu baya, sosai hankalinsa ya tashi dan haka da gudun sa yaje ya ƙira doctor, koda Doctor yazo halin da yasame Ummar Hafsat baƙarimin tayar masa da hankali yayi ba, sauran ƴan uwansa likitoci ya kira suka zo dumin a ceto rayuwar ta.
Wannan karun Abba da yaransa gabaki ɗaya hankalinsu ya tashi aka rasa ma me rarrashi wani, su yaran sai kuka suke aka rasa wazai ba wani haƙuri a cikin su, lokaci ɗaya shima ya fara tuni ƴan uwansa.
Baban Safiyya ne ya hana kowa zama yace wallahi sai sun nemumi shi Hafsat kan su samu kwanciyar hankali, aikuwa haka suka je neman ta amma duk inda suke tunanin zata je bata jeba, sosai hankalin mamar Safiyya ya tashi da ita da yayan Safiyya dan Baban Safiyya yafi ganin laifinsu akan nakuwa.
Mamar Safiyya tace ma Safiyya taje makarantar su taga ko tana can, sai Safiyya tace bata can da yanzu weekend ne amma wata ƙila Monday tashiga.
Haka dai suka cigaba da nemanta cikin kwana biyu hankalin su tashe.
Anwar yanzu yasamu sauƙi dan har abinci ya kanci saɓanin lokacin da aka kawoshi, bayan ya dawo hankalinsa yake tambayar mai gida Hafsat, sai mai gida yace shi bai saki ganin taba tun lokacin da tafaɗimin baka da lafiya.
Hankalinsa ne ya tashi sose amma yayi alwashin da ya fita daga hospital duk inda take sai ya nemuta.
Tunda dare duk wani abin buƙata Hafsat ta haɗashi cikin ikon Allah da taimakon ƙawar ta Naja'atu dan yanzu Naja tasan waye Hafsat itama tasan waye Naja.
Tun ƙarfe huɗun dare ta tashi tayi wanka haɗi da shiryawa dan ita bata son ajirata kuma gashi antabbatar musu ƙarfe shidda na safe za su tashi zowa abuje dan ƙarfe goma jirginsu zai ɗaga.
Bayan tashirya suna zaune suna fira Naja'atu ta ɗako wasu kuɗi ta bata tace, "Hafsat, ga wannan canjin kiriƙi a hannuki kafin su baku kuɗi yana da kyau kirƙi koda kinga wani abu ko ace kasaya da kanka".
Kai Hafsat tafara girgiza mata kana tace, "dan Allah Naja kibarsu wallahi ko yanzu nagode da karmcin da ki kayimin dan Allah kibar kuɗinki dan nasan duk wani ɗan makaranta yana buƙatar kuɗi".....tun bata rufe bakin taba sai Naja tace,
"Nasan da haka amma duk baki karɓa ba bazan ji daɗi ba".
Ba yadda ta iya haka ta karɓi kuɗin haɗi dayimata godiya sose.
Suna zaune a ka kira sallah asuba dan haka suka tashi sukayi alwala suka gabatar da sallah.
Hospital koda Umma ta farka ba abinda take kira sai sunan Hafsat, Abba na cikin bacci yaji ta farka kuma da sunan Hafsat a bakin ta, doctor yaje ya faɗa masa farkawar ta.
Bayan doctor yazo ya ƙara dubata kana ya koma yimata allurar bacci kana ya dube Abba yace, "gaskiya yana da kyau kaje kanemu mai wannan sunan dan wallahi da gani tana buƙatar taga mai wannan sunan, kuma kodan matsalar ta ya kamata kanemuta dan mu kan
mu zamuji daɗin haka ".
Yana faɗan haka yafice daga ɗakin ya bar Abba da tunani.
Tunanin yaga bashine mafita ba dan haka yakira ɗansa Marwan yace yayi sauri yazo dan fita yake sunyi.
Ba ɓata lokaci sai ga Marwan yazo yana zuwa yayi masa sallama ya fice daga hospital hankali ta she.
Sai da ya fito ya fara tunanin ina zaije neman Hafsat, a nanne hankalinsa ya tashi saura kiris ya faɗi ƙasa a wannan lokacin.
Gidansu Safiyya ne ya faɗomi shi a rai, dan haka da sauri yayiwa mota kye ya tafin gidan nasu.
Yana isa gidan dai-dai Safiyya tafito domin taje makaranta neman Hsfsat,da jiya ba wanda ya runtsa a cikin su dan Baban ta yaki bari kowa ya runtsa sai masifa yake musu.
Tana ganin Abban Safiyya da sauri tazo gareshi ta fara gaidashi, bai ma karɓa ba ya jefumata tambaya yace,
"Safiyya ina Hafsat?".
Kasa karɓa masa tayi sai da yasake mai-mai tamata kana ta ɓuɗa baki idonta na fitar da kwalla kana tace, "muma itace muke nema yanzu ma haka school ɗinmu ce zanje na ƙara dubawa ko zan sameta".....tun bata rufe bakinta ba Abban Hafsat yace,
"Shigo mota mutafe ko Allah nasa mudace".
Tace, tom". Haɗi da buɗe mota tashiga.
Har zasu tafi sai ga yayan Safiyya yafito, ganisu dayayi ne yasa da gudunsa ya zo garesu, bai ma tsaya tambayar ina za su je ba ya buɗe mota yashiga kana suka kama hanya..
Tun shidda saura motocin da za su kaisu abuja suka ƙaraso, kuma ba ɓata lokaci duk waɗanda za su yi tafiyar suka zo kowa yashiga motarsu, kuma kowace mota namiji huɗu macce ɗaya.
Kowa ƴan uwansa suka rakoshi saɓanin Hafsat da ƙawarta ta rakota, lokacin da zata shiga motar jikin Naja ta laƙe sai rusar kuka take ba ƙau-ƙautawa, da ƙyar Naja ta rabata da jikinta tana bata haƙuri kana ta buɗe mata mota tashiga dan tafiya za suyi.
Har motoci za su fara tashi sai Hafsat ta buɗe jikarta ta dauko wata takarda taba Naja tace dan Allah kibawa Safiyya".
tana bata motoci suka fara tafiya.....
*Dan Allah kuyi haƙuri da wannan*
*#Vote*
*Comment*
*Share*
*©SUMY NA'IGE.*
[4/17, 22:08] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_
```🎐 G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGE✍🏼*•
*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.
*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.
*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
*SHAFI NA 19📑*
*__________*📖 Hawayen da suka zoba a idonta ne ta shafe haɗi da ɗaga musu hannu har suka fita daga makarantar, sose ta tausaya ma Hafsat wannan halin da takeci, ita dai fatar ta Allah yasa Hafsat suyi nasara a karatun da suka je.
Bayan kamar minti goma da tafiyar su, sai ga motar Abban Hafsat ta shigo hara bar makarantar cikin hanzari, suna shigowa Safiyya ta hango Naja zaune tayi tagumi kamar mai tunanin wani abu, tun Abban Hafsat baiyi packing ɗin mota ba tace,
"Abba bari naje ga ƙawarta can nasan wata ƙila tasan gun da take"....tun bata rufe baki ba yace, "je kisame ta Safiyya".
Da sauri ta ɓuɗe marfin mota tafito ta ƙarasa wajan da Naja'atu ke zaune tana tunanin Hafsat.
Sallama tayi mata haɗi da gaishe ta, Naja ta amsa mata haɗi da murmushi a fuskar ta kana tace, "Safiyya ke kuwa nake nema kuma gashi har sun wuce baku haɗu ba, amma tabani saƙo nabaki".....cikin hanzari Safiyya tace, "wace?"
Tana faɗa tana zare ido.
Jikin Naja a sanyaye tace, "Hafsat".
Jikin Safiyya na karkarwa tace, "ina taje Naja".
Ahankali ta ɓuɗi baki tace, "kin san ai tasamu scholarship na zuwa india karatu, to shine suka je yanzu ".
Ido ta zare kana tace, "Hafsat ta tafi kenan? ina zanganta Naja, dan Allah ki gayamin ina zan sameta, wallahi muna matuƙar buƙatar ta".....kuka ne ya kufuce mata sose wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar da zatayi.
Wajan da Abba yake shida Yaya Abbas suna hangota, dan haka da sauri suka ƙaraso gare ta suji mitake ma kuka.
Ko da suka ƙaraso tafaɗa jikin Naja sai rusar kuka take kamar ranta zai fita tana faɗin, "Naja dan Allah ki gayamin inda zangan ta".....Abban Safiyya ne da ya ƙaraso yace,
"Safiyya lafiya kike kuka? kodai ta ɓata ne?".
Baki ta buɗe tana son magana amma ta kasa sabida kukan da yaci ƙarfinta.
Naja ce tamasa bayanin abinda ake cike.
Ai tun bata kai da rufe bakinta ba, Abban Safiyya yayi magana cikin rawar murya yace, "wani airport za su shiga jirgi?".
"Na abuja". Tafaɗi haka ataƙaice.
Hankalinshi ne yayi ƙolo-lowar tashi, aikuwa ba shiri yakai zaune haɗi da dafe kansa, dana sani da baƙinci suka haɗe masa waje ɗaya, tunani ya fara to ina zai ganta? da sauri ya miƙe tsaye kamar wani zararre , duban sa ya kai ga Safiyya yace, "ta tashi mutafi" ba musu ta tashi sai famar rusa kuka takeyi.
Irin yadda Naja taga halin da Abban Hafsat ya shiga a wannan halin ne yasa hawayen da suka maƙale a idonta tun tashi su Hafsat suka zobo bata shirya ba.
Yana ƙarasawa wajan mota ya buɗi mota ya shiga, suma suka shiga dan shi Yayan Safiyya kasa magana yayi sabida bai san mi zai ceba.
Gida ya sauke su kana ya koma hospital, koda ya shiga ɗakin da Mama take lokacin ta farka, kuma sai sunan Hafsat take faɗa, gashi jininta ya hau kuma duk wani taimako da likitoci za su bata sun bata amma jinin yaƙi sauka dan ko bacci takasa samu sai sunan Hafsat da take kira.
Abinda ya gani ne lokacin da ya shiga ɗakin yayi matuƙar bashi tsoro, dan ƙirs kaɗan ya kai ƙasa, ɗayan likitan da yaga shigowar sa ne yayi masa magana yace,
Kazo da Hafsat ɗin ko?".
Abban Hafsat rasa bakin magana yayi,sai can da yaga likita ya tsare shi da ido kana ya buɗa baki yace, "gatanan zuwa, amma bari² na kirata"..... Yana faɗin haka ya fice bai ma tsaya jin mi likita zai ce ba.
Yana fita daga ɗakin yaga Ammar zaune yayi ta gumi yana tunani, sunan sa ya kira kana yace, "Ammar ba tunani ya dace kayi ba, addu'a ita tafi dacewa da ita, dan haka ga kuɗi ka riƙe ko za su buƙaci wani abu kasayu, dan ni yanzu wanuri zanje na dawo, amma kar kaga najima ban dawo ba dan zanje wani wuri mai ɗan nisa".
Yace, "tau Abba Allah ya dawo da kai lafiya".
Yace, Ameen".....kana ya fice daga hospital ɗin cikin sauri.
Mai napep ya tsayar ya faɗa masa wurin da zai kaish, ba ɓata lokaci ya isa ta shar mota, kuma koda yaje motar abuja saura mutum biyu ta ciki, dan haka yace sutafi shi zai biya kuɗin ɗayan, ba ɓata lokaci suka ɗau hanyar abuji ciki yake da fargabar Allah kasa ya ganta.
*****
Hajara ce tafito cikin shiryan ta cikin wasu ƙananun kaya musu bayyanar da surar jikin mutum sose, iya kyau tayi, sai da kashiii, idan ka ganta bazaka ɗauka ƴar musulmi bace, tafiya takeyi kan titi sai can ta tsayar da mai napep ta faɗa masa wurin da zai kaita kana tashiga, basu tsaya da ita ko ina ba sai hospital ɗin da aka kwantar da Anwar.
Bayan ta sallame shi taƙarasa cikin ɗakin da aka kwantar da shi, tana wata tafiya kamar bata son taka ƙasa.
Ahankali ta tura ƙufar ɗakin da yake kwance tashiga, kwanci ta tarar dashi yana baccin sa cikin kwanciyar hankali, dan idan ka ganshi zaka zata lifiyar sa ƙalau.
Kamar anshigo ɗakin yaji, dan haka da sauri ya buɗi idonsa, Hajara yagani, itako tana ganin ya farka da sauri ta ƙaraso gareshi tana faɗin,
"Gaskiya kaji sauƙi sose "....tana faɗa tana sakar masa da murmushi haɗi da kai hannuta saman nasa.
Sai da yagama yimata wani kallo kana yace, "eh naji sauƙi, dan yau ma nake son su sallameni naje gida dan so nake muje kikaini wajan Malamin da kikace".
Tace, "to kama daina wahalal da kanka da wadda kake danta ta bar ƙasar gabaki ɗaya".
Tun bata rufe baki ba ya ɗago kansa da sauri yace,"wace kenan!.
Yafaɗi haka cikin razana.
"Hafsat". tace dashi ataƙai ce.
Ido ya zare haɗi da cakomuta kana yace, "ina kika kamin ita?".
Dariya ta sanya masa kana tace, "scholarship tasamu, yanzun nan ba jimawa motocin makaranta suka ɗauke su zuwa airport ɗin abuja dan acan ne za su tashi.
Ai tun bata rufe bakin ta ba ya ɗauko waya yakira wata number, ana ɗauka yace, "Salim zai samu jirgin da zai kaini abuja yanzu?".
Bansan mi akace dashi aɗayan ɓangarin ba yace, "oky ganin zuwa yanzu".
Ko kallon ta baiyi ba ya ɗau kayansa ya bar hospital ɗin, batari da an sallame shiba.
Har zai fita tayi sauri taci gabansa tace, "ina zakaje ne?".
Ko kallon ta baiyi ba ya ture ta gyafe ɗaya ya fice warsa.
Bayan shi ta biyu tana kiran sunanshi, yana jinta amma yayi kamar bai jiba.
Haka har yazo kan ti-ti ya tsayar da mai napep ya shiga tana kallo amma batayi gi-gin magana ba dan taga yau ba sauƙi, filn jirgi ya kashi, kuma yana sauka ba ɓata lokaci jiringin nasu ya ɗaga.
Tunda suka shiga motar ta haɗe kanta da ƙafafunta sai famar rusar kuka takeyi kamar wadda za'a raba da ranta.
Ko waɗan da suke tare a motar ba wanda bai mata magana ba, har dai suka gaji suka kyaleta, tana kuka haka dai har bacci ya ɗauke ta.
Cikin ikon Allah tara da rabi suka isa airport ďin Abuja, kuma koda suka ƙaraso ba ɓata lokaci suka shiga jirigi suka wuce India.
Minti talatin da ta fiyarsu sai ga Anwar ya dira garin abuja kuma aka tabbatar masa da basu jima da tashi ba.
Wata ƙara yasaka sabida wani bakin cikin da ya rufeshi, rasama abinyi yayi, sai can ya ciji yatsa kana yace,
"wallahi ko ƙarshin duniya kika kai Hafsat sai na nemuki, bari makarantar india".
Awa ɗaya da tafiyar su Hafsat sai ga Abbanta ya shigo garin abuja, ba ɓata lokaci yasa aka kawoshi airport ɗin garin, tambaya yayi ko jirigin india ya ɗaga aikuwa aka tabbatar masa da ya ɗaga nan da awa ɗaya da suka wuce.
Aikuwa ba shiri sai ga hawayen baƙin ciki sun fara zoba a idonsa, lokaci ɗaya ya fara rawar sanyi, kuma lokaci ɗaya ya hango halin da matar sa take ciki, ba shiri ya samu waje ya zauna haɗi da dafe kansa.....
0 comments:
Post a Comment