Yana gama shiri yafito dumin su tafi dan baya sun suyi rana.
Kiran ta ya farayi,ita ko tana can tana tunani ta tafi ko karta tafi,rasa me zatayi tayi,gashi tana tsoro rashin yin exmas ɗinta, kuma tana tsoron ɓacin ransa.
Kiran da taji yana mata yasa gabanta dukan uku-uku,alamun zai shigo ɗaki data ke ciki taji dan haka da sauri ta fara haɗa kayan ta cikin jikar da zata tafi da ita.
Koda ya shigo har tasa tufafin ta tana yafa mayafin ta,amma fuskar ta a ɗaure kamar tayi kuka.
Magana yayi mata yace, "kefa nake jira".
Tace,"nashirya mutafi" tafaɗa haka kamar tayi kuka.
Fitowa tayi ɗauke da jika a hannunta,jikin ta a sanyaye ta rasa ya zatayi,tana cikin haka taji yace, "muje zan kulle ƙofa".
Fita tayi ya kulle ƙofa kana ya shiga mota ya tada.
Gabanta ne ya tsanan ta faɗuwa sosai, lokaci ɗaya wasu hawaye suka fara fita a idon ta.
Magana yayi mata yace ta shigo sutafi.
Kamar bata ji shiba tayi sai da yayi magana cikin faɗa-faɗa kana tabuɗe motar tashiga tana mai saka kuka kamar wani yayi mata dole sai taje😏.
Aikuwa yana tada mota kukan da takeyi ya tsanan ta.
Dubanta yayi kana yace, "mi akayi miki da zaki saka min kuka,ko tafiyar ce bazakiyi ba ne?".
Kanta ta fara girgiza masa kana tace, "a'a kayi haƙuri na daina".
Yace, "to ki shafe hawayin ki dan bana son jin kuka kinji ko".
Hawayen ta tashafe haɗi da cemasa "to".
Tunda suka kama hanyar tafiya gaba kiɗaya hankalin ta atashe yake, dan tunda take dashi bata taɓa jin irin wannan tashi hankali ba kamar na yau,amma kuma bazata iya ce masa baza ta jeba,har suka fara fita daga cikin gari ba wanda ya cema ɗan uwansa komai.
Saura minti biyar afara exmas sai Safiyya tazo bakin class ɗinsu taga ko Hafsat tazo,aikuwa tana ƙarasuwa taga class ďin kowa yazo amma sit ɗin Hafsat wayam,gaban Safiyya ne ya bada dummm da sauri tashigo class ɗin.
Wata abukiyar karatun Hafsat, Naja'atu ta tambaya tace, ina Hafsat?".
Sai Naja'atu tace, "ai Hafsat ta daina zowa school dan tun dawo wa hutu sau biyu ta shigo class,kinga ma exam card ɗinta yanzu haka ita nake jira".
Safiyya tace, "bata da lafiya,amma nasan yanzu zata zo,bani card ɗin nabata dan sauran kayan ta ma na hannuna".
Ba musu Naja'atu ta bata.
Aikuwa tana ƙarɓa da sauri ta fito ta kama hanyar hostel,tana zowa tasumu arun niƙaf tasa afuskar ta ta dake ma ran,ta tashiga class ɗin haɗe da addu'oi Allah kasa kada agane ba Hafsat ce ba.
gaban ta na duka uku-uku haka taje ta zauna saman sit ɗin Hafsat batari da tawa kowa magana ba.
Ko minti biyu batayi da zama ba aka fara raba Question paper.
Ana kawo wa gaban ta,gabanta ya bada dummmm,addu'a takeyi Allah kasa kada ace sai ta ciri niƙaf ɗin da ta sanya.....
*To fah Safiyya kin iya ganganci*🤔
*# Vote*
*Comment*
*Shere*
*©SUMY NAIGE.*
[4/17, 22:07] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 9📑*
*__________📖* Bayan ta idar da sallah asuba tajima kafin ta ta shi sabida ko da ta tashi faɗuwa zatayi dan bata da wani kuzari a jikin ta.
Tana kan sallaya yatashi yaje yayi wanka kana yayi sallah,bearkfast yaje ya karɓo musu,yana dawo ya kai duban shi gareta kaifin yayimata magana ita tafara gaisheshi ciki da ladabi.
bai ma karɓa ba yace, "kizo kiyi bearkfast dan yanzu nakeson mu kama hanya kuma idan kika tsaya wasa sai na barka" yana faɗa yana antaya mata harara.
Ahankali ta tashi kayan da yanuna mata na beark su ta ɗauka ta haɗa tea ta farashi,sosai taci kayan da ya kawo mata,sai da taji ta ƙoshi kana ta tashi taje toilte tayi wanka.
tana cikin shiri sai gashi ya fito cikin shirinsa na tafiya,ko kallon ta baiyi ba ya kama hanyar fita.
Ɗakin da taga yana ƙoƙarin rufewa yasa da sauri ta ɗauko kayan ta tafito waje ta karasa yafa mayafin ta.
Key yakai ma masu hotel ɗin kana yazo ya ɓuɗe mota ya shiga itama tashi kana suka kama hanyar garin sokoto.
Tafiya sukeyi amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai har sukayi nisa sosai.
Wayar Hafsat ce tafara ruri dan haka ta ɗauko ta duba wake kiran ta.
Safiyya taga ya bayyana dan haka taja tsaki kana ta ɗauka.
Safiyya tace, "Hafsat kina ina wallahi yau zan koma gida kuma kinsa zasu dameni da tambayar ki dan Allah kidawo mutafi tare".
Sai da ta kai ƙarshen zancin Hafsta tace, "wai Safiyya ke waci iri ce,nace kirabu dani kinƙi to bazanje gidan ba kije kifaɗa kinji koma bari kiji kada kisaki kirana sabida ba ajiya kika bani ba ehe" tana gayamata haka ta tsinki kiran.
Duk abunda takeyi yana kallon ta amma yayi kamar baisan tanayi ba.
Haka suka cigaba da tafiya har suka shiga garin sokoto.
Suna kawowa Flyover
yayi packing ďin motor sa yace, "ki sauka dan ni zan wuce".
"Haba Hayat kayi haƙuri muje gidan ka idan na ɗan huta zuwa ajima sai naje gida".
Wata tsawa ya daka mata wandda tasa tafice daga motar bata shiyar ba.
Har zai tada motar tace,"Hayat bani da kuɗin da zan ƙarasa gida kuma bazan iya ƙarasawa da ƙafa ba gashi kuma dare yayi".
Ko kallon ta bayi ba yaja motar sa yabar ta tsaye a hanya.
Hawayen da kifita a idonta ta goge kana ta ɗau jikar ta tafara tafiya kan ti-ti.
Mai napep ta tsayar dashi, ta faɗa masa sunan unguwar da zai kaita.
Bai tsaya da ita ko ina ba sai ƙofar gidan su.
Fita tayi tace dashi zata shiga ta karɓo masa kuɗi yace to.
Sallam tayi ta shigo cikin gidan,aikuwa ƙannin ta najin muryar ta suka fara yimata oyoyo kamar zasu kayar da ita gashi ba wani ƙarfin jiki ne da itaba.
Da ƙyar tasamu suka saketa,ita ko Mama tunda taji suna oyoyo tasan ƴar ɗiyar tace ta dawo dan haka da sauri tafito waje sabida ta ganta.
Gaban tane yayi muguwar faɗuwa lokacin da taga Hafsat,dan gabaki daya ta rame tayi fari sosai.
Har zata tambaye su Mama sai suka haɗa ido da ita,murmushi Hafsat ta ƙaƙalo tace, "Mama ya nasameku?".
Bata karɓa ba dan kallon ta takeyi sosai dan kamar tana son ta kartu wani abu,sai Hafsat ta katsa mata tunani tace, "Mama nafa tsayar da mai napep ban bashi kuɗi ba".
Sai Mama tace, "dole na kifeki da ido wannan ubar ramar da fari da kikayi Hafsat, lafiya kike kuwa?".
Tace, "Mama bari na sallame mai napep nazo".
Tambayar ta kuɗin sa tayi ta faɗa mata sai Mama tabaiwa ƙaninta Ammar ya kai masa.
Sai Mama tace, "kinyi tsaye ki ƙaraso daga ciki".
Parlour Mama ta shiga ta zauna Mama tace,"Hafsat mike damunki ki kayi wannan ramar haka?".
Sai da ta ƙaƙalo murmushi tace, "Mama wahalar exams ce ta ramar dani" tana faɗa tana yin ƙasa da kanta.
Sai Mama tace, "a'a Hafsat da alamu akwai ramar zazzaɓi aciki".
Tace, "eh Mama dan jiya ma naje hospital suka rubutumin magani kin gama tagarda maganin" tana faɗan haka tana buɗe zip ɗin jikar ta ta ɗauko mata tagardar maganin da aka rubuta mata a can hospital ɗin da ya kaita dan cewa yayi tunda bata yarda azubar da cikiba to ko magani ba zai saya ba.
Ɗaukowa tayi taba Mama itako Mama takira Marwan tace yaje pharmacy ɗin Baban shi ya karɓo magani.
Karɓa yayi yaje itako Mama tace Hafsat ta koma ɗakin ta tayi wanka tayi sallah tazo taci abinci ta sha magani.
Tashi tayi taje ɗakin ta, tana shga kafin tayi komai wayar ta ta dauko ta fara kiran Anwar.
Kusan missed call biyar tamasa amma bai ɗaga ba daga ƙarshe ma kashe wayar sa yayi gabaki ɗaya.
Sai da taji yakashi wayar kana ta tashi taje tayi wanka tayi sallah magarib da isha'i.
Tana idar da sallah Marwan ya shigo ya kawo mata magani da abinci.
Bayan ta ci abinci tasha magani ta koma ɗauko waya ta ƙara kira ko ya ɓuɗi?.
Amma har yanzu kashe take,tunani tafarayi ko taje gidan sa dan gabaki ɗaya batada natsuwa dan ita kanta tasan ko tana samun natsuwa sai ta ganshi,kuma tasan Mama baza ta barta tafita ba.
Tana cikin wannan tunani barci ya fara ɗaukarta saboda maganin da tasha har da na barci akwai.
Ko da babanta ya dawo daga masallaci har barci yayi awongaba da ita dan ko da Mama ta aiki Marwan ya kirata ta yi bacci sai babanta yace ka da a tasheta abarta sai da safe sai su gaisa.
Ko da gari yawaye Mama taje ɗakin ta dan ta ƙira ta, amma sai ta tarar har yanzu bacci takeyi bata tashi ba, abin ya ba Mama mamaki dataga har rana takusa fitowa Hafsat bata tashi ba sabod tasan ba halin taba ne baccin asubah.
Tayar da ita ta farayi tana kiran Hafsat tashi kiyi sallah rana tayi, miƙa ta farayi alamun zata tashi Sai ta fara magana cikin muryar bacci tace,
" Mama rana ta fara fitowa?".
"Eh Ki tashi ga Abbanki can yana jiranki ku gaisa saboda yanzu fita zaiyi,Tashi tayi ta nufi toilat Cikin hanzari tayi wanka sannan ta daura Arwala.
Itako Mama tana ganin ta tashi ta shiga toilat sai ta fice daga dakin
Koda tafito bata tarar da Mama ba dan haka ta gabatar da sallah kana ta shirya tafito taje ta gaishe da Abbanta.
Da sallama ta shiga parlour,bayan sun ƙarɓa mata ta ƙarasu gaban Abban nata wanda tun shigowar ta yake kallon ta ciki da so da ƙaunar ƴar tasa.
Bayan ta gaisheshi ya karɓa kana yace,
"Hafsat ashe har ciyo kikayi?Allah ya ƙara sauki kuma kiriƙa shan magani muga kwana biyu abunda Allah zaiyi".
Ya ƙara da faɗin "ya exmas dafatar kun kammala lafiya?".
Tace, "eh Abba munga sai dai muna baran addu'a".
Sosai yayi musu addu'ar samun nasara ita da Safiyya kana yayi musu sallama yafita wajan aiki.
*********
Bayan kwana biyu da dawowar ta tasamu sauƙi sosai dan har cikowa ta farayi bakamar lokacin da tadawo ba.
Kuma tundaga ranar da ya sauke ta bai saki nemantaba kuma bai saki ɗaukar wayar taba dan ko takira ba zai ɗauka ba shiyasa gabiki ɗaya bata cikin natsuwa dan yanzu burin ta taganta tari dashi dan haka taje tagayawa Mama zataje gidan ƙawar ta ta dubata sabida batada lafiya,da kyar tasamu Mama tabarta amma tace kada tajima.
Wanka tayi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗikin rika da sikt ne sosai suka karɓe ta tayi kyau abunta har ta ɗauko turare tasa jikinta sai ta tuna Mama bazata barta tafitaba idan tasa dan haka ta saka shi ajika ta har sai tazo gidan sa haɗi da wani mitsi-tsin gyale.
Babban hijab tasaka ajikin ta kana ta fito tanufe ɗakin Mama.
Da Sallama tashiga tace, "Mama zan tafi".
Kuɗi napep Mama tabata haɗi da ƙara faɗamta karta jima.
Karɓa tayi haɗi da faɗi, "bazan jimaba" kana taficewar ta.
Tana fita ti-ti ta tsayar da napep,sunan unguwar da zai kata tagayamasa, shiga tayi yaja suka tafi.
Basu tsaya ko inaba sai bakin gidan sa.
Bayan ta sallame mai napep ta ƙarasu bakin gate ɗin gidan ta fara knocking,bata jima tana knocking ba mai-gadi ya leƙo yaga wanene?aikuwa yana ganin ta yayi sauri ya buɗe mata ƙofa haɗi da gaisheta.
bayan ta ƙarɓa take tambayar sa ko Anwar nanan?.
Yace "eh yana ciki".
Part ɗinsa ta ƙarasa , kafin ta isa ga part ɗinsa ta buɗe jikarta ta ɗauko turare tafeshi jikinta dashi kana taciri hijab ta sanya wannan mitsi-tsin gyale wanda dashi da babu duk ɗaya.
Ƙofar da zata sadata da falon shi tashiga kai tsaya.
Ahankali take tafi har takawo gab dashi yana zaune yana kallon labaru bai masan ta shigo ba.
Ƙamshin turarin da yabige hancin sane yasa ya dago kasa,aikuwa suna haɗa ido dashi ta fara sakar masa murmushi mai ciki da nuna tsan-tsar so da ƙauna.
Har yaso ya ƙoreta amma yadda yaga ta ƙara kyau kuma ga ko ina nata ya ciko musammam abunda yakeso wato dukiyar fulani.
Irin kallon da yake matane yasa tafara tafiya ɗaya-ɗaya har ta ƙaraso gareshi.
Ahankali tazo ta zauna saman cinyarsa haɗi da kai masa kiss abaki tare da faďin,"I miss you so much My Hayat".
Aikuwa yana jin bakinta cikin nashi lokaci ďaya yaji wata Sha'awa tabi jirumasa bai san lokaci da yafara kissing ďinta ba.
Hannunsa yasa cikin rikar ta yafara shafar duk wani ilahirin jikin ta,musammam abu sonshi sosai yake matsarsu itako sai ƙara narke masa takeyi ajiki tana wani nishi ɗaya-ɗaya.
Cak ya ɗauke ta yayi bedroom ɗinshi da ita,kayan jikin ta yacire mata kana yacire nasa romance ɗin ta yafara cikin zafin nama kana yashiga aiki,sosai yabata wuya dan har wani abu taji ya tsaya mata amara amma bazata iya cewa ya daina ba.
Sai da yagaji dan kansa kana ya sauka daga gareta ciki da samun gamsuwa danshi yake masifar sonta,sosai yake samun natsuwa gareta.
Itako yana gamawa ta gagara tashi dan gabiki ɗaya marar ta ta ƙulle, gawani ciyon da takeji a ƙasan ta.
Shi bai masan tanayi ba,janyota jikinsa yayi yafara baccin hutu itako ta jima kafin taji dama-dama,daga baya bacci yayi awun gaba da ita.
Sai kusan ƙarfe shidda yabar ta ta koma gida koshi saida taga neman halakata yake ta sanya masa kuka da kyar ya barta tatafi gida.
Shiko duk abunda yake mata da gayyane yakeyi sabida burinshi yaga cikin ya zube.
Tun ahanyar zuwa gida taji mararta na ciyo kuma gawani zazzaɓi da ya taso mata lokaci ɗaya.
Batafi minti biyar da shiga gida ba cikin ta yafara juyawa kamar abunda ke cikinta ya fito.
Kuma gashi ita kadai a ɗakin, tajima kwance tana birgima a ɗakin sai can Mama ta shiga ɗakin ta dan tayi mata faɗan jimawar datayi bata dawo ba sabida ƙarfe huɗu tayi da ita tadawo.
Aikuwa koda Mama tasha ɗakinta halin da tasameta ne yayi matuƙar razanata.
Rasa mezatayi tayi sabida gabaki ɗaya tafita hayyacinta gakuma wani jini dakefita ta ƙasanta.
Da gudu Mama tashiga ɗakin su Marwan tace "yakira mai napep Hafsat ba lafiya zasu kaita hospatal".
Dayake basuda nisa da ti-ti yana fita ya tsayar dashi suka ƙarasu gida.
Shida Ammar da Mama suka ɗaukota suka sa a napep suka wuce hospatal ko mayafi babu ajikin Mama sabuda firgita😢.......
*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*©SUMY NA'IGE•*
[4/17, 22:07] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 10📑*
*__________📖* koda suka isa hospital emregency room suka kaita,ba ɓata lokaci aka fara bata taimako cikin gaugawa.
Tunda suka shiga da ita Mama sai safa da marwa takeyi a harabar hospital.
Marwan Mama tasa yakira Abban su yafaɗa masa abunda ake ciki,kana yaje gida ya ɗauko mata hijab ɗinta.
Tare suka shigo da Abba hijab ɗinta Marwan ya bata tasaka Abba yace, "ina suka kwantar da ita?".
Jikin Mama sai rawa yake tace, "Abban su har yanzu basu fito ba"....tun bata kai da ƙarasa maganar ba sai ga doctor yafito daga cikin ɗakin.
Da sauri Abba da Mama suka zo wajan sa.
Tambayar su yayi kosu suka kawo Hafsat? sai Abba yace, "eh".
Magana doctor yayi musu yace su biyushi office.
Bayan ya shiga office ya zauna suma suka shigo kallon su yayi yace, "wanene mijin ta?".
Kallon-kallon suka fara tsakanin Mama da Abba.
Sai Abba ya buɗe baki yace, "batada miji mune dai iyayen ta".
Doctor kallon Abba yayi sosai kana ya nuna masa kujera yace ya zauna.
Bayan ya zauna sai doctor ya kai duban sa ga Mama yace, "kefa miye matsayinki a wajanta?"...... tin kan Mama tayi magana sai Abba yace, "mahaifiyar tace".
kujere doctor ya nuna mata yace ta zauna.
Bayan ta zauna sai doc tor yace, "ba abinda zan ɓoye muku gaskiya,muyi nasarar tsayar da jinin da yafara fita jikin ta,amma cikin dake jikin ta nanan bai fita ba.....tun kan ya kai ƙarshen zanci sai Mama tace,
"a'a ba ƴata baca ka duba danni ƴata batada ciki kada kayi mata sharri" magana Mama keyi amma gabiki ɗaya bata cikin natsuwar ta.
Abba yace, "kada kisa ke magana ki bari muji me doctor zai ce".
Abba kallon doctor yayi yace "inajinka".
Doctor yace, "iya binciken da mukayi mata, munganu tana ɗauke da ciki har na tsawon wata huɗu, kuma cikin na gab da zubewa saboda irin yadda ....bai ƙarasa zancin ba saboda da nauyi maganar da zai faɗa, ya faɗa musu ko yanzu saduwar da yayi da ita ne yajamata wannan ciyo sai yaƙi faɗa yace, amma yanzu tasamu sauki dan har barci ta samu sai zuwa kosan awa huɗu zata farka saboda mun mata allura bacci.
Yana kai ƙarshin zancin Abba ya sauke wata ajiyar zuciya haɗi da goge ƙwallar da ta zubo masa yace , "to doctor muna godiya".
Sai Mama tace, "yanzu Abbansu har ka yarda Hafsat na da ciki?wallahi nikam ban yarda ba dan nasan ba halin ƴata bane" magana takeyi amma kamar zata faɗi.
Doctor ya dube ta bayan yaba Abba ta kardar maganin da za'a sayo mata yace da Mama "zaki iya gane ƴar taki idan kin ganta?".
Tace "sosai kuwa".
Sai yace, "zo muje kiga ko ita ce" yana faɗin haka ya tashi ya kaisu ɗakin da aka kai ta.
Suna shiga gadon da take kwance ya nuna mata yace, "gata ko ba ita bace?".
Kallon Hafsat Mama keyi wadda ke kwance tana barci bata masan abunda akeyi ba.
Gaban gadon Mama ta ƙaraso tace, "Hafsat! Hafsat! mi kika rasa wanda bamuyi miki ba,ci kika rasa ko sha ki gayamin miyasa zaki sakamin da haka Hafsat!, kinsan aure kikeso meyasa bazaki gayamin ba" tana magana tana wani kuka mai ban tausai.
Alamun zata faɗine Abba yagani dan haka da saure ya tare ta ta faɗu jikin sa sume.... ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba lokaci ɗaya jikin sa yayi sanyi yama rasa me zaiyi.
Doctor ne yakira wasu nurse suka ɗauke ta aka ɗura ta kan godon yafara dubata.
Cikin lokaci kaɗan ta farfaɗo.
Sunan Abba ta fara kira,doctor yasa aka kirashi,yana zowa yafita dan yaga ba komai ne ke damun taba sai ruɗuwar da tashiga.
Jikin Abba tafaɗa tana kuka tace, "kaga abunda Hafsat tayi muna yau mu zata sakama da ciki kuma ko ciki na shege".
ajiyar zuciya Abba ya sauke kana yace, "ta dai yi ma kanta, dan haka ki rage sa damu wa aranki,kuma ki tashi mukoma gida idan tafarka gasu Marwan nan su dawo tare".
Sai Mama tace, "da ka barni idan ta farka mu dawo tare sai kuje kai da su Marwan......tun bata kai ƙarshen zancin ba ya daga mata wata irin tsawar da yasa ta sauka daga gadon bata shirya ba.
komai bai ce da itaba ya kama hanyar fita ya barta.
Itama tana ganin yafita ta bi bayan sa.
Waje suka tarar da Ammar da Marwan suka ce sujira idan Aunty su ta farka su dawo gida tare.
Haka kuwa akayi tana cika awa huɗu ta farka.
Dubi- dubi tafarayi Marwan da Ammar tagani sunyi tagumin kamar sun san mike faruwa.
Ammar ne ya kula da farka warta dan haka da sauri ya ƙaraso gare ta yace, "Aunty ya jikin naki".
Da sauki tace dashi kana tace, "Ammar ina Mama?".
Yace, "ta koma gida ita da Abba".
Yana faɗa mata haka wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncin ta sabida tasan yanzu kowa yasan tana da ciki.
Lokaci ɗaya tafara rera kuka mai ƙunar zuciya tana faɗin, "Ammar kada kugujeni wallahi nima ƙaddara ce ta afka kaina ni kaɗai nasan me nakeji gami dashi,duk duniya banajin abunda nakeji dashi ga kowa sai gareshi dan Allah ƴan uwana kutayani da addua, dan wallahi ina cikin wani hali".
Sosai ta baso tausai duk da su kansu basu san me ake ciki ba.
Duk da Abba yace kada su kwana komai dare su dawo amma basu gaya mata ba sukayi kwanciyar su har safiya ta waye.
kuma basu fito ba sai da doctor ya dubata ya rabuta mata magani Marwan yaje yasayo haɗi da kayan beark bayan tayi beark tasha magani suka kamu hanyar zuwa gida.
Abba da Mama ba wanda ya samu bacci a ckin su kowa nin su tunani abunda ƴarsu wadda suka fi so a duniya ta aikata ya keyi
Tun cin dare yake zuba ido amma basu dawo ba,dan haka koda akayi kiran sallah asuba yaje masallaci ana gama sallah ya dawo .
Bai jima da dawo ba sai gasu sun dawo.
Sallama sukayi bayan Abba ya ƙarɓa suka wuce suka zauna.
Komai Abba bai ce dasu ba kuma suma basuyi masa magana ba saboda basuga wurin yimasa magana ba dan fuskar sa haɗe take.
Kallon sa ya maida ga Ammar kana yace, "jeka kiramin Safiyya".
Tashi Ammar yayi yafice yaje kiran Safiyya.
Mama na fitowa ɗaki bata ce da kowa kamai ba ta fara dukan Hafsat tana faɗin kin ci amana ta Hafsat mikika rasa tana faɗa tana dukanta iya ƙarfin ta.
Tashi takeso tayi dan ta gudu amma takasa saboda bata da wani ƙarfin jiki.
Abba na kallo amma yayi kamar bai san abbun da ke faruwa ba.
Wani ice Mama ta raramu dan ta bugama Hafsat aikuwa da sauri Marwan ya riƙe yana kuka yana faɗin, "dan Allah Mama kirabu da ita me ta muku kika dukan ta, ki dakeni mada-din ta ko lafiya fa bata da komai tayi kuyi mata uzuri mana".
Tun bai kai ƙarshen zan cin ba Mama takafeshi da mari har sau biyu.
Abba ne yayi magana yace "ta ƙyalesu kada ta koma magana ta barshi da su.
Anacikin haka sai ga Ammar da Safiyya sun zo tare.......
Nagaji🤦♀
*#Vote Comment Shere*
*©SUMY NA'IGE•*
[4/17, 22:07] Summy Nah 1: *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*Allah sarki masoyana nima ina yinku sosai Allah ya bar ƙauna,ina godiya da kulawa sosai*😘
*SHAFI NA 11📑*
*__________📖* Bayan ta ƙaraso ta gaishe da Abba da Mama amma bakowa ne bai samu damar karɓa mata ba sai ma tambayar da suka jefa mata.
Abba yace, "Safiyya ashe kin san halin da ƴar uwarki take ciki amma kika kasa faɗa mana?".
Tace, "wani hali Abba....!
Ai bata kai ga k'arasawa ba ya daka mata tsawa haɗi da faɗin.
"Ki bani amsar tambayar dana miki?".
Jikin ta na karkarwa tace, "Abba kayi haƙuri amma ni ban san wane hali take ciki ba".
Mama ce tace mata, "baki san tana ɗauke da ciki ba ne".
Aikuwa Mama na rufe bakin ta, Safiyya ta fashe da kuka mai tab'a zuciya kana tace.
"Wallah Mama ban sani ba".
tana faɗa tana kuka.
Abba ne yace.
"Ba komai Safiyya kuma ina fatan baki biyema halin taba?kuma daga yau narabaki da ita kada ta koya miki mugun halin ta, kuma kisani wallahi bazaki zauna min a gida da wannan ciki ba, dan haka ki tattara kayanki ki koma wurin wanda yayi miki ciki na bar masa ke har abada, dan wallahi daga yau na cireki daga cikin zuri'a ta, kuma bari kiji minti biyar na baki ki tashi ki barmin gidana ko na illataki" .
yana faɗin haka ya shigewar sa ɗakin sa.
Kuka mai tsanani Hafsat keyi kamar ranta zai fita,rasa bakin magana tayi dan gabaki ɗaya kalaman sa sunyi mata tsauri.
Ko Mama abunda Abba yace yayi mata zafi kuma tasan tunda ya furta to ba abinda zai canja,dan haka taja bakin ta ta kulle amma zuciyar ta na mata zafi.
Safiyya najin abinda Abban Hafsat yace dan haka da gudu taje gida su ta zo da Baban ta.
Tace masa ga Abban Hafsat can ya kore Hafsat.
Safiyya na fita sai ga Abban Hafsat ya fito a ɗakin sa,kallon Hafsat yayi haɗi da antaya mata harara kana yace, "bazaki tashi ki barmin gidana ba?".
Kafin tayi magana Marwan da Ammar suka fara bashi haƙuri,magana yafara musu cikin faɗa yace, "bari ma kuji wallahi duk a cikin ku duk wanda ya taimaka mata ko da bayan idona ne to banyafe ba". sai Mama tace, "a'a ka dai ce ta bar maka gidanka amma ba ruwanka tsakanin ta da ƴan wuna ta, kuma tabar maka gida taje ina Abbansu?, komai zakayi yana da kyau ka dubi gaba dan komu muna da namu laifi....kafin ta rufe bakin ta ya daka mata tsawar da tasa tayi shuru bata shirya ba.
Duban sa ya kai ga Hafsat yace,"ki tashi kibarmin gidana kafin nasa afitar dake".
Ahankali ta tashi ta fara tafiya har ta kai ɗakin ta,kayan ta ta haɗa gabaki ɗaya ta fito tana kuka mai cin zuciya,kallon ta Mama tayi tace, "kinga abinda kika jama kanki kika kuma jamin dan haka......Abba ne yafito yace Mama tayi masa shuru kana ya dube Hafsat yace, "fita ki barmin gidana" yana faɗa yana nuna mata ƙofar fita.
Kuka take kamar ranta zai fita, ta kama hanyar fita Mama ta dube Abba tace, "yanzu barin ta zamyi ta tafi? to ina zata je?".
Sai Abba yace, "tafiki sanin inda zata je" yana kawai nan ya koma cikin ɗakin sa.
Gabaki ɗaya kannen ta kuka suke lokacin da zata fita,har ta kawo bakin ƙofa sai ga Safiyya da Baba ta sun ƙaraso da sauri Safiyya ta ƙarasa wajanta tana faɗin, "ina zakije haka da kaya?".
Tace, "Abba ya koreni yace na bar masa gidan sa,...Baban Safiyya ne ya katse musu magana yace Safiyya taje ta kiramasa Baban Hafsat.
Shiga tayi tafaɗa masa ba jimawa ya fito fuskarsa haɗe ba alamar fara'a.
Bayan sun gaisa da Abban Safiyya sai Baban safiyya ya faɗa masa abunda Safiyya tafaɗa masa tace ya kore Hafsat shin ko gaskiya ne?.
Bayanin da Safiyya tayi masa to shi Abban Hafsat yayi masa kana yace, "wallah bazata zauna gidana da cikiba,Alhaji Abbakar minene banyi ma Hafsat da har zata saka min da cikin, wallah bari gaji yanzu ko ganin ta bana sonyi, gabaki ɗaya Abban Hafsat ya rikice duk yadda Baban Safiyya yaso yayi haƙuri Abban Hafsat yaƙi,kunsan abu ga mai haƙuri idan ya tashi bai iya ba.
Da Baban Safiyya yaga Abban Hafsat yaƙi haƙuri sai yace, "tunda kace bazata zauna gidan kaba to ni zan ɗau Hafsat ta zauna gidana har nayi mata aure.....tun bai kai da rufe bakin shiba sai Abban Hafsat yace, "kada kasoma kace zaka haɗeta da ɗiyan ka dan zata lalata musu tarbiya".
Sai Baban Safiyya yace, "naji kuma na ɗauka Allah ya shirya min su gabaki ɗaya" rigima sukayi sosai da Baban Safiyya kafin su rabu.
Baban Safiyya nafitowa falon Abba dube su Hafsat yayi yace,"ko zo muje gida" yana faɗin haka ya kama hanyar gida sa ranshi a ɓace.
Suna isa gidan su Safiyya sai Baban Safiya ya kira Ummar Safiyya ya faɗa mata abunda ake ciki kuma ya shaida mata cewa Hafsat nan gidan zata ci gaba da zama har Allah ya sauke ta lafiya kuma ya kawo mata mijin aure.
Aikuwa Ummar Safiyya najin ace Hafsat zata dawo gidan da zama ta fara kumfar baki tana faɗi, "itakam gaskiya baza'a kawo mata Hafsat a gida ba salon tazo ta lalata mata tarbiyar yara,wallah bazata yarda ba" sai da ta kai ƙarshin zanci sai Baban Safiyya yace,
"wallahi ba wanda ya isa ya hana Hafsat zama ana gidan, nan ya dinga ci mata mutunci har yace idan tasake cewa Hafsat bazata zauna gidan ba bakin auren ta,ba shiri ta kama bakin ta,Safiyya yace da ita suje ɗakin ta su cigaba da zama ita da Hafsat,ba musu suka je ɗakin.
Bayan kwana biyu da faruwar haka gabaki ɗaya Hafsat bata da natsuwa, gashi ko fita batayi kuma ko takira shi a waya baya ɗauka.
Kuma yanzu ko barci take mafarkinsa take, ko me taki tunanin sa take, gabaki ɗaya ta koma wata iri gashi Ummar Safiyya da ƙannen ta har ma da yayun ta duk sun tsane ta abu ka ɗan sai Ummar Safiyya ta dinga yimata faɗa, sosai abun ke ɓata mata rai amma sai ta dake ma zuciyar ta saboda irin yadda Safiyya da Baban ta ke nuna mata amma daba dan suba da tuni ta bar gidan .
Yau ma kamar haka suna kwance da dare dan har bacci ya ɗauke su tana cikin bacci taji kamar antsaƙure ta,da sauri ta zabura ta tashi,komai bata gani ba, lokaci ɗaya taji tana son taji koda muryar sa ce dan haka ta ɗau waya ta kira koda Allah zai sa ta samu.
Missed call biyar tamasa amma bai ɗauka ba,har taso ta aje wayar ta kwanta sai tace bari ta koma kira,aikuwa tana kira ringing da bai wuce uku ba ya ɗaga tare da faɗi, "wake magana?".
Toilet ɗin dake ɗakin ta shige kana tace, "Hayat nice fa,baka ganeni ba?".
Yace, "oh nagane shin kece?lafiya dai ko?".
Tace, "eh kodama nakirane naji ko lafiya kake?".
Yace, "eh ƙalau nake"...har zai katse kiran tace Hayat kayi haƙuri nasan ko dan mi kake fushi dani amma in har nasamu fita zan zo dan nayi missing ɗinka sosai, kuma kayi haƙuri ka yafemin idan na ɓatama"......tana faɗi tana fitar da ƙwalla.
Gajiya yayi da surutun ta dan haka ya datse kiran batari da yaji sauran zancin ba,daga baya ta lura da ya kashe wayar dan haka taci gaba da kuka dan gani take kamar ta aikata babban laifi fushin da ya keyi da ita.
Washi gari baya sungama aikin su na gida ita da Safiyya sai Mamar Safiyya ta shirya tafita unguwa ta barta daga ita sai Safiyya tace sai ta dawo.
Fitar ta ba da jimawa ba Safiyya ta kwanta barcin rana,aikuwa Hafsat naganin haka taje tayi wanka ta shirya cikin hanzari ta bar gidan, tana fita ta tsayar da mai napep ,basu tsaya ko ina ba sai gidan sa, kuɗi da suka rage mata taba mai napep kana ta shiga gidan.
Parlour tasame shi yana waya, da sauri ta ƙarasa jikin sa tana faɗi, "Missing you Hayatee nah".
Yana jinta jikinsa ya ɗago ya kalle ta haɗe da katsi wayar da yakeyi, dan jinta kawai yayi dan har taso ta bashi tsoro,har ya buɗe baki yayi magana ta haɗe bakin ta danashi tana kissing ďinshi kamar tasamu lolipop,lokaci ɗaya ya fara karɓar saƙon da take aika masa, martani yafara mai dama ta sannan yafara ƙoƙarin rage mata kayan jikin ta,
bayan ya cire mata ya fara romance ɗinta son ranshi,daukar ta yayi ya kai bedroom ďinsa daga can yafara sarrafata yadda yake so,dan kowane buƙace yake da wani.
Sosai hankalin Safiyya ya tashi, lokacin da ta farka bataga Hafsat ba dan ta ɗauka ko guduwa ne tayi sabida abinda mamar take mata,sai da taga kayan ta hankalin ta ya ɗan kwanta.
Tunani tafarayi to ina Hafsat ta tafi ne tasan ba gidan su tajeba .
Shiko ya samu jaka sai yadda yaso yakeyi da ita,tagaji iya gajiya amma takasa buɗe baki tace ta gaji,sai da ya gaji dan kansa sannan ya barta.
Sai da suka ɗan huta ta ƙara shigewa jikin sa,a hankali ta buɗa baki ta fara faɗa mishi abinda ya faru da ita,sannan ta ƙara da cewa, "Hayat ko na ɗauko kayana na dawo nan da zama zan fi samun natsuwa bisa ga inda nake".
Sai da ya kalle ta kana yace, "a'a kada ki dawo dan nima ko wata bazanyi garin nan ba zan koma garin mu dan nagama aikin dana zo yi".
Kuka ta fara masa wai zata bishi garin su,bai kulata ba yaci gaba da abinda yake so da ita.
Roƙon sa tayi ya barta taje gida amma yayi kamar bai jita ba,sai can yace taje ɗin kuma gobe ta dawo.
Wanka kawa tayi ta sanya kayan ta tafito,roƙon sa tayi ya bata ƙuɗi ta hau napep,sai da yagama jamata aji kana ya ɗauko dubu ɗaya ya bata yace taje.
Taci sa'a koda ta dawo mamar Safiyya bata dawo ba Safiyya kadai ta isake a tsakar gida tana safa da marwa.
Kallon ta Safiyya tayi tace, "daga ina kika fito?".
Bata karɓa mata ba ta shige ɗaki ta barta tsaye,ɗikin Safiyya tabi ta tace, "dake nake magana kinyi min shuru"
sai Hafsat tace, "mi zance miki to, fita nayi ko so kike na faɗamiki inda naje,to ba aikina kikayi ba bare na faɗa miki" tana magana tana antaya mata harara.
Komai Safiyya bata sake cewa da itaba dan tasan ba ida taje sai gidan shegen saurayin ta kuma ta ɗau alwashin sai ta ci mutunci sa duk ranar da ta ganshi.
Ko da dare yaya ba wanda yayi ma ɗan wunsa magana har suka zo kwanciya ,Hafsat a tunanin ta Safiyya bacci take dan haka ta ɗau waya ta kirashi,bayan ya ɗauka ta gasheshi to fa nan suka cigaba da fira amma mafi yawan firarsu ta batsa ce,hirar ce ta dame Safiyya wai a ce ƴar uwar ta ke wannan firar dan haka ta farar kuka har da shisheka, kukan Safiyya da Hafsat taji ne yasa tayi sauri ta katse wayar kana tace, "Safiyya lafiya kike kuka?".
Kyaleta Safiyya tayi dan abin nan na Hafsat yanzu tsoro yake bata, a ce har mutum yayi sanadiyar barin ka gidan iyayenka amma ka kasa barishi wannan wani irin so ne,tana kuka tana tunani cikin zuciyar.
Jin da tayi Stuna in bata amsa mata ba yasa ta ƙaraso wajan ta hawayen da suka Zuni matane ta goge tace, "My Safiyya kiyi haƙuri nasan dan kinji wayar danakeyi ne kike kuka,wallahi Safiyya koni zuciya ta na ƙuna abinda nakeyi dashi amma ya zanyi dan wallahi bani da natsuwa duk banji shiba ko bantare dashi ba, nidai abinda nake so dake kiyi min addu'a kada na mutum ina cikin wannan hali kinji ƴar wuta".
Jikin ta Hafsat ta faɗa gabaki ɗayan su kuka suke mai ciki da kunar rai.
Haka Hafsat taci gaba da zama gidan su Safiyya har aka kuma hutun makarantar su amma duk ranar da tasamu damar fita sai taje wajansa,itako yanzu Safiyya da dare yayi take tashi kuma ta tashe da Hafsat suyi alwala sufara nafil-fili suna kai kukan su ga Allah.
Kuma cikin ikon Allah yanzu Hafsat tarege jin soshi a zuciyar ta sosai.
Bayan sun koma makaran ta da kwana biyu ranar Safiyya na zaune class ɗinsu sai ga wata ƙawar ta tazo wajan ta kuma ƙawa ga Hajara dan abinda yasa Safiyya ta barta saboda taga ko ina Hajara take itama tana can danshi ta bar ta...
0 comments:
Post a Comment