Badeeyerh Beauty Queen*✍πΌ
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
π Zaku iya samun littafan mu a Facebook ππ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
π© Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu ππ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com
GARGADI
BAN YARDA A SARRAFA WANNAN LABARIN TA KOWACCE HANYA BA, YIN HAKAN ZAI SANYA MUTUM YA FUSKANCI HUKUNCI DAGA SHUWAGABANNIN KUNGIYA A KIYAYE.
TUNATARWA
WANNAN LABARIN BANYI SHI DOMIN CIN ZARAFI BA FA CE DOMIN NEMAN MAFITA GA YANAYIN ZAMANTAKEWAR MU A IRIN WA'INNAN GIDAJEN. IDAN HAR YAZO DAI-DAI DA RAYUWAR WASU AYI HAKURI KIRKIRA NE.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*1~5*
_SHIMFIDA_
*'YAN GIDAN HAYA*
Gida ne mai dauke da dakuna goma sha biyu sai bandaki *guda hudu, wato kowanne biyu.* Suna da rijiya a hanyar kicin dinsu wanda ke manne da famfo guda daya, sai igiyar shanya guda biyar. Gida ne mai dauke da mutane masu bambamcin ra'ayi da harshe. Suna zaune tare yayin da wasu suke da sana'ar yi a unguwar. Suna da mai unguwa sunanshi Malam Tanko yana da mata biyu Jummai da Hannatu sai yara biyar Lado shine babba, Buba, Sani, Saratu da laraba. Duk manoma ne mazan, matan kuma sun yi aure. Malam Tanko ya kasance mutum mai saka idanu kan wannan gida na yan haya wanda su kuma basa kaunar hakan. Maman Ladi ita ce kusa da rijiya tana sana'ar waina da daddare, Maman David tana saida akamu da safe, Ladidi bata saida komai sai gulma, matar malam tana sana'ar kayan miya, Iya beji mai kosai, Mama akintola mai kankara, Mama Dare mai icce, Abule bata sana'a sai Maman Usman itace babba a gidan ma'aikaciyar gwamnati ce, sai Inna Talatu tana da injin nika. Kusa da hanyar bayi Mairon Ado mai sana'ar kuli da man gyada, Inno dillaliya itace hanyar kofar gida.
*BARI MU LEKA CIKIN WANNAN GIDA NA YAN HAYA*
Zaune Maman Ladi take a kofar dak'inta tana tsintar shinkafar da zata yi waina da ita yau. Da gudu ta hango dillaliya ta shigo cikin gidan tana fadin "Taimako Maman Ladi ga yara can na fada, na raba sun ki rabuwa kwarankwatsi".
Ajiye shinkafar ta yi tare da bin bayan dillaliya.
"Kai! Butar ruwan iyayen ku idan baku daina fada ba" cewar Maman Ladi. Caraf ta ji an riko hijabinta ana janta, da sauri ta waiga tana sababi.
"Wanne mai ido a tsakar ka ne ke jana don uwatai?"
"Nine nan ka ji ko Mama Ladi, ni ne waye ya ce ka zagi yaro nawa yanzu?" Maman David kenan ta dauka butar iyayen ku da Maman Ladi tace zaginsu ta yi, tana hargowa tare da rike kugu.
"Jar uban nan yanzu dan nazo rabon fada shi ne za ki min rashin kunya? To alkur'an sai na sabautaki yau" tana gama fadi ta kai ma Maman David wani irin mangari a baki, take saiga jini na zuba. Ihu Maman David tasa tana kiran "Mama Ladi ya kesheni Iya beji kazo fa" Da gudu sauran matan gidan suka fito don jin kururuwar Maman David.
Gyara tsayuwa Maman Ladi ta yi tace " sai na sauke ma ko wacce shegiya abun dake kanta a gidan nan ai dama ina sane da gulmata da akeyi idan na fita, kullum sai Ladi ta fadamin. to yau..." gum taji an rafka mata abu akai wanda ya hanata karasa maganar da ta keyi. Tsaye ta yi gaban Maman Ladi tana huci cikin tsananin fushi tace" to wata shegiyar ce ke gulmar ki? Kinzo kina zagin mutane a tsakiyar titi waye sa'an ki? Ko dan.." tass taji saukar mari a fuskarta, Matar Malam kenan wacce ba ayi tai shiru. Juyawa ta yi dan ganin waya mareta? Maman David ce "da kaine anayi fadan da kazo ka hana na rama dukeni da Maman Ladi ya yi?" "Kan butar duma, ni kika mara? To wallahi zakisan kin tabo Matar malam yau a gidan nan" kafin Maman David ta ankara kawai jinta ta yi a kasa matar Malam ta turmushe tana duka. Tim tim ka keji Iya beji ta hau kan matar malam tana duka ita ma. Jitai an buga mata abu a baya, ba shiri ta tsagaita da dukan matar malam domin mai dukan ya shammaceta taji dukan sosai. Abule ce tsaye rike da icce tana hararar Iya beji tace "yo hidi miki ankai matar malam batta da gata? Na rantse ina fasa kanki da wanga icce kinka kuma dukanta" tashin hankali ashe gefe ma fadan ne tsakanin Ladidi da Mairon Ado. Gida fa ya rikice da fada, dama kowa na da cikin kowa. Ganin haka yasa dillaliya ficewa da gudu don kiran mai unguwa.
*********
Zaune yake kofar Jummai tana dama musu kunun da zasuyi karin safe dashi, Hannatu na tsifar kai. Jummai tace "Malam kaga ragowar kullin kunun nan kadai ya rage mana cikin gidan nan ka taimaka a bude rumbu mu debe abinci".
"tabdijam! Rumbun da na kidaya sai karshen wata shine zan bude yanzu? To wallahi ku sake shawara bazan bayar da ko kwayar hatsi ba ai nasan siyarmin da hatsi akeyi, mugaye kawai". Shigowar dillaliya da gudu tana kiran "mai unguwa kazo yau unguwar ka babu lafiya kwarankwatsi za ai kisan kai a gidan haya" da hanzari ya mike ya yi facali da robar kunun mai dak'insa. Rawani na warware wa yana daurawa ya fice ko waige.
*Mezai faru da mai unguwa kenan?*
Muje zuwa
*Badeeyerh Beauty Queen*✍πΌ
[3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: ⚜⚜π±π±⚜⚜π±π±⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
π±π±⚜⚜π±π±⚜⚜π±π±
. π¨π»π»π©π»π»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
WΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍πΌ
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
π Zaku iya samun littafan mu a Facebook ππ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
π© Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu ππ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*6~10*
Fada sosai sukeyi kaman zasu kashe junansu, ga mazajen su basa nan. Sai makwafta ne keta kokarin raba wannan rigima.
Mai unguwa ya iso da sauri yana gyara babbar rigarsa.
"Yanzu saboda Allah bazasu bar wannan fadan ba? Yaran ku na kallon ku fa wannan ai abun kunya ne gareku."
"Abun kunya ya wuce sa'ido irin naka" cewar Ladidi.
Gyada kai ya yi lokaci daya kuma ya daga salularsa yana fadin "Ranka-ya-dade mai unguwa Tanko ne, yauwa sai kunzo" cak suka tsaya da fadan jin mai unguwa ya kira yan sanda.
Dillaliya dake tsaye kusa da mai unguwa ne ta saka dariya hade da mika wa mai unguwa batirin wayarsa tana fadin. "Mai unguwa ga batirin sanda ka ciro wayar naga ya fadi kasa, ashe dama ana magana ko ba batirin?"
"Ke kam anyi matsiyaciya basai kiyi shiru ba tunda sun daina fada da barazanar da nayi ba? Ai dama nasan ko kwandala banda ita a wayar" ya fadi yana muzurai.
Saukar katako dillaliya taji tsakiyar kanta wanda ya haddasa mata zubewa kasa ba shiri,ga jini na zuba.
"munafuka bayan kin sani na ajiye shinkafar sana'ata shine kika zagaya kiran wannan kidahumin ko?"
"Haba Maman Ladi da girmanki kike irin wannan abun?"
"Dalla rufemin baki munafiki mata maza, in banda gulma baka ajiye komai ba uban me kazo yi nan inba gulma ba".
"Yanzu Maman Ladi da girmana kike zagina?"
"Anzage ka din, talakan banza kawai" tass ya dauke ta da mari.
Aikuwa saijin saukar katako ya yi tsakiyar goshin sa, shima sai jini. Nan fa fada ya kara kaurewa tsakanin matan gidan aka bar dillaliya da mai unguwa zube a kasa da jini.
Jiniyar motar yan sanda ya dakatar dasu kowa ya yi tsaye cirko-cirko. Yan sanda suka fito bisa jagorancin wani makocin gidan hayan, aka tasa su gaba zuwa station shi kuma mai unguwa aka kaisu kemist da dillaliya.
Zaman sulhu akayi kasancewa DPO mai kirki ne, ya sanya yace ayi sulhu.
Bin ba'asi akayi inda aka baiwa Maman David da Maman Ladi rashin gaskiya kan cewa sune suka haddasa rigima, sai matar Malam data siya fada a sama. Mai unguwa kuma aka tuhume shi kan bai kyauta ba bisa marin Maman Ladi da ya yi, ita kuma an tuhumeta da amfani da makami sannan dole ta biya kudin maganin su. Nasiha sosai DPO Muhammad Abubakar ya yi musu kan muhimmancin zaman lafiya, sannan ya sallame su suka dawo gida.
**********
A gidan mai unguwa kuwa bayan ya barar da kunun ya fita ya barsu, sukai shiru suna tunanin yanzu me zasu sha gashi basu da ko kwayar gero.
Jummai tace "Hannatu idan kina da gero ki bani na sirfa nayi kunu wallahi yunwa nakeji."
"Maman Sani kenan, nima nan yunwa nakeji gashi ya barar da kudin, ya tafi neman suna. kawai mu balle rumbu mu debo hatsi mu dafa"
"uhm tsoran jarabar shi nake yi Hannatu"
"to mu zauna da yunwa tunda kina tsoro"
"A,a to bari mu debo idan yazo sai mu nemi abun cewa."
"Yauwa Maman Sani gara haka ai."
Suka debo shinkafa suka daura suna zaune tare da addu'ar Allah yasa ta dahu kafin ya dawo. Aikuwa suna saukewa mai unguwa ya shigo da bandeji manne a goshi.
*Badeeyerh Beauty Queen*✍πΌ
[3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: ⚜⚜π±π±⚜⚜π±π±⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
π±π±⚜⚜π±π±⚜⚜π±π±
. π¨π»π»π©π»π»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
WΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍πΌ
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
π Zaku iya samun littafan mu a Facebook ππ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
π© Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu ππ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*10~15*
Da mamaki suka bishi da kallo ganin shi manne da bandeji ga leda a hannu da alamun magungunane a ciki.
"Malam sannu da zuwa"cewar Jummai.
"Yauwa Jummala"
"Malam hatsari kayi ne na ganka haka?"
"Tirela ce tabi ta kaina." ya bata amsa cikin tsawa tare da zama bakin kofa.
"ke Hannatu baki iya sannu da zuwa ba ko?"
"Allahu Malam gajen hakuri ka yi, ina jiran Maman Sani ta gama ne sai nayi nawa"
"Ja'ira mai ladabin munafukai."
Girgiza kai kawai sukayi domin sun saba da halin mai gidan nasu, irin mazajen nanne masu zagin matan su.
"Malam dan Allah meyafaru kaji ciwo?"
"Bari kedai Jummala wadannan shegun mutanen ne suka kusan sabautani."
"Wasu mutane kuma mai gida?"ta tambayeshi da mamaki.
"Yan gidan haya mana matsiyata daga rabon fada saijin saukar icce nayi a fuskata."
Dariya dukkansu suka saka suna farin ciki dama gashi ya barsu da yunwa dalilin zuwa neman suna. Aikuwa a fusace ya mike yana fadin.
"Duk shegiyar data kara yi mani dariya saita bakunci gidan uban ta yau wallahi, shegu marasa tausayi kawai na fada muku madadin kumin jaje shine ko wacce zata bude baki kamar kofar gari tana dariya, to wallahi na karaji ku gani."
Shiru sukayi suna kallon shi, jin ya kuke yana sababi hade da tallafe kanshi dake tsananin bugawa ya shige dak'i.
"Maman Sani abinci ya sauka"
"to Hannatu zuba mana muci"
"Nima a zuba min zanci insha magani."
Suka ji mai unguwa na fadi.
Zuba mai sukayi aka kai mai, nan suka zauna sunaci, sai da ya cinye yasa ruwa ya kalle su.
"Amma kuwa abincin nan da dadi yake, ina kuka samu shinkafa?"
"Malam kenan, ai rumbu muka bude muka debo."
"Rumbu Jummala?"
"Eh Malam ko so kake mu zauna da yunwa bayan ka zubar mana da kumallon safe" ta bashi amsa cikin zafi itama.
Da yake yasan halinta idan ranta ya baci bata mai da sauki, dan haka yace, "To shikenan an debo Allah ya isa, kuma anci Allah ya isa."
********
Zaune ko wacce take a bakin kofarta tana gyaran kayan sana'arta. Maman Usman tana ta yi musu nasiha kan abun da suka yi yau basu kyauta ba.
" Yanzu ba kuji kunyar kanku ba don Allah, ace matan aure a ofishin yan sanda?"
"wallahi Maman Usman duk laifin wa'innan munafukanne" cewar Ladidi tana nuna su Iya beji.
Aikuwa Maman David ta mike tana fadin, "Ledidi kace nine munafuki? ehen baban kane munafuki."
"Babana fa ki kace, don uwarki na kira sunan ubanki ne?"
"Ladidi amma magana nake yi daku ko?"Maman Usman ta fadi cikin tsawa.
"Haba Maman Usman kina ji fa wai ubana take cewa munafuki" kawai ta saka kuka tana cigaba da fadin, "Malam mai carbi har ya bar duniya bai taba zagina ba, amma yau ga wata tsinanniya ta zage shi dalilina."
"Wallahi ki zagi uban babanta Ladidi karki yarda taci bulus" cewar matar Malam dake zaune tana gyaran kayan miya.
"Au Matar Malam ina magana kina kara iza wuta ko?"
"A,a ayi hakuri Maman Usman na tuba."
Nan dai Maman Usman ta sasanta tare da kara basu hakuri, da nusar dasu illar abun da sukeyi. Da yake suna ganin girmanta yasa suka aminta da abun da tace musu kamar gaske.
Da daddare Maman Ladi ta kafa kaskon wainarta ta fara sana'arta a kicin din gidan. Bata kula kowa ba da yake tana ciki dasu kan kudin maganin data kashe, ta fara sana'arta masu siye nata zuwa.
Mama akintola ce ta fito da niyyar daura girki, bayan ta dawo daga wurin sana'arta.
"Iya Ladi kenan ya kasuwa fa"
"lafiya, kuma sunana Maman Ladi ba iya Ladi ba."
"oh I'm sorry Maman Ladi"
"Allah ka tsine ma duk matar data zageni da yare."
Inna Talatu dake zaune bisa rijiya ta kwashe da dariya, "Kai jahilci dai baiyi ba wallahi, su oo a taimaka a je makaranta"
"Malam Dauda dai baida kudin zuwa makaranta nasani" Maman Ladi ta bata amsa.
"Aifa shiyasa a kace sorry mutum ya zata zagin shi akayi, gara ubana zamanin su babu makaranta"
"Wai cin danko harda su kaza"cewar Ladidi.
"Ganemim hanya Ladidi wai makaho yaso tsegumi"
"a,a ba dani ba gada a hurumi Maman Ladi"
A fusace Inna Talatu tai kan Maman Ladi dake zuba waina, aikuwa kaya-kaya aka hau dambe kan tandar waina.
"Maman Usman taimaka ki fito kafin ayi aika-aika cikin gidan nan"
Baiwar Allah da sauri ta fito jin maganar Ladidi, wanda yasa sauran matan gidan fitowa.
Tana shiga kicin din lokacin Inna Talatu ta daga bokitin kullun waina sai a jikin Maman Usman.
*Badeeyerh Beauty Queen*✍πΌ
[3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: ⚜⚜π±π±⚜⚜π±π±⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
π±π±⚜⚜π±π±⚜⚜π±π±
. π¨π»π»π©π»π»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
WΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍πΌ
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
π Zaku iya samun littafan mu a Facebook ππ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
π© Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu ππ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*Ummyn Yusrah nida sweet mum Rano muna godiya da dedicating Allah ya kara basira, muna Jin dadin Rayuwar Aseeya.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*15~20*
Wani irin zabura Maman Ladi ta yi ganin an shekar da kullin waina kasa. Ita kuwa Maman Usman mamaki ya hana ta motsi ganin wannan almubazzaranci irin na Inna Talatu.
Bakin wuta Maman Ladi ta dauka ta yi kan inna Talatu tana duka inda Maman Usman ke kokarin raba su, ganin ta kasa yasanya ta fara kiran sauran matan gidan dasu kawo mata dauki.
Dai-dai shigowar malam Isah mijin Inna Talatu, yana hango wannan fada ya afka kicin din da niyar ceto matarsa. Rufe su da duka Maman Ladi ta yi ta ko'ina tana fadin, "Dama haushin ku nake ji, kuma wallahi a biyani kullin wainata ko na daki kudina yau." ganin da gaske ba zata bar dukan su ba, yasa Maman Usman shiga tsakani. Maman Ladi ta sauke bakin wutan tana haki gata dama jibgegiya.
"Zo ki fita daga kicin dinnan inna Talatu" cewar Maman Usman tana nuna mata hanyar waje.
"Ba inda zani wallahi sai na rama dukana da ta yi harda hadawa da mijina."
"A,a Talatu mu fita kawai ina ganin aljanu gareta."
Cikin takaici ta kalle shi "kaidai wallahi anyi matsaoracin namiji, to yau kodai ka rama min dukana wallahi ko kuma ayi tashin hankali a gidan nan". Shiru ya yi yana kallon Maman Usman wacce ke tsaye cikin takaicin fadan su ga shi anyi mata wanka da kullin waina.
"baki daku bane wallahi shiyasa kike tunanin ramawa, saura kudin wainata wallahi kodai a bani ko kuma mutum yaji a jikinsa." Fadin Maman Ladi kenan dake tsaye rike da robar wainarta.
"Maman Ladi nawane kudin wainar?" malam Isah ya tambaya domin bai kyaunar a sake wani tashin hankali tunda yasha jibga.
"hadin dubu uku da dari tara nayi, na saida ta dari tara" ta bashi amsa.
Lalibo aljihu ya fara yi yaji an riko shi da karfi. Gaban shi ya fadi ya zata wani fadan ne dan haka a tamanin ya waiga, Inna Talatu ya gani, ya saki ajiyar zuciya. "lafiya kuwa Talatu?" "Na rantse da Allah ba zaka biya kudin nan ba, bata isa ba ubanta ya yi kadan bayan dukan da tai mana, sai kuma a kara da kudi to wallahi bazaka biya ba." kau! Taji an dauketa da mari.
Maman Ladi kuwa kallon matan dake leke ta yi tace "Angama ai sai ko wacce shegiya ta bar lekena"
"A, a Maman Ladi karki sake ki zage mu wallahi" cewar matar Malam dake tsaye gefen rijiya.
"Na zaga nace ko wacce shegiya naji duka, yan iska maglmata"
"Ko wacce ta tafi dak'in ta don Allah na roke ku" Maman Usman ta fadi lokacin da take fitowa daga wanka.
Sumi-sumi suka wuce ba wacce ta kara magana.
Washegari Lahadi
Kasancewar yau lahadi, yasa da yawansu wanki su keyi da kwalemar dakunansu.
"Matan gida zanje sunan kanwata sai na dawo, don Allah mu zauna lafiya" cewar Maman Usman sanda ta fito daga dak'inta.
Sukai mata a dawo lafiya ta fice.
Mairon Ado zaune kofar Abule suna wanki tare, ta dubi Abule tace.
"Ban baki labari ba kawata."
"Menana ankayi hwadi mun".
"Wata mata ce a tsohuwar unguwar da muka taso, kullum saita tsine ma mijinta, gata da masifa amma bata da karfi."
"Kai Mairo taya kinka sani?" Abule ta tambaye ta tana cigaba da wankinta.
Mtsw... Mairon Ado ta yi tsaki "kefa dadina dake wulakanci, to ai a kusa da gidanta nake".
Girgiza kai Abule ta yi tana dariya domin ta gane dawa Mairon Ado ta keyi, tace "Alkur'ani Mairo wanga batu nake haka yiki, kin hwadi gaskiya" ta mika mata hannu suka tafa hardasa shewa.
Ba tare da sun lura ba, saijin saukar ruwa sukayi a jikinsu. Cikin masifa suka mike tsaye suna kallonta, Maman Dare ce mai icce ta wanke su da ruwa.
"Me mukai miki ke kuma?"Mairon Ado ta tambaye ta cikin bacin rai.
Kasancewar tana jin hausa sosai yasa ta fahimci abun da suke nufi tace. "Mairo muna zaune lafiya shine zaki janyo mana masifa ko, ina ruwanki da ita?"
"Tabdijam! Shine zaki watsa mana ruwa, to kanwar tsohuwar kice kenan?"
"Mairo kenan, kinsan dai bani da lokacin batawa don haka ki shiga hankalinki dani."
Tass! Abule ta dauketa da mari tana huci take fadin,"Kekam anyi bagidaja walla, yo mi naki da zaki wanke muna jikki da wanga ruwan wanki?to walla ki yi abun da yadda meki ba ruwana ta dake".
"Yauwa Abule tawa haka nake so kicimin kaniyar duk wacce ta yi damu a gidan nan."
"Barsu ta dani ina ma mace dukan tsiya walla ni bani daukar reni".
"Ni kika mara Abule?" Maman Dare ta tambaya tana dafe da kuncinta.
"Yo me zaki yi?"
"Ina zuwa zakiga abun da zanyi yanzu kuwa" ta wuce dak'inta da sauri.
Ita dama Mairo bata da karfin yin fada, dan haka tana ganin Maman Dare rike da wuka tai daki da gudu tare da danna sakata a kofarta.
Abule ta ruga kicin ta dauko bakin wuta gashi sai ci yake wanda matar Malam ta hada ta dora girki.
0 comments:
Post a Comment