*A TSAKAR GIDAN 'YAN HAYA*
Kowa dake gidan ya hallara wurin wannan taro, bayan an zauna ne malam Isah ya mike da bayani kamar haka.
"Ina fatan zaku mai da hankali ku fahimci ainahin abun da ya taramu anan? Dalilin wannan taro kuwa bazai rasa nasaba da fadace-fadacen dake yawan faruwa ba a gidan nan. Misali na yau wanda ya kai mizanin babu mai hankali a cikin matan mu, ko wacce kokari take na ganin ta yi fad'a badai ta raba fadan ba yau, mai unguwa da ya kasance uban al'umma kuma matsayin mai kula da wannan gida yau shima sun ji masa ciwo a hannu. Kuyi sani cewa mai unguwa bazai taba barin wannan magana ba face ya danganta ta da hukuma, shiyasa nace ko wacce ta kira mijinta domin sanin abun yi"
Cikin takaici Baban Dare yace " sunayi fad'a kaman kaji wada beci abinci ba".Dariya wasu suka yi dajin hausar shi. Mijin Maman Ladi ya mike yace" Tabbas abun da matan mu keyi kwata-kwata basu tsare mana mutunci, sai kace mu kadaine 'yan haya cikin wannan gari, kullum sai sun ja mana jaraba wurin mai unguwa. Ranar cewa ya yi wurin sarki zai kai karar mu a koremu domin ya gaji da masifar matan mu" ya karasa cikin bakin ciki.
Haka aka dinga mai da bayani kan halayyar matan gidan, inda aka hana matan magana. Kowa ya yi ma matarsa kashedi kan wannan halayyar tasu. Ana cikin wannan magana ne suka ji jiniyar motar 'yan sanda, cikin takaici mazan suka mike da niyar fita waje, amma sai ganin 'yan sanda suka yi tare da jagorancin mai unguwa dake sak'ale da hannu a wuya kai babu rawani.
Mazan ne suka yi musu tayin zaman sulhu, amma mai unguwa yace sam babu sulhu sai dai a tafi da Maman Dare ofishi tunda itace taji mai ciwo.
"Kwarankwatsi sai an tafi da ita, matsiyaciya ita ta bugamin icce kawai don nazo rabon fad'a, shi kuma shegen mijinta ya barni a waje harda cewa wai na mutu ai basu suka kirani ba."
"Haba me unguwa kiyi hakuri mana ki fadi gaskiya" cewar Baban Dare jin bayanin mai unguwa.
"Yauwa Usmanu kaji ba? Mace yake kirana shegen kwanon" Mai unguwa ya fadi yana nuna Baban Dare.
Dariya dan sandan da ya kira da sunan Usmanu ya yi yace "afuwan mai unguwa bai iya hausa bane shiyasa"
" Yo dama an fadi mai hausar kayan banza ce? Ai dole ya kasa tunda ba muhallinsa bace" Mai Unguwa kenan.
Sauran mazan ne suka shiga maganar don ganin ba a tafi da Maman Dare ba albarkacin mijinta, sunyi ma mai Unguwa Alkawarin biyan kudin jinyar hannun shi har ya warke. Jin haka dama gashi da masifaffen son kudi, take ya amince da wannan tayin.
Nasiha sosai 'yan sanda sukai musu, tare da basu hakuri ganin an zauna tare, sannan mai unguwa ma yace "Na daina zuwa gidan nan koda zaku kashe kanku." Dariya sosai suka yi, sannan kowa ya kama kansa.
*SHIGAR MAI UNGUWA GIDANSA*
Matan na zaune tare da Lado, Sani da Buba suna hira. suka ganshi kai babu rawani, da sauri yaran suka mike cike da mamaki suna yi mishi sannu da zuwa. Ko kallon su baiyi ba ya zauna cikin zafin ciwo yana fadin "Hanne kawo min ruwa"
"Malam meyasa meka a hannu?"
"Jummala! Jummala! Kar wata banza ta kuma tambayata abun da ya faru muddin nine mai gidan nan"
"To babu mai kara tambaya Malam, kayi hakuri." taja bakinta ta yi shiru tana binshi da ido.
Ruwa yasha sannan yace "wato Jummala mata matsiyata da ban suke". Banza ta yi da shi.
Cikin hassala yace" magana fa nake kuka shareni"
"Baba kayi hakuri"cewar Lado.
"Don uwar ka na saka bakinka ne a wannan maganar?"
"Yi hakuri Malam bazai kara ba" Hannatu ta fadi tana mikewa.
"Zauna ma za anan munahika kawai, za aje dak'in don ga bala'i ya dawo ko?"
"Abince zan kawo maka Malam " ta fadi ta yi hanyar dak'inta.
Abincin ta kawo mai, amma ko kallon kayan bai yi ba sai ma cewa da ya yi ta kwashe bazai ci ba. Ta kuwa kwashe a ranta tana fadin"Mun samu na karyawa da safe".
"Baba ga wannan ka sai magani, ni zan wuce sai da safe." cewar Sani ya mika mai dari biyu.
Amsa ya yi yana dariya yace "Sani dan albarka, yaro mai halin dattijai na gode sosai magaji na"
"Yauwa Baba had'ari kayi ne?" Sani ya tambaya.
"Hmm! Sani in fad'a maka matan 'yan gidan haya ne suka kassarani yau wallahi"
Kunshe dariya suka yi dukkansu, sannan yaran sukai mai sallama suka tafi. Su kuwa matan dak'i suka shige suna dariya jin mai unguwa na fadin,"wallahi ban kara zuwa gidan 'yan hawa billahillazi kuwa".
*ANYA KUWA MAI UNGUWA? MADARA KIN YARDA DA HAKAN KUWA??*
*********
*' YAN GIDAN HAYA*
Kwana biyu an samu kwanciyar hankali babu fad'a, amma ko wacce na nan da cikin yar'uwarta.
"Ke Inno jibi ranar cika ciki fa" cewar Ladidi dake wanke-wanke.
"Ayererere" Inno tasa guda, sannan ta dora da fadin"Za muga k'wanjin mazaje masu zuciyar siyan akuya, da masu cin bashi irin na waccan shekarar.
Mairon Ado ta yi tsalle ta ja gefe tana fadin "Uban mata zanci wallahi muddin ta kasa dani cikin zancenta."
"Uba fa kinka ce Mairo kawata? Ai wanga uban Baban ta shi ad dai-dai walle" suka tafa suna dariya.
Ladidi ta yi murmushi ta kama waka"_ayye nanaye wacce mijinta bai da sulalla, wazai taimaka yaji tausai, ya aiko da gashin kaza ran dadi"
Kau! aka dauketa da mari, da sauri ta dafe kuncinta tana waigen mai marin. Inna Talatu ce tsaye gabanta.
*Hmm yanzu aka soma*
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*35~40*
Ba tare da tambayar ba'asi ba ita ma ta kwashe Inna Talatu da mari. Jin zafin marin yasa Inna Talatu durkusawa kasa dafe da kuncinta.
"Ahayye gidan haya gidan dadi, gidan da ba uwar ka ba uban ka sai kallo." cewar Mairon Ado.
Gaurewa Ladidi da Inna Talatu suka yi da fad'a, yayin da Abule da Mairon Ado ke kara iza wutar ta hanyar yi musu waka.
Hayaniya ta yi yawa yasa Maman Usman wacce ke bacci a dak'i fitowa ganin maike faruwa, aikuwa taga wannan fad'a da ake. Da sauri ta karasa wurin tana janye Inna Talatu tare da kokarin shiga tsakani, amma ina bata yi nasara ba. Riko Ladidi ta yi da nufin janta, ganin yasa Ladidi kai ma Inna Talatu wani wawan duka wanda ya sauka a fuskar Maman Usman ta kuwa durkushe kasa. Ganin Maman Usman kasa ya sanya duk sukai kanta suna tambayar lafiya.
Dago da fuska ta yi, ganin jini da alamu habo ta yi, yasa Abule rugawa ta kawo ruwa, Maman Usman ta wanke fuska. Kallon su ta yi tace "Na gode sosai da abun da kuke yi, ina fatan watarana ku gane illar da hakan zai haifar muku a gaba, domin yaran ku na kallo kuma duk abun da kukayi shi zasu koya." daga haka ta shige dak'inta.
Shiru suka yi dukkansu suna jinjina fushin Maman Usman, daga bisani ko wacce ta koma kan aikinta ba tare data kula kowa ba.
Yau ranar cika ciki.
Matar Malam dake kiwon kaji ce ta debo su cike da isa ganin tun safiyar yau babu wacce aka aiko mawa ko fiffiken kaza. Don haka ta debo kajinta guda biyar kosassu ta mika ma wani yaron makwotansu ya yanka mata.
Ko wacce na zaune kofar dak'inta suna hira kamar ba mafadata ba.
"Mairo zoki taya ni fikar kaji" cewar matar Malam.
"Yo ni kuma ina da tumatiri zan gyara na kai nika."
"Haba mairo kardai bakin ciki kike don kinga zanci kaji?"
Murmushi Mairo ta yi tana fadin "Matar Malam aikuwa ko saniya zaki yanka alkur'an bazan taya ki ba, nima ina da nawa aikin."
"Kai jama'a wai anai maka hassada har kan abun da za kaci."
"Kedai kika sani" Mairo ta bata amsa sannan ta shiga ta dauko tumatirinta ta hau wanke wa.
"Bari na taya ki matar Malam."
"Yauwa Ladidi na kuwa gode miki wallahi" Nan suka zauna suna gyara wa suna hira, wanda rabin hirar duk gulma ce kan babu wacce aka kawo ma nama.
Yaro ya yi sallama suka amsa ya shigo yana tambaya ina Abule. I fito ya mika mata bakko cike da nama inji mijinta daga kasuwa. Ta amsa ta ajiye kofarta ta dauko roba babba ta juye, nama ne mai yawa wanda ya dau hankalin su matar Malam.
"Wallahi Ladidi na tsane makaryacin namiji mai cin bashi, dube naman can, bashi ya amso fa kila, amma shine ya kimo shi da yawa."
Dariya Ladidi ta yi tace "ga kuma su makwadaita a kusa ba". Ta fadi ganin Mairon Ado taje taya Abule gyaran nama.
Basu tanka su ba suka cigaba da aikin su suna hira.
Maman Ladi ta shigo janye da akuya wani saurayi na biye da ita. Bayan ta ajiye kayan Hannunta ne the dubi saurayin tana fadin "Yanka acan wurin" ta nuna mai wurin wanke-wankensu, ya kuwa tafi wurin ya hau aiki.
"Matar Malam wasu fa miji bashi da ko sisi amma sai anyi karya harda siyo dabba." cewar Ladidi cikin bakin cikin har yanzu ba a kawo mata komai ba tunda mijinta y fita.
"Na banza ne wallahi gara mu mazajen mu na kaunar farin cikin mu shiyasa zasu siya da guminsu." suka sanya shewa. Maman Ladi na jinsu ta yi bakan dasu ba tare data tanka musu ba.
Inno zaune tare da yaranta suna gyaran kaji guda biyu tace "Maman Ladi yanzu nawa akuyar nan?"
"Dubu hudu da dari shidda na siya Inno."
"Gaskiya ta yi arha sosai."
Dariya Maman Ladi ta yi tace "Inno kina burgeni baki da gadara irin nasu oo masu kiwon kaji."
Dariya suka sanya suna kallon matar Malam da Ladidi.
Mijin Ladidi ne ya shigo, don haka tabar taya matar Malam ta bishi dak'i. Can ya fito ya tafi, ita kuma the fito tana yatsina fuska rike da leda a hannu. Ta zauna bakin kokarta tare da dungurar da ledar. Aikuwa Maman Ladi dake zaune ta mike tare dauko ledar the bude.
"Aeyerere yau zamu ci ganda."
Warce ledar ta yi hannun Maman Ladi cikin fushi take fadin "zanci uban mata wallahi muddin ta shiga sabgata."
Shewa su Abule suka sanya, wanda yasa Ladidi da Maman Ladi juyawa don ganin menene.
Mairon Ado ce aka aiko mata da nama da yawa kamar na Abule. Takaici ya kuma kama Ladidi ganin daga ita sai Inno ce masu nama kadan, don haka ta dau ledarta hadi da shigewa dak'i.
Mario, Ladidi,Inno dillaliya da Abule suna zaune kofar kicin sun dora girki.Matar malam da Maman Ladi sun dora tafashen nama duk a cikin kicin suke aiki suna hira sabanin Maman Usman da ko lekowa bata yi ba.
*To fah gasu a kicin daya duk suna girki, ko mai zai faru??*
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*40~45*
Suna ta kai kawo cikin kicin ko wacce na duba girkin ta na tafashen nama dana kayan miya.
Matar Malam ta dora tafashen kaji, Maman Ladi ta dora ruwan shinkafa duk a cikin kicin din. Maman Akintola ce ta shigo tana fadin "Yau zamu ci dadi fa a gida namu kowa ya nayi kirgi nama."
"Eh wallahi yau mai kallon gabas zaici dadi" cewar matar Malam.
Da yake bata san mai hakan ke nufi ba dariya ta yi tana fadin "mata malam menene kina dafawa ne?"
"Ina dafa kaji masu motsi ba ganda ba" cewar matar Malam.
Cikin huci Ladidi data fuskanci da ita ake ta mike tana fadin "Don uban mata idan ta isa ta fadi sunana ta gani."
"Uban wa kike zagi mara kunya?" matar Malam ke fadi lokacin data mike tsaye.
"Idan ana saida kunya ki siyo ki kawomin banza 'yar sa ido kawai."
"A'a Ledidi babu fad'a yau fa kayi hakuri please" Maman Akintola kenan sannan ta wuce ta barsu.
Robar da Ladidi ta jika ganda ciki matar Malam ta yi kwallo da ita tana fadin"Ga rashin kunyar nan na siyo miki, banza mai kirar samudawan farko."
"Jar uban nan, zaku wa kisan kin zubar min da nama wallahi."
Maman Ladi ta mike tace "Ku dakata don Allah, meyasa baku da hakuri ne, ace kullum sai kunyi abun fade cikin unguwa?"
"Maman Ladi ba ruwanki cikin wannan magana, kina gani ta zubar min da ganda."
Shewa su Abule suka sa ita da Mairo jin Ladidi tace ganda. Wanda hakan ya kara tunzura Ladidi ta daga kafa ta sauke kan tafashen kajin matar Malam, sai ga kaji zube a kasa. Ruwan ya zuba kan kafar Inna Talatu, ai kuwa ta mike ta dauke Ladidi da mari, zafin marin yasa Ladidi cakumar Inna Talatu da fad'a. Matar Malam ta kalli kajinta dake zube a kasa, ta yi kan Ladidi da duka ita ma. Su kuwa sauran matan ba wacce ta yi yunkurin raba wannan fad'a sai ma kara ingizawa suke.
Kiff! Aka watsar da tukunyar tumatir din Abule na tafashe. Tashin hankali ganin wannan aiki ya harzuka Abule ita ma ta kifar da tukunyar tafashen naman Inna Talatu. Ganin haka Maman Ladi ta sunkuci tukunyar namanta ta yi hanyar barin kicin din, tana kawowa kofa matar Malam ta kwashe mata kafa, sai ga Maman Ladi a kasa nama ya watse har tsakar gida.
Yaran gidan suka shigo, ganin nama zube ga Maman Ladi ta kasa tashi, suka sanya wa-wa suna rugawa waje da gudu.
Mikewa Maman Ladi ta yi ta koma cikin kicin din. Shakar matar Malam ta yi suka hau dambe. Naman Mairon Ado Ladidi ta juye ma Inna Talatu gaba daya a jiki. Zafin da taji yasa ta kwalla kara wanda yasa Mairon Ado k'wasa da gudu ta yi daki ta danna sakata tana haki.
Gaba daya sukai kaca-kaca da kicin din, ga duk sun watsar da wuta. Maman Dare ta shigo, ganin ana fad'a yasa ta koma waje da gudu ta yi hanyar gidan mai unguwa ko takalmi babu.
*GIDAN MAI UNGUWA*
"Malam gaskiya ka kyauta da wa'innan kaji, amma da akuya ka yanka mana kasan dai kaji hudu baza su ishe mu ba."inji Jummai.
"Uhm wallahi a kiyayi fushi na a gidan nan, domin babu wacce tsohon ta ya taba cewa Tanko ga ciyawa ka ba dabbobi."
"Kenan Iyayen mu kake zagi Malam?"
"Oho ban sani ba, nidai a kular min da nama ko kafar kaza bance a ciba idan an gama ni zan raba abuna da kai na."
Hannatu dake zaune ta yi tagumi ta doka tsaki. Jin tsakin ya sa mai unguwa juyowa yana fadin "Yar matsiyata kinyi ma mai alewa."
"Matsiyaci shine wanda bai san ya wadata iyalinsa ba."
Aikuwa mai unguwa ya mike ya nufota, ganin haka Jummai ta shiga tsakani tana aikamai da mugun kallo. Sanin idan ya tanka bazai ji dadi ba yasa ya juya yana fadin" Shegu mayu kawai, kuma ni zan dafa kajina da kaina yau billahillazi." ya karasa bakin murhu ya dau mafici yana fifita wuta.
Babu wacce ta kuma kula shi duk mikewa suka yi suka kama sauran ayyukansu na gida.
Shi kuwa mai unguwa cire malun-malun dinshi ya yi yana fifita wuta. Nama ba ruwa sai kamu yake amma bai masan yana yi ba. Matan najin yanda naman ke konewa sukai banza dashi.
Maman Dare ta shigo da gudu wanda hakan y tsorata mai unguwa ya mike zai gudu, ta dakatar dashi ta hanyar fad'owa gabanshi tana haki hade da fadin"Sun kashe sun kashe."
"Ke wa suka kashe?" ya daka mata tsawa.
"Don Allah mai unguwa kazo sun kashe kansu a gidan mu."
Jin haka ya fahimci mai take nufi don haka yaja tsaki "Babu inda zani su kara nakasa ni alkur'an."
"Don Allah kazo wallahi sunyi barin nama yara nata diba fa."
Jin ta ambaci nama yasa ya saba babbar riga yace" Muje na gani." suka fice bayan y babbaka m tukunyar naman shi wuta.
*Mezai faru kenan ga mai unguwa ya kuma komawa gidan 'yan haya, bayan yace bazai kara zuwa ba.*
0 comments:
Post a Comment