Matan shi na dak'i suna ji har ya fita, babu wacce ta kalli tukunyar naman.
Lado ya yi sallama hannunshi rike da bakar leda. Suka amsa mishi ya zauna bayan ya gaidasu, ya ajiye ledar yana fadin "Gashi nama ne na siyo muku na cika ciki."
Murna sosai suka yi suna fada mishi 'yanda suka yi da mai unguwa kan nama. Dariya ya yi sosai ya mike" Na wuce ba nasan yazo ta sameni gidan nan." Nan ya tafi abun shi.
"Maman Sani mu dafa mu boye kafin ya dawo." cewar Hannnatu.
"Basai kin fadi ba yanzu zamu dora mu raba, idan ya dawo ya dau nashi naman."
Suna hira suna aiki ko kallon naman mai unguwa basu yi ba.
*CIKIN GIDAN 'YAN HAYA*
Dambe ake na kin karewa, gashi duk sun tattake naman da tumatirin da suka zubar.
Maman Usman na dak'i tana girki, duk abun da suke tana jinsu ta yi banza dasu, domin tasan halinsu.
Inno ce tsaye gefen rijiya tana kwashe sauran naman Maman Ladi da ya zube. Jin saukar duka ta yi bayanta wanda ya haddasa zubewar naman hannunta.
Maman Ladi ce ta kai mata wannan duka bayan ta baro matar Malam cikin kicin ko motsi ta kasa yi. Cikin bala'i Inno tace "Maman Ladi ashe ke matsiyaciya ce ban sani ba, taya ina kwashe miki zakiyi min wannan duka?"
"Na zata ai cikin namanki zaki zuba yi hakuri."maman Ladi ta fadi tana haki.
Watsar da naman Inno ta yi tace "To don kaza-kazan mata na fasa kwashe wa."
Kau! Maman Ladi ta kwashe ta da mari, cikin huci take fadin" Ba a haifi matar da zata zageni ba wallahi don ubanta, nice nan Maman Ladi murucin kan dutse an buga an barni."
Nan sabon dambe ya kaure dai-dai shigowar mai unguwa. Aikuwa yana zuwa ya hau rabo yana rokon don Allah su bari, amma ina kamar basu ganshi ba. Gashi sai take nama suke yi, can ya leko kai cikin kicin da niyar ganin mai na ciki keyi. Saukar ruwa yaji a fuskar shi wanda ya haddasa daukewar ganinsa na wani lokaci.
Jin ba ruwan zafi bane ya sanya mai unguwa bude ido tare da goge ruwan fuskar shi da rigarsa. Inna Talatu ce ta watso ruwan da nufin ya sauka kan Ladidi, ganin bai zuba inda ta watsa ba yasa ta kuma daukar tukunyar ta nufi Ladidi ta k'wada mata. Mai unguwa na tsaye yana kallon wannan rikice ya rasa yanda zai yi ganin da gaske fad'a suke ba kakkautawa.
Matsawa ya yi kusa da dak'in Maman Usman yana sallama. Tana ji ta yi shiru domin ta gaji da rabon fad'a. Jin mai unguwa nata doka sallama yasa ta leko tace "Kayi hakuri mai unguwa, bansan ya zanyi su daina ba ni kaina takaicin fad'an nake wallahi."
"A'a Maman Usmanu baza mu barsu su kashe kansu ba, ki taimaka ki fito don Allah."
Jin magiyar mai unguwa yasa ta amince ta fito. Matar Malam na kwance ta kasa motsi sai taka ta suke yi. Maman Usman ta shigo ta daga ta da taimakon Abule suka fitar da ita suka aje ta kan dandamalin kofarta.
Maman Usman ta shiga tsakanin Ladidi da Inna Talatu ta rabasu suka fito waje, ta kalli yanda kicin din ya yi kaca-kaca da nama da kuma tumatiri. Girgiza kai ta yi tana takaicin halayyar matan gidan.
Duk suna tsaye ga mai unguwa dake yi musu fad'a da sunan nasiha. Maman Ladi ta kalle shi cike da takaicin fad'an da yake musu tace "Dalla malam rufe mana baki."
"Walle wanga mai unguwa gulma ta dashi, sai kace shi na da wanga gida." cewar Abule tana aikamai da harara.
"Billahillazi zanyi karar duk shegiyar data kuma zagina, kaji mahaukata ana yi..."
"Kaine mahaukaci wallahi ba dai mu ba, banza mai bakar fuska." Ladidi ta katse shi.
"Uban ki ne banza ba Tanko ba matsiyaciya mai zubin munafukai."
"Kai kuma mai zubin 'yan wuta ba." cewar Inna Talatu.
Takaici ya cika Maman Usman dake tsaye tana kallon duk abun da suke yi. Ganin abun nasu zai yi kamari ga mai unguwa kamar zai yi duka yasa ta daka musu tsawa. Duk sukai shiru suna kallon ta.
"Sai yaushe za kuyi hankali, ku gane abun da kuke bai dace da ku ba?, yara gare ku fa kuma tarbiyyar ku shi zasu dauka na roke ku don Allah ku yi ma kanku karatun ta natsu, ku gane zaman lafiya yafi komai dadi."
"Kiyi hakuri Maman Usman zamu gyara." cewar Mairon Ado dake tsaye jikin kofarta.
Sauran shiru suka yi suna hararar mai unguwa jin yana fadin " hankali ne bai ishesu ba shiyasa suke wannan haukan."
"A'a mai unguwa kai babba ne bai kamata kana fadin haka ba"
"To Maman Usmanu ayi hakuri, amma dubi yanda suka wulakanta nama kamar ba kudi aka sanya aka siya ba, dubi kiga matar Malam zube ko motsi ta kasa."
"Dadin abun mazajen mune suka siya mana, ita kuma matar Malam gulma ya kawo ta." Maman Ladi ta fadi tana jefa mai mugun kallo.
"To nidai na fada muku kuyi hankali domin watarana duk bama nan." cewar Maman Usman ta shige dak'i.
Ganin Maman Usman ta wuce yasa mai unguwa shima ficewa yana sababin anci mutuncin nama.
Sanin cewa sunyi ma juna ta'asa ya sanya babu wacce ta nemi a biyata namanta ku tumatir. Mai saura ta deba ta cigaba da girka wa.
*GIDAN MAI UNGUWA*
Matanshi sun gama nasu girkin tsaf sun raba, inda suka bar mishi nashi bisa wuta ko dubawa basu yi ba. Suna zaune suna hira ya shigo da sallama.
"Barka da dawowa Malam." cewar Hannatu tana dariya kasa-kasa ganin jikin shi duk ruwa.
Banza ya mata ya wuce tukunyar naman yana duba wa.
"Jakar uban nan, yanzu dama duk bakin ciki kuke dani ko, arzikin da tsohon ku bai dashi kuke wulakanta wa ko?, kaji tun dazu dana fita babu shegiyar data duba min."
"Haba Malam! Haba Malam! kai fa kace kar mu taba amma yanzu ka zo kana zagin iyayen mu?"
"Na zaga Jummala, nace na zaga akwai 'yar kwal uban da zata rama ne?, shegu masu zubin ifiritai."
Sanin idan suka biye shi makota na iya ji, yasa Jummai ta yi ma Hannatu alamun ta yi shiru.
"Kuma wallahi Allah ya isa tsinannu kawai, zanga uban da zai baku abinci yau a gidan nan. Kuma wallahi sai na kai karar ku gun ubannin ku, ko wacce sai ubanta ya biyani kazata data kone." ya fadi yana facali da tukunyar ya yi waje.
*GIDAN 'YAN HAYA RANAR LARABA*
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*'Yan uwana abokan aiki wannan shafin ya zamu naku kyauta wato Zamanawa masu karamci, mutane masu halin dattako, ina gaisuwa the musamman gareku. Allah ya daukaka Zamani ya kara hade kanmu.Ina son ku sosai domin kodayaushe Kuna fadakar da al'umma da dunbin basirar ku, Allah ya kara basira ya kare mu daga sharrin mahassada ameen. One Love ZAMANI WRITERS*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*50~55*
*GIDAN 'YAN HAYA RANAR LABARA*
Suna ta aikin su, duk sun shirya da juna a nata raha ana dariya. Inno ta fito zata je unguwa tace "Mutan gida da alheri zan tafi sai na dawo."
"Adawo lafiya dillaliya."duk suka fadi.
Tana fita Ladidi tace" Tabdijam! Kunga atamfar da Inno ta saka kuwa?"
"Uhm Ladidi aini mamaki ya hanani magana, yaushe Inno ta yi kudin siyan wannan atamfa?" cewar Inna Talatu tana tafa hannu.
Shewa Mairon Ado tasa suka tafa da k'awarta Abule da suke zaune kullum tare. Tace "Mijinta ya siya mata ai tun wancan watan ta nuna min."
"Kwarankwatsi bari yallabai dawo dole nima ya siyamin."Ladidi ce ke wannan magana.
" Ayerere ina mijin ki yaga kudin siyan wannan atamfa?"
"Haba Maman Ladi wallahi kinsan dai yafi mijin Inno samun kudi."
"Amma bai fi shi zuciya ba ko?"Mairon Ado ta tambaya.
A hasale Ladidi ta juyo tana kumfar baki "Ke Mairo idan ina magana ki daina saka min baki kwarankwatsi kona miki shegen duka."
"Da shike an hwadi miki ina barin ki ki taba Mairo kawata ko?" Abule ta fadi tana hararar Ladidi.
Maman Ladi ta yi dariya tace "A'a fa dama kwana biyu mai unguwa bai shigo ba, da alama yau zai shigo."
Dariya suka sanya dukkansu sanin cewa ko wacce da tanadin dake ranta game da mai unguwa.
" Inno ta saka atamfa mai tsada, idan kuna da zuciya gobe kuma ku siya."cewar matar Malam dake fitowa daga dak'inta.
"Fadi ma mai zuciya zuwa biki ba mai abun kai wa ba matar Malam, domin ina da kudin da zan siya sofa waz wallahi."cewar Maman Ladi don tasan da ita matar Malam take.
Dariya ta kama Inna Talatu ta dinga yi, suna ta kallon ta har ta tsagaita tace "wallahi Maman Ladi kina burgeni super wax ake cewa fa ba sofa waz ba"
"Yo sai me dan ban iya fadi ba, na dai san nafi wasu kidahuman."
Nan ko wacce ta daure fuska, ita kuma Inna Talatu ta dinga dariya tana tsugunne kusa da injinta.
"Mairon Ado hala ke baki taba yin boko bane?"
"Babana ya hanani matar Malam, da yanzu na wuce wulakanci."
"Ke Mairo walle ni kuwa nayi boko har aji biyu walle kafun ankayi mun amre da Haladu."
"Iyye ashe Abule anyi boko har aji biyu?" Inna Talatu na dariya.
"Talatu zanci ubanki idan baki daina ma mutane dariya ba, matsiyaciya kawai kin tasa mu gaba kina dariya kamar wacce hau ya hau kanta." cewar Maman Ladi.
"Banda zagin iyayena Maman Ladi bana san wulakanci."
"Na zage ki din, ko za ki rama ne Talatu?"
"Ku dakata haka, abun raha ne ba fad'a ba sababbu."cewar Ladidi.
"Ina raha anan Ladidi ana zagin iyayen ka?"
"Abar maganar haka don Allah ya wuce babu fad'a."
Haka kuwa ko wacce ta kama aikin ta.
*GIDAN MAI UNGUWA*
Yana zaune kofar gida ya yi tagumi. Abokin shi malam Kallah yazo ya zauna kusa dashi yana fadin "Ranka-ya-dade fatan dai lafiya kayi tagumi haka?"
"Ina fa lafiya Kallah?"
"Ashsha Allah ya sauwaka, mai ya faru?"
"Wato Kallah idan Allah ya baka mata irin nawa, na tabbata mutuwa zaka yi."
"To babbar magana kenan dai mata ne suka tasa ka gaba Ranka-ya-dade?"
"Kwarai kuwa matan gidana Jummala da Hannatu duk munafukai ne, don yanzu zakai fad'a da wannan idan kaje wurin dayar to billahillazi ita ma fad'a zaku yi."
"toh na gane, kenan sun hade kai?"
"Kamar kashin awaki kuwa."
"wannan ai abune mai sauki, kawai aure zaka kara."
Da sauri mai unguwa ya dubi shi yana zare idanu "Aure fa kace Kallamu?"
"Kwarai kuwa aure zaka kara, kuma yarinya zaka auro."
Shiru mai unguwa ya yi can kuma yace "To ina zan samu matar auren Kallamu idon gari?"
"Don wannan ai mai sauki ne, Ladi kawai zaka samu ka aure ta."
"Wacece Ladi kuma?"
"Diyar Maman Ladi ta gidan 'yan haya."
Zabura mai unguwa ya yi yace "Kallamu baka kaunar farin ciki na billahillazi, ban da haka ta ina zaka hadani da wannan matar mai kirar samudawa kace na aure diyarta?, matar da ko mutuncina bata gani?"
Kallah ya dubi mai unguwa yana dariya" Ranka-ya-dade ai uban yarinyar yana iya komai kan kudi"
"Kenan zai bada diyarsa don kudi?"
"Na rantse maka zai bayar, amma ga wata shawara." ya matsa sosai kusa da mai unguwa sukai kus-kus, dariya suka sanya. Mai unguwa na fadin "Haka za a yi Kallah shawara mai kyau, nagode sosai Kallamu idon gari zan same ka gobe."
"To Allah ya kaimu."
Sukai sallama ya wuce, shi kuma mai unguwa ya shiga gida cike da farin ciki.
*Tabdijam! Wata sabuwa kenan, muje zuwa..*
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
Dedicated to
*GSS Dr. Ahmad makarki hayin Banki kawo. Ina mutukar alfahari daku sosai duk inda kuke, Allah ya kara ilmi. One love 2013*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*55~60*
Mai unguwa na shiga gida ya nemi wuri kan turmi ya zauna, yana cika yana batsewa shi ga mai gida sai zare ido yake. Ya dubi matan ba wacce ta kalle shi ya yi kwafa yace "Na kusa kawo karshen wulakanci a gidan nan."
Babu wacce ta kalle shi sai aikin su suke ta yi.
" Jummala zan kara aure kwananan nan billahillazi."
Duk suka kalle shi cike da farin ciki kwance kan fuskar su, Hannatu tace "Kai amma naji dadi wallahi, yaushe ne bikin Malam?"
Harara ya daka mata" Munafuka mai bakin hali kawai, harda murna ko?, to billahillazi ba da wasa nake ba."
"Malam ai murna muke yi zaka kara aure shiyasa muke tambaya." cewar Jummai.
"Lallai matan nan iyayen ku sun koya muku mugun hali, inace idan za ayi ma mace kishiya haushi take jin, amma ku don tsabar algungumai ne wai murna kuke ko?"
"Malam kenan mai hali bai canzawa."
"Ke Jummala alqur'an ki fita idona, bazan canza halin ba inga uban da zai can zani."
"Allah ya baka hakuri." ta shige dak'i, ganin haka Hannatu ma ta shige dak'i tana hararar shi.
"Duk zaku gane kuranku billahillazi bari na auro yarinya danya sharkaf ku gani." ya kakkabe rigarsa ya fice daga gidan yana sababi.
*CIKIN GIDAN 'YAN HAYA*
Kwana biyu anyi sauki da fad'a, ana zaman lafiya gidan yasha iska. Ko wacce na sana'arta cikin lumana, mazan su na cikin kwanciyar hankali.
Gashi an fara wahalar ruwa kuma babu na fanfo, da kyar ake samu a rijiya. Da asubar fari suke rige-rigen fitowa dibar ruwa a rijiyar, kowa na kokarin ya ri ga wani diba, idan ka ri ga tashi ka diba sai a dinga hararar ka ana yada habaici.
Yau duk suna dak'i basu fito ba, sai matar Malam tana zaune tana wanke-wanke hanyar fanfo ita kadai, kawai taga an kawo ruwan fanfo. Da sauri ta karasa ta kashe fanfo tana waige kar wani ya ganta, ta ruga dak'i ta kwaso robobinta masu yawa ta nufi fanfo. Ta dinga tarawa tana cikawa. Jin karar zuban ruwa yasa Maman Dare lekowa, aikuwa tana ganin ruwan fanfo ne ta koma dak'i da sauri ita ma ta debo kayanta harda tukwane ta nufi fanfo, daga ita sai matar Malam ke jidar ruwa suna kai wa dak'i.
Abule ta fito zata bandaki ita ma taga wannan al'amari, amma maimakon ta yi yanda sauran suka yi na yin shiru, it kurma guda ta yi tana sanar da mutan gidan an kawo ruwan fanfo. Da sauri suka dinga fitowa da manyan robobi suna rige-rigen bin layi. Haushi ya kama Maman Dare ganin gayyar da Abule ta yi musu tace "Shegiya mai hankali a hannun riga." matar Malam ta fashe da dariya "Banza ce ai bata da nutsuwa."
Ba wacce ta kula su, kowa so yake ya samu ruwa. Maman Ladi ta ga alamun za a raina mata hankali ganin harda tukunya ake diban ruwa, gashi bata da ruwan ko kadan dan haka tace "Yakama ta kusan me kuke yi, kubari muma mu diba gaskiya."
"Maman Ladi a dai bi layi sannu a hankali zamu samu." cewar Inno.
"A'a Inno duba fa ki gani harda tukwane dan bakin ciki ake dibar ruwa."
"An saka ayi yanda za ayi damu." cewar matar Malam.
Shiru Maman Ladi da Inno suka yi basu kara magana ba, ganin Iya beji na hararar matar Malam. Can dai da suka ga zasu iya rasa ruwan, Iya beji ta kutsa ta warce tukunyar hannun Maman Dare ta yi jifa dashi ta aza nata robar. Maman Dare ta kalle ta ta kalli tukunyarta dake yashe a kasa tace " iya beji nawane fa bana matar Malam ba kika yadda."
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*Wannan shafin na kune hazikan masana, jagororin adabi, _MARUBUTA GROUP_ gaskiya bani da group a whatsapp dake ilmantar da al'umma da kuma koyar da zallar adabi irin ku, ina alfahari daku a kodayaushe fatan alheri ga ilahirin al'ummar wannan gida, Allah ya kara daukaka ya bar zumunci mun gode.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*60~65*
Harara Iya beji ta zabga nata, "Ai nasan na kine shiyasa na yarda shi."
"Lallai ma Iya beji, mun ri ga ki zuwa layi ai." cewar Inno.
"Baku damu ku samu ruwa ba, ai wuri kuka samu ku ka tsaya."
"Dalla can matsa min." Maman Ladi ta bige robar hannun Iya beji ruwan y zube, ta sanya nata robar.
Haushi ya kama Iya beji ita ma ta kifar da ruwan Maman Ladi. Nan fa fad'a ya kaure tsakanin su, Abule ganin yawanci hankalin su na wurin rabon fad'a yasa ta dinga jidar ruwan tana kaiwa dak'i. Maman Dare ta yi dariya ita ma rabi sahun Abule, lura da hakan da Inna Talatu ta yi ne yasa ita ma ta tara robarta bakin fanfo, aikuwa Matar Malam ta kifar da shi tana fadin"Algungumai kun wani zo kuna jidar ruwa kamar.." Mari aka sauke mata wanda ya tilasta mata yin shiru. Inna Talatu ce rike da robarta tsaye tana hararar matar Malam, "Kece dai algunguma bani ba, banza kawai mai halin matsiyata."
"Talatu ni kika mara?"
"Kina da abun yi ne?"
Haba sai fada kuma ya tsarke, suna yi suna jifar juna da robobin ruwa. Maman Ladi ta yarda Iya beji kasa gashi wurin duk ruwa ne, aikuwa ta bugu sosai ta kasa tashi. Maman Dare nasan shiga kuma tana tsoro don haka ta je taimakon daga Iya beji wanda ya yi dai-dai da Matar Malam ta jeho bokitin karfe ya sauka kuwa kan Maman Dare ta zube kasa jikin Iya beji. Kuka Iya beji tasa tana tsine masu Maman Ladi, da kyar Maman Dare to mike tana dafe da kanta ta taimaka ma Iya beji ta mike.
Hayaniya da fad'a sosai suke yi a bakin fanfo. Shigowar Malam Lawal mijin Maman Ladi ne ya sanya Maman Ladi barin wurin da sauri ganin shi da manyan ledoji a hannu, ta amsa tana mai sannu da zuwa. Washe baki ya yi yace " ke kam kin iya haihuwa wallahi, wannan arzikin duk dalilin haihuwa ne."ya fadi tare da shigewa dak'i.
Gudar da Maman Ladi tasa ce ta dakatar da fad'an da matan gidan ke yi, suka juyo suna kallonta. Yara suka dinga shigowa da kayan abinci suna zubewa kofar Maman Ladi.
Ladidi ta karaso tana fadin " Maman Ladi wannan kayan fa?"
"Ahayye duniya Ladidi gulma, to bari naje dak'i na tambayi wanda ya kawo sai nazo na baki satonri (story)" ta shiga dak'i ta same shi.
"Baban Ladi ina ka samu kaya haka?"
"Kedai bari uwargida kayan toshen Ladi ne, wani attajiri ya ganta shine dazu y kirani ya ban wa'innan kayan."ya fadi yana kirgo kudi a aljihun 'yan dari biyu. Maman Ladi t warce kudin tana cewa"Wannan rabo na ne kenan ko?, nasan dai an baka naka."
"Kayya Maman Ladi kina da gajen hakuri baki zanyi dama wallahi, yanzu yaushe zamu sanya bikin?"
"Sati biyu kawai za a saka saboda mahassada malam."cewar Maman Ladi.
Gyada kai ya yi yana gyara aljihun shi wanda ke damke da kudi.
Galala matan gidan ke bin kayan da kallo kamar makafi sun warke makanta, nan suka fara kus-kus aka manta da batun fad'an ruwa. Fitowar Maman Ladi daga dak'i tana washe jajayen hakoranta yasa suka marmatso kusa da ita domin jin kanun labarai.
"Ladi ce zata auri wani attajiri shine aka kawo wa'innan kayan, ku duba harda su buhun shinkafar waina wallahi na samu karin jari."
"Yanzu Ladi nawa take da zaki aurar da ita?"
"A'a Talatu kardai kina bakin ciki kan wannan abun arzikin dana samu ne?"
"To wani mai arziki kenan zata aura?" matar Malam ta yi tambayar.
"Sai ranar auren zaku sani, nan da kwana goma sha hudi zaa yi bikin."
Nan aka dinga cafta ana duba kayan arziki, Inno da Inna Talatu muraran suke nuna bakin ciki kan kayan, yayin da Maman Dare wacce har gefen goshinta ya kumbura sanadin wannan bokiti ke nuna ma Maman Ladi illar auran. Iya beji dama data samu ta tashi dak'i ta wuce da alwashin sai ta rama.
Maman Ladi kuwa sai rawar kai take tana nuna isa da takama diyarta zata aure mai arziki.
*MAI UNGUWA*
Matan mai unguwa sai murna suke ganin ana gyara dak'in amarya, suna fatan zasu huta da wannan masifar tashi. Sun tambayeshi wacece amaryar yaki fadi musu wai kada suje suyi mai munafuncin da suka saba, shiyasa suka saka mai idanu suna kallon duk abun da yake yi.
Mai unguwa zaune a cikin zaure tare da Baban Ladi.
"Kai Lawal nawa ne sadakin?, sannan ka tabbata wannan shegiyar matar taka bata san ni zan auri diyarta ba." cewar mai unguwa.
"Ka bada jaka goma Ranka-ya-dade, kuma na rantse maka bata sani ba ce mata nayi wani attajiri ne."
Haka ya kirga ya mika yana washe baki ya kusa zama ango.
Shikuma Malam Lawal gida y nufa ya damka ma Maman Ladi kudin sadakin, ita kuma ta mika ma Inno dillaliya data kawo mata kayan gado da dorowa. Ana ta shirye-shiryen aure sai gyara amarya Maman Ladi take, yayin da matan gidan wasu ke bakin ciki wasu kuma suna taya ta murna.
Sosai Maman Ladi ta shirya ma wannan aure ganin kudin sadaki jaka goma wanda a tarihin unguwar ba wanda aka taba ba irin wannan kudin matsayin sadaki. Hidima sosai matan gidan ke ta yata kama daga kan alkaki, dubulan, nakiya, da sauransu.
*RANAR AURE*
Ranar gidan 'yan haya ya cika sosai, domin gayyata Maman Ladi ta yi na auren tilon diyarta. A nata hidimar girki, amarya ansha atamfar batik cikin kayan auren da mai unguwa ya aiko.
Karfe biyu aka daura auren Zainab wato Ladi da ango Nasiru Tanko mai unguwa.
Maman Ladi anci kwalliya ana tsakiyar jama'a wannan sakon the isketa, a hargitse take tambayar "wani mai unguwa aka ba auren Ladi?"
"Wanne kuwa bayan mai unguwa Tanko."cewar Inna Talatu dake tsaye bakin kofa.
Ai a tamanin Maman Ladi ta fito tana kwallo da duk abun da tagani a hanya, tamkar zararra tana kwalla kiran sunan Baban Ladi. Mutane da aka gayyata suka dinga kallonta domin basu san komai ba, matan gidan kuwa sai yamadidi suke da ita suna dariya.
Shigowar su kenan daga wurin daurin mazan gidan, Baban Ladi na gaba suna biye dashi a baya.
Yana sako kai yaji an shake shi sosai ba da wasa ba, kokari yake ya ya kece daga rikon amma ya kasa. Maman Ladi data yi shakar ta wanke shi da mari tana fadin " munafuki macuci kace min wani attajiri zai auri Ladi, ashe wancan shegen ne to wallahi sai an warware auren nan muddin kana bidar zaman lafiya dani."
Juya kai kawai yake yana kokarin kwace wa daga rikonta, mazan nata aikin bada hakuri inda matan dake wurin suka maidata tamkar talabijin suna ganin ikon Allah.
Da kyar ta sake shi, aikuwa yana jin yasha ya sa kafa sai hanyar waje yana fadin "Na rantse da Allah aure ya auru naga uban da zai kwance shi mahaukaciya kawai."
" Zaka dawo ai wallahi zaka san da Hajara uwar Ladi ka yi a gidan nan".
*INA LABARIN ANGO MAI UNGUWA TANKO??*
0 comments:
Post a Comment