JARABABBEN KISHI part 1 Posted by Bashir Sani Fesan on 16 Dec 2016 - 13:53 Hannunta ri'ke da bindiga ta setashi akan rawanin dake kan waliyyin da ke shirin d'aura auren mijinta da wata macen tana mai cewa "wallahi tallahi ka kuskura ka d'aura wannan auren,sai na d'aura ranka da mutuwa"! Cikin muryar mai d'auke da tsawa mijinta ya mi'ke yana cewa "ke menene haka kin haukace ne? meye kawo ki nan gurin? wannan ai dabbanci ne". A zafafe ta katseshi ta hanyar cewa "idan akan soyayyarka ne na cancanci in amsa sunan dabba domin bana gani bana ji kuma bani da hankali, akan sonka ina iya aikata komai ko da kuwa d'aukar rai ne, bana 'kaunar ko wacce mace ta ra6eka ko da kuwa ta kasance muharramarka ce, ina kishinka mijina, kishina ya bambanta da kishin da ka sani ina maka kishin da bana kaunar ko da jaririyace tayi maka murmushi ka maida mata martani, mijina me ka nema ka rasa a guna da kake shirin kulla alaka irin tamu ni da kai da wata? duk wani kyautatawa da kulawa da mace ta ke wa mijinta ina yi maka, ta ina na tauyeka a zaman aurena da kai? a zamana da kai sai dana tabbatar na maye maka duk wani gurbi a zuciyarka, me ka nema ka rasa a guna? ta ina na gaza?". Ta tambayeshi idanunta na zubar hawaye. Cike da bacin rai yace "ra'ayi! domin ni ban shirya zama da mace d'aya tilo ba, ra'ayina ne kawai in 'kara aure,saboda Allah da manzonsa [s.a.w] basu haramta ba!'' ya bata amsa A fusace, ta maida bindigar kan goshinsa tana cewa "ra'ayi ko dai *JARABA* irin taku ta maza? toh wallahi tallahi idan har ba'a fasa d'aura aurenan ba sai na kasheka,inya so ni da ita mu rasa ka Idan kai *JARABA* ce tasa zaka 'kara aure toh ni zanyi amfani da *JARABABBEN KISHINA* da nakeyi akan ka in da'kushe duk wani tasirin *JARABAR* dake d'awainiya da kai". "Keeee dakata nagaji dajin munanan kalamanki akaina *SUHAYR* meyasa kika dau kishi kumallonki bayan kinsan irin soyayyar dake tsakaninmu?". " *SAHEEB* bakada abunda zaka iya gamsar dani a halin yanzu, amma naci alwashin ruguza aurennan inko ba haka ba yanzu za'a haifi dan daba idoo". Tuni waliyyi da sauran jama'a suka arce don baxasu yarda ayi musu sawarwarin rayuwarsu ba. *LABARIN SUHAYR DA SAHEEB*I novels / JARABABBEN KISHI part 2 JARABABBEN KISHI part 2 Posted by Bashir Sani Fesan on 16 Dec 2016 - 13:57 Suhayr takasance ya ta biyar daga cikin yayyinta maza da take bii daga ita sai autansu, a wajen iyayenta *Alhaji kabir sulaiman da kuma hajiya ikilima* Mahaifinta yakasance hamshakin mai arziki kuma babban Dan siyasa da'ake damawa dasu acikin gwamnati mai ci, suhayr takasance yar gaban goshi sannan duk abunda zatayi a wajen mahaifinta daidaine, Bayason ganin bacin ranta hasalima dayaga bacin ranta gwara a kunduma mishi ashar, hakan yasamo asaline saboda ita kadaice yarsa mace. Amma kuma takasance mai ladabi ga duk Wanda ya girme mata atakaice zamuce tanada ladabi da biyayya gana gaba da ita. Wata asabar ne sakaliya suhayr ta tashi da dokin zuwa bikin kawarta wacce sukayi Hassan Gwarzo tare, ta shirya tsaf ta shiga dakin mummy don tayi mata sallama, tace "Mummy yakika gani ,shigannan tayi?" Ta fadi tana fari da ido, hjy ikilima murmushi tayi tace "my beautiful daughter you are such a pretty damsel, Allah ya azurtaki da miji nagari Wanda zai kula da surar da Allah ya azurtaki da ita," Tsalle tayi tace "Mummy kina fasamun kai sainaji duk duniya babu wata ya mace datakaini". Mummy tace "tabbas hakane babu koda ita aikam sai ansamu banbanci ko wajen shafa jambaki, Maza yata Allah ya tsare ga wasu yan kudi kibiya koda shop rite ne ki siyamata gift Wanda zaki kaimata". Ta amsa tare da cewa "toh ngd umma Allah yakara girma da tsawon kwana da daukaka" "Amin!" Tuni aka wanke motar dazata fita dashi tana baya direba na tuki a gaba saida sukayi siyayya kana suka wuce *GOLDEN DRAGON* *dake hanyan nasarawa G.R.A inda ake friends Eve* Tun a waje taga wani gaye Wanda kunnenta yajiyo mata sunansa SAHEEB dagani ba tambaya kanwarsa ya rako wajen, tuni taji ya shiga ranta yadda bazata iya rayuwa inba dashi ba. Wucewa tazo yi tace "hey" ko kallonta baiyi ba saboda bawata mace a gabansa inba HUMAIRAH ba wacce aski yariga yaxo gaban goshi bikinsa saura wata biyu. Rashin amsatan da baiyi ba bai wani bata mata rai ba illah wani sonsa dataji yake shiganta kaman yarda iska ke ratsa mutun idan yana bakin rafi. Da shigarta tanata ware ido don ta hango kanwarsa taxauna kusa da ita don dakwai tambayoyi data tanada zatayi mata akan SAHEEB. Can ta hangota kusada amarya maryam wadda suna ganin juna sukayi wani irin shewa aka tuno da school life, janta tayi gefe tace "ke waccan yarinyar kawarkice?" "Eh" maryam tace, Suhayr tace "wallahi wani naganta dashi kaman Dan uwanta wallahi am in love, pls help me kinsanni idan inason abu gaba daya nake ruftawa". Maryam tace "Kash suhayr ai kinyi latti inajin bikinsa bai wuce saura wata biyu ba,"ARABABBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 3 JARABABBEN KISHI part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 16 Dec 2016 - 14:00 Suhayr ta cigaba da cewa "Pls maryam just tell me u r joking ?" Maryam tace "haba suhayr yaushe muka fara yar wannan dake kinsan cewa I can't lie or tell you a joke,it's the truth u better accept it or leave . "Ohsshh' suhayr ta furta sannan tace "yazanyi kenan?" daidai da zuwan wasu friends din maryam hakan yasa ta dubi suhayr Tace "am coming nayi baki". suhayr kujera ta samu ta zauna saboda kafafuwan ta suna Neman kasa daukanta, dafa kanta tayi gaba daya taji ranta yabaci wani irin kishine ke bijiro mata, Wanda bashida maraba da leben wuta..... Ahaka aka fara event amma gaba daya hankalinta da tunaninta yana wajen Saheeb Wanda yaketa zuba love acikin waya shida masoyiyarsa Humairah, Inyana tareda ita gaba daya jinsa yake kaman ba'a duniyaba, saboda dadadan kalaman da Humairah take tanada kullum don ganin farin cikin hubbinta. Daga ciki suhayr tana kallonsa daga waje yadda farinciki da annashuwa yake dawainiya dashi. "Oh ni suhayr mezanyi ganin na lalata alakar dake tsakanin sa da wadda ake ikirarin zai aurah?". Tambayar da takewa kanta kenan agun. "yes!!" tuni wata dabara tazo mata direbanta ta kira tace yadan zagaya tunda bayanxu zasu gamaba. Bayan yan mintuna ta fita harabar waje bata nufi ko inaba sai wajen da Saheeb ke tsaye jikin wata mota, "Salamu alaikum!" tace amma ina yayi nisa, Ta kara masa sallama shiru har saida ta buga saman motan sannan ya juyo. "Yi hkr gimbiya zankiraki yanzu", yana juyowa sai yakasa koda motsi saboda kyawun sura da Allah yayi mata, amma ina is too late to cry went the head it cut off. "Yah lafiya ?" Ya jefe ta da tambaya, Tace "Wallahi nayi running out of battery ne inaso inkira direbana ne, daga yaje yadawo amma shiru" suhayr ta maida martani. "OK badamuwa gashi ki kira" saheeb ya fadi tare da mika mata wayarsa. Wani murmushi tayi Wanda bashi da maraba da Dana mugunta, a zuci tace "ina matukar kishin Wanda nakeso don haka kana bani tausayi don saina rabaka da ita aure kuwa sai an fasa" matsawa tayi daga gun tare da fara yin wayar bogi, bayan ta gama wayar bogin sai ta juyo ganin hankalinsa ba ya kanta ,hakan yasa ta yi flashin layinta da wayarsa, sannan tadau number Humairah a recoeved calls dinsa, sannan ta juya ta bashi wayar sannan tace "gashi ngd Allah yasaka da alkhairi" sai kuma tace "Dan Allah in bazaka damuba inason sanin sunanka" cike da rashin damuwa yace"OK sunana SAHEEB kefa ?" Da sauri ta amsa da cewa "sunana suhayr kabeer sulaiman", "Waw NYC name" suhayr tayi murmushi tace"in bazaka damuba zanso muzama abokai" tare da kallonsa ido cikin ido saheeb yace "badamuwa ngd" domin yasan cewa fadi take kawai ,ina ma zata ganshi har suyi wata abota! A wannan lokacin tafi kowa farinciki domin plans dinta sunkusa fara aiki, a ranta tace "saina rabaka da duk wata ya mace ,hatta uwar data haifeka, balle kuma kanwa ko yaya indai mace ce, bakai ba ita.a duniyaba, saboda dadadan kalaman da Humairah take tanada kullum don ganin farin cikin hubbinta. Daga ciki suhayr tana kallonsa daga waje yadda farinciki da annashuwa yake dawainiya dashi.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 4 JARABABBEN KISHI part 4 Posted by Bashir Sani Fesan on 16 Dec 2016 - 14:02 A ranar anyi shagali ,nan ta samu shiga wajen nimrah kanwar saheeb saboda ta dinga jin duk wani details, Har wajen mota ta raka nimrah tace "ki gaida su mummy Dan Allah insha Allah zan kawo miki ziyara kamar yadda kikamin kwatance" dariya nimrah tayi tace "Allah yakawoki " suhayr tace "amin" har suka bar harabar wajen tana daga ma nimrah hannu Wanda ba nimrah takema ba da Saheeb take Wanda baima San tana yi ba. Mota tashiga cike da damuwa,direba ya bata wuta. Saheeb yana tuki yace "Nimrah ina kika jajibo waccen yarinyar? karfa ki hada kanki da ita yar gdan masu kumban susace ,kuma kinsan hudubar da baba yake mana, Nacewa mutsaya a matsayin da Allah ya ajiyemu don mu tsira da mutuncinmu". nimrah ta dubeahi tare da cewa' Nasani yaya Saheeb amma itace ta bukaci hakan daga gareni kaga kuma bai kamata na wulakanta taba tunda acikin mutane muke" saheeb ya kaseta da cewa "OK naji, amma nidai nagaya miki waccan yarinyar ta wuce ajinki". nimrah ta bata fuska tare da cewa" "Toh nace naji yaya shikenan" saheeb ya dan dubeta tare da kai hannunsa kan fuskanta yace, "haba my sweet sister don't be upset with me". SAHEEB shine da na farko a wajen iyayenshi sai kanninsa saikuma mata su uku, gabadaya su biyarne wajen iyayensa, Alhaji Garba dan'kolii shine mahaifin Saheeb bawani mai arziki bane amma yanada rufin asiri gakuma wadatar zuciya, Dan kasuwa ne a cikin kasuwar sabon gari dake kano rufuna gareshi Wanda yake saida kayan yari mahaifiyar shi kuwa ZAMAN gda takeyi bata sana'an komai. Yan dangine don zuri'ar Dan koli tanada yawa sannan sun kware a fannin auren zumunchi Wanda hakan yasa yan garinsu ke tsegumi akan cewa iyasu isua tsakaninsu suke ,ba ashiga ba'a fita. Saboda basu yarda bare yazo Neman auren yayansu ba, shi yasa ma aka hadashi aure da Humairah yar gdan wan babansa, Kuma ikon Allah hadin yayi daidai saboda suna kaunar junansu! 鈽� 鈽� 鈽� 鈽� 鈽� Suhayr tunda ta koma gida takasa cin abinchi sai tunani gaba daya yan uwanta sun shiga damuwa ganinta cikin wannan halin, shiko mahaifinta daya dawo daga Abuja ya shiga rudanin ganin halinda take ciki. Ganin sun isheta da tambaya sai kawai ta amsa musu da cewa "da tambayoyinnan dakuke mun kawai Ku tayani da Addu'a don a yanzu ita kadai nake bukata daga gareku" Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ,yayin da suhayr bata da aikin yi illa a kullum ta kira Humairah da boyayyen number tana yi mata barazanar saduwa da mutuwarta in har matukar bata fasa auren Saheeb ba. A bangaren Humairah tana ganin abun kamar wasan kwaikwayo amma daga baya taga abun yana Neman fin karfinta, ganin a kullum in ta fita sai suhayr ta bugo tace mata ta ganta waje kaza. Hakan yasa bashiri tasawa iyayenta kuka tana cewa ita gaskiya bazata auri saheeb ba saboda ana baraxanan kasheta. Mahaifinta ransa a bace yace "Baki isa ba domin ba'a taba yar da taki auren Dan'uwanta a danginmu ma kuma baxaa fara a kanki ba" Kwatsam saiga wayar humairah na kara ,jikinta na rawa ta dayka tare da cewa" hello" a tsorace ,a daya bangaren muryar suhayr ce take cewa "Kin janye, ko kuwa saina karar da danginku daya bayan daya sannan in nannadeki, sanin kanki ne cewa saheeb baxai aureki da munin halitta". humaira bata san lokacin da bakinta ya fara fadin "wallahi na hakura na rabu daShi koda kuwa shine autan maxa" Dayake a loudspeaker tasa kuma iyayenta sunji komai, hankalinsu ya tashi, Ba tareda bata lokaci ba, aka hada family meeting aka raba saheeb da humairah, batareda dayansu nasoo ba. Tun daga ranar da suhayr ta je gidansu saheeb, nimra take bata labarin abinda ya faru, shikenan ta fara nuna masa kulawa,tausayawa da kuma uwa uba , soyayya mai tsafta Wanda ba gauraye aciki.I novels / JARABABBEN KISHI part 5 JARABABBEN KISHI part 5 Posted by Bashir Sani Fesan on 16 Dec 2016 - 14:04 Kamar wasa suhayr da saheeb suka zama addicted da juna, saidai kuma tsantsar kishi da take nunawa a kullum, Wanda yin hakan yake damun saheeb, har ya kasa hkr yayi mata magana yace "Gaskiya suhayr yakamata kisani nifa ba d'an kowa bane asalima banda wata Sana'a Dana dogara dashi saina mahaifina, sannan kinga da da wacce zan aura amma aka fasa kuma banso na yaudareki, Kinfini komai suhayr mexai hana kinemi wani daidai dake baniba? Sannan kuma gashi yanzu haka ankara yimun baiko da yar uwata Salma banda bakin dazan musawa mahaifina saboda haka ne tsarin family dinmu Suhayr ina sonki amma gani nake kwarya tabi kwarya, niba abokin burminki bane. " Zancen saheeb ga suhayr ya katse ne dalilin zuwan wata wacce sukayi makaranta da ita, "saheeb barka da rana!" kamar daga sama kalamanta suka dirgo, suhayr ta ware ido tayi tsalle ta watsa mata wani mahaukacin mari tare da nuna ta da yatsa tana cewa "karki kuskura ki sake yiwa mijina magana inba hakaba, zanyi Ajalinki ni wallahi narasa meyasa wasu matan suke shiga hurumin daba nasuba" Oh!!!!!! suhayr ta furta tare dan jan hannun saheeb, ko ta bari ya yi wa budurwar magana taki balle kuma harya bata hkr, ita kuwa cool baby abun ya daure mata kai don a iya saninta saheeb baida mata baiyi aure ba amma ,hakan yasa ta tambayi kanta da cewa "ita wannan din wacece?" (Nidai cewa nayi dadai kin tafi karki fiye kallonsu takara watsa miki wasu tafin) Cike da damuwa saheeb ya fisge hannunsa tare da cewa "For God sake suhayr meyasa kike son ganin bacin raina? Yar class dinmu ce fa, gashi kin mareta batare da tasaan hawa ba balle sauka kuma kin hanani inbata hkr" a fusace suhayr ta amsa da cewa "Saheeb nifa gaskiya inhar zaka dinga yiwa yan mata magana gaskiya zan nisanceka, saboda zan iya kashe ko ma wacece saboda *JARABABBEN KISHIN* dana ke akanka...." saheeb ya katseta ta hanyar cewa " Go ahead suhayr go ahead kisani indai kika aikata kisan kai, hukuma bazata barki da rai ba" suhayr tace" Who cares? suwaye hukumar in bamu ba,so I can do anything and I see no reason da wani zai dakatar dani". saheeb yace" OK haka kikace?, toh shikenan suhayr bana sonki ,kuma inhar kin saurari kalamaina a baya ya isa ki gane komai, Inada wacce nakeso kuma .......", bata bari ya karasaba ta juya fusace ta shiga mota ta tayar tare da barin gun a fusace. Gudu take batare da tana cikin hayyaci ba, ikon Allah ne kadai ya kawota gida ba mutum ba, Da kuka ta shiga gda tana cewa "mummy yace baya sona mummy baya sona Yazanyi?" mummy ta tare da tambayar "wai waye?"suhayr ta amsa da cewa "Saheeb yace baya sona mummy mutuwa zanyi baxan iya rayuwa inbada saheeb ba Mummy wai auren zumunchi zaa mishi" Mummy tace "Ki kwantar da hankalinki insha Allah xaki aureshi". Tun daga ranar suhayr tafara ciwo Wanda aka rasa meke damunta baci basha, Anje asibiti amma sun kasa gane musabbabin ciwonta, Hakan yasa mummy ta bugawa daddyn suhayr waya tagayamai halinda yarsa take ciki kasancewar baya gari. A Daren yabaro Abuja, yana isowa ko ruwa baisha ba, kebewa yayi da suhayr don jin Damuwanta. "Abba cewa yayi baya sona wai auren zumunchi zaayi mishi." wasu zafafan hawayene suka fito daga idanunta. A fusace daddyn yace "Wayeshi ?waye ubansa a garinnan? Kisa ranki a inuwa insha Allah saiya zama mallakinki ke kada" sannan kuma yace" Amma fa nasanki da mugun kishi maybe shiyasa yace baya sonki? da sauri tace "noo daddy watace tayi mai magana nikuma na gaura mata mari shikenan fa, Pls Abba muje inbashi hkr shine farin cikina, banida wani burin Wanda ya wuce in farantawa saheeb rai." Washe gari suka daddy da direbansa sukayi samnako zuwa gdansu saheeb. Sallama akayi da Alh Garba, yafito dayake mahaifin suhayr sananne ne ko'a TV, hakan yasa ba shiri mahaifin saheeb ya saukeshi a falonsa, bayan sun gaisa ,sai daddy ya fara magana kamar haka "Daman nazone akan Dan wajenka yata daya tilo tana gida rai a hannun Allah dukta dalilin danka mai suna saheeb Ka taimakemu yadda Allah ya taimakeka, Farincikin suhayr shine nawa, banida katabus indai tana cikin wani hali, kuma Na Dade da sanin tradition din family dinku amma Dan Allah akan yata a sassauta mana nasan saheeb na kaunar suhayr amma shi gani yake tamkar tafi karfin sa Kuma yata ba haka na tarbiyantar da itaba da amai arziki da talaka duk daya suke gun Allah" Mahaifin saheeb ya bude baki yace "amma fah maganar da muke anyi mishi baiko da yar kanwata salma". daddy ya katseshi da cewa "malam kayi mana wannan taimakon suhayr tanacan kwance ba lafya" mahaifin saheeb yayi jim sannan yace "A gaskiya saina tuntubi yan uwana zan nemeku nan da satii daya".SHI part 6 JARABABBEN KISHI part 6 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:05 Alhj kabir sulaiman Yayi godiya. Ankai ruwa rana, anyi dauki ba dadi a family din dan'koli'. Saheeb yace shifa mace guda bazata kawo rarrabuwan kawuna a cikin family dinsu ba kawai shiya hkr. Ya fadi cikeda damuwa a fuskansa. '"Itako suhayr ta nace babu Wanda takeso saishi cutafa ta karu bawani sauki. Amma daga bisani dole suka hkr, saboda halinda takeciki kowa cikin family dinsu saheeb ya tausayawa Suhayr, ciki harda Alhaji sanusi Wanda ya tsaya kaida fata cewa saheeb baxai auro wacce ba yar dangiba, Daman saheeb yana kaunanta amma gani yake yar manyace mezatayi dashi cima zaune. "Yakaiga duk yar da saheeb zai Neman sai anyi baraxanar kashe yarinyan shiyasa yazama bora, babu yarinyar datake kulashi daman abunda suhayr takeso kenan. "Soyayya sukeyi ba dare ba rana ji sukeyi kaman su Cinye Kansu, Abu daya kesawa ajisu shine inya fiye kallon mata masu wucewa, shiyasa suka koma zance acikin gida. Wata rana ne sun fita yawon bude ido shida suhayr. Sai wata tace ma kawarta "kinga wani gaye mai kyau wallahi harnaji sonsa acikin raina". 'Karaf sai a kunnen suhayr kukan kura tayi tayi kan budurwar cike da jin kishin Saheeb, ta cakumi wuyanta ta tsinka mata mari, idonta duk ya rufe tsabar bakin kishin da take ji. Janyota saheeb yayi yace "ke wace irin macece? Meye gaminki dasu dake suke? kinga suhayr indai abunda zaki dinga yi kena inmun fita toh gaskiya zansa doka kowa ya fita batareda wani ya raka kowa ba" Jinsa kawai take amma idanunta sun kada sunyi jajir kamar garwashi. Suhayr ta rike k'ugu tana huci tace, "Daga yau koda a dakinki kika ganshi zaki kiyayeshi mayya kawai Ina ruwanki da kyawunsa kekika yishi? Masu shegen surutun tsiya da kalle kallen tsiya ke ana babbakan giwa waxai jiyo kamshin Giwa? Toh ki kula mahauniyarki ta kiyayi ramata Kadan namiki nagobe saiyafi na yau idan kika sake mun katsalandan". Tsaki tayi tace "banza kawai juyowan dazatayi, ta nemi saheeb ta rasa, sai neme neme takeyi amma bata ganshi ba! Saboda bakin ciki batasan lokacin da wasu hawaye suka kwaranyo daga idanunta ba, Da sauri ta ruga cikin mota ta kafa kai da sitiyari, jitayi an ruko hannunta a tsorace tace "Ya salam"! ",Karkiji tsoro suhayr saheeb ne masoyinki," Tuni taji dadii acikin ranta, "Meyasa kike kishina dayawa? Ni nakine suhayr karkiji komai" suhayr tace "saheeb zan iya rasa rayuwata ganin kanawa mata magana Toh kaga da in rasa raina indaina ganinka ai is better inne mawa kaina yanci tafadi tana kallonsa cikeda soyayya amma damuwarta bata boye ba. Saheeb yace "Amma suhayr,"shiiiishhh!!!!! tacemai tasa hannu a lebensa, "don't say a word saheeb...." "You deserve more than dis from me, look right into my eyes what can you see?" "Kura mata ido yayi yace mata " * JARAB EL GHIRA (Flames of jealousy)*" 'Tabbas ba karya saheeb ,"abunda kafadi daidai ne" suhayr ta kalleshi tace say a word DAT will make me to be happy now" "Saheeb yace I LOVE YOU wholeheartedly"," Suhayr taji dadii kwarai. "toh yakake gani Saheeb bazan iya komai a kanka ba?" Yace "Zaki iya amma kuma yakamata ki sassauta saboda nifa mijin mace hudu ne???????" Zare Ido! Suhayr tayi tace "karka kuskura inba hakaba zaka iya rasani sannan zan iya amfani da *jarababen kishina* in katse duk wata halaka dake tsakaninka da wata mace" "Look" Saheeb yace "abar maganan" muje ki kaini gida kinsan yau saboda ke banje kasuwaba" "Toh" tace suka kama hanya waka takemai da harshen larabci.SHI novels / JARABABBEN KISHI part 7 JARABABBEN KISHI part 7 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:06 "Kaine masoyina na gaskiya mijina kuma uban yayana Zanyi fito nafito da duk wata mace datake Neman ruguza alakata dakai",..... Kallonta kawai yakeyi Azuciyansa yace tabbas akwai aiki a gabana nida nakeda burin auren mata hudu? Ni maison Tara zuri'a mai yawa gashi suhayr batason taga nayi alaka da wata ya mace. Suhayr ce taji Shurun yayi yawa, ta juya tana kallonsa amma baisan Abunda ke faruwa ba burki taja Wanda yayi saurin dawo dashi daga dogon tunanin dayake yi, "suhayr da lafiyanki kuwa"? "Hmm" murmushi tayi cikeda da takaici Suhayr tace "kai yakamata inyiwa wannan tambayan saboda da alamu Kaine Mara lafya Kusan minti goma kana tunani bayan gani a kusa dakai, Me kanema ka rasa dazaka dinga tunanin wata?". Saheeb zare Ido yayi "suhayr wallahi ba tunanin komai nakeba illah tunanin rayuwa mai daukeda *so da kauna* dazamuyi in munyi AURE, Narasa ta yadda zan nuna miki yadda nakeji". murmushi kawai suhayr tayi don tasan kawai kwaskwarima ce yayiwa kala mansa bawai gaskiya bane amma ta basar, Itadai burinta ya cika ta mallakeshi a matsayin mijinta daganan saitasa kafa yaki da duk wata mace koda kuwa yau aka haifeta, shiyasa fatanta akoda yaushe Allah yabata yaya maxa, saboda mugun kishin da take dashi akan diya mace. (Nikam nace To Allah ya rabamu da irin wannan *JARABABBEN KISHIN*) (Na kuma cewa suhayr kin manta Allah keyi ba mutunba, kana naka babatun Allah na can na shirya maka nasa tanadin, Wanda inya baka bakada bakin kin amsa, inko harka ce bai iyaba lokacin zai nuna maka ikonsa") Ansa ranan aurensu wata biyu, amma fa daqyar Baban Saheeb ya shawo kan danginsu suka amince. Kowa a dangi ya sanda bikin saboda bikine na yar gata ya daya tilo Amma saidai kash daidai sa second daya suhayr bata samu kar buwaba wajen mahaifiyar Saheeb ba. 'Saboda tace duk itace silar rusa mishi aure shida yan uwansa, gashi tana Neman ta rabashi da yan uwansa mata tunkafin tashigo cikin family dinsu. Ita kanta suhayr tasan cewa mahaifiyar saheeb bata kaunanta amma koh a bakin gyalenta, don cewa take wata ranama saikin so ganinsa in hanashi. Biki yanata matsowa anfara shiri gadan gadan Amma babu gdan da zaa sa suhayr , gdane saheeb yasamu ciki da falo Wanda a kalla mutanen gdan da yara sunkai Dari Tuni suhayr ta kai kukanta wajen mahaifinta tuni yabasu gdanshi dake zooo road, gdane Wanda ya amsa sunansa gida. Saidai mahaifiyar saheeb tace Sam bata yarda da wannan tsari ba saboda gudun gori, 'Danta baxai zauna a gdan surukai ba, tasan cewa ai talakane ta Nace tana sonsa. Indai bazata zauna a gdan daya kamaba saidai afasa wannan auren haka umman saheeb tace tun lokacin data samu labarin cewa anbasu gida. Suhayr tashiga tashin hankali dajin wannan sako daga wajen umman saheeb Tace lallai ne ma Zanyi maganin wannan shu'umar tsohuwar cije labe tayi tace yayanta ya rakata gidansu taje da kissa tana bata hkr harda kuka "Wallahi umma duk abunda kike tunani ba haka nakeba, inason saheeb baxanso bacin ransa ba, umma kiyi hkr muzauna a gdan da abbana ya mallaka mana" Umma tace" baxan taba rabuwa da saheeb ba soyayyarsa nakeso ba kudinsa ba, indon kudi nakesonsa wallahi bayida abunda zai mallakamun". Nan tayi tayi mata magiya Da kyar dasa bakin yan uwa umma ta aminche. Biki saura sati daya Anje an fara shirya gida da kayan alatu, Ankawo akwati guda biyu a wulakance tirmin zani hudune kuma duka super print ne sai takalmi kafa daya sai gyale guda daya shima. Shiyasa komai umma suhayr taki basu koh ruwa, Amma duk suhayr bataji komaiba, saima boye kaya da akayi don karyaxama abun zunde a cikin danginsu. Sadaki kuwa dubu goma sha biyar suka kawo sai kace wata bazawara, Duk don suhayr tace tafasa amma ina sonsa Dada karuwa yakeyi acikin zuciyarta. Biki ya rage saura satii daya ne suhayr sunje kasuwa sukayi batan hanya, sukabi ta layinda runfunan su saheeb suke. Mace tagani tanamai magana tuni taji numfashinta na Neman daukewa Zuciyarta na bugawa uku uku!!! Da sauri taja kawarta suka fita daga kasuwar. Waya ta dauka ta kira saheeb tace "ina kasuwa ka fito bakin titi zakagaI novels / JARABABBEN KISHI part 8 JARABABBEN KISHI part 8 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:07 Jikinsa na rawa yafito daman angaya masa anganta a layinsu, Yana isa Suhayr ta balla masa wani irin harara Wanda sai daya shiga taitayinsa, "Saheeb abunda baxan taba lamuncewa ba kenan yin sana'ar dazaka dunga mu'amala da mata, dole ka canza Sana'a Wanda mazane abokan cinikinka Dole kayi nesa da duk wata mace hatta yan uwanka mata saboda kwanciyan hankalinmu baki daya". Saheeb Kallonta ya tsaya yi cikin tsananin damuwa sannan cikin bacin rai yace "bantaba Sanin cewa Suhayr ke mahaukaciya bace sai yau? kina ganin zan bar sana'ar mahaifina ne inyi wata daban? Kinsan cewa Sana'ar koli ita muka gada mukeyi tun iyaye da kakanni, Oh suhayr meyasa kika shigo rayuwata? For the first place am not in love with you amma saboda kaunar danaga kike nunamun ne yasa kikaga na amince miki har kika fara shiga zuciyana a hankali Amma shine zakizo ki ruguzamun rayuwa? Toh ki sani baki isaba Saidai ki mutu! kokuma Abu mafi sauki ki rabu dani auren afasa banayi" Saheeb ya qarasa maganar cikin hargowa. Suhayr Ji tayi kalaman saheeb na Neman haukatata me yasa Saheeb xaiyi mata haka? Bayan yasan zata iya mutuwa akansa, gashi talaka mafi kaskanci a idanunta amma takasa ganin wayannan bayaga soo da kaunansa dake dawainiya da ita. Dishi 2 kawai ta fara gani ta xube a wajen a sume. "Na shiga uku" saheeb yafadi cikin tashin hnkl, wasu mutane suka taimaka masa suka sata cikin mota itada kawarta, sai asibiti. Bayan awa uku ta farfado da sunan Saheeb acikin bakinta, "saheeb karka juyamun baya kishinka wajibine a gareni zan iya jure komai amma banda ganin kanayin mu'amala da mata" Tuni saheeb yafara zubarda hawaye Wanda shikansa besan dalilinsa na zubdasu ba. (Nida ILILEE mukace "sone saheeb ka kamu da son suhayr baka saniba") Rike mata hannu yayi yace "suhayr tabbas ke macece wacce kowani da namiji zaiso samu matsayin mata Bakida wani aibu a tattare dake, ki share hawayenki nime kaunankine," 'Shuru tayi lokaci guda taji ta warke tashi tayi tace "pls and pls saheeb inzakamun magana kadunga sassauta kalamanka a gareni". "Karki damu bazan karaba". Saheeb yafadi hakane don ya faranta mata rai" 'Dariya tayi can ta lura da kallon da Noor take musu tuni tace "maxa ki fita ki bacewa ganina kafin inyi takanki Kallon me kike mai? Karki sake zuwa inda nake, tunda naga take takenki so kike ki fara shiga hurumin daba nakiba". Haka nan noor ta fita don tasan halin kawartata. Shuru shuru zasu dawo ina basu dawoba, gashi zaa fara mata gyran jiki, Hajy rahmatu Maiduguri aka kira taxo ta gyra suhayr umma CE ta dau waya ta kirata tace "suhayr meyasa kika Dade? Bayan kinsan schedule dinmu na yau?" "Umma ganinan tahowa, in the next few minutes," Ta fada. Umma tace "Toh tace saikin dawo". Ta kalli Saheeb, Kallon da suhayr tayi masa yasa saheeb jin wani yanayi ajikinsa, Suhayr tace "Yauwa saheeb dakwai wasu dinkuna danayima sannan daddy yasiyo ma wasu takalma daga England, muje inna saukeka sai inbaka, sannan ga wasu yan kudi kayi amfani dasu nasan kanada hidima". Qin karba yayi sai da ta nuna bacin ranta sannan ya karba. (ILILEE yace inama shine ai tafadi gasassa Nidai dariya Nayi) Har kofar gida takaishi inda umman saheeb ta leko ta taga'. $uhayr tagani sanye da kaya tsadaddu ta dannan wani Abu boot din mota ya bude. Wasu Abu ta dauko a Leda "saheeb gashi zan tafi" ya karba, da sauri ta shiga mota ta figi mota kaman zata tashi sama, Shiko tsayawa yayi yana kallonta harta bacewa ganin sa sannan ya shiga cikin gida sai ji yayi ana cewa angon suhayr, bai tanka su ba ya shiga cikin daki Ya zauna akan katifarsa, "Dakwai aiki agabana, gaskiya suhayr inna ce bazan miki kishiyaba na munafunceki" Banida burin zama da mace daya". (Nace Toh pa kace akwai budiri a gidan Suhayr da Saheeb, muje xuwa dai) novels / JARABABBEN KISHI part 9
JARABABBEN KISHI part 9
Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:08
Ayau Sha Tara ga watan November Wanda yayi
daidai da ranan asabar ne, Dubban Mutane ciki
harda "senator na kano central", suka halacci
daurin auren *Suhayr kabir sulaiman da Angonta
Saheeb Garba Dan'koli* Bikine na manya bikine
Wanda ya amsa sunansa biki. Ba ai wani event
ba saboda suhayr tace bata iya jure kallon da yan
mata zasuyi wa mijinta ba, walima kawai akayi
bayan daurin aure. 'Suhayr tayi kyau dukda ba
wata kyakkyawa bace amma dayake ance ko
amaryar buzuzu ce ranan bikinta kyau takeyi,
Badon farar fataba inajin dasaidai akai kasuwa,
Suhayr gajerace badai sosai ba sannan tanada
idanu Wanda zamu iya kiransu da sexy eyes,
bakinta Dan karami Dan das, tanada jiki Wanda
bazamu iya kiranta da siririya ba, Saikuma hanci
kwarai batada hanci amma tanada kara. Da
misalin karfe Tara na darene yan daukan amarya
suka hallaro Domin daukar amaryarsu, motaci
uku ne Golf guda biyu sai wata space wagon
guda daya. Ga dunbin jama'a yan rakiyar amarya
kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake Itako
suhayr fada ake mata sosai Wanda ko wacce
uwa takeyiwa yarta inzata kaita gdan miji. Ciki
harda fada akan jarabebben kishin data sawa
kanta, "Hjy ikilima ce ke magana da kakkausar
murya: "suhayr kishi a jininmu yake Kuma Allah
ne ke halittan kowani bawanda dashi, amma
saiyasa nawani yafi na wani Karki kasance me
nuna kishinki a fili yata ki sassauta kishinki, don
kishi ba hauka bane Wallahi indai kikayi koyi dani
toh tabbas suhayr zaki zama yar gaban goshi a
gdan saheeb". kuka suhayr keyi Wanda saida
tasa kowa na wajen kuka Wanda zan iya cewa
kukan yazame ma kowacce amarya al'ada,
dazaran zaa kaita gidan miji ta dinga kuka
saboda tunanin ta rabu da gida yan uwa da
abokan arziki, kenan saidai ziyara. Mahaifinta
shima yayi mata fada kwarai me shiga jiki. An fito
za'a sata a mota bawata mota mai tsada tanajin
abunda ake cewa Amma bataji komaiba illah
kosawa datayi akaita gdan saheeb, Acikin daya
daga acikin golf din akasa suhayr sai yan uwan
hjy ikilima, Dana mahaifinta suka cika sauran
motacin biyu..... Don ba kawa ko daya data shiga
motar kai amarya daman tun asalinta suhayr
daman bamai jaye jaye bace. *Ankaita gdanta
dake zooo road kowa ta watse saboda mahaifinta
yabada umurnin kar Wanda ya kwana," daga
suhayr sai saheeb aka bari acikin gdansu*
~Kubiyo yar mutan zazzau kuji labarin zaman
auren saheeb da suhayr shin wace waina zasu
toya ?????????gadaishi kowa ya watse ?KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 10 JARABABBEN KISHI part 10 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:11 A Daren yau hankali ya kwanta, suhayr taxama mallakin saheeb, "Suhayr ayaune zamu kafa tarihi a rayuwar mu, yaune muka kasance ma'aurata," Kunyarsa suhayr keji Wanda abaya ba haka takeji akansa ba. "Tashi muyi sallah ko?" Cewar saheeb Wanda farin cikinsa yakasa boyuwa, "toh" tace. Alwala suka dauro suka gabatar da sallah da godiya ga mahaliccinsu, Wanda ya kawosu zuwa wannan lokacin. Sun danyi ciye ciye daga bisani Suhayr ta tashi tahau gado ta kwanta a tsorace don tasan Daren yau shine Daren farko dazata kwanta gata ga namiji Wanda a yanzu shine annurin zuciyarta. Tuni bacci yayi awon gaba da ita, saida saheeb ya kammala ya tashi ya matsa kusa da ita yana mata rada a kunne "cutey kitashi ki cire wannan kayan kinsan sunada nauyi zasu hanaki bacci". Tashi tayi tana cewa "Umma Dan Allah ki kyaleni kinsanfa nagaji dayawa," tana bode Ido saitaga Ashe saheeb ne. Ya mata murmushi rungumeta yayi yace "yar umma daga yau kindaina kwana da umma", dariya tayi tace "hakane saheeb sabo ne kawai kasan bana iya bacci saida umma," 'Saheeb yace "gashi yau xakiyi bacci ba tare da umman ba" dariya sukayi duka, tashi tayi ta dauko kayan bacci tasa amma fah saidata shiga cikin toilet saboda kunyarsa data keji. A Daren yau saidai muce Alhamdulillah saboda saheeb ya cimma burinsa akan masoyiyarshi, Ya maida mugun yawunsa "Assalatun farko saheeb yatashi yayi wanka ya fita zuwa masallacin dake kusa dasu, Bayan yadawone yatadda Suhayr kwance sai faman kuka takeyi, Wanda hakan yaba saheeb tausayi, saboda yasan cewa yayi laifi. Amma hkr yaxama wajibi daman haka auren ya gada, haka ko wacce mace tayi going through. Daukanta yayi cik yakaita toilet ya hada mata ruwan zafi, yataimaka mata ta gyra kanta, tagabatar da sallah. Suka koma suka kwanta farkawa tayi ta shiga kitchen don ganin abunda zata iya dafa musu, Amma taga wayam hakan bai bata mamakiba saboda tasan mijinta bashi gareshi ba. Wani corner ta leka taga kayan garanta daki guda nan tafara tunanin abunda zata samfara amma babu kayan hadi, Tana cikin wannan nazarin ne taji ana knocking kofa, Budewa taje tayi Ali direba tagani yace ina "kwana uwar dakina ya bakon waje?," "Lafya" tace, yace "Daman hjy ce tace in kawo muku abinchi". Tace "shiga dashi mana," Coolers ne na abinchi ya shiga dasu ciki ya a falon. Juyowa yayi yace "sannan tace kiyimun lissafin abubuwan dakikeda bukata yanzu kasuwa nayi" tace "toh" sannab ta lissafa komai a littafi ta rubuta ta mikamai ya tafii. Tsayawa tayi tana tunanin irin sonda iyayenta ke mata, abunda iyayen saheeb ne yaka mata suyi mana wannan hidimar amma sai gashi umma ce dakanta, Duk yanayin da suhayr take ciki saheeb na kallonta. Jitayi an dafata da sauri ta juyo tace "my life sannu da tashi". Sam bata nuna mishi a wane hali takeba, "Suhayr tunanin me kikeyi?" Ya fada yans kallonta. Tayi saurin cewa "Lah my life ba komai kawai tunanin yadda zan faranta maka rai nakeyi". Dariya don yasan kwaskwarima tayiwa kala manta, tace "Kaji mijina muje dinning kaga abunda umma ta aiko mana dashi tace muhuta karmu dafa komai". Daukanta yayi suna dariya cikin nishadii da kaunan juna, Sunci sunyi kat suka koma falo suna kallon Indian film.
0 comments:
Post a Comment