JARABABBEN KISHI Page 11 to 15
JARABABBEN KISHI part 11 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:14 Bayan wata biyu, suhayr ta kasance mace mai kiyaye duk wani hakkokin mijinta babu abin da ya nema ya rasa daga gareta, matsalarta daya a duniya kishi bata son kishiiya kuma bata kaunar duk wata mace ta rabeshi hakan yasa ta roki alfarmar mahaifinta ya bashi kudi ya ja jari ya bude shagon sai da hula da agogon maza, domin bata son yayi "white collar job" Da hakan zai kawo cudanyrsa da mata ko da kuwa yan uwanta ne bare Kuma nashi. kyawawan dabiunta da kuma son da ta ke masa yasa ta samu love dinsa 100pecent domin duk wuya duk dadi tana jurar yi masa komai, Tana zaune a falo taji ana knocking ta miqe taje ta bude kofar taga wasu yan mata kyawawa, sunsha mai da foundation, kallonsu takeyi shekeke Wanda haka yaba nimrah haushi tace wai ko baki ganeni bane?". Suhayr balla ma nimrah harara tayi tace "mekikazo yi gdana da wayannan masu kama da aljanun?" Suhayr ke magana cikeda isa sa fankama. "kut gaskiya nimrah matan wannan naki batada mutunci mine ma masu kamada Aljannu?" Suhailah ce ke magana tana taunan cingam. "Suhayr magana muke kina kallonmu", Dariya tayi tace "inajiran inji dukane saboda Nace muku masu kamada mami water". "Ke !!!!" Nimrah ce ta dakawa suhayr tsawa "dakata kiji karki ga kinama sauran mutane insunzo gdanki kice zakimun, danni nafi karfin yinki wallahi saidai inyida gyatuminki". Suhayr ce tace "Habawa Nimrah kinso ki tafka babban kuskure wajen tabamun iyaye Wanda nasan sunfimun naki iyayen sau miliyan, ai kinsan bakin rijiya ba gurin gadar makaho bane, Nimrah kafin inbude idona in rufe ki fitarmun da wayannan masu kamada yan ruwan inba hakaba I will surely sure you gals mah true colour". Nimrah tace "Aikam da wuya yau inba'a haifi da Mara Ido ba" inji nimrah Wanda ta runtse Ido bataji bata gani, don tsabar takaicin abinda Suhayr tsyi masu. "Mai gadii John" Yayi saurin shigowa yana cewa "yes mah hjy lafya irin wannan kira". Cikin bacin rai Suhayr tace "How many times have I warn you that I don't want to see any lady in dis house apart from my mum? Haven't I warn you?" John jiki na rawa yace "yes mah," "oya before the count of three I don't want to see any of this things infront of me". Da duka john ya rakasu ammafa nimrah baki yaki mutuwa "cewa tayi "yau kin nunamun gida nakine Suhayr amma saikinyi ladaman cimun mutunci shegiya yar matsiyata." Ciki ta koma ta harde kafa Ashe saheeb nanan suhayr ke cima nimrah da friends dinta mutunci, "Hayaniyyan me nakeji suhayr?" shuru tayi kaman bada ita yakeba can ta dago ts kalleshi tare da cewa "Pls saheeb ka gayawa kanwarka, nasa mata boundary da gdannan". Shima cikin bacin ran yace "kozaki iya gayamun dalili?". Tace "Dalili shine zan iya raunatata inta kara shigomun da kawayenta, masu suffan jinnu gdannan, Akan mema saitaxo gdannan nifa banason shisshigi ka gaya mata," Saheeb ne ke zaune kusa da ita yace "suhayr nimrah kanwata ce kiyi hkr da abunda zan fadi Nimrah nada ryt din zuwa inda nake". Tayi saurin dakatar dashi da cewa "dakata Saheeb inada kishi da banaso kayi tozali dawata mace inba niba, don haka ta kiyayi gidannan, don ko jaririyace ina matukar kayi mata murmushi bare baliga kaman nimrah." Yace "Amma dai kinsan nimrah muharramata ce?". Tace "Koma me CeCe nagama magana" tashi tayi tashiga daki. A ranan ya shiga wani hali ummansa ce ta kirashi tacimai mutunci, sannan da sharadin saiya kara aure ko yana so ko baya so.Home / JARABABBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 12 JARABABBEN KISHI part 12 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:34 Tunani mai zurfi ya shiga amma bashida yadda zaiyi, Suhayr ta hanashi mu'amala da mata harma da yan uwansa, Gashi saheeb yana matukar kaunar matarsa bayason yaganta cikin damuwa, bayason ganin bacin ranta, Amma yana mamakin kishi irin nata, inda za'a bashi littafi da Biro tsaf saiya rubuta kishin suhayr gaba daya. Saheeb Yakama sana'a ba kana hannun yaro acikin manyan plaza dake kan hanyan Hotoro. Dayake wajen center ne inda manyan mutane ke wucewa, Gaba daya kayansa na wajene saidai kayan gida kaman su shadda, huluna, dadai sauransu. Amma fah koda yaushe akan waya sukeyi da sahibar tasa wato suhayr, arana saita kirashi fiye da sau talatin, saboda kishi dake dawainiya da ita Amma hakan bai hanashi yin budurwaba, Daman masu iya magana nacewa duk wayon amarya sai ansha manta, Haka shure shure baya hana mutuwa. Ranan yatashi da wuri daga shago ya kashe wayansa, saboda yanaso yaje family house dinsu ance ana Neman sa, don yasan inya gayawa suhayr saitasan yadda tayi ta hanashi zuwa, adaidaita yahau sai dorayi, Yana shiga aka yimishi cha mijin hajiya! Mijin hajiya!! Mijin hajiya!!!. Yadanji kunya kwarai amma ya maxe Yaga dangi kowa ya hallara abun yayi matukar razanashi, Zama yayi ya gaidasu, "yauwa saheeb abunda ya taramu anan shine gameda matarka suhayr Data hanaka sakat saboda kana zaune a gdansu sannan Kuma tabaka jari". Inna larai ke magana shuru yayi baice kala ba saboda yasan daman za'a Rina, "Dalilin taruwanmu shine munaso ka kara aure". Zare Ido yayi yace "aurefa kukace? Dan Allah karkuyimun haka dududu watanmu nawa da aure zaa kawomun zancen wani aure yanzu Haba Dan Allah kucanza wata shawarar amma ba wannan ba". Ummansa dake gefe tace "dole kayi aure don samun kwanciyan hankali". Bashi da yadda xaiyi dole ya amsa masu ba don xuciyarsa na so ba, a haka yakoma gida cikeda tunani iri daban daban, ta ina ma xai fara sanar da Suhayr wannan xancen?. Da shigarsa yaji kakarin amai da sauri ya yadda ledojin dake hannunsa, Da gudu ya shiga toilet suhayr yagani tafita hayyacinta. "Subhanallah cutie meke damunki haka"? Bata iya bashi amsaba, illah hawaye dake tsirarowa daga idanunta "Saheeb zan mutu ka kaini asibiti". Mota ya dauko yasata suka wuce asibiti. Likitane yace ashiga da ita, amma suhayr dukda ciwon da take bata sassauta kishinta ba, gam ta rike hannun saheeb tare suka shiga anyi mata test kusan kala uku, " congratulations yallaboi madam tana dauke da ciki wata biyar". Saheeb yayi saurin cewa "Likita wata biyar fa kace ya akayi bata saniba Kuma nima haka?" Likita yace "Tana iya yuwuwa inna farine baxata ganeba,haka kaima, amma ya kamata a kula da ita sosai musamman ma abinchi, tadinga cin kayan marmari irinsu zogale dama dai sauran kayan Karin jini A yanzu bata bukatar motsa jiki saboda Dan bai rigada yayi kwari ba". Murna wajen saheeb sai Wanda yagani don ji yake kamar ya hadiyeta don murna.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 13 JARABABBEN KISHI part 13 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:36 An sallamesu, hjy ikilima musamman taxo don ganin yartata, Sunsha fira tsakanin ya da uwa tuni aka fara siyayyan kayan ahaihuwa. BAYAN WATA Uku ne lokacin cikin Suhayr yana wata na takwas, Dangi fah sun tashi haikan ganin saheeb yakara aure, Domin sunce suhayr tayi musu Kane Kane gashi yanzu arziki yaci uban Nada, sai a cika gida da iyali, Saheeb yafara Neman aure gadan gadan, amma duk abunda yakeyi suhayr bata saniba, Har ansa ranan wata uku duk ya maidata biri boko, makota tashi ga saiga wata mata tashigo, tana cewa, "ke ummu aiman Ashe makocinki aure zaiyi? Duk kishin da ake cewa matarsa nadashi". Ummu aiman sai siginal takewa indo amma itako sai zuba takeyi, Saidata gama tsaf suhayr taji wani irin ciwo na naman cin karfin ta tace,"Baiwar Allah kozakimun kwatancen gdansu yarinyar?". "Kwarai maizai hana". Inji indo. Nanfa indo tayita mata kwatance harta gane. "Ngd" tace tashi tayi taje gda, tace "yau saiya gane cewa, ruwa ba sa'an kwando bane, sai ya gane shayi ruwa ne saina nunawa saheeb cewa yayi kuskure namiji munafiki, ni xai munafurta? Ya qara aure? kabashi dukkan yardarka yacima amana". Gyale kawai ta chanja ta nufi Gidansu yarinyar tayi sallama da uban yarinyar, cike da mamaki ya fito yana kallon Suhayr. Tace "naji labarin cewa, zaka aurawa mijina yarka? toh Kasani yarka zatayi kwanan prison matukar tace zatayi kishi dani, Don saina aikata inda baxata kara jin kamshin mijina ba, sannan inkun shirya yarku tazo gdana, toh Ku kawota na nikafali, don sainayi ajalinta". Uban yarinya yace "aikin banza, kewacece? Aikam saimunyi Shari'a dake har yaumut tanadi". Suhayr tace "Mune gwannati kaje ka tambaya waye Alhj kabir sulaiman inajin kasanshi, toh nice diyarsa daya tilo, Inyazo shi mijin nawa kace yaci gaba da Neman aure nikuma, inci gaba da rusamai tsari". Tura cikinta tayi ta shige mota ta badamai kura, Uban yarinya yace "tab ai aure anfasa, baxai iya da wannan ja'ibar ba Daganinta zata aikata duk abunda tace. Saheeb yaje zance uban yarinyar Yace "karya sake zuwamai gida saboda matarsa taxo tayi barazanar kashe musu ya". Gda yadawo cikin bacin rai ya iske Suhayr yace "Suhayr hankalinki ya kwanta kin raba abunda Allah yahada, Tun kafin muyi aure kike abu daya haryanzu kinki ki daina". Tanadaga zaune tace "kamanta dakwai ranan danace ka kalli kwayar idona? nacema maika gani"? Kacemun *JARAB EL GHIRA? Flames of jealousy?* Toh I can do more than wat you are thinking saheeb, Bantaba Sanin cewa kai munafiki bane sai yau butulu kawai Wanda ke manta alkhairi, Bacin so baya dubi da nasaba da chanchanta, Yaushe zan aureka Saheeb? Amma shine zaka zaga bayana kaci amanata? Kayi hkr da kalamaina, nasan kai mijinane, dole infadi Nasan duk umma ce kesawa ka kara aure, Kuma Wallahi Allah ya saukeni lafya, sainaje har gdan tagayamun dalili, Inace ita kadaice wajen mahaifinka? Ohh shine saboda kiyyaya zatasa ka kara aure toh zan gani, Ga fili gamai doki Saura sukuwa". Mari taji ya sauka a kuncinta, "Karki sake yima mahaifiyata cin zarafi a gabana inke bakisan darajar iyayeba Toh ni nasani Kuma aure ba fashi sainayi Kuma ra'ayinane, bana umma ko Abba ba, Saina cika gdannan da zuri'a mai yawa, saidai ki mutu.SHI novels / JARABABBEN KISHI part 14 JARABABBEN KISHI part 14 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:38 Kuncinta ta rike tana mai kallon saheeb Ido cikin Ido, Cike da takaici tace "tabbas saheeb sai kayi ladaman marina saika San cewa ka mareni Akan wata yar iska? Kayi kuskure wannan. *So ne ko kiyayya*? (Na sanah s matazu,) Saheeb magana nakeyi kana jina, aikam inhar numfashi bakai ba kara aure acikin gdannan, Na yima rana shine zakamun dare"? Wasu zafafan hawayene suke kwaranya a cikin idanunta, Amma saheeb koh kallonta baiyi ba, bare Kuma ya tausaya mata saboda abunda take dauke dashi a cikinta. Fuuuuuu Saheeb ya wuce kaman zai tashi sama kuka suhayr keyi tana cije baki saboda wani ciwo datakeji, Tana cikin wannan halinne taji Sallama Ashe kawartace tashi tayi ta bude kofa "ah ah maraba da mutanen jigawa saukan yaushe ina yaran da oga?". Qawar tace "Tab suhayr uwar biyu kenan wannan ciki naki dakwai bayani". Dariya suhayr tayi a Falo suka zauna tasa mai aikin ta takowo bakuwa abinchi da abunsha, "Kawata naji dadin zuwanki wallahi, inada damuwa sosai", tas ta kwashe komai ta gayawa kawarta. Qawar tace "Tabbas suhayr keme lefi ce yazaki dinga yin Abu irin wannan? Bayan kinsan halin maza insuka so Abu sai sunyi ko'a boyene? Tunda nake da baban hydar ban taba cewa bazan zauna da kishiya ba, dama zai kara auren wallahi Nina shigemai gaba don ganin yayi auren Kuma gashi muna zaune lafya". Suhayr tace "Tab aini *Jarababben kishi*na bazai barniba, Akan saheeb zan iya rasa raina". Ummu hydar tace "Tab bari kiji kadan daga cikin wani littafi na matan aure Dana taba karantawa," Kila ya miki amfani don bance dole ba". " Idan har Kika yarda da cewa namiji ba zai qara aure ba suhayr to wllh kinyi wauta domin basu da tabbas a wannan bangaren, karki yarda namiji yayi miki alqawarin baxai miki kishiya ba, shi kanshi ai bai san me yake gaba ba, idan Allah ya rubuta sai yayi auren nan to fa ya xama dole yayi shi". Ta cigaba da cewa "Idan Kuma kika ce ba zaki rike dan Mijinki ba (dan Kishiya) Nan ma kin tafka shashanci babba, don Idan kin haifi naki 'Ya'yan babu tabbacin cewa xaki dawwama a gidan ko a duniyar ma, Idan kuwa kika ce namiji ba dan goyo bane kin zama sakarya, domin kin mance da cewa ai kece baki Iya yanda ake goyon namijin ba" Idan kuma kika ce Kishiya ba abokiyar zama bace ba, mijinki baxai qaro wata matar ba toh ke naki 'Ya"yan Idan kin haifa jere Za Kiyi dasu a dakin ki? Karki raina uwar mijinki domin tamkar uwa take a gurinki. Da dan numfasa snnan ta cigaba "Idan kina wulakanta dangin mijinki, Toh naki dangin waye zai girmamasu? Idan kika ce ke bakya son kishiya toh sauran Yan mata da zawarawan gari suyi yaya?. Suhayr tabbas yaka mata kifarka daga nannauyan baccin dake dibanki Suhayr shuru tayi don tasan dakaman wuya gurguwa da auren nesa, yadda takeda kishinnan aikam bazai taba yuwuwa ba, Ummu hydar taci gaba da cewa, "Idan kika ce ke bakya son Kishiya toh kisani, da yiwuwar ayi miki kishiyar waje wacce Idan akayi rashin sa'a Kishiyar nan taki ta waje ta aiko miki da "SAKON MUTUWA" (HIV Aids) SUBHANALLAH, Suhayr meyasa baxakiyi amfani da wannan hudubar ba ki gyra, lahiranki?". "Tabbas ummu hydar da kishiyar gda tabbas na kwammace ta waje Inta tashi ta kashemu mu duka". Ummu hydar tace "Kash yayan da kika Haifa Kuma fa?". Cewar ummu hydar. Suhayr kai tsaye tace "Suzama marayu" (Ni kam dai nace Suhayr kin fara bani tsoro)ISHI novels / JARABABBEN KISHI part 15 JARABABBEN KISHI part 15 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:39 Duk abunda kawar suhayr ke fade duk a kunnen saheeb, Hannu yadaga sama yace "Allah kasa suhayr tayi amfani da wayannan fatawa" Amma saiyaji akasin haka. A ranan ummu hydar ta tafi tabar suhayr da dumbin tunani. Shi kuma saheeb ya rasa yadda zaiyi, akullun yanada shaawar ganin ya tara mata domin ya tara yaya masu yawa. A haka suhayr taci gaba da tsula tsiyarta, duk inda taji yaje neman aure saita wargaxa, sai da tayi sanandin lalacewar auren daya nema guda 7. Danginsa suma sun bashi mata duk yadda akayi da boyewa sai da ranar daurin aure taje da bindinga tasawa waliyyin a goshi yana daurawa zata aika dan banza lahira. *CIGABAN LABARI* Nan yan'uwa aka fara cece kuce akan saheeb lallai suhayr tafi karfin shi, harta isa ta hanashi qara aure?. Saheeb ne ya juyo cikeda bakin ciki, dajin kunya ga dubban abokansa harda abokan cini kayyanshi Yace "suhayr am disappointed in you, you disgrace me in public? Had I know zaki zaman mu matsala a rayuwana, tabbas daban au........" "Saheeb dakata" wata murya yaji kakkausa Da alamu babu wasa acikin muryan. Juyowan da Saheeb yayi mahaifinsa yagani, Mahaifin nashi yace "Tabbas auren ka da suhayr alkhairi ne, Sannan bakada wata kallaman daxaka aibanci suhayr, Tacika mace jaruma, Sannan Wallahi tayima komai duk abunda akeso mace tadunga yiwa mijinta kasamu". Shidai Saheeb bakin ciki ne ya isheshi, yarasa makemai dadii yaci gaba da cewa" Kaida kanka Saheeb duk randa zan tambayeka cewa ya zaman takewanka da Suhayr? Kakan cemun babu wata matsala, Toh banga dalilin ka na kara aure ba tunda bata gaxa wajen kyautata maka ba". "Amma Abba".... "Bansanjin wani kalma daga bakinka ba ku tafi gida kawai". Sun koma gda ba Wanda yace ma kowa kanzil, Ahaka suka cigaba da rayuwa har Suhayr ta haihu baice da ita komai ba, ko barka bare kuma yadauki da yayi masa huduba tundaga asibiti daya kaita bai kara hada Ido da itaba. Bayan mahaifin Saheeb yazone ta gayamai halin da ake ciki, Yayiwa da huduba yasa masa sunan mahaifinta wato kabir Wanda tayimai lakabi na NOOR wato (haske). Murna a wajen Suhayr bai misaltuwa. Suhayr ta hana kowa zuwa mata barka daga danginta har na mijin, Sannan tafadi ma ummanta bazatayi suna ba kuma baxata koma gda wankaba, Abunda ya daurewa ummanta kai shine yadda Suhayr ke magana ba koh alamar shakka, ta kaleta tace "Suhayr meye dalilinki na Na cewa baxakiyi sunaba? Kuma kinsan yin suna yaxaman mana al'ada" Tace "Umma nace baxanyi sunaba' saboda bazan juri ganin mata acikin gdana ba Sannan meye abun doki dahar sai anyi suna bayan uban d'an baya maraba da zuwansa duniya". Tana magana tana zubda hawaye Wanda duk Wanda ya kalleta saiyasan cewa Rashin kulatan da Saheeb bayayi yana cimata tuwo a kwarya. Umma tace "Suhayr hakanan Saheeb bazai juya miki bayaba saidai inkin yimai laifi" Suhayr tace "Wani laifine umma nayi banda ya wuce naje na wargaxa mai auren da yake shirin karawa? Nibanyi fushiba daya munafunceni bai sanar dani cewan zai'yi aureba sai shi? Nikuma nayi amfani da kishina Wanda bashida maraba da leban wuta na ruguza komai, Kishiya a gdan Saheeb sai bayan raina". Umma Suhayr ce tace "kull inba hakaba zaki tafka kuskuren da sai kinyi Dana sani, wannan maganar inkikayi wasa yan Amin suka amsa toh Wallahi zaki mutu kuma yakara aure ke har hudu sai yayi".
0 comments:
Post a Comment