JARABABBEN KISHI Page 16 to 20
JARABABBEN KISHI part 16 JARABABBEN KISHI part 16 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:41 Duk abunda kawar suhayr ke fade duk a kunnen saheeb, Hannu yadaga sama yace "Allah kasa suhayr tayi amfani da wayannan fatawa" Amma saiyaji akasin haka. A ranan ummu hydar ta tafi tabar suhayr da dumbin tunani. Shi kuma saheeb ya rasa yadda zaiyi, akullun yanada shaawar ganin ya tara mata domin ya tara yaya masu yawa. A haka suhayr taci gaba da tsula tsiyarta, duk inda taji yaje neman aure saita wargaxa, sai da tayi sanandin lalacewar auren daya nema guda 7. Danginsa suma sun bashi mata duk yadda akayi da boyewa sai da ranar daurin aure taje da bindinga tasawa waliyyin a goshi yana daurawa zata aika dan banza lahira. *CIGABAN LABARI* Nan yan'uwa aka fara cece kuce akan saheeb lallai suhayr tafi karfin shi, harta isa ta hanashi qara aure?. Saheeb ne ya juyo cikeda bakin ciki, dajin kunya ga dubban abokansa harda abokan cini kayyanshi Yace "suhayr am disappointed in you, you disgrace me in public? Had I know zaki zaman mu matsala a rayuwana, tabbas daban au........" "Saheeb dakata" wata murya yaji kakkausa Da alamu babu wasa acikin muryan. Juyowan da Saheeb yayi mahaifinsa yagani, Mahaifin nashi yace "Tabbas auren ka da suhayr alkhairi ne, Sannan bakada wata kallaman daxaka aibanci suhayr, Tacika mace jaruma, Sannan Wallahi tayima komai duk abunda akeso mace tadunga yiwa mijinta kasamu". Shidai Saheeb bakin ciki ne ya isheshi, yarasa makemai dadii yaci gaba da cewa" Kaida kanka Saheeb duk randa zan tambayeka cewa ya zaman takewanka da Suhayr? Kakan cemun babu wata matsala, Toh banga dalilin ka na kara aure ba tunda bata gaxa wajen kyautata maka ba". "Amma Abba".... "Bansanjin wani kalma daga bakinka ba ku tafi gida kawai". Sun koma gda ba Wanda yace ma kowa kanzil, Ahaka suka cigaba da rayuwa har Suhayr ta haihu baice da ita komai ba, ko barka bare kuma yadauki da yayi masa huduba tundaga asibiti daya kaita bai kara hada Ido da itaba. Bayan mahaifin Saheeb yazone ta gayamai halin da ake ciki, Yayiwa da huduba yasa masa sunan mahaifinta wato kabir Wanda tayimai lakabi na NOOR wato (haske). Murna a wajen Suhayr bai misaltuwa. Suhayr ta hana kowa zuwa mata barka daga danginta har na mijin, Sannan tafadi ma ummanta bazatayi suna ba kuma baxata koma gda wankaba, Abunda ya daurewa ummanta kai shine yadda Suhayr ke magana ba koh alamar shakka, ta kaleta tace "Suhayr meye dalilinki na Na cewa baxakiyi sunaba? Kuma kinsan yin suna yaxaman mana al'ada" Tace "Umma nace baxanyi sunaba' saboda bazan juri ganin mata acikin gdana ba Sannan meye abun doki dahar sai anyi suna bayan uban d'an baya maraba da zuwansa duniya". Tana magana tana zubda hawaye Wanda duk Wanda ya kalleta saiyasan cewa Rashin kulatan da Saheeb bayayi yana cimata tuwo a kwarya. Umma tace "Suhayr hakanan Saheeb bazai juya miki bayaba saidai inkin yimai laifi" Suhayr tace "Wani laifine umma nayi banda ya wuce naje na wargaxa mai auren da yake shirin karawa? Nibanyi fushiba daya munafunceni bai sanar dani cewan zai'yi aureba sai shi? Nikuma nayi amfani da kishina Wanda bashida maraba da leban wuta na ruguza komai, Kishiya a gdan Saheeb sai bayan raina". Umma Suhayr ce tace "kull inba hakaba zaki tafka kuskuren da sai kinyi Dana sani, wannan maganar inkikayi wasa yan Amin suka amsa toh Wallahi zaki mutu kuma yakara aure ke har hudu sainovels / JARABABBEN KISHI part 17 JARABABBEN KISHI part 17 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:43 "Umma bazan iya jure jin kalamanki ba, Maiyasa bazaki bani goyon bayan yaki da kishiya ba? Wallahi umma kishiya ba abokiyar zama bace" Suhayr ke maganar cikin muryar kuka. Umma tace "Tabbas suhayr kishiya abokiyar zamace idan kikayi dace" Tayi saurin cewa "Umma kiji kalamanki? cewa kikayi idan nayi dace? Nikam kishiya ba kwai bace umma bare in kwankwasa inji irinta, Umma idan kishiya abunyi ce maiyasa bantashi naganta agdanmu ba? Idan kishiya dadii ce maiyasa bakice Abba yakara aureba? Idan kishiya dadii ce meyasa Yawancin marubuta na duniyar yanar gizo ke fada mana illolinsu? Ita kanta *"Humairah B Melody"* tana daya aga cikin victim." Umma tace "Suhayr Karki zurfafa kishi don koba jima koba Dade namiji mai son aure saiyayi, Allah ya hadaki da miji jarababbe saidai kiyi hkr" tayi saurin cewa "Hkuri umma? Nikuma zanyi amfani da jarabata da *jarababben kishina* inci gaba da wargaxa mai tsari". Itadai umman Suhayr cewa tayi "Allah yaganar dake hanya madaidai ciya, Amma duk abunda kike na kyautatawa, tabbas kici gaba Karki fasa namiji wawa ne?. An hado mata sha Tara na arziki harda k'yautan mota tsalleliya daga mahaifinta, Akwati biyar nata' uku na jariri NOOR, Sannan ga kudi masu yawan gaske. Rago biyu Saheeb ya yankawa yaro, mai aikice tayi gyran nama ta soyashi tsaf makota kawai tamikama suma ba dukaba, dangin Saheeb sunyi tsaigumin Rashin kawo musu naman dabatayi ba ( *Nida belly mukace kuma da shegen zalama kuke*) Saheeb yafara sauyawa, yadaina fushi da ita Sun koma kamar da amma fa burinsa yananan na kara aure. Wata safiyane aka buga kofa, Direban gdansu tagani, "lafya naganka da sanyin Safiya?". Driver yace "Eh Alhaji ne yace in sanar miki da cewa kishirya wani sati ansama miki makaranta a *NORTH WEST UNIVERSITY*" "Dan Allah?". Tayi murna sosai, saboda murna saida tabashi tukwaici. Saheeb na shigowa ta karbi ledar dake hannun sa, tayi mishi maraba Yayi wanka ya gabatar da sallah sannan take gayamai cewa ansama mata makaranta, yaji dadii Kwarai yace Allah yabata sa'a Shiri suhayr takeyi zata gdasu tun Asuba ake dauki Tare suka fita da Saheeb ta saukeshi a shago itakuma ta wuce da alkawarin inzata dawo zata biyo tadaukeshi, " I love you Saheeb" tace tana mai kallonshi, yayi murmushi yace "your love to me is like a priceless Gold" itama ta mayar masa da cewa "You are expensive in my life Saheeb I can go on without you in my world". Dariya yayi yace, "Suhayr kenan duk abunda kika fadii nima haka nakeji a zuciyana". Kissing dinta yayi yashafa kan Noor Yace "ka gaida grany da takwara" Har yayi nisa ta kirashi "pls Saheeb banda kalle kalle". Hancinta ya lakuta yace "I promise you dat my love". Akan hanya ta sauka tayiwa Umma siyayya, tufa ta saimata da kayan marmari. Rike take da noor saiga wata mata daganinta baxawarace don bazaka kirata da budurwa ba. Duk'da ba abun mamaki bane samun babban mace kamarta batayi aure ba.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 18 JARABABBEN KISHI part 18 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:44 Kusada Suhayr ta matso tace "Sannu fah inason yaronki". Washe baki tayi abunka da mai yaro wawa "Tnx alot kin ganshi duk ya kosa yaje yaga grany". Matar tace "Ehyah inbazaki damuba Dan Allah meye sunansa dake kanki". Suhyr tace "Sunansa NOOR nikuma Suhayr". Daidai da an miko mata kayan data siya na kayan marmari. Tace "Dan Allah bawan Allah biyoni dashi". bayan boot ta bude ta zubasu. Tuni suhayr ta manta da wannan matar, motarta ta shige don Suhayr batason zakewa. "Baiwar Allah tsaya". Ina tuni suhayr ta figi mota..... Tana isa bakin gate tayi horn aka bude mata, Packing loge Ta nufa ta jera tata motar da sauran. Waya ta dauka don ta sanar ma Saheeb ta isa amma akasamu akasi yana waya kasar waje, don yayi odan kaya Ta kirashi yafi sau tulin gashin tinkiya amma shuru" Tuni zuciyarta tafara tafar fasa, cewa Saheeb da mace yake waya. K'ara k'ira tayi aka samu ak'asin a 'network' kiran yashiga wayar wata..... Bugu daya aka dauka Ba jira Suhayr ta fara bala'i ta inda take shiga batanan take fitaba "Ka tuna Saheeb you promise me cewa bazakayi waya da wata mace ba pls Saheeb kasan ko yadda nakeji yanzu?. Shuru taji Suhayr tace "mijina abun alfahari answer me pls" "Hello kiyi hkr ba mijinki bane" Damm!!!!!!!! Taji zuciyarta ta buga jin muryar mace Dayake shu'uma tasamu dukda bata Santa ba amma tana bakin cikin ganin mace ta hana mijinta sake wa Koh kuma mace mai shegen kishin tsiya. "Kinyi shuru nace ke wacece?" cikin zafin rai Suhayr take magana. "Islam ce Kuma ni budurwan mijinki ce, gashi kusa dani yana bacci daya tashi wanka zaiyi yayi sallah don bashida cikakken tsarki saimu wuce juffatu muyi shopping". Jiri Suhayr take gani idonta na juyawa, Karfin hali tayi tace "baki isaba yar iskama irinki harkin isa mijina yaxama abokin iskan cewar ki???? Karyarki tasha karya Wallahi kin gamu da ajalinki indai nice yar iska Mara mutunci Mara Sanin ciwon kai" Tsaki tayi tace "kinibibi sakarya indai mijinki ne ke kadai sai ingani. Katse wayan tayi. Mai gadi taba NOOR yashiga dashi tace tana zuwa Mota ta shiga Shagonsa ta nufa cikin ikon Allah yana ciki yana ta sallaman customers. Saida tabari ya sallami kowa tace "Saheeb kataimakeni ina cikin rudani wacece kaba wayanka?" Saheeb dafe kirji yayi yace "nooo Suhayr you most be dreaming tunda na shigo shago Wallahi ko waje ban lekaba". Mamaki duk ya cikata Kira wayar kiji cikin ikon Allah ta kira yadauka taji gashi dai muryan mijinta ne Duk sai taji kunyan ta kamata "Saheeb kayi hkriiii....." "Shhhhh!!!!! Karkiban hkr abunda nakeso dake shine./ JARABABBEN KISHI part 19 JARABABBEN KISHI part 19 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:45 "Abunda nakeso dake kizama mai yimun kyakkyawan zato, Kiyarda dani Suhayr " Suhayr tace "Saheeb kayi hkr amma kaji na rantse maka mace tadau wayanka". Saheeb yace "Haba Suhayr ana samun matsala daga network In mutun yakasa samun ka kawai sai suyi Diverting Call dinka saiya shiga wayar wani Inkuma dashi wacce ta dauka zata duba baxataga lambar ba" Tashi tayi tace "natafi don koh umma bata ganni ba" Saheeb yace "OK love you " kallonta Saheeb keyi Kaunar matarsa kawai yakeyi a ransa. Gida ta wuce ummanta tagani rikeda noor sai kuka yakeyi "Oyoyo umma" Umma ta tarbeta da cewa "dakata Suhayr narasa gane miki, wannan kishin ina rabaki dashi amma kinkiji." Suhayr tace "Umma menayi kuma" Suhayr tabata rai Umma tace "inajin duk Abunda ke faruwa shine kikaje shagonsa koh? kitadamai da hankalinki? In baki ba mijinki farinciki ba Suhayr mezaki bashi? nidai ina baki shaawara ki daina don bashida amfani, Amsheshi kibashi madara yasha". Haka sukayita hira har yamma gashi Abbanta baidawo ba, Tabar sallahu cewa tana gaidashi Zata dawo kafin ya koma. Saida tabiya ta shago ta daukeshi, Suna isa nimrah suka gani a bakin gate Sai cin magani take tana cika tana batsewa. Mai gadine ya bude gate suka shigo, Fitowa Saheeb yayi rikeda noor a hannun shi, ya kalli Nimrah yace "Nimrah lafya kike kuwa? Baki iya ki gaidani ba?" Nimrah tace "Dan Allah yaya kasan tun yaushe nazo gdannan? Kuma umma tace karna dawo saina ganka". Zaro Ido yayi yace "lafya?" Nimrah tace "Inafah kusan sati umma batada lafya bakaxo ka gaidata ba Koh kiranka akayi bakason dauka". Nimrah ta tabe baki ganin Suhayr taxo wajen Saheeb yace "Nidai banga kiranku ba gaskiya" Suhayr tace "nicenan nake kashewa, saboda muna cikin jin dadii ba Wanda ya isa ya hanamu sukuni" "keeehh Suhayr kinsan koh uwa tawuce gaban wasa? Yanxu da mutuwa tayifa? Saheeb ke magana cikin bacin rai. Suhayr tace "Dana shiga uku". Nimrah dake tsaye tana ballama suhayr harara , tace "kuma umma tace inna ganka mutaho tare". Suhayr tayi saurin cewa "Ba inda zashi sai gari ya waye" Nimrah tace "Aikam kinyi kadan inace kema wajen naki uwar kikaje? Kuma sainaga bai hanaki ba". Suhayr tace "ai uwata ce" Nimrah tace "shima Uwarsa ce" Kallonsu kawai yakeyi yana kallon son zuciya irinna Suhayr..... Baice da ita komai ba hannun nimrah ya rike taji kaman ta kurma ihu, tace "Saheeb ina kake shirin zuwa?" shuru yayi nimrah tace "gurin ummansa zashi" tafadi tana mata gwalo. Ciki Suhayr ta shiga tace "lallai sainayi maganin nimrah Saina nuna mata cewa ita karamar yar iskace", Kwafa tayi Sallah tafarayi Sannan ta shiga kitchen tafara girki. Taliyace macaroni ta Dafa Wanda yaji kayan lambu" Wanda ya hada da carrot, pea, harma da cabbage, Ga hanta Sai tadanyi pineapple juice Dan daidai. Farfesu tayi musu na kafan sa Tajerasu a dinning. Jikin mahaifiyanshi ya tsananta, Tuni yashiga rudu asibiti aka wuce da ita, Ruwa aka Samata. Dayake kusa da zoo road ne "Bari naje gda" yacewa kanninsa ya kawo musu abinchi Yana isa gdan yashiga Suhayr yake kwalawa kira Fitowa tayi cikin wasu yan iskan kaya Wanda bashida maraba da ace tsirara Take. Bata nunamai wani abu ba, Saima murmushi datake tana taku daya kan daya, Wanda tuni Saheeb yaji gaba daya jikinsa ya mutu, Kusa dashi ta matso "Wani irin kamshi yaji tuni ya sunkuceta ta sai daki kan gado ya ajeta. Yafara.HI novels / JARABABBEN KISHI part 20 JARABABBEN KISHI part 20 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:48 "Lafya yaya bai dawo ba har yanxu?" Cewar Sarah mai bima nimrah. "hmmm inkika bibiya wannan yar'iskan matar tasa ta hanashi ya fito" cewar Nimrah. Amrah dake zaune tana kallonsu Batace dasu uffan ba don arayuwarta ta tsani ayita cece kuce don ita tace Suhayr bata kai matsayin dazata dinga maganarta ba. Amrah hatsabibiya ce rigimanma don tace Nimrah batai komai ba. Nimrah tace "Amma bari na fita waje inje in siyo mana koda dankaline muchi". Nimrah ce ke magana daga ganin fuskanta kasan cewa akwai damuwa kwarai. Wata budurwace daganinta kasan tasha boko ta koshi tajiyo duk hirarsu. Tace daga gani da matar wansu suke Amma kuma sunban tausayi. Tashi tayi ta dafa kafadan Amrah tace "beautiful yanaga kin bata fuska? Kina neman ki bata kyawunki?" Amrah tace "Kamar yadda kika gani mahaifiyar muce ba lafya Kuma da yayanmu mukazo yaje ya kawo mana abinchi kinga bashi ba labarin sa Kuma baya rasa nasaba da matarsa don taki jinin mu balantana kuma umman mu Kila ita ta hanashi dawowa, yadda kikasan tayimai asiri". "Karki damu ya mai jinkin" ta cewa Nimrah. Nimrah tace "Da sauki bacci takeyi". "OK bari ina zuwa" flask taje ta dauko makare da abinchi ta kawo gabansu tare da cewa "Pls kannina kuci abinchi idan umma ta tashi kubata taci". Mamakin kirki irin nata sukeyi Sarah tace "inba zaki damuba inason Sanin sunanki". Budurwar tace "Ni sunana Atika". "Suna mai dadi" cewar Amrah. Har dare ya tsala Saheeb bashi ba alamansa, Haka suka kwanta a kujera sukasa Kansu a gefen gdon da ummansu take kwance. Washe gari kaman a mafarki Saheeb ya tashi, sai a lokacin yake tunawa da ummansa harma da kanninsa, tagumi yayi kawai sai hawaye Wanda nima Humairah bansan kona meye ba. Nashiga uku kallon Suhayr yakeyi wacce batasan me duniya take ciki ba Duka ya Dada mata ji kake tas!!!!! "tashi tabbas Suhayr zaki iya halakar danii bansan cewa kin kware a yaudara ba, bansan cewa bakida imani ba" Saheeb ke maganar cike da takaici. "Saheeb wat is the matter? You wake me up and you're insulting me? For goodness sake wat have I dont?". Suhayr ta fada itama da bacin rai. Saheeb yace "Ai daman baxaki saniba tunda kinyi succeeding nabar mahaifiyata da kanina da yunwa bayan nagaya miki cewa ummata tana asibiti kizuba abinci inkai musu". "Yanzu mekakeso kace Saheeb? Nabar mahaifiyarka da yunwa? Toh h you are wrong saboda hakkina dake kanka ka sauke, so i don't care". Ta fada tana mai niyyar komawa ta kwanta. Cikin bacin rai yace "Suhayr kafin in irga uku ki tashi kishiga kitchen kidafama umma abinci ki hadamun inkai musu inba haka ba Zan nuna miki true color na". Ya qarshe da tsawa. Haka Suhayr ta tashi Minti arba'in yayi yawa ta kammala. Ya dauki hanya sai asibiti, Yanata tunanin wace karya zaiyi ya gamsar da kanninsa? Yana shiga cikin asibiti wata ya hango ba wata bace Abeeda ce take ba ummansa abinchi a baki. Lokaci guda yaji sonta yashiga cikin zuciyarsa, "Inama Suhayr ce takewa ummata haka Danaji dadii" Abinda yake fada kenan a xuciyarshi. karasawa yayi yace "umma Ina kwana" koh kallonsa batayi ba Kanninsa ma kowa ya bata rai. "pls my sisters kuyi hkr wallahi........" Bai karasaba nimrah tace "nasan yaya tunkafin kaxonan kashirya irin karyar dazaka sharara mana Dan haka bamu da bukatar jin wani Abu daga bakinka" Umma dake kwance tace "kinyimun Daidai Nimrah kai dai kam kaji kunya wllh". Tsayawa yayi jikinsa duk yayi sanyi kunya duk tabi ta isheshi. "umma kiyi hkr tunda yasan yayi kuskure" Abeeda ke magana cikeda ladabi. "Umma albarkarku itace kadai ke tasiri a rayuwar mu Kishi mishi albarka sannan kidinga mishi Adu'a Allah ya tsareshi daga kaidin mace", takarasa tareda kallon Saheeb Wanda yayi nisa a fagen son Abeeda. (Tir kashi Abeeda dai kawar Suhayr ce amma batasan cewa saheeb mijin Suhayr bane kubiyoni donjin sauran labarin
0 comments:
Post a Comment