JARABABBEN KISHI Page 21 to 30
JARABABBEN KISHI part 21 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:49 Kwanan su biyu a asibiti Amma ba suhayr ba labarin ta, abun yana damun Saheeb amma bashida yadda zaiyi, Washe garin ranan da zaa sallamesu Saheeb yace "suhayr bakije kin gaida umma ba gashi har za'a sallamesu" Koh kallonsa batayiba tace "pls Saheeb kadameni wai shin ina ruwana da Rashin lafiyarta? Koh inada matsala da hakanne? Pls Saheeb ka kyaleni, ask you can see am ready to school So inkaje ka gaidata ga abinchi a dinning bissimilah". Koh kallonta baiyiba yace "kitashi kidauko cooler kisamun nawa abincin xankai musu asibiti". "ah ah Saheeb wai meye amfanin su nimrah da bazasu gda su daho abinci ba Tika tika dasu?". Inji Suhayr "Ba matsalanki bane inkinji toh kitashi inkuma bakijiba Zan fita can waje insiya musu". Suhayr tace "Tafi nono fari Kasan da hakan ka tsaya jaka ta dafa ka kai musu?". Tashi yayi don yanajin inya cigaba dajin munanan kalamanta zasu tarwatsa zuciyarsa. Akan hanyansa na zuwa ne yayi musu adar abinchi sunci sun sha Daga bisani aka sallamesu, adaidaita suka hau har gda. Abeeda tayi missing dinsu amma batada yadda zatayi Sunyi exchange na number, Domin sudinga gaisawa, itqma Abeeda takamu da son Saheeb. A hanya suhayr ta hadu da Abeeda tana tafiya tana yanga Packing tayi tace "yanmata ran gari Takawarki lafya". Dariya Abeeda tayi tace " wata sabon gani suhayr". Suhayr tace "Shigo mana kinsan mun tsaya akan titine". Ab茅eda ta shiga sannan tace "suhayr yaushe kikayi aure?" Suhayr tace "Hmm last year badai ke kintsaya ruwan Ido ba? kinganni harda Dana noor" "Nyc name" inji Abeeda. Suhayr tace "Northwest University nake zuwa kefah" Abeeda tace "Aini poly nakeyi, Ina HND ne". "Allah ya taimakemu "Yasu hjy keko Abeeda nadade inason ganinki Inaso ki rakani wajen wannan malamin hajyan Akwai Marsala". Abeeda tace "Suhayr matsalar me dagayin aurenki koh 2yrs bakiyiba?". Suhayr tace "Abeeda kinsan koh kishin danake akan saheeb? Kinsan irin taaddancin dana dinga yi? Akan so ya kara aure? Kafin aurena saida narabashi da yan mata sunkai biyar, bayan aurenmu kuwa bakwai na lalata, Ke har wajen daurin aure" "Wat!!!!!" Zare Ido Abeeda tayi tace "tab Suhayr ke shu'umace". Ta tabe baki tare da cewa "ai nafi haka ke Niko uwarsa bata zuwa gdana bare kuma kanninsa koh yan uwansa" Abeeda tace "tirkashi Ashe dakwai bikin zuwa babu Zane" A zuciyarta tafadi "tabbas Saheeb yayan Amrah shine mijin Suhayr" "OH my God Suhayr kin kade sai kinyi dakinsanin fadamun sirrinki, saina shigo rayuwar Saheeb Na hanaki sakat" A baki tace "OK xan rakaki amma yaushe kika shirya?". Ta danyi jim tana naxari sai kuma tace "ummmm Abeeda mu barshi weekend kinga am free ba school". Abeeda tace "Haka zaayi". Ahaka sukayita hiran har takai Abeeda bakin poly sannan ta wuce nata makarantar. Cikeda farin ciki Suhayr tace "Saheeb bakaiba kara aure, Sai anyimun maganinka Saheeb bawai muzgunama nakeso nayi ba sonka nakeyi Banaso wata taBBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 22 JARABABBEN KISHI part 22 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:07 Abeeda na isa gda tace da hajiya "Hjy kinsan meya faru yau Suhayr nagani Har tayi aure kinsan harta haihu?". "Iyeeh tabdi jam" inji hjy saude. Abeeda tace "Hjy ina Wanda nake baki labarin Rashin kirkinta ?" Hjy saude tace "eh" "Toh Ashe Suhayr ce Hjy duk yadda za'ayi inshiga gdan saina shiga koh ta halin kaka". Hjy saude tace "Yauwa yata haka nakesonki da jarumta, Karki sake ki karaya". Abeeda tayi dariya tare da cewa "Bakiji ba wai zan rakata gurin Malam ai kibari hjy (tsuntsu biyo zan jeho da dutse daya) Itace sakarya hjy" "Yauwa yata" hjy ta rungumo Abeeda tace", "Yar hjy, uwar hjy, yar lelen hjy, yar gaban goshin hjy, Kishiga ya auro hudu kuma ki zauna dasu, indai kisssace yanzu kai ya waye ba boka ba Malam iya ruwa fidda kai Wanda ya iya allonsa ya wanke". "Hjy yanzu zan kira Malam inyimai bayanin komai, yafara aiki tunda nasan a irin kallon da yakemun, hjy dakwai so a ciki" Malam suka kira tayimai bayani yace angama cikin kankanin lokaci zaki zama halak malak dinsa ammafa Saikinci damaran zama a gidan Saboda matar shu'umace duk yadda kike tunani tafiki Sannan ta mamayeshi kwarai Saboda yana masifan sonta Sannan gdan da suke ciki mallakin mahaifinta ne ke harta kasuwancin dayake kudinta ne". "Malam ai wannan duk ba wata matsala bace Masifa kuma ai saimuyita gwabzawa Mekarfi ya kwaci kansa". Malam yace "Angama" Washe gari tun safe Suhayr ta kammala aikinta, Saheeb yana zaune Tunanin Abeeda kawai yakeyi, duk Suhayr tana kallonsa da yanayinsa. Mai aikinta ta goge ko'ina Sun kammala. kusa dashi taxo ta haye kan kafarsa tace "Nurul-Q'alby Lafiyarka kuwa gaba daya ka canza? Kodai akwai matsalane a kasuwa?" Rungumeshi tayi har sunajin numfashin juna. "Talk to me Saheeb Your silence it wat I hate". Dagota yayi yace "my blood ba abunda ke damuna Saidai har yau nakasa cikama zuciyana burinta" "Zare Ido tayi tace "buri kuma? Wani burine Wanda ya wuce mu karasa rayuwar mu nidakai da yayana har abada?" murmushi yayi Amma na ciki na ciki yace "Hakane Suhayr Allah yabarmu tare" "Amin" tace "inaso zanje unguwa Amma bawani dadewa zanyiba Sannan a gda zan bar Noor". Saheeb yace "Amma Suhayr dakin tafi dashi inajin da hankalina yafi kwanciya" "Toh" tace tana dariya tace "your wish is my command". A hanya suka hadu da Abeeda, suka kama hanya sai wani kauye can gaban dawanau Gaban "kwa" in an wuce "Dungurawa" Wato "Doruwar shehu" Cikin unguwan suka shiga sai gasu a kofar gdan Malam din, Sunyi mishi bayani yace dubu talatinne ba yawa Da sauri Suhayr tafito da kudi zunzurutun kudin ta bayar. ( ni HUMAIRAH danida beelybadaru, akaba kudin muyita mata tsayuwar dare) Abeeda tace "Malam kar ayi sanya" yace "karki damu" Kallon suhayr takeyi tace "saikinyi dakin sani don saina maye gurbin duk abinda kika kasa Hakan zaisa nasamu matsayi a birnin zuciyan Saheeb" duk a xuciyarta take xancen. Sun kama hanya kowa da abunda yake sakawa Bayan sati hudu wata guda kenan, Saheeb yarasa sukuni har saida ya binciko gdansu Abeeda, Daga zuwansa yace aure yakeso nanda wata guda Sannan bayaso kowa yasani saboda karya koma kunnen matar sa. Soyayya mai ma'ana ce tashiga tsakanin su Baya iya barci sai yaji muryanta, Kullun saisun gaisa da yan uwansa, harma da umma lokaci guda ta asirce zuciyansu da akhairai. Shiko kanin Saheeb ba wadda yaki jini irin Abeeda, Don yace batai masa ba gwara Suhayr sau miliyan, So gamon jini" Kwatsam mustapha yaji ana zancen yayansa zaiyi aure kuma a boye musty yace "shikam bazai yarda a munafunce Suhayr ba," Gdansu Abeeda anata shiri biki saura satii biyu.I novels / JARABABBEN KISHI part 23 JARABABBEN KISHI part 23 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:11 Shiri akeyi gadan gadan, akalla saida Saheeb yayiwa Abeeda akwati biyar harda kit, Sadakinsa naira dubu hamsin Yabada komai na kawayen amarya. Saheeb ne tsaye yace "Abeeda daga yau baxaki sake ganina ba, sai ranan daurin aure". bata rai tayi "saboda me my Blood?" Yace "Saboda banaso Suhayr ta gane komai saboda tafara mun complain cewa Bata gane yanayina ba kinga karta dagoni" (Rikicin duniya damai rai akeyinsa) "hakane Amma dai zakazo dinner koh?" Cewar Abeeda. Yace "Eh zanzo karki damu" "Toh" tace ta juya tana jujjuya sassan jikinta komai na kadawa, Saheeb ya bita da ido har ta bace ma ganinsa. Shiko musty nazarin yadda zaayi a Raguza aurennen yake, Gashi yakasa zuwa ya sanar da suhayr, kwatsam saijin labarin dinner da aka shirya Yace "toh koh saina sanar da suhayr Kartace na munafunceta". Ayau ne daurin aure tun safe Saheeb ke shiri yakasa zaune yakasa tsaye. Suhayr duk tana kallonsa daga bisani tace "oh my God Dan Allah Saheeb safa da marwan me kakeyi? Saikace Mara gaskiya?" Da sauri ya juyo yace "suhayr kamanya wane irin zancene wannan" (Cewa tayi gulty conscious) " ! dole in tambaya saiwani rawan jiki kake kaman me shirin yin sabuwar amarya?". Dam gabansa ya fadi "Yauwa inaso ka kaini gdansu Abeeda kawata inyi mata godiya". "Godiyan me ????" Ya fada a dan tsorace, sai kuma ya maxe ya ce "Look suhayr yawonki yafara over fah kiyi hkr next week kyaje" tace "Allah yakaimu", Yana fita dagashi sai boxer, Daki ta nufa wata tsaleliyar shadda tagani bugagga Ga wata hula mai shegen tsada. mamaki ne duk ya cikata ina Saheeb zashi? Tab yau akeyinta (Rakumi da kayan tanka). "Saiko na hanashi zuwa koh ina falo ta dawo ta kalmashe kafa, Yazo ya wuce yasa shaddar sa fara kal, kitchen ta nufa da sauri ta debo miyar datayi na manja, fitowa yayi yana duba irin kyan da yayi Baiyi auneba ta taho da sauri Daidai da saheeb ya dago Gaba daya miyar ta kwaremai Gashi miyar da zafi". "Subhanallah!!!!!" Ta fadi tareda da cewa "swthrt am sorry it's a mistake " Kallonta yakeyi kaman yasa hannu aka ayita ihu!!!! "Suhayr kin kyauta kwarai" a zuciyarsa yace "Amma Daga gobe zaki gane kurenki". Daki ya wuce baice da ita uffan ba. Wata shadda yasa tsohuwa sawa daya Yasa hula ya fita, Abokinsa Marwan ne ya zo ya daukeshi a mota. Saheeb yace "My guy kaga abunda suhayr tayi mun? Miya ta watsamun a kaya" marwan yace "Mutumina gaskiya saika zama namiji inba hakaba Suhayr saita zamema annoba Saukinta ma Abeeda itama A ce". Andaura Aure kowa ya shaida, Abeeda sai murna take umman saheeb sai godiya take ga Allah, Yan uwa kowa sai barka yake mata. Musty ne Yakama hanyan zuwa wajen Suhayr don ya sanar da ita, saboda sauri yakalmi daban daban yasa Rigarsa a baibai. (Niko mexanyi banda dariya) take ya fada koh sallama babu "Lafya musty naganka hajaran majaran???". Musty yace "Ina lafya maye ya cinye amarya". zare Ido Suhayr tayi tace "a ina??ABBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 24 JARABABBEN KISHI part 24 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:13 Musty yace "Aunty bafa nufina meye ya cinye Amarya bane Yaya Saheeb yayi aure". "What???" batasan lokacin data mike tsaye ba, tace "musty kana nufin Saheeb dina yayi aure?" Musty yace "Kwarai aunty har an daura ma nima dazu nakeji". Suhayr tace "Tabbas Saheeb yayi kuskuren boyemun komai, amma kuma ban makara ba Naji ma zaayi reception". Ah ina musty ya gaya mata shiri ta tashi yayi tana zubda hawaye, a gda tabar Noor wajen mai mata aiki. "Musty zo muje" motarta ta dauka ta dauki madoki abunyin golf tasaka a bayan boot. gudu takeyi har suka isa wajen da ake partyn. Dayake tinted glass ne bawanda ya ganeta, tace "musty kazauna a cikin motan karka damu bari na shiga don banaso afara komai". Ta fita ta shiga ciki Saheeb ta hango yanata washe baki, Wato yayi amarya, chan ta hango kawarta Abeeda bakaramin razana Suhayr tayi ba, " what!!!!! Abeeda itace ta auri Saheeb????" Take tambayan kanta amma idanunta kodai gizo suke mata. "Nooo in mafarki nakeyi yaka mata in tashi, Nooooo dis won't be possible". ji tayi ankira Saheeb da,amaryar sa Abeeda ai sakato tayi Basu ankaraba duka suka faraji tako ina da sandar golf, kuma gata da bindiga kowa yakasa tunkararta, Tuni Saheeb ya fadi sumanme, itako Abeeda tuni kamanninta suka canza, baki ya kumbura amma Suhayr duka takeyi baji ba gani. saida tayi nasaran sumar da Abeeda Hjy saude lbr ya risketa tuni ta tsure. Loudspeaker ta dauka Tace "ina ma kowa murnan zuwa gaggarumin bakin biki Wannan da kuke gani maciya amana ne, Abeeda kawata ce wadda na yarda da ita amma shine taci amanata, Shikuma wannan da kuke gani ba kowa bane illar mijina kuma uban yayana, nasan dayawa mutane zasu kirani da mahaukaciya tabbas basuyi karya ba, Indai akan miji nane. Wutan kishi na damuna kwarai Bansan wace jaraba bace kecin sa yayi mun kishiya kuma kawata?, Kadan kuka gani". ta fadi tana kallonsu koh motsi basayi. Tiryan tiryan ta sakko tana taku daya bayan daya tace "kafin in irga uku kowa ya bace" ta nuna bindiga, Kan kace me kaman anyi ruwa an dauke. Ta tsallake su tayi waje, Tashiga mota suka koma gda. Suhayr tayi kuka kaman ranta zai fita amma duk abunda tayi tace bata huce ba.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 25 JARABABBEN KISHI part 25 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:14 Ambulance aka kawo aka kai Saheeb da Abeeda asibiti, Hankalin kowa saida ya tashi ciki harda umman saheeb. Abbansa yace "duk abunda ya faru Halima kece sila kuma ina gaya miki kisa kafar zuwa kashe gobarar da kika hada Da hannunki kuma a gdan danki Don ni ba abunda ya dameni wallahi " Shuru umman saheeb tayi, batace dashi uffan ba, Fuuuuuu tafita Suhayr ce tace "musty muje gdan naku". Hanya suka kama sai dorayi suna tafe kowa ba baka sai kunne A kan kwana ta ajiye shi Sbd kar ace tare suke, Koh Sallama babu Suhayr ta fada dakin umman Saheeb. "Ban taba Sanin cewa ke gurmi bace mai hada guri, umman innace miki uwar banza nasan wallahi banyi laifi ba, Umma tabbas kin saiwa kanki fetir din dasaiya konaki, Kin ziga Saheeb yayi aure don farin cikinki Bakisan akasin haka zaki samu ba, Zama da kishiya baxan iyaba saidai yau kitashi daga dakinnnan kibasu su zauna, sannan ki ciyar dasu Amma bada kudin ubana ba." Shuru umma tayi tarasa bakin magana. Suhayr tace "Dole kiyi shuru saboda kinsan baki shuka alkhairi ba Munafukar tsohuwa". "tub" tayi ta watsawa umma miyau tace "kadan kika gani saikinzo *zaman makoki (na Rashkardam*) Zaki gara ganewa idonki, Zakisan yadda zafin Kishi yake." Kai tasa zata fita kawai taci karo da Abeeda tsaye tace "zafin Kishi koh hauka????? Tambayanki nake?" Suhayr dago jajayen idonta tayi ta hankada Abeeda saida ta fadi. Suhayr ta taka wuyanta tace "ke in bakisan cewa ni yar taaddan mijina bace yau zaki sani, Kinyi gangancin shigowa hurumin daba nakiba, Saheeb is mine Abeeda mine alone" Kakari Abeeda keyi kaman zata mutu. Nimrah ce tace "tabbas bakisan darajar taki uwarba, dabaki zo har cikin gdanmu kinciwa uwarmu mutunci ba" A fisace Suhayr ta juyo tace "nimrah dake nake wayasa bakinki a ciki, oh baki sanni ba amma yau zaki sani bana daukan raini a wajen kowa bare ke" wanka ma nimrah mari tayi tace " Say a word again and I will show you the other meeee" tub tayi ta watsawa nimrah miyau. Kan Abeeda ta dawo tace "saidai wannan tsohuwar ta fita tabar muku dakin, amma badai gdan ubana ba Kinji". itama miyau ta watsa mata saitin bakin Abeeda. Sannan ta fice ta shige motarta saida tasa motar tayi gunji kannan ta figeta, don saura kadan ta take AbbanI novels / JARABABBEN KISHI part 26 JARABABBEN KISHI part 26 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:15 Juyowa yayi yace "tabbas wancan Suhayr ce Lafya take gudu kaman zata tashi sama?" Tabe baki yayi yace "Allah ya tsare." Tsakiyar tanka sheshen falonta ta tsaya tana huci, Tace "tabbas hakurina ya kare, Baxan iya jurewa irin abubuwan da Saheeb yakemun ba harya je ya aura kawata Koda yake bakomai Allah yana sama yana kallo ban gaxa ba, wajen yiwa mijina biyayya ba wajen sauke duk wasu hakko ki waje daya na gaza Wajen Rashin boye garwashin kishina, *JARAB EL GHIRA* (Akaro na farko da suhayr tafara karaya kenan) Saheeb baya ya farfado ya nemi Abeeda ya rasa, bai zarce koh ina ba sai gda koh a mutu koh ayi rai koda Suhayr zata yanka tsokanshi ne saiyaje ya fayyace mata komai. Abinchi takeci takeba noor abaki yana mata kwaranci, "Abba! Abba!!!" Kallonsa tayi tace "Abba baya sonmu karka sake kiran sunan Abba kaji." Hancinsa ta lakuta. "Saheeb yana tsaye yace "abbanka yana sonka sosai, karka sake kayi amfani da Kalmar umma She's rong" Dagowa Suhayr tayi da mamaki tace "what!!!!!? Mekazoyi gdannan? Kafin in rufe idona in bude Ka fit......." bata karasa ba ya rufe mata baki," *"Am going no whr suhayr you can do your worse but today you have to learn me your ears* Bantaba zatan zaki iya aikata munmunan aikin da kika aikata yauba". Hmmm wata dariyar mugunta tayi tace "koh ???". Saheeb yace "Ki tuna Allah subhanahu wata'ala yafadi acikin littafinsa mai tsarki, yace auri bibbiyu, uku uku hurhudu Sannan yace inbazamuyi adalciba muyi daya, Toh kinga inada kwakkwaran hujja ta kara aure". "Dakata Saheeb" cire hannu tayi daga cikin abinchin ta kira mai mata raino tace dauki noor kuje dakin wasa. Kusada Saheeb taxo tace "dole kasamu bakin yimun wa'azi tunda yanzu kasamu masu gdan rana, I don't blame you saheeb I never new that you are *Savege* till today, da baka da komai ai ka hkr da aure saboda jaraba dake cinka, na mamajo Saheeb inkaso kayi Hudu I don't care amma abunda nakeso Kasani, Inhar ka cuceni Daidai da kwayar zarra ban saniba toh Allah kadai zai isarmun ba mutum ba, Sannan indai anan gdan zakasa Abeeda toh bazan taba yarda ba, Sannan inaso muzauna Ayau muyi lissafi kabani uwar kudi kadauki riba, Saika ciyar damu dashi." TirkashiKISHI novels / JARABABBEN KISHI part 27 JARABABBEN KISHI part 27 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:16 Saurin juyowa yayi ya kalleta tace " kwarai yau za ayita ta kare tunda har ka iya kara aure, Nasan katsaya da kafanka kuma gdannan da kake gani na barshi nima Saidai ka kama mana haya mu biyu". Zare Ido yayi cikin rudani, nashiga uku meyasa Suhayr zata yankemun irin wannan hukuncin? "Pls Suhayr kiyi hkr kiyafemun," Tace "Ai ni bakamun ba amma kayiwa kanka, Inace kudi gareka? Kasani yanzu basai anyi nisaba, Zauna muyi lissafi gobe muje ka turamun a account dina". Saheeb bashida bakin magana Sai zufa yakeyi. Anyi lissafi ancire kudi naira miliyan biyu, Kudin da aka bashi jari, Saheeb yayi matukar mamaki ganin riba zunzurutun, riba har tafi uwar kudi yawa Baiyi mamaki ba saboda yasan cewa, ya San yadda yake tafiyar da kasuwancin shi, Murna ya dinga yi itako Suhayr bataso ba. "Toh ina saurare zuwa jibi Don baxan zauna a cikin gdannan ba, Gdanka nakeso inzauna bana ubana ba, Sbd ko wacce mace da gdan miji take takama ba gdan uba ba." "Toh" yace tunda yaga ta sauko, tashi yayi yace "zani gdan umma,Da sauri tace "Wace umma look man you are not going any whr we are sleeping together Harsai ranan daka sama mana gda mubiyu mu koma, In short koh shago bazaka budeba," Saheeb yana masifar son Suhayr shiyasa komi tayi yakanji haushi amma, sonta baya koh girgidi a cikin ziciyarsa. Gdansu Saheeb koh amarya tana chan tayi tsuru tsuru, sai hawaye ke zuba a idanunta. Kowa yaganta saita mikamai buhun tausayi, gaba daya halittarta Suhayr ta canza, Hatta hakoranta na gaba babu guda daya *"Nida ILILEE mezamuyi banda dariya, an maidata tsohuwar karfi da yaji"* Umman Saheeb ce ke lallashi, yan'uwan Abeeda duk sun zo. Umma tadinga basu hkr, Abeeda tace "yanzu wani mataki hjy ta dauka akan Suhayr?". "Wani mataki ta dauka kuwa suda sukeda sojaji da mopol da yan sanda? Ai sune gwamnati", cewa auntyn Zaria kanwar hjy saude ce aure ya kaita Zaria shiyasa ake ce mata auntyn Zaria. "Ke kinsan cewa matarsa yar iskace kika shigemai?" Abeeda tace "Aunty koda Suhayr zata kasheni ne naji nagani, zama da Saheeb ba fashi," Wage baki aunty Zaria tayi tace "Allah yabaku zaman lafya Kuzo mutafi, Ba Wanda yace kala, Sai kanwar babanta "inya samu gdan a kawo miki kayan dakin." "toh" Abeeda tace jiki ba kwari gashi ba Saheeb ba labarinsa. Musty ne yashigo yana waka, mai rabon shan wahala koh a karkashin gado yake saiya iskeshi, Kowa binsa yayi da kallo daga karshe ya fashe da dariya yace " ke kadan kika gani wahala yanzu kika fara sha, yanzu kika tsoma kafa indai Suhayr ce, kin kade, Ji yadda ta canza miki halitta wata rana kar yaki zatayi ta watsaki waje....." "Kai dakata" cewar ummansu "bansan shashanci".Home / JARABABBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 28 JARABABBEN KISHI part 28 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:18 Dariya yayi ya fice aguje. Saheeb yadamu kwarai Rashin ganin Abeedah haka itama. Neman gda yakeyi shida Suhayr suke zuwa koh ina, Anyi nasara ansamu gda a wajajen, kofar famfo. Flat ne kato mai falo biyu, akowani falo ana akwai dakuna biyu sai kitchen a ciki Suhayr tace "gda yayi kyau, yanzu zan dawo gdan mijina insakata in wala," kallon ta kawai Saheeb keyi. Yakasa cewa uffan, can yace "Yanzu hankalinki ya kwanta koh?" Juyowa tayi da sauri tace, "Ina ka taba ganin mai kishiya hankalinta a kwance? Ai har abada tana cikin tashin hankali har sai, saitaga tarabu da kishiyar nan lafya, ko kuma kishiyar ta mutu" Kasa cewa uffan yayi yace "muje insamo miki mai kwashe kaya" "Toh" tace acikin zuciyanta tace " hmmm na dauka zakayi magana ne Saheeb Dana fede ma bindi har wutsiya" Sun tare a gda daya Saheeb ya tarasu Don yayi musu fada, Sannan uwar gda ta fadi kwana nawa ta yanke? Zaa dinga raba kwana. "Dan Allah Ku hada kanku Suhayr banason tashin hankali, nayi aurene Don samun natsuwa da kwanciyan hankali, badon indinga raba fadaba,...... "Kai har kanada bakin cemun, kayi aure Don kwanciyan hankali? Daman duk zaman da mukayi daman zaman azaba kakeyi?" Saheeb yace "Ah ah Suhayr kinyi misunderstanding dinane ba haka nake nufiba".... " ai baka ba kwanciyan hankali, tunda ka iya kara aure, kwanciyan hankali sai dai kaji a makota, Kwana kuma kuya shafa kuna iya yankewa", fuuu ta tashi kitchen ta shiga tafara dafa abinci itada hawwa mai aikinta. Tuni kamshi ya bude koh ina gashi Saheeb yunwa yakeji, Tashi yayi ya fita duk akan idon Suhayr, Abu ya ruko a Leda guda daya.. " wato naka kaida amarya toh kayi kadan, kofar taje ta bude tace "Memuka samu ne Ango mijin amarya"? Bata tsaya ba ta amsa ledan taga kaza daya da kemuka, dagowa tayi tace "Ashe adalcin da kake ikirarin zakayi kenan.....
0 comments:
Post a Comment