"Na dauki wannan ka koma ka siyo muku Wanda zakuci nima inada bakin cin kaza." bata tsaya ta kalli fuskanshi ba, ta wuce kara fita zaiyi Abeeda tace karka damu Mijina na hkr, (Tabbas indai haka zaa cigaba da zama tabbas ba adalci) Koh sauraran Abeeda baiyi ba ya fita yaje ya siyo mata wasu, Ya wuce dakinta dashi, Wani irin darene Wanda gaba daya sunkasa tantace irinsa, babu Wanda ke dokin wani cikin su, kowa bakinciki yakeyi, (Ni HUMAIRAH mezance saidai fatan azauna ayita hkr). Suhayr sallar dare takeyi kullun har kwanan Abeeda suka kare, Tana Neman tsari Allah ya kareta daga sharrin kishiya. Ya shirya tsaf zashi shago, ya fito yace "Suhayr zan fita," Tace "Allah ya tsare ya kiyayeka yabaka sa a." wani irin dadi yaji Wanda baitaba jiba, tuni ya rungumeta yayi mata"hot kiss "Zan aiko harisu anjima zai kawo muku kayan abinchi." "Toh" tace "nima zani school, kabari kawai inzan dawo zan biyo in kwashi Kayan," komai cikin gdan Saheeb yana tafiya Daidai amma fah baida wani sakewa, Saboda Suhayr ta tsaya kaida fata cewa bata yarda da cuta ba, Wata Safiyar juma'a ne Abeeda na kwance tajiyo Suhayr ta kure waka, *Romantic* na korede bello da tiwa savage Itakuma a rayuwa ta tsani jin wani sauti dazai dame jinta. Tashi tayi koh Sallama ta fada falon Suhayr direct wajen home theatre ta wuce ta zare socket din. Suhayr abun yabata mamaki, baki bude Suhayr tace "ke wace irin karyace mara sanin ciwon kai? Banshiga harkanki ba kishiga nawa? Meye matsalanki da wakana, You must be very stupid Abeeda, you heard me ryt?". Abeeda tace "Kin wani cika mana gda da sauti ki tuna nan gdan mijinane Suhayr ba gdan ubanki ba". Ta nuna Suhayr da yatsa. Tuni Suhayr ta karya Dan yatsan tace, "kinyi kuskuren sako ubana cikin wannan maganan". wayarta ta dauko ta kira Saheeb yana dagawa tace "Saheeb yanzu zanyi kulikulin "Saude" da matarka." Saheeb yayi saurin cewa "Suhayr meya faru???". Tace "Bari na gama da ita tukun sai insamu daman yimaka bayani" Yayi saurin cewa "Noo Suhayr pls don't do that." Karaf ta katse wayan Tace "yau zan nuna miki cewa nima gdan mijinane, bulala ta samu takama Abeeda tayi mata lilis da jiki tace " get out of my room" ta nuna mata hanyan fita. "Yau naji ikon Allah na hana akawoki da redio ne? Zaki takurama rayuwana Yaunaji masifa Banda kaddara data Riga fata ke kin isa in tsaya dake?". Ta dinga sababi ita kadai Saheeb ne yabaro shago yazo kafin yazo tuni Suhayr ta gama da Abeeda, Kiransu yayi gaba daya yace "Suhayr meye dalilin fadannan?" "Saheeb nan dakinane koh dakina ba" yace "kwarai naki ne". Tace "inada ryt din yin yadda nakeso koh banda shi?" Saheeb yace "kina dashi" "Shine wannan kyankyason zata zo har dakina ta kashemu wakar da nakeji?????" Saheeb ya kalli Abeeda yace "Abeeda meyasa kikeson shiga sabgar daba takiba? Karki sake koda wasa Don wallahi Suhayr bazata raga miki ba, Kowa ya zauna a matsayin sa". *Bayan shekara biyu* Saheeb arziki ya bunkasa har kasar waje yake zuwa ya daina bada sako. Lokaci guda ya kankara katon gda flat hudu , (Aiki ga mai yinka) Ga sasan yara Gana mahaifinshi, Gana mai gadi. Suhayr kam ta kammala karatu, Aiki take a GtBank. Abeeda tunda tayi aure narasa dalilin ta na tsayawa. Suhayr tuni ta kara haihuwa, yara biyu lokaci guda, da Sadiq da farouq, Itako Abeeda yarta daya mai sunan mahaifiyar Saheeb. Kwatsam Saheeb ya kara Neman aure, Suhayr tace Sam vada itama ba wata sha'awa dazata bashi, Nanfa Abeeda ta tsaya kaida fata. Itace ta shirya akwati, Suhayr tace "yau naga sabon salo tusa a loudspeaker Hmmm kishiya har wata abun zakwadi ce? Anyi aure komai normal suka koma sabon gdansu Komai na daki saida Suhayr ta canza, Harta TV irin katonnan tasa, Suhayr yace zaiyi musu kaya itada Abeeda tace bataso abata kudinta. Gida yayi albarka da yaya. Duk shekara sai Abeeda ta haihu haka ma amaryar maryam, Itakoh Suhayr tace tagama Allah shi raya mata ukun, Saida saheeb yayi mata hudu ya rufe kofa, yayi farinciki yakuma godewa Allah daya barshi a Raye ya cika burinsa,ISHI novels / JARABABBEN KISHI part 30 JARABABBEN KISHI part 30 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:21 Kowa a cikin gdan yanabama suhayr girma, aunty kasa aunty sama. Har biyota sukeyi sasanta, Dukda tana Kishi amma daga baya taga Ashe abun ba haka yakeba, Inkayi Dacen abokan zama tabbas kayi babban sa'a Ana girma ana hankali, kannin Saheeb duk sunyi aure, haka Suhayr ta tsaya kaida fata, Amrah wan Suhayr ta aura Sulaiman, Rayuwar gdan Saheeb abun shaawa, Shikanshi girma yazo. *Noor yana Nile university dake Abuja, yanbiyu suna Turkish international college*, Ammafa fada tsakanin Abeeda da maryam anayi saboda maryam bata iya gani ta kyale, Suhayr ce tazama alkali, Maryam batada kunya haka takewa umman saheeb Rashin kunya, Suhayr tayi dariya tace "hmmm maryam kenan" ta dafata tace "Wata rana zaki bari nayi abunda yafi wannan Wallahi haka duk Rashin kunyanki nafiki, tunda kika ganni haka toh duniyace, ta horani, Naga ba sarki sai Allah abunda ake bazaa fasaba," Juyowan da maryam zatayi tace. "Bana bukatar wa'azinki, karki kuma shiga sabgan daba takiba". Suhayr ta mutu da manaki batasan lokacin data wanke maryam da mariba, tace "kinzo zamanin nayi sanyi kalau, Dabaki isa ki nunamun Dan yatsaba, Kaza kawai wacce bata gajiya da masifa Banda jaraba irinta maza me saheeb zaiyi dake? Yau nasan darajan iyaye baxan yarda kiciwa umma mutunciba, Never" ta tofa ma maryam miyau Abeeda tace "Suhayr antuna da kenan", babban abunda zatama ta wuce shine ya tofama miyau. Saheeb na tsaye yace "good Suhayr kinyimun Daidai". Da Sauri ya rungumeta. Yace "Duk cikin matana babu wacce rigimanta takaina Suhayr, tunda kikaga tayi sanyi toh Wallahi tayi Wanda yafi wannan muni, Kafin kizo." Nan ya tarsu yayi musu nasiha. Gda yadawo normal kaman da. novels / JARABABBEN KISHI part 31 the end
JARABABBEN KISHI part 31 the end
Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:23
Inna-nallahi wa'inna ilaihir rajiun, Tabbas dukkan
mai rai saiya dandana mutuwa, Allah yayiwa
mahaifin Saheeb rasuwa, sanadiyan mashin daya
bigeshi, Banda yaxo da ajali, koh kujewa baiyiba.
Family din Dan-koli sunyi babban rashi inda
Saheeb yakasa zaune yakasa tsaye. Anyi bakwai
kowa ya watse, Musty shine ke kan komai na
dukiyar mahaifinsu, dayake basuda yan'uba
Bayan kwana biyu suhayr tadawo daga office
karfe shidan yanma, Tajiyo hayaniya dayake da
gajiya sallar kawai tayi ta fita, maryam tagani sai
tada jijiyan wuya take, Tana cewa "don kin tsaya
kaida fata a auroni shine me? Sai naga niba cin
amana nayiba keko, ananar kawarki kikaci kika
aure mata miji Kece keda rabon shan kunya
baniba," Suhayr takasa koda motsi kallon Abeeda
takeyi wacce take cikeda ladama, Muryar suhayr
sukaji tana cewa "maryam banda shirme irin naki,
dani da Abeeda mutu a raba takaimin kaxa, Indai
akan cin amana ne nayafe mata duniya da lahira,
Sanadiyyan aureta nayi ladaman wasu abubuwa
da dama, ciki harda. rage *JARAB EL GHIRA
(flames of jealousy)* Danayi nagane cewa Kishi
ba hauka bane, Nagane cewa kishiya abokiyar
zama ce, tabbas kaman yadda nayi dace Daga
baya Da Abeeda taxo da zafin kai daga bayaba
taga ba riba fadan da kishiya, Maryam inaso kiba
Abeeda hkr Sbd munriga munzama daya, tunda
munada zuri'a". Ana haka saiga zulaihat taho
cikeda isa da takama, Tace "tabbas aunty suhayr
kinyi gaskiya, Munrigada munzama daya saidai
fatan Allah yakara hada kan duk wasu kishiyoyi,
dake fadin duniya, yabamu hkr zama da juna
sannan ya sassauta Kishi a tsakanin mu". Gaba
daya suka rungume juna, daganan kowacce tarike
girmanta, Saheeb koh anzama Alhaji, Saida
yakaisu duka Makkah harda mahaifiyarsa, da
mahaifiyar kowace matarsa, Saheeb yana cikin
farin ciki, a cikin gdanshi burinshi ya cika,
kowacce kokarin faratamai rai takeyi.
********************* Tamat billahi ina godiya ga
Allah mekowa me komai daya bani ikon kammala
wannan Dan kankanin littafin dafatan mun karu
kuma zamuyi amfani da abunda ke ciki. COPY AND SHARED BY SAKEENAT USMAN AND MARYAM AMEERAT YOLAAA
0 comments:
Post a Comment