Bissmillahir rahmanin rahim๐๐ป๐๐ป๐๐ป
Mama bata k'ara tambayar ta ba,dan tafi kowa sanin matsalar y'arta
Addu'a taci gaba da tofa Mata,bata bari ba harsai da tadawo cikin natsuwata
Lokacin ana kiraye-kirayen sallar asuba
"Kina yin wasa da azkar ko Rauda?
Mama tafad'a tana kallonta
Rauda ta girgiza kai alamar aa
Mama ta cigaba da cewa
"Aa kina wasa dashi banace miki duk sanda zakiyi bacci kiyi alwala ba, sannan kitofa ma jikinki addu'o i?yaushe rabon da kiyi hakan?
Rauda ta yi shuru tana tunani,dan ita rabonta da tayi alwala ko azkar d'in bacci har ta manta
Mama ta girgiza kai cikin damuwa
"Karatun al'qur ani ma kin rabu da yi ko?
Shuru Rauda tayi nanma mik'ewa mama tayi tafice daga d'akin dan d'auro alwala
Rauda ta jingina da jikin gado kanta nawani irin sarawa, gabad'aya yanzu tunanin ta nema yikeyi ya tsaya jitayi kamar ba ita ba
B'angaren Aasim,atsaye ya tadda ammi jikin wata k'atuwar bishiyar da ke cikin sahara
Wacce take gefen shiga masarautar
Kallo d'aya yamata yagano tashin hankali da tsananin damuwa a tare da ita
Kama hannunsa tayi suka zauna suna kallon juna
"Ammi,wai meke faruwa ne naga sak'on me martaba"
Ammi ta sauke numfashi tana bashi amsa
"Akan tarayyarka da Rauda ne,kasan tun bayan haihuwar shahida be kuma cewa komai ba,to jiya abu saima yaje fada
Yike cewa abunda kakeyi sam be dace ba,saboda da wanine yike aikata hakan da tuni an d'auki mataki akansa
Amma saboda kai d'an sarki ne,sai azuba maka ido ak'i cemaka uffan
Shine sarki yaturama sak'on Kira,kafin na turama nawa sak'on sai da naje na sami me martaban akan wani mataki yike shirin d'auka
Shine yace bega laifin abu saima ba,dan tabbas ba adalci bane,kana d'an da ya haifa kana aikata laifuka wanda kaine jigon masarautar,kuma ya zamar maka dole ka rabu da ita,domin auran jinsin d'an adam baya daga cikin tsarin masarauta"
Numfashi Aasim ya sauke,ya na kad'a kai
"Inbanda munafurci meya ruwan abu saima da rayuwata,nafahimcesa tunda nak'i auran y'arsa na nuna banason ta yashiga bak'in ciki Dani"
Ammi tadafasa cikin damuwa tare da cewa
"Nidai duk wannan bashi bane,abunda nikeso da Kai dan Allah ka amince ka rabu da ita, banaso ka bijirewa umarnin da mahaifinka ze baka,nayi maka alk'awarin tara maka kyawawan mata a jinsinka kazab'i wacce tafi maka........
Katseta yayi ta hanyar girgiza kai
"Bazan iya ba ammi,wallahi bazan iya ba,bazan iya rabuwa da ita ba"
Ammi tayi shuru tana kallonsa,durk'usawa yayi agabanta yana kama hannayenta
"Ammi kitaimaki rayuwata dan Allah,ammi bazan iya rayuwa inba tare da ita ba,idan da abunda zaki iya yi kiyi dan Allah"
Yafad'a cikin tsananin damuwa
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon cikin idonsa
"Aasim babu abunda zan iyayi,kasani kai kad'ai gareni bayan kai banida wani d'a aduniya, narok'eka kada ka fusata mahaifinka dan nasan ze iya d'aukar ko wani hukunci akanka,bar ganin yana sonka amma yafi son kimarsa da darajarsa fiye dakai kuma zeyi komai ne abisa adalci"
Aasim ze kuma magana ta had'e mai hannunta guri d'aya
"Kaga dai nice na haifeka amma narok'eka daka bi umarnin da ze baka,banaso wani abu ya sameka kai kad'ai nike dashi aduniya"
Ta k'arasa fad'a hawayen daya cika idanuwanta na gangarowa
Runtse idanuwansa yayi yana cize leb'ansa
Ammi ta mik'e tana kallonsa tare da cewa
"Zan wuce,gobe katabbata dakazo a lokacin da ya baka"
Jingina yayi da jikin bishiyar wasu zafafan hawaye na gangaro Masa
Ya bud'e idanuwansa yana kallon sararin samaniya
"Bazan iya rabuwa da ita ba,ya allah kataimakeni"
Yafad'a cikin damuwa da rashin sanin abunyi
Ita ko Rauda kasa komawa ta kwanta tayi,tunda tayi sallar asuba tana kan darduman
Gabad'aya jinta takeyi cikin damuwa,da kuma tsananin fargaba
Har mama ta kammala abun kari ta dawo d'akin bata tashi daga kan darduman ba
"Wai ke lafiyan ki k'alau kuwa? kintashi bazaki je kigaida baban ku ba"
Mik'ewa tayi jikinta babu k'wari,ta ninke dar duman tana yin hanyar waje
Mama ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta
"Rauda"
Rauda ta juyo tana amsawa
"Na'am"
"Meke damunki?
Mama ta tambaya tana tsare ta ido
Girgiza mata kai Rauda tayi
"Babu komai,banjin dad'ine kawai kai na ke ciwo"
Mama ta gyad'a kai had'i da cewa
"Shikenan jeki gaishe sa kidawo kisha magani"
Jinjina kai tayi tare da ficewa
Da sallama ta shiga d'akin Abba
Ya amsa,ta tsugunna tana gaishesa
Amsawa yayi yana kallon ta a tsanake
"Raudatu baki da lafiya ne?
Ta k'ak'aro murmushi tana cewa
"Aa baba,kaina ne ked'an min ciwo,shima kuma ba sosai ba"
Ya kad'a kai yace
"To tashi kije ki karya kisha magani,idan bedena ba anjima idan nadawo kasuwa sai inkaiki chemist"
"To"
Tace tare da mik'ewa tafito daga d'akin
Kan gadon mama tadawo takwanta
Tana jin maganar sa a cikin zuciyarta
"Habibty,anjima da daddare zamu tafi"
Shuru tayi tana lumshe idanuwanta,mama tadawo d'akin hannunta rik'e da kofin tea da paracetamol
Ta amsa tasha,tasha maganin sannan ta koma ta kwanta
Ranar mama ce da girkiDan haka bata zauna ba,tana ta ayyuka, Rauda tayi k'ok'orin fitowa ta tayata amma tace aa taje takwanta tunda bata jin dad'i
Wunin ranar haka Rauda tayi shi sukuku
Da yamma, tana bayi zatayi wanka ta tasa ruwan agaba tana kallo
Wani haske tagani ya b'ullo cikin bayin,sai ga Aasim ya bayyanaKallo d'aya suka ma juna suka gano damuwar da kowanensu yike ciki
Kauda kanta tayi daga kansa, gabanta na fad'uwa
Shiko wani kalar abune ya k'ara sukar sa,Wanda yasan tsan-tsar k'aunar tane
Tayaya ze iya rabuwa da wannan kyakkyawar halittan?
Yasan akwai kyawawan mata a duniya amma bega tamkar ta ba, tabbas baze iya rabuwa da ita ba
Gab da ita ya tsaya,dan tana jingine ne da bangon bayin
"Rauda"
Ya kira sunanta,ta juyo da kanta tana kallonsa ba tare da ta amsa ba
Shima shuru yayi suka kalli juna na y'an wasu sakwanni sannan yace
"Meyasa kika tada hankalinki?ba wani abun tsoro zaki gani ba idan munje,zaki ga kowane a suffar mutane kamar yadda kike ganina,kuma sannan ina tare dake,babu wani abun da zesa meki"
Juyawa tayi da niyyar fita daga bayin
Yasa hannu ya dafe bangon ya tare mata hanyar
"Rauda ki yarda dani, wallahi bazan cutar da ke ba"
Kallonsa tayi da idanuwanta da suka fara cikowa da hawaye
"Aasim,dan allah ka rabu Dani, kabarni inji da abunda yike damuna please"
Tak'ara sa fad'a tana tana juyawa da sauri ta d'ayan gefen
Jitayi ya rungumo ta tabaya,tayi saurin runtse idonta danji tayi illahirin jikinta ya amsa
Nannauyan numfashi yasauke yana sak'alo kansa ta gefen wuyanta
"Rauda,ina sonki,nasan kema kina sona dan allah kada kik'ara ambaton in rabu da ke"
Juyowa tayi dasauri,still Tana rungume a jikinsa,suna fuskantar juna
"To in ina sonka fa?yazanyi, zanciga ba da rayuwa dakai ne ahaka?
Meyasa kakasance a wani jinsi meyasa?
Tak'arasa fad'a tana fashewa da kuka
"Aasim ina sonka,dan girman allah idan mafarki nikeyi cewa kai ba mutum bane ka tasheni,nayi alk'awarin bazan sake yin baccin ba bare inkuma yin makamancin irinsa"
Tausayinta had'i da k'aunarta suka sake mamaye mai zuciya
K'ara rungumeta yayi yana runtse idanuwansa,cikin tsananin damuwa
Sai da suka kwashi minti biyar ahaka,sannan ya d'agota yana kallon kyakkyawar fuskarta data jik'e sharkaf da hawaye
"Rauda,nayi alk'awarin zan rayu dake ako wani irin yanayi, zanyi miki komai kamar yadda jinsin ki zeyi Miki,dan allah ki kwantar da hankalinki kinji?
Ta bud'e jik'akk'un idanunta tana kallonsa kawai batare da ta ka'ra cewa wani abu ba
Hannunsa yasa yana share mata hawayen
"Kinsan abunda natsana shine ganin hawayenki,shine abunda ke tada min da hankali,kibar yimin asarar su please"
Ya d'an numfasa sannan yacigaba da cewa
"Kinsan ya fuskarki take komawa idan kina kuka?
Ta tsaresa da kyawawan idanuwanta tana kallon yadda yike ya mutsa fuskarsa alamar haka tata fuskar take komawa idan tana kuka
Murmushi tayi,duk da batayi niyyar yi ba
Ya dafa kafad'unta yace
"Yauwa kokefa, Baki ga kinfi kyau ba"
Ya k'arasa fad'a yana sauke ajiyar zuciya
"Bari inbarki kiyi wankan,anjima dai kar ki manta"
Gyad'a masa kai kawai tayi,yayi murmushi tare da manna mata kiss a goshi
Ta sauke doguwar ajiyar zuciya bayan b'ace warsa sannan tayi wankan a sanyaye
Da daddare,misalin k'arfe goma,mama tagama Shirin ta tana mik'ewa
"Kisamin sakata a k'ofa,kada kibar min k'ofa ta kwana a bud'e sannan kiyi addu'a kafin ki kwanta"
"To"
Rauda tace,mama ta fice daga d'akin tana janyo mata k'ofa
Rauda tamik'e ta sa sakata a k'ofar falon sannan ta dawo ta zauna tana d'aukar wayarta dake k'ara
Numban Salma tagani,ta d'auka tana sallama
Daga can b'angaren salma tace
"Mara kirki,tunda baki kira kinji ya na sauka ba nina kiraki"
Rauda ta yi murmushi
"K'awa kina Raina,ya kike"
"Habibty"
Taji an fad'a abayan ta,ta waiga Aasim tagani
Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa salma
"Bari zankira ki ina zuwa"
Ta katse wayar tana kallon sa
"Muna iya tafiya?
Yatambaya,ta jinjina masa Kai alamar eh
A cikin y'an sakwanni taganta acikin sahara,babu gida gaba babu gida baya
Kallonsa tayi k'irjinta na dukan uku-uku
Amma takasa yin magana
"Abun hawa na hanyar zuwa yad'auke mu"
Begama rufe baki ba saiga wasu dokuna guda biyu,d'aure da wata kujera ta zaman mutum biyu da rumfa a samanta
Saurin rik'esa tayi,dan girman dokunan ya wuce misali,wani irin tsoro yafara d'arsuwa acikin zuciyarta
Aasim ya lura da hakan,ya yi mata murmushi cikin k'arfafa mata gwiwa
"Habibty kada kiji tsoro kinji?muje"
Yak'arasa fad'a yana kama hannunta,babu yadda ta iya suka shiga suka zauna,dokunan suka juya inda suka fito a guje
Rauda ko mamakine da aljabi ya dabai-bayeta
Gabad'aya gurin Sahara ne,amma kuma ga wasu bishiyoyi masu shegen kyau dasukayi ma wurin ado
Daga nesa ta hango wani katafaren gari wanda katanga ta za gayesa
Jitayi tsigar jikinta ta tashi yarrr
Ta yi saurin runtse ido tana ambaton sunan allah
Kallonta Aasim yayi ganin yanayin data fara shiga
Yasa ya kama hannunta ya damk'e cikin nasa
Ahankali taji tsigar jikin ta dena tashi,suka kalli juna yayi mata murmushin k'arfin Hali dan gabad'aya hankalinsa a tashe yike
A k'ofar garin dokunan suka tsaya,wacce take a kulle
K'ofar tana da fad'in gaske,tsayawar dokunan keda wuya k'ofar tabud'e
Wasu zabga-zabgan mutane Rauda tagani masu matuk'ar girma sanye da bak'ak'en kaya da wasu manyan takobi ahannayensu
Idanuwannasu jawur kamar gauta,tayi saurin rufe idanuwanta k'irjinta nawani mugun bugawa
Maganar su ce tasa tabud'e idon dasauri jin muryoyinsu a kausheshe
Gabad'ayan su zubewa sukayi a k'asa suna fad'in
"Barka da isowa,yarima,allah shi baka nasara"
Ya d'aga masu hannu yanayi musu magana da wani yare
Nan da nan suka basu hanya,dokunan suka cigaba da tafiya
Rauda sakin baki tayi tana kallon cikin masarautar,da tsayawa fasalta ta b'ata lokacine
Ga mutane kala-kala iri-iri kuma duk inda suka gifta sai sun zube suna kwasar gaisuwa
Kallonsa tayi taga kayan jikinsa sun sauya zuwa kayan sarauta,idanuwansa ma k'wayar ciki sun tashi daga bak'in dasuke sun koma wani kala
Shima d'in tsoro yabata,ta k'an-k'anme jikinta tana ambaton sunan allah
Cikin sauri yace
"Rauda,yazamarmin dole inkoma yadda nikene,ki kwantar da hankalinki dan allah,"
Bata sauraresa ba tacigaba da karantasu addu'o i, jikinta na kakkarwa
Bata yadda tak'ara bud'e idanuwanta ba harsaida taji dokunan sun tsaya
Tabud'e idanuwanta a tsorace tana kallon inda suke
Wani k'ayataccen wurine me shegen kyau daga can gabansa kuma wata k'atuwar fada ce
Inda take hango wasu sanye da fararen kaya zazzaune
Ta kuma runtse idanuwanta tana fad'in
"Aasim,kataimakeni kamayar dani"
Hannunta yakama yana karanto wasu abubuwa da batasan ko menene ba
Take taji tsoron da takeji yatafi,sai abunda ba a za rasa ba
Takuma bud'e idanuwan ahankali tana watsasu akansa
"Habibty babu abunda zesameki,mutafi fada,kuma idan munje duk abunda kiga nayi kiyi irinsa kinji?
Gyad'a masa kai tayi tana bin bayansa
Har k'ofar fada, gabad'aya wad'anda ke zazzaune rusuna masa sukayi suna kwasar gaisuwa
Banda wani me kama da larabawa da ya hakimce a kan wata kujerar zinari
Aasim ya rusuna agabansa,itama Raudan ta rusuna kamar yadda taga yayi
Aasim yace
"Allah ya taimaki me martaba"
Sarki Ramzad ya kad'a kai batare da ya amsa ba
Mik'ewa Aasim yayi suka d'anyo baya sannan ya zauna,itama ta zauna kamar yadda yayi
"Yarinya!
Sarki Ramzad yafad'a yana kallon Rauda
Ta kallesa batare da ta amsa ba, gabanta na fad'uwa
"Shin kinsan waye Aasim?
Ya tambaya still idanuwansa na kanta
Nan ma shuru tayi,dan bata da bakin magana
Sarki Ramzad ya cigaba da cewa
"Aasim d'ane,kuma magaji a wannan masarauta,sannan kuma rauhani"
Ya d'an numfasa kad'an,sannan ya cigaba da cewa
"Amma duk da sanin hakan,kika amince zaki cigaba da rayuwa da shi?
Nayi miki uzuri,awancan lokacin domin ko kina cikin rashin sani,amma ayanzu zan yanke hukunci a bisa saninki"
Ya maida kallonsa kan Aasim yana ambaton sunan sa,
Aasim yad'ago da kansa k'irjinsa na bugawa
"Ina buk'atar ka furta kalmar saki,ayanzunnan sannan kayi alk'awarin rabuwa da ita,taje ta auri jinsinta"
Cikin kad'uwa da jin kalaman mahaifinsa ya zube,cikin tashin hankali yace
"Kayi min afuwa,abi bazan iya furta kalmar saki a gareta ba"
Sarki Ramzad ya had'e fuska ya kuma mai-maita abunda yace
Nan d'inma kuma zubewar yayi
"Abi kataimaki rayuwata, wallahi ita kad'ai nikeso bazan iya rayuwa idan babu ita ba"
Sarki Ramzad ya kad'a kai yace
"Amma kasan a dokar masarautar mu babu auran jinsin bil'adama ko?
Aasim ya jinjina kai
"Nasani abi,amma kayimin rai kabarni naciga ba da rayuwa tare da ita"
Sarki Ramzad ya girgiza kai
"Abune da baze tab'a yuwuwa ba kana d'an dana haifa inbarka ka sab'awa shari'ar masarauta,dan haka ka furta saki agareta"
Ammi dake gefe ta taso cikin tashin hankali ta wanka masa mari
"Baka da hankali ne Aasim?da mahaifinka kake jayayya?
Sarki Ramzad ya d'aga mata hannu
"Ya Isa,ki k'yaleshi zanga iya kafiyarsa dakuma taurin kansa"
Komawa tayi inda take,tanayi ma Aasim wani kallo me cike da bada umarnin ya aikata abunda akace Masa
"Na baka minti biyar,ka aiwatar da abunda nace"
Sarki Ramzad yafad'a cike da k'asaita
Aasim ji yayi kamar kansa ze juye saboda tsananin tashin hankali
Gabad'aya fadar tayi tsit,kowa maganar Aasim yike jira
Ahaka har minti biyar d'in tayi
Sarki Ramzad ya sauke numfashi tare da cewa
"Bazaka bi umarnina ba kenan?
Aasim jan gwiwowinsa yayi zuwa gabansa ya fashe da kuka
"Abi, kagafarceni bazan iya rabuwa da ita ba"
Runtse ido sarki Ramzad yayi,cike da tsananin takaici
Yabud'e su ya watsa su akansa
"Aasim akan bil'adama kake jayayya Dani?
Aasim ya kuma fashewa da kuka
"Ni me biyayya ne agareka abi,amma ina rok'onka da ka yimin agaji"
Sarki Ramzad ya jinjina kai yana kallon me fad'an hukunci
"Miye hukuncin duk wanda ya karya dokar masarauta?kuma akace ya bari ya yak'i bari"
Me fad'an hukunci yayi shuru,yana tunanin abunda zece ganin d'an sarki ne dakansa
Sarki Ramzad ya katse mai tunani ta hanyar cewa
"Kada kayi la'akari da wai d'anane,kafad'i hukuncin da ya rataya akanshi"
Me fad'an hukunci yasauke numfashi tare da cewa
"Za'a koresa daga masarautar gabad'aya"
Sarki Ramzad ya jinjina kai yana kallon Aasim yace
"Kaji hukuncin da ya rataya akan duk wanda ya aikata laifi irinnaka,dan haka sai ka zab'a cikin biyu,
Ko kasaketa karabu da ita,ko kuma ka bar masarautar gabad'aya"
"Abi ni d'anka ne,kaji tausayina........
Sarki Ramzad ya katsesa
"Tunda ni amatsayina na mahaifinka ban isa inbaka umarni kabi ba,yazamar min dole ind'auki hukunci akanka,dan haka fad'i ina jiranka,wane kazab'a"
Yak'arasa fad'a cikin d'aga murya
"abi,kayi hak'uri ka gafarceni........
"Nace kazab'a d'aya ko?
Sarki Ramzad ya katsesa a fusace
Kallon Rauda yayi wacce gabad'aya itama hankalinta ya gama ta shi
Ya maida kallonsa ga me martaba da yike cewa
"Zan irga uku,idan har na irga uku baka saketa ka rabu da ita ba,to tabbas zaka bar min masarauta"
"D'aya.....
Biyu........
Cikin tashin hankali Aasim yace
"Abi dan girman allah.........
Sarki Ramzad ya d'an dakata yana jiran jin abunda zece
Amma kuma sai yayi shuru,yana cize leb'ansa da k'arfi tare da runtse idanuwansa
"Uku"
Me martaba yafad'a,ammi ta taso da sauri tana jijjiga Aasim
"Aasim,kadawo hayyacinka,takan mace,macen ma bil'adama zaka zab'i rabuwa da ahalin ka,maza ka rok'i gafarar mahaifinka ka aiwatar da abunda yace"
Tafad'a a zafafe cikin kid'ima
Bud'e idanuwan sa Aasim yayi yana zuba su akanta
"Ammi kigafarceni,bazan iya rabuwa da ita ba..."
Yafad'a cikin zafin zuciya
Ammi baya tafara ja tana girgiza kai
"Aa,aa, Aasim kada kayi min haka"
Abu saima ne ya mik'e shima cikin tashin hankali dan betab'a zaton Aasim ze zab'i barin masarautar akan Rauda ba,ga saima can tana kukan inda babu shi bazata iya rayuwa ba,kuma shi yayi hakanne dan sama ma y'arshi farin ciki dan yasan idan Aasim yarabu da Rauda dole ze auri saima
"Yarima kasan hukuncin duk wanda ya zab'i barin masarauta kuwa? Dole fa sai ka bi ta tauran
(Tauran wani wurine zagayayye,da yike da k'unci da zafi, Wanda duk bayan minti biyu yike fitar da wani k'ara me kama da sautin tsawa,wanda duk wanda yike ciki sai hucin k'arannan ya tsattsaga jikinsa)
Abu saima ya cigaba da cewa
"Wanda sanin kankane sai rauhan yatsaya acikin tauran har sai ya tsallake k'arar tauran guda arba'in da tara,shin kamanta da azabar dake cikin tauran ne?
Aasim yayi masa wani kallo me cike da tsana dan inba da din munafuncinsa ba da yanzu wannan abubuwan basu faru ba
"Nasani,kuma na amince ko da hakan zeyi sanadiyyar rasa rayuwata ne"
Gabad'aya fadar zaro ido sukayi cike da al'ajabi
Rauda da jikinta ya gama mutuwa hawaye suka gama wanke mata fuska saboda tsananin tausayin Aasim,shin wani irin so yike mata da ze zab'i rabuwa da ahalinsa saboda ita?
Cikin kuka ta matsa kusa dashi tana fad'in
"Aa Aasim,kada ka bijirewa umarnin iyayenka akaina"
Girgiza kai yayi yana kallonta da idanuwansa da suka rine
"Rauda ina k'aunar ki,zan iya hak'ura da komai inhar zan rayu dake"
Sarki Ramzad da jikinsa yagama yin sanyi duk da b'acin ran dayike ciki kukan d'annasa na tab'a masa zuciya
"Na baka daganan zuwa gobe,kaje kanatsu kayanke wa kanka abunda yafi maka,wannan ne adalci na k'arshe da zan maka
Idan har ka amince da rabuwa da ita,to kazab'i ko y'ar sarkin wace k'asa ce zan aura ma ita
Idan kuma har kakai goben kana kan bakanka na k'in rabuwa da ita to tabbas zaka bar min masarauta
Sannan kuma zaka tsallake tauran ninki biyu, d'aya na barin masarauta d'aya kuma na jayayya dani"
Bubbuga k'ofar da akayine ya sa Rauda ta tashi,akan gadon mama ta ganta
Tana jiyo muryar maman tana cewa
"Kitashi kiyi sallah"
Dafa kanta tayi da yike sarawa kamar ze rabe biyu tana girgiza shi
"Aasim,kada kayi haka dan Allah"
Y'arfillo.
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION๐ซ๐ซ๐ซ~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*๐นJINNUL*
*AASHIQUE*๐น
๐ง♂ ๐ง♂
๐ง♂
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_๐ง๐ป
_Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu_
๐
ฟAGE๐ 1⃣6⃣
Ina yima ษaukancin masoyana barka da sallah, dafatan anyi sallah lafiya, wannan Page na baku shi amatsayin barka da sallah, sannan ina me baku haฦuri akan jina shuru da kuka yi bani da lafiya ne ina buฦatar addu'arku
_7:32_๐ PM
FRI, JUN 7
_Bissmillahir rahmanin rahim_
"Aasim kada kayi haka,kada kayi haka dan Allah"
Tafad'a cikin tsananin damuwa
Bubbuga k'ofar mama ta kuma yi akaro na biyu
Cikin rashin k'warin jiki ta mik'e jiri na d'ibarta,ga kanta da yayi mata mugun nawi tana jin kamar an d'aura mata gingimemen dutse
Ta zare sakatar falon tana jingina da bango da sauri,dan ji tayi tana neman fad'uwa
Mama ta kalleta sosai tace
"Haryanzu kan bedena ciwon bane?
D'aga mata kai kawai tayi batare da tayi magana ba
Mama tasauke numfashi cikin damuwa tace
"Sannu,ina ganin idan gari yayi haske kawai zamu je k'aramin asibiti adubaki, k'ilan harda typhoid,kidaure kiyi sallan"
To Rauda tace tafito ta d'au buta tayi alwala,tana rawar sanyi
Lokaci d'aya zazzab'i me zafi ya rufeta,
A gaggauce tayi sallar saboda sanyin datake ji sosai,tana idar da sallar ta koma kan gado ta lullub'e
B'angaren Aasim kuwa,tunda taron fada ya tashi,yashige d'akinsa tare da kullewa dan gabad'aya baya son a damesa
Yana jiyo muryar ammi daga bakin k'ofar tana fad'in ya bud'e
Amma yak'i saboda baya son yaga tashin hankalin dake tare da ita,harta gaji ta wuce
Ya na zaune a k'asa kawai, cikin tsananin tashin hankali
K'wan-k'wasa k'ofar aka kuma yi,yaja gajeren tsaki tare da kifa kansa
Daga can k'ofar d'akin muryar mus'ab yaji Wanda ya kasance babban amininsa
Hannunsa ya d'aga yayi nuni da k'ofar, tabud'e
Mus'ab ya shiga d'akin Yana fad'in
"Wai meke damunka ne Aasim? Ace tun daren jiya ka kulle kanka a d'aki kakuma sawa d'akin takunkumi tayadda bawanda ze iya shigowa"
Aasim numfashi ya sauke yana d'auke kansa da ga kan mus'ab
"Kawai banaso a dameni ne,ina buk'atar natsuwa ne"
Mus'ab ya jinjina kai yace
"Hakan yayi kyau,inafatan a natsuwar da kasamu ka canza abunda ke zuciyarka,
Dan nasan jiya kana cikin rud'ani ne,shiyasa kak'i yin abunda me martaba ya umarce ka"
Aasim Ya sauke gauron numfashi tare da lumshe idanuwansa wad'anda suka kad'a sukayi ja
Mus'ab ya gyara tsugunnuwar da yayi yana k'ara fuskantar Aasim d'in
"Kayi shuru,ba kace komai ba,ko haryanzu kana kan bakannaka?
Ya bud'e idanuwansa yana d'aura su akan mus'ab
"Mus'ab,bazan iya rabuwa da ita ba,bazan iya ba"
Yafad'a cikin wani irin yanayi
Zaro ido mus'ab yayi yana kallonsa cike da mamaki
"Mekake nufi Aasim?kana nufin kazab'i rabuwa da ahalinka,takan bil'adama?
Yad'an numfasa sannan ya cigaba da cewa
"Ni wallahi banga abunda kagani agurin waccan bil'adamar ba,da yasa gabad'aya ka rikita tunaninka,
Dan allah kadawo cikin hankalinka,akwai kyawawan mata aduniya,ga kuma saima..........
Katsesa yayi ta hanyar d'aga masa hannu
"Dan allah kada ka k'ara b'ata min Rai,ni ita nike so kuma ita na zab'a zanyi rayuwa da ita,abunda nagani da ya rikita min tunani akanta kuma
Wannan ba damuwar ka bane,idan zaka bani shawara a matsayinka na aboki na kabani,idan kuma maganganun banza kazo kafad'a min ga hanya"
Ya k'arasa fad'a yana nuna mai hanyar fita
Mus'ab ya sauke ajiyar zuciya cike da juyayin al'amarin abokinnasa
"Aasim nikake fad'a ma haka?
Aasim ya d'aga kai yace
"To mekake so ince maka? A matsayinka na aminina kamata yayi kabani shawarar yadda zanyi insamu mafita amma kazo kana fad'a min abunda kasan ze k'ara min b'acin ran danike ciki"
Mus'ab yakuma sauke numfashi yana kad'a kai
"Shikenan,allah ya baka hak'uri"
Yafad'a yana mik'e wa ze fita
Sannan yace
"Bazan takuraka ba,akan fasa abunda kayi niyya,amma ina me baka shawara da kada ka bijirewa umarnin mahaifinka,katuna da haihuwar ka da yayi,da kuma rainonka har izuwa girmanka ko ba komai yaci wannan arzik'in "
Yana gama fad'ar haka ya fice
Doguwar ajiyar zuciya Aasim ya sauke tare da jinginar da kanshi
Tabbas yasan abunda yike shirin yi ba dai-dai bane,to amma ya zeyi? Ya zeyi da muradin zuciyarshi?
Ya runtse idanuwansa yana hango kyakkyawar fuskarta
"Bazan iya rayuwa babu keba *Rauda*"
Yafad'a tare da furzar da wata iska me zafi
Mik'ewa yayi yana fad'in
"Nasan zaka fahimceni abi,idan nak'ara yimaka bayanin yadda nike jinta a cikin zuciyata"
B'acewa yayi,be bayyana a ko ina ba sai abakin falon sarki inda yike hutawa
Kallo d'aya yayima kuyangin dake tsattsaye bakin k'ofar ya kauda kai tare da cewa
"Ku isar da zuwa na"
D'aya da ga cikinsu wacce take daf da k'ofar tace
"Yarima Aasim na buk'atar iso ranka shi dad'e"
Tafad'a cikin d'aga murya
Daga ciki aka basu izinin su bud'e k'ofar
Suka bud'e suna rusunawa
Gabanshi na fad'uwa ya shiga k'asaitaccen falon da akayi masa ado da zinarai kala-kala
Sarki Ramzad na zaune kan wata kujera me d'an fad'i ya jingina idanuwansa a lumshe
Shigowar Aasim d'inne yasa ya bud'e idanuwansa yana zubasu akansa
Cikin ladabi Aasim ya rusuna yana fad'in
"Barka me martaba,ina fatan kana cikin k'oshin lafiya"
Sarki Ramzad ya ce
"Lafiya,Ina fatan kaima haka?
Aasim yace
"Nima ina lafiya"
Sarki Ramzad ya gyad'a kai yana kauda kansa daga kallonsa
"Me ke tafe dakai?
Aasim ya d'an yi shuru sannan yace
"Inason magana dakai ne"
Jinjina kai sarki Ramzad yayi yana yima wazirin sa nuni da hannu alamar yafita ya basu guri
Cikin girmamawa wazirin ya rusuna tare da b'acewa
Sarki Ramzad ya maida hankalinsa kan Aasim yana cewa
"To ina jinka,fad'amin abunda kayanke ko sai munje fada tukunna?
Aasim ya sauke numfashi yana mik'e wa ya k'arasa gaban sa
Ya durk'usa tare da d'aura kansa a kan k'afafuwan mahaifinsa
Wasu hawaye masu zafi suka shiga gangarowa daga idanuwansa
Sarki Ramzad ya sauke numfashi tare dasa hannunsa yadafa bayan sa
Tabbas babu abunda yi keso sama da Aasim, yana matuฦar jinsa acikin zuciyarsa
Kuma babu abunda yafiso irin yaga Aasim cikin farin ciki
Amma dole ne ya dakatar dashi
Cikin kwantar da hankali yace
"Aasim, ka sani bawai na hanaka abunda kake so bane, dan jin daษina
A'a, saboda adalci ne, domin babu wani rauhani daya isa yayi haka a ฦyalesa, Kaga ko bekamata na ฦyaleka ba dan kana ษan dana haifa
Kasani da zarar akace babu ni, to kaine mai mulkin wannan masarautar
Ya kamata ka fahimce ni, nayi maka alฦawarin ko ฦดar gidan wacece idan Kaga tayi maka zan auramaka in har a jinsin ka ce
Amma baze yuwu in barka ka cigaba da rayuwa da bil adama ba bazeyu ba"
Aasim ya ษago kansa cikin muryarsa da ta dishe yace
"Abi,dan Allah kabarni nayi rayuwa tare da ita,ita kaษai nike so banajin zan iya rayuwa da wata mace a duniya in ba ita ba........
" dakata!
Sarki ramzad ya katse sa, sannan ya cigaba da cewa
"nabika ta faษa bakaji ba, na bika ta lallami nanma bakaji ba
To kasani bazan takura ka ba, tunda har ban isa dakai ba, nan da awa ษaya zamu je fada, duk abunda kayanke kafaษa acan"
Aasim ze kuma magana ya dakatar dashi ta hanyar ษaga masa hannu
"bana son na kuma jin komai daga gareka, tashi ka bani wuri"
"Abi.....
Be ฦarasa ba, sarki ramzad yasa hannu ya ษatar dashi
ฦarfe takwas suka isa ฦaramin asibitin gwamnatin, sun tadda mutane da yawa akan Layin ganin likita
Hakan yasa suka zauna suna jiran layi yazo kansu
Kallo ษaya zakama Rauda, kagano ramar da tayi acikin kwana ษaya kacal
Kallon jama'ar dake wurin kawai take yi amma zahiri hankalinta baya gurin
Damuwarta ta kuma ฦaruwa yayin da taga har zuwa lokacin bata ji wani alamun Aasim ba,
Me ya faru dashi, bayan dawowarta? Shin ya amince ya rabu da itanne ko yaya?
Tambayar da tayi ma kanta kenan wacce bata da amsar ta
Maganar sa ce ta dawo mata
_"Rauda ina ฦaunarki, zan iya haฦura da komai inhar zan rayu dake"_
"baze amince ya rabu dani ba nasani"
Tafaษa a fili batare da tasan maganar ta fito filin ba
Mama dake zaune kusa da ita ta kalleta cikin rashin fahimta tace
"mene?
Kallon maman tayi itama cikin rashin fahimtar
" waye baze amince ya rabu dake ba?
Mama ta jefo mata Tambayar tana kafeta da ido
Daburcewa Rauda tayi, dan ita bata san maganar da tayi a zuciya ta fito fili ba, ta rasa me zata ce
Numfashi mama ta sauke tana kaษa kai, lokacin layi yazo kansu tamiฦe tayi gaba batare da ta kuma cewa komai ba
Rauda tabi bayan ta, gwajin farko da likita yayi ya gano BP ษinta yayi ฦasa sosai
Kallon ta yayi yana cewa
"meke damunki? Da BP ษinki yayi ฦasa haka?
Shuru Rauda tayi, likitan ya cigaba da cewa
" BP ษinki yayi ฦasa sosai, shi yasa kike jin ciwon kai da kuma jiri, zan rubuta miki magunguna Asiya kisha, sannan kidena barin kina shiga cikin tunani Allah ya ฦara lafiya"
Mama ta amshi takaddar maganin suka, fito kowanne zuciyarsa babu daษi
Napep suka hau ta kawo su gida suna gab da tsayawa taji maganar Aasim
_"kisameni a bayi yanzu"_
ko tsayawa bata bari mai nepep ษin ya gama yi ba ta diro
Cikin faษa mama tace
"wani irin ganganci ne wannan? miye kikema sauri da ba zaki tsaya yagama tsayawa ba?
Cikin sauri Rauda tace
" bayi nikeso na shiga"
guntun tsaki mama ta ja,tana zage Jakarta zata ba mai Napep ษin kuษi
itako Rauda ta ฦagara tagansa,juyawa tayi da sauri ta shige cikin gidan
Ko buta bata tsaya ษauka ba ta shiga bayin
A tsaye tagansa,rufe ฦofar bayin tayi da sauri tare da ฦarasawa inda yike
"Aasim, kana lafiya? Me ya faru na jika shuru? Ince dai ba wani abu a kayi maka ba?
Ta jero mai tambayoyin cikin zaฦuwa da son jin abunda ta tambaye sa
Be bata amsa ba, illa rungumeta da yayi,yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya
Ita ษinma ajiyar zuciyar ta sauke, tana jin sonsa na bin duk wani sassa na jikin ta
"kabani amsa mana Aasim"
ฦagota yayi ya zuba ma fuskar ta ido amma kuma har lokacin beyi magana ba
Kawai yana hango yadda za ace yayi rayuwa babu ita ne
Girgiza kai yayi yana ฦara rungumeta sosai
"baze yuwu ba, baze yuwu ba"
Yafaษa cikin tsananin damuwa
"miye baze yuwu ba, kayi min magana yadda zan fahimta dan Allah"
Kuma ฦagota yayi yasa hannayensa duka biyu ya tallabo fuskarta yace
"Rauda inaso kiyimin alฦawarin cewa ba zaki taษa rabuwa dani ba,har ฦarshen rayuwarki"
Kallon sa ta keyi sosai,
"Aasim kasani ai, bazan iya rabuwa dakai ba"
Girgiza kai yayi, yace
"nasani a yanzu, amma bansan meze iya faruwa nan gaba ba, shi yasa nikeso kiษaukar min alฦawari da kanki da kuma bakinki"
Kaษa kai tayi tare da cewa
"shi kenan nayi alฦawari bazan taษa rabuwa da kai ba"
Gauron numfashi ya sauke yana gyaษa kai
"nagode, wannan alฦawarin da kika ษauka a yanzu ya kuma ฦarfafamin gwiwa,zanje in sanar dasu abunda na yanke"
"amma Aasim, bekamata.......
Katseta yayi
" kinga Rauda kada kice komai,na san watarana zamu dai-daita dasu, amma ke bazan iya jurar rashinki dai-dai da rana ษaya ba"
Be jira jin mezata ce ya ษace
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi, tare da fitowa daga bayin, ษaki ta shiga ta zauna akan gado
Maganar daya faษa ce kawai take yi mata yawo a kunne
_"kinga Rauda kada kice komai nasan wata rana zamu dai-daita dasu amma ke bazan iya jurar rashinki dai dai da rana ษaya ba"_
Sauke ajiyar zuciya tayi, ta janyo filo ta ษaura kanta
Meyasa ze zaษi rabuwa da ahalinsa saboda ita? Me yasa?
Tayi wa kanta tambayar
Lumshe idanuwan ta tayi, tana fatan ace har yanzu Mafarki take yi
Dan har lokacin ta kasa gasgata abunda ke faruwa
ฦangaren Aasim kuwa, lokacin da ya koma masarauta saura ฦดan mintoci a tafi fada
Yana zaune a ษakinsa ya zuba tagumi, fulawar saฦo ta shigo ษakin
Hannu yasa ya damฦe, saฦon ammi ne tana son ganin sa
Kamar baze je ba, sai kuma yaga rashin dacewar Hakan
Miฦewa yayi ya bayyana a ฦofar sashenta
"ku isar da zuwa na"
Yace ma kuyangin dake bakin ฦofar
Tun kan su kai gayin magana aka basu izinin buษewa
Shiga yayi da sallama yana rusunawa
Ammi tayi ma jakadiyarta nuni data fita sannan ta dawo da kallon ta kansa
"Aasim ni kake wulaฦantawa ko? Ace tun jiya nikeson yin magana da kai amma ka sawa ฦangaren ka takun kumi ko?
ฦasa yayi da kansa
" kiyi haฦuri ammi, ba nayi Hakan danna ษata miki bane, nayi ne dan nasamu natsuwa"
Ta jinjina kai tace
"yayi kyau, saura minti biyar taron fada, me ka yanke a zaษin da aka baka?
Shuru yayi yana nazarin abunda zece
" tambayar ka nikeyi kayi min shuru"
Cikin fargaba yace
"ammi ki gafarceni, amma banajin zan iya haฦura da duka zaษi biyu"
Kaษa kai tayi cike da ษacin rai da kuma tashin hankali
"kadai ce kawai ka zaษe ta a kanmu, ka fifita bil adama akan iyayenka
Wai shin Aasim lafiyar ka ฦalau kuwa? Ko ko taษin hankali ne yasa meka?
Taษan numfasa sannan ta cigaba da cewa
" shin kana tunanin bil adama zata sama ma dauwamamman farin ciki ne?
Kayi babban kuskure Aasim, ko da yike laifi na ne da na goyama baya tun farko
Amma ina so ka sani nadama da danasani zasu biyo bayan ka inhar kazaษi rayuwa da ita sannan........
ฦarar sanar wa data Kaษa ita ta dakatar da ita
Numfashi ta sauke tana ษauke idanuwan ta a kansa
"lokaci yayi, zaษi ya rage gareka, abu na ฦarshe da nike so kasani shine. Idan har kazaษi rayuwa da ita to kada ka ฦara zuwa inda nike,kaje inayi maka fatan alheri"
Tana gama faษar haka ta ษace daga gurin
Aasim numfashi ya sauke Yana Miฦewa cike da tsananin ruษani tabbas ya san ze aikata babban kuskure amma yana da yaฦinin iyayen sa ba zasu iya jurar rashin sa ba, nan da wani ษan lokaci zasu nemesa kuma ma ya san da wuya Abi ya zartar da hukuncin kora a kansa ฦilan yafaษi Hakan ne dan ya tsorata sa ya rabu da rauda
ฦacewa yayi ya bayyana a fada, kamar kullum fadar cike take da manyan rauhanai
Suna zazzaune, Aasim na bayyana suka rusuna suna gaishe sa
Saida Aasim ษin ya zauna a kujerar sa sannan suka ษago
Shuru ya biyo baya na wasu mintoci, sannan sarki ramzad yayi gyaran murya
Hakan yasa fadar yin tsit
"Aasim, kafaษa ma fada abunda ka yanke, shin ka haฦura zaka rabu da itanne? Ko ko kana kan bakanka na rayuwa da ita?
Aasim yayi shuru cike da tsananin fargaba
Sarki ramzad ya kuma mai-maita tambayar sa sannan ya ฦara da cewa
" bana buฦatar jin shurun ka, rayuwa da mu kazaษa ko rayuwa da ita?
Aasim saukowa yayi daga kan kujerar ya durฦursa
" Abi ka gafarceni, har yanzu nakasa yanke komai, bana jin zan iya Haฦura da duka zaษi ษiyun da ka bani"
Sarki ramzad ya jinjina kai yace
"kenan har yanzu kana kan bakanka na ฦin rabuwa da ita?
Aasim ya ฦara dur ฦurshewa
" Abi dan Allah, kayi haฦuri kabarni na cigaba da rayuwa da ita, nayi maka alฦawari bazan sake aikata kuskure ba.......
ฦaga mai hannu sarki ramzad yayi cike da ฦunar zuciya
" ya isa, ka riga da ka bani amsar tambaya ta, dan haka kada ka ฦara cewa komai"
Aasim ya runtse idanuwan sa yana ambaton sunan Allah
Sarki ramzad ya maida kallon sa ga rauhanan da suka yi jugum jugum saboda mamakin kafiyar da Aasim yayi
Yace
"tunda abunda ya zaษa kenan, to bazan fasa hukuncin dana yanke ba, dan haka aje a shirya tauran zuwa jibi za a zartar da hukuncin"
ฦaya daga cikin manyan fadawanne ya durฦusa cike da tashin hankali yace
"mai martaba, Aasim ษan kane, be kamata ayi masa hukuncin kora ba, a sassauta masa ranka shidaษe"
Shima wani ba faden zubewar yayi yana faษin
"a sassauta masa ranka shidaษe, a canza masa wannan hukuncin"
Sarki ramzad ya girgiza kai
"babu ruwan ku da matsayinsa, na riga da na yanke hukunci kuma wannan hukuncin shine adalci dan haka bana so na ฦara jin wani daga cikin ku ya furta komai, aje a shirya tauran kamar yadda na bada umarni"
Gabaษaya jikin Aasim ya gama mutuwa, amma ya kasa ฦara furta komai
Hawaye kawai yikeyi, a haka aka watse daga fadar cike da juyayin al'amarin
Tunda Aasim ya koma ฦangaren sa ya kwanta, yana ta tunanin bijire ma mahaifinsa da yayi
Tabbas yayi kuskure kuma be kyauta ma kansa ba
Buษe ฦofar ษakin aka yi aka shigo
Ya ษago yana duban me shigowan, shaida ce
Ya tashi ya zauna yana kamo hannunta
"shahida, lafiya na ganki wani iri? Baki da lafiya ne?
Cikin gwaran cinta tace
" ba kai bane,kake ta yin kuka ษazu"
ฦดarfillo.
[7/12, 10:50 AM] Harira Aliyu Mrbcy: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION๐ซ๐ซ๐ซ~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*๐นJINNUL*
*AASHIQUE๐น*
๐ง♂ ๐ง♂
๐ง♂
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_ ๐ง๐ป
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
๐
ฟAGE ๐ 1⃣7⃣
Wannan Page nakane......... Ina alfahari da kai a ko da yaushe
_9:15_๐ PM
SAT, JUN 8
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_
Murmushin ฦarfin hali yayi yana ษaukan ta ya ษaura ta ajikinsa
"dan kinga ina kuka, shi ya sa kika yi wani iri? Ba kyaso kiga ina kuka ne?
Shahida ta ษaga kai alamar eh
Murmushi ya kuma yi yana tallabo kyakkyawar fuskarta
"shi kenan farin ciki na, daga yau bazan sake yin kuka ba, kinsan Abi ษinki na sonki da yawa baya so ya ganki cikin damuwa"
Shahida tayi murmushi tana kwanta wa a jikin sa
"abbi,ina ammi na?
Aasim yayi shuru, yana kallon ta
Shahida ta ษago kanta tana kallon sa tare da nanata tambayar da tayi
Yayi ฦoฦorin kauda damuwar dake fuskar sa yace
" kinaso kiganta ne?
Shahida ta ษaga kai da sauri
Ya rungume ta ajikinsa yana sauke numfashi
" shi kenan, ki ฦara haฦuri kinji? Zaki ganta har sai kin gaji, yanzu faษamin me kikaci yau?
Haka ya dinga lallaษata har tayi barci, sannan ya kwantar da ita
Ya tsura mata ido yana jin tausayinta, kullum bata da maganar da ta wuce ina amminta?
Gashi da wuya ta rayu da ita yadda take so numfashi ya sauke tare da nuni da hannun sa
Wani ฦaton madubi ya bayyana, ya sake yin nuni da hannun sa
Sai ga Rauda ta bayyana a ciki, har lokacin tana kwance akan gado tana rawar sanyi
Ta duฦunฦune da bargo
"Rauda!
Ya kira sunan ta, ta buษe idanuwan ta a hankali tana duba inda ta jiyo muryarsa amma bata ga kowa ba
Ya sauke ajiyar zuciya yana jin ฦaunarta na ฦara ratsasa
Hannu yasa ta cikin madubin ya ษaura a wuyan ta yaji zafi rau
Ita ko zabura tayi dan bata ga kowa ba ta kuma ji antaษata
Guntun murmushi yayi tare da faษin
"matsoraci ya, nine"
Ta ฦara duba kan gadon bata ganshi ba, a hankali tace
"to kana ina? Ya aka yi bana ganin ka?
" ina masarauta, nima banajin daษine bazan iya zuwa ba, kinsan duk abunda kikeji ajikinki inaji ajikina,ga kuma damuwar da nike ci"
Ta maida idanuwan ta ta Lumshe tare da cewa
"da gaske kana jin yadda nikeji a yanzu?
Ya ษaga kai kamar tana ganin sa
" sosai habibty,zafin jikin ki yayi yawa,kinsha magani?
Ta ษaga kai alamar eh
Ya jinjina kai
"sannu Allah ya baki lafiya,nan da ฦan-ฦanin lokaci zakiji sauฦi in sha Allahu"
"yanzu me kake yi? Ina so in ganka"
Ya gyara zamansa yana dai-dai ta saitin madubin
"to shi kenan rufe idanuwan ki ki natsu sosai"
Ta rufe kamar yadda yace, amma ba ta ganshi ba har zata buษe, sai taga duhun dake cikin idanuwan ta ya fara yayewa
Ahankali Ahankali har duhun ya yaye gaba ษaya ya bayyana
Guntun numfashi ta sauke tana cewa a zuciyar ta
"wannan kyawun naka dama ai sai jinsin aljanu"
"habibty"
Ya kira ta,ta amsa na'am
"kinyi mafarki ษazu ko?
Ta ษaga kai alamar eh
Ya jinjina kai
" to ba mafarki bane, abunda ya faru a fada ne kika gani"
Jikinta yayi sanyi
"amma Aasim Meyasa zaka yi haka, Hakan ba dede bane, Meyasa bazaka bi umarnin su ka rabu dani ba?
Ya sauke nannauyan numfashi, tare da dafa ฦirjinsa
" ba zaki gane yadda nike jinki a nan ษina ba, wallahi Rauda bansan dalilin da yasa nike miki irin wannan son me zafi ba, jini keyi kamar idan na rasa ki zan iya rasa rayuwa ta, nima ba da son raina na bijire wa umarnin su ba, amma nasan ba zamu jima ba zamu dai-daita dasu"
Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina girman ฦaunar da yike mata
"amma ya maganar tsallake tauran da Naji anyi magana?
Ya sauke gauron numfashi yace
"zan tsallake jibi"
Jikinta ya ฦara yin sanyi
"Aasim dan Allah inda hanyar da zaka bi kabi, bana so kasha wahala"
Yayi murmushi yana sa hannu ta cikin madubin ya kama hannun ta tare da matsewa cikin nasa
"kar ki damu habibty, tabbas nasan tsallake tauran akwai wahala kuma nima hankalina na tashi idan na tuna azabar dake ciki
Amma kuma hankalina ya kan kwanta idan na tuna cewa zan samu ฦดancin yin rayuwa dake bayan wannan wahalar, fatana dai kiriฦe min alฦawarin da kika ษaukar min"
Haฦiฦa ta ฦara jin ya shiga zuciyar ta to me ma zesa ta karya alฦawarin data ษaukar mai?
Ta tambayi zuciyar ta tana ganin babu, Guntun murmushi yayi tare da katse mata gajeren tunanin da ta tafi
"ki tuna ke mutum ce, kuma halin mutanen yanzu sai Allah, zasu ษaukar ma alฦawari amma daga baya su nuna su basu ma san da maganar wani alฦawari ba, amma dai ke na yarda dake na kuma san ba zaki taษa juyamin baya ba"
Hmmmm Ta sauke ajiyar zuciya kawai batare da ce komai ba
Murmushi ya kuma yi yanayi mata nuni da gefen sa
"baki ga wacce take kusa dani bane?
Sai lokacin ta lura da Shahida dake kwance gefen sa
Ta ฦura ma yarinyar ido tana jin ฦaunar ta acikin zuciyarta
" na tashe tane? Dan ษazu ta gama tambaya ta ina amminta"
Girgiza kai Rauda tayi alamar a'a tana cigaba da kallon ta
"Meyasa?
Ya tambaya
"saboda kanta ze iya yin ciwo idan ka tashe ta"
Dariya yayi yana duban Shahida dake ta baccinta
"wa yace miki muma rauhanai irin ku ne mutane ragwaye,babu abunda kanta zeyi"
Ta gyaษa kai tace
"shi kenan tashe ta"
Ya durฦuso sai tin fuskarta yana shafa fuskarta da ambaton sunan ta
Sai ko tabuษe idon
"Shahida tashi ga amminki"
Tashi zaune Shahida tayi da sauri tana rarraba idanu
Yayi murmushi tare da nuna mata madubin
Haka suka cigaba da fira har saida barci ya fara ษaukar Rauda sannan ya kaudar da madubin
Yana jin kamar bashi da wata damuwa, dan firar da yayi da ita yasa hankalinsa ya ษan kwanta
Miฦewa yayi ya isa sashen ammi, sai dai kuyangin ฦin buษe masa ฦofa suka yi dan sunce tace bata buฦatar ganawa da kowa
*Ranar tsallake tauran*
Duk wani masoyin Aasim da ke cikin masarauta hankalinsa a tashe yike, musamman ammi da gaba ษaya ta fita hayyacinta
Haka Shima sarki ramzad dauriya kawai yikeyi yana nuna kamar abun Be dame shi ba, amma zahiri ฦasan zuciyarsa cike take da tashin hankali
Ammi kasa haฦuri tayi saura minti goma sha biyar ta shiga ฦangaren sarki ramzad
Umarni ta bawa waziri da ya fita sannan ta ฦarasa gaban sa ta durฦusa
Cikin tashin hankali da tsananin damuwa ta fara magana
"na roฦeka ka janye wannan hukuncin akan ษana, shi kaษai gareni"
Sarki ramzad yayi mata wani kallo yace
"in janye hukunci fa kika ce? Kema kinsan abunda baze taษa yuwu wa ba kenan,akwai sauran minti sha biyar, kina iya zuwa kisa ษanki ya bi abunda nace mai, dan shine kika isa dashi.
Amma ni baki isa kisani in canza abunda na yanke ba
Yadda bawa zeyi laifi in hukunta sa, haka zan hukunta abunda na haifa dan haka babu maganar janyewa"
Kuka ta fashe dashi
"amma kasan bayan Aasim bani da wani ษa a duniya ko?
Gyara zama yayi cike da ฦaguwa da kukannata dan tashin hankalin da yike ciki kaษai ya ishesa
"kinga Samira,bana buฦatar jin wannan kukan naki, ki tashi ki ษace min da gani"
Miฦewa tayi cike da ษacin rai
"na fahimci ni kaษai nike son Aasim, kai wahalar da ze shiga ko ajikinka, to shi kenan zan tafi amma ka sani duk abunda ya sami ษana da kai zanyi kuka"
Shima miฦewar yayi a fusace
"ki dakata min da waษannan kalaman naki, duk ba laifinki bane da Ace tun farko baki basa goyon baya ba da munkawo wannan matakin?
Juya wa ammi tayi ta fice tana kuka bata zame a ko ina ba sai ฦangaren Aasim
Yana tsaye jikin bango, ya Lumshe idanuwan sa da suka kaษa sosai
Jin kukan ta yasa ya buษe su da sauri
Ganin halin da ta shiga ya ฦara ษaga mai hankali
Durฦushewa tayi a wurin tana cigaba dayin kukan
Ya ฦarasa gaban ta da sauri ze ษaga ta
Dakatar dashi tayi ta hanyar ษaga masa hannu
Ya durฦusa yana tambayar ta
"ammi me yafaru?
" idan kai baka son rayuwar ka ni ina so, ka duba wahalar da za kasha idan ka shiga tauran"
Ammi tafaษa
Aasim ya sauke numfashi yana kama hannun ta
"ammi indai tsallake tauran ne,ki kwantar da hankalinki zan tsallake lafiya insha Allahu Babu abunda ze same ni"
Ta kallesa da jiฦaฦฦun idanunta
"Aasim......
Katseta yayi ta hanyar cewa
" ammi dan Allah kada ki ฦara cewa komai, ammi Rauda itace farin ciki na na kuma son kina son duk wani abu da ze faranta min
Kinsan kema bazan taษa yin nisa dake ba, dan haka ki kwantar da hankalinki dan Allah, kada ki karya min gwiwa"
Miฦewa tayi tana jinjina kai
"shi kenan, tunda abunda ka zaษa kenan, Allah ya baka sa'a"
Tana gama faษar haka ta ษace
Ajiyar zuciya Aasim ya sauke cike da tausayin mahaifiyar tasa
Sai dai baya jin ze fasa abunda yayi niyya
*filin tauran*
Wurin ya cika sosai da rauhanai, Aasim na tsaye daga gefe inda babban ba fade yike
"Yarima Aasim, shin da gaske ka amince da barin masarauta ta hanyar tsalle ke tauran??
Me faษar hukunci ya tambaya
Aasim ya ษaga kai
" na amince "
" ka tabbata?
Me faษan hukunci ya kuma tambaya
Aasim ya jinjina kai
"na tabbata"
Sarki ramzad ya runtse idanuwan sa cike da tsananin takaici
Babban ba fade yayi nuni da tauran take ฦofarta ta buษe
Kai tsaye Aasim ya dumfareta
Yana kallon yadda haya ฦin hucinta ke fita
Runtse idanuwan sa yayi yayin da ya isa ฦofar, ya ษan tsaya ya karanto wasu abubuwa sannan ya kutsa kai
Yana shiga ฦofar ta rufe
Nan da nan garin yayi duhu, iska ta fara kaษawa da ฦarfi
Wani baฦin hayaฦi ne ya dunฦule yayi tsawo baka iya ganin ฦarshensa a saman tauran ษin
Wasu kibiyoyi masu haske suna shiga cikin hayaฦin
Zuwa can hayaฦin ya fitar da wata ฦara me razanar wa wanda ta sauka a jikin Aasim
Faษuwa yayi a ฦasa saboda tsananin azaba,gashi ba a so a kwanta dan danne mutum take yi
Yun ฦurawa yayi ya tashi da ฦyar yana duban jikinsa daya fara huhhujewa
Haka ฦarar ta dinga sauka a jikinsa har sau arba'in da tara
Iya jigatuwa Aasim ya jigatu
Gaba ษaya jikinsa ya huhhuje,lokacin da ฦofar ta buษe faษowa yayi
Mus'ab ne ya ruga da gudu ya taro sa yana Kiran sunansa cikin kaษuwa da halin da ya shiga
Aasim be kuma sanin inda kansa yike ba, har saida yayi kwana biyu
Sannan ya farfaษo, lokacin da ya farfaษo mus'ab ya gani a kusa dashi
Mus'ab na ganin ya buษe ido ya matso kusa dashi sosai yana faษin
"sannu Aasim ka tashi? Yaya jikinnaka?
Aasim ya kaษa mai kai kawai ba tare da yace komai ba
"sannu, ga magani ammi ta aiko maka, tace da ka farka kasha ze taimaka gurin komawar jikin ka dai-dai"
"Allah sarki ammi"
Aasim ya faษa a cikin zuciyar sa, yunฦurawa yayi ze tashi
Mus'ab ya dakatar dashi
"kada ka tashi, baka ga halin da kake ciki bane?
Aasim ya girgiza kai
" mus'ab barni na tashi, taimaka min dai in jingina"
Mus'ab ya jinjina kai tare da tallafa masa ya jinginan
"amma ya kake ji yanzu? Da kwai wani guri da yike ma ciwo?
Mus'ab ya kuma tambayansa
Aasim yayi murmushin ฦarfin hali yana sake girgiza mai kai
" a'a abokina, ka kwantar da hankalinka babu inda ke min ciwo"
Ya faษa da muryarsa da ta dashe sosai
Mus'ab ya jinjina kai,yana miฦa mai maganin da ke cikin wani kofin silver
"gashi kasha, me kake buฦatar kaci?
Jar abarba ko koriyarta?
Aasim ya girgiza kai yana kai kofin bakin sa
Sai da ya sha rabin maganin sannan ya ajiye yana kallon yana yin garin
" yau kwana nawa anan?
"kwanan ka biyu da yini"
Mus'ab ya bashi amsa
Ya ษan zaro ido
"kwana biyu??
" eh kwana biyu me ya faru?
Mus'ab ya tambaya yana kafesa da ido
Cikin ฦดar damuwa Aasim yace
"Rauda mana, Nasan tana cikin damuwa da jina shuru da tayi"
Mus'ab ya kauda kansa da ga kan Aasim yana mamakin irin ฦaunar da yike wa wannan bil'adamar
"to Meyasa zata damu, bayan ta juya ma tunani, ta san yanzu ka zama nata ita kaษai"
Yana yin fuskar sa ya sauya
"Kaga mus'ab bana so kana faษan magan ganu marasa daษi a kanta"
Mus'ab yace
"to maida wuฦar angon bil'adama"
Guntun tsaki Aasim ya ja tare da yin nuni da hannun sa madubi ya bayyana
Ya kuma nuna sa da hannu, sai ga Rauda zaune ta zuba uban tagumi
Kallon mus'ab yayi yace
"ka nemomin ko ma miye ina jin yunwa"
Mus'ab yayi murmushi tare da faษin
"kadai ce kana son ganawa da tauraruwar mata"
Ya faษa yana Miฦewa
Aasim banza yayi dashi, sai da ya fice sannan yaja gajeren tsaki
Tare da fuskantar madubin sosai
" *habibty!*
Ya kira ta, ta ษago kai da sauri tana kalle-kalle
" Aasim kana inane, me ya faru da kai najika shuru?
Ta tambaya a ฦagare
"ina nan lafiya habibty, ki kwantar da hankalinki"
Hmmmm ta sauke nannauyar ajiyar zuciya
"inaso inganka yanzu please"
Ya kalli jikinsa yadda ya huhhuje tare da sauke numfashi
"habibty kiyi haฦuri baza ki iya ganina ba"
"amma Meyasa? Ka san damuwar da na shiga kuwa? A sanadin na Dena jinka, na Dena ganin ka"
Ya kuma sauke numfashi yace
"da gaske habibty?
ฦaga kai tayi da sauri
" da gaske Mana, nidai Ina son inganka yanzu dan allah"
"habibty bana so kiganni a yana yin da nike ciki ne, kiyi haฦuri a kwana biyu tukunna"
Ya faษa
Ta jingina da kujerar da take kai tana sauke ajiyar zuciya
"ni ko a yaya kake Ina son ganin ka ahaka"
Yayi Guntun murmushi tare da cewa
"to bazan iya zuwa ba, sai dai in janyo ki ta cikin inda nike kallon ki, amma kafinnan ina mama?
" Mama bata nan"
Ya jinjina kai
"shi kenan"
Cikin minti biyu ta ganta a ษakinsa
Sai dai yana yin data gansa ya yi mugun ษaga mata hankali ta tsorata sosai
Gaba ษaya tsigar jikin ta tashi take yi
Cikin kiษima ta ja da baya tana kallon sa
A tsorace
"A...a..sim"
Ta Kira sunansa cikin rawar murya
Miฦewa yayi daฦyar ya ฦara sa inda take, dan har lokacin yana jin jiki
"kingani ba, shiyasa banso kika ganni ba"
Ya faษa yayin da ya isa gabanta
Kallon sa kawai take yi cike da al'ajabi
"me yasa Meka haka? Ya aka yi kakoma haka?
Yayi murmushin ฦarfin hali yace
" tauran, ko kin manta?
Idanuwan ta ne suka cicciko da hawaye
"Aasim, saboda ni ka koma haka?
Ta faษa hawayen da suka ciko idanuwan ta suna gangarowa
Murmushi ya kuma yi
"dan Allah kada kiyi kukannan, kinsan dai abunda bana so na gani a fuskar ki kenan ko?
Ji tayi zuciyar ta ta karye, Bata damu da yanayin data gansa ba ta rungume sa
Cikin shesshekar kuka tace
" duk a sanadina Aasim? Yanzu ahaka zaka cigaba da zama kenan?
Ajiyar zuciya ya sauke me nawi yana jin guguwar ฦaunarta na daษa lulluษesa
ฦago ta yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta
"a'a habibty, nan da wani ษan lokaci zan koma yadda nike, ki kwantar da hankalinki kinji?
Mai da kanta tayi kan ฦirjinsa tana cigaba da yin kukan
Ya Lumshe idanuwan sa yana jin kukan ta har cikin ransa
"ki yi shuru hakanan dan Allah, ko kinaso Nima in fara ne?
Girgiza kai tayi tana share fuskarta
ฦณarfillo.
[7/12, 10:51 AM] Harira Aliyu Mrbcy: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION๐ซ๐ซ๐ซ~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*๐นJINNUL*
*AASHIQUE*
๐ง♂๐ง♂
๐ง♂
NA
HARIRA ALIYU _(ฦดarfillo)_๐ง๐ป
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
๐
ฟAGE๐ 1⃣8⃣
_wannan Page nakune ฦดan golden forum, haฦiฦa bana gajiya da yabonku domin kun can-canta Allah nike roฦo ya ฦara mana basira da fasaha ya kuma ฦara mana danฦon zumunci a wannan gida na mu me albarka amin_
_8:52_๐ AM
SUN, JUN 9
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍๐ป✍๐ป✍๐ป✍๐ป✍๐ป
Ya kuma yin murmushi ya na kama hannun ta zuwa bakin gadon suka zauna suna fuskantar juna
"to shi kenan ya isa haka,Nasha faษa miki cewa idan kina kuka bakya yin kyau amma kinฦi yarda"
ฦarasa goge ragowan hawayen tayi tana zuba masa fararen idanuwan ta
"ni dama bani da kyau, ko banyi kuka ba"
Ya ษan fito da idanuwan sa waje tare da faษin
"inji wa ya faษa miki? Ai ke idan akwai abunda ya wuce kyakkyawa dashi ya kamata a kira ki, domin kyawun ki na daban ne"
Murmushi tayi tana girgiza kai
"zan iya yadda da Hakan amma a gurinka, dan nasan son da kake min ze iya sawa Kaga kyau na fiye da kima, amma ni nasan ni ba kyakkyawa bace"
Ya kama hannun ta yana matsewa cikin nasa
"da gaske habibty kina da kyau, bawai idona rufe wa yayi ba"
Ta kaษa kai tace
"to shi kenan Naji, amma ya kake ji ajikinka nasan ko ina yima ciwo yike yi ko?
Ta ฦarasa faษa idanuwan ta na kuma yin rau-rau da ฦwalla
" ya ilah, habibty baki ji abunda nace miki ba ko? Kina so raina ya ษaci ko?
Girgiza kai
Yace
"oook idan bakya so raina ya ษaci ki maida hawayen nan kada ki bari su zubo"
Tayi ฦoฦorin maida hawayen amma ina kafin tayi wani yunฦuri su biyo kumatun ta
Hannayen sa yasa ya tare hawayen suka ษiga akai
"bazan taษa bari hawayenki su zuba a ฦasa ba, indai ina tare da ke Rauda, dan Allah ki bari"
Kwantawa tayi a jikinsa tana haษiye wani ฦullutun damuwa da ya dunฦule mata maฦogoro
"ka barni inyi kukan dan Allah,in banyi ba ina jinsa yana dunฦule min a ฦirji"
Hmmmm ya sauke numfashi tare da cewa
"to wai kukan me kike yi ne? Faษa min,indai kukan halin da nike ciki ne kibari, nan da wasu kwanaki zaki ga na koma dai-dai"
Dai de lokacin mus'ab ya shigo ษakin ษauke da tiren abinci
Ganin su a tare ya sa ya shigo da sallama
Aasim ne ya amsa yana tambayar har ya dawo?
Be bashi amsa ba illa ajiye tiren da yayi ya fice
Cike da takaicin ganin ta da yayi, dan shi gaba ษaya haushinta yike ji
Dama ya san ze ganta Aida da ainihin suffarsa ze shiga ษakin dan ya razana ta
ฦwafa yayi tare da ษacewa
Ita ko Rauda bayan fitar mus'ab ษago wa tayi tana duban Aasim dan a kallon da mus'ab ya yi mata ta hango tsanarta ฦarara a tare dashi
"wanene wannan da ya shigo?
"abokina ne"
Ya bata amsa
Ta ษanyi shuru sannan tace
"amma nayi masa wani laifi ne?
Girgiza kai yayi yana murmushi
" kinga ฦyalesa akwai abunda ya ษata masa rai ne kawai"
Jinjina kai tayi tana duban tiren da ya ajiye
Wasu kalar abinci ta gani da bata san dasu ba a duniya
Abu ษaya ta fahimta a tiren itace arbaba, kuma abarbar ma ja
Mamaki ne ya kamata dan ita a sanin ta abarba ba ja bace
Ganin yadda take kallon tiren yasa yace
"yadai, me kike mamaki ne?
"dama akwai abarba Jane?
" eh akwai amma anan duniyar mu"
Ta jinjina kai tana duban madubin
Mama ta gani ta dawo
Zaro ido tayi cikin fargaba
"mama ta dawo"
Ya kalli madubin yace
"to yanzu yaza ayi? Ta ina kike so in maida ki?
A gaggauce tace
" bayi, sai in yi kamar daga bayi nike"
Duba bayin yayi yaga akwai mutum a ciki
"da akwai mutum a bayin"
Dafa kai tayi cikin damuwa
"maidani uwar ษaka kawai tunda tana falo"
Jinjina kai yayi ya maida ta yana cigaba da kallon madubin
Ita ko tana ganin ta a ษaki ta miฦe ta yo falo
Ganin ta ba ฦaramin faษar mama da gaba yayi ba
"ke ta ina kika ษullo?
Rauda tayi saurin ษoye fargaban da take ciki tace
" daga uwar ษaka mana mama"
Mama mamakine ya bayyana a fuskarta
"bangane daga uwar ษaka ba, ba yanzu na shiga na ajiye hijabi ba, ya aka yi ban ganki ba?
Tayi mata tambayar tana kafeta da idanu
Gaban Rauda ya cigaba da faษuwa
"baki dai lura bane, ina kan gado,"
Ta faษa cikin dake wa
Mama ta jinjina kai tace
"to gaskiya zanje adubamin hawan jinana ฦila ya hau da yawa da ni banga kowa ba a ษaki wallahi"
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ganin mama ta yarda
ฦarasowa kan kujera tayi ta zauna kusa da maman tana dariya
"mama Bawani hawan jini fa, tsufa ne kawai da kika fara"
Mama tace
"gidan ku, dudu nawa nike? Bari kiga kiyi aure kibani wuri yadda zan koma yarinya shataf, dan gayu zan dinga ci"
Dariya Rauda tayi sosai
"Haba ainasan babu wani gayu da zaki rinฦayi, ni da baba ze ji shawara ta ma da ya ฦaro muku ฦดar budurwa"
Mama kai mata duka tayi
Ta goce tana cigaba da yin dariyar
Bayan sati biyu,hankalin Rauda ya kwanta sosai bata da wata damuwa musamman data ga Aasim ya warware ya koma yadda yike
Uwa uba ga soyayyar da suke yi me zafi, wacce tasa ko da yaushe bata rabo da tunanin sa
Kamar ko wani dare bayan mama tayi bacci
Rauda na zaune a falo tana guga
Maganar sa taji
"habibty ina son ganin ki"
ฦan ษagowa tayi tace
"kabari in gama guga please....
Kafin ta ฦarasa maganar taji wata iska me daษi ta lulluษeta tana janta
Lumshe ido tayi tana faษin
"oh Aasim kasan fa Bama samun wuta sosai yanzu waze ฦarasa min gugar"
Jin iskar ta lafa yasa ta buษe idon, a kwance tagansa gefen gado
Kanne mata ido ษaya yayi yana faษin
"ba dai guga bace? To juya kigani"
Juyawan ko tayi tana duban madubin
Abun mamaki ion ษin da kansa taga yana yin gugan
Ta zaro ido cike da mamaki
Dariya yayi yana janyo ta ta faษa jikin sa
"miye na wani zare idanu, abunda yafi haka ma zaki gani, zaki wani ce in bari ki gama guga, kinsan yadda na matsu in ganki kuwa?
Ta marai-raice fuska tace
" to ni yanzu me zan maka?
Murgina wa yayi da ita, ya zama itace a kwancen
"me ma zaki min kike tambaya na?
" to ni bacci nike son nayi"
Ta faษa a shagwaษe
Yadda tayi maganar ya ฦara rikita sa
Ya tsa yasa yana zagaye gefen fuskarta
"bacci? To kiyi mana aiban hanaki ba"
Ji tayi wani abu ya fara taso mata ta Lumshe idanuwan ta daga kallon sa da take yi
Shiko sun kuyowa yayi daf da fuskarta yana kallon ษan ฦaramin bakin ta
Yatsan sa ya dawo dashi yana zagaye tausasan lips ษinta wanda Hakan ke ฦara sa tana shiga wani yanayi
Kissing ษinta ya fara Ahankali yana bin duk wani sassan jikin ta
Gaba ษaya jin ta take yi a wata duniya da bazata iya fasalta irin ta ba
Haka ya cigaba da sarrafa ta bata masan sanda ta shiga duniyar bacci ba
Shi ko Hakan ya bashi damar aiwata muradin zuciyar sa
Sai wuraren ฦarfe uku ta farka, yana kwance kusa da ita ya zuba mata ido
"habibty!
Ya faษa cikin shauฦin ฦaunarta
ฦago da kanta tayi tana kallon sa ba tare da ta amsa ba
"habibty ina sonki ina ฦaunar ki"
Murmushi tayi idanuwan su na cigaba da sarฦewa da juna
"Nima Ina son ka Aasim"
Ya rungume ta tsam a jikinsa
"ki faษi,duk abunda kike so, nayi miki alฦawarin zanyi miki shi a take batare da ษata loka ci ba"
Murmushi ta kuma yi
"babu"
Ya ษago ta yana kuma kallon fuskarta
"mu cigaba da rayuwa a haka dan Allah habibty"
Gyaษa mai kai tayi
"shi kenan"
Washegari
Bayan ta fito daga wanka tana zaune tana shafa
Bayan tagama ta ษauko doguwar riga ta saka tana zage zip ษin
Ji tayi zip ษin ya kuma zagewa, ta kuma zagewa still ya kuma
Juya wa tayi dan tasan shine
Aiko shi ษin ta gani ya harษe hannayesa yana murmushi
Ta maida mai martanin murmushin tana cewa
"nifa bana son tsokana"
Ya matso gab da ita yana mai-maita abunda tafaษa
"nifa bana son tsokana"
Dariya tayi dan yadda yayi maganar shi a dole ya kwai-kwaye ta
"ka ganka ko? To me ya faru na ganka da rana haka"
Wani zobe yaciro yana nuna mata
"wallahi kin gansa nan, nazo wucewa ta wata kasuwa nagansa naga ze yi miki kyau a hannun ki shine na siyo miki"
Murmushi tayi tana duba siririn zoben zinarin
"wow gaskiya yayi kyau kamar kasan kuwa ina son siririn zobe"
Ya kama yatsanta yana zura mata zoben
"yaza'ai bazan san abunda matata take so ba?
Har lokacin da ragowar murmushi a fuskar ta
"na gode, abban Shahida"
"shhhhh"
Yayi yana ษaura Yatsan sa akan bakin ta
"kar in ฦara jin kalmar godiya abakinki, dan babu ita a tsakanin mu"
Sallamar da aka yi a falon ce tasa ya sumbace ta a goshi
"kije kunyi baฦuwa,sai mun haษu anjima"
Gyaษa kai tayi tana murmushi
Ya ษace ฦara zage zip ษin tayi ta fito falon
Anty ummi ce
"zama tayi kan kujera cike da nisha ษi tana duban Anty ummin
"kune da rana haka?
Anty ummi kallon ta tayi tace
" eh me ya faru a gidan ne?
Cikin rashin fahimta Rauda tace
"bangane ba"
"gani nayi kina ta farin ciki"
Anty ummi ta faษa
Dariya Rauda tayi tana girgiza kai
"to babu abunda ya faru kinsan wata ran zakiji ki cikin annashuwa"
Anty ummi ta jinjina kai tana kallon zoben hannun ta
"wannan zoben fa, kamar zinari, ina kika samoshi?
Rauda ta girgiza kai tace
" a'a ba zinari bane, ษarawon zinari ne, a makarantar mu wata take saida wa dubu ษaya to tunda na siya ma ban taษa sawa ba sai yau"
Anty ummi ta jinjina kai
"aiko kamar zinari wallahi,zan baki kuษi idan kun koma
Kisiyomin, ina mama?
" ta shiga gidan maman murja anyi haihuwa"
Anty ummi ta miฦe
"dama hanif zanษauko a makaranta nace bari in biyo, kince zakizo har yanzu baki zo ba"
Rauda ta miฦe itama tana yafa ษan kwalin ta dan ta rakata
"kinsan banji daษi ba kwana biyu amma zan zo jibi in Allah ya kai mu"
Anty ummi tace
"shi kenan in maman ta dawo ki gaishe ta"
Washe gari suna zaune a tsakar gida gabaษayan su suna gyara masarar da baba ya kawo
Suna cikin gyaran aisha ta shigo yarinyar umma da ฦaramin akwati a hannun ta idanuwan nan nata sun yi jawur da alamu kuka taci
Tana shigowa umma tace
"me zan gani Aisha, yau ma ya jin kikayo"
Aisha ta tsugunna tana fashewa da kuka
"umma ni wallahi na gaji,Ace kullum nasiru sai yayi waya da ฦดammata"
Umma maka ta kai mata cike da harzuฦa
"ubanki kenan, nace ubanki kenan Aisha, dan yayi waya da ฦดammata shine abun yaji?
Mazan yanzu ba haฦuri ake yi da su ba, ina farin ciki hankalina ya kwanta na gama aurar da ku shine kike kike so ki tattago naki auran?
Ga wasu nan auran ma ya gagare su suna neman mazan ruwa a jallo basu samu ba"
Inna ta jinjina kai tace
"ฦwarai kuwa jummai, a zamaninnan in ka samu ka aurar da ฦดaฦดanka ai ka gama hajji da ummara"
Umma tace
"faษa mata dai, wata ma sau biyu ana fasa auran ta kuma babu wanda ya ฦara shinshinar ta, sai ke da Allah ya tarfa ma garin ki nono ya rufa miki asiri kikayi auran zaki rinฦayin yaji
Maza tashi ki ษace min da gani in ba kinaso in rufe ki da duka ba, sakarya kawai"
Mama Miฦewa tayi ta shige ษaki dan tasan da ita suke yada haibaicin
Rauda ma Miฦewa tayi tabi bayan maman
A zaune tasa meta ta zuba uban ta gumi
Ta zauna gefen ta tace
"mama dan Allah kada abunda suka faษa ya ษata miki rai"
Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jingina da kujerar
"dole ya dameni Rauda, kullum fatana Allah ya kawo miki miji kiyi aure amma har yanzu shuru, yanzu ankai matakin da babu me sallama wa yace yana kiranki
Addu'a nike, maganin nike nemar miki amma shuru"
Ta ฦarasa maganar cike da tsananin damuwa
Jikin Rauda yayi sanyi sosai, tausayin mama take ji, anya wannan rayuwar da tekeyi a ษoye da Aasim tayi wa kanta da mama adalci kuwa?
Ya zamar mata dole ta yi masa magana dan ta samu mafita
Dan tasan yana da hannu wajen ษaukewar mane manta
Guntun numfashi ta sauke
Tace
"komai lokaci ne mama, kuma komai yayi farko yana da ฦarshe ki kwantar da hankalinki ai da banyi auran ba ba a zaune nike ba, karatu nikeyi"
Mama ta girgiza kai
"aure ai mutuncin ฦดa mace ne, hankali na zefi kwanciya idan Naga kinyi auran kina cigaba da karatun"
Rauda tayi shuru kawai tana ฦara yin nazari
Allah Allah take yi dare yayi
A gaggauce tagama ayyukan da zata taya mama dan ranar itace da girki
ฦarfe goma mama tayi mata sallama taja mata ฦofar da yike hadari ya taso sosai
Tana fita Aasim na bayyana a ษakin
Cikin sauri Rauda tace
"yauwa dama yanzu nike shirin kiranka"
Kama hannun ta yayi yana ฦoฦarin janyo ta jikinsa
Ta dakatar dashi
"a'a Aasim, magana nike so muyi dan Allah"
Ganin yana yin fuskarta yasa ya gane da gaske take yi
Hakan yasa ya zauna a kan kujera itama ta zauna
"maganar me kike so muyi habibty?
Ta gyara zaman ta tana fuskantar sa
" ina so muyi wata muhimmi yar magana, kuma dan Allah inaso ka fahimce ni, ka kuma yarda da abunda zan faษa ma"
Ya kaษa kai
"to insha Allah ina jinki"
Ta sauke numfashi sannan ta fara cewa
"a gaskiya babu abunda nike so sama da kwanciyar hankalin mama, kuma hankalin ta baze kwanta ba har sai taga nayi aure sannan...........
Katseta yayi
" sannan me? Faษamin kawai me kike so kice"
Ta kuma sauke numfashi a karo na biyu
"ina so kadena korar min mane mana kabar su su cigaba da zuwa....
" sannan me?
Ya tambaya cikin tsare gida da ษaure fuska
"sannan kabarni inyi aure........
" dakata dakata Rauda, kin san me kike cewa kuwa?
Ya faษa cikin ษacin rai
Jinjina kai tayi tace
"na sani Aasim, kuma kai ma ka san baze yuwu In cigaba da zama a haka ba, idan ni nasan ina tare da kai ai mutane basu sani ba.......
"kinga kima dakatar da waษannan shirmamman maganganun naki"
Yafa ษa yana kauda kansa
"magan ganun nawa ne shirme?
Ya jinjina kai yace
"eh shirmammu ne mana, ina so ki sani bazan taษa barin wani ษa namiji ya raษeki ba, dan haka ki ma cire maganar aure a rayuwarki duk wani abun da ษan adam zeyi miki nayi alฦawarin zanyi miki ninkin shi"
Kallon sa kawai take yi yadda ya tamke fuska kamar be taษa dariya ba
Durฦusawa tayi a gaban sa idanuwan ta suka cicciko
"Aasim dan Allah na roฦeka,Hakan shine kwanciyar hankalin mama, ka riga da ka san a yanzu babu wanda nike so sama da kai, kuma bawai ina nufin kabar ni in yi aure dan inyi nisa da kai bane, a'a...
"kinga Rauda idan kinji abunda nafaษamiki to, idan kuma baki ji ba bari in sake nanata miki
Bazan taษa barin wani ษa namiji ya raษeki ba"
Runtse idanuwan ta tayi wasu siraran hawaye na gangarowa
"kenan haka kake so incigaba da rayuwa?
ฦacewa yayi ransa a ษace batare da ya ฦara ce mata komai ba
Ita ko Rauda fashewa tayi da kuka cike da tsananin damuwa
Haka ta kwana bata runtsa ba
Sai da suka yi kwana biyu be kuma zuwa inda take ba,bata damu ba dan haushin sa take ji sosai dan ta fahimci ba zasu daidaita dashi ba dan baze yuwu ta cigaba da rayuwa mutane suna yada Mata habai ci ba
Rana na ukun tana tsaye a ษaki tana ninke kayan da ta kwaso akan igiya
ฦagowar da zata yi suka haษa ido
Maida kanta tayi kamar Bata gansa ba cigaba dayin abunda take yi
Hakan ya sosa masa rai amma sai ya danne ya ฦara so tare da rungume ta ta baya
"habibty fushi kike yi dani?
Janye jikin ta tayi tana kallon sa
" dan Allah ka rabu dani,ka ฦyaleni"
Ta faษa cikin dakiya
Ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa gab da ita
"shi kenan Naji nayi miki laifi, amma kiyi haฦuri"
"nayi"
Tafaษa tana cigaba da ninke kayan
Cikin damuwa yace
"miye haka Rauda,? Nine fa?
Ta ษaga ta watsa mai fararen idanuwan ta
"to inkaine sai mene Aasim? Me kake so ince maka? Tunda ka kasa fahimtata"
Ya girgiza kai yace
"ba haka bane, dan Allah ki saurareni, ranar ma raina ne ya ษaci, kinsan ina ฦaunar ki, kishin ki da sonki ne suka hanani fahimtar ki a ranar"
Ta ajiye kayan tana faษin
"shi kenan ina sauraron ka"
"amma ai ba atsaye zamuyi maganar ba ko?
Ta zauna bakin gado batare da ta sake magana ba
Ajiyar zuciya ya sauke yana zauna wa a kusa da ita
"to dan Allah ki saki ranki kinji? Ba na son ganin ki a yana yin ษacin rai"
Ta sassauta ษaurin da tayi ma fuskarta tana duban sa kawai
Gauron numfashi ya sauke yana kama hannun ta
"kinsan irin son da nike miki ba zaki taษa neman wani abu agurina ban miki ba, amma gaskiya kamar yadda na faษa miki bazan iya barin wani ษa namiji ya raษeki ba sai dai ina da wata mafita guda ษaya"
Ta kallesa sosai
"mafita? To wace kalar mafita? Faษi inji"
Ya gyara zama yana kuma fuskantar ta
"kinga ฦarfin da nike dashi idan na bayyana ga mutane da yawa ba zasu iya ganina ba
ฦarfin da nike dashi mutum biyar ne zasu iya ganina,
To akwai wani kogo da ake zuwa a ฦasar Iraq inda wani tsohon rauhani yike
Idan rauhan yayi training awurinsa na tsawon watanni ฦarfin sa ze ฦaru ta yadda ze iya bayyana a bainar mutane da yawa
Kinga idan nayi sai inbayyana a gidan ku a matsayin mutum in kuma auranki kinga shi kenan baki da wata damuwa"
Kallon sa tayi da mamaki
"da gaske ana yin Hakan?
Ya jin jina kai
" da gaske, dan haka ina ganin jibi zantafi"
Jinjina kai tayi da sauri dan dama burinta be wuce ta rayu dashi ba, kuma tunda ga hanyar da babu wanda ze gane ai shi kenan
"dama ka san da wannan hanyar shine bakayi ba tun tuni?
" yanzu ai zanyi dole na"
Ya faษa
Kama ษayan hannun sa tayi cike farin ciki
"dan Allah ka tafi yanzu, wallahi ina son ka da kai kaษai nike so nayi rayuwa a yanzu"
Murmushi yayi
"kwantar da hankalinki, jibi in Allah ya kai mu zan tafi,sai dai innata fi babu wata hanya da zata sa damu har sai na gama watannin da zanyi"
Kaษa kai tayi tace
"to miye abun damuwa? In ka dawo ba shi kenan ba"
Ya jinjina kai
"shi kenan, yanzu hankalinki ya kwanta ko?
Ta ษaga kai tana murmushi
Bayan kwana biyu suna tsaye suna sallama dan ranar ze tafi
" habibty dan Allah ki kula da kanki,na ajiye miki kuษi a cikin akwatinki duk abunda zaki buฦata kiyi dasu,inda zan shiga bani da damar koda ganin ki ta madubi dan haka ki kula min da kanki"
Jinjina kai tayi tana ษan murmushi
"baka da matsala, zan kiyaye insha Allah, kaima ka kula da kanka sosai"
Ya sumbace ta a goshi
"shi kenan ni zan wuce"
"Allah ya kiyaye hanya ta faษa"
Ya ษace, zama tayi zuciyar ta cike da kewarsa da ฦaunar ta
Bayan sati ษaya lokacin komawarta makaranta yayi
Dan haka ta gama shirin ta tsaf, motar rana zata bi
Mama nasiha ta mata sosai akan ta cigaba da tsare mutuncin ta
Baba da kanshi ya kai ta tasha
Sai da yaga motar su ta tashi sannan ya tafi
Ita ko Rauda kallon gefen hanya take tayi zuciyar ta cike da tunanin Aasim
ฦarfe biyar ta sauka a bakin makaranta
Inda Salma ke tsaye tana jiran ta dan ta riga ta dawowa
Tana ganin ta suka rungume juna cike da kewar juna, salmar ce ta ษauki akwatinta tana tambayar ya hanya
"lafiya lau"
Ta bata amsa suna tsallakawa
Wata rantsattsiyar mota ce ta shanyo kwana a guje
Salma ta ฦarasa tsallakawa da gudu yayin da takalmin Rauda ya turguษe
Kafin tayi wani yunฦuri tuni motar ta bugeta
Faษuwa tayi tana ambaton sunan Allah tare da tashi da sauri tana kallon motar
Ganin motar ta tsaya yasa ta duba ฦafarta inda take jin zafi da alamu anan ne taji ciwon
Wanda yike tuฦa motar ya fito hankalinsa a tashe
Fari ne tas, dogo kyakkyawan gaske
Da hanzari ya isa gabanta
Ganin ta durฦusa tana duba ฦafarta yasa shima ya durฦusa yana faษin
"sannu baiwar Allah, kinji ciwo haka? Tashi mu tafi asibiti wallahi bada niyya ta na buge ki ba, saurin da nike yi ne"
ฦirjinta ne ya fara bugawa yayin da taji tausassar muryarsa
"dan Allah tashi inkaiki asibiti, kinga jini na zuba a ฦafarki"
Gabanta ne ya sake faษuwa,ฦarfin hali ษagowa tayi ta kallesa suka haษa ido
Atare gabansu yayi mummunan faษuwa
Kallon-kallo kawai suke yi
Shine ya katse ษauke wutar da suka yi ta hanyar kiran sunan ta
*"Rauda"*
ฦirjinta ne yaci gaba da bugawa, zuciyar ta ta fara harbawa da sauri
Ganin wanda bata taษa sa ran zata gansa a duniya ba
Har zata amsa sai magan-ganunsa na baya suka dawo mata
_"kada ki ฦara kirana ko nemana, kisa a ranki cewa baki taษa sanina ba a duniya, ki gogeni daga rayuwarki"_
Nan da nan ษacin ran shekarun da suka wuce ya dawo mata sabo fil
Miฦewa tayi tana jin raษaษin dake ฦafarta ya tafi sakamakon tuno wa da maganar sa da tayi
shi ko jikinsa na rawa ya kuma kiran sunan ta
"Rauda ba zaki amsa min ba?
Wani kallo tamasa tare da haษe fuskarta
"ba sunana Rauda ba"
Tana gama faษar haka tayi gaba
Yayi saurin shan gabanta
"Haba Rauda, nasan kece ki tsaya inkai ki asibiti"
Ranta ya soma ษaci
"nace maka ni ba sunana Rauda ba, ka tafi ka ฦyaleni"
ฦณarfillo.
[7/12, 10:51 AM] Harira Aliyu Mrbcy: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION๐ซ๐ซ๐ซ~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*๐นJINNUL*
*AASHIQUE๐น*
๐ง♂๐ง♂
๐ง♂
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_ ๐ง๐ป
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
๐
ฟAGE๐ 1⃣9⃣
_Wannan Page nakune masoya ฦดarfillo, haฦiฦa ina jin daษin yadda kuke yaba labarina a koda yaushe, nayi kuma matuฦar mamakin yadda labarina ya samu karษuwa a gurinku, babu abunda zance muku face godiya Allah ya bar zumunci_
*_Aishatu babayo_*
_ina jinjina miki a koda yaushe,ina kuma godiya da kulawar ki gareni_
*_fatan alkhairi_*
_ga babbar aminiyata da babu kamar ta, *Aisha a Ibrahim* marubuci yar hilwana_
_11:34_๐AM
TUE,JUN 11
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍๐ป✍๐ป✍๐ป✍๐ป✍๐ป
Ze kuma yin magana ta dakatar dashi ta hanyar ษaga masa hannu
"malan ka bani hanya in wuce? Taimakon kai ni asibiti ne bana so ko ana yima mutum dole ne?
Mama kine ya kama sa sosai kallon ta kawai yike yi
" wai shin Rauda ko baki gane ni bane? Umar ne fa"
"Umar?
Ta mai-maita sunan tana kaษa kai
"Kaga Malan ni bansan ka ba"
Kafin ya kuma wata magana tuni ta ratse ta gefen sa ta wuce
Binta yayi da kallo yana tambayar kansa to wai ko ba ita bace ne? Ko gizo idanuwan sa suke masa
Binta Salma tayi da sauri tana kiran sunan ta
"Rauda kinfaji ciwo sosai, ya kamata ki tsaya muje asibiti a dubaki"
Rauda ko waigo wa bata yi ba taci gaba da tafiya
Kira ta da Rauda da Salma tayi ya tabbatar mishi da itace
Har ze bisu cikin makaranta
Wayar sa ta fara ฦara
Ya zaro ta daga aljihu, ganin me kiran yasa yayi saurin ษagawa tare da karawa a kunnen sa
"doctor Umar mutanen nanfa suna cikin wani hali suna gab da rasa rayukansu dan Allah ka hanzarta"
Be ce komai ba ya kashe wayar yana ฦara kallon get ษin makarantar ganin sun shige yasa ya koma motar sa
Tare da tada wa ya jata a guje
Amma gaba ษaya hankalinsa ya rabu biyu
Ita ko Rauda ba ta tsaya ba har sai da ta isa ษakin su tana shiga ta wurgar da ฦaramar jakar dake hannun ta tare da zubewa a ฦasa tana mai da numfashi sama-sama
Gaba ษaya ganin sa ya hautsina mata hankali gami da daburta zuciyar ta
Salma ce ta shigo ษakin ganin halin da take ciki yasa tace
"Rauda kita shi mutafi asibiti"
Rauda ta girgiza kai alamar a'a
Salma ta durฦusa tana duba ฦafar Raudan da har lokacin take zubar da jini
"bangane a'a ba, kina ganin yadda jini ke zuba, ga kuma numfashin da kike yi sama-sama"
Rauda ta kuma girgiza kai a karo na biyu
"nace miki baza ni ba, ki ฦyaleni dan Allah"
Salma ta kaษa kai tana miฦewa
"aiko bazan ฦyale ki ba, tunda ba zaki tashi mutafi asibitin ba bari na kira sadiya ฦดar medicine tazo ta dubaki"
Rauda jingina tayi da bango tana ฦara sauke numfashi
ฦarfe shida da kwata ya isa Abuja
A harabar tamfatsetsen asibitin yayi parking
A gaggauce ya shiga office ษinsa ya sanya kayan aiki
Tare da fitowa inda sauran likitocin suke
Basu ษata lokaci ba suka emergency room inda Majin yatan suke
Basu suka fito ba sai. Sai ฦarfe tara
Office ษinsa ya koma ya yi wanka sannan ya zauna akan kujera tare da miฦar da ฦafafunsa ya jingina su da zagayayyen tebur ษin dake gabansa
Jingina yayi da kujerar zuciyarsa na hango masa fuskarta
Maganar ta ce kawai take yi masa yawo a kunne
_"Kaga Malan ni ban san ka ba"_
Ya Lumshe idanuwan sa yana tambayar zuciyar sa
"anya kuwa Raudar da ya sani ce kuwa?
Dan ya tabbata inda itace bazata yi masa haka ba
Zuciyar sa ta kuma hasko Masa ita a lokacin da ta ษago fareren idanuwan ta ta kallesa
Mamaki haษe da fargaba da kuma tashin hankali ya gani a cikin idanuwan ta
To idan ba ita bace me yasa zata yi masa wannan kallon?
Ya kuma tambayar kansa
Numfashi ya sauke yana Miฦewa tare da ษaukar makullin motar sa
"ko ma dai yaya ne gobe zankoma katsinan in tabbatar"
Ya faษa yana ficewa daga cikin office ษin
Washegari
Rauda na zaune riฦe da plate ษin abinci tana jujjuya cokalin dake hannun ta
Dan gaba ษaya ba ta jin cin abincin hakanan take tsintar kanta da faษuwar gaba a duk sanda ta tuna sa
_"kada ki ฦara kirana ko nemana, kisa a ranki cewa baki taษa sanina ba a duniya, ki goge ni daga rayuwarki"_
Maganar sa ta kuma yi mata yawo a kunne
Aje plate ษin tayi tana jijjiga kanta
"meyasa Nike yin tunaninsa? Meyasa?
Ta faษa cikin yana yin damuwa
Salma kallon ta tayi sosai tace
"Rauda, wai me ke damunki ne wai?
Ta kuma sauke numfashi a karo na biyu tana kallon salma da idanuwan ta da suka canza launi
"babu komai"
Salma ta girgiza kai tace
"a'a da akwai komi fa, tun jiya yana yinki ya canza, wai shin ma waye ne wannan na jiyan da ya bugeki"
ta zame daga gefen gadon tana Lumshe ido
"waye kuwa Salma, a gabanki fa na fara ganin sa"
"to amma Meyasa tunda kika gansa yana yin ki ya canza?
Ada nayi tunanin ciwon da kika jini, sai da Naga ana wanke miki ciwon naga ko a jikin ki hankalinki da tunanin ki ma basa gurin gabaษaya
Hakan ya tabbatar min da ba ciwon da kika ji bane"
Ta buษe idanuwan ta da suka kaษa suka yi ja saboda ษacin ran da ta shiga sakamakon zafafan magan ganunsa da suka kasa dena yi mata yawo a kunne
"Salma dan Allah bana son Magana a halin yanzu"
Salma ta tana kaษa tace
"shikenan"
Wunin ranar haka Rauda tayi shi cikin rashin wal-wala
Shi ma Umar haka ta kasance gareshi ko abincin kirki ya kasa ci Allah Allah yike gari ya waye ya tafi Katsina
Washegari da wuri ya tashi ya shirya ya ษauki jakar sa wacce ya sa kaya kala biyu a ciki ya fito falo
A kan dining ya tadda Anty kaltum tana haษa abun kari
Ya gaishe ta ta amsa tana kallon jakar hannun sa
"yadai na ganka da jaka"
Ya gyara ratayar da yayi wa jakar yana cewa
"tafiya zanyi zuwa Katsina"
"Katsina kuma? Ince shekaran jiya ka dawo daga katsinar? Me zaka je kayi kuma?
Ta tambaya tana kallon sa
" wani abu ne ze kaini, amma bazan wuce kwana biyu ba zan dawo insha allah"
Sanin sa baya son yawan tambaya yasa ta jinjina kai
"shikenan Allah ya tsare"
"amin"
Ya faษa tare da juyawa ya nufi hanyar fita
Har ya kusa kaiwa ฦofa ta dakatar dashi ta hanyar cewa
"to bazaka tsaya ka karya ba?
Ya girgiza kai yana cigaba da tafiya
" no Anty bana jin yunwa"
Bata ฦara cemai komai ba ta bisa da kallo
A harabar gidan ya buษe haษaษษiyar motar sa ya shiga ya tada
Me gadi ya buษe masa get yana gaishe sa
ฦaga masa hannu kawai yayi ya figi motar a guje
ฦangaren Rauda kuwa ta samu ษan sassauci dan har ta shirya dan zuwa duba sakamakon jarabawar su da ya fito a ranar
Tare da Salma suka fito suna tafiya suna fira jefi-jefi har suka isa wurin
Kamar yadda wurin ya saba da cika maฦil da ษalubai a duk sanda sakamakon ya fito
Haka yauma, dan ko wani ษalubi burinsa yaga abunda yaci
Rauda tsayawa tayi daga baya kaษan tana na zartar yana yin wurin yayin da Salma ta kutsa cikin ษaluban
Rauda na tsaye har Salma ta dubo nata ta fito tana mai da numfashi
Ganin Raudar a tsaye a inda ta barta yasa tace
"ha'a baki duba ba?
Rauda ta ษaga kai
" kema kinsan bazan iya shiga cikin dandazo nan ba, ya kiga na ki?
Salma tace
"ba laifi, bari na dubo miki"
Ta faษa tana juyawa ta koma cikin dandazon
Daga ฦasa ta fara duba na Rauda kamar ko da yaushe
Sai dai ba ta gani ba, Hakan yasa taษaga kai sama tana dubawa
Numban jarabawar Rauda ta fara gani a farko ta ษan ware idanu tana sake dubawa
Numban raudan ce kuwa, wani irin farin ciki ne ya lulluษeta ta daka tsalle tana ihun murna
Tare da fitowa daga cikin dandazon
Tana ฦan-ฦame Rauda cikin tsananin farin ciki
Rauda riฦe ta tayi da sauri jin tana niyyar faษuwa
"miye haka, Salma kada ki kadani mana"
Rauda ta ษago tace.
"ฦawa result ษinki first class, da first class Kika fito"
Rauda zaro ido tayi cikin mamaki
"first class? Bana son zolaya Salma please faษamin me ki kagani"
Salma tace
"wallahi Rauda first class"
Rauda ta girgiza kai tana faษin
"banyadda ba, bari in duba da kaina"
Ta ฦarasa faษa tana kutsawa
Tayi matuฦar mamaki ganin first class ษin kuwa
Wani irin farin ciki ne ya mamaye mata zuciya
Fitowa tayi fuskarta ษauke da tsantsar farin ciki, dan har wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncin ta
Salma ta riฦe mata hannu tana dariyar jin daษi
"yanzu kin yarda ฦawa?
Rauda ta jinjina kai kawai dan ta ma kasa magana
Salma ta cigaba da cewa
" kinga zauna a wurin bishiyar can ki jirani inje in haษo mana drinks dan munana farin cikin mu"
Tana gama faษa ta juya a guje ta nufi wurin da ake sai da drinks
Rauda ta ฦarasa gurin bishiyar ta zauna Aasim ne ya faษo mata
Tare da maganar da ya faษa mata a rana ta farko da ya fara koya mata karatu
_"Rauda ina tabbatar miki da cewa zaki iya, kuma jarabawa me zuwa da first class Zaki fito Abu ษaya nike so dake ki mai da hankali akan abunda zan rinฦa koya miki"_
Guntun murmushi tayi tana furta sunan sa a hankali
"Aasim nayi rashin ka sosai,zan so ace kana tare dani ayau nasan sai ka fini farin ciki"
Dai-dai lokacin Umar ya shigo cikin makarantar wuri ya samu yayi parking yana kallon ษaluban da ke kai da komowa
"ta ina zan fara neman ta?
Ya tambayi kansa yana sauke ajiyar zuciya
wayar sa ya ษauka tare da buษe marfin motar
Tunda ya zuro da ฦafafunsa ฦดammatan dake zaune suna tattauna wa akan saka makon jarabawar su suke kallon sa
Sai da yaษan ษauki wasu sakwanni yana nazarin wurin dan ta cikin glass ษin motar yana hango yadda ฦดammatan suka zuba masa ido suna jiran suga fitowarsa
Guntun tsaki ya ja dan shi a rayuwar sa ya tsani kallo
Ya ฦarasa fitowa da jikinsa tare da dafa marfin motar
"wow"
Wasu daga cikin ฦดammatan suka faษa ya yinda wasu daga cikin su suka saki baki suna kallon sa
Haษe fuskar sa yayi sosai yayi kamar be san da wasu a wurin ba
Hange-hangen inda ze hango ta kawai yike yi amma bega ko alamar ta ba
Ya ja Guntun tsaki
"to wai ta ina zan fara ne manta ne?
Ya faษa a fili yana ci gaba da hange hangen
Wata daga cikin ฦดammatan ta taso ta ฦaraso inda yike tana yauฦi wai dan ko zata ja hankalin sa
Ko kallon ta beyi ba, bare yasan ma wace kala ce
"yallaษai akwai wanda kake ne mana?
Ta faษa cikin karya murya
Kallon ta yayi a fusace yace
" idan da akwai wanda nike nema miye ya shafe ki? Miye ya ruwan ki? Ko akwai abunda ya dameki dani ne"
Ya faษa cikin ษacin rai
Tsaye kawai budurwar tayi dan gaba ษaya kunya ta gama lulluษeta ganin yadda ya yarfa ta cikin jama'a
Zuciyarsa ce ta ษan lallashe
"fushi ba naka bane, kai da kake so ka nemo ta, kuma ai dole sai da tambaya zaka gano inda take"
Numfashi ya sauke ya juya sosai yana fuskantar budurwar tare da zare glass ษin idanun sa
"I'm sorry, I'm sorry na ษaga miki murya"
Ya ษan numfasa yana ci gaba da cewa
"ina neman wata ne me suna Rauda"
ฦarfin hali budurwar tayi dan ganin kyawawan idanuwan sa sun ฦara rikita ta
A ษan daburce tace
"a wani department take?
Girgiza kai yayi yace
"no bansan department ษinta ba"
Budurwar tace
"masu suna Rauda suna da yawa a makarantar nan, gano ta batare da sanin department ษinta ba, zeyi wuya gaskiya amma miye sunan mahaifin ta?
Kuma ya kamannin ta suke? Dan akwai wata dana sani a department ษin mu"
Gyara tsayuwar sa yayi yana so ya tuna sunan mahaifin ta
_"Cikakken suna na shine Rauda isma'il"_
ฦwaฦwalwarsa ta tariyo masa maganar ta
"yauwa sunan ta Rauda isma'il,bata da jiki,kyakkyawa ce me fararen idanu"
Ya faษa cikin sauri
Girgiza kai budurwar tayi
"gaskiya ba ita bace dan wannan sunan ta Rauda mannir kuma ita tana da jiki"
"ook bayan ita fa? Baki san wata ba?
Ya tambaya a ฦagarance
ษaga kai tayi alamar eh
Ajiyar zuciya ya sauke yana kaษa kai
" shikenan nagode "
Juya wa budurwar tayi da sauri tabar wurin
Shiko jingina da motar yayi cikin da muwa
Haka yayi ta tambayar mutane amma duk wanda ya tambaya sai yace be san ta ba
Rauda na zaune taji gaban ta na faษuwa
Kamar ance ta waiga ta hango sa yana tambayar wasu
Gabanta ne yayi wani mugun faษuwa
Tayi saurin ษauke kanta tana dafa ฦirjinta dake bugawa da sauri
Shi ko Umar juyawa yayi da niyyar komawa mota dan ya fara gajiya
Karaf suka ci karo da Salma
Wani irin farin ciki ne ya lulluษesa
Cikin jin daษin ganin ta yace
"yauwa alhamdulillah Allah na gode maka"
Rauda tayi saurin Miฦewa tana girgiza ma salma kai
Dayike ita take fuskantar inda take yayin da Umar ya juya mata baya
Salma ta kalli Rauda ta dan bata gane abunda take nufi ba amma sai ta mai da kallon ta ga Umar tana cewa
"bawan Allah lafiya?
" dan Allah ki nuna min inda Rauda take, ina son in yi magana da ita ne please "
ฦara kallon Rauda tayi har lokacin girgiza mata kai take yi
"OK ษan jirani bari in kai saฦon nan indawo"
Gyaษa kai yayi yana bin bayan ta da kallo
Karaf suka haษa ido da Rauda da ke shirin barin wurin
Cikin sauri ya ฦarasa gurin bishiyar yana yi mata sallama dan kafin Salma ta ฦarasa tuni ya riga ta ฦarasa wa
Tattaro dauriyar ta tayi duk da faษuwar da gaban ta keyi ta dake
Tare da yin banza da shi
"Rauda ko ba komai kya amsa min sallama aiko?
ฦagowa tayi ta watsa masa wani kallo me cike da ma'anoni da yawa
"ok wa alaikumussalam"
Ya yi murmushi yana cewa
"nafi awa ษaya ina neman ki, duk wanda na tambaya sai su ce basu sanki ba....
"nemana kuma? Akan me kake nema na? Lafiya?
Ta tambaya tana kafe sa da ido
Ya sauke numfashi yana gyara tsayuwar sa
" kinga Rauda dan Allah kiyi haฦuri, ki tsaya ki saurare ni ki sauko daga fushinnan please"
Itama ta gyara tsayuwar tata tana fuskantar sa sosai
"nifa bawan Allah bangane abunda kake nufi ba wani fushi?
Duka-duka inace yau ne haษuwar mu ta biyu
Ta ษan daka ta sannan ta kaษa kai tana ci gaba da cewa
" ohh na tuna wai na bugeni da kayi? Ai babu komai nasan tsau tsayi ne, sai anjima"
Ta ฦarasa faษa tana niyyar wuce sa
Tare ta yayi da sauri ta hanyar shan Gabanta
"wai me kike yi ne haka ne? Me yasa kike nuna kamar baki sanni ba?
Ta harษe hannayen ta a ฦirjinta tana ฦara kallon sa
"da alamu dai kayi ma kuwa ne, dan ni Banta taษa ganin ka ba face ranar da ka bugeni"
Mamaki ne ya ฦara ka masa
Ya zuba mata ido kawai
zuciyarsa na cigaba da harbawa, wata kalar sabuwar ฦaunar tace ta fara bi masa jinin jikinsa
"Rauda nasan nayi kuskure a baya amma dan Allah kada kiyi min irin wannan hukuncin na nuna baki sanni ba..........
" daka ta bawan Allah, na gaya maka bansan ka, ban san ka ba, kaje Kane mi Raudar da ka sani dan Allah ka ฦyaleni"
Tana gama faษar haka tabar wurin dan ji tayi zuciyar ta ta fara karye wa
Jingina da bishiyar yayi yana bin ta da kallo kawai
Numban zayyad ya kira babban amininsa bugu ษaya ya ษauka
"zayyad kana ina ne?
Daga can ฦangaren zayyad yace
" gani zanje Katsina, mama ta aikeni kai kana ina ne?
Ya sauke ajiyar zuciya yace
"Nima Ina katsinan"
"kana Katsina? Yaushe kaje baka faษa min ba"
Numfashi ya kuma sauke wa yace
"zayyad ina cikin damuwa ka hanzarta kazo dan Allah"
Zayyad yace
"ook ok ganinan zuwa, amma ka kwantar da hankalinka dan Allah, a Ina zan same ka?
Sunan hotel ษin da ya sauka ya faษa mishi, sannan ya kashe wayar ya koma motar sa
Tunda ta koma ษaki take kuka wanda bata san taka mai-mai na menene ba, tana yi ne kawai dan ta samu sassauci a cikin zuciyar ta wacce take yi mata suya
Salma kallon ta kawai take yi tana mamakin irin wannan al'amari
ฦarfe biyar zayyad ya isa hotel ษin Numban ษakin ya tambaya a ka nuna masa
Ya ฦwan-ฦwansa ฦofar
Umar na kwance kan gado ya Lumshe idanuwan sa jin ana ฦwan-ฦwansa ฦofar yasa ya miฦe
Ji yayi kansa ya sara, ya dafa kan yana cigaba da tafiya ya buษe ฦofar
Zayyad kallon sa yayi sosai ganin yana yin sa ya tabbatar mai da yana cikin damuwan
Zama suka yi kan kujerar dake ษakin zayyad na tambayar sa
"wai me yake faruwa ne umar? Me ke damunka?
Kwashe komai umar yayi ya faษa masa
Zayyad yayi murmushi yana cewa
"to miye na damuwa anan? ince Rauda ce yarinyar da baka so Meyasa zaka dami kanka dan kawai tace bata sanka ba?
Umar ya sauke doguwar ajiyar zuciya yace
" zayyad bazaka gane ba, wallahi a yanzu zuciya ta ta kamu da tsananin ฦaunar ta, tun ranar dana haษu da ita Naji naka sa sukuni"
Zayyad ya kuma yin murmushi
"aini wallahi Rauda tayi min dai-dai da ta nuna bata ma taษa sanin ka ba
Yarin yar nan tasha wulaฦanci a wurin ka, dan kawai Kaga Tana mutuwar sonka kai ta wulaฦantata ni kaina ta sha kirana tana kuka akan abubuwan da kake mata
Har ta gaji, sai yanzu ne zaka zo kace wai kana son ta?
Ni wallahi dama nasan wannan ce damuwar taka dan ban tada hankali na nayi ta gudu akan hanya ba"
Hannun sa umar ya kama ya na marai-raice fuska
"zayyad tabbas nasan nayi kuskure a baya amma yanzu wallahi ina son ta, ka taimake ni muje tare da kai ka bata ha ฦuri nasan tana ganin girman ka"
0 comments:
Post a Comment