Sai da yayi wanka ya sauya kaya zuwa blue jeans da farar t-shirt sannan ya sauko ƙasa
A kan dining ya same su, anty kaltum da mijinta, hajiya,da kuma zayyad
Ya zauna yana faɗin
"wai hajiya yaushe kika zo ƙasar ne? Sam ni na kasa fahimta ga yana yin gidannan duk ya Sauya kamar bashi ba"
Kasa bashi amsa suka yi dan basu san me zasu ce mishi ba
Amsar plate ɗin da anty kaltum ta miƙo mai yayi, har ɗiba a cokali ze kai bakin sa idanuwansa suka sauka kan zayyad,a iya sanin sa da zayyad baya ƙaunar gashi a fuska amma gashi duk ya bar sake da gemu
Aje cokalin yayi da mamaki sosai a fuskar sa
"zayyad yau Kaine da saje? Shekaran jiya fa da muka rabu babu komai a fuskar ka"
Zayyad ya ɗan daburce yana tunanin amsar da ze basa
Tsura musu ido umar yayi tabbas akwai abunda suke ɓoye masa cikin yanayin damuwa yace
"wai dan Allah me yike faruwa ne? me kuke ɓoye min?
Alh sadik(mijin anty kaltum) shine dabara ta faɗo masa yace
"umar dole fa zaka sauye-sauye da yawa,domin yau shekarunka biyar kenan kana barci sai yau Allah yasa ka farka"
Zaro ido umar yayi yana kallon Alh sadik, daga bisani kuma ya kece da dariya
Ido kawai suka zuba masa, sai da yayi dariyar sa me isar sa sannan yace
"wani irin bacci ne kuma na shekara biyar?dan Allah baban Salim ka ajiye wasannan a gefe ku faɗamin me yike faruwa?
Hajiya tace
" da gaske ne abunda ya faɗa ma,Allah ya jarabce ka da lalura kuma dai tunda ya yaye maka banason yawan tambayoyi"
Shuru umar yayi yana kallon hajiya, dan Sam be yarda da maganar su ba,amma ganin yanayin da suka shiga yasa yace
"shikenan hajiya, kice inji tsoron ƙara kwantawa barci kada insake yin na shekara goma"
Ya ƙarasa faɗa yana guntse dariya
Zayyad ya miƙe yana faɗin
"ni ina ganin zan wuce"
Umar shima ya miƙe yace
"bari mu fita tare,inga gari dan nasan abubuwa sun caccanza shekaru biyar ba wasa bane"
Ya faɗa cikin tsokana da dariya
Anty kaltum ta girgiza kai tace
"bafa inda zaka je umar dan baka gama warware wa ba kabari ka ƙarasa jin sauƙi tukunna"
Be saurare ta ba yayi gaba yana ɗan jijjiga jikin sa
"anty ni wallahi ƙalau nike,sai na dawo"
A tsakar gida ma, motocin da ya sani basu ya gani ba har ze yi magana sai kuma ya fasa yana faɗin
"komai ya canza, hajiya tace banda yawan tambaya, zayyad wacece motar ka a ciki?
Ya ƙarasa faɗa yana kallon zayyad
" banzo da mota ba"
Zayyad ya bashi amsa
"Ok mu shiga waccan Naga kamar da makulli a ciki"
Shiga suka yi ya tada motar,tunda suka hau titi babu wanda yayi magana, jefi-jefi dai umar kan kalli zayyad ya tun tsire da dariya
Abun ya fara ba zayyad haushi cikin ƙufula yace
"wai mahaukaci na zamar ma ne?
Umar ya kuma yin dariya har da buga sitiyari
" no abokina sajennan ne naga yayi ma kyau sosai, sai yasa ka zama kamar wani ustaz wallahi"
Tsaki zayyad yayi yana maida kallon sa gefe
Umar ya kuma dariya
"yi haƙuri abokina, faɗamin yanzu ina zamuje?
"ka ajeni a gida inyaso duk inda zaka je sai kaje"
"ai baka isa ba wallahi, tare muka saba fita kuma dolenka yanzu ma mu je da kai"
Sanin halin sa da zayyad yayi yasa marai-raice fuska yace
"please umar wallahi kaina ciwo yike yi"
Umar gyaɗa kai yayi yana canza hanya zuwa hanyar gidan su
A ƙofar gida ya ajesa sannan ya dinga zagaye gari bashi ya koma gida ba sai sha ɗaya da rabi
Lokacin duk sun kwanta,Rauda na tsaye a kitchen tana tsiyaya ruwan zafi a kofi dan sai lokacin taji tana jin yunwa
Bayan ta gama haɗa tea ta fito zata koma ɗaki
Dai-dai lokacin shi kuma umar ya shigo be kula da ita ba dan babu haske sosai a ɗakin suka ci karo
Kofin hannun ta ya faɗi ƙasa tean ya zube,ɗan ja baya tayi da sauri gudun kar ya fallatsan mata a ƙafa
Ido umar ya zuba mata,yana so ya tuna a inda ya Santa
Duk da babu wadataccen haske falon ne hana ta ganin kyakkyawar fuskar sa kasancewar sa fari sosai
Hannu ya kai ya kunna glop ɗin falon, still idanuwansa na kanta
Ji tayi kamar kar ta ɗauke nata idanun dan gani tayi yayi mata wani irin kyau
Jin hawaye na neman cika mata ido ya sa tayi saurin sadda kanta ƙasa
A hankali ya fara taka wa zuwa inda take sai da ya rage be fi taku ɗaya tsakanin su ba sannan ya tsaya
Ɗago kanta tayi, karaf idanuwan su suka sarƙe da juna
Yarrr yaji wani abu ya tsarga a jikin sa,yayi saurin lumshe idanuwan sa zuciyar sa ta fara bugawa a hankali
Ganin haka yasa tayi saurin hayewa sama, buɗe idanuwansa yayi yana bin bayan ta da kallo
Har ta shige sannan ya sauke idanuwan sa tare da zama kan kujera
Wacece ita?Meyasa yaji zuciyar sa na bugawa a sanda ya kalli cikin idanuwan ta?
Ya jero ma kansa tambayoyin da ya bayi da amsar su
Miƙewa yayi jikin sa babu ƙwari, wani ɗaki anty kaltum take? Dole yaje ya tambaye ta
Sama ya hau ya buɗe ɗakin farko,hajiya ya gani kwance tana ta munshari
Ya maida mata ƙofar ya rufe a hankali sannan ya wuto ze dawo ƙasa
Shesshekar kuka ya fara ji a hankali a ɗakin da ke kusa da wanda hajiya take
Murɗa ƙofar yayi a hankali tare da turawa
Gefen gado ya hango ta ta kifa kanta tana kuka
Runtse ido yayi dan jin kukan nata yayi har cikin ƙoƙon ransa
Murɗa ƙofar da taji anyi ne yasa ta ɗago kanta
Tayi ƙoƙarin mai da ragowar kukan tare da share fuskar ta da sauri
A jiyar zuciya ya sauke
"wani ɗaki anty kaltum take?
" tana ɗakin ƙasa"
Ta bashi amsa,juyawa yayi ya maida mata ƙofar ya rufe
Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar sannan ta buɗe dan ta rufe
Ganin sa yasa taɗan yi mamaki
"umar baka kwanta ba? Ba dai jikin bane ba ko?
Girgiza kai yayi yace
" a'a lafiya ta ƙalau, inaso muyi magana ne"
Bashi hanya tayi ya shige sannan ta bi bayan sa, a gefen gado suka zauna
"inajin ka"
Sai da ya sauke numfashi sannan yace
"anty wacece wannan dana gani?
Ta san Rauda yike nufi kuma dama ta tanaji amsar da zata bashi dan ta san dole ze tambaya
"ƴar'uwar baban Salim ce,ya ɗauko ta ta dawo wurina da zama"
"amma meyasa Naga tana kuka, akwai wani abu dake damun tane?
Manage plz banda caji
*~ƴarfillo~*.
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 4⃣0⃣
_wannan Page nakine fretu muna godiya da yabawa ma rubuta golden pen da kike yi muma muna yinki kuma muna tare dake irin sosai ɗinnan_
_10:19_🕒 AM
Thu, Nov 7
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Addu'a Yayin Da Aka ga Tumu,
اَللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِي ثَمَرِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مَدِينَتِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي صَاعِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مُدِّنَا.
Allahumma barik lana fee thamarina, wabarik lana fee madeenatina, wabarik lana fee sa'ina wabarik lana fee muddina.
Ya Allah! Ka albarka ce mu a cikin kayan gonarmu, ka albarkan ce mu a garinmu, Ka alabarkance mu a kwanon awonmu, Ka albarkan ce mu a mudun awonmu.
Washe gari
Tana tsaye saman bene ta tsakar gida,ta dafa jikin zagayayyen ƙarfen da yayi ma wurin gajeruwar katanga,wasu tsuntsaye biyu ta tsura ma ido da suke ta shawagi a jikin bishiyar gidan
Jikin ta ne ya bata ana kallon ta, ta sauko da kallon ta ƙasa
Umar ta gani tsaye ya harɗe hannayen sa a ƙirji ya zuba mata dara-daran idanuwansa
Tsawon minti biyu suna kallon juna daga bisani ta janye nata idanun ta maida su gurin bishiyar
Numfashi umar ya ajiye sannan ya fara taka matakalar a hankali, duk da tana jin sawun hawowar sa besa ta kuma juyawa ba
Har sai da ya ƙarasa hawowar, kamar yadda tayi shima haka yayi dafa ƙarfen yayi da hannayen sa duka biyu
"barka da yammaci"
Umar ya faɗa yana ƙoƙarin saisaita idanuwansa a kanta
"yauwa barka"
Ta amsa mai a taƙaice
Yayi ɗan shuru yana tunanin abunda ze ce mata,ita ko gaban tane ya fara faɗuwa dan gani take kamar yana gab da dawowa cikin tunanin sa
"anty ta cemin gobe zaki koma garin ku ko?
Ya tambaya
Ɗaga masa kai kawai tayi alamar eh batare da tayi magana ba
Ya sauke guntun numfashi tare da faɗin
"shin bakya jin daɗin zama damu ne?
Shuru bata amsa mai ba,ya lumshe idanuwansa na ƴan sakwanni sannan ya sake buɗesu ya kuma ɗaura su akan ta
"bansan me yasa nike jin zuciya ta na bugawa ba a duk sanda na ganki,dan Allah kada kiyi nisa dani"
Yana yin yadda ya ƙarasa maganar ya sa jikinta ya ƙara yin sanyi
Tabbas ƙaunar da yike mata ba kaɗan bace,tunda har yanzu ya kasa dena jinta a cikin ransa duk da tuggun da Aasim yayi a tsakanin su
Take idanuwanta suka ciko da hawaye,matso wa yayi gab da ita yana ci gaba da cewa
"ki ci gaba da zama a nan please"
Sai lokacin ta ɗago ta zuba mai idanuwanta wanda suke cike taf da hawaye
A hankali hawayen suka fara gangarowa daga kurmin idanun ta
Juyawa tayi tabar wurin da sauri dan bazata iya jurar tsayawa a wurin ba
Ɗakin ta ta faɗa tana fashewa da kuka me ciwo,ya zamar mata dole tayi gaggawar barin gidan dan inbahaka ba ta san al'amarin yana gab da kuma jagulewa
Kayan ta ta fara haɗawa a akwati,tana haɗawa tana kuka
A haka anty kaltum ta shigo ta same ta, gabaɗaya tausayin ta ya gama cika zuciyar anty kaltum
Nasiha tayi mata sosai da kuma cewa ta kwantar da hankalin ta dan sauran kwanaki tafiyar ta Sudan
Cikin dare,Rauda ta kasa runtsawa ko kaɗan,tana zaune kan darduma bayan ta idar da nafiloli
Hakanan taji tana son taga umar,har ta miƙe wani sashi na zuciyar ta ya haneta
"yanzu idan kika tafi kinsan ranar da zaki ƙara ganin sa?
Wata zuciyar ta tambaye ta,jikinta ba kuzari ta kalli agogon ɗakin
Ƙarfe biyu na dare, tasan yanzu yayi barci hakan yasa ta fito daga ɗakin ta, ta murɗa ƙofar bedroom ɗinsa a hankali
Kwance ta hango sa yana bacci,ta maida ƙofar ta rufe sannan ta taka a hankali zuwa bakin gadon
Durƙusawa tayi sai tin fuskar sa ta tsura mai ido
Tunda take a duniya bata taɓa ganin me kyan umar ba, yana da wani irin sihirtaccen kyau me cike da haiba
"karki tafi please ki zauna tare dani"
Ya faɗa cikin barci da alamu mafarki yike yi
Ɗan murmushi tayi me cike da damuwa tare da kama hannun sa a hankali cikin murya ƙasa-ƙasa tace
"zantafi ne ba dan inaso ba jaana,zan barka a zahiri amma kasani zuciya ta na gare ka gangar jikina ce kaɗai zata yi nisa da kai..
Ta numfasa tana kai bakin ta dai-dai goshin sa ta sumbata
Hawaye ne masu ɗumi suka fara gangaro mata
Tayi saurin kauda fuskar ta daga tasa tare da miƙewa tabar ɗakin
Asubar fari tayi wa su anty da hajiya sallama dan bata so umar ya dawo masallaci ya same ta
Dama driver na jiran ta, ta shiga motar tana hawaye
Basu ɓata lokaci ba driver yaja suka wuce
Suna tafe tana tunanin yadda rayuwar ta zata cigaba da kasancewa
A haka bacci ɓarawo ya sace ta tunda dama bata runtsa ba ko kaɗan
Sanda ta farka mamaki ne ya kamata ganin ita da tasan tana cikin mota suna tafiya amma ta ganta kwance kan wani ƙayataccen gado
Yunƙurawa tayi ta zauna tana ƙare ma ɗakin kallo, babu shakka gidan Aasim ne
Ta dafa kanta cikin damuwa,dan tasan su mama zasu shiga tashin hankali tunda sun san ta taho
A haka Aasim ya shigo fuskar sa ɗauke da walwala da nishaɗi
"habibty sannu kin farka"
Bata bashi amsa ba illa zuba mai ido da tayi,ya ƙara so ya zauna yana sakar mata lallausan murmushi
Kallon sa ta cigaba da tayi, cikin tsananin damuwa tace
"Meyasa kake yimin haka ne, duk abunda kace inyi nayi me yasa ba zaka barni in samu natsuwa ba tukun?
Aasim ya sauke ajiyar zuciya yace
"duk natsuwar da kika samu ta kusan shekara bata isheki ba, wata kuma kike buƙata?
Kinga habibty a yanzu bazan iya jurar rashin ki ko da na misƙala zarratun ba,bazan kuma yarda nayi sakacin da nayi a baya ba"
Guntun numfashi ta sauke me cike da takaici
"me kake nufi kenan,ka rabani da mijina iyayena suma rabani da su zaka yi?
Ya ɗan kauda kansa da ga kallon ta garin irin kallon da take masa
" bance Hakan ba"
Ta sauke gauron numfashi tana saukowa daga gadon ta durƙusa a gaban sa
"dan girman Allah ka mai dani nasan mama tana can hankalin ta ya tashi in ya so daga baya duk yadda kake so sai inmaka"
Ta ƙarasa faɗa idanuwanta na ci kowa da hawaye
Numfashi ya sauke tare da ɗago kyakkyawar fuskarta
"habibty ki kwantar da hankalin ki,ki kalli can"
Yayi mata nuni da madubin sa,mama ta gani dasu anty ummi,tsakiyar su kuma wata Rauda ce tunda dai ita gata anan
Mamaki sosai ya bayyana a fuskar ta,ta mai kallon rashin fahimta tare da cewa
"waccan kuma wacece?
" wata rauhaniya ce nasa tayi shigar ki, zata ci gaba da zama tare dasu mama a madadin ki har zuwa wani lokaci dan gaskiya bazan yadda in kuma rasa ki ba"
Kallon sa kawai ta cigaba da tayi, ya sauko shima ƙasan yana janyo ta jikin sa
"habibty nayi rashi da kewar ki sosai, dan Allah ki rayu dani ni kaɗai"
Janye jikin ta tayi tana ɗaga mai hannu
"ina buƙatar natsuwa kabarni da Allah"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya fice daga ɗakin
Ita ko jingina tayi da gadon wasu siraran hawaye na biyo kuncin ta
Be kuma dawowa ɗakin ba falo ya koma ya kwanta kan kujera
Iyaka dai ya tura mata tire shaƙe da abinci,bata kula abincin ba sai bayan wasu awanni da taji cikin ta na neman agaji sannan ta tsakuri kaɗan
Sai dare ya dawo ɗakin, Rauda na tsaye jikin window ta zuba ma dogayen bishiyoyin dake dokar dajin ido
A bayan ta ya tsaya,bata wai ga ta kallesa ba,hannu yasa ya fara zage zip ɗin rigar ta ta baya
Tayi saurin waigowa a ɗan tsorace,murmushin nan nasa ƙasaitacce yayi yasa hannu ya saƙalo ta taba ya tare da manna ta da jikin sa
"miye ne na wannan tsoron, bafa wani abu zan miki ba wanka ne"
Ta riƙe zip ɗin tana girgiza mai kai
"ka bari zanyi da kaina"
Ya matso da fuskar ta gab da tata dan karan hancin su ma yana gogan juna
"da raina da lafiya ta inbar matata tayi wanka da kanta?ki sani a yanzu zan nuna miki tsantsar soyayyar da tafi tada ta yadda zaki yadda cewa zan iya yin abunda ze ninka wanda ɗan adam ze miki"
Zata kuma magana ya ɗaura yatsun sa biyu kan ƙaramin bakin ta
"shhhhhh kar ki ce komai"
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon idanuwansa wanda kalar ƙwayar ciki take caccanzawa
Ya ci gaba da zage zip ɗin har ya kai ƙarshe sannan ya zame rigar
Runtse idanuwanta tayi da sauri, yayin da ya cigaba da kallon ta yana tambayar kansa
"ta yaya ze yadda ya rasa Rauda, ina!!!!
Bata ankara ba taji ya ɗauke ta cak,sai da ya tsundu mata a ruwa sannan ta buɗe idanun ta
Ruwane me ɗumi wanda saman sa yike mamaye da pink ɗin fulawowi
"kabarni nace zan yi da kaina"
Bece mata komai ba yaci gaba da abunda yike yi, da kansa yayi mata wankan ya naɗo ta da tawul sannan ya zaunar da ita a gaban madubi
Yana sunkuyo da kansa dai-dai wuyan ta
Ta cikin madubin suke kallon juna,gaba ɗaya idanuwansa sun narke da tsananin ƙaunar ta
"Rauda wallahi ina sonki"
Ya faɗa cikin wata murya me cike da shauƙin ta
Wani mai ya ɗauko ya shafe ta da shi sannan ya shafa gefen gadon sai ga wata rigar bacci me kyau ta bayyana sai da ya zura mata rigar sannan ya zame tawul ɗin
Ya kama hannun ta ya miƙar da ita tare da rungume ta sosai a jikin sa
Tabbas yayi kewar farin cikin rayuwar sa
Itako gabaɗaya jikin ta ya mutu,lumshe idanuwanta tayi kawai
Sai da suka kwashi minti biyar a haka sannan ya ɗago ta,ya na sunyo da fuskar sa zuwa bakin ta
Ta gane abunda yike shirin yi a kasalance tace
"hakan ba daidai bane kasan..........
Yayi saurin haɗa bakin su guri ɗaya dan baya so ta ƙarasa abunda zata faɗa
Minti uku baya ta janye jikin ta da ƙyar tana sa mai kuka
Bakin gadon ya zauna yana zuba mata ido cike da yanayi na galabai ta
Be lallasheta ba sai da tayi kukan ta me isar ta sannan ya kamo hannun ta ya zaunar da ita kusa dashi yana fuskantar ta
"habibty tunda bakya so bazan yi miki komai ba, ki dena kuka kinji?
Ya ƙarasa faɗa yana share mata hawayen fuskarta
" kwanta kiyi barci bazan yi miki abunda ranki ba ya so ba"
Kwantawar ko tayi,tana ɗan rawar sanyi wani lallausan bargo me taushi yasa ya lulluɓe ta
*~ƴarfillo~*.
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'a Idan Mutum Ya yi fushi.*
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ.
*A'oothu billahi minash-shaytanir-rajeem.*
*Ina neman tsarin Allah daga shaidan tsinanne.*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 4⃣1⃣
*_wannan Page ɗin nakine JAMILA ALIYU dake sa group ɗin ku masu ƙaunar jinnul aashique ina yin ku irin sosai ɗinnan_*
_7:45_🕒 AM
Wed, Nov 13
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bayan sati ɗaya
Umar ya jigata ƙwarai tun bayan tafiyar ta yike jin kamar ya rasa wani sashi na jikin sa ya rasa meke faruwa da ake ɓoye masa
Dan yanzu ma anty kaltum ta tilasta masa komawa gidan ta wai har sai ya ƙarasa samun lafiya
Ya rasa gane abunda ke faruwa kuma wanda ya tambaya baya samun gamsasshiyar amsa
Yana zaune cikin mota gaban wani shagon turaruka yana jiran mutanen da suka cika shagon su ɗan ragu sannan ya shiga
Gabaɗaya ya shiga cikin rikitaccen tunani dan ranar da ta shiga ɗakin sa idanuwansa biyu ba barci yike yi ba
"zantafi ne ba dan inaso ba jaana,zan barka a zahiri amma kasani zuciya ta na gare ka gangar jikina ce kaɗai zata yi nisa da kai..
Ya rasa gane abunda take nufi a cikin maganar ta,ya dafa kansa da yike jin yana ɗan sa rawa kaɗan
Da ƙyar ya iya fitowa ya shiga shagon yana tsaye yana duba turaren da yike son siya yaji ance
"Doctor umar dama talaka na ganin ku?
Umar ya juya inda yaji maganar yana kallon mutumin,tsayin sakwan uku yana so ya tuna a inda ya san mutumin
Be kai ga gama tunani ba mutumin ya ƙara so yana miƙamai hannu
Bayan sunyi musabaha mutumin yace
"doctor mutanen Allah,ya gida ya iyali? Ko ince amarya kayi haƙuri sanda aka yi auren ka bana ƙasar kuma naso na kira ka nayi maka Allah ya sanya alkhairi ashe numban ka na cikin Layina da ya ɓata"
Umar yayi sororo ya na kallon sa dan Sam be fahimci abunda mutumin ke faɗa ba
"nasan yanzu ƙila amarya ta haihu ko? Samin numban ka dan Allah zanzo har gida na ga amarya"
Mutumin ya ƙarasa faɗa yana miƙa mai faskekiyar wayar sa
Sa mai numban kawai yayi batare da ya ƙarasa sa numban ba ya fice daga shagon motar sa ya faɗa ya kifa kan sa akan sitiyari
"to yaushe yayi aure be sani ba? Kuma wacece wacce ya aura?
Yayi ma kansa tambayoyin a jere,
"zantafi ne ba dan inaso ba jaana,zan barka a zahiri amma kasani zuciya ta na gare ka gangar jikina ce kaɗai zata yi nisa da kai..
Maganar ta ta kuma yi masa yawo a kunne,tabbas idan ya kasance yayi aure to itace matar sa
Ya girgiza kai cikin dagulewar tunani, dole ne ya san abunda ake ɓoye sa
Tada motar yayi ya nufi gidan sa kai tsaye
A tsakar gida yayi parking ya zaro makullin gidan ya buɗe falon
Ya daɗe tsaye yana kallon cikin falon kamar yau ne karo na farko da ya fara ganin sa
Daga bisani ya shiga ya zauna akan kujera
Nan ma ya daɗe ƙwaƙwalwarsa naso ta tuno masa wani abu amma sai yaji kan sa ya cushe
Bedroom ɗin sa ya shiga ya zauna gefen gado idanuwansa suka sauka kan laptop ɗin sa
Jikin sa ba ƙwari ya miƙe ya ɗauko laptop ɗin dan ya san baze rasa wani abu da ze taimaka masa wajen gano abun da yike so ya gano ba
A can Kaduna kuwa gidan su mama mamaki da ban al'ajabi ne yike ta kama su
Dan tun bayan zuwan Rauda ta bogi suke shiga jimami, dan da farko kishiyoyin mama habaici da gori suka fara yima mama da faɗan maganganu masu ciwo
Farha wacce itace Aasim ya turo a madadin Rauda rauhaniya ce Mara haƙuri hakan yasa duk ranar da wani yayi ma mama habaici ko ita ɗin kanta to idan dare fa yayi mutum ya dinga tsala ihu kenan
Dan abubuwan tsoro take tura masa,tun basu Fahim ta ba har suka fara fahimta
Hakan yasa suka shiga ɗari-ɗari da ita,ga aiki dan idan ta soma aiki Sam bata gajiya
Abun yayi ta bawa mamaki sanin Rauda da tayi sam bata son aiki, aiki kaɗan zata yi tace ta gaji amma yanzu har so take ma ace ga aiki
Mama tasha jinin jikin ta sosai dan taga canje-canje da yawa wanda yasa ta fara zargin anya ba canza mata ƴar ta aka yi ba?
Amma dai tayi shuru tana cigaba da zubawa sarautar Allah ido
Ɓangaren Rauda kuwa a yanzu duk wani tsoro ya fita daga ranta dan zuciyar ta ta ƙeƙeshe wuni take da kwana tunanin umar
Wani zubin idan Aasim ya fita ta kan je wurin madubin sa ta ambaci sunan umar tayi ta kallon sa
Yana yin data ga yana shiga na damuwa da kuma tunani shine abun da ya ƙara sanya ta cikin damuwa
Ta rasa inda zata sa kanta,kamar kullum tana tsaye jikin bishiyar gidan tana kallon da jin
Taga Aasim ya bayyana a gaban ta dan tun safe ya fita
Kallon sa tayi yana yi mata murmushi
"habibty"
Duƙar da kanta tayi ƙasa batare da ta amsa ba
Ya matso gab da ita yace
"baza kimin sannu da zuwa ba ko?
Nan ma bata amsa ba
Ya sauke ajiyar zuciya yana fito da kayayyakin da ya siyo mata
Manyan sarƙoƙin lu'u-lu'u ne da awarwaron su
Dan a yanzu duk abunda ze sa ta farin ciki ƙoƙari yike yi yayi mata
" kinga habibty nasan zasu yi miki kyau shine na siyo miki duba kigani"
Kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta, gaba ɗaya sai yaji yadda tayi masa babu daɗi
Zama yayi a ƙasan bishiyar yana jin wani iri
Sun jima a haka daga bisani ya juyo yana kallon ta
Zaunar da ita yayi tare da kama hannayen ta cikin damuwa yace
"na rasa yadda zan yi miki Rauda,dan Allah ki faɗamin me kike so sam bana son ganin ki a irin wannan yanayin"
Hawayen da suka maƙale a idanuwanta suka gangaro a hankali
"ya Salaam,kinsani na tsani Naga kukan ki ko?
Cikin muryar ta da tayi san yi tace
"to ya kake so inyi Aasim?duk wani roƙo da ya dace in maka nayi amma ka kasa tausaya min,babu yadda zanyi zan cigaba da rayuwa da kai kamar yadda kake so amma kasani bazan taɓa ci gaba da farin ciki ba"
Ya lumshe idanuwansa da suka canza launi
Ya daɗe a haka yana tunani sannan ya buɗe su ya ɗaura su a kanta
Har lokacin kuka take yi mara sauti
"kin kasance komai na rayuwa ta,na kuma baki dukkanin amanar kaina ban taɓa tunanin zaki juya min baya ba Rauda sai gashi ni kike gudu ni kike kuka dan ina tare da ke"
Ya ɗan dakata yana jin wani dunƙulen baƙin ciki na taso masa
"tunda kin zaɓi rayuwa da umar a kaina zan barki ki cigaba da rayuwa da shi amma da sharaɗi guda ɗaya"
Tayi saurin kallon sa yayin da ya cigaba da cewa
"kamar yadda na sadaukar da rayuwa ta dan in rayu dake na tsalle ke tauran to shima ze tsallake"
Wani irin kallo ta ci gaba da yi masa dan tasan ba abu bane da ze taɓa yuwuwa ba,shi rauhani ma ya ya ƙare da ya tsallake bare mutum
"amma kasan dai hakan baze yuwu ba,taya ya yana ɗan adam ze tsallake tauran ya kuma rayu?
Aasim ya sauke numfashi yace
"bazan taɓa manta wahalar da na sha a lokacin dana tsallake ba,kuma na amince dan in rayu dake a yanzu kuma da kike son rabuwa dani to wannan shine abunda ze sa in haƙura da ke, nayi alƙawari idan har ya tsallake zan rabu dake har abada zan bar ku ku cigaba da rayuwar ku cikin kwanciyar hankali"
Zata yi magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu
"bana son na kuma jin komai daga wurin ki wannan shine alfarmar da zan iya yi miki,tun da kinzaɓi rabuwa dani"
Umar yana zaune ya tsura ma hoton da ke cikin laptop ɗin ido hoton sa ne da ita sun saƙale juna suna murmushi
A hankali ƙwaƙwalwar sa ta fara tariyo masa komai
Ya dafa kansa da sauri jin yayi wani mugun sarawa kamar an buga mai guduma
Jikin sa ne ya fara rawa ya runtse idanuwansa cikin tashin hankali
"kina ina Rauda?me yasa zaki yi nisa dani?
Karaf abunda ya faɗa a kunnen Aasim, mamaki ne ya kama Aasim ganin yadda cikin ƙanƙanin lokaci umar ya dawo cikin tunanin sa
Cikin hanzari ya ɓace daga wurin da yike ya bayyana a ɗakin da umar yike
Kallon tsana suka ma juna lokaci ɗaya yayin da umar ya miƙe cikin dakewar zuciya yace
"ina mata ta?ina ka kai min ita?
Aasim yayi murmushin takaici yace
"matar ka ko matata?kayi nasarar dawowa cikin tunanin ka amma kasani ba zaka taɓa nasara a kaina ba"
"ban damu akan yin nasara ko rashin ta akan ka ba,damuwa ta akan matata ne ka gaya min tana ina dan nasan tana tare da kai"
Aasim ya kuma yin murmushi yace
"haka ne matata tana tare dani sai dai kash zuciyar ta na tare da kai,kasani ban taɓa tsanar wani ɗan adam kamar yadda na tsanake ba Kaine wanda ka ruguza min farin cikina,idan naso zan kuma mantar da kai ko kai waye zan iya zautar da ƙwaƙwalwar ka amma bazan yi hakan ba kasan me yasa?
Ya ɗan dakata yana furzar da wata iska me zafi,sannan ya cigaba
"saboda bana son na cigaba da ganin damuwa a fuskar farin cikina,nazo ne na baka zaɓi idan har kana son Rauda ka na kuma son ka ci gaba da rayuwa da ita to zaka tsallake tauran ni kuma nayi alƙawari idan har ka tsallake to zan bar maka ita har abada"
Umar ya rausayar da kai yace
"idan har tsallake tauran ɗin ze sa kabar min matata ka kuma nisan ce ta na amince zan tsallake"
Aasim yayi wani mugun murmushi yana jinjina kai
"tsallake tauran ba abu bane me sauƙi, na baka kwana biyu kaje kayi tunani a kai"
Kafin umar ya kuma yin magana tuni ya ɓace
*~ƴarfillo~*.
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Addu'ar Kin shu'umci
اَللَّهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلاَّ طَيْرُكَ، وَلاَ خَيْرَ إِلاَّ خَيْرُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ.
Allahumma la tayra illa tayruk, wala khayra illa khayruk, wala ilaha ghayruk.
Ya Allah! Babu shu'umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 4⃣2⃣
_Wannan page nakune masoya na masu haƙuri dani Allah ya bar ƙauna😄_
_gaisuwa ga *Fatima batula* ina taya ki murnan kammala littafin ki wanda ya faɗakar damu sosai Allah ya baki lada ya ƙara basira da fasaha_
_8:26_🕒 PM
Thu, Nov 28
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bayan kwana biyu umar yana tsaye jikin window ya ji motsi a bayan sa
Ya waigo a hankali Aasim ya gani
"kwanaki biyun da na baka sun cika shin ka gama shawarar?
Aasim ya tambaya yana zuba masa razana nun idanun sa
Umar ya jinjina kai yace
"shawara tun a lokacin na yanke ta na amince"
Aasim yayi murmushi yana jinjina kai
"da kyau amma Naga baka nemi shawarar iyayen ka ba,kuma dole akan idon su zaka tsallake tauran"
Umar yayi murmushi da ya tsaya masa iya laɓe kawai
"wannan ba damuwar ka bace zan tsallake ko da amince warsu ko bada amince warsu ba tunda Naga kaima lokacin daka tsallake bada amincewar naka iyayen ba dan da kabi shawarar su da hakan duk be kasance ba"
Aasim ya kaɗa kai cikin yanayi na ɓacin rai
"shikenan kafaɗa ma shaƙiƙan ka nan da kwana uku zaka tsallake tauran
Ka kuma yi sallama da duk wanda ya kamata dan walau ka rayu walau a kasin haka na barka lafiya"
Umar ya zauna shuru bayan ɓacewar Aasim gabaɗaya tunanin sa ya tsaya sai dai baya jin ze fasa abunda yayi niyya dan ko da ya rasa ransa yasan Rauda zata gane cewa yana yi mata so na haƙiƙa
Miƙewa yayi ya nufi gidan anty kaltum
A falo ya tadda ta ita da hajiya
Bayan ya gaishe su ya zauna shuru
Anty kaltum ta dawo kujerar da yike ta zauna tana tambayar sa
"ya dai umar na ganka wani iri ko jikin ne?
Ya girgiza mata kai a hankali
" to menene? Banason ina ganin ka a haka kasan bana son ganin ka cikin damuwa ko?
Ya kalle ta da idanuwansa da suka canza launi yace
"anty jarabawar da Allah ya ɗauro min kenan dole kiganni a haka, anty na dawo cikin tunani na meyasa kika ba Rauda goyon baya ta aikata min haka Meyasa?
Kefa ƴar uwata ce kuma auran ta da rayuwa da ita shine farin cikina shin bakya son farin cikin ɗan uwan ki ne?
Jikin anty kaltum yayi sanyi hajiya ko zuba mai ido tayi kawai cike da al'ajabi
"Sam ba haka bane umar.......
Ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"na fahimci komai ba sai kinyi min bayani ba, yanzu abu ɗaya nike so a gare ku ina so ku bani goyon baya koda kuwa zan rasa raina ne"
Kallon sa kawai suka cigaba da yi yayin da ya zayyane musu abunda Aasim yace game da tsallake tauran
Shuru suka yi dan sun rasa abun da zasu ce
Durƙusawa yayi gaban hajiya idanuwansa na zubar da hawaye
"hajiya dan Allah ki bani goyon baya Rauda ita ce farin cikina dan Allah hajiya"
Hajiya itama hawayen ta fara yi
"tabbas soyayyar ka a gareta daga Allah ce,akwai wata hikima da ubangiji ya ɓoye a tsakanin ku na baka goyon baya umar ubangiji Allah ya baka sa'a Insha Allah zaka tsallake lafiya kaci gaba da rayuwa da matar ka"
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana hamdala a zuciyar sa dan beyi tunanin zasu amince mai ta sauƙi ba
Hannun ta ya kama yana ɗan murmushi
"nagode hajiya"
Rauda kuwa tana zaune ta Lula cikin tunani bata ma san Aasim ya dawo ɗakin ba sai da taji gyaran murya
A hankali ta zare tagumin da tayi tana kallon sa da lunshasshun idanun ta wanda suka yi luhu-luhu saboda kukan da taci
Kallon juna suka yi na ƴan sakwanni daga bisani ta ɗauke idanuwan ta a kansa ta maida su ƙasa
Shi ko kallon ta yaci gaba da yi yana jin wani irin yana yi na daban
Ya sauke numfashi me nawi yana matso wa kusa da ita a hankali
_"Rauda"_
Ya kira sunan cikin yana yi na damuwa
Ta ɗago ta kuma kallon sa, gabaɗaya ya koma yana yin tausayi ya canza kamar ba shi ba
Kuma sauke idanun ta tayi dan ba zata iya jurar ci gaba da kallon sa ba
"shin ko da sau ɗaya ne ni ba zaki tausaya min ba?
Ya faɗa yana ruƙo hannun ta sannan ya cigaba da cewa
"Sam ni bakya tunanin halin da zan shiga a yayin da zan rabu dake?me yasa ki ka kasa yimin adalci ne?
Ki tuna abubuwan da na rasa a sanadin ki
A da bana komai sai abunda bayi da fadawa suka min,Sam bansan wani abu wahala ba a rayuwa babu gatan da bana samu
Amma a sanadin ki,ki duba wahalar da nasha Rauda na rasa muƙami na na yarima narasa soyayyar iyaye na duk dai akanki
Amma ke.......
Be ƙarasa ba ta faɗa jikin sa tana fashewa da wani kuka me tsuma zuciya
Dan gabaɗaya tausayin sa ya cika mata zuciya
Ya runtse idanuwansa dan yana jin kukan ta har cikin ƙoƙon ransa
Sun kwashi minti biyar a haka ya kasa lallashin ta dan jikin sa yayi sanyi ƙalau
Ɗago kanta tayi tana kallon sa cikin kuka take faɗin
"na sani banma adalci ba Aasim tabbas na cika me son zuciya amma yadda rayuwar mu tazo dole mu amshe ta a haka
Baze yuwu mu cigaba da rayuwa.......
Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu
Yana murmushin takaici
"ya isa haka Rauda,nasan dama bani da kalaman da zan sa ki fahimta babu damuwa har a bada ni me ƙaunar ki ne zan rabu dake a jibi idan har umar ya tsallake tauran kar ki damu"
Ya faɗa cike da takaici
Zata kuma magana ya miƙe ya bar mata ɗakin
Kifa kanta tayi kan gwiwar ta wani sabon kuka na ƙwace mata
Shin ya za tayi da ranta ne,anya idan ta rabu da Aasim tayi ma kanta adalci kuwa?
Rayuwar da suka yi da shi ce tayi ta dawo mata da irin yadda ya nuna mata tsantsar ƙauna
_"habibty nace ba ina sonki"_
Kalaman da yike faɗa kullum idan zasu yi sallama a makaranta
_"Rauda ina sonki zan iya haƙura da komai nawa in har zan rayu dake"_
Zuciyar ta ta cigaba da hasko mata fuskar sa yana murmushi cike da nishaɗi
"tabbas ban maka adalci ba ka cancanci na rayu da kai har a bada amma umar fa?
Ta tambaya a fili tana juya idanun ta cikin yanayi na fara fitar gayyaci
Duk wahalar ya sha ta gubar nan besa yaji ƙaunar ta ta ragu a ransa ba ta san inda wani ne da idan ana saki ɗari yayi mata dan ya samu lafiya
Amma shi ko kaɗan be nuna gajiyawar sa ba illa ma ƙarfafa mata gwiwa da kwantar mata da hankali
_"chuchu ina tsananin ƙaunar ki ba zan taɓa iya rabuwa dake ba,na amince na cigaba da rayuwa a haka in har zan ci gaba da kasancewa tare dake"_
"ya Allah"
Ta faɗa cikin tsananin tashin hankali dan jin kanta take yi kamar zeyi bindiga
Daren ranar bata yi barci ba kamar yadda Aasim da umar ma ko kaɗan basu runtsa ba
Washegari tana zaune bayan ta idar da sallah taga tiren abinci ya shigo shaƙe da kayan kari
Shafa cikin ta tayi da ya laƙume dan rabon da taci abinci har ta manta
Bata bi ta kan abincin ba ta miƙe ta fito
A tsaye tagan sa yana shirin fita
Tayi sauran tarar sa tana faɗin
"ina son Magana da kai"
Be kalle ta ba ya ci gaba da abunda yike yi
"faɗi inaji"
Ya faɗa a taƙaice
Tayi shuru tana tunanin yadda zata mai maganar
Ɗagowa yayi ya kalle ta
"ke nike saurare"
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce
"dan Allah kabani dama ina so inyi magana da umar"
Ya ɗan yi shuru yana cigaba da kallon ta kamar ba ze sake yin magana ba sai kuma yace
"shikenan na baki minti goma"
Yana gama faɗar haka ya ɓace
Zura ma wurin da ya ɓace ido tayi tana tunanin to ina zata fita daga dajin
Bata kai ga gama tunanin ba ta ganta a bedroom ɗin umar
Babu kowa a ciki sai iskar fanka dake ta kaɗawa
Numfashi ta sauke tana faɗin
Ƙiri-ƙiri a maida mutum aljanin ƙarfi da yaji
Umar ya turo ƙofar dan dawowar sa daga masallaci kenan
Da kyakkyawar fuskar ta yayi karo
Ƙarasa shiga ɗakin yayi da sauri
Ya nufe ta da nufin rungume ta sai kuma ya fasa dan be san wani abun Aasim yace ta kuma yi ba
Ɗan murmushi tayi dan ta fahimce sa
"Jaana guduna kake yi ne?
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ƙarasa wa gaban ta
Ya kasa magana illa tsura mata ido da yayi
Gabaɗaya gani yayi ta rame masa
Wani irin tausayi da son ta ne ya kuma dabaibaye sa
Besan sanda ya rungume ta sosai a ƙirjin sa ba
Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncin ta wanda bata san na menene ba
Na kewarsa ne ko kuma na ƙaunar sa
Sun kwashi minti uku a haka tunawa da minti goma Aasim ya bata yasa tayi saurin janye jikin ta
Tana faɗin
"minti goma kaɗai ya bani zauna muyi magana"
Ta ƙarasa faɗa tana jan hannun sa zuwa gefen gadon
Bayan sun zauna tace
"Jaana dan Allah ka janye maganar tsallake tauran da ba abune da zaka iya ba, mu ci gaba da addu'a kawai.......
Girgiza kai yayi yace
"Rauda kisa aranki kamar na tsallake ne dan bazan fasa ba"
Cikin damuwa take kallon sa
"shi kanshi rauhani fa jikin sa huhhujewa yayi ina ga kai mutum? Idan har ba so kakeyi in rasa ka ba dan Allah ka fasa"
Ta ƙarasa faɗa idanuwan ta na ci kowa
Yayi ɗan murmushi ya na dafa kafaɗun ta
"yace idan har na tsallake ze rabu dake ze barki kiyi rayuwa cikin kwanciyar hankali dan haka koda na mutu bani da faɗuwa tunda zaki cigaba da rayuwa babu takurawar sa"
Ta kasa ƙara magana
Umar ya cigaba da cewa
"ki kwantar da hankalin ki chuchu abu ɗaya nike so dake idan Allah ya sa na rasa rayuwa ta kada kisa ranki a ƙunci kiyi rayuwa cikin farin ciki....
Toshe mai baki tayi da sauri tare da faɗawa jikin sa
" umar dan Allah ka janye na tabbata idan babu kai nima bazan iya ci gaba da rayuwa ba"
Ya kuma yin murmushi wanda yike tattare da ɗumbin damuwa
"chuchu a baya kin taɓa kuka a sanadina kin faɗi cewa ke kaɗai ke sona ni bana sonki
Nasan idan har na tsallake zaki yarda da cewa son da nike miki ya ninka wanda kike min"
Tayi saurin girgiza kai
"nasan kana sona umar dan Allah..........
Bata ƙarasa ba tagan ta akan kujerar falon Aasim
Kuka ta cigaba da yi dan tabbatar da baze shiga tauran ya fito da ran sa ba
Shiko umar zuba tagumi yayi,bayan ɓacewar ta
Ɓangaren Aasim kuwa can wurin tauran ya je
Mus'ab ya tarar a wurin hannun sa riƙe da wani haske me tartsatsi yana ta nuni ga tauran
Ya yin idan tartsatsin ya dake cikin ta take ƙara fitar da wani hayaƙi me zafin gaske
Aasim yayi saurin dakatar dashi
"Mus'ab me kake yi haka? Ƙarama tauran zafi fa kake yi"
Mus'ab ya jinjina kai
"eh mana yarima saboda ina so wannan bil'adaman ya gane yayi babban kuskure
Aasim ya girgiza kai yace
"shifa mutum ne taya kake tunani idan ya shiga ze kasance?
Mus'ab yayi ma Aasim wani irin kallo
" wai kai har ma tausayin sa kake ji?
Aasim yayi ɗan murmushi tare da zaunawa a kan kujera yana kallon yadda hucin tauran ke fita
Mus'ab ya kuma faɗin
"tambayar ka nike yi Aasim, mutumin da ya jagula ma rayuwar ka shine kake tausayi?
Aini wallahi so nike ko ɓurɓushin naman sa kar a gani"
Aasim ya kuma yin murmushi a karo na biyu sannan ya maida kallon sa ga babban abokin nasa
"Mus'ab ka sanyaya ranka kaji? Nasan kafini jin zafi amma inaso ka dawo da natsuwar ka mubi komai a hankali"
Mus'ab ya furzar da wata iska me zafi yace
"ni banga abun bi a hankali ba anan"
Wani irin ƙamshi me daɗi ne ya zagaye wurin
Aasim ya ɗago kansa da sauri dan yasan mahaifin sa ne kaɗai ke amfani da kalar turaren
Ga mamakin sa kuwa sarki ramzad ya gani cikin shigar sa ta ƙasaita
Mus'ab yayi saurin rusunawa cikin girmamawa yayin da Aasim ya cigaba da kallon mahaifin sa cike da tsananin kewar sa dan ya manta rabon da yayi tozali da shi
Sarki ramzad ya ƙara so wurin fuskar sa ɗauke da guntun murmushi
Mus'ab yayi gaggawar barin wurin ya rage daga Aasim sai me martaba
"Kaga yadda halin bil'adama yike koh? Aasim naji daɗi ƙwarai da suka koya maka hankali
Na zo ne na kuma baka zaɓi idan gobe bil'adaman nan ya tsallake tauran to fa kasani ba ka isa ka karya alƙawarin da kayi na rabuwa da matar sa ba, dan haka ka ka kiyaye"
Yana kaiwa nan ya bar wurin
Aasim shuru yayi zuciyar sa na yi masa wani iri kallon tauran ya kuma yi sai kuma yaɗan yi murmushi dan yana da yaƙinin sai dai gawar umar ta fita badai da ransa ba
*~ƴarfillo~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 4⃣3⃣
Wannan page nakine nabiha kiyi yadda kike so dashi.
*Addu'ar Da Mutum Zai Fada Idan Wani Al'amari Ya zo Masa na Farin Ciki ko na Bakin Ciki*
الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin
Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowane hali.
_2:02_🕒 PM
Mon,Dec 16
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Kiran sallar assalatu yayi dai-dai da bugawar ƙirjin ta.
Tashi tayi da sauri ƙirjin ta na ci gaba da bugawa.
"yau ne, umar bazai iya ba".
Abunda zuciyar ta ta tunatar da ita kenan.
Tashi tayi ta fito falo bata ga Aasim ba. ta duba ɗakin sa nan ma baya nan.
Zamewa tayi ta zauna a ƙasa tana dafa kanta cikin tsantsar damuwa.
Ta lumshe idanuwan ta, zuciyar ta na hasko mata tauran.
Tabbas ta san yau zata rasa Umar, rashi na har abada.
Wasu siraran hawaye masu zafi suka biyo kwarmin idanun ta.
"kin manta da cewa Allah ya na nan kuma shi ke maganin komai? Addu'a tafi ƙarfin komai".
Wani sashe na zuciyar ta ya tunatar da ita.
Miƙewa tayi da sauri ta ɗauro alwala, bayan ta idar da sallah ta ɗaga hannayen ta sama.
Cikin kuka take faɗin;
"Ya Allah, Kaine sarkin da ka halicci sarakuna, kai ke da iko a kan dukkan halittun ka, ya ubangiji ka duba lamarinmu ka taimaki Umar ka kare sa daga sharrin tauran da sharrin duk wani halitta, ka taimake sa ya ubangiji"
Ta ƙarasa faɗa, zuciyar ta na ƙara raunane wa.
Aasim yana tsaye yana kallon ta, jin jikin sa yike yi wani iri.
Ƙarfe sha ɗaya dai-dai manyan rauhanai abokanan Aasim suka hallara a wajen tauran.
Anty kaltum, hajiya, da kuma zayyad, suma suna zaune a falo suka ga wata iska ta zagaye su kan kace kwabo suka gansu a wata kalar duniya.
Sun tsorata sosai ganin yadda tauran ke fitar da wani tartsatsi.
Addu'a kawai suke karantawa dan sun rikice.
Can kaduna ma, mama ce zaune da anty Ummi suna tattauna wa ƙasa-ƙasa akan Rauda ta bogi, dan gaba ɗaya basu yarda da ita ba.
Suna cikin tattauna war Farha ta fito ta zauna tana kallon su.
Da ɗan murmushi a fuskar ta tace;
"kuna yin tantama a kaina koh?".
Basu bata amsa ba illa kallon ta da suka ci gaba da yi.
Ta kuma yin murmushi tana ci gaba da cewa;
"To a yau tantamar ku zata ƙare insha'allah, kamar yadda kuke zargi hakane ni ba Rauda bace".
Ta ƙarasa faɗa tana shafa fuskar ta sai ga fuskar Rauda ta ɓace, ainihin fuskar ta ta bayyana.
Anty damƙe hannun mama tayi cike da tsananin tsorata.
Mama ko bata yi mamaki ba dan dama tayi tunanin hakan.
"ina ƴata ina kuka kaimin ita?!".
Mama ta tambaya, zuciyar ta a dake.
Farha tayi murmushi tace;
" ƴarki tana duniyar aljanu a yanzu haka, ana can ana shirye-shirye dan yau ne mijin ta yace zai tsallake tauran, dan haka kuma yanzu zan tafi daku dan dole ayi komai a kan idon ku".
Basu kai ga yin magana ba suka gansu a wani kalan wuri.
Babu inda baya rawa a jikin anty ummi dan har fitsari sai da tayi.
Banda mama da zuciyar ta take a dake.
Kallon kallo suka wa juna da su anty Kaltum amma babu wanda ya iya ma wani magana a cikin su.
Umar da tun cikin dare yake kan darduma har lokacin yana kai.
Ya ɗaga hannaye sa yana ta kai kukan sa ga ubangiji.
Motsin Aasim da yaji a ɗakin yasa ya shafa addu'ar tare da waigowa a hankali.
Yana tsaye ya harɗa hannuwan sa a ƙirji.
Ɗan murmushi Umar ya sakar masa tare da cewa, cikin dakiyar zuciya;
"muna iya tafiya yanzu koh?",
Aasim gyaɗa masa kai kawai yayi ba tare da yace komai ba.
Cikin sakwanni suka isa, tabbas hankalin Umar ya tashi da yaga yadda tauran take.
Amma tunawa da yayi Allah yana tare da shi yasa yaji tashin hankalin ya ɗan ragu.
Anty kaltum na ganin umar ta ƙara so gurin sa da sauri ta riƙe sa
Cikin tashin hankali da tsananin tsorata tace
"umar dan girman Allah ka haƙura da yarin yar nan kadu ba inda zaka shiga fa"
Umar ya sake kallon tauran sannan ya mai da kallon sa ga anty kaltum
Cikin ƙoƙarin kwantar mata da hankali yace
"Anty na riƙe Allah na kuma san insha'allah ze bani nasara ki ci gaba da yi min addu'a kinji?
Kuka kawai ta fashe zata kuma magana Rauda ta riga ta dan isowar ta wurin kenan
Ita ma a gigice take gabaɗaya ta daburce
"umar ka kalli inda kake son shiga fa? Na roƙe ka ka janye
Umar ya dafa kafaɗun ta yana yi mata guntun murmushi
"Rauda ba zan taɓa janye wa ba koda ko hakan ze yi sanadiyyar rasa raina ne, bare ma insha'allah zan tsallake lafiya ki kwantar da hankalin ki kinji?
Ganin bayi da niyyar fahimtar ta yasa ta juya gurin Aasim cikin tashin hankali take yi masa magiya
"Aasim ka ɗaukeni mu tafi can wata duniya inda ma baza a ƙara ganina ba na amince zan ci gaba da rayuwa da kai amma kar ka barsa ya shiga tauran dan Allah ka taimake ni idan na rasa sa bansan ya zanyi da rayuwa ta ba"
Aasim da fuskar sa ba annuri idanuwan nan nasa sunyi jawur ba wata alamar ƙwaya aciki dan dama duk sanda ransa ya ɓaci haka idanuwansa ke komawa
Zuba mata idanun yayi masu firgita duk wanda aka kalla dasu
"ni ba rai bane kenen da na tsallake a baya? Tsallakewa ya zama dole tunda ya gani da idonsa kuma be janye da kansa ba idan har ya shiga ya tsallake ya fito kuma da ransa to da ga yau na barki har a bada!!!
Ya ƙarasa faɗa cikin ƙaraji
Mus'ab dake tsaye yace yana duba umar
Yayin da tauran tayi wani baƙin hayaƙi a Samanta cikin ta kuma wasu siraran wuƙaƙe ne masu kafin gaske wanda iska take ta kaɗa su da ƙarfin gaske ta yadda duk wani abu da ya shiga ciki zasu yayyanke jikin sa
"tauran tana yi maka marhaba dan a yanzu ta shirya tsaf da tarbanka"
Mus'ab ya ƙara sa faɗa yana yi masa nuni da ita fuskar sa ɗauke da wani mugun murmushi
Umar jinjina kai yayi yana kuma kallon tauran a hankali ya juya ze fara tafiya
Rauda ta ƙanƙame sa tana kuka tana faɗin
"umar kar kaje dan Allah mutuwa zaka yi"
Aasim ne ya fizgo a fusace
Ya yin da umar ya ci gaba da tafiya
A gigice ta kuma rugowa sai kafin ta ƙarasa inda umar Aasim yayi nuni da hannun sa wani kalar abu me kama da glass ya zagaye wurin gabaɗaya
Jita yi taci karo da abu gashi taku befi biyu ba tsakanin ta da umar amma wannan abun da Aasim yasa yayi shamaki a tsakanin su
Cikin kuka take bubbugawa tana kiran umar
A hankali ya juyo yana kallon ta
Tsananin tausayin ta ya ƙara za gaye zuciyar sa ya ɗauki tsayin biyu yana kallon ta daga bisani ya juya ya ci gaba da tafiya
Sai da ya karanta adduo i sosai sannan ya fara taka mata kalar wani kalan huci me zafi yaji yana dososa
Addu'ar dake bakin sa ya cigaba da karantawa har ya isa ƙofar tauran
Gaban sa ne ya fara faɗuwa yayin da yaga yadda wa'annan wuƙoƙin suke kaɗawa da ƙarfi
Jiyayi kamar ana fizgar sa yayi ƙarfin halin zura ƙafar sa ciki
Sai dai me? Jiyayi wani raɗaɗi ya mamaye sa yayi saurin kallon inda ya taka
Wasu mugayen allurai ne a caccake gabaɗaya kuma haka ƙasan wurin yike
Yayi shahada ya ƙarasa shiga yana ci gaba da ambaton sunan Allah
Cikin sakwanni wuƙaƙennan suka yo kansa ya runtse idanuwansa da sauri dan baya so yaga sanda zasu iso jikin nasa
Sai dai a me makon yaji yanka sai yaji ƙarar wuƙaƙen
Yayi saurin buɗe idon sa abun mamaki duk wuƙar da zo jikin sa sai ta lauye
Take sai ga wuƙaƙe birjik sun zube a ƙasa
"Allahu Akbar!!".
Ya faɗa, take wata izza me ƙarfi tazo masa ya ci gaba da tafiya duk da raɗaɗin da yake ji a ƙafafun sa.
Cikin mintuna biyu ya fara ganin duhu yayin da saman tauran ya ƙara baƙinƙirin.
Murmushi Aasim yayi dan yasan ƙarar farko da tauran zata yi zata halaka sa.
Daram!!
Wata kalar ƙara me razanar wa ta fita.
Sai da aka kwashi minti biyu sannan haske ya fara gauraye cikin tauran ɗin ta yadda suke iya hango cikin ta.
Umar suka hango kwance a ƙasa jini na malala a jikin sa.
Cikin farin ciki Mus'ab ya kalli Rauda yace;
"kingani ko, ƙara ɗaya ta tauran ji yadda ta mayar dashi, nasan a yanzu kuma sai dai wani Umar ɗin ba dai wannan ba".
Ya ƙarasa faɗa yana fashewa da dariya.
Su anty Kaltum kuka suke yi kamar ransu zai fita, yayin da Rauda ta zama kamar wata butumbutumi dan ko motsin kirki ta kasa yi, hawaye ne kawai ke bin fuskar ta.
Cikin hukuncin Allah Umar ya farfaɗo daga gajeruwar Suman da yayi.
Da sunan Allah ya farfaɗo a bakin sa.
Ya yunƙura ya tashi cikin juriya ya cigaba da tafiya.
Mamaki ne ya kama rauhanan dake wurin, suka saki baki suna kallon sa.
Rauda da sai lokacin ta samu damar magana ta kalli Mus'ab tace;
"Miye naka na sakin baki kuma? kana mamaki da ikon Allah ne??".
Mus'ab yayi ɗan murmushi tare da cewa;
"Me kike ma sauri? Duka-duka ƙarar tauran ɗaya ce fa amma ji yadda ta maida shi, ƙarar ta guda arba'in da takwas ta rage, ki ci gaba da zuba ido".
Dai-dai lokacin duhu ya ƙara mamaye tauran alamar ƙara na biyu na zuwa.
Jikin Rauda ya ƙara yin sanyi, zamewa tayi a wurin idanuwanta na ci gaba da zubar da hawaye.
Bayan minti talatin wanda yayi dai-dai da ƙarar tauran sau ashirin.
Umar ne kwance a ƙasa ya galabaita iya galabaituwa, amma duk da haka da ragowar ƙarfin sa sakamakon ƙarfin addu'ar da yake yi, kuma har lokacin ko wuƙa ɗaya ta kasa yankar sa.
Aasim yana tsaye yana kallon Rauda da taci kuka har ta gode Allah.
Tauran zata kuma sakin wata ƙarar yayi nuni da hannu ya dakatar da ita.
Mus'ab ya kallesa cikin sauri yace;
"me kayi haka yarima? Dakatar da ita fa kayi?".
Aasim ya jinjina kai kawai.
Mus'ab zai kuma magana ya dakatar dashi ta hanyar faɗin;
"sanin kanka ne ba wani mahaluki me rai da zai shiga cikin Tauran da wannan zafi da aka ƙara mata face ya mutu, ni kaina da nike jinsin rauhan sai da me martaba ya sanyaya ta sannan na iya tsallakewa, amma shi ka duba har yanzu ba alamar karaya a tare dashi, har yanzu babu wuƙar da tayi nasarar yankar sa bare ta illata sa, tabbas nayi kuskure da na manta cewa addu'a ma karin mumuni ce, idan har nace zan bar sa ya cigaba zanyi babban kuskure domin ko kamar na ja da hukuncin Allah ne".
Rauda ta kallesa da sauri jin abunda yace.
Shima kallon nata yayi idanuwansa na cikowa da hawaye.
A hankali ya rusuna inda take yana kallon ta cikin ido.
"kamar yadda na miki alƙawari yau zan barki, bazan ƙara bibiyar rayuwar ku ke da mijin ki ba, domin duk wanda ya sadaukar da rayuwar sa akanka ba ƙaramar ƙauna yake maka ba, abu ɗaya nike so ki sani ki kuma sa a ranki, ina sonki, kuma zan ci gaba da son ki har zuwa ranar da zanyi numfashi na na ƙarshe....",
Ya ƙara sa maganar cikin wani irin yanayi, tare da miƙewa ya juya da sauri.
Washegari Rauda ce zaune gaban gadon asibiti, Inda umar ke kwance, tana zaune kawai ta rasa meke mata daɗi.
A hankali Umar ya buɗe idanun sa.
Cikin rashin kuzari ta matso da kujerar da take zaune a kai gaban gadon, tare da ɗaura hannun ta saman nasa.
"ka farfaɗo?".
Tambayar da ta mai kenan tana kallon kyakkyawar fuskar sa.
Guntun murmushi ya sakar mata.
"na farfaɗo chuchu, alhamdulillahi mu gode ma Allah".
Siraran hawaye ne suka biyo kwarmin idanun ta.
Ta kwantar da kanta jikin gadon saitin fuskar sa ta yadda suke kallon juna ido cikin ido.
"yanzu kin yarda cewa ina miki so me tsanani chuchu?".
Ɗaga mai kai tayi tare da fara magana cikin sanyin murya.
" na yarda Umar, bansan kuma da me zan saka maka irin ƙaunar da ka nuna min ba".
Murmushi ya kuma yi tare da shafa gefen fuskar ta.
"Idan baki sani ba ni zan faɗa miki, yanzu tunda hankalin mu ya kwanta sai ki fara shirin biyana bashin da na daɗe ina binki".
Cikin rashin fahimta tace;
"bashi fa?".
Ya ɗaga kai.
"Eh ko baki san ina binki bashi ba?".
Ta ɗaga kai alamar eh.
Ya ɗan yi shuru yana tsura ma kyakkyawar fuskar ta ido.
"faɗamin bashin miye?".
"lallai ma yarinyar nan, wato da gaske baki sani ba, to bashin angoncewa na ko kin manta?".
Murmushi tayi cikin jin kunya.
"kana gadon asibiti kake wani maganar angoncewa, ai kabari ka samu lafiya ko?".
Shima murmushin yayi.
"Eh wai dama ina faɗa miki ne saboda ki shirya dan zaki gwaguru yarinya kamar ba gobe".
Ƴar dariya tayi har fararen haƙoranta suka bayyana.
"zan gwaguru sai kace wata goruba?".
"yaushe rabon da inga dariyar ki?har na manta?".
Ya faɗa idanuwansa na kanta.
"kana son ka rinƙa ganin dariya ta ne?".
Ya jinjina kai.
"sosai ma kuwa, dan idan kika yi tana ƙara miki kyau kuma tana sani farin ciki".
Tayi murmushi tace;
"shikenan Jaana, bari in kira zayyad ya duba ka ko?".
Ta ƙarasa faɗa tana miƙewa. Hannun ta ya janyo ta faɗo jikin sa.
Da sauri ta yunƙura zata tashi dan gudun kada ƙarin ruwan dake jikin sa ya goce, ya dakatar da ita ta hanyar faɗin;
"Please ki tsaya Ina son inji ɗuminki ne".
Ta ɗan ƙwalalo ido tare da faɗin;
"A asibiti kake fa, kuma ka duba yana yin da kake ciki".
"Dan a asibiti nike sai me? Ai ɗumin ki nace ko?".
Ta ɗan girgiza kai, dai-dai lokacin da Zayyad ya turo ƙofa.
Tashi tayi da sauri tana matsawa.
Zayyad yayi murmushi.
"A lallai abokina sauki ya samu, ashe ka farfaɗo har ka fara soyewa! Allah ya taimake ka da yanzu kana lahira".
dariya suka yi gaba ɗaya.
Bayan sati biyu
Umar ya samu sauƙi sosai dan har sun dawo gida
Tunda ga bakin get Rauda ta saki baki tana kallon gidan,dan a canza mai feti bata ƙara shiga mamaki ba saida suka shiga falon
An canza komai na gidan, ta maida kallon ta ga umar fuskar ta cike da mamaki
"Jaana Naga gidannan ya canza, Anya ba ɓatan hanya muka yi ba?
Yayi murmushi yana matso wa kusa da ita sosai, kyawawan idanuwan sa ya zuba Mata
Cikin murya me taushi yace
"gidan ki ne chuchu Bawani ɓatan hanya,nine nasa aka canza komai"
Ta sauke ajiyar zuciya tace
"amma gani nayi kayan gidan nan sababbi ne ba abunda suka yi"
Umar ya ɗaga kai yace
"nasani chuchu, rayuwar da mukayi a gidannan rayuwa ce me cike d firgici da tashin hankali, shiyasa na sa aka canza komai saboda banason muna ganin duk abunda ze rinƙa tuna mana da waccan rayuwar, na kuma sa anyi saukar alqur'ani me girma saboda kariya"
Murmushin jindaɗi tayi,tana kallon fuskar sa
"nayi farin ciki sosai,nagode"
Ya girgiza kai
"A'a fa ba anan ya kamata ki nuna farin cikin ki ba?
Har lokacin da ragowar murmushi a fuskar ta
" to a ina ya kamata in nuna ranka shidaɗe?
Surar ta yayi, yayi mata ɗaukar jarirai
"bari in kai ki, kigani"
Sama ya fara hawa ya nufi bedroom
Dariya ta fara yi tana zullo da ƙafafun ta
"nagane wayo kake so kamin, to banyar da ba ka sauke ni"
Shima dariyar yike yi cike da nishaɗi, ya tura ƙofar bedroom ɗin tare da kwantar da ita a kan gadon
Tayi saurin yunƙurawa zata tashi,ya hana ta hanyar yi mata rufa d faffaɗan ƙirjin sa
Kallon cikin ido suka fara yi ma juna,saboda shauƙin soyayya har basa ƙyaftawa
Sunyi minti uku a haka daga bisani ta mirgina,ya koma ƙasa ita kuma ta koma sama
Sunkoyo da fuskar ta tayi daidai tasa,yayin da karan hancin su yike gogan juna
"in faɗa ma wani abu??
Tayi tambayar cikin maƙoshi
Da ido ya bata amsar alamar eh
"ina sonka fiye da yadda kake sona"
Ya ɗan zaro ido yace
"kambu, wallahi banyar da ba,nafiki"
Tayi dariya har farare haƙoran ta suka bayyana
"to shikenan bari dare yayi zamu gani"
Ta faɗa cikin tsokana
Matseta yayi a jiginsa yace
"eyyeh wato har zumuɗin dare yayi kike? Ai ba sai da daddare ake yi ba bari ma kigani....
Ya ƙarasa faɗa yana yunƙurawa
Tashi tayi da gudu ta fice daga ɗakin tana dariya
Washegari da safe
Tana kwance Jikinsa tayi luf
Yana shafa Suman kanta da ta baje a bayan ta
_"chuchu"_
Ya kira sunan ta, ta buɗe idanuwanta da suka yi mata nawi, batare da ta amsa ba ta kalle sa kawai
Lallausan murmushi ya sakar mata
"Allah yayi maki albarka ya saka miki da gidan aljanna, kinsani farin cikin da ban taɓa shiga irin sa a rayuwa ta ba nagode"
Ta maida mai martanin murmushin tana jin ta cikin wata kalar sabuwar rayuwa me cike da natsuwa
Maida idanuwan ta tayi ta rufe dan sam bata jin ƙarfi
Da kanshi yayi mata wanka ya haɗa musu abun kari, be yarda taci da kanta ba a baki ya dinga bata bayan sun gama suka dawo cikin falon
Shagwaɓe masa tayi sosai ita ta gaji bacci take so ta sake yi
Ya zauna akan doguwar kujera sannan ta kwanta tayi matashi da cinyar sa
Lallaɓata ya dinga yi kamar ƙwai
Bayan wata biyu
Basu da wata matsala soyayyar su kawai suke sha,umar ya koma bakin aikin sa
Ranar wata Laraba yana zaune gefen gado yayin da take sanya kaya dan fitowar ta daga wanka kenan
Kallon ta yike tayi,ta ɗan tsaya hannun ta riƙe da riga tana kallon sa tace
"wai Jaana baka gajiya da kallona ne?
Murmushi yayi yana miƙewa idanuwansa akan ƙirjin ta
"kem kinsan har abada bazan taɓa gajiya da kallon ki ba"
Baya ta ɗan fara ja tana faɗin
"Jaana dan Allah kayi haƙuri ka bari muje siyan ice cream ɗinnan MU dawo"
Dariya yayi yana girgiza kai
"raguwa kawai, ba wani abu zanyi miki ba ni, gani nayi duk kin canza anya ba ciki ne dake ba kuwa?
Ta ɗan waro ido
"ciki?
Ta faɗa, umar ya jinjina kai
"eh haka nike zargi dan duk kin sauya amma bari mu bincika mu gani"
Gwaji na farko ko da yayi ya gano ciki ne
Farin ciki a gurin sa baya misaltuwa ɗaga ta yayi yayita juyi da ita
Har sai da ta fara ganin jiri
"Jaana ka saukeni dan Allah jiri nike gani"
Ajeta yayi a gefen gado ya durƙusa gaban gadon yana zuba ma kyakkyawar fuskar ta ido
"chuchu me kike so, me kike buƙatar kiga kin mallaka da ze saki farin ciki kifaɗamin zanyi miki shi yanzu"
Rauda tayi murmushi tana rusuno da fuskar ta kusa da tasa
"burina ɗaya ne a rayuwa inga na mallake ka,na riga da na samu Allah ya bani kai a matsayin miji bani da wani buri bayan wannan kasance wa dakai shine farin cikina"
Umar ya lumshe idanuwansa saboda daɗin kalaman ta da suka ratsa masa zuciya
"nagode Rauda, yanzu bari inje in siyo miki ice cream ɗin ki kwanta ki huta bayan shi kina buƙatar asiyo wani abu ne?
Girgiza masa kai tayi alamar A'a
Ya miƙe yana manna mata kiss a goshi
"sai na dawo"
Jinjina mai kai tayi, sai da ya kai bakin ƙofa sannan ta kira sa
Tsayawa yayi tare da juyowa
"ya aka yi madam?
Rauda tayi murmushi tace
" ka kula min da kanka sosai"
Shima murmushin yayi yace
"angama Ranki shidaɗe"
Bayan fitar sa, sujada tayi ga ubangiji na nuna godiyar ta garesa
Shafa cikin kawai take yi tana ayyano abunda zata haifa
Tunda ga wannan lokaci umar ya ƙara ƙaimi gurin nuna mata tsantsar kulawa.
Bayan wata tara
Cikin ta ya tsufa sosai dan da ƙyar take iya tafiya
Ranar ya shirya ze tafi aiki yaga yanayin ta sai a hankali ya fasa
Ashe ko haihuwa zata yi
Abunka ga likita da kanshi ya karɓi haihuwar abarsa
Tasha wuya sosai, shi ko ya shiga damuwa ya ƙara tausayawa mata
Cikin hukuncin Allah ta haifo kyakkyawan yaro namiji
Sai da ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta sannan ya sanar da anty kaltum
Ba afi minti goma ba sai gata ta ƙara so
Cikin farin ciki take faɗin
"ah Lallai sannu wato dan kana likita shine ba zaka sanar damu tun tana na ƙuda bako?
Dariya umar yayi yana miƙa mata jaririn
"ga ɗanki nan sai ki shirya sa, ki barmini mata ta zan kintsa abata da kaina"
Anty kaltum ta amshi Yaron tana faɗin
"masha Allah sannu da ƙoƙari da Rauda"
Rauda dai ba bakin magana dan anji yadda mata keji
Da kansa ya kira anty ummi da mama ya faɗa musu
Sunyi murna sosai anty ummi tace tana nan tahowa Washegari
Da daddare Rauda na zaune kan gado ta tsura ma jaririn ta ido
Ji take ƙaunar sa na ratsa zuciyar ta ba abunda ya bari na mahaifin sa, har ma yaso yafi sa kyau
Bata san umar ya shigo ba sai da ya ɗan zungure ta
Ta ɗago ta kalle sa
Murmushi yayi tare da zaunawa
"sannu Maman baby, babyn ake ta kallo haka?
Ta maida mai martanin murmushin tace
" ina kallon kamannin ka daya kwaso ne ba abunda ya ɗauko nawa"
Ƴar dariya yayi me bayyana tsananin farin cikin da yike ciki
"Haba dai wannan ƙaramin bakin ai irin naki ne"
Ta maida kallon ta ga Yaron tana faɗin
"Bawani nan,kadai yimin wayo bari Allah ya kaimu next time idan nasamu ciki bazan sake kallon ka ba har sai na haihu, dan ina ganin kallon ka da na dinga yi ne yasa"
Dariya yayi sosai
"tofah to Allah ya kaimu,wani suna kike ganin ya dace mu saka masa?
Tayi ɗan shuru tana nazari
"ni ina ganin Musaka masa Aasim"
Rauda tayi saurin kallon umar jin abunda yace
"Aasim fa kace?
Umar ya jinjina kai
" eh, miƙo sa ma inmasa huɗuba"
Rauda ta girgiza kai tace
"A'a Jaana kadai duba wani sunan....
Murmushi umar yayi tare da faɗin
" Aasim be cancanci Musaka sunan sa bane?
Shuru tayi tana cigaba da kallon sa
Umar ya cigaba da cewa
"Aasim masoyin ki ne na haƙiƙa wanda a yanzu ya sadaukar da soyayyar sa dan dai ki kasance cikin farin ciki,kisani da ace yana yana da mugun hali da tuni ya halaka ni, ya sha matuƙar wahala akan ki,ya sadaukar da abubuwa da yawa duk dai akan ƙaunar ki,bantaɓa jin tsanar sa a raina koda sau ɗaya ba saboda duk me sonki masoyi na ne,dan haka babu sunan da ya dace musa sai nasa"
Rauda ta kasa magana dan gabaɗaya jikin ta yayi sanyi
Lokaci ɗaya soyayyar ta da Aasim ta dawo mata
Umar ya ɗauki jaririn yayi Masa huɗuba sannan ya maida mata shi kan cinyar ta
"Allah ya Raya Aasim, bari inje in watsa ruwa"
Har lokacin ta kasa cewa komai
Ya ɗan tsaya yana kallon ta
"wai miye kika wani sauya, Haba madam smile mana"
Ajiyar zuciya ta sauke kawai
Dariya yayi yana ficewa daga ɗakin
Shimfiɗar da yaron tayi, ta kwanta tare rufe idanun ta
_"zan barki kamar yadda nayi alƙawari bazan sake bibiyar rayuwar ki, amma kisani bazan taɓa dena sonki ba har ƙarshen rayuwa ta"_
Kalaman shi na ƙarshe suka dawo mata
_haba habibty, kiyi murmushi mana idan kiƙa ƙi yifa zanyi kuka_
_Ina son ki fiye da yadda nike son kaina Rauda_
_Na amince na rasa komai inhar zan rayu dake_
Kalaman sa suka yi ta yi mata yawo a kunne
Ta shi tayi ta zauna, tana jin babu daɗi
Yanzu ko wani hali yike ciki oho, ya datse duk wata hanya da zata sa dashi da ita, yanzu shikenan ba zata ƙara ganin sa ba har abada?
Tayi wa kanta tambayar, sake rungume jaririn tayi tana jin wata sabuwar ƙaunar sa sakamakon sunan da aka sa masa
_matsayin ka a raina baze taɓa canza wa ba Aasim Allah yasa kana cikin farin ciki_
Ta faɗa cikin zuciyar ta
Ranar suna dangi sun taru sosai anci ansha anyi wadaƙa da kuɗi
Jariri ko ya samu kyaututtuka
Bayan wata huɗu Aasim ƙarami yayi wayau sosai dan har ya fara zama
Yaro ne me farin jini kowa sonsa yike yi
Yarima shine sunan da Rauda take kiran shi dashi
Ranar suna zaune tana ma yarima wasa yana ta dariya
Umar kallon su yike yi cikin farin ciki da nishaɗi
Miƙewa tayi ta ɗaura ma umar yarima aji kinsa
"Kaga idan na biye wa wannan yaron bazan je inyi wanka ba"
Umar ya ɗaga shi sama yana faɗin
"daɗin ta ga ubanshi a kusa bari na cigaba da ma wasan kaji ɗan albarka"
Dariya tayi ta haye sama, ta faɗa toilet tayi wanka
Shirin shadda pink tayi, tayi kyau sosai tana cikin ɗaura ɗan kwali ta lura da mutum a ɗakin
A ɗan tsorace ta ɗago, umar ta gani tsaye ya zuba mata idanun sa hannayen sa harɗe a ƙirji
"kai Jaana kabani tsoro wlhi yaushe ka shigo ban sani ba"
Ƙasaitaccen murmushi yayi yace
"ya za ai kisan na shigo hankalin ki ya tafi gurin kwalliya"
Ta sauke ajiyar zuciya
“hmmm to ai dan kai nike yi koh"
Jinjina kai kawai yayi, ya ware mata hannayen sa
“zo inji ɗumin ki plz“
Aje ɗan kwalin tayi ta shige ƙirjin sa
Ajiyar zuciya ya sauke me nawi tare da rungume ta sosai
murmushi tayi tana faɗin
"wannan irin ajiyar zuciya haka? Sai kace ka shekara batare dani ba, banfa fi minti ashirin da baroka ba"
"ba zaki gane ba,yanzu dai baki da wata matsala koh?
Ta jinjina kai
"bani da wata matsala mijina,nagode da kulawarka gare ni ina sonka"
Murmushi yayi tare da faɗin
"Nima ina sonki habibty"
Lumshe idanuwan ta tayi cikin farin ciki
"kasan wani abu.......
Kasa ƙarasa wa tayi, tare da saurin buɗe idanun ta
Idan batai kuskure ba habibty taji yace
"me kafaɗa yanzu? Mai maita"
Ta faɗa tana kallon cikin idanun sa,tabbas ze iya canza komai amma baze taɓa iya canza idanun sa ba
"Aasim......
Ta faɗa cikin rawar murya
"na'am habibty"
Ya amsa yana shafa fuskar sa kamannin sa suka bayyana
Baya taja da sauri tana faɗin
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Yana yin fuskar sa ta canza zuwa damuwa
"sai kace kinga sheɗani Rauda?
Zubewa tayi a kan gwiwowin ta nan da nan idanuwan ta suka ciko da hawaye
" Aasim alƙawari fa ka ɗauka Meyasa ka karya? Dan Allah kada ka cutar min da mijina kada ka cutar min da ɗana........
Shhhh
Ya faɗa yayin da ya durƙusa gabanta
"ba wannan ya kawoni ba Rauda, tsakanina da mijin ki sai dai kariya ba dai cutar wa ba,ɗanki kuma ɗana ne bazan taɓa bari wani abu ya samesa ba, ki kwantar da hankalin ki dan Allah"
Kallon sa tayi da mamaki sosai tana tantamar abunda ya faɗa
"wallahi da gaske nike yi Rauda kiyarda dani"
Numfashi ta sauke tana jinjina kai
"shikenan me ya kawo ka gareni?
" zamu iya zama muyi magana?
Ya faɗa yana tsare ta da idanun sa
Gyaɗa kai tayi, bayan sun zauna yace
"Yanzu ba da bane Rauda, Bawani cutarwa da ze ƙara shiga tsakanin mu, tun ranar da umar ya shiga tauran na tabbatar da yana miki so me tsanani bazan ƙara yunƙurin raba shi dake ba,a shekara ɗaya da rabin da nayi ba tare dake ba na shiga tsananin ɗimuwa na koma rayuwa a ƙasan ruwa da ƙyar na yarda na koma masarauta
Rayuwa bata min daɗi Sam, bana shiga cikin ƴan uwana sai dai na kulle kaina a ɗaki
Ganin halin da na shiga me martaba ya auro min wata ƴar sarki
Amma bantaɓa jinta a raina koda sau ɗaya ba, Rauda bazan iya rayuwa babu ke ba kinkasance wani sashe na rayuwa ta
Ki amince kiciga da rayuwa dani nayi miki alƙawarin babu abunda ze faru da izinin Allah"
Rauda ta sauke ajiyar zuciya tace
"wace kalar rayuwa kenan Aasim amma dai ba irin wacce muka yi a baya ba koh?
"nidai ki amince min inrinƙa zuwa ina ganin ki, ko hakan ma ya isheni"
Kaɗa kai tayi tana ɗan murmushi dan sai lokacin hankalin ta ya kwanta
"nagode sosai habibty"
Da daddare suna kwance ita da Umar yana shafa gashin kanta ta kira sunan sa
Ya amsa, tace ɗazu fa Aasim yazo"
Umar yayi murmushi
"nasani ai,zan shigo ɗakin naji maganar ku"
Ta kalle sa da mamaki
"amma shine ranka be ɓaci ba?
"kan me raina ze ɓaci chuchu? Yariga ya zubar da makaman sa yanzu ya zama ɗan uwa agurina"
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ta jinjina kai kawai
Rayuwa ta canza,Maganar rikici ya ƙare
dan anriga anzama ɗaya, Aasim da umar sun koma kamar abokai musamman Aasim ya kan ɗauke su zuwa duniyar su
Rauda Sam bata da wata matsala dan bata aikin komai Aasim ya ajiye rauhanai mata masu yi mata,umar arziƙi ya ƙara haɓaka dan ya gina ƙaton asibiti na sa na kansa
Sukan haɗu su biyar, Aasim, umar, Rauda shahida da kuma da kuma Aasim ƙarami
Ayi ta nishaɗi su suna hira shahida na wasa da yarima
Ranar ma hakan ta kasance
Suna zaune a falo,yarima yayi bacci yayin da umar suke ta wasa da shahida
Aasim kallon Rauda yike tayi, ta cikin zuciyar sa ya aika mata da magana
"ina son ki Rauda"
Murmushi tayi tana kallon su gaba ɗaya wani farin ciki na ratsa zuciyar ta.
Alhamdulillahi anan na kawo ƙarshen wannan labari na jinnul aashique
Babban abunda nike so na isar shine,rayuwa ta kan zo ma mutum a yadda ubangiji ya tsara masa
Labarin jinnul aashique kashi talatin cikin ɗari 30/100 ya faru da gaske a zahiri
Dan Aasim akwai shi a zahiri yayi soyayya da wata budurwa wacce kuma saurayin ta shine umar
Amma sauran labarin na tsara shi ne dan na faɗakar na nishaɗantar
Aduk halittun da ubangiji yayi babu halitta me kyau kamar ta bil'adama
Shiyasa aljanu suke bibiyar mu,ya kamata mu kula sosai musamman ƴammata dan sunfi samun irin wannan matsalar
Murinƙa azkar, yayin shiga bayi, lokacin kwanciya da sauran su
Dan ba kowani aljani bane yike jin tsoron Allah akwai mugaye akwai kuma na kirki
Jinnul aashique shine matsalar da yawancin ƴammata suke fama da ita, zaka ga yarinya da saurayi yazo indai maganar aure ne sai ka ga ya dena zuwa ko kuma ita taji bata son kowa
Irin wannan matsalar tana da wuyar sha'ani,sai mun kula sosai mun dage da addu'a.
Allah ubangiji ya ƙara karemu da zuri'ar mu baki ɗaya.
Mu haɗu a sabon littafi na, me suna *_ZAFEERAH_* da kuma ɗayan me suna *_JIDDAH_*
Taku a kullum *_ƴarfillo_*.
0 comments:
Post a Comment