Binshi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Gaskiya yana da kyau maza ku san abinda yake ɗaukar hankalin matayenku daga gareku , kuma ku ɗan riƙa cancaɗewa kuna yin kalar burgewa a gaban matayenku , ita fa mace abu kaɗan ke ɗaukar mata hankali , idan dai bakayi ma matar ka gayu ba tou gaskiya baka haɗu ba , wallahi wasu mazan ko ɗaki ɗaya baka iya haɗawa dasu , ba wanka bare kuma kasa ran samun ƙamshi a jikinsu , yadda yaje kasuwa ya dawo haka zai dawo ba wanka ba wanke baki duk ƙurar kasuwa ta gama barbaɗeka , ita kuma matarka tasha wanka taɗauki fili da gayu kamar zataje gasar wanka , ta haɗu tana ta zuba ƙamshi kamar matar sarki sai kace a haka zaka zo ka wani rungumeta , tsakanin ka da Allah kayi mata adalci kenan ? Gaskiya duk mu haɗu mu gyara gaba ɗaya sai a zauna lafiya. Idan kuwa ba haka ba ta sauke ka daga saman gadonta har sai ka koyo wanka wanke baki da kuma shafa turare.... {{ ba cewa nayi ki saukeshi ƙasa ba , ah kidai ɗan gyara mishi dan kema zakiji daɗin tafiyar idan da ƙamshi , ai kindai gane ba , kinsan wasa bai tafiya idan ba abokin wasa haka kuma baya daɗi idan babu abun wasar , kenan wancan hikimar da nake magana tafi daɗi idan da gyaran fili }} haba kuma kuyi koyi da Dikko mana. Ku zama "yan gayen mazaje shalelen matayenku.
Da sauri Ashiru ya fito yana cewa Mai gida bari in kaita , bai mishi magana ba ya wuce wurin mota ina bin bayanshi , da kanshi ya buɗemin na shiga ya rufe , wurinsu Ashiru ya koma suna gaisawa , duk banajin me suke cewa bayan ya gama ya dawo yana ɓata rai , juyar da kaina nayi nima ina fushi har muka fita daga gidan.....
Har mukaje makaranta baimin magana ba , nima banyi mishi ba. Tuƙinshi ya jawo hankalin mutanen dake kusa dan baya tuƙi da natsuwa kwata² , fita. Yace bayan yayi parking , matsawa nayi na shafa fuskarshi nace amana nayi maganar idona cike da hawaye , naji jeki , saida na sumbaci gemunshi sannan nace ina sanka na faɗa ina kallon idonshi , murmushi jin daɗi yayi yace Allah yasa da gaske kike , da gaske nake Dikko , riƙeni yayi tare da cewa zanzo in ɗaukeki idan kun tashi , kuma ki daina ɓatamin rai An mata kinga banajin daɗin abinda kikemin , wallahi maganar da kikamin shekaran jiya bakiji yadda naji ba har yanzu zuciyata ciwo takemin , ki daina haka babu kyau , to , ngode ya faɗa yana ɗan gyarawa. Nima godiya nayi mishi tare da fita , addu'ar Allah ya tsare yaimin nima nayi masa Allah ya tsare hanya , saida ya tafi na wuce......
A aji kuwa Mai gilashi ta tambayeni yadda aka ƙare jiya , kai tsaye nace mata janshi nayi mukayi faɗa duk dai abinda ya faru na faɗa mata. Cewa nayi kuyi faɗa ? Ta tambayeni ? Waike baki iya irin ɗan karuwancin nan ba ? Waye yace miki da faɗa ake hukunta namiji ne ? Ai namiji bakiyi mishi hauka , da sannu kike latsashi , kuma da kinja kika ga yaja sakar mishi ki kuma bishi da swry My President. Shiru nayi bayan wani lokaci nace nima yadda kika ganki a da haka nake , wani abokin Babana ne yayi min asiri naɗan firgice bayan kuma an samu nasara lalatawa na zama sai a hankali , tunda kinga abinda nakeyi dama bani ce nakeyi da kaina ba , tsoki Mai gilashi tayi. A hankali ta ɗan fara labarta min halin Sharifa tare da cewa kuma idan ta faɗamin na daina zuciya ina aikawa Dikko da saƙon zagi , in kwantar da hankali in bata haɗin kai yauma inyi ƙoƙarin riƙe Dikko karya fita domin tana shirya ma Sharifa gadar zare ne , so take ta rifto cikin rami ita kuma sai ta bita da ƙasa ta rufe , tana min maganar taga wani malami ya wuce , miƙewa tayi tare da cewa bari inje wurin wancan mai zanzaron inji me yasa zai ɗauro mana ƙugu yana tayar mana da hankali , tana faɗin haka ta fice daga ajin.
Har aka tashi makaranta Mai gilashi bata dawo ba , Dikko ne yazo ya tafi dani gida , ina ta tunanin yadda zanyi in hanashi fita a daren yau , dan nayi imani yadda ya samu sauƙin nan tou fa lallai babu abinda zai hanashi fita.........
*JAMILA MUSA....* ce.
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*
*SAI NA AURI D ' K*
🅿 ------ 6
Gareku 👇🏻
UMMIEE ZARIA
UMMU FATIMA
&
ZAINAB MUSTAPHA MUSA { Mmn Sadig }
Wata irin zufa ce ta ratato ma Dady. Da sauri ya cire hular saman kanshi ya fara firfita da ita , itama wayar tashi ya sauke daga saman kunnenshi. Miƙewa tsaye yayi bayan ya ajiye wayar da hular a saman tebirin gabanshi ya cire babbar rigarshi ya ajiye cikin tashin hankali , kamar wani zararre ya dafa tebirin yana furzar da hayaƙin ɓacin rai , ganin banza bata kai zomo kasuwa yasa ya ɗauki makullin mota da waya ya fita.... Da irin tuƙin Mai gida Dikko ya fita kuma dashi ne yaje har gidanshi......
Ba kowa gidan. Dan haka kai tsaye ɗakinshi ya wuce. Inda yake ajiye takaddar ko wane ƙaddara nashi ya nufi wurin ya fara ɓaro kaya harya sauko da kaf kayan ya ɗauko fiyel in. Salati ya farayi jikinshi yana kyarma , a hankali yake ɗagawa yana salati harya gama dubawa amma babu takaddun gidajen da akace masa anga Hafsa tana takai dillah² , da gaske kenan ? Wata irin luƙeƙiyar ashariya ya atura yana fizge² ya ɗauki wayarshi.....
Matarshi ya fara kira , amma harya ƙari kiranta ya gama bata ɗauka ba dan bata da lokacinshi. Hafsa ya fara kira itama tanaji tana kallo ta watsar da kiran nashi wanda Amisty ce ta hanata ɗaukar kiran , fita yayi da sauri yabar sauran takardun watse a tsakar ɗaki , har ya fita me ya tuno ? Oho ya dawo ya tattara su ya ƙanƙame a jikinshi kana kuka kamar gawar jaririn mahaukaciya......
Hello......... Ta faɗa cikin irin yanayin da mata keyi idan zasuci banzar samari. Tsoki Yazeed yayi cikin gunguni yace ummm , Ya Yazeed ya naji sai wani riƙe fili kakeyi ko baccin rana kakeyi ne ? Ummm ya faɗa da yanayin rashin san yayi wayar , kuɗi fa sunzo ta faɗa cikin farin ciki da zaƙuwa , yaji daɗi sosai amma bai nuna ba , yace wasu kuɗi kuma ? Yayi maganar yana ɗan sakin muryarshi kaɗan. Cikin warwarewar lissafi tace Yaya D' K ya turomin da 10miliyan na biko , da sauri Yazeed ya miƙe tsaye yace kina ina ne yanzu ? Ina inda ka sameni jiya , yanzu D ' K yana sanki kenan ko ? Ummm itama ta bashi amsa cikin yanayin jin daɗi da kuma kunya haka kaɗan , ba damuwa gani nan zuwa muyi magana , sai......ka.....zo muah. Ta bashi kiss tare da tsinke kiran.
Yazeed yace wawiya wane ɗan tashar bokan ne yace miki D ' K yana bikonki ne ? Halan yayi haka ne dan ya ruftaki , tunani yayi sosai bayan wani lokaci yace kai ai ba haka yake fitar da zakka ba , jakunnan banzaye kuso Yazeed ko ba kuɗi yarinya ta hau network mai service , ai dake da Sharifa da ma duk wata ƙazarma mace na rantse da girman Allah baku gabanshi , da dai yana ɗan biya allon mata { danbe } da sai ince zai wanke ku ne yayi gaba abunshi. Bara dai in tafi da wuri kafin wani malamin tsubbun ya rigani ƙwacesu.
Da wata irin rashin lafiya mijin Halima ya tashi yau , ko idonshi baya iya ɗagawa , yayi amai tun cikin dare baisan iyaka ba , yayi na safe yayi na rana har a marecen nan sai yunƙuri yakeyi , waƙƙƙ , yaci uwashi yaci ubanshi har yai laushi. Duk ƙawayen matarshi zagaye dashi sai jera mishi sannu sukeyi kamar sakin kurwar mayu. Halimatu kuma na gefe tana ta duba sabbin kayan matar da ƙawarta ta aiko mata dasu tana karantawa da kuma irin matsayinsu da wutar da suke bayarwa idan an shiga tsakiyar filin wasan danbe. Saidai ayi murmushi idan aka karanto "yan bala'e , ita a gefe ƙawaye a gaban gado.....
Da gudu na fito daga toilet jin wayata na ƙara , nayi tunanin kila ma ko Mai gilashi ce ? Dikko na gani tsaye gaban wayar zai ya ɗauka , aikinshi kenan idan yana nan aka kirani , An mata waye ya kiraki ? An mata me akace ? Kawo in gani ? Shi gani yakeyi ta waya ake zuge mishi ni. Da Allah nace ka daina taɓamin waya , kai ake nema ko ni ne wai eye ? Haƙuri ya bani tare da miƙomin yana cewa na ɗauka fa Mama ce ta kira. Idan Innar ce kai take kira ne ? Nifa gaskiya bana san abinda kakemin ko kai zuwa nakeyi ina tsareka idan kanayin cht da karuwowinka ne ? Sa ido kamar maƙocin mai kura. Ansar wayar nayi daga hannunshi , baƙuwar number ne kuma kiran ma ya tsinke. Kayan dana cire na ɗauka na wuce ɗakina ba tare dana gama wankan ba , ina zuwa na rufe ƙofa na zubar da kayan ƙasa na wuce toilet.
Gefen gado Dikko ya zauna cikin ɓacin rai.... Yana ƙoƙarin riƙe ɓacin rai amma An mata bata gani dai ko ? Tou wallahi idan dai ta kuskura ya riƙeta na lahira sai yafita jin daɗin , wai karuwowinshi ? Jinjina kai yayi cikin tsananin ɓacin rai a hankali ya furta saina kashe ki.... Ya faɗa yana riƙe wuyanshi... Rufe idanuwanshi yayi yana hasko lokacin data fito da gudu daga toilet , banda ma hauka da yarinta ji yadda ta wani fito da gudu ? Da taje ta faɗi ta kashe mishi babynshi , taci albarkacin ko ma waye kwance a cikin cikinta , amma akwai ranar ƙin dillanci , wato ranar da wandon mai gari ya ɓace.......
Tunda na shiga wanka kiran yake ta sake shigowa har na gama wanka ba'a daina kira ba , ni nayi tunanin Mai gilashi ce dan haka na ɗauka , suna na *SHARIFA...* , wai Allahna na rantse da girman Allah na kaɗu gabana ya yanke ya faɗi kawai dai naji tsoro , dakel nace to ya akayi ne ? Kiranki nayi in faɗa miki nice wacce Dikko yake so. Kuma ni kaɗai yake ma soyayyar da bata da farko ballantana ƙarshe , ya gina min soyayya mai girma tsakanin saman sararin filin zuciyarshi zuwa tawa. Ni kuma na gina mishi tawa soyayyar bulo da bulo tsauni da tsauni tafiya da tafiya kalma da kalma tsakanin dare da rana na gina a cikin zuciyarshi..... Nice yake ma soyayyar da bayayi miki irinta , iska ce ni idan na kaɗo saina ɓaro da "ya "yan kanya daga jikin uwarsu iska ta tana ƙarfi. Ki tsaya ki gani haka zan kakkaɓeki tsaf inyi waje dake.......
Murmushi nayi mai sauti tare da cewa aikin banza an tura agwagwa ruwa. Duk lokacin da kikabi kika gina ko ya gina wannan ba matsala ta bace ba. Nidai abinda na sani na kuma fahimta ke daƙiƙiya Dikko ya ɗaukeki , idan kuma kina ganin shi zai aureki tou ƙarya yayi miki dan har yanzu zuciyata ta ƙaryata aurenshi. Bata faɗamin ƙarya akanshi wallahi duk abinda ta faɗamin ko ta ansa akan shi tou wallahi zai faru , liƙi a idon bainan nasi bashine yake tabbatar da soyayyarki a zuciyarshi ba , idan ke iska ce to Dikko guguwa ne. Gittawarshi tashin hankali ne domin idan ya taho kowa saiya gudu ya ɓoye saboda girman hatsarinshi , sahun keke ne shi mai gasawa mata azaba a tafin hannu , naji ke iskace. Kanyar kaɗai kike iya ɓarowa banda ɗan kuka , zubdo ɗan kuka saida babban makami badai iska ba ko jifar ƙananun yara , Dikko kuwa iccen kuka ce shi koda karfinka saida rabonka ko ka jira bushewarshi , to shi ɗanye ne yini ɗaya zur kana jefa amma baya faɗowa sai kayi jan ido , idan kuma kika ce ki hau tou lallai sai kin sauko gurguwa. Icce kuka hawanshi sai an shirya , idan ba'asha dare ba asha rana. Dan haka ni soyayyar da yake miki bai shafeni ba , nawa na tabbatar tunda ya kawoni gidanshi ya adanani a matsayin matarshi , ku ya ɗauka mahaukata abon firarshi idan ya fita , jakuna banza da baya zuwa firar zance wurinku a gidan iyayenku saidai ku baro gidajen iyayenku ku biyoshi , ni ban ɗaukeki a bakin komai ba. Saboda duk abinda zaki faɗa masa ko ya faɗa miki a kaina ya fara faɗa , kuma daga gareni ni kalamanshi kaf suka ƙare banza sharar bisa titi mai kauyawan kalamai Dikko baya auren karuwa.......
Zagina tayi sosai tare da cemin *SAI NA AURI D ' K* nace ƙarya takeyi , ta sake maimaitawa , nima na maimaita ƙarya takeyi Dikko ba ƙaddarar mallakin ballagazun mata bane ba , haka mukai ta caccakar juna kowa yana yanka kalamai masu ciwo tare da yima abokin faɗar tashi gori , ita ta gaji da kanta ta kashe wayar ta bayan ta tabbatarmin da sai na fita a gidan Dikko. Tsoki nayi bayan ta kashe nace shirmen banza shirmen wofi.
Haka yaita garari tsakanin Qerau da duk inda yasan akwai wata madakata ta "yan iska har dare amma baiga Hafsa ba kuma babu Amisty , Qerau ya koma ya kafe motarshi ya fito ya daki gaban motarshi ya halbi tayar da ƙafarshi yace wallahi idan Amisty da Hafsa basu fito ba saiya cinna wuta ga duk wani gida dake cikin Qerau kuma haka duk wata karuwa daga yau kasuwarta ta mutu dan duk wata karuwa dake anguwar nan sai ta koma gidan ubanta , "yan iska kowa tabar jaharta da iyayenta sunzo sun zamar musu annoba a cikin garin Katsina. "Yan iska zuwen banza da wofi , tou yanzu zanyi waya a kawo min tankar man fetur duk saina babba gidajen dake cikin anguwar nan , haka yaita ɓuɓɓurma zagi kamar sabon hauka lokacin da sarara.
Babu wanda yayi ma Dady magana. Haka ya kashe santa yaci gaba da ƙaryar rashin kunya iskanci kuma sanka² , karuwan dake zaune a ƙofar gida saman dakali suna lido ko kallo bai ishesu ba , ganin zasu ɗaukeshi mahaukaci da hankalinshi yasa ya samu wani yaro yace yaje maza bakin titi ya kira mishi duk wani ɗan bunburutu kuma su taho da jarkar fetiri. Yaro ya ƙwalƙwala da gudu ya tafi dan tattaro duk wani mai siyar da fetir. Wata tsohuwar karuwa ce da ta gaji da karuwanci har ta gagara tuba ga Allah ta tsufa iya tsufa , breziya ne a jikinta sai zani ɗaurin ƙugu da kallabinta tayi mishi ɗauri irin na tsofaffin "yan iska , kai da ka kalleta kasan ba Allah a lamarinta domin har yanzu duniyar gaba suka bata ba baya ba , tsaye take a ƙofar gidan Amisty fitowarta kenan daga cikin gida tana shan sigari , riƙe tabar tayi da bakinta ta dafa hannayenta a ƙofar. Saida ta gama kalle waje tass sannan ta fito da rangwaɗa....
Wuri ta samu ta zauna ƙafa ɗaya saman ɗaya tana ci gaba da kora hayaƙi tana wani hankaɗe kai sama cikin iskanci da sanin hannunta wurin kwarema iya jan sigari. Kallonta Dady yayi yace ke tsuhuwar karuwa ko kinga Hafsatu ne ? Banza tayi dashi taci gaba da jan hayaƙi tana aikashi sama , wurinsu ya matsa yana cewa zaku fiddosu ko saina tona muku asiri ne ? Sai yanzu tsohuwar tayi magana cewa , karuwan yanzu kamar man kitse ne a saman wuta , yayin da suka ga hasken rana sai su gudu su koma ciki gudun karsu narke , zamaninmu mu kuma , ta nuna kanta tana tafiya da maganar ta cewa mu wutar muke nema ido rufe amma da ta hangomu sai ta suƙe kafin mu iso , ni da lokacin da nake Adda ta ce da saina rabaka gida biyu bayan na ɗaukeka na saka cikin ɗakina shegen nan dasai nayi maka fyaɗe , karuwan yanzu matsorata ne. Su ke gudun mazan ba mazan ke gudunsu ba , zamani na ni kuma da nayi iskanci maza idan suka ganni ɓoyewa sukeyi saboda wutace ta doso wuri , kallon taron yara²n karuwan dake zaune tayi tare da cewa mataye....... Gareku tayi maganar tana nuna Dady. Sannan ta haɗe kai dasu tayi musu ƙus² a dai² lokacin da yaron ya dawo da "yan bunburutu layi ɗaya kowa ɗauke jarkar fetir.....
Gaba ɗaya karuwan suka haɗa baki cewa. Dan Allah Dady kayi haƙuri , 🙏🏻idan ka ƙone mana gida ina zamu zauna ? Wannan gidan da kake gani ba namu bane ba , amma tunda munga da gaske kakeyi bara mu faɗa maka gaskiya , har yanzu tare suke magana kuma a tare kowa ta nuna da ɗan yatsanta manuni suna cewa ai Hafsa da Amisty suna hango motarka suka shige can gidan suka ɓoye suka nuna gidan da Dikko ke kiwon dawakan shi , tare sukeyin magana babu wanda yake wuce wani kamar suna biya karatu , amma kayi haƙuri karka ƙona gidan idan ka ƙonashi wannan gidan za'a siyar a biya masu gidan can kuɗin fenti da abinda ya ƙone , idan kuma aka siyar kaga shikenan kasuwarmu zata mutu kamar yadda kace kayi haƙuri don Allah , suka ƙarasa maganar suna haɗa hannayensu wuri ɗaya na neman gafara.....
Dady ganin sun tsorata shima ya haɗa kanshi da masu bunburutu yace tou kuyi da wasa ku yayyafa fetir ɗin nasan zasuyi musu waya su fito , masu fetir zasuyi magana Dady ya toshesu da kuɗi yana cewa idan dai dan wannan ga kuɗinku , su kuma suna so su faɗa mishi gidan Dikko ne ya duba yaga wace karuwa ta isa ta mallaki gida layi ɗaya tun daga farko da kuma ƙarshen santa , amma sai Dady yace ai bafa ashana za'a ƙyarta ba , ya ƙara musu kuɗi , aje ma Dady fetir sukayi ya ɗauka yaci gaba da watsi dashi yana cewa saina ƙone shi , su kuma karuwai sukaci gaba da cewa Dady dan Allah ka rufa mana asiri karka toya gidan nan. Idan ka ƙoneshi asirinmu zai tonu komai da muka mallaka zamu rasashi wurin gyaran gidan nan , Dady yace saina tona muku asiri , a tare sukaci gaba da cewa ka rufa mana asiri karka tona asirinmu , ci gaba yayi da mita yana saiya tona musu asiri , saida ya gama zazzaga fetir ya ɗauko layter ya kunna yana cewa zan cinna fa.... A dai² lokacin da Umar ya fito shi kuma warin fetir in ya fiddoshi , idanuwa ya zaro tare da cewa kai׳ kashe mu zakayi ne ?
Dariya Dady yayi tare da cewa halan ka tsora ko ? Umar yace ba dole inji tsoro ba zaka kashe mu ? Matsowa Dady yayi da wutar yana cewa to koma ka fiddomin Hafsa da Amisty ance sun sayar min da gidaje 3 da suke duk a cikin lay-out masu haya a gidan ne suka kirani akan ban musu adalci ba na siyar da gida babu notice , su fito su kaini wurin wanda suka siyi gidan ni a bani gidajena , kasan ko miliyoyi nawa na siya ? Tou kaf kuɗin gadon "yan ɗakinmu ne na lashe yayi maganar yana nuna lashewa da harshenshi. Murya ƙasa² tare da matsawa kusa da Umar yana cewa dukiya...... Akan kuɗi babu abinda bazanyi ba , da hannun haggunshi ya murza "yan yatsu biyu sukayi ƙara cewa koma ka fitomin dasu kafin in toye wannan gidan.....
Karuwai kuma cewa sukeyi mun tuba Dady kayi haƙuri karka toye , shi kuma Umar cikin rashin fahimta yake kallon Dady , dariya Dady yayi tare da nuno bayanshi yana cewa ya kaji suna cewa....? In rufa musu asiri fa , saina toye , shin na toye ko kuwa ? Zaɓa mutuwa ko kuɗin gidajena ne ? Umar ya fara takawa baya Dady yana binshi yana cewa me kace ne ? Hannu Umar yakai da niyar ɗora hannunshi akan layter amma sai Dady ya fizge , wurin fizagewar ne ta faɗi wuta kuwa taci gaba da ci.... Karuwai sukace yawwa tou kane asirin ka zai tonu gidan Dikko ne....... Suna dariya , aimu babu wani da ya isa ya kashe mana kasuwar karuwanci ko ya tona mana asiri saidai mu , mu tona asirin mutum , ana baka haƙuri kana rashin kunya , kaga sai kaje ka saido sauran gidajenka kayi mishi gara da ramuwar dokunanshi , tsohuwar tace dokin da aka kawo shekaran jiya na miliyan talatin da biyar ne , shin ka ajeta....? Kwaiwayon maganar Dady sukaci gaba dayi , yayin da Umar yayi gaba yana akawo ɗauki Dady kuma ya fara kiran "yan kwana² asara goma da ashirin.....
Amisty da Hafsa kwance a wata lafiyayyar hotel dake cikin garin Abuja , banƙararren rago ne aka gaso musu , sai kaji da aka kaso musu sunkai ashirin , manyan lemuna na kwali masu tsadar gaske da kwaleyen sigari an jera su da kwalaben giya , ɗakin cike yake da manyan karuwai da suka gode ma zamani da zuwan wannan rana , ita kuma Hafsa daga kwance ta kwance hannunta ta ƙara ƙwalƙwaleshi tasha kukanta sannan ta maidai abunta ta rufe..... Daga kwance Amisty ta fara gabatar da bayani kamar haka.......
Barkanmu da kasancewa a wannan lokaci manya karuwa maza da mata , na baya , gaba , haggu da dama duk muna muku barka da zuwa , {{ wato masu maɗigo da "yan luwaɗi sai kuma mazinata.... }} kamar dai yadda kuka sani muɗin masu sa'ar rayuwa ne kullum nasara muke samu babu faɗuwa , mune manyan jajirtaccin karuwai da muka kafa manya² tarihi a cikin jahar birnin garin Katsina , kuma mune zamani na farko da muka kawo wasan danbe a duniya , kullum nasara muke samu dan haka ya kamata a jinjina ma bariki don Allah , shewa sukayi gaba ɗaya tare da ɗaukar kwalaben giya kowa ya ɗaga.....
Saida kowa yasha yayi gyatsa alamar ta sauka ciki Amisty taci gaba da cewa. Bariki tayimin komai , ta biyani kuma ta raineni fiye da yadda nayi tunanin samu daga gareta , bariki ta itace uwata kuma itace ubata a cikinta na rayu tun bansan wace ce ita ba. Mutane na cewa bariki bata da tabbas , tou ni kuma na ƙaryata masu wannan maganar , bariki kuwa itace mai tabbas ga amana haɗin kai da kuma ƙaunar juna , a taƙaice dai ni bariki tamin tabbas....
A gurguje dai muyi abinda ya taramu a wurin nan , manyan gidaje dake can cikin lay - out na Dadyn su Hafsa mun siyar dasu akan farashi mai tsoka saboda kunsan komai shi ke siyar da kanshi , dalilinmu na siyarwa kuwa sirri ne tsakanin rayuwarmu mu biyun duk dai bama ɓoye ma juna sirrin juna tare ake ci kuma idan an samu , ku nawa ne duk taron ku ? Irga kansu sukayi sannan aka faɗawa Amisty ko su nawa ne , Amisty tace mutum goma ? Tou za'a bawa kowannen ku a ciki zunzurutun kuɗi har naira miliyan ɗaya a cikin kuɗin. Jibi kuma dani da Hafsa zamu wuce india mu wanko zumibi mu dawo..... Idan kuma aka sake samun wata sa'ar sai a tura wasu a cikinku su tafi , tou ya kuka ga tsarin ne ? Kowa yace haka yayi Kaka......
Shagali...... Suka faɗa gaba ɗaya , dan haka aka rufawa kwalaben giya da sigari , suma kaji da naman rago aka ciccinye aka kora da ruwan lemu , bayan sunci iya cinsu aka tattara sauran aka fitar.......
Mutumin da Amisty ta kai Hafsa a matsayin malamin tsibbu shine ya kira Amisty akan shima ta fiddashi , cikin maye tace ai babu kasonka a cikin , haɗata ya farayi da girman Allah amma fur Amisty tace ai ko Hafsa bata kashi da gaurayen kuɗin nan , kuɗi duka suna wurinta sun kuma zama nata. Mallakinta bata rage musu ko sisi kuma da asuba zata fece abunta ta tafi can ƙasar waje ta buɗe sabuwar da'irarta , karuwan suma da tace za'a basu one² miliyan ƙarya takeyi , ai ita ba daƙiƙiya bace ba tasan hannunta , ta siya sabuwar mota ta miliyan 5 dan haka daga nan zata canja akalar tafiyarta zuwa Mambila , idan taje ta huta daga can zata wuce gaba abunta ta wani ɓace cikin duniya kamar yadda jirgi yake lumewa a cikin giza²i dake saman sararin samani , dariya tayi sosai cewa kusha zamanku a Katsina Amisty ta tafi yawon buɗe ido sai mun haɗu a lahira. Hahahahaha tayi dariye cike da iskanci kamar zatayi kuka , Allah sarki zanyi ƙewarku Katsinawa...... Dariya ta sakeyi bayan ta kashe wayar tace Amisty tayi gaba kuma babu dawowa........
Wata irin ashar ya fesa bayan Amisty ta kashe wayarta. Cikin ɓacin rai ya sake daddana ashar kamar rainon mutane gafiya , yarinya idan kinsan wata baki san wata ba , shima dake kwallon gigiye ne wurin iskanci da taurin kai , cikin garin ya famtsama a daren saida ya gano har hotel in da Amisty take a Abuja , mutanensu na can Kaduna da kuma "yan iskan dake saƙe a sansanin yanki Abuja manyan "yan ta'adda ya buga ya rattaɓa musu komai ya kuma ƙara da cewa su hari Amisty. Su ƙwace kaf kuɗaɗen har motar karsu bar mata....... Shima yana zuwa Abuja a daren nan , suma bayan sun gama waya dashi suka sanar da mutanensu na Katsina suka kuma tura hotonshi da adireshin cewa su ɓarar dashi suna da kaso biyu a cikin kashi goma na kuɗin , shiri suka farayi ta yadda zasu riƙe Amisty da kuɗin cikin sauƙi......
Kirari yake ta goga mata kamar tsohon maroƙin da yayi shekara baici ba , su Jiddah saidai a juyar da kai ayi dariya kan׳ dariya irinta jakkan mata , haka Yazeed yaita ɗorata tana hawa shi kuma ya rungume banzar yaita lalubarta. Daƙiƙiyar ta saki baki taci gaba da dariya kamar kwarto yaga wa²n zama. Haka yaita suɗeta yana bazo mata manyan kalaman batsa , a cikin motar dai ya labbaceta ya buga round ɗaya na danbe , yau yanajin shi wani babban shege ne yabi hanyar da D ' K ya taka ya wuce..... Bayan ya karance tayi mishi transfer na 5miliyan. Sannan tace a tsaida ranar aure tunda an samu kuɗi , kai tsaye yace sati mai zuwa.... Da farin ciki Jiddah ta fice Yazeed kuwa ya wuce wurin harkar danbenshi tunda ya samu kuɗi.
A ɗakinta dake gidan Rabiya ta kwanta ruf da ciki a saman gado tana tunanin Dikko , jinjinoshi tayi sosai sannan ta jinjino haɗuwarta da Yazeed kai zanen ba ɗaya bane ba kuma karatun yasha ban². Dikko fa daban ne yayi zarra + zarra , gaskiya da gaskiya ce , jarumta ta zahiri duka da duka , salo bisa salo ƙwarewa da iya gugar zanar sanin abinda ake kira da danbe yana nan wurin Dikko , wannan shi ake kira jarumin namiji ba lusari ba , kana ta ina ne haka ? Me kakeyi yanzu ? Kana tunani na ? Koma dai miye ina nan dawowa gareka ka ƙara haƙuri ɗan uwana.
Sun nemeta har sun kaji , bokansu ya bugi ƙasa ya zana , ya goge amma ya kasa ganin inda Mardiyya ta shige , haka nan Suwaiba ta haƙura ta dawo Katsina. Kuma bata wuce Daura ba tana nan ta saƙe a cikin Katsina !
Bayan anyi nasarar kashe wutar dake ci a wajen gidan Umar ya riƙe Dady tare da cewa saiya kaishi wurin Mai gidansu. Haƙuri Dady ya bawa Umar cewa shi baisan haka abun yake ba , iyakar dai wutar waje , babu abinda taci sai fulawowin da sukasha fetir dan haka suka babbake bangon wurin yai duhu. Umar ganin tashin hankalin da Dady ya shiga bai faɗawa Dikko abinda ya faru ba , saidai zaiyi sabon zubi na filawowin da sukaci wuta , sai fenti da yace gaba ɗaya kaf gidan daga ciki har waje zaiyi fenti dan idan akayi a wajen gidan kaɗai Dikko zai gane , idan kuma ya gane zaiyi tambaya shi kuma zai faɗa masa kai tsaye baya munafirci , sai shi kuma a bashi na toshiyar baki.
Wannan tsohuwar karuwa ba haka taso matsalar ta tsaya ba , taso a toye kaf gidan dan Dady yaci uwarshi wurin yaron nan , ita sau ɗaya ta taɓa ganin Dikko shima abinda yasa yadda taji Hafsa tana zuzutashi , ita tasharshi da aka bata labarin abinda yayi ma Sultana ya burgeta yadda taga Dikko tana so taga Sultana itama , to shine fa ta matse lamba taga ɗan iskan yaron nan , da taga hotonshi ta matsa sai ta ganshi da idonta , matashi ne kyakkyawan yaro amma kai da ka kalli Dikko kasan baida mutunci ko kaɗan ɗan iska ne bugu ɗaya , kuma wasu irin firgitaccin idanuwa gareshi tsaitsaye na rashin kunya , ita a yadda ta auna shekarunshi zasu fara daga 35 har zuwa 38 ita dai a yadda ta ajiyeshi fa , dan yana da suffa mai ɓoye shekaru yana da cikar zati da ƙwarjini saidai daga ganinshi kasan sangartacce ne , yana da tsayi dai² kyau , yana da murzajjen jiki na zubin jaruman maza ba ƙaton jiki ba dan baida ƙiba kuma ba siriri bane ba yana dai da jiki mai kyau sai hutu ya zauna. Gaskiya Dikko yayi mata kyau , kuma kyakkyawar fatarshi ta dace da gemun daya ajiye mata , zuwa ɗaya idan kayi mishi dogon kallo yana da ɗabi'un mutanen kirki amma gogaggen ɗan iska ne kuma bashi da kunya yadda ta fahimce shi , tou taso ace gidan ya ƙone taga yadda zaizo yayi ranfar da akace yanayi wallahi yau taso aci ƙaniyar Dady a murje bakin tambayar kuɗin gidaje har sai Kaka ta dawo suma ta basu kasafinsu.... Itama dai Dikko ya burgeta gaskiya addu'arta ɗaya Allah yasa da rabon Hafsa a cikinshi.
Misalin ƙarfe 11 da wasu "yan mintuna na dare na ɗaure Dikko dake kwance yana bacci saman gado da igiya. Buɗe idonshi yayi ya kalleni cikin ɓacin rai , cike da rashin kunya na murguɗa baki tare da zazzaro ido nace yau na ɗaure ƙafar yawo wallahi , sai naga ta inda zaka bi ka fita , da chat in dare da fita yau gaba ɗaya An mata ta hana nayi maganar ina watsa hannunawa alamar babu , fiffizgewa ya farayi yana cewa idan na kwance sai na zaneki An mata , zama nayi gefen gado tare da faɗa cikin rainin wayau cewa ai bama zaka iya kwuncewa ba , taimako ɗaya zanyi maka. Bara in kunna maka kwallo ka kalla , nayi maganar ina ɗauka rimot kusa dashi na kunna tv. Tsoki yayi a gajiye ya koma ya kwantar da kanshi yana bina da kallon takaici....
Ka daina kallona ka kalli talabijin na nuna mishi tv , ajiyar zuciya ya sauke tare rufe idanuwanshi. Tashi nayi daga inda nake zaune na koma cikin kujera na zauna inacin gurguruna { pop corn } ina cin abuna ina kallon kwallo , buɗe idonshi yayi ya kalli Sultana sannan yace An mata kizo ki kunce ni kafin raina ya ɓaci , naji shi sarai amma sai na ƙure volume ina cewa ka rufe min baki bana san surutu ina kallon kwallo ka kalla nace , nayi maganar ina watsa gurguru baki. Ke......... Zoki kunce ni nace , cikin faɗa nace anƙi a kuncen kan kuma ka rufemin baki bana san surutu idan ina kallon nace maka , An mata......... Ban barshi yayi magana ba na zaro ido tare da haɗa masa da shittttt 🤫 nayi masa ina ɗora ɗan yatsa na a saman baki.
Kallona ya ƙarayi. Bayan wani lokaci yayi ɗan taƙaitaccen murmushi kaɗan ya kauda idonshi gefe yana nazari..........
*JAMILA MUSA...*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*
*SAI NA AURI D ' K*
🅿 ------ 7
Ƙasa² nake magana ina cin gurguru cewa. Ƙaryar rashin kunya. Ai sai an bar zomo yake zama guza. Kowa ai ɗan iskan kanshi ne , ni har an nunamin hanyar hukunci , a dai² lokacin daya sake kalloni da dogon kallo , murmushi nayi kaɗan tare da ibar gurgurun kamar zan bashi bayan kuma muna da tazara. Ya² ne ? Zakaci ? Na faɗa ina murmushin nasara. Girgizamin kai yayi alamar a , a , ya bani amsa. Ban sake magana ba na ci a bakina ina cewa saina..... Na nuna da hannun hagguta yankawa alamar zan yanka mishi wuya kenan. Idan bai daina kallona ba kalli can nace ma na ƙara nuna mishi tv...
Gyara bakinshi yayi ya kalli talabijin. Ni kuma naci gaba da cewa wato da ka kwanta kayi bacci , misalin 12 saura ka tashi. Daga saman gado zaka wuce bayi ka watsa ruwa , zaka fito ɗaure da rigar wanka. Kana fitowa sai ka tsaya jikin madubi , zaka goge jiki da towel , da hannuwa na na nuna yadda ake shafa mai ina shafawa a fuskata , daga fuska naci gaba da nuna duk inda ake shafa mai a jiki. Bayan ka gama saika fara goge fuska , ummm na nuna yadda yake sharce gemu da kuma yadda yake shafa turare dariya nayi sosai tare da komawa da baya na kwanta cikin kujera , bayan ka saka kaya sai ka wani fece abunka. Cikin dariya naci gaba da cewa tou yau Jarumarka ta ɗaure kafafuwan yawo , no cin cingom & no cht na nuna yadda yake riƙe waya da wayata , da hannun dama na sake nuna babu. Ina cewa kaji....??? Na riƙe kunne na dan ya tabbatar min yaji.
Baiyi magana ba kuma bai kalleni ba yaci gaba da kallon tv kamar yadda na sashi. Banda tuƙuƙi babu abinda zuciyarshi ke mishi , yana ta ƙoƙarin riƙewa da kuma dannewa ya gagara , cikin wata irin murya yace ke kunceni nace miki. Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da hannu na nuna karka dameni da baki kuma nace ka fita idona in ba haka ba mizanete kana daga kwancen nan. Kai............. Nine zaki dakar ? Tou saina kunce kuma saina kashe ki , da sauri na tashi ganin yana fiffizgewa da ƙarfi , saina kashe ki........ Da gudu na fita a bakin ƙofar fita daga ɗakinshi na zame , shi kuma ihunshi ya ƙara yawa , ninen ma zaki daka ? Yau idan basai na ma kasheki ba tabbas saina kashe kaina...... Da sauri na tashi nayi ɗakina ina kuka ashe har yanzu Dikko bai warke ba. Rufe ƙofa nayi har nayi fitsari saboda tsoro. Har yanzu ina jiyo ihunshi yana faɗin saina kashe ki...........² ƙyarma jikina ya farayi kodai in fita in gudu ? Nine zaki daka ma.......... ? To zo ki dakenin , kai.............. Saina kashe ki............. Kowa da kowa ma saina kashe shi....... Ah² ba lafiya ? Na faɗa ina ƙara fashewa da kuka. Babu wani ruwana da ciki har babyn shima sai na kashe shi................. Kai......... Wai nine ma mace zata zane , a sauƙaƙar murya yace aiko dana zama lusarin namiji. Daga haka ya ɗauke. Tunda ai kunga yana kwance ne , dan dama idan ciwon ya taso mishi kwantar dashi ƙasa akeyi , idan dai aka kaishi ƙasa anci galabarshi. Sai a bashi magani dan idan ya tashi dawowa ya dawo da tunani.
A firgice na juya inda na yada wayata tana ƙara , ummm na faɗa tare da goge zufar dake bin fuskata. Rairafawa nayi inda take na ɗauka , Ashiru ne yake kirani , ɗauka nayi cikin kuka nace Dikko ne baida lafiya , ke kina ina ne ? Na kulle a ɗakina. Waye ya ɗaureshi ne ? Cikin kuka nace ai kaine ka siyo igiyar , Ashiru yace ba wanda ya siyo igiyar ba wanda ya ɗaure shi nake magana , nice na ɗaureshi , meya haɗaku ? Shiru nayi banda abin cewa , Ashiru yace kizo ɗakinshi. Cikin kuka nace ni gaskiya bazan zo ba , ranki ya daɗe kizo mu duk muna ɗakin , tou na faɗa tare da ajiye waya. Toilet na shiga na wanke jikina sannan na fito na gyara inda na ɓata da fitsari , kaya na canza bayan na gama na kira Ashiru yana nan ? Ya tabbatar min suna nan , hijabina na saka na buɗe ɗaki na nufi ɗakin Dikko.
Gaba ɗaya su Ashiru suna wurin , Dikko yana kwance a ƙasa ya dafe kanshi da hannun damarshi cikin yanayin jigata , ya fiffizge igiyar , wurin saukowa daga saman gadon ƙafarshi ta riƙe shi yasa ya faɗi kenan ? Kallona Ashiru yayi cikin ɓacin rai yace amma me kika faɗamin maganar siyo miki igiya ? Shiru nayi ina ta karkasa ido kamar an kama ɓarawon "ya "ya ina kallon Dikko sai kuma in kalli Ashiru. Gaskiya baki kyautawa abinda kikeyi. Mai gida dai kike ma haka ? Ya faɗa yana jinjina kanshi , kausasa murya yayi da fushin zuciya yace tabbas ke yarinya ce. Amma komin yarintarki ya kamata ki riƙayin abu da lissafi , tunani da kuma hasko abinda kaje ya dawo. Wannan ɗin dai da kika raina shine bangon rayuwarki idan har kika ɓata mishi ko wulaƙantashi kanki , idan kuma ya mutu tabbas ke zaki shiga3nki. Shawara da neman mafita ya rage naki. Ya ƙarasa maganar yana gyara mishi kwanciyarshi.
Durƙusawa yayi gaban Dikko yana kuka kamar ranshi zai fita , bayan wani lokaci yayi magana cikin hayaniya cewa ke bake kaɗai ba. Bango ne kuma jegone ga duk wani da kika ganshi yana tsaye a wurin nan yayi maganar yana nunasu hada kanshi , ƙasa² yayi da murya cewa duk yawancinmu nan da kika ganmu kusan mu goma sha wani abu rabin mu duk mu marayu ne , rabi daga cikinmu duk basu da uwa uba ko ahali , haka akaje aka kwaso mu aka kawo mu domin kula dashi , an ɗaukomu ne kamar karnukan shi muyi haushi yayin da wani yake tunkaroshi , babu wanda yasan darajarmu ko tausayin mu rayuwar da zamu shiga. Mu rayu ko mu mutu ba damuwar su bane ba shiɗin dai ake so mu ba rayuwarshi kariya , muyi haushi wan² yayin da wani yake zuwa dan taɓashi , mu kula dashi bayan ƙarshen wata biyu abamu naira dubu hamsin.
Cikin ɗaga murya yace amma shi bai mai damu karnuka ba........... Shine ya jawo mu jikinshi ya ɗauke mu kamar "yan uwanshi , ya soke wata banzar dubu hamsin da Mai gidansu yake bamu {{ wato Dady }} bayan ya nuna mana kowa yaje yayi rayuwarshi , haka mukai ta kuka ya rufa mana asiri ya barmu mu zauna dashi koda an daina biyanmu albashin zamu zauna dashi saboda dubu hamsin ɗin dashi bai ɗauketa kuɗi ba , ganin yadda muka shiga tashin hankali yasa shi da kanshi yace zai riƙa biyanmu , shin kinsan farashin da yake biyan ko wane ɗaya a cikinmu ? Me mukeyi masa ne ? Bamayi masa wanka bama dafa mishi abinci bama masa wanki bama shara komai bamuyi mishi , zaiyi fita goma bai fita damu ba. Muci musha kowa dake wurin nan mazaunin shi yana a cikin gidan da yake rayuwa. Duk inda yake muna da gidanmu muma a can ƙarshen gida , palo bedroom toilet yadda yake da A C a ɗakinshi muma namu dashi. Yaga munyi kuka shi yasa yake san ya rayu damu domin muma muyi farin ciki kamar shi. Masu kuɗi nawa sukeyin haka ? Wanda sun ɗauki duk wani ɗan aikinsu kamar wani jakinsu. Shi yasa suka kira talaka da suna bawa.......... Cikin kuka yace wai talaka shine bawa , wai bawa ? Kuma alere dangin jaki wai ya mutu gobe a sake sabo. Tou shi bai banbanta ba saboda soyayya , abincin da mukeci shi kanshi abun duba ne , idan ciwo ya kama ɗayanmu shine magani kuma ba'a cikin wanda zai bamu ba , albashin kowa a cikinmu da yake biyanmu idan kikaji sai kanki ya kwance , kafin albashi kuma ya bamu׳ , ya ƙara mana² , kullum cikin bamu yake , da marainiyar murya yace wai dandai muyi farin ciki , shi bai ɗauki duniyar a bakin komai ba dan ba itace gabanshi ba , tsaye yake ba dare ba rana , ya hana idonshi bacci zuciyarshi da kwalwarshi sunƙi samun natsuwa , bawai dan ya rasa yake nema ba. Ba kuma dan zai rasa yake tarawa ba , akwai su... Kullum zuwa suke da yawa..... An tarasu tun ba'asan amfanin kuɗi ba , tashi yayi ya ganshi cikin arziƙi tunda ya buɗe idonshi duniya kuɗi ya fara gani ba labarinsu yaji ba. Tunda Mai gidanmu ya girma suma kuɗin san ganinshi sukeyi , da kansu suke zuwa domin suma kansu sun san shine zai yaɗasu domin suje inda ba'a da labarinsu. Yana nema ne domin al 'umma kuma nemanshi yanayin shi ne domin ya gina rayuwar duk wanda yake da rabo a ciki. Akan Mai gida gaba ɗayanmu zamu iya sadaukar da rayuwarmu dan nema masa farin ciki. Ya ƙarasa maganar yana dukan ƙirjinshi bisa gaskiyar shi. Mu bazamu yadda ba , haka kuma bazamu lamunta ba , idan ke baki san darajarshi ba mu mun sani , idan bashi da amfani a wurinki mu yana dashi a wurinmu , idan kin gaji mu bamu gaji ba. Ya ƙarasa maganar suna maida Dikko saman gado. Duk ma wani mai cewa Mai gidanmu bashida mutunci ko ɗan duniya ne ko ya raina mutane koma dai miye mu yana da kyakkyawan hali a wurinmu. Mune muka sanshi muka zauna dashi muka kuma san ɗabi'unshi dan haka mune zamu faɗi ko waye shi...... Yayi maganar yana kaima bango naushi da hannunshi. {{ yadda yayi maganar hasashe na ya bani da Inna yake... }}
Duƙawa yayi tare da dafa gefen allon gaban Dikko yana ci gaba da cewa. Me kike so ? Idan soyayyar ce an baki , kuɗi ne damuwarki ? Suma an baki. Sultana me kike nema ne wai .....? Ko har yanzu kuɗirin fansa bai goge ba ? Rungume Dikko yayi ya ƙara yawan kukanshi yana cewa bawan Allah da wannan dalilin ya ƙwammaci ƙare rayuwarshi ba aure. Yana sanki amma yarinta da rashin tunani ya hana ki fahimta. Iya ruwa iya fidda kai......... Ko wae'...iya allonshi ya wanke. Gaki ga Mai gida tunani da samun mafita yana wurinki , dabara da sanin sirrin rami ya rage ga mai shiga rijiya. Daga haka bai sake magana ba ya riƙe hannun Dikko cikin soyayya yana mishi kallo mai nuni da tausayi , janshi aka suka bar ɗakin Ashiru yana ci gaba da kuka.
Kamar wata jaka haka nabi bayansu da kallo har suka gama fita daga cikin ɗakin. Goge hawayen daya taru a fuskata nayi. Na maida kallona inda Dikko yake kwance yana bacci. Tou ya haka ? Meya faru Dikko ya sake warwarewa ? Ko wayau yayi min daya bani labari cewa ya warke ? Ko yayi tunanin ni bazan iya ci gaba da zama dashi ba idan bai warke ba ? Labarin daya bani G R A a ɗakinshi ya tunomin da yacemin.....
_Naso naga Al ' Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba. Shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda suka binne tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lunfashi na ya dawo , tunda nake ban taɓajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin numfashi kiji wani masifa ? Hmmm Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba._
Dogon nazari nayi , na hasko duk maganganunshi na baya. Tabbas a maganar Dikko akwai lauje cikin naɗi. Wato ni zaima ƙarya ? Dani da ku masu karatu idan baku manta ba , ni yacemin wai yaje yayi jinya har na tsawon shekarun da nayi ina zaune a gidan Inna , ku kuma tuno. Tou ya akayi ya saki Jiddah bayan shi baisan inda kanshi yake ba tun daga ranar da ni nabar gidanshi naje gidan Inna ? Ya akayi takebinshi har Abuja ? Me yasa yayi min ƙarya cewa dawowarshi kenan yazo ya tafi dani a ranar daya aiko Abbakar ya kawomin waya ? Bayan tafiyar Abbakar kuma Ummar yazo da Umar ya tafi kuma shi Dikkon yazo da kanshi ! To me gaskiya ? Ni miye matsayi na a wurin shi ? Meya ɗaukeni ne ? Me yake nufi dani ? Tabbas duk yadda akayi maganar Inna itace gaskiya Dikko baya so na......... Mai gemun yaudara na faɗa cikin hayaniya ina cewa yau saina bar maka gidanka kaje ka samu daƙiƙiyar da zata zauna dakai , ka raina mutane ni nafi ƙarfin kai ka rainani...... Wai ni zaka faɗawa ka ɗaure kanka da wayar wuta ni zaka ba labarin "yan sfires {{ Express }}....? Fuuuu na fice daga ɗakin na koma ɗakina. Wayata kawai na ɗauka da makullin mota na fice.....
Da gudu na fito waje ina kuka har wurin mota ta , ina shiga mota Ashiru ya iso wurin yace ina zakije ne ? Cikin ɓacin rai na nunashi da makulli cewa zanje gidan Babana. Ai kasan nima Babana da Mamana suka haifeni ko ? Yadda iyayen Dikko sukeji dashi kuma suke ƙaunarshi nima Babana haka yake so na , yadda yakeji shima ɗa ne a gidansu nima ɗiyace na nuna kaina , yadda aka haifeshi nima haifata akayi ba ta sama na faɗo ba , har yanzu hannu na yana kan ƙirjina ina nuna kaina. Goge hawaye nayi da hannun haggu na ina ci gaba da cewa duka׳ kullum Dikko saiya dakeni doke²n shine soyayyar da kake iƙirarin yana nunamin wacce har kake min gori akan ta ? An baki soyayya da kuɗi. Cikin marainiyar murya nace shin baka tambayeni me nake nema ba ? Saki nake buƙata daga wurin Mai gidanku. Bana san ɗaya ko biyu a rubutoshi duka a aiko dashi a gidanmu na ƙarasa maganar ina karta makullin motar a jikin sitiyari , zana makullin nayi a goshina ina ci gaba da cewa Sultana bata ɗaukar fansa kuma ba ƙudirin wata fansa zamana da Dikko , kafin insan Dikko inayin rayuwa dan mun rabu yanzu kuma bazai sa in mutu ba , nayi maganar nima ina dukan sitiyari cikin ɓacin rai. Nuna Ashiru nayi da makulli sannan na cije leɓina na ƙasa na tashi mota ina kallonshi..... Riƙe murfin motar yayi yana cewa idan dai kinga kin fita a gidan nan sai idan bana numfashi.....
Ko kayi rayuwa ko ka mutu bai shafeni ba , nasan dai ni na gama magana kuma tunda na yanke hunkunci magana ya ƙare. Ba tare daya kalleni ba yace can baya na taɓa faɗa miki kiyi haƙuri idan baki manta ba , yauma shine nake daɗa baki Hajiya , bayanshi banda abinda zan iya baki a duniyar nan , tunda kike a duniya kin taɓajin wanda yace rashin haƙuri ya sa yacimma nasara ne ? Saidai kiji ance haƙurinta yasa ta cimma nasara , ba wanda zaiyi haƙuri yaji nadamar yinshi saidai nadama takan zo yayin daka gagara haƙuri.
Ban faɗa miki maganganun nan ba dan kiyi zuciya ba , raina ne yaimin babu daɗi. Baki gaji fushi da gudu daga gidan aure ba dan wani ƙalilin abu. Tarbiyya kika gada , Babanki idan yana nan bazai so yaga kinyi yaji ko kina cewa a sakeki ko faɗa da miji. Kuma da yana raye ko kin tafi zai dawo dake bayan yayi miki faɗa da ƙara nuna miki matsayi da kuma martabar miji , dika² ma miye abun fushi ? Ya tambayeni yana murmushin ƙarfin hali , yaci gaba da cewa ai anyi wanda yafi wannan kuma anyi haƙuri sai ɗan wannan Hajiya.....? Wanda bai dakeki ba bai zageki ba ? Ki ƙara haƙuri tunda an hau tudu ai gangarewar baya wahala , kalli ya nunomin hoton Papi a wayarshi , ji yanayin farin ciki kin ajiye ɗan digu²n Papi ina zakije ki barshi ne ? So kike yayi kukan rashin uwa bayan kina raye ? Rayuwar aure da kika ganta gaba ɗayanta haƙuri ne a cikinta , idan akayi haƙuri sai a samu mafita , kiyi haƙuri sai Allah ya baki ladar haƙurin , kibi mijin ki zauna lafiya kiyi masa biyayya saiki samu albarkar rayuwa. Ki nemi gafararsa sai ubangiji ya gafarta miki , fito ki koma dan Allah ki kwantar da hankalin mijinki kema sai naki hankalin ya kwanta. Ya ƙarasa maganar da yanayin tausayi..... Yana ci gaba da cewa ba'asan maci tuwo ba sai miya ya ƙare , masha ruwa magirbi karki biye fushin zuciya kiyi abinda zai jawo miki damuwa. Da yaji da tambayar sakin aure sai "yan gidan da basu da tarbiya , ke ko kina da tarbiya da ɗa'a kiyi haƙuri ki koma idan har kika tafi zaki naƙasa matsayinki da kuma mutuncinki. Kiba Mai gida haƙuri zai haƙura kuma bazaiyi fushi ba danshi mutum ne mai mantawa da damuwa , a inda akayi mishi yayi faɗa ya gama da wurin. Yana da zuciya amma yana da ba abun duniya baya..... Fita ki nuna masa ke ɗin "yar Babanki ce..... Ki basa haƙuri domin ya ƙara tabbatarwa keɗin mai tarbiyace , ki nemi gafararshi sai yayi alfahari da iyayenki domin sune suka koya miki tarbiyar bawa miji haƙuri.
Ko ba komai naji daɗi daya kira iyayena da masu tarbiya duk dai nasan za'ace niɗin eyar ɗan caca ne , ci gaba yayi da magiya yana bani haƙuri , kashe motar nayi tare da zare makullin na wuce banyi magana ba , ɗakina na koma na zauna gefen gado. Yayin da wani sashe na zuciyata yake cemin inyi haƙuri kamar yadda Ashiru yace , kuma in bawa Dikko haƙuri , ba ruwana da wani ciwonshi idan yayi aljannunshi idan ya gaji zai sauka , ya warke ko bai warke ba , ba damuwarki bane ba Sultana , abinda ya hanashi zuwa ya dawo dake tuni shima bai dameki ba , lokacin da ya saki Jiddah da binshi da takeyi dashi da ita da kowa ma can su ta matsemawa , kiyi tunani ki rufawa kanki asiri ki dawo daga rakiyar shaiɗan tun kafin duniya tai gwanjonki.
Tunda ta gama waya da Sultana take ta ɓaɓɓarka zagi , wayar Mai gilashi ta kira amma kafirawan company suka ce mata a kashe yake. Dan haka ta bugi mota tayi gidanta , ba yabo ba fallasa Mai gilashi ta tarbi Sharifa kuma bata , bata izinin shiga ɗaki ba. Haka kuma babu maraba bare kuma sannu da zuwa. Da yanayin tsinkuwa Sharifa tace Mai gilas an fa samu matsala , dakel ta kalli Sharifa tare da tambayarta meke faruwa ne ? Mu shiga daga ciki cewar ita Sharifa , Mai gilashi tace ba buƙatar sirri a ƙuryar ɗaki , magana dake a fili da ɓoye duk iri ɗaya ne. Da mutum yayi maganar sirri dake gara yaje B B C ya faɗa kila idan anci sa'a a ranar wani bai kamo tashar ba. Faɗi abinda ke tafe dake ko na iya baki shawara. Mai gilashi ni a gwadamin iskanci ne ? A , a , waye ya isa ya nunawa na rigingine hasken farin wata ? Cewar Mai gilashi. Sharifa tace to ni matar D ' K ta zaga , ta faɗamin magana , tayimin gori ta wulaƙantani ta muzantani ta tozartani sannan kuma ta tonamin asiri.......
Cikin ko in kula tace duk me yayi zafi haka ne ? Zama kusa da ita Sharifa tayi cewa kwana biyu kenan bama waya bama cht kuma bana ganinshi , Mai gilashi tace kila a tunaninta yana wurinki ne ko ? Cikin rashin fahimta Sharifa tace kamar ya ? Riƙe bakinta tayi da sauri tare da cewa rufama kanki asiri kar aji mutuwar sarki bakinki Ade.... Inji Mai gilas.
Sharifa tace kamar ya haka kuma ? Me zaki ɓoyemin ne bayan kinsan duk karatun iri ɗaya. Mai gilashi tace aini kin daina shawara dani faɗin gaskiya kuma zamanin nan yayi wuya , ina iya faɗa miki kije kiyi ta tallar terere dani , dan girman Allah Mai gilas faɗamin , Mai gilas tace gaskiya Sharifa ni inajin tsoro , dafa Mai gilashi Sharifa tayi tare da cewa idan dai baki faɗamin ba duk yadda tarenmu take tou lallai ƙullu yaci amanar koko , ɗan motsa kanta tayi alamar ta sanar da ita tare da cewa na baki dama kuma nayi miki alƙwari babu wanda zaiji ba wanda zai san anyi.
Mai gilashi tace:• shin bana faɗa miki kina da kishiyoyi ba ? Wanda suke ta harar Dikko a waje ba ? Sharifa tace kin faɗa , shin tunda kike ke Dikko ya taɓa² koda hannunki ne ? Ai bama ya kallo na , tou lallai cikin hijabi kike je mishi zance , Sharifa tace ey wallahi , kina zama kusa dashi ko a , a ? Shiru Sharifa tayi , Mai gilashi tace tou lallai nesa kukeyi da juna ta faɗa tana dariya tare da nuna Sharifa da ɗan yatsa , kallonta Sharifa tayi cewa ai babu ma ta yadda za'ayi ni na zauna kusa dashi , Mai gilashi tace da irin wannan baƙauyar soyayyar zaku cinma nasara har a kai ga matakin aure ? Miƙewa Mai gilashi tayi ta kalli Sharifa sosai sannan tace duk dabbar da tayi kuka tana da dalilin da yasa ta koka , yayin da wasu kan koka lokacin da suke buƙatar abinci , wasu kuma sukanyi kuka yayin da suka ƙoshi ne , kare yakanyi haushi yayin da rigimarshi ta motsa , duk wanda kika gani kwance kila yana rashin lafiya ne ko kuma yana da ƙatotuwar damuwa , haka take ga duk namiji daya tirki ƙarin aure.....
Dalili kuwa shine :• duk gero sunanshi gero. Yayin da aka sarrafashi zai tashi daga sunan gero ya koma wani suna na daban , misali , za'a sarrafashi zai zama fura , kunun kanwa , kunun tsamiya , wainar gero , tuwon gero , gumba , farin kunu , kunun zaƙi ke har danbun gero na gani kuma naci shi a bakina.... Amma duk miye silar zamar da duk wannan abubuwan dana lissafo ? Gero ne ! Shine duk aka sarrafa yayi duk abubuwan nan dana faɗa , tou haka take ga duk namijin daya baro gidanshi. Wasu mazajen zasu fito ne cikin soyayya da rashin jin daɗin sunyi nisa da ilayinsu , me yasa sukejin haka ? Kula , soyayya kissa kisisina kwarkwasa iya fira mai daɗi uwa uba kuma kindai gane ba........? Matansu zasu ɗauke musu tunani su kasance sunayin kewarsu da wa'ancan abubuwan dana lissafo har suje su dawo zuciyarsu da ƙwalwarsu baya barinsu su kalli wasu matan , ko kuma suyi tunanin kowa sai nasu , yana kasuwa ko office amma lissafinshi yana gida , burinshi ya tashi daga kasuwa ya koma dan kasancewa da shi wannan farin cikin dai. Dan haka zasu koma gida cikin farin ciki a taresu da soyayya kuma........ Kinga namiji ne ba , amma hikimar mace ta juyashi yasa ya zama wani daban..
Wasu mazan kuma zasu fito gidansu da ɓacin rai. Su fito kasuwa ko wata ma'aikata , idan ogane a wurin aikin abu ƙalilan zakayi ya ɗaga murya , ɓacin ran gida ya shafeka wanda kai bakaji baka kuma gani ba , idan ɗan sanda ko alƙali kila ma idan makuyi sa'a ba yace ku duk ɗin ayi gidan yari daku , tou a fara faɗo mishi karatun da shi kanshi baida lokacin da zai tsaya sauraronku ko yayi lokacin fitar da haƙƙin mai gaskiya dan haka zaice da mai ƙarar da wanda ake ƙarar duk a haɗaku a kaiku magarƙama. Shima mace ce ta juya mishi lissafi da kuma tunani , mazan haka suke sukan canja ne daga horon da matayensu suka basu , mai tunani ya zama lurasi , lusarin kuma ya zama jarumi. Ya danganta dai da horon da aka bashi daga gida , Sharifa anshe goruba a hannun kuturu ba abu mai wuya bane , tunda har ya ƙetaro iyakar matarshi ya fito sai ki bari matan waje su duma mishi wa² ? Shikenan ke kin haƙuri ? Ki bar musu ? Ke bakya da buƙata ? Sharifa tace ina da... Tou Yusra Jiddah da wata banzar yarinya dana manta sunanta duk kiyi ƙoƙari ki rabasu da Dikko , {{ banzar yarinya da ita Mai gilashi ke nufi itace Sharifa , }} taci gaba da cewa idan kin shirya kin kuma shirya ɗaukar huɗubata bisimillah , tashi sharifa tayi ta matsa kusa da Mai gilas kunneta ta kama tayi mata raɗa bayan sunyi alƙawari da kuma yarjejeniyar amana. Sharifa ta yadda ta kuma ansa , ta yadda da huɗubar *MAI GLASS...* abinda ta faɗa mata zamuji shi idan taje wurin Dikko ne. Dariya Mai gilashi tayi tana kallon Sharifa aka wani tafa , Mai gilas tace haka suke ai mazan iri ɗaya ne , kije ki jaraba. Wannan farashin da zakiyi tukuici sai buƙata ya biya.....
Bugu:• bugun bala'e sukayi ma Amisty bayan sunyi nasarar cafke banza. Kuma dukan bawai irin na yara ba ko na susar jiki ba. Basu bigeta da wasa ba duka na tashin hankali sukayi mata , dukan da idan dai akayi ma mutum irinshi to sai mutuwa. Tafiya babu dawowa. Tunda sukaji zancen kuɗi sukaje wurin suka kafa tarko , duk wani da zai shiga ko fita a gaban idonsu. In banda wawanci da rashin lissafi kuɗin nan wai suna cikin motar Amisty idan taje wai inda zataje sai ta canja da kuɗin ƙasar tayi hidimominta. Haka sukayi mata duka kamar wanda ya tun kari fadar shugaban ƙasa rungume da bindiga.... Ita kuma bayan ta tabbatar kowa yaje ya kwanta ta sulale dan ta gudu saboda bata yadda kowa ya kwana ɗaki ɗaya da wani ba. Ƙarya tayi musu wai zatayi baƙo shine taga dare yayi zata wani ɓace abunta. Tafa ci ƙaniyarta yadda tunani baya zato. Suka ɗauke motar da kuɗin suka barta nan zube kamar asarar tsakar dare.
Har gari ya waye ban samu nayi wani baccin kirki ba , haka kuma na kasa zuwa ɗakinshi , tsoro da fargaba kawai ke damu na , sai zantukan Ashiru dake tayimin luguden san zaman lafiya a zuciyata. Wannan dalili shine ya hanani san zuwa makaranta naji ni kamar wata mara lafiya. Ganin har 1 saura yasa na tafi ɗakinshi a tsorace , da sallama na shiga yana fitowa daga toilet ran nan nashi a haƙe fuskar nan tayi kalar ban tsoro dasa mutum ya shiga cikin yanayin firgicewa , ɗan rakuɓewa nayi cikin rawar murya nace barka da safiya , baimin magana ba bai kuma kalleni ba ya ɗauki wayoyinshi ya nufoni dan fita daga ɗakin..... Cike da tsoro na sake cewa Dikko ina kwana , ke........ Ya faɗa tare da yankamin wani irin firgitaccen mari saida na juya naje jikin bango dakel na haɗiye yawu lokaci guda zufa ya tsatstsafomin a fuska cikina ya juya yayi wani irin zakuɗa a tsorace na kalleshi , da ɓacin rai ya tambayeni wannan marin meya bayyana miki......?
Cikin kuka da marainiyar murya nace har yanzu jikinka da ƙwari , yace to ina nan a yadda nake , ban sauya ba ban kuma tashi a yadda kika sanni ba , dama idan baki manta ba na faɗa miki. Tou yauma na sake maimaitawa idan zaki kiyayi fushina tou ki kiyaye sai ki zauna lafiya , na warke ko ban samu sauƙi ba wannan bai shafeki ba saboda daga matar gida baki kau ba , ya nuna da hannunshi. Rayuwa da ƙaddara abokan juna ne , komai yana da ranar tashi daga aiki kama daga kifin gwangwani har zuwa mu "yan adam , kin gane ba ? Jeki........ Ya nunamin , tafi ya nunamin hanyar fita , ƙara yawan kukana nayi na taho daga inda nake na shige jikinshi ina cewa na bari Dikko na faɗa maganar ina ɗagowa dan kallon idonshi , sassauta murya yayi yana cewa bakijin magana , iskancin ki kullum gaba yakeyi , wai nine kike faɗa zaki zane ? Haba An mata....? Kayi haƙuri bazan ƙara ba , tou me nayi miki kika ɗaureni bayan ni ba mahaukaci ba. Ko abokin wasanki ne ni ? Ya tambayeni yana ɗagoni daga jikinshi , saida nayi shashshekar kuka nace bana so kana yawon dare ne , sai kuma ki ɗaureni ? Wannan wane irin hukuncin hauka ne ? Ai bana so kana fita na ƙarasa maganar ina komawa jikinshi. Murmushi yayi kaɗan a sakace yace An mata......... Ya ƙarasa maganar yana rumgumeni sosai. Cikin dariya yace wai wane mai bahaggon tunanin ne ya baki wannan shawarar ne ? Ɗagoni yayi kowa yana kallon idon kowa yace sai kawai tace miki idan kika ɗaureni zan daina fita ne ehem. Yayi maganar yana shan idanuwanshi. Suna shanyewa a hankali tare da murza su da salon duniyanci. A kasalance na koma na sake kwanciya , dariya yayi da murya mai kama zuciya ya ɗaukeni yaje ya kwantar dani saman gado , saida ya lulluɓeni ya sumbaceni yace jirani ina dawowa yanxu. Yayi maganar yana fita daga ɗakin........
Bayan sati 1.
Mijin Halimatu dai har yanzu baida lafiya. Jinya har ta kaisu asibiti zugar ƙawayenta kuma babu wanda ya bita sai Hadiza. Da ita ake yini akeyin komai sai dare suke dawowa gida ƙannen shi Abdul in maza suke kwana dashi. Da Halimatu ta tambayi sauran ƙawayenta me yasa basa zuwa cewa sukayi mazajensu basu yadda ba.....
Har sati ya cinye Yazeed bai zo ba kuma bayayin waya da Jiddah. Shiru kuma har yanzu baiyi maganar turo magabatanshi ba tunda ya tafi waccan ranar sai yau yazo , duk an ɗaɗɗaure mishi jiki da tsumma an sagale hannunshi da igiya an sargafa igiyar a wuyanshi , wai Jiddah ta bashi mamaki shine dan ta tura mishi wata banzar 5million zata turo mishi ɓarayi suzo su kashe shi su ansar mata kuɗinta. Ai ba dole² yasa ta bashi ba , basai ta turo a kasheshi ba , tou ya basu kuɗin ta daina kiranshi kar yayi mata rashin mutunci , shi da ta ganshi duk cikar garin katsina babu ɗan iska kamarshi. Kuka Jidda ta farayi ita wallahi bata tura kowa ba , Yazeed yace ƙarya zaiyi mata ne ? Bafa a wata banzar miliyan biyar inta ya fara riƙe kuɗi ba. Me yasa a lokacin can da bai santa ba ba'aje an dakeshi ba ? Sai akan ita data bashi ne ? Tou ya fasa auren taje tayi da wani.
Jiddah ta fara wallahi². Yazeed yace shi tama wani daina mishi kukan makirci yasan sharri irin na mata , haka taita bawa Yazeed haƙuri dakel ta shawo kanshi a yadda ya nuna kenan , saida ya sake buɗe fili akayi danbe Jiddah ta tura mishi miliyan biyu tace ta ba malamin ta anayin aiki , dakel Yazeed ya yadda ya anshi biyu , kuma ya tabbatar mata da kuɗin danbe ne ta biya , shi baya wani ra'ayi yana mata yayyafi ne dai dan ta rayu karta mutu. Tayi ma Dikko waya ya ƙaro wasu kuɗin......
Dady kuwa ya bugu iya bugu a yadda yayi fentin gida da sabbin filawowi , Umar ɗan iska ne kuma baƙin mugu , da Dady yasa aka sauke fentina yace ya bada kuɗin ma'aikata zaiji da komai , ya anshi kuɗi masu yawan gaske a wurin Dady hada na toshiyar baki , Umar kuwa wajen gida kawai yasa aka gyara sauran fenti yaci kasuwa...
Duk satin nan Mai madubi bataje makaranta ba , naso zuwa gidanta Mai gida D ' K ya hanani , makaranta ma shine yake kaini yake kuma ɗaukoni , ga wayar ta idan an kira ba'a samu , sai na haƙura kawai.
Har yanzu Dikko bai cire wayarshi a jirgi ba , kuma satin nan ya bigeshi bai fita , ko gidansu rabon da yaje tun ranar daya kwantar dani a gado yaje. Kuma ya taho da Papi saboda Nabeela ta tare gidanta. Banje ba , abinda yasa kuma saboda ciki shi yasa ya hanani zuwa.
Sharifa da Aunty Bilki ganin ana neman a buga musu game over yasa ta samu Dady akan yayi ma Dikko magana yaje wurin Sharifa , ya kama waya ya rufe sati 1 kenan da kusan kwana 2 basa waya kuma basa haɗuwa. Tadaiyi "yar barikinta a gaban mijinta irin tamu ta mata , Dady kuma ya kira Dikko yace duk abinda yake yau yaje ya haɗu da Sharifa. Shi Dady gani yakeyi ita Aunty Bilki tafi Momy mutunci tunda tana san "yan uwanshi har take tunatar dashi akansu.
Wani irin ihu Dady yayi tare da zubewa ƙasa somamme. Yayyen Hafsa suka rufa mata da duka wanda sune sukayi tsaye wurin nemota. Can abuja suka kamo "yar iska a wata asibiti wai tana jinyar Amisty tana so ta dawo taji ina kuɗi suke ? Shine suka tattaro su dukansu da Amisty da ita Hafsa..... Shine fa kawai ya wani some dan Hafsaf fa kawai ta tabbatar mishi da ɓarayi sun kwashe kuɗi , daga an faɗa mishi shine kawai zai wani zama mataccen bakin maƙabarta.........????
0 comments:
Post a Comment