Saida sukayi mata lullusar fitar hayyaci sannan suka shafawa Dady ruwa ya dawo. Kamar ƙaramin yaro haka ya riƙa gumza , muuuuu , tutu² sai kace sabuwar mota ta haɗu da tsohon inji. Dady kayi haƙuri ka daina kuka , saida ya gama kallonsu sannan ya kalli Hafsa yace shin an kamo ɓarayin ne ? Suka ce a , a , luuuu Dady ya sake komawa suma. Haka sukayi ta dawo dashi daya dawo sai yace an kamosu ne ? Amma da ance masa a , a , sai ya sake somewa. A na ƙarshen ne ya wani babbanƙare ya riƙe yaƙi lanƙwasuwa baya gaba kuma yaƙi yayi baya kamar aljannun mata sun taso. Bayan ya tabbatar musu da cewa kada wanda ya sake dawo dashi idan har ba'a kamo ɓarayin nan ba. Babban ɗanshi yace Dady idan ba'a gansu ba fa ? A hankali ya maida kanshi ƙasa ya lumshe idanuwanshi cikin tashin hankali sannan yace ku barni kawai in mutu.....
Cike da farin ciki Yazeed ya isa majalisarsu. A mota ya warware tsumman daya ɗaɗɗaure jikinshi yana dariyar ƙeta. Lallai Jiddah muguwar daƙiƙiya ce. Wato ita har ga Allah ma ta yadda anje anyi mishi dukan ? Ballagar mace uwarki tayi asarar aihuwa. Fita yayi daga cikin motar haka ya shiga cikin da'irar abokansu yaci gaba da fallasa Jiddah , wai wasu zawarun ballagazu ne. A kyauta yake shan iska babu wani damuwa. itama kanta a kame take kamar barden goyon daya yini baisha nono ba , da yaji gari yayi mishi zafi can yake tafiya yawon honey time. A can dai yake zubda ƙura ya dawo gida , ga kuma kuɗi kwance a account , ya nuna kwanciya da hannun shi yana ci gaba da cewa lallai Yazeedu babbar ƙaddarar mata ne ni. Ɗan yatsina fuska yayi sannan yaci gaba da cewa bafa laifi tana barbaɗa wuta a filin wasa D ' K ya kowa mata doguwar tafiya. D ' K...? Hmmm Dikko duniya sai Allah , ya faɗa yana riƙe haɓarshi da yanayin mamaki ya ƙurawa wuri ɗaya ido alamar tunani.
Tambayarshi akayi ina ya samo zawara a arha haka ? Dariya yayi sosai tare da jinjina kanshi yace matar D ' K da suka rabu. Cikin dariya yaci gaba da cewa wai dan uwar biko shi D ' Kn yake bikonta dan ta ɗauki kanta alalan gero. Hmmm lallai iska tana wahalar da mai kayan kara , idan dai D ' K ne cikin ruwan sanyi zai kasheta bata san iskancinshi ba aradu labarinshi takeji. Tou kai meya haɗa ka da ita ne ? Waye ma ya sanar ma angulu a masai...... Ya ƙarasa yana ƙara gaggaɓewa da dariyar fita addini.
Bayan wani lokaci ya nuna kanshi yace wai ni ? Nine zan aureta , in banda haukar mata da rashin tunani ni ? Wai ni Yazeedu nine zan aureta ? Gaskiya bata da lissafin rayuwa. In banda abunta bata duba can²nta ne ? Idan na aureta uwar me zan bata ? Filawa ai tafi kyau da gidan masu kuɗi , shanyar dusa kuma da kauɗar bushashen tuwo wannan kuma ai sai gidan talaka. Zanyi ta zuwa dai ina karantawa inyi gaba , wata irin azzalimar dariya ya sakeyi yana cewa bata san itama ta gidan neman hanyar tsira takeyi amma bata samu sa'a ba , hahahahaha kai yarinya bakiyi ma cikinki da gangar jikinki adalci ba , zo zo² zoki mana idan dai nine ni naci uwar ɗan tasha , dan bana tunanin duk cikar faɗin birnin jahar katsina kawai irina , banda mutunci kuma na tabbatar da cewa tantiri iri na a duk faɗin yankin katsina bafa za'a taɓa samu ba. Dan babu tantirin ɗan iska kamata , idan dai kinajin wasa ki tambayi Dikko ya baki labarina.
Fat , Fat , ² haka lumfashin Amisty ke halbawa tsakanin rayuwa da mutuwa. Yau duk abokan tashar nata babu wanda yake ɗakin da sunan jinyarta. Uwa ko uba nata kuma ? Basu da labarin halin da take ciki. Tunda ko tana da lafiyarta basa ganinta basa kuma jin labarinta , a gari ɗaya ake amma kowa yana nashi matsugunin. Wani bushashen ɗan sanda aka aje wanda koke mace idan baki da yunwa kina iya bashi kashin bala'e. Wai shine aka ajiye dan ya kula da Amisty. Idan ta dawo hayyacin ta , ta nemo musu inda takai musu kuɗin Baba. Likita ne ya shigo tare da malaman jinya bayan yayi ɗan abinda zaiyi aka taimaka ma tafiyar numfashin nata da iskar bature. {{ Oxygen }}.
Kallon agogon dake ɗaure jikin tsintsiyar hannuna nayi sannan na kalli inda yake tsaye jikin madubi yana murza hula , ta cikin madubin ya kalleni so ɗaya sannan yaci gaba da abinda ya shafeshi. Bakin ƙofa na koma na tsaya ina cewa gaskiya ba inda zakaje na ƙarasa maganar kamar zanyi kuka. Juyowa yayi tare da jingina da jikin madubi ya dafa hannunshi ta baya cewa. Nace miki bazan daɗe ba , tou kuma tunda kasan baka daɗewa ai ba buƙatar fitar ko...? A hankali ya fara tahowa yana cewa tou ki hanani fita da ƙafafuwa na in gani mana. Kwanciya nayi ƙasa a bakin ƙofa kaina na kallon sama na miƙe ƙafafuwana da hannuwana nayi irin kwanciyar gawa. Cikin kuka nace shikenan ka tsallake kabarina Dikko ka wuce. Da sauri ya maida ƙafarshi baya daya ɗago da niyar tsalleki ne ya wuce. Cike da shagwaɓaɓɓiyar muryarshi yace haba An mata wai miye kike haka dan Allah ? Ban tashi ba kuma ban daina kallonshi ba nace ba kace sai ka fita ba ? Kai da ƙafafuwan ka ? Tou gani nan kwance ka tsalle gawata kawai kaje abunka na ƙarasa maganar ina zarge hannayena a ƙirjina na rufe idanuwana. {{ hmm taf aradu idan wani namijin ne ba kabarinki ba ko makomarki ya gani sai yayi abinda yasa kanshi can ke ta matse mawa . }}
Cire cingom in bakinshi yayi yana wasa dashi a hannun shi , bayan wani lokaci kuma yayi ɗan latse² a waya ya kara a kunnenshi. Saida na cikin wayar yayi magana Dikko yace Abbakar kuje , ya ƙarasa maganar yana ɗan shan idanuwan shi da suka canja launi. Ey ya faɗa yana komawa ciki. A , a kawai dai na fasa fita ne , kaina yanamin ciwo ya faɗa a dai² lokacin da yake zama gefen gado yana nuna kan nashi da yanayin damuwa. Ey , yayi bacci tun ɗazu. Babu damuwa saida safe. Ya faɗa yana ajiye wayar , ɗayan wayarshi ya ɗauka ya cireta a jirgi , data ya buɗe tare da antaya duniyar yanar gizo.
Saida saƙonni suka fara shigowa ya ajiye wayar ya tashi yana rage kayan jikinshi. Tasowa nayi daga inda nake kwance na matsa inda yake nace yi haƙuri. Ba tare daya kalleni ba yace kawai ya wuce yayi maganar yana komawa inda ya ajiye wayoyinshi ya ɗauka ya koma palo , ƙasa² nayi dariya bayan ya fita a zuciyata nace shegiya ni , na ƙarasa maganar ina kwanciya a gado na ɗauki wayata na fara kiran Hajiya Mai gilashi. Wayarta a kashe har yanzu lallai duk yadda za,ayi in Allah ya yadda sai naje gidanta idan Allah ya kaimu. Allah dai yasa ya barni inje , wani sashi na zuciyata yace kawai cewa zakiyi ya kaiki , wannan shine gaskiyar magana , saukowa nayi daga saman gadon na fita palo inda yake.
Ya toshe ɗayan kunnenshi da abun sauraron magana , ya ƙurawa waya ido yana murmushi. Duk maganar da nayi kwata² ma bayajina sam² , zagawa nayi ta baya da niyar in ɗan riƙeshin nan irin idan mata suka tashi labbatar namiji idan suna san wani abu daga gareshi. Amma kafin in riƙeshi sai me...? Wani irin ruɗaɗɗen ihu nayi tare da faɗar da wayar daga hannunshi. A firgice ya juyo ya kalleni sannan ya tashi da sauri zai ɗauki wayarshi a lokacin har na zagoyo na rigashi ɗauka , bani wayata yayi maganar ranshi a matuƙar ɓace , kyarma jikina ya farayi saboda na tsorata da irin kallon da yakemin. Dakewa nayi tare da cewa idan fa naƙi bayarwa ? Sai in kashe ki............ Ya faɗa yana nuna shaƙewa da hannunshi saman wuyanshi , cike da tsantsar ɓacin rai nace ai yau nice zan kashe ka. Nayi maganar idona yana kallon ƙasa. Wani irin wulaƙantaccen kallo yayi min tare da nuna kanshi nine zaki kashen ? Kafin inyi magana Papy ya shigo yana kuka , ihun da nayi ne ya tasoshi daga koma ina yake yana bacci , cike da ɓacin rai Dikko ya jinjina kanshi ya matsa yaja hannunshi suka fita.
Wuri na samu na zauna na shiga binciken waya. A raina kuma addu'a nakeyi Allah yasa Papy yaita kuka ya hanashi dawowa da wuri , dan abinda na fahimta baya so yanayin wani abu wanda bai kamata ba idan ɗan shi yana gidan. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , wata irin yamutsa kaina yayi da sauri na rufe idanuwana dan irin ƙazantar dana gani , tunda nake da Dikko duniya bai taɓa abinda naji na tsaneshi ba sai yau , wayyo Allahna ? Mayun mata wai ina ruwanku da mijina ne ? Kunzo kun daddaɓeshi sai kace ƙuda ya samu ruɓaɓɓen nama. Ga kira waya sai shigowa yake ba ƙaƙƙautawa , saƙonni sai kokawa sukeyi wurin shigowa , jikina na kyarma idona cike da hawaye na fara neman number Sharifa , dakel na gano ta ɗan iska wai "yar uwarshi ya rubuta a jikin numberta , kam bala'e wai duk ina , ina wannan iskanci ya faru ? Da wata ɓeranyar yarinya shegiya zata girmeni baifi da shekaru biyu zuwa 3 ba , ta ciko mishi saƙon nata itama da ɗanyayen kalamai daɗaɗa , sanyaya , Sharifa kuma ta rubuto mishi cewa ni na kirata na zageta , nayi mata gori wai ni injini ni Sultana wai nice nace wa Sharifa ita karuwan Dikkon ne , a taƙaice dai ita Yusra kaf a cikin kwaratan itace ta saman iska , kaf babu feƙaƙen ɗan tasha na sama a wayar nan sama da ita , guguwar "yar iska ce , dan kalamanta data faɗa tana tattaɓa wasu sansa na jikinta nida kunya ta haifa na rantse da girman Allah ba a baki ba a rubuce duniya ni bana iya rubutawa bare kuma azo fagen in furta. Karuwai.....?׳ hmmm karuwai na sha'aninsu idan suka samu mazajen ballagazanzun mata , a hayaƙe ya dawo saida ya wanwanka min mari ya anshi wayarshi. Cike da rashin tsoro nace kadaiji kunya kuma kayi asara daka kallar da idonka tsiranci haram , naji kunyar kuma naje na kalla haram ɗin naki ne ko nata ? Banyi magana ba na nufi hanyar fita , har na fita zuciyata ta hayaƙoni na dawo ,
Nima dai a daren nan nayi ɗan ƙaramin hauka , haka na rufe idona naci gaba da zage² ba shi nake zagi ba su Yusra nake ta ɓaɓɓarkawa zagi , keda ke gidanki idan kinsan halin da nake ciki Dikko yasan ina nan ko yanajin abinda nake cewa ya basar dani yaci gaba da cht inshi hankalinshi kwance , inda yake saman kujera naje na kamo ƙafarshi na jawo da ƙarfi ina cewa saina faɗar dakai na ƙarya maka kashin baya , da ɗayar ƙafarshi yayi min wani irin kyakkyawan harbi a fuska saida hancina ya fashe. Shi kuma yaci gaba da latse² a wayarshi da yanayin shauƙi , baya nayi inajin juwa ɗakin na gani yana juyamin duniyar tayi shiru banajin motsin komai watan saurarena ya ɗan ɗauke shima numfashin an riƙeshi. Ina dawowa jin sauti na sake tafiya inda yake ina faɗar saina kashe ka , janye wayarshi yayi daga fuskarshi yana kallona da wani irin jarabben kallo , a kasalance yace wai nine zaki kashe....? Ya nuna kanshi , ey , An mata dukana ? Ey , har wannan shima zaki ? Ya nuna daddatsewa da hannunshi , gemunshi kenan , dai² lokacin dana iso kusa dashi , riƙeni yayi da yanayin mayata yace muje saman gado mu kashe kanmu nima saina kashe ki...... Ni ka sakeni , anƙi a sakekin ya ƙarasa maganar yana rufe ƙofofin hancina da "yan yatsunshi biyu , da hayaniya nace wai ba nace ka ƙyaleni ba ne iye ? Shima da irin magana na yace wai bana ce bazan ƙyale ba iye ? Ya faɗa a gajiye yana sauke numfashin jaraba yana min wani irin kallo.
Kwacewa nayi , ya riƙoni da sauri yace ai ƙarya kikeyi yarinya , ina ne zakije ? Sai kin kashe ni..... Ya ƙarasa yana lumshe idanuwanshi tare fitar da numfashi cike da kissa , ƙiƙi² muka fara rigel². Ni ina so in ƙwace , shi kuma yana so ya riƙoni har ya sauko daga saman kujerar , saina tafi , bana sanka׳ na ƙarasa ina ƙara yawan kukana. Ai basai kinsha wahalar faɗa ba nasan wannan shekaru 3 zuwa huɗu da suka wuce. Jana ya farayi hanyar bedroom wai muje in kasheshi. Da Allah ka ƙyaleni kaji , ah ni bazan ƙyaleki ba aradu sai kin kasheni yayi maganar yana murmushi tare da kafe ni da mayataccen kallonshi.
Nanfa abun yaci tura naci gaba da ɓarin maganganu , tun yana kallona har ya fara rufe ido ya sake hannuna. Nan gori ya tashi tunda na lura yana da buƙatuwa dani , haka na warware kamar farfera na ci gaba da zazzaga ranshi mutunci ni matar da za'a sauke buƙata a kaina , ƙarshen film in nace tafiya zanyi , cike da ɓacin rai yace ina ne zaki iya zuwa ? Bayan baki da gidan da yafi wannan ya nuna ƙasa da ɗan yatsanshi na hannu dama , yana ci gaba da cewa kije mana ? Idan kin tafi zan mutu ne ? Ya nuna kanshi cikin tsatsanin fushi mai sa kaji cikinka ya juya na kasa kallonshi , dan kinga ina lallaɓaki ? Idan kinyi haƙuri baki je ba kin zama banza , ki tafi ya nuna hanyar fita , rage murya yayi da cewa ina da dubunki a waje sai me ? Ko an faɗa miki wai bana iya rabuwa dake ne ? Kullum² zakije sai na tafi gidanmu kaza² tou kije ko wani ne ya baki haƙuri ? Hmmm ke baki san iskanci na ba , nafi ki ƙaryar rashin kunya wallahi , inda duk kike zato na tuni na wuce wuri nayi gaba.... Idan kina nan wata zan kawo idan ma kin tafi haka dai zan sake kawo wata.
Kina iskanci ana baki haƙuri tou an daina cewa kiyi haƙuri ki tafi duk gidan da zakije , ba burin daya fi duk macen da bata da lissafi tanayin faɗa da miji tace gidanmu zanje , fuuuu tayi yaji ya nuna da hannu , tou idan baki sani ba babu babban kuskure da yafi wannan jakancin , ko shi mijin dake aurenki bai san kuna da gida ba ? Ai yasan ba a sama kika faɗo ba , ya nuna yana ci gaba da cewa ai ina ganin idan yaso zaice kije gidanku. Mahaukaciya ma dake da Allah , fitarmin daga ɗaki yanayin fushi ya fara hawa kaina kafin inji miki ciwo , kuma na rantse da girman Allah idan kika fita gidan nan ko ina kikaje har can zan biki saina lalata miki fata , kaca² zan miki. Fita nace........................ Ya faɗa yana nuna hanyar fita tare da rufe idanuwanshi cike rashin mutunci. Fashewa nayi da kuka nace yi haƙuri don Allah , zo nan , ya kirani da hannunshi , tafiya nayi ina kuka ina kallonshi. Riƙeni yayi a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya bakiji An mata , wai ni miye matsalar ne ? Kullum sai kin ɓatamin rai wai me nayi ne ? Haba An matana ya ƙarasa mganar yanamin kyakkyawan riƙo , cikin shashshekar kuka nace kaine , nine kuma ? Tou wai meye nayi da zafi haka ? Ka daina so na ai , haba Yarinya ke ko wani ne ya faɗa miki ai zaki ce a , a , duk duniyar nan wai waye yake dani idan bake ba ? Haba ƙaramar yarinya.... Duk kin burkeni na zama wani lusari sai anfani kike da soyayarki kina murzamin zuciya san ranki ya ƙarasa yana min kyakkyawan murmushi , shiru nayi ban mishi magana ba , kefa yarinya ce ? Kalli Dikko fa ? Akwai tazarar tsayi shekaru da kuma tunani , cikin dariya yace wallahi kin maidani kamar wani zararre ke ko tsoron Allah ma bakyaji ? Haba An mata , ɗagoni yayi daga jikinshi yace ai nasan ma kin yafemin ko ? Ey tou zo muje. Yana riƙe dani har toilet da kanshi ya wankemin fuska yana cewa dan Allah An mata ki daina ɓatamin rai gaskiya banajin daɗin abinda kikemin.
Wai ke baki san ba'a ɗagawa miji harshe ba ? Baki san idan mijin yanayin zuciya yadda ake saukeshi ba ? Ba'a hawo namiji yayin da yakejin tuƙuikin ɓacin rai , komai yana iya faru a dai² lokacin da yakeyin fushi , Juyowa nayi na riƙeshi ina ci gaba da kuka , a wahalce yayi gajeriyar dariya cewa ai nasan baki iya tafiya ki barni wasa kike , ƙaramar yarinya. Wai miye ke damun kanki ne ? Meye nake miki wanda baya miki daɗi....? Ni kifaɗamin , faɗamin matsalata dake sai nima in faɗa miki matsalolinki kowa ya daina ɓatawa kowa sai a daina faɗan tunda kin gaji. Kinga ko a rigima kin fahimci ni nafi sangarta bana gajiya haka zakiyi ta hawoni ina baki kashi kullum kina fama da jinyar fata , kuma kinsan banayi zuciya in zaneki kuma in maƙalƙaleki anjima inyi ta warwarewa ya riƙeni yana nuna yadda yakeyi idan yana kwance dani , dariya nayi ina kallonshi. Shima dariyar yayi tare da ɗagamin gira yace wallahi kuwa , tou ni ina ruwana ? Gani ga "yar yarinta ina fa morewa , niɗin mai sa'ar rayuwa ne , duk da dai kince wai niɗin tsoho ne , amma a haka dai ai ina bada wuta a tsakiyar filin wasa ko ? Ya ƙarasa maganar yana ɗan taɓe bakishi tare dayin wasa da girarshi.
Murmushi nayi ba magana amma har yanzu ina kwance a jikinshi , ɗan wayancewa yayi dai yaci gaba da yabona wanda nidai nasan a zuciyarshi ba haka bane ba , yana dai yabo na ne dan inyi farin ciki ya kuma sauke buƙatuwarshi yayi bacci da natsuwa. Koma dai bada gaske yakeyi ba ni naji daɗi , yana da kyau maza su riƙa farfaɗawa matayensu kalaman da zasuyi farin ciki su girmama musu kansu sai suji su suma ashe dai wasu manyan shegu ne , ta hakan ne zaka riƙa zaliƙo mata matsalolinta a hankali idan mai hikima ce saita riƙa gyarawa , irin dai kana yabonta kana cewa ai idan kikayi kaza kinga yadda kike bada haske ? Ko kike ruɗani ? Ko bana tare dake sai inyi ta tunaninki , kaza². Nan zaka ga ta warware tace you ai kaza da kaza ma da nakeyi kaza. Ni nayi farin ciki da yacemin duk nafi su Yusra kyau , gani "yar gayu kuma ni "yar yarinya su duk sun tsufa ma , ai haɗuwa ta ta wuce duk inda bana zato , shi a ganinshi ma yafi ko wane namiji sa'ar aure , bayan ni nasan Dikko ƙarya yakeyi , kuma wai da nace masa ba wani cewa yayi in kalli kaina a madubi fa , An mata kalli idanuwanki , ji lallausar bakinki ya nunamin saman lips ina , kalli nan ji can uwa uba kuma saikin dafe uztaz D ' K a gado. Kalamanki suna da daɗin sauraro bayan ni nasan duk lokacin da zai kwanta dani sai ankai ruwa rana , yanzu nan ya gama min faɗa ina ɗaga mishi murya , amma da yayi dai nayi farin ciki ,
Wai ni ina da kyakkyawar fata idan kuma nayi mata ado da lalle zan ƙara haɗuwa wai kuma lallen na hausa amma a zuba turare a cikin lalle dan ya kashe ƙaurin lallen , warware kaina yayi yana shafa gashin kaina wai na iya gyaran gashi ya mishi kyau a haka. Shiko banyi kitso ba yafi ibar mishi lissafi , haka na saki baki naita dariya kamar sakara ina cewa ai idanma nayi kitson warwarewa yakeyi , ey ai dama nima bansan kitso , saidai ina san wannan kitson kin tunashi ? Wani mai kyau ? Kai yayi miki kyau An mata , nifa nasan bana kitso harma gara kalaba , amma da nace masa ni banyi kitson nan ba , cewa yayi na manta yana ta nunamin yadda kitson yake. Yadda yake nunamin irinshi ni nasan ban taɓayin irinshi ba a tarihin rayuwata. Amma Dikko ya kafe kai wai nayi shi in tuno mana , saida na natsu sosai na gane irin kitson dake kan Yusra ne , dakel dai nayi yaƙe mai ciwo , shima zanen lallen a wurinta ya gani ai na gani itama lallen hausa ne akayi mata wani irin ado mai ɗaukar hankali.
Wato duk duniya ita mace baka da abinda takeso sama da a yaba mata , suma mazan haka suke , haka kuke mana "yan rainin hankali , kuma so kuke a yaba ku kan nan naku yana muku wani girma kunajin ku wasu manyan "yan duniya , kuna wani ciccika fuska ku masu gida ana zugaku kuna wani karkace baki kuna dariyar ƙasaita kan׳ dariyar cikin izza da nuna isa. Yana da kyau mazaje ku riƙa gyarawa matayenku da irin yajuju wama jujun da ku kuke gani a waje. Kuma a hikimance , ba zagi ba duka ba gori wance ta fiki ko wane matar shi kaza² a , a , ba haka akeyi ba a hankali zakayi mata dan kune kaɗai kuka san a inda kuke shiga kuna gano irin wannan duniyanci. Bawai nace kuɗin "yan duniya ne , ina nufin irin matan da kuke huɗɗoɗi dasu. Ba kuma ina nufin tasha ko sakarci ba , kamar a kasuwa ko a ofisoshinku da dai sauran wuraren da kuke mu'amula dasu , tunda suna ɗauko wanka da gayu kamar zasu tashi duniya dan haɗuwa , su barbaɗo muku turare a ciko ido da kwalli ana firfira muku idanuwa. Ku saki baki ba aji kuyita gaggaɓa dariya irin wacce ko matanku bakuyi ma irinta. Tou karta burgeka kuma karta ruɗa maka lissafi da tunani , ka riƙe karka bari tayi wasa da tunaninka nata ƙarya ne zahirin tana gida , idan tayi nata sai yafi baka sha'awa akan na sharar bakin titi , wai su kun gane matsalarsu.....? Matsallar auren su ba a gabansu yake ba. Haka zasu shaƙe miki wuyan miji suyi ta ranfa dashi , idan kuma ta gaji da cin aljihunshi taci shi har babunshi saita tura wata itama taci gaba da gayar miki miji babu tausayi , itama idan ta gaji tayi gwanjonshi shi kuma zuwa wannan lokacin ya zama ɗan gari. Ma'ana ya gane hanyar yadda take , kafin ki ankara an firgita miki miji , wata macen ma su biyu ne a wurin miji amma dai lusaranci da hauka yasa sunyi sake sun barwa karnukan bisa titi suna ta mishi haushi , baki jin haushin ta waje wai ta gidan itace ta tsone miki idon tsabar hassada , kullum kika tashi da ita a zuciyarki baki da buri da kwanciyar hankali yadda zakiyi waje da ita , tou idan ta tafi ance miki shikenan bazai sake aurar wata ba ? Ba matan gida ya kamata kuyi hassada dasu ba yaƙi zakuyi da matayen dake matse mazanku a waje , ku kuma maza gaskiya kuma kuji tsoron ku tausayawa matayenku , ku kyautata musu , kuyi musu magana da sanyi² ku lallaɓa su , ku tarairayesu , ku ririta su ku jawo su jikinku da farin ciki. Kuyi kwanciyar aure dasu cike da soyayya da kuma nuna musu finsu buƙaturwa hakan , ku gode musu ku yaba ƙoƙarinsu ku basu ƙwarin guiwa ku jinjina musu ko bakuji daɗi ba , a hikimance zaku riƙa nuna musu yadda abun yake har su ƙware su anshewa ɗan tama doki. Wasu matayen sunfi wasu mazan gogewa ta wannan harkar da kuma gogewar rayuwa ta zamantakewar rayuwarmu tayau da kullum. Wasu kuma mazan sunfi matan , idanuwansu a tsaye yake tsakiyar kai , tou koma dai waye tafi gogewa ta gogar da abokin rayuwarta sai kuyi rayuwarku gidan aurenku da natsuwa.
Kuma bawai ina nufin kuna biyewa matan waje ko ku fahimci magana ta da wani yanayi. Ku fahimce ni da kyakkyawar fahimta amma aradu ku ƙyale gaibu ku kama zahiri , idan kuma ka nuna mata taƙi gyarawa kayi mata...... Ba cewa nayi ka ƙaro aure ba , nufi na a ƙaro miki kayan ado a ci gaba da baki kula ana ta kwantanci nuniya da gyara har ki gane ki gyara , dan kunsan mu mata ba kishi mukeyi ba hassada muka iya. Sanin sirrin kishi zahiri babu munafurci da yadda akeyin shi kanshi kishin aradu yana nan wurin maza. To kuyi kishi yayin da akafi matayenku ku tsaya tsaye da gaskiyarku kuyi gyara.
Tou lallai fa idan taƙi gyarawa ka lallaɓa kayi mata ƙarin...... Haske , dan inda kuke shiga mu bama shiga wurin , irin matayen da kuke gani mu bama ganinsu , kuke ganinsu kune kuma kuka san inda kuke ganosu har sukeyin abinda kuke ganin mu bamayi muku irinshi , wata matar daga gidan aurenta maƙotanta sai familynka da nata ahalin su kaɗai ta shiga kuma ta sani , sai abokan arziƙi , kuma kila su basu da wayayyun idanuwa bare ta waye da wayewarsu. Sanin da daka santa dashi tun tana budurwa kafin kuyi aure shine dai har yanzu babu wani ci gaba , wata macen kuma da wayewar ido take zuwa gidan auren amma sai ta zama wata aljihun gefen riga ta daƙiƙance ta zama wata sai addu'a kawai. Tou kai da kake shiga kana fita kana zuwa inda ita bata zuwa kuna ganosu suna labbatarku da irin abubuwan da suke jan hankaliku ka sanar da ita mana , ka koyar da ita , idan ka faɗa mata raguwa kayi ne ? Kaɗan faɗaɗa mata kwalwarta ka buɗar mata da idonta dai² irin yadda ka gano suka ɗauki hankalinka. Ka wadata matarka da sutura dai² ƙarfinka ka wadata ta da kayan ƙamshi mayuka masu kyau hoda sabulun wanka ka ciyar da ita karka riƙa maƙalewa wurin mai indomie ko mai tsire da wasu lafiyayen kaji kabar matarka taita kokowa da tuwo , wallahi kuji tsoron Allah kuci irin abinda kuke ba iyalinku irin abun nan da kukeyi kuci daɗi ku barsu da marmarin irin abinda ku ya gundireku dan nacin cinsa da kukeyi wallahi zalinci ne. Cuta ce , ku kuma matan kuma muji tsoron Allah masu siyar da shinkafar miji kuna zubin adashe Allah yana kallonku tom.....
Idan an gyara miki kema ki riƙa gyarawa mana , kar yace kije kiyi kisto two step , ki karkace baki ah ni wallahi bana san wannan kitson kaza² , to wane iri kike so ? "Yar rainin hankali. Ke harma sai ya faɗa miki kiyi irin style kaza ? Ashe ma baki san abinda kike ba. Idan akwai abinda yafi two step kiyi mishi mana , ke meye naki a ciki ? Ba shine yake so ba ? Tou ayi mishi mana a zauna lafiya ? Ko yace miki wallahi kaza na gani ya burgeni , kiyi irinshi , ke uwar tsiwa maimakon kice tou sai kice ah sai kaje can idon daya gano a wurinsu kaje kayi ta gani. Ƙalu balenki da bawa namiji wannan ansar idan ya fara gani tou fa lallai ƙaryaki ya ƙare , kenan kinma yadda yaje ya gano na wajen ko ? Shin wai mema kika tsaya yi har namiji yafi ki hikimar rayuwa ? Ke bakya kishin kanki ne eye ? Haba Hajiyata da Allah karki bani kunya mana. Ko ke baki so tou kiyi mishi idan dai shi zaiyi farin ciki mana , sai sunje sun kallo na wajen a ɗauke miki hankalin miji ayi yamma dashi a barki da ciwon tunani , idan shima ɗan rainin hankali ne kuna gari ɗaya fa da kinyi waya zaice yana abuja ko kaduna ina nan airport zan hau jirgi in tafi lagos , ke ya maida jirgin tana can ta ɗaukeshi an barki gadin gida , kar kuma mijinki yayi tafiya ki tuno cewa kila yana miki ƙarya ne baije ko ina ba , kulli inki ahir inji tsofi , ƙalubalen ki da zargi. Damuwa ta dameki daga nan sai neman shawarar abokai , idan kinyi sa'a da ƙawar kirki ta baki shawara ta gari , idan baki dace ba ta haska ki da malam tsibbu suma daga nan kasuwa ta buɗe , idan kuma kika hau layin maijin taushinki tasa ki , ki kakkaɓo auren , dama tana can tana ta yawon zawarci ita ɗaya ta rasa ƙawar cin titi tou ta samu abokiyar yawo , idan kuma ta ƙwarewa cin amana ta auren miji a barki da wallahi² , ke baki gane illar abun sai kin shiga makarantar , baza ki fahimci wuyar karatun ba sai an shiga second semester ku kula dai......
Gadai Dikko yana faɗawa Sultana , wanda ita a ranta tasan ba haka bane ba. Amma taji daɗin yadda ya yabeta tare da nuna mata tasha gaban mata da yawa. Tou kai idan ka tashi faɗar naka kalaman ka faɗa mata su da gaskiya cikin soyayya. Ku daina haɗe fuskoki wa matayenku haka babu kyau , wani namijin idan kika ganshi a majalisa yafi kowa harshe dariyarshi tafi ta kowa , duk mai tallar da tazo sai yajata da surutu , sai matarka zaka rainawa wayau idan ka tashi shigowa gida ka haɗe fuska kayi ta wani gadarar banza wai kar ta raina ? You bayan ka manta kun haɗu a tsakiyar filin wasa ? Allah wani namiji idan ya shigo gidanshi kamar "yan fashi sunyo samamen dare. Ba "ya "ya ba iyayen suma kansu gabansu harbawa yake kamar an ɗorawa mutum wuƙa a maƙoshi.....
Cike da soyayya mukayi wanka muka baro toilet in cike da tsantsar muradin san kasancewa da junanmu. Kuma har muka fito bai daina zugani ba sai dariya nakeyi ina watse baki kamar lefen wacce babu uwarta a gidan babanta , ina ta sakin layi , zuwa wannan lokaci gaba ɗaya na manta da wasu banzayen hotunan da na gani a wayarshi na fuskanci rayuwa mai daɗi da gusar da damuwa a wurinshi........
Bayan kwana huɗu.
Ni na rasa inda mai gilashi ta sake a cikin jahar katsina , na nemeta na rasa inda take , kuma har gidanta naje bata nan kuma Dikko da kanshi ya kaini. Wayarta ma a kashe. Daga gidanta gidan Inna mukaje kamar dai kullum yauma haka taita habaice² tana zagin Dikko wai bazai zauna mata a kujera ba , ƙiri² Inna ta koma wata zararra , shiko murmushi yayi kaɗan ya samu wuri a saman kafet ya zauna , nima kusa dashi na zauna. Haka taita zaliƙe²n da ita kanta bata san dalilin yinshi ba , taita zaginshi tana aibatashi saida ta gama kaf tace idan yaji fushi ya sakar mata "ya , shafa kanshi yayi ƙasa² yace ban gaji ba ya faɗa yana suɓaro baki a sakace , saida ta gama dashi ta juyo kaina tace kema ɗayar mara zuciyar kaza² nima taci gaba da sheƙeni har ta gaji tayi shiru , saida ta sauka ta gama da kanta ta rufe bakinta mukayi mata godiya mai gida Dikko ya sauke mata manya kuɗi muka wuce gidansu.
Ajiyeni yayi ya tafi huɗɗoɗin shi , Momy kuwa sai ɗan zungurar min ciki takeyi tanasan ta gano wani abu ne daga gareni akan Sharifa. Shiru nayi nidai idan ta matsa min da tambaya saidai ince mata Momy ban sani ba wallahi , wai har yanzu munayin faɗa da Dikko ? Tambaya ɗaya takemin ni kuma ansa biyu nake bata , ah umm. Gajiya dai tayi ta ƙyaleni , har ɗaya saura na dare bai dawo ba saidai ya turo Ashiru ya maidani gida , wato yau ya samu hanyar tafiya wurin "yan iskan matanshi ko ? Ita kuma Momy harma ta yadda da ƙaryar da yayi mata wai ya fita da Dady. Dan da Ashiru yazo tafiya dani sai ta kirashi wai shi yazo da kanshi ya tafi dani mana , shine yace mata yana tare da Babanshi kenan dan karta dameshi. Tun a mota nake kiranshi , shine ya turamin da saƙo wai yana meeting , danma ya ɗaukeni kidahuma. Ci gaba nayi da kiranshi ƙarshe kashe wayarshi yayi. Ashiru ka kaini wurin Dikko , lafiya ? Ya tambayeni ? Lafiya qalau shine yace ka kaini. Mai gidan ranki ya daɗe ? Tou meye a wurin da bazanje ba ? Ai banma san inda yaje ba , daga haka bai sake magana ba , nice naci gaba da cewa amma ai a wannan motar yake a ina ka samoshi ka ɗauko motar ne ? Shiru yayi ya ƙyaleni , fita nayi daga motar ba tare dana sake cewa komai ba na nufi ciki , Papi yana kwance a palon ƙasa yana bacci saman kujera. Ɗaukarshi nayi ina taɓashi ya buɗe idonshi yana shashshekar kuka , ɓata fuska yayi a hankali ya rufe idonshi yana cewa Yaya.... Kila ya dakeshi ne. Me yayi maka ? Saida ya sake sauke ajiyar zuciya da yanayin bacci ya sake cewa Yaya.....
Majalisar ɗinkin "yan matan tashi. Muji , yau da Jiddah ya fara zama sai kuka take masa wai Ya Yazeed yace zai aureta kuma tayi hidima dashi mai girma amma yana ta wani zamewa baya ɗaukar wayarta kaza׳ , shi Dikko ma daga farko bai gane wane Yazeed take magana ba saida tayi mishi bayani , tou shi Yazeed harma ya zama Yaya baida labari ? Hidimar da ta ita Jiddahr tayi ma shi Yazeed ya tambayeta , cikin inda² tace kawai dai kayi mishi magana muyi aure. Cikin rashin fahimta yace waike kece zaki auri Yazeed ? Ey , jinjina kai yayi tare da ɗan karkace kanshi ya tafi duniyar tunanin rayuwa irin ta gidan Yazeed.....
Ƙaton gidane ginin zamani , ya tsaru gidan iya tsaruwa kuma anyi mishi ado da ciyayi masu kyau. Ɗakin mai gadi da ɗakin janareto , a gefe kuma ga wasu irin zabga²n motoci masu masifar kyau da tsada an jera wanda shi mamallakin gidan ne ya ciyosu a harkar wasan danbe. Ajiyar zuciya Dikko ya sauke a wahalce yana jinjina kanshi , duk duniya shidai baya so yaga mace tana wahalar rayuwa. Baya so yaga rayuwar mace tana tangal² , kallon Jiddah yayi sannan ya gyara zamanshi ya miƙe ƙafafuwanshi yana daga saman kujera ƙafa ɗaya saman ɗaya. Wannan inji haka ake cika shi da mai safe rana da dare har gari ya waye a cikin awanni 24 haka yake aiki ba'a kashe shi saida idan za'a zuba mishi mai ko idan ya lalace , duk fitulun gidan a kunne suke suma cikin awowi 24 da wasa ba'a kashe su dare ko rana addau² haka suke amma ɗakin matar gida ko kwan fitila bata dashi , babu wata cima a gidan ita kanta matar gidan duk haɗuwar gidan da tsaruwarshi wankau takeyi tana ciyar da kanta.
Ga hausawa da wani irin hali wai sai kaje zuminchie wa ɗan uwanka amma ka tattara burinki baka kallon rayuwar gidan sai girman gidan , idan ka ɗora mata buƙatarka tace bata dashi sai zagi da gulma munafuka ta tattare komai ta hanamu , daga ita sai "yan uwanta sai iyayenta , ta shanyeshi ta hana ya bamu ko ya bata ta bamu ta hanamu , shin tana samu tana dashi ko bata da ? Kudai , a baku.........׳ kamar mutuwa. Shi Yazeed inuwar giginya ne shi , yana dashi da ya bawa matarshi gara yaje ya zuba harajin wasan danbe , gashi cikakken ɗan iska wata rana ma a gidanshi yake kai mata matan bariki , azzalimin namiji ne dan shi matarshi ta gida ma bai ɗauketa a bakin komai ba , "ya "ya ne ta kwarkwartsa mishi bi da bi a tunanin ta idan ta aihu da yawa ko zai gyara halinshi amma abun sai ci gaba yakeyi kamar ana daka mishi tsawar bakin iyaye. Ni a tunanina duk mai shi zai bada ne , kyauta dai bata kawo talauci. Haka kuma rowa bata kawo arziƙi , duk mai bayarwa baya rasawa , idan kuma ka samu kaci kai ɗaya dan kar ka bayar ka rasa ? Tou wata rana ma gaba ɗaya barin duniyar zakayi da kuɗin da duk tattalin da kakeyi karsu ƙare ko kuma ka tara da duk wani tsari naka na rayuwa , tou fa lallai duk zaka barsu ka tafi kai ɗayanka kaje wata rayuwa ta daban. Gara dai idan kun samu kuɗan taimakawa masu buƙatar taimako sai kuma Allah ya ƙara taimaka muku.
Caf Yazeed cikakken ɗan tasha ne. Baida mutunci ko kaɗan , dan ko A C ɗakin matarshi da yasa daga farko daga baya ƙwaƙwulewa yayi taci gasar danbe. Amma saboda riya yabar iyalinshi da wahalar rayuwa , ko tace baya bata abinci tana cikin wahala , sai ace bata godiyar Allah , abinci buhunna² gasu na ajiye a store taci ɗin ma ta ci ƙaniyarta dan tasan ba nata bane ba kwalliyar gidane saboda mutane su gani suce yana da kirki , bayan wani lokaci kuma ya jera mutane layi ya rarraba musu shi sadaka.
A anguwar sai zaginta akeyi ita marowaciya ne tabar "ya "yanta da yunwa sai azabar neman kuɗi kamar zataje dasu lahira. Wani faɗa da sukayi har iyaye suka shiga ciki tace har a c ya cire a ɗakinta da palo tace yasa musu fanka ya ƙiya , shine yace tana wurin gyara , ganin iyaye yasa yaje ya samo hoton a c n yazo ya maƙala mata , shima tayi magana yace ya gyaro itace ta lalace shi bata da tattali kaza² , aka haɗu aka bata rashin gaskiya , shi kuma ganin ya samu sa'a yasa yaketa gurje mata mutunci da wahala. Duk wanda ya kalli gidan Yazeed akace ansan sunan wani abu waishi wanki ko wankau ? Sai su "yan cikin anguwa sunce ƙarya ce , ita kuma tunda anguwar masu kuɗi ne take sa ana tattaro mata kaya tana wankewa ta goge tunda dama kayan "yan gayu ba wani datti yakeyi ba , haka azzaliman maza sukeyi dan rashin imani. Shine Jiddah zata shiga ? Allah ya basu zaman lafiya..... Allah ya rufawa An matarshi asiri da tana can tancin ƙaniyarta gata yarinya , wani hali nata ya tuno dan haka yayi taƙaitacciyar dariya , da tace wai ya tsalleke kabbarinta ya wuce , cikin dariya yace niɗin banza An mata , saida yasha dariyarshi Jiddah tana daga gefe tana kallon ikon Allah , shi yama fita daga wannan sabgar ya tafi kallon hotunan matarshi.
Duk hoton daya kalla zaiyi murmushi a ranshi yace An mata rigima , wai Dikko ka tsalleke kabarina kaje kawai , haba An mata kar Allah ya nunamin ranar da zaki tafi ki barni a duniyar nan , bana fatan naga ranar da ni zaki shige cikin ƙasa ki barni , ina so in rayu dake har ƙarshen rayuwata in tafi in barki ki rayu rayuwa mai cike da farin ciki , gaki ga Papi da "yar ƙanwarshi ko ɗan kaninshi , burina yanzu a duniya bai wuce in mutu a hannunki ba , ina sanki׳ ki jarumata..... Hayaniyar dake tashi ne ya dawo dashi daga duniyar kallon hotunan da yakeyi....
Salati yayi tare da fiddo duk girman idanuwan shi ganin Sharifa da wata irin bahaguwar shiga ta jahannama ga fasinja. Rankatakaf su Ashiru suna wurin , shi wallahi kunya ma abun ya bashi , gata ta shigo full battery wato cake take. {{ tana cikin maye }} tasha wasu irin zaƙo²n akaifu ansha girar ido atach har tsakiyar baya , wasu irin "yan kunne girman round insu yakai girman ɗan hannu sai ibar hayaƙi take tana barbaɗashi sama yana bin iska. Jiddah na riƙe da ita sai zazzabga mata mari takeyi wai ranar da Ya D ' K yai mata liƙi ita Sharifar wai tanayi ma ita Jiddah gwalo wai an saketa , tun ranar nake nemanki shegiya ƙazama , shine fa aka cakume rigima. Dikko kuwa lallaɓawa yayi yai layar ɓata bai yadda kowa yaga fitarshi ba. Har baya ganin gabanshi ya shiga mota dakel. Shi gaskiya bawai zaice yana san Sharifa ba , ah tunda dai zai aureta ya kamata ta kasance mai tarbiyar da kamun kai. An mata har hannunshi ta zauna kafin suyi aure amma kullum tana cikin hijabi , gaskiya yana san matarshi ta kasance mai sirrinta jiki yayin da wasu mazan da ba muharramanta ba suke a wuri. Baifa isa yace baya auren Sharifa Dady zaiyi damuwa.
Taya za'ayi shi matar da zai aura ta kasance haka ? Irin wannan dressing ai ba nan akeyi ba , ko a gidanka kayi irin shigar ai zaka saka hijabi idan mutane suna zuwa , tirr mtsww... Gaskiya zai faɗa mata ta daina yin haka shi baya so. Haka ya iso gida da tunani barkatai a zuciyarshi , bayan yayi parking yake ƙara hasko yadda ya ganta zuciyarshi na daɗa soyuwa da ɓacin rai , kai a , a gaskiya a , a , haka ya shiga ciki ranshi a matuƙar ɓace kawai dai yaji babu daɗi yana tayin damuwa har zuwa safe.
Dady kuwa an kaishi asibiti. Bayan likitoci sunyi bincike²nsu suka tabbatar wa da iyalinshi cewa ya samu shanyewar ɓarin jiki , ai uwar Hafsa cewa tayi ita bada ita sa lallen kaza ba , dan ba zata wani iya zaman jinya ba. Da sauranta zata taga gaba tayi aurenta ta gurji sauran shekarun da suka rage mata , wallahi bata zama tayi ta kwasar ƙazanta , Dady ya karkace baki yadda masu irin lalurar suke magana yace baya sakinta , tace bara ta kira inda za'a ansar mata tikitinta na saki a hannunshi tunda ba tare aka haifesu ba , wayarta ta ɗauka tana cewa zaka ga yadda za,a ansar min idan kazo musu da rainin hankali ƙarfin shari'a ba wani ruwanshi da shanyewar jiki zasu tafi dakai su calika ka. A taƙaice dai sun rabu kuma dan rashi inami ta tattara duk ɗan sauran abinda ya rage na ƙaddororinshi tayi gaba dashi wai karya cinye tattalin arziƙin kuɗi "ya "yanta su tashi a hoto , yadda ya nannaɗen nan idan ta zuba mishi ido sai ya cinye kaf kuɗin a wurin jinya.....
Haka taje asibitin da Amisty take ko tausayin Amisty bataji ba , ta ɓanɓare abun ƙarin lumfashin , Amisty ta fara rawar kyarawa , Momy tace kuɗina suna ina ? Faɗamin gidan uwar da kika kaimin kuɗina ko ki tafi lahira tsaye....... Ha׳ Amisty keyi , dariya Momy tayi cikin rashin imani tace rayuwa ko mutuwa.....? Amisty ta nuna rayuwa watom ta mayar mata da abun , mayarwa tayi tare da jaddadawa Amisty kwana biyar ta bata ta haɗo mata kan dukiyarta idan ba haka ba zataje gidan yari , akwai wani sabon d p o da aka kawo acan sabon gari police station inyamuri ne zata haɗata dashi , zatace idan ya anshi kuɗin ya ɗauki one miliyon haba kundai san inyamurin mutum da kuɗi.....
Halima mijinta da sauƙi sosai anma sallomoshi ya dawo gida , yana dawowa kuma da zancen ƙarin aure yazo , fitina ya tashi da rashin kunya nan fa ta tattara ƙawaye ana neman mafita. Kowa da irin shawarar da yake kawowa gashi lokaci ya ƙure ita tanayin mamaki a inama ya haɗu da matar da har zasuyi aure.......? Ɗaurin aure ranar juma'a yau saura kwana 4 , wace ce zai aura.......? Wace ce.....׳ ita..........??? A iya sanin da tayi mishi bashida budurwa dan kullum saita zindire wayarshi tayi bincike amma ba wani alamar soyayya , ashe suma maza sun iya munafurci....? Hmmm maji dai.
Hafsa abun yaci tura alhamdu ta kakarewa malam. Itama tana can sun jagalgaleta sun kaita asibiti saboda ciwon hannunta. Sai masifa takeyi itafa lafiyanta qalau duk wanda ya taɓa mata magani zatayi ma mutum uwar watsi..... Gata nan dai suka watsar a asibiti kamar asarar noma , muje gaba daga baya maji me likita yace..........?
Jiddah data ishi Yazeed da kira cewa abokanshi yayi ya tafi hutun honey time , ƙaraurawar nasararshi ta doka zaije ya buga lamba tara ya dawo.......
Shi kuma mai gida Dikko da yayiwa Sharifa faɗa dan toshewar basira sai taje ta faɗawa uwarta Mai gilashi , raɗa ta ƙara yiwa Sharifa tunda ita daƙiƙiya ce. Mai gilashi tace ta dage karta sa shakku fatan nasara.
A tsagina kuwa , yau tunda na tashi jikina yayi min wani irin sanyi , gani nan dai ni ba mara lafiya ba kuma ba lafiyayya ba , yau komai ya kasa shiga cikina saidai in bi wannan kujera inbi gado. Gajiya nayi nacewa Papi yaje yace Yaya banda lafiya. Babu wani ɓata lokaci shi yazo , Pa-Pi kuma bai dawo ba.
Gabana ya tsuguna ya riƙe cikina da duka hannayenshi cike da tausayi yace meye ne ? Yayi tambayar yana kallona. Fashewa nayi da kuka tare da ɗora fuskata a saman kanshi nace nidai banajin daɗi inajin wani abu yanamin babu daɗi kamar zan rasa wani abu a rayuwata , murmushin ƙarfin hali yayi sannan ya da dawo kusa dani ya zauna. A hankali ya jawoni jikinshi yace babu wani abu da zai faru sai alkairi , ummm ? Ki daina biyewa tunanin zuciya zataje tasa ki shiga ruɗun rayuwa , ba gani ba ? Ya nuna kanshi Kalli kuma ina tare dake , meye zai faru ne ? Munayin zaman lafiya kuma ni nakine ke kaɗai. Tou tayama kike tunanin zaki rasa wani abu mai muhimmanci bayan ni ina tare dake , ai kinsan bazan taɓa rabuwa dake ba har abadan duniya , ki kwantar da hankali ki daina wahalar saƙa tabarmar kabar da bata dace da zamanki ba gimbiya Sultana. Idan kinayin kuka hankalina tashi yake tsikar jikina duk ta mimmiƙe , hawaye basayin kyau a wannan kyakkyawar fuskar. Kuka bai dace da rayuwarki ba. Ke kiyi shiru bara ni in miki kukan tunda kina so kiga hawaye a fuska yana zuba. Ah ai sai inyi ke ki huta , baki san ba'asan mai ciki tanayin damuwa ba ? Ko so kikeyi ki haihu ne ? Yayi maganar cikin sigar zaula. Nace ey , hmmm kima ƙara dagewa kina da sauran kwanki zai kai 90 da Allah kiyi shiru ya ƙarasa yanamin hararar so, tou naji kawomin wayata , tashi yayi ya ɗaukomin wayar , bayan ya bani ya zauna ya sake riƙeni. Kowa dai daga ni harshi muna saƙa wani abu a zuciyoyinmu. Wayar Inna na kira babu daɗewa ta ɗauka , bayan gaisuwa mukayi fira da ita lafiya lau babu wani zage²n nan , kuma na haɗata da Dikko shima suka gaisa cikin mutunci , tace ina Pa-pi ? Yace ya fita yanzu. Wai jiya ba'azo dashi ba.
Me yasa shi ba'asan kawoshi ne wai ? Dikko yace insha Allah Ashiru zai kawoshi bayan la'asar , har sai wannan lokacin ? Kubar shi bana so tunda ba zaizo min yini ba. Ashirun ne baya nan idan ya dawo zasu zo insha Allah , har suka gama wayar babu wani alamu na rashin mutunci kowa ya ajiye waya da farin ciki.
Ni kuma kuka naci gaba dayi , yace bari fa ganin ina baki haƙuri ni kinsan abu kaɗan yake ɓatamin rai kodai kiyi shiru ko in tafi ko kuma ke kibar ɗakin nan sai ki zaɓa , nidai gaskiya bazan yi shiru ba , kasan yadda nakeji ne wai ? Sannu yaimin tare da tashi ya fita nima na miƙe nabi bayanshi har ɗakinshi......
*ZAINAB ABBAKAR MATAWALLE. Ina godiya sosai da saƙo uwar gidan KWARATA...*
06/02/2019
*JAMILA MUSA...*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*
*SAI NA AURI D ' K*
🅿 ------ 9
A palo na sameshi zaune saman kujera. Ci gaba nayi da kuka na nufeshi. Hankalinshi yana saman wayanshi yace so kike dai in zaneki ko ? Kusa dashi na zauna nace baka san ya nakeji ba. Riƙoni yayi da hannun da wayar take riƙe cikin tausasassar murya yace baki so in zaneki ne ? Yayi tambayar yana kwantar da firgitaccin idanuwanshi masu saukar da kasala. Kaɗan na kalleshi a kasalance na ɗaga mishi kaina alamar ey. Yace to shikenan jeki ciki ki kwanta ina zuwa. Miƙewa nayi na riƙo hannunshi ina janshi , ba tare daya kalleni ba yace ya wai meye kuma ? Ban bashi amsa ba naci gaba da jan hannunshi , taƙaitaccen kallo yayi min sannan ya tashi muka shiga ciki tare.
Cike da farin ciki Yazeed ya isa gidan Rabiya. Yau ciki aka shiga kasancewar ita matar gida bata nan. Yazeed kuwa tun a waje ya ɓalle botiran gaban rigarshi yana nuna yanayin haɗama. Kai tsaye ɗakin da aka bawa ita Jiddah a ɗakin ta wuce da Yazeed , suna shiga ya rumgumeta suuuu suka sulale saman gado gaba ɗayansu sunayin farin ciki tare da nunawa junansu kowa yayi maraicin kowa.
A gaggauce dai aka shiga gabatar da wasa. Ya nemi yaddar gado da kuma sa'ar makoma sai addu'a na gaba ya samu nasara mai girma. Danshi a tunanin shi a filin wasa ake. Wasan yau yafi ko wane wasa martaba da mutumci a wurin Jiddah , kasancewar an samu wadatuwar fili da tsaftatuwar muhallin da akeyin wasan. Yazeedu kuwa ya ɓata manyan awowi kuma ko wace awa minti da seconds ya bada lafiyayyen naushi mai zama a zuciya har abada. Jiddah ma ta mayar da martani domin ita dama tuni Yayanta ya gogar da ita kuma ta ɗauki karatu.
Rabiya kuwa tunda Yazeed da Jiddah suka shiga ita ta iso gidan , biyosu tayi tana lafiya ? Ina ne zataje da namiji ? Duk babu wanda yaji bare kuma yasan tana magana , suna shiga suka turo ƙofa garam har aka bige ma "yar sa idon banza goshi. Ai bawai Jiddah taji kunya ba ita Rabiya itace taji kunya dan haka ta koma ɗakinta tana neman mafita.
Taya zata iya furtawa Momy wannan zance ? Shedar zina wahala gareshi. Shin wai waye ma yace mata suna aikata saɓo ? Kuma ita bata kamasu sunayi ba , tou dan kawai sun shiga ɗaki ? Ta yuwu wani abu ya faru , sai saƙawa takeyi tana warwarewa lokaci² kuma tana kallon agogo kamar mara aikin yi har Yazeed ya fito , sai yanzu ta gane Yazeed. Shi ɗaya ya fito Jiddah bata biyoshi ba , tou meya faru ? Me sukeyi a ɗaki tsawon awowi 2 har zuwa 3... Ta shiga 3 zafa a samu matsala.....
Saida Yazeed ya wuce itama ta fito ta nufi ɗakin Jiddah. Kwance ta sameta riƙe da wayarta tana ta latse². Da hannunta ta nuna da yanayin karta shiga haƙƙinta cikin warwarewar haruffa tace am Ji-dd- , ah Jiddah am dama nace lafiya naga Yazeed ya fita ? Ba tare da Jiddah ta kalli Rabiya ba tace lafiya qalau kawai kaina ne yake min ciwo ta ƙarasa maganar tana nuna kanta. Ɗan yatsina fuska tayi tare da ajiye wayar ta taci gaba da cewa gashi gida ba kowa kawai sai nayi ma Yaya D ' K waya ina buƙatar magani , shine fa ya aiko abokinshi ta ƙarasa maganar tana watsa hannunta....
A ɗan tsorace Rabiya tace Dikkkkkkkkkko ? Ta kira sunanshi da mamaki cikin jan kalmomi wurin faɗar sunan tare da warware kaf ilahirin gininta. Ummm Jiddah ta faɗa tana jinjina kanta alamar gasgatawa. Rabiya tace taf Dikkon ? Jiddah tace shifa. Fuuu Rabiya ta fita , murmushi Jiddah tayi tare da cewa ai nasan idan na shigo dashi a tafiyar dole zai fito yayi masifa ya tilassa ayi auren , ba jiya naje muyi magana ba shine ya basar dani yana waani dariyar banza , An mata rigima , rigimo. Dariya ta sakeyi kaɗan tare da nunawa da "yan yatsunta sati biyu cif zanyi nayo waje. Wata 3 idda a cikin wata na huɗu zamu tare a sabon gida. {{ G R A }} a wata na biyar kuwa Caca zata kama gabanta , Pa-Pi zai zama nawa , wama ya sani ko jinina ne aka kai can.....? Da yanayin tunani tace babu shakka Pa-Pi nine uwarshi shine yake ƙwaƙwata , oho dai hakan ma bazai hana in kasheshi ba.......
A tsagin Rabiya kuwa tunani takeyi , meye tsakanin Dikko da Jiddah ? Wane irin magani ne ya bada a kawo ma Jiddah ? Ciwon kan ƙaniyarta ? Karfa su maida ita wata gwanjon bisa titi , tana can tana huɗɗoɗinta suyi ta wucewa ba tare da tasan so adadin da ake wucewa ba. Anya Dikko yana da gaskiya ? Kardai zagayewa yakeyi idan bata nan.....? Har zata kira Momy ta fasa kawai ta kira Dikko. Babu daɗewa ya ɗauka ko gaisuwa babu tace yazo yanzu²n nan tana nemanshi. Magana yayi sannan ta bashi amsa da cewa kawai kazo nace idan kuma ni inzo tou... Magana ya sakeyi ita kuma tace shikenan kayi sauri ina jiranka.
Dan Allah kaje tare dani. Cikin faɗa yace wai ina ne zanje dake ? Saida nayi kalar ban tausayi da marainiyan murya nace dan Allah. Baimin magana ba ya ɗauki wayoyinshi , shikenan tunda bara ka fita dani ba Allah yasa ka dawo ban..... Bakiyi me ba ? Gyara bakina nayi ina kallon ƙasa , bai sake kallona ba yace zo muje. Da sauri na wuceshi na tafi ɗakina , hijabi kaɗai na ɗauka ko wayana ban tafi da , nayi waje. Pa-Pi shima biyoni yayi yana kuka jaije.... Kafe kai yayi shi bazaije da Pa-Pi ba , shi kuma Pa-Pi riƙeni yayi idan ba'a zuwa dashi nima babu inda zanje. Dikko yace ka sakarmin mata kaji ? Yayi maganar yana zaro mishi ido. Da ita zanje kaine bazan tafi dakai ba. Riƙeni yayi Momy karci tafi ci barni. Dikko yace kai so nawa ka tafi ka barta ɗan rainin hankali sakarta nace maka. Kamar an matsi bakinshi yace kaicuwa jakuje....? Ya faɗa da yanayin tsoro ! Yaci gaba da cewa kuma fa'a cuwa da Pa-Pi ya ƙarasa maganar yana ma Dikko wani irin kallo haɗe da murmushi. Kete Momy ce cinyi kuka , jinjina kanshi yayi sannan yace cima Yaya ce yayi kuka ya ƙarasa yana dariya. Nuna kanshi yayi sannan na nunamu yace ni kuma can muku dayiya wayyayi.
Yadda yayi abun ne yaba Dikko dariya , yace ni kuma wallahi in zaneka. Dariya Pa-Pi yayi cewa kowa ce yayi kuka wayyayi. Yana ƙara yawan dariyar wai zaiga Yaya yanayin kuka. Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji lokaci guda wata irin zufa ta ketomin , murya a sanyaye nace ma Dikko nidai na fasa zuwa. Dariya Pa-Pi yayi tare da cewa wayyayi Momy taji tsoyo. Dikko yace keda Allah manta dashi taho muje yayi maganar yana jan hannu na , kinga sai kirana takeyi zo muje kinji....? Ƙwacewa nayi nidai kawai kai kaje , cikin rarrashi yace ke An mata haukan Pa-Pi zai tsorataki ? Da Allah zo muje yana ci gaba da jana. Fizgewa nayi nidai na fasa , cikin ɗaga murya yace kada Allah yasa kije kuma tunda har kika ce zaki kika fasa , idan na fita sai 2n dare zan dawo.
Jiki a sanyaye na kalleshi. Ɗagamin gira yayi tare da kwantar da idonshi na haggu , a hankali ya fidda sautin sumba cikin natsuwa da salo mai tada hankali yana ƙara riƙe ganin idanuwanshi , duk iya masifar sa idonka bara ka gane abinda yayi ba , wannan karatun daga ni saishi kaɗai muka fahimci yaren juna. Ajiyar zuciya nayi kaɗan cikin ƙarfin hali , shi kuma ya ɗagamin hannu ya wuce. Tunda na fasa zuwa ya tafi da Ashiru....
Dariya Pa-Pi yaci gaba dayi yana riƙe da hannuna har muka shiga ciki. Saida muka zauna na tambayeshi wai waye yace mishi zamuyi kuka ? Zama yayi kusa dani yace wai a cikin wayar Yaya ya gani , cike da ɓacin rai nace dan ubanka a wayar aka ce zamuyi kuka ? Kallona yayi ya ɗaure fuska shima da yanayin fushi yana hararata wai saiya faɗawa Yaya nayi zagi ya zaneni , shima ai jiya Yaya ya dakeshi da yayi zagi wa kare.... Tsoki nayi sannan nace ya tashi ya bani wuri. Ƙin sauka yayi saidai ya juyamin baya wai yama fata dani. Kaje ka ɓatan. Ba'a ciyyawa dake.... A palo na barshi na koma ciki , kasancewar zufar da naji inayi dole tasa naje nayi wanka. Ina fitowa kuma masassara tace gata nan zuwa , dakel na iya shafa mai kaɗan sannan naɗan kashe masƙin man da fauda , kayana na saka na kwanta.
Dikko jin kiran waya yayi yawa , ya fara faɗa wai ita Rabiya bata da haƙuri gashi yana tafiya zuwa wurinta amma ta dameshi da kira. Wannan ɗan abun harya hasalar dashi danshi baida wahalar fushi amma yana saurin sauka. Cike da ɓacin rai ya ɗauki wayar a inda take ajiye amma sai yaga Inna ce take kiranshi. Ɗauka yayi da sallama ba Inna ce ta ansa sallamar ba mijinta ne ya ansa dakel yace kana ina ne ? Saida Dikko ya kalli hanya sannan ya faɗa masa ta inda yake. Tou wai kazo gidan Kaka dakai da Sultana. Lafiya Dikko ya tambaya ? Umm ai na tura maka saƙo ka duba , a , a , wai meye ne....? Baiyi magana ba ya ajiye waya.
Wai Allahna , Inna ta tafi itama..... Lahaula walaƙuwat illabillah shine abinda ya furta. Dakel ya nunawa Ashiru ya koma gida , taya Ashiru yaci suka dawo gida , dawowarsu ne shi Dikko ya shigo ya samu Sultana tana wanka , ɗakinshi ya koma yana tunanin ta wace hanya shi zai iya furtawa Sultana wannan saƙo....? Ita ya zata kalleshi ? Saƙon mutuwa baƙin saƙo ne , har abadan duniya baraka manta da wanda yazo maka da wannan aike ba. Ya juya ya rasa yadda zaiyi , ko Ashiru bai faɗawa ba. Wane hali An mata zata shiga ? Zatayi kuka kamar zata cinye ranta ya sani , shima kuma za shiga tashin hankali , duk duniya a wannan rayuwa idan akwai abinda ke tada mishi hankali yake firgita mishi tunani yake sashi ɗimuwar rayuwa da manta shi ɗin ko waye wallahi bai wuce tashin hankalin Sultana ba. Shi kaɗai ya isa yayi mata amma idan wani ya taɓota bayan shi ? Tou fa lallai zaici gari da yaƙi.....
Kira ne yake ta shigowa a wayata babu ƙaƙƙautawa. A wahalce na miƙa hannu na dakel dan ɗauko wayar dake saman bedsite. Kafin in ɗaukota a hannuna tuni ta tsinke har wani kiran ya sake shigowa ya fita. Saƙo ne ya shigo dan haka ban fara duba rashin kiran dana samu ba na fara da saƙon.
_Ke Sultana an faɗa miki uwarki ta mutu baki tahowa ? Tou ta mutu can wurin siya ma ɗanki abun wasa , mota tayi ƙoli² ta dakota da ƙasa sannan tabi ta kanta ta wuce. Ba wata tsiya nake kiranki ki bani ba bare kijamin aji ke surukar gwamna..._
Yayar Inna ce surukar Sultan wanda zan aura da farko tasa aka fasa auren ya auri "yar ta. Duk me ya kawo wannan dogon bayani tou ? Salati nayi na sanar da mahalicci na daya isa da rayuwata. Dakel na iya gano number Dikko a wayata na fara kiranshi komai bana iya gani kasancewar inaji na a cikin wata irin baƙuwar rayuwa. Shikenan na zama marainiya gaba da baya , babu uwa ba uba , Allahu Akbar , tabbas ubangiji shine mai iko akan komai da kowa.
_Kema ɗayar mara zuciyar_
Itace kalmar data fara dawomin a cikin kaina , ina hango Inna palonta a daren jiya......
_Me yasa shi ba'asan kawoshi ne wai ? Har sai wannan lokacin ? Kubar shi bana so tunda ba zaizomin yini ba._
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , wani irin ihu na kurma , na fara magangu na sakin layi , kai... Wai Allahna , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , nayi kuka sau adadin yadda naji ciwon mutuwar Inna a zuciyata , haba Inna sai kuma kema ki tafi ki barni ? Shikenan ? Tou wai mema yasa kika je siyen wani abun wasa ? Waye ya aikeki ? Haba Innata meya sa²..... ? Kema shine dai kika tafi kika barni ? Gaskiya nadai zauce nayi maganganu marasa daɗin rubutawa. Dikko yayi maganar shi banama jinsa dan gaskiya bana iya gane abinda yake cewa. Kukan da nakeyi ne shine ya tayar mishi da hankali shima yaita kuka kamar ƙaramin yaro wai zai mutu. Shi baya so yaga inayin damuwa , in rufa mishi asiri nasan bashi da lafiya , shima yaji ɓarin maganganu kamar aradu ta faɗo.
Ko a gidan rasuwa haka naita bori ina ihu mai tayar da hankali duk wani imani , babu wanda ya damu dani bare yace ke daƙiƙiya ki gyara kalamanki ko kiyi ma mutane shiru , Kaka ce kaɗai take rarrashi na , sai Pa-Pi daya riƙeni yana ta ihu wai waye ya dakeni. Yayar Inna ni bansan abinda yasa bata ƙaunana ba , bansan me nayi mata ba ta tsaneni da zafi haka. Ko waye ya rasa yayi kuka , nidai a duniyar rayuwata banga abinda yafi rashin iyaye raɗaɗi da ciwo ba. Inajin yadda aketa faɗar yadda mutuwar Inna ta kasance. Wai bayan tayi waya dani a yadda shi mijinta ya basu labari.
Baiwar Allah ashe abinda tayi mana jiya ya dameta. Ta faɗawa mijinta cewa gaskiya Dikko jajirtaccen namiji ne , kaifi ɗaya ne ita a yadda ta fahimta , tsaye yake babu munafurci a lamarinshi. Idan zaiyi kawai zaiyi idan bayayi ko za'a mutu zai tsaya a wurin. Wai tace masa idan yaji fushi ya sakar mata "ya , shine yace bai gaji ba , wai me yake nufi ? Ta ɗauki biro da takadda tayi rubutu akai , bayan ta gama sukazo gidan Kaka dashi da ita. Yace shi baisan abinda ya kawota ba , haka kuma baiji firarsu ba. Yau kuma tace a kawo mata Pa-Pi , wai shine taje ta sissiyo mishi abun wasa wai tasan Dikko zaiyi farin ciki dan ta goge damuwar data saka mishi a daren jiya. To shine fa ta gama sissiye²n tana zuwa wurin motar ta mota yabi ta kanta ya wuce.....
Ni ɗaya a wurin Inna , banda Ya banda ƙani haka nake ni ziƙau ina , ba uwa ba uba ba Yaya ba ƙani. Ga "yan uwan Inna ni basa so na , ahalin Babana kuma gasu dai ga yadda suke , "yan uwan Dikko sune suketa bani haƙuri , bawan Allah shi kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye sai turowa Rabiya saƙo yakeyi wai An mata tayi haƙuri ta daina kuka , bayan wani lokaci kuma ya rubuto cewa wai shi yana nan bazai tafi ya barni ba insha Allah , hmmm haka dai yaita rubuce² har akaje aka rufo Inna aka dawo.
Duk ahalin Dikko sun tayani zaman makoki har Momy. Mai gilashi da zugar ƙawayenta "yan tasha amma banda Halima tayomin gayyarsu zuga guda. Akayi ta gulma na wai ni na tara karuwai a wurin rasuwar Mamana , Nabeela ma tazo kuma tayi kuka kamar yadda taga inayi itama , ta tausayamin sosai , tamin sannu da rashi. Sati ɗaya nayi a gidan Kaka nan nake kwana , Dikko kuma idan yazo sai dare sosai yake tafiya dashi da Pa-Pi.
"Yan uwan Inna kuwa bawai ta mutuwarta suke ba , abinda ta bari kawai suke ta lissafi. Babu kunya bare tsoron Allah suke farfaɗo suturunta kowa yana cewa ya kamasu , ita surukar Sultan itace take maganar kayan ɗaki wai dama wallahi ita kafinta yayi mata ha'inci kullum tana fama da "yan ƙwanƙwashe² gado ba kirki , kujerun ma duk sun rubza kaza². Shin aisai ta kwashe ita da zata tsaya tsaron duniya.
Ranar da akayi addu'ar 7 a ranar na bar gidan saboda wulaƙancin da sukemin. Da zan tafi ne Kaka ta bani wata takkada cewa Maryam gashi mahaifiyarki tace a baki. Meye a ciki ? Nima bansan ko ta miye ba , tadai cemin zata turoki ki ansa , amma itama kanta gaskiya batayi tunanin zaki anshi takardar bata a raye ba. Ansa nayi nabar palon. Dikko da kanshi ya ɗaukeni muka koma gida.
Nidai babu wanda a cikinsu yayi min magana game da duk wani abu daya shafi Inna. Basa gabana dan ni basu ne damuwata rashinta shine ƙaton ciwon dake damuna. Suke san abun duniya wanda har ya gusar da imani daga zukatansu , ana kukan mutuwa suna lissafin abinda zasu gada. Tun a mota Dikko kemin nasiha har muka je gida. Da kanshi yayi ma Pa-Pi wanka ya kwantar dashi. Duk inda na juya Pa-Pi sai yayi ta kallona sai kuma ya kalli Dikko.
Har bacci ya fara fizgarshi ya buɗe idonshi yace cinci abinci ? Murmushi nayi kaɗan tare da nuna mishi da kaina alamar eh. Shima murmushi yayi ba tare daya sake magana ba ya rufe idanuwanshi yaci gaba da bacci. Nima saida nayi wanka sannan naɗan taɓa fura. Saman gado na koma na warware takaddar da Inna ta bayar a bani , Dikko kuma yana tacan gefen Pa-Pi yana latse² a wayarshi...... Ga abinda Inna ta rubuta a takadarta.
_Aminci Allah , yaddar Allah wadatar zuci zaman lafiya da kwanciyar hankali su ƙara tabbata a gareki ɗiyata...._
_Sultana ki gafarceni a rayuwa. Nasan bakyajin daɗin abinda nake miki... ? Ni wallahi duk abubuwan da nakeyi ma Dikko dake banyi da nufi ba. Saidai ina hasko miki rayuwar gaba. Ke ɗaya na haifa a duniya baki da Baba haka kuma baki da "yan uwa da kika fita ciki ɗaya dasu. "Yan uwana kuma bakya gabansu , daga ni saike muka rage a duniyarmu , ina neman yafiyarki dan Allah , ki yafemin kuma insha Allah bazan sake ba..._
_Amma ki san wani abu a rayuwa. Nifa ba san Dikko ne banayi ba , a , a ni iskancin shi ne gaskiya bana so. Idonshi ya waye da yawa. Ni gaskiya a tsarin rayuwata bana sha'awa ko muradin namiji mai buɗewar ido da gogewar rayuwar irin na Dikko , amma ya za'ayi tunda haka Allah ya rubuto ? Nidai ina neman yafiyarki karki ɗaukeni a matsayin uwar data fi san kanta akan "yarta. Ban hanaki zaman aure ba haka kuma ban tilasta ki kashe ba. Saboda aure dai sunna ne mai ƙarfi daga cikin sunnonin Manza Allah S. A. W , kamar yadda ayoyi da dama suka nuna mana:•_
_Allah {{ S W T }} yana faɗa a suratul rum cikin alqur'ani mai girma. "Kuma daga ayarSa ne ya halitta daga garemu mataye domin mu samu natsuwa daga garesu. Kuma ya sanya tsakaninmu ƙauna da tausayi , haƙiƙa wannan aya ce ga ma'abota hankali. "Wannan aya ta tattara duk wani ma'ana na aure a cikinta. Saura namu farfasawa mu auna mugani , shin ma'anar aure da abinda yake cikinsa kuwa kamar yadda Allah ya nuna mana hakan mukeyi. Da farko Allah ya ambaci ma'aurata da ababen samun natsuwa duk anan ya kawo jinsin mata ne. To amma ai mun sani idan har macen bata samu natsuwa ba ? Shi kanshi namijin natsuwarshi ragaggiya ne. Tambaya anan ta ina ma'aurata zasu sami kwanciyar hankali.......?_
Hah. Ci.. Nayi tare da yin murmushi mai ciwo na goge hawayen dake bin idona. Ina ci gaba da kuka. Naci gaba da karatun takardar Inna.....
_Na farko:• a samun natsuwar aure shine hadafin yinsa. Bai taɓa yiwuwa aure ya kasance an ginashi kan wani hadafi sannan ya zamo ɗorarre. Wannan shi yasa Annabi {{ S A W }} bayan ya zayyano kaso na matan da ake aure. Ƙarshe yace "na hore ku da ma'abociyar addini. To haƙiƙa abun nufi anan shine ba wni hadafin da zai haifar maka da cikakkiyar kwanciyar hankalin aure sai hadafin tarayya domin Allah..._
_A cikin aure mai kawo natsuwa kenan. Haƙiƙa a yau munyi sake tare da watsi da haƙƙin junanmu ta yanda takei har wasu abubuwan ma an shafesu daga rayuwar auren sai wajen mutane jefi² mun barwa turawa wanda kuma mu addininmu ne ya koyar damu su. Ina horonki da ki zama mai biyayya , ki zama mai kunya da juyawa abin duniya baya. Kiyi kara ki zama mai haƙuri. Rayuwar gaba ɗayanta haƙuri ce , ki guji yaɗa sirrin mijinki wa kowa da koma waye. Kar kiyi abinda bakiyi shawara da mijinki ba , ki kiyaye fushin shi ki guji ɓata masa rai da gudun duk abinda baya so idan har bai tsaɓawa Allah ba. Haƙuri׳ ki zama mai haƙuri da biyayyar aure kinji uwar masu gida. ?_
_Ki kiyaye munanan kalamai. Karki kuskura ki jiyar da kunnuwan mijinki ɓatattar magana daga gareki. Magana mara daɗi ko muni kiyi ƙoƙarin kare kunnuwan mijinki dasu. Kar kiyi masa:• ƙarya. Ki kula dashi , ki zama mai tsafta , kar kici amanar shi , banda zargi ki guji abokai , karki raina masa iyaye. Ki kiyaye kuma kisan yadda zakiyu ma'amula da "yan uwansa._
_Kinga wa'anan abubuwan da zan lissafo su ? To ki kiyayesu domin sune ke taka rawa wurin rusa aure matsawar ba'a kiyayesu ba._
_Rashin ilimin zamantakewar aure , al'adu , rashin binken halin miji , rashin binciken halin mace , matsalar iyayen miji , rashin tsafta , matsalar dangin miji , rashin iya magana , rashin iya ciyarwa , rashin iya kwanciyar aure , rashin adalci , auren kisan wuta , cin amanar aure , ƙawaye , zafin kishi , sata , gulma , wayar miji {{ phone }} , rashin lafiyar miji wajen gamsar da iyali da itama rashin lafiyar macen wajen gamsar miji , sharrin boka. Ke kina tunanin ni bana sanki ? Taya ma zaki yadda ki fara wannan tunanin ? Tunda kike a duniya kin taɓa ganin uwar data haifa "yarta tace bata santa ne....? Ni ina so ne ki goge da rayuwa ke ɗaya , ki kuma iya haɗiyar baƙin ciki da magance damuwa dan ki zamar da kanki garkuwar rayuwarki. Domin idan yau ina nan gobe bana nan , yadda kike ke ɗayan nan babu abokin shawara ko na bar duniya barakiji wahalar rayuwa da kowa ba. Ina so ne kawai in auno iya girman soyayyarki a zuciyar mijinki. Na gani kuma ni nasan yana sanki dan nayi masa wani abu a abuja. Wallahi nayi tunanin yadda ake faɗar rashin mutunci zaizo ne kawai ya sakeki. Sai baiyi ba kuma nima baimin rashin kunya ko kallon banza ba kamar yadda nayi tunani... Wallahi inajin kunyarki ne , abun nan da nayi muku banyi da nufi ba , yayi ta damu nane banji daɗi ba , shi yasa na fara rubutun neman yafiya kafin mu haɗu dan mashala.Tou dake dashi duk ina san ganinku domin na nemi gafararku , sai kuma kema zamuyi zama na musamman...... sai mun haɗu kafin inyi tafiya_
_Fatima Salis Abbakar {{ Inna }}_
0 comments:
Post a Comment