Hararata yayi yana jinjina kanshi baraki bani ba. A shagwaɓe nace umm² ina maƙale kafaɗa daga kwance. Tou bani ya sake tambaya a karo na biyu da kwantacciyar murya. Kuka na farayi ina cewa nidai ka barmin kayata idan baka barmin ba aradu kashe kaina zanyi..... Hawowa yayi saman gadon a shagaɓe yace baki iyawa. A hankali na juya mishi baya ina shashshekar kukan ƙarya na rufe idanuwana tare da ɗora hannun damana a saman fuskata. Kusa dani ya kwanta ya fara ƙoƙarin cire hannuna daga saman fuskata.
Juyowa nayi da sauri na riƙeshi. Yiyh.... Yaja ajiyar zuciya da yanayin buƙatuwa tare da lumshe idanuwanshi da shauƙi. Wai me yasa ne.... ? Da yanayin matsuwa yace riƙe jigidarki mayi magana daga baya.
A makare na fito daga ɗakina da sauri. Yau na makara ko kalaci bazan tsaya yi ba. Ɗakinshi na wuce yana ta wani tattare²n wasu "yan guntattakin tarkacen dashi buƙatuwar shi ne , a ɗan zumuɗance nace muje na makara fa. Ba tare daya kalleni ba yayi ɗan gajeren tsoki wai ya manta bai faɗamin ba zaiyi tafiya. Cike ɓacin rai na matsa kusa dashi da hannuna na tambayeshi cewa ina kuma zakaje ne ? Nima ban sani ba saina fita , cika idona yayi da hawaye da siririyar murya nace haba Dikko bana baka haƙuri ba ? Shine kuma zaka tafi ka barni ? Riƙe kunnuwa na nayi a dai² lokacin hawayen idona suka samu damar gangarowa a saman kumatuna cewa dan Allah na bari na ƙarasa maganar ina riƙeshi. Tunda na baka haƙuri sai kayi haƙurin kuma ka bari idan na sake sai ka tafi haba Dikko........ Na ƙarasa maganar ina ɗagowa daga jiki nai mishi jigataccen kallo.
Kiyi haƙuri bazan wani daɗe ba. Ya faɗa yana taɓa hancinshi da ɗan yatsa manuni. Nima gaskiya idan ka tafi yau zanji kamar ince ban yafe maka ba , taƙaitaccen murmushi yayi tare da duƙawa yana gyara takalmin ƙafarshi. Ci gaba nayi da cewa tou kafa sani tafiya yau gaskiya shiga haƙƙina ne idan ka tafi ka barni zanji irin yanayin daka faɗamin jiya dan Allah , wallahi idan ka tafi gaskiya zan shiga tashin hankali. Da sauri ya ɗago kanshi ya kalleni da yanayin damuwa yace ke meye haka ? Ai gaskiya na faɗa idan ka tafi fa matsala za'a samu. Riƙeni yayi jikinshi ta baya da kwantacciyar murya yace wace irin matsala ƙaramar yarinya? Faɗamin inji mana yayi maganar yana wasa da gashin gemunshi a jikina. A kasalance nace kawai dai zanyi kewarka , mtsww yaja tsoki dan a yadda na fuskance shi ba haka yaso in faɗa mishi ba.
Rufe idanuwanshi yayi cewa taya ake kewar miji ? Faɗomin da me zaki ibe kewa yayin da kike tunowa idan muka kasance a inuwa ɗaya ? "Yar marainiyar dariya nayi cikin yanayin jin kunya nace Dikkkkoooo. Wata sheɗaniyar dariya yayi mara sauti mai ƙarewa da hmmm An mata kenan , yanzu dai idan na fahimceki kar inyi tafiya ? Ey wallahi kawai muyi zamanmi mu daina faɗa na ƙarasa ina juyowa na rumgumeshi. Me yasa baka san jigidar da aka bani ?
Takawa ya farayi ina kwance a jikinshi har zuwa bakin gado yake cewa. Mace ita gaba ɗayanta ƙyalƙyali ce , da hannunshi ya nuna yana ci gaba da cewa tangaram ne saboda su mata an haifesu ne domin kwalliya shi yasa ana haifarta ake mata huje dan ado. Baki ga komai na mace yasha ban²n dana namiji ba ? Maganarta tafiyarta kallonta sigarta da komai nata ya ban²ta. Tayi ado da kayan ado masu burgewa da ɗaukar hankali kamar zinari saboda yana gyara mata jini. Ko cikin duhu kikaji maganarta basai an faɗa ba kinsan ita mace ce , domin zakiji maganarta da sanyi² cikin natsuwa tako nagarta matsayi da kuma aji. Ha kuma maganar namiji yake. Kalli takalmin ƙafata kinga irin nawa da naki da ban²ci , naku masu ado ne na maza kuma ko oho. Ayi masu wani tsini² a saka musu duwatsu da maɗauri macen kenan shi yasa komai nata yake da burgewa. Ni ina san matana ta kasance mai ado da zobe , "yan hannu , ɗan kunne tsarkar wuya da ƙafa amma tsabar sharri yanzu ba damar mace ta saka tsarƙar ƙafa shike nan an kaita wani wurin daban dan rashin adalci. Hmm itama dai ado da ita wani ɓoyayyan sirri ne. Jigida duk tana cikin kayan ado na mata sirrinta daban ne amma matan bariki su suka sanshi shi yasa sukafi yin amfani da ita....
Mata 10 idan kika tarasu zaiyi wuya a cikinsu kaf ɗin su ki samu mace ɗaya data saka jigida a ƙugunta. Amma idan zaki tara karuwan da suka san kansu suka goge suka kuma daɗe tare da sanin sirrin bariki zaiyi wuya kika haɗa mace 10 ki samu mace biyun da ƙugunta bata ɗaura jigida ba....! Dalilin ɗaurata da sukeyi ni nasani amma bazan faɗa ba. Dalilinsu na sakawa da motsinta ai sunsan abinda take haifar da , kuma nima nasan dalilinsu. Nine dai ke baki isa ki ɗaurata ba tunda bana ra'ayi amma duk abubuwan da kikaji na faɗa a farko idan kika saka wannan ra'ayi na ne har tukuici ma saina bayar. Nidai dan Allah ka barmin abuna in saka , An mata na barki a saka lafiya amma da sharaɗi , tom , karki sakata ki fita , na yadda , duk kuma lokacin da kika buga ƙaraurawar tou fa lallai zanzo kuma kinsan ni bana zuwan banza. Wannan shine idan kin yadda ni da kaina ma zan ɗaura miki ita..... Na yadda , kin yadda ? Ey na yadda , banajin yi haƙuri babu wani wallahi² , jinjina kaina nayi tare da tabbatar mishi da ey na amince. Saukeni yayi daga jikinshi yace ina zuwa , inda ya ajiye jigidar yaje ya ɗauko da kanshi ya zagayamin ita so adadin ruɓin daya ruɓanyata a ƙuguna. Nima na shiga sahun mata masu ɗaura lambar ƙugu.
Yau banje makaranta ba haka kuma Dikko baiyi tafiya ba. Yadai shiga gari. Pa - Pi kuma yana wurin Momy dan tun jiya da yaje yakai ƙara wa Ashiru ? Ashirun cewa yayi suje yakai shi wurin Momy. Shine yakai shi kuma yace a faɗa mana dani da yaya ya fata damu , kuma duk bamuyi cau ba wayyayi. Itama Momyn goyuba bata hatu ba. Shima Yaya baiyi cau ba. Dokin ma shima baiyi cau ba. Itama motarshi bata da cau ta Dady tafi hatuwa. Kuma kada mu sake muma muzo musu gida.
Saida na gama hidimar gida kaf duk abinda zanyi nayi na ƙare sannan na ɗauki wanka na kulle wanka da wani irin kafirarren leshi mai sauƙin nauhi. Nasha ado da duwatsunan wuya kunne hannu da "yan yatsu. { bawai dutse ba no׳ cikin tsarabar da mai gida ne ya kawo na saka wani daga ciki dan burge shi a wannan sansanyar maren sakaliya. } na wani kawo ɗaurina dai² da zamani na kafe wankan dashi. Naɗan yayyafa ruwan turare bawai yadda kamshin zai zama mai cutarwa ba haka kuma bazai tashi zuciyar mai shaƙa ba. Cikin kujera na koma na soke da zama irin na matan masu kuɗi ina ta ƙasaita ni matar Dikko. Wayana dake gefe ta na ɗauka na kira Mai gilashi , cikin sakonnin da bata wuce 30 ba ta shiga , tana shiga ta ɗauka. Bayan gaisuwa nace mata maganar jigida wai meye sirrin ne ? Ke malama wannan jigida da kika ganshi yasha ban² da jigidar da zaki je kasuwa ki bada kuɗi ki siya kinji ? Wannan ɓoyayyar sirri ce kuma bawai na baki dan kije ki saka weldrop kiyi ajiyarta ba , ki ɗaurashi a ƙugunki hajiya kiyi tafiya da isarki.
Halbawarta ɗaya tsallen zuciyar duk namijin daya ji kukanta , adadin buguwar zuciyarshi adadin buƙatuwa , ke wannan jigidar bala'enta yasa sukayi mata suna da huce takaici. Baga namiji ba har kishiya saita shafa miki lafiya , idan uwar naci ce da rashin zuciya taita zama tana haɗiyar baƙin ciki , idan kuma tunburƙuƙu ce wato mai zuciya a maƙoshi filin gidan zata barmiki. {{ miye ribarki idan kin kora wata ? Idan ta tafi ma wata zata zo , itama idan kika sake korata wata rana a kawo wacce kema zatayi out dake.... }} Ma damar dai zaki motsa ? Idan har tayi kuka tou fa lallai ke kasuwa ya buɗe ba gareki ba garemu masuyi domin kasuwanci.
Hmmm amma ni kinaji da farko Dikko cewa yayi baya so fa , dariya tayi tare cewa ɗan duniya wai ko yace miki akan wani dalili ne ? A , a , kawai dai yace bana ɗaurawa danshi wai baya ra'ayin lambar ƙugu. Sake sheƙewa tayi da dariya tace kai kiyi haƙuri amma duniyanci mijinki ya shafe tudun da bakya tunani , yanzu ina jigidar ne ? Ce masa nayi dan Allah ya barmin ina so , shin ya baki ita ne ? Ya bani mana gashi a ƙuguna ɗaure. Taf lallai kam Sultana sannu da ƙoƙari. Yawwa na faɗa ba tare dana sake magana ba ita kuma taci gaba da cewa. Baice miki komai ba bayan haka ? Ni baicemin ba ? Karfa kiyi ƙarya ? Ai kinsan ni ƙarya ba ɗabi'a na ne ba. Ki ranste baice wani abu ba , Mai gilashi kinsan bana san ayi ta tsayuwa a magana ɗaya mu matsa gaba ko macimma matsaya. Gaskiya sirrin irin jigidar nan rufaffen sirri ne , buɗeshi da sanin matsayinshi sai tuɓaɓɓin mata. Mafiya yawan maza dubu a cikin ƙaso miliyan zaiyi wahala ki samu namiji dubu dake ra'ayinta , domin ɗaurata cikar duniyanci ne shi yasa mafi'akasari mu matan bariki ne mukafi amfani da ita. To ke me yasa baraki sakawa naki ba idan dai harshi mai ra'ayi ne domin gyara adonki da burgewa. Sarƙa "yan kunne zobe da ɗan hannu duk domin mata akayi su , shin "yan hannun basa ƙara ne ? Ke kanki da kika saka shin ya kikeji kanki dan Allah idan suka motsa ? Mata masu hikima sune suka san yadda abun yake badawa , amma iya ado dasu sai jajirtaccin mata masu duniya , ƙasaitacci bugun farko a filin sanin sirrin rayuwar zaman takewar aure.
Idan dai har ke mace kinsan damarki da haggu bazakiyi sake ko sakaci da ado ba. Kaso casa'in na mata , auna sauke min gashin kansu kiga yadda suffarsu zata zama ? Amfanin wanka da ma'anar yinshi ya tattara a wurin mu da mukeyin shi. Idan har mace ta sauke gashin kanta domin rashin buƙatuwarshi idan har ta haɗa da girarenta wane suna mu zamu kirata dashi ? Duk da dai cewa gaban rigarta ya turo. Zuwan farko ba'a kallon structure saidai a kalli yawan ado da wanka. Buƙatar duk data barki barin gashin kanki da gyara , gyaran gira a duk ƙarshen mako ko wata dalilin ne ya kamata yasa ki kasance cikin ado da kayan ado masu burgewa. Misali , macen data bar gashin kanta bujur² bata tajewa ba kitsawa da banbanci da wacce ta gyarashi , wacce ta kitsashi kuma fitar ainahin kyawun fuskarta yafi na wacce ta taje ta barshi a kunce , matsayin "yan kunne da rashin su a jikin mace tamkar ƙururrumar buta ce mara murfi. Kallo ɗaya zakiyi mata ta baki kyankyami ko amfani zaki da ida tou zakiyi shine ba cikin natsuwa ba , kema kanki idan kikayi baƙon kunya kinajin kunyar bashi ita yayi amfani , tou haka macen da babu ado matsayinta yake a wurin mijinta. Gugar zana , fushi ga masu ɗabi'ar riba ga masu ɗaukar gyara.
Idan baki manta ba kwanaki na fara baki labari akan naje asibiti ranar da muka zo gidanki dasu Hadiza ko ? Umm , yawwa tou tsaya kiji kaɗan daga ɓarnar jigidar Mai gilashi. Tunda na ɗora idona akan Alhajin da muke zaune a gidanshi raina ya biya dashi , duk wata alama da akeyi nayi mishi ɗan iskannan yaimin taurin kai. Gadai yadda abun yake.....
Banda murƙushe² babu abinda Mai gilashi takeyi. Lokaci bayan lokaci ita Hadiza takan ce mata sannu , haka suka kasance a asibiti har layin ganin likita yazo kan Mai gilashi. Tunda ta miƙe ta fara tafiya hankalin duk wani mace ko namiji dake wurin saida ya kallonta har ta shiga inda zata ga likita , tunda ta maida ƙofa ta rufe bayan ta shiga taci gaba da bada tako jigida taci gaba da kuka , wuri ta samu ta zauna inda marasa lafiya ke zama domin shi likita yayi miki "yan tambayoyi dan gano damuwarki. Tana zama jigidar ta bada wani zutt² domin dai²tuwa kamar yadda mai sarrafata tayi.
Kiran sunanta likita yayi bayan ya kalli fayil inta sannan yayi ɗan rubuce² yake tambayarta abinda yake damunta ? Ciwon sha'awa shine amsar data bashi , ummm ? Ya sake tambayarta a karo na biyu , a ɗan yatsine ta sake cewa ciwon sha'awa nace maka , kallonta yayi tare da cewa ban fahimta ba ? Kauda kanta tayi gefe cewa kai likita ne ko kuwa dai ? Meya sameki ne ? Nadai fahimce ka kanajin daɗin kalmar nan kaji , sake maimatawa tayi , shiru yayi bai sake tambayarta ba , ita kuma ci gaba tayi² da maimaitawa cike da iskanci. Hajiya ai naji , yawwa wai idanma bakaji ba dan dai kasan nidai bana gaji da faɗa ta ƙarasa maganar tana faɗar kalmar sha'awa. Rubutu yayi a fiyel ɗin sannan ya rubuta mata magunguna yace ta ɗauka taje ta siya....!
A malam likita da sauri haka har ka gano ciwona ? Bayan kuma ni banyi maka bayani ba ? Ɗauka ya faɗa a ɗan ɗaure. Taɓa takaddar tayi tare da dafa hannunshi da yake turo mata cewa idan kuma ban ɗauka ba fa ? Sai kici ƙaniyarki , murmushi tayi tattare da salon yaudara tace saidai kai kaci min ita , ta faɗa tana masa kallon saka shi a tarko take ci gaba da cewa ka taɓa ganin inda aka yanka ka kaci kanka kuma bayan ka mutu ? Adireshin gidanta kawai taci gaba da faɗa mishi tare da ɗaukar biron gabanshi ta juya takadar daya rubuta mata maganin ta rubuta lambar wayarta , sakaran likita mai zubar da abinci a tsari. Tana faɗin haka ta miƙe ta fara tafiya , jigida kuma taci gaba da tsuwwa , kamar wani gelele haka ya bita da kallo , saida tazo bakin ƙofa tace ai nasan maganin ciwona ɗan raini , bana muradin shan maganin saidai in shanye mai rubutawa. Harararshi tayi irin ta kwaɗayi sannan ta riƙo saitin jigidarta ta kakkaɓa mishi , wani irin ihu tayi cocas casss chuss , na barka lafiya ta fice daga ofishin.... Dariya yayi bayan Mai gilashi ta fita tare dayin ɗan gajeren tsoki yana jinjina ma lambar iskancinta...... A maimakon abinda ya kawoni saina ɓige da karatun ƙarya domin amfani da wata manufa sai nabar waccan buƙatar nayi amfani da wacce ta samu. Likita ya biyoni kuma na ƙaddamar dashi a jam'iyata.
Alhajin da muke gidanshi kuwa , can wurin gantalina na ganshi ya rumgumo wata tsohuwar mace. Matsalar gidanshi shi matarshi ma'aikaciyar gwamnati ce , bata da lokaci da safe da dare kuma tana bacci. Ba'ayin wata shaƙuwa sai weekend. Idan ɗan abu yasa tayi masa sai tasa a kira mata ni , inzo inyi mata kaza². Ɗan sharomin ɗakin Alaji fita zanyi na makara Office ? Ɗan dafa mishi tea da Allah na dawo a gajiye , idan na dafa zatace ɗan miƙa mishi ya cika tsattsafa. Tsayayyen namiji ne mai ji da kuzari , yana da shekaru kusan hamsin da "yar ɗoriya amma nidai a hakan yayi min wallahi. Ina buƙatarshi , karo na farko nace masa Alhaji zan baka jikina wurin E yane idan dai har zaka iya jurewa har gari ya waye. Ka more ƙuruciyata da tsufanka ni kuma in more da dukiyarka. Yamin wulaƙanci ya korani.
Shine dana ganshi da wata mace a hotel naje wurinshi nace masa Alaji wai miye banyi ba ? Sirrin da akayi da ɗaki ai ya isa ayi da tsakar gida. Bai bani amsa ba ya wuce sha'aninshi. Wata rana ina gyaran ɗakinshi ya shigo dan gaskiya yayi faɗawa matarshi akan ta daina tura mishi ni ɗakinshi taƙiji , ina gyaran gado ya shigo zai wuce toilet , aiko na bishi ina cewa ina ne zakaje haka ? Ka tsaya in raka ka..... Shigewa yayi ya kullo ƙofa. Da gudu na fita na nufi sashinmu.
Jigida ta na ɗauro na dawo , daga nan na fara ɗanashi a tarko shima , dan gaskiya da bana ɗaura jigida a gida sai zan fita saina gane ashe duk inda ka kasa kasuwarka siya akeyi saidai idan baka baza abun siyarwa ba. Ashe da wauta nake ƙoƙarin jibgawa rashin saka hannun jari a gida dan na fahimci rashin ɗaurata a gida yin hakanan babban kuskure ne , tou jigida ce ta ciwon ɗan wasa a gida. Tun yana ɗan satar kallona har ya fara dogon kallo. A falonshi dai in goge tv na sakar mishi zani. Shikenan nan fa muka riƙa ɗauke wuta tare , tana can tana bacci ya kulle mata ƙofar ciki ni kam ya buɗemin ta baya naje mu shige bargo ayi dani ba matar gida ba , maganin macen da bata taya miji bacci kenan.. Tun daga wannan ranar nayi saving nashi a alminjar na jawo banza izuwa cikin duniyar rayuwata. Kashi saba'in na kuɗinshi nice nake cinye kaso arba'in , matar gida taci goma mijina yaci biyar Alhaji da sauran matan waje suyi maleji da sauran. Karatuna motar hawata kuɗin mai da duk sauran buƙatuna shine abu a sauƙi fa dare da yawa na ɓata kafin na taka babban matsayi. Malaman makarantarmu suma dai muna ɗan rage yinin karatu a ofisoshinsu. Na samu kuɗi wannan harkar fiye da yadda bakya tunani Sultana amma dai matsalar har yanzu ko gwamna ban samu gani ba , bayan kuma naji ance manyan karuwai gwamnati tasan da zamansu. Ashe ban sani ba farashin karuwanci yanzu ta faɗi har haka ƙasa wan²r. Tirr da karuwancin zamani marar digi wallahi. Karuwan wancan ƙarnin su sukaji daɗin karuwanci banda karuwan yanzu da gwamnati take ma hassada , a iya a hasko ka a talabijin domin a bawa sauran masu sha'awar shiga karuwanci su shiga da ƙwarin guiwarsu gwamnatin jaha ta daƙile wannan hanya. Jinjina ga gwamna mai kishin jahar sa , mai daƙile gudun tafiyar ɓarna a yankinshi. Allah ya ƙarawa mai girma gwamnan jihar katsina lafiya da nisan kwana...... Irin wannan shuwagabanni muke fatar samu masu daƙilar da ɓarna suyi ƙoƙarin bada ƙwarin guiwa wurin kafuwar ci gaba da ƙoƙarin koyar da ci gaban rayuwar yara masu tasowa , da su gane shi iskanci ba wani riba bane dashi.
Mutanen kirki masu daraja su suka dace da a nuno hotunansu a akwatin talabijin ba mutanen banza ba , na gari sune abun nunawa duniya domin al'umma tayi koyi dasu , tsakanin karuwa da talabijin saidai a nuno hoton shegiya ana zaneta...... Hmmm gaskiya Nana Mai gilashi ina zuwa nayi baƙuwa zan kiraki zuwa anjima idan kuma ban samu kiranki ba sai mun haɗu makaranta.... Ina faɗin haka na ajiye waya inawa baƙuwa barka da zuwa. Bata ansa sannu ba tace ashe yasan baya nan yacemin yana gida ? Mai bin Rabiya ce , kila yana kusa ki kirashi kiji , ina faɗin haka na gaisheta tare da wucewa ciki dan gabatar da sallah magrib.
Dikko shida Pa - Pi ya dawo can ta matsoshi da Momy itama yayo mata yaji , yace itama wayyayi ya fata da ita abincin su ma babu daɗi Momy goyuba ta iya , zagi yayi ta zane mishi baki yace bazai ƙara zuwa ba kuma ko ta ganshi idan tace Pa - Pi zaice ya manta ta. Shi Yaya baya dukanshi. Shine ya tattara kayanshi Dikko yana zuwa ya biyoshi. Tashi na har nayi mata abinda zatayi gulma wa mijina , bayan sun gama tattaunawa tace Dikko kabar matarka ta ɗaura jigida ? Ra'ayinta ne kema kije ki sakawa mijinki. Amma ai baka san jigida yaushe ka fara so ? Da matata ta fara ra'ayin ɗaurawa sai kawai nima naji ina muradi domin tayi farin ciki. Zata sake magana yace dakata da Allah , ke "yar uwata ce matsayinki daban hurimin matata daban. Kiyi magana abinda ya shafeni dake matsala ta gida na ko gyara abinda ya shafeni da iyalina ni ba yaro bane ba nasan abinda ya kamata. Dikko kar kamin rashin kunya kaji ? Ko nayi miki dai ai nasan bana buguwa wurinki. Tou ko dukana zakayi ne ? Haba ina zanyi abun kunya in daki Yayata yayi maganar yana murmushi. Ai da irin haka namiji ke zama mijin tace , ba tare daya kalleta ba yace ni mijin kan tace ne ni. Tana so dai ta suko Sultana Dikko ya tare kuma har sukayi firarsu suka gama ta tafi ita Sultana bata sake fitowa ba.
Cike da farin ciki ya nufi ɗakin An mata. Pa - Pi na kwance wai daga nan yake bawa Mamanshi labari ita dake toilet tana wanka. Shigowar Dikko ɗakin ne yasa yace Yaya zoka nan kaji ya nuna mishi kusa dashi , naƙi inzo ba cewa kayi ka ɓata damu ba , dokina ma baiyi kyau ba ? Ai sai kayi bacci zan maida ka wurin Momy , ɗan guntun tsoki yayi yana turo bakinshi yace ai babu yuwana da wannan Momyn wayyayi ya ƙarasa maganar yana harara... Tou zo kaji. Saukowa yayi yazo inda yake tsaye , kaje kace ma Ashiru ina gaishe shi. Har ya fara tafiya yace kuma dani jakaje ? Dakai zanje mana kayi zamanka idan ka dawo bazanje dakai ba , can janjauna ce kazo ? Ey mana , kuma Pa - Pi kayyayi facci ? Kayi bacci Babana kanayin bacci ina zuwa sai kawai in saka a mota. Amma wayyayi ban zuwa wurin Momy can gackiya , nima bazanje ba kaidai jeka , da sauri ya fita daga ɗakin yana gunguni.
Lumshe idanuwanshi yayi tare da sauke ajiyar zuciya a wahalce bayan Pa - Pi ya fita. Da gudu na fito daga toilet suuuuuu na taho na shige jikinshi. Murmushi yayi amma bai riƙeni ba yace yarinya ya akayi ne ? Kawai inayin farin ciki na faɗa ina fita daga jikinshi na fara tafiya cikin salo mai ibar hankali jigida kuma ta fara ihu. Rufe ɗakinki yayi ni kuma naci gaba da kakkaɓa ƙugu , shima dariyar yayi yaɗan tako da zamarshi. Dariya na sakeyi tare da hayewa saman gado dan a tunanina ko zaimin cuta ne. Cike da shauƙi shima ya hayo gadon ya riƙeni yana shaƙar iska cike da muradi. Zuƙewa nayi ya sake riƙoni a gajiye ya rumgumeni jikinshi da yanayin ƙuruciya. Wai shi shine nake kaɗawa ganye ko ? Saiya lullusani a daren nan , wannan ƙugun da nake masa ingije dashi zai bani labari dan masu garinmu.....
A "yan kwanaki biyun nan dai ban leƙa makaranta ba , gida kawai domin yafi min daɗi saboda mun buɗe sabuwar rayuwa da muke raya kawunanmu cikin tsantsar soyayyar da bama san rabuwa da juna. Rabon da muyi faɗa ko wani yaji fushi harya ɓatawa wani rai yanzu mun daina , Dikko ya jajirce yana ta kwatanci da nuniya. Ranshi fes domin duk yadda ya bada saƙo anshewa nakeyi shi yasa yakeyin farin ciki. Mai gilashi ma a gefe tana ta ɗirkako nata bakin gwargado amma duk abin nan dai Dikko bai haƙura da Sharifa ba Dady yana ta tunatar dashi akan muhimmancin auren sati na gaba za'a saka rana , Yusra dai har yanzu babu ruwanshi da ita kuma ta sameshi har G R A domin sasanci a ranar ta auna iskancin da tunda take duniya bata taɓa ganin namiji da irin shi ba , ta tsorata dan bata taɓa ganin aljani akan namiji ba sai a wurin Dikko , saida tayi fitsarin tsaye saboda firgita , tunda ya rufeta ta inda take tura tsiraici shi yasa ta tafi gabanta gaɗi ta kama tuɓe²n kaya , tunda Yusra take a duniya ita bata taɓa ɗana ya namiji yake ba sai akan Dikko taso taji su kuma mazan ya tasu darajar take ? Anan ne fa yayi bakandamiyar shi. Tunda ta samu aka fito da ita dakel saida tayi jinyar fargaba. Wannan Yusra ba ko wace ce ba itace Yusran data ɓata Sadiyya matar Dikko na farko. Kuma ita bata san shi Dikko ya auri wata Sadiya can ba. A jirgi ta ganshi taji ya mata , nan tayi mishi bariki irin namu na mata hardai suka rabu bai bata numbershi ba. Amma da masifa saida taje ta samoshi.....
Jiddah kuwa wuta kawai take sha a gidan Yazeedu. Shidai Dikko yace ba ruwanshi , kuma bazai wani je ko yayi magana wa Yazeed ba , can suje su babbake ba abinda ya dameshi da sabgar gidan kowa dan shima baya so a shiga sabgar nashi gidan bare har a samu damar sawa matarshi ido. Taje ta sakata An mata ta wala abunta , duk wanda ya taɓota zaici ubanshi ne kawai abunshi , amma idan tayi iskanci shine zai bata wahala kuma dare yayi su shige bargo asha soyayya.
Gadon Inna kuwa suma danginta cewa sukayi ai basai an bani komai ba , dan duk abinda za'a bani ni na girmeshi inji su. Basu bani ba ko tayinshi basuyi min ba haka suka sha shagalinsu kuma suje suma kansu sukayi ma. Halima da abiyar zamanta suna can suma suna cuɗa zaman kishi , Halimatu taga ta kanta ɓarowo hannun maza.
Saida nayi sati ina hutun da babu dalili. Ranar da naje makaranta a ranar Sharifa tayo zugar karuwai suka bani kashin bala'e dakel aka ƙwaceni a hannunsu. Mai gilashi itace aka sa ta kawoni gida ita da Farisa. A waje muka haɗu da Dikko shi zai fita mu zamu shiga , fita nayi na nufi wurin motarshi ina kuka. Mai gilashi itama da kalar sherinta ta fito shima Dikko fitowa yayi cikin tashin hankali. Dakel nakejan ƙafa cikin wahaltuwa kamar zan mutu saboda bala'e , muna haɗuwa na kwanta jikinshi ina ƙara yawan kuka na , cikin faɗa yace me ne² ? Da shashshekar kuka nace karuwanka ne ta dakeni , cikin rashin fahimta yace wace karuwa kuma ? Nanfa Nana Mai gilashi ta ɓalle ta fara rattafa sharri kamar an tirke musulmin da yayi ridda. Tana bashi labari jikinta yana ƙyarma shi kuma zuciyarshi tana fin jirgin sama tashi. Dakel ya haɗe yawun ɓacin rai zufa ta tsirgo mishi da yaga jini nabin jikinta. Lokacin daya ɗago Sultana tuni ta some , wannan kenan.....
Bayan wasu shekaru.....
Wancan duka da Sharifa ta gayyato akayi min saida akayimin aiki. Dukan ya janyo min matsaloli , giccewar ɗa a ciki {{ breech }}. Zubar jini mai tsanani daya ƙi tsayawa. Bayan anyi hoton ciki wato {{ scanning }} sai likita ya sanar dasu cewa akwai buƙatuwar yimin aiki na gaggawa saboda placentar ta safko , matsalar bugawar zuciya da sama da yadda ya kamata wato {{ fetal tachycardia }} sannan kuma matsalar bugun zuciyar akwai alamun zai koma ƙasa ga yadda ya kamata wato {{ fetal bradycardia }} duk da ganin cewa lokacin haihuwa baiyi ba , nan sukayi ta allureni da alluran da zai taimaka lafiyar ɗan kafin ayi aikin. Suka kuma shirya sanya baby a kwalba da kuma ci gaba da yi mishi wasu allurai har zuwa wani lokaci saboda l b w ciki wata bakwai. Satinmu shidda a asibiti aka sallamemu muka dawo gida da wani ɗan magen yaro suka haɗomu da wanin zanin raino mukai ta fanan goya yaro ta gaba daga ni har Babanshi. Pa - Pi kuwa tunda yaga wannan ɗan mitsitsin ɗa ya daina ɗagama gidan ƙafa koda wasa. Ba'ayi taron suna ba wannan umarni daga mai gida yaro yaci sunan Baba Binna muna kiranshi da Khalifa.
A ranar da sukayimin dukan kuwa Dikko a wurin ya barni ya shiga mota cike da ɓacin rai ya tafi neman Sharifa. Mai gilashi da taimakon wasu daga cikin yaranshi suka tafi asibiti dani. Duk wanda yaji bana lafiya acan ya sameni kafin wani lokaci duk wani ɗan uwan Dikko ya bayyana idan dai yana kusa. Dikko kuwa ya nemi Sharifa harya gode Allah bai ganta ba , ita kuma daƙiƙiyar taita kiran Mai gilashi. Ƙarshe Mai gilashi cewa tayi Malam yace da zaiyi mata aiki amma daya buga ƙasa ya gano ta taɓacin amanar wata aminiyarta , wani attajiri ɗan siyasa yazo auren ita aminiyar ke kika rufe ciki wai haka yace , shine nace shin ko kin gane ko wace ce ? Iyakar tunanin Sharifa ta kasa hasasowa. Mai gilashi tace tou daƙiƙiya wannan ba ko bace nice..... Kuma nice nan na shirya komai ta yadda kika gani na rusa miki wannan auren jaka , tunin duniya nake ƙufule dake yadda kika hanani ci ga kaiwa ga nasara tunda naji kince SAI KIN AURI D ' K nace ma zuciyata idan dai ta bari kika aureshi saina rabata rayuwa da gangar jikina. Nice nan na ɗauki nauhin komai na shirya na kuma gabatar , idan kika sake kirana zan saki sauran hotunan wa duniya naki kamar yadda kema kika ɗauki hotuna na da nake a gurɓataccen yanayi kika samu nasara wurin ganin kin hana auren. Kin hana nawa kema na hana naki 1/1 sai kuma kin sake , idan kuma kika sake kirana saina shafe farin ciki daga rayuwar ahalinki tana faɗin haka ta ajiye waya.
Shi kuma a ranar har dare yana gidansu yana yayyafa ruwan rashin mutunci , waishi ko shi baya dukan An mata tunda ta samu ciki. Shine aka samu wata tsagera taje tayo gayyar ƙatti ? Waishi maza zasu dakar mishi mata ? Da ciki aka dakar mishi mata ? Har dare yana can yana abu ɗaya , Momy tace a fitar dashi ta daina ganinshi , wannan riƙo da akayi mishi da zumar lallashi shikenan ya birke ya fara sai kashe , waye yace wai a riƙe shi ne ? Yace baya so ana taɓashi kaza². Shikenan fa ya mimmiƙe ko za'a tashi duniya saiya ramawa An mata dukan nan bazai yadda ba , wai ko an faɗa musu jakace matarshi ? Sai ayi mishi abu dan cuta idan kuma yayi magana sai ace bashi da haƙuri , tou saiya rama kuma bamma gajiya duk wanda yayi mata sai yayi mishi ko waye kuma ko wacece............. Daga nan ya ɗauke.
Dady kuma tara su Ashiru yayi yace gaba ɗayansu sun cuceshi sun kuma munafurceshi. Me yayi musu sukayi mishi haka ? Bayan su sukace mishi Babanshi ya warke ya haƙura ya daina neman magani , me yasa² ? Me yasa sukayi mishi haka ne ? Wannan ce soyayyar da suke bugun ƙirji cewa suna iya bawa Babanshi fansan rayukansu ? Karo na farko daya ga cin amana zahiri. Ba kuma zai sake yadda da kowa ba. Haƙuri Ashiru ya bashi sannan ya buɗe mishi gaskiyar lamarin yadda yake cewa.
Rashin lafiyar da Mai gidansu yayi bayan ya samu sauƙi. Sun faɗa mishi abinda Mustapha yace , amma sai kuma wata matsala dashi dai Mustaphan yace. Wai asirin da mutum yaci a abinci da wanda mace tayi "yan maƙale² dashi a jiki ta kwanta dana miji wannan asirin wahalar fita gareshi wallahi. Cikin magungunan dashi Al ' Ameen ya bawa Sadiya da sunan taimako yace wannan na kayan mata ne , shine taje tayi amfani dashi kuma shi Al ' Ameen ya bawa Mai gida magani a london , sanin manufarshi da aikin maganin bamu sani ba kuma shima Mai gida bai sani ba , wannan dalilin ne yasa yace yaso ya haɗu da Al ' Ameen akwai tambayoyin da zaiyi mishi. Gadai asiri an fitar na fili amma na jiki bai daina tasiri ba , ganin bai warke ba yasa yace kawai bara ya haƙura da Hajiya yaci gaba da sabgoginshi dan yasan bazata yadda ta sake zama dashi ba , a ranar daya bar gidan gwamnati ya koma gidanshi lalurar ta tasoshi a gaba , daga nan ne ya tafi jinya bayan ya dawo ya ƙarƙare aurenshi da Hajiya Jiddah yace itama Hajiya Sultana zai jira yaji me gidansu zasu ce. Shidai Allah ya sani shima yasan tunda yake a duniya rayuwarshi bata taɓa san wata mace ba wallahi sai a kanta.
Akanta ya san soyayya kuma akanta ya farayi ma shaƙuwa kuka , itace macen farko daya sa hannu ya daka a duniya wacce bata gidansu ba , kuma itace mutum ta farko data ɗaga hannu ta mareshi , yace shi a gidansu wallahi baisan wani abu da ake kira duka ba , tayama za'ayi tunanin dukanshi bayan kowa sanshi yake amma zuwanta rayuwarshi yasa ya anshi hukunci mari daga iyaye , itace macen da ta ɗaukeshi kamar wani sa'arta kuma bata iya zuciya dashi. Shine yace a yadda suka rabu yasan har abadan duniya ta gama dashi ashe ba haka ba. Yayi alƙawari har abadan duniya ya gama aure zai jira daga gidansu ita Sultana ayi magana kawai zai haƙura da ita , yasan babu uwar da zata haƙura tabar "yarta ta zauna da shi da kuma lalurashi. Yayi kuka shi da kanshi yaji tausayin kanshi.
Kamar ya haƙura amma ya kasa. Duk abinda yakeyi zaiyi zuru yana tunani , idan zaici ko zaisha zaiyi murmushi yace ko a wane hali kike ? Ya shiga ɗimuwar rayuwa da zaucewa ganin zai ida warwarewa yasa yasha ta dubu ya tafi gidansu bayan ya fara tura Abbakar. Bayan ya dawo da itane yake faɗa mata ya warke dan abinda yasa ya ɓoye mata kila idan tasan har yanzu yana da damuwa bara ta zauna dashi ba.
Sa hannun masu sa hannu a ciki Ashiru ya faɗawa Dady , Bilki yasa aka kira mishi tana zuwa ta fara zazzaga rashin mutunci. Wai ita zai tirke ? Tou tayi taje tayi yayi maganinta , ta fara azaƙaƙura rashin mutunci nan fa gida ya ruɗe aka fara tone²n asiri , Dady yace Bilki sai ta bar mishi gida , "ya "yanta suka fara kuka Dady zai tona musu asiri. Ita kuma cewa takeyi su daina kuka ya saketa, saboda mahaukacin ɗanshi zai tara yaran Dikko a gabansu yaci mutuncinta ? Har nawa ma Dikkon yake ? Wato shi tunda baya nan bara yayi a gaban yaran Dikkon idan shi Dikko ya dawo daga duniyar ɗimuwar rayuwa su bashi labari yaji daɗi.
Har tsakar dare ana abu guda Momy ita kuma tana cewa sai an warkar mata da ɗa wallahi. Kuma shi Dady karma ya kuskura ya saki Bilki dan wallahi bata riƙe mashi "ya "yanshi , Dady yace ko bata riƙesu shi ya isa ya kula da rayuwar yaranshi. Har Dikko ya dawo ba'a gama faɗa ba , shine ya bawa Dady haƙuri akan kar yayi saki wa Aunty Bilki , Dady yace tou kinji haƙuri yake bani akan ki duk ke kinyi masa abu na rashin kyautawa. Cewa tayi wallahi idan dai akan Dikko zaiyi haƙuri ya zauna da ita wallahi ta haramta zaman aurenta dashi , nan suka sake buɗe sabuwar rigima Dady yace saboda Babanshi yayi haƙuri rigima dai da tashin hankali har aka rabu , ita bata zama albarkacin Dikko saboda bata ƙaunarshi kuma sai ta kashe Dikko ta ɗauki alƙawari a gaban Dady , dariya Dikko yayi cewa inma ki kasheni ko ki fasa lumfashi yana wurin Allah sai lokacin daya so zai tsinkeshi. Shawara ɗaya zan baki kidai bi sannu domin ni ko hassada mutum ya cikamin saiya lalace......
Jiddah ta ladaftu domin Yazeed ya zabga mata bulalar saki mai ɗan bara'un zafi. Tayi iya ƙoƙarinta a koma G R A da ita amma ina ? Nima na rama maganar data faɗa a lokacin aurena nace nima G R A nawa ne ni ɗaya daga ni sai yarana. Umar Faruk {{ Pa - Pi }} Aliyu {{ Khalifa }} DIKKO {{ Junior }} Maryam {{ Ummie }} sai ayarin gidanmu da kuma wanda naso nima nace mata Dikko nawa ne ni ɗaya. Bata ga Sharifa ba da tace SAI TA AURI D ' K yadda ta ƙare ? Taje tayi haƙuri tayi maleji da Yazeedu. Dole ta lallaɓa ta koma gidanta kuma ya rage iskancin hanaci masa abincin gida saidai shine yake auna musu kamar "yan boarding.
Mai gilashi ta rabu da tsohon mijinta tana Abuja tana aure sa'ar rayuwa dabance , wato duk iya iskancin mutum idan Allah yaso mishi jin daɗi saiya shiryar dashi.
Halimatu dai ƙanwar Hadiza bata samu kwanciyar hankali ba saida tayi waje road da ita ga miji ya samu ƙarin matsayi a wurin aiki. Ta dafe kan mijinta ram an shiga lugudan wuta.....
Amisty Mardiya Hafsa Aunty Suwaiba kowa tana can tana ansar wuta dai² da irin rayuwar data aikata a zamanin ƙuruciyarta , duk wadda bata mori rayuwar ƙuruciyarta da kyakkyawar ɗabi'a ba ƙarshen faɗan tayi makauniyar ƙarshe.
Sharifa dai har yanzu ba'a samu anyi aure ba. Ita dai Mai gilashi ta haye ta ibi filin abuja suna can sunacin duniyarsu. Tacemin kila dai tana da rabon a nunota a talabijin tunda ta auri ɗan siyasa nikam nace mata kila dai aljannun shiga talabijin gareta.
Jamila Musa gareki jinin katsinawa.
Tam Alhamdulillahi Hajiya Maryam ko nace Hajiya Sultana. Duk dai baki faɗa mana shin Mai gidanki ya warware ko har yanzu yana ta faɗar saina kashe ki........ *Sultana:•* Murmushi ni harma kin bani dariya , gaskiyar lamari Mai gida Dikko dadai sauƙi ba kamar cancan baya ba , dan mafi akasari saina ɓata mishi yake wannan ihu kuma ai kinsan yanzu ba'ayi. Gulmar Dady kukeyi ko ? Inji Pa - Pi tou bari in kirawo shi , ɗage kanshi yayi tare da cewa Ya.......................Ya........
Abun arziƙi ai yayi bari kiranshi kar yazo ya karkashemu muma a bar mutanen Qerau da jimami.......
Alhamdulillah
Masu biye da labarin kwarata anan ne ubangiji ya bani ikon dakatawa. A madadin duk wani bakatsine ko ina yake a faɗin duniyar nan muke ma duk wani daya karanta littafin kwarata fatan alkari domin nuna muku halakci da kara irin namu na katsinawan Dikko. Kai har wanda bai karanta ba kyakkyawar fata da dubun gaisuwa ta musamman data fito daga yankin jihar katsina,
Jinjina da gaisuwa gareku Kanawan dabo tunbin giwa , saƙon gaisuwa da jinjina a gareku mai kyau albarkacin Umar Sanyi.
Alhamdulillah.
🔚
Rubutawa.
*JAMILA MUSA QERAU....*
14/02/2020
Na barku lafiya. Cike da kewarku , sai Allah mai kowa mai komai ya sake haɗamu idan muna da rayuwa a cikin labarin *ƁOYAYYAR SOYAYYA...*
Allah y biyaki muna tare dake
ReplyDelete