π»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI..!
*1*
~~~" _*LAMIDO*_ yanzu wai shikenan idan katafi mun rabu kenan ba zamu sake ganinka ba? Kai gaskiya wallahi zamu yi missing dinka bama ni kadai ba harda sauran students domin kowa yana amfanuwa dakai"
Wannan shine furucin da wani matashin saurayi yayi daidai lokacin da suke zaune a farfajiyar hotel din _Zango hotel_ acikin garin yola babban birnin jihar yola ta arewacin Nigeria,
Wanda aka kira da suna Lamido yana sanye cikin bakar t shirt mai gajeren hannu tareda blue din jeans, hannunshi daure da agogon azurfa na _Rolex_ ,farine tatas dogo marar kiba, yana da manyan idanuwa masu shape din kwai, gashi da dogon hanci kamar biro, lips dinshi jajaye ne masu dauke da dan madaidaicin bakinshi, ya dan aje saje a fuskar tashi, gashin kansa kuwa kallo daya zaka yi masa ka gane cikakken bufulatani ne gaba da baya domin sumarshi akanannade take yalo yalo tamkar yana yi mata shanfo,
Zamanshi ya gyara akan motar da yake wacce ta kasance red colour kirar BMW,
Fuska ya dan ya mutsa take dimples dinshi suka bayyana wadanda kusan ko magana yake yi sai sun lotsa,
"Bash ka bari kawai, ni kaina bana son tafiyar nan amma baffa ya dage sai nabar kasar nan saboda wa indai ina tare daku bazan taba shiryuwa ba"
Yafada cikin daddadar muryarshi mai hadeda maganarshi irin ta fulani,
"To kai ya kagani on top?" Bash yace dashi yana kallonsa,
"Bash kenan kana ganin zan iya daina halayyata? Kawai dai aci gaba da addu'a may be zan iya shiryuwar nan gaba"
Yafada yana wani basaraken murmushi,
"Kai dan duniyane Lamido harma wani aci gaba da addu'a?"
"Atoh kai ya ka gani" Lamido yafada yana duba agogon hannunshi,"karfe 10:30 agogon ya nuna dan haka yayi tsalle ya diro daga kan motarshi wacce ajiki aka rubuta *ON TOP*
"Bash muje gida kasan yau baffa zai dawo kuma kasan halinshi da zarar ya dawo ya tarar bana nan fada zai hau yi"
"Ok muje"
Motar suka shiga bash yana gefenshi shikuma yana driving, aljihunshi ya karkace ya ciro kodin yafara sha,
Suna tafe suna shan disco har suka yi tafiya mai dan nisa, gefen titi Lamido yasamu yayi packing ya jiyo yana kallon bash, hannunshi yakai ya dafa mararshi ya rike cikinshi,
"Bash...! Marata tafara ciwo gashi mun baro club a baya" Lamido yafada yana yayyamutsa fuska,
"Kawai kai dai jarabarka ta motsa kawai, fito"
Fita bash yayi ya zagaya bangaren da driver yake zama yana mita,
"Ace mutum kullum bashida wani abu sai jarabar mata?"
Fitowa lamido yayi yana rike da mararshi har lokacin,
"Zanyi maka rashin mutunci, yau kwana na 3 rabona dasu ai nayi kokari"
Zagayawa yayi ya koma kujerar kusa data driver ya zauna yana runtse idonshi domin shi kadai yasan abinda yake ji,
"Yanzu ina muka dosa" bash ya tambayeshi yana tsaki,
"Muje kawai, idan mun shiga cikin gari 11 ba tayiba sai ka kaini guest house dinnan idan kuma 11 yayi sai asan abin yi"
Wuta bash ya kara suka tasamma cikin gari, daf da zasu shiga garin abakin titi kusa da wasu shaguna Lamido ya bude idonshi wadanda suka yi jajur suka sauya launi,
Wata mahaukaciya ya hango takure acikin runfar wani shago ta hada kanta da gwiwa tana sanye cikin wani Pakistan ja riga da wando wadanda suka yi dukun dukun saboda tsananin daudar dake jiki, kanta babu dankwali sai uban tulin gashi wanda yake har gadon bayanta duk da cewar a cukurkude yake gashi duk ya dundunkule harda kasa da yayi ajiki amma hakan bai hanashi sauka akan kafadunta ba,kafarta babu takalmi da gani ta dade tana dauke da wannan lalurar ta tabin hankali,
Cikin wata irin murya lamido yace, "bash wait, kaga wata yarinya can tsaya naje wurinta"
Burki bash yaja ya waiwaya ya kalli inda mahaukaciyar take ya jiyo yana kallon Lamido,
"Lamido me zakayi? Badai waccar mahaukaciyar zaka nema ba?"
Kallonshi Lamido yayi da rinannun idanuwanshi "bash ba kasan yanda nake ji bane, wallahi wurinta zanje tun kafin na mutu..!"
"Lamido mahaukaciyar? Ka kalli fa a halin da take ciki hali irin na kazanta na rashin tsafta, wanda ba lallai ne ma ka iya samun nutsuwar da kake so ba"
"Waya fada maka? *AI RUWAN KASHE GOBARA BA SAI MAI KYAU BA* wallahi zuwa zanyi, bari ma ka gani"
Lamido yafada yana kokarin bude kofar motar, kafin bash ya sake magana tuni har ya fita ya tunkari wurin da mahaukaciyar ke zaune atakure kanta cikin gwiwoyinta.
_*Ummi A'isha*_ππ»
[12/1, 11:00 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA..!*π₯
_(labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga kawata Khadija Sidi_
_2_
~~~ Batare da tsoron komai ba Lamido ya karasa wurinta, ahankali yakai hannunshi jikinta ya dago fuskarta, duk da dattin daudar dake dank'are ajikinta bai hana hasken fatarta fitowa ba,
K'ura mata ido yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta wacce take bud'u bud'u da kura gamida dauda,
Bash yana daga cikin mota yana kallonsu ta glass, kamo hannunta Lamido yayi yana kokarin tayar da ita tsaye, nan suka fara kokawa wadda har shi kanshi lamidon sai da yayi mamakin karfinta amma kuma kasancewarta mai rangwamen hankali shiyasa take da wannan karfin,
Dakyar ya iya murde hannuwanta ya kinkimeta zuwa wani kango wanda yake a baya kadan da shagunan da take zaune, ihu take son yi amma ya toshe mata baki, duk tsananin daudar dake jikinta bata sanya Lamido jin kyamatarta ba gashi dan gayu mai mutukar class amma haka ya iya hada jiki da ita,
Kusan awa guda cif lamido yana manne da ita, wata irin runguma yayi mata yana kallonta duk jikinshi zugi yake masa saboda yakushin da ta yiyyi masa gashi faratanta zako zako suke,
Tashi yayi yana gyara belt din jikin jeans dinsa yana kallonta kwance shame shame ko motsi ba tayi, daga ganinta bazata haura shekara 25 ba sannan har acikin ranshi yasan ya sameta a matsayin cikakkiyar budurwa domin shine namiji na farko da yafara rabata da *MARTABAR TA*,
Kinkimarta yayi ajikinshi ya nufi inda ya daukota da farko, sam shi baiji wani warin dauda ko karnin dauda atare da ita ba amma kuma gata nan dak'a dak'a, shinfidar da ita yayi ya tsaya yanata kallonta wanda shi kanshi bai san dalili ba,
Yana nan tsaye yana kallonta bash ya cika masa kunne da horn dole ba dan yana soba ya juya da niyyar tafiya har yayi taku daya biyu ana uku ya tsaya ya jiyo da sauri yazo ya kama dan yatsanta ya cire wani zobe dake jiki na bakin karfe yayi jifa dashi ya zare wani a karamin dan yatsanshi na azurfa wanda aka rubuta L ajiki ya saka mata a babban dan yatsanta,
Tashi yayi da sauri ya karasa wurin bash ya shiga suka tafi, kwantar da kujera Lamido yayi yana fitar da numfashi ahankali yana kallon hadirin dake gudu a sama ta cikin glass din motar,
"Gaskiya Lamido sai yau na tabbatar da cewar kai marar imani ne, in banda rashin imani da rashin tausayi ta yaya mutum zai samu mahaukaciya wacce tunaninta ya gushe har ya tara da ita"
Ya jiyo muryar bash yana fada, jiyowa yayi ya kalli bash,
"Bash bazaka gane bane, wallahi ni kaina tabani tausayi kwarai saboda bakaga yadda ta rinka kokarin hanani abinda nayi niyya ba amma takasa, banyi haka da niyyar zalunci ba, kawai dan babu yadda na iya ne"
"Wai kai ko warin da jikinta yake yi bai hanaka sukuni ba?" Bash ya sake tambayarshi yana kallon titi,
Shiru yayiwa bash bai amsa mishi ba saboda shi kadai yasan irin abinda yakeji yana ratsashi domin bai taba jin irin wannan yanayin ba sai yau,
"Lamido ka dade kana bin yaran mutane kana lalatawa ashe abin naka bai tsaya a iya nan ba har mahaukaciya zaka bi"
"Bash shifa *RUWAN KASHE GOBARA* nafada maka basai mai kyau ba, rashin mafita ne yasani bin mahaukaciyar nan,sannan duk yan matan da nakebi ai da yardarsu ne ba fyade nake yi musu ba, wannan mai tabin hankalince kadai nasan na taba yiwa fyade tunda uwata ta haifeni"
Jinjina kai bash yayi yaci gaba da driving daf da zasu shiga kwanar gidansu Lamido ruwa ya kece kamar da bakin kwarya,
Hankalin Lamido ne yatashi sakamakon tunowa da yayi da wannan mahaukaciyar,
"Bash ka juya mu koma mu dauko yarinyar nan, wallahi nasan nayi mata illa, na illatata bash, nayi mata abinda ba zata iya kare kanta daga dukan ruwan nan ba, idan bamu koma mun taimaketa ba ruwan nan akanta zai kare gashi da alama yau sanyi za ayi"
Lamido yafada cikin tashin hankali gashi muryarsa har rawa take amma hakan bai hana kyawunsa sake bayyana ba,duk maganar da zaiyi sai kumatunsa ya lotsa,
"Gaskiya nifa kafara takura min, yanzu sai mun sake komawa?"
Jijjiga kai Lamido yayi,
"Idan ba zaka koma ba bani motar ni nakoma,bazan iya kyaleta acikin wannan yanayin ba, gashi wani irin zazzafan zazzabi nakeji yana neman saukar min ajikina"
Dole haka bash yayi ribos suka juya, kwanciya Lamido yayi akan kujerar yana dan karkarwar sanyi domin zazzabi yafara rufeshi, tunanin mahaukaciyar yarinyar nan kawai yake yi sai dai yabarwa zuciyarshi nishadin da yaji agame da ita,
Saboda gudun da bash ya sharara basu wani jima ba suka karasa wurin lokacin har ruwan yayi yawa,suna isa wurin suka ga wayam,
Zazzabin dake jikin lamidone yaji yasake tsananta, zuciyarsa ce tafara dukan uku uku saboda ganin yarinyar bata nan.
_*Ummi Shatu*_π
[12/2, 2:15 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA..!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_3_
~~~Wata irin faduwar gabace ta addabi zuciyar Lamido gashi zazzabin jikinsa ya tsananta tamkar wanda ake karawa,
"On top yarinyar nan fa bata nan may be tayi wani wurin" bash yace dashi yana kallonshi,
Fuskarshi ya yamutsa wanda take kumatunsa suka lotsa ya tashi daga dan kwanciyar da yayi ya juyo yana kallon bash,
"Bash bari na leka waje ko wancan kangon ta koma" Lamido yafada yana kokarin bude kofa,
Rikoshi bash yayi yace "haba Lamido da wannan ruwan zaka fita alhalin kuma kace zazzabi kake ji"
"Bari nadubo kawai" Lamido ya fada atakaice ya bude kofar motar yayi waje ruwa yana dukansa, kangon da yakaita dazu ya hara amma koda yaje babu alamun mutum aciki haka ya dawo yanata dube dube ruwan sama kuwa sai laftarshi yake yi,
Cikin motar ya koma duk yagama jikewa nan sanyi yace muje zuwa, kakkarwar sanyi ya shiga yi sosai tamkar mazari,cikin rawar murya yace,
"Bash dan Allah muje mu dan dudduba hanya ko tafiya tayi"
Batare da bash yayi magana ba yafigi motar suka tafi amma har sukayi tafiya mai nisa titin babu kowa hatta abin hawan dake wucewa ma tsilla tsilla ne saboda dare yayi,
"Kaga Lamido yarinyar nan ba ganinta za muyi ba kawai mu hakura mu tafi gida"
Kada kai Lamido yayi yana rawar sanyi yabi duk ya kankame jikinshi, heather bash ya kunna acikin motar take motar ta dumame da dumi amma Lamido shidai har lokacin kakkarwar sanyi yake yi.
Misalin karfe 12:00 suka isa gidansu Lamido, har barandar side din Lamido bash ya kaishi sannan ya fita ya tafi da motar zuwa gida,
Yana tafiya yana dafa bango har ya shiga bedroom dinshi wanda yasha kyawawan furnitures komai agyare limbis, heather ya kunna ya cire rigar jikinshi da jeans dinshi ya saka kayan sanyi riga da wando red colour masu layi layin blue ajiki,
Kan katon gadonshi yaje ya kwanta ya lulluba da bargo nan kuma yafara tunanin mahaukaciyar dazu, hannuwanshi yafara shafawa sai radadi wurin data yakusheshi yake yi, wurin yayita bi yana tabawa har su wuyanshi duk ta daddaye masa fata,tausayinta yaji yana shigarshi,
"Yanzu shikenan yarinyar nan narabata da darajarta wacce Allah ya halicceta da ita, na cuceta gaskiya, na rabata da abinda yafi komai daraja awurinta kuma ba acikin hayyacinta ba" yafadi hakan acikin ranshi,
Juyawa yayi ya rungume pillow yana tuno kyawun surarta domin bata da maraba da buzuwa duk yadda akayi ta hada iri da buzaye domin tun daga kan gashin kanta har zuwa hasken fatarta duk irin na buzaye ne, ko daga wanne gari tazo nan oho Allah ne kadai yasan daidai.
Kasa bacci Lamido yayi sai wani uban zazzabi da ya rufeshi take yafara fitar da numfashi mai dumi, yana cikin wannan halin har asuba tayi bai iya tashi ba sai lokacin ya samu bacci ya daukeshi.
Har 9 lamido yana kwance adaki yana bacci jikinsa zafi zau da zazzabi,
Cikin bacci yaji ana tashinshi,
"Lamido, Lamido!"
Ahankali ya bude idonshi, mahaifiyarshi ya gani tsaye tana dubanshi,
"Innah,karfe nawa yanzu?" Yafada yana kokarin tashi amma jiri yake ji sosai,
"Yanzu karfe 10 Lamido, baffanka yana jiranka shiru baka zo ba"
Komawa yayi ya kwanta, "innah banida lafiya zazzabi nake yi" yafada yana yamutsa fuskarshi,
"Shiyasa fa naji jikinka da zafi, sannu bari naje na fada masa"
Tashi tayi ta fita yana ganin fitarta ya dauki wayarshi ya soma kiran bash, yana dagawa yafara yi masa magiya,
"Bash dan Allah kaje ka dubo min wannan yarinyar, wallahi jiya da ita na kwana araina"
"Wai meyasa ka damu da yarinyar nan ne? Haba Lamido dan Allah ka manta da ita tunda ka rigada ka samu abinda ka nema agareta, shikenan kawai awuce wurin"
"What?" Lamido yafada cikin daga murya,
"Haba bash idan nayi haka wallahi Allah bazai barni ba, dole ne na nemo yarinyar nan na nemar mata lafiya nabata dukkan farin ciki na rayuwa"
"To Allah yasa asameta" bash yace dashi,
"Amin, idan zaka zo ka taho min da kodin, dan Allah bash kayi dukkan kokarinka ka nemo min yarinyar nan ayau"
Kashe wayar yayi yafara neman number din wani likita wanda ya kasance abokinshi,
Yana dauka yafara yi masa bayanin yanada marar lafiya mai tabin hankali yana son ya hadashi da likitan mahaukata domin samar mata magani,
"Babu damuwa akwai dr na mahaukata yana zuwa duk ranar Thursday kuma kwararre ne insha Allah za adace"
Likitan yabashi amsa ta cikin wayar.
*_Ummi Shatu_*π
[12/2, 2:19 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA..!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_4_
~~~ Tsinke wayar yayi yana murmushi domin daga jin irin amsar da likitan yabashi yasan za ayi nasara,
Tashi yayi da kyar ya shiga toilet yayi alwala ya fito sai alokacin yayi salla, yana zaune akan abin sallar yana tunanin wannan mahaukaciyar, baffa da inna suka shigo,
"Lamido, me kuma ya sameka? Ina fata ba shaye shayen naka da ka sababa kaje kayi ka dauko wata lalurar ba?" Mahaifinsa yafada lokacin da yake kokarin shigowa cikin dakin,
Dagowa da kansa Lamido yayi,
"Baffa zazzabine fa kawai"
"Rufe min baki yaron banza, duk kabi ka gama zubar min da mutuncina agarin nan, baka da aiki sai shan kayan maye da lalata yayan mutane"
Sunkuyar da kai Lamido yayi domin dama ya kwana da sanin zai sha fada awurin baffan,
"Baffa tunda bashi da lafiya kayi hakuri.." Mahaifiyarshi tafara magana kafin baffan ya katseta,
"Ki barni dashi Zaituna,wannan yaron bashida hankali ko kadan, bashida tunani, kullum shi kenan acikin shan abubuwan maye, to ka saurara kaji, idan kaje can turai din ya rage ga naka ka tsaya ka nutsu ko kuma sabanin haka, nidai nagama duk abinda zanyi maka a matsayina na uba,ka duba kaga jiya har 12 baka dawo gidan nan ba kana can kana yawon gantalinka, to duniya dai ta ishi kowa riga da wando, wanda bai zo bama tana nan tana jiransa"
Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga cikin dakin cikeda takaicin halayya irinta danshi Lamido,
Inna ce ta matsa wurin lamidon ta dafa kafadarshi,
"Lamido dan Allah ka tsaya ka nutsu ka daina wannan shashancin kaji, baka koyi da dan uwanka wanda shi ya kasance nutsattse mai hankali, ka zauna kayi karatun ta nutsu kaji,Allah yayi maka albarka"
Tashi yayi ahankali batare da yace komai ba ya hau kan gadonshi ya sake kwanciya ya tukunkune acikin bargo domin wani zazzabin ne yake neman rufeshi.
*
Ahankali ta bude idanuwanta, wurin datake tafara bi da kallo, kallonta ta mayar kan jikinta,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" tafada ahankali tana shafa kanta,
Ayanda taji gashin kanta acukurkude ya sanyata mikewa arazane amma babu shiri ta koma ta zauna sakamakon wani irin zugi da radadi da take ji ajikinta,
Bin ko ina take yi da kallo tana mamakin meya kawota nan,yanayin yanda wurin yake ya sanyata gane cewar tabbas wurin kasuwa ne,
Jin danshi akasanta ya sata dubawa jini tagani ajikinta sannan ga wani zafi yana ratsata,
K'arar hadarin da yake ta gudu a sararin samaniya ne yasata mikewa ahankali, kafarta babu takalmi haka ta doshi bakin titi tana dingishi, jinta take kamar sabuwar halitta kamar ba itaba,
"To nan inane? Ni kuma meya kawo ni nan? Kodai mafarki nake?" Wadannan tambayoyin ta jerowa kanta amma bata da wanda zai bata amsar tambayoyinta.
Titi ta mike sambal tabi tana tafiya ahankali batare da tasan inda zataje ba.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/3, 1:33 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_5_
~~~ Tafiya taci gaba dayi ahankali ahankali cikin dingishi har ta danyi tafiya mai dan nisa, daidai lokacin aka fara yayyafi yif yif,
Haske tagani sosai ya haske mata ido wanda har bata iya hango gabanta,
Wata irin faduwa gabanta yayi zuciyarta ta harba da karfi, take ta sulale awurin ta fadi,
Cikin sauri mai motar ya fito da gudu yazo ya kinkimeta yayi cikin motar da ita,wuta yabawa motar ya nunku cikin gari, bai tsaya ako ina ba sai awani dan karamin asibiti mai zaman kansa,
Yana zuwa ya kira nurses mata guda biyu suka taimaka masa suka kinkimeta suka shigar da ita wani dan madaidaicin daki, shidai wannan bawan Allah waje yakoma ya zauna yana jiran abinda zaije ya zo domin likita yasamu zarafin shiga dakin da marar lafiyar tasa take ciki.
Sai da likitan ya kwashe kimanin sama da sa'a daya sannan ya fito hannunsa rikeda wani jan file,
"Kaine wanda ya kawo wannan baiwar Allahr ko?" Likitan ya tambayeshi yana gyara zaman farin tabaran dake manne a fuskarshi,
"Ehh nine likita, Allah dai yasa ba mutuwa tayi ba" yafada bakinsa yana rawa,
"Bata mutu ba sai dai inada wasu yan bayanai wadanda nake son sanar dakai amma yanzu ka biyoni zuwa office dina" likitan yafada tareda juyawa ya nufi office dinsa,
Bin bayansa shima mutumin yayi duk hankalinsa atashe,
Kujera likitan ya samu ya zauna tareda nunawa mutumin wurin zama,nan shima ya zauna yana fuskantar likitan,
"Bawan Allah ko zaka iya fada min alakarka da wannan marar lafiya da ka kawo? Da kuma dalilin dayasa ka kawota nan?" Likitan ya tambayeshi tareda kura masa ido kurr,
"Ehh to zan iya, dafarko dai ni sunana barrister elmustapha mamman, ina zaune anan garin yola awata unguwa wacce ake kirada sabon loko, tun tsawon lokuta masu yawa fiyeda shekaru biyu ina ganin ita wannan yarinyar abayan kasuwa da cikin tasha ko gefen titi tana yawo cikin hali irin na lalura wato tabin hankali to kuma dazu nadawo zan wuce ta gaban sabbin titunan nan kawai sai naganta tana tafiya amma kuma sai naga haka kawai ta yanke jiki ta fadi awurin, wannan dalilin ne ma yasa na taimaka mata na daukota nakawota nan"
Ajiyar zuciya likitan yasaki ya dan dafe kumatunsa da hannuwansa guda biyu,
"Tabbas naji bayaninka kuma na gamsu, wato a binciken dana gudanar nasamu damar gane cewa wannan yarinyar mai tabin hankali ce sai dai yanzu haka ta samu lafiya, sannan abu na biyu shine anyi mata fyade acikin wannan daren domin har yanzu da akwai sauran alamun hakan atattare da ita"
Ido barrister elmustapha ya zaro yana mai jijjiga kai, "hakika indai hakane to lallai acikin mutane akwai marassa imani, da ace zan samu wanda yayiwa yarinyar nan wannan mummunan aikin da wallahi sai na gurfanar dashi agaban shari'a, da sai na kwato mata yancinta, wannan ai cin zarafine in banda haka tayaya mutum zai yiwa mahaukaciya fyade" ya karasa maganar yana hucin takaici,
"Babu komai Allah zai saka mata, yanzu dai mun gudanar da dukkan gwaje gwajen da suka kamata muyi mata mun samu bata dauke da kowacce irin cuta, nasan nanda karfe 1:30 nadaren nan zata iya farfadowa" likitan yace dashi yana duba agogon hannunshi,
"Nagode dr yanzu ina son ka sanar dani duk wasu abubuwa wadanda ake bukata"
"Ba a bukatar komai sannan nima duk wata kulawa da za abata to zan yishine abisa kyauta, bana bukatar ko kobon ka, Allah ya bata lafiya"
"Mun gode dr Allah ya saka da alkhairi"
Hannu barrister elmustapha ya mika masa sukayi musabaha ya tashi yafita daga cikin office din.
_*Ummi Shatu*_π
[12/3, 1:38 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_6_
~~~ Tsaye barrister elmustapha yayi yana tunanin lallai zamanin yanzu abun tsorone domin mutane sam basuda tausayi kadanne daga ciki masu jin tsoron Allah,
Agogon dake daure a hannunshi ya kalla misalin karfe 1 nadare gashi sai ruwan sama ake tsugawa kamar da bakin kwarya,
Yadade atsaye kafin dr din yafito yazo ya sanar dashi cewar patient dinshi ta farfado zai iya shiga ya ganta,
Cikin halin tausayawa ya shiga dakin da take, tana kwance da drip ahannunta ana kara mata,
Jiyowa tayi ahankali tana kallonsa kallo irin na kurulla, bakine dogo mai dan jiki amma ba can ba,
"Sannu baiwar Allah, yajikin naki?" Yace da ita daidai lokacin da ya karasa bakin gadon da take,
Idanuwanta masu mutukar girma ta dago tana kallonsa cikeda tambayoyi fal abakinta,
"Bawan Allah inane nan? Wanne garine wannan? Meya kawo ni nan? Meya sameni?"
Kallonta yayi da dan murmushi akan fuskarshi,
"Kiyi hakuri baiwar Allah, wadannan tambayoyin naki duk zan sanar dake amsoshinsu amma sai bayan komai ya daidaita"
Kanta ta girgiza hawaye na bin kuncinta sakamakon tunowa da tayi da ko ita wacece, motsi ta danyi da zummar gyara kwanciyarta amma sai ta kasa sanadiyyar wani irin radadi da ya ratsa kasanta,
Kallonshi tayi akaro na biyu "dan Allah ka sanar dani abinda ya sameni, wallahi ban san abinda yafaru dani ba, jikina ciwo yake, ina jin wani irin zazzafan ciwo atare dani,ga wani zazzabi mai zafi da nake ji"
Tausayine ya kamashi to amma baya son sanar da ita halin da ta tsinci kanta aciki yanzu saboda yasan dolene hakan yayi mata ciwo duk da cewa bashida tabbacin cewar ita budurwa ce ko sabanin haka,
"Kiyi hakuri kar ki daga hankalinki, insha Allahu zaki samu lafiya nan bada jimawa ba,kuma zan baki dukkan amsoshin wadannan tambayoyin naki"
Idonta ta mayar ta rufe tanata sake saken abubuwa acikin ranta, ita dai iya tsawon rayuwarta bata taba sanin wani gari makamancin wannan ba sai gashi yau ta tsinci kanta aciki ko inane Allahu a'alamu,
"Nasan kina bukatar abinci bari naje nagani ko zan samo miki"
Kai ta girgiza masa "kar kayi wahalar nemo min abinci domin banida bukatarsa ahalin yanzu"
"To shikenan ni zanje natafi gobe da safe insha Allahu zan dawo"
"Allah ya kaimu"
Tabashi amsa tana bin bayanshi da kallo, ita dai ba saninshi tayi ba asalima bata taba ganinshi ba sai yau, tunani taci gaba dayi har bacci ya samu damar dauketa.
Washe gari kamar yadda ya alkawarta misalin karfe 8:30 yadawo asibitin anan ya samu likitan ya karbi sallama bayan an harhada masa magungunan da zata rinka sha sannan likita ya jaddada masa cewar suna komawa gida ta shiga ruwan zafi.
Dakin da take ciki ya shiga, azaune akan gado ya isketa tayi tagumi, jin alamun shigowar mutum ya sanyata dagowa tana kallonsa, shima ita yake kallo komai na jikinta dankare yake da dattin dauda, yanda ya kawota jiya da daddare yau dinma haka take dauke da kayan da tayi rayuwar tabin hankali dasu,
"Sannu ko, taso muje gida likita ya sallameki" yace da ita,
Mikewa tayi ahankali ta sauko daga kan gadon tafara takawa ahankali saboda har yanzu bata ji saukin jikinta ba, bin bayanshi tayi har harabar asibitin inda ya adana motarsa awurin da aka tanada musamman domin adana abin hawa.
*_Ummi A'isha_*π
[12/5, 2:59 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai taba zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_7_
~~~Bud'e mata kofar motar yayi ta shiga ta zauna, ita dai binsa take kawai da kallo hakama dukkan wuraren binsu take da kallo ba tare da tace uffan ba,
Motar yayiwa key suka fita daga harabar asibitin, cikin gari suka hara yana tuki sannu ahankali cikin nutsuwa da kwarewa har suka isa wata unguwa mai karancin gine gine,
Agaban wani dan madaidaicin gida ya yayi packing yafita ya bude gate ya shigar dasu cikin gidan, fitowa tayi daga cikin motar kamar yadda shima ya fito, bin bayanshi tayi suka tasamma cikin gidan Wanda daga gani babu tambaya gidan mace daya ne,
Matar gidan tana hakince acikin falo suka sameta tadora daya akan daya, ganinsu ya sanyata mikewa tsaye tana kare musu kallo,
"Barrister wacece wannan?" Ta tambayeshi tana huci,
"Ki kwantar da hankalinki ni'ima zaki san ko wacece nan bada jimawa ba amma yanzu abinda nake so dake kinga ayanayin da take to ina so ki kaita tayi wanka ta shiga ruwan zafi sosai kibata kaya ta shirya ta saka kafin tazo taci abinci"
Kamar zata sake magana sai kuma ta fasa ta juya tayi gaba,
"Bi bayanta" yace mata yana nuna mata hanya,
Binta tayi sumi sumi duk kanta adaddaure, amma daga gani tasan za asamu matsala,
Wani daki taga matar ta shiga dan haka itama tabita ciki,
"Ga towel, ki shiga bathroom akwai dukkan abun bukata aciki sannan idan akwai wani abu wanda kike bukata sai kiyi min magana"
Karbar towel din tayi ta shiga bathroom din batare da tayi magana ba, fuuuu! Ni'ima tayi falo inda elmustapha yake zaune tana zuwa ta tsaya agabanshi cikin masifa tafara magana,
"Wai wacce yarinyace waccen ka kawo min ita gidannan sannan tsabar rainin hankali har kana sanar dani cewar wai ta shiga cikin ruwan zafi sosai, meye alakarka da ita?"
"Haba ni'ima ki kara hakuri mana ai zan sanar dake komai"
"Kaga malam babu wani hakuri kawai ka sanar dani inda ka samota"
"Ni'ima wallahi ban santa ba mahaukaciya ce kuma muna kyautata tsammanin ta samu lafiya yanzu shiyasa nayi niyyar taimakon ta"
"Yanzu naji batu" tafada tana murmushi,
"Bari naje na fiddo mata da kayan da zata saka,juyawa tayi tafita daga falon tabar elmustapha tsaye yana kallonta yana murmushi saboda sanin zafin kishi irin na ni'ima.
Tsayawa tayi agaban mudubin dake manne a bangon bathroom din tana kallon jikinta da fuskarta, hawaye ne suka fara bin fuskarta, dakyar ta iya samu ta tsaida hawayen ta tari ruwan zafi ta zauna aciki,gashin kanta mai mutukar tsawo da yawa tafara wankewa wanda sai da yaci ruwa bokiti 3 kafin dattin dake jiki ya fita,
Wanka tayi ta sake karawa sannan ta dauraye jikinta tafito bayan ta yi alwala,
Jinta take kamar sabuwar halitta gashi iska sai shigarta take yi tako ina, acikin dakin ta iske ni'ima tana tsaye tana zabo mata sutturar da zata sanya ajikinta,
"Har kin fito?" Ni'ima ta tambayeta cikeda fara'a, kai kawai ta daga mata batayi magana ba,
"Kiyi hakuri kinji,ki sanar min da sunanki saboda ban san da wanne suna zan kiraki ba" ni'ima tasake yi mata wata maganar tana kokarin rufe akwati,
"Sunana IKHLAS"
Yanda tayi maganar asanyaye ahankali cikin sanyin murya ya sanya ni'ima jin tausayinta,
"Allah sarki ikhlas, to ki shirya ga kaya nan ki saka sai kifito muci abinci kinji"
"Nagode" ikhlas ta bata amsa tareda dosar wurin da ta ajiye mata kayan,juyawa ni'ima tayi tafita daga cikin dakin tabar ikhlas domin ta shirya.
*_Ummi A'isha_*π
[12/5, 2:59 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga kawata Khadija Sidi_
_8_
~~~ Ba wata doguwar kwalliya tayi ba, mai kawai ta shafa sai farar powder da ta gogawa fuskarta amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba,
Kayan da ni'ima ta ajiye mata ta dauka ta saka, riga da skirt ne na bakin leshi mai tsananin tsada da kyau, dinkin yayi mata kyau ajikinta domin ya bayyanar da shape dinta afili,
Sallah tayi raka'a biyu kafin ta fita zuwa falon gidan, ni'ima da elmustapha ta gani zaune suna zaman jiran fitowarta domin yin breakfast,
Ido elmustapha ya zuba mata yana kallonta domin ba karamin kyau tayi masa ba, babu wanda zai ganta yayi tsammanin ta taba samun tabin hankali, gata takai duk inda wata kyakkyawar mace takai, tausayinta yaji yana shigarsa saboda tunowa da yayi cewar yanzu ita ba budurwa bace sakamakon fyaden da wani marar tausayin yayi mata amma shi yana da yakinin cewa har yanzu ita bata da masaniyar abinda ya faru da ita,
"Ikhlas kin fito? Karaso nan muci abincin"
Muryar ni'ima ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula,
Anutse cikin nutsuwa ikhlas ta karasa ta zauna akusa da ni'ima amma har lokacin shi elmustapha bai bar binta da kallo ba,
Soyayyen dankali da kwai ni'ima ta shirya musu sai ko tea, zubawa ikhlas tayi ta mika mata sannan ta zubawa elmustapha nasa ta ajiye masa agabansa,
Babu wanda yayi magana sai dan lokaci zuwa lokaci da elmustapha yake dan yiwa ni'ima hira, da haka suka kammala cin abincin.
Gyaran murya elmustapha yayi ya juya yana kallon ikhlas sannan ahankali yafara magana,
"Baiwar Allah hakika ki godewa Allah da ya baki lafiya adai dai lokacin da baki sani ba kuma baki tsammata ba, kisani rayuwar da kika yi abaya lokacin da kike hali na rashin lafiya to Allah ya dauke alkaluma akanki amma ahalin yanzu andawo da alkaluman rubutu akanki za arinka rubuta dukkanin ayyukanki na alkairi ko sabanin haka, Allah yasa kaffarace sanadiyyar rashin lafiyarki, sannan idan kin kwana biyu kin nutsu kin huta zan kaiki har gaban iyayenki, yanzu nan kina cikin garin yola ne babban birnin jihar Adamawa amma ina son ki sanar dani ainihin labarinki kafin ki hadu da lalura"
Ko dagowa ikhlas ba tayi ba amma kuma da alama kuka take yi marar sauti Wanda iya hawaye ne kawai yake kwarara daga idanuwanta.
*
Zazzabine mai mutukar zafi ya sake rufe Lamido nan ya shiga surutai marassa kan gado dama shi yana dadewa baiyi rashin lafiya ba amma duk lokacin da kuma ta kamashi to yana jigatuwa,
Kudundune yake shi kadai adakin nasa sai maganganu yake,
"Washh zazzabin nan Allah yasa iya ni kadai ne bai kama min ke ba, washh jin kaina nake kamar zai tsage, bash dan Allah kaje ka samo min ita..!, washh innah, innah, innah, Baffa wayyo baffah, inna, innah, innah..!"
Haka yayita fada har bacci ya samu nasarar daukeshi sai alokacin bakinsa yayi shiru, ya dan jima yana bacci kafin ya iya farkawa.
*_Ummi A'isha_*π
[12/5, 2:59 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_9_
~~~Jikinsa amace ya tashi har lokacin da sauran zazzabin ajikinsa,hawaye ya fara yi yatashi ya nufi part din innah,
Yana shiga ya sameta zaune a falonta tana kallon tv,tana ganinshi ta mike taje ta rungume shi,
"Lamido jikinne? Dadina dakai rangwanta daga rashin lafiya ta kamaka sai ka zauna kayita kuka, kai dai akomai jarumi ne amma banda a bangaren jinya domin komai kankantar rashin lafiya kuka kake yi mata"
Kan doguwar kujera ta kaishi ta kwantar dashi tafara shafa sumar kanshi tana murmushi,
"Baka ci abinci ba, in kawo maka ko?"
Kai ya girgiza alamun a'a,
"Haba Lamido ka daure kaci mana sai kasha magani, kaji lamidon innah"
Juyawa yayi ya gyara kwanciyarsa, hakan ya sanya inna tashi ta shiga kitchen taje ta bararrako masa indomie ta kawo masa, har lokacin yana kwance yana kuka,
"Tashi kaci sarkin kuka"
Tayar dashi zaune inna tayi tafara bashi abaki yana ci har ya dan ci dayawa, panadol ta dauko masa tazo tabashi yasha,
Kwanciya ya sake yi har lokacin salla yayi sannan ya mike yashiga bedroom din inna ya je ya dauro alwala yafita zuwa masallaci,fitowa yayi bayan an idar da salla anan ya hadu da bash yana kokarin shiga gidan,
Packing bash yayi ya fito yana murmushi,
"On top" bash yafada gamida mika masa hannu, mika masa hannun shima Lamido yayi yana dan murmushi,
"Bash ya akayi"
"Normal, ya jikin naka? Kazo mu shiga sch mana"
"Kayi salla ne?"
Lamido ya tambayeshi,
"Muje kawai sai la'asar tayi sai nahada nayi"
Kallonshi Lamido yayi "bash baka tsoron Allah, kayi duk iskancin da zakayi agarin nan amma ya zamana tsakaninka da ubangijinka akwai alaka mai kyau,ni ka ganni nan duk iskancin da kaga ina yi to ina yin salla akan lokacinta sannan bana taba bari da ta wuceni sai dai idan acikin hali na lalura"
"Naji muje ka shirya mu fita"
Wucewa suka yi suka nufi cikin gidan Lamido sai faman yayyamutsa fuska yake yi irinta marassa lafiya,
Wanka Lamido yayi ya fito ya shirya cikin jar t shirt da bakin trouser, rigar ba karamin kamashi tayi ba,
Fita suka yi suka nufi cikin gari bash yana driving Lamido yana zaune agefenshi yana kallon gari ta cikin glass,
"Lamido ya jikinne? Wai kodai...?" Bash ya fada cikeda tsokana,
Yamutsa fuska Lamido yayi sannan ya danyi wani basaraken murmushi, "bash ban taba yin zazzabi irin na jiya ba, kai ni rabon ma da nayi zazzabi har namanta sai wanda nayi jiya"
"Shiyasa nace kodai...?"
"Bash mubi ta wannan hanyar ko Allah zai sa muga wannan yarinyar"
"Angama ranka ya dade, on top"
Murmushi Lamido yayi yaci gaba da rarraba manyan sexy eyes dinshi yana bin ko ina da kallo domin yanzu bashida burin da ya wuce na ya sake haduwa da wannan mahaukaciyar yarinyar.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/5, 2:59 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_10_
~~~Har suka bar harabar wurin da ya hadu da mahaukaciyar nan jiya bai ga koda mai kama da ita ba hakan ba karamin tayarwa da Lamido hankali yayi ba,
Cikin makarantar su suka shiga,suna shiga yan mata suka fara washe baki suna bin motar da kallo,
"Lamido na mata, mata suna sonka" bash yace dashi,
"Nima ai ina sonsu" Lamido ya bashi amsa yayinda yake zaro wayarshi daga cikin aljihun jeans din dake jikinsa,
"Bash dan Allah ka taimaka min mu nemo yarinyar nan tajiya, wallahi bash ina ji ajikina i can't do without her.."
Cikin sauri bash ya kalleshi,
"On top anya kuwa yarinyar nan ba aljana bace? Kai ina jin kila aljana ce tazo maka a siffar mutane har ka kusanceta shiyasa ka kasa mantawa da ita idan ba haka ba yan mata nawa kayiwa dabara ka rabasu da budurcinsu amma duk hakan bai dameka ba sai wannan wacce ko hankalima bata dashi, tababbiya"
Sai da Lamido ya Ciro kodin daga aljihunsa yafara sha sannan ya kalli bash ya lumshe idanuwansa masu mutukar girma,
"Bash ina son yarinyar nan wallahi.."
"That's why nace aljana ce duk yadda aka yi, Lamido kaifa baka taba son wata mace ba sai dai ita ta soka, amma yau kana furta cewa kana son wata mace with your mouth, macen ma mahaukaciya marar hankali, kai gaskiya da walakin wai goro a miya"
Bude idonshi Lamido yayi ya danyi dan karamin tsaki,hannu yakai ya taba wuyanshi,
"Kaga ni ka kyaleni pls, zazzabi nake ji"
"Zazzabi kuma? Allah Lamido ina jin gamo kayi"
Murmushi Lamido yayi yakai dubanshi zuwa ga window din motar, ta glass yafara hango daliban makarantar sunata kai komo kowa yana sabgar gabanshi,
Glass din saitin da yake aka kwankwasa,a kasalance ya sauke glass din yana kallonta,fadila ce budurwarsa tana sanye cikin leshi kalar ruwan madara tasha kyau har ta gaji,
"On top ya akayi" tafada tana rankwafowa kusa da fuskarshi,kallonta yayi ya dauke kanshi batare da yayi mata magana ba, kallonshi itama take acikin ranta kuma tana cewa
"Kaji matsalarshi ai wannan gayen mugun dan rainin hankali ne,yanga kamar wani mace ga shegen jan ajin tsiya"
Amma afili sai ta dan yi murmushi takai hannunta ta kamo nashi,
"On top ya naji jikinka da zafi, ko baka da lafiyane"
Sai da ya dan lashi lebenshi nakasa har dimple dinshi yafito sannan yace,
"Bana dan jin dadine yau"
"Ayya sorry, Allah yabaka lafiya"
"Thanks" yafada yana kokarin daga glass din, sanin halinshi ya sanya fadila matsawa ta juya ta tafi, tana tafiya ya ji bash yana yi masa magana,
"On top kana yarfa yarinyar nan fa gaskiya, wlhi ka sauya hali"
"Bash muje gida ka saukeni zazzabi nakeji"
Yafada yana kankame jikinsa sakamakon sanyin da yafara ji yana bugarsa.
0 comments:
Post a Comment