~~~Kafin wani lokaci tuni har zazzabi ya sake rufeshi, nan da nan ya fara karkarwar sanyi kamar wanda yake cikin kankara,
"Lamido Kodai asibiti za muje?" Bash ya tambayeshi lokacin da yake bawa motar wuta,
"No basai munje ba bash kawai ka mikani gida kayi dropping dina" duk cikin karkarwar sanyi Lamido yake yin wannan maganar,
"Shiyasa nace muje asibiti, yanzu dubi yanda kake yin rawar dari"
Lamido bai sake magana ba suka tasamma barin cikin makarantar, idanuwanshi jajur jikinsa zafi rum haka bash ya kaishi gida ya ajiye shi, dakin innarshi ya nufa yana kankame da jikinshi yana karkarwa, bai sameta acikin dakin ba saboda da alama tana cikin kitchen tana girki kasancewar lokacin dora girkin dare yayi.
Kan bed dinta ya hau ya kwanta yaja bargonta ya lullube jikinsa, hawaye yafara yi domin zafin zazzabin da yake addabarshi,
"Washh, wayyo jikina, washh...!" Yafada yana hawaye, kamar wani karamin yaro haka yaci gaba da kuka har bacci ya daukeshi.
*
Kuka ikhlas taci gaba dayi tun tana marar sauti har tafara yin mai sauti, ni'ima ce ta matsa kusa da ita tafara rarrashinta tana bata baki,
Har tsawon lokaci ikhlas ba tayi shiru ba hakan ya sanya elmustapha yin magana ahankali,
"Idan maganar da nayi aciki akwai wacce ta bata miki rai to ina mai baki hakuri da kiyi hakuri hakan bazata sake faruwa ba"
Girgiza kai tayi cikin kuka tace "ni ba maganarka ce tasani kuka ba"
"To koma dai menene kiyi shiru ki daina wannan kukan haka" ni'ima tace da ita tana shafa kanta,tashi tayi daga falon ta nufi dakin ni'ima tana zuwa ta tukunkune akan carpet din dake malale acikin dakin tuni zazzabi mai zafin gaske ya rufeta,hijabin dake jikinta taja ta lullube jikinta dashi,
Ni'ima ce ta bita cikin dakin tana zuwa ta isketa cikin wannan hali, falo ta koma wurin elmustapha,
"Barrister yarinyar nan fa bata da lafiya"
Dagowa yayi da Sauri "meya sameta?" Ya tambayeta yana kallonta,
"Naji dai jikinta da zafi ina jin zazzabi ne"
Mikewa elmustapha yayi ya nufi hanyar fita yana cewa "akwai maganinta acikin mota mantawa nayi, dama dr yace da zarar mun dawo gida abata tasha, bari naje na dauko mata"
Binshi da ido ni'ima tayi acikin ranta tana tunanin tayaya ma zata bar ikhlas ta zauna mata agida, yazama dole elmustapha ya dauketa ya mayar da ita ga danginta idan kuma bata da dangi to ko hannun hukuma ne sai ya mayar da ita domin zaman ikhlas agidan tana da masaniyar cewar bazai haifar mata da d'a mai ido ba.
_*Ummi A'isha*_๐
[12/6, 2:56 PM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_12_
~~~Cikin hanzari elmustapha yabude motarsa ya dauko ledar magungunan da likita ya hadowa ikhlas,
Afalo ya samu ni'ima tsaye tana rike da kugunta tana jiran shigowarshi, wuceta yayi ya nufi dakinta inda ikhlas take kwance yana fadin,
"Ni'ima zo muje mu kai mata maganin"
Batare da tayi magana ba tabi bayanshi cikeda kunar rai,
Agaban ikhlas ya dunkusa yana mata magana ahankali,
"Ikhlas tashi kisha maganin, meya sameki? Zazzabin ne?"
Daga kai ikhlas tayi sannan tafara kokarin tashi zaune ahankali tana ciccije llips dinta,
"Ni'ima kawo mata ruwa"
Juyawa ni'ima tayi tafita tana zancen zuci "kalli duk yanda yabi ya wani rikice sai kace wata yar uwarsa, tab impossible wlh, yarinya bazata zo har gidana ta dauke min hankalin mijina ina zaune ina kallonta ba"
Ruwan ta mika masa acikin roba, karba yayi ya mikawa ikhlas,
"Amshi kisha maganin"
Dakyar ta daure tasha tana ta faman yatsina fuska, komawa tayi ta kwanta bayan ta gama shan maganin, hakan ya sashi tashi yaja hannun ni'ima suka fita zuwa falo.
Akan kujera three sitter ya zaunar dasu yana kallon fuskar ni'ima wacce sai faman cika take tana batsewa,
"Meya faru ni'ima?" Ya tambayeta yana juyo da fuskarta gareshi,
"Magana ta gaskiya barrister gaskiya damuwarka akan yarinyar nan yayi yawa, ina son ka sanar dani menene matsayinta acikin zuciyarka?"
Murmushi yayi yaci gaba da kallonta "ni'ima ace muyita repetition magana daya? Wlhi ban dauko yarinyar nan da wata manufa ba face ta taimakonta, idanma akwai wani tunani acikin ranki to ki cireshi, kin san dai ni lawyer ne inada damar na taimaki mutane tako wacce irin hanya, so stop blaming me, there is nothing inside my heart..!"
Sai alokacin taji ta sake samun nutsuwa amma duk da haka tana dan kokwanto akanshi,
"Pls ni'ima stop doubting, trust me"
"Shikenan yawuce amma dai zaka mayar da ita ga danginta ko?"
"Insha Allahu, nima wannan shine burina naga na hadata da danginta tafita daga hannuna"
"To Allah yasaka da alkairi". Tafada tana kashe murya,
"Amin ni'ima ta"
Murmushi tayi ta narke ajikinsa tana murna.
Misalin kusan awa daya ikhlas ta dauka da zazzabi ajikinta mai mutukar zafi da kashe jiki, bacci ta dan samu tayi marar dadi wanda sam bataji dadinsa ba kasancewar tana cikin hali na rashin lafiya,
Misalin karfe 1 narana ta tashi daga barcin, toilet tashiga tayi alwala tafito tazo tayi salla,addu'a ta zauna yi tana yi tana kuka wanda ni ummi Shatu ban san dalilin kukan nata ba,
Ta jima tana addu'a kafin ta tashi tafita zuwa falo, elmustapha kadai tasamu afalon yana karanta jaridar daily trust, ita kuma ni'ima tana kitchen tana girka musu abincin rana,
Ganin ikhlas ta sanyashi ajiye jaridar dake hannunshi ya dan kalleta kadan aransa yana yaba irin kyawun halittarta domin agaskiyar magana kyakkyawa ce sosai irinsune matan da ake kirada first class,
"Ya jikin naki?" Ya tambayeta yana mai kallon jaridar hannunshi,
"Ah jiki yayi sauki alhamdulillah" tabashi amsa cikin sanyin maganarta,
"Allah yasa kaffara ne"
Ahankali ta amsa da "amin"
Shiru ne ya gifta a tsakaninsu babu wanda ya sake magana sai dai shi elmustapha acikin zuciyarshi yana son sanar da ita wata magana to amma bai san tayaya zai sanar da ita ba domin sanar mata da maganar zai iya haifar mata da tashin hankali gamida bakin ciki acikin rayuwarta.
Ajiyar zuciya mai nauyi ya ajiye sannan ya dan sake kallonta,
"Ina fata dai babu abinda yake damunki domin likita yace idan da damuwa to lallai lallai akoma wurinshi"
Dan murmushin yake tayi tace "babu komai wlhi, kalau nake jina"
"Ato Abu yayi kyau gaskiya, good"
Bata sake magana ba ta sunkuyar da kanta kasa,
"Um ikhlas ina so ki dauki duk abinda ya sameki amatsayin jarrabawa daga Allah, ki dauki duk abunda yafaru agareki a matsayin wani mataki nasamun kyakkyawan rabo acikin rayuwarki, nasan baki da masaniyar abinda ya sameki alokacin da kike hali na lalura, ba ason raina zan sanar miki ba face dan ya zame min dole, tilas kuma wajibi,
Ina ganin babu amfanin nabarki acikin duhu kici gaba da tafiya batare da na haska miki wata fitila wacce zata sanar dake halin da kike ba,
Maganar nan da zan sanar dake ahalin yanzu wallahi ko matata ni'ima ban sanarwa ba saboda sirrinkine, sirrin rayuwarki ne idan nafadawa wani tamkar naci amana ne,
Ikhlas ina son ki dauki kaddara, kisani alokacin da baki da lafiya ansamu wani marar tausayi marar imani yayi miki fyade, wannan shine abinda likita ya sanar dani bayan na mika ki asibiti, amma ki godewa Allah domin dr ya aunaki ya gwadaki bakya dauke da kowacce irin cuta,
Ina son ki dauki wannan abu a matsayin sirri dan Allah kiyi hakuri"
Tunda yafara maganar kanta yana kasa amma jin ya ambaci cewar anyi mata fyade ya sanyata dago kanta da sauri cikin razani tana dubanshi,
"Haba ashe shiyasa nake tajin radadi da zugi akasana ashe abinda yafaru dani kenan" tafadi acikin ranta, mikewa tayi zuruf tatashi tsaye kwalla fal idanuwanta.
*_Ummi Shatu_*๐
[12/8, 8:43 AM] Ummi A'isha๐๐ป: : *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
_*Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI*_
_13_
~~~Dubanshi take idanuwanta cikeda kwalla hankalinta atashe amma ta kasa furta koda kalma daya sai hawayen dake sharara akan kumatunta,
"Dama nasan haka zata faru amma dan Allah kiyi hakuri ikhlas, ki dauki kaddarar da Allah ya aiko miki,ki sani wlhi ko matata ban sanarwa ba, duk duniya babu wanda yasan wannan abun"
Batare da tace komai ba ta juya ta nufi dakin ni'ima, kwanciya tayi tafara kuka mai cin rai wanda babu bata lokaci zazzabi mai zafi ya rufeta,elmustapha kam ta barshi a falo a tsaye yana nazari domin dama yasan haka zata faru dole,
Dakin yabita yaje ya babbata hakuri ya fito, tun daga ranar ikhlas ta shiga cikin kunci kullum ita kenan cikin kunci, gashi sai ta kule adaki tayita kuka, ko kuma ta shiga toilet ta zauna tayita faman kuka,
Elmustapha yana kokarin kyautata mata a kullum amma hakan baiyi sanadiyyar gogewar bakin cikin dake narke acikin zuciyarta ba, kullum cikin kuka take gashi zoben dake hannunta tarasa a inda ta sameshi dan haka ko wanne lokaci cikin zuba masa ido take tana kallonsa mintuna kadan kuma sai tafara kuka kullum ita kenan cikin kuka ga wani zazzabi da take fama dashi mai mutukar zafi.
Yauma tana kwance akan gadon ni'ima ta zubawa zoben dake hannunta ido sai kawai ta fashe da kuka mai sauti,
Sautin kukanta har falo domin hatta elmustapha da ni'ima suna jiyota,
"Barrister anya kuwa yarinyar nan tagama warkewa daga haukan nan? Ni ina ganin mu mayar da ita asibiti asake dubata domin kullum ita kenan acikin kuka, koda wanne lokaci acikin kuka take"
Mikewa elmustapha yayi ya nufi dakin da ikhlas take ni'ima ta mara masa baya,
Suna shiga suka sameta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,
"Ikhlas meya faru?" Elmustapha ya tambayeta cikin tashin hankali, shiru bata amsa ba sai rage sautin kukan da take yi da tayi, tambayar duniya taki amsa mishi hakan yasa ni'ima kama hannunshi ta fitar dashi waje ta dawo wurin ikhlas,
Akusa da ita ni'ima ta zauna ta dafa kafadarta tana kallonta,
"Kiyi hakuri ikhlas, dan Allah kidaina wannan kukan, wai meyake damunki ne? Ko zazzabin da kike yine yake saki kuka kullum?"
Hawayen idonta tafara kokarin sharewa amma har lokacin hawayen basu tsaya ba,
"Babu abinda yake damuna Anty ni'ima"
Hannuwanta ni'ima ta kama ta rike cikin nata "haba ikhlas tayaya kike tunanin Zan yarda da wannan bayanin naki wanda yafi kama da tatsoniya"
Murmushin karfin hali ikhlas ta kakaro tayi ta kalli ni'ima tace,
"Ba tatsoniya bace anty ni'ima gaskiyata na fada miki sai dai nikaina ban san abinda yake sani kuka ba, narasa dalili"
"Yakamata dai ki daure kidaina domin wannan kukan da kikeyi bashida wani amfani atare dake, narokeki pls kiyi hakuri kidaina"
"Anty ni'ima nadaina, bazan sake ba insha Allah"
Tashi ni'ima tayi tafita domin komawa wurin elmustapha,
Abakin gadonshi ta sameshi azaune yayi tagumi yana kallon sama daga gani acikin damuwa yake,
Zama tayi akusa dashi tana mamakin yadda yadamu da ikhlas sosai,
"Barrister naje na lallabata dakyar ta hakura tabar kukan"
"Yawwa ni'ima Allah ya saka miki da alkairi"
"Amin, amma wannan bazai hanamu kaita asibitin ba anjima"
"Ehh ina sane zamuje ai".
Misalin karfe 5 na yamma suka nufi asibiti,
Asibitin da elmustapha yakai ikhlas lokacin da ya tsintota yanzun ma can ya nufa, kasancewar clinic ne na kudi yasa babu wani dogon layi,likitan elmustapha ya samu yayiwa bayanin duk abubuwan da suke faruwa da kukan da ikhlas take yi kullum dare da rana,
Checking dinta dr yayi amma ba lalurar haukan bace dan haka yagane cewar bacin ran fyaden da akayi matane yake damunta shiyasa take yin wannan kukan,
Bayani yayiwa elmustapha cewar arinka kwantar mata da hankali kullum sannan adaina barinta ita kadai adaki tana zama, zaman kadaicin shine yake haifar mata da tunane tunane har ranta ya baci,
"To amma dr zazzabin dake damunta akullum fa?" Ni'ima ta tambayeshi,
"Wannan ma babu damuwa zan rubuta mata magani yanzu inyaso sai ku rinka bata tana sha, insha Allah zata daina"
"Mungode dr" elmustapha yace dashi bayan dukkaninsu sun mike domin tafiya,
Sai da suka tsaya awani chemist suka sai mata magungunan sannan suka nufi gida, yanzu kam ta dan saki ranta da zuciyarta ta dan rage damuwar dake addabarta, koda suka koma gidan ma bin ni'ima kitchen tayi ta taimaka mata suka shirya abincin dare sunayi suna hira har suka kammala.
Haka zamansu ya kasance tare kullum elmustapha yana kokarin yiwa ikhlas abubuwan da zasu sanyata farin ciki danma wani lokacin yana tsoron idon ni'ima domin babu wuya ta tayar masa da daru, kullum cikin fita dasu wuraren hutawa yake, musamman ma da ya fahimci cewar ita ikhlas ma'abociyar son irin wadannan wuraren ce, amma har yau bai sake yimata maganar danginta ba tunda ya fahimci bata son maganar asalima duk ranar da yayi mata maganar to wuni zatayi tana kuka.
Haka zamanta yaci gaba da tafiya acikin gidan, kullum elmustapha cikin yi mata hidima yake kamar ya goyata dan kulawa hakan ya sa ni'ima fara canjawa ikhlas fuska domin ita ta tsani duk wata wacce zata yi kokarin rabar mijinta.
Yau ta kama ranar lahdi elmustapha yana gida baije ko ina ba, misalin karfe 10 nasafe yana zaune afalon gidan yana karanta jaridar weekly trust, ikhlas ce tafito sanye cikin doguwar riga Arabian gown wacce elmustapha yasai mata lokacin da ya siyo mata kaya,
"Kai kadaine azaune?" Tafada tana dan murmushi,
Dago kanshi yayi yana kallonta, ba karamin kyau tayi masa ba komai nata das das kamar ita ta tsara halittarta,
"Ni kadaine sai ko ke da zaki tayani zama"
Murmushi tayi ta zauna akujerar dake fuskantarsa,
"Ina anty ni'ima?". Ta tambayeshi sai dai ko rufe bakinta batayi ba ni'ima tafito daga cikin kitchen a fusace hannunta rikeda cup guda biyu, tun daga nesa ikhlas ta fahimci sauyin fuskar da ni'iman tayi, ahankali ta sauke kwayar idonta kasa.
_*Ummi shatu*_๐๐ป
[12/8, 8:43 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_14_
~~~Fuska babu walwala ni'ima ta wuceta ta karasa wurin elmustapha ta mika masa cup din hannunta tana harararsa kasa kasa,
Cup din ya karba yayinda ita kuma ta zauna akusa dashi tafara kurbar furar da ta damo musu,
"Inata ikhlas?" Yace da ita yana kallonta,
Kallonshi itama take yi aharzuke cikeda masifa akan fuskarta,
"Kamar ya? Ita bata da hannu ne ko kuma bata da kafa da har sai nakawo mata tana zaune? Wai ni baiwa aka daukeni ne agidan nan ko yaya?"
Dauke kanshi yayi ya juya ga ikhlas wacce take zaune jugum tana saurarensu,
"Ikhlas kije kitchen ki zubo fura da nono tana nan acikin fridge"
Girgiza kai tayi "a'a bazan sha ba"
Tana gama fadin haka tamike ta nufi daki tana sharar kwalla, ya zama dole ta tattara tabar gidannan domin zamanta agidan zai haifar da rashin zaman lafiya tsakanin wadannan ma'auratan,
Tana zaune tana kuka elmustapha ya shigo cikin dakin,
"Ikhlas kiyi hakuri kinji"
Daga kanta tayi tana kallonsa, batare da tace komai ba, har ya karaci bata hakurin yatashi yafita batace komai ba, yana fita yaga ni'ima tsaye abakin kofa tana kallonsu cikeda takaici,
Wuceta yayi bai tanka mata ba hakan ya sake kular da ita, key din motarshi ya dauka yafice daga cikin gidan yabar ni'ima tana zancen zuci,
"Shiyasa kawayena da yan uwa suketa bani shawara kan kar nasake nayarda nabar yarinyar nan agidan nan gashi yanzu tun ba aje ko inaba nafara ganin sakamako wlh bazai yiyuba dole sai tabar gidan nan"
Mikewa tayi tafice daga falon ta nufi farfajiyar gidan taje ta zauna.
Kuka sosai ikhlas ta keta yi har tsawon wani lokaci,tana nan zaune sai taga rashin dacewar zaman dakin alhalin kuma gidan nan ba nasu bane, toilet ta shiga taje ta wanke fuskarta tafito tafita falo, ni'ima tasamu mike kan doguwar kujera tana kallon wani american film _50 ways to kill your mammy_ a kujerar kusa da ita ta zauna,
"Sannu anty ni'ima"
"Yawwa sannu ikhlas, kin gaji da zaman dakin kin fito?"
"Wallahi" ikhlas tafada cikin yake, babu wanda yasake magana acikinsu har elmustapha ya shigo,
Mikewa ni'ima tayi ta tareshi da murna cikin kissa,amma shikuma duk hankalinsa yana kan ikhlas domin ya ganta wani jugum,
"Ikhlas ga kayan makulashe nataho muku dashi" yafada cikeda fara'a akan fuskarshi, hakanne ya sa ni'ima sakinshi takoma gefe tana kallon ikon Allah,
Da kanshi ya dibarwa ikhlas dukkanin kayan da ya shigo dashi ya mika mata, ya dauki sauran yakama hannun ni'ima zuwa dakin baccinshi,
Kayan tafara bi da kallo, su chocolates ne manya kala kala harda takarcen cheeze sai kace wasu yara,
Murmushi tayi tana yaba kirki da kuma adalci irin na elmustapha domin duk abinda ya siyo agidan to itama sai ya bata nata, ko matarsa ya saiwa abu itama sai ya siya mata.
Kayan ta diba ta nufi dakin ni'ima dasu. Aranar da daddare suna zazzaune yatashi yafita zuwa wurin motarsa ya dawo hannunsa dauke da bakar leda,
Lesuka ne guda biyu masu kyau ya siyo musu iri daya ai nanfa ni'ima ta tada masifa,
"Wlhi bazai yiyuba yau sai kafada min idan matsayina dana wannan yarinyar dayane awurinka, haba nagaji nagama gajiya da wannan cin fuskar da kuke yimin acikin gidannan"
"Menene haka ni'ima?" Ya tambayeta cikeda mamaki,
"Oho muku, ban sani ba, wannan abun da kakeyi ni ban san ma'anarsa ba, ka kawo min yarinya gida ka ajiyeta ban san alakarku da ita ba, banida da dangantaka da ita, wallahi bazai yiyu ba, idan kishiyata ce ya kamata ka fito fili ka fada min"
"Ni'ima ki cire kowanne irin zargi acikin ranki"
"Was? Walhi bazai yiyuba haka kawai ka dauko yarinya ka kawo min tahanani sakewa agidana, komai tare kake yimana sai kace wasu kishiyoyi, wallahi sai tabar gidannan adaren nan bazata sake kwanar min agida ba.."
Cikin fada shima ya mike "dayake gidan nakine ko? Kece kika gina min gidan da har kike tutiya dashi? Babu inda zataje sai dai idan kece zaki bar gidan"
"Babu inda zanje amma ita wlhi sai tabar gidan nan"
Mikewa ikhlas tayi tafada daki da sauri, hijabi kawai ta dauko wanda elmustapha ya sai mata amma baya dashi bata dauki komai ba,
Wurinsu takoma tana kuka hawaye fal kuncinta,
"Anty ni'ima nagode da taimakon da kuka yimin keda mijinki, sannan ina mai baki hakuri sanadiyyar fadan da nake hadaku keda mijinki, kiyi hakuri zan bar miki gidanki acikin daren nan basai gari ya wayeba"
Rike kugu ni'ima tayi ta dauke kai, "babu inda zakije, anan zaki ci gaba da zama har sai idan kece kika gaji da zaman dan kanki" elmustapha yafada cikin fushi,
"Wlh bazata zauna ba, muddin zata zauna agidan nan to ni bazan zauna ba,sai tabar gidan nan idan bata da dangi akwai gidan gajiyayyu tatafi can mana"
Ita dai ikhlas bata sake magana ba tayi hanyar waje tana tafe tana kuka.
*_Ummi A'isha_*๐๐ป
[12/8, 8:43 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai taba Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_15_
~~~ Cikin Sauri elmustapha yabi bayanta yana kiranta,
"Ikhlas, ikhlas karki tafi, ina zakije da wannan daren?"
Ko waiwayowa batayi ba har tafita daga gidan, baiyi kasa agwiwa ba yaci gaba da binta har yasamu ta tsaya,
"Ikhlas bai kamata ki biyewa maganar ni'ima ba, kin san halinku na mata babu wuya kun dauki kishi akan dan abinda bai kai ya kawo ba"
Murmushin karfin hali tayi ta kalleshi,
"Hakane amma kayi hakuri domin wlh nagama zama agidanka, nagode da irin taimakon daka bani alokacin da bani da wanda zai bani, ubangiji Allah ya saka maka da alkairi, zan tafi asalina zanje na nemi dangina domin kaima nabaka dama ka zauna da iyalinka lafiya"
"A'a ikhlas babu inda zakije zaki cigaba da zama tare damu"
Girgiza kai tayi "idan naci gaba da zama agidanka ina haifar maka da matsala kaida iyalinka banyi maka adalci ba sannan na mayar da alherin da kayi min da sharri, bai kamata nayi maka haka ba, yin haka zaisa mutane su kyamaci yin Alheri bayan kuma shi ALHERI DANK'O NE"
Dafe goshinsa yayi da hannunsa,
"Ikhlas kar ki tafi acikin daren nan bana son abinda yafaru dake abaya ya sake faruwa dake yanzu"
Shiru tayi tana kallonsa, "kiyi hakuri narakaki gidan abokina ki kwana, gobe da safe zanzo na kaiki tasha nasaki a motar da zata kaiki garinku"
Tuna alherin da yayi mata yasata kasa yi masa musu, gaba yawuce tabishi abaya har zuwa layin dake baya da gidansa,
Wani gida suka shiga wanda yake madaidaici kamar nasa, gidan abokinsa ne musbahu wanda shima lawyer ne me zaman kansa,
Sun tarar dashi tareda matarsa Asiya mace mai kirki da fara'a, cikin sakin fuska ta taresu,
Karya yayi musu cewar kanwar abokinsa ce zata wuce gida gobe daga sch take kuma gashi ni'ima bata nan shine ya kawota nan domin ta kwana,
Murna sosai Asiya da musbahu suka yi, nan yayi musu sallama ya tafi azuwan gobe da safe zaizo ya dauki ikhlas yakaita tashar motar da zata hau zuwa garinsu.
*
Har inna ta shigo cikin dakin yana kwance da zazzabin ajikinsa yana rawar dari,
"Kaico, Lamido wannan zazzabin naka wanne irine? Sai ya sakeka sai ya sake kamaka ko asibiti zakaje?"
Dakyar ya iya girgiza kanshi,
"A'a innah, bani magani kawai"
"Lamido dazu mafa saida nabaka maganin nan kasha gashi yanzu ya sake rufeka"
Kansa ya dafe yana haki "innah wannan zazzabin wlhi mai zafine, har cikin kashina nake jin zafinshi, washh, wayyo Allah na"
Matsawa tayi kusa dashi "sannu to daina kuka kar kanka yayi ciwo"
Tashi zaune yayi "innah bani ruwan zafi nayi alwala banyi salla ba"
Bathroom dinta ta shiga ta tarar masa ruwan zafi ta ajiye masa ta dawo inda yake zaune yana rawar dari,
To taso kayi alwalar maza, tashi yayi yabi ta gefenta ya shige bathroom din yayi alwala ya fito, salla yayi yana daga zaune, yana idarwa ya sake tukunkuna ya kwanta.
Sai da ya kwashe kwanaki 8 yana wannan zazzabin,aranar da yaji ya dan samu sauki yafita yawon neman wannan mahaukaciyar ko Allah zaisa ya dace amma shuru bai ga alamunta ba,
Wurinda ya sameta har yayi mata fyade ya nufa anan ya iske mutane kowa yana hada hadarsa ta siye da sayarwa,shago mai lamba 2 ya shiga, kamar Wanda zai sai wani abu yafara dube duben kayan dake jere akan kanta,
"Malam me kake so?" Mai shagon ya tambayeshi,
Sumar kanshi ya shafa,
"Ina neman turare ne explore"
"Bamu dashi sai dai ka duba wasu"
"Ok bani nagani"
Turaren aka shiga jido masa yana dubawa yana tambayar kudinsu,
"Uhm bawan Allah nikuwa da ina ganin wata mahaukaciya amma yanzu kwana biyu narabu da ganinta"
"Ayya ai wannan yarinyar rabonta da nan anjima ina jin wani gun tayi ko kuma saceta akayi kasan mutane da rashin tausayi"
Iya kaduwa Lamido ya kadu da jin kalaman wannan mai shagon dandanan yaji hankalinsa ya tashi nutsuwarsa ta goshe yayinda bacin rai ya ziyarceshi, batare da yakara cewa komai ba ya zabi turarurrukan guda uku yabiya kudin yafita, motarsa ya shiga amma kuma yakasa tukin zama yayi kawai jugum yana tunata hakika bazai taba iya mance kamanninta ba duk da cewar acikin duhun dare yaganta amma duk da haka yana ganin hotonta radau acikin zuciyarshi.
*_Ummi A'isha_*๐๐ป
[12/8, 8:43 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_16_
~~~Kujerar da yake kai ya kwantar ya mike yana tunata acikin ranshi, har yanzu yakasa mancewa da ita haka kuma ya kasa mancewa da yanayin da ya tsinci kansa aciki lokacin da ya keta mata mutuncinta,
Wani kunci yaji yana shigarsa sakamakon tunowa da yayi da maganar da me shagon nan yafada masa cewar may be saceta akayi,
"To asaceta akaita ina? Mtsww Allah yasa ba haka bane,kai karyane ma wlh"
Zaune yatashi yana bubbude lumsassun idanuwanshi,
Shigowar kiran bash cikin wayarsa ne yasashi karkacewa ya zaro wayar yana duban kan screen din,
"Hello bash" yace ahankali,
"On top ya" bash yabashi amsa daga dayan bangaren,
"Bash ka ganni akusa da plaza dinnan ta bakin kasuwa dan Allah kazo ka sameni awurin"
"Ok bari nazo"
Kashe wayar yayi yana mai duban hanya sai yan waige waige yake yi wai ko Allah zaisa yaganta,
Sabuwar reza ya ciro daga wani dan akwati wanda aka tanada acikin motar domin yin ajiya,
"I Luv you pretty" ya furta ahankali gamida bude rezar, hannun shi nadama ya samu yafara tsagawa yana rubuta 'pretty' tuni jini yafara fita daga jikin fatarsa yana sauka akan jeans din dake jikinsa,
Runtse idonshi yayi,ahankali ya budesu sakamakon jin shigowar bash cikin motar,
Kallonshi bash ya danyi idonsa jajur kamar gauta ga jini kuma yana fita a hannunsa,
"Lamido menene haka" ya tambayeshi atsorace,
"Bash narasata, wlhi ina sonta, ita kadai ce macen da nake so, bash ka tayani nemanta domin ta tafi da farin cikina,bash ina sonta, i love her soo much,ina ji ajikina kamar i can't survive with out her, she's part of my life, pls bash ka taimakeni na nemota"
Tunda yafara wadannan sumbatun kallonsa kawai bash yake yana tausaya masa domin da alama ya dan zautu kadan akan wannan mahaukaciyar,
"Ya isa haka Lamido,insha Allahu zaka sameta amma kuma yakamata ka cireta daga cikin ranka because may be you will not meet her again, so kaga karka jawowa kanka damuwa and nikuma nama rasa ta yadda akayi yarinyar ta shiga ranka haka farat daya"
"Bash nikaina ban san yadda akayi ba, banida masaniyar tayaya nafara sonta sai dai wlhi bash ina jin sonta acikin ruhina fiyeda tunaninka, she's very beautiful and amazing, bash rashin samun yarinyar nan atare dani wlhi kamar rashin samun rayuwata ne I love her..!"
Dafashi bash yayi cikeda tausayawa aranshi yana mamakin wai Lamido shi dayake wulakanta mata yau gashi kuma yashiga wani hali akan wata, watanma mahaukaciya,
"Lamido tun farko kaine ka jawowa kanka wannan matsalar, tun farko kaine kayi sakaci har sonta ya ratsaka gashi yanzu kashiga wani hali, ni ina ganin ka daure ka cireta daga ranka, ga yanmata nan hadaddu classic bebs da yawa masu sonka"
"No bash, i can't, wallahi bazan iya ba"
"To shikenan yanzu a ina kake tunanin zaka iya samota,danni wallahi idanma naganta ba lallai naganeta ba"
"Bash zan samota, duk inda naganta zan ganeta domin wlhi aranar da nayi mata fyaden nan fuskarta kawai nake kallo, ban taba ganin mace mai kyau kamarta ba"
"Allah yabaka lafiya abokina dan dama nadade ina zargin cewa da aljana kayi karo wallahi"
"Wallahi ba aljana bace mutumce kamar kowa, yanzu kazo ka tuka mu ka kaini cikin kasuwa layin artists domin ina son azana min hotonta ayanzu"
Murmushi bash yayi amma aransa yagama yarda kawai Lamido gamo yayi da aljana ta zautashi.
*_Ummi Shatu_*๐๐ป
[12/9, 8:47 PM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_17_
~~~ Farin handkerchief ya dauka ya nannade wurin da ya yanka ahannun nashi gashi rubutun ya fito rado rado,
Fita yayi sukayi exchanging din wurin zama shida bash, inda shi bash din ya koma wurin zaman driver yajasu suka shiga cikin kasuwa,
Basu sha wahalar samun artist din da zai zanawa Lamido hoton ba, wuri suka samu suka zazzauna Lamido yafara siffantowa mai zanen kamanninta, shidai bash kallon Lamido kawai yake yi yana tausaya masa domin yasan aljana ne yarinyar nan, lallai indai hakane Lamido yayi kuskure da ya dauka RUWAN KASHE GOBARA BA SAI MAI KYAU BA,
Suna nan zaune aka gama zanen, Lamido ya kurawa hoton ido hakika bazai taba iya mantawa da ita ba,
Kudin zanen ya biya ya dauki hoton suka tafi, kai tsaye gidansu Lamido bash ya wuce dasu, fita Lamido yayi ya nufi dakin baccinsa yana zuwa ya ajiye hoton akan bedside drewar dinshi.
Dakin innah ya nufa, itada baffa ya samu suna zazzaune afalo,
Akasa ya zauna ya sunkuyar da kai,
"Barka da hutawa baffa" yafada kansa akasa,
"Yawwa lamido, ina fata dai kana shirye shirye ko? Domin tafiyarka yau saura kwana 6 kuma wannan tafiyar kanka zaka yiwa bani ba, amma duk da haka ina baka shawara da ka zama mutum nagari, ka ajiye wannan shashanci da kake yi, inda zakaje garine wanda babu wanda zai saka babu wanda zai tsawatar maka, ni nayi maka hakane domin kasamu ingantacciyar rayuwa domin acikin sharrudan tuba sauya matsugunni yana ciki ma'ana mutum ya nisanci wurinda yake sabon Allah idan garine to ya sauyashi ya koma wani, shiyasa kaima zan daukeka daga kasar nan in kaika wata domin kayi nesa da abokanai wadanda suke zugaka suna rubzaka izuwa ga halaka"
Tunda aka fara maganar baice komai ba sai sunkuyar da kai da yayi yana shafa sumarsa,
"Kana jina ko?"
"Ina jinka Baffa kuma insha Allah zan kasance kamar yadda kake so"
"Yawwa Allah yayi maka albarka"
"Amin baffa"
Mikewa yayi ya koma dakinsa yana shiga ya zauna agefen gado yana kallon hotonta, daukar hoton yayi ya rungume akirjinsa yana mai fatan Allah yasa yanada rabon ganinta.
Tun daga ranar ya fara duk wani shiri domin barin kasar Nigeria zuwa kasar Kenya,kullum cikin rokon bash yake yi akan ya taimaka ya cigaba da duba masa wannan mahaukaciyar ko bayan tafiyarsa,
Daren ranar da zai tafi yadade azaune yana kallon hotonta ji yake kamar zai rasata Idan yatafi, dakyar yasamu yayi bacci yana rungume da hotonta.
Washe gari da safe iyayensa da yan uwa suka yi masa rakiya zuwa airport domin jirgin karge 9 zai bi zuwa garin Nairobi babban birnin kasar Kenya,
Daidai lokacin da yagama sallama dasu innah ya juya domin tafiya bayan yaja hannun abokinshi bash wanda shima yaje rakiyar,
"Bash dan Allah karka manta da sakon da nabar maka, kayi duk iya kokarinka ka binciko min ita dan Allah, bash nasan kai gani kakeyi kamar ba mutum bace a tunaninka aljana ce, to wlhi ba haka bane pretty mutum ce"
"Karka damu abokina insha Allahu burinka zai cika zaka hadu da ita"
"Allah yasa haka" Lamido yafada yana goge yar kwallar data taru acikin idonshi, hannun bash Yakama suka yi musabaha yajuya yatafi domin anata shelar cewar jirgin yakusa tashi.
*_Ummi A'isha_*๐๐ป
[12/9, 8:47 PM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_18_
~~~Dukkaninsu sai da suka ga tashin jirginsu sannan suka nufi gida,
Lamido kam zama yayi jugum acikin jirgi yana raya abubuwa da dama acikin ranshi, hakika wannan tafiyar tashi ta yi sanadin da zaiyi nisa da wannan mahaukaciyar watikil kuma lokacin da zai dawo ba lallaine tana garin ba,domin bazai dawo ba sai nanda shekaru 3 ko 2,amma duk da haka dai zai ci gaba da tuntubar bash ko Allah zaisa adace, screen din wayarshi ya kalla anan take hotonta ya bayyana wanda aka zana,bakinshi yakai wayar yayi kissing din hoton gamida lumshe idanuwanshi.
*
Ikhlas sun jima suna hira itada asiya kafin su kwanta bacci wanda ita ikhlas sam bata samu runtsawa ba, kuka tafara marar sauti domin bata san inda zata dosa ba, domin sam bata son komawa gidan mahaifinta saboda dalilai masu tarin yawa amma ta yanke shawarar komawar koda kuwa hakan zaiyi sanadiyyar faruwar abubuwan da bata so.
Gyara kwanciyarta tayi tana share hawayen dake gudu akan fuskarta,
"Allah gani gareka kayi min maganin matsalolina" tafada acikin zuciyarta, yanda taga rana haka taga dare sam bata samu bacciba har gari ya waye.
Wanka tayi da ruwan dumi ta mayar da kayanta tasaka asiya ta gabatar musu da abin karyawa, Suna tsaka da cin abincin elmustapha ya shigo yana sanye da blue din shadda da hula,
Idonsa kur akan ikhlas yana kallonta shidai sam baya gajiya da kallonta domin kallon fuskarta yana sashi nishadi,
Zama yayi suka gaggaisa har ikhlas ta kammala tayiwa su asiya sallama, nan asiyan ta hadata da turarrurruka tarakota har kofar gida, ba karamin burgeta asiya tayi ba domin daga jiya zuwa yau ta fahimci macece me kirki.
Agaban motar elmustapha ta zauna tana kallon titi,
"Ikhlas wanne gari zamuje?"
Cikeda mamaki ta kalleshi,
"Zamuje ko zanje?",
"Za muje" yace da ita bayan ya hau titi,
"Kayi hakuri ka kaini tasha nashiga motar Zaria, wannan shine taimakon kadai da nake bukata daga gareka ahalin yanzu, sannan ina son ka rubuta min number wayarka domin zan runka kiranka muna gaisawa" ta karashe maganar tana goge hawayen idonta,
"Ikhlas hankalina yakasa kwanciya na nabarki ki tafi ke kadai, gashi kuma kin ki sanar dani wani abu game dake"
"Babu komai, ba wani abune yasani boye maka labarina ba sai don bana son bayyanashi ahalin yanzu amma kayi hakuri ai zumunci yanzu muka fara insha Allahu"
"To a Zaria awanne unguwa kike?"
"Kayi hakuri zan sanar dakai amma ba yanzu ba"
Shiru motar tayi babu wanda ya sake magana acikinsu har suka karasa tasha, da kansa ya fita ya samar mata motar da zataje Zaria ya biya kudin sannan yadawo inda take,
"Ikhlas Allah ya kiyaye hanya sannan dan Allah da zarar kin sauka ki kirani"
"Nagode madalla da irin taimakon da kayi min, Allah yasaka maka da alkairi, insha Allahu ina sauka zan kiraka koda kuwa a business center ne"
Wani kudin ya bata wanda zai kai kimanin dubu biyar, tana tafe tana hawaye har tashiga motar, bai bar tashar ba sai da yaga motarsu tabar cikin tashar, shi dinma kamar yayi kwallar yake ji domin yasan yagama shakuwa da ikhlas kuma yaso yaci gaba da zama da ita sai dai ina matsalar ni'ima tasha gaban zaman nasu,
Runtse idonsa yayi yana jin wani abu gameda ita, hakika tayi masa duk da cewar yasan koma daga ina ta fito to daga gidan arzikine domin surarta irin ta tsatson masu abin hannune, duk da haka ya kuduri niyyar bayyanar mata da soyayyarshi agareta ko Allah zaisa yadace.
Tagumi ikhlas tayi acikin motar sai zazzare ido takeyi domin rabonta da Zaria shekaru biyar kenan cif domin idan bata mantaba tun tana yar shekara 20 tabar gida cikin hali irin na tabin hankali,
Tunanin rayuwarta tashiga yi har suka karasa cikin Zaria,tana sauka daga motar ta nufi wani shago Wanda ake bayar da hayar waya,
Karba tayi takira elmustapha ta sanar masa da cewar ta sauka lafiya yanzu zata karasa gida,
Taxi ta shiga domin zuwa gidansu, tun ahanya tafara tambayar me taxi din ko yasan gidan ALHAJI AHMAD BUZU,
Nan da nan me taxi ya washe baki "haba hajiya waye bai san wannan mutumin ba acikin fadin garin nan, mutumin da yayi senata har na tsawon shekara takwas yanzu kuma ana cewa shi za abawa takarar gwamna ai dole yayi suna, can za akaiki?"
"Ehh" kawai tabashi amsa atakaice, titin Kaduna road ya dauka ya nufi wani hamshakin layi Wanda tun daga nesa suka fara hango jami'an tsaro suna kaiwa da komowa.
*_Ummi Shatu_*๐๐ป
[12/11, 6:24 PM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_19_
~~~Dakyar jami'an tsaron suka barsu suka wuce bayan mai taxi din yayi musu bayanin inda zasuje,
Har kofar gidansu yakaita ta dauki naira dari biyar tabashi kudin ladanshi,
Makeken gate din gidan ta hara komai na gidan nasu ya sauya mata ba wanda tasani bane da alama wannan sabone mahaifin nata ya gina yatare aciki,
Tambaya iri iri tashata awurin masu tsaron kofar gidan kafin su kyaleta tawuce,
Gidane mai mutukar girma dan haka sai da tambaya tasamu isa cikin asalin gidan.
Falon hajiya Nafi ta shiga ai kuwa tun daga nesa ta hangota hakince akan doguwar kujera ta dora kafarta akan center table tana waya, kamar kullum cikin kwalliya take tasha wani dan ubansun din leshi ja,
Tunda tayi sallama hajiya Nafi ta mike da Sauri tana nunata da dan yatsa,
"Ikhlas... Dama... Dama baki mutu ba?" Tafada cikin rawar baki,
"Ban mutuba anty gani nadawo da raina"
Dafe kai hajiya Nafi tayi tana jijjiga kai, "baki mutu ba? Meyasa baki mutu ba? "
"Saboda kwanana bai kareba Anty" tasake bata amsa, zama hajiya Nafi tayi jagwaf akan kujera tare da sakin wayar hannunta ta fadi akasa,
Zama ikhlas tayi akasa tana kallon falon wanda yasha kayan alatu na more rayuwa domin babu ce kawai babu aciki,
"Anty ina abbana?"
Kallon ikhlas tayi kafin tayi dan murmushin munafurci,
"Abbanki yau zai dawo daga kasar chairo yaje medical check"
"Allah yadawo dashi lafiya"
"Amin amin, yanzu kitashi kije second to the last bedroom akwai komai wanda zaki bukata aciki inyaso idan abban naki yadawo sai ki sanar damu abinda yafaru dake har kika bar gida tsawon shekara 5,sannan gameda abinci kuma idan kina bukata akwai kuku sai ki sakashi ya kawo miki"
"Shikenan nagode anty, bari naje"
Mikewa tayi ta nufi hanyar da hajiya Nafi ta nuna mata tana tafe tana karewa wuraren datake wucewa kallo,
Bin bayanta da harara hajiya Nafi tayi tana mai cizon yatsa, daga bisani ta dauki wayarta wacce ke yashe akasa ta fara kokarin kiran abban ikhlas.
Daki na biyun karshe ta shiga nan ta ganshi shirye da kaya na alfarma masu kyau da burgewa,
Drewar din da aka tanada domin Adana kayan sawa ta bude nan taga kayan sakawa masu tarin yawa shirye aciki,
Zama tayi agefen gadon tana nazari,
"Anty bazan ci abincinku ba domin dama can tun asali bana cin girkin kowa agidan nan, yanzun ma bazan ci ba da kaina zan dafa abinda zanci"
Mikewa tayi tabi hanyar fita, a inda ta bar hajiya Nafi yanzun ma anan ta tarar da ita tana zaune tana waya, tana ganinta kuma sai tayi firgigit ta kashe wayar ta jiyo tana kallonta,
"Uhm ikhlas ya akayi? Kina bukatar wani abune?"
"Ehh anty kitchen nake son ki nuna min"
"Uhm ga kitchen can ikhlas, kin ganshi can kitchen din nawa, akwai kuma central kitchen acan gaba idan kinada bukatar wani Abu wanda babu anawa"
Wucewa tayi ta nufi kitchen din wanda tsaruwarsa tafi gaban kwatantawa,
Gas ta kunna ta dora indomie domin ba zata iya yin dogon girki ba gashi kuma kawai tsintar kanta tayi da son cin indomie din.
Guda biyu tadafa kanana tahada da kifin gwangwanin ta zubo a filet ta nufi dakinta har lokacin hajiya Nafi na falon azaune amma kallo daya zaka yi mata ka gane hankalinta atashe yake domin hatta jikinta rawa yake yi kamar mazari,
Dakinta tawuce taje ta zauna tafara zira indomie din data dafa,tana kammalawa ta shige toilet, wanka tayi tafito tazo gaban drewar ta tsaya tafara duba kayan daya dace da tasaka.
*_Ummi A'isha_*๐๐ป
[12/11, 6:24 PM] Ummi A'isha๐๐ป: *RUWAN KASHE GOBARA...!*๐ฅ
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_20_
~~~Wata jar doguwar riga ta ciro yar kanti mai santsi dama can ita ma'abociyar saka dogayen riguna ce shiyasa ma suka fi yawa acikin kayanta,
Gaban mudubi ta karasa tafara kokarin gyara gashin kanta wanda yake kaya guda,
Tana tsaka da taje gashin natane taji alamun bude kofa, juyawa tayi ahankali, kakarta yakumbo tagani wato mahaifiyar abbanta,
Tsayawa yakumbo tayi tana kallonta cikeda tsana da bacin rai wanda hakan ya bayyana karara akan fuskarta,
"Yar gadon masifa da jaraba da bala'i ashe sai da kika dawo gidan nan? Ai mu tuni muka manta dake saboda munyi tunanin kin dade alahira ashe kina nan araye, yayi kyau idan kin san wata ai baki san wata ba, jarababbiya mai nacin bala'i indai nice wallahi sai naga bayanku keda munafukar uwarki"
Sakin baki ikhlas tayi ta tsaya kawai tana kallon yakumbo wacce a haife yanzu zata kai kimanin shekaru 70 aduniya koma harda doriya,
Kafin ta ankara tuni har yakumbo ta bude kofar dakin tafice tana huci,
Gaban gadonta ta karasa taje ta zauna agefen gadon tana jin wani irin jiri,
Hawayene suka shiga kai komo akan kumatunta, kuka tafara mai cin rai wanda ya kasance aikinta akoda yaushe domin abubuwa biyu take yiwa kukan, nafarko halin data tsinci kanta tun tasowarta sai kuma martabarta data rasa a matsayinta na 'ya mace budurwa wacce bata taba aure ba,
Tadade tana risgar kuka har na tsawon wani lokaci kafin daga bisani ta mike tana mai jin wani irin jiri yana daukarta, daurewa tayi takarasa gaban mirror ta samu ta hade gashin kanta ta tufkeshi wuri daya wanda jelar har saida ta sauko gadon bayanta,
Kan gadon ta koma ta kwanta sakamakon dan zazzabin datafara ji yana shamayarta kamar yadda ya saba.
Karfe 8:30 nadare tana zaune akan abin salla bayan ta idar da sallar isha, hajiya nafi ta shigo cikin dakin tana yan kalle kalle,
"Ikhlas kizo Allah yadawo da mahaifinki"
Tashi tayi batare da tayi magana ba tabi bayan hajiya Nafi domin ita bata san inane dakin abban nata ba,
Ta wani dan lungu taga sunbi har suka isa sashen mahaifin nata, yana zaune shida mahaifiyarshi, ido ya zuba mata lokacin da suka shiga falon,
Kusa dashi ta karasa ta zauna tana jin kamar taje ta rungume shi,
"Ikhlas" mahaifinta yakira sunanta cikin rawar murya tamkar zai saka kuka,
"Na'am abba" ta amsa masa tana kwalla,
"Ikhlas yanzu kin kyauta kenan? Tsawon shekarun nan kina ina?"
Dagowa tayi ta kalleshi tana hawaye "wallahi Abba ina yola can Adamawa state,ban san menene yakaini can ba, nidai kawai tsintar kaina nayi acan ahannun wani lawyer, shine yakaini asibiti yabani dukkan taimakon daya dace har zuwa yau da ya sakoni a mota domin dawowa gida"
Hawayene ya gangaro daga idon mahaifinta saboda tsananin tausayinta,
"Ikhlas dama tabin hankali kikayi? Hauka? Ikhlas hauka fa? Innalillahi, hakika godiya ta tabbata ga Allah wanda yabaki lafiya...!"
Shiru yayi sakamakon katse shi da yakumbo tayi,
"Ya isa haka, wai kai yanzu har ka yarda da wannan tatsoniyar da wannan yarinyar tazo ta shirya maka? Yarinyar da dakanta ta dauki sawunta tafice daga gida tace ta tafi yawon duniya amma yanzu dan ta dawo shine har kake kuka kana murna?"
"Nima dai haka nagani yakumbo" hajiya Nafi ta fada cikin makirci,
"Yarinyar nan fa ita da bakinta tace min duniya zata shiga babu irin bada bakin da banyi mata ba amma taki, sai yanzu da taje tagama barewa duniya gyada ta cinye ta sheka ta Sheka taga babu tsaba sannan zata dawo gida,to wlhi bari kiji, kinyi asara kuma kin bata sunanki Dana uwarki aduniya domin ni baki bata sunan dana ba munafuka mai bakin halin tsiya"
"Yakumbo dan Allah abar maganar nan haka ya isa"
"Iye! Dakyau mai 'ya,yanzu amadu ni kake fadawa haka akan yarka? Yayi kyau"
Mikewa yakumbo tayi tana kallon hajiya Nafi " 'yarnan tashi mu tafi kinji, tashi"
Tashi itama hajiya nafin tayi tabi bayanta suka fice,
Binsu da kallo kawai ikhlas take cikeda mamakin makirci irin nasu kodan bai kamata tayi mamaki ba tunda dama tasan hali,
Juyowa mahaifinta yayi yana kallonta cikeda soda kauna irinta uba da 'ya,
"Ikhlas labarin da kika bani gaskiya ne Kodai akwai kuskure aciki?"
Girgiza kai tayi har lokacin hawaye ne ke zuba daga idonta,
"Wallahi Abba dagaske nake babu karya acikin maganar dana sanar dakai, shi kansa lawyer din da ya taimaka min ma inada number wayarshi zan baka ka kirashi kaji"
Girgiza kai yayi "nayarda dake 'yata ubangiji Allah yayi miki albarka yaci gaba da tsareki"
"Amin abba" ta amsa tana mai share hawayen fuskarta.
0 comments:
Post a Comment